Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

KUDIRI CHAPTER 6

KUDIRI CHAPTER 6

- - Post a Comment
KUDIRI
CHAPTER 6

Asiya ta kura wa makeken akwatin da ke kan gadon ta idanu, ta gagara cewa uffan. Muhibbat ta kwashe duk wata suturar da ta fada idanun ta. +

“Muhi, tafiyar ta kwana bakwai ce, ba ta barin garin ba.” Ta furta, a kokarin ta na hana ta kara zuba wasu. Zallan kayan matsu ne da tsuku irin na turawa. Atamfa da leshi bas u wuce kwaya hudu ba. Kuma su ta fi saba sakawa. 8

“Mece ce matsalar a nan? A kan ki za ki dauka har can, ko kuwa?” Muhibbat ta tambaya a lokacin da ta ke kara lafta kayan barci kala kala a kan wadan da ke akwati. 6

“Matsalar a nan, su Ummah za su dauka kin zo ne ki sace ni. Ji fa yadda ki ke kara lodin kaya. Sai ka ce wacce za ta rika canjin kaya kowane bayan awa?”

“Ya na da kyau ki san muhimmancin honeymoon a rayuwar aure, tun da Allah Ya sa kin samu damar samun hakan.”

Duk da sanin cewa Muhibbat ce kadai a wajen, sai da kunya ta dan kamata. Ta shiga kame-kame, “Ba fa wani abu ba ne. Rakiya kawai zan yi.” 5

“Mijin ki zai dauke ki zuwa wani waje, ba kuma tare da Amatullah ba. Ki kira shi yadda kika ga dama, amma mu nan, honeymoon za mu kira.” 7

Ta ci gaba da lafta kaya har da na barci kala kala. Kunya duk ta ishi Asiya. Me Yusuf zai ce idan ya ga kayan nan? Yaya za ta yi ne da Muhibbat? Don kuwa ta san ba za ta saurare ta ba duk yin ta. Haka Allah Ya yi ta, idan ta saka su a gaban ta, to fa sai ta aiwatar. Sai ko wani ikon Allah. Idan kuwa ta ki abu, to fa ta ki shi ke nan. 2

Ta nisa. Muhibbat ta ki fada ma ta yadda suka yi da Dokta Hadi. Amma ta san dai har a lokacin ba ta gam aba da kai ba bori ya hau. Saboda ita Muhibbat ce, ko za ta amince da shi, sai ya dan wahala. A halin yanzu dai bau wanda ya san gobe. Ta da ice wa Asiya, a taya ta addu’a, idan alheri ne to Allah Ya tabbatar; idan kuma babu alheri, to Allah Ya canja da abin da ya fi shi alheri.

Muhibbat ta zuba kayan kwalliya ma su yawan gaske, wanda Asiya ba ta san amfanin fiye da rabin su ba. Ta zuba turarruka ma su kamshi irin na Larabawa da na Turawa.

“Turare abu ne mai taimakawa wajen dauke hankalin namiji, ya kuma zuba masa sha’awa. Wajibi ne a kan ki, ki ja hankalin sa zuwa gare ki. Kin san ba za a rasa turawa a can Yankari ba. Kar ki sake ya karkata zuwa gare su.” 5

Asiya ta dan so ta yi dariya, “To Anty Muhi.” Amma a can kwaryar zuciyar ta, taraddadi da zumudi sun mamaye zuciyar ta. Da gaske ne, wannan ne karo na farko da za ta taba yin irin wannan kebantar da namiji, wanda kuma ya kasance mijin ta ne.

Ya kamata a ce ta tabbatar da ba zai manta da wannan rakiyar da za ta ma sa ba. Sai dai ba ta san yadda za ta yi ba. Za ta bari ne kawai komai ya bi yadda ya dace ya bi ba tare da tsananta wa kan ta ba.

Bayan azahar Yusuf ya dawo daga asibiti, kafin nan ya sa Bature ya mayar da Muhibbat.

Ta ji dadin hakan, amma ta shiga kadaici da kewa. Ta dan koma wajen Umma ta yi mata ‘yar kwalema zuwa lokacin da Sara ta iso. Ta yi ma ta bayanin cewar Yusuf ne ya nemi ta je don tallafa ma ta wajen kimtsa gidan kafin su bar garin.

Ta san ba wai don gazawar ta bane ya sa shi hakan, don ko ita da Larai bai fi karfin su ba. Sai don ita ma ta rage mu su kadaici kafin su tafi. Tare suka kimtsa kicin, sannan suka koma dakin Asiyar, wurin da take tambayar ta yadda a ke shafa kayayyakin adon fuskar nan da Muhibbat ta zuba ma ta su cikin akwati.

STORY CONTINUES BELOW


Sara mai son caba ado ce. Ko da dama ta samu gare ta, sai kawai ta shiga yin bayani ta na nuna mata a zahiri ta hanyar yi ma ta a fuska. Ta nuna mata su eye shadow prima, foundation, da sauran su. Har ma da koya mata zana gira mai adda. Lokacin da ta gama ta nuna ma ta madubi a gabanta. 8

“Ki ga yadda ki ka sha kyau, masha Allah Tabarakallah.”

Asiya dai murmushi kawai ta yi, ta na neman wurin da fuskar ta ta shiga. Ta san dai ta na karkashin wannan hodar da sauran jagbe-jagben da a ka shafa ma ta.

A lokacin Yusuf ya leko, “An gama?”

Asiya kusan ta gagara numfashi ganin irin shigar sa ta wando jeans da shat mai launin sararin samaniya. Kayan sun karbe shi, sun mayar da shi saurayi dan shekara sha biyar. 8

Ta zuki numfashi, lokacin da ya jefa ma ta wani irin kallo. Ita ma ta gagara kawar da nata idanun daga nasa. Gaba daya duniya ta tsaya cik. Yusuf ya mamaye zuciyar ta. Dan gusawar da ya yi ma tayi kewar sa fiye da zaton ta. Mata nawa ne ke yin sa’a irin nata a duniya?

“An gama Yaya. Saura tafiya.”

A lokacin ne Asiya ta sunkuyar da kai kasa, ta na mai jin kunya sosai. Sarah ta fita daga dakin da kayan ta, ta bar Yusuf tsaye a bakin kofa. Sai da ba sa jin motsin ta, ya mika mata hannun sa, idanun sa na rokon ta same shi wurin da ya ke.

A hankali ta tashi zuwa gare shi, Ta dora hannun ta cikin nasa, shi kuma ya rike gam-gam. Ya ja ta zuwa jikin sa a hankali. A lokacin rudani da zogin zuci sun hana ma ta wani tunani. Kamshin sa kawai ke kara birkita kwakwalwar ta. 4

Ya sauke muryar sa sosai, ya koma ga rada-rada, ya ce, “Kin kawo min farin ciki sosai cikin rayuwa ta Asiya. Kamar ne a ce mutum ne daga duhu ya koma haske. In Allah Ya yarda, daga yau zan dandana mi ki kwatancin farin cikin da ki ka saka ni ciki. Zan shayar da ke daga tabkin kaunar ki.”

Ya ja hannun ta ya dora bisa kirjinsa, ta na iya jin motsin bugun zuciyar sa, a yayin da idaniyar sa ke nuna buguwar so da kauna cikin su, “Yau zan gwada mi ki cewa kowane bugun wannan zuciya tawa da sunan ki ta ke yi. 13

Babu wa ta cikin zuciyar, sai ke.”

Asiya ta rude, rudanin ya wuce kwatance. Ga kunyar da ta matsa ma ta tuntuni. Ashe haka so ya ke? Ashe haka kauna ta ke? Ba ta taba sanin dadin sa ba, sai yanzu.

Ta na da bukatar yi ma sa magana, don haka ta daure zuciyar ta, ta ce, “In Allah Ya yarda, daga yau zan zama abar alfaharin ka. Zan yi ma ka biyayya bisa zallar so da kauna. Don hakika, yau na tabbatar Allah ya min baiwa, da Ya mallaka min kai, da son ka, da Ummah, da Amatullah. Alhamdullilahi, burina yau ya cika. Na fi son ka kwantar da hankalin ka, domin a yau, ka yi dace da matar da ta ke son ka, ta ke kaunar ka, wadda duk duniyar nan ba za a samu wacce ke ma ka irin son da na ke ma ka ba. Har abada...” 13

Irin sautin dariyar sa ta kara jefa ta cikin shaukin kaunar sa, wanda ya kara tabbatar ma ta da kalaman ta. Lallai ba za a samu mai son sa ba kamar ta.

Ba yanzu ba, har abada. Ta fara ne da yin aure domin Amatullah. Yanzu tana son zaman aure ne domin Allah, da kuma bin umarnin manzonmu(SAW), tare da yin biyayya ga yusuf, da kuma nuna masa dimbin kauna.

“Mu je mu salami Ummah.”

