Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

EL-MUSTAPHA CHAPTER 10

EL-MUSTAPHA CHAPTER 10

- - Post a Comment
EL-MUSTAPHA

CHAPTER 10El'mustapha ya tsayar da cin abincin da yake ya xuba mata narkakkun idanuwansa cikin mamakin jin abinda take koro masa, +

'meyasa ibrahim xai auri Uwani, ke kina gudun ta kuma kike liqawa wani, wanda ya riga ya san halinta? 13

Amma El.... yayi saurin katseta, ibrahim baxai taba iya auren uwani ba, ya bani lbr tsanar da yayi wa yarinya, bayan wannan Ma meyasa xaki kira anty ikram ta fitar da uwani a gidannan, idan a gaban iyayen ta kin amince ta xauna sun tafi sun bar ta saboda me xaki tura ta daga baya, why jiddah?

Meyasa uwani xata cigaba da xama a gidannan, tana xama gidannan before saboda karatu da aure yanxu kuma babu xaman me xata min a gida.

Mtsew yaja tsaki hade da ture plate din arish dake gabansa, tashi yayi ta biyo bayan sa tana fadin,

Breakfast din fa, nasan baka qoshi ba, baiyi mgn ba dakin sa ya nufa, wayarsa ya kunna kafin ya xauna bakin gado yana dialing number Abba, bata jima da fara ringing ba ya dauka.

'Abba ya hanya,

'Alhamdulillah mun iso tun daxu, ya jikin naka,

'Jiki 'Alhamdulillah, Uwani ta iso kuwa?

'Abba yace aa tana hanya ne?

El'mustapha yace tana hanya, idan ta iso ta huta xuwa gobe ka turo min ita,

'Abba yace ba dai wani abin tayi ba ko?

Yace aa,

Tau shikenan abba ya fada yana tsinke wayar.

Jiddah ta tsura masa idanu, xuciyarta na bugawa me el'mustapha ke nufi da uwani ta dawo, yana son xama da ita ne kada dai el'mustapha yana son uwani ne a yanxu, indai har uwani xata dawo ta cigaba da xama a gidan tabbas xata barshi kuwa.

Meyasa uwani xata dawo el'mustapha? Ta tambaya tana kallonsa idanunta cike da kwallah.

Fada ko bacin rai bashi xai gyara uwani ba, rarrashi da tausayi shine xai gyarata, ni xan iya xama da uwani na gyara ta. 4

Xaka iya xama da uwani ka gyarata bafa matar ka bace You know it, ko dai kana son ta ne kana son maida auren ku kake min yawo da hankali, da can da take matar ka baka gyara ta ba sai yanxu da ba aure tsakanin ku.

Kallonta yake cikin ido, yace duk yanda kika dauka hakane, in ma son ta nake in ma auren ta xanyi, I have the right. 17

Tace hakane nasani kana da iko el'mustapha bayan uwani ma xaka iya auro wasu biyun ka aje, ta juya ta bar dakin da sauri, kitchen ta nufa duk da xuciyarta ba dadi bai hana mata dora girki ba sai dai tana yin komai ne tana sharar kwallah cikin damuwa.

*

Hajiya sun koro ni, hajiya xo kiga yanda suka koro ni da komai nawa saboda ana min baqin ciki xan xauna da el'mustapha ko tsinke nawa baa bari a gidan ba, harda cewa naje na auri nawa mijin.... Shine abinda uwani ke fada lokacin da ta shigo harabar gidan kusan magrib kenan, abba na shirye shiryen xuwa masallaci.

Ya tsaida idanunsa akanta yanda ta xube gurin tana kuka kamar qaramar yarinya, 1

Yace uwani sai yaushe xakiyi hankali kisan kin girma ne, menene amfanin wannan abin da kike,

'Abba koro ni sukayi, dubi kayana gabaki daya na dawo dasu, jiddah tace na xauna amma ita wannan yayar tana xuwa ta fito dani da qarfi, sai kaga yanda take turoni na fito gidan kamar gidan ubanta, ni ba wannan ne damuwa ta ba yanda ta saka ni gyaran gidan gabaki daya na share nayi mopping, nayi wanke wanke har da wanki ta sakani abba bayan ga masu yi ga washing machine amma tace lallai sai ni, uwani ta cigaba da kuka. 2

Yace to menene dan kinyi ai yar uwarki kika yimawa, qila taga bakyason aiki ne ta saka ki ko kin mata rashin kunya ta koro ki, banda haka ni ban yarda xaa iya koro ki gidan a gaban jiddah ba kuma ta kyale.

STORY CONTINUES BELOW


Wlhy koro ni suka yi abba, wai inje in nemi mijina harda cewa idan naqi xasu saka bindiga su harbeni na mutu kowa ya huta dama babu mai sona.

Yace amma el'mustapha ya kira idan kika huta xuwa gobe kije yana neman ki,

Tayi wuf ta tashi tana kallonsa cikin bude ido.

Yaushe ya gayamaka hakan, ya kira ka ne, amma shine abba ka barni tin daxu ina surutu kaqi gayamin ai da yanxu na dade da kai.

Yace kije ina yanxu uwani ai kin bari har gobe idan kin huta yanxu dare yayi.

Wallahi abba yanxu xanje ai baxan iya barci ba, ni ba sai na huta ba.

Yace to baxakije a yau ba sai gobe ynxu dare yayi har yaushe kika je.

'Abba dan Allah ka barni kaida baka min baqin ciki kuma kake hanani komawa, haba abba daxu ina barci a mota har mafarki nayi muna aljanna banda yan baqin ciki. 2

Ki xauna ba inda xakije, ya fita da sauri xuwa masallaci.

Uwani bata may shiga cikin gidan ba ta bude katuwar jakarta ta dibi wasu kaya ta saka a qaramar jaka ta fice tana murna, el'mustapha yana son ta yana son xama da ita amma ana mata baqin ciki dashi sai ta koma.

Fitowar jiddah daga daki yayi dai dai da dawowar el'mustapha daga masallaci, ta gabatar mashi da abinci fuskarta ba annuri, ta qarasa tsakiyar falon ta xauna tana duba arham da aka maido mata saboda xaxxabin da yake.

Xaka ci abinci naxo na baka, ya girgixa kansa yana kwantawa cikin jikinta,

Mummy kibani magani,

Ba yanda xaa yi kasha magani babu abinci a cikin ka, bari na kawo maka ko yoghurt ne kasha, ya qanqameta yana kuka,

Ni bana so kibani magani nasha,

Ba wani magani da xan baka yanxu arham, paracetamol na airah I don't think xai maka aiki, ko xamuje asibiti ne?

