Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

DAN ADAM CHAPTER 3

DAN ADAM CHAPTER 3

- - Post a Comment
DAN ADAM CHAPTER 3
Wani sanyi da daddadan kamshin (roomfreshner) ne ya soma yi musu marhabin kafin dariya da hirar jama'ar falon ta doki kunnawansu. Suka shiga da sallama, Ummi gabanta banda bugu babu abinda yakeyi. Ga wadanda kunnensu ya ji suka amsa musu sallamar, wadanda basu ji ba kuwa, sai hira suke. Babban falo ne wanda ba'a cikashi da kayan ado sosai ba, saidai iyakar wadanda aka dan kawatashi da su masu kyau da tsada ne. Kujeru masu jikin leda farare tas ne zagaye a tsakiyar falon, iyayen na zaune saman kujera harda dattijon kwarai, wato maigidan Alhaji Atiku Modibbo, tare da uwargida ran gidansa, mahaifiya ga Hajiya Fatima, Hajiya Madina da karamarsu gaba daya wato Hajiya Sadiya(Hajiya Mama). Sune a zaune saman kujera, su kuwa jikokin suna a kasan tattausan kafet din dake shimfid'e a tsakar falon. Kallo d'aya Ummi tayiwa 6angaren da suke tayi gaba ta bi bayan Amina zuwa inda ta nufa. Tsakiyarsu ne Amina ta shimfid'a katuwar leda ta cin abinci, suka ajiye komai anan. Anan ne ta ji Amina ta shiga gaishesu, itama ba shiri ta gaishesu. Ba zata iya tantance wadanda suka amsa ba da kuma wadanda basu amsa ba don kuwa sauri takeyi su bar wajen, haka kawai ta kara jin ta raina kanta, ji take kamar wari takeyi ma tsabar kamshin wajen. Cikin yaren fulatanci ta ji wata cikin yanmatan tayi magana da bata fahimci ko menene ba. Gaba daya matasan suka dara, tana ganin sadda wani a samarin ya jefamata filo. "Baki da kirki." Daga haka bata da masaniyar abinda ya karu don kuwa tuni sun bar wajen sun sauka da niyyar dauko sauran kayan. Larai ta taimaka musu itama. Haka sukayita zirga-zirga, bayan sun kammala kawowa, suna shirin tafiya, Hajiya Mama tayi musu magana. "Yauwa Amina sauranku lemu da ruwa ko?" "Toh." Amina ta amsa. "Muje." Cewar Amina tana duban Ummi wacce ke tsaye. Suka nufi falon kasa, suna jin sadda Hajiya Fatima ke tambayar Inna ko Ummi sabuwar yar aikinta ce. Inna ta amsa da aa, Hajiya Mama ta sanarmata a wajen Mami take. Nan fa Alhaji ya hau fadan yawan chanje-chanjen masu aiki da takeyi. Daga haka basu kara jin tattaunawar ba suka yo k'asa suna dariya don abin ma dariya ya basu. Amina ta dubeta. "Kinsan wani abu kuwa? Duk fa abin su Mami, suna gudun abinda zai 6ata ran iyayensu, duk abinda suka ce suyi basa musawa shikenan ta zauna. Wallahi suna burgeni yanda suke kaunar iyayensu." Ta karashe lokacin da take kokarin bude firij. Ummi tana murmushi tace "Toh Anti ai sune abin alfaharin, idan baka da mai maka fad'a ina wani jin dadi a rayuwa?" Amina ta jinjina kai sadda ta soma ciro lemuka tana dorawa a saman firjin. "Gaskiyane kam, mik'o tire a kicin mu dora." Larai ta tambaya ta mikamata, ta goge sannan ta koma suka dora akai, wannan karon Ummi ce a gaba tana biye da ita, saida suka zo daidai dan korido wanda daga shi sai kofar shiga, ta ja baya ta marairaice. "Don Allah Anti shiga gaba." Abin sai ma ya bawa Amina dariya, babu musu ta shiga gaba da sallama sannan itama Ummin ta bi bayanta. Ido hud'u tayi da wannan matashin na dazu, ya tamke fuska ya kauda kai, hakan da ta gani yasa itama dauke nata idanun da sauri ta cigaba da tafiya a tsanake, tuni sun soma zubawa, har Hajiya Fatima na yiwa wani cikin matasan fada akan bayason cin abinci alokacin da kowa yake ci, wanda akeyi domin shi murmushi kawai yakeyi. "Shiyasa fa bana sonshi, wannan idan mukayi aure mai yiwuwa nima haka zai dunga hora ni da yunwa, barni dai na lalla6a da Gadanga." Cewar Inna kenan, aka sanya dariya gaba d'aya. "Kai tsohuwa, dad'ina dake kenan. Ai Faruk banda harkar neman kudi bana jin akwai abinda yasa a gaba, yanzu sai ya juya miki biyar zuwa dubu." Cewar wani wanda ga dukkan alamu shine babbansu, don fuskarsa kadai ya nuna akwai shekaru. "Yauwa Usmanu, ashe ka fahimta." Ummi da Amina tuni suka bar wajen, Amina na rike da Samir d'a awajen Rahila babbar d'iya ga Hajiya Madina. Haka sukayita zolayarsa ko kusa bai mayar da martani ba, asalima banda murmushi babu abinda yakeyi, idan kuma abin ya wuce murmushi, sai ya dara. Acan k'asa suma abinci suka ci sukayi nak, bayan sun kammala kuma sukayi zaman hira har zuwa sadda akayi kiran sallar La'asar. Sai lokacin samarin suka sauko, Ummi ta bisu da kallo kamar yanda Amina ta umarceta. Ta kara jaddada mata cikin rad'a-rad'a. "Kinga na farkon nan mai dan jiki shine babban d'an Hajiya Babba ta Abuja, Yaya Usman yana da matarsa d'aya da yaransu uku, na biyun shine Yaya Faruk, shine autansu baiyi aure ba, na ukun mai farar shadda shine Yaya Ridwan, shima yana da matarsa daya 'yar Ghana ce, yaransu biyu. Na karshen shine Yaya Haidar, shi ake shirye-shiryen bikinsa yanzu tare da Yaya Intisar babbar d'iya ga Hajiya Mama, bikin baifi ragowar sati uku ba."
data-ad-client="ca-pub-1056799479111612" data-ad-slot="8067794805"> Wannan dogon bayanin da Amina takeyi, tuni wadanda akeyi don su sun fice saidai Ummi ta fahimta kuma ta gane, kenan dai Yaya Faruk shine wanda ta gani dazu a tsakar gidan yana waya? Ta tambayi kanta kuma ta bawa kanta amsa. Ba karshen dai Adnan ne wanda ba sai an mata bayaninsa ba. Koda suka idar da sallah, anan suka zauna tsakar gidan suna ta hirarsu har zuwa lokacin da samarin suka dawo suka shiga ciki banda Faruk wanda ya tsaya amsa waya acan farfajiyar gidan. Kiran da Larai ta kwalawa Amina yasa ta mikewa tana amsawa. Nan ta bar Ummi da Samir yaro mai shiga rai. Wasa ta shiga yi mishi, babu ruwansa sai 6angale dariya yake. Ya shiga jan dankwalin abayarta yana dariya, ta rike hannun. "A'a Samir, daina." Maimakon ya daina, saima ya karasa janyewa gaba daya yana ihu da dariya, ta mike da zummar kamoshi, saidai da gudu ya shiga zagaye a wajen. Abin ya bata mamaki da dariya, a garin ta cafkoshi ganin yayi hanyar kofa, ba tsammani tayi karo da mutum har ya kai ga faduwar abin hannunsa. "Bismillah." Ta fad'a batare da ta shirya ba. Ta dago kai sukayi ido hud'u da Yaya Faruk, fuskarsa ba yabo ba fallasa. Bakinta ya soma rawa saidai ta kasa fidda ko kalma d'aya, tana so ta bashi hakuri amma batasan ya akayi hakan ya kasa fitowa ba, wani kwarjini kawai ta ga yayi mata. Ta durkusa da sauri ta dauki wayarsa da ta tarwatse ta hado mahadinta wato batir da murfi ta mik'a mishi batare da ta mike ba. Sai lokacin ta samu yin magana. "Don