Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

MAKOTAN JUNA CHAPTER 10 KARSHE

MAKOTAN JUNA CHAPTER 10 KARSHE

- - Post a Comment

MAKOTAN JUNA CHAPTER 10. KARSHETun daga nesa Ameer ya kura mata ido dan tunda yake da ita bai tab'a ganinta ba dogon Hijabi ba sai yau duk da doguwar rigarta ba matsatsiya bace yana hango baiwar kyau da diri da Allah ya mata.

Aliya kuwa kanta a sunkuye ta k'arasa wajen Ameer Tana d'an murmushi yau wani sabon kunyarsa take ji sabida tunda ta fito ta lura da irin kallon da yake mata sabida akwai wadatacen haske a tsakar gidan nasu tasan kallon nasa na ya ganta ba Hijabi ne dan bai tab'a ganinta ba Hijabi ba kara sunkuyar da kanta tayi tana wasa da yatsun hannunta daya sha bak'i da Jan lalle

Ameer kuwa da k'yar ya amsa sallamar da tayi mishi yana sauke ajiyar zuciya tare da godewa Allah daya Mallaka mishi Aliya dan ba ikonsa ko dabarar sa bace Allah ne yayi ikonsa ya bashi ita.

Lumshe ido yayi yana shak'ar kamshin dake fitowa daga jikinta.

Sai da suka kwashi minti biyar ahaka kafin Ameer yace "Amaryata kinsha kyau kyaun ma har zuba yake dan wlh na ma kasa fassalta miki irin kyaun da kikayi"

Aliya murmushi tayi ta cigaba da wasa da yatsunta.

Ameer kuwa yayi murmushi dan Kunyar Aliya na bala'in burgeshi kamar wacce bata tab'a aure ba.

Hira ya ringa Jan Aliya dashi sosai amma Aliya kuwa ta kasa sakin jiki dashi ya lura kamar a takure take sabida mayafin data fito dashi ya matsu Jibi yayi a d'aura musu aure ya cire mata wanan kunyar da take ji.

Akan dole yayi mata sallama ya tafi dan idan yana tare da Aliya har wani irin nutsuwa da nishadi ke shigarsa a kasan zuciyarsa kuma yana jinjina irin rashin rabon Adnan dan Mara rabone zai k'asa gane baiwar da Allah ya mishi ta Mallakar Aliya.

Mommy Hauwa zagaye asibitin kawai take inda ta ringa sharar kwalla Dr shima tuni ya iso asibitin hankali a tashe haka ma duka yayyen Zara da Khaleed har da Aunty Khadija addua kawai suke akan Allah ya sauke Zara Lafiya dan kusan awa hud'u kenan da aka shiga da ita banda ihun sallatin da take yi babu abinda suke jiyowa.

Dr kuwa Massallacin dake cikin asibitin ya je ya ringa jera nafilolli dan baisan meyesa gabansa ke ta fad'uwa ba.

Har akayi sallar isha Zara bata haihu ba dan ansama ta ruwan nakuda har guda biyu ya kare amma bata haihu ba.

Zuwa wannan Lokacin Mommy Hauwa wani irin zazzabi Zazzabi ne ya ringa shigarta dan haka kawai taji gabanta na mummunan fad'uwa zuciyarta na mata wani iri.

Aunty Khadija ce kawai take da k'arfin halin kwantar mata da hankali.

Zara kuwa bazata iya misalta irin Azabar da take sha ba tunda take arayuwarta bata tab'a jin irin wanan ciwon ba bayanta kamar Sara mata ake haka ma mararta sallati kawai takeyi tsoron Allahn daya Halliceta na shigarta Babu abinda take tunani sai Mommy Hauwa da tayiwa rashin kunya yanzu irin wanan azabar uwa take sha awajen haihuwa yanzu duk Laulayin nan da tayi Ashe nafila ce akan nakuda sunan Allah kawai take iya kira idan azaba yayi azaba ma bata iya kiran sunan Allah a fili sai dai a zuciya.

STORY CONTINUES BELOW

Likitan dake kan Zara ganin har ruwan nakuda leda biyu ya kare a jikin Zara banda kwayoyin dake tunzura jariri ya fito duk tasha babu alamar haihuwa sai ma bak'ar wahalar da take sha yasa ya fito ya samu Dr yace mishi sai dai ayiwa Zara operation dan Sam bazata iya haihuwa da kanta ba duk da ga kan baby yana hangowa.

Gaban Mommy Hauwa wani irin yankewa yayi ya fad'i haka ma Dr da suka ji abinda likitan yace take Mommy Hauwa ta tuna yayarta data mutu agarin operation.

Mommy Hauwa da sauri tafara girgiza kanta tana "aaa likita ba sai anyi mata operation ba insha Allahu zata haihu da kanta ka bata nan da anjima da izinin Allah zata haihu da kanta"

Likitan da ya riga ya lura tunda ya ambaci operation hankalin Mommy Hauwa ya tashi murmushi yayi yace "Hajiya ki kwantar da hankalinki insha Allahu za'a Ciro mata abinda ke cikinta successfully batare da an samu wata matsala ba tariga da tayi weak da yawa bazata iya haihuwa da kanta ba sai dai a mata operation".

Mommy Hauwa da sauri ta kara girgiza kanta tace " Aa likita kar ayi mata operation insha Allahu zata haihu da kanta"

Dr kuwa kasa ma magana yayi in banda jikinsa dake rawa.

Likita ganin ya kad'a ya rayya akan su bari ayi mata operation sunki yasa ya rabu dasu yaje ya k'ara yiwa Zara 'yan dabaru ko zata iya haihuwa amma ina har k'arfe goma sha d'ayan dare Zara ta k'asa haihuwa sai bak'ar wuyan da take sha.

Mommy Hauwa kuwa sai kuka take Tana jera adduoi.

Nurse d'in dake kan Zara a lokacin da likitan yaje duba sauran patient din Zara ta yafito akan tazo.

Nurse d'in ta matsa da sauri taje saitin kunnenta dan Sam bata jin mai Zara take cewa da k'yar ta iya jiyo mai Zara take cewa

"Dan Allah ki kiramin Ummana kice tazo akwai maganar da zan mata"

Nurse bata tsaya wani b'ata lokaci ba ta fita waje ta samu su Mommy Hauwa tace Mahaifiyar Zara taje Tana san ganinta.

Tun kafin Nurse d'in ta rufe baki Mommy Hauwa tayi saurin nufar d'akin hankalinta a tashe.

Tana turo k'ofar d'akin gabanta ya yanke ya fad'i sabida wani irin dashewar da Zara tayi idonta yayi wani irin fari kamar wacce bata da jini.

Zara kuwa murmushin iya lebb'en baki tayi har Mommy Hauwa ta k'araso gadon da take kwance tana share hawaye.

Sai da ta gwada magana sau biyu muryarta bata fita kafin Tayi magana da iya k'arfinta wani irin azababben ciwo na taso mata.

"Mommy Allah ya saka miki da alheri Ashe haka kika sha wuya akanmu Mommy Dan Allah ki yafemin duk abinda nayi miki daga ranar da kika kawoni duniya har zuwa yanzu danake kwance akan gado Mommy yarinta da rashin Ilimi yasa bansan darajarki ba bansan ciwon ki ba hakika banida abinda zan biyaki dashi inama ina da dama Mommy da na miki biyayya na bauta miki har karshen rayuwata da na gyara kura kuraina da ban bari kin zubar da hawayenki ko sau d'aya akaina ba Mommy inaji ajikina Mutuwa Zanyi Mommy Dan Allah ki yafemin abubuwan da nayi miki"

Cikin matsanacin kukan fitar rai Mommy Hauwa ta rufewa Zara baki da hannunta tana girgiza mata kai tare da cewa "kul Zara bazaki mutu kibarni ba insha Allahu na Dade ina adduar K'ada Allah ya kawo ranar Da zan binne dan cikina dana Haifa sai dai ya binne ni Zara zaki haihu Lafiya zafin nakuda yasa kike ganin kamar mutuwa zakiyi babu abinda da kikayi min sai dai na roki wasu su yafe miki idan kinyi musu ba dai dai ba da izinin Allah zakiyi kyakyawar rayuwa nan gaba za'ayi koyi dake al umma zasu yi alfahari dake zan Goya y'ay'anki a bayana Zara zaki aurar da 'yarki tamkar Yanda na aurar dake dan Allah kibar fadin mutuwa zaki haihu Lafiya insha Allahu"

Zara cije lebb'e tayi cikin tsananin azabar da take sha tace "Ngd Mommy Allah ya biya ki da Gidan Aljanna Mommy Dan Allah ki taimaka min ki kira min Ameer in nemi yafiyarsa dan Allah Mommy ki kirashi kice kina nemansa idan ya yafemin hankalina zai kwanta kullum zuciyata nauyi take min idan na tuna bai yafemin ba Mommy ki kira shi yazo dan Allah"

STORY CONTINUES BELOW

"Zara wai meyesa kike irin wanan maganar ne kina karyamin zuciya Zara ki bari idan kin haihu zan kirashi da kaina in rokeshi ya yafe miki"

"Mommy nasan mai nake cewa Mommy ni naci amanarsa dan Allah ki kiramin shi dan Allah nace"

"Innalillahi wa inna ilahi rajiun Zara yanzu dare yayi kusan sha biyun dare ki bari gobe sai na kirashi nasan kafin nan kin haihu insha Allahu"

"Mommy ki kira shi yanzu kice yazo da sassafe dan Allah Mommy na rokeki da girman Allah"

Mommy Hauwa kallon Zara kawai take Hawaye na zubo mata

Wayarta dake rik'e a hannunta da tunda zu sabida irin kiran da aka ringa mata ana tambayarta Zara ta haihu ta d'auko tayi dailing number Ameer tasa a handsfree taji yana ta waya dan call waiting kawai yake sa mata.

Adai dai lokacin da Ameer suke ta soyewa da Aliya ta waya ba k'aramin mamaki yayi ba dayaga kiran Mommy Hauwa wajen sha biyun dare bai d'aga ba sai dayaga kiran nata shigowa gabansa ya d'an yanke ya fad'i yana tunanin mai zai sa ta kira shi awanan lokacin mai kuma hadinshi dasu Aliya yacewa yana zuwa ya d'aga wayar Mommy Hauwa tare da Sallama.

Mommy Hauwa ce ta fara gaishe shi da sauri
Ameer shima ya gaisheta tare da bata hakuri akan k'in daga wayar da yayi daga farko

Mommy Hauwa cewa tayi "Ameer dan Allah Dan annabi wani alfarmar nake nema duk da nasan zan takura maka ka dubi girman Allah kayimin wanan alfarmar"

"Subhanallahi Mommy ya kike ta had'a ni da girman Allah haka ai tamkar Mahaifiyata kike kin wuce duk wani alfarma a wajena idan Kinga kin tambayeni Abu banyi ba to Sai dai idan bani dashi Karki ga wai dan mun rabu da Zarah kiyi tunanin zan daina girmamaki ko mutuncinki zai ragu a idona ko d'aya wlh fatana Allah ya bani ikon yi miki abinda kike Neman"

Zara lumshe ido tayi hawaye masu dumi na biyo kuncinta dan a hands free tasa wayar.