Ya girgixa kansa yana qara shigewa jikinta, jikinsa yayi xafi sosai har bata son yana shiga jikinta,

Duk abinda suke el'mustapha na sauraren su yana cin abincinsa, yana gamawa ya tashi ya bar falon, arham kuwa ya soma amai sosai hankalin ta ya tashi.

Hadixa taje ta kira ta gyara gurin kana ta dauke shi ta nufi toilet dashi, wanka tayi masa ta shiryasa ko ta kan airah bata bi ba ballantana el'mustapha ta dauki key din mota ta fita.

Har goma na dare bata dawo ba tana xaman jiran likita, dai dai wannan lokacin uwani taxo gidan, tana shiga falon idanunta na sauka akan dining, ta jefar da jakarta da gudu ta nufi dining da alama yunwa take ji sosai.

Shiru shiru el'mustapha baiji motsin jiddah ba tun yana wasa da airah da ta tashi tun daxu har ya soma gajiya da alama yarinyar kuka take son farawa yanda yaga tana mutsuniya.

Ya dauko ta ya fito da ita anan yaci karo da uwani xaune sai loda abinci take a cikinta,

Ita wannan yaushe taxo gidan? Xaiyi amfani da son da take masa da kuma tsoron anti ikram da take wajen ganin ya gyara rayuwarta.

Yaushe kika xo gidan waye ya baki ixinin ki xauna kici wannan abincin?

Ta xuba masa idanu bayan ta dago tana kallonsa, nan take taji gabanta ya fadi wani tsoron sa ya risketa lokaci daya,

Tace kayi haquri,

Ya tako a hankali har xuwa inda take, ya xauna yana fuskantarta cikin jijjiga airah,

Ke da nace sai gobe ya akayi kika dawo cikin wannan daren,

'Na kasa haquri ne nasan xaka maidani dakina kada kamin baqin ciki kasan ina son ka. 1

STORY CONTINUES BELOW


Yace kinyi sallah kuwa?

Tayi caraf tace ai banayi tun jiya bana yi, kwana hudu nake yi na ga.... yayi saurin katse ta,

Kin san meyasa nace kixo?

Ta girgixa kanta da sauri tana sud'e yatsun hannun ta,

Ai nasan kina sona ko uwani,

Sosai ma wlhy har mafarkin ka nake yi, kullum ina tunanin ka, ina son ka sosai dan Allah kayi haquri ka taimaka ka maidani dakina kada kamin baqin ciki, ko barci nake kai nake gani, idan naji muryar wani namiji kai nake tunawa, ko dan sanda nagani birgeni yake yi saboda kai.

Tau shikenan naji uwani idan kina so na yarda kina sona kuma kina so na maidaki dakin ki sai kin nutsu, duk wannan shashancin ki daina, girmama iyayen ki da duk wanda ya girmeki, banda maidawa mutum magana idan ana maki fada, banda tsokanar mutane  musamman maxa, ki riqa girmama duk wanda ya girmeki, wawancin da kike da rashin ji duk ki daina, ina ga kin xama mutum irin jiddah nan da wata biyu kacal na miki alqawari xan maidaki dakin ki.

Ta langabar da kanta, ai kasan ina son ka kome kake so xanyi, ni yanxu ba ruwana ma da kowa baxan qara kula kowa ba koda xagina aka yi, idan na nutsu xaka aure ni ko,

Ya gyada kansa yana kallonta,

Tace kuma xaka riqa kirana Uwanitilmusty ko?

Nan ma ya gyada kansa, tayi murmushi tana kallonsa,

Yace yanxu xamuje dake driver ya kaimu inda anty ikram dan baxan iya driving ba,

Xumbur ta miqe tana fiddo idanuwa,

'Wannan matar ai wallahi baxan je ba, ai itace ma ta koreni a gidannan saboda tana min baqin ciki da xamana a gidan mijina.

Yace ashe baki sona uwani tunda har bakyason abinda nake so, idan nace ina son abu baxaki iya yi min ba kenan, banda wannan ma yanxu na gama yi maki mgnr girmama wanda ya girmeki amma yaya ta kike cewa tana maki baqin ciki.

Kayi haquri sweet baxan qara ba, ai xanje wasa nake ma, kuma nasan dama bata min baqin ciki tana sona.

'Yauwa gurin ta xaki xauna duk yanda tayi dake haka xaki bi, idan kika nutsu kika gyaru ita ce ma xata maidaki dakin ki.

Allah ko?ta xauna cike da farin ciki dai dai lokacin jiddah ta shigo dauke da arham a kafadarta, duk suka juya suna kallonta, cak ta tsaya qofar falon tana kallonsu cikin faduwar gaba, haka taji kamar falon yana juyawa da ita, da kyar ta iya daga qafafunta ta qarasa cikin falon.

'Anty jiddah kin dawo, kinga nima na dawo ai yaya ne yace na dawo xai maidani dakina.

'Ko kallonta jiddah batayi ba ballantana tasa ran xata amsa ta,

Uwani xata yi magana el'mustapha yasa qafa ya bigi qafarta, ta juyo da sauri tana kallonsa, harararta yayi yana fadin tashi marar sirri.

Ta tashi da sauri, shima ya taso da airah, ya shimfide ta akan sofa kana ya nufi arham yana taba jikinsa, har lokacin akwai xafi.

Arham ya dube sa yana fadin, mummy ta kaini anyi min allura asibiti,

Ya shafa kansa yana fadin sorry, kaci abinci kasha magani yanxu xanxo maka da ice cream ka ji.

Arham ya gyada kai yana fadin harda Pringles daddy,

Yace to shikenan, ya dubi jiddah a hankali yace xamu fita da uwani.

Komai bata ce ba amma gabanta na tsananta bugawa, ya juya ya fita uwani tabi bayansa da jakarta tana waiwayen jiddah.

Wa nake gani kamar uwani cewar anty ikram tana kallonsa da mamaki a fuskarta,

Uwani ta qara matse jakarta tana boyewa bayan el'mustapha,

Ikram tace kada dai uwani bakije gida ba kika dawo?

El'mustapha yace ni na dawo da ita sister?

Meyasa ta tambaya tana kallonsa da tsananin mamaki,

Ya riqa hannun uwani ya xaunar da ita kana ya dubi ikram yana fadin, xo muyi magana sister.

Ikram tabi bayansa, suka fita ya koro mata bayanin komai da dalilinsa na son uwani ta xauna a gidan.

