Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

MAKOTAN JUNA CHAPTER 3

MAKOTAN JUNA CHAPTER 3

- - Post a Comment
MAKOTAN JUNA

CHAPTER 3

Wani irin dum dum kunnen Mommy Hauwa keyi mata taji kamar suma tayi na wucin gadi sakamakon d'aukewar da Numfashinta ke yi babu abinda ke yawo a kunnenta sama da "Allah ya isa"da Zara tace mata

Jikinta kuwa kamar wacce aka sakawa electric shock sabida k'ark'arwar da yake yi kallon Zara kawai take yi dake Jan duwawu ta nufi wajen da wayarta ke yashe ta d'auka still tana Jan Duwawu ta nufi hanyar waje sai kuka take tana Jan majina tana zuba mata harara

Mommy Hauwa k'ark'arwar da jikinta keyi ne yasa ta k'asa motsawa daga inda take wani irin dunkulellen abune ya toshe mata makogaro zuciyarta kuwa kamar an cinna mata wuta
1

Runtse idonta kawai ta yi tana tuno 'yar data raini a cikinta tsawon wata Tara bacci Mara dadi tashi da mik'ewa sai da dabara wani zubin abinci bazai ciwu ba sabida amai

Ta kwana biyu a asibiti tana nakuda dan halin da take ciki har tana iya jiyo k'amshin lahira tazo ta haihu dak'yar Raino da wahala wani zubin bata isa tayi bacci ba sabida rigima haka zata tashi zaune rarrashi kashi fitsari itace duk wanan wahalar da ta sha a yau itace Wanan 'ya zata yiwa Allah ya isa banda zaginta da tayi

Duk bak'ar wahala da take sha da wulak'anci iri irin da Dr yake mata tun aurensu tana shanyewa ne kawai sabida 'ya'yanta tana gudun ta bar gidan ya Auro wata tazo taci zallin 'ya'yanta amma sai gashi wai akan fad'awa 'yarta gaskiya tace mata Allah ya isa tafisan mahaifinta akanta"

Zuwa wanan lokacin Mommy Hauwa wasu hawayen da kamar an kunna famfo ya fara zubo mata kanta sai juyawa yake

Bud'e idonta tayi da sauri a lokacin da aka b'anko k'ofar d'akin

Dr ne a tsaye sai huci yake Zara tana daga bayansa sai share Hawaye take tana girgiza jiki irin ta samo Wanda zai zo ya rama mata d'inan.

"Ke wacce irin Mahaukaciya ce zaki samu 'yar yarinya ki mata mugun duka har ya kai ki da ki tsitsige mata gashi ke uban waye ya dakeki da zaki mata irin wanan dukan uban mai ta miki haka" 3

Tunda Ya fara Magana Mommy Hauwa ta kama lebb'enta na k'asa ta dartsa hakoranta a ciki bata damu da lumewa da hakoranta sukayi ba jini ya fara zubowa dan da k'arfi ta danna hakoranta jikinta na wani irin k'ark'arwa tana kallon Dr da Zara dake tsaye

Dr kuwa ganin yanayin da take ciki yasa ya fara slow da fad'an da yake dan tunda ya Aureta bai tab'a ganinta a irin wanan halin ba

Mommy Hauwa kuwa d'aurewa tayi ta mik'e duk da jirin dake d'ibanta still tana cige da lebb'enta idonan nata jajawur kamar an diga jini ta nufi wajen da suke a tsaye

STORY CONTINUES BELOW


Zara gyara tsayuwarta tayi dan duk a tunaninta idan wani dukan zata k'ara mata Dr zai shigar mata

Dr kuma haka kawai wani d'an tsoro ya shige shi dan a dake ta taho wajensa babu wannan alamar tsoro da girmama shin da take a tattare da ita

Sai da ta tsaya agaban Dr tace Cikin wani irin murya numfashinta Na sama da k'asa "kazo ka rama mata ne"?

Dr wani yawu ya had'iye ya k'asa magana dan ya hango wani k'wantacen bak'inciki da tafasar zuciya a idon Mommy Hauwa

" Karka damu ka dakeni dama tace min zata kiraka ka rama dukan dana mata ka rama mata ka tafi"

Tace tana k'ara matsawa kusa da Dr.

For the first time Dr yaji jikinsa yayi sanyi ya fara tunanin abinda yake yiwa Mommy Hauwa bai dace ba ko ayanayin da ya ganta kawai yanzu yasa yaji jikinsa ya k'ara sanyi dan gwara ta ware murya tayi ta ihu zata ji sa'eda a ranta akan shirun nan da tayi bak'inciki na cinyeta

Mommy Hauwa ganin Dr ya zura mata ido ya k'asa magana ne yasa ta Juya ta kalli Zara dake girgije girgije tana jin Haushin Dr na k'in dukan Mommy Hauwa tun dazu. 1

"Daddynki ya k'asa rama miki Zara kizo ki rama dukan Dana miki da kanki ki matso ki rama dukan Dana miki Zara"

Zuwa wanan lokacin wanan dunkulellen abun dake makogaron Mommy Hauwa ya narke take Hawaye suka ya hau bulbulowa yana diga a k'asa

Zara harare harare ta cigaba da yi a lokacin da Mommy Hauwa ke kallonta ko ina na jikinta na rawa

Gaban zaran taje ta tsaya ta cakumo wuyar rigarta tana

"Zara ki dakeni nace nasan bani na haifeki ba Zara Zara mai kike jira tunda zu ki rufeni da duka nace Zara wai akan ina gaya miki gaskiya kike min Allah ya isa Zara ni Dana tsugunna na haifeki kikewa Allah ya isa Zara duka ya rage kawai kiyimin ki dakeni nace"

Mommy Hauwa tace Cikin wani irin yanayi tana girgizata

Dr jikinsa ne yayi sanyi a lokacin da yaga Mommy Hauwa ta zube agaban Zara tana ta kuka kamar ranta zai fita

D'aurewa yayi yace "wai mai yake faruwane Zara mai kika mata haka"?

Zara k'asa magana tayi sai girgije girgije take yi

"Ba tambayarki nake ba kika min shiru dan ubanki mai kika mata haka take kuka"?

Dr yace a tsawace

" Allah ya isa tayimin Dr dan ina mata nasiha akan ta koma gidanta Zagina tayi tace ta tsaneni tafi sanka akaina Dr 'yar dana tsugunna na Haifa ce yau take min Allah ya isa akan ina k'ok'arin ceto ta daga halaka ina nusar da ita hanyar daka d'orata akai ba hanya bace mai kyau  domin Goya mata baya da kayi yasa take kula wani da Aurenta"

Dr ware ido yayi yana kallon Zaran da take ta zubawa Mommy Hauwa harara tunda ta fara magana 

"Zaraaaa dagaske mahaifiyarki take kula wani kike da Aurenki? kina da hankali kuwa da Auren naki kike huld'a da wani namijin"?

Zara tsoro ne ya d'an shigeta ta fara ja da baya dan Dr bai tab'a mata ko da kallon banza ba ballantana akai ga tsawa.

Dr jawota yayi ya fara dukanta yana " dan bakida mutunci mahaifiyarki kike yiwa Allah ya isa dan tana  gaya miki gaskiya.

Zara ihu kawai take suna guje guje dashi tana ganin ta nufi hanyar fita daga d'akin ta juyo tana "Allah isa ban yafe maka ba bak'in mugu azzalumi wlh sai na bar muku gidan kai da Mommy bana sanku. 2

Tunda ta Zara ta fara magana Dr  yaji kamar guduma take kwad'a masa kirjinsa kuwa  sai dukan goma goma yake kunnensa kawai repeating d'in kalmomin Zara yake  kansa na  i wani irin  juyawa.
1

STORY CONTINUES BELOW


K'afafunsa gaza d'aukarsa sukayi har sai da ya kai shi  ga zubewa a k'asa zuciyarsa na wani irin harbawa.

Mommy Hauwa itama ta tuni kukanta ya  tsaya cak dan bata tab'a tunanin Zara zata iya furtawa mahaifinta haka ba shi da baya San laifinta yake Goya mata baya a duk abinda tayi.Dr ta kalla da jikinsa ke wani irin rawa gumi na keto masa idanan nasa jawur kamar garwashi.

Babu abinda yake furtawa sai 
"Innalillahi wa inna ialhi rajiun" dan ko a mafarki bai tab'a tunanin 'yar daya  Haifa zata iya zaginsa ba.

Hawaye ne suka hau zubo masa yana girgiza kai wanan shine karo na farko da tsananin nadama ya rufesa sai ayanzu ya gano illar freedom d'in da ya bawa 'ya'yansa suke abinda suke so baya San ganin laifinsu ko kad'an 4

Mommy Hauwa kuwa girgiza kai tayi Cikin takaici Cikin raunaniyar murya tace

"Dr kaga irin tarbiyyar da kayiwa 'ya'yanka ko?ka ga sakamakon irin sangarta da  gatan da kake cewa kana yiwa 'ya'yanka ko? Dr kaga yau Zara 'yar gwal da baka san a tab'a ko afadi laifinta itace ta bud'e baki ta maka Allah ya isa tace maka Bak'in azzalumi mugu dama nasha  gaya maka  akwai lokacin da zaka zo kayi dana sanin sangarta yaran nan  da kayi nasha  gaya maka hanyar daka d'ora yaranan  ba hanya bace mai kyau yau ga 'yar cikinmu Na mana Allah ya isa bata yafe ba"

Dr girgiza kansa kawai yake maganar Zara na masa amsaa kuwaa a kunne  kamar a yanzu Mahaifiyarsa ke cewa yaje zai gani shima 'ya'yansa sai sun sa shi kuka tunda ya zabi 'yan mata akanta tunda ya zabi ya kashewa 'yan mata kudi akan ya bata naira biyar taci abinci bayan irin abubuwan da tayi dan kawai ya kai matakin da yake kai yanzu amma sai gashi amadadin ya kula da ita a lokacin da bata da k'arfi take bukatar taimakonsa a lokacin zai juya mata baya ya ringa yawo da yan mata a gari yana kashe musu kudi.

Wani irin kuka ya fashe dashi daya tuno abinda Mahaifiyarsa tace gashi is too late ballantana ya nemi yafiyarta 
2

Mommy Hauwa kawai kallonsa take tana mamakin abinda ya sa shi kuka haka to mai abun kuka ai bai kamata yayi kuka ba tunda shine silar lalacewar su.
1

Dr mik'ewa yayi dak'yar yana Jan k'afa tare da barin d'akin dan shi kadai yasan abinda yake ji.

Zara kuwa dama tana barin d'akin a guje ta fad'a d'akinsu Sadiq ta kulle da mukulli sai kuka take tana kiran wayar Adnan dan bata so gari ya waye tana Cikin gidanan gwara yazo ya d'auketa 

Khalid da tunda ta shigo yake tambayarta abinda ya faru dan duk dramar nan da akayi bacci yake.

Ko kula shi bata yi ba ta cigaba da gwada wayar Adnan a kashe.

Dr kuwa bai iya k'arasawa d'akinsa ba ya zube akan kujerar Palo take wani irin zazzabi ya rufe shi.
2

A takaice sai da Mommy Hauwa ta tsaya akansa sabida mugun zazzabin da ya kama shi duk magungunan da ta bashi yak'i ya k'arba ya sha sai Hawaye yake yana kiran sunan mahaifiyarsa akan ta yafe masa hakkinta ya fara kama shi.


B'angaren Aliya kuwa  tana iddar da  sallar asuba  bata koma bacci ba sai da tayi breakfast ta d'an gyara gidan ta koma d'aki dan Sam bata San had'uwa da Adnan.

Adnan bacci yayi cike da fargaba dan bai San halin da Zara take ciki ba shima tunda yayi sallar asuba ya kasa komawa bacci yana San ya kunna wayarsa yana tsoro.