Mommy Hauwa kuwa tace "Ameer dan Allah idan da Hali inaso gobe da sassafe kazo ka sameni a standard hospital dan Allah"

"Subhanallahi Mommy waye ba lafiya"

"Ameer ka dai kawai sai kazo ka kwantar da hankali ka ba wani Abu bane"

Ameer ajiyar zuciya ya sauke duk da hankalinsa bai kwanta da abinda tace ba yace "toh insha Allahu Mommy zan zo da sassafen"

"Yauwa Ameer ngd kwarai sai naganka"

Daga haka Mommy Hauwa ta kashe wayarta tare da kallon Zaran da idonta ke lumshe tace "toh na kira shi Zara kuma kinji Yanda mukayi dashi Zai zo da sassafe"

Zara bud'e idonta tayi da d'an murmushi a fuskarta tace "Ngd Mommy kinsan kuma wani abun mamaki wlh Kinga ciwon ya koma sakayau nake jina"
Mommy Hauwa da d'an mamaki tace "Ciwon ya koma kamar yaya kin daina jin Nakudar"?

Zara girgiza mata kai tayi tace " eee wlh nakudar ya koma"

"Ikon Allah ya akayi nakudar ya koma bari na kira likita dai ya dubaki dan bangane kin daina jin Nakuda ba"

Daga haka Mommy Hauwa ta fice waje da sauri.

Fitarsu da minti biyar sai gashi sun dawo da likitan

Inda likitan ya dudduba Zara yace "ta koma 4cm shiyasa ta daina jin nakuda amma zai kara sa mata ruwan nakuda kila ta haihu kafin gari ya waye"

Sai da ya saka mata ruwan ya bar d'akin.

Mommy Hauwa kuwa ta zauna a gefenta tana kallonta har bacci ya kwashe Zaran.

Zara baccinta tasha har akayi Sallar asuba bata ko motsa ba inda Mommy Hauwa ko kad'an batayi gyangyadi ba a kasan ranta kuma tana mamakin Yanda akayi Zara ta daina nakudar.
Likita kuwa ya dawo ya duba Zara yafi sau biyar amma har lokacin baccinta kawai take yi.

STORY CONTINUES BELOW

Bakwai na safe Ameer yafara shirin zuwa asibitin standard dan Sam bacci bai wani kara d"aukarsa daya samu kuwa bacci yayi awon gaba dashi Mafarkin Zara ya ringa yi tana ta Neman yafiyarsa a mafarki.

Haka ya tashi sukuku yana mamakin Mafarkin da yayi ahaka ya shirya kafin ya fito daga gida ya kira Aliya awaya dan su gaisa kamar dai Yanda suka saba.

Gaisawa sukayi ya tsokaneta kamar dai Yanda ya saba jin da yayi kamar a bakin titi suke yasa ya tambayesu suna ina ne yajisu a bakin titi.

Aliya ce mishi tayi Hajiyarsu ce ta aikesu tarauni zasu karbo mata sako.

Ameer murmushi yayi yace mata ai hanyarsu d'aya ma shima zaije asibiti bari yazo sai ya kaisu daga nan.

Cikin minti biyar ya k'arasa layinsu Aliya inda yagansu a tsaye da wata 'yar uwarsu data zo daga Jos

Aliya tana sanye da doguwar Rigar atamfa da farin Hijabi kal mai hannu hijabin har gwiwarta ya kai mata babu kwalliya a fuskarta amma ba k'aramin kyau tayi ba.

Ameer k'asa d'auke idonsa yayi akanta har suka shigo cikin motar inda Aliya ta zauna agaba 'yar uwarta ta zauna a baya.

Ameer kunyar Yar uwar Aliya ne yasa bai mata santin kyaun da tayi ba yaja motar suka d'auki hanyar asibitin dan sai an fara zuwa asibitin za'aje gidan da aka aiki su Aliya.

Yana karya kwanar da zasu shiga asibitin Ameer yace musu "Dan Allah bari na duba Mara Lafiya anan kunga kuma zaku samu lada".
Kusan atare sukace babu komai.

Adai dai lokacin da ya shigar da kan hancin motarsa a harabar asibitin yayi parking ya fito yace Su Aliya ma su fito su shiga ba dadewa zasu yi ba.

Fitowa sukayi suka jeru da Ameer ita kuma 'yar uwar Aliyar na binsu abaya.

Ba k'aramin dacewa sukayi ba inda kana ganin Aliya kasan Amarya ce sabida Yanda take kyalli k'unshin hannunta yafito rad'au.

Ameer wayar Mommy Hauwa ya kira adai dai lokacin da Zara ta bud'e idonta sakamakon wani azababben ciwo Mara daya tasheta.

Sallati kawai take tana kiran sunan Mommy Hauwa Inda Mommy Hauwa ta rude tayi waje da gudu dan ta kira likita.

Kafin ta k'arasa office d'in likitan taga Ameer a tsaye yana ta danna wayarsa da alama ita yake ta kira.

Ameer ganin Mommy Hauwa na sauri kamar zata tashi sama sai kuka take Ameer sallati ya saki ya nufi wajenta adai dai lokacin da ta shige office d'in likitan.

Inda suka k'ara fitowa da likitan.

Likitan yayi d'akin da aka kwantar da Zara

Mommy Hauwa kuwa ta tsaya cikin tsananin tashin hankali ta gaya mishi halin da suke ciki tun jiya da kuma Neman da Zara take mishi dan ta nemi yafiyarsa.

Ganin Yanda Mommy Hauwa keta kuka yasa Ameer ya hau kwantar mata da hankali akan insha Allahu Zara zata haihu lafiya lau.

Sai a lokacin Mommy Hauwa ta Lura dasu Aliya tacewa Ameer "Wadanan kanenka ne"?

Ameer murmushi yayi yana d'an Sosa kai cike da jin nauyin Mommy Hauwa yace " aa ai tunda zu suke ta gaisheki bakiji ba Mommy Wannan sunanta Aliya itace matar da zan Aura gobe za'a d'aura mana aure Wanan kuma kanwarta".

Mommy Hauwa Aliya ta zubawa ido tana yaba kyaunta da nutsuwarta tana kuma mata murnar samun miji kamar Ameer da Sauri Mommy Hauwa tace musu Allah ya sanya alheri ta nufi d'akin da Zara take dan har lokacin Likita bai fito ba.

Tana barin gurin Aliya tacewa Ameer "Allah sarki Ameer wanan ce Mahaifiyar Zara"

Ameer girgiza mata kai yayi Aliya tace "Allah sarki Ashe Zara haihuwa zatayi ita kazo dubawa kenan"

STORY CONTINUES BELOW

Yana k'ok'arin magana Dr dasu Aunty Khadija suka nufo wajen da suke.

Dr awajen Ameer ya tsaya dan duk a tunaninsa shima Yaji labarin haihuwar da Zara zatayi shiyasa yazo.

Kadaran kadahan suka gaisa da Ameer dan Dr yayi laushi sosai duk wanan zafin kan babu.

Inda Aunty Khadija tayi wajen d'akin da sauri .

Aliya wajen Ameer ta nufa dan tace mishi ita zata tafi kar ayi musu fad'a dan haka kawai taji wani kishi kishi ya rufeta data ga Yanda Hankalin Ameer d'in ya tashi akan Zara kenan har yanzu yana san matarsa .

Tana k'ok'arin yi mishi Magana Adnan ya shigo asibitin Khaleed na biye dashi abaya dan tunda asuba yabaro gida dan Safwan shawara ya bashi akan yafara zuwa ya nemi yafiyar Zara yaga halin da take ciki kafin ya nemi su Aliya dan Zara tafi bukatarsa inda ya d'auki shawarar Safwan ana iddar da asuba yafito daga gidan rashin abun hawa yasa sai da gari yafara wayewa yasamu abun Hawa ya nufi gidansu Zara.

Sai daya sha wahala kafin ya samu Wanda zai aika ciki dan akan idonsa su Dr suka fita tsoro ne yahana shi zuwa yayi musu magana inda sai da suka tafi ya samu wani yaro ya aike shi ciki akan ayi mishi sallama da Zara.

Khaleed dashi kawai aka bari a gida shi yafito dan yaga wanda yake Sallama da Zara dan duk a tunaninsa Ameer ne.

A bakin gate ya tsaya yana kallon Adnan dan bai san shi ba

Adnan kuwa ya k'arasa wajensa da Sauri ya mik'a mishi hannu tare da gaishe shi bai tsaya b'ata lokaci ba ya fad'awa Khalid Zara yake nema dan Allah ya kira mishi ita.

Khalid ganin Yanda yake magana kamar hankalinsa ba'a jikinsa yake ba yasa ya fad'a masa Zara na asibiti tun jiya taje haihuwa har yanzu kuma bata haihu ba shima so yake yayi wanka yaje.

Adnan cikin tsananin tashin hankali ya rik'e k'afar Khalid yace dan Allah ya raka shi asibitin yaga Zara ya taimaka mishi.

Khalid mamakine ya rufe shi dayaga Yanda yake had'a shi da Allah Dan har hawaye ne ya fara zubo mishi yana so ya mishi tambaya amma Adnan bai bashi dama ba sai had'a shi yake da Allah akan dole yaje ya shirya suka taho asibitin.

Aliya da Ameer Adnan suka zubawa ido da gashi ya cika wa fuska yabi ya zama wani siririr kamar mai cutan kanjamau babu abinda kake hangowa sai dogon wuyansa da idonsa daya shige ciki.

Ameer da Aliya ko kad'an kasa d'auke idonsu sukayi akan shi dan suna kwokwanton anya ma shine dan har carbi suka gani a hannunsa.

Adnan kuwa ko kad'an bai ma lura dasu ba dan bashida burin daya wuce yasan halin da Zara take ciki sai zabga sauri yake kamar zai tashi sama.

Haka kawai gaban Aliya ya yanke ya fad'i ta cigaba da kallon Adnan daya kusa isowa wajen da suke a tsaye.

Adai dai lokacin Adnan ya kallo inda suke a tsaye inda numfashinsa ya nemi d'aukewa sakamakon tozali da yayi da Hadaddiyar Aliya da kyaunta ke zuba sabida gyaran da ta sha bai yarda ita bace sai da ya k'ara Murza idonsa ya ga tabbas ita d'in ce dan itama bata d'auke idonta daga kan shi ba haka zalika Ameer dake gefenta.

