Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

FETTA CHAPTER 19

FETTA CHAPTER 19

- - Post a Comment
FETTA CHAPTER 19
Tasleem a hargitse ta iso asibitin, kallo d'aya zaka mata kasan bata cikin natsuwar ta, Gaf da shiga ward na masu haihuwa tayi kokarin tattaro natsuwa tare da b'oye damuwar ta, Wata Nurse taci karo da ita, "Excuse me Madam" Ta fad'a tana shan gabanta, "Yes can i help you?" , "Ina tambayar Matar Suraj da ta haihu yau?" "ohh wata nigerian?", "Yes" Ta fad'a tana nodding kai, "Ni na karb'i haihuwar" , "Ohh wow", Hannun ta taja gefen can lungun da ba kowa, Tace "wani taimako zaki mun", Ta zaro dollars cikin jaka wanda zasu kai kimanin dubu d'ari biyar, "Idan kika mun aikin da zan saki sa zan baki su" + Nurse ta zaro ido tace "Wane aiki?", "Ki sato mun babyn", Cike da tsoro tace "Am scared Madam idan aka kamani kashe ni za'a yi", " Ba za'a kama ki ba, da daddare zan zo na karb'i babyn" Tayi k'asa da murya tana rad'a mata yadda zasu yi, Cike da gamsuwa Nurse tayi nodding kanta. Suraj throughout asibitin ya wuni, duk abunda ake buk'ata sai dai ya kira a kawo, Yaso a sallame su a ranar, Dr yace za'a k'ara duba lafiyar babyn. 12 na dare ya bar asibitin zuwa gida, basa bari a kwana, Ya tafi cike da kewar babyn sa, Allah ya dasa mishi wata zazzafar k'auna ta babyn. Fetta na rungume da babyn ta tana bata nono, zuciyarta cunkushe da tsananin k'aunar ta, tare da tsantsar farin cikin da Allah ya sauke ta lafiya, wani b'angare na zuciyarta na fargabar wulak'ancin Suraj tasan yana d'aga mata k'afa ne saboda babyn sa da take d'auke dashi, babbar fargabar ta shine ya raba ta da gudan jinin ta, Bata so yar'ta tayi rayuwar maraici kamar yadda tayi. Nurse ta turo k'ofa ta shigo, Fetta ta d'aga kai ta kalle ta, tayi murmushi, "Zamu maida baby ward na jarirai", Ta mik'a mata ita tana jin kamar a barta ta kwana wurin ta, ta karb'i jaririyar ta nufi d'akin jarirai da ita, A can Dr zai duba ta tare da sauran babies da aka haifa yau. *2:00am* na dare Tasleem ce sanye da kayan nurses, ta saka facemask, zaka rantse tana d'aya daga cikin ma'aikatan asibitin, Ward na jarirai ta shiga, Mai kula dasu ta b'ingire a kujera tana bacci, wanda da had'in bakin ta, taba Nurse Charlie lemo mai d'auke da maganin bacci, ta bata tana sha ba'a yi minti biyu ba, bacci ya d'auke ta. Nurse Charlie ta d'auko babyn ta mik'awa Tasleem, Tayi saurin ficewa daga ward d'in tana sauri sauri, gudu gudu, Fatan ta ta fice daga asibitin ba tare da kowa ya ganta ba. K'arar wayarta ya tashe ta daga nauyayyen baccin da take, Kamar ba zata d'auka ba, Ta jawo ta kanga a kunne ba tare da ta duba mai kiran ba, "Me kuke needing?" Taji muryar Suraj, "Nothing" Ta bashi amsa tana mamakin kiran sa cikin dare. Ya kashe wayar ba tare da ya sake cewa komai ba, Ta ajiye wayar, ta koma baccin ta. Suraj hankalin sa yaji ya kasa kwanciya, yana son dawowa asibitin, Ya mik'e ya d'auki mukullun mota ya nufo asibitin. Da dai k'ofar shiga yaci karo da Tasleem zata fito tana sauri bata kallon gabanta, Kaurar sa tayi dashi, yasa tayi saurin ja da baya, idonta cikin nasa, Gabanta yayi mummunan, tashin