Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

DAN ADAM CHAPTER 7

DAN ADAM CHAPTER 7

- - Post a Comment
DAN ADAM CHAPTER 7
Saude ta bata hannu suka cafke kafin ta k'ara gyara zamanta akan kujerarta wadanda ta siya a sakan tana musu kallon masu kyau adalilin a baya bata mallakesu ba. Habiba ta zauna sharab akan kujera tana k'ara washe hak'ora. "Wallahi duk sadda na ganki kina watayawa bakiji yanda nakejin dad'i a raina ba, kai duniya." Wata dariya Saude ta saki. "Bari kawai Habiba, a duniya banajin inada aminiyar da ta kaiki, karki tona zuciyata kiga tarin kaunar da ke dank'are aciki tamkar wata yar uwata ta jini, ke kin fiyemin dayawa cikin 'yan uwannawa ma wallahi." Habiba har lokacin bakinta ya gaza rufuwa. "Burinmu kenan, yanzu don Allah ya kikaga ranar wannan shegiyar? Ai matukar za ki cigaba da bin shawarata za kiyita ganin aiki da cikawa." Saude ta lumshe ido ta budesu tsabar dad'in da zantukan Habiba sukayi mata. "Tabbas nagani, yanzu fa Balarabe ba shi da kata6us a rayuwa, komai nashi nike iko da shi, hatta da kadarorin da ya gada na iyayensa, yanzu sun dawo mallakina. Bakiga yanda k'aramin albashin wannan Shegiyar na farko ya juyemin zuwa babban jari na siye da siyarwa ba? Ai har abada ke mai kaunata ce Habiba, shiyasa na damu da damuwarki." "Ga kuma k'iyayyar da kika jazamata a dangin Mahaifiyartata." Cewar Habiba kenan suka feshe da dariya har suna fidda ruwan hawaye. Saude ta nunata da yatsa. "Maakira." "Ban kaiki ba." Habiba ta amsa mata.+ Sai kuma Saude ta koma kalar damuwa. "Yanzu Habiba babbar damuwata bai wuce na ranar da Boka yace mu kiyayi zuwansa ba, ranar da Balarabe zaiyi tozali da Ummi." Habiba ta harareta. "Wa zai bar wannan ranar ta zo aka gayamaki? Har abada bazamu kyale ba, wannan bari sai Yaha ta dawo daga Kaduna, ita zatasan tuggun da zata shirya duk lokacin da bukatar zuwa ganin gidan Ummin ya taso." Saude ta jinjina kai cike da gamsuwa daga haka suka rufe babin Ummi suka koma na Dija inda take bata labarin maganin da ta samo mata. "Hakan ma yayi, Allah dai Yasa a dace. Ni kaina rashin namiji tsayayye ga Dije yana ta6an zuciya. Allah Ya had'ata da mai mota." Habiba ta dara cike da jin dadin wannan kyakkyawar addu'ar da ya fito daga bakin aminiyar kwarai. "Amin." Nan suka shantake suna hira, can sai ga Mariya d'iyarta mai shekaru bakwai ta shigo hannunta rik'e da kud'i. Da gudu ta k'arasa ga Habiba tana dariya. "Lah, Baba yaushe kika zo?" Habiba ta rungumeta tana dariya. "Yar Baba, ban dad'e ba. Mene wannan a hannunki kamar d'ari biyar?" Mariya ta kwakume kudinta tana dariya. Ganin haka yasa Saude rik'ota. "Waye ya baki kud'i auta?" Ta mik'awa uwarta. "Usi mai kanti ne fa ya bani, wai na kawomiki ki sakamin a bankin gwangwani." Ta kar6a tana washe baki. "Kai madallah, Usman ba dai kyauta ba, ince dai kin mishi godiya?" Habiba ta gutsiri goro ta soma tauna. "Haka yaronnan ya ke ai, ba dai kyauta ba." Daga nan suka cigaba da hira kafin daga bisani suyi sallama.3 *** *** *** BAYAN SATI BIYU Rai a matukar'ar 6ace ta ke dubanta, duban da ba k'aramin kad'a 'yan hanjinta ya yi ba. Ta daure ta numfasa, cikin dakiya ta russuna. "Ina wuni Umma." Maimakon ta amsa, sai ta nunata da yatsa, da kakkausar murya ta soma magana. "Kar ki ce za ki ci amanata har haka! Kinyi kad'an ba ki isa ba wallahi!" Cikin rawar murya ta soma magana. "Me..me..nayi Umm.." Bata kai ga k'arasawa ba, ta sanya hannu ta d'auketa da mari wanda har ta daina ji na wasu 'yan dak'i k'u. Maganarta ce ta maidota hayyacinta babu shiri. "Ya kikayimin aikin da na sanyaki?". Gaban Ummi ya fad'i. Ta had'iyi wani miyau dakyar tana duban ofishin mai kula da makarantartasu inda anan ne Hajiya Binta ta zo ta sameta har Malamin ya basu wuri suyi magana bayan an jik'ashi da kud'i. Babu dai alamar akwai wanda zai kawomata d'auki, dole ta maido dubanta gareta idanuwanta na zubda ruwan hawaye, dakyar ta iya magana. "Nayi yanda kikace bayan nayi bismillah." Hannu Hajiya Binta ta d'ora a ka tana buga salati. Kin kasheni Ummi! Uban wa yace kiyi bismillah? Akan wane dalili zaki karyamin dokar..." Sai kuma tayi shiru don tsabar takaici da tsananin 6acin rai har idanunta sun ciko da ruwan hawaye, ita kad'ai tasan irin wuyar da ta ci kafin samun magani garanti wanda aka tabbatar zaiyi aiki sosai akan Hajiya Madina, har bokan ya tabbatar mata cewar matukar'ar bata ga aiki da cikawa ba, toh ta dawo ta kar6i kud'inta. A dokokin saida ya tabbatar cewar a kiyaye ambaton Allah. (Wa'iyazubillah). Mik'ewa tayi jiki babu kwari ta watsawa Ummi wani mugun kallo tayi kwafa sannan ta fice a zuciye. Bayan tafiyarta Malamin makarantar ya dawo, da sauri Ummi ta mik'e ta fice, saida ta zagaya bakin famfo ta ci kukanta ta kuma godewa Allah da Ya kimtsa mata wannan dabarar sannan ta wanke fuskarta ta bar wajen zuwa aji. Salma wacce ta kasance k'awarta kuma abokiyar shawararta ta dubeta. "Lafiya dai Ummi?" Ummi ta k'ak'alo murmushi. "Bakomai." Salma ta girgiza kai. "Ina mamakin wannan amincin namu, sai nake ganin tamkar ba ki daukeni komai ba." Ummi ta girgiza kai. "Kiyi hakuri Salma, wani abin ba ya bukatar magana. Kedai ki tayani addu'a. Kada kiyi kokwanto akan yacce nake ganinki, Allah ne Ya had'a zumuntarmu." Salma ta murmusa. "Shikenan, Allah Ya yayemana dukkan matsalolinmu." "Amin." Ummi ta fad'a sannan suka bar magana sakamakon karatun da aka soma. Tun zuwan Ummi makarantar bata shiga harkar kowa, daga baya ne suka saba da Salma d'iya ga d'aya daga cikin malaman makarantar, Malama Zainab. Tun bata bayarda fuska, har dai ta dan sakarmata suka saba ganin da ta yi nutsastsiya ce. Haka ranar suka tashi jikinta duk babu kwari. Tana zuwa gida ta soma kici6us da Ramma a tsakar gida. "Au, kinga 'yar halak d'inma, to ki shiga ku gaisa da Yaha." Gabanta ya fad'i. "Yaha?" "Eh, wacce dai kikasani." Ramma ta bata amsa wanda ya sa ta fahimci maganarta ta fito fili. Ta saki murmushin yak'e, ta tabbatar zuwan na kar6ar kud'in watanta ne ba wai na bincikar lafiyarta ba. Allah Sarki, shiyasa ta ke tausayin kanta, tana tsoron ranar da Mami zata soma gajiyawa da ita ta korata, ita kam wa zata runguma? Ta ja kafafunta wadanda suka k'ara yin sanyi ta k'arasa cikin falon da sallamarta. Yaha ta amsa tana daga zaune saman kafet yayinda Ihsan ke zaune ko kayan makarantar islamiyya bata cire ba tana danne-dannen waya. Fahad kuwa ya cire daga shi sai singilet da short yana kallon (cartoon). Ta washewa Ummi hak'ora cike da mamakin yanda ta chanja. 'Shegiya, birnin ya kar6eta.' Ta fad'a a ranta. Ummi ta k'arasa ta gaisheta tana mai k'ok'arin sakin fuskarta bayan ta kauda kanta daga duban Ihsan wacce ke jifanta da murmushin rainin hankali da k'ara kallonta a ba komai ba. "Ashe kinzo, sannu, ina wuni."1 "Yauwa Ummi, lafiya lau. Oh! Haka kika bi kika chanja? Eh lallai." Ta karashe tana k'aremata kallo gami da d'an ta6e baki. Murmushi kawai Ummi tayi. "Ai dole ta chanja, cimar ai ba d'aya ba. Anan ai akuyar d'aure ta samu sake." Muryar Ihsan suka tsinta ta tsomo musu baki. "What the hell is this?" Daga baya aka bata amsa. Suka dubi mai shi, Adnan ne wanda ya fito daga d'akinsa daga shi sai dogon wandon makaranta da singilet. Yana watsawa Ihsan wani kallo mai nuni da lallai bai ji dadin maganarta ba. Ihsan ta had'e gira gami da d'aga kafad'a mai nuni da ko ajikinta ta cigaba da danne-dannenta tana dariyar rainin hankali. Yaha kuwa ta bata amsa. "Ai fa, da gaskiyarki 'yar Mami." Ummi ta mik'e. "Bari na chanja kaya." "Muje toh." Suka d'unguma da Yaha zuwa ciki, duk kokarinta saita hawaye ya zubomata ta daukesu da hannunta, wannan cin zarafi ya soma yawa, amma bakomai, tana ji a jikinta komai zaizo k'arshe in sha Allah.1 Tana chanja kaya, Yaha kuwa na tsaye tana k'arewa d'akin da ita kanta kallo. Dakin yana ayanda ta ta6a ganinsa saidai suturar Ummi take kallo duk ta chanja. Baki ta ta6e. "Oh'oh, hum, da gaskiyar Ihsan. Wannan irin samun sake? Yaushe aka sanyaki a makarantar?" Ummi cikin dakiya ta amsa. "An kwan biyu." "Lallai, amma bakomai tunda kina abinda ya dace, har kud'i Hajiya ta k'ara na aikinki. Kinga nan dubu shida, ta bani dubu uku. Idan naje zan damk'awa uwarki." Ummi ta amsa da to kawai, daman batasa ran za'a bata komai ba. "Ina su Baba?" Yaha ta harareta. "Kalau suke, da dai kin bar saka kanki a layin 'yan gidan Balarabe, bana tunanin ma wani cikinsu yana tunaki." Ummi ta jinjina kai tayi 'yar dariya na dole. "Bazan bar tuna shi ba, ko ba komai shi ne ya haifeni." "To 'yar makaranta. Bari na rage mara dai." Bayan shigarta bandaki, kuka sosai Ummi ta yi, dakyar ta rarrashi kanta. Saida akayi Magriba sannan Yaha ta shirya tafiya, har titi ta rakata, tafiyar bata dad'i ba don kuwa magana take gaggasamata wai ita ko 'yar satar nan ma batayi don a samu a tara na aurenta cikin sauri, har suka rabu batayi mata hud'ubar arziki ba. Ummi dai ta gama tabbatarwa a duk duniya babu wani dan uwanta na jini mai kaunarta. Ko a hanyarta ta komawa gida tana tafe ne tana hawaye saids ta iso daf da gidan sannan ta gyara fuskarta. A farfajiyar gidan suka had'u da Adnan, ta dauke kai zata shige yayi azamar shan gabanta. Ta dubeshi tana dan murmushi. "Lafiya?" "Sorry." Ya fada cikin sassanyar murya harda rik'e kunne. Abin sai ya bata dariya, ta dara. "Me kayimin?" Ya gyara tsayuwa. "Banyimiki ba amma Ihsan ta miki." Ta girgiza kai. "Ayya, ni ya wuce. Kuma ai gaskiya ta fad'a." Ya daure fuska. "Ba gaskiya bace. Karki k'ara daukar hakan amatsayin gaskiya. Ga idanunki sun nuna alamun ma kin koka. Kiyi hakuri Ummi." Ya burgeta, yasan darajar DAN ADAM. Ta numfasa hakoranta a bayyane tana murmushi har zuciyarta. "Ya wuce." Ya dara. "Yauwa kokefa, keep smiling always." Daga haka ya juya ya tafi, me yake nufi? Oho, bata da masaniyar fassarar turancinsa, amma duk da haka ya burgeta. Ta girgiza kai ta shige ciki itama.1 *** *** *** UMARUL FARUK DANZAKI Kwance yake saman doguwar kujera dake a tsararren falon mahaifiyarsu. Idanunsa a lumshe kai ka rantse bacci ya ke, a can d'aya 6angaren na falon kuwa wanda nan ma komai ya ji, Hajiya Babba ce da bak'uwarta suna lissafin kayayyaki. Rabin hankalinsa na garesu, rabin kuwa kan jefashi duniyar tunani wanda kokusa baya kaunar hakan. Ya ja guntun tsaki gami da mik'ewa zaune, wayarsa ya d'auka ya bud'e (data), nan take sak'onni suka shiga tururuwar shigowa wayarsa, duk daga (Whatsapp). Ba sabon abu ne awajensa ba, yana da tabbacin kusan maza abokan aikinsa da yan uwansa sunfi yawa, mata masu turomasa sak'o k'alilan ne don bai basu damar mallakar lambarsa ba, saidai har mamaki yakeyi na yacce mafi yawa na 'yanmatan suka samu. Babban dalilin kenan da ya yiwa kannensa gargad'i akan kada su yarda su k'ara bawa kowace yarinya lambarsa. Sun ji gargad'in kuwa don sun kiyaye.+ Kai tsaye ya soma bud'e sak'onnin yana karantawa. Ga mamakinsa ya tsinceshi a wani group na Zumunta. Koda ya shiga yan uwansu ne burtik, mata da matasan. A sunayen (Admins) ya hangi wacce ta tsundumoshi ciki. "Iklima?" Ya fad'a a fili fuskarsa cike da mamaki, ya koma cikin group inda ya ji tana mishi marhabin da shigowa. Ayayinda wani dan baffansu dake Adamawa ya sanyo alamun dariya. Guntun tsaki ya ja gami da ficewa batare da yace uffan ba. Yana fita kuwa suka hau kyakyata mata dariya harda masu turo sak'on murya wanda hakan ba k'aramin k'ular da ita ya yi ba. Daman sun san halinsa, ba yau ya soma arcewa daga groups ba, da dai zaka mishi magana ta akwatin sirri, anan kam zai iya baka amsa, harma idan ka ci sa'arsa kuyi hira mai tsayi da dariya. "To sai anjimanku." Muryar Bak'uwar Hajiyarsa ce ya katseshi daga danne-dannen da ya ke a waya. Ya dubeta ya gyad'a kai cikin dan murmushi ya amsa "Allah Ya kiyaye hanya." Daga haka ta yi gaba tana mai amsawa da Amin. Mik'ewa ya yi ya koma wajen da Hajiyarsa ke zaune. Ta maida lesussukan gabanta gefe ta dubeshi fuskarta dauke da murmushi. "Miskili kafi mahaukaci ban haushi, Sadauki nawa ya akayi ne?" Ya d'an turo baki kamar mace, abin ya bawa Hajiya dariya ta girgiza kai. "To shagwa6arce ta motsa?" Ya shafi sumarsa yana 'yar dariya, itama tana tayashi, aduk yaranta tafi so da tausayinsa kasancewarshi mutum marar son hayaniya ga kuma hak'uri da rauni. Kullum addu'arta bai wuce na Allah Ya had'ashi da mace ta gari ba, ba wacce zatayi amfani da rauninsa da hakurinsa ta cuceshi ba. Ya katse tunaninta ta hanyar sanarmata batun group da aka sanyashi ya fice. Da murmushi dauke saman fuskarta tace. "Toh banda abinka Sadaukina, ai k'ara dank'on zumunta ne, ina zaka so ku had'u da d'an uwanka a hanya ayi abin kunya ba ka san da zamansa ba? Kaga mu ma duk muna da group na zumunci, na yan Adamawa daban, namu na dangin mahaifinku daban." Ya dauki filo ya sanya agefenta ya kwanta yana mai juya mata baya. Ya lumshe ido. "Hajiya duk wannan takura rayuwa ce, nafi ganewa mu gaisa ta private ko kuma na kira mutum ko ya kirani. Surutu ne zalla sukeyi." Ta dafa kansa. "Zumuncin kenan Sadauki, wani ma hakan ya nema ya rasa. Wasu na can basu da dangin ma da zasuyi musu hakan." Bud'e idanu ya yi, tabbas Hajiya ta fad'i gaskiya, babu wacce ya tuna sai Ummi. Yana ji ajikinsa, akwai wani babban lamari a rayuwarta, har yau ya kasa cire kwad'ayi akan sanin tak'amaiman tarihinta. "Hakane Hajiya." Daga haka ya basar da zancen. "Wai yaushe yarannan zasu dawo?" "Af, su Baraka ai ansamu gidan zuwa, suna can nasan suna zuba da Intisar." Ya girgiza kai gami da ta6e baki. "Ai Yaya Haidar shi ya barsu." Hajiya ta rik'e ha6a. "Au kai kace babu mai zuwa gidanka?" Ya mik'e zaune ya rungume filon yana dariya kad'an-kad'an. "Bance ba, amma kada a yawaita." "Eh lallai Sadaukina, ga shi har yau ni banga surukar tawa ba, Alhajinku ma na fama." Ya yamutsa fuska. "Ni wai..." Sai kuma ya yi shiru gami da mik'ewa da daukar wayarsa. "Aifa, daga ansoma maganar gaskiya saika gudu." Ya yi murmushi mai bayyana hak'ora. "Kai Hajiyata, ya dace dai ku d'an huta, ga na Baraka nan fa tafe, abin sai ya yi muku yawa." Hajiya ta harareshi. "Wane irin yawa? Ai hutunmu yana bayan aurar da ku lafiya." Ya gyada kai. "Hakane, bari na d'an fita." Ya fice da sauri kada ta cigaba da magana d'aya wanda shi amsarsa har zuwa lokacin bai wuce A'a ba, don kuwa ba zaice ya ta6a soyayya ba balle har ya ji yana son auren wata mace.

Post a Comment for "DAN ADAM CHAPTER 7"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...