A slow Adnan ya fara takawa inda suke a tsaye har lokacin bai kalli Ameer ba dan hankalinsa na kan Aliya.

Agaban Aliya ya tsaya hawaye Na sauko mishi bakinsa sai rawa yake sabida yana so ya furta sunanta.

Aliya kuwa cikin tsananin tsoro da mamakin Yanda Adnan d'in ya koma yasa ta juyar da kanta da sauri Tana "Ameer mu tafi"

Adnan da sauri ya kalli gefenta yaga Ameer ne daya zama First class Alhaji gentle guy ya zuba mishi ido yana mishi shima kallon mamakin Yanda ya zama.

STORY CONTINUES BELOW

Adnan kasa d'auke idonsa yayi akan Ameer ya Kalli Ameer ya juya ya kalli Aliya data Kau da kanta.

Aliya magana ta kara yi akan Ameer yazo ya maidasu gida ta fara k'ok'arin ratsa gefen Adnan ta wuce.

Adnan ya zube agabanta ya fashe da kuka yana "Aliya dan Allah Dan Annabi ki yafemin wlh nayi nadamar abinda nayi miki Aliya kinga Yanda na koma Aliya ki rufamin asiri ki yafemin dan Allah Dan annabi wlh bansan Yanda zan yi ba idan baki yafemin Na nasan an cutar dake na zalunceki amma ki bani dama dan Allah Dan annabi Na gyara kuskurena"

Aliya a kyamace ta zabga mishi harara ta ja da baya tace "kai da wa Allah ya kiyaye mai zanyi dakai Adnan ai ka Riga da ka makaro dan sai dai ka nemi wata kuma bani ba dan gobe insha Allahu za'a daura mana aure da angona Ameer Allah ya saka min abinda kayi min ya bani nagartacen miji Ameer ai baka ga komai ba Adnan ba dai bariki kasa agaba ba Kaje ka cigaba da yi ai baka ga ribar bariki ba tukunna"

Adnan tunda tace angonta Ameer ya maida kallonsa kan Ameer dake kallonsa shima yana tab'e baki kirjinsa wani irin bugawa yake kamar ya fad'o kasa wai Aliyarsa ce zata Auri Ameer mak'ocinka.

Hawaye ne suka cigaba da sauko mishi yana daga tsugunan Aliya kuwa taja tsaki tare da ruk'o hannun Ameer abinda bata tab'a yi ba.

Adnan runtse idonsa yayi sabida wani irin Abu daya sokeshi a kirji Ameer kuwa Yaji wani irin shock har kwakwalwarsa sabida taushin hannun Aliya.

Yana k'ok'arin bin bayan Aliya ya jiyo Mommy Hauwa Na k'walla mishi kira Tana wani irin kuka yana zabga sallati.

Ameer a kidime ya kwace hannunsa ya nufi wajen Mommy Hauwa inda Aliya itama ta rufa mishi baya Adnan kuwa yayi saurin mik'ewa hankalinsa a tashe dan yama manta dan Zara yazo asibitin sabida ganin Aliyar da yayi.

Mommy Hauwa cikin tsananin kuka tacewa Ameer yazo inji Zara daga haka ta koma d'akin da sauri

Ameer yabi bayanta Aliya da Adnan ma haka

Dan haka kawai Aliya taji hankalinta ya tashi data ga Yanda Mommy Hauwa ke kuka.

Zara kuwa tunda ta farka azabar da take sha yake karuwa tun Tana sallati da k'arfi har tazo ta kasa sai gwallo ido take awaje.

Likitan shi kansa hankalinsa a balain tashe yake dan bai kuma wani sauraran su Mommy Hauwa ba yafara processing yanda za'ayi mata operation Zara kuwa ganin zaa shiga da ita d'akin theatre yasa tacewa Mommy Hauwa ta kira mata Ameer ta nemi yafiyarsa.

Ameer jikinsa ne ya fara rawa dayaga Zara a kwance kamar ba ita ba yana had'a ido da ita gabansa ya fadi dan ansaka mata kayan operation d'akin kawai za'a kaita ta hana tace sai taga Ameer.

Adnan cikin masifaffan tashin hankali ya matsar da Ameer daya k'asa k'arasawa wajenta ya k'arasa bakin gadon yana

"Zara dan Allah ki yafemin abinda nayi miki nagane kuskurena yanzu na dawo gareki idan kin haihun za'a d'aura mana Aure kinji dan Allah ki yafemin Abubuwan danayi miki"

Tunda ya k'ara so bakin gadon Zara ta rufe idonta Dan Sam bata san ganin Adnan dan shine silar shigar ta masifar data jefa kanta.

Bud'e idonta tayi ta sauke shi akan Ameer da Aliya da suka zuba mata ido wani abun mamaki wani irin k'arfi ne yazo mata ta bud'e bakinta hawaye na zubo mata tace "Ameer dan Allah ka k'araso gareni kai da Aliya na nemi yafiyarku"

Kamar wayanda ake turawa haka suka k'arasa wajenta inda haka kawai Aliya ta fara zubar da hawaye na tausayin Zara.

Ameer kuwa shima tausayin Zara ne ya rufe shi ya zuba mata ido

Zara kuwa ta cijje lebb'e ta sabida wani azabar ciwon daya taso mata magana ta fara yi tana "Ameer dan Allah ka yafemin abinda nayi maka ka dubi girman Allah ka yafemin ko da zanji saukin azabar da nake ciki Ameer na cuceka ma hainceka naci amanarka alhalin kana iya bakin k'ok'arin ka dan kaga ka faranta min dan baka rageni da komai ba amma dayake shaidan da san zuciya na dawainiya dani haka na butulce maka naci amanarka da mak'ocinka na keta alfarmar aure Ameer dan Allah Dan annabi ka yafemin nasan da wuya ka manta abinda nayi maka dan Allah ka yafemin ka dubi halin danake ciki"

STORY CONTINUES BELOW

Ameer da Sauri yace "karki damu Zara na yafe miki Allah ya yafemu gabaki d'aya kiyi ta Neman yafiyar Allah Dan shi kika sab'awa dan ya hane mu da mu aikata zina Kiyi ta neman yafiyarsa shi gafurur rahim.ne mai yawan gafara ne zai yafe miki tunda har kika gane abinda kikayi ba dai dai bane ni dai na yafe miki har ga Allah sabida Allah ya Riga da ya musanya min da abinda yafi alheri ta hanyar bani Aliya"

Zara murmushin k'arfin hali tayi tace "Ngd Ameer Allah yasaka da alheri dan Allah ko da na mutu ka ringa tuna alherina kana bina da addua"

Ameer da Sauri ya girgiza kansa yace "insha Allahu bazaki mutu ba Zara Zafin nakuda ne kawai"

Zara murmushi tayi ta maida kallonta kan Aliya dake ta share hawaye tace "Kawata Aliya dan Allah ki yafemin sharrin shaidan ne kinsha yimin nasiha akan in gyara halina nikuma sai nake ganin baki waye ba yar kauye ce ke Ashe kece wayayyar dan akan hanya kike nikuma na kauce hanya kawata dan Allah ki yafemin abinda nayi miki ki dubi irin zaman da mukayi abaya kafin shaidan ya fara kad'a min ganga"

Aliya da Sauri ta matsa kusa da Zara ta rufe mata baki cikin tsananin tausayin Zara tace "na yafe miki kawata Allah ya yafemu gabad'aya"

Ameen Zara tace ta kalli inda su Mommy Hauwa suka tsaya cirko cirko suna share hawaye tayi murmushi tace "Mommyna Daddyna pls Ku yafemin abinda nayi muku kuyi min addua naji dadi araina"

Mommy Hauwa kasa magana tayi sabida kukan dayaci karfinta Dr kuwa ya daure cikin zubar hawaye yace "Na yafe miki 'yar albarka Allah ya yafemu gabad'aya Allah ya miki albarka ya saukeki lafiya insha Allahu bazaki mutu ba mamana zafin nakuda ne"

Zara murmushi tayi ta kalli yayenta ta kalli Khalid da Aunty Khadija ta sakar musu murmushi ta maida kallonta kan Adnan dake ta kuka kamar zai shidde dan bai san meyesa wani irin tsoro ke shigarsa ba duk Kalmar dake fitowa daga bakin Zara tsoratashi yake dan tamkar mutuwa zatayi sunan shi data kirane yasa yayi Sauri ya sunkuya kusa da gadonta yace "Zara pls ki daina irin wanan maganar bazaki mutu ba insha Allahu zamu raini abinda muka Haifa tare zamu haifi wasu 'yayan kin manta kinsha cemin dani kika dace Aliya da Ameer ta dace kinga yanzu aure zasuyi kema idan kin haihun sai a d'aura mana aure pls karki tafi ki barni a lokacin danakeso mu gyara rayuwarmu muyi tsarkakkakiyar rayuwa.

Zara cijje leb'enta tayi cikin tsananin azaba tace " Adnan munyi kuskure daga ni har kai kayi ta istigifari kana neman yafiyar Allah na yafe maka sabida nima inaso Allah ya yafemin idan na mutu kayi ta min addua ka fad'awa abinda na Haifa kaddara ce tasa yazo duniya ta wanan hanyar karka manta dani a adduarka naji dadi da kaima ka gane gaskiya kamar Yanda nagane gaskiya"

Sallati tasa sakamakon wani azabar ciwon marra daya murd'ota gadan gadan taji kan baby ya taho inda Likita ya koresu gabad'aya daga d'akin Mommy Hauwa kuwa ta k'afe akan bazata fita ba.

Likitan yana k'ok'arin saka hand glove Zara tayi nishi da k'arfi kan baby yafito.

Da Sauri likita ya taimaka mata ya fito da babyn inda Babyn ya fito ba rai sabida wahalar da shima ya sha aciki.

Zara kuwa wani irin jini ne ya yanke mata mai gudaje manya manya kafin a Ankara Jini yafara biyo wa ta kasan gadon.

Likita a. Rude ya mik'awa nurse gawan baby boy d'in yayi kan Zara dan ya tsayar da jinin amma ina sai bulbulowa yake .

Zara sallati kawai take Mommy Hauwa na sallati a gigice.

Likita a rude ya aiki nurse akan ta hado mishi allurai inda kafin Nurse din ta bar d'akin Zara ta fara wani irin jijjiga.

Mommy Hauwa aguje taje ta rik'eta Tana sallati.

Zara kuwa ta rik'e mata hannu gam Tana Sallati a can ciki a hankali ta fara rage rukon da tayi mata a hankali Mommy Hauwa kuwa ta ware idonta Tana kallonta cikin tsananin fad'uwar gaba.

Zara murmushi tayi mata tace "Mommy zan sha ruwa"

Aguje mommy Hauwa ta bar d'akin dan ta d'auko ruwan inda fitowarta yasa gabad'aya su Dr suka mik'e suna tambayarta abinda ya faru ta haihu kuwa.