Allah kayi hakuri." Ta fada cikin sanyin murya. Yasa hannu ya kar6a. "Is ok." Ok din karshe kawai ta fahimta, ya kad'a kai ya barta anan, ganin haka da sauri ta mike ta bi Samir wanda maigadi ya cicci6o a hanya ganin zai fice, ta kar6eshi ta kuma kar6i dankwalinta ta rufe gashinta. Ba su suka tashi tafiya ba sai bayan Magriba, anan dinma kamar baza'a tafi ba, don ta jima a tsaye a farfajiyar gidan bayan ta kammala sanyamusu kayayyakinsu a mota tana jiransu. Su dinma ji sukeyi kamar kada su rabu don dadin da gidan yayi musu ganin kowa an had'u. Haka dai suka fito suka fice. Tana jin sadda Ihsan ke rok'on 'yan Abuja akan su kawo musu ziyara kafin su tafi. "Haba Lil, ai ba saikin rok'a ba." Cewar Yaya Haidar cikin sakin fuska. Daga haka suka rabu, Ummi ta saki ajiyar zuciya ganin sun hau titi don daman gaba daya ta gaji likis har ta ji inama a gidan suka barta bata biyosu ba.A gajiye likis Ummi take, suna zuwa sallolin dake kanta kawai tayi ta kwanta. Bata kara sanin abinda ke faruwa ba a duniyar sai bayan farkawarta da Asuba. Bayan ta idar da sallah ta zauna anan addu'o'i har garin Allah Ya waye, kasancewar babu makarantar boko ballantana ta tashi had'e-had'en karin yaran yasa ta komawa tayi kwanciyarta, baccin da tayi har ya fiye mata na farko dadi, ta jima tana bacci kafin kuma ta soma jin ana bubbuga kafarta ana kiran sunanta. Farkawa tayi a firgice tana salati, ganin Fahad yasa ta sauke ajiyar zuciya. Kira ne daga Maminsa akan ta soya mishi kwai ta had'a da biredi da shayi. Dole ta mike ba don baccin ya isheta ba ta fad'a bandaki ta wanko bakinta da fuska sannan ta bi bayansa. Saida ta kammala komai sannan ta fad'a d'akinsu, ganin Ihsan bata farka ba yasa ta fitowa batare da tayi abinda ya kaita ba(wato gyaran daki). Tana gudun ta shiga bandakin don wankewa Ihsan ta yi mata rashin mutunci tace ta hanata bacci. Misalin karfe biyun rana, kowannensu yayi shirin Islamiyya, kai tsaye yaran wajen mahaifinsu suka nufa sanin da sukayi cewar yana garin suka kwashi gaisuwa ya sallamesu da abin kashewa bayan makaranta sannan suka d'uru cikin mota, suka tafi. Sai lokacin ne Ummi ta samu sararin yin nata shirin na makaranta tana ta zabga uban sauri adalilin lattin da ta so yi, haka ta fito cikin shiri ta yiwa Mami sallama. Mami ta amsa gami da yi mata fatan alheri, har ranta ta ji dadi don abu ne da sam Mamin bata saba ba, alamun Mami gaba daya a yau sun nuna tana cike da nishadi wanda babu damar tambayar dalilinsa. Ta sanya kai ta fice daga gidan. A makaranta nan dinma ta ji dadi sosai don kuwa ta kai haddarta saidai ta sha gyara duk da baikai yawan yanda a baya Malamin nasu ke cin gyaranta ba, ta lura yana yi mata uzuri ganin ko bak'i bata iya had'awa ba, wannan dalilin yasa ya ware mata lokacinta daban yake koyar da ita wasula da bak'ak'e. Koda suka tashi, cike da nishadi ta dawo haka kawai a yau batasan farincikin ko menene takeyi ba, ta godewa Allah yafi sau biyar a zuciyarta. A farfajiyar gidan ta iske motar Danliti, hakan ya bata tabbacin cewar Ihsan sun dawo. Hajiya Binta ta gani tare da wata wacce ba yau ta soma ganinta ba ga dukkan alamu kuma kawarta ce. Ta gaishesu a ladabce, suka