Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

BATUUL CHAPTER 22

BATUUL CHAPTER 22

- - Post a Comment
BATUUL
CHAPTER 22A guje ta fice daga d'akin tana riqe da bakinta, ko Ammah dake shirin shiga d'akin bata lura da ba tayi wucewarta , hanyar staircase tabi zata yi k'asa taji an rik'ota, Mum ta gani riqeda hannun nata, kuka kawai take tana girgiza kai alaman ta sakar mata hannu, wani uban harara da ta bita dashi ta fincikota tace "Sallamamiya Ce mishin kikayi kinada masaniya kan abinda ya samu tsinanniyar yarinyar?, toh Dan Ubanki duk abinda ya biyo baya ki kuka da kanki tambadadda, In banda lalaci irin naki Dan uwarki har ya isa ya wulakantaki ina gidan nan?, banda sunci darajar gidansu nake daga shi har uwar tasa da na karta musu rashin mutunci, shashashar yarinya, yanzun ma bata baci ba muje in keh baki iya kare kanki ni zan yi, wlhy ban san asarar haihuwa nayi ba da na zubdashi tun kamin kizo kina cusa min kuttu", ganin Ajiddeh na k'ok'arin k'wace hannunta yasa Mum cikeda fusata tace "kinsan Allah in baki kiyayeni ba sai naci mutuncinki, yarinya ana neman k'watar miki y'anci kina neman yi min tijara? Kuma wlhy kika kuskura kika tozartani saidai gidan wata uwar bani ba, tsine miki zanyi ki k'arasa lalacewa kibi duniyar gaba d'aya", ta fizgota sukayi hanyar d'akin, kan kujera Ammah ta tarar da Abu zaune ya dafe kai yana kallon marbles d'in d'akin, hannun Ammah da yaji jikinshine ya sauk'ar mishi da nutsuwa, hannayenta duka biyu tasa ta tallabo kanshi tareda shafa kanshi tace "Are you okay?", ido ya lumshe kamar maijin bacci da k'yar ya bud'esu yana kallonta ya girgiza mata kai alamun "Yeah am fine", kan nashi ta sake ta kamo duka hannayenshi tace "Badai dukan yarinyar nan kayi ba ko Aliyu, naga ta fice a guje tana kuka", ya kalli Ammah for some seconds snn ya bud'e baki da k'yar yace "I just don't want to see her anywhere around, not now not ever", Ammah da taji dad'in maganganun shi taja wata kujerar ta zauna tace "Alhamdulillah, Allah yayi mana tsari da masharranta, tayi maka admitting d'in sunada hannu ciki koh?," ido kawai ya lumshe ya bud'e dan gaba d'aya hankalinshi na wajen Batuul, ganin baison zancen tace "Ba komai ai ka kwantar da hankalinka, zamu jirayi hukuncin Abui, muji ya za ayi dasu, amma albasa batayi halin ruwa ba dan mahaifinta ba halinsa ba kenan, kuma nasan in har yaji wannan ta'asa da sukayi sai ransa ya b'aci, baiwar Allah yarinya k'arama da ita sun sata cikin azaba, mey sukeso mucewa Maryam ya sami y'arta?", ta matso kwallar dake idanunta tace " koma dai menene dukdai nina jawo shi tunda yarinya na gaban iyayenta hankali kwance nasa aka nema maka aurenta, bayin Allah ba tareda second thought ba suka bamu, Allah dai ya mata katangar k'arfe da mugaye", har Ammah ta gama magana bai bud'e bakinshi yace uffan ba, tunanin Batuul dake dad'a yi mishi yawa yasa ya zame hannayenshi cikin na Ammah ya mik'e yayi hanyar k'ofa, hannu yasa zaiyi sliding k'ofar yaji an rigashi ta d'ayan gefen, Mum ce janye da Ajiddeh ta shigo tana sababi, "Har mu za ayiwa sharri, Bilki kinyi