Daga Ameer Adnan har Aliya a rude suke.

Mommy Hauwa bata tsaya kulasu ba ta kinkimi ledan pure water guda tayi d'akin da gudu.

Kasa hakuri sukayi suka bi bayanta dukansu .

Inda dai dai lokacin da Mommy Hauwa ta shigo d'akin likita yaja Zani ya rufewa Zara fuska.

Dukansu sai da kirjinsu ya buga suka zubawa likitan ido.

Mommy Hauwa kuwa ta saki ruwan ta nufi wajen Zara a guje ta bud'e zanin.

Wani irin Razanann k'ara Mommy ta sa tare da kiran sunan Zara.

Adnan kuwa ya zub'e a k'asa a sume.

Dr shima zubewa yayi a kasan .

Inda gabad'aya aka rude da sallati.

Likitan kuwa yayi sauri yabar d'akin sabida tausayi.

"Innalilahi wa inna ilahi rajiun watarana haka zamu tafi inda Zara ta tafi ko yau ko gobe ka shirya baka shirya ba dole ka tafi Domin Kulli nafsi za'ikatul maut pls dis page should increase our iman Allah yasa mudace duniya da lahira ameen.Aunty Khadija da sauri ta nufi wajen Mommy Hauwa data kankame Gawan Zara bayan ta bud'e mata fuska tana "Zara ya zaki min haka Ashe mutuwa zakiyi shiyasa kikace min ruwa zaki sha Mutuwa meyesa baki d'aukeni kin bar Zara ba" +

Kuka take sosai tana jijjiga Zara tamkar wacce take Bacci fuskarta Tayi fayau da haske.

Aliya kuwa kamar sumewa tayi na wucin gadi dan Gawan Zara kawai ta zubawa ido Hawaye na zubo mata gani take kamar Zara bata mutu ba dan idonta har wani gizo yake mata kamar Zara tana numfashi.

Ameer kuwa sallati kawai yake jikinsa na rawa daga inda yake tsaye take ya fara tuno lokacin da ya had'u da Zara da irin Soyayyar da sukayi da fara'arta dan bazai manta ba Auduga abokanansa ke ce mata sabida yawan fara'ata ko kad'an tunanin mugayan Halin Zara basu darsu a Zuciyarsa ba illa ma kyawawan Halinta daya rinjiyeshi ya aureta a hankali ya runtse idonsa shima hawayen tausayin Aliya na zubo mishi yana zabga mata addu'a.

STORY CONTINUES BELOW

Nurses d'in da suka shigo dan su baiwa Adnan da Dr taimakon gaggawa suna d'an yayyafa musu ruwa suka farfado.

Inda Dr yafarka da sallati yana zabga wa Zarah addu'a jiyake inama ace shi mutuwa ta d'auka ba Zara ba.

Adnan kuwa Zumbur ya mik'e bai ko ji nauyin da kansa ke masa da jirin dake d'ibansa ba ya nufi wajen Gawan Zara jikinsa na wani irin k'yarma tsoron Allah na shigarsa ko ta ina Addu'a yake yi Allah yasa Zara dogon suma tayi ba Mutuwa ba.

Tsugunna wa yayi a bakin gadon ya janye rufin Zanin daga fuskar Zara.

Mommy Hauwa da Aunty khadija da ta Dade da maidata gefe tana tausarta tana gayyato mata duk wani d'auriya a matsayinta na uwa akan ta d'aure sabida sauran yayanta kar ta d'aga musu hankali sabida irin kukan da take karta manta kowane rai sai ya dandana mutuwa Ba kuka ya kamata tayiwa Zara ba addu'a ya kama ta tayi mata inda kamar da remote take controlling d'in ta Dan take ta fara rage kukan da take yi ta fara sallati a zuciyata ta fara duk adduar da yazo bakinta Adnan Suka zubawa ido daya tsugunna agaban Gawan Zara yana bud'e fuskarta mommy Hauwa tayi sauri ta kau da kanta wasu sababin hawayen na kara bulbulo mata gani take kamar Mafarki take wai Zara ta mutu Zaran da take adduar Allah ya bata dama tayi tsaftaciyar rayuwa dan a yanzu ta fito daga duhu zatayi rayuwa a haske a yanzu ne Zara zata san rayuwa ta san mai take yi sai gashi Allahn daya bata Zara ya k'arbi abunsa.

Adnan kuwa kallon Zara kawai yake kirjinsa na sama da k'asa hawaye na zubo mishi ya kasa yarda wai Zara ta mutu a tsakiyar lokacin da yake bukatar ta kuma ta mutu ta sanadiyar cikin daya mata runtse idonsa yayi da k'arfi daya tuno shine sanadin shigarta koma mai tayi dan da bai taka k'afarsa ya shiga b'angarensu ba babu Yanda za'ayi har Zara ta kauce hanya da babu Yanda za'ayi tak'i zaman aure har tayiwa mijinta biyayya banda dan banzan wahalar da ya bata ya mata sanadin mutuwar Aurenta ga dan banzan dukan da ta ringa sha a hannunsa cima ta arziki babu banda wulak'anci da ya ringa zuba mata sai gashi a lokacin daya gane gaskiyar abinda yake aikatawa yazo dan ya gyara kuskurensa ya biya mata bukutar ta da ta Dade tana mafarkinsa na hanyar Suyi Aure sai gashi Zara ta tafi mutuwa ya d'auketa ta bar shi da mugun nauyin da har ya mutu bazai daina jinsa ba dan bazai iya yafewa kansa abubuwan da yayi mata ba wani irin kuka ya fashe dashi yana "Zara meyesa kika tafi a lokacin danake bukatarki meyesa baki bari munyi aure munyi tsaftaciyar rayuwa ba kika tafi kika barni ni d'aya abun da kika Haifa da zan ringa gani ina tunaki ma ya biki kuka barni ni kad'ai Alhalin banida sama daku yanzu da wa kukeso nayi Rayuwa Zara inama Mutuwa tare ya d'auke mu muje muyi rayuwarmu acan Zara dan Allah ki tashi dan nasan bazaki min haka ba bazaki tafi ki barni ba Wlh na gane kuskurena bazan k'ara zallintarki ba nima Allah ya shiryeni nagane abubuwan da nake yi basu da kyau "

Adnan kuka yake sosai har yana shid'ewa numfashinsa na d'auke wa .

Mommy Hauwa kuwa girgiza kanta kawai take yi tana sallati dan ita kad'ai tasan mai takeji.
Dr kuwa waje yayi duk da jiyake kamar iska zata d'auke shi ahaka yaje ya zauna acan nesa da asibitin yasamu waje ya zauna yafara Rusa kuka kamar wani k'aramin yaro dan yaji mutuwar Zara fiye da tunanin mai tunani dan kaf cikin 'yayansa yafi santa dan sunan mahaifiyarsa da taci da kamanin da suke da ita mutuwar Mahaifiyarsa dawowa yayi sabo fil a zuciyarsa inda kukan ya zame masa guda biyu na nadamar abubuwan da ya aikatawa Mahaifiyarsa da yafiyar ta da bai samu ya nema ba har ta mutu har gwara Zarah ita ta nemi yafiyarsa shi fa da har Mahaifiyarsa  ta mutu  bai nemi yafiyar ta ba da kila har ta mutu da bakincikinsa a ranta inama shima yasamu damar da 'yarsa ta samu haka kawai ya danganta duk abubuwan da yayi ne Allah ya jarrabce shi ta silar 'yarsa.

Ahaka Dr ya zauna yana ta kuka har mutane Suka taru suna kallonshi.

*Juma'atul Babbar Rana*

Ana saukowa daga sallar Juma'a akai kai Zara gidanta na gaskiya da rakiyar dubanin mutane dan har babu hanyar wucewa inda Ameer adnan da Dr sune kusan mutanen Na karshe da aka bari inda Suka tsaya suna ta jera mata addu'oi  Dr kuwa sai tsiyayar hawaye yake yi Ameer kuwa shima sai da hawayen suka zubo mishi Na Tausayin Zara da tsoron Allah daya shige shi wai Zara yar gayu wayayya da komai nata classic ce yau a kwance k'asa ya rufe mata ido duk san da danginta suke mata da abokanan arziki gatan da zasu mata a wanan lokacin shine addu'a yanzu suma zasu tafi su barta shikenan sai dai kuma ayi labarinta Lailai rai ba abakin komai yake ba da ace mutane zasu gane da basu tsaya batawa Kansu lokaci wajen neman duniya ba tunda koman daren dadewa ko ka k'i ko ka so dole zaka barta.

Adnan kuwa  sai da aka binne Zara ya k'ara jin wani irin tsoron Allah na shigarsa daya tuna tare fa Suka ringa sab'awa Allah sai gashi ita ta rigashi mutuwa gani yake mutuwa na iya d'aukarsa shima a kowane lokaci.

Da k'yar Ameer yaja Adnan suka bar wajen inda Suka koma suka cigaba da amsar gaisuwa.

Cikin gidan ma Acike yake tap har babu wajen zama acikin 'yan zaman makokin ma har da Aliya dan ko gida bata koma ba sabida yanda mutuwar Zara ya shigeta kuka kawai take tana zubawa Zara adduar dacewa da rahamar ubangiji dan ba Laifi Zara tana da saukin kai da dadin Zama.

Sai wajen k'arfe biyar Na yamma Aliya ta fito daga gidan dan Ameer ya maidata gida inda Suka kuma yiwa su Mommy Hauwa gaisuwa da Dr da  Zazzabi  ya rufeshi tunda Suka dawo Mommy Hauwa kuwa ko magana bata yi ballantana ta amsa gaisuwar da ake mata.

Adnan kuwa ganin Su Ameer zasu tafi Har Aliya tayi wajen motar ta tsaya yasa ya mik'e yabi bayan Ameer idon nan nasa yayi jajir banda wani irin ciwon kai dayake yi na b'ari d'aya.

Adnan cikin muryarsa da baya fita yacewa Ameer "Dan Allah Dan uwa Ka yafemin abinda nayi maka nabi san zuciyata Na sab'awa Mahallicina naci amanar mak'otaka Ka dubi girman Allah ka yafemin Ku biyun nake so na nemi yafiyarku ko na d'anji nauyin da zuciyata ya min ya ragu"

Ameer da Sauri yace "karka damu Adnan na Dade da yafe maka banaso ma Ka ringa yin maganar nan sabida wacce kuka sab'awa Allahn da ita ta Riga mu gidan gaskiya Ko ban tambayi Aliya ba nasan itama ta yafe maka fatan mu Allah ya kara shiryaka kaje kayi ta istigifari kana neman yafiyar Allah mutuwar da Zara kawai tayi ya isa ya zame maka ishara Allah ya jikanta da rahama".