Kanta a manne ya ke da kirjin sa, ta na jin sautin bugun zuciyar sa, wanda yayi daidai da na ta. Tunanin cewa karo na farko tun shigar ta gidan da zata fita, ta bar Amatullah da Ummah ya fado ma ta. Ta yay a za ta kalli Ummah ta sallame ta? Ta yay a za ta fara rabuwa da diyar ta har na tsawon kwanaki bakwai?

Har a lokacin bai mots aba, amma ya ci gaba da cewa, “Mu je wajen Amatullah mu lallabe ta don kar ta yi kewar mu sosai. After all, mu na burin kawo ma ta babban tsaraba ne bayan mun dawo.” 5

STORY CONTINUES BELOW


Ta dan kalle shi, “Tsarabar me?”
Ya yi murmushi, “Tsarabar ‘yan biyu mana, kannen ta. Har kin manta?”

Ta sake manne kanta da kirjin sa, kunya da farin ciki su ka cike zuciyar ta. Hakika, za ta so a ce ta samu hakan, ta samu wannan farin cikin a rayuwar ta.

“Yaya ku mu ke ta jira a waje, tun dazu. Ko kun fasa tafiyar ne?”

Muryar Sara kawai su ka ji, ba su ganta ba. Ga alama ta gan su ne, ta makale a lungu ta na daga muryar ta. Hakan ya kara saka ta jin kunya sosai. 5

Ta yi sauri ta janye daga jikin sa, ta nufi sashen Ummah, ta wuce Sara, wacce ke ta yin ‘yar dariya. Ita kuma ta kusa yin tuntube don tsananin kunya.

Sun bar gidan misalin biyar da rabi na yamma, bayan sun yi sallama wa kowa. Su na tafe su na daga hannaye wa junan su. Asiya na kallon Amatullah ta mudubi, wacce Sara ke daga ‘yan dugwuin hannun ta a matsayin bankwana. Za ta yi kewar ta sosai.

Yusuf ya dafe tafin hannun ta ya rike. Hannun sa ya cinye na ta wajen girma, ta dan kale shi, ya yi ma ta murmushi. Nan ta ji haske ya cike zuciyar ta.

Tabbas! Ta kara tabbatar da cewa ba kowace mace ba ce a duniyar nan ta yi sa’a kamar yadda ta yi. Ita ma ta mayar ma sa da murmushin a kunyace, sannan ta gyara zaman ta a motar, ta na kara yiwa Allah godiya!
*              *             *

Gidan a cike yake da mutane, maza da mata. Babban falon cike da mazaje, mata kuma suna bangaren da Dokta ya wae wa Asiya don taba bakin ta a duk lokacin da suka je. Hatta sashen Umma a cike yake da yawan ma su shiga da fita wadan da yawancin su kawayen ta ne da ‘ya’ya ko jikokin su.

Har da ma’aikatan Asibitin Sauki sun halarci gidan Dokta Yusuf Haruna a wannan rana, don ta ya Asiya da Yusuf murnar samun ci gaba, na matsayin Chief Medical Director wato CMD na Asibitin koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke garin Bauchi. 2

Duk da dai ba babban alo ko shagali su ka shirya ba, an yi tanadin ciye-ciye  da lashe-lashe don tarbar ma su zuwa taya murna. Matan abokan Dokta da ma Sara duk sun hallara a kicin, suna ta dorawa su sauke kawai.

Filin ta baya a ka yi tanadi wa yara don su yi wasa, su kuma ci abinci. A can suka baje kolin su, suna ta wasa da tsalle-tsalle a kayan wasan da Yusuf ya tanadar wa Amatullah idan ta girma ta yi wasa da su.

Leshi Asiya ta saka mai launin sararin samaniya, Amatullah kuma ta tsuke cikin kayanta na riga da siket mai kyau designer (Mark and Spencer) cikin wadan da Yusuf ya kawo mata su akwati guda daga Ingila, wata guda da ya wuce. 2

’Yan kafafuwan ta dugwi-dugwi, ta na dan taka su cikin takalman ta ma su ban sha’awa, da kuma tsada. Sai ihu ta ke yi na murna, ta na sheka dariyar jin dadi. Ita dai kawai ta ga an cika gidan su ana aha, abin ya burge ta.

Kowa maganar ta yake yi irin yadda ta girma cikin koshin lafiya. Asiya ta kara gode wa Allah fiye da kirgen ta. Diyar ta ta kawo misali, domin ta cika shekara daya ke nan da sati biyu da haihuwa.

Amma a duk lokacin da ta gan ta, kammanin Mariya ke kara bayyana a fuskar ta. Wani irin bakin ciki sai ya rungumi zuciyar ta. Da a ce Maree ta na nan, ya ya za ta ji cikin zuciyar ta? Wane irin kumburin dai zuciyar ta zata yi? Sai dai ta riga ta yi watsi da wannan dama tun ranar da ta bace mu su. Har yau ma fa babu duriyar ta.

Amatullah ta je da gudu ta fadi jikin Yusuf, wanda ya daga ta sama ya na jijjiga ta, ita kuma ta na kyalkyatar dariya, ta na ihun. Zuciyar Asiya ta kara sosuwa.

Ya ya ma za a ce wannan yarinyar ta rasa mahafiyar ta bayan kwanaki kadan da haihuwar ta? Anya, Mariya ta na hayyacin ta kuwa a lokacin? Me ta yi tunani ne da har ya sa ta yar da Ama ta gudu ba tare da waiwaye ba?

STORY CONTINUES BELOW


“Mama.”Ta jiwo muryar Amatullah na ambato. Zuciyar ta ta kara cikewa da farin cikin ganin ita su ke gani a lokacin. Yusuf ya riko ta sun shiga kicin din, ya na mata wasa. Amatullah kuwa sai kara dariya ta ke.

“Mama.”Ta kara ambata tare da mika wa Asiya hannu kan ta dauke ta. Ta sa hannu ta karbe ta, ta na jin zuciyar ta kumbura kamar za ta fashe. Ama kuwa ta rungume ta tare da makalkalewa.

Tun ranar da ta fara jin wannan kalmar daga bakin Ama, zuciyar ta ta yi makil da farin ciki. Tabbas, ba ta yi sadaukarwa a banza ba. Domin duk wani farin ciki na duniya ya na gefe guda, farin cikin zama uwa ya koma gefe guda shi ma sun a takara.

Asiya, babu shakka ta samu kan ta cikin farin ciki marar misaltuwa. Yusuf ya cike zuciyar ta da kaunar sa, ya gwada mata ma’anar soyayya ta yadda ba ta da sauran shakka game da rikon amanar sa. Ta yarda da shi, dari bisa dari. Ta san zai kasance kusa da ita a lokacin da za ta fadi don ya kama ta. Muddin sun a tare, babu abin da zai same ta cikin ikon Allah.

Ba ta shayin nu na ma sa hakan. Shi ma kuma bay a ma ta koron kaunar sa. A halin da a ke ciki ma ta yi nisa a karatun ta na share fagen shiga jami’a. daga wajen sa har Umma, ta samu goyon baya matuka.

A lokacin da mutane su ka tsagaita suka rage abokan sa kawai da matan su, Sadi ya mike ya bayar da sanarwar, “Ya kamata yanzu mai hoton nan ya shigo ya dauke mu, ko ya ya?” Da kan say a kira mai shagon hoto na B Shaggy don ya dauke su hotuna a samu na tarihi.

“Kai ka fiye son daukar hoto.”Hadi ya furta ma sa, “Sai ka ce wani karamin yaro.” Dukkan su sun san halin Sadi ta wannan fannin. Ko dan zama a ka dan yi sai ya dauki hoto. Don haka wayar sa cike ta ke faal da hotuna iri iri. Balle a ce kyamarar sa ta hannu, wanda har biyu ya mallaka.

Sadi ya mayar ma sa martani, “Well, ba zai yi kyau ba a ce kullum mu rika abubuwa kamar manya. Wani  lokaci zai yi kyau idan mun dan taba yarintar.” A lokacin mai kyamarar ya shiga falon, ya ci gaba da cewa, “Yauwa, shigo nan ka watsa ma na filasha don Allah. Mu nan yara ne.” 2

Mai hoto ya yi murmushi, sannan ya shiga shirya yadda kowa zai dauki hoton. Su ka kira matan na su, a ka shiga dauka ta waya da kyamarar hannun ma duk.

Farko kowa dai dai a ka dauke shi. Sai kuma a ka dauki kowane miji da matar sa. Sannan kuma a ka saka Amatullah cikin kowane miji da matan. Daga nan kuma sai su dauka dukan su. An kuma yi zallan maza, da kuma zallan mata.

“Saura Umma.” Asiya ta furta, ta na kallon sa tare da neman y aba da izini wa mai hoton don shiga cikin gidan har sashen Umman. “Zai yi kyau ta yi hoto da kawar ta.”

Yusuf ya gyada kan sa, alamar ya amince, y ace, “Ki je ki sanar ma ta cewa mai hoton na tafe nan da mintuna goma.”