'Naji banqi maganar ka ba, duk wanda ya gyara d'an wani tamkar ya gyara nashi ne, kuma ga lada amma kasani el'mustapha ko ta nutsu ta shiryu baxaka taba auren uwani ba.

Ya sauke numfashi yana fadin na sani sister, kina son jiddah ta barni kenan yanxu haka ma fushi take tun da na kira nace uwani taxo, ko abinci bata ci ba, arham ma bashi da lfy da kanta ta kaishi asibiti duk saboda tana fushi uwani xata dawo.

Banga laifinta ba saboda abinda aka mata da farko bata ji dadi ba kuma baxata qara yarda da uwani ba ballantana ta dawo gidanta.

Nifa ba wai ina son maida uwani bane, kawai ina so nayi amfani da son da take min naga na shiryata da taimakon ke da take tsoro, amma idan nace na barta gida tare da jiddah kishi baxai saka jiddah taya ni gyaran uwani ba.

Uwani tayi mamakin ganin anty ikram ta dawo har tana murmushi, ta kira mai aikinta cewa ta shigar da uwani dakin su amira.

Uwani taji dadi anty ikram ta daina mata baqin ciki.

El'mustapha yayi masu sallama ya tafi, bai manta da saqon arham ba sai da ya saka driver ya biya dashi ya siya masa kafin su dawo gida.

A wannan lokacin tasha kuka sosai kamar ranta, idanunta sunyi jawur tana tuna wahala da tasha a baya saboda uwani amma el'mustapha keson maidata, wannan ke qara tada hankalin jiddah dan batasan plan din uwani na biyu akanta ba duk ranar da ta qara auren el'mustapha, ba wai son xamane bata yi da uwanin ba illah tsoron rashin imanin ta da take.

Kallonta el'mustapha yayi sai da gabansa na fadi saboda ganin yanda idanunta suka yi jawur,

Kuka kika yi jiddah, kukan me?

Tayi masa banxa, ya matso yana tambayar kinci abinci kuwa, nan ma shiru tayi masa,

Yana qoqarin xama kusa da ita, ta tashi xumbur ta dauki airah ta nufi dakin ta, ya bita da kallo har ta shige kafin ya maida kallonsa ga arham dake kwance yana lumshe idanunsa yana bude wa.

Mummy taci abinci kuwa?

No, tun daxu take kuka.

Xo ga ice cream din kasha sai muje mu kwanta dare yayi,

Daddy ni bana jin barci yanxu.

Yace aa, sha ice cream din tukunna kafin naxo, ya tashi ya nufi dakin jiddah, ga mamakinsa jiddah ta rufe qofar da key, hankalinsa ya qara tashi, jiddah bata taba rufe masa qofa ba, meyasa take tsiro da abubuwan da bata saba yi masa ba a xamantakewar auren su? 4

Saboda tana xargin ka da son abinda take gudu take ganin kamar cutar wane yanxu a gare ta, yaji xuciyar sa ta bashi amsa.

Ya soma buga qofar a hankali yana kiran sunan ta amma tayi masa biris.

Daddy ni baxan sha ice cream din ba sai gobe, idan nasha amai xanyi.

El'mustapha ya juya yana kallon yaron a sanyaye. Pringles din fa? +

El'mustapha ya tambaya yana kallonsa,

Baxan ci ba sai gobe,

Yace tor shikenan, ya riqa hannunsa suka nufi dakin sa,

Daddy yau tare xamu kwanta ne?

Ya gyada kai yana kallon yaron,

Ya xauna yana dialing number jiddah, tana fara ringing yaji an kashe gabaki daya, ya dafe kansa, arham ya kwanta jikinsa yana fadin,

Daddy baka sakamin kayan barci ba, kullum momy sai ta sakamin kafin na kwanta.

El'mustapha ya tashi cike da damuwa yace cire kayan kafin na dauko ma kayan barcin naka,

Bai jima da fita ba ya dawo yana fadin,

Meyasa baka cire kayan ba arham,

Daddy ni bana iya cirewa,  el'mustapha ya xauna yana cire masa kayan, ya saka masa na barci ya dubesa har yanxu jikinsa akwai xafi, suka kwanta.

*

'Washe garin ranar koda suka tashi jiddah ta gama komai na breakfast ta ajiye masu, ta shigewar ta dakin ta rufe., koda suka yi wanka suka fito ta gama komai amma bata falon.

Arham ya sami lfy amma ba qarfin jiki, ga maganin sa a falo amma bai san kansu ba, ya dauke sa suka yi breakfast, ya dawo yana buga qofar jiddah taqi budewa.

Yayi juyin duniya yana rarrashinta amma tayi masa banxa, tunanin sa jiddah bata ci abinci ba tun jiya kada wani abin yaxo ya same ta. 1

Ya kira anty ikram ya gayamata itama tayi kiran jiddah taqi dauka kuma taqi ta kashe wayar,

Cikin damuwa ya qara xuwa bakin qofar, kome kike ji jiddah ki fito kici abinci ba danni ba please,

'Ko alamar motsinta bai ji ba, yaji kamar ya bige qofar dakin.

Kusan goma na safe anty ikram taxo gidan, tayi magana tayi rarrashi ta dawo fada duk jiddah bata bude qofar ba, idan har suna son ta sun damu da rayuwarta saboda me xasu dawo da uwani.

Anya yarinyar nan tana da rai kuwa ko motsin ta bana ji cewar anti ikram tana kallon el'mustapha.

Yace lafiyar ta qalau sister tunda baki ji kukan airah ba kinsan ta da fitinar tsiya, ni ban sani ba ko jiddah taci abinci ne?

Kaima da laifin ka el'mustapha, yarinyar nan an maidata saboda me xaka ce ta dawo, baxaka iya shirya wannan yarinyar ba tun da safe sai da sukayi dambe da mai aikina wai bata kai mata ruwan wanka ba, ban sani ba ko na dauki mai aikin ne saboda ita, kawai sai ta fara dukan yarinyar mutane, 1

Ta juya a fusacce tana fadin ko menene laifin kane idan ma son yarinyar kake tun wuri ka cire sonta a xuciyarka na gayama baxaka taba maida wannan yarinyar ba wadda tayi yunqurin kashe yar uwarta da gudan d'anka ai da yanxu babu arham banda taimakon Allah. 2

Yace sister tafiya kuma xakiyi keda na ki.... tayi saurin katse sa,

Xaka bani headache ne el'mustapha, laifin kane wannan karon bansan me kake so nayi ma ba, nayi magana taqi budewa so kake nayi ta tsayuwa? Idan naje gida xan gwada kiran number ta inta dauka xan mata magana.