amsa ciki-ciki suna karemata kallo. Bata kai ga karasawa ba ta ji suna maganarta, inda matar ke cewa. "Ina mamakin Hajiya Madina, ko a ina ta kwaso wannan mai ruwan buzayen? Wannan ko Alhajinku ya gani mai yiwuwa yayi ta hud'u da ita." Ta karashe tana dariyar zolaya. Hajiya Binta ta ja tsaki. "Ai kuwa da anyi girman kwabo, ballantana kuma sanin kanki ne Alhaji banda waccan shegiyar babu mai fad'amasa ya ji acikinmu, abin na kona raina." "Ai ku kukayi sake, ki bada hadin kai kika yanda komai zai chanja mana." Iyakar abinda Ummi ta tsinkaya kenan cikin zantukansu kafin kuma ta ta6e baki kawai, a kasan ranta kuwa tana tsoron ranar da Mami zata gaji ta korata daga gidan, watakil shikenan kuma dukkan gatan da ta soma samu na ilimi ya rushe. Saidai kuma tayi mamakin yanda Hajiya Binta take kula kawaye irin haka, da ace sun saba kwarai, da babu abinda zai hanata yin shishshigi wajen bata shawarar watsi da zantukan wannan mata. Da sallama ta nufi shiga falon, saidai kuma tayi turus ganin takalman maza har sawu hud'u da kuma na mata a bakin kofar, haka kawai ta ji gabanta ya fad'i, koda ta shiga bata ga kowa ba a wannan falon, ta numfasa ta karasa ciki, har ta chanja sutura tana cike da tunanin wadanda suka zo, sai kuma ta tunano da su Yaya Haidar, watakila su d'inne suka zo. Ta shirya cikin atamfa riga da zani da dankwali bayan tayi wanka sannan ta d'auro alwala ganin Magriba na dab da yi, fitowa tayi falo, tana son zuwa sanarwa Mami cewa ta dawo saidai kuma batason iske bak'in gaba d'aya nauyinsu take ji. A kicin ta had'u da Ramma, ta gaisheta. Ramma ta amsa tana fad'in. "Yanzu kuwa Hajiyar ke tambayarki, ta ji shiru nace kin dawo kina ciki. Kije tana nemanki." Gaba daya ta ji tsoro ya kamata har yanayin fuskarta ya nunawa Ramma. "To ai naga tana tare da bak'i yanzu." Ramma ta kama baki. "Su waye bak'in? Ai 'yan gida ne, Hajiya Babba ce fa da yaranta." Ta gyada kai sannan ta juya ta nufi hanyar falon Mami gabanta na dukan tara-tara, ita da ba don ance Mami ke nemanta ba da babu inda zata. Har ta kai kofar shiga sai kuma ta juya da sauri don ji tayi ba zata iya ba. Muryoyin da ta jiyo daga bayanta na matasan yasa dole ta juyo. Gaba daya mazan ne suka fito da alamu dai masallaci suka nufa sakamakon kiraye-kirayen sallar da aka soma. Kallo d'aya tayi musu ta durkusa da sauri ta gaishesu. Suka amsa sannan ta basu wuri don su wuce. D'ago idon da zata yi sukayi ido hud'u da Faruk wanda dagaske kallonta yakeyi, ta gwammace ace bai kalleta din ba domin kuwa kallo ne ba na arziki ba face kallon raini, fuskarsa babu wata alamar fara'a; ta sadda kanta da sauri. "Ai kuwa Mami na ta cigiyarki da alama kin mata wani gagarumin laifi Ummi." Cewar Adnan ya karashe da dariyar zolaya. "Um." Shine abinda ta furta kawai da murmushi dauke saman fuskarta. Bayan sun wuceta ta bi bayansu da kallo. Wannan karon, Yaya Usman ne kadai ya sanya manyan kaya, gaba daya su ukun k'ananun kaya ne jikinsu. Hajiya Babba Allah Ya bata arziki na zaratan maza wadanda dukkansu basuyi kama da ragwaye ba a komai da ya shafi gwagwarmayar rayuwa da sauransu. Saidai da ace za'a bata za6in wanda yafi kyau da burgewa a fuska acikinsu, toh