Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

FETTA CHAPTER 5

FETTA CHAPTER 5

- - Post a Comment
FETTA


CHAPTER 5


D'an gudun da tayi zuwa ciki yasa ta haki, tana sauke ajiyar zuciya, "Lafiya dai Fetta", Cewar Hajiya Tumba, Natsuwarta ta tattaro, ta d'an duk'a tace " Ina wuni?", "Lafiya lau", +

Su'ad da Feena kallon k'ask'anci suke bin ta dashi, sun raina ajin ta, Yaran hamshak'an masu kud'i sune level d'in su, Gaba d'aya friends d'in su yaran manyan mutane ne.

Cike da ladabi tace " Umma tace nazo na karb'ar mata sak'o", Mik'ewa tayi tace "Ina zuwa", D'aki ta shiga.

" Falon nan warin bararoji yake wallahi", Feena ta fada tana toshe hanci, Su'ad ta yatsina fuska tace "Ashe ba ni kad'ai naji ba"

Fetta da tasan da ita suke, Ran ta ya kai k'ololuwa wurin b'aci, Ta tsani a wulak'anta ta, Had'iye b'acin ran tayi ganin bata da wata mafita,

Hajiya ta fito da kud'i k'ulle a leda, Tace "Gashi ki kai mata, dubu ashirin ne, ta kaiwa Asabe wacce mijin ta ya rasu kwana uku da suka wuce", Tasa hannu ta karb'a, ta amsa da " Toh"

Su'ad tace "Mama da kin ba driver ki ya kai, baki da tabbas fah ko zasu kai, kinsan talaka da kud'i", Kallon da Hajiya ta mata yasa taja bakin ta tayi shiru, Tana b'ata rai.

Fetta tazo fita daidai saitin Su'ad tace " Talakan ma, ba kowanne yake da kwad'ayin abun duniya ba, rayuwar da yake ciki ta wadatar ", Tayi maganar yadda Su'ad kad'ai taji, Ta fice abun ta,

   A harzuk'e ta mik'e zata bi bayan ta, Ganin Hajiya na kallon ta, Yasa ta koma ta zauna cike da takaici, A ranta ta k'udiri duk ranar da ta dawo sai ta nuna mata matsayin ta.

    Fetta a hanya tana tafiya tana mamakin hali nasu Su'ad, Idan haka yaran masu kud'i suke, bata burin wata mu'amala ta had'a su.

    Suraj kwance yake kan gadon d'akin sa, Yana ta faman juyi da tsaki, Isowar sa ya fara cin karo da abubuwan b'acin rai, Auren Bilkisu ba abunda ya amfanar dashi, Idan haka aure yake, lallai masu cewa aure nada dad'i basu san me suke ba, Tsaki ya k'ara yi, Ya mik'e ya shiga toilet ya watsa ruwa.

     Bilkisu waya ta kira ta sanar da Aunty Jummai, Aiko ta shiga ruwan masifa akan me zai mari yar' ta, Gata nan zuwa gidan ayi ta k'are, Tana cikin masifar ne mijinta yaji, Fisge wayar yayi ya kashe, A fusace yace " Wai ke Jummai sai yaushe zaki yi hankali, ki fara tambayar yar' ki laifin me ta mishi, ba ki hau masifa da zugata ba, tarbiya ce wannan kike koya ta mata", "Yanzu fisabillahi sai ya mare ta, nayi fad'a kuma shine laifi", " Rufe mun baki, wallahi kika sake kika taka gidan nan da niyyar taka husuma, a bakin auren ki"

   Furucin shi ya razana ta, Tayi shiru da baki, Rai a b'ace.

    Fetta tayi shirin ta na islamiyya, Hijabi k'ato har k'asa, Tana sanya niqab, Rumaisa ta shigo, (K'awarta kusa dasu gidansu yake, tare suke zuwa islamiyya),

    "Yawwa Rumaisa saka mun niqabin nan, tun d'azu na kasa", Ta karb'a tana sa mata, Tace " Yo ai ya igiyar ta tsinke", "Ya Salam", Ta furta rai bai so, " Yau dai ki hak'ura da sawa, muje" "Tab wallahi ba zan iya bi hanyar nan babu niqabi ba, yadda maza ke gungu tun ba da yamma ba idan mun taso", " Toh ina ruwan ki dasu, mu da muke bin hanyar cinye mu suka yi"

   "Kallon su na k'urilla ba zan iya dashi ba, idan suka tsura ma ido kamar zaka fad'i, ki jirani na d'inke yanzu a telar Umma", " Uhmm ni dai kiyi sauri kada ki ja mana dukan makara"

STORY CONTINUES BELOW


   Da sauri ta hau keken d'inki, Ta d'inka, Ta saka suka tafi, Suna tafiya a natse suna hira.