hankali ya bayyana kan fuskar ta, Sam bai ganeta ba, Ta manta akwai face mask a fuskar ta, tuni ta sadak'ar ya gama gane ta, Idon sa ya kai kan babyn dake hannun ta, "My little angel" Ya furta da k'arfi, Tuni ta saki guntun fitsari tsabar tsoro, "Ina zaki kai mun babyna?" Tayi shiru ta kasa bashi amsa, zuciyarta na dukan uku uku, tamkar zara fasa k'irjin ta ta fito, "Nurse" Ya fad'a a d'an tsawace, Jin bai ganeta ba, Tayi k'ok'arin tattaro natsuwa tace "Zan kai babyn wurin mum d'inta ne she have been crying", "I guess nan hanyar fita ce kuma banjin babyn na kuka ba" Ya fad'a yana bin ta da kallon tuhuma, Tayi k'arfin hali cewa "I was carried away, yanzu tayi shiru", Hannu yasa ya karb'i babyn ya wuce ba tare da ya sake ce bata komai ba, A zuciyar sa bai yarda da ita ba. Tasleem a guje ta fice asibitin ta shiga motar ta, taja a 360 bata dawo natsuwar ta ba sai da taga tayi nisa da asibitin. Ajiyar zuciya ta sauke da hamdala bai ganeta ba, Wani k'ullotin bak'in ciki taji ya tsaya mata na rashin cikar burin ta, "Ba zan tab'a hak'ura da kai ba Suraj, sai na raba ka da shegiyar baroroji da yar'ta" Tayi assuring kanta ta buga sintiyarin mota. Direct office na Dr ya nufa, ba b'ata lokaci ya samu ganin sa, Bayan sun gaisa, ya buk'aci sallama, Dr yace sai gobe, Suraj ya mishi narrating abunda ya faru, Ya k'ara da cewa ba zai bar family shi su kwana ba, Dr yayi mamakin jin lamarin yace zasu yi bincike, Ya rubuta musu takardar sallama. Fetta bacci take hankali kwance, Suraj ya turo k'ofar d'akin ya shigo, Haushin ta ya kamashi ganin tana bacci a natse, Yana k'ok'arin rasa babyn sa. Bottle na ruwa dake gefen gado ya d'auka, ya zuba a baki, ya watsa mata a fuska, Firgigir ta mik'e, ranta ya matuk'ar b'aci, "Salon wulak'ancin da ya fara dashi kenan, idan da ta d'auka yanzu bara ta d'auka ba" Wani kallo ta jefa masa mai cike da takaici, "Wacce irin uwa ce ke da bata damu da yar'ta ba" , Mamaki ne ya cika ta gani yazo da sabon rainin hankali, ta raini ya' wata tara cikin cikinta, ta haife ta bayan azabar da tasha sannan yace bata damu da ita ba, idan ma yazo da salon raba su toh wallahi bai isa ba, "Duk duniya babu wanda ya kaini so, k'auna da damuwa da ya'ta idan ma wani shiri kake ka gaggauta warware shi", Da kallon mamaki yabi ta, ya kasa furta komai, Ya fice daga d'akin da babyn a hannun, Ganin haka ta mik'e tabi bayan sa, Tayi saurin shan gabansa, "Ina zaka je mun da ya'?", Ganin idan ya biye ta zasu yi creating scene, Yace "Je ki kwaso kayan ki zamu koma gida" Ta sauke ajiyar zuciya, ta koma da sauri ta tattaro kayanta, ta nufi motar, ganin take tamkar zai rabata da yar' ta. A motar ba mai cewa kowa komai har suka kawo gida. Ita ta fara fita daga motar rik'e da basket na abinci, Jane tayi saurin karb'a a hannun ta, Suraj ya fito rungume da babyn , Key na motar ya jefawa d'aya daga cikin ma'aikatan yace idan sun gama kwashe kaya yayi locking. 