kad'an kuma wlhy hukumace zata rabamu daku, wato tun kiyayyar da kikemin muna yarinta shine ya koma har kan y'ay'ana sai kin bisu da sharri ko, mu za ayiwa k'azafin yiwa wata figaggar yarinya can asiri, billahil azim sai kinyi Dana sani", Ajiddeh da damuwa ya cika ta rasa inda zata sa rai taji dad'i zubewa k'asa tayi tana kuka, Mum ta dubeta tace "Sun sallameki kin zama bakida amfani shine suke tunanin muma munyiwa wata can ko, kai kuma d'an mace an tura maka karuwa kanata cin amanar y'ata shine Dan Allah ya kamaku zaka lak'awa y'ata da bata san zance ba", ido Abu ya rintse yana fisting hannayenshi jin ta dangana Batuul da karuwa, kai yasa zai fice daga d'akin Ammah ta rik'oshi ta jawo shi gabanta tace "Abutturab inajin aure ne ya had'aka da y'arsu tun farko, inaso yanzun nan ba anjima ba ya rabaka dasu, mey za ayi da mugun iri irin wannan?, maza sallamar musu y'arsu, Allah ya had'a kowa da rabonshi", a firgice Ajiddeh ta tashi har wani dishi dishi take gani tazo gaban Ammah ta had'a hannayenta duka biyu tana kuka tace "Ammah Dan Allah kimin rai, nasan ban tab'a zame miki sirikar kirki ba, babu abin arziqi da na tab'a yi miki amma Dan Darajar Annabin tsira da aminci kar kisa ya sakeni, nasan ko bai sakeni ba tunda yace bai kuma son ganina nasan mutuwa zanyi, ki yafemin, ki roka min yafiyar Batuul ki rok'a min yafiyarshi in mutu da aurensa akaina, badan halina ba sai dan nasan ke uwace ta gari mai halin dattako, inayiwa d'anki son da bansan adadinshi ba a rayuwata", sanyi jikin Ammah yayi amma ko kallonta batayi ba tace "Babana ina jiranka, ka sallamesu su bar min gida", Jiki a sanyaye itama Ajiddeh ta kalleshi amma ko kallon inda take baiyi ba ya karb'e hannunshi daga rik'on Ammah ya fice daga d'akin, Duka Mum ta d'aka mata tace "Dan uwarki sai ki tashi tunda ke asararriyace, ban taba sanin ke mara hankali bace sai yau, har uwarsa ta bud'i baki tace ya sakeki uwar mey zaki zauna yi gidanta, kike wani cewa keh kinsan uwace ta gari ita, da y'arta ce baza ta tsaya....", ko kallonsu Ammah batayi ba ta fice daga d'akin itama, a guje Ajiddeh ta biyo Ammah tana ci gaba da magiya, Sau d'aya Ammah ta dubeta tace "Ba yafiyata zaki nema ba, wacce kika cutar zaki tambaya ta yafe miki", har ta sauk'o k'asa bata dena binta abaya ba, Abui da Farida tare suka fito jin hayaniyar Ajiddeh da Mum, kallon Mum yayi yace "Bilkisu lafiya?, mey ya sameta?", jin muryar Mum sukayi tana cewa "Ki fita harkar k'ananan mutane kizo mu wuce, kema uban ki nada gidan", Abui ya kalleta jin mey take fad'i snn ya kwalawa Abutturab k'ira, ba b'ata lokaci ya fito d'akin da Batuul ke kwance, yana ganin Ajiddeh ya had'e rai, Abui ya dubi Ammah yace "Mey yayi mata kina wajen baki hanashi ba", Ammah ta had'e rai ta tab'e baki tace "cewa nayi ya saketa", Abui ya dubeta da kyau jin abunda ta fad'i yace "Kan wane dalilli zakisa ya saki matarsa?, kaji shirme, kai Aliyu da hankalinka zaka saki matarka, kuskurene tayi kuma yarinya Allah ya tashi kafad'unta sai dai fatan Allah ya tsare gaba", Ammah ta fashe da kuka tace "Abui ya saketa kawai, dubi