     Suraj da abokin sa ne Munir ne a cikin mota, Munir ke driving zasu fita shak'atawa, Suraj ya kira shi su fita, ko zai rage b'acin rai.

     Munir yaja burki, ganin su Fetta sun tafi da tunanin sa, Yana son mace mai natsuwa, "Daga ganin su yara ne masu tarbiya", Ya fad'a a ran sa,

   " Lafiya ka ja burki?", Suraj ya tambaye shi, "Am sorry Abokina, naga kalar matar da nake so, bani minti biyu", Kafin Suraj ya bashi amsa ya b'alla murfin motar ya fita, Ya bisa da kallo yana jan tsaki, cike da takaicin yadda yake rawar k'afa akan mace.

   Sallamar da ya musu yasa Rumaisa tsayawa, Fetta gaba tayi kad'an ta tsaya ba tare da ta juyo ba.

    Suraj dake kallon su ta cikin mota, A ransa yace "Mai aji ce", Yaji ta burge sa dan kama ajin ta da tayi.

     Rumaisa ta amsa sallamar sa, Da murmushi yace "Kuyi hak'uri na tsayar daku a titi, bani da option da ya wuce haka, gudun kada ku sub'uce mun, naga yar'uwar ki taji haushi", Murmushi tayi tace " Ba komai, Haka take bata son hayaniya",  "Allah Sarki, ko zan samu number ki", Ya fad'a yana mik'a mata wayar shi, Ba tare da wani tunani ba, ta karb'a ta saka.

   Da murna ya mata godiya, Ya nufi mota.

   " Sam Rumaisa baki da aji wallahi, daga tambayar number sai ki bashi", "Ba zan iya wulak'anta shi bane", " Ba wani wulak'anci, ki ja ajin ki mana", "Uhmm ni dai ya isa haka", Taja tsaki tana yin gaba,

   Rumaisa kam a ranta bata jin zata iya barin wannan had'add'en guy ya sub'uce mata.

   
    " Saboda wannan marar ajin ka tsayar damu", Cewar Suraj, "Ni fah yar'uwar ta taja hankali na, natsuwar ta da diran ta yafi d'aukar hankali na, duk da banga fuskar ta ba", " Amma a wurin marar ajin na ganka ai", "Abokina kenan, kamun k'afa zan yi da ita",

   Suraj ya kwantar da kansa jikin kujera ba tare da yace komai ba, Munir yaja motar, Cikin zuciyar sa yana hasko suffofin Fetta, dan ita ta tafi da tunanin sa.

    Da daddare ya kira Rumaisa, bayan sun gaisa ya mata zancen Fetta, Ranta taji ya b'aci dan ya tafi da tunanin ta, Tace mishi an sama Fetta rana, Ranshi yaji ba dad'i, Yace to ita fah, Cike da murna tace mishi bata da kawo, Yace yana kamu, Suka d'an tab'a hira, Ya kashe wayar yana jin haushin rashin samun Fetta, amma zai lallab'a da Rumaisa.

     Mu'azzam ya fito cikin shirin sa zashi wurin sahibar sa, " Mu'azzam zo nan", Mahaifiyar sa ta kira shi, Yazo ya durk'usa gaban ta "Ina zaka je?", Yana sosa k'eya yace " Gidan Aunty Aliya", "Kace mun wurin tsitacciyar mage zaka, Mu'azzam ina raba ka da yarinyar nan mara asali, wacce ba'a san daga ina take ba"

   Cike da damuwa yace "Mami yarinyar tana da tarbiya", " Ina amfanin tarbiyar babu asali, haka zaku haifi yara basu da dangin uwa, ka sake tunani", Ya mik'e rai a jagule, Ya fice.

    Har ya iso gidan su Aliya, Rai ba dad'i, Fetta cike da murna da d'okin ganin sahibin ta ta fito, Yana ganin ta kaso saba'in na cikin damuwar sa ya ragu, "Ina fatan Yayana yana lafiya, dan na hango damuwa a k'wayar idon sa", Murmushi yayi yace " Babu wata damuwa, sai ta rashin saki a ido kwana biyu, kuma gaki na ganki", Bata san sanda dariyar farin ciki ta sub'uce mata ba,

    Ta zauna, Ta d'auki cup ta tsiyaya mishi zob'o, Ya karb'a yasha yana yaba dad'in da yayi, Taji dad'i sosai dan ita tayi.

   Sun dad'e suna hira, Kafin yace zai wuce, Ta mishi rakiya, Ta dawo cikin gida cike da k'aunar sa.