Da sauri ta fita, don kuwa alla-alla take yi ta bar wurin ko ta samu shan iska mai ni’ima. Ta na sane da yawan tsare ta da idanu da Suhaima ke yi tun zuwan su dazu. Suhaima ba ta nuna alamar ta san wani abu game da neman da ke tsakanin mijin ta Hadi da Muhibbat ba.

Ba mamaki, kila Hadin bai fada ma ta ba, kamar yadda y ace, har sais hi da Muhi sun tsayar da Magana mai karfi tukunna. Amma alamu sun nu na, ta san wani abu a kai. Haka kawai Asiya ke jin hakan a jikin ta. Balle ma magana irin wannan ba ta buya. 

Hadi mutum ne mai nacin tsiya. Duk kin Muhibbat, sai da ya kutsa sannan ya sha kan ta. A kusan duk karshen mako biyu, sai ya kai ma ta ziyara can Dagauda. A kullum kuma, sai su dade suna soyewa a waya. 2

Musamman ya sayi waya, ya kai wa Asiya har ma da layin sa, ya roke ta kan ta aika wa Muhibbat din a matsayin ita ce ta saya mata, don gudun gurguwar fahimta daga bangaren Muhi din. An dai yi sa’a ta karba ba tare dacewa komai ba.

STORY CONTINUES BELOW


Hadi ya fahimci Muhibbat mace ce da mutum zai yi nasarar shiga zuciyar ta ba don burgewar arziki ko nu na isa ba. Sai dai ta tafiyar da rayuwa yadda ya dace, a tsare. Ba mace ba ce mai son kasancewa cikin mafarki ba. Ita mai rike ne da zahiri a bayyane, babu ruwan ta da munafurci, abin da ya ke cikin ta, shi ya ke waje.

Wadan nan dabi’u na ta su ka kara sa Hadi zube wa, wanda ya sa shi yi ma ta kuka da hawaye a wani lokacin da ta nemi su dakata da zancen neman kawai, ya hakura. Abin har tsoro ya ke ba wa Asiya. Wace irin so ne haka, kamar yaron da bai taba soyayya ba? 2

Lokacin da Asiya ta ke barin falon tare da Amatullah a hannun ta ta na murmushi, ba ta san dalilin da ya sa idanun ta ya hade da na Suhaima ba a karshe.

Suhaimar murmushi ta ke ko kuma yake, amma idanun ta su na bayyana tsananin bacin ran ta. Abin ne da Asiya ke gudu tun farko. Kawai dai komai ya fi karfin ta ne. Sai kuma gyaran Allah.

Ba ta karasa wajen Umman ba, ta jiwo muryar Yusuf, wanda ya nemi ta tsaya. Ya kwala kira wa Sara, kan ta karbi Amatullah ta kai wa Umma, sannan sai da ta bace gaba daya, sai ya ja hannun Asiya zuwa wani dakin da ke gefe, wanda ba sa komai da shi.

Akwai dai tarukucen ababen da ba a amfani da su, kamar kwalayen talabijin din gidan, na home theatre, cooker da na kwan lantarki da sauran su.

Bai bata lokaci ba, ta ji ya rungume ta. A dan dakika biyun da suka bi bayan hakan ita ma ta biye ma sa, ta shagala ta na jin dumin jikin sa mai garwaye da kamshi, sannan ta nutse cikin bugun zuciyar sa. Nan kuma ta yi kokarin zare jikin ta, amma ya kara rike ta gam.

Tsoro da fargaba su ka kama ta, “Me ka ke yi?” ta tambaya idanun ta a zare, ta na kalle-kalle. Su kadai ne, amma duk da haka ba za ta yi sakaci ba. “Nan fa waje ne. idan a ka gan mu fa?”

“Kin san ba na so ku nisanta da ni, ko da na minti daya ne.” murya sa a shagale ta ke, ta na nuna dimbin sha’awar ta.

Ta dan yi dariya tare da nasarar ture shi, alhali zuciyar ta akasin hakan ta roke ta da ta yi. Ta kalli idanun sa, wadan da ke buge da mayen kaunar ta, ta ce, “Kai da ke barin mu kullum fa?”

Shi ma ya yi murmushi, “Wannan dole ne ya sa. Amma in kin ce na bar aikin, sai na bari.”

Ta sake yin dariya, “Wace ni? Aikin taimakon al’umma, idan ban goya maka bay aba kuwa ai b azan sanyaya maka gwiwa ba.”

Ya saki dariya, “Shi yasa na ke kara kaunar ki, tare da gwada mi ki a ko yaushe. Na fi son idan ban a nan, ki yi ta kewa ta kamar yadda na kan yin a ki a wajen aiki.”

“Amma ai yau a gida mu ka yini, tare kuma.”

Ya dan shafa gefen fuskar ta, ya na lallausan murmushi, “Eh, na yi mi ki wannan ne don nu na mi ki jin dadina ga me da yadda ki ka tsaya a kan kafafuwan ki, ki ka tarbi bakina tare da fidda ni kunya. Thank you.”

Ya na gama furta hakan ya sumbaci gefen kumatun ta. Nan take ta ji yaar din wutar lantarkin kaunar sa. Kunya ta lullube ta, ta sunkuyar da kai kasa ta na shafa wajen sumbar. Ta daure tare da cewa, “Aikina ne, ba sai ka gode min ba.” 1

Ya kalle ta sosai, daga sama har zuwa kasa. Ya rika kurbar adon ta da kuma tsarin yadda rigar ta ta karbe ta. Ya ce, “Wannan kwalliya Masha Allah.”

Sannan ya dan duka dab kunnen ta na hagu, ya sauke muryar sa sosai, “An jima za ki min bayanin kalar ta ko?”

Ya Allah! Gaba daya ta saka tafukan hannun ta ta rufe fuskar ta, sannan ta fice daga dakin kusan a guje. Ta na iya jin sautin dariyar sa mai dauke da sakon da ke sa zuciyar ta daduum!

Watanni shida ke nan da dawowar su daga Yankari, amma soyayyar tsakanin sub a alamar tsagaita wa. Kullum Likita sai ya fitar da sabon salo. 2

Ba su cika haduwa da safe ba kam. Amma duk bayan azahar, misalin karfe biyu, Asiya za ta kira lambar wayar sa, don ta ji lafiyar sa a wannan yinin.

Har ya saba, ko da ba ya kusa ta yi, sai ya zo ya ga rashin kiran ta wato missed call. Wasu lokutan kuma sako ta ke ma sa, wanda yawanci na kara karfafa ma sa gwaiwa ne da addu’ar sa’a, musamman idan ya na da tiyata a ranar.

Shi kuma a ta bangaren sa, yak an fita da su yawon shan iska duk karshen mako, sai ko idan bay a garin, ko ayyuka sun ma sa yawa a asibiti. Ya san hakan bai wadatar yadda yake so ba. Shi yasa yak an yi ma ta abubuwa a duk lokacin da ya samu dama kasancewa da ita.

                  *         *         *

Ba ta fi mintoci sha biyar ba a wajen Umma, amma ta gaji tamkar wacce ta yi yini ta na aikin noma. Amatullah ta tabbatar mu su ta na da karfin jiki, da ma na lafiya. Rike ta waje guda ma don a yi hoton aiki ne jajur. Amma dai sun samu sun dauka da dama. An kuma yi mata ita kadai da dama.

Yusuf ya isa gare su, a daidai lokacin da mai daukar hoton zai kara yi ma ta hoto ita kadai. Ya dafa kafadar sa, ya ma sa magana kadan. Ta lura ya dan razana, amma dai ya yi murmushin dole, sannan ya dauke ta.

Yusuf ya ma ta alamar ta je gare shi da hannu, a lokacin da Ummah ba ta lura ba. Ita ma din sai da ta tabbatar da ba mai kallo tukunna ta je. Ba ta san dalili ba, amma ta hango wani abu a idanun sa musamman a lokacin da ya tsaya gefen mai hoton kafin ya dauke ta. Ko kuma a cikin muryar sa ce a lokacin da ya ke magana ne?

Bayan sun dan fita suna tafiya ne ta tambaye shi, “Me k ace wa mai hoton nan ne lokcin da ka tsaya?”

Ya tsaya ya na fuskantar ta. Ba su yi nisa ba da dakin Umma. Hasali ma su Umman sun a iya kallon su. Ya amsa, “Ce ma san a yi ya tabbata ya dauki wannan a matsayin na karshe ne. don idan ya ci gaba da kallon min ma ta to zan kwakule idanun na sa, ba bus hi ba sake daukar hoto.” 7

Ta dan yi dariya, “Allah Sarki bawan Allah. Shi yasa man naga duk ya tsure. Dauriya na yi, ai da na fashe da dariya.

Yusuf murmushi kawai ya yi, idanun sa suna kyalli, amma dai hakan ya kaa tabbata ma ta cewa akwai abin da yak e son fada ma ta.