Yayi shiru baiyi magana ba ta fice ya xauna yana shafa kan arham,

Daddy meyasa mummy bata fito ba,

STORY CONTINUES BELOW


Nima ban sani ba,

Daddy kace aryan ya dawo yau.

Tau shikenan xan kira anty yusrah ta kawo shi.

Suna haka ibrahim ya shigo,

'Ashe haka hannun ya kasance bayan rabuwar mu, cewar ibrahim yana qoqarin xama a sofa.

El'mustapha baiyi magana ba,

Ibrahim yace naji ana qishin qishin xaa yi promotion fa a office jiya,

El'mustapha ya ware idanu yana kallon sa, kai haba amma yaushe xasuyi,

Shine ban sani ba, Muna addua Allah ya sa damu a ciki,

El'mustapha yace amin,

Ibrahim yace yau ina jiddah ne sarkin rigima kaji abinda take son liqamin, wannan mahaukaciyar yarinyar marar imani.

El'mustapha yayi murmushi yana fadin ai na gayamata baxaka auri uwani ba,

Yace kai haba, bani da burin qara aure a yanxu matan nan biyu sun isheni kansu a hade yake kuma gwargwado ina iya bakin qoqarina akansu suma suna faranta min, yanxu tunanin ka idan na dauki uwani na jefa gidana wallahi ko rantsuwa nayi baxanyi kaffara ba xanje na sami ta raba min kan matana wannan tayi gabas wannan tayi yamma ita kuma tana kudu mahaukaciyar, before I know b.p na ya hau inma ban kwanta asibiti ba, kai qila watarana naxo na sami yan sanda qofar gidana saboda wannan yarinya, na tabbata har maqota idan akwai mata biyu sai ta ware su ko ta hada mata da miji fada, yanda kasan saukar boko haram a Maiduguri haka yarinyar take, 2

El'mustapha yace shiyasa bana son yarinya komai ina yine saboda jiddah ashe kuma laifi nake ban sani ba.

Ibrahim yace dubi ja'irar yarinyar nan saboda rashin imani tana kwance a asibiti fa sanda ka harbeta a qafar nan har tambayata take wai jiddah ta mutu, ji fa.... haba... haba.... ina.... ai wannan tafi qarfin ibrahim wallahi bana sonta ko kadan, jiddah ta cuceni da take son hada ni da ita, in kai ta ina, na dawo mijin hajiya kenan d'an albashina da naji alert na kwashe duka na kai mata.

El'mustapha ya kyalkyace da dariya, yana fadin babban dan sanda da kai sai tsoro, yarinya ce fa kada ka bada maxa,

Bala'in ta yafi yarintarta tunda har tasan ta kashe yar uwarta saboda namiji, tasan ta cutawa yaro saboda namiji to menene baxatayi ba, barni da yan matana guda biyu, ina juya nan a rungume ni, na juya nan naji kiss, ina ce wash a koro min sannu yafi goma, komai na siyo ana min godia da addua, wallahi watarana har rikicewa nake na rasa dakin wa nake sai su tamin dariya.

El'mustapha yace wai ko nima xan xo na shiga layin masu mata biyu dinnan ne.

Ibrahim yace da kuwa kaci ubanka gurin jiddah, kuma wallahi babu ruwana kada kace dani kayi xancen. 5

El'mustapha yace rufamin asiri wasa ma nake bani da sha'awar yin haka, jiddana ta isheni rayuwa my one an only wife,

Ibrahim yace a to gwanda ka dawo cikin hankalinka ni kaina yanxu nace xan qara aure nasan gidannan baxan qara jin sanyin sa ba, kullum sai an min gargadi duk xani fita aiki akan mata, wai ina jiddah ne, ya soma kallon sashen ta cikin daga murya yana fadin, Jiddatulmusty yau me akeyi haka ne a ciki ba ko gaisuwa.

El'mustapha ya dubesa yana fadin fushi takeyi tun jiya take a rufe,

Subhanallah, ibrahim ya fada yana kallonsa, kuma kake xaune kabarta, sai ka balla qofar mana kasan halin da take ciki.

El'mustapha yace nima nayi tunanin yin haka, ba fushin nake mawa ba illah rashin cin abincinta,

Ibrahim ya tashi ya nufi qofar dakin yana kiran sunan ta amma bata amsa ba, ya juya yana kallon el'mustapha yace,

STORY CONTINUES BELOW


'Wannan qofar ba wadda xaa bige bace, ka kira masu hada qofar nan suxo su bude, wai me ma kayi mata ne, lafiya qalau muka rabu da ita a jiya,

Yace saboda na maida uwani ne.

Ibrahim ya xare idanunsa yana kallonsa ban fahimce ka ba, ina ka maida uwani auren ku ko me.

El'mustapha yaja tsaki ya soma tafiya yana fadin kai ka kasa xama da ita ballantana ni dana dandani axabar xama da ita, tana gidan anti ikram da xama ina so na shirya tane.

Ibrahim ya dube sa cikin takaici, ka shiryata as in how, mtsew sai idan son ta kake ka tsiro da wannan baya ga haka miye naka da ka shirya uwani, kai xaka iya shirya tane, ya juya qofar jiddah yana fadin, 3

Kada ki bude masa qofar, cigaba da xama aciki yaje ya xauna da uwanin.

El'mustapha ya dube sa lokacin da yake qoqarin ficewa,

Wai meyasa kun kasa fahimta inda na dosa ne, duk bakin ku daya saboda baku son uwani. 4

Ibrahim yayi masa wani kallo kafin yace yanxu na gane inda ka dosa ai, idan ka gyara uwanin ka maidata dakin ka tunda mu bama so, ka maidata kagani wallahi rantsuwar musulmi bata xama gidannan kai jiddah ma sai ta bar gidan kaje ka cinye uwani.

Ibrahim ya fita ransa a bace, el'mustapha ya xauna xuciyarsa ba dadi dai dai lokacin wayarsa ta soma qara,

Yana dubawa yaga Dr Merah, ya daga wayar suka gaisa,

Yace gani na shigo abuja tun jiya, naxo gaida mai martaba xuwa gobe xan koma.

El'mustapha yace bani address sai naxo mu gaisa kafin ka tafi,

Merah yace aa kai xaka turo min address yanxu xanxo na kawo maka xiyara, ina so naga qafafun jiddah yanda suke a yanxu.

Yace tor shikenan ya tsinke wayar kana yayi masa test na address din,

Ya tashi a rude shi bai masan yanda ake tarban baqi ba duk xaiyi baqi jiddah ce ke komai sai dai yaxo ya sami har ta gama shirya komai,

Ya taba jikin arham dake barci babu xaxxabi tare dashi da alama ya sauka, ya dafe kansa kafin ya soma dialing number jiddah, kusan sau biyar tana ringing bata dauka ba, ya tura test fiye da minti ashirin babu ko reply, yana haka yaji ana sallama,

Ya amsa batare da ya bada izinin shigowa ba saboda muryar daya daga cikin yaran sa ne.

Sir akwai baqi qofar gate suna son shigowa,

Yace yes nasan da xuwansu, sauke su a falon baqi ina xuwa.

Shi tunda yake a gidan bai taba shiga cikin gidan nasa inda masu aiki ba sai wannan karon shima dan ta kama ne,

Suna ganin sa kuwa suka soma gaidashi cikin mamakin ganinsa,

Baisan kowa acikin su ba, gwanda Inna ya nufe ta yana gayamata abinda yake so tayiwa baqin nasa,

Tace akwai hadixa bari na gayamata saboda tasan komai tun banan tana nan tare nake ganin suna komai.

Yace yauwa Inna ayi sauri ba abinci ba kada ki manta, snacks haka kayan marmari da sauransu taxo sashen jiddah ta duba

Ya fita kai tsaye babban falon sa ya nufa na sauke baqi,

Suna hada ido suka sakarwa juna murmushi bayan sun xauna.

El'mustapha ya xauna yana fadin nayi mamaki ganin mai girma merah yau  batare da fadawan sa ba sai mutum biyu kacal.

Merah yaja tsaki yana fadin yanxu ma dan mai martaba bai san da fitowa ta bane da ka gansu jibge duk inda xanje suna tare dani ina jin haushin abin.

STORY CONTINUES BELOW


Sun taba hira sosai aka soma shigo masa da kayan ciye ciye,

Merah ya ware ido yana kallon el'mustapha sanda ya kai Apple bakinsa,

Yace ina qanwata ne, bata san naxo bane ko kana min rowar ta.

El'mustapha ya shafi kansa cikin murmushi kafin yace tana can ta kulle kanta a daki tun jiya tana fushi,

Merah ya dube sa cikin seriousness yace kar dai har yanxu kan maganar mai aikin nan ce el'mustapha,

Yace aa wallahi haba, ai tayi aure week dinnan ma, didn't I told you bana son yarinyar.

Yace why jiddah xata rufe kanta a daki, direct me na ganta.

El'mustapha ya tashi suka nufi sashen jiddah,

Merah ya dubi arham dake kwance kan sofa,

Yace idan na canka dai dai wannan shine twins naku da kuke magana,

El'mustapha ya gyada kai yana fadin shine amma dayan yana gurin sister na anjima xata xo dashi.

Very cute dashi, ashe da kai suke kama, kayiwa qanwata wayo yaran sai suke biyo ka amma suna dauko hasken maman su.

El'mustapha ya nuna masa qaton pic din su dake manne a falon, ga d'an uwansa can mai rigima kamar Merah.

Dariya merah yayi yana fadin kamar Sultan xaka ce, I love this identical twins el'mustapha, kuma a hakan kuke banbanta su kamanin nasu yayi yawa.

El'mustapha ya gyada kai yana kallonsa,

Yace nima xanxo Afiya ta haifamin twins dinnan very soon,

El'mustapha yace sai ka dage kuwa bada sauqi ake samun su ba, Nothing worth comes easy,

Suka yi dariya lokaci daya tare da tabawa,

Merah ya isa qofar dakin da el'mustapha ya kaishi,

Magana yayi cikin kwantar da murya,

Qanwata, ga yayan ki yaxo ya duba qafarki da damuwar ki.

Kamar a mafarki jiddah taji muryar Dr merah, ta taso a hankali xuwa qofar dakin tana leqen sa,

Shine kuwa taji muryarsa yana fadin,

For the sake of me jiddah xo ki bude qofar,

Haka taji a xuciyarta kamar damuwarta ta kau, hijab ta saka dama airah barci take sai bata bi ta kanta ba ta soma qoqarin bude qofar, merah na jin haka ya koma cikin falon inda el'mustapha.

El'mustapha ya cika da mamaki sanda jiddah ta fito, wane girma ne na merah a gurin ta haka, meke tsakanin su, meyasa ta dalilinsa ta fito bayan duk magiya da roqon da ake mata tun jiya, ya xuba mata manyan idanuwansa yana kallonta,

Dr merah ya juyo yana kallonta,

Ya salam, meya sami jiddah haka, menene ya saka ki kuka haka har idanunki suka kumbura?

Kamar jira take ta soma kuka kuwa,

Yace saboda me na baki number na jiddah, kin gaya min ke marainiya ce ba uwa ba uba, ba yaya ba qanwa only you an your husband, nace ki dauke ni matsayin yayan ki, xan hada ki da iyayena su xama naki, xan hada ki da yan uwana, matata har qanwata Rumaisa ashe ke baki dauke ni yayan ki ba idan har baxaki iya gayamin damuwar ki ba.

Ya xauna yana fadin, xo xauna nan naji waye ya taba ki haka, idan mijin kine ko yana babban dan sanda baifi qarfin Sarautar mahaifinki ba haka bai fi qarfin Mulkin yayan ki ba, idan ta kama sai na saka a daure min shi na baki bulala kiyi ta dukan sa har sai inda ranki yayi sanyi.

STORY CONTINUES BELOW


Murmushi tayi wanda bai kai xuciyarta ba, ta qarasa ta xauna inda ya nuna mata,

Banji dadi ba jiddah naxo na same ki cikin wannan halin baki kira kin gayamin ba, aiko a waya ne tsab xan kira na kwatar maki yancin ki, kin ganni nan qanwata rumaisa idan ta sami matsala da mijinta irin wannan, ba wanda xata nema a gida sai ni koda bana gari, kuma ba wanda xai taba ji daga ni sai ita sai mijinta, kuma he is my friend jinina ne shi I told you before, haka xan kirashi idan shine bashi da gaskiya na masa fada ya gyara idan kuma itace ita ma nayi mata fada, Afiya ma sai ta gane ko nayi mata laifi sai taje ga yayanta Bilal xaki ga ya kirani yamin yanda nake masa, and we live happily, idan haka ne meyasa jiddah baxata gayawa nata yayan matsalarta ba.

El'mustapha na xaune baice komai ba ya xuba masu idanu, yana mamakin sauqin kai irin na Dr Merah, a waje idan yana mulki kamar bashi ba, dariyar sa ma baxaka gani ba.

Merah ya dan matso yana fadin, tell me jiddah, don't look at him ba ruwanki dashi da yayanki kike magana,

Batare da bata lokaci ba ta kwashe komai ta gayamasa, tana gamawa kuwa ta fara kuka,

Merah ya dube shi yana fadin, maida uwanin xaka yi ne?

El'mustapha ya girgixa kansa, 1

Merah has tsuke fuska yana fadin idan kayi haka kuma ka cutar da waccan yarinya, idan kasan baxaka maidata ba saboda me xaka mata qaryar idan ta shiryu xaka maida auren ku, baka tunanin dalilin qin maida auren sai ta koma ruwa ta cigaba da abinda take inma baifi hakan ba, to wane gyara kayi mata?

Idan har iyayenta baxasu iya tankwasa ta su gyarata ba I don't think you can do, kaine wa, uban ta 'ko me?

Xai yi magana dr merah ya katse sa, baxan baka damar magana ba a yanxu just take me to your sister house, ina so naga yarinyar....

Suka tashi suka tafi, a falon anty ikram suka xauna, aka kira uwani tun da ta shigo ta kafe merah da idanu, ina el'mustapha ya sami bature haka mai kyau.

Kallo daya dr merah yayi mata ya gane yarinyar bata da nutsuwa,

Kowa bata gaida ba ta xauna tana kallon el'mustapha da murmushi,

Ai daxu ina taso na kira ka naji muryar ka amma ba kudi a wayana, kuma gidannan ana min baqin ciki ba wanda ya bani wayarsa n.... Merah ya katse ta a fusacce,

Shut up.... ya fada cikin tsawa,

Nan da nan uwani ta nutsu tana kallonsa cikin mamaki da tsoro, shi wannan kuma waye.

Yace yayar mu wannan yarinyar a maidata inda iyayenta, suke da haqqi akan kula da tarbiyar ta idan kuma ta gagare su ne su bani inta naje da ita akwai kurkukun da xan jefata a ciki xata gyaru. 3

Ya dubi uwani yana fadin, el'mustapha yana maki qarya baxai aure ki ba ko kin nutsu ko baki nutsu ba, ki cire wannan a xuciyarki, shi mijin mace daya ne jiddah kawai, alqawarin da yayi maki na maganar xai aure ki idan kin shiryu shima babu, ki dauki kayanki kije gidanku ki xauna da iyayen ki, idan kin  ga dama kada ki nutsu kanki kika cuta da iyayenki kuma ba mai auren ki a haka is better ki dawo cikin hayyacinki kisan me kike.....

Duk maganar da yake uwani ido ta xuba masa, bata ma taba tunanin yaji hausa haka ba, shi kuma waye ina ruwanshi da soyayyarta da el'mustapha, ko dai sonta yake yi yaxo ya rabata da el'mustapha dan ya aure ta idan kuwa hakane xata amince da..... Ya katse mata tunani yana fadin daina kallona haka, ashe baki da kunya idan har xaki tsaya kina kallon tsakiyar idanuna. 2

Uwani tayi saurin sunkuyar da kanta qasa xuciyarta na bugawa kamar ta fashe da kuka take ji.

Ikram tace amma naji dadin wannan abin dan baxan iya xama da wannan yarinyar ba xan karya mata qafafuwa, da axo ana aikin dana sani gwanda tabar gidannan inma gidanka xata je ta xauna wannan tsakanin ka ne da jiddah ba ruwana.

Dr merah yace daga nan gidan ubanta xata je ko jiddah baxata gani ba, ki fito da naki mijin kixo ni xan maki aure in kuma baki dashi ina da wani dogari nawa dake neman matar aure matarshi ta rasu sai na hada ku ai ba wani abu bane, amma ke bakya jin kunya ki dawo kina son mijin jiddah?

Jiddah da kika so kashewa ki rabata da duniya saboda mijinta da ta rufa maki asiri ta baki kika aura, kika sa aka nakasa mata qafa, duk bakya jin nauyi da kunyarta a yanxu, kin manta da wannan, shi wannan mijin naki da kike son koma masa jinin sa fa kika so kashewa a gaban mahaifiyarsa, kinsan xafi da radadin da uwa keji a xuciyarta a duk lokacin da wani abu ya sami dan cikin ta, idan har bakyason jinin el'mustapha qarya kike kice kina sonsa.

Inaji jiddah tare aka raineku kuka taso cikin gida daya qarqashin iyaye daya ta riqe ki da amana tana xaune dake da xuciya daya amma kika iya mata wannan ballantana el'mustapha da baki hada komai dashi ba, kenan shima idan ya bata maki rai watarana xaki iya saka a kashe shi.

Kuma saboda Allah dan baki da kunya da imani ki dawo kina son mijinta, hala ita bata da xuciya a jikine ko an gayamaki dutse ce bata son mijinta, kinxo kina saka damuwa a tsakanin su kina son raba mata da miji kina so ki raba farin ciki da soyayya saboda wata buqata taki ta banxa, to baxaki aure sa ba, kuma el'mustapha baxai aure ki ba.

Duk abinda kika ga kin ma iyayenki sun xuba maki ido kina ganin kamar sun kyaleki ne to akwai wannan baqin cikin a xuciyarsu naki wanda ko basu fito sun gayamaki ba yana damun su a xuciya saboda ke jinin su ba yanda xasu iya dake, dan haka kije ki nemesu gafara ki kuma je ki nemi gafarar jiddah, domin mace ce mai haquri, da ace kin tsaya kin nutsu tun farko wallahi xaki ji dadin xama da ita kuma el'mustapha har yanxu yana mijinki, amma kinyi sake da wannan damar kuma baxaki taba samun sa ba.

Kuka sosai uwani keyi tamkar ranta, sam bata da nutsuwa a tare da ita, hankalinta ya tashi sosai tana ji tana gani anti ikram taje ta fito da kayanta.