   Aliya dake zaune tsakar gida tace "Fetta zo", Ta k'arasa ta zauna kusa da ita tace " Wata yar shawara zan baki", "Toh Umma", " Ki rage sawa kanki soyayyar Mu'azzam saboda halin rayuwa", Ta amsa da "Toh", " Yawwa kiyi ta muku addu'ar zab'in alkhairi", "Toh Umma", " Tashi kije kici abinci", Ta mik'e jiki a sanyaye, Tana jin zuciyar ta ba dad'i,

   Aliya labari ya kawo mata, Mahaifiyar Mu'azzam bata goyon baya, Shiyasa ta gargad'i Fetta bata so ta shiga damuwa da zata iya cutar da ita nan gaba, duk da babu Wanda yasan gobe, zata iya canza ra'ayi Mahaifiyar tasa.

   "K'awata nayi kewar ki sosai", Cewar Bilkisu tana waya", " Wallahi nafi kewar ki, ga wannan dan' rain in wayon mijin naki ya kasa ya tsare", "Ni kaina na k'osa ya tafi wallahi, a takure nake ji na", " Allah yasa ya tafi, na gaji da rashin ki kusa dani kwana biyu", Jin kamar shigowar mutum, Tayi saurin kashe wayar,

   Suraj ne tsaye kan ta, Yana jefan ta da kallon da ta rasa na meye, Juyawa yayi ya fita ba tare yace mata komai ba, A ransa yana ayyana abubuwa da yawa, Zargin da yake akanta yake son tabbatarwa, Tun ranar da ya dawo ya saka mata alamar tambaya, Idan kuwa ya tabbata sai tayi nadamar auren sa.

    Bilkisu mamakin me ya kawo shi d'akin take, Bai tab'a zuwa ba sai yau, Ta tab'e baki tace "Can masa", Tayi dialling number Zulaihat.*Zainab Yola, Hauwa isa, Safira bala labaran, Hafsat bello Ruma wannan shafin naku ne๐Ÿ’ž* +

    Fetta sun fara zana jarabawar gama makaranta (WAEC), Karatu take sosai duk da tana samun interval kafin wata exam d'in.

   Zaune take d'aki, Tana ta faman calculation, Maths exam ce dasu washegari, Wayarta ta hau ruri, sam ta manta ta saka silent, Idan zata yi karatu silent take sawa ko ta kashe, Ganin Mu'azzam ne mai kiran, Ta saki murmushi, tana d'auka.

    "Sahiba ta", Ya fad'a yana jan numfashi, " Na'am Yau kin jini shiru ko ki neme ni ko?", "Tuba nake, kana cikin zuciya da tunani na, rashin credit a waya yasa ban kira ba", " Na karb'i uzurin ki, Ya kike?", "Lafiya lau", " Yasu Ali?", "Duk lafiya", " Mashaa Allah, Yanzu me kike yi?", "Ina karatu ne", " Bari na barki ki cigaba, Allah ya bada sa'a da nasara", "Amin", " I Love you", "Same", Ta fad'a cike da kunya, bata tab'a fad'a mishi I Love you, nauyin kalmar take ji, Kullum cikin yi mata complain yake, sai tace kunya take ji.

   Hajiya Tumba ta tashi da zazzab'i, idonta sunyi jajir suna zubar ruwa, Ko k'asa bata samu damar saukowa ba.

    Suraj ya fito cikin shirin sa, Shadda ce a jikinsa mai kalar coffee, Ta matuk'ar yi mishi kyau, Komai na Suraj mai kyau ne, komai yasa kyau yake mishi haka mutane da yawa kan ce.

   Ganin babu Mahaifiyar sa a falon, kamar kullum, Yasan by this time tana falon, Samee dake kallo ya tambaya, "Ina Mama?", " Tana d'aki, yau bata fito ba", Jikin sa ya bashi ba lafiya ba, Hajiya Tumba bata tab'a kaiwa warhaka bata fito ba.

   Saman ya hau zuwa d'akin ta, Sallmar shi uku ba'a amsa ba, Sai a na hud'un ta amsa da k'yar, ba k'aramin jin jiki take ba, Ya murd'a k'ofar d'akin ya shiga.

   Hankalin sa ya tashi yanayin da ya sameta, A rud'e yace "Mama baki da lafiya ne?", Kai ta gyad'a masa.

    " Tashi mu tafi asibiti", Ba musu ta shiga k'ok'arin mik'ewa, Ya kama mata ta mik'e, Ya d'auko hijab ya bata ta saka.

    Ya kamata suka sauk'o k'asa zuwa mota, Feena da Su'ad nata bacci basu san meke faruwa ba.