" Ameen"  Suka ce atare  Adnan kuwa ya juya ya kalli Aliya yana k'ok'arin magana Aliya ta d'aga mishi hannu tace "Ba sai kace komai ba Adnan na yafe maka duk abinda kayi min Allah ya yafemu gabaki d'aya"

Daga haka ta bud'e motar ta shige.

Adnan kuwa ya ringa zubawa Ameer godiya yana tsaye har sai da Suka tafi inda Hawaye masu dumi Suka kara zubo mishi Na nadamar abubuwan da yayi yau gashi babu Aliya babu Zara babu dangi kusa take tunanin komawarsa Maiduguri ya k'ara darsuwa aransa inda ya yanke ana Yin sadakan bakwai d'in Zara zai koma Maiduguri ya fara neman yafiyar yayansa kafin yaje Niger fatansa dai Allah yasa su yafe mishi.

Ahaka ya koma suka cigaba amsar gaisuwa sai da akayi isha  ya shiga gidansu Zarah ya k'ara yiwa matan gaisuwa ya koma gidan Safwan tare da wani irin zazzafan Zazzabi.

B'angarensu Aliya dinner da basu je ba kenan ita da Ameer  dan har gwara Ameer ya d'an fi Aliya dauriya duk da Zara tsohuwar matarsa ce Aliya kuwa dayake mace ce tana da rauni haka ta kwana sukuku babu walwala in banda tunani da adduar da take jerawa Zara dan Ameer har mamakin Yanda Aliya ta d'aga hankalinta yake akan mutuwar Zara sai iya Summayya ce taje dinner  da aka had'a musu da angonta.

Washegari k'arfe goma sha d'aya aka daura Auren Ameer da Aliya Sumayya da Angonta Nura  ana gama daura Auren Ameer ya kuma komawa gidansu Zarah ya kara yiwa su Mommy Hauwa gaisuwa da Dr har da Adnan da ya zama wani irin silent da fuskarsa kawai zaka kalla tsantsar tausayinsa  ya rufeka.

K'arfe biyar Na yamma aka mik'a amare gidajensu inda aka kai Aliya katon gidanta dake  'yankaba upstairs har yanzu mutuwar Zara bata saketa ba dan in banda kuka babu abinda take yi haka kawai take ganin kamar taci amanar Zara da ta aure mata miji.

Ameer kuwa tuni mutuwar Zara ta sake shi  farincikin Auren Aliya ya mamaye mishi Zuciya Na irin tanadin da yayi wa rana irin ta Yau na Mallakar Aliya.

Ango bashi ya shigo gidan ba sai da kowa ya watse da fara'arsa ya shiga gidan da ledojinsa amma tozalin da yayi da fuskar Aliya daya kumbura sabida kukan data sha yasa jikinsa wani irin sanyi zama yayi a gefenta ya jawo ta ya rungume ta sabida ya rarrasheta inda Aliya tayi saurin janye jikinta haka kawai tana jin kamar tana ta cin amanar Zarah.

Ameer kuwa dayake wayyaye ne komai nashi a tsare yake a ilimance ya kuma san yanda zai bi da amaryarsa a hankali yafara kwantarwa da Aliya hankali har ya samu ta saki jikinta dashi inda suka gudanar da duk abinda Amarya da ango sukeyi na nafilfili da sauransu awajen kwanciya Aliya taso bijire masa dan kuka take bil hakki tana CE mishi bazata iya cin amanar Zarah ba amma dayake Ameer a matse yake ya dade rabonsa da mace tuni yayi duk wata dabararsa da duk salon daya sani a matsayinsa na  namiji  har ya samu ya mallaki Amaryarsa daya jita tamkar buduruwa sosai ya samu nutsuwa da Aliya inda wani irin bacci mai balain dadin gaske yayi awon gaba dasu...A ranar da akayi sadakan bakwai d'in Zara gidan Dr a cike yake tap da jama'a tamkar a ranar akayi rasuwar inda makusantar Zara mutuwar Zara ya kara dawo musu sabo fil tamkar a ranar tarasu amma ina kwananta bakwai yau da k'asa ya rufe mata ido wanda ahankali Zara ta fara Zama tarihi sai dai ayi labarinta.

Ango Ameer da Amarya Aliya suma sai da suka zo Sadakan bakwai inda Aliya tozali kawai da tayi da gidan sai da hawaye ya hau zubo mata da kuwa ta shiga cikin gidan ta zauna a cikin jerin wayanda suka zo gaisuwa sai da ta fashe da kuka data ga ana fito da kayan Zaran waje sabida  za'a kyautar da wasu za'a kuma akai wasu  gidan marayu.

Mommy Hauwa kuwa har lokacin Azumin magana take duk da zuwa lokacin ta bar zubar da hawaye a fili sai dai a ciki yatsunta kuwa wani irin zafi suke mata sabida Yanda take Jan carbi babu dare babu rana harshenta kuwa kullum cikin ambaton Allah yake da addu'ar samun rahama ga 'yarta.

Dr kuwa har lokacin bashida cikakken lafiya dan ko k'adan baya iya zama sabida rashin kwarin jiki kallo d'aya zaka mishi tausayinsa ya rufeka.

Adnan kuwa da tunda akayi rasuwar bacci kawai ke maidashi gida da sassafe yake dawowa gidansu Zara.

Shima kana ganinsa zai masifar baka tausayi sabida ko kad'an idonsa baya rabo da hawaye banda wani irin tsoron Allah dake hud'a shi duk kwanan da zai yi ya tashi shima bakinsa kullum d'auke yake da isitigifarin abubuwan da ya aikata komai na duniya ya fice masa arai babu abinda yake sha'awa arayuwarsa yanzu sama da gyara Lahirarsa da sauran lokacin da yake dashi abinda ke d'ad'a d'aga mishi hankali bai wuce wayar garin da yayi da  kaikaiyin gaba ba  dan kamar yayi k'aramin hauka idan yafara  mishi kaikai sai ya samu kusan minti talatin yana Sosa gabansa  kafin kaikai yin ya lafa mishi kuma ko kad'an babu alamar kuraje agaban nashi ahaka ake zaman makoki dashi yana yi yana tashi sabida yayi susa  yasan koma menene cuta su Ajjidde suka saka mishi dan dama yasan za'a rina sabida yawan mazan da take mu'ammalla dasu idan shima jarrabtar da Allah zai masa kenan a gidan duniya zai amshe shi da hannu bibiyu har Allah ya bashi ikon cin jarrabawar idan kuma cutar ta zame masa Ajali addu'arsa a kullum shine Allah yasa ya dace da rahamar  ubangiji. 2

Koda lokacin dasu Aliya suka zo da Ameer gidansu Zara  akan idonsa ne  da kallon sha'awa ya bisu yana inama shi yake da kwanciyar hankalin Ameer ba tare da fargabar komai ba inama shi yasamu yayi ingantaciyar da tsaftataciyar rayuwar da Ameer ke yi ko da bakasan Ameer ba kasan  hankalinsa a kwance yake dan banda bud'in arziki dayake ta samu ga mace tagari da Allah ya bashi ga wani haske da Annuri dake fita a jikinsa baya mantawa ada bala'in kauyancin Ameer yake gani amma a yanzu Ameer shine ya zame masa abun sha'awa da kallo Aliya kuwa dama bama zai soma kallonta ba dan ta yi mishi mugun nisa sai dai hange daga nesa.

Akan idon shi Aliya ta k'ara fitowa daga gidansu Zara Ameer dake cikinsu a zaune ya mik'e ya mimik'a musu hannu tare da addu'a ga Zara ya nufi wajen motarsa ya bud'ewa Aliya suka tafi.

STORY CONTINUES BELOW

Adnan hawaye ne suka ciko masa a ido ya kara sharewa ya kara maida kansa ya sunkuyar ya cigaba da Jan carbinsa a hankali yafara jin kaikai na taso mishi tun yana d'aurewa yana sallati sai da ya mik'e da Sauri ya nufi band'akin dake boys quarters d'in gidan dan wani azabar kaikai gabansa ke masa.

Da hannu bibiyu yafara sosawa yana kuka dan har jiwa kansa ciwo yake yayi agarin sosawa sai da ya lafa masa ya fito d'aga band'akin yana jin azabar rad'adi.
1

Yana gidansu Zara har akayi sallar Ishai inda suna dawowa daga Massallacin aka fara fito da abinci kamar Yanda aka saba dan suci amma ko kallon abinci baiyi ba dan dama bayaci bazai iya tuna rabonsa dayasa abu a bakinsa ba dan Sam bashida kwanciyar hankali.

Ana fara cin abincin ya tashi ya shiga cikin gidan inda suka kusa karo da Khalid daya fito dan ya kai musu ruwa.

Sai da Khalid ya kai ruwan ya dawo ya same shi atsaye batare da b'ata lokaci ba yace dan Allah ya mishi iso cikin gidan yana san ganin Mommy Hauwa da Dr dan idan ya tafi yau bazai sake dawowa ba sai za'ayi sadakan arba'in idan dai yana da Nisan kwana.

Khalid ce mishi yayi yana zuwa ya fad'o musu inda yaje ya samu Mommy Hauwa data k'unshe kanta a d'aki ita kad'ai tana zaune akan Sallaya idonta a rufe tana Jan Carbi kamar dai Yanda ta sab'a tunda akayi rasuwar.

Bata ko d'ago ta kalli Khalid daya gaya mata sakon Adnan ba har sai da ya kara maimaitawa.

Inda Mommy Hauwa ta mik'e Khalid yabi bayanta dan bashida burin daya wuce yau yaji Mommy Hauwa tayi magana dan rashin maganarta na damunsu tun a asibiti data yi magana bata k'ara magana ba.

Haka ya ringa binta a baya har sai da ta shiga palon da Dr yake a kwance shima yana rik'e da nashi carbin.

Ta samu guri ta zauna Khalid na ganin haka yagane mai take nufi yayi waje ya yiwa Adnan iso har palon.

Sai da Adnan ya zauna a k'asa Khalid ya fice.

Inda Adnan yayi k'asa da kansa sosai yana k'ara yiwa Mommy Hauwa gaisuwa da Dr.

Dr da muryarsa bata fita sosai ne ya amsa.

Mommy Hauwa kuwa ta ringa gyad'a kanta tana kallon shi can k'asan ranta tana mai bala'in tausayin shi dan tana ganin idan aka d'auke ita da Dr babu Wanda yaji mutuwar Zara kamar Adnan ko wayanda suke jini d'aya basu ji mutuwar ta haka ba.