Ameer kuwa shima da ya iddar da Sallah bai koma bacci ba sabida dattin da gidan yayi

Gyare gyare ya fara yi dan ya tsani k'azanta a rayuwarsa duk da Zara tana da San jiki baya wani saurararta zagewa yake ya gyara ko'ina ya feshe shi da turare girki ne kawai bai iya ba.

STORY CONTINUES BELOW


Zara kuwa ko sau d'aya bacci bai d'auketa ba dan tsananin tashin hankali da fargaba da take ciki ta lek'a Palo ya kai sau goma dan taga ko Dr da dake rawar d'ari da  Mommy Hauwa dake  gefensa na mishi sannu sun tashi sun bar Palon amma ina suna nan a palon.

Burinta bai wuce ta bar gidan ba dan bazata sake tsayawa a tab'a lafiyarta ba tunda Dr shima yanzu ya fara dukanta ga zagin da ta mishi har gwara ma ta koma gidan Ameer ta samawa kanta mafita akan ta cigaba da zaman gidan.

A lokacin da khaleed yazo fita massallaci a guje ta nufi band'aki ta kulle dan tana tsoron su biyota su daketa.

Dr kuwa da k'yar yayi sallar asuba kansa kamar ya dare biyu kirjinsa    wani irin nauyi yayi masa   yana so yayiwa   Mommy Hauwa magana amma ya k'asa sabida nauyin da harshensa ya masa.

Mommy Hauwa kuwa kuka kawai take data ga Halin da Dr ke ciki dan bata tab'a tunanin dan Zara ta masa haka zai shiga irin wanan tashin hankalin ba sadiq da Abdulsalam dake shaye shaye suna biye biyen 'yan mata bai damu ba ballantana ya d'aga hankalinsa Sai gashi akan Zara ya tashi hankalinsa ko dan acikin 'ya'yansa yafi Santa ne oho.

Har k'arfe takwas na Safe Dr na kwance baya iya motsi sai Hawaye dake fita ta gefen idonsa

Mommy Hauwa kuwa Sai Sannu take mishi 

Mik'ewa yayi a hankali ya zauna Mommy Hauwa tayi sauri ta taimaka mishi 

Bud'e bakinsa yayi da k'yar yace "ina Zara"?

Mommy Hauwa Sai da ta share hawayenta tace " tana d'akinsu Sadiq"

Bai ce komai ba ya mik'e yana cije lebb'e sabida nauyin da kansa ya masa 

D'akinsu Sadeeq d'in ya nufa yana Jan k'afa

Mommy Hauwa tayi sauri ta sha gabansa ta fara basa hakuri akan ya rabu da ita taje duniya ce itama zata Haifa ai

Dr ko kulata bai yi ba ya cigaba da Jan k'afarsa

Mommy Hauwa kuwa ta cigaba da masa magiya dan ta d'auka zuwa zaiyi ya daki Zara.

Zara dan bata Dade da lek'asu ba tana zaune akan gado ta buga tagumi tana tunanin yanda zata bar gidan dan har yanzu tana gwada wayar Adnan a kashe 

Mik'ewa tayi da  sauri a lokacin da su ka shigo d'akin zata gudu

Dr Cikin k'arfin hali da sauran kuzarin da ya rage masa ya daka mata tsawa yana "dakata kike sake kikayi taku d'aya Sai na kasheki da hannuna"

Zara cak ta tsaya jikinta na wani irin k'yarma  har Dr ya k'araso wajen data tsaya 

Mommy Hauwa kuwa tunda taji Dr yace zai kasheta da hannunsa itama jikinta ya fara mugun rawa gabanta na fad'uwa

Sai da ya share Hawayen da ya zubo masa ya kalleta yace "Zara ni kikewa Allah isa nine bak'in mugu azzalumi Zara ni mahaifinki kika zaga"

Cije lebb'ensa yayi wasu sababin hawayen na zubo masa

Zara kuwa sunkuyar da kanta tayi babu wani alamar nadama a tattare da ita sai tsoron kar a tab'a lafiyarta dan da akwai hali sai tace eee d'in ta fad'a 1

Dr sai da ya samu minti biyar bai iya ce komai ba sabida Jan numfashin da yake yi dak'yar

"Daga yau karki k'ara taka k'afarki kizo min Cikin gida na yafeki a Cikin 'ya'yana kije duniya ce ta isheki Riga da wando har da zanin d'aurawa"
1

Mommy Hauwa ido kawai ta gwallo tana kallon Dr

D'aurewa tayi tace "Dr kalaman nan sun mata tsauri kayi hakuri ka nema mata shiriya a wajen Allah"

Dr ko juyawa bai ba ya kalli Mommy Hauwa yace "karki k'ara minti biyar a gidanan"

Daga haka ya juya ya nufi hanyar fita

Mommy Hauwa tayi sauri tabi bayansa tana "Dr idan ka koreta ina zataje"?

" idan Kinga dama zaki iya maidata gidan mijinta  idan kuma bazaki iya ba kibarta ta shiga duniya"

Dr yace yana nufar d'akinsa dan idan ya cigaba da magana numfashinsa zai iya d'aukewa 

Ajiyar zuciya Mommy Hauwa ta sauke tana "Allah ka shirya mana zuria"

Daga haka ta nufi d'aki ta sako Hijabinta ta koma d'akinsu Sadiq

Zara tana nan a tsaye a inda suka barta 

Cikin d'aurewar fuska tace "kifito na maidaki gidan mijinki idan kuma kin gwammace ki shiga duniya to gaki gata Allah ya baki sa'a yanzu ma zaki iya zagina idan zagi ya miki kad'an ki dakeni".

Daga haka ta juya ta bar d'akin.

Zara tana ganin ta fita ta ja tsaki tana " ai da inada halin wlh da sai na dakeku amma ba komai dan ni na kwaso k'afata nazo wanan mitsayacin gidan naku ba sai kun k'ara ganina ba zaku tab'a lafiyata" 1

Itama Cikin minti biyu ta fito da shirinta dan jinta take kamar akan k'aya fuskarnan tata a murtuk'e.

Mommy Hauwa kuwa Allahuma ya hadiki kawai take cewa a zuciyarta.

Adai daita sahu Mommy Hauwa ta tare musu babu Wanda yace da wani uffan.

Mommy Hauwa ta fad'a musu inda zai kaisu.

Tafiyar minti goma sha biyar ya k'ara so dasu gidan a lokacin Tara da rabi.

Zara ce agaba Mommy Hauwa abaya

Zara tana tura gate d'in kamar had'in baki

Adnan ya fito daga b'angarensu da shigar sa ta kananan kaya yayi masifar kyau 

Ameer shima ya fito daga nasu b'angaren sanye da manyan kaya kayan kuwa sun masifar amsar shi.

Zara tuni ta manta da halin da take ciki sakamakon taga sanyin idaniyarta ta gayyato wani irin murmushi a fuskarta tana yaba kyaun da Adnan yayi a zuciyarta ko d'auke idonta ta k'asa yi.

Adnan kuwa kallo d'aya yayi mata yayi sauri ya d'auke kansa gabansa na d'an fad'uwa dan haka kawai yake tsoron Ameer aransa kuma yana mamakin yanda akayi aka dawo da Zara.

Ameer kuwa kallon da Zara ke bin Adnan da shi har tana Neman bangaje shine yasa ya kalli inda take kallo yaga Adnan dake k'ok'arin bud'e motarsa ya shiga take kallo haka.

Wani irin bak'inciki da takaici ne suka rufe shi adai-dai lokacin da ta bangajeshin sabida bata kallon gabanta

Tureta yayi yace "ballagaza kawai Mara kamun kai sai kibi shi ai"

Daga haka ya ratsa ta gefenta ya k'arasa wajen Mommy Hauwa da gwiwarta ya sage sabida wanan Abu da Zara tayi dan tunda suka shigo taga abinda Zara keyi kamar zata lashe  Adnan.

Aliya da Adnan na fita daga gidan ta fito da gudu daga d'akinta tazo ta tsaya daga bakin window dan taga tafiyarsa.

Mamakine ya rufeta data ga abinda ke faruwa take numfashinta ya fara fita da sauri da sauri data ga irin kallon so da kauna da Zara ke bin Adnan dashi Wanda har ta k'asa d'auke idonta sai data bamgaje mijinta..

Zara kuwa a fusace ta fara yiwa Ameer rashin kunya tana ita ba ballagaza bace yaje ya nemo ballagaza daga haka taja ta tsaya tana girgize girgize tana jiran yazo ya bud'e k'ofar ta shige k'asan zuciyarta kuwa ta  matsu ta kebb'e ta kira Adnan......Ameer kallonta kawai yake zuciyarsa na tafasa Wanda b'acin ran  hakan ya Gaza b'oyuwa a fuskarsa ahaka Mommy Hauwa ta k'araso ta samesu 
3

Ameer ya shanye b'acin ransa tare da tsugunnawa ya gaisheta.

A sanyaye ta amsa gaisuwar tashi tace mishi yayi hakuri ya bud'e k'ofar su Shiga daga ciki.

Ameer bud'e k'ofar yayi Zara tayi sauri ta shige bayan ta gama harare su biyun.

Ameer mamakine ya rufeshi dayaga har da Mommy Hauwa ta had'a ta harara

Bata tsaya a palon ba ta wuce d'aki


Ameer kuwa yayiwa Mommy Hauwa iso har kan kujera ta samu guri ta zauna.

Gaisawa suka k'arayi sai da Mommy Hauwa ta sauke ajiyar zuciya ta fara magana.

"Ameer bazan gaji da baka hakuri ba akan abubuwan da Zara take maka  Yarone ka haifeshi baka haifi Halinsa ba wlh bansan inda Zara ta kwaso wanan dabiun nata ba babu ranar da zata fito ta fad'i ban yi musu addu'a ba akan Allah ya shirya min su yanzu Zara bata da gidan da ya wuce gidanan Kaine uwarta Kaine ubanta anan  Dan Allah dan annabi Ameer ka cigaba da hakuri da Zara kana tayata addua a matsayinka na mijinta insha Allah zata shiryu nasan kana hakuri da ita ka k'ara wani hakurin dan ko mu iyayenta bata barmu ba icce tun yana d'anye ake lank'wasa shi bata lank'wasu ba tun tana yarinya kaga kuwa sai a hankali insha Allah zata gyara halayenta nima Ina daga gida zan ringa binta da addu'ar Allah ya shiryeta ka ringa kai zuciyarka nesa idan tayi ma ba dai-dai ba idan zan samu ne dan Allah ko islamiyya ne ka sama mata ta ringa zuwa". 2

Tunda ta fara magana Ameer ya sunkuyar dakansa k'asa sai da ta gama magana ya d'ago tare da sauke ajiyar zuciya haka kawai yaji yana bala'in jin nauyin Mommy Hauwa amma idan ba haka ba wlh babu abinda zai hana ya bata takardata yana jin tausayinta dan muryarta rawa yake har ta gama magana.

Cikin sanyin murya shima ya fara cewa

"Insha Allahu Mommy zan ringa hakuri da Zara amma Mommy naso ace kun barta agaban naku ta d'an koyi hankali kafin a dawo da ita Mommy wlh Zara babu abinda take yi a cikin gidanan kullum da b'acin ranta nake kwana a gidanan a matsayina na Mijinta ban isa tayi min girki ba sai dai ta bani cornflakes da madara tace basa cin abinci mai nauyi a gidansu bata bin umarni na  Mommy Aure kana yin shine dan ka samu kwanciyar hankali da nutsuwa amma ni hankalina a tashe yake kullum yaushe zama zai yiwu ahaka fissabilillahi Mommy a gaskiya idan Zara bata canza halinta ba wlh Aure zan k'ara dan dama na gama gini na fenti ya ragemin" 1

Mommy Hauwa da sauri tace "Ameer wlh na baka goyon baya ka karo auren k'ila asanadin Auren da zakayi idan taga yanda kuke zaman Auren da wacce ka auro d'in ta shiryu"

Ameer girgiza kansa yayi yace "to shikenan Mommy ngd da kika goyamin baya"

"Allah ya maka albarka yauwa nace ka k'arbe wayar hannunta idan da hali ka canza mata sabon sim k'ila kawaye ke hure mata kunne idan ka canja mata layi ta rasa contact d'insu zata shiga hankalinta"

STORY CONTINUES BELOW


Mommy Hauwa ta fad'i hakane dan Wanda yake neman Zara da Aurenta ya daina samun layinta bazata iya fitowa ta fad'awa Ameer dalilinta ba.