“Akwai wata ‘yar matsala.” Ya shaida mata, bai jira ta tambaye shi ba. Fuskar sa ta nuna alamar fargaba.

Nan take hankalin ta ya natsu, ya koma a gare shi. Ba ta taba ganin sa cikin wannan yanayi ba. Yanayin da ya kusan wannan, shine ranar zuwan Yafendo ne na farko gidan. Amma duk da haka, bai birkice haka ba.

“Me ya faru?” Ta tambaya, muryar ta na rawa.

Yusuf ya nisa. Ya kalli wurin da Umma ta ke da Amatullah, sannan ita Asiyar.

“Mene ne?” Ta sake tambaya, zuciyar ta na gudu da sauri. Wani abu ya faru, tabbas. Fatan ta, ba mai tsanani ba ne. Ko dai Hadi ne da Suhaima suka kaure da tashin hankali? Asibiti ne a ka kira shi? Hatsarin mota a ka yi, a ka kai mutanen asibitin su? Ko me ye ne?

“An samu Mariya.” Ya furta, bayan ya nisa.Diib, wuta ta dauke ma ta na dakika biyu. Ta ji kamar da wani harshe Yusuf ya ke ma ta magana. “Maree? ‘Yar uwata Mariya?”

Ta san dai ba zai ma ta wasa a kan hakan ba. Sannan ba zai taba fada mat aba idan har bai tabbatar da abin da yak e fad aba. Shi yasa wata kila wancan karon bai sanar da ita a kan an gan ta a Jos ba.

Ta kura ma sa idanu, zuciyar ta na bugu, ta na son jin ya maimaita furucin na sa. Wata kila zagin kunne ne tun farko.

“Eh, ita.”

Ba ya taimakawa da amsar nan da ya bayar. So ta ke yi a muntsine ta, ko wani ya cije ta ko za a samu a cikin mafarki ta ke ba, ba zahiri ba. Ta dade da son jin wannan labarin da a yau kuma ba ta tabbatar da yadda ta ke ji ba da ta samu.

Hakan ya na nasaba ne da cewar ta fidda ran ta a kan bullowar Mareen ne. ko kuma zuwan da ta yi kwatsam a yau ya jijjiga ta ne ta yadda tunanin ta ya birkice.

“A ina a ka same ta? Yaushe kuma? Ta na cikin koshin lafiya?”

Ba fata ba ne, amma wannan tunanin za a iya samun Maree cikin halin rashin lafiya ko tagayyara ya gifta cikin tunanin ta lokaci-lokaci.

Ya dan yi murmushi, “Ai kya bari na amsa daya bayan daya dai ko.”

Ta gagara yin ko da murmushin don muddin ba ta ji amsar ta ba, ba za ta sake ba. Wayyo Dada, yau wane irin hali za ta kasance a ciki? Addu’o’in su sun samu karbuwa a wajen Allah.

“A Kaduna a ka same ta. Ta na kuma cikin koshin lafiya.”

“Alhamdulillah! Allah mun gode maka.” Ta furta, ta re da zukar numfashi ta fitar. Idanunta suka ciko da kwalla, ba ta san ko na me ye ba ne. A yau kusan shekara guda ke nan da bace mu su, ko waiwayen sub a ta yi ba. Sau nawa ta sha tunanin Maree cikin wani mummunar yanayi, cikin fargaba da zullumi.

Sai ga shi a lokacin da ba ta tsammani ba zato, an samu ‘yar uwar ta, mahaifiyar Amatullah. Amma mece ce matsalar da ya ce an samu?

“Amma me ye matsalar dazun?”har a lokacin gani take yi za ta farka daga mafarkin da ba ta kwanta barcin sa ba.

Ya sake nisawa, idanun sa na bayyana bacin rai, da bakin ciki. Ya ce, “Ina son ki san cewa duk abin da ya samu bawa, to daga Allah ne. Sai ki yi hakuri, domin Yafendo ta dawo. A yanzu haka tan a falo.” 3

“Yafendo? Me Yafendo za ta iya yi, musamman a yanzu ma da a ka samu Mariya?”

Ya yi ma ta kallon ba ta fahimce shi ba, ya amsa, “Yafendo ta zo ne tare da Mariya. Ya lura da gwalo idanun da ta yi, sannan ya sauke muryar sa sosai.

“Mariya ta na bukatar a ba ta Amatullah, diyar ta.” 8

Iya abin da ta iya ji ke nan. Bayan nan sai karar bugun zuciyar ta, wadda ta yi rugu-rugu...

                      *             *             *

Wuri ya yi tsit, ko ina ya yi shiru. Wurin da ke cike da hayaniyar jama’a a dazu ya zama tamkar makabarta, in an dauke karar iyakwandishan, da wasu na’urorin lantarki na sanyaya rayuwar dan Adam.

Asiya ta kura wa ‘yar uwar ta Mariya idanu cike da kwalla. Shekara guda ke nan da idanun su ba su hadu ba. Ya dace a ce sun rugumi juna ne cikin farin ciki da tsalle. Amma kuma in ban da kwalla, babu abin da ke gudana cikin idanun Asiya.

Kusan za a ce ba ta gane ta ba, domin Mariya ta rame. Ta kara bakin fata, har cikin idanun ta na bayyana kunci da wahala, da ma rashin abinci mai inganci. Atamfa ce ke jikin ta, irin roba-robar nan, dinkin riga da siket. Wuyan dinkin rigar sai faduwa ta ke yi daga kafadar ta. Wani irin tsami ke bayyana rashin samun kula jiki ta bangaren ta. 2

STORY CONTINUES BELOW


“Ina ki ka shiga ne tuntuni, Maree? Kuma me ye dalili?”

Cikin muryar da ke nuna ba ta damu ba, ta ce,“Yanzu mene ne? Ba ga shi na dawo ba? Shi ke nan ai! Magana ta kare.” 4

Wannan abu ya soki zuciyar Asiya, amma ta daure ta ci gaba da cewa, “Amma ai ya dace a ce kin fada mana wurin da ki ka shiga. Ko kin san irin halin da mu ka shiga bayan tafiyar ki? Musamman ma Dada da ma Amatullah.”

Mariya ta amsa, “Wane hali Dada za ta shiga alhali ta na tare da ke, ‘yar lelen ta?” 7

Mamaki ya kama Asiya. Mamakin yadda tunanin Mariya ya ke. “Maree kin fi kowa sanin bah aka ba ne.”

Mariya ta daga hannu, ta katse ta, “Kar ki dauka ban san irin son da Dada ta ke mi ki ba tuntuni. Ina lura da yadda ta fifita ki a kaina ko yaushe. Komai a ce Laminde, kowa ya tashi ke ce. Ni ban taba abin gwanin ta ba.”

A lokacin idanun ta ke ci tamkar wuta. Bacin ran ta ya nuna karara. Hakan ya ba da mamaki wa Asiya, fiye da kalaman da ke fita daga bakin ta.

“Shi yasa na fada neman mijin aure mai arziki, don na burge ta. Ya kasance na zama mai fada a ji, mai wuka da nama a cikin dangi. Nan ma ya gagara. Shiri nay a wargaje, na zama abar kyama ga kowa. So ki ke yi na koma can Dagauda, don Dada da Baba su ci gaba da azabtar da rayuwa ta? Ki na son su ci gaba da nuna min sun yi nadamar haihuwa ta? Hakan ki ke so?” 6

Kuka yanzu Mariya ta shiga yi wi-wi duk da karfin halin da ta nuna a farko. Asiya ta yi yunkurin rungumar ta, don ta tabbatar ma ta cewar tunanin ta sam ba hakan ya ke ba.Ta nuna mata tsananin tausayin ta da ke tare a zuciyar ta. A kullum it ace a ke mayar wa a kasa, amma Maree ashe ba ta ganin hakan.

Mariya ta ci gaba da cewa,, “Na fa san abin da na bari a baya. Na san Baba zai gwammace mutuwa ta da jaririya ta, a kan ya bari mu zauna a gidansa. To ki gaya min me zan koma na yi a gidan? Wa zai kula da ni da jarirya ta? Uwar da ta gwammace a yi aure na da ciki, don guje wa abin kunya? Ko uban da ba zai taba karba ta ba? Da wannan Minde, na zabi shiga duniya, ko zan samar wa kaina saukin rayuwa.”

Asiya ta tuhumi ‘yar uwar ta, “Idan su Dada sun mi ki laifi a ganin ki, sai ke ki jefa Amatullah kamar wata ‘yar tsanar da ba ta da amfani? Ita wane laifin ta yi mi ki?”

Maree ba ta amsa ba, don haka Asiya ta ci gaba da cewa, “Ba kya da ‘yancin jefa jaririyar ki kamar yadda ki ka yi. Ke fa uwa ce a wancan lokacin. A kalla da za ki duba irin rayuwar da za ki jefa diyar ki ciki. Kin yi tunanin cewa idan ki ka tafi ki ka bar ta, wane hali za ta shiga ciki? Shin, kin damuwa ba ki yi ba?”

