Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

DAN ADAM CHAPTER 5

DAN ADAM CHAPTER 5

- - Post a Comment
DAN ADAM CHAPTER 5
Ta sauke ajiyar zuciya, gami da zame jiki ta durkusa a wajen. Yau Faruk ne yayi mata murmushi? Sai tace tun zuwansu bata ta6a ganinsa cikin fara'a haka ba. Mai yiwuwa saboda farincikin bikin dan uwansa ne. Jin da tayi ana ihu da shewa daga falon ne yasa ta saurin mikewa itama ta samu dama dakyar tana lek'e. Turare ta gani wata tsohuwa cikin wadanda suka zo daga Adamawa tana ta fesawa Ango da Amarya. Masu hoto suna faman yi, Faruk na daga hannun kujera zaune agefen wata mace da bata fi shekaru ashirin da bakwai ba, wacce itama cikin bak'in Adamawa take. Sai hira sukeyi suna dariya. Sunyi kama kwarai, kana gani ko ba'a fada ba kasan jini d'aya suke. Haka dai aka gama hotuna, Ango Haidar da tawagarsa suka fita. Wannan karon banda yayyun Haidar da Faruk, su kam zama sukayi ana gaisawa da hira da 'yan uwa. Tana ji anata yiwa Faruk tsiya akan shima ya dace yayi aure, abin banda dariya babu abinda yake ba shi, domin shi dai har kawowa wannan lokacin bai ga matar da ta kwanta mishi a rai ba har yakejin cewar zai iya aurenta. Duk cikin masu nuna masa kauna da so, duk cikin masu yi kishi tallar jikkunansu batare da sun buk'aci ko sisinsa ba, babu wacce ya ta6a yiwa kallon rahma. Asalima wannan d'abi'ar gaba daya haushi take ba shi wai ace mace ke tallatawa namiji kanta, yana daukar hakan a matsayin rashin aji da sanin darajar kai. Dakyar ya samu ya silale ya fito daga falon, Ummi ta bi bayansa da kallo sannan ta maida hankali ga tsoffin dake faman shige da fice suna rabon abinci. "Ummi." Ta ji muryar Amina a kanta. Wani sanyi ya mamayeta, ko babu komai zata samu abokiyar hira. Ta zaro ido tana murmushi. "Anti, kinga kuwa yanda kikayi kyau? Masha Allah." Ta harareta kadan "Lallai ma Ummin nan, wallahi ban kaiki ba, kinga yanda kikayi kyau kuwa yau?" Ummi ta girgiza kai. "Ban kaiki ba Anti." Amina ta dara gami da jan hannunta. "Taso mu zagaya baya, tun dazu ai ina can." Ummi ta mike suka zagaya. Babban fili ne mai shuke-shuke, nan dinma akwai mutane saidai ba kamar cikin gidan ba, kusan ma yanmata sunfi yawa anan. K'asan wata bishiya suka zauna asaman kujeru inda wasu yara biyu da Mace rike da yarinya wacce bata fi watanni uku ba suke zaune. Ummi ta hango kamannin matar sosai da Amina, hakan yasa ta gaisheta, cikin sakin fuska itama ta amsa. Amina ta dubi yaran. "Ahmad, ja Kulsum ku tafi wasa Antinku ta zauna." Ba musu yaron ya amsa sannan ya mike suka bar wurin, daman sun k'agu su tafi wasansu amma ta hanasu da cewar sai sun ci abinci. Bayan sun zauna Amina ta kalli 'yar uwarta wacce daga ita sai ita a haihuwa. "Anti Hauwa, wannan itace Ummi da nake baki labarinta. Ummi wannan itace yayata Anti Hauwa, daga ita sai ni a wajen Innarmu. Babbar yayarmu Anti Fiddausi tana Katsina, acan take aure. Yaranta biyu, da Kulsum da kuma wannan bebin, Anisa. Ahmad shine auta wajen Innarmu." Bayan ta kai aya, Anti Hauwa ta sanya dariya. "Toh 'yar jarida, oh Amina." Ta karashe tana kama ha6a, abin sai ya bawa Ummi da Amina dariya. Anti Hauwa ta dubi Ummi fara'arta ta k'aru don kuwa