"Insha Allahu mommy zan canza mata layi dan dama inada niyyar haka dan wani zubin idan ta fara chattn dasu bata iya d'aga kai ta kalleni"

"Hakan yafi gaskiya dan kasan wasu kawayen suna kai mutum ga halaka kirawomin ita zan tafi"

Ameer mik'ewa yayi ya nufi d'akin Zara ya tarar da ita agaban mudubi tana duba fuskarta daya fara d'an sab'ewa daga kumburin da yayi dan ta daku awajen Mommy Hauwa da Dr sai Allah ya isa take musu aranta akan sun canza mata kamani kila shiyasa ma Adnan yana mata kallo d'aya ya d'auke kansa.

Ameer fuska a d'aure yace "sai kifito Mommy tana kiranki zata tafi"

"Kace mata bazan zo ba" 1

Shine Kalmar daya fito daga bakin Zara tana zubawa Ameer harara

Cikin tsananin mamaki da Razanar Kalmar daya fito daga bakin Zara ya saki baki yana kallonta kunnensa na maimaita masa abinda tace ganin ta cigaba da tab'e tab'e a fuskarta yasa ya d'aure ya k'ara cewa

"Kinsan mai nace kuwa Mommy Mahaifiyarki ce tace na kiraki zata tafi"

"Naji sarai ko ba Hauwa kake nufi ba nace kace mata bazan zo ba" 5

"Kin fara shaye shayene Zara kinsan mai kike cewa kuwa Mahaifiyarki nace fa tana kiranki wacce ta tsugunna ta haifeki ita kike cewa naje nace bazaki zo ba har kike kiran sunanta gatsau" 1

"Ai sai kayi tinda uwarka nacewa bazan zo ba nace bazan zo ba ko ana dolene"
1

Ameer bai San lokacin daya lailayo wani ashar ba ya maka yana "Zara Ashe jahilicin naki har akan Mahaifiyarki  kanki d'aya kuwa ko kin fara shaye shayene"?
1

Zara tsaki tayi ta shige band'aki ta barshi a tsaye dan ta gasa jikinta 

Ameer kuwa yafi k'arfin minti biyar atsaye tsananin mamaki ya hana ya motsa

Sai da yaji Mommy Hauwa ta fara k'walla masa kira yaja k'afarsa da k'yar ya nufi palon dan har wani gumi ya had'a na kad'uwa da abinda Zara tayi.

Murmushin dayafi kuka ciwo Mommy Hauwa ta sakar masa a lokacin da take mik'ewa tsaye tace muryarta na rawa

" Karka damu Ameer najiyo abinda tace duniya ce Wanda bai zo bama jiranta take Allah ya shiryeta yasa ta gane da wuri kafin lokaci ya kure mata na tafi Ameer kayi hakuri ka kuma cigaba da hakuri da ita abinda tayi yanzu kad'an ne akan Abubuwan da tayi mana nida mahaifinta hannunka baya rub'ewa ka yanke ka 'yar  Allah ya ganar da ita"

Siraran hawayen da suka zubo mata ta share ta nufi hanyar fita daga palon

Ameer da jikinsa ya mutu murus k'asa rakata yayi har ta fice daga palon.

Har yanzu kunnensa basu daina jiyo masa abinda Zara tace ba astagfurullahi kawai yake nanatawa dan gani yake Zara babban zunubi ta aikata 

Akan kujera ya zube yana  so yayi tunani amma kwakwalwarsa ta cushe bai tab'a tunanin rashin hankali da Jahilcin Zara ya kai haka ba har ta iya bud'ar baki ta zagi mahaifiyarta wai ya akayi yaje ya Aure mace irin Zara ?"Kaddara" yaji ya fad'a a fili tabbas kaddara ce idan ba haka ba Zara Sam ba matar Aure bace"

Ya Dade a zaune yana tunanin hukuncin da matakin da zai d'auka akan Zara a k'arshe ya mik'e a fusace ya nufi d'akin Zara yana huci.

Zara kuwa tana fitowa daga wanka ganin ta daina jin motsin su Ameer a palone yasa tayi sauri ta zauna a gefen gado ta fara kiran Adnan 

Tayi mishi miss call wajen biyar bai d'aga ba hankalinta ba k'aramin tashi yayi ba ta cigaba da kiransa awaya ganin bai d'aga ba yasa ta fara mishi text adai-dai lokacin Ameer ya banko k'ofar

STORY CONTINUES BELOW


Zara d'agowa tayi  a firgice Ta maida wayar bayanta tana Zara ido tsoro duk yabi ya cikata 

Ameer kuwa wajenta ya nufa yana zuwa ya kwasheta da Mari kafin tayiwani yunkuri ya k'ara mata wani ya jawo hannunta data maida baya tana b'oye wayar ya murd'e hannun tare da k'wace wayar baiyi wata wata ba ya rotsa wayar da k'asa ya k'ara d'aukar wayar duk da ta fashe ya k'ara makata da k'asa jikinsa sai rawa yake dan ji yake kamar ya shak'e ta har lahira 
2

Sunkuyawa yayi ya d'auki wayar tare da zare Sim d'in yace "Dabba akuya dakikiya ban tab'a sanin cewar ke katuwar jahila bace sai yau abun naki ya wuce daga kaina ya koma kan iyayenki da suka kawoki duniya to bari kiji na fad'a miki wlh wlh bazan jure iskancinki ba nayi mugun Dana sanin aurenki kuma zan gyara miki zama na haramta miki rik'e waya har sai naga kin fara shiga hankalinki"

Daga haka yasa kai ya fice daga d'akin yabar Zara dafe da kumatunta tashin hankalinta bai wuce wayarta daya rotsa ba ya zare mata sim yanzu da wane waya zata kira Adnan gashi bata rik'e lambarsa ba kukan bak'inciki ta fashe dashi tana tunanin yanda zata samu number Adnan.

Ameer kuwa yana fitowa ya kakarya layin ya zubar ya koma ya canza kayan jikinsa ya fice daga gidan yana tunanin lokaci yayi da zai fara neman Aure ko da ba Auren so zai yi ba dan ya bala'in tsanar Zara albarkacin Mommy Hauwa kawai takeci.

Adnan kuwa yana kallon kiran Zara yak'i dagawa dan duk a tunaninsa Ameer ke kiransa ta layin dan kila ya gano lambarsa awayar Zara a mutuk'ar tsorace yake inda yake tunanin sai ya canza takunsa idan ba haka ba tsaf asirinsa zai tonu dan yaga alamar Zara tana cikin tashin hankali dan yaga yanda fuskarta ya kukumbura kuma yasan ba k'aramin abu ne ya hana  jiya tak'i d'aga wayarsa.

1

Aliya kuwa kanta ne ya d'aure ta kamo wanan tunanin ta saki ta kamo wani zuciyarta nasan diga ayar tambaya akan Zara da Adnan wani b'angare na zuciyarta na hanata dan bai kamata ace Adnan daya San Zara tana tana da Aure ya nemeta ba duk da kad'an da aikin mazinaci amma mai ma'anar kallon da Zara ta ringa bin Adnan dashi dazu?

Kusan haukata kanta tayi da tunane tunane inda a k'arshe taci damara sai inda k'arfinta ya kare zata saka musu ido sosai dan ta gano idan akwai wani Abu a tsakaninsu.

Zara kuwa baccin wahala ne ya kwashe ta sai kusan uku na rana ta farka cikinta sai kug'in yunwa yake aguje ta fito tafara dube dube ko zata samu abunda zata saka abakinta amma ina babu sai dai kayan abinci da indomie.

Indomie ta dafa taci ta fara tunanin ina zata samu aron waya ta kira Adnan ta gaya masa halin da take ciki idan zata samu ne ma ya kama mata haya ta tattara tabar gidan Ameer ta samu yancin kanta da dan ta bala'in tsanar Ameer gashi ba kud'i bane a hannunta ballantana ta saci fita ta siyo koda k'aramar waya ce da Sim dan su ringa communicating da Adnan amma ko da yake tasan dabarar da zatayi zata fita waje ta tsaya har taga dawowar Adnan ta tare shi ta fad'a masa halin da take ciki da wanan tunanin ta saki ranta tare da komawa ta kwanta tana murmushi ita kadai dan haka kawai abinda ya shiga tsakaninta da Adnan ya hau yawo a idonta tana lumshe ido ita kadai ta bala'in missing komai nashi.

1

K'arfe biyar da rabi Zara tayi wanka ta d'anyi kwalliya dan tafita waje taga dawowar Adnan dan tasan yana Riga Ameer dawowa K'arfe shidda yake dawowa wani zubin bakwai.

Ashar ta fara qundumawa data ga Rabin kayanta da take sawa babu su a wadrobe sai manyan kaya da dogwayen riguna da basu wani matseta ba Ashar ta fara lailowa Ameer tana zaginsa kamar yana gabanta sai bambami take tana dube dube amma har ta gama duba kayan bata ga irin Wanda takesan Sawa ba.

Takaici da bak'inciki ne suka bi suka rufe ta kamar ta kamo Ameer ta hau ruwan cikinsa tayi ta dukansa ganin lokaci na ta tafiya yasa ta d'auko wani doguwar rigar atamfa mai d'an dama dama acikin kayan tasaka ta feshe jikinta da turare ta yafa wani k'aramin gyale tafito da sauri ta nufi gate d'in gidan tare da ficewa.

STORY CONTINUES BELOW


Aliya da bata Dade da gama aikace aikacen gidan ba tana cikin turare gidan tana bin labulen palon tana sakinsu taji motsin ana bud'e gate d'in gidan da sauri ta yaye labulen dan taga waye adai dai lokacin Zara ta fice daga gidan

Aliya haka kawai ta tsinci gabanta da fad'uwa da tunanin inda Zara zataje da irin wannan shigar daga dawowarta yau jikinta na rawa ta ajiye kask'on turaren hannunta ta zari Hijabi tayi waje sai data tsaya ta lek'a ta wajen ramin k'ofar aikuwa ta hango Zara a tsaye a tsallaken gidansu ta nad'e hannayenta a kirjinta ta kalli hagu ta kalli dama.

Aliya gyara tsayuwarta tayi ta cigaba da lek'ata dan taga mai take jira sun samu kusan minti Ashirin ahaka daga ita har Zaran, Zara sai kalle kalle take yi Ita kuma Aliya sai tsaki take yi tana tunanin mai nata ma zata zo ta tsaya tana lek'enta.

Gajiya tayi da tsayuwar ta juya da zumar komawa ciki aikuwa ta jiyo k'arar motar Adnan dan ko a mafarki take tasan k'arar motarsa da sauri ta maida idonta ta cikin ramin k'ofar aikuwa ta hango Zara ta d'aga hannuwanta biyu tana tsayar da Adnan.