Adnan cikin rawar murya yace "Daddy Mommy zuwa nayi na nemi yafiyarku akan abinda na aikatawa Margayiya dan Allah Dan annabi ku yafe min wlh sharrin shaidan ne na kuma yi nadamar abinda na aikata bantab'a sanin"""

Mommy Hauwa ce tayi saurin d'aga mishi hannu hawaye na zubo mata ta bud'e bakinta dayayi bala'in yi mata nauyi sabida maganar da batayi ba kwana biyu tace "Adnan baka yi mana komai ba wacce kake neman yafiyarmu akanta ta Riga da ta Riga mu gidan gaskiya fatanmu Allah ya gafarta mata yayi mata rahama banaso na tuna wani abu da Zara tayi illa ma na ringa tuna ta da alheri ina mata addu'a dacewa da rahamar Allah kai ma ina mai baka shawara kaje kayi ta neman yafiyar Allah kana istigifari ka kuma nemi yafiyar wayanda ka b'atawa kayi amfani da damar da kake dashi ka kusanci Mahallicinka dan mu muke ganin muna da lokaci amma lokacinmu kalilan ne dan kana rayuwa ne baka san lokacin da mutuwa zata d'auke ka kamar Yanda Zara ma ban tab'a kawo mata mutuwa kusa ba Ashe mutuwa na tafe mun yafe maka Allah muma ya yafe mu gabad'aya".

Zuwa wanan lokacin Mommy Hauwa Dr da Adnan kuka suke sosai da hawaye suna jin wani iri a zuciyarsu Inda wani irin fargaba da Nadama ya rufe Dr da Adnan Dr shi yana nadamar abubuwan da yayi wa Mahaifiyarsa Adnan kuwa na nadamar abubuwan da ya aikata.

Adnan godiya ya ringa musu sosai inda Mommy Hauwa da Dr suka ringa binshi da addu'ar har ya tashi yatafi.

A ranar Adnan ko kad'an bacci bai d'auke shi ba sabida matsuwa da yayi gari ya waye ya d'auki hanyar Maiduguri dan Gabad'aya hankalinsa ya koma can burinsa ya gansa agaban Mahaifiyarsa ya nemi yafiyarta Dana yayansa Anwar dan yanzu wajen shekara biyu da rabi rabon shi dasu hankalinsa kan tashi idan ya tuna Yanda Mahaifiyarsa ke damuwa akan shi.

STORY CONTINUES BELOW

Da Asubar fari ya d'auki hanyar Maiduguri bayan doguwar addu'ar daya yi na Allah ya sauke shi Lafiya.

K'arfe biyar na yamma ya isa Maiduguri inda duk guraren daya sani suka cacanja mishi sabida sababin gine ginen da akayi.

Machine ya hau dan ya kai shi Family House d'insu dake can idan ya huta sai yaje gidan Yayansa Anwar ya nemi yafiyarsa ya kuma rok'eshi akan ya raka shi Niger wajen Mahaifiyarsa dan babu Yanda zaiyi ne da a yau zai je Niger dan babban Burinsa yanzu yayi tozali da Mahaifiyarsa ya nemi yafiyar ta.

A lokacin da ya isa Family house d'in Nasu da  Cousin din Mahaifinsa ke Zaune a ciki da 'ya'yansu bai gane gidan ba sabida mugun canza shin da akayi ya dawo na birni ginin 'yan gayu dan bene aka maidashi banda wasu irin fitilu daya haska gidan  tuni  ya shiga tashin Hankali dan yana tunanin siyar da gidan akayi suka tashi sai da yayi tambaya akace basu tashi ba suna nan hankalinsa ya kwanta.

Jiki a sanyaye ya shiga cikin harabar gidan inda kansa ya k'ara d'aurewa dan shima cikin gidan an canza shi ya zama part part jiki ba kwari ya nufi part d'in da yake jiyo maganganun mutane A bakin k'ofa ya tsaya yafara rafka Sallama da k'arfi sabida su jiyo shi.

Inda kawun shi Abdullahi ya amsa tare da nufo k'ofar dan sam bai gane shi ba cike da nauyi da jin kunyar gudarsu da yayi ya zube a kasa yana gaishe shi.

Inda kawu Abdullahi ya amsa yana so ya tuno inda yasan muryar shi dan sam bai gane wanan siririn mutumin da gashi ya cika mishi fuska ba.

Ganin wahalar da kansa kawai zaiyi ba iya gane shi zaiyi ba yasa yace "Bawan Allah Daga ina wa kake nema"?

Adnan cike da fargaba da tsoro cikin inina yace " Kawu nine fa Adnan"

Kawu Abdullahi waro ido yayi cikin tsananin mamaki yaja da baya da Sauri yace "Wane Adnan d'in Adnan dai Dana sani"?

Adnan da Sauri ya gyad'a kansa hawaye na sauko mishi yace " Nine Kawu"

Sallati Kawu Abdullahi ya rafka yana tafa hannuwa yana "kai Mai ya sameka haka cuta kayine ko yaya"

Adnan kuka ya fara yi ya kasa magana inda sallatin da yayi ne yasa mutanen cikin gidan suka fara firfitowa suna tambayar Kawu Abdullahi Lafiya waye wanan d'in?

Sai da Kawu Abdullahi ya gama rafka salallami ya iya fad'a musu Adnan ne inda dukansu suka hau tafa hannaye suna mamakin sabon Adnan d'in dake gabansu da bashida maraba da mai cutar kanjamau sabida rama dan tsohon Adnan dan gaye ne na fitar hankali gashi dan dumur dumur wanan kuwa kamar kayi bulala dashi.

Matar kawu ce tayi k'arfin cewa ya shigo Daga ciki inda ganinsa da sukayi yasa suka tuno da Asmau Mahaifiyar Adnan  da ta rasu watani uku da suka wuce inda hawan jini yayi ajalin nata sabida yawan tunanin Adnan da take yi da sa shi da tayi aranta wani kaddara ma kaf cikin yayan nata tafi san shi babu irin kasashen da Anwar da ya zama fitaccen d'an siyasa bai kaita ba dan kawai ta ringa rage tunanin Adnan Amma hakan ya faskara dan musamman ya k'ara nadar k'afa yaje neman Adnan dan kawai ya farantawa Mahaifiyar tasu dan ba dan ita ba ko kad'an babu abinda zai sa ya Kara waiwayar Adnan sabida ma irin wulak'anci da ya mishi dayaje kano dan ya bashi shawara akan ya daina wulak'anta Mahaifiyar su ya ringa zuwa yana ganinta.

Inda sai daya samu kwana biyar a kano yana jigilar neman Adnan sabida wasu ne a gidansu Adnan.

Akan dole ya koma Maiduguri inda Jikin Mahafiyarsu ya rikice dataji labarin ba'asan inda Adnan yake ba ahaka jininta ya ringa hawa Kullum tana kuka inda Anwar da Aliyun daya zama fitaccen dan kasuwa suka ringa iya k'ok'arinsu  dan su kwantar mata da hankali kowane na iya k'ok'arin yaga ya faranta mata rai amma a Banza dan ta Riga da ta sa Adnan a ranta.

Ahaka ta ringa fama da rashin lafiya tana rokon a nemo mata Adnan inda wanan karon Aliyu shi yazo kano dan ya nemi Adnan Amma shima Sam bai ko samu labarinsa ba ahaka ya hakura ya koma yace mata yasa a nemo shi ta kwantar da hankalinta Adnan zai zo.

STORY CONTINUES BELOW

Amma ina dawowar Aliyu kamar kara mata rashin lafiyar yayi sabida gani take kawai B'oye Mata suke yi Adnan ya mutu.

Tunda ya dawo jikin nata ya rikice inda suka kaita Egypt dan a duba lafiyarta Anan Allah ya amshi ranta suka dawo gida da mugun bak'in cikin rasa Mahaifiyar su Inda suka ji tsanar Adnan a ransu dan a tunaninsu a sanadinsa Suka rasa Mahaifiyar su Anan kowane ya yanke koda sunga Adnan ya dawo musu sai sun kore shi dan ba jininsu bane shi Aminatu ce kawai bata yi fushi da Adnan sosai ba sabida raunin da take dashi.

Adnan da ido ya ringa binsu dayaga suna share hawaye a b'oye kawu Abdullahi kuwa ya sunkuyar da kansa.

Adnan gabansa ne yayi bala'in fad'uwa ya zubawa Kawu ido yana k'ok'arin magana kawun ya d'ago da kansa yana "Adnan ina ka shige duk tsawon lokacin nan aka ringa nemanka Adnan kasan tun lokacin da kazo akan aje a nema maka Auren matar da ka aura baka kara zuwa gida ba  ko waya baka tab'a bugowa ba meyesa kayi haka duk muna nan hankalinmu ya tashi muna tunanin ko wani abune ya sameka"

Adnan cikin tsananin nadama hawaye na zubo mishi yace "Kuyi hakuri kawu nayi kuskure fatana dai Ku yafemin yanzu ma so nake Ku kwatanta min gidan yaya Anwar shima naje na nemi yafiyar sa gobe ya rakani Niger naje naga Umma itama na nemi yafiyar ta Dan nasan na mata ba dai-dai ba fatana itama Allah yasa ta yafemin Kawu dan Allah"""

Shiru yayi cikin fad'uwar gaba dayaga suna share hawaye suna sunkuyar da Kansu ciki kuwa har da Kawu da kana ganinsa kasan hankalinsa a tashe yake.

Jikinsa ne ya fara rawa cikin inina yace "Kawu lafiya mai yake faruwane ko wani abun ne yasamu Umma"?

Kawu d'agowa yayi hawaye na zubo mishi yace " Adnan ka makara zuwa neman  yafiyar Mahaifiyarka dan yau wata uku da kwana shidda kenan da rasuwar  Mahaifiyarka"

Adnan numfashinsa ne ya d'auke na wucin gadi maganar Kawu ya ringa amsaaa kuwaa a kunensa kansa na wani irin Sara mishi.

Luuuu ya tafi zai fad'i Kawu yayi Sauri ya tare shi

Adnan kuwa yayi amfani da d'an karfin daya rage mishi yace cikin wani irin murya mai ban tausayi "Kawu dan Allah kace min wasa kake yi Ummana bata mutu  ba ina zan saka raina idan ta mutu ta yaya zata yafemin bayan ta mutu ta yaya zan bauta mata a matsayinta na gatan data rage min Innalillahi wa inna ilahi rajiun kawu ina zan saka kaina kawu ya zanyi idan da bak'in cikina Umma ta mutu kawu meyesa a yanzu Dana gane kuskurena nayi nadamar abubuwan danake aikatawa nake bukatar addu'ar ta zata mutu"

Adnan kuka yake sosai kamar zai shidd'e hankalinsa na neman gushewa sabida tsananin tashin hankali dan abinda yake ji aransa bai ji ba a lokacin da Zara ta mutu ko Dan ya nemi yafiyar ta ne amma Mahaifiyar sa data kawo shi duniya bai samu ya nemi yafiyar ta bar har ta mutu k'ila ma da bak'in cikin sa ta rasu..