babu abinda Amina ta 6oyemata dangane da Ummi. "Sannu Ummi, fatan kina lafiya?" Ummi ta gyada kai gami da sakin kyakkyawan murmushinta. "Lafiya kalau Anti. Ya wajen su Inna?" Abin ya yiwa Anti Hauwa da Amina dadi. "Inna tana lafiya, taso ta zo amma matar kaninta bata ji dadi ba, ta je dubota. Watakil daga can tayo nan." Ta gyada kai gami da yi mata fatan samun lafiya. Nan kuma hira sosai ta 6arke tsakaninsu. Anti Hauwa da Amina suka gangaro kan batun Saurayin Aminan, Bello wanda ya matsa akan shi zai turo magabatansa. Anti Hauwa ta bata shawara akan ta sanarwa Inna idan yaso sai a had'ashi da wani ya rakashi har can Nijar su gaisa da yan uwan mahaifinsu. Haka suka tsayar da shawara. Sun wuni tare, Anti Hauwa sai bayan la'asar ta bar gidan, Hajiya Mama harda bata kudi tayi na mota. Dakyar ta kar6a don mutunci da karamci irin na Hajiya Mama har yana so yayi yawa, mace ce da babu ruwanta. Harda kayan rabo ta had'a ta bata, ta sanya aka yiwa Inna (takeaway) na abincin biki tace ta kai mata domin ba wani nisa ne tsakanin gidansu Inna da gidan Anti Hauwa ba. Ta kar6a da godiya. Tafe suke gaba dayansu da Anti Hauwa da Ummi da Amina, wadanda suka yo mata rakiya don ta samu abin hawa, kasancewar babu laifi akwai 'yar tazara tsakanin gidan da babban titi. Ummi na rike da Anisa wacce ke faman kalle-kalle idanunta tarr a bud'e. Yarinyar ta shiga ranta, haka kawai ta ji tana kaunarta ko don bata ta6a ganinta rik'e da yarinya k'arama haka bane? Oho. A farfajiyar gidan, samari ne da d'aid'aikun yanmata suna hira, daga ganinsu kaga yan uwan juna. Suka wucesu suka fita. Suna tafe suna hira a haka har suka iso titi, bayan sun samarmata d'an sahu, ta shiga sukayi sallama. Ta dubi Ummi da murmushi mai bayyana hakora a saman fuskarta. "Toh Ummi, sai na ganki a gidana wataran ko?" Ummi ta amsa da toh tana maida martanin murmushin. Suka juya tare da Amina suka kama hanyar komawa. A hanyar ma hira sukeyi, Amina na yi mata korafi akan ita ko dan fita unguwa bata tambayar Mami ne? Ummi ta ta6a baki kadan. "To Anti wa nake da shi a garinnan?" "Kina da mu, wataran ki tambayeta kizo na kaiki wajen Innarmu ku gaisa." Murmushi Ummi tayi wanda yayi daidai da giftawar wata farar honda mai bakin gilasai ta gabansu. "Wannan kamar motar gidan su Alhaji." Cewar Amina kenan. Ummi da batasani ba ta bi motar da kallo kawai wacce ta koma tafiya sannu-sannu tamkar matuk'in baya so. Kafin daga bisani ya fisgi motar ya k'ara gudu. Ai kuwa kamar yanda Amina ta fad'a haka dinne, don suna isa kofar gidan suka iske motar a fake, na cikin motar baikai ga fitowa ba saidai kafarsa d'aya da ya fiddo waje. Ta madubin hannun kofar, Ummi ta hangeshi. Kansa a jingine jikin kujera yana amsa waya. Akayi katari suka had'a ido, gani tayi ya yafito ta da hannu. Abin ya bata tsoro, gabanta ya hau dukan tara-tara. Tayi saurin dauke idanunta don bata gaskata hakan ba. Har zasu shige ciki ya danna hon. Wannan ya sanyasu dakatawa. "Da ku ake." Cewar Maigadi. Amina ta dubi motar, saidai bata hangi ko wanene ba sakamakon duhun gilashin. Suka zagaya suka isa ta mazaunin direba, idanunsa akansu, suka durkusa a ladabce suka gaisheshi. Yaya Faruk ya dago kanshi