    Bai nemi taimako ko rakiya kowa ba, Shi kad'ai da ita sai driver suka nufi asibiti,

   Suna zuwa ba b'ata lokaci suka samu ganin Doctor, Bayan yayi mata yan gwaje-gwaje, Yayi admitting d'in ta, Yace "Zasu duba idon ta, dan gano meye matsalar su", Suraj da duk hankalin sa a tashe yake Yace " Dr ina fatan ba wata matsala ba ce sosai", "Bamu sani ba for now, sai mun bincika", Ya numfasa yace "Please do ur best My mum ta samu lafiya, ita kad'ai nake da ita", Ya dafa kafad'ar sa yace "Relax, In Shaa Allah zata samu lafiya", Ya sauke ajiyar zuciya yace " Allah yasa", Dr ya amsa da "Amin" 1

    D'aki mai kyau da komai a ciki, hadda TV da Fridge, aka bata abun ku da masu naira.

    Kwance take, hannu mak'ale da drip tana bacci, allurorin da aka mata akwai mai saka bacci, Ya kalli Mahaifiyar tasa cike da tausayawa, Ya dad'e bai ga ta kwanta ciwo ba.

    Wayar sa ya jawo yayi dialing number Su'ad, Cikin bacci taji wayar na k'ara, Kamar ba zata d'auka ba, Ta duba mai kiran, Ganin Ya Suraj ne yasa tayi saurin receiving tana tashi zaune, Tasan halin sa baya so ya kira waya ba'a d'auka ba.

     "Ki had'o breakfast kizo asibitin Dr Galadanchi", Bai jira amsar ta ba ya kashe, " Ohh Ya Suraj hukuma, Toh waye ba lafiya?", Ta dag'e k'afa, A ranta ta saka cikin yan'uwa ne, Feena dake kusa da ita, ta shiga tashin ta,

STORY CONTINUES BELOW


   Tsaki taja tace "Wai lafiya", " Ya Suraj yace ki tashi mu tafi asibiti", Ai da sauri ta mik'e zaune, Su'ad ta fashe da dariya.

   Masu aiki ta umarta suka had'a, Ba b'ata lokaci suka shirya sun san Suraj baya son jira,

   Motar Su'ad suka shiga zuwa asibitin ita ke driving, A wurin parking suka ga Driver Suraj, Suka tambaye shi "Waye ba lafiya?", " Hajiya", Ya basu amsa,

   Tashin hankali ne ya bayyana akan fuskokin su, Su'ad tace "Tana wani d'aki?", " Sama room 6",

     Da sauri kamar zasu tashi sama suka shiga asibitin, Feena ta fara shiga, Su'ad ta biyo baya.

  Basu lura da Suraj dake zaune ba, hankalin su ya tafi kan Mahaifiyar su da kallo d'aya zaka mata, Kasan tana jin jiki.

    Tuni hawaye ya wanke fuskokin su, Feena ta duk'a tana kama hannun ta, "Allah ya baki lafiya Mama", Cewar Su'ad, " Ku tashi a gurin nan", Suka ji muryar Suraj, Da sauri suka mik'e, suka nemi wuri gefe suka zauna, Suna sharar k'walla.

    Bilkisu tashin ta daga bacci kenan, Da yunwa ta tashi, Brush kad'ai tayi, Ta nufi dining table tayi breakfast, Ta cika cikin ta tam, Ta koma d'aki tayi wanka, Ta shirya, Bata damu ta nemi wani a gidan ba, Ko Hajiya Tumba tana sati bata saka ta a ido ba, Dan bata zuwa gaishe ta.

     Masu aikin gidan a bakin Samee suke ji Hajiya bata da lafiya, Sunji ba dad'i a ran su tare da mata addu'ar samun lafiya, Mace ce mai sanyin hali da daraja dan' adam.

    Hajiya Tumba ta samu bacci sosai, A hankali ta bud'e ido tana jin zazzab'in ya sauka sosai, Sai idonta dake ruwa, bata gani sosai.

    Suraj ya taso ya zauna gefen gadon da take kwance, Ya kama hannun ta yace "Sannu Mamana", Tace " Yawwa Suraj", Ta muryar shi ta gane shi, dishi-dishi take gani kamar an saka mata yana a idon.

    Feena da Su'ad suka shiga yi mata sannu tana amsawa, Abincin rana da aka kawo yayi serving d'in ta, breakfast sai komawa aka yi dashi.

   Da kanshi ya zaunar da ita yana bata, Taci sosai ta saka mishi albarka,

    Suraj yace Su'ad ta kwana da ita, Feena ta koma gida washegari tana da exam, Shima a asibitin yace zai kwana, Doctors ba yadda basu yi dashi ba kan ya koma gida yak'i, Dan dole suka bar sa, Har d'aki suka ce zasu bashi, Yace a'ah, Kusa da ita yake son kwana, Sun jinjina soyayyar da yake mata,

Hajiya bata san wainar da ake toyawa ba, tunda taci abinci Nurse ta shigo ta bata drugs da injections bacci ya d'auke ta, Da ta hana shi kwana.

