Wednesday, 23 September 2020

FETTA CHAPTER 18

FETTA
CHAPTER 18


Jirginsu yayi landing a airport na Madina, Fetta tayi nisa a bacci, Suraj ya kai duban sa gare ta, Yayi tapping d'inta da hannu, Ta bud'e ido ta zube su a kan shi tare da karanta addu'ar tashi daga bacci, Har ya mik'e tana zaune saboda jikinta da ya mata tsami, +

"Baki gaji da jirgin ba ne, naga ya miki dad'i hadda bacci", Shiru ta masa tamkar ba da ita yake ba, Ganin bata kula shi ba, Ya fice ya barta,

Da k'yar ta mik'e tabi bayan sa, Taxi suka d'auka zuwa hotel, Had'add'en hotel suka nufa, Ya musu lodging d'aki, Fetta ba abunda take buk'ata kamar kwanciya, Suna shiga tabi lafiyar gado, Suraj toilet ya shiga yayi alwala, ya fara rama sallolin da ake bin sa, Itama mik'ewa tayi ta shiga toilet tayi alwala, Ta gabatar da salloli,

Telephone na d'akin ya d'auka, Yayi dialing number kitchen, Yayi ordering shinkafa da kaza, Cikin mintuna kad'an aka kawo, Daga bakin k'ofa ya karb'a, Fetta wacce bacci ya fara d'aukar ta akan sallaya, taji muryar sa " Tashi sarkin bacci",

Mik'ewa tayi tana mamakin yaushe bacci ya d'auke ta, Da hannu ya mata alama tazo taci abinci, Kusa dashi ta matsa, Ta kai hannu zata d'auki spoon, ya rik'e hannun ya matsar dashi gefe, Ya d'auki spoon d'in ya d'ibi abinci ya kai bakinta, Ba tare da wani tunani ba, ta bud'e baki ya saka mata, tasan yana yi ne saboda babyn shi, A tare suka cinye abincin, Yana feeding d'inta, Ya saka tissue ya goge mata baki, ya goge nashi.

Kayan sa ya shiga tub'ewa, Ya umarceta ta cire nata, Da kallo tabi sa, Ya d'aga mata gira alamar Ya dai, "Ka fara yin wankan", " A tare zamu yi", Zata sake magana, Ya saka hannu akan lips d'inta alamar tayi shiru, Zip na rigar ta ya zuge, tare da b'alle bra d'inta, Tayi saurin saka hannu tana kare gabanta, "Wane dare ne jemage bai gani ba", Ya fad'a yana kafe ta da ido,

Ta sunkuyar da kai cike da kunya, Hannun ta yaja zuwa toilet, Tabi sa tamkar rak'umi da akala, a tare suka yi wankan cike da kunyar sa.

Ta riga shi fitowa, da sauri ta shafa mai, tana saka kayan bacci, ya fito, tayi saurin kawar da kanta gefe, sam bata so su had'a ido, A gaggauce ta saka kayan, tabi lafiyar gado tare da jan bargo ta rufa.

Aunty Jummai ta dawo daga kasuwa rik'e da ledoji a hannu taci karo da Sahabi a zaure, " Sahabi" Ta kira sunan shi cike da mamaki da fargabar ganin sa, "Hajjaju", " Lafiya dai?", "Lafiya ce ta kawo haka", " Toh Madallah", Ta fad'a tare da sauke ajiyar zuciya, "Nazo ne kawai mu gaisa", " Ka kyauta kuwa", "Ni zan koma", Ya fad'a tare da saka hannu a aljihu ya zaro dubu biyar ya bata, Ta zaro ido tace " Sahabi ina ka samu kud'i?", Yayi guntun murmushi yace "Yanzu komai ya zauna, wani hamshak'in mai kud'i nake wa aiki, shirin aure ma nake, zan zo na d'auke ki muje kiga gidana", " Ahh abu yayi kyau, Allah ya sanya alkhairi", "Amin"

    Ta rako shi bakin k'ofa, Ya nufi dalleliyar mota ya shiga, Aunty Jummai tabi motar da kallo, ta tafi da imanin ta, "Lallai Sahabi yaja kaya, bari ya dawo na rok'e sa kud'i naja jari",

Ta koma cikin gida, a tsakar gida ta tarar da Balkisu, tana kwalliya, " Umma sannu da zuwa", "Yawwa sai ina?", " Wurin aiki", "Wai wannan aikin naku ba'a zuwa ne sai da kwalliya", " Umma ai gara ka k'ure a daka kar a raina ka", "Ke ko, da Allah yayi ki yar' masu kud'i da bansan ya zaki yi ba", " Kai Umma", "Ai gaskiya ne", Tayi dariya tana cigaba da kwalliyar ta, Aunty Jummai ta shige ciki.

      Washegari Suraj da Fetta sun zagaya garin Madina, ya kai ta wurare Fetta nata raba ido, garin ba k'aramin kyau ya mata ba, Sun ziyarci kabarin Manzo SAW, Sunje wani shopping mall, kayan babies da yawa ya siya, Itama yace ta zab'i abunda take so, Turare kad'ai ta d'auka, Ya harare ta yace " Kilibibi", Gefen dogayen riguna yaje ya zab'o mata guda biyar masu masifar kyau da tsada, Wurin biyan kud'i tayi mamakin jin tsadar su, Daga nan suka wuce wurin cin abinci, Yayi musu order dankali da kaza, Kad'an taci, Ta ture plate d'in gefe,

STORY CONTINUES BELOW

Da kallo yabi ta, Tayi tamkar bata ga yana kallon ta ba, "Me kike nufi?", " Na k'oshi", "D'auka ki cinye", Ya fad'a with command, " Allah na k'oshi, amai zanyi", Ta fad'a cikin shagwab'a, "Kici kiyi aman", " Ni dai na k'oshi", Ta turo baki, "Kinsan Allah ko kici ko na miki d'ure", Ta waiga taga mutanen dake wurin, kuma tasan ba k'aramin aikin sa ne yayi ba, Bata shirya ya kunyatata ba, Ta jawo plate d'in, ta shiga ci cike da takaicin sa,

" Ayi ta ma mutum dole", Yaga bakin ta ya motsa, but bai ji me tace ba.

     Ana kiran isha'i suka koma masaukin su, Sallah suka gabatar, Ya jawo system d'insa yana operating, Fetta wayarta ta d'auka ta kunna data, messages suka shiga, Yasmeen na online suka shiga chatting, Tana tsokanarta akan Suraj.

    Wayar sa ta d'auki ruri, Ganin mai kiran ya saki murmushi ya d'auka, "Hannu na a wuya my love", Fetta wacce hankalin ta ke kan chat, jin sunan da ya fad'a ta d'ago ta kalle sa, tare da jin b'acin rai,

     " Ai nayi fushi" Cewar Hajiya, "Am sorry My one and only momma", Jin ya ambaci Momma taji zuciyar ta tayi sanyi, " Are u OK?, meyasa zaki ji haushi?", "Ya ilahi", Ta furta tare da kawar da tunanin, ta mayar da hankalin ta kan chat.

     " Naji, ya kuka isa?", "Lafiya lau", " Ina Fetta?", "Lafiya lau", "Bani ita",

   Ya mik'a mata wayar, ta taso ta karb'a tare da kangawa a kunne, " Ina wuni?", "Lafiya lau Fetta", " Ya gajiyar hanya?", "Alhamdulillah", " Ya jikin ki?", "Alhamdulillah", " Mashaa Allah, Allah ya raba Lafiya", Ta amsa da "Amin", Cike da kunya, Suka yi sallama ta mik'a masa wayar, shima suka yi sai da safe.

    
     " What! Sun bar k'asar", Tasleem ta fad'a tare da jefar da wayar, Ta fad'a kan gado, ta cukwikwiya bedsheet, "Noo wallahi sai na auri Suraj, sai na raba shi da yar' iskar baroroji dangin tsiya", Mik'ewa tayi ta nufin sashen Mahaifin ta,

   Yana zaune falon shi yana karanta newspaper, Ganin yanayin ta hankalin sa ya tashi, " My daughter meya faru?, waya tab'a ki?", Ta fad'a jikin sa ta saki kuka, A rud'e yace "Gaya mun mene ne?", " K'awata ce tamun gori", "Gorin me?", " Wai babanta ya kaita London karatu", "Meye na tada hankalin ki toh, ko ina kike so a fad'in duniyar nan zan kai ki, bana so kiyi nisa dani shiyasa ban  kai ki abroad karatu ba, fad'i wacce k'asa kike so, farin cikin ki shine nawa"

     "Daddy nima bana so nayi nisa da kai, ka biya mun naje nayi 1month a can, tasan Daddyna nada kud'in kai ni", " Toh My daughter yaushe kike son tafiya?", "K'arshen watan nan", " Kin tafi kin gama, kada na k'ara ganin hawayen ki", "I love you My Daddy", Ta manna masa kiss, Ta fice.

   Kan gado tayi tsalle tace " Ina nan zuwa gare ka Suraj, kai nawa ne ni kad'ai"

   Kwanan su biyu Madina, suka tafi Makkah, Fetta a gajiye ta iso, zaman mota da suka yi na awa biyu, taji tamkar sunyi awa takwas, A kusa da harami ya kama musu hotel, Yadda zasu ji dad'in zuwa ka'aba ba tare da wahala ba,

    Fetta hadda hawayen farin ciki tayi na ganinta d'akin ka'aba, Tayi addu'o'i sosai, Ta rok'awa iyayenta rahma da gafarar ubangiji, Suraj shima yayi addu'o'i wanda rabi akan Allah ya sauketa lafiya ne, ya raya masa babyn shi.

    "Sauke ni anan na shiga gidan Hajiya, kwana biyu ban je ba", Cewar Bilkisu, (zuwan ba Allah da Annabi ba ne, sai dan jin me suke ciki), Driver Hajiya Rabi ya sauketa ta shiga, Ganin motocin Suraj tayi murmushi tace " Yana nan", Turare ta fiddo a jaka, ta sake fesawa, Ta shiga tana rambad'a k'amshi,

   Dukkansu suna zaune falo suna hira, Ta shigo da sallama, Hajiya kad'ai ta amsa, Su'ad da Feena ko kallo bata ishe su ba, itama bata bi ta kansu ba.

   "Ina wuni?", Ta gaishe da Hajiya, " Lafiya lau, Yasu Jummai?", "Suna lafiya, tana gaishe ki", " Ina amsawa", "Bari naje na gaishe da Matar Ya Suraj ance bata da lafiya", " Ai basa k'asar, suna umrah daga can zasu wuce London haihuwa", Gabanta yayi mummunan fad'uwa, tayi k'ok'arin b'oye tashin hankalinta ta hanyar cewa "Allah sarki, Allah ya sauke ta lafiya", Hajiya ta amsa da " Amin", "Zan koma ana jirana", " Ki gaisa su Jummai", "Zasu ji"

    Da k'yar taga ta isa gida, Tamkar an jefota ta shigo d'akin Aunty Jummai, "Lafiya?", " Ina fah lafiya Umma, Ya Suraj ya tafi da Fetta Umrah daga can zasu wuce London haihuwa", Aunty Jummai ta dafe k'irji tare da zaro ido tace "Mun shiga uku", " Umma meyasa al'amura ke tafiya haka?", (Nace duk wanda bai mik'a al'amuran sa ga Allah ba, ba zai tab'a ganin daidai ba)

    Hawaye suka wanke fuskarta "Shikenan na rasa Ya Suraj, bazan koma gid....", Aunty Jummai tayi saurin katse ta " Inji wa, ko ta haihu dashi sai kin koma, wallahi sai kin koma", Mayafi ta zura, Tayi waje, taci karo da Sahabi, "Ina zaki kike ta sauri?", Tayi k'ok'arin daidaita natsuwarta tace " Nan gidan Aminiyata", "Da nazo ne muje kiga gidan nawa", " Muje toh, idan na dawo naje", A ranta tace "Na samu kud'in zuwa wurin boka, ya zama dole na kawar da Fetta a doron k'asa"

   Ya bud'e mata gidan baya ta shiga, "Da ka bari na shiga gaba, kar na mayar da kai driver", " A'ah ai ba komai", Ya fad'a yana murmushi, ya shiga driver's seat,

    "Wacce ungu....?", Bata k'arasa ba sakamakon hodar gusar da hankali da ya watsa mata, ta sulale bata numfashi, Ya kalleta yayi dariyar mugunta, ya fisgi motar a 360. Bai zarce da ita ko'ina ba sai gidan da Yelwa ta same shi, Da taimakon Dan' bala suka fitar da ita cikin mota, D'aki suka kai ta, suka kwantar kan gado, Ya umarci Dan' Bala ya fita, Kayanta ya shiga tub'ewa, hadda pant da bra d'inta sai da ya cire, Allura ya mata, idonta suka bud'e, ta zama mutum mutumi ba uhmm ba a'ah, hotona ya mata, Ya tub'e kayansa, boxer kad'ai ya bari, Ya rungomuta ya musu hoto tare.

    "Sorry Hajiya Jummai", Ya fad'a yana dariyar mugunta, Kayanta ya mayar mata, Ya saka nashi, Ya kira Dan' Bala ya taimaka mishi suka fitar da ita zuwa mota,

    Bakin gidansu ya ajiye ta, Yaja motar ya bar unguwar da sauri,

   Kusan minti biyar da ajiyeta, babu wanda ya wuce balle ya ganta, A hankali ta dawo hayyacin ta " Wayyo Allah, me Sahabi yamun?", "Me kike anan waye kuma Sahabi?", Taji muryar mijinta kamar daga sama wanda dawowar sa kenan, Tayi saurin tattara natsuwarta tace " Ba kowa, ka dawo sannu da zuwa", Da kallon tuhuma yabi ta, Ya wuce ba tare da ya amsa ba, Ta sauke ajiyar zuciya ganin bai yi insisting on knowing ba, tabi bayansa.

    Yelwa na kitchen na had'a miya, wayarta dake gefe tayi alamar shigowar message, Da sauri ta jawo wayar ta duba, hotonan Sahabi ya turo mata, ta bud'e,

   "Ka biyani Sahabi, lokacin ramuwa yazo, ba'a tab'a Yelwa yar' gidan tabawa a kwana lafiya, sai na hana miki farin ciki Jummai"

   
     "Yaushe zai turo ne a saka rana, bana so a d'auki lokaci ba tare da aurar daku ba, idan bai shirya ba, a mayar masa da kayan sa a nemi wani", Cewar Hajiya, " Mama cikin satin nan In Shaa Allah zai turo ", (Ta fad'a dan Hajiya tayi shiru), " Toh Allah ya tabbatar da alkhairi", "Amin"

   Ta juya kan Feena "Ke kuma kada ki yarda na sake miki maganar tsayar da miji, ina sane da samarin da kike kulawa, ciki ki fitar da d'aya, bana son shashanci", Tayi nodding kai, " Ku tashi ku bani wuri", Suka mik'e rai ba dad'i.

  Bilkisu na kwance d'akinta kan katifa suna chatting da Zulaihat wacce duk hirar batsa ce, Taga an turo mata message da sabuwar number, Ta d'auka wata ce da suka had'u yau sukayi exchanging number, cikin rawar jiki ta bud'e, Hotonan da ta gani suka matuk'ar d'aga mata hankali, Ta saki wayar, "Um...ma d..a sa...h...a..bii, na shiga uku wayyo Allah na",  
  
   Ta fito ta nufi d'akin Aunty Jummai, " Why Umma, meyasa zaki yi haka?, da auren ki?, ban tab'a zaton zaki aikata haka ba", "Ke dan ubanki kinsan me kike fad'a?", " Umma me ya kai ki mu'amala da Sahabi?", "Sai yau kika san ki tuhume ni akan Sahabi, Kinsan duk wata alak'a da nake dashi dan ganin kin koma gidan Suraj ne", " Shine zaku aikata alfasha irin wannan? ", " Dan ubanki wacce alfasha?"

   Ganin bata fuskanci me take nufi ba, Ta koma d'aki ta d'auko wayarta,

   "Meye hakan?", Ta fad'a tare da nuna mata hoton,  " Na shiga uku na lalace, sharrin da Sahabi zai mun kenan, me na masa ya zab'i cutar dani ta wannan hanyar", Ta durk'ushe a wurin tare da d'aura hannu saman kai, "Da baki je wurin sa ba, ai ba zai muku hoto tare ba", " Wallahi ba da sanina ba, mamaya ta yayi", "Taya?", Ta zayyane mata abunda ya faru,

  " Allah ya tsine masa albarka, me kika mishi zai cutar damu haka?", "Tsorona hoton nan yaje wurin baban ki", " Ta Baba mai sauk'i ne zaki iya fahimtar dashi mutanen duniya fah", Aunty Jummai tace "Na shiga uku ni Jummai", " Ki kira shi Umma mu rok'e shi, idan kud'i yake buk'ata mu bashi", Aunty Jummai ta jawo wayar ta tayi dialing number sa a kashe, "Shikenan na mutu na lalace wayyo Allah na", (Nace dama addu'a kika yi, da kin samu sauk'in ubangiji).

STORY CONTINUES BELOW

   Suraj da Fetta satin su d'aya a Makka, sunje wurare irinsu Top ten, Twenty4, hadaya, markaz dubai, Sunyi ibada sosai da addu'o'i, Garin ya mata dad'i sosai, taji tamkar ta dawwama anan, Sunyi siyayya da yawa wanda rabi kayan baby ne, Jirginsu ya d'aga zuwa London.

    *1:30am* 
Jirginsu yayi landing, Ba b'ata lokaci suka sauka, Driver yazo d'aukar su, " Welcome Sir", Ya fad'a tare da sara mishi hannu, Suraj yayi nodding kai, Ya juya kan Fetta "Welcome Madam", " Thank you", Ta amsa tana mamaki dama yasan shi.

    Bayan mota suka shiga tare, Driver yaja zuwa Oxford street, Unguwar masu kud'i ce, gida k'erarru, Fetta ta saki baki tana kallon had'uwar su, "Masu kud'i na sha'anin su", Ta fad'a a ranta, A bakin gate na mansion house driver yayi horn, security ya bud'e gate, compound ne mai d'auke da gidaje da yawa,

    Ma'aikata ne suka fito cikin uniform, Mata biyu, namiji d'aya, Suna musu sannu da zuwa, Da sakin fuska Fetta ta amsa, Oga Suraj kamar ko da yaushe fuska a tamke ya amsa, Luggage d'insu suka d'auka zuwa ciki, Fetta na biye dashi a baya, house no 5 taga sun shiga,

    " Aljannar duniya", Ta furta saboda had'uwar falon, an zuba kayan alatu, D'akin da taga ya shiga, Tabi bayan sa, Shima ya had'u ba k'arya, Toilet ya shiga, Ta zauna bakin gadon tana mamakin irin dukiya ta Suraj, Dan duk wanda zai kama gida irin wannan a london ba k'aramin mai kud'i ba ne,

    Ya fito sanye da rigar wanka, da towel a hannu  yana goge gashin kansa, Mik'ewa tayi ta shiga toilet, Tsayawa tayi tana kallon tsaruwar bayin, duk had'uwar na Suraj a 9ja, wannan yaci uban sa, Wanka tayi a natse ta d'auro alwala, Ta fito.

     Yana zaune bakin gado yana waya, "Zan sake kiran ka", Ya kashe yana bin ta da kallo, Ta tsargu da irin kallon da yake mata, Da hannu ya mata alama tazo, Ta k'arasa gaban shi, Kunnen sa ya d'aura saman cikinta, Yace " My baby na jin yunwa, ki shirya ki sameni falo nayi feeding babyna", Ya mik'e ya fice tabi bayan sa da kallo, "Baby baby komai baby huu"

    Aunty Jummai yadda taga dare haka taga rana, ta kasa bacci sai faman juye juye take kan gado, zuciyarta cike da tsoro da fargaba, Ta kira Sahabi yafi sau ashirin a kashe, Addu'arta Allah yasa ya rasa wayar, ta yadda pictures d'in sun tafi kenan.

    Bilkisu tana cikin zullumi but hakan bai hana mata bacci ba hadda minshari.

    K'arfe goma na safe, Aunty Jummai na zaune tsakar gida tayi tagumi, Ga kunu da k'osai gabanta ta kasa ci, Bilkisu da tashin ta daga bacci kenan, ta tarar da ita haka, "Haba Umma, Dan Allah ki kwantar da hankalin ki, kici abinci", " Hankalina ba zai tab'a kwanciya ba sai naji daga Sahabi", "Tunda kika ji wayar sa a kashe zuwa yanzu to an sace ta ne", Ta sauke ajiyar zuciya tace " Allah yasa", "Amin", Kunun ta d'auka ta fara sha.

    " Assalamu alaikum masu gidan na nan", Suka ji muryar Yelwa, "Wa'alaikumus salam", Suka amsa, " Ashe kuna nan?", "Eh ina zamu da safiyar nan", " Na sani ko kunyi gudun hijrah tunda anyi abun kunya", Gaban Aunty Jummai ne ya fad'i, Wayarta ta zaro ta nuna musu hoton da fad'in "Meye amfanin haka?, ba kunya ba tsoron Allah", " Wallahi sharri yake mun ban aikata ba"

   Yelwa ta tuntsire da dariya tace "Wasik'ar jakai kenan, ga abu nan zahiri", " Wall...", Ta katse ta "Kin ga ba abunda zaki gaya mun na yarda, yanzu zan turawa Hajiya Tumba taga abun kunyar da kika jawowa dangi", Cike da tashin hankali tace " Dan Allah kar kimun haka Yelwa, ki rufa mun asiri", "Ashe akwai dad'i rufin asiri kika kasa rufawa Karima, yau zaki d'and'ana yadda ake ji", Tana fad'ar haka ta fice, Aunty Jummai ta shiga kiran sunan ta, Tayi banza tamkar bata ji ba.

    " Na shiga uku na lalace asirina ya tonu", Aunty Jummai ta fad'a tana hawaye, Bilkisu shiru tayi ta rafsa tagumi cike da tashin hankali.

   "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un" Hajiya ke ta nanatawa ganin hotonan Jummai da wani, Ta runtse ido cike da tashin hankali, "Mama meye faru?", Feena ta tambaya cike da damuwa, Da hannu ta mata alama ba komai, D'aki ta shiga ta zauna kan gado, tana mamakin Meya kai Jummai ga aikata haka, wannan abun kunya har ina, Number da aka turo mata tayi dialing a kashe, " Ya Salam", ta furta tare da dafe kai.

    " Mama ta matsa akan ka turo a saka rana, ina tsoron ta rabamu", cewar Su'ad cike da damuwa, Ya rungumota jikin shi tare da cewa "Don't worry my baby, jibi zasu zo asa rana", " Really?", Ya d'aga mata kai, Ta manna masa kiss tace "I love you"

   "You are wasting my time", Ya fad'a yana kallon wristwatch dake d'aure a hannun sa, Fetta dake d'aki ta fito tana gyara veil d'in ta, Turaren ta mai sanyin k'amshi ya daki hancin sa, Ya sauke sanyayyar ajiyar zuciya, tare da kallonta ta gefen ido, ya mik'e tabi bayan sa,

Driver da sauri ya taso ya bud'e musu gidan baya suka shiga, A ranta tace " Tsabar isa baya zama gaban mota, sai tak'ama kamar Dan' sarki"

     St Thomas hospital ya umarci Driver ya kai su, best hospital a London, asibitin masu kud'i, Ya had'u ya k'eru, Fetta a ranta tace "Wani abu sai masu kud'i"

   A tare suka jera suna tafiya cikin asibitin, Sun samu ganin likita ba b'ata lokaci, Sun bud'e file nan zata rik'a zuwa ante-natal har zuwa lokacin haihuwar ta, Dr James yace "Za'a mata scanning", Ya umarci ta kwanta kan wani gado, Yana k'ok'arin bud'e mata ciki, Suraj ya taso cikin zafi nama ya rik'e hannun sa yace " What are you trying to do?", Da mamaki Dr yabi sa da kallo yace "Scanning ofcourse", " Shine zaka bud'e mata ciki", "Haka ake scanning",  " No barshi ai scanning d'in ba dole ba ne", "OK then" Dr ya fad'a tare da d'age kafad'a, Duka da harshen turanci sukayi maganar, Ya juya kan Fetta ya watsa mata harara yace "Kin wani kwanta, kina gani zai bud'e miki ciki", " Mutum kamar mai juju" Ta fad'a a ranta tare da mik'ewa, Dr ya rubuta musu drugs da zata rik'a sha, Suraj ya siya a phamarmacy na asibitin,

   A mota sai d'aure fuska yake, haushin ta yake ji, na k'in hana Dr bud'e mata ciki, Ta basar dashi tamkar bata san yana yi ba, har suka kawo gida, Shi ya fara fita motar ya buga k'ofa da k'arfi, Tayi murmushi tare da girgiza kai "Meye abun jin haushi to, ko ya d'auka babyn sa za'a cutar", Ta kawar da tunanin, ta fita motar ta shiga gida.

   A falo ta tarar dashi yayi crossing leg, Ta wuce zata shiga d'aki,

  " Ke zo nan", Ta dawo ta tsaya saitin shi, "Are u OK?", me kake yi haka?", Zuciyar sa tace mishi, Da hannu ya mata alama ta tafi, Ta wuce tare da girgiza kai,

    " Why zaka ji haushi wani zai bud'e mata ciki?", "Saboda babyna na ciki", Yayi assuring kansa. (Nace Oga Suraj hoo😂)Hajiya Tumba ta buk'aci a had'a family meeting dan shawo kan matsalar Aunty Jummai, kada pictures d'in su cigaba da yawo, wanda hakan zai tab'a reputation na family, Mijinta bai san me ke faruwa ba. +

   Kowa ya hallara a babban falon Hajiya Tumba, Bayan anci abinci da lemo, Aunty Jummai lemo kad'ai ta iya sha, sam bata cikin natsuwar ta.

    "Ina tayamu jajen al'amarin da ya faru", Cewar Hajiya, Kawo Sule yace " Wane al'amari kenan?", "Na Jummai", " Ita za'a wa jaje ba mu ba"

   Hajiya tace "Abunda ya shafeta ai ya shafe mu, mu had'u a san yadda za'a shawo kan lamarin", Kawo Lamid'o yace " Kinga Hajiya ba wani had'uwa da za'a yi, lokacin da zata aikata ta nemi shawarar mu", Kawo Shehu (Yayan su) yace "K'warai kuwa, kanta ta b'atawa suna bamu ba, taje can ta k'arata", " Duk tsutsun da yaja ruwa shi ruwa ka duka, kunga tafiyata", Cewar Kawo Sule ya mik'e,

    "Ku tsaya ku saurare ni wallahi sharri ake mun", " Ba abunda zamu saurara fasik'ar banza", Cewar Kawo Shehu, Duka suka mik'e suka fice.

    Aunty Jummai ta d'aura hannu a kai ta fasa kuka.

   Hajiya tsananin mamaki na halayyar dangin mijinta ya cika ta, yadda dan' uwa ke guje ma dan' uwan sa, "Hak'uri zaki yi, ki koma gida kiyi ta istigfari, ki tuba zuwa ga Allah", Tana fad'ar haka bata jira amsar ta ba, ta wuce ciki, abunda ta aikata yasa tana jin haushin ta.

    Aunty Jummai ta rasa ina zata saka kanta taji dad'i kowa ya guje ta, kowa ya kasa fahimtar ta, ina zata ga Sahabi ta rok'e shi ya wanke ta daga wannan mummunan zargi.

    Ta koma gida rai a jagule, a tsakar gida ta fara cin karo da kayanta, Bilkisu durk'ushe tana kuka, " Umma ki ba Abba hak'uri kada ya kore mu",

   Kafin ta bata amsa ya fito, Yanayin sa ya matuk'ar tsorata ta shiga ja da baya, "Macuciya azzaluma, Allah ya isa tsakanina dake Jummai, me na rage ki dashi, kije na sake ki saki biyu", Ihu ta kurma ta d'aura hannu a kai, " Na boni, wayyo, na shiga uku na lalace, ka rufa mun asiri, wallahi sharri ake mun", Kururuwar da take yasa mak'ota shigowa suka ga lafiya, kan ace haka gidan ya cika da jama'a, Suna tambayar ba'asi, Ya kori kowa yace su fitar mishi a gida,

    "Kafin na dawo, ki bar gidan nan ko ki had'u da mummunan wulak'anci", Ta kamo rigar shi tana rok'on shi, ya fisge ya fice, Ta kwanta a k'asa tana birgima kamar k'aramar yarinya.

    Suraj na zaune yana kallon wani programme a TV, gefen sa coffee ne yana sha, Fetta na d'aki tana bacci tun zuwan ta London bata aikin komai ya hana, masu aiki ke yi, ko kitchen bata shiga, Duk abunda take so sai dai ta fad'a a dafa mata.

     K'arar doorbell da yaji ya tashi ya bud'e k'ofa, Williams ne (wanda shi ke musu wanki da sauran aikace aikace), K'atuwar jaka ya mik'o masa yace " From John Daniel", Ya karb'a tare da nodding kai, Ya mayar da k'ofa ya rufe,

   D'ayan d'akin ya shiga, Ya bud'e zip dollars ne mak'il, Yayi smiling yace "John is very clever", Ya mayar ya rufe, wayar sa ya zaro daga aljihu yayi dialing number Sabeer, " Hello Sir", "Yes Sabeer", " Ina wuni, ya mai jiki?", "Alhamdulillah", " Ya business ke tafiya?", "Komai lafiya Sir, but muna buk'atar....", " Ba sai ka k'arasa ba zuwa jibi zan turo", "OK sir, jiya Alhaji Badamasi ya shigo gari", " Ya kawo new models ne?", " Eh yazo neman ka ma", "Ku lura da movement d'inshi ban yarda dashi ba, ina ganin kamar so yake ya damfare mu", " OK Sir ", Yayi hanging up, Ya shafa gemun shi wanda ke k'ara mishi kyau, Yace " Huu Alhaji Badamasi kada ka yarda zargin da nake akan ka ya tabbata"

STORY CONTINUES BELOW

    Ringing na wayar ta, Ya tashe ta, Aliya ce ke kira, Ta kashe, tabi kiran nata, bugu d'aya ta d'auka,

   "Mutanen Landan", " Umma ina wuni?", "Lafiya lau", " Ya k'arfin jiki?", "Alhamdulillah, Ya Malam dasu Hajar?", " Kowa lafiya", "Ina gaishe su", " Zasu ji, Allah ya sauke ki lafiya", Ta amsa da "Amin", " Sai anjima ki gaishe da Suraj", "In Shaa Allah", Ta kashe wayar, ta duba agogo, Magrib ta wuce, Salati tayi ta mik'e.

     
     Adnan ya turo iyayen sa, Manyan mutane cikin shiga ta kamala, an karb'e su hannu biyu cikin mutunci, Sun kawo kayan sa rana an saka biki wata biyu masu zuwa, Hajiya hankalin ta ya k'ara natsuwa, ta k'ara tabbata da gaske yake, Ta kira Suraj ta sanar dashi, Yayi fatan alkhairi, yaji dad'i sosai.

   Aunty Jummai da Bilkisu sun kwashe kayan su sun bar gidan, Yan' uwa kowa yak'i karb'ar su, Hajiya Rabi ta fad'awa halin da suke ciki, Ta basu k'aramin gida cikin gidajen hayar ta, Suka koma can, Aunty Jummai ta rasa natsuwa, ta rame a yan' kwanakin kamar wacce ta shekara tana ciwo, Bilkisu kam sabgoginta ta cigaba, kud'i na shigo ta.

   Tasleem ke saukowa daga matattakalar jirgi, ta sauke k'afarta step na k'arshe, ta kalli filin jirgin tace " Nazo gare ka Suraj Sa'id, soon zaka zama nawa ni kad'ai, I love you Suraj", Ta fad'a tare da d'aura hannun ta kan zuciyar ta.

     Taxi ta d'auka ya kai ta gidan k'awarta dake schooling a garin, wacce tayi k'arya da ita, Tana da information duka akan Suraj wanda take samu ta hanyar Rabi'u, Kud'i masu yawa ta basa, kafin ya amince ya fara sanar da ita, da sharad'in ba zata cutar da Suraj ba, Tayi alk'awari.

    Sim ta siya na garin ta bud'e sabon WhatsApp, taje kan contact na Suraj ta tura mishi Friday text, kasancewar yau jumu'ah, Wanka tayi ta sake shiryawa tacewa k'awarta Fauzy zata fita, "Daga zuwa sai fita", Tayi smiling tace " Zanje asibiti, I need to see doctor ", " Alright a dawo lafiya", "OK"

    Taxi ta shiga ya kai ta St Thomas Hospital, Ta zauna tana jiran zuwan su Suraj, tasan yau yake kawo Fetta ante natal,

    Kusan minti ashirin da zaman ta, ta hango su sun fito daga mota, Da sauri taje hanyar data nan zasu bi, saitin da Fetta zata wuce, ta ajiye b'awon ayaba, Ta lab'e tana jiran fad'uwar Fetta, babyn cikin ya mutu.

    Fetta santsi taji ya jata tana gaf da fad'uwa, Suraj yayi saurin rik'e ta, Ya d'ago ta tare da fad'in "Sorry hope baki ji ciwo ba?", Tayi nodding kai, A kan idon Tasleem wacce take ji kamar zuciyar ta, tayi bindiga tsabar haushi da kishi,

   Mamaki yake Meye kawo b'awon ayaba wurin, maybe wani ya jefar mistakenly, Ya d'auka ya saka a dustbin na kusa da wurin, Ya rik'eta zuwa ciki gudun sake samun matsala.

   Bilkisu ta dawo gantalin ta, ta tarar da Aunty Jummai zaune jigum, tayi nisa a tunani sam bata ji shigowar ta ba, Ta zauna gefen ta tace " Kina so ki fita damuwa?", Aunty Jummai tayi firgigit daga tunani tace "Sosai Bilkisu", " Kiyi k'ok'ari na koma gidan Suraj ita kad'ai ce hanyar da zata fitar dake, da kin samu kud'i zaki ga kowa yana so ya rab'e ki, yanzu ganin baki dashi ne", Tayi nodding kai cike da gamsuwa da maganganun Bilkisu, A ranta ta k'uduri sake aniyar mayar da auren su, ko dan ta fita damuwa.

    Kwanaki, awanni, seconds sun wuce Cikin ikon Allah cikin Fetta ya shiga watan tara, watan haihuwa at anytime zata iya haihuwa, Zama da k'yar tashi da k'yar, Suraj na bata kula sosai duk wani motsin ta akan idon shi, wanda hakan ya k'ara shak'uwa mai k'arfi tsakanin su, dan hatta wanka shi yake mata, ya shirya ta, abinci baya bari taci da kanta,

    Mak'iya basu fasa k'ulla k'ulla ba, Tasleem kullum sai ta mishi text ta WhatsApp ya bud'e yayi ignoring, abun ba k'aramin zafi yake mata ba, Gashi duk makircin da ta had'a bata succeeding, but she never give up, burinta babyn kar yazo duniya, ko ta kashe shi a ranar da yazo duniya.

    Fetta na zaune k'asan carpet, ta mik'e k'afar ta da suka kumbura, Suraj na matsa mata, Gefen sa bowl ne na apple, an yanka k'anana, Yana d'auka yana saka mata a baki,

   "Anjima akwai zuwa strolling", Ya fad'a yana kafe ta da ido, Lips d'inta na k'asa ta d'an ciza tace " Yau bazan iya zuwa ba, bayana na ciwo", "Wayon dai kar kije, yadda k'afar ki ta kumbura ya kamata kije ko zasu sake", " Allah bazan iya ba", "Ok Maman baby", Ta jinginar da kanta jikin kujera tare da lumshe ido, ita kad'ai tasan ciwon da take ji yau a jikin ta.

   *4:35am*

    Matsananciyar nak'uda ta tasowa Fetta, " Innalillahi wa inna ilaihir raji'un zan mutu, bayana, marata", A rud'e Suraj ya farka yayi kanta, ganin halin da take ciki ya matuk'ar d'aga masa hankali,

Masu aiki ya kira, suka kamata zuwa mota, ya shiga baya tare da ita, Yana rungume da ita, yana tofa mata addu'o'i, Driver yaja su zuwa asibiti.

   Suna zuwa nurses suka karb'eta aka nufi d'akin haihuwa da ita, Suraj sai faman zirga zirga yake ya kasa natsuwa, Yana addu'a Allah ya sauketa lafiya, Jane(Mai'aikin) ta biyo su da kayan baby.

   *6:00am*

    D'aya daga cikin nurses ta fito take sanar dashi ta sauka lafiya an samu baby girl, Hannu ya d'aga sama yana ma Allah godiya, Ya nufi d'akin,

    Fetta na kwance na bacci wanda na wahala ne, Babyn na hannun nurse, Ya karb'e ta, kamar su d'aya, Ya manna ta k'irjinsa tare da jin tsananin k'aunar ta, Ya kalli Fetta dake bacci a ransa yace " Ta gama mun komai tunda ta haifa mun little angel", Ya sumbaci yarinyar wacce itama bacci take, Ya mata hud'uba, Bakinta ta fara juyawa alamun tana neman abinci, ta fara kuka,

   Kukan ya tashi Fetta, Idonta ya sauka kan su, Ya d'ago ya kalle ya yace "Kin tashi?", Ta d'aga masa kai, " Sannu", Ya fad'a tare da mik'a mata babyn, Ta karb'e ta, yana breastfeeding, sai faman cije baki take saboda azaba kasancewar farko ne,

     Suraj na kallon su cike da sha'awa, ba zai iya fassara wani yanayi yake ji ba, Tana gama sha ya karb'e ta, Ya kira gida yace su kawo kayan tea, su had'u da pepper soup na kayan ciki.

     Hajiya ya fara kira ya sanar da ita, Tayi murna matuk'ar taji tamkar tayi tsuntsu ta ganta a London, Ya ma sauran yan'uwa da abokan arzik'i text message, Ana ta kiran sa ana mishi barka, wasu na mishi text message.

    Fetta taji bai kira Aliya ba, wayar ta na gida balle ta kira,

"Ara mun wayar ki na kira Umma", Kunya yaji ta kama shi sam ya manta ya kira ta, Ba tare da yace komai ba, Ya mik'a mata, Tana da number a kai, tasa ta kira, Tayi mamakin ganin suna ta yayi appearing kan screen d'in *Umman Fatima* Ta nanata sunan a ranta, Sai da ta kusan tsinkewa ta d'aga,

    " Umma ina wuni?", "Fetta kece, naga number da ban sani ba, da kamar ba zan d'auka ba", Tayi dariya tace " Yasu Malam?", "Lafiya lau", " Uhmm dama?", "Dama me?", " Uhmm", "Kin sauka ne?", "Eh", " Alhamdulillah Allah mun gode maka, shine kika kasa fad'a, bansan sai yaushe zaki daina kunyar nan ba, kunya kamar Fulani", Tayi dariya, "Me aka samu?", " Mace", "Allah ya raya", " Amin", "Bara naje na sanar da Malam", Ta kashe wayar, Ta mik'a mishi tace " Thank you", "Meye na godiya, ni ya kamata na miki godiya kin haifar mun little angel", " Allah zaka ma godiya, shi ya baka", "Nayi ma Allah godiya kuma na miki", Tayi murmushi,

     Sun kawo kayan tea da pepper soup, Shi ya had'a mata tea, ya zuba pepper soup ya tilasta mata taci, A ranta tace " Yace akan babyn sa, yanzu na haihu, yayi freeing d'ina"

   Tasleem taji labarin haihuwar hankalin ta ya tashi, taji bak'in ciki, mara misaltuwa, Gyalen ta yafa zuwa asibitin, Da alwashin kawar da babyn a doron k'asa.
Comments


EmoticonEmoticon