ya dubesu da idanunsa masu tafiya da dukkan wata diya mace mai lafiya da zata kalleshi. Ya gyad'a kai kafin ya maida dubansa cikin motar, hannu yasa ya janyo leda bak'a babba ya mik'awa Ummi. "Ki mik'awa Hajiyata." Ta sanya hannunta dake faman rawa don gaba daya wani kwarjini yayi gareta, ta kar6i ledar wanda bisa kuskure hannayensu suka gogi juna har ta gogi tattausan gashin dake kwance a hannunsa, a gigice ta dauke hannunta had'i da kar6ar ledar tana mai amsawa da toh wanda bai fito sarari ba saidai kawai le66anta da ya nuna alamun hakan. Baice uffan ba har suka fice ya bisu da kallo, ya lura yarinyar kamar a tsorace take da shi. Ya dan ta6e baki cike da mamaki, mamakin bai wuce na ganin yara kyawawa haka ba ace wai suna aikatau ba karatu ba, tabbas ya tausayamusu. Ya kuma raina iyayensu wadanda tunaninsa yafi ba shi cewar kwadayin abin duniya ne kawai yasa suke sakin yaransu sakaka suna yawon gidajen mutane don bauta da neman kudi wanda duk yawan abinda zasu samu bazai haura dubu goma ba, aganinsa wannan cutar da rayuwarsu ce kawai. Ya lumshe ido, ya jima a haka kafin ya maida kafafunsa ciki ya rufe kofar gami da yin ribas yabar unguwar. Acan kuwa Ummi kasa shiga ciki tayi haka kawai bata son shiga cikin mutanen gidan, tana jin nauyinsu. Amina ce ta kar6a ta mik'awa Hajiya Babba sannan suka koma inda suke. Sai misalin karfe bakwai kowa ya soma shirin tafiya wajen (Party) wanda Ango ya shirya na musamman da iyayensu da yanmata da samari. Abin har ya bawa Ummi mamaki, aganinta wannan kawai rashin sanin abinda za'ayi da kudin ne, ko kuma dai kudin ne suka yawaita garesu. Tana gani Amina tayi mata sallama suka wuce sakamakon yara da zata kula dasu a gida kafin dawowar Hajiya Maman. Ummi ta dubeta. "Nima na tabbatar yanzu zamu wuce ko don Ramma." "Wace Ramma? Ramma ai ta tafi gida tun dazu tare da su Hajiyar Iklima. Baki ga su Iklima sunzo dazu ba?" Ummi ta zaro ido. "Aa banma gansu ba wallahi, na tabbatar Mami ta manta ne da ta had'a tafiyata da su. Toh yanzu wa zan bi?" Amina ta jinjina kai. "Mamin ce zata barki ki tafi da kishiyoyinta? Wasa kike ma. Na..." "Ummi, kizo inji Mami." Suka tsinci muryar Fahad wanda yayi sanadin katse Amina daga maganarta. Ta dubeta. "To saida safe, nasan kuma mu da kara haduwa ba yanzu ba." Sukayi sallama Amina ta wuce. Ummi tana d'ari-d'ari haka ta daure ta shiga falon, Mami na daga zaune wata tana d'aura mata d'ankwali. Ta gaida mutanen falon sannan ta koma gefen Mami. "Gani Mami." Mami ta dan dubeta. "Ramma ta riga ta tafi, nikuma da wuya idan zan dawo ta nan gaskiya don gaba d'aya zamu tafi can wajen party, ki zauna a inda zan ganki idan mu fito." "Toh Mami." Daga haka tayi gaba, tana ji wata tana zolayar Mami wai da alama ita bata iya rayuwa saida 'yar aiki, har sauran suna dariya. Suna tsokanarta wai sai kace itace autar innartasu. Ummi ba haka taso ba, don alal hakika ita zuwa wajen wani party ko waje mai hayaniya baya burgeta, da ace Mami zata barta anan da ta zauna har zuwa lokacin da zasu ci su cinye su dawo su tafi. Ta dubi jikjnta bayan wucewar wasu yanmata da suka dauki ado cikin wani leshi yellow da nadin kai ja, ta yaya ma zata shiga taron