   Bilkisu ganin har dare bata ji motsin sa ba, Taji dad'i sosai dan a tunanin ta ya koma Lagos, Zulaihat ta kira tace tazo Suraj ya koma, Cike da murna tace gata nan zuwa, Tacewa Mahaifiyar ta Bilkisu ta kirata bata da lafiya, mijinta baya nan zata je taya ta kwana.

     Fetta ta gama cin abincin dare, Tana shirin shiga d'aki ta kwanta, Aliya tace "Gobe zamu je duba Hajiya Tumba asibiti", " Bata da lafiya ne?, Meya sameta?", Ta tambaya cike da damuwa, "Zazzab'i da ciwon ido", " Allah ya bata lafiya", "Amin, Gidan yayi tsit kamar duka jama'ar gidan ne basa nan, Gaskiya Hajiya Tumba mutum ce, Allah dai ya bata lafiya yasa zakkar jiki ce", Fetta ta amsa da "Amin", Ta shiga dak'i jiki a sanyaye, Tana k'aunar Hajiya Tumba saboda kyawawan halin ta.

    Kiran sallar asuba a kunnen Suraj, sam bai runtsa ba, Damuwa da son sanin meye rashin lafiyar Mahaifiyar sa ya hana shi runtsawa,

  Toilet dake d'akin ya shiga yayi alwala, Ya fito ya kabbara sallah, Da ya idar yayi addu'o'in samun sauk'i ga Mahaifiyar sa, Ya tashi Su'ad itama tayi,

    Hajiya Tumba ta farka, Ta buk'aci shiga toilet, Suraj ya kama ta, Ta shiga tana dafa bango,

   " Ya zama dole na nemi masu kula da ita har lokacin da zata samu lafiya", Ya fad'awa kansa, Su'ad da Feena baza su iya ba, ko dan zuwa makaranta, Lalurar ido tana buk'atar komai a taimaka mata, Fatan shi Allah ya bata lafiya.

     Dr ya buk'aci ganin Suraj office d'in sa, "A bisa bincike da muka yi, Tana d'auke da ciwon ido ne, wata jijiya ta tsinke a idon, shiyasa bata gani kuma yake zubar ruwa, dole zamu mata operation gudun kada su daina aiki-aiki kwata kwata", Cike da tashin hankali yace " Please Dr Ku mata yanzu ko nawa ne zan biya, Kada ku bari Mamana ta zama makauniya",

    "Kada ka damu, Ga papers kayi signing a nan", Ba b'ata lokaci yayi signing ya amince a mata aiki, Suka bashi teller na kud'in aikin, Ya laluba aljihun shi bai zo da ATM d'in shi ba ya musu transfer ta POS, and baya mobile banking, Ya zama dole ya koma gida ya d'auko ATM ko Cheque book.

     Fitowa yayi cikin sauri, Driver sa kanshi ya tsorata da yanayin da ya gansa, a zaton sa ma Hajiya ce ta rasu, Da sauri ya bud'e masa k'ofa ya shiga,

   Ya shiga ya tada motar " Ranka ya dad'e ina zamu gida?", "Gida", Ya fad'a murya can k'asan mak'oshi,

    Driver na tuk'i amma gani yake baya sauri, " Yi parking", Ya umurce sa, Yayi parking gefen titi,  Ya koma driver's seat, Yaja motar a 360, Driver kam hanjin cikin sa sai da suka kad'a, Sauran kad'an ya saki fitsari a wando saboda tsoron irin tuk'in da yake, Horn yake kamar tashin duniya, A guje mai gadi yazo ya bud'e gate,

Hamdala Driver ya shiga yi da yaga sun isa gida.

  Kansa ya d'auki zafi, Hanyar d'akin Bilkisu ya nufa, a zaton sa nan ne d'akin shi, Ya murd'a k'ofa ya shiga.

   Bilkisu da Zulaihat ne kwance haihuwar uwar su suna aikata mad'igo, Kansa ne ya mugun sara, ya koma gani dishi-dishi, Abunda idon sa suka gane masa sun matuk'ar girgiza k'wak'walar sa, luu ya tafi zai fad'i.Saurin rik'e k'ofa yayi, Ya kare kansa daga fad'uwa, Addu'a ya karanta cike da k'arfafa ma kansa gwiwa ya tura k'ofar ya rufe tare da murd'a mukulli, Ya cire key ya jefa aljihu. +

    Bilkisu da Zulaihat sun lula duniyar masha'ar su, Sam basu ji shigowar sa da rufe k'ofa ba,