1 Fetta toilet direct ta nufa, ta tub'e kaya, ta fara wanka, Gaba d'aya bata jin dad'in jikinta, wankan da tayi asibiti bai gamshe ta ba, Suraj motsin ta yaji a band'aki, ya kwanta kan gado tare da d'aura baby kan k'irjin sa, Cikin minti biyu bacci ya d'auke sa, dama bacci ne sosai a tare dashi. Fetta ta fito ta kai dubanta gare su, ta girgiza kai, ta shirya cikin kayan bacci, ta kwanta gefen su, in less than 5mins bacci ya d'auke ta. Bilkisu kullum sai ta duba Suraj a facebook da instagram, whatsapp tuni ya dad'e da blocking d'in ta saboda messages da take damun shi, ganin haka yasa bata mishi a facebook da IG amma duk post da zai yi sai ta kalla. Tana zaune tsakar gida tare da Aunty Jummai wacce duk ta rame ta fige, ba damar ta fita sai ta samu masu nuna ta, ana zund'en ta hakan yasa ta rage fita idan ba ta kama dole ba. Wayarta take faman latsawa tana tauna chingum kamar tsohuwar karuwa, Ta kai kan hoton jaririyar da Suraj yayi posting, K'irjinta yayi mummunan bugawa tace "Umma Fetta ta haihu", Aunty Jummai ta mik'e zumb'ur "Da gaske?", "Wallahi kinga hoton yar' ya saka a facebook", Tamkar an soketa da kibiya haka taji wani bak'in ciki ya soko zuciyar ta, "Umma mu kashe yarinyar nan kinga yadda yake nuna farin cikin sa, ina tsoro na rasa Ya Suraj" "Kwantar da hankalin ki ba zaki rasa shi ba, ai zasu dawo ba can zasu tabbata ba, dole ta daina numfashi a doran k'asa, wannan karon har uwar zan had'a", Bilkisu ta fad'a jikinta tace "Ki taimakeni Ummana Dan Allah wallahi ina masifar k'aunar Ya Suraj", Ta shafa bayanta tace "Kamar kin koma gidan Suraj kin gama", Bilkisu a ranta tana fatan hakan, da tafi kowa farin ciki. Kukan baby ya tashe su lokaci d'aya, Fetta tasa hannu ta d'auke ta, Ta shiga breastfeeding d'in ta, Suraj wayar sa ya jawo ya duba time, 10mins pass 7, Yayi salati ya mik'e yana mamakin irin baccin da yayi, Toilet ya shiga ya d'auro alwala, Ya gabatar da sallah. Babyn ta koma bacci, Ta tashi zata shimfid'e ta, Ya mik'o hannu alamun ta bashi ita, Ta mik'a masa, murya k'asa k'asa tace "Ina kwana?", "Lafiya", Ya amsa kamar dole, Ta tab'e baki ta shige toilet. Wayar sa ya jawo yayi kira, "Hello Sir", "Ya maganar ticket na 9ja da na maka", "Sir za'a samu amma sai nan da 1 week wasu sunyi booking since", Tsaki yayi yace "Ina so in less than 2days zanyi doubling kud'in da suka bayar", "Ok Sir", Yana kashewa, kiran Hajiya ya shigo, Yayi rejecting, Yabi kiran, "My mum ina kwana?", "Lafiya lau My son, Ya kwanan jikalle?", Yayi dariya yace "Alhamdulillah gata tana bacci", "Toh Mashaa Allah, Ina Maman ta?", "Tana toilet", "Yaushe zaku dawo, ya kamata ku dawo da wuri saboda wankan jikalle da ita kanta Fetta", "In Shaa Allah zuwa jibi, "Allah ya kaimu ya dawo daku lafiya", "Amin Mum", "A shafa mun kan jikalle", "Ok Mum", Yayi hanging up Shi ba ma dan wankan baby ba, Hankalin sa ya karkata 9ja tunda yaga ana attempting guduwar mishi da baby, duk da 9ja d'in ma akwai mak'iya masu harin babyn tun kafin tazo duniya, Zai yi iya k'ok'arin shi wurin kare yar' shi, "No harm will come to you my baby" Ya fad'a tare da sumbatar ta. Fetta ta fito daga wanka, tana goge jikin ta da toilet, Kallo d'aya ya mata ya kawar da kansa, "She is always glowing tana k'ara kyau", Ya fad'a a ransa, wata zuciyar tace "Ba dole ba ta samu hutu", Ya katse tunanin yace "Zo