fa babu abinda zai hanata nuna Yaya Haidar bisa hujjarta na ganin duk ya fisu fara'a. Koda kuwa tasan da yawa cikin wasu matasan yanmata irinta, zasu iya bugun kirji su za6i Yaya Faruk, ita kam banda ita. Tsakani da Allah ta ji haushin kallon da ya bita da shi tamkar wanda ya ci karo da kashi, ta numfasa don tuni sun jima da kauracewa ganinta ta juya, gabanta ya fad'i ganin Ihsan tsaye ta harde hannuwa a kirji ta zubamata na mujiya fuskarta dauke da wani mugun murmushi. Ummi ta kauda kai ta bi ta gefenta zata wuce saidai maganganun da ya soma fitowa daga bakin Ihsan ya tsayar da ita cak! "Mutum dai ya tsaya iyakar matsayinsa, ko kusa kada yayi tunanin zai iya da Babban Goro, duk cikinsu babu sa'an aurenki, don haka ki maida maitarki, kurwar kaf dinsu, ta fi karfinki." Daga wannan ta sanya kai ta fita tana kwalawa Ramma kira. Iyakar radadi da bacin rai, Ummi ta ji shi a ranta, batasan sadda idanunta suka ciko da kwalla ba, wannan cin zarafi har ina? Kai tsaye an yankemata mummunan hukuncin da ko a mafarki bata yi zaton koda mak'iyinta zai shaideta da aikatawa ba, toh daman ina ita ina ire-iren wadannan mazan? Yaudarar kai ne, koda ta auna cewa Ihsan batasan irin zargin da ya kamata tayi mata ba, yasa ta yin murmushi mai ciwo, da alama Ihsan bata gama sanin bambancin matsayinta da su ba, tabbas ta cucesu tunda har ta had'asu da ita, watakil da zasu ji da sai sun had'a da kai mata bugu don haushin abinda tayi musu. Ta share batun gami da goge fuskarta sannan ta juya ta koma don ta tabbatar a yanzun Mami ta shiga sallah. Dakinta ta koma itama ta tayar da nata sallar, saida ta idar ta kaiwa Allah kukanta akan Ya ji6anci lamuranta. Bata da kowa sai Shi, Shi ne gatanta. Yayi rahma ga Mahaifiyarta. Haka tayita kwararo addu'o'i har tana fidda ruwan hawaye kafin kuma ta shafa. Bata kai ga mikewa daga wurin ba ta ji Fahad na kwala mata kira adaidai sadda ya murd'a kofar dakin nata. "Ummi! Kizo inji Mami." Ta mike batare da ta cire hijabin ba ta bi bayansa. + Anan falon farko ta iske yanmatan suna ta hirarsu. Gaba d'aya suka zubomata ido. Ta gaishesu suka amsa suna binta da kallon tara saura. Bata kara cewa uffan ba ta yi hanyar falon Mami. "Wannan 'yar aikin taku ai har ta so ta k'ere ki a kyau." Abinda ya daki kunnuwanta kenan har saida ta ji faduwar gaba. Ta tabbatar da Ihsan sai ta fusata. Da sallama ta isa falon, Hajiya Babba (Hajiya Fatima) na zaune saman darduma tana addu'a yayinda Mami ke zaune saman kujera tana danna waya. Ganinta baisa ta d'ago kanta ba. Ta durkusa ta gaisheta. Mami ta amsa har lokacin idanunta na kan wayarta. "Ya akayi ba ki wankemin bandaki ba?" Sai lokacin ta tuna, shaf ta mance sakamakon sadda zata wuce makaranta, Mamin na wanka, hakan yasa ta fice da zummar idan ta dawo sai tayi. Cikin tausassan muryar Ummi, ta amsa. "Kiyi hakuri don Allah Mami, dazun kina wanka shiyasa ban samu yi ba." Kafin Mami tayi magana Hajiya Fatima ta rigata. "Wannan 'yar fulanin fa Madina?" Mami ta dubeta. "Ummi ce, ita ku ka gani ranar (meeting) dinnan ai. Aiki takemin." Hajiya Fatima ta sauke mayafinta har lokacin tana duban Ummi wacce ta gaisheta, ta amsa mata. "Shikenan ai, shiga