Asiya ta ga kamar gilmawar nadama cikin idanun ta, amma ya yi saurin bacewa, “Waye ya ce jefar da ita na yi? Barin ta na yi a hannun Allah kuma yanzu na dawo na same ta lafiya. Don haka na zo ina son a bani abata.”

Asiya ta dan mike kadan, ta na nazari. Lokaci ya yi, da za ta tsaya wa Amatullah domin kare hakkin ta da ma duk wata matsala, ko da kuwa matsalar, wadda ta haife ta ce.

“Ba zai yiwu ba.”Ta furta kai tsaye wa Mariya.

Cikin mamaki Mariya ta kalle ta sosai, “Me? Ki ka ce ba zai yiwu ba? Ni da diya ta ki ce ba zai yiwu ba?”

Asiya ta tsare Mariya da idanu, “Kwarai ba zai yiwu ba. Domin kuwa jefar da ita ki ka yi ki ka shiga uwa duniya. Ko sau daya ba ki taba juya wa kin waige ta ba. Sai yanzu za ki ce ta ki ce? Don me ya sa ki ka dawo a yanzu ki tumbuke ta daga rayuwar da ta saba?”

Mariya ta mike tsaye, “Ba ruwa na da rayuwar da ta saba. Ni kawai a bani diyata. In kuma ki ka ce ba haka ba to lallai zan kai ku da mijin ki kotu.”

Wasu kwalla masu dumi suka tsungili kumatun ta. Mariya da gaske ta ke yi, ta na son a bata Amatullah. Ita kuma gaskiya a yadda su ka shaku ba ta jin za ta iya rabuwa da ita. Ta gwada yi ma ta magiya a hankali, ko Allah zai sa su fahimci juna.

STORY CONTINUES BELOW


“Mariya ni fa kanwarki ce....me zai kawo kotu tsakanin mu?”

Mariya ta yi wata busashiyar dariya, “Eh, ke kanwata ce. Amma ke ga shi kin samu dukiya ki na walawa cikin ta. Ni kuma ina can ina shan wahala. A yanzu na samu mafita ba ki isa ki hana ni ba.” 5

“Mafita kuma?” Ta kara jin yamutsi cikin zuciyar ta. Abu daya ta ke gudu, ta na fatan ba zai zama gaskiya ba.

“Su Khalid da mahaifiyar sa sun min alkawarin nera miliyan uku, idan har na karbi diyata. Kin ga ta hakan na samu warakar talauci.” 8

Wannan abu ya girgiza Asiya ainun. Da ma ta yi tunanin da walakin, wai goro a cikin miya. Amma jin hakan daga bakin Mariya ya sa bakin ciki cushewa cikin kirjin ta ,yana neman zuke iskar numfashin ta.

“Mariya, na hada ki da girman Allah, kar ki aiwatar da niyyar ki. Ki yi tunanin yadda hakan zai shafi Amatullah.”

Mariya ta daga kafada ta sauke, “Me zai same ta? Ai ni ce mahaifiyar ta ce ko?”

“Kar ki manta, cewa tun farko ke ki ka jefar da ita. Na dauka kin dawo, za ki yi kokarin ba ta soyayyar da ta rasa. Amma ke ba hakan ba ne a gaban ki.”

Mariya ta gyara zaman ta cikin rashin tsoron ta ja da kowa. Ta riga ta rike ra’ayin ta, babu mai iya canja ma ta shi. “Eh to, na san na yi hakan. Amma a wancan lokacin kai na a daure ya ke, hankali na a tashe. Amma a yanzu gaskiya na samu hankali na, ina kewar ‘ya ta.”

Cikin takaici Asiya ta tambaye ta, “Kin ma kuwa san sunan diyar ta ki?”

“Ba lallai ne na kira ta yadda ku ke kiran ta ba. Canja ma ta suna zan yi, na kira ta da suna Mansura.”

Asiya ta nemi wuri ta zauna. A bayyane ya ke, Mariya ta yi kudirin karbar Amatullah. Abin da ita kuma ke ganin ba za ta iya bari ya yiwu ba. Sai ko abin ya fi karfin ta.

A halin da a ke, abin ya na son ya fi karfin ta. Mariya mai taurin kai ce a tun a yarintar su. Wannan hali ne ya jefa su cikin wannan yanayi. Wannan karo, har da jaririya a tsakanin su.

“Yanzu abin da ki ke yi ya dace ke nan? Idan kudi ki ke so ki zo, zan ba ki, ko ma Yusuf ya ba ki. Amma na roke ki, kar ki sayar da Amatullah zuwa ga wadancan mutanen da mu ka kare ta daga mugayen hannun su.”

Cikin murya mai kaushi, Mariya ta ce, “Ni ke nuna son kai, ko kuma ke? In ban da abin ki, in na ba su ita ba jinin su ba ce? Don me za ki na ce da rikon ‘yar da ba ke ki ka haife ta ba? Yanzu na zo ki bani ajiya ta ba tare da an ji mu ba.” 4

Hawaye su na zuba daga idanun Asiya, tausayin su duka ya cike ma ta zuciya. Ita, Maree, Amatullah da ma Yusuf.

“Na san ba ni na haifi Amatullah ba, amma ni ke rikon ta shekara guda. A yanzu kin gwammace ki raba ni, ‘yar uwar ki da Amatullah, don ki ba da wasu?”

“Wasu? Wadan da ki ke kira wasu mahaifin ta ne da kakar ta, sun kuma fi ki kusa da ita a kan ki. Balle ma ba karbar ta za su yi ba. Ni zan rike ta, bayan an yi auren mu da Khalid. Idan ki na son ‘ya ki haifi na ki mana. Ko ke juya ce?” 2

Da wadan nan kalamai ma su kama da mashi, Asiya ta kura wa ‘yar uwar ta idanu, ta na mai tsaninin mamaki da takaici. A yau ta kara tabbatar da Mariya za ta iya yin komai don kudi. Aure da Khalid kuma?

Ba wai haramun ba ne...amma anya, maganar gadon nan ba ya ciki? Ga shi Yafendo ce da kan ta ta samo ta. Ga kuma zancen aure.Tabbas, su na neman karbar Amatullah ne don dukiyar da a ka yi takaddama a kan ta.

Ya rabbi-samawati! Ashe har yanzu bas u hakura ba? Ya ya za ta yi cikin wannan yanayi? Ya ya za ta kare Amatullah daga sharrin mahaifiyar ta da kakanni? 2

Kukan Amatullah ne ya ja hankalin ta zuwa ga kofa. Larai ta na rike da ita, ta shiga ta mika mata, “Amatullah ta na kuka ta na neman ki. Don na ba ta abinci, amma ta ki shiru, ta na ta kiran maman ta.”

Kafin ta kai hannu ta tuni Mariya ta karbe ta, “Kawo ta. Ya kamata mu fara sabawa tun yanzu.” 2

Hawaye ma su dumi su ka kwaranyo daga kumatun Asiya. Ta yi sauri ta share gudun kar Ama ta fahimci matsala a tare da su. Bugu da kari kuma, sai ta yi tsit bayan Mareen ta karbe ta, ko uhum ba ta yi ba. Ta dai kura ma ta idanu ne kawai. Ita kuma Mariya ta na ta ma ta wasu gwalaben yara, wai a dole ta na ma ta wasa.

“Kin gani? Har mun fara saba wa.” Mariya ta ci gaba da yin wasa wa Amatullah.

Asiya ta ji zuciyar ta ta yi nauyi. Ba ta so a ce Amatullah ta yarda da Mariya ba. Amma kuma ba za ta so kan ta ita kadai ba. Za ta ba da Amatullah wa uwar ta. Ko da kuwa hakan zai tafi da rabin zuciyar ta ne. wanda har ya riga ya tafin.

Waaa! Waaaaa!! Amatullah ta fashe da kuka. Kamar wadda a ka kunna rediyo mai kara.

“Mamaa! Mammamaa!!” Ta kara da ihu ma tsire dodon kunne. Cikin tsananin kaduwa da rudani, Mariya ta yi saurin mika ta wa Asiya.Ta na ganin Asiya sannan ta kuma ji muryar ta, sai ta yi tsit. Kamar an yi ruwa an dauke.

Ba sai ta kalli fuskar Mariya ta san cewa ta ji haushin hakan ba. Amma ta san ba za ta janye daga maganar karbar ta ta ba. Don haka ta makala Ama a kafar ta ta na jijjiga ta, ta ce, “Zan dawo mi ki da ita, da zarar ta yi barci.”

Da wannan ta fice daga dakin bakin da su ka kai Mariya, ta na tafiya idanun ta na ganin duhu-duhu. Ta  kara rungume Amatullah. Tabbas! Yau ta ke ganin farin ciki a mamaye da zuciyart a.Ta shi guda komai ya raguje.