Gaban Aliya ne yafara dukan uku uku ta k'ara ware ido tana kallon ikon Allah

Adnan kuwa a mutuk'ar tsorace yafara waige waige kafin yayi slow da motar kai kana ganin idonsa kaga katon kwarto 2

Zara da murmushinta ta nufi motar Adnan yayi sauri yafito daga motar yana waige waige yana "ke kinada hankali kuwa ko so kike akama mu bakya tsoro Ameer ya taho yanzu ya ganmu a tsaye"

Zara wani irin rangaji takeyi tana wani farr da idanuwa tana zabga wani irin murmushi kamar zata rungumeshi haka ta tsaya agabansa tana "ka fiye tsoro wlh to sai me dan yaganmu kai nifa babu dan iskan danake tsoro indai akanka ne I miss you" ta k'arshe zancenta tana kashe masa ido d'aya 

Adnan kuwa waige waige kawai yake alamar bashida gaskiya yace cikin sauri "Zara mai haka we are not save at all za'a iya ganinmu a tsaye pls kije anjima zan miki text idan kina free"

"mtsss wane text babu waya a hanunna we have alot to discuss dan Allah ka shiga mota mu tafi wani wajen muje muyi magana tunda naga u are not comfortable tsayuwarmu anan"

Adnan da Sauri yace "kina hauka ne muje ina dan Allah Zara ki rufamin asiri I promise zamuyi magana dan Allah kije kar 'yan unguwa su ganmu a tsaye Ameer zai iya dawowa at any time inya dawo yaga bakya nan fa pls kije idan ya fita gobe zanzo muyi magana"

Zara wani irin narkewa tayi ta langab'ar dakai tana mishi wani irin kallo kamar mai jin bacci a hankali tace " i miss u Ad dan Allah gobe yana fita ka shigo"

Da sauri Adnan ya gyad'a mata kai yana waige waige kafin ya shige mota yaja da sauri tare da nufar gate d'in.

Aliya a 360 ta shige b'angarenta jikinta na wani mugun rawa zuciyarta sai harbawa yake ji take duniyar na juya mata a daddafe ta shige d'akinta ta zube a bak'in k'ofa kamar wacce tayi tsere ta ringa jera ajiyar zuciya.


Sai da Adnan ya shiga da minti biyar Zara itama ta shiga gidan tana wake wake dan wani irin farinciki ke ratsata tunda taga Adnan she really love this guy.

Adnan kuwa yana shiga b'angarensu ya d'aura fuska dan haushin Aliya yake ji shi zai bata hakuri ta cigaba da wani ja mishi Aji yau har ya gama cin abincinsa bai sata a idonsa ba ita tasani su zuba shi da ita ita zata kawo kanta ne  idan ta gaji.

Ameer kuwa da b'acin ran  Zara ya wuni a office ko abinci ya k'asa ci tunani kawai yake matakin da zai d'auka akan Zara ahaka ya wuni a office d'insa zuciyarsa a cunk'ushe ana sallar Magriba ya nufi gidansu dan ya gayawa Mahaifiyarsa halin da yake  ciki ta kuma taimaka ta samo mishi yarinya mai hankali ya Aura.

Sai da ya gama cin dadd'an abincin da Mahaifiyarsa ta jera masa yayi gyatsa da hamdala ya tank'washe k'afafunsa ya kwashe irin zaman da suke yi da Zara ya gaya mata da irin hakurin da yake yi da ita da kuma matakin  dayake tunanin zai d'auka na k'ara Aure.

Mahaifiyarsa Hajiya Ameena sai data Dade tana jimami da al-ajabin halin Zara ta sauke ajiyar zuciya tace "Allah ya shiryeta ta gane gaskiya bakayi dace da mace tagari ba kwata kwata zan tsaya maka kasamu mace ta gari akwai wata Batula  dake k'asan layinmu muna mutunci da mahaifiyarta sosai asanadin haka yarinya tana shigowa wani sa'in mu gaisa har d'an aikace aikace tana tayani na Dade ina sha'awar inama inada wani d'a namiji ya aureta sabida hankali da nutsuwar yarinyar insha Allahu zan yiwa mahaifiyarta magana idan dai ba'ayi mata miji ba sai kaje ka ganta idan tayima"
3

Ameer da sauri "yace insha Allahu ma ba'ayi mata miji ba idan tayi miki nima tayamin Allah ya zaba mana abinda yafi alheri jibi ma za'a fara fentin gidana dan wancan d'in a takure nake"

"Masha Allah Allah ya taimaka"

"Ameen Ameen"

Hira suka cigaba da yi da ita inda Rabin hirar na Batula ne duk da Ameer bai ganta ba jiyake duk muninta zai iya Aurenta sai wajen sha d'ayan dare ya dawo gida ko kallon k'ofar d'akin Zara bai yi ba yayi shigewarsa d'aki dan ya riga da ya cika cikinsa.......Aliya aranar tamkar mahaukaciya haka ta zama dan ko kuka ta k'asa yi ko yaya ta juya Sai ta ga yanda Adnan ke juye juyen rashin gaskiya ta kuma hango irin kallon so da sha'awa da Zara kebin Adnan da shi bata tab'a tunanin Adnan rashin tsoran Allahnsa ya kai haka ba  ya iya Neman matar mak'ocinsa wanan wane irin masifa ne tun yaushe suka fara soyayya ba tare da ta sani ba +

babu shakka gidan da Zara taje Adnan yaje suka had'u har taji k'amshin turarenta a jikinsa da shattin Jan bakinta.

Aliya bata tab'a sanin Kuka rahama bane sai Aranar dan wani abune ya tsaya mata a kirji da mak'ogaro babu abinda take yi Sai juyi tana hasko yanda taga Adnan da Zara dazu.

Sai da ta Dade a matsanacin hali tare da tafasar zuciya kafin abin da ya tokareta a kirji yafara narkewa Hawaye suka hau zubo mata.

Aliya tayi kuka idonta har wani Zafi yake

Tana  tausayin kanta dan babu mummunan jarrabta daya wuce Allah ya jarrabceka da Mazinaci Wanda bai San hakkin mak'otaka ba bai dubi darajar mak'otaka ba babu tsoron Allah a ransa ya iya muamalla da matar Aure ina Adnan zai kai wanan zunubin ga k'eta had'in Aure ga na mak'otaka bata wani ga laifin Zara ba dan can asali bata da kamun kai babu abinda bazata iya aikatawa ba

Adnan fa yasan Zara tana da Aure matar mak'ocinsa  ce amma ya iya huld'a da ita wanan wane irin bala'i ne dame ta ragi Adnan  da zai ringa Neman mata banza awaje ciki kuwa har Da matar Aure dame Zara tafita tayi tunanin Duniya taga abinda take mishi da har  bata iya gamsar dashi amma Ina bata gano abinda take mishi ba.

Aliya tayi kuka kamar hawayenta zasu k'afe Wanda sabida kuka da tunani kanta ya ringa wani irin ciwo ko sallah ta kasayi sabida tashin hankali da rashin  nutsuwa.

Adnan kuwa bai waiwayi d'akin Aliya ba duk da yana jiyo sheshek'ar kukanta tab'e baki yayi yace ita tasani yana zaune zata kawo kanta amma idan shi take jira ya bita d'akinta ya bata hakuri zata shekara duk da yana tsananin bukatar ta abincin da ta dafa ya take a cikinsa yayi gyatsa ya koma d'akinsa yayi wanka ya shirya ya k'ara ficewa daga gidan dan yana bala'in bukatar mace zai fita ya zab'a a cikin 'yan good evening masu tsayawa a bakin titi suna jiran masu tayasu at least ya rage zafi kafin ya samu Zahra.

Zarah  kuwa juye juye kawai take tana Allah Allah gari ya waye Ameer ya fice daga gidan Adnan yazo dan tana San kasancewa tare dashi ta kurmance akan Adnan ta makance bata sha'awar zama da Ameer ko k'adan bata da burin da ya wuce ya saketa ta Auri Adnan.

Washegari da sassafe Ameer ya shirya ya bar gidan dan baya San abinda zai ringa had'ashi da Zara ko kad'an  dan tsanarta link'uwa yake aransa a duk lokacin da ya tuna irin rashin Kunyar da tayiwa Mommy Hauwa.

Zara tana jin Fitarsa taji kamar ta buga tsalle ta taka rawa dan mafarkai kawai take da Adnan abun shaidan wani mugun sha'awarsa takeji  Yanda take ji indai ta samu Adnan ya shigo gaskiya sai ya kashe mata k'ishin dake damunta.

STORY CONTINUES BELOW


Adnan kuwa bashi ya koma gida ba sai k'arfe hud'u na asuba dan bacci ne ya d'auke shi daya biya bukatarsa da karuwar da ya d'auko suka yad'a zango a  hotel itama sai da ya mata rashin mutunci dan ba duka kud'in data bukata ya bata ba a fad'arsa ta yaudareshi itama Surarta ciko ne ga nankarwa ko ta ina ahaka yafito ya barta tana jera mishi Allah ya isa.

Aliya tana jin lokacin da ya dawo gidan hawaye ya k'ara wanke mata fuska bata tab'a nadamar Auren Adnan irin yau ba da tasani bata  biyewa san zuciyarta ta Auri Wanda takeso ba da ta Auri  Muktar saurayinta mai bala'in santa ya za'ayi ta cigaba da Zama da Adnan ahaka idan ya kwaso cuta  ya sa mata fa gaskiya da sake bazata iya cigaba da zama da mazinaci ba daga haka ta mik'e ta fara had'a kayanta.

A cikin k'aramin akwatinta ta had'a kayanta ta koma ta kwanta tana jiran gari ya waye ta fice daga gidan duk da zazzabi da ciwon kai da ke Neman sumar da ita ajiyar Zuciya kawai take saukewa sabida kukan da ta sha.

Adnan kuwa yana shiga d'aki yayi wanka ya d'aura alwala sai da yayi sallar asuba ya koma kan gado ya kwanta dan ba laifi ya d'an Samu nutsuwa jiya ko kad'an bayi tunanin ya duba Aliya yaga halin da take ciki.

Bacci ne yayi awon gaba dashi sai wajen 8 na safe  yunwa ta farkar dashi mik'ewa yayi yana hamma tare da nufar k'ofar fita

A dai-dai lokacin da Aliya itama ta fito jikinta sanye da doguwar Riga da dogon Hijabi idon nan nata kamar an watsa borkono tana janye da k'aramin akwatinta.

Adnan da ya d'auki hanyar dinning dan duk a tunaninsa ta gama breakfast kamar yanda ta Saba cak ya tsaya yana kallon Aliya data fito da akwati tana nufar k'ofar fita daga palon ba tare da ta juyo ta kalleshi ba.

Tana dab da fita yace "Ke Aliya gidan uban wa zakije da Wanan akwatin hannun naki"

Aliya ko kula shi batayi ba ta fice daga palon  zuciyarta na k'una

Adnan har yayi taku biyu zai bi bayanta yaji akan me zata tafi gidansu da kaya har a akwati ya fasa   wani zuciyar na ingiza shi akan ya rabu da ita uban me yayi mata banda kishin balai irin nata daga ganin Jan baki a rigarsa zata bi ta d'agawa kanta hankali duk da ya bata hakuri tak'i ta hakura idan ma yaji tayi take tunanin zai je bikonta tayi karya Yanda ta bar gidan da kanta ita zata dawo da kanta tunda bashi yace ta tafi gida ba.

Yana tsaye a bakin window yana kallon Aliya dake ta share hawaye har ta fice daga gidan yaja wani dogon tsaki yana "Allah ya raka taki gona nama sakata in wala idan kin gaji zaki dawo da k'afarki" 1

Aliya kuwa duk a tunaninta Adnan zai zo ya sha gabanta ya rungumeta ya nuna mata tsantsar nadamar da yayi akan abinda ya aikata ya bata hakuri ita kuma ta nuna mishi illar abubuwan da yake yi da kuma tarin zunubin da yake kwasarwa kansa na huld'a da matar Aure sai gashi ko ajikinsa ya barta ta tafi mai amfanin zama da Wanda baya kaunarka mai amfanin zama da wanda bai San darajarka ba

bai damu da damuwarka ba ko da mutuwa kayi babu abinda ya dameshi Adnan hasali ma ganinta da yake yi tamkar ta takura masa ne

Aliya tafe take abakin titi tana surutai ita kad'ai hawaye na zuba a fuskarta sai da tayi tafiya mai d'an banzan Nisan dan da a hayyacinta take bata isa tayi wanan tafiyar ba

sai da wata mata ta tsayar da ita tana ta cewa  "baiwar Allah mai yayi zafi haka kina tafe kina kuka komai yayi tsanani maganinsa Allah"

Kallon matar kawai tayi bata iya ce mata komai ba kawai ta ciri hannu ta tsayar da tricycle ta fad'a mishi inda zai kaita dan tama  kusa isa unguwar tasu a k'afa ba tare da tasani ba.