kiyi yanzu." "Toh." Ta mike ta shiga d'akin Mamin. Kai tsaye band'aki ta nufa. Cikin mintuna baifi goma sha biyar ba ta kammala wanke band'akin ta fito. Acan kuwa bayan shigewar Ummi, Hajiya Babba ta dubi kanwarta. "Ga dukkan alamu kinyi sa'ar mai aiki wannan karon Madina, na lura yarinyar tana da nutsuwa kamar ba zata bada matsala ba." Mami ta jinjina kai da murmushi dauke saman fuskarta, ko babu komai tana jin dadi idan wanda ya fita ya dame ta a kudi da komai na rayuwa ya yabi wani abu nata. Tabbas Mijin Hajiya Babba ya fi nata kudi da komai, da shi ake damawa a k'asar gaba d'ayanta kasancewarshi tsohin soja wanda a shekarun baya ake matukar ji da shi. Bayan wannan ma, ita kanta Hajiya Babba tana kasuwanci sosai, takan fita zuwa Dubai ta saro kayayyaki, a yanzun da yaranta suka tasa, sai ta hutarwa kanta don kuwa Yaya Usman shi ya cigaba da fita yana saro mata, a karshe sai ta bud'e shago babba na suturun mata. Shiyasa babban burinta bai wuce Faruk ya nuna yana son Ihsan ba, koda ita Ihsan din ta nuna, to babu abinda zai hana auren. Ta gyara zamanta ta numfasa. + "Haka Ummi take, a farko ma nayi zaton rashin sabo ne, sai bayan ta kwana biyu na gane haka halittarta take, bata da rawar kai sannan ba laifi tana da kamun kai." Hajiya Babba ta girgiza kai. "Kai ai kuwa kinyi sa'a, ni kinga da na dauki mai shekarunta bamu wanye lafiya ba, don saida ta dankaramin sata na kudi da sutura sannan ta gudu." Mami ta mike sosai ta zauna tana dubanta. "Yaushe akayi wannan banda labari?" Nan akalar labarin ta chanja. Acikin wannan hirartasu ne, Ummi ta fad'o falon bayan ta kammala, a ladabce ta sanarwa Mami ta kammala. Mami ta amsa da toh shikenan, daga nan ta mike ta fice. A falon farko ta tarar da 'yan matan da mazan sai hira da dariya sukeyi. Kallo d'aya ta yiwa 6angaren da suke ta kauda kai, ta so ta wuce batare da ta gaishesu ba gudun kada Ihsan ta k'aramata wani sharrin, saidai ta ji ba zata iya aikata hakan ba, ta durkusa daga nan bayan kujera ta gaidasu. Hankalinsu sam baya kanta don ya tafi a hira hakan yasa basu ko lura da ita ba. Tana kokarin mikewa suka had'a ido da Faruk, kai ya gyad'a mata alamun amsawa, sai ta dan ji sanyi, ko babu komai an amsa mata, ta bar wajen a nutse. Saida ta isa kofar dakinta ta juyo kadan, ga mamakinta idanun Faruk a kanta har lokacin, saidai suna hada ido ya kauda kansa ita dinma da sauri ta fad'a d'akin ta rufe da mamaki dauke saman fuskarta wanda ko kadan ya gaza 6uya. Toh shi kuma wannan haka yake da kallo? Ta tambayi kanta, sai kuma ta girgiza kai had'i da ta6e baki. Yunwa ta ji ya addabeta, rabonta da abinci tun wajen sha biyu na rana, ga shi batason fitowa ba don komai ba sai don nauyin mutanen falon da take ji. Hakanan ta hakura ta yi sallar isha'i sannan ta zauna tana jiran tafiyarsu. Babu jimawa sosai ta tsinci muryar Mami tana kiranta. Da sauri ta fito falon, Hajiya Babba tare da ita suna tsaye, Hajiya Babba ta sha mayafi ta zura takalmanta. "Dauki ledar can ki bi bayan su Ihsan a sanya a mota." "Toh Mami." Ta fad'a a ladabce sannan ta bi umarninta.

Post a Comment for "DAN ADAM CHAPTER 3"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...