Tamkar jirgin sama ne. Cikin minti daya ka na hawa sama a dakika guda, sai ka ji ka fado kasa tare da rugurgujewa kuci-kuci. Haka ta ke jin rayuwar ta a yanzu.
                    
*              *           *
A dakin ta ta tarar da Yusuf ya na zaune bakin gado, ga alama jiran su ya ke yi.Ya fi ta kokari, don kuwa shi ya kasance a natse ne.

“So, ya ya? Kun gama maganar?”

Ta kalle shi sosai muryar sa da fuskar sa abu daya su ke nuna wa; cewa tilas su hakura da Amatullah. Sannan shi ma zai shirya yaki da su Yafendo a kotu.

“Bai dace ba...hakan bai dace ba.”Ta furta, ta na mai shirin sake sabon kuka. “Me ya bata ‘yancin yin haka? Don ta haife ta kawai?”

Yusuf ya karbi Amatullah, wacce ke shirin barci, ya runguma. Ya nisa sannan ya amsa, “Mariya da Khalid su ne mahaifan Amatullah. Idan su na raye su na kuma son a ba su diyar su su rike, ba ma da ‘yancin hana su. Duk kotunan duniya ba za su mallaka mana ita ba.

“Na taba fada mi ki tun a baya, cewa komai zai iya faruwa a kan Amatullah. Don haka, ni da ke tilas mu rungumi kaddara, mu kuma mika wa Allah komai. Mu na bukatar cin wannan jarabawar Asiya. Don haka, mu yi hakuri domin Allah Ya na tare da ma su yin sa.”

Hawaye wasu na korar wasu ke zuba kan kumatun ta.Ta gagara daurewa. Ba za ta iya mayar da su ba. Rabuwa da Ama tamkar yage wani bangare ne na zuciyar ta. Sam ba za ta iya jure hakan ba. Amma babu yadda ta iya. Jarabawa ba ta kare ba, ba gare su ba, ba ga Amatullah ba.Yusuf ya na manne da kan waya a kunnen sa, ya ba da matukar hankalin sa a jiki. Bai dade ba da komai a rayuwar sa ke tafiya sumul. Amma a yanzu komai ya birkice. +

Mariya ta dauki Amatullah, Yafendo ta tabbatar ma sa da sakon nasarar takun sakar farko. Don ta yi alwashin mallakar dukiyar jikar ta!

“Na fahimce ka.”Yusuf ya furta wa wanda su ke maganar ta waya. “Babu gudu. Zan aiwatar da duk abin da na yi kudiri, ba gudu ba ja da baya.”

Ya dan kara saurare, sannan ya gyada kan sa, “Kar ka damu da wannan. Na san yadda zan yi da al’amarin. Na gode.”

Daga nan ya ajjiye kan wayar, ya kalli Hadi, wanda ke zaune tun farkon wayar ta sa, ya na fuskantar sa cikin ofis din sa. “Mun gama.” Kawai ya sanar da shi.

Hadi ya ce, “Are you sure, ka tabbata kan kudirin ka?”

“Its the only way, abin da ya fi dacewa ke nan na yi. Ka fi kowa sanin ba damuwa da Amatullah dukan su su ka yi ba. Dukiyar ce ke jan su. Duk da ina son tsirar da mutuncin mahaifina, ba zan bari wasu su hau kan dukiya ta don su lalata rayuwa yarinyar ba. So, tilas na janye duk wa ta yarjejeniyar da mu ka yi, wanda na amince kan biyan kudin wasiyyar sa domin na cika ma sa.

Na amince da shawarar lauyan Alhaji da ma manajan bankin da ke rike da dukiyar tuntuni, kan a sayar don a karasa biyan basussukan da ya karba. Sauran abin da ya rage sai a raba gado wa magada. Zancen wasiyya kuma, mun warware ta gaba daya. So su na iya kai wa duk wurin da su ke da niyya. Ba bu yadda suka iya. 2

“Ita kuma Amatullah sai na bude sabon account da sunan ta, na zuba ma ta wasu kudade a ciki na boye. Duk da ba ni na haife ta ba, zan iya yi ma ta wannan kyauta, don kuwa na san ko yau na mutu, ba ta da gadona.”

Hadi ya nisa, “Shin ka yi shawara da Ummah da Asiya game da niyyar ka?”

“Me ka ke gani? Tun jiya na tara su duk na kuma sanar mu su da komai.”

“Ka na ganin shawarar nan ba zai shafi Amatullah ba ta hanya marar kyau?”

Wannan karon Yusuf ne ya nisa, “Mu na fatan kila in sun ga abin ba yadda su ke zato ba ne, za su mallaka ma na Amatullah a karshe.”

Hadi ya gyara zaman sa, “Kar ka rudi kan ka. Ka fi kowa sanin Yafendo. Idan har ba ta samu abin da ran ta ke so ba, to kai ma lallai ba za ta ba ka abin da ka ke so ba. A karshe Amatullah ce za ta sha wahala.”

Yusuf ya fi kowa sanin haka.Ya kuma san cewa samun kudin ba shi zai kare Amatullah daga shan wahala ba. Duk daya ne wajen su Yafendo. Don ba su san da kowa ba, sai kan su.

“Ba su kudin da rashin ba su duk daya ne, Hadi. Amatullah dole ta sha wahala wajen su. Shi yasa na yi kudirin hana mu su komai, don na tabbata gaba za a zo babu kudi, babu kaunar Ama. Ban san gaibu ba, amma ina fatan Allah ya kawo ma na saukin kawai.”

Hadi ya nisa, “Amin.” Sannan ya tambaya, “To, ya ya Asiya ta ke ji a yanzu?”

Sake ambaton matar sa ya sa shi jan numfashin sa cikin huhun sa, ya fitar a hankali. Yau kwana uku ke nan rabuwar su da Amatullah, amma har yanzu ba ta sake ba. Ba ta ci ko sha, har sai an tilasta ma ta. Ya yi kokarin danne na sa zuciyar don ya kwantar ma ta da na ta. Amma abin ya ci tura.

“Asiya na iya kokarin ta na shanye abin. Amma yadda ta ke ji ne ba zan iya fassarawa ba. Zafi ne da uwa ce kadai ke iya jin sa, in an raba ta da diyar ta.”

Tunanin Asiya ya kara mamaye shi. Ba ya son sake komawa gida ya tarar da ita cikin halin da ya bar ta kafin fitowar sa. Ya ma ta magana, kuma ta yi ma sa alkawarin za ta ci abinci. Dazu ma waya ta ma sa, ta sanar da shi ta ci abinci, don kawai hankalin sa ya kwanta.

STORY CONTINUES BELOW


“I am sorry.” Hadi ya furta. “Tun da Mariya ba mutuwa ta yi ba, dole ne wannan lokaci ya zo. Ina so ka sani, cewa ni da Sadi, mu na bayan ka dari bisa dari. Za mu taimaka ma ka ta kowacce hanya, don wannan matsala ta warware.”

Yusuf ya yi murmushi, “Na san haka. Kuma na gode kwarai. Allah Ya kara zumunci.”

“Amin.” Din da Hadi ya furta, tare da Sadi su ka yi shi. Lokacin Sadi ya karasa ciki ya same su.

“Done for the day. Na gama tiyatar yau, sai jibi kuma.” Ya sake kallon su dai dai, sannan Yusuf, “Yaushe ne za ka koma sabon ofis?”

“Zan kai sati mai zuwa. Wa’adin wanda yake kai bai kare duka ba. Sannan akwai takardun da za a bayar ranar karbar aikin.”

Sadi ya ce, “Allah Ya kai mu. Ka yi magana da lauyan?”

Yusuf ya gyada kan sa, “Yanzu mu ka gama. Zan kara zuwa na samu Baba Mai keke da Alhaji Dalhatu. Baba Musa ba ya gari, sai ya dawo tukkuna.”

“Hmm, abubuwa sun cunkushe. Lallai dukiya kan makantar da wasu. Its so unfortunate.” In ji Sadi.

Yusuf ya amince da hakan. Dukiya, ya dade da sanin kan cewa ta sha kan su Yafendo. Amma bai san za su iya abin da su ka aikata ba sai yanzu.

Ya sha damarar kare kan sa, da iyalan sa daga sharrin su. Hakan, zai yi ne tare da neman taimakon Allah! 

Daya daga cikin ma’iakatan sa na asibiti ma su kula da ajiye fayel-fayel na majiyyata ya shiga, ba tare da an ba shi izini, ko ya tambayi izinin ba. Fuskar sa dauke da alamar tashin hankali. Hakan bait aba faruwa bas am.

“Yallabai, mahaifiyar ka ce a waje. Ta ce na yi ma ka magana, ka same ta a wajen ajiye motoci na nan.” Muryar sa ke nuna tashin hankalin sa.

“Ummah?” Mamaki da tsoro su ka kama shi lokaci guda a lokacin da ya mike tsaye. Me ya kawo Ummah a wannan lokacin? Kuma ba ta sanar da shi ba kafin ta zuwan ta? Tabbas, akwai matsala.