Zara kuwa motsin bud'e gate d'in gidan yasa ta mik'e da sauri ta lek'a ta window taga Zara ce ta fice da uban akwati a hannunta

Zara wani uban tsalle ta daka murna fal cikinta dan tasan kila fad'a Aliya da Adnan sukayi shine tayi yaji dama Aliya ta tsaya mata a hanci

STORY CONTINUES BELOW


Fitowa tayi da sauri taje ta kulle gate d'in gidan data ga daga ita sai Adnan acikin gidan ta koma b'angarenta da sauri dan tayi wanka ta shek'a kwalliyar da zata tafi da imanin Adnan.

Cikin minti goma tayi wanka tayi kwalliya ta saka wani doguwar Riga da ya bayyana ko ina na jikinta tazo tayi wanka da turare ta jefa cingum abakinta ta nufi b'angarensu Adnan dan gani take yana b'ata mata lokaci tunda har yanzu bai shigo ba kamar Yanda ya alkawarta.

Adnan kuwa yana ganin Aliya ta fice ya nufi kitchen dan ya had'a  shayi ya sha  bazai iya tsayawa dafa indomie ba
Sabida yunwa dayake ji.

  fitowa yayi Palon  hannunsa d'auke da tea cup d'in shayin d'aya hannunsa kuma d'auke da bread da butter sai da yasha shayin yaji ya koshi.

Ya  k'unna TV tare da kamo tashar da yake masifar so wato Bomb TV dan kad'e  kad'e da Raye Raye kawai ake a tashar tamkar Wanda bashida wani matsala ya ware volume d'in sosai yafara  taka rawa yana juyi shi kad'ai dan shi ma'abocin zuwa club ne Auren Aliya yasa ya daina zuwa yana cikin tikar rawa har yana gumi sabida shayi mai zafin daya sha yaji ana kwankwasa k'ofa

Yana bin wakar ya nufi k'ofar ya bud'e numfashinsa ne ya kusan d'aukewa da yaga Zara a tsaye da sauri ya d'aga wuyansa dan yaga inda Ameer ke parking motarsa yaga baya nan sai a lokacin yayi ajiyar zuciya ya dawo da kallonsa kanta yafara binta da wani irin kallo tundaga sama har k'asa yana wani irin Abu da ido

Zara kuwa ji take kamar ta daka tsalle ta rungume shi dan tsananin so da irin shigar da ta gani a jikin Adnan arayuwarta tana bala'in San namiji yasa 3qtr da Armless kwantacen gashin  dake kirjin Adnan  ta zubawa ido taji wani Abu na tsirga mata tundaga tafin k'afarta har tsakiyar kanta.

Adnan kuwa Hannu ya mik'a mata dan bashida fargabar komai Aliya bata nan Ameer baya nan

Da sauri Zara ta mik'a mishi hannunta ya jawo ta da k'arfi ta fad'a jikinsa ya rufe k'ofar da Hannu d'aya

Har tsakiyar palon ya jata suka tsaya yana binta da wani irin kallo

A hankali yasa Hannunsa ya zagaye k'ugunta ya matso da ita jikinsa ya saka hannunsa d'aya ya rik'e mata hannu ya fara rawa da ita.

Zara da sauri ta fara bin step d'in rawar tana b'angala murmushi dan arayuwarta tana San irin wanan rayuwar ta wayewa Adnan irin Wanda take mafarkin samu ne ya had'u ko ta ina.

A hankali rawar tasu ta fara sauyawa zuwa romance inda su biyun suka rikice suka dakumi juna kamar zasu maida junansu ciki Adnan kuwa ganin Tsayuwa na Neman gagararsu ya sa ya d'auketa cak ya nufi d'akinsa da ita shaidan kuwa ya ringa kad'a musu ganga suna k'ara k'wadaituwa da juna.

Abunka da shedan Zara ji tayi tunda tazo gidan duniya bata tab'a jin dadin da taji da Adnan ba

Adnan kuwa had'in kan da Zara ta bashi ya sarrafata San ran shi yasa yaji bai tab'a gamsuwa da wata 'ya mace tamkar Yanda ya gamsu da Zara ba duk da yasan idan aka zo kan Matarsa Aliya  ita ta dabban ce.

Sai da Zara ta kwashi awa uku a b'angarensu Adnan kafin Adnan ya rok'eta akan ta koma b'angarenta kar ta damu yanzu zasu ringa had'uwa akai akai tunda Aliya tayi Yaji Zai kuma samo mata waya da sim su ringa communicating dan sai da suka gama watsewarsu Zara ta kwashe duk abinda ya faru ta gaya masa

Da k'yar Zara ta bar b'angaren dan bata k'i su Dawwama da Adnan ahaka ba.

Adnan kuwa cike da farinciki yayi wanka ya shirya yabar gidan kafin ya bar gidan sai da Zara ta k'ara fitowa da gudu ta rungume shi suka k'ara wata romance d'in  ta bar shi ya tafi.

Sallati  kawai Hajiya Rukayya ke yi a lokacin da Aliya ta shigo gidan dan gabad'aya a hargitse take cike da fad'uwar gaba ta mik'e dan duk a tunaninta mutuwa Adnan yayi sai da ta Dade tana tambayar Aliya akan abinda ya sameta amma Aliya ta k'asa magana sai kuka take tana rik'e kanta .

STORY CONTINUES BELOW


Hajiya Rukayya
Hannu tasa ta tab'a jikinta taji da zafi zau tana bukatar taimakon gaggawa

da sauri ta fara k'wallawa kanwar Aliya kira Sumayya akan tazo ta kira mata likitan dake k'asan layinsu ya duba mata Aliya.

Sumayya a gigice ta fita waje bata tsaya tambayar abinda ya sameta ba dan kana ganin Aliya kasan tana cikin matsanacin hali

A tak'aice sai da aka yiwa Aliya karin ruwa har dasu allurar bacci sabida tasamu ishasshen bacci

Likita kuwa yana gama treating d'inta yacewa Hajiya Rukayya "A gaskiya 'yarku tana cikin wani Hali a daina d'aga mata hankali a daina bari tana tunani mai zurfi dan asanadin haka ta kamu da hawan jini kuma bai kamata mai juna biyu jininta ya ringa hawa haka ba dan Allah kuringa k'ok'ari kuna hanata yawan tunani bai dace mai juna biyu jininta ya ringa hawa haka ba"

Hajiya Rukayya babu abinda take nanatawa sai hawan jini da juna biyu da aka ce  Aliya na dashi.

Godiya tayi mishi tace insha Allahu zasu kiyayye daga haka Likita yasa kai ya fice daga palon.

Zama tayi a gefen Aliya da duk da bacci take ajiyar zuciya kawai take tabi ta rame ta dashe idonta ya shige ciki.

Hajiya rukayya  tunanin ta fara yi akan  mai zai haddasawa Aliya   hawan jini ga ciki a jikinta wane irin abu ta saka aranta haka

ko dai sakinta Adnan yayi sai a lokacin hankalinta ya kai akan ta kira Adnan ta tambayeshi abinda ke faruwa tunda taga Aliya har da kayanta ta tazo.

A lokacin Adnan yana Zaune a office d'insa sai   juyi yake  akan kujerarsa fuskarsa d'auke da farin cikin cikar burinsa babu abinda ke amsaa kuwa a kunnensa sai ihun da Zara keyi alamar tana jin dadinsa haka yakesan mace arayuwarsa Aliya kuwa ba k'aramin Abu zai mata tayi ihu ba shi kuwa ihun nan k'ara masa k'arfin gwiwa yake yana kuma jin wani k'arfi agaskiya yaji dadin kasancewa da Zara.

Ringing d'in da wayarsa keyi yasa ya daina juyi akan kujerarsa ya d'auko wayar ganin "inlaw" ke kiransa yasa ya tuna da Aliya tana gidansu sai da ya dai-daita kansa ya samo abinda zai cewa Hajiya Rukayya ya d'aga.

Tamkar yana gabanta ya rusuna yana gaisheta cike da ladabi

Hajiya Rukayya amsawa tayi bayan ta tambayeshi aiki da sauransu tace mishi

"Adnan wai mai ke faruwane naga Aliya ta dawo gida da kaya na tambayeta mai ke faruwa tak'i gayamin sai kuka take ga zazzafar zazzabin dake jikinta sai Dana kira likita ya dubata yace tana da hawan jini ga juna biyu mai yake faruwa haka Adnan"?

Tunda Hajiya Rukayya ta ambaci ciki gaban Adnan ya buga da k'arfi dan Sam Ba yanzu ya shirya haihuwa ba sai nan gaba ganin ta k'ara cewa hello yayi sauri yafara magana yana

" Hajiya wlh ni kaina bazan ce miki ga abinda yake damun Aliya ba kwana biyu haka ta tsiri zama a d'aki idan na tambayeta mai yake damunta sai tace min kar na dameta Data ga na tsananta mata tace min ita cikin jikinta ne bataso sai an cire Hajiya nikuma danaji ta ce sai ta cire shine nace mata ni Kuma ban yarda ta ciremin ciki ba shikenan tun daga lokacin na daina gane kanta bata min girki babu abinda ke had'amu sai  harara sai  jiya na dawo daga wajen aiki ina zuwa na ganta a zaune a Palo tana k'ok'arin ta sha maganin zubar da cikin shine nayi sauri na watsar na rufeta da fad'a shine tun jiya daddaren take kuka tana rantsuwa akan sai ta bar min gidana ta tafi gidansu yau da sassafe naga ta fito da kayanta babu irin rok'o da magiyar da ban mata ba akan kar ta tafi amma haka ta tureni tayi ficewarta" 1

Adnan yace yana sauke ajiyar zuciyar irin wanan karyar da ya sharara

Hajiya Rukayya sallati kawai takeyi  da taji abunda Adnan yace dan bil hakki ta yarda da abinda Adnan yace tunda muryarsa har rawa take

Hakuri ta fara bawa Adnan akan yayi hakuri tana farkawa zata taso keyarta ta dawo da ita za kuma tayi mata fad'a

Adnan da sauri yace "Aa Hajiya dan Allah karki mata fad'a kinsan ciki babu abinda baya sawa kibarta ta huta idan an kwana biyu zan zo na d'auketa da kaina inaga cikin ke sata wanan abunda take yi dan Allah kibita ahankali idan fad'an zaki mata ki Bari sai hankalinta ya kwanta sosai"

Hajiya Rukayya girgiza kanta kawai tayi tana sa mishi albarka tace masa nan da kwana uku yazo ya d'auki matarsa

Yace mata insha Allahu zai zo daga haka sukayi sallama Adnan na k'ara sauke ajiyar zuciya yana jinjinawa kansa irin wannan karya daya sharara.

Hajiya Rukayya kuwa duk da bacci Aliya  take ji take kamar ta tasheta ta rufeta da duka sabida irin rashin hankalin da tayi sai fad'a takeyi ita kad'ai.

Da Yamma Adnan ya koma gida sabida ya bawa Zara wayar da ya siyo mata da sim ya kuwa ci sa'a Ameer bai dawo ba lokacin bai sha wahalar shiga b'angarensu Zahra ba aikuwa ta tafi fa gudu ta rungume shi kamar wani mijinta sai da sukayi kiss mai tsayi har Zara ta fara k'ok'arin kai shi kan kujera yayi sauri ya janye daga jikinta ya d'auke ledar wayar daya yasar a k'asa ya mik'a mata yace gashi su ringa communicating yayi wa wayar full charge ta b'oye karta bari Ameer ya gani.