    Cije lips yayi yana tunanin me zai musu su farga, waige-waige ya shiga yi, Can ya hango flask na ruwan zafi, Ya d'auka ya bud'e, Ya shek'a musu a jiki,

   Zafin ruwan zafin a jikinsu yasa suka saki ihu, A rud'e Bilkisu ta diro daga gadon, Tana sosa jiki tana ihun azaba, Zulaihat tana d'aga ido suka had'a ido da Suraj, idon sa ya koma jajir kamar barkono, Guntun fitsari ta saki tsabar tsoro, Ta shiga k'ok'arin sa kaya,

    Bilkisu tuni ta zura riga tayi hanyar fita, Sai k'ok'arin bud'e k'ofa take, Ya jawo ta ya buga kanta da k'asa, Ya shiga k'wallo da ita, Zulaihat tuni ta fara ruwan hawaye a tsorace take,

   Bilkisu ihu take tana neman taimako, "Wayyo Allah Baba Surajo Yaya Surajo, Kawo Surajo kayi mun rai, na tuba", Bakin ta ya kaiwa wani naushi, Dole tayi shiru, jini ya shiga zuba, Sai da ya mata lik'is,

   Ya koma kan Zulaihat, itama ta jibgu, Da k'yar take numfashi, Ya had'a kansu su biyu ya gwara da k'arfi, Kowaccen su ta rik'e goshi saboda azaba, Ya juya kan Bilkisu " Na sake ki saki d'aya, biyu, uku, ki tattara kayanki ki bar gidan nan kafin na dawo", Ihu ta kurma tana fad'in "Na shiga uku na lalace"

   Ya fito, Yana jin kansa na sara mishi, Damuwar shi ta ninku, Al'amarin mata ya k'ara sire mishi, samun mace ta gari a zamanin nan yana da matuk'ar wahala, daga mai neman maza sai neman mata, Baya sha'awar k'ara aure a rayuwar sa, dama tun farko ba shi da ra'ayin aure.

    A daddafe ya shiga d'akin sa, Ya d'auko cheque book, Ya rubuta amount na kud'in da suke buk'ata yayi signing,

  Kamar mara lafiya haka ya fito, Driver ya tausaya masa, "Lallai ciwon Hajiya ya tab'a oga da yawa", Ya fad'a a ransa, Yaja motar zuwa asibiti.

   Office ya samo Dr ya bashi cheque d'in, Yace " Zuwa da daddare za'a mata operation ", Kai kad'ai ya iya d'aga mishi, Ya fito yana dafe kai da yake ji kamar ana buga mishi guduma.

   K'ok'arin b'oye damuwar sa, da tattaro natsuwa yayi kafin ya shiga d'akin da Hajiya take, baya son ko kad'an ta fuskanci yana cikin damuwa.

      " Wallahi ban saku ba, Allah matar sa ce ni har yanzu", Bilkisu ta fad'a tamkar zararriya, "Kamar ya baki saku ba, baki ji me yace ba, ki rufawa kan ki asiri ki tashi mu bar gidan nan kafin ya dawo ya karya mu, wallahi tsoron sa nake", Cewar Zulaihat da a tsorace take,

   Tana kuka ta yafa gyale tace "Muje", Jikin su banda rad'adin zafin duka da k'onuwa na ruwan zafi ba abunda yake.

   Bilkisu babban tashin hankalin ta sakinta da yayi, Zata yi bankwana da daular arzik'i.

    Aunty Jummai ta fito kitchen rik'e da tray zata kaiwa bak'i ruwa da lemo, Bilkisu ta shigo tana kuka da ihu, Zulaihat bata biyo ta ba gidansu ta nufa,

    " Wayyoo Allah na, Suraj ya sakeni saki uku", Ta fad'a tana shigowa cikin gida, A razane Aunty Jummai ta saki tray dake hannun ta, kofunan suka fad'i suka fashe,

STORY CONTINUES BELOW


    "Ke dan uwarki kinsan me kika fad'a, Ya sake ki fah kika ce", "Wallahi ya sakeni Saki uku", Ta fad'a tana k'ara sautin kuka,

    "Yau ni Jummai na shiga uku na lalace, me kika masa?", Sharar k'walla ta cigaba da yi bata ce komai ba, " Zaki fad'a mun ko sai na had'a kan ki da bango", "Kawai dan Zulaihat tazo wurina ta kwana", " Meyasa baki lallab'a shi kin bashi hak'uri ba, Ya zama dole a maida auren nan", "Saki uku ne fah Umma",  " Ko saki dubu ne sai kin koma wallahi",

   "Lafiya nake ta jin hayaniya?", Baban Bilkisu ya fito yana tambaya, " Suraj ne ya mata duka da saki biyu",(Ba tace uku ba, dan k'udurin ta na son Bilkisu ta koma gidan),

"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un, Ke Bilkisu laifin me kika mishi?", " Dan Zulaihat tazo ta kwana", "K'arya kike munafuka da wata a k'asa, zan kira shi naji me kika mishi", " Allah Abba kome zai ce maka kada ka yarda", "Rufe mun baki mutuniyar banza", Ya wuce, Aunty Jummai tabi bayan sa da harara, Ta juyo kan Bilkisu "Kwantar da hankalin ki, gidan Suraj ne kin koma kin gama"

     Bak'i kam tuni suka fito, suka wuce da mamakin me tayi aka sako ta, Sun so jin ba'asi, Ganin ba fad'a zata yi ba, Suka tattara suka tafi.

   Fetta tayi shirin ta cikin atamfa yar' roba d'inkin riga da skirt, Vaseline kad'ai ta shafa a baki, Ta d'auki hijabin ta da yasha guga ta saka, Akwai ta da tsafta, komai nata tsaf yake  bata son k'azanta, Wayarta tayi haske alamun d'aukewar chaji,

   "Yan NEPA sunyi halin nasu, Allah ya nuna mana ranar da zamu rik'a samun wutan lantar ki kamar sauran k'asashe", Ta fad'a, Wayar ta cire jikin chaji, Ta kashe socket, Number masoyin nata tayi dialing, Bai d'auka ba har ta tsinke, Ya biyo kiran,

  Ta d'auka da sallama, Ya amsa, " Sarauniyar kyakkyawan matan duniya", Tasa dariya tace "Kaii Ya Mu'azzam", " Allah kuwa, wai kina kallon kan ki a madubi, kefa ba k'aramar kyakkyawa bace, da zaki je gasar kyau na tabbata ke zaki yi ta d'aya", Ta sake yin dariya, a ranta tana jin dad'in yadda yake yaba ta,

   "Kinci abinci?", " Eh", "Sau nawa?", " Biyu", Baki yi k'ok'ari ba, sau biyar ya kamata kici", "Tabb na zama k'atuwa kenan", " Eh mana", Zata bashhi amsa taji muryar Aliya na kiran ta, "Umma na kira zamu je duba Hajiya Tumba asibiti", " A dawo lafiya, ki kular mun da kanki, duk namijin da ya kalle ki, ki harare shi", Tayi dariya tana kashe wayar, Mu'azzam mutum ne mai barkwanci, duk lokacin da Fetta take tare dashi takan tsinci kanta a nishad'i.

   Napep suka shiga zuwa asibitin, A hanya suka tsaya suka siyan mata fruits na d'ari biyar a matsayin kyautatawa, sun san tafi k'arfin shi.

    Ma'aikatan wurin suka tambaya, Suka nuna musu d'akin da take, Aliya na gaba Fetta na baya,

    Tana shiga idon ta ya sauka kan shi, Zaune yake kan kujera, Yayi crossing leg, Yana danna waya, Bai d'ago kai ba, balle ya amsa sallamar su, Tsintar kanta tayi da fad'uwar gaba, Bata ji dad'in ganin sa ba, Ji tayi kamar ta juya, Ta dake ta k'arasa ciki, Tana kauda kanta daga kallon sa.

Aliya ta fara gaishe ta da mata ya jiki, Ta amsa cike da far'a, Cikin sanyin murya tace "Ya jiki?", " Da Sauk'i", "Allah ya k'ara lafiya, Allah ya tashi kafad'un ki, Allah yasa zakkar ciki ce",

   Add'u'o'in yaji a kunnuwan sa, Yaji dad'in su, Ya d'ago dan ganin wacce, Yarinyar ranar mai lab'e ya gani, Ganin Aliya gefen ta yasan tare suka zo, Ko itace Mamanta amma basa kama, Wata zuciyar tace " Ina ruwan ka da son sanin wacece", "Ina wuni ya mai jiki?", Cewar Aliya, " Kalau", Ya amsa can ciki yadda babu wanda yaji, Idan kana kallon sa ne zaka gane mai yace ta motsin lebb'an sa.

   Ganin amsawar wulak'anci da yama Aliya, Fetta ta d'auke kai tak'i gaishe shi, Ta tsani wulak'anci, Aiko rashin gaishe shi ba k'aramin k'ullar dashi tayi ba, Yana son a bashi girma.

   Ya basar tamkar bai san bata gaishe shi ba, Mik'ewa yayi yace "Ku zauna da ita kafin na dawo", Bai jira amsar su ba, Ya fice, Baya bada umarni ya jira amsa, muradin sa a cika ko a had'u da hukunci.

   Su'ad bata nan, an kira ta tana da test, Ta tafi.