fa yadda suka cutar da Fatima amma uwarta ke musun sharri mukayi musu har da cewa k'ara zata kai mu munyi musu sharri", Sai lokacin Farida ta fuskanci kan zancen, Ajiddeh ta duba da wani mugun kallo ta tab'e baki ta matso wajen Ammah, Mum cikeda masifa tace "Yo ba Sharrin kukayi mana ba, wacece Maryam ma bare Fatimar har a wani yi mata asiri, kai kaga", ta nunawa Abu yatsa taci gaba "In ka fasa sakin nata baka cika haifaffen d'an bilki ba", Abui da mamaki yake kallon Mum, Abutturab da tunda yazo ya kasa d'ago kai a hankali cikeda nutsuwa batareda ya kalleta ba yace "I don't need a second thought, get out of my sight before I loose my cool, before you regret ever knowing me", yana fad'in haka ya juya batareda yabi ta kan kowa ba", Ajiddeh na jin haka ya fito daga bakinshi kuma a gaban Abui tasan zamanta gidanshi ya k'are, har wani dishi dishi take gani ta miqe tayi waje cikin hanzari batareda ta kula kowa ba ta fita a guje, Mum ce ta bita a baya tana kwala mata k'ira, girgiza kai Abui yayi yace Allah ya kyauta yayi sama , bayan kamar minti biyu Mum ta sake shigowa ta nuna Ammah da d'an yatsa tace "duk mey zai Samar min 'ya wlhy ki kuka da kanki", ta juya ta fice fuuu kamar wata iska+

Yana komawa d'aki ya d'auki Batuul cak a hannunshi ya rungume ya fito da ita, ganinshi riqe da Batuul Ammah ta tambayeshi "lafiya ka d'aukota, ko ta tashi ne?", kai ya kad'a mata yace "Inaso ne ta huta a saman" snn ya k'ira Farida ta biyoshi, yana shiga d'akinshi ya kwantar da ita kan gado, dai dai nan Farida ma ta shigo, yace "Je ki samo mata kaya mara nauyi, I want her to change", kai ta kad'a mishi tace "okay", ta fice, ya kurawa fuskan Batuul ido y'ana kallonta a hankali ya kamo siraran yatsunta ya kai bakinshi ya manna mata kiss yace "I love you Batuul", kamar taji abinda ya fad'a a hankali ta bud'e ido ta kalleshi, ido ya lumshe ya bud'e yana so ya tabbatar dagaske ta farka, da sauri ya matso yana riqeta yace "Alhamdulillah, am glad kin farka", murmushi tayi mishi ta shiga k'okarin tashi ta zauna, shima d'in murmushin yayi mata ya rungumeta jikinshi yana lumshe ido yana shak'ar k'anshinta da yakeso a koda yaushe, jin yaqi saketa yasa ta d'an turashi, ya d'agata daga jikinshi yana kallon fuskanta, hawaye ya gani cike da idonta kuma har lokacin da murmushinta a fuska ta k'arewa d'akin kallo tace "Yaa Abu inane nan?", ya dad'a matso da ita kan cinyarshi yace "Cry no more kinji, baza ki sake kuka ba sai na farin ciki In sha Allah, We are home, and you will be safe here in sha Allah", Farida ce ta shigo riqe da kaya a hannunta, watsar da kayan tayi ta fasa ihu ta hawo kan gadon ta k'ank'ame Batuul tace "Alhamdulillah, omg Batuul am happy kin warke, don't fall sick Dan Allah kinji?", sai kuma ta fashe da kuka, Abu ya kalleta yace "Keh mey haka, kin shigo kina ihu, ina aiken da nayi miki?", Farida ta cunno baki tace "Yaa Abu am just happy my friend is well again", Batuul tayi murmushi ta kamo hannunta tace "Yeah Alhamdulillah, am feeling much better now, Ammah fa", zata bata amsa yace mata "Leave", ta zumb'uro