jama'a da kayan nan? Ta tabbatar ita kadai zata bambanta acikinsu. Ta langa6ar da kanta, kodayake daman ita din ba kowa bace face 'yar aiki. Bata da wani daraja, babu wani wanda zai ra6eta da sunan kauna ta jini ta yan uwantaka, shiyasa take matukar kaunar Amina, ta tabbatar su Amina suna kaunarta saidai bata da sa'ar 'yan uwa. Batasan halin da suke ciki ba a yanzu, da ace ma zatasan dangin mahaifiyarta, lallai da ta kai kanta garesu komin nisan dake tsakaninsu. Ta sauke ajiyar zuciya kafin kuma da saurinta ta share hawayen da suka zubomata. Ko mintuna biyar batayi ba awajen, Mami ta aiko kiranta, kaya ta dunga kwasa tana kaiwa boot din motarsu, sannan ta zauna a motar tare da Fahad da wasu iyaye matan, Mami na fitowa suka wuce wajen party. Tun a farfajiyar otel din Ummi tayi bala'in raina kanta. Ta sauke ajiyar zuciya gami da sakin baki galala tana kallon yanda wajen ya k'ayatu, anyiwa wajen adon fulawoyi wadanda sai buso sanyi sukeyi, hakanan kuma wajen sai kamshi yakeyi. Daga can ciki kana jiyo tashin kid'a. Wadanda basu shiga ba suna tsaitsaye a farfajiyar wajen. Haka suka dunguma zuwa ciki. Sanyi ba bak'on Ummi bane don tun bata saba shan sa ba a falon Mami, har ya zamana yanzu ta saba. Wajen kowa ya dauki kwalliya. Matasa masu ji da ilimi da gayu sai kuma iyaye wadanda kallo daya zakayi musu ka tabbatar cewa kud'i sun riga sun gama jik'asu. Zugwui-zugwui take bin bayansu Mami, gaba dayanta a d'arare take, gani takeyi kamar kowa awajen ita ya zubawa ido. Idanunta suka cika da kwalla, bata saba da irin haka ba. Tunaninta ya katse sadda ta ji an damki hannunta. Ta juya da sauri, Ihsan ta gani ta ci ado har ta gaji da haduwa, saidai fuskarta a murtuke. Bata ce mata uffan ba ta soma janta, gaban Ummi na faduwa haka ta bi bayanta har zuwa d'an (Corridor) na shiga dakin taron. "Uban wa yace ki shigo? Kalleki kiganki, typical 'yar kauye, wallahi kika yi kuskuren shigowa wajennan sai na miki wulakancin da baki ta6a zato da tsammani ba. Shegiya kawai marar galihu!" Daga haka ta ja tsaki tayi gaba ganin mutane sun nufo hanyar shigowa. Ummi kuka ya taho mata, da saurinta ta juya zata fita, ta bawa mutanen hanya suka wuce ta bi ta gefe ta fita da gudu-gudu. Kai tsaye ta wuce bayan motoci inda babu mai ganinta ta durkushe ta soma kuka mai shiga rai. Kuka sosai takeyi, lallai ta k'ara gaskata cewar halayen DAN ADAM sun bambanta. Ta gaskata cewar ita din ba wata bace face marar galihun kamar yanda Ihsan ta jaddada mata. Kaiconta! Kaicon rayuwarta! Ace mahaifinka ya bude baki yayi furucin cewa ko bangon duniya za'a kaika, ba matsalarsa bace, baka da wani makusanci mai kaunarka, daga dangin mahaifin harma da shi kansa mahaifin. Takan rasa abinda ta yiwa mutane, wai meyasa dangin mahaifiyarta bazasu nemeta ba? Ta tabbatar koda duniya ta k'i ta, su bazasu ta6a gudunta ba, ta tabbatar zasu bambanta da sauran 'yan adam din da ta sani kuma ta rayu da su. Tana fatan su zamto irin Amina da su Anti Hauwa, tana fatan su zamto masu nunamata so da kauna ta gaskiya. K'arar rufe motar da ta ji ne yasa ta saurin mik'ewa a firgice. Ido hud'u sukayi, kallonta yake cike da tsantsar mamaki, yayinda ita kuwa take mishi