Adnan kuka yake sosai yana istagifarin halin da yake ciki dan bai san makomarsa ba idan Mahaifiyarsa bata yafe mishi ba har ta mutu.

Kawu ne ya ringa kwantar masa da hankali akan ya ringa yiwa Mahaifiyar sa addu'a insha Allahu tama yafe mishi.

Tuni wani irin Zazzabi ya rufeshi da ya ringa tunanin shima mutuwar kawai zai yi banda azababben kaikain daya sako shi agaba.

Tuni su Kawu suka rufu akansa inda Matar kawun tayi saurin latso lambar Anwar ta fad'a mishi Halin da suke ciki tsaki yayi yace mata  babu ruwansa da Adnan ko da mutuwa zaiyi Daga haka ya kashe wayarsa.

Ga mamakinta kamar had'in baki data kira Aliyu shima kamar Yanda Anwar yace shima yace mata.

Bata hakura ba ta kira Aminatu ta fad'a mata halin da ake ciki abunka da mace da zuciyarta keda rauni tuni hankalinta ya tashi  tace su taimaka mata su bashi duk taimakon da zasu iya gobe zata zo dan yanzu dare ya Riga da yayi.

STORY CONTINUES BELOW

Tana kashe waya ta kira 'ya'yyenta dan ta d'auka basu Sani ba amma ga mamakinta duk tsaki suka yi suka kashe wayar .

Adnan sai da ya samu kwana uku a kwance in banda kukan nadama babu abinda yake yi yabi ya kara ramewa yanzu har da cokali yake Susa sabida kaikaiyin da gabansa ke masa karuwa kawai yake.
1

Aminatu kuwa kullum sai tazo dubashi banda hidindimun da take mishi .

Adnan hankalinsa ne ya kara tashi daya ga ya samu kusan sati d'aya a Maiduguri amma Yayansa Anwar da Kaninsa Aliyu babu Wanda ya zo inda yake inda take jikinsa ya kara sanyi dan yasan ba k'aramin fushi sukayi dashi ba.

Washegarin daya samu kwana takwas a Maiduguri ya dage sai an raka shi wajen Yayansa Anwar dan Sam bashida wani kwanciyar hankali gwara ya nemi yafiyar Anwar ko zai d'an samu sauki a zuciyarsa.

Tashin hankalin da ba'a samishi rana.

A lokacin da Adnan ya isa gidan Anwar k'asa rufe bakinsa yayi sabida daular da  yayan nashi yake ciki dan gidansa kamar gari guda ga wani shima babban gida da ya ginawa Almajirai kawai suna kwana a ciki banda girkin da ake musu safe rana dare.

Da k'yar ya samu aka bar shi ya shiga gidan inda masu gadi sukayi tunanin ko masu neman taimako ne kamar Yanda gidan baya rabo da masu neman taimako.

A lambu gidan ya tarar da Anwar da matansa guda biyu 'yay'ansa  shidda a zagaye dasu kana ganinsu zaka san suna cikin kwanciyar hankali da jin dadi.

Anwar ya zama wani d'an lukuti ya zama Alhaji

Adnan gwiwa a tsage cike da fad'uwar gaba ya isa wajensu ya zub'e a k'asa yana musu sallama waigawa sukayi gabad'aya suka amsa inda Anwar bai wani b'ata lokaci ba ya zura hannu a Alhajihunsa ya kirgo dubu goma ya mik'awa Adnan dan duk a tunanin sa masu neman taimakon ne dan Sam bai ma gane Adnan ba.

Adnan kuka ya fashe dashi sabida tsananin takaicin yana "Yaya nine fa Anwar baka gane ni bane nine"

A  fusace Anwar ya mik'e ransa a b'ace ya fara bin Adnan da mugun kallo dan da muryarsa ya gane shi.

Cikin tsananin b'acin rai yace "Waye ya bud'e maka gidnan ka shigo mai had'ina da kai bayan duka abubuwan da kayi har kana da k'arfin halin da zaka zo inda muke a sanadinka Umma ta mutu da bak'in cikin ka ta mutu amma sabida bakada kunya sai data mutu zaka nad'o k'afarka kazo inda muke mai kuma kake nema kafin na kirga biyar ka tabbata ka bar gidanan tun kafin nasa ayimin waje dakai"

Adnan k'ok'arin kamo kafarshi yake Anwar ya janye da Sauri ya fara kwallawa mai gadi kira.

Matansa na k'ok'arin bashi hakuri ya daka musu tsawa akan su b'ace mishi Daga nan jiki na rawa suka bar gurin adai-dai lokacin da mai gadin ya k'araso Anwar kuwa yace ya mishi waje da Adnan kar ya kara barinsa ya shigo mishi gida har waje Anwar ya bisu yana korawa mai gadi warning inda Adnan ya ringa kuka kamar ransa zai fita.

Adnan sai dayaga Maigadi ba kuma barinsa zai yi ya shiga cikin gidan ba yasa ya nufi gidan Aliyun da aka kwatanta mishi.

Yana isa kantamemen k'ofar gidan Aliyu da kana gani kasan naira tayi kuka Aliyu ya shawo kwana a cikin wata 'arniyar motarsa shima ko kad'an bai gane Adnan da bashida maraba da irin masu bara nan ba bai ko kalli Adnan dake tsaye yaba ya fara danna horn.

Adnan kuwa yayi Sauri afara kwankwasa masa glass din mota

Aliyu cikin mamaki ya sauke glass d'insa kasa yana kallon wanan bawan Allah mai k'arfin hali haka.

Adnan hawaye ne ya zubo mishi da kaninsa shima bai gane shi ba

Fuska a yamutse Aliyu yace "Mallam Lafiya zaka zo ka tsaya Min a k'ofar gida"?

STORY CONTINUES BELOW

Adnan girgiza kansa yayi hawaye na cigaba da sauko masa yace " Aliyu kaima baka gane ni ba yayanka ne fa Adnan wai meyesa kuke min hakane mai yayi zafi haka zaku min irin wanan hukuncin dan Allah Ku yafemin nasan nayi kuskure"

Aliyu tsaki yayi ya kara danna horn Adnan kuwa yayi Sauri ya zub'e a k'asa kamar ba yayan Aliyu ba rok'onsa yake sosai akan ya saurare shi amma Aliyu ko kallonsa bai yi ba ya shige cikin gidansa bayan shima yayiwa Mai gadi warning.

Take Adnan ya kara shiga tashin hankali bai hakura ya bar gidan Aliyu ba sai da aka fara kiran sallar Magriba yana barin wajen yaje wajen kanwarsa data rage mishi ya kai kukansa wajenta akan ta taya shi rok'onsu Anwar dan idan basu yafe mishi ba bai san ya zaiyi ba.

Aminatu kuwa har da kukanta ta ringa kwantarwa da Adnan hankali akan zata rok'esu su yafe mishi.

Wasa wasa sai da aka Samu wata da komawar Adnan Maiduguri Yayansa Anwar yak'i ya saurare shi har gwara Aliyu ya sauko sabida tausayin Yayan nasa dan har dashi ake rok'on Anwar yanzu sai da akayi family meeting inda manyan suka saka baki aka Samu Anwar ya hakura.

Adnan kamar zaiyi wa Anwar Sujadda haka ya ringa yi.

Inda take tausayin Adnan ya rufeshi ya d'ago shi ya rungume shi yanajin soyayyar dan uwan nashi na ratsa shi.

A ranar Anwar ya tafi da Adnan gidanshi inda yace ya huta gobe suyi magana.

Haka kuwa akayi washegari bayan sun karya tare Anwar yace ya bashi labarin abinda ya same ya dawo haka .

Adnan ido cike da Hawaye yafara labartawa  Anwar halin da ya shiga da abubuwan da ya aikata babu abinda ya  b'oye mishi ko kad'an a karshe ya tsugunna yana neman yafiyar sa akan Zinar da ya aikata da tsohuwar matarsa inda yake nuna mishi tsantsar nadamar da yayi.

Anwar ya girgiza da labarin da Adnan ya bashi dan ko kad'an bai kawo shaidanci da shu'umancin Adnan ya kai haka ba kasa magana yayi ya cigaba da Kallon Adnan dake ta zubar da hawaye yana tsugunne a gaban shi.

Ahaka ya cigaba da kallonsa wuyan daya sha a hannun Ajjidde yasa tausayin Adnan d'in ya rufe shi yana k'ok'arin magana yaga Adnan ya rufe idonsa da k'arfi ya zaro cokali Daga Aljihunsa yafara Sosa gabansa da iya k'arfinsa yana hawaye. 2

Sallati Anwar yayi ya rik'e hannun Adnan cikin tashin hankali yana tambayarsa da mai haka.

Adnan cikin tsananin kuka da azabar da yake sha ya gaya mishi Halin da yake ciki na kaikaiyin gaban da yake fama dashi tunda Ajjidde da kawayenta suka ringa saduwa dashi.

Inda sabida azabar dayake sha sai da ya cire wandonsa bai sani ba.

Anwar kuwa yayi saurin runtse idonsa sabida Yanda gaban Adnan a koma ya kankance.

Anwar cike da tausayin Halin da Anwar yake ciki jiki na rawa ya kira abokinsa likita dake aiki a Egypt inda ya mishi bayanin Halin da Kaninsa ke ciki.

Abokinsa ya shaida mishi cutar sanyi ne ya janyo mishi kaikaiyin gaba sai an kashe kudi sosai  za'a iya magance mishi matsalar.

Jiki na rawa Anwar yace babu matsala zaiyi processing visa d'insu nan da kwana biyu su taho kudi ba matsala bane fatansa dai Adnan ya warke.

A cikin kwana biyu jirginsu ya d'aga zuwa Egypt suna isa batare da wani b'ata lokaci ba suka isa babban asibitin da za'a d'ora Adnan akan Magani.

Kwararrun likitocine suka duba Adnan inda suka gano cutar da Adnan ke d'auke dashi na mugun cutar sanyi da Idan ba'a magance shi da wuri ba har kashe gaban mazan yake ya daina aiki.

Dayake Anwar ya saki kudi.

Tuni likitoci suka duk'ufa akan Adnan suna d'ora shi akan Maganunguna dan har awani irin engine suke Zura Adnan duk Dan ya samu lafiya.

STORY CONTINUES BELOW

A cikin wata d'aya Adnan yafara samun lafiya duk da kaikayin bai tafi gabad'aya ba sai Hankali.

Adnan garin Egypt ba k'aramin dadi ya mishi ba duk da yayi fari da fresh amma hakan bai sa ya maida jikinsa ba.

A cikin wata uku ya gama amsar magungunansa Anwar yazo dan su koma Nigeria tare.

Kwanan Anwar biyu a Egypt Adnan ya tare shi da maganar ya taimaka mishi yasama mishi Makaranta ya ringa zuwa bashida burin daya wuce ya nemi sani akan addininsa ya cigaba da neman yafiyar Ubangiji.

Anwar sosai yaji dadin shawarar da Adnan ya yanke inda a take ya nemi abokinsa dake Egypt ya sanar dashi halin da ake ciki.

A cikin kankanin Lokaci Adnan ya samu Admission  a wani makarantar da ake koyar duk abinda ya shafi Addninin musulunci.

Sosai Adnan ke jin dadin makaranta yana jin Haske na bayyana a gare shi kuma wani hukuncin Allah sosai kwakwalwarsa ke ja duk abinda aka koya mishi sai ya d'auke akansa.

B'angaren Ameer da Aliya kuwa soyayya ake gudanarwa cike da kwanciyar hankali kowane burinsa yaga ya farantawa d'an uwansa rai.

Sosai Ameer ke tattalin Aliya dan ji yake babu Wanda ya kai shi dace da samun mace tagari inda Aliya kuwa taji sai a yanzu tasan dadin Aure dan Ameer namijine da kowace mace zatayi fatan samu dan tunda ta samu ciki Ameer shi yake tayata aikace aikacen gidan yana bala'in tausayinta rayuwa suke cike da ilimi da fahimtar juna zamansu gwanin ban sha'awa dan haka kawai Ameer zai kirata yace yau ta shirya zance zasuyi tazo mishi kamar lokacin da yake nemanta ahaka zai ci gayu ya fita yayo siyayya yayi parking a k'ofar gida ya kirata awaya yace yana waje.

Aliya kuwa sai taci gayu ta fito da d'an k'aramin cikinta sai su hau zance kamar saurayi da buduruwa abun nasu gwanin sha'awa.

B'angaren Ajjidde kuwa iskanci sai abinda yayi gaba dan zuwa yanzu ta zama Hajiya ta b'angaren iskanci dan yanzu musamman take had'a maza da mata a gidanta a taru a d'aki d'aya ayita iskanci kamar dabbobi inda idan suka gaji zasuyi ta shaye shaye.

Ahaka rayuwar Ajjidde yake cikin duhu tana rayuwa a hagunce ko kad'an bata d'auko hanyar tuba ba ballantana ta gane rayuwar da take yi ba mai b'illewa bace.

Abunka da wanda bashida rabo a cikin irin wanan Halin Maman Nur ya had'ata da wani balarabe mai shegen kudi dan Mahaukatan kudi ya turawa Ajjidde akan tazo ta same shi a hotel d'in dayake.

Ajjidde jiki na rawa ta nufi hotel d'in bayan ta dirka kwayoyi a cikinta da isarta.

Suka gaisa da Balaraben ta cire kayanta dan duk a tunanin ta tana zuwa zai fara aiki tunda yace aikin nasu kwana zasu yi suna abu d'aya.

Amma me Alhajin cewa yayi ta maida kayanta zasuyi aikin sai anjima kad'an.

Ahaka Ajjidde ta zauna tana kallon Balaraben dake Zaune yana ta amsa wayar.

Bayan minti talatin sai gashi ana kwankwasa k'ofar hotel d'in.

Balaraben mik'ewa yayi yaje ya bud'e k'ofar sai ga Manya manyan Alhazawa Sama dasu Ashirin na shigowa d'akin kowanensu sanye yake da bakin kaya da Jan abu a d'aure a kanshi.

Ajjidde tunda take abu bai tab'a sata fad'uwar gaba ba sai da tayi tozali dasu take wani irin tsoro ya rufeta tafara bin Alhazawan da kirarsu kamar irin ta samudawa ga girma ga kib'a ga tsayi.

A hankali ta juya ta kalli Balaraben daya biyata akan tazo tace mishi "Wadanan suwaye"?

Dariya ya kwashe dashi kamar wani boss yace " ta daina Hanzari da sannu zata san su"

Daga haka taga dukansu sun fara cire kayan jikinsu cikin minti biyar kowane yayi tsirara agabanta.

Wani irin gumi ne ya hau tsatsafowa Ajjidde dan halittar gabansu ba kamar irin na mazan data sani ba nasu ga tsayi ga kauri har yana neman tad'o k'asa .

STORY CONTINUES BELOW

Tuni tafara k'ok'arin janyo kayanta ta saka

D'aya daga cikin Alhazawan dayafi kowane tsayi da girma daga cikinsu ya hau kan gadon tare da hawa ruwan cikinta nauyi da doyin da yake yi kawai yasa hanjin cikin Ajjidde yamutsewa amai na taho mata bata gama tunanin da zatayi ba taji ana tura mata abu kamar itace agabanta.

Ihu take so tayi amma murya ta baya fita dan nauyin daya d'ora mata.

Ahaka ya ringa gana mata azabar da tunda take bata tab'a jinsa ba dan kamar attaruhu yake watsa mata a ciki haka ta ringa ji sai da ya samu awa d'aya akanta ya sauka a lokacin tana neman sumewa.

Tunanin ta bai gama dawowa dai-dai ba shima d'aya ya hawo kan gadon ya hau ruwan cikinta.

Ajjidde tuni taji gabanta kamar ba'ajinta yake ba sabida ji tayi kamar ya zazzago k'asa dan ayanzun da take kwance tafi tunanin wadanan Alhazawan ba mutane bane Aljannu ne ahaka Ajjidde ta ringa sumewa tana farfad'owa su kuwa suka ringa hayeta d'aya bayan d'aya. 1

Na karshen kuwa daya gama daya zaro jikinsa daga nata wani jan kyalle ya zaro daga rigarsa ya goge mata gabanta dashi ya jefa acikin wani tukunyar da bata san yaushe ma suka shigo dashi ba.

Zuwa wanan lokacin ta Riga da tasan da 'yan yankan kai ta had'u dasu a  firgice ta mik'e da d'an k'arfin daya rage mata sakamakon motsin data ringa ji agabanta inda tayi tozali da wasu irin tsutsotsi manya manya suna fitowa daga gabanta.

Ajjidde razanann k'ara ta saki sabida wani irin azabar rad'adin da gabanta keyi mata ahaka tsutsotin  suka cigaba da fitowa daga gabanta sabida azabar da take sha dan har wani cizonta suke ta fara rok'on mutuwa.

Tun tana iya ihu da k'arfi har tazo ta daina inda  sukuwa Alhazawan suka jeru a  layi tsirara suna kallonta sai da suka ga kamar idonta na neman rufewa wanda yafi su girma a cikinsu ya d'auko wani irin sharb'eb'en wuk'a biyu daga cikinsu suka rik'e Ajjidde suka saita mishi wuyan Ajjidde zuwa lokacin Wani irin Hawaye ya wanke Fuskar Ajjidde dan tasan she is no more kit suka d'auke kan Ajjidde da wuk'an inda Kan Ajjidde yayi gefe d'aya daga cikinsu ya d'auka yasaka acikin tukunyar da suka shigo dashi.

Suka yanke mata nonuwa da idanuwa suka kuma jefawa acikin tukunyar suka saka kayansu suka saka gangan jikin Ajjidde a cikin buhu suka fito d'aya bayan d'aya suka hau dirka dirkan motocinsu  sai da sukayi nisa suka wular da gangar jikin Ajjidde suka k'ara gaba.

Sai da aka kwana biyu su Mamman Nur suka ji labarin mutuwar Ajjidde dan ko kad'an bai kawo Balaraben d'an yankan kai bane sai da suka ga gangar jikin Ajjidde da tsutsoti suke fitowa daga ciki.

Dayake Ajjidde ba kowa gareta ba ballantana har awani damu.

Mamman Nur  tuni ya kwashe dukiyoyin Ajjidde da takardun komai data mallaka banda gwala gwalai ya siyar da komai na gidan yayi banking kudin ya had'a inashi inashi ya d'au hanyar barin garin dan ya koma garinsu ahanyarsa na zuwa garin nasu wani katon trailer ya mark'ad'a motarsa dashi a ciki ko kad'an gawansa bai ganu ba sabida mannuwa dayayi da kwalbatin.

*Allah ka tsare mana imaninmu kabamu ikon cikawa da kyau da imani ka d'auki ranmu a lokacin da kake farinciki damu*
3

B'angaren Adnan kuwa tuni ya zama ustaz ya zama Mallami shima mai zaman kansa bashida lokacin komai sai na bautawa Allah da neman yafiyar ubangiji Kullum cikin yiwa Mahaifiyar sa da Zara Addu'a yake babu abinda ya nema ya rasa dan Yayansa Anwar ya tsaya mishi akan komai har kudi ya bashi akan ya ringa kasuwanci inda a lokacin aka sako shi agaba akan ya kamata yayi aure amma yak'i akan yanzu babu Aure agabansa bai sani ba ko nan gaba.

Har a lokacin a Egypt yake a zaune inda yake tab'a kasuwanci Allah kuma ya saka mishi albarka bayan shekara uku ya Auri wata dalibarsa mai suna Zara ahaka ya ringa  rayuwa cikin tsantsar Ilimi da nadama idan ya tuna Rayuwar da yayi abaya yakan yi kuka kamar ransa zai fita dan a lokacin rayuwa kawai yake yi cikin duhun kai.

Musamman ya d'auki matarsa suka je Kano wajen iyayen Zara inda suka ji dadin ziyarar da ya kai musu Daddy kuwa har glass ya koma sawa sabida kukan daya ringa yi yayi affecting idonsa.

Mommy Hauwa kuwa tana nan Yanda take sai dai d'an tsufan da tayi sai daya musu Alheri ya baro gidan inda suka nufi gidan Ameer nan ma suka tarar dasu da yaransu har guda Uku maza biyu mace d'aya macen kuwa Sunan Zara aka saka mata wanda hakan ba k'aramin dadi yayiwa Adnan ba musamman ya kara neman yafiyar su suka  ce sun yafe mishi inda suka yi exchanging number da Ameer sai da suka ziyarci 'yan uwa da abokanan arziki suka je Maiduguri suka zagaye dangi suka koma Egypt.......

*Alhamdulillahi Anan na kawo karshen novel din Makotan juna ya rabbi ya rabbi ka yafemin kura kuran danayi a ciki naso na zayyona manyan masoyana nayi musu godiya kaunarsu ga littafin makotan juna na zayyano sunayen grops d'in da suke yawan comment amma hakan bai samu ba sabida rashin lokaci amma inaso kusan ina kaunarku fissabillahi da taimakon Ku na idda littafin nan Koda ban ambaci sunan kowa ba ya zama dole ma ambaci sunanki Aunty Zainab( Aunty Sis) sabida irin kaunar danake miki Allah ne ya had'amu fatana zumuncinmu ya d'aure har Aljannatul firdausi*

Post a Comment for "MAKOTAN JUNA CHAPTER 10 KARSHE"