baki ta sauk'o daga kan gadon, Batuul ta kalleshi da idanunta da sukayi raurau tace "Yaa Abu mana, let her stay", bai kulata ba ya sake kallon Faridan data fita kamar mai shirin karya k'ofan, ya kalleta yace "Baby you hungry ko?", kai ta girgiza mishi, hancinta ya d'an ja yace "Nasan kina jin yunwa, and my lil champ too", ya kai hannu kan mararta, sam ta manta da wani ciki a jikinta sai yanzu, murmushi kawai tayi mishi, yace "Let's freshen you up, sai kici abinci", tace "Ni bacci zanyi, am not hungry", tashi yayi ya tattare kayan da Farida ta watsar snn ya dawo kan gadon ya shiga k'ok'arin cire mata kaya, hannunshi ta riqe tace "Zan cirefa", kamar baiji mai take cewa ba yaci gaba da abinda yakeyi, cak ya d'agata yayi toilet da ita, wanka yayi mata tayi brush snn tayi alwala ya d'aukota suka fito, shi ya shiryata ya canja mata kaya, a lokacin Ammah da masu aikinta suka shigo da abinci, ba abin mamaki bane dan tasan irin son da Ammah ke yi mata tun kamin ta auri d'anta, ranan ko Sallah Abu bai fita ba a d'aki yake yinshi ya jasu jam'i, lokaci lokaci Ammah ke shigowa dubata, da daddare ma shi yayi mata wanka ya shiryata cikin kayan bacci snn ya tofa mata addu'a tareda ja mata bargo,wutan d'akin ya kashe ya jawota jikinshi yayi pecking lips d'inta yace "Have a sound sleep Haya", sake shigewa jikinshi tayi, a hankali kamar mai rad'a tace "Ban ganta ba duka yau?, ina ta tafi?, kamar baiji abinda tace ba ya dad'a gyara mata kwanciya yace "You need rest, kiyi bacci", sake maimaita mishi tambayar tayi tace "Yaa Abu mana, she needs to know na warke, ina Ajiddeh?", jin ambaton sunan Ajiddeh yasa yaji abubuwa da dama na taso mishi, hannunta ya kamo cikin nashi yace "Fatima Kiyi bacci Dan Allah", k'ok'arin tashi ta shigayi tace "Toh ina taje mana, I just need to know", a fusace ya janyota yace "I will slap you right away in baki kwanta ba, bakisan you are still weak bane? komawa tayi ta kwanta, ajiyar zuciya yaji ta sauk'e, yaja d'an tsaki, bada son ranshi yayi mata fad'an nan ba, so yake ya dena tunawa da Ajiddeh, gabanshi har fad'uwa yakeyi in ya tuna abinda tayi, he have to caution Batuul d'in da kanta ta dena tuna mishi da ita, atleats for the mean time, ajiyar zuciya ya sauk'e ya rungumota jikinshi yace "Am sorry Fatima", bata ce mishi komai ba, hakan yasa ya mirginota tana fuskantarshi yace "You should rest Fatima Dan Allah, I love you"Ba Zuciyarta kad'ai ba , har jikinta rawa yakeyi jin kalaman da suka fito bakin Abu, tasha jin ana fad'in wadannan words d'in a films da kuma novels amma bata tab'a tunanin haka mutum keji ba in aka furta mishi su, bata tab'a jin irin wannan abinda take experiencing ba yanzu, wani irin fad'uwa gabanta ya shiga yi lokaci d'aya zuciyarta na mata nauyi, hawaye ne taji yana gangarowa kan  fuskarta, ta d'auka baza ta tab'a jin wad'annan kalaman daga wajen wani ba bayan y'an uwanta, shak'ik'anta, tasha jin Farida na ce mata "I love you" duk randa wani abin farin ciki ya giftasu a lokacin, batasan mesa wannan ya fita daban ba, wannan har cikin ranta take jinshi gabanta na tsananta faduwa, she wasnt expecting it, not from him, tunani takeyi itama kamar yadda taji ana fad'a a movies "I love you too zatace?, ta dad'e da sama ranta salama akan jin wadannan kalmomi sabida tasan har sai in ana sonka za a nuna maka, batasan ko tana son nashi ba but tasan yayi casting effect ba kad'an ba cikin rayuwarta, jin tayi shiru snn jikinta na kyarma yasa Abuuturab dafata, kamar jira take taji hannunshi jikinta ta fashe da wani irin kuka, da hanzari ya miqe ya zauna tareda kunna bedside lamp d'in snn ya d'agota, ganin hawaye shimfid'e fuskarta yasashi furta "Subhanallah, Batuul kuka kuma, kinsan I hate jin kukanki, Dan Allah kiyi shiru, am sorry kinji, you don't have to love me back, its okay, ni d'in I will love you with all my myth kinji, just keep yourself safe for me, Be happy", kamar wacce aka daka sai ci gaba da kukan nata takeyi, hannayenta duka biyu ya kamo cikin nashi ya d'an murzasu a hankali yace "Its okay I won't say it to you again tunda bakiso, I promise, kwanta ki huta kinji, its getting late", har lokacin batace komai ba sai jinta take kamar akan iska take zaune, rungumeta yayi ganin kukan nata yaqi tsayawa, jin ya rungumeta yasa feeling d'in da take experiencing yafi Nada,bakin shi ya d'aura daidai kunnenta ya d'an hura mata iska yana patting bayanta snn cikin rad'a yace "Shhhhh, I won't say it again kinji, its a prom....", kasa k'arasa maganar yayi jin fragile tiny hannayenta da tasa ta zagayeshi ta baya dukda ba k'arasawa sukayi ba, nutsuwa da baisan yana da ita ba a yau yaji na ratsa shi jin hannayenta zagaye jikinshi, wani irin ajiyan zuciya ya sauk'e tareda sake k'ank'ameta a jikinshi ya lumshe ido yana shak'ar k'anshinta, dukda yadda yakejin heartbeat d'inta is at a faster pace amma bayason wannan yanayin ya wuce shi ko kad'an, sunfi minti biyar a haka snn ya d'an sassauta rik'on ya d'ago hab'arta, har lokacin idonta lumshe suke, kallon kyakkyawan cute face d'inta yayi da yadda lips d'inta suka koma pink sbd kuka tana d'an twitching d'insu,murmushi ya saki yanajin wani kasala na sauk'o mishi tareda sunkuyowa ya had'e goshinsu waje d'aya sunajin sauk'ar numfashi su na fanning juna, a hankali ta bud'e idonta jin yayi shiru ko motsi bayayi, suna had'a ido tayi maza ta mayar ta rufesu, hannunshi ya d'aura bayan kanta d'ayan kuma kan waist d'inta ya matso da kan nata ya cikata gap d'in dake tsakaninsu, lips d'inshi yayi crashing kan nata har wani sauk'e ajiyar zuciya yayi ya shiga kissing d'inta with passion, batasan sanda ta fara maida masa martanin kiss d'in da yakeyi mata ba a hanKali, saida ya gaji dan kanshi ya k'yaleta yana maida numfashi, jawota yayi ta fad'a kanshi shima ya fad'a ya kwanta, hannu yasa kan lips d'inta yana making circles,yana shaping lip d'in nata  a hankali, yana sata jin kamar ana royal rumble a cikinta, rintse ido tayi da k'arfi dan baza ta iya d'aukan feeling d'in da takeji ba yanzu, cikin maganarshi da ke dad'a sata jin wani iri yace "I missed you, your kiss though.....", sake shigewa jikinshi tayi batace komi ba ta k'ank'ameshi dan tasan mey yake shirin cewa, dukda bata ma ganin fuskanshi tasan murmushi yayi jin chuckles d'inshi datayi, turo baki tayi ta kai mishi dukan wasa tace "But I did well today ai", caraf ya rik'e hannun ya d'an matse, d'an k'ara ta saki tace "oucchh, it hurts mana Yaaa Abu, let me be I want to sleep", "That's exactly what I want you to feel, its okay you not loving me, but then missing me, shima bakiyi?", shiru tayi kamar bazata yi magana ba, batasan much about love ba ita, batasan ya yakeba, dukda taji wani al'amari na daban d'azu da ya furta mata yana sonta amma har yanzu ta kasa gane yaya wanan feeling d'in yake, she doesn't know if she loves him but missing d'inshi, ko bata fad'a mishi yasan she did, yasan tayi kewarsa,  she is used to him now, kamar zatayi kuka a shagwab'e tace "Toh do I have say it, ai kasan nayi, much more than you do, I missed you more", ko da wannan ta barshi zaiyi baccin farin ciki ba sai ta furta son da take masa ba, yasan with time kamar yadda ya samu kanshi da sonta, yadda ya shigeshi farat d'aya ba tareda ya tab'a kawo hakan a ranshi ba, itama zata soshi da yardar Allah, murmushin dake fuskarshi ya fad'ad'a ya gyara mata kwanciya, bayanta na a jikinshi yayi cuddling tiny figure d'inta da duka hannayenshi biyu, Addu'a ya kuma yi, saida ya gama ya tofa ya shafeta dashi , ya sauk'o da hannunshi saman cikinta cikin rad'a yace and "Lil princess too, sleep safe Daddy loves you" snn ya shafawa kanshi ya dad'a matso da ita jikinshi yaja duvet ya  kashe musu bedside lamp d'in, Batuul duk rufe ido da zatayi kalmar "I love you" d'innan ke ringing cikin kanta, ta kasa dena jiyoshi, batasan lokacin da bacci ya d'auketa ba a haka, saida ya tabbata tayi bacci snn ya fara tunanin abinda ya faru yau, mesa Ajiddeh zata mishi haka, does he really deserve this?, laifin nashi ne, meyasa suka zab'i Batuul ba shi ba, how could she be so heartless and cruel, duk irin wannan azaba da Batuul tasha was because of her, wani d'aci yakeji daga mak'oshinshi, ya tabbata da wani ne ba Ajiddeh ba to da saidai yayi kwanan prison, ido ya rintse yana son kawar da tunanin, daga haka bacci ya d'aukeshi +

STORY CONTINUES BELOW


       
         Tana fita Allah yasa taci karo da cab, lokacin da Mum ta fito bata ganta ba drivern ta dake zaune yana jiran ta tambaya ko yaga Ajiddeh yace yaga fitanta a guje, komawa tayi ciki tayiwa Ammah gargad'in wani abin in ya samu Ajiddeh she wont take it lightly, snn ta fito suka tafi da driver, sai kalle kalle takeyi ko zataga Ajiddeh, saida sukaje gida taga cab d'in parke k'ofar gida, ta tambayeshi ko shi ya kawo Ajiddeh by description yace ehhh amma bata bashi kud'i ba kuma ta fita ba tareda bayani ba, Mum ta ciro kud'i cikin jakarta ta mik'a mishi ta koma mota driver ya k'arasa da ita cikin gida, sak'e sak'e kawai takeyi a ranta, abubuwan sun mata yawa as of this time, batasan da wanne zata fara bama, komai ya dagule mata lokaci d'aya, masu aikinta ta kwalawa kira sukazo su biyu a tare, ta tambayesu ko sunga shigowar Ajiddeh, "Ehhh ta shigo amma tayi side d'in can na gefