Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

EL-MUSTAPHA CHAPTER 13 KARSHE

EL-MUSTAPHA CHAPTER 13 KARSHE

- - Post a Comment
EL-MUSTAPHA
CHAPTER 13 KARSHE


'Ta bi bayansa tana tunxuro baki,

Kai tsaye dakinta ta nufa a tunanin ta nan ya shiga, wayam babu shi, batare da tunanin komai ba ta nufi toilet din ta wai neman sa take. +

Fitowa tayi tana kiran sunan sa,

Yusuf.. Yusuf, ina ka boye ne, meyasa kake guduna?

Bata ji ya amsa ba, sai ta nufi dakin dake kusa da nata, da alama nan ne dakin nasa.

Yana tsaka da cire dogon wandon shaddar sa ta shigo, xuba masa idanu tayi ganin babu riga a jikinsa.

Ya rage daga shi sai gajeran wando a jikinsa, ya juyo yana kallonta cikin mamaki sam bai san da shigowar ta ba, yanda ta xuba masa idanu ya saka shi jin kunya, sai ya soma kokarin kare jikinsa cikin mamaki wace irin macece wannan yarinyar. 2

Uwani kuwa tana kallon sa ne tana tuna El'mustapha, sai take ganin yusuf yaro ne akan el'mustapha, bata manta fadin qirjinsa dan bata iya tsayuwa ma ta kalle sa kamar yanda take kallon yusuf a yanxu.

Ta sami guri ta xauna tana cigaba da kallonsa,

Yana qoqarin saka doguwar riga ya kare jikinsa sai wani tunani yaxo masa, idan ita bataji kunyar kallonsa ba saboda me xaiji kunyar rufe mata jikinsa, sai ya cire rigar ya ajiye, da gangan ya soma qoqarin cire gajeren wandon dake jikinsa ya gani xata dauke kai ko me.

Uwani na ganin yana qoqarin cirewa ta qara tsura masa ido, idanunta na kan yanda xata ga abin nashi so take ta gani ko irin ta el'mustapha ce, har wani murxa ido take yanda xata gani da kyau. 2

Gabansa ya tsananta bugawa, ko surayya da suka haihu da ita bata taba qoqarin gwada hakan tare da shi ba, ya kasa cire wando yayi tsaye kamar statue yana kallonta cikin tsananin mamaki.

Uwani ta dube sa tana murmushi bata yi magana ba, shima juyawa kawai yayi ya nufi toilet.

Har ya fito wanka uwani na xaune gurin,

Tace wanka kayi, Allah yasa kayi alwallah muyi sallah, na qagara naci kifina na kwanta tun daxu shi nake jira.

Baiyi magana ba, uwani ta cigaba da fadin,

Baka kyauta min ba kayi wanka kai kadai bada ni ba, Anty jiddah ai tare take yi da mijinta, ko xamanin su abba tare yake yi da hajiya nasani sai ni da kake wa baqin ciki da samun lada, ba komai na yafe ma haqqina amma gobe ni xan ma.

Wani tunani yusuf yayi kafin ya juyo yana kallonta,

Je kiyi wanka kixo ina jiranki magana xamuyi.

Ta tashi tana murmushi, ai nasan ka matsu dani kai dai kace kana so mu kwanta ba wata magana da xamuyi, ta fita da sauri ya bita da kallo baki a bude.

Bata jima da fita ba ta dawo da kayan barci a hannunta kusan Kala uku ta xube a gabansa.

Nifa baxanyi wani wanka ba, ai kafin muxo nayi wanka ka kira gida ka tambaya kowa yasan ni ba qaxama bace, xaba min kayan da kake so nayi ma kwalliya da su saboda na faranta ma, ance farin cikin ka shine nawa, baqin cikin ka naka ne kai kadai danni bana son abin baqin ciki. 5

Kallonta yayi kafin ya maida kallonsa ga kayan da ta xube a gabansa, hannu yasa yana daga kayan d'aya bayan d'aya, wata riga ya dauka qarama mai kyau iyakar ta cibiya, sai qaramin wandon ta iyaka cinya,

Ta yatsina fuska tana kallon kayan, su kake so?

Ya gyada kai yana kallonta tunaninsa ko xatace baxata iya sakawa ba sai ganin yayi ta soma qoqarin cire kayan dake jikinta anan gabansa,

STORY CONTINUES BELOW


Da gaske baxakiyi wankan ba?

Nifa baxan yi ba, sai kace wata agwagwa, idan nayi yanxu fa sai nayi da safe, so kake fatar jikina ta kode a banxa ta fara warin ruwa, shiyasa ai kaga anty jiddah bata qiba kullum take ramewa yawan wanka ne da takeyi ruwan ke cin jikinta ita tana so ta birge miji kullum cikin wanka sai kace yar ruwa.

Yaja numfashi yana fadin, tunani na uwani a yanda abba yace lamarin naki yayi sauqi ban dauka haka xan same ki ba, xaman da mukayi dake a farko nayi haquri dake sosai kowa ya sani daga baya kika guje ni...... ta katse sa,

Kace gori kake min saboda ka aure ni yanxu, ni dama na dade da sanin ka aure ni saboda ka ci mutuncina na yaudare ka a baya, amma baka min adalci ba wannan ba so bane.

Yace if I can't control you tabbas baxan iya xama da ke ba uwani idan har baxan iya saka ki kiyi ki bari ba, ko na fada maki kiji kiqi ji ba, idan babu biyayya a auren mu babu amfanin xaman mu tare, bana jin ta halin ki saboda tun farko na sanki haka da abin ki, na dauka abin naki yayi sauqi ashe babu wani sauqi a tare da ke, baxan iya xaman aure dake a hakan ba uwani idan har baxaki nutsu ki dawo cikin hayyacin ki ba.

Hankalinta ya tashi sosai, tace kada kamin baqin ciki yusuf kasan ina son ka, bana so na rabu da kai, yanxu idan ka sake ni anty jiddah xataji dadi qila harda Party xatayi, baka san akwai yan baqin ciki a auren nan namu ba, kamar su Sumee, Serdia, Ummy fingers, Ayusher, habeeba, da Ummy koko ba, ka barsu da baqin cikin su, tunda kace nayi wanka xanyi kome kake so xan maka kada ka rabu dani kaji mijina.

Bai yi magana ba illah idanu da ya xuba mata, ta tashi da sauri ta dauki kayan ta fice tana fadin bari naje nayi wanka, ni ko a tsakiyar dare ne ka tadani xan maka girki dan na maka biyayya, ni bana maka baqin ciki da jin dadi a rayuwarka.

Tana fita yaja numfashi tare da girgixa kansa, wayarsa ya dauka ya kira surry, tunanin sa baxata daga ba, yanda yaji muryarsa ya tabbatar masa da tayi kuka.

Kin qara yin wani kuka ne surayya?

Da kyar tace aa,

Amma muryanki ya nuna hakan, why? Kin manta maganar da muka yi dake.

Tace yanxu yusuf uwani ce matarka, kana tare da uwani, kuma tare xaku kwana a yau ka barni ni kadai, kace mafarki nake yi dan Allah yusuf, sai ta fashe masa da kuka.

Jikinsa yayi matuqar sanyi sosai kafin yayi magana ta kashe wayar, ya kira wayar taqi ta dauka har ta tsinke, ya sake gwada kira yaji ta switch off.

Shigowar uwani ta katse masa tunanin da yake, tana sanye da hijab, ya tashi ya xura doguwar jallabiyar sa, ya ja su sallah.

Bayan sun kammala komai ya dauki ledar kifin ta ya bata yana fadin kije falo kici kifin bana son warin sa.

Ta tashi ta fita da sauri yawunta sai tsinkewa suke saboda kwadayi da ganin kifin.

Haka yabi lafiyar gadon ya kwanta cike da kewar sahibar sa surayya,

Uwani kuwa taci kifi iya cinta komai bata rage ba, kaf ta cinye, ta Kora da ruwan lemu, sai da tayi gyatsa kana ta tashi tana fadin, Alhamdulillahi Allah nagode maka da ka rabani da gidan baqin ciki ka kawo ni gidan mijina na gaskiya, komai nace yayi min yana min, Allah ya kare shi daga idon maqiya su ummy fingers da aysher barmo, Allah ya kare shi daga sharrin masu sharri da masu baqin cikin auren nan, kasa duk wacce taxo tamin snatching din sa bakinta ya koma kamar na karya, ta riqa magana kamar kukan jaki, ka maida idon ta daya a rufe irin na munafukai, amin summa amin, ta tofa addu'ar a tafin hannunta ta shafe fuskarta.

Taje ta wanke hannunta sosai yanda baxaiji warin ba, tayi brush ta qara nufar dakin sa, (wai ni inda amarya ke bin ango dakin sa daren farko🤔)

'Ashe har ka kwanta shine baxaka jira ni ba, yayi mata banxa.

STORY CONTINUES BELOW


Ta kwanta bayansa tana shige masa a jiki sai washe haqora take yau gata kwance da mijinta itama. 1

Yayi shiru yana sauraren ta, sai ji yayi ta rungumosa tana fadin, ni ina so kayi min wannan abun ne.

Da kyar yace wani abu kuma,

Tace in baka iya ba, ka kira el'mustapha ya koya maka shi kam ya iya sosai.

Yaji wani haushi, ya dube ta yana fadin idan muna tare dake kada na qara jin kin kiramin tsohon mijinki, ya soma qoqarin janye ta, ta qanqame shi tana fadin, ni sai kayi min xan kyale ka😨. 1

Yusuf tashi yayi yana cire kayan jikinsa, duk da acikin duhu ne bai hana masa hango yanda take wiqi wiqi da idanu ba, da alama a tsorace take cika baki ne kawai ai kuwa xaiyi maganinta.

Tana ji ya soma cire kayan jikinta, har tana taya sa ma 🤣,

🏃🏻‍♀🏃🏻‍♀🏃🏻‍♀

Yusuf ya kasa yardarwa kansa cewa uwani ba budurwa bace, har ya kasa haqura a karo na biyu ya sake yi, uwani ta tsine masa harda sakin sa😂, wani abin ma idan ya tuna dariya yake basa, yanda itace ta far nemansa da abin tun baa je ko ina ba ta soma bashi haquri tana kuka, uwani a wannan fannin bata da jarumta kamar surryn sa. 2

Tun bayan sallah asuba bnda barcin wahala ba abinda take, harda su minshari da alama harda gajiya a tare da ita.

Murmushi kawai yayi yana kallonta, ashe akwai ranar da xai mallaki uwani da komai nata, tabbas matar mutum kabarin sa ya yarda da wannan.

Ji yayi ana buqa qofar falon nasu, da sauri ya fita gudun kada a tada masa ita daga barci😯,

Yaro ne surayya ta aiko da breakfast ya kawo masu, yusuf ya karba yana murmushi, 1

Ka gaida ta kayi mata godia, Allah yayi mata albarka.

Yaron yace amin ya fice.

Tun bayan tashin uwani take tunani, yanda yusuf ke ta rawar kai da ita abinda el'mustapha bai mata ba, lallai ta yarda baya son ta baya qaunarta, ta tuna wahala da axabar da el'mustapha ya bata a sau daya da yayi amma yusuf ko kwatan kwancin wahalar bai bata ba duk da sau biyu yayi mata, ita yanxu baxata manta ba sau uku akayi mata amma na el'mustapha yafi xafi, lallai anty jiddah tana qoqari da shi.

Yusuf ya tambayeta xamantakewar ta da el'mustapha hala bai taba kasancewa da ita ba.

Tace yayi min sau d'aya ku.... ya katse ta, shikenan basai kin qara ba, xo ga breakfast surayya ta aiko mana.

Ta yatsina fuska, tace ni baxan ci abin hannun kishiya ba, waya sani ko ta saka min magani a ciki dan ta rabani da kai.

Ya bata fuska sosai, surayya matata ce, ina sonta sosai bana son na qara jin kin jefeta da wata kalma marar dadi, ki girmamata ki so ta idan har kina so xaman mu dake yayi kyau, maxa matso kici abinci.

Ta matsa tana tunxure baki.

Sanda yaxo fita taxo raka sa ta tsinkayo vespa dinta a kusa da motar sa, 1

'Yauwa kabari naje na kaika da vespa dina, ai na iya tuqashi tuntuni.

Ni na hau wannan vespa din, Allah ya sauwaqe min, kuma kada ki kuskura ki hau sa ki fita wlhy.

To miye amfanin siyen sa idan bana fita dashi, ko xan ajiye sa ne ina ta kallonsa haka, kasan yanda nake son abu na kuwa.

Yace duk yanda kike son sa bai kai son da nake maki da kare mutuncin ki ba, kudin da kika says vespa din ki gayamin ni xan siye na baki kudin amma bana son ganin ki dashi.

Kai haba, bana saidawa bane, idan kana so ka siya kaje kasuwa, amma wannan ina son abuna, har training nayi masa fa.

Ya tabe bakin sa ya nufi motar sa, taje taja vespa din gefe har masa kiss kafin ta nufi inda yusuf yake,

Cwty Allah ya kaika lafia, kayi min addua Allah ya rabani da yan baqin ciki.

Murmushi kawai yayi yana tada mota, uwani kayan Allah ya lura bata da magana sai ta baqin ciki a rayuwarta.

Bayan wasu awanni jiddah taxo gidan da kuyangunta as usual kun san su🤪

Uwani ta rungumeta cikin farin ciki,

'Anty jiddah ai naji dadi da kika xo da har xanxo fa akan vespa dina idan nayi wanka xuwa anjima,

Kinga yusuf jiya da dare sau biyu yayi min fa, abinda ake sau d'aya, kuma yanda yaya el'mustapha yayi min ba haka yayi min ba, yaya el'mustapha ya taba min nan ya taba min nan naji dadi amma shi bai min ba, kuma yaya el'mustapha y..... tayi shiru sakamakon bige mata baki da jiddah tayi iya qarfinta cikin bacin rai, sai ga jini a bakin uwani.

Ban gaya maki jiya sirrin ki da mijin ki kada ki bari kowa ya ji ba,

Cikin kuka tace amma ke ai yar uwata ce kakan mu daya fa saboda me xan boye maki. 3

Tace ko ni uwarkice bai kamata ki gayamin ba, har kina nuna kinfi jin dadin el'mustapha da yusuf ko, ashe baki da hankali uwani, da wani ne yaxo bani ba shima duk xaki gaya masa wannan labari.

Amma anty j..... Yimin shiru shashasha, dama abba ya bani saqo wlhy duk baki gyara rayuwarki da wannan shegen bakin naki ba xai xo ya dauke kine ya raba ki da yusuf ya hada ki aure da malamin ku dama shine dai dai ke.

'Anty jiddah kiyi haquri baxan qara ba kada ki gayamasa.

Kuma dama Malam guzuma abba yayi magana da yusuf xai xo yacigaba da karantar dake anan yana kula da takunki duk kika yi ba dai dai ba ya hukunta ki kamar da, yanxu haka xaa nema masa islamiya anan garin saboda ke.

'Na shiga uku ni uwani jikar sarki merah, wallahi xan nutsu anti jiddah, komai bakuso xan daina harda magana Ma amma kada ku kawo shi nan gidan dukana xaiyi. 4

'Wannan ya rage naki, harda fadin ana maki baqin ciki duk baki daina fada ba an bashi dama ya daki wannan bakin, da maidawa mutane magana, da rashin tarbiya duk xaiyi maganin ki.

Ki xauna ki kula da mijinki kinga kina da kishiya, ki kyautata masa ki masa abinda xaiji dadi wanda xai saka shi son kasancewa dake sannan ki boye sirrin ku kowa kada ki fadawa, in ba haka na Allah xai yi fushi dake sosai.

Sannan dan Allah uwani ina roqon ki kada ki maimaita abin da kika yi a baya kiji tsoron Allah kiji tsoron Mahaliccinki, ki tuna akwai mutuwa akwai hisabi, ki tuna akwai kwanciyar qabari ki tuna baxaa tabbata a duniya ba jin dadin ta kadan ne xai xo ya wuce, kada kiyi wa surayya abinda kika min, ki riqe ta da hannu biyu ki sota ki mata biyayya kada ki cutar da ita saboda bata da niyar cutar dake uwani dan Allah.

Cikin kuka uwani ta riqo hannunta, tana fadin baxan yi ba anty jiddah, babu wannan a xuciyata *Nayi Nadama*, ki yafe min abinda na miki sharrin jamcy ne wlhy itace ta tsaramin komai. 2

'Na dade da yafe maki uwani sai dai ki kula kuma ki kiyaye,

Tace insha Allah anty jiddah sai na baki mamaki xan xauna gidan aure na da amana saboda nasan masu baqin ciki da auren yawa ne dasu.

Jiddah tace baxaki daina kiran baqin cikin ba kenan.

Murmushi uwani tayi tana kallon ta kawai.Jiddah bata bar gidan ba sai kusan magrib, sunyi girki tare da uwani, ta qara koya mata wasu abubuwan sosai dama uwani ba girki aka iya ba. +

Bayan ta gama sallah tayi wankan ta, ta shirya cikin kayan barci sai qamshi take xubawa tana jiran angon nata.

Yana shigowa da sallama ta amsa tana masa sannu da xuwa.

Abinda ya fito bakin ta ya bashi mamaki,

Tun safe ka fita ka barni sai yanxu kake dawowa, hala kana gurin matar ka kuna yin wannan abin ne? Idan mutum yaci amanata Allah baxai barshi ba.

Yace uwani baxaki bari ko xama nayi ba, kinsan gajiyar da naxo da ita kuwa?

Tace ai nayi maka sannu da xuwa kuma na amsa sallamar ka, banda anti jiddah tace na riqa welcoming dinka xaka ji dadi Allah baxan yi ba tunda kana can kana wannan abun da matar ka.

Wane abu?ya tambaya yana kallonta,

'Wannan abun da kayi min jiya, ya dube ta da kyau yana fadin,

Ni bani da abin yi ne sai hawan mace ko kuma babu abinda mata da miji xasuyi sai wannan abin kadai?

Ta fara kuka yaci amanarta yaje ya barta, haka yusuf ya soma rarrashinta akan baxai qara yin dare haka, dama ya barta ne saboda yan xuwa dubin amarya.

Ta share hawayen tana fadin xo kaci abinci sai muje ka min, ni naji ina son wannan abin kuma. 8

Baisan meyasa yarinyar bata boye feelings din ta ba, ko kunya da nauyin fada bata ji Allah ya sa uwani ba irin jarababbun matan nan bane. 3

Batare da ya kalle taba yace ba yau ba, sai gobe yau na gaji.

Tayi shiru batayi magana ba, xuciyarta kamar xata fashe saboda bacin rai, yana kallo ta tashi taje ta dauko paracetamol, ya dauka ko ita ce xata sha sai yaga tana xuba masa a juice din da xai sha, 1

Miye haka uwani, meyasa kika saka min aciki.

Ai kace baka son wannan abun ni kuma ina so shiyasa na saka ma idan kasha kamin wannan abun.

Yace an gayamaki paracetamol d.. ta katse sa tana fadin ai shima kwayoyin magani ne kuma su ake sakawa mutum.

Yace gayamin a ina kika san ana sakawa namiji kwayoyin sha'awa uwani.

Ta tsura masa ido, ganin yanda ya kafe ta da idanuwa ya saka duk taji hankalinta ya tashi,

Tace ai nima ban sani ba,
Yace qarya kike, gayamin ina kika san wannan, kuma wa kika taba sakawa.

Ita kam tana jin kunya ta fada masa itace ta jawo el'mustapha gare ta, ai wannan abin kunya ne a gareta, (su uwani ansan kunya) ta tunxuro baki tana fadin ai a film nagani an saka wa wani tun a gida Ma na kalla, kuma da yasha yayi mata, akwai dadi kuma akwai ciwo. 3

Taya kika san akwai dadi da ciwo, kai tsaye tace ai kayi min jiya naji. 1

Mtsew yaja tsaki, ya cigaba da cin abinsa batare da ya kula ta ba, yana gamawa kuwa wanka yaje yayi, uwani har ta isa dakin nasa ta haye gado tana jiransa.

Shi kansa yana da buqata da uwani sosai sai ya bada kai bori ya hau😂

*

'Washe gari yana shirin fita sai ga uwani ta shigo da alama daga kitchen take, (uwani an san ayiwa miji breakfast) 1

STORY CONTINUES BELOW


Tace kafin kayi breakfast xaka qara yi min wannan abin ne naji kuma ina so, 2

What? ya fada yana kallonta cikin fito da idonsa alamar mamaki, yana tuna jiya bata barshi barci ba da ta motsa sai tace ya mata, shi yanxu tsoro ma take bashi. 4

Ke bakya gajiya ne?

Ni ban gaji ba, muje,

Yace muje ina, You are not serious, gwanda ki rage son wannan abun cos tafiya xanyi na barki, nan da two wks umrah xamu je da surayya.

Ta xaro idanu waje, ni fa baxaka je dani ba, me nayi maka a rayuwa yusuf kake min baqin ciki.

Ya fita yana fadin tun kafin na aure ki na biya mana, kema wani lokacin xaa je dake.

Wallahi baxan yarda ba, nima sai kaje dani, ta soma kuka sosai, haka ya gama breakfast dinsa ya fice bai qara kula ta ba, tana ganin ya fice ta dauki hijab ta saka da key din vespa din ta, ta fito. 4

Gidan su jiddah ta nufa,

El'mustapha na daure da towel a qugunsa da alama fitowar sa wanka kenan yaji alamar bude gate din gidan nasa,

Waye haka da sassafe da securities xasu budewa gida, ya qarasa bakin window yana daga labule,

Kamar mace ya gani akan vespa ta shigo gidan, wacece wannan, ya qara bude idanunsa sosai yana kallonta lokacin da take shigowa harabar gidan. 1

Uwani ya fada da qarfi cikin mamaki, jiddah dake fito masa da kayansa ta juya tana kallonsa jin ya ambaci uwani, da sauri ta nufi inda yake tsaye tana kallon window, dai dai lokacin uwani tayi parking din vespa din ta sauko, ta cire hijab din ta daure a qugunta, sannan ta fashe da kuka tayo cikin gida tana kiran anty jiddah. 2

Jiddah da el'mustapha tare suka dubi juna cikin mamaki, ko me ya fito da uwani yanxu, a tarihin sa bai taba ganin mace Bafillatana mai asali da tushe irin uwani akan vespa ba sai dai qabila,

Ihun da take tana kiran anty jiddah ya saka el'mustapha fadin je ki same ta jiddah kinsan xata iya shigowa,

Jiddah ta fita, uwani na ganinta ta qara sautin kukan ta,

'Anty jiddah yusuf baya sona yana min baqin ciki xasu je umrah da matar sa su barni😭

Jiddah ta bata fuska tana kallon ta, saboda wannan kike wannan haukan, bashi iko yaje da matar sa duk inda yaga dama ne, idan bashi da halin biya maku ku biyu ba sai ki haqura ya fara xuwa da surayya ba ai itace babba ke kuma daga baya sai aje da ke.

Uwani ta share hawaye tana fadin kema kina bin bayan sa kenan, mijina xaije da wata umrah kice na haqura na xauna gida suje can suna soyayya suna wannan abin ni ina nan ina gadin gida, sun shiga jirgi ni ina nan akan vespa, suna bauta ni ina nan ina barci lallai anti jiddah har yanxu kina min baqin ciki a rayuwa.

Fitowar el'mustapha cikin uniform ya hana jiddah magana, uwani na ganin sa ta kafe sa da idanu kamar mayya, harara ya jefe ta dashi cikin daure fuska, ta hade yawu da kyar Allah ya gani har yanxu tana son el'mustapha a rayuwarta, ta qarasa a hankali inda yake,

Cikin hawaye ta soma fadin yaya kaga xasu je umrah su barni shi da matarsa saboda baya sona yana min baqin ciki da na sami rahamar ubangiji.

Yace to miye aciki dan yaje da matar sa ta farko ya barki, ke ba daga baya kika shiga gidan ba.

Tace amma inda so da qauna ko yanxu na shiga xaije dani, ai kaima nasan xaka je da anti jiddah shikenan ni sai a barni, ta fashe da kuka.

Kowa baya sona, ina son kowa bana ma kowa baqin ciki amma ni ake min, kuka take sosai wanda ke nuni har cikin xuciyarta take yin sa babu alamar wasa.

STORY CONTINUES BELOW


El'mustapha yaja numfashi yana fadin shikenan share hawayen ki daina kuka, ni xan biya maki kudin sai muje tare, baqin ciki ya qare. 2

Fuska cike da hawaye take masa godia tana murmushi, shiyasa ta kasa cire sa a xuciyarta, lallai shine babban masoyin ta na haqiqa wanda baya mata baqin ciki,

Yace amma uwani meyasa kike hawan vespa kuma ki tuqa da kanki, kina matar aure.

Murmushi tayi tana fadin ai ni na says vespa din da kudina saboda na debewa kaina takaici duk inda xanje da abuna, yanxu da babu shi dame kake tunanin xanxo akan qafa ko me, ai ni bana daukar wulaqanci a yanxu.

Yace kuma gashi ni naga vespa din ina so uwani xaki bani?

Tace aa, kasan yanda nayi hustling na sami kudin ne, ai ko mijina ya roqe ni na saida masa naqi ina son kayana, ta bata fuska.

Yace shikenan uwani ashe akwai ranar da xan nemi abu a hannunki ki hanamin, (yana so ya rabata da vespa din)

Tayi shiru tana kallonsa ga mamakin sa shida jiddah sai yaga ta miqa masa key din vespa din tana fadin,

Gashi amma kada ka 'dana kowa akan sa, kuma kada ka arawa kowa, idan na haihu ya'yana sunxo duniya xan xo na karbar masu dukiyar maman su ce,

Ya karba yana fadin idan anyi kyauta baa dawowa a karba uwani, kyauta kika min kuma nagode, ya juya yana kallon jiddah dauko mata key din motar ta ki bata, dama tun farko na bata,

Uwani tayi murmushi tana fadin, jamcy ta cuce ni, ashe haka kake amma yaushe ka fara sona haka, kodai kana tausayi nane saboda ina jikar merah kana so kakana yayi maka kyauta. 1

El'mustapha bai yi magana ba, ya soma tafiya a hankali, uwani tabi bayansa,

Yaya dan Allah kayi min alfarma ka fitar da qawata ladidi daga prison, ita mai sona ce, kuma fa bata da laifi.

Wacece ladidi me tayi aka kaita prison,

Tace ladidi qawa tace ai acan muka hadu, itace wacce akawa qaxafin kissa akan ta kashe wadda ta riqe ta bayan mijin ne ya kashe matar sa da hannunsa.

Yace au na tuna, yanxu ake shari'a din ta, insha Allah xata kubuta dan ankama mijin ma, duk sanda xaa yi sharia xanxo naje dake ki ganta.

Taji dadi sosai, bayan jiddah ta baa key din motar ta fito sai kallon vespa din ta take tama fi sonsa akan motar, lallai da ba el'mustapha bane ba wanda ya isa ya raba ta dashi.

Bayan tafiyar uwani el'mustapha ya saka driver dinsa ya dauki vespa din ya kaiwa abba akan kada a sake bata shi ta hau.

Uwani saboda murna xata je umrah ta soma yawo ma'aikata ma'aikata tana neman inda yusuf ke aiki ta gayamasa, taji baxata iya haqura har ya dawo ba, sannan bafa aikinsa ta sani ba ballantana tasan inda xataje ta gansa, har wurin masu wanki da guga take xuwa neman sa😂 1

Ta kasa samun sa ta gaji sai ta nufi asibiti, tana so a duba ta ko tana da ciki idan baxata manta ba yau kwananta biyu da aure kuma yayi mata ya kai sau biyar dole kuwa tana da ciki.

Abinda likitan ya fara tambayar ta tana da aure?

Tace eh yau kwanan ta biyu da aure, ya dube ta sosai kwana biyu da aure kike maganar kina da ciki.

Ta gyara xamanta tana fadin saboda sau biyar yayi min, kuma na fara jin motsi a cikina ina so a dubamin mace ne ko namiji yaushe xan haihu.

Likitan ya xuba mata idanu nan take ya tuna ta, ta taba xuwa da irin wannan magana haka watannin baya ne ko anyi shekara ma.

Dabara ta fado masa, yace kije nan da wata hudu ki dawo a lokacin ake duba ciki agani mace ko namiji ne sannan kada ki fadawa kowa ki boye abin har mijinki kada ki gayawa.

STORY CONTINUES BELOW


Wani jin dadi da farinciki suka xiyarce ta, tace ai likita baxan gayama kowa ba har hajiya ta kada amin baqin ciki aje a xubar da cikin ina barci, da anyi wata hudu ko uku inxo kenan, bayan wata tara sai na haihu, likita gayamin nawa kudin kane.

Cikin murmushi aa kyauta na miki ai kin xama qanwata,

Au kaima dan gidan sarki merah ne?

Ya girgixa kansa,
Tace to ni ba qanwar ka bace, ni jikanyar sarki merah ce, anty jiddah yaya tace.

Baiyi magana ba shiru kawai yayi yana kallonta har ta fice,

Tana xuwa gida babu mgnr girki aka xauna ana list din wadanda xaa yiwa tsarabar umrah,

Xan bawa xoxo amma baxan baiwa Sally ba, Qaumi da mom sadeeq xasu samu amma sumayya da Serdia komai baxan basu ba, yan baqin ciki ne.

'Yauwa xan baiwa hajja, saina da Maman 4h amma baxan bawa ummy da aysher ba, kuma baxan bawa shafa ba, suma suna min baqin ciki,

'Abba xan siya masa praying mat da casbi kadai tunda su yafi baiwa muhimmanci a rayuwarsa, idan kudi na ya isa xan qara masa da qur'ani ko jallabiya. 1

Ita hajiya qila goron umrah xan siyo mata sai na hada mata da hijab tunda ita matar ustax ce.

Yusuf ma komai baxan siyo masa ba, ko sisi baxan kashe masa ba tunda yake min baqin ciki,

Shi wannan likitan da yace ina da ciki xan siyo masa biro tunda naga rubutu kullum ya keyi. 1

El'mustapha kuma xan siyo masa wani sabon vespa, da jallabiya goma, harda kayan yan sanda idan na gani xan siyo masa tare da xobe na gwal tunda baya min baqin ciki yana sona.

Ita anti jiddah komai baxan siya mata ba, amma xan siyawa twins kayan wasa,

In siyawa kakana merah alkyabba ta umrah amma wannan afiya da baturen ko sisi baxan kashe masu ba😏

Ya'ya na xan siyo masu kaya masu kyau da tsada, harda kayan wasa ma,

Ni kuma xan siyowa kaina sabon vespa, qatuwar sarqa ta zinari, takalmi masu kyau, dogayen riguna, nasa haqorin zinari idan nayi dariya kowa ya gani, amma pherty komai baxan siya mata ba taje jiddah ta siya mata. 1

Haka ta gama rubuce rubucen ta, ta ajiye har yusuf ya dawo.

Labari ta soma bashi akan komai da ya faru.

Shidai shiru kawai yayi yana kallonta, Allah ya shirya uwani.

A gurguje pls😏

7 months😃

Ina ce maku a wannan lokacin uwani nada ciki You ppl will not be surprised saboda kowa yasan jarababbiya ce bata da haquri🤣 1

Yanda uwani ke kula da cikin tana riritashi xakuyi mamaki, uwani bata yarda tayi wanka ta wanke cikin ba kada jaririn ya kamu da sanyi, ta fiso ta jiqa towel ta goge cikin dashi.

Bata cin abinci mai xafi kada jaririn ta ya qone,

Game da kayan dadi ba abinda bata ci koda ita bata so xataci wai saboda yaron yaji dadi, idan cikin ya fara motsi ta xuba ido tana murna tana daukar cikin vedio, da yusuf yaxo a nuna masa.

Bata yarda yusuf ya dora hannunsa akan cikin ta kada nauyin hannunsa ya jiwa yaron ciwo, kiss kawai take bari ya masa shima da kyar idan ya nace wai bata so ya lalata mata yaro. 1

Ta daina kwanciya da yusuf kada yaxo yana magagin barci ya shure mata ciki😨, uwani masu ciki.

Duk wannan abin da uwani keyi akan cikinta tana yine iyakar gskyr ta, kuma gwargwado uwani ta nutsu daga yanda kuka santa yanxu komai tana yinsa cikin nutsuwa ta daina maida magana tun bayan dawowar ta umrah.

STORY CONTINUES BELOW


Da kace hajiya uwani xata washe bakin nan dan kawai kaga haqorin da ta saka, ko baka mata mgn ba kuka hadu a hanya xata yi ma dan kawai kaga abinda ke cikin bakinta.

Tare suke xuwa kullum da yusuf asibiti a duk sanda xata je ganin likita, wani xuwa ne da suka yi uwani ta hadu da hajiya Mariya da kyar ta gane ta saboda yanda matar ta rame tayi baqi ta lalace.

Da tsinin cikin uwani ta bi bayanta tana fadin kamar Mariya nake ganin wannan tambadadiyar,

Hajiya Mariya ta dubi uwani, bata manta da fuskar uwani ba,

Tace Allah sarki uwani kinyi aure kenan ashe xan qara ganin ki.

Uwani tace me ya same ki haka kika lalace.

Tace wlhy rashin lafia nake fama da ita kullum ina hanyar asibiti kan wannan abun da nake na kamu da lalura.

Uwani ta tabe baki ta fice ta barta bako Allah ya bata lfy, Mariya ta bita da kallo cikin mamaki.

A kasuwa sunje siyayyar kaya ita da yusuf suka hadu da mahaifiyar jamcy inda take gayamata ai sai daga baya ta sami labarin jamcy taje America, har an kama ta ita da saurayin anyi hanging din su, uwani tayi wa matar alheri suka tafi,

Sai take qara jin wata nadama da nutsuwa a tare da ita, lallai ba qaramin cutar da jiddah tayi ba, haka ta shirya taje tana qara roqon jiddah akan ta yafe mata.

Uwani bata cin wani abinci mai nauyi, daga kifi, sai indomie da kwai, sai bread, sai apple, wai kada taci wani abinci yaron ta ya fito da qaton ciki ko kuma ya kasa tafiya,

'Ko turare xata sakawa jikinta sai ta shafawa cikin, yaron ta ya fito mai qamshi.

Bata aikin komai har mai aiki ta saka aka nemo mata ummi fingers, ita ke kula da gidan da komai.

Sun shirya da surayya suna xama na mutunci a yanxu a duk sanda suka hadu, babu wannan kishin sai dai wanda baa rasa ba.

Kullum xancen uwani baya wuce da ta haihu bayan biki xata fara koyawa yaron tafiya yaje makaranta da wuri ya gama saboda yan baqin ciki, har keken koyon tafiya duk ta siyo masa.

Haka yusuf ke xaune da uwani yana son ta yana kula da ita kuma yana biye mata duk da tayi sanyi sosai akan da.

'Abba kullum cikin sakawa yusuf albarka yake duk wanda xai iya xama da uwani tabbas abin a jinjina masa ne.

Cikin uwani ya shiga watan haihuwa.....

El'mustapha ina so na yaye airah na gaji da wannan tsotson nata shi ke hana min jiki,

Ya xauna yana fadin shekara daya da wata biyar fa jiddah, ina laifin ki barta tayi two to three months ta qara sha, haba jiddatulmusty me kike son taci.

Tace tana cin abinci sosai fa You know, dana yaye ta yanxu ne xaka ga na maida jikina sai kayi mamaki.

Yayi murmushi hade da Jan dogon hancinta yana fadin a qara mata two months ta kai da wata bakwai pls jiddah.

Xatayi magana wayar sa ta dauki qara yana dubawa yaja tsaki hade da ajiye wayar,

Waye yake kiran ka kake bata fuska haka musty,

Xaiyi magana ta qara ringing karo na biyu, ya dauka cikin bacin rai yana fadin didn't I warned you not to call me again, bai jira amsarta ba ya tsinke wayar.

Murmushi jiddah tayi tana fadin el'mustapha mai yan mata, ya kai mata dukan wasa ta goce tana dariya, suna haka wayarta ta dauki qara tana dubawa sunan banan tagani, ta dauka.

'Anty jiddah na haihu yanxu,

Masha Allah banan, me aka samu,

'Na sami baby girl,

STORY CONTINUES BELOW


Da kace hajiya uwani xata washe bakin nan dan kawai kaga haqorin da ta saka, ko baka mata mgn ba kuka hadu a hanya xata yi ma dan kawai kaga abinda ke cikin bakinta.

Tare suke xuwa kullum da yusuf asibiti a duk sanda xata je ganin likita, wani xuwa ne da suka yi uwani ta hadu da hajiya Mariya da kyar ta gane ta saboda yanda matar ta rame tayi baqi ta lalace.

Da tsinin cikin uwani ta bi bayanta tana fadin kamar Mariya nake ganin wannan tambadadiyar,

Hajiya Mariya ta dubi uwani, bata manta da fuskar uwani ba,

Tace Allah sarki uwani kinyi aure kenan ashe xan qara ganin ki.

Uwani tace me ya same ki haka kika lalace.

Tace wlhy rashin lafia nake fama da ita kullum ina hanyar asibiti kan wannan abun da nake na kamu da lalura.

Uwani ta tabe baki ta fice ta barta bako Allah ya bata lfy, Mariya ta bita da kallo cikin mamaki.

A kasuwa sunje siyayyar kaya ita da yusuf suka hadu da mahaifiyar jamcy inda take gayamata ai sai daga baya ta sami labarin jamcy taje America, har an kama ta ita da saurayin anyi hanging din su, uwani tayi wa matar alheri suka tafi,

Sai take qara jin wata nadama da nutsuwa a tare da ita, lallai ba qaramin cutar da jiddah tayi ba, haka ta shirya taje tana qara roqon jiddah akan ta yafe mata.

Uwani bata cin wani abinci mai nauyi, daga kifi, sai indomie da kwai, sai bread, sai apple, wai kada taci wani abinci yaron ta ya fito da qaton ciki ko kuma ya kasa tafiya,

'Ko turare xata sakawa jikinta sai ta shafawa cikin, yaron ta ya fito mai qamshi.

Bata aikin komai har mai aiki ta saka aka nemo mata ummi fingers, ita ke kula da gidan da komai.

Sun shirya da surayya suna xama na mutunci a yanxu a duk sanda suka hadu, babu wannan kishin sai dai wanda baa rasa ba.

Kullum xancen uwani baya wuce da ta haihu bayan biki xata fara koyawa yaron tafiya yaje makaranta da wuri ya gama saboda yan baqin ciki, har keken koyon tafiya duk ta siyo masa.

Haka yusuf ke xaune da uwani yana son ta yana kula da ita kuma yana biye mata duk da tayi sanyi sosai akan da.

'Abba kullum cikin sakawa yusuf albarka yake duk wanda xai iya xama da uwani tabbas abin a jinjina masa ne.

Cikin uwani ya shiga watan haihuwa.....

El'mustapha ina so na yaye airah na gaji da wannan tsotson nata shi ke hana min jiki,

Ya xauna yana fadin shekara daya da wata biyar fa jiddah, ina laifin ki barta tayi two to three months ta qara sha, haba jiddatulmusty me kike son taci.

Tace tana cin abinci sosai fa You know, dana yaye ta yanxu ne xaka ga na maida jikina sai kayi mamaki.

Yayi murmushi hade da Jan dogon hancinta yana fadin a qara mata two months ta kai da wata bakwai pls jiddah.

Xatayi magana wayar sa ta dauki qara yana dubawa yaja tsaki hade da ajiye wayar,

Waye yake kiran ka kake bata fuska haka musty,

Xaiyi magana ta qara ringing karo na biyu, ya dauka cikin bacin rai yana fadin didn't I warned you not to call me again, bai jira amsarta ba ya tsinke wayar.

Murmushi jiddah tayi tana fadin el'mustapha mai yan mata, ya kai mata dukan wasa ta goce tana dariya, suna haka wayarta ta dauki qara tana dubawa sunan banan tagani, ta dauka.

'Anty jiddah na haihu yanxu,

Masha Allah banan, me aka samu,

'Na sami baby girl,

STORY CONTINUES BELOW


Duk gurin aka cika da mamaki aka hana uban d'a aka baiwa wani😨, El'mustapha wani jigo ne na rayuwar uwani da take matuqar gani qima da girmansa,

El'mustapha ya karbi yaron cikin murmushi lallai uwani tayi gasky yaron duk abba ne, a hannunsa suka samu suka karbi yaron suka gani.

Ta nace baxata bi su hajiya wankan gida ba, a gidan jiddah xata xauna haka suka haqura suka je da ita can gidan,

Yan barka masu ganin jariri da yawa idan sunxo sai dai suga jariri a hannun uwarsu bata yarda ta basu ba yanda take ganin sa fari haka kada a sama sa datti yayi baqi, tayi ta tabin fatar jikinsa tana jin dadi, sai ta hanawa yaron ya samu yayi barci saboda taba nan taba can.

'Ko barci yake sai an tada shi yasha nono kada ya xauna da yunwa, idan wanka aka je yi mata da taji kukan sa xata fito toilet da gudu ta dauki abinta.

Idan yana kuka uwani tana kuka, idan yana barci tana yi idan ya tashi ita ma ta tashi.

Mutanen gidan suna ganin ikon Allah.

Yusuf bawan Allah, yaxo yana tambayar uwani wane suna take son a sakawa yaron?

Kai tsaye tace a saka masa *EL'MUSTAPHA* saboda ya biyo hali, haxaqa, da kwarjinin mai sunan, tana son El'mustapha, yusuf yasa hannu ya bige bakinta yana fadin,

Kada na qara jin kalmar uwani, Allah ya raya el'mustapha.

Ranar suna fa an cashe babu laifi anyi taro lfy an watse lfy.

El'mustapha yayi namijin qoqari ga takwaran nasa, bayan suna uwani ta tada masa fitinar sai ya bata vespa din ta xata baiwa yaron ta Affan dama shi ta siyawa, da kyar el'mustapha ya kashe wutar vespa din.

Wata daya da haihuwar uwani har lokacin bata koma gidan yusuf ba jiddah taqi ta bari ta koma har sai ta gama yarda da nutsuwarta tukunna.

A dai dai wannan lokacin el'mustapha ya sami qarin girma daga A. I. G xuwa D. I. G, farin cikin su baxai misaltu ba,

Ibrahim yana daya daga cikin mutanen da suka sami promotion din,

Dr.Merah da kansa yayo tattaki har Nigeria dan taya El'mustapha qarin girman da ya samu.

Yusuf yana buqatar matarsa ta koma duk da anty ikram tayi wa jiddah mgnr komawar uwani dan yanxu suna shiri sosai da uwani ta nutsu ba kamar da ba, haka Ma anty yusrah.

Yan uwan yusuf a yanxu sun dan ko waye uwani haka suke xaune da ita ana haquri,

Akwai ranar da jiddah ta risketa da bindigar el'mustapha lokacin tana shayar da jaririn, kai tsaye ta cewa uwani kashe yaron xatayi.

Saboda tsoro da raxana uwani harda sakin fitsari ganin lallai jiddah da gaske take xata kashe mata yaro tunda har ta saita ta da bindiga,

'Anty jiddah ki kashe ni kibarmin shi ya rayu, dan Allah ki yafe min kada ki kashe min yaro ina son sa, idan kika harbesa nima mutuwa xanyi.

Cikin daure fuska jiddah tace sai dai ki mutu amma sai na harbesa kamar yanda kika harbi arham, ta qara saita bindigar akan yaron, nan take uwani ta xube gurin a sume.

Jiddah ta dauki yaron tana fadin ko ba komai kinji radadin da naji lokacin da aka harbi 'dana aka bani shi rai a hannun Allah, baki dubi halin da nake ciki a lokacin da nake da juna biyu ba, jiddah ta fita da yaron tana jijjigashi.

Bayan farfadowar uwani sai kuka take tana qara roqon jiddah gafara, tana jin nadama mai tsanani a tare da ita a duk lokacin da ta tuna sanda tace a harbe arham har ya fadi hannun jidda, ashe abinda jiddah taji kenan amma shine bata suma ba har ta iya riqe sa tana kuka, lallai jiddah tayi namijin qoqari Allah ya yafe mata.

Yau kam yusuf yaxo yana so matar sa ta koma ya gaji da kawaicin da yakewa jiddah, ya sami uwani a dakin ta, ya san ta da jaraba.

Uwani yaushe xaki koma ne, nayi missing din ki kinsan bana gajiya dake.

Tace ai kaine da kaqi gayawa anty jiddah har yau fa mu ango da amarya ne maso son junan mu bama gajiya da wannan abun.

Murmushi yayi yana kallonta darun uwani na birgeshi, yana son matarsa a hakan, yace ban taba fada mata ba ina jin nauyinta kin sani.

Uwani tace haba shiyasa ta qudundune mu a wannan gidan nata take gasa mana aya a hannu, idan kana jin nauyin ta ni xanje na gayamata daukar haqqin da take yayi yawa.

Rufamin asiri uwani, ai baxan iya ba,

Ta soma qoqarin tashi tana fadin ni bari naje na fada mata saboda ina son wannan abun dai dai lokacin jiddah ta shigo, yusuf ya gaida ta,

Uwani ta dube ta tana fadin, anty jiddah ko xaki yiwa yaya El'mustapha magana ne a bude mana wancan part din nida yusuf da affan mu dawo da xama a cikinsa, 1

Jiddah tace ban gane ba, naki gidan fa?

To ai naga kin tsare mu a wannan gidan naki bayan kinsan muna da namu, tuntuni nake son maki magana ana kwaba ta kuma ke kinqi ki gane kina daukar haqqi, ke kullum kina tare da mijinki amma ni ana min baqin ciki da nawa mijin.

Mamakin uwani ya hana shi motsi daga inda yake xaune,

Jiddah da ta saba da halin uwani murmushi kawai tayi tana fadin, Uwani will never change, Uwanitilyusuf kayan Allah, Allah ya baku xaman lafiya ya qarawa yusuf haquri da ke.

*

El'mustapha ya siyowa jiddah form na jamb ta cika yana so ya maida ta makaranta tayi karatu kamar yanda mahaifin jiddah Uncle B ya bashi shawara,

Jiddah ta kwashe yanda suka yi da uwani ta fadawa el'mustapha sai dariya yake,

Jiddah yarinyar nan baxata kashe ni ba, she is olways funny katobarar tace kawai bana so.

Jiddah ma cikin dariya tace like serious El'mustapha, Uwanin ka ce fa, Uwanitilmusty wanda mutuwa kadai xata raba ku duk mai mata baqin cikin xama da kai bata son shi.

Taja hancinsa tana murmushi, Matar El'mustapha before mai neman takara ta fito yar siyasa bayan ta gama gashin masara a qofar gidansa, Uwanitilmusty mai xubawa mijinta pills,

El'mustapha ya matse ta sosai a jikinsa yana fadin, uwani ta yusuf ce a yanxu kada ki mata baqin ciki da mijinta Uwanitilyusuf, El'mustapha kuwa na jiddah ne ita kadai har qarshen rayuwarsa Jiddatulmusty,

Suka kyalkyace da dariya cikin rungume junan su......


A'UZU BILLAH MIN AZABIN NARI WA AZABIL KABRI WA FITINATIL MAHYA WAL MAMATI WA FITINATIL MASIHID DAJJAL (AMEEN) 1

ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAHI (kuskuren dake ciki Allah ya yafe mana) 2

BISSALAM.

Post a Comment for "EL-MUSTAPHA CHAPTER 13 KARSHE"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...