Gaddafi ya kara tsananta tsoro da fargaba cikin muryar sa, “Ta ce emergency ne, ga me da matar ka.”

Bai tsaya tambaya ba. Haka ma abokan aikin sa ba su tsaya nazari ba. Duka su ka fita, tare da nufar wajen da su ka hangi Ummah na tsaye a gefen daya daga cikin motocin san a gida, ta na cike da damuwa. Zuciyar sa cikin bakin sa, ya isa gare ta.

A lokacin ne ya lura da Asiya, wacce ke zaune a bayan motar, ta jingina kan ta da kujerar da saman kujeran gaba. Numfashi sama-sama ta ke yin sa.

Subhanallah! Sadi ya nemi nas-nas su kawo kujerar tura marar lafiya ko gado, don a dauke ta zuwa ciki. Hadi kuma zuwa ya yi don ya sa a shirya ma ta daki.

Amma kafin nas-nas su zo, tuni Yusuf ya ciccibi abar sa. Ya wuce kai tsaye zuwa ‘special private room’, wanda da a kan kwantar da wadan da ba sa sha’awar zama wuri daya tare da sauran mutane. Ya san idanun mutane a kan su ya ke, amma bai damu ba. Matar sa ce ba lafiya, dole duniyar sa za ta tsaya.
                            *             *                * 3

Sanyin da hade da kamshi su ka shiga hancin Asiya. Kamshin ba irin na gidan ta ba ne, don haka ta san wani dakin ta ke. Ta dan bude idanunta, ta rufe sannan ta bude a hankali.

Hasken wutar dakin baya da karfi sosai, sannan labulen dogo ne har kasa. Ba ya da fadi sosai, ba kamar na dakin ta ba. Sannan gadon irin na asibiti ne, karami. Nan ta tuna fitar su da Ummah daga gida, su na zuwa asibiti. Zafi da azabar ciwo sun hana ma ta tunani mai kyau a lokacin.

Ta yi yunkurin canja yanayin kwanciyar ta, nan ta lura da igiyar ruwa da a ka daura mata. Tabbas a asibiti ta ke kwance bisa yadda ta ke ganin yanayin dakin.

STORY CONTINUES BELOW


A hankali ta ke bin ko ina da idanu har su ka sauka kan Dokta Yusuf, wanda ke tsaye jikin daya daga cikin tagogi biyun da ke dakin, bayan sa gare ta. Ta yi yunkurin masa magana amma muryar ta ta ki fitowa. Ta sake yunkurin motsi. A lokacin ne ya ji alamar ta. Ya juya cikin sauri, ya nufi wurin ta ke, fuskar sa cike da damuwa.

Hannun ta ya rike cikin nasa, ya zauna kusa da ita, idanun sa cike da dimbin so da kulawa, “Hey, beautiful!” ya dan kai hannun na ta bakin say a sumbaci bayan a hankali,  “How are you doing sweetheart? Ya ya ki ka kara ji da jikin ki?”

Murmushi kawai ta yi, a kalla yunkurin murmushin ta yi, don zuciyar ta ce ta yi haske, ganin yanayin sa, da jin muryar sa a hankali.

Ya nisa, “Kin ba ni tsoro, Asiya. Duk na rude dazu, na rasa wurin da zan jefa raina.”

Nan ta ke nadama ta murda zuciyar ta. Ta yi yunkurin magana, wannan karon muryar ta ta fito. “Ka yi hakuri... na ci abincin, wallahi na ci.”kwalla suka yi barazanar cike idanun ta.

“Shhh...,” Ya saka hannu ya dafe bakin ta da yatsar sa, “Na san kin ci, tun da kin fada min kin ci. Ai idan baki ci ba, me za ki amayar?”

A lokacin ta sake jin wani karni cikin bakin ta, amma cikin ta ba ya murdawa irin yadda ya ke yi kafin zuwan su asibiti, “Aman jini fa na yi.”

Ya da yi dariya mai sanyi ya ce, “Yes. Ummah ta fada min. Shi ya sa ma mu ka daura mi ki ruwa mai gishiri zalla, mu ka dauki jinin ki na yin gwaji, kar ya kasance ciwon suga ne.”

Tsoro ya kamata, “Ciwon suga?” Ta hadiye yawu, ta na kallon ruwan da a ka daura ma ta tare da gwalo idanu.

“Eh, ciwon suga. You see, idan ciwon suga ya rike kafar ki, sai an guntule shi kaaat! Sannan daya kafar ma a...” ya na yi ya na ma ta kwatance da hannayen sa yadda za a yanke kafar.

“Guntulewa?” ta zare idanu sosai cikin fargaba.  Sai kuma ta lura da fuskar sa cike da zolaya a lokacin, ya na murmushi.  “Me ka ke yi ne?” Ta kara tambayar cikin harare shi. Tabbas, ta san tsokanar ta ya ke yi.

Ya kuwa kyalkyale da dariya, “Matsoraciya kawai! Kin ga yadda fuskar ki ta yi kuwa?”

Ta yi rau-rau da idanu cikin kwalla, ta ce, “Ni gaskiya sai na fada wa Ummah abin da ka ke min. Kuma sai ta rama min.”

Ya yi sauri ya zauna bakin gadon, idanun sa a rude, ya na kokarin rarrashin ta, “Oh no, I was just teasing you, tsokanar ki na ke yi.”
Ta kifa fuskar ta kasa tare da jan hancin ta, “Sai ka tsokani marar lafiya?”

Hankalin sa ya kara tashi, ya ce, “Ok, Ok. Ki yi hakuri, ba zan kara ba.”Muryar sa cike da nadama da magiya.

Ta fashe da dariya, “Wa ye matsoracin yanzu?”

Ya dan tsaya ya kalle ta a lokacin da ya ga ta na goge fuskar ta.Ya ce, “Oh my… Amma lallai Asiya kin dauki bashi.” 2

Ta yi ma sa gwalo, idanun ta suna kyalli. Shi kuma ya lakaci hancin ta. Ya dan yi murmushi, “Yanzu ya ya ki ke ji?”

A lokacin ta lura ta warware sosai. Sabanin jin ciwo a kirjin ta da cikin ta a farkon faduwar ta a gida dazu. Ciwon kai din na ta ne ya dan dame ta kadan-kadan nan ma. Ga kuma ta ji sanyi a zuciyar ta.

Ta ce, “Da sauki sosai.”

Ya ce, “Ko kin san wannan ne karo na farko da ki ka yi dariya, tun tafiyar Ama? Ba ki ga yadda ta yi mi ki kyau ba.”

Asiya ta sunkuyar da kan ta kasa. Tabbas, ta san ba ta kyauta mu su ta hanyar boye kan ta, ta nutse cikin tunanin da ba zai ficce ta ba. Ta sake yin nadama kan halin da ta nuna, wanda ga shi nan ta jefa kowa cikin damuwa. Kuma hakan bai dace ba.

STORY CONTINUES BELOW


Za ta yi magana ya yi sauri ya ce, “A’a. Ki huta kawai. Zan je na dawo an jima...”

Ta rike hannun sa ga-gam da hannun da ba a daura mata ruwan ba. A yanzu ta fara jin karfi a jikin ta. Ta sauke muryar ta cikin shagwaba, “Kar ka tafi ka bar ni, don Allah.”

Ya yi murmushi mai fadi, “To, ba zan je ko ina ba. Har sai kin sake komawa barci.” Ya dora daya hannun nasa ya rufe nata.

Ta ji dadi sosai, hakan ya sa ta sake kwanciya a tsanake, ta na kallon sa. Shi ma ita ya ke kallo. Ta fara jin tsarguwa, don kuwa fuskar ta ba a wanke ta ke ba. Wata kila ma da yawun barci a gefen bakin ta, ko ma kwantsa a idanun ta. 4

“Me ka ke gani a fuska ta?” Ta tambaya

Ya saki murmushi mai fadi, zuciyar ta ta mata sanyi. Ya kai hannun sa ya shafa fuskar ta, idonsa cike da dimbin kauna, ya ce, “Ko kin san ke ce macen da tafi kyau a duniya?”

“Ni kuma?” Ta san ba zolaya ba ce, don kuwa da gaske ya ke yi.

“Ke. Don ba na gajiya da kallon kyawawan idanun ki, ma su sani tsima. Ba na gajiya da ganin murmushin ki, mai sa zuciya ta ta yi sanyi. Hakika na yi sa’ar macen aure. Ba bu abin da na ke yi a kullum, sai gode wa Allah kan wannan baiwa da Ya yi min.”

Ta yi sauri ta manne idanun ta sannan ta boye kan ta cikin matashin da ta saka kan ta a kai. Dadi marar misaltuwa ya mamaye zuciyar ta. Lallai ita Allah Ya yi wa baiwa.