    Hajiya Tumba tana ta jan su da hira,  Aliya ce mai k'arfin mayar wa, suna hirar, Fetta kunya take ji dama ba gwanar surutu bace.

   Har aka yi azahar bai dawo ba, Aliya tace zata tafi, tabar ayyuka a gida, ko girkin rana bata yi ba, Fetta ta zauna har ya dawo, Hajiya Tumba ta mata godiya da ziyara, Duk cikin masu aikin ita kad'ai ce tayi hankalin zuwa.

    Fetta ta kama Hajiya ta kaita har cikin toilet, tayi alwala, Ta fito da ita,  Ta shimfid'a mata darduma ta kama mata tasa hijabi, Itama ta shiga tayi alwala ta kabbara sallah,

   A kusan tare suka idar, Ta taimaka mata ta koma kan gado, Suna sallah driver da Samee suka shigo da warmers na abinci, Shi ya wuce ya bar Samee, Jikin Hajiya ta fad'a tace " Mamana I miss you, Ya jikin ki?", "Da sauk'i My baby", Ta fad'a tana shafa kanta.

    Ko kallo Fetta bata isheta ba, Ba wulak'anta mutane ne da ita ba, tsabar miskilanci yasa bata magana, Ya Suraj part 2 haka su Feena kece mata.

   " Hajiya a zuba miki abincin?", Ta tambaya cike da ladabi, "Eh kad'an amma", Plate ta d'auka ta zuba jollof rice da taji kayan lambu da nama,

   Ta mik'a mata, Gani tayi tana laluben ina cokali yake, D'aukar cokalin tayi ta shiga bata a baki, Hajiya Tumba ta k'ara jin k'aunar Fetta a ran ta.

    Tana cikin bata Suraj ya shigo da sallama, Fetta a ran ta tace ashe yana sallama, Zama yayi a kujera, Ya d'aura k'afa kan d'ya, A ranta tace " Sai jin kai da isa kamar Dan' sarki", Ya ma Hajiya Tumba sannu, Ta amsa da kai.

   Shigowar sa yasa Fetta duk taji ta a takure, Hajiya ta kalleta da murmushi tace " Na k'oshi", Ajiye cokalin tayi ta d'auke plate ta ajiye gefe, "Sannu da k'ok'ari", " Ba komai Hajiya, Zan tafi tunda ya dawo",

   "Naji dad'in zuwan ki sosai, da zaki mun alfarma da kin zauna dani har zuwa lokacin da za'a sallame ni",

    " Ba alfarma muke nema ba, magana ce ta kud'i biyan ki za'a yi", Suraj ya fad'a cike da isa, Da mamaki ta d'ago ta bisa da kallo,

   "Ai ko biyan ta za'a yi, sai an tambayeta idan zata iya", " Zata iya Mum, kud'i fah aka ce",

   Fetta a ran ta tace "Wai me masu kud'i suka d'auki talaka ne, a tunanin su bashi da wani buri sai kud'i, sunyi kuskure kuwa da suka d'auka kowa haka yake, kud'i baya cikin abubuwan da ta d'auka mafi muhimmanci",

   Tunanin ta ya katse jin yace "  You! Ki fad'i nawa za'a biya ki?", Cike da takaici tana jin kamar tace ba zata iya ba, Daraja da k'imar Hajiya Tumba da take gani ta wuce komai.

   Saitin Hajiya ta kalla, Tace "Hajiya ke mace ce da tasan darajar dan' adam ba ruwan ki da talaka ko mai kud'i, zan kula dake fisabillah ko dan na samu ladar jinya" (Da biyu tayi maganar)

  Tab'e baki yayi, A ransa yace "Taji da gulmar ta",

   Hankalin Fetta ya burge Hajiya tace " Allah ya sada ki da alkhairin sa Fetta", "Amin Hajiya",

Ta juya kan Suraj " Toh ka ji ita ba kud'in take so ba", Ya d'age kafad'a with i don't care manner Yace "Kunyar ki yasa bata fad'a ba, meyasa bata ce ba zata yi aikin ba, tana son kud'in kenan", Ya juya kan Fetta " Ina so ki kula da Mahaifiyata kamar yadda zaki kula da taki, kika yi ganganci wani abu ya sameta, zaki fuskanci hukunci mai tsanani, ranar da aka sallame ta zan biya ki daidai da kulawar da kika mata"

   Fetta ranta ya masifar b'aci " Wannan anyi dan' wulak'anci da rainin hankali", ta fad'a a ranta, Darajar d'aya yaci, Hajiya Tumba ta nemi alfarmar ta da wallahi ba zata yi ba, ta nuna mishi ba kowanne talaka ke da kwad'ayi ba.

Post a Comment for "FETTA CHAPTER 5"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...