Suka fito da ita, sai ga yusuf qanin mijin anty ikram,

'Yauwa yusuf xo ka kai uwani gida,

Yace aa anty ikram ina da wani uxuri baxan iya xuwa har wani gari yanxu ba ki hadata da driver, ya gaisa dasu merah yayi ciki abinsa,

Uwani ta bisa da kallo. 3

Merah ya dubi el'mustapha kai kuma muje gida inda qanwata nayi maka hukunci a gabanta in ta kama ta dake ka da kanta....Uwani ta tsurawa yusuf ido cikin mamaki, yusuf din ta ne fa, yusuf din da qawarta surry tayi snatching ta aura, ashe qanin mijin anty ikram ne amma bai taba gayamata shiyasa tayi mamakin yanda akayi jiddah tasan yusuf, bai gane ta bane kome? +

Tayi saurin shan gabansa tana kallonsa,

Haba yusuf baka gane ni ba, nice fa uwani masoyiyar ka ko ka manta, dan Allah kayi haquri ka yafe min, ni dama kai nake so wlhy. 7

Duk gurin suka xuba masu idanu,

Merah yace wannan bata san wanda take so ba kenan, Mijin qanwata shiga mota muje kafin mai martaba ya ankara da bana gidan.

Suka ma anti ikram sallama suka fice,

Yusuf ya dube ta, idan yace baya son uwani ya yaudari xuciyarsa, cos itace first love din sa, sun fara soyayya da ita a skul har jiddah tasan da soyayyar su amma bai taba gayawa anty ikram a lokacin ba saboda yasan yanda basu qaunar yarinyar, uwani ta cuce sa ta guje sa saboda el'mustapha shine yau take dawo masa saboda auren ta ya mutu, yaja dogon tsaki cikin takaici ya raba ta gefenta yayi shigewar sa.

'Anty ikram ta shige tana fadin idan kin tashi ga driver nan ya kaiki in kuma xaki tsaya kwadayin maxa ne to, tunda ke kowa ma so kike, banxa tayi shigewarta. 1

A sanyaye uwani ta shiga motar jikinta ba kwari, haka take jin wata nadama na ratsa xuciya da gangar jikinta, sau biyu tana samun dama tana kubce mata, meyasa hakan, tabbas harda haqqin iyayenta. 
6

Tasan bata cancanci jiddah ta yafe mata ba, ta aikata babban kuskure a rayuwarta, inama hannu agogo xai dawo baya da ta canxa rayuwarta da xamantakewar xamanta da jiddah, amma ta sani a yanxu abu ne mai wuya jiddah ta qara yarda da ita, lallai el'mustapha ya mata nisa kuma baxata taba samun irin sa ba. 1

Sanda suka iso gida driver yana ajiyeta ya juya, ta dauki kayanta ta shiga cikin gida,

Kuka take sosai sanda tayi toxali da iyayen nata xaune a falo,

Ta xauna tana kallonsu, hajiya da abba ku yafe min, nidai naga ta kaina ko yanxu naga rayuwa kowa baya sona a duniyar nan kowa baqin ciki yake min, suna ta cewa na canxa halina, ya xanyi na canxa abba.

Duk suka mata shiru musamman ma hajiya da har yanxu bata huce haushin ta ba, 4

Uwani ta cigaba da fadin, shine suka kirani naje aka hadani da wani bature dan baqin ciki wai el'mustapha baxai aure ni ba sai dai ya hada ni da dogarin sa kuma shima din idan aka bincika sona yake kawai dai yana min baqin ciki ne. 1

Ta matso kadan kusa da abba,

'Dan Allah abba ku yafe min ko naga haske a rayuwata, duk nasa buri a abu baya kasancewa sai dai ya lalace, bana ganin haske a duk al'amari na, ni na gane harda haqqin ku dana anty jiddah, ku yafe min abba.

Hajiya dai bata ce komai ba, abba yace Allah ya shiryaki yasa kigane abinda kike kina quntatawa iyayenki.

Uwani ta dubi hajiya tana fadin, hajiya kinyi shiru har yanxu kina min baqi..... bata qarasa ba taji saukar Mari a kuncin ta, 3

'Ashe baki da mutunci ban sani ba cewar abba yana kallonta a fusacce, iskancin ya kai har ki kalli mahaifiyar ki kice tana maki baqin ciki, baqin ciki yafi duk wanda ta kawo ki duniyar kika bijire mata, ya janyo wayar cable a fusacce,

Uwani na ganin haka ta soma roqonsa tana bashi haquri, abba ya soma dukanta yana fadin, dama ba na barki bane jira nake har mahaifiyar ki ta dawo na yanke maki hukunci a gabanta akan rashin kunyar da kike ma mutane tuni na gane iskancine ke damunki, anci kudina kawai a asibiti ba wata lalura dake kanki. 2

Ya soma dukanta sosai baji ba gani, hajiya na xaune har wani sanyi take ji yau anyi mata maganin uwani.

Gskyr abba abin na uwani iskancine tunda har tasan ta rufe bakinta da hannun kada ta fadi abin da xai qara tunxurasa,

STORY CONTINUES BELOW


Banda gurnanin kukan ta ba abinda kake ji a falon,

Hajiya tashi ma tayi ta bar falon, abba kuwa sai da ya gaji dan karan kansa, lokacin uwani ko kwakkwaron motsi ta kasa yi, kukan ta kuwa har qofar gate ana jiyo ihun ta, duk jikinta yayi tsamin duka, tana kwance tana maida numfashi.

*

Yanda suka bar jiddah haka suka dawo suka same ta xaune a falon, wannan karon arham na kwance a jikinta yana cin pringles din sa.

Merah ya xauna yana kallon el'mustapha, wannan hannun da kake maqalewa haka meya same sa,

El'mustapha yace qanwar kace ta min wannan raunin wajen kishi.

Amma fa ta kyauta, muga hannun, El'mustapha yaqi bada hannun yana fadin an riga an duba min kabarshi hakan.

Ya dubi jiddah yana fadin very soon Afiya da Rumaisa xasu shigo Abuja biki, idan sunxo El'mustapha please take her to them, olready xan masu mgn akanta xasu kaita inda ammi da mai martaba,

Idan yaqi, ki kirani jiddah serious baxaka ji dadi na ba,

El'mustapha yace to yayan jiddah sai me kuma,

Sai maganar wannan yarinyar kuma, ba dan na isa ba amma ina roqon ka, ka fita hanyar yarinyar tun da ba auren ta xaka yi ba, inma taimaka mata xakayi jiddah should be the first person da xaka fara gayawa, idan bata amince ba ka barta in kuma ta amince mai sauqi ne, she is your wife, your life partner, share your secret with her nasan tana da sauqin kai xata fahimce ka.

Jiddah idan ta xauna da Afiya ta gayamata wasu sirruka believe sai ka raina kanka, ni kaina mulkina da sarauta ta a waje take kawai amma da xaran na shiga gida munyi two eyes da Afiya to itace sarkin, sai kayi mamaki duk ranar da ka ganmu tare.

El'mustapha ya tabe bakinsa baice komai ba,

Jiddah kema You have to be respectful to your husband, duk abinda yayi maki ku xauna ku fahimci juna, idan shine bashi da gaskiya you let him know ba sai wani ya ji a waje ba sirrin ku ne, idan kuma kece baki da gaskiya kiyi gaggawar bashi haquri, mijin kine, aljannar ki tana gurin sa, kiyi masa biyayya, idan ya bada haquri ayi haqurin dan xama yayi dadi, na tuna sanda mai martaba ya aura min Afiya ba abinda yake ce min a koda yaushe, na riqe ta hannu biyu, nayi haquri, nayi haquri, ban gane haqurin da yake mgn ba sai bayan tafiyar Afiya wanda a lokacin ganewar bata da amfani a gurina.

Ki daina rufe kanki a daki, akwai irin fushin da mace ke yiwa namiji wanda ke daga hankalinsa ya kuma ruda sa ba sai ta hanyar rufe qofa kawai ba, domin xaki iya cutar da kanki a ciki baki sani ba.

So, on behalf of El'mustapha ina bada haquri, a yafe masa kuskuren da yayi baxai qara ba, please qanwar merah.

Murmushi tayi ta sunkuyar da kanta qasa batare da tayi magana ba,

Kai kuma idan ka qara maimaita irin wannan xan dauke kane na kaiwa mai martaba, ni naga kamar ma jiddan bata haqura ba, in kuwa haka ne gaskiya dundu xan tayi maka har sai ta bude baki tace ta haqura.

Dariya ta subulcewa El'mustapha yana kallonsa,

Yace jikin mu ba daya ba, sai dai kajiwa hannunka ciwo.

Dr merah ya tashi cikin wasa yana fadin bari a gwada a gani, idan na fara baxan bari ba har sai jiddah tace ta haqura.

El'mustapha yace to shikenan indai akan jiddah ne xan jure komai idan har xata saki fuska ta daina fushi dani.

Ganin fa da gaske merah  dukan el'mustapha xaiyi a baya, tayi caraf tace,

Yayan mu ai na haqura fa,

Cikin dariya yace ai da kin barni nayi masa ko daya ne, ashe dai kina son sa haka.

Merah bai bar gidan ba sai da yaga ma'auratan sun saki jiki da junan su sosai kamar ba abinda ya hada su, har jiddah tayi masa abubuwa sosai naci sai murna yake domin wani abin ma bai san dashi ba, ya saki jiki sosai dasu kamar daman sun saba da juna,

Sanda xai tafi el'mustapha tsadaddiyar shadda guda biyu ya bashi ya kaiwa mai martaba, sosai merah ya nuna farin cikin sa yayi masa godia.

Har merah ya shiga mota el'mustapha ya sunkuya yana kallonsa da murmushi,

Karka manta idan har kana son twins ka dage, kace Afiya ta dage nothing worth comes easy mu ma sai da muka dage,

Merah dariya yayi yana fadin, xan baka mamaki kuwa, triplet xamuyi nida Afiya insha Allah.

Allah ya kawo masu albarka cewar el'mustapha,

Ameen merah ya amsa cikin murmushi,

Shiru el'mustapha yayi yana kallon yanda merah ya hade fuska tun bayan fitowarsa inda masu tsaronsa, kamar bashi bane suke dariya dashi a daxu, ya daga masa hannu sanda suka fice. 2

Yana shiga falon ya rungume jiddah sosai yana sauke numfashi,

For only yesterday jiddah, kinsan yanda naji?

Ta janye jikinta tana murmushi,

Arham is watching us,

Ya juya yana kallon arham, yaron kuwa yayi masu qur da ido kamar na Serdia. 1

El'mustapha ya nufe sa yana fadin, I hug mum let me hug my arham too,

Arham ya soma dariya sosai lokacin da el'mustapha ya cira sa sama,

Daddy saura aryan shima,

Yace baya nan sai ya dawo tukunna,

Airah fa, arham ya fada yana kallonsa.

El'mustapha ya xauna yana fadin tana barci sai ta tashi.

Yaran xamani kenan duk abinda kake idanun su yana kanka, iyaye sai an dage an kauda ido.

*


A gurguje😏Acikin wata biyu abubuwa sun gudana ko ince sun faru, ciki kuwa harda engagement din uwani, ku tambayeni da waye, baxa kuji a bakina ynxu ba🏃🏻‍♀ 4

Amma fa ba laifi tun dukan da abba yayi mata abubuwa sun ragu sosai daga uwani, kullum abba yana hukuntata, acikin gidan komai ita keyi ya sallami mai aikin su, ta dawo wata iri sai kunyi mamaki duk da ba duka aka nutsu ba akwai dan rawar kai tukunna.

Haka ya dauke ta ya kaita islamiya ya hada ta da wani malami duk ranar da bata je ba ko tayi wani abin Allah wadarai acikin makarantar ya mata duka sosai kada yayi Dublin girmanta,

Uwani bata dauki xancen da gaske ba sai ranar da tayi fada da wata a aji akan biro kuma itace beta da gaskiya saboda anqi aramata ta karbi biron  ta karya tana fadin idan akwai uban da ya tsaya maki yaxo yace na biya.

Aikuwa a ranar ta daku, ko da taje gida tana kuka ba wanda ya kula ta illa girki da aka ce ta dora. 1

Tun daga lokacin take tsoron ta nemi wani da fada, kuma ganin yanda yake takura mata akan karatunta ya saka ta maida hankali,

Dalilin haka abba har kyauta yayiwa malamin domin ya qara jin dadin kula masa da uwani.

Bari mu leqa amaryar mu banan😊

Banan anyi kyau ta kwantar da hankalin ta sosai ta rungumi mijinta da hannu biyu, kulawa da soyayyar da take masa bata son ko kadan mace ta rabe sa.

Shi kansa yaji dadi sosai samun soyayyar banan, tana da hali mai kyau kuma tana da biyayya akan duk abinda ya umurceta dashi, bugu da qari tana girmama yan uwansa sosai, ya yarda banan rainon jiddah ce kuma yana roqon Allah yasa ta dore a hakan.

Akai akai take xiyarta jiddah, ita ma jiddah tana xuwa ba laifi, suna xumunci sosai duk abinda ya shige mata duhu tana gayawa jiddah ta wayar mata da kai.

Waye wannan mijin uwani🤔

Post a Comment for "EL-MUSTAPHA CHAPTER 10"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...