Ya ya za a yi ta na kwance a gadon asibiti, fuska duk a hargitse, wata kila ma a kumbure, amma Yusuf ya ga kyaunta? Ko wankewa ba ta yi ba, balle kwalliya?

Shi kuma a na sa bangaren, ya yi kyau matuka. Ya yi aski a fuskar sa tsaf, ga gashin kansa a saisaye, sai sheki ya ke yi, ya na kamshi. Da kyar ta dan bude idanu ta kalle shi a hankali.

Shigar sa na shat da wando. Sun yi masa kyau. Ya kuma yi kyau sosai. A duk lokacin da ta kalle shi ta kan yi tinkaho a zuci, cewa ta samu miji, gwani, abin dubawa. Ta kan dauki kambun sarautar matan duniya, ta nada wa kan ta. Domin kuwa Allah Ya yi ma ta baiwar samun sa a matsayin mijin ta.

A lokacin wayar sa ta yi kara. Ya kashe kidar amma sai ta yi kara kamar kwaro ne ya makale a yanar gizo, wato vibration ke nan. Ya yi jinkirin dauka. Bayan ya dan yi maganar, sai ya kashe. Fuskar sa na bayyana son tafiyar sa a lokacin, amma bai motsa ba. Tabbacin ba ya son barin ta ita kadai.

Ta yi murmushi, ta ce, “Ka je kawai, kar ka damu. Zan kula da kaina har ka dawo.”

Ya daga hannun ta da ya rike zuwa lebban sa ya sumbata, idanun sa su na sheki. Ta dade da sanin cewa hakan na nufin ya na ma ta godiya bisa fahimtar yanayin aikin sa da ta yi. Ya ce, “I will miss you, zan yi kewar ki. Amma zan je na dawo In shaa Allah.”

“Zan jira dawowar ka.”

Ya nisa, sannan ya mike ya nufi kofa, “Oh, kafin na mance, Dada ta na hanyar zuwa. Na aika a dauko ta.”

Ya na fadin haka ya kai hannun sa bakin sa, ya sumbata sannan ya hura a iska ta wajen ta. Ta yi dariyar jin dadi. Shi kuma ya fice ya bar ta da kewar sa tun bai yi nisa ba.
                   *          *          *

Ba ta san yawan lokacin da ta dauka ta na barci ba. Amma dai ta san ta dade. Don kuwa ta na farkawa ta ga Dada a gefen ta, fuskar ta cike da damuwa.

Motsin da ta ji ya tabbatar ma ta ba Dada ce kadai a dakin ba. Zuciyar ta cike da farinciki, lokacin da ta ga sauran ‘yan uwan ta, yayyen ta da ke dakunan mazajen su.

Ta dade ba ta gan su ba. Tun bayan bikin Mariya, a takaice. Na ta auren ya zo kwatsam ne. Don haka babbar yayar su Asabe ce kawai ta halarta. Yau ganin su gaba daya; Asabe, Uwani, Jummaiya, da kuma Indo su ka saka ta yin kwallar farin ciki. 1

‘Yan uwan ta, yayyen ta duk sun taru a kanta. Ga mahaifiyarsu. Wayyo dadi!

Ta ji karfin zama a kan gadon sosai. “Ya ya jiki?” Dada ta tambaye ta, bayan sun gaisa.

“Da sauki Dada. Sosai ma kuwa.” Daga nan ta gaida sauran yayyen ta. Ai a dole jiki ya yi ma ta garau. Ta gyara zama sosai, tare da taimakon Asabe. Daga nan su ka kuma shiga hira.

“Ya ya a ka yi ku ka sani Adda Asabe?” Ta tambaya.

Jummaiya ce ta amsa, “Mijin ki ne ya nemi izini wajen mazajen mu, ya kuma tura ma na har gida bayan mun hadu a wajen Dada. Ya na son mu kasance tare da ke a wannan lokacin.”

Yusuf ne ya ma ta hakan? Kuma ko ya sanar da ita? Dadi ya kara kamata.

“Ba mu ji dadin abin da Yalwaji ta yi ba. Amma don Allah, kar ki tayar da hankalin ki. Kin ji ko?” Indo ta shawarce ta.

Asiya ta yi murmushi, “Ba komai. Na riga na yi hakuri. Maree ce mahaifiyar Amatullah. Kuma karbar ta da tayi ba laifi ba ne.”

Dada ta nisa, “Duk laifi na ne. Ni na yi sanadin abin da ya ke faruwa tun daga farko. A kokarina na rufa wa kaina asiri, na rusa rayuwar mu gaba daya. Mariya sangartacciya ce, tun ta na karama. Komai ta na son a ce na ta ya fi na kowa. Wata kila da na mayar da hankalina wajen ba ta kulawa da tarbiyya ta, da ba haka ba.”

A lokacin Dada kamar za ta yi kuka. Asabe, babbar ‘yar Dadar ta ce, “Dada, Allah Ya gani, ba ki yi laifin komai ba. Ke ki ka yi wahala da mu tun mu na yara, ki ka aurar da mu, har mu ka kawo yanzu. Dukkan mu mun san zafin kan mu. Don me za ki ba da kan ki laifi a dalilin Yalwaji?”

Dada ta kalle su duka, “Hakika, Allah Ya min baiwa da ku, ma su son faranta min rai a ko yaushe. Amma a lokacin da maganar cikin Yalwaji ya bayyana gare ni, na tabka laifi babba; na bari a ka mata aure a wannan hali. In ba laifi na ba, to na waye?”

Uwani ta ce, “Don Allah Dada, kar ki rika bata ran ki. Ita Yalwaji ce ta jefa kanta cikin matsala. Mu shida ki ka haifa, amma ita kadai ta sangarce. Don haka addu’a kawai za mu ma ta, ba zama mu na tayar da hankulan mu a kanta ba?”

Kowacce cikin su ta amince da hakan. Da wannan su ka shiga hirar su ta bayan rabuwa sabuwa. Ummah ma ta kai mu su abinci, ta dan zauna sun a hira da Dadar.

Ba ta dade da zama ba, Yusuf ya shiga dakin. Ya yi wanka ya canja kayan jikin sa. Jamfa ya saka, ta shadda mai launin shudi da hula damanga launin shaddar. Kamshin sa kadai ya juya kwanyar ta, balle kyaun da ya yi.

Har kasa ya durkusa, ya gayar da Dada, sannan yayyen ta. Su kuma Umma ta dauke su zuwa gida, wajen da za su yi wanka, su kuma dan huta.  Ganin su biyu ne, Yusuf ya zauna gefen gadon ta, fuskar sa bai bar murmushi ba, “Ya ya jikin na ki? Na lura akwai ci gaba.”

Ta yi murmushi, “Na ji sauki sosai. Kuma ban sake aman jinin ba. Sai dai magugunan ne sun yi yawa. Ga su ba dadi.”

Ya dan yi dariyar ganin yadda ta turbine fuskar ta, “Shi ne har da bata fuska? To ai dama magani ba ya da dadi. Kuma dole ne ki sha. In ba haka ba, babyn mu ai ba zai samu lafiya ba.” 4

Ta kyafta idanu sau biyu na rashin fahimtar abin da ya furta. Ta bude bakin ta tare da kyafta idanu na uku, na wata kila ko kunnuwan ta ne ke ma ta zagi, ko ma kila zolayar ta ya ke yi. Amma ga alama da gaske ne. Ko kuwa?

“Baby?” Ta tambaya da kyar, don neman sake tabbatar mata da kalaman da ta ji. Zuciyar ta wane kalangu wajen bugawa.

“You are pregnant.” Ya kara dukawa dab da fuskar ta, ya sauke muryar sa, “Wata uku ke nan.”

Dadi da kunya su ka lullube ta. Ta gagara kallon idanunsa, ta furta, “Ni?  Juna biyu?” ku san ta kasa gaskata muryar ta cikin kunnuwan ta.

Ya saki murmushi lallausa, “Lallai ke din kuwa. Kamar yadda na fada mi ki ne, kar mu yanke zaton samun rahamar Ubangijin mu.” Ya ja ta zuwa jikin sa, ya rungume ta, “Allah Ya yi mana mu ma. Allah ya mana kyautar Sa, wanda ba kowa ke samu ba. Sai mu kara gode ma Sa.”

Hakika, Allah Ya mu su baiwar samun na su. Tabbas! Allah mai rahama ne ga bayin Sa. Mariya ta karbe na ta, su kuma sun samu rabon su, wanda ba bu wanda ya isa ya raba su da shi ko ita, sai Allah.

Babu abin da ya kai hakan dadi a duniya. Ga Dadar ta, yayyen ta, Umma da ma Yusuf, su na tare da ita a wannnan lokacin da ta ke bukatar su. Ta kara manne kan ta a jikin sa, ta na jin dadin da ba ta taba jin irin sa ba a duniya. Kasancewa sun samu wannan kyautar ta san Allah Ya na tare da su.

Post a Comment for "KUDIRI CHAPTER 6"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...