kallo tamkar wacce ta ga wani dodo. Gaba d'aya tsoro takeji kada ya bud'emata wuta akan me takeyi anan. Ta sunkuyar da kanta tana duban motar, sai lokacin ta lura cewa motar da suka ganshi dazu a ciki ce. Kamar yayi mata magana, saidai ya fasa ya juya ya soma tafiya. Ta mike ta bar wajen ta soma tafiya kai tsaye ta nufi k'ofar fita daga Otel din. Kamar ance ya juyo, ya ganta. "Ke!" Ya fad'a a sannu yanda yasan zata ji don ba wani nisa tayi ba. Ta juya gabanta na fad'uwa. Sai lokacin ta lura da shigarsa, ya had'u karshen haduwa, a yanzun yana sanye da shadda ruwan kasa mai duhu wacce aka yiwa dinkin da ya zauna daidai a jikinsa. Takalmi da hular da ya dora ma su kansu abin a kalla a k'ara kalla ne. A haka har ta karasa wajensa ta durkusa. Ya bata umarnin ta mik'e. Bayan ta mike ya kare mata kallo sannan ya jefota da tambaya. "Ina zaki?" Ta soma rawar murya. "Gi..da." Ya yamutse fuska. "Ke kika kawo kanki?" Ta girgiza kai. "To shiga ciki." Tunanowa da maganar Ihsan yasa ta soma zubar hawaye ta dubeshi da jajayen idanunta wadanda kuka ya maidasu hakan, sai lokacin shima ya lura da su. "Kayi hakuri Yalla6ai, bazan iya shiga ba." Shiru ya biyo baya ayayinda ya kafeta da ido yana kallon fuskarta. Haka kawai sai ya ja guntun tsaki. "Akan wane dalili?" "Ih..ih.san tace kada na shiga zata wulakantani." Ya ji wani abu a ransa, sai kuma ya cije le66ansa na kasa. "Ko menene ku kuke jawowa rayuwarku, da ace kun hakura da yanayin rayuwa, kun godewa kad'an din da kuke samu a gidajenku, da babu abinda zaisa kuzo ana wulakantaku ana baku tamkar wasu karnuka." Batasan sadda ta cigaba da 6ul6ulo da ruwan hawaye ba. Ta so tayi shiru ta barwa zuciyarta amsa, saidsi ta tsinci kanta da kasa aikata hakan. "Ka gafarceni Yalla6ai, saidai akwai lokutan da ba'ason ran mutum yajr aikata abinda ya aikata ba. Akwai tilastawar rayuwa, wani ba shi da yanda zaiyi ne, sai yaga da yaje ya aikata abin turr gwara ya gwammace ya rufawa iyayensa da kansa asiri ta hanyar nema ta halal. Wani kuwa, rashin gata da rashin samun kulawar yan uwa ke sanyashi tsintar kai a halin da yake ciki. Kowane bawa da yanda Allah Ya tsaro rayuwarsa, ba mu muka za6awa kanmu wannan rayuwar ba. Akwai KADDARA." Daga haka ta juya da sauri-sauri ta bar wajen gami da nufar get, batayi wata-wata ba ta fice daga wajen batare da tasan inda ta nufa ba, burinta kawai tabar wajen ko ranta zaiyi sanyi....!Ta dubi sararin samaniya, hasken farin wata ya taimaka kwarai wajen k'ara haskaka unguwar, hakanan kuma akwai hasken fitili domkn unguwa ce ta manya. Ta numfasa ta soma bin hanyar da taga Danliti ya biyo da su dazun. Tafiya kawai takeyi batare da tasan takamaiman inda zata nufa ba bayan nan, hakazalika batajin ko son ta koma wajen walimar. Ta gwammace idan ma saceta ayi muddin za'ayi nasarar rabata da wajen nan. Ita kam ta tsani cin zarfi da disgi. Tayi nisa amma ba sosai ba, ta ga mota a gefenta tana tafiya sannu-sannu, wannan baisa ta tsaya ba ballantana kuma ta waigo. Ta ji k'arar hon da k'arfi, ta runtse ido tana mai cigaba da tafiya kai ka rantse Ummi tsabar yanga ce takeyi, ga wanda ya santa kuwa yasan tafiyarta ce hakan, saidai duk da hakan na yau yafi na kullum don tana taku ne jikinta babu laka, gaba daya a sanyaye yake, zuciyarta banda bugu da sauri-sauri babu aikin da takeyi. "Ummi." Taji faduwar gaba jin muryar Yaya Faruk. Ta waigo da sauri ta dubi motar, kasa jure kallon kwayar idanunsa tayi masu kyau da fisgar hankali tayi gefe da idanunta batare da ta cigaba da tafiya ba. "Shigo." Ta daure ta kara dubansa tana mai share hawayen da suka zubomata, girgiza kai tayi. "Kayi hakuri Yaya Faruk, bazan iya komawa..." "Gida zan kaiki." Ya katseta da fad'in hakan. Ta danyi jim, tana tsoron kada Hajiya tayi fad'a saidai kuma ta gwammace fad'an Hajiya da dai ta k'ara komawa wajen da ba'a dauketa a bakin komai ba face wulakantacciya. Jiki babu kwari ta sanya hannu zata bud'e gidan baya, ya rigata bud'e na mazaunin gefensa. "Nan za ki shigo." Gabanta ya fad'i. Ta kasa cewa komai duk kuwa da cewar ta raina aji, matsayi da kuma girmanta ace wai itace zaune agefen matashin da ya had'a dukkan wadannan abinda takejin ita din bata da shi, abin kamar dai a mafarki. Da bismillah a bakinta ta shiga ta rufe a sannu, ajiyar zuciya ta saki jin wani azababben kamshi ga kuma sanyin Ac da ya ratsa jikinta. Ya soma tuk'i cikin gwanancewa bayan ya maida gilas ya rufe, ya k'ara k'arfin Ac kad'an. Saida suka bar layin gaba daya sannan ya rage gudun da yakeyi ya soma magana tamkar baya so, magana mai cike da nutsuwa da kasaita. "Bansan da haka ba, idan ma nasani toh watakila zuciyata ce wacce ke jin tsananin tausayi yaran da kuma jin haushin iyaye masu barin yaransu yawan aikatau, ya sanyani kasa nutsuwa nayi tunani mai kyau akan haka. Akan abinda na fad'a, ina neman afuwa, kiyi hakuri kinji?" Ya karshe yana k'ara k'ank'an da muryarsa tamkar mai rad'a. Wannan yasa zuciyar Ummi cigaba da harbawa da sauri-sauri. 'Nayi hakuri fa yace?' Ta tambayi zuciyarta, ta lumshe ido ta bud'esu, ashe daman masu kudi sukan yi laifi kuma su bawa 'yan aikinsu hakuri? Ikon Allah. "Kinji?" Ya k'ara furtawa cikin kara kankanta murya, sai kuma alokacin ya dubeta. Gani yayi fuskarta ta yi fayau, hakanan idanunta sun d'an kumbura adalilin kukan da ta ci. Haka kawai ta ga ya gangara gefen titi ya tsaya. Tayi duba da wajen, wajejan gidan gwamna ne na garin Kano, abinda yasa ta rike hakan ma bai wuce adalilin Fahad da ta ta6a ji ya fad'a ba. Ta dubeshi kad'an, shima ita ya fuskanto. Ta kauda kai tayi narai-narai da fuska tamkar mai shirin yin wani kukan. "Na hakura, ni daman banyi fushi ba. Ni wace da zanyi fushi da.." "Ni d'in wanene da na fi karfin ayi fushi da shi?" Ya katseta ta hanyar jefomata tambayarnan. Tayi kasa da kanta batare da tace uffan ba. "Ni ba kowa bane face DAN ADAM, kuma duk dan Adam ajizi ne, yakan kuskuro, wani da saninsa wani kuma baisan ma kuskuren bane. A rayuwa, bani da raayin shiga lamuran da bai kasance matsalata ba, ban fiye damuwa da shiga rayuwar mutane har ma na takura musu ba ok? Abinda ya kaini har nayi miki batun bai wuce na fusata..." Sai kuma yayi shiru bai k'arasa ba. "Kiyi hakuri." Shine abinda ya k'ara furtawa. Cikin rawar murya Ummi ta share fuskarta wanda zuwa yanzun batasan dalilin kukannata ba, ta dangana da tuna mahaifiyarta da tayi wacce kokusa bata ta6a jin dumin jikinta ba. "Ya wuce Yalla6ai, don Allah ka daina bani hakuri." Ya zubawa fuskarta ido kafin ya saki murmushi mai 6oyayyar fassara. "Thank you." Daga haka ya soma tafiya, tana jin wayarsa na faman ruri. Duk bai dauka ba, sai ana uku ta ga ya dauka. Haidar ne, hakuri ya shiga ba shi ya sanarmishi wani uzuri ne ya hanashi karasowa da wuri amma yana nan tafe. Daga haka sukayi sallama. Ummi tayi lamo tana tunane-tunanenta, ko a mafarki idan akace mata Faruk nada mutunci har haka, toh zata iya musawa idan tayi la'akari da yanayinsa koyaushe cikin daure fuska, sa'a ce ke sanyawa kaga fuskarsa a sake kamar yanda sa'ar ce ta ci ta ganta dazun dauke da murmushi. "Mene sunanki na ainahi?" Ya watsomata tambayar batare da ya maida hankali ga dubanta ba. "Hasiya." Ta fad'a a tsanake kamar ta karawa sunan dadi domin kuwa babu wacce ta fad'omata a rai alokacin sai mahaifiyarta wacce sunanta ne ta ci. "Nice name, suna kika ci ne?" Ta gyada kai. "Sunan mamana ce." Da mamaki ya dubeta. "Mamanki tana nan?" Ummi idanunta suka k'ara ciko da ruwan hawaye, ta k'ara narkar da murya tana son yin kuka. "A'a ta rasu wajen haihuwata." Maganar ta dakeshi, ya daure ya hadiye abinda ya ji na tausayinta, saidai duk da hakan saida muryarsa ta kasa 6oyewa. "Allah Yayi rahma agareta." Ta amsa da amin cikin zuciyarta. Duk da wani 6angare na zuciyarsa tana so tasan fin haka game da ita, saidai bai ga wata hujja da zai kare kansa ba idan ta nemi sanin dalilin tambayar duk da baya zaton haka din. Har suka isa babu wanda ya k'ara cewa uffan, hakazalika, kowanne da irin tunanin da yake. A zahiri Ummi ta fi karkata ne ga tuna rayuwarta, babban abin tambayar da bata da amsa shine inda zata ga dangin mahaifiyarta, a 6angare guda kuwa, tana mamakin Faruk da halinsa wanda batasani ba. Bata manta gargadin Ihsan gareta a kwanakin baya. 'Mutum dai ya tsaya iyakar matsayinsa, ko kusa kada yayi tunanin zai iya da Babban Goro, duk cikinsu babu sa'an aurenki, don haka ki maida maitarki, kurwar kaf dinsu, ta fi karfinki.' Wani murmushi mai ciwo ya su6uce mata daidai kuma lokacin da Faruk ya kallota, kawai sai ya tsinci zuciyarsa cikin jin sanyi, ko babu komai bazata fita motarsa da fushinsa ba. Tsayuwar da ta ji yayi ne yasa ta fahimtar sun iso don gaba daya ta luluk'a tunanin dabi'un Ihsan wanda ya sha bamban da na sauran yaran Mami. Suka dubi juna ido cikin ido, gaba daya sun ji wani iri wanda tsakaninsu babu wanda ya bada tunani na daban. "Saida safe." Ya sanya hannu ta 6angarensa ya ciremata (lock). Batare da ta amince sun kara hada idanu ba ta amsa. "Nagode, Allah Ya tsare hanya. Don Allah ka sanarwa da Mami na taho gida kada ranta ya 6aci, idan da hali kada ka nuna kai ka kawoni don Allah." Yayi shiru yana mamakin dalilinta na fadin hakan, sai kuma ya ta6e baki ya daga kafada kadan. "Nifa ban iya karya ba, ba kuma zan fara saboda ke ba ok? Idan ta tambaya zan fadamata." Ya karashe da murmushi yana dubanta, ta kauda kanta. Banda toh babu abinda tace ta sauka. Ta rufe kofar batare da ta kara kalla ba sakamakon duhun gilashin. Ya bita da kallo har ta shige ciki, ya numfasa. Mace kam har mace Ummi ta kai. Shine kawai abinda ya ayyana a ransa daga haka ya ja motarsa yabar wajen a miliyan. Mintuna goma bai cika ba ya isa ga wajen party. Ya kuwa iske Mami na nemanta, nan ya sanarmata yanda akayi, yayi kokarin cewa a hanya ya ganta tana kuka tana tafiya ya taimakamata baisan abinda ya faru gareta ba. Mami tayi mamaki, karshe ta yanke da zarar sun koma zata ji ko menene. "Mutuminki gashican ya iso." Da sauri Iklima ta kai dubanta ga inda kawarta Hassana take mata nuni, wani wawan ajiyar zuciya ta sauke har tana hamdala a fili. Abin ya bawa Hassana dariya, kawai gani tayi Iklima ta ja hannunta. "Muje ki rakani na gaisheshi." Hassana ta so k'in zuwa don gudun kada ya disgata, saidai dole hakanan ta bi bayanta suka nufi inda yake a tsaye bayan amarya da ango suna gaisawa.Haidar ya dubeshi yana mai kai bakinsa saitin kunnensa. "Tsaya muyi hoto mana." Yana murmushi yayi kokarin zillewa, abin saima ya bawa Haidar domin kuwa yafi kowa sanin Faruk bai fiyeson hoto ba. Ya dank'eshi, a hakan ma sunsha hotuna wajen jama'a masu wayoyi, dakyar ya tsaya yana duban Haidar fuskarsa dauke da wani hadadden murmushi, a haka aka daukesu. Cikin masu daukar hoton, har da Iklima wacce gaba daya ta gama narkewa cikin so da kaunar Faruk wanda ya gama tafiya da ruhinta. Bata bi ta kan Hassana ba ta mara mishi baya da sauri tun baikai ga k'arasawa wajen yan uwansa ba wadanda su yake yiwa kallon abokai domin Faruk ba shi da babban amini ke6antacce da za'a kira nasa akoyaushe. Bazai rasa abokan ba, duk wata shawara acewarsa yayyunsa sun isheshi. "Ina wuni Yaya Faruk." Muryar da ya tsinkaya kenan daga gefensa. Ya kai dubansa gareta, take kuma sai ya tsuke fuska tamkar ba shine ke murmushi ba yanzun. Kansa kawai ya gyada sannan yayi gaba. Da sauri ta juya itama tun baikai ga bata kunya ba. Tun kafin ta kai ga Hassana, take watsa mata harara har ta dangana da mazauninta. Alokacin ne ta samu damar yi mata magana. "Ai ga irinta, saida nace kada kije amma kika k'i saurarona, yanzun da ya jefeki da kallon banza ai kinji dadi." Tana maganar a fusace. Iklima idanunta akan Faruk wanda ke hira abinsa hankali kwance, ta murmusa. "Yasan ya had'u ne shiyasa yake shan kamshi ga yanmata. Wallahi ina sonsa fa." Hassana ta ta6e baki. "Shi kuma baisan da zamanki ba." Sai alokacin ta dubeta tana harara. "Wai me kikeson ki cemin? Kin manta alak'armu da shi ne?" "Naga Ihsan ma k'arewar alak'a da shi ai." Hassana ta fada gami da jan dogon tsaki sannan ta cigaba da maganarta. "Shi namiji idan yaga kin fiye zakemishi rainaki zaiyi wallahi, ki kula dakyau leema, kisan dai dabarar da zakiyi ki shawo kansa, amma idan har zaki cigaba da yi mishi irin wannan shishshigin agaban jama'a, toh fa zaki raina kanki." Iklima tayi shiru tana sauraronta, ga dukkan alamu dai maganganun Hassana yana shigarta. Tayi na'am da shawararta na cewa ta dinga yi mishi ladabi a fili da kuma online.(chatting), a sannu idan suka saba sai tayi kokarin shawo kansa. Haka aka tashi taron kowa cike da farinciki idan an cire Iklima wacce bataji dadi ko kadan ba na yanda Faruk ya gwatsaleta ba.

Post a Comment for "DAN ADAM CHAPTER 5"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...