ki d'auke ta ki mata wanka", "Ban iya ma babies wanka ba", Wani banzan kallo ya watsa mata yace "Wankan baby har wani abu ne, oya zo ki d'auke ta kafin ranki ya b'aci" Ganin tilasta mata zai yi kuma ita har ga Allah bata iya ba, Ta shagwab'e fuska tace "Wallahi Allah ban iya ba", Yaja tsaki yace "Ragguwa, i wonder yadda kika haihu nasan sun sha raki", "Naji dai, tunda har na haihun" Ta fad'a tare da murgud'a mishi baki, "Wallahi zan zubar miki da hak'ora", Sanin k'aramin aikin sa ne, Tayi shiru ta d'auko cream tana shafawa, Bath na wankan yara ya d'auko ya zuba ruwan d'umi, ya d'auko sabon babies ya ajiye, Ya d'auki baby ya cire mata kaya, Yana sata cikin ruwan ta tsala ihu, yayi saurin cire ta, "Sorry my little angel", Kamar tasan abunda yake cewa tayi shiru, Ganin tayi shiru ya d'auki sabulu, ya goga mata, ya mayar cikin ruwa, santsi yaji yana neman sakinta ta nutse cikin ruwan, yana ta k'ok'arin rik'e ta, tana k'ara sub'ucewa, ya tsorata hankalin sa ya tashi, gashi sai tsala ihu take, Fetta na gefe na dariya, Suraj duk ya had'a zufa, ya santsi ya hana shi fitar da ita cikin ruwa, da ya d'agata zata koma, Fetta ganin idan ta k'yaleshi babyn zata iya nutsewa cikin ruwa, Tazo ta d'auke ta, Tana mishi dariya, Ajiyar zuciya ya sauke, Ganin tana mishi dariya ya wani maze kamar ba shi ba, "Ke lafiya zaki d'auke ta, kince baki iya ba, ina mata kuma zaki hana", Wata dariya ta sake fashewa da ita tace "Kana mata me, ko dai kana k'ok'arin nutsar da ita cikin ruwa" Ya d'aure fuska tamkar bai tab'a dariya ba "Wallahi zaki fuskanci hukunci, Suraj baya d'aukar raini", Yana fad'ar haka ya fice d'akin, "Borin kunya" Ta fad'a tana dariya, Jane ta kira ta kama mata, tana watsa mata ruwa ta mata wanka, Ta shirya babyn ta fito d'ass da ita, So cute kamar ka sace ka gudu. Suraj falo ya koma yayi breakfast, ya jawo system d'in shi yana dubawa, "What!" Ya fad'a da k'arfi, Wayar sa ya jawo yayi dialing number yaron sa Sabeer, Bugu d'aya ya d'auka, dama yana jiran kiran ogan nasa, "Sabeer me nake gani?", "Wallahi Sir", "Shut Up Useless naga ka fara sa wasa ko, kana so nayi smashing head d'in ka", "Kayi hak'uri Sir" "Make sure you clear the mess kafin na dawo" Yana fad'ar haka ya kashe wayar tare da buga k'afar sa. + Fetta tunda ta shiga labour bata k'ara bi ta kan wayarta ba, sai yanzu ta d'auka taga missed calls na yasmeen sunfi a k'irga, Tayi dialing number ta, Sai da ta kusa tsinkewa tayi picking, "Hmmm Nasan matsayina ace kin haihu sai dai naji a gari", "Kiyi hak'uri k'awata wallahi sai yanzu na d'auki wayar, kinsan haka kawai bazan k'i sanar dake ba", "Naji yanzu dai kiyi pics na babyna ki turo mun shi zai sa ki wanke kanki", "An gama", Tayi hanging up Cikin minti 15 tayi ma baby pics ta tura mata, Sai ga kiranta ta whatsapp call, "Wow wallahi babyna so mashaa Allah kamar ta d'aya da babanta ko kad'an bata biyo ki ba", "Naji", "Ni dai ku dawo 9ja, can't wait to hold my baby", Kiran da taji yana mata yasa ta kashe wayar. D'aukar babyn tayi ta fito da ita, ba bacci take ba, Tun daga bakin k'ofa yake kallon su, wani kyau yaga sun mishi abun burgewa, kamar ya