Zara k'ara rungumeshi tayi tana mishi godiya Adnan kuwa yayi sauri ya fice daga b'angarensu ya nufi b'angarensa dan so yake yayi girki ya kallon ball dan ba laifi ya iya girki.

Yana girki suna chattn da Zara sai exchanging dirty talk suke inda Zara tace bari tazo ta taya shi girki yayi sauri yace ta rufa masa asiri da k'yar yasamu ta hakura da zuwan dan yaga alamar Zara bata tsoron asirinsu ya tonu babu kuma Kunya a tattare da ita.

Ameer kuwa ana sallar Magriba ya nufi gidansu dan ya matsu yaji ya Hajiya Ameena tayi da iyayen batula.

K'asa ma cin abincin da Hajiya Ameena ta jera masa yayi kawai so yake yaji an bashi dama ya fara zuwa wajen Batula.

Sai da Hajiya Ameena ta wana shi tace mishi sunyi magana sunce babu matsala zai iya zuwa su fahimci juna ga lambar wayarta nan

Jiki na rawa Ameer ya shigar da lambar wayarsa Hajiya Ameena sai Dariya take mishi kamar wani saurayin da bai tab'a buduruwa ba.

Abincin da bai ci ba kenan ya mik'e ya nufi gidansu Batula bayan ya kirata awaya yace mata gashi nan zuwa muryarta kawai yaji yasan zata kwanta mishi idan ya ganta.

Ameer tsurawa Batula ido kawai yayi a lokacin da ta fito da shigarta irin ta Aliya duk da sunkuyar da kanta tayi hakan bai hana yaga mugun k'yaun da take dashi ba.

Ameer kusan shi kad'ai ya ringa maganarsa dan Batula ta k'asa magana sabida kunya Wanda hakan kuwa yayi masa dadi sosai yana San mace mai kunya bai San tsautsayin da ya kai shi ya Auri Zara ba ahaka yayi mata sallama ba dan ya gaji da ganin fuskarta ba sai Dan ganin goma ta kawo kai.

Sai da ya koma gidansu ya samu Hajiya Ameena yace Batula tayi mishi over ta fad'awa kanin babansa yaje ya  nema masa Aurenta dan in zai samu ma da ita zai tare a sabon gidansa ahaka sukayi sallama da Hajiya Ameena zuciyarsa fal da farinciki.

Batula ma kuwa tunda ta shiga gida take murmushi ita kad'ai dan Ameer yayi mata itama tana ganinsa taji tana sansa.

Ameer sai wajen k'arfe goma sha d'aya ya shigo gidan sai da ya kulle ko'ina na gidan zai nufi d'akinsa yaga bak'in agogo na maza a k'asa a hankali ya sunkuya ya d'auki agogon yana mamakin mai agogon namiji ke yi a cikin palonsa dan wannan ba agogonsa bane take gabansa ya yanke ya fad'i da yayi tunanin ko dai Zara ce ta kawo mishi namiji har gida dan tunda yaje gidansu yafara zargin k'ila tana huld'a da maza awaje tunda da idonsa yaga Wanda tayi niyyar zuwa wajen sa badan ta ganshi ba aranar.

Bai tsaya wani dogon tunani ba ya nufi d'akin Zara a fusace

Zara da ta cire kayanta ta shige cikin bargo suna video call da Adnan sai lumshe ido take tana zaro harshe waje.

Ji tayi ana buga k'ofar kamar za'a b'allata tayi sauri tayi wurgi da wayar hankalinta a tashe ta duro daga kan gadon dan tasan Ameer ke neman b'alla Mata k'ofa

Ajiyar zuciya ta sauke a lokacin da ta tuna ta kulle k'ofar tabar mukulli a jiki

Tsaki tayi ta koma cikin bargo duk da tanajin irin kiran da Ameer ke mata kamar zai fasa makogaronsa.

Adnan kuwa yana ganin Zara tayi w'uli da wayar yayi sauri ya kashe wayarsa gabad'aya gabansa na fad'uwa...Zara kiranshi ta ringa yi amma taji a kashe taja tsaki tana mai jin haushin Ameer da yazo ya katse mata jin dadi badan tana tsoron asirinta ya Tonu ba da zuwa zata yi ta taya Adnan kwana tunda Aliya bata nan tana San kasancewa dashi. 1

Pillonta ta jawo ta rungume ta lumshe ido tana tunanin moment d'insu da Adnan sai murmushi take ahaka bacci ya d'auketa.


Ameer kuwa a fusace ya nufi d'akinsa yana ayyana irin rashin mutuncin da zai yiwa Zara dan yanzu zarginta yake bai yarda da ita ba kwata kwata duk da baya jin digon Santa a zuciyarsa amma babu Yanda za'ayi ya zuba mata ido ta ringa abinda ranta yakeso tunda da Auransa a kanta.

A ranar kiran Batula da yayi awaya yasa yaji ya manta da duk wani b'acin ran Zara yaji wani irin farinciki da nutsuwa na shigarsa.


Aliya kuwa sabida allurar baccin da aka mata ba ita ta tashi ba sai wajen k'arfe biyar sai da ta samu minti biyar da farkawa ta tuna abinda yasa ta baro gidan  Adnan hawaye na ya hau zubo mata ta gefen fuska 

Hajiya Rukayya dake zaune a gefenta tana girgiza k'afa sabida jiranta kawai take  ta farka wani mugun harara ta fara zabga mata duk da Aliya bata lura da ita ba dan idonta a runtse yake.

"Kukan uban me kike wa mutane ba haka kikeso ba ki dawo gida mu jere Aliya Ashe bakida mutunci bansani ba  Aliya tarbiyyar Dana miki kenan Allah ya baki kyautar da bazaki iya siya ba wasu da kud'insu ma  suke nema basu Samu ba amma Aliya sabida rashin mutunci da rashin hankali kice bakya so sai kin zubar har ya kai ki barin gidan sabida kawai ya hanaki zubar masa da ciki"

Zumbur Aliya ta mik'e duk da sai da ko'ina na jikinta ya amsa ta k'walalo ido tana kallon Hajiya Rukayya

Hajiya Rukayya kuwa ta cigaba da zabga mata harara tana "ai dole ki mik'e Mara mutunci kawai Wlh kin bani mamaki badan Allah yasa mijinki mai hakuri bane  da yanzu tuni ya sakeki cikin sunna fisabillillahi kice sai kin zubar yanzu da kika taho gida uban me kika zo yi"? Ko kina tunanin muma shashashai ne biye miki zamuyi"


Aliya cikin tsananin mamaki da d'aurewar kai tace murya na rawa "Umma wlh bangane inda maganarki ya dosa ba umma  mai kike nufi"?

Hajiya Rukayya wani mummunan kallon ta k'ara watsawa Aliya tana girgiza kai dan gani take Aliya ta gama raina mata hankali sai da aka samu minti biyar batayi magana ba tana watsawa Aliya kallon Banza 

Aliya kuwa jikinta sai rawa yake kanta na Sara mata Dan tana so ma ta had'a maganganun Ummanata waje d'aya ta gane inda maganar nata ya nufa amma ina kanta ya kulle.

" Lailai Aliya abin naki yazo da rainin hankali ni kike ma cewa baki gane inda na dosa ba ko Aliya rashin mutuncin da kikewa Adnan d'in nima zaki min ko"?
2

STORY CONTINUES BELOW


Aliya kuka ta fashe dashi tana "Wlh umma bangane abinda kike nufi ba mai zan zubar"

Hajiya Rukayya fad'a ta rufe Aliya dashi ta inda take shiga bata nan take fita ba kamar zata rufe Aliya da duka acikin fad'ar da take fad'a mata yanda sukayi da Adnan.


Aliya kuwa kukan da take ne ya  tsaya  cak ta zubawa Hajiya Rukayya ido cikin tsananin mamakin abinda tace Adnan ya gaya mata wani irin kukan bak'inciki ta k'ara fashewa dashi

badan na karyar da Adnan ya mata ba sai Dan yardar da Hajiya Rukayya tayi da Adnan alhalin ya kama ta ace ta Riga da tasan abinda zata iya aikatawa da Wanda bazata iya aikatawa ba ada bata da burin da ya wuce ace yau ta samu ciki cikin ma na Adnan amma yanzu babu Wanda ya kai ta bak'incikin samun cikin dake jikinta.
1

Hajiya Rukayya baki ta rik'e tana kallon Aliya dake kuka kamar numfashinta Zai d'auke bak'inciki itama ya rufeta inda ta fara tunanin k'ila sai ta rufe Aliya da duka zata shiga hankalinta zuba mata ido tayi taga iya gudun ruwanta.

Aliya kuwa da k'yar ta tsagaita kukan da take numfashinta na d'aukewa  tace "Haba Umma ya Zaki yarda da maganar da Adnan ya gaya miki batare da kin tambayeni ba kinji ta bakina karki manta Umma babu Wanda ya kai ki sanin halina ciki da waje kinsan abinda zan iya aikatawa kinsan abinda Bazan iya aikatawa ba akan me zan zubar da cikin da Allah ya bani Umma akan me zan zubar wlh tallahi karya yake min ni banma San inada ciki ba sai yanzu da kika fad'a wlh karya yake min"

Tace tana fashewa da kuka

Tunda ta fara magana jikin Hajiya Rukayya yayi sanyi lakwas shiru tayi tana tunani dan tabbas tasan halin 'yarta akan me zata zubar da cikin tace bataso mai yasa tayi saurin yarda da maganar Adnan bata tsaya taji ta bakin Aliya ba. 1

Ajiyar zuciya ta sauke cikin sanyin murya tace "Aliya to kina nufin mijinki sharri ya miki kenan akan me Zai miki sharri mai ribansa idan yayi miki haka"?

Aliya runtse ido tayi hawaye masu Zafi na k'ara k'waro mata Sam bata so ta tona sirrin Adnan bata so adaina ganin mutuncinsa ko  zuwan da tayi gida wani Abu daban taso tazo ta fad'a kafin ta samu hanyar da zata b'ullowa Adnan da Zara.

Hajiya Rukayya ganin tana ta kuka tak'i tayi magana ne yasa ta tashi taje ta zauna a gefenta ta kwantar da kanta a cinyarta ta fara rarrashinta tana kwantar Mata da hankali cikin dabara ta cigaba da tambayarta abinda ke faruwa tsakaninta da Adnan karta manta bata da sama da ita.

Aliya a hankali ta kwashe komai ta fad'awa Hajiya Rukayya babu abinda ta k'ara har soyayyar dake tsananin Zara da Adnan sai da ta fad'a mata.

Hajiya Rukayya sallati kawai ta ringa yi tana tafa hannuwa dan babu abunda ya girgizata sama da tarayyar Adnan da Zara ga wani mugun karya da sharri da yayiwa Aliya dan kawai ya b'ata Aliya awajensu  wanan wane irin tashin hankalin da masifane Adnan ya rasa wacce Zai nema sai  matar Aure   Babu Kunya babu tsoron Allah matar Auren Ma matar mak'ocinsa wanan wane irin bala'i ne ahaka kamar Adnan ba Zai aikata haka ba.

Aliya kuwa hawaye kawai ke zubo mata tana sharewa dan ta hango itama tashin hankali a fuskar Ummanta.

Sai da suka kwashi minti Ashirin ahaka kowa da abinda yake sak'awa aransa kafin Hajiya Rukayya ta sauke nannauyar ajiyar zuciya tace 

"Aliya kin tabbata babu abinda kika ragi mijinki dashi?

kin tabbata kina bashi hakkinsa yanda ya kamata?

kin tabbata kina bin shi sau da k'afa?
kin binciki kanki kuwa kina iya gamsar da mijinki ya gamsu dake yana jin dadin tarraya dake?"

Aliya hawaye ta k'ara sharewa tace "wlh Umma ina iya k'ok'arina dan naga na mishi duk abinda yakeso ko laifi ya mun bana nuna mishi naji haushi ba wai dan banji haushin ba nasha in zauna inyi tunani inga mai nake masa da bayaso da har matan waje suke d'auke mishi hankali amma sai naga babu abinda nake masa Umma yanzu gashi har  matar mak'ocinsa yake bi yanzu Umma kina ganin zamana dashi Zai yiwu ahaka 
idan yaje ya kwaso wani cutar yazo ya  saka min fa ina zaman zamana Umma wlh banso na had'a zuria da mazinaci 
Adnan ya dade yana cin amanar Aure wlh da ya min haka gwara yaje ya Auro mata uku lokaci d'aya"

STORY CONTINUES BELOW


Ajiyar zuciya Hajiya Rukayya ta k'ara saukewa ta ruk'o hannun Aliya tace "Aliya kowace mace da kika gani a gidan miji sai Allah ya jarrabceta kiyi hakuri ki ringa taya shi da addu'ar Allah ya shiryeshi ya gane gaskiya ki kuma mik'awa Allah al amuranki watarana sai labari ki k'ara dagewa da mishi biyayya ki kara hakuri ki kai zuciyarki nesa ki kau da idonki akan duk abinda yake yi wlh watarana sai yayi nadamar abinda yake yi Allah bazai bashi ikon cutar dake ba ki duba halin da kike ciki yanzu abinda Zai d'aga miki hankali baso ake ba nima zan ringa tayaki da addua akan Allah ya shirya miki shi yagane gaskiya ai bashi yayi kansa ba Zai shiryu insha Allah"

"Umma idan na cigaba da zama dashi ya saka min cuta fa me makomar yaran dazan Haifa dashi yanzu idan na haifo mazinaci ko mazinaciya fa"?

"Kul na k'ara jin wanan maganar abakinki idan bazaki fad'i alheri ba kiyi shiru ai ke ba mazinaciya bace insha Allahu bazaki haifi mazinata ba kuma da ikon Allah bazai saka miki cuta ba ki cigaba da gayawa Allah kinji tunda yace abarki nan da kwana biyu bari na zuba mishi ido naga iya gudun ruwansa idan bai zo ba da kaina zan maidaki zan kuma mishi nasiha na mishi hannunka mai sanda ita kuma wannan Asararriyar mak'ociyar taki da bata tsoron Allah idan kin koma ki nuna mata kinsan mai ke tsakaninta da Adnan ta rabu da mijinki ko kuma ki gayawa mijinta halin da ake ciki kiyi hakuri kinji"

Aliya gyad'a mata  kai kawai tayi ta cigaba da share hawayen dake zubo mata.

Hajiya Rukayya kuwa ta mik'e ta nufi kitchen dan ta samowa Aliya abinda zata ci.Washegari kuwa Ameer da wuri ya fice daga gidan dan tun jiya daddare ya kuduri niyyar zubawa Zara ido tayi duk abinda taga Dama bashida lokacinta tunda yanzu ma Aure Zai yi yana zaune da Zara ne kawai dan Mommy Hauwa shi yanzu Neman Auren Batula kawai Zai sa agaba amma fa duk ranar da ya kama Zara tayi ba dai-dai ba sai na lahira yafita jin dadi.

Tamkar dai jiyan Ameer na ficewa Zara ta nufi b'angarensu Adnan.

Suka shek'a ayarsu babu Kunya babu tsoron Allah Dan har girki sukayi tare suka ciyar da junansu kamar wasu ma'aurata Zara har da taya shi gyaran gidan da wanke boxers D'insa tamkar bazasu rabu ba sabida yanda suke jin dadin kasancewa da juna.


Aliya kuwa  Hajiya Rukayya  ta dage sosai wajen kwantar mata da hankali da nasiha akan ta barwa Allah komai yana sane da ita komai mai wucewa ne kamar ba'ayi ba.

Sati d'aya kenan Adnan da Zara na shek'a ayarsu Ameer idan ya fice da sassafe

Adnan har mantawa yake da Aliya dan So da sha'awar Zara ya k'ara linkuwa a zuciyarsa baya ma jin da matar Aure yake mu'ammalla.

Haka ma b'angaren Zara tana bala'in jin dadin kasancewa da Adnan dan gani take bazata iya rayuwa babu Adnan ba Adnan shine irin namijin da ta Dade tana mafarkin samu jarrababe Wanda ya kware a tafiyar da mace cikin salon soyayya mai tsayawa arai dan Adnan yaki ya bata had'in kan da takeso ne da tuni ta shak'e wuyan Ameer tace ya bata takardarta wani tsana da kishin Aliya takeji a kullum idan tana tare da Adnan dan gani take ta Dade tana more  soyayyar Adnan babu irin  zugar da bata yiwa Adnan ba akan ya kaiwa Aliya takardar sakinta sai yace mata kar ta damu lokaci yake jira in tanaso ta k'ara magana sai ya kashe ta da soyayyarsa.

Ameer kuwa wani irin so da shak'uwa ne ya ringa shiga tsakaninsa da Batula bashi da burin daya wuce ya mallaketa duk da har an bashi Aurenta shi kad'ai ake jira ya gama shirye shiryen da Zai yi San da yake yiwa Batula ya taimaka wajen share Zara a zuciyarsa dan a gidansu yake cin abincin safe rana dare badan Mahaifiyarsa ba babu abinda Zai ringa dawo dashi gidansa kwana ko kad'an bai tab'a Zargin mak'ocinsa Adnan na cin amanarsa ba dan bai ma San Aliya tana gidansu ba.

Mahaifin Aliya  Alhaji Abubakar kuwa ganin shiru shiru Adnan bai waiwayi Aliya ba ballantana ya kirata awaya yasa ya nemi Adnan da kansa dan Hajiya Rukayya duk ta fad'a mishi abinda ke faruwa.

A lokacin Adnan na Zaune a office d'insa dan bai Dade da zuwa  bayan fad'an da ogansa ya masa akan zuwan da yake yi a makare akan ya kiyaye idan aikin ne bayaso sai ya fad'a masa mutane dubu suna so.

Tsaki yake akai akai na takaicin irin Fad'an da ogan nasa ya masa kiran Alhaji Abubakar ya shigo wayarsa Zaro ido yayi gabansa na d'an fad'uwa dan bai San mai Zai ce mishi ba dak'yar ya d'aga wayar ya k'ara wayar a kunnensa tare da sallama kamar mutumin kirki 

Dayake Alhaji Abubakar yana da zuciya bai tsaya amsa Sallamar da ya masa ba yace

"Inaso na San matsayin 'yata ka saketa ne ko har yanzu matarka ce"

Cikin rawar baki Adnan yace "Alhaji Dama yau nakeso nazo na taho da ita ayyuka ne suka sha min kai shiyasa banzo ba tuntuni"

"Dakata Adnan bafa rok'on ka nake akan lailai ka zauna da Aliya ba ba Neman kai nake da ita ba 
Wulak'anci ne banaso yau tsawon sati d'aya Aliya na gida baka waiwayeta ba baka kirata  awaya ba idan gajiya kayi da ita ka kawo min takardarta idan Allah ya sauketa lafiya sai kazo ka d'auki abinda ta Haifa bayan duk abinda kayi mata a sanadinka ta kamu da hawan  jini 'yata duk tabi ta fita hayyacinta idan kasan bakayi ba dole bane kaji ko"

"Ba haka bane Alhaji Allah ya huci zuciyarka anjima zanzo insha Allahu"

Alhaji Abubakar bai tsaya jiran mai yake cewa ba ya kashe tare da Jan dogon tsaki dan badan Hajiya Rukayya data dage ba wlh da Aliya ta gama zama dashi dan ba k'aramin Abu Adnan Zai wa Aliya ta kama hanya ta taho gida ba duk da yaji matan Banza yake nema awaje.
1

Adnan kuwa ashar ya ringa kundumawa Alhaji Abubakar tamkar yana gabansa  dan dai yana jin nauyin Alhaji Abubakar ne da bama Zai d'auko Aliyar ba dan yana jin dadin holewarsa da yake yi da Zara babu ruwan shi da wani kama hotel yanzu idan ya dawo da ita dole yafara bin hotel hotel......Aliya kuwa Alhaji Abubakar na gama waya ta fashe da kuka tana bata San komawa gidan Adnan ita abarta tayi zamanta a k'arba mata takardar sakinta kawai.
+

Hajiya Rukayya tsawa ta daka mata ta rufeta da fad'a akan bata jin magana  duk nasiha da wa'azin da take mata bata ji ba kenan.

Alhaji Abubakar katseta yayi shima da sauri akan kar ta takurawa Aliya dan Aliya Tana da hakuri dole tace bazata koma ba mai  za'ayi da namiji mazinaci.
1

Hajiya Rukayya ganin Alhaji Abubakar yana k'ara tunzura Aliya yasa taja hannunta suka tafi d'aki ta cigaba da rarrashinta Tana kwantar mata da hankali.

Adnan kuwa har Magriba yana tunanin Yanda zaije gidansu Aliya dan Allah yasan babu Yanda zai yine da babu inda za shi dan yanzu yana morewa rayuwarsa dawowar Aliya zai  takura rayuwarsa ahaka ya gama tunane tunanensa a karshe yaja motarsa ya nufi gidansu Aliya duk da gabansa na fad'uwa dan haka kawai yana shak'ar mahaifin Aliya dan mutum ne shi da baya tolerating nonsense tun akan Neman Auren Aliya yasan mutum ne shi da ya tsaya sosai akan duk wani Abu daya shafi iyalinsa ba k'aramin bincike yayi akansa kafin ya yarda ya bashi Auren Aliya ba ba kuma shi kad'ai yayiwa haka ba duk Wanda ya nemi wata a gidan hakan yake masa.

A lokacin da ya isa gidansu Aliya sai da yasamu minti biyar awaje ya rasa Yanda zai shiga gidan sai da maigadi ya lek'o yaganshi a tsaye da yake ya San shi yace bari ya gayawa Alhaji yazo.

Adnan gumi ya hau had'awa dan bai San mai Aliya taje tacewa mahaifinta ba haka kawai tsoro yabi ya rufe shi.

Fitowar maigadin tare da mai iso cikin gidan yasa ya d'an gayyato nutsuwa fuskarsa ya ari kamalla ya yafa kamar mutumin arziki dan manyan kayane ajikinsa sai wani sunne kai yake.


Alhaji Abubakar na zaune a palon yana jiran isowar Adnan fuskar nan tashi a murtuk'e ciki ciki  ya amsa gaisuwar da Adnan ya masa ya fara karewa Adnan kallo.

Adnan kuwa kamar zai shige cikin carpet d'in dake shimfid'a akasan tiles d'in palon sai narkawa Alhaji Abubakar zagi yake a zuciyarsa.

Sai da suka kwashi minti kusan goma babu Wanda yayi magana acikinsu kafin Alhaji Abubakar yayi gyaran murya yace 

"Adnan ka gaji da zama da Aliya ne"?

Adnan da Sauri ya d'ago yace " Aaa Alhaji wlh ban gaji da zama da ita zuwan ma datayi gida sabani muka samu"

Hannu Alhaji Abubakar ya d'aga masa alamar ya dakata yace " ban tambayeka mai had'a ku ba ina tambayarka ne akan idan ka gaji da zama da ita ka bani takardar sakinta dan a rayuwata babu Yanda za'ayi na yarda a wulakanta Min d'an Dana Haifa kwata kwata bakuyi shekara d'aya da Aure ba Aliya tabi ta fita hayyacinta kasaka mata hawan jini ga juna biyu da take d'auke dashi ni nasan halin duka yaran Dana Haifa na kuma San irin tarbiyyar Dana basu duk 'ya'yana babu mai hakurin Aliya dan haka Bazan yarda a cutar da ita ba dan anga tana da hakuri idan kasan ka gaji da zama da ita ka bani  takardarta kawai idan ta haihu sai ka zo ka d'auki abinda ta haifa".


STORY CONTINUES BELOW


Tunda Alhaji Abubakar yafara magana gumi ya hau ketowa Adnan ko ta ina jikinsa har wani rawa yake yawu ya hadiye da k'yar yace muryarsa na rawa

"Kayi hakuri Alhaji wlh ban gaji da zama da ita ba sabani dai muka samu insha Allahu hakan bazata sake faruwa ba"

Alhaji Abubakar bai ce masa komai ba ya mik'e dan Hajiya Rukayya ta rok'eshi sosai ba dan haka ba da Sai yaga Alamar Adnan ya shiga hankalinsa zai yarda ya tafi da Aliya d'akin Hajiya Rukayya ya nufa dan ya musu magana akan su fito su same shi dan bashida abinda zai kuma ce mishi dama tambayarsa kawai yakeso yayi Idan ya gaji da zama da Aliya ya bata takardarta.


Adnan kuwa wani mugun harara yabi Alhaji Abubakar dashi har ya shige corridor d'in dake palon.

Yanda zuciyarsa ke tafasa da ace zai iya mik'ewa yabar gidan ba tare da ya tafi da Aliya ba da yaji dadi amma ina ba zai iya ba.

Alhaji Abubakar akan gado ya Tarar da Hajiya  Rukayya da Aliya a zaune Hajiya Rukayya sai kwantar mata da hankali take tana mata nasiha ita kuma Aliya sai kuka take dan babu Yanda zata yine Mahaifiyarta ta sakota agaba da babu abinda zai sa ta koma gidan Adnan dan tasan baya kaunarta yanzu Neman matan Banza kawai ya saka a gaba.

Alhaji Abubakar ce musu yayi ga Adnan can suje su same shi shi ya gama mishi magana Aliya kuma tabar kukan haka ta tashi tabi mijinta idan ya mata ba dai-dai ba taga bazata iya jurewa ba ta dawo gida zai k'arba mata takardarta.
1

Hajiya Rukayya da k'yar ta samu Aliya ta wanke fuskarta ta biyota suka fito palon.

A lokacin Adnan ya cika yayi fam kamar zai fashe dan gani yake angama  wulak'anta shi Yanda aka shanya shi a Palon.

Da k'yar ya dai-dai ta nutsuwarsa ya gayyato fara'a fuskarsa ya fara gaida Hajiya Rukayya data samu waje ta zauna Aliya kuma ta zauna daga wajen k'afarta.

Aliya itama gaishe shi tayi fuskarta a sunkuye Adnan ya amsa da fara'arsa yana tambayarta ya jikin nata.

Hajiya Rukayya nasiha tayi musu gabad'aya idan ta ringa yiwa Adnan hannunka mai sanda akan zai iya k'ara Aure idan Aliya bata gamsar dashi Allah ya hallata mishi ya Auri mata hud'u bata dai fito tace Aliya tace yana bin matan Banza ba amma Adnan duk ya gane inda maganarta ya dosa  

Godiya yayi mata sosai a lokacin da Hajiya Rukayya ta mik'e tace su tafi Adnan shi kuma ya d'auki akwatin Aliya yayi gaba yabar Hajiya Rukayya da Aliya na cigaba da magana Inda duk Rabin maganar Nasiha ce da shawarwari da Hajiya Rukayya ke bawa Aliya.

Har gate Hajiya Rukayya ta rako Aliyar sai da taga tafiyarsu ta koma ciki.


Adnan kuwa suna barin k'ofar gidan ya k'arawa motar speed ya ringa tsaki akai akai yana k'unk'uni dan ji yake kamar ya jibgi Aliya ya huce haushin Alhaji Abubakar dayake ji.


Aliya ita dai kwantar da kanta kawai tayi a cinyarta tana tunanin irin zaman da zatayi da Adnan dan agaskiya yanzu tsoron ya kusanceta take yi.

Tara da  rabi suka k'araso gidan.

Zara da wani zubin take cin kwalliya tazo ta tsaya taga dawowar Adnan idan ta kama har d'an soyayya suyi kafin ameer ya dawo dan Adnan yana Riga Ameer dawowa dan masifa ko daga nesa taji k'ugin motar Adnan sai ta gane yanzu ma kwalliya Tayi da wani gown mara hannu kirjinta duk awaje tana jiyo dirin motarsa tafito aguje ta tsaya a tsakar gida tana jiran ya shigo da motarsa taje ta rungume shi tamkar Yanda ta saba.

Shima Adnan haka kawai gabansa ya hau fad'uwa dan ya tuna Zara na zuwa mishi oyoyo gashi bata San ya d'auko Aliya ba addu'a ya hau yi a zuciyarsa akan Allah yasa Ameer yariga shi dawowa sabida kar Zara ta samu fitowa.

STORY CONTINUES BELOW


Adai-dai lokacin da numfashin shi da Aliya ya nemi d'aukewa tare da wani mummunan fad'uwar gaba sakamakon Zara da suka hango a  tsaye ta hard'e hannayenta a kirjinta ta tallafo kirjinta sunyi sama tana jiran Adnan yayi parking ta tafi ta rungume shi

Adnan ko parking bai gama yi ba cike da tashin hankalin abinda ke Neman faruwa agaban Aliya Zara ta taho da gudu b'angaren da yake Zaune tana "oyoyo hubby I miss you"

Adnan sandarewa yayi ajikin kujera yawun bakinsa ya k'afe 

Aliya kuwa ta saki baki cikin tashin hankali tana kallon ikon Allah adai-dai lokacin da Zara ta bud'e k'ofar motar Adnan kuwa kamar ya saki fitsari a wando duk da ba tsoron Aliya yake ji ba amma yasan bai kamata ta san yana dating matar Aure ba, matar Auren ma mak'ociyarta mai yasa ya manta bai mata text message akan karta fito yau tarar sa suna tare da Aliya

Zara  dake k'ok'arin sunkuyawa ta rungume Adnan cak ta  k'ammar da hannunta waje d'aya a  lokacin da suka had'a ido da Aliyar da idanuwanta ke Neman fad'owa k'asa sabida tsananin mamaki.

Zara k'asa motsawa tayi ta zubawa Aliya ido jikinta na d'an rawa still lokacin hannunta na k'ame 

Adnan kuwa kamar ya shige cikin kujerar ya b'ace gumi sai keto masa yake yana wani naso kamar Wanda aka shafawa man kulli
1

Aliya d'aurewa tayi tace

"Ya kika tsaya ki rungumeshi mana"
1

Zara ja da baya tayi da zumar barin wajen da sauri Aliya ta fito daga cikin  motar

cikin zafin nama tasha gabanta tace cikin Lion Voice "ina zakije ba mijinki kika zo yiwa oyoyo ba akan me zaki fasa dan kin gani kije ki mishi oyoyon mana"


Zara duk da gabanta fad'uwa yake sai da ta d'aure  ta ari k'arfin Hali tace "Kinga Aliya banida lokacin ki kibani hanya na wuce"

Aliya Da Zuciyarta ke wani irin zafi finciko Zara tayi ta shak'e mata wuya ta hau zabga mata mari tana kiranta da karuwa 

Adnan kuwa kamar Wanda akayi glueing ajikin motarsa ya k'asa koda motsawa ballantana ya fita waje ya kaiwa Zara d'aukin duka  da  naushin da take sha awajen  Aliya 

Aliya sai data raba rigar dake jikin Zara gida biyu ta had'a kan Zara da jikin bango ta ringa gwara shi dan Yanda take jin ta a yanzu tas zata aika Zara Lahira dan bata tab'a tunanin Zara bata jin tsoron Allah ba sai yau da Aurenta take bin wani namijin.

Zara kuwa sai ihu take tana Neman d'auki dan duk k'ok'arin da ta ringayi dan ta Dan rama dukan da Aliya ke mata ta kasa dan Aliya a zuciye take dukanta duk da jinin dake zuba a hancinta hakan bai sa Aliya ta k'yalleta ba   naushinta kawai take tana gwara kanta da bango ko bata duba ba tasan kanta ya fashe.


Adnan da k'yar ya zuro k'afarsa waje ya nufi wajen da suke dan yama rasa abinda ya kamata yayi tamkar Aliya ta kama shi red handed da  Zara suna making love haka yakeji.

Hannu yasa yafara k'ok'arin janye hannun  Aliya daga shak'etan da tayi Aliya a zuciye ta ture Adnan

Adnan taga taga yayi  kamar zai fad'i dan sosai ta tureshi bai tab'a sanin Aliya nada k'arfi haka ba sai yau 

Wajensu ya k'ara komawa da gudu dayaga Zara na kakarin mutuwa sakamakon shak'ar da Aliya tayi mata

Hannun Aliya ya rik'e da k'arfi yana daka mata tsawa akan ta cika Zara amma ina ko gezau Aliya bata yi ba dan da alama ba ahayyacinta take ba 

Zara kuwa a wahalce tace "Adnan do something am dying"

Adnan fusgo Aliya yayi da k'arfi tare da wurgar da ita yace "ke bakida hankaline kisan kai zakiyi"

A haukace Aliya tace "Eee kisan kai zanyi gwara na kashe ta dan bata tsoron Allah"

Zara kuwa aguje ta shige b'angarenta tare da kulle k'ofar dan gani take Aliya zata iya biyota sai shafa keyarta take da duk inda ke mata radadi.

Aliya kuka kawai take Tana kallon Adnan wani mugun tsanarsa na ratsata bazata tab'a iya zama da Adnan ba  Adnan yayi nisa bayajin kira.
2

Aliya zumbur ta mik'e ta nufi b'angaren Zara da gudu ta fara bubbuga k'ofar tana "Zara wlh a yau sai na gayawa mijinki Yanda kike cin amanarsa da mijina Ashe da ba na nan ke kika maye gurbina wlh yau sai na fad'a mishi ina zaune Anan Ina jiran dawowarsa.

Aliya tace Tana zubewa ak'asa dan yau ta sha alwashin sai Ameer yasan abinda ke faruwa.
2

Adnan kuwa dayaji mai Aliya tace hankalinsa ne ya tashi ya nufi wajenta da sauri ya durk'usa agabanta yana " Aliya karkiyi haka Dan Allah ki rufamin asiri Karki sa adaina ganin mutuncina ya za'ayi ki soma tare Ameer da irin wanan zancen wlh is not what u think sharrin shaidan ne pls.

Aliya wani mugun harara ta watsa mishi tace "wlh kaji kunya kayi asara ka rasa wacce zaka nema. Sai matar mak'ocinka wlh ko ni nagama zama dakai amma ina nan ina jiran Zuwan Ameer dan shima yayi taka tsan tsan Karku saka mishi cuta Allah yasan banida hakkin Ku biyu shiyasa Allah ya nuna min komai ina can gidanmu kai kana nan kana watsewarka da matar mak'ocinka tirrr Adnan tirrr nayi dana sanin Aurenka wlh Bazan iya had'a zuria da kai ba na tsaneka Adnan na tsaneka"

Adnan shiru yayi yana kallon Yanda take kuka kamar ranta zai fita tashin hankalinsa bai wuce Ameer da tace zata  gayawa ba in ya dawo rok'onta ya fara yi akan ta tashi su tafi b'angarensu suyi magana amma fir Aliya tak'i ta dage akan sai tajira zuwan Ameer.

Adnan kuwa dayaga idan ba dagaske yayi ba Aliya is Eva ready ta tozarta shi  k'ink'imarta yayi da k'arfinsa yayi b'angarensu da ita sai wuntsila k'afa take Tana ihun ya ajiyeta.......

Post a Comment for "MAKOTAN JUNA CHAPTER 3"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...