tashi ya rungume su, ya maze, Tazo gabanshi ta d'aura mishi ita kan cinya, Turaren ta mai sihitaccen k'amshi ya daki hancin sa yasa shi lumshe ido, bai san lokacin da ya kamo hannun ta ba, Ya bud'e idonshi cikin nata, ba wanda ya iya kawar da kansa, Wani abu suke ji game da juna da ba zai fassaru ba, Kusan minti uku suna haka, K'arar wayarshi yasa suka farga, tayi saurin janye hannun ta, ta juya, ta shige kitchen. Noodles ta dafa, ta had'a tea, ta gaji da cin abincin masu aikin, Dining table ta zauna tana ci, Suraj na satar kallon ta, Yau wani irin kyau yaga ta mishi. Tasleem gaba d'aya ta kasa natsuwa, kwata kwata bata runtsa ba, Breakfast da Fauzy ta kawo mata ta kasa ci, "Frnd wai meke damun ki ne?", "Ba komai", "A'ah tun jiya da daddare na lura akwai abunda ke damun ki", "Kar ki damu", "Shikenan tunda ba zaki gaya mun ba, zan tafi lectures", "Ok" Ta fad'a ba tare da ta d'aga kai ta kalle ta ba, "Ban tab'a neman abu na rasa ba, dan haka bazan fara akan ka ba Suraj", Ta mik'e tana zagaye d'akin. Fetta na d'aki kwance tana sauraren wa'azin Malama Khadija a wayarta, Suraj ya shigo "Ki tashi zamu fita", Ta amsa da "Toh" tana mik'ewa, ta kashe wa'azin, K'aton mayafi ta d'auka ta yafa, Suraj tuni ya fice daga d'akin da baby a hannun sa, Fetta ko da ta fito har ya kai mota, Ta bud'e gaba ta shiga ba tare da tace mishi komai ba, 6 Bakin wani had'add'en mall taga yayi parking, Ya mata umarceta ta fito, Ciki suka shiga, yaja basket guda biyu, Ya mik'a mata d'aya, Wurin kayan babies ya nufa, Tabi shi a baya, Kaya ya shiga jida hadda na wasan yara, Mamaki ya cika ta ganin uban kayan da yake kwasa, bayan akwai wasu da yawa gida, "Uhmm nace ba kamar kayan nan sunyi yawa", Harara ya watsa mata yace "Ina ruwan ki, abeg je ki zab'ar wa su Hajiya da Umman ki tsaraba", Ba tare da tace komai ba, Ta nufi wurin dogayen riguna, Kowa sai da ta d'aukarwa tsaraba hadda su Su'ad, Hajar da Ali ma bata manta dasu ba, Ganin bata d'aukar wa kanta komai ba, Yace "Don't you need anything", Ta mishi nodding kai, Wurin dogayen riguna ya nufa ya zab'o mata masu azabar kyau, yana so yaga tasa abaya ba k'aramin kyau yake mata ba, Ita mamaki ya bata ganin yadda bai damu da kashe kud'i ba, tamkar wanda bai san zafin su ba, abaya har sun soma mata yawa, ko a saudia ya siyan mata wasu, gudun kar tayi laifi yasa tayi shiru, Kud'i masu yawa taji an ambata duk da ba wani gane kud'in america take ba, tasan kud'i ne masu yawa, Ya mik'a ATM d'in sa suka zara, Ma'aikatan suka biyo su da kayan har mota. Gida suka koma, A falo su Jane suka baje kayan da suka shigo dasu, "Ki shigar dasu d'aki, ki shirya gobe zamu koma 9ja, flight d'in mu 6:30am", Bata san lokacin da ta saki wani murmushi ba, Farin ciki ya lullub'eta tayi missing Umman ta dasu Yasmeen, D'aki ta shiga ta hau had'a kaya, bayan ta shirya komai ta jawo wayarta tayi dialing number Aliya, bugu d'aya ta d'auka, "Mutanen landan", "Umma ina wuni?", "Lafiya lau, ina kishiyata?", "Gobe dai zaki ganta", "Kaii amma naji dad'i, me kike so a dafa miki? duk da nasan Hajiya zata had'a muku algwagwajiya", "Dan' wake", "Dan' wake Fetta ki rasa abunda zaki ce sai shi", "Eh Umma tunda nazo nan garin nan ban ci ba", "Toh shikenan, ki gaida Mai gidan, naji Mallam na kirana", "Sai anjima ki gaishe shi", "Zai ji" Fetta ji take kamar ta jawo gobe, ta ganta a 9ja, bacci ma rabi da rabi tayi, Suraj ya lura da d'okin da take, bai ce mata komai ba. Kiran assalatu a kunne ta, ta tashi ta shiga kitchen ta had'a musu breakfast, kasancewar bata sallah, Ko da ta dawo d'akin Suraj na sallah, Toilet ta shiga ta had'a ruwan wankan baby, Ta kira Jane ta kama mata, Tayi mata ta shirya ta, itama tayi ta shirya cikin abaya ta matuk'ar yi mata kyau, Suraj sai satar kallon ta yake yana jin tamkar ya rungumeta, 6:00am daidai suka gama duka shiri, Jane suka shigar musu da kaya mota, Suraj ya musu alheri mai yawa, Suka shiga mota suna waving juna, Driver yaja zuwa airport. Su'ad na gaban dressing mirror tana kwalliya, Tace "Sis ashe baroroji ta haihu", "Haba dai?" , "Wallahi", "Yaushe? Me ta haifa?", "Wai yau 3days, Baby girl, nima d'azu Mama ke tambayata wai mun kira mun mata barka", "Nace ai ban ma san ta haihu ba, ta hau ni da fad'a wai bama kira mu gaishe ta kiji fah", Feena tace "Tabb wannan banzar zamu kira mu gaisar, ta tsinana mana me", "Ai shine, ni wallahi ko dawowa sukayi kallo basu isheni ba", "Sune zasu dawo yau kenan, shine Mama ke ta faman hidima, tasa masu aiki suyi girki ya kai kalar biyar bayan snacks da drinks, ana ta fama gyaran gida", Su'ad taja tsaki tace "Kai kace yar governor za'a tarba, ba yar mai gadi ba", "Bari ke dai, ni ko babyn bana son gani", "Nima wallahi" Wayar Su'ad da tayi k'ara ta katse musu hirar, "Am sorry darling, gani nan fitowa", Ta d'auki turare ta bad'e jikinta dashi, Feena ta kalle ta tace "Mu dai Allah ya nuna mana ranar biki mu chashe", "Kar ki damu Sis very soon", Ta fice. Yana jin shigowarta motar, Ya d'auke kai ya b'ata rai, Kwantawa tayi jikin shi tace "Haba habibina Am sorry" Ta sumbaci lips d'in shi, "Bazan hak'ura ba" Ya fad'a yana sake d'aure fuska, "Babyna please me kake so na maka ka hak'ura", A kunne ya rad'a mata "Muje hotel", Ba tare da wani ja ba tace "Muje", Su'ad tayi nisa a soyayyar Adnan, ko kad'an bata son b'acin ran sa. *AMINU KANO INTERNATIONAL AIRPORT* Jirginsu Suraj yayi landing safely, Ya kalli Baby dake hannun sa yace "My little angel kin dawo origin d'in ki", Fetta ta kalleshi tayi murmushi, "Yana magana tamkar tana jin sa", A zaton ta a zuci tayi maganar sai ji tayi yace "Is she deaf da bara taji ni ba", Fetta ta tab'e baki ta mik'e tayi hanyar fita jirgin, Drivers d'in shi already suna airport suna jira, ba b'ata lokaci suka shiga, Suka ja zuwa gida. Yasmeen tuni tana gidan ita da Aliya dasu Hajar suna jiran isowar su, Ana yin horn Yasmeen tace "My baby is here", Banda tana shakkar Suraj, waje zata fita ta tarbe su. Tun daga bak'in k'ofa ta buga tsalle ta rungume Fetta, "Oyoyo Maman Baby", Hajiya tuni ta karbi babyn hannun shi, Ta shiga juyata tana fad'in jikalle oyoyo, Aliya kuwa sai washe baki take, Hajar da Ali suka mak'ale Fetta, Bayan gaishe gaishe, aka dabaibaiye su da abinci kala kala, Fetta kad'an taci shima dan kar Hajiya taji ba dad'i, Ta jawo cooler dan' waken da Aliya ta mata, Ta fara ci, sosai taji dad'in shi. Feena na d'aki na jiyo su, tayi tsaki, taja bargo ta lullub'e tamkar mai bacci, "Ina su Su'ad ne?", Suraj ya tambaya, "Su'ad sun fita tare da Adnan, Feena kuma na d'aki ina ga bacci take", "Mum bai kamata ana barin ta suna fita tare ba, tunda ba auren ta yayi ba", "Hakane kuma In shaa Allah daga yau bazan k'ara bari ba", "Zanje na watsa ruwa na huta", "Toh Allah ya hutar da gajiya", Ya amsa da "Amin", Ya mik'e, a zaton sa Fetta zata biyo sa, sai ma k'ara gyara zama da tayi. "Fetta ga d'aki can nasa an gyara miki, idan kika buk'atar wanka ki huta, anan zaki zauna har sai kinyi arba'in", Fetta murmushin k'arfin hali tayi tace "Nagode Hajiya", "Meye na godiya, kefah ya'ta ce", Har cikin ranta bata jin dad'in haka ba, taso ta koma ta zauna da Umman ta, tayi kewar zama dasu shine babban dalilin da yasa take zumud'in dawowa, Aliya ma sam bata ji dad'i ba, taso Fetta ta zauna dasu, har d'akin Fetta ta gyare tass tayi sabon fentin, yanzu ba laifi tana samun kud'i. Fetta ta mik'e jiki a sanyaye ta shiga d'akin, ba k'aramin gyara Hajiya tasa aka mishi ba, Komai na buk'ata akwai, Aliya ta biyo bayanta, Bakin gado ta zauna kusa da ita, tare da kamo hannun ta, Tace "Kar ki sa damuwa a ranki kinji Fetta, k'aunar da Hajiya kema tasa haka, nima na so ki zauna a wurin mu, Amma In Shaa Allah kullum zan rik'a zuwa ina wuni anan, ni zan rik'a ma baby wanka", Taji dad'in jin haka kullum zata rik'a ganin Umma dasu Ali, Yasmeen ta shigo rik'e da baby tana kuka, "Gata ki bata", Ta karb'eta tana jijjigawa, Kunyar Aliya take ji, ba zata iya breastfeeding a gabanta ba, Aliya ta fuskanta tace "Bansan sai yaushe zaki daina kunyar nan ba, yarinya kamar fulani", "Wai kunyar ki take ji", Yasmeen ta fad'a tana dariya, "Eh wai, ai bari na tashi na bata wuri", Fetta ba tace komai ba, sai faman jijjiga baby take, Aliya ta fita, sannan tayi breastfeeding d'in ta, "Baki ji kunyar d'aukar cikin aka ganki dashi ba, sai shayarwa", Harara ta wulla mata tace "Ki fita a idona Yasmeen", Ta cigaba da dariya, Sai da tayi bacci ta shinfid'e, Tace "Dan Allah kama mun na fitar da tsaraba", "Ba zaki bari ki huta ba", "A'ah gara nayi gaba d'aya na huta" Ta fitar ma kowa da tsarabar shi, har yasmeen kowa yayi farin ciki, sab'anin su Su'ad da ko d'aki basu fito ba, tana dawowa ta shige abun ta. Aunty yelwa ta rafsa tagumi, rashin sanin halin da yar'ta ke ciki ba k'aramin damun ta yake ba, Binta tazo ta janye mata hannu tace "Ba kyau tagumi Mama", "Dole nayi tagumi, rashin sanin wane hali yar'uwar ki take ciki ba k'aramin damuna yake ba", "Addu'a zaki rik'a mata Allah ya kareta a dukkan inda take", "Ina yi Binta", Ta fad'a tana matsar k'walla. Kiran sallar magrib ya tashi Suraj daga bacci bai ga alamun Fetta tazo part d'in ba, "Me take nufi? Meya hana mata zuwa?", Alwala yayi, ya gabatar da sallar magrib, Ya nufi sashen Hajiya dan jin dalilin Fetta na rashin zuwa part d'in ta har ana magrib bata zo ba.

Post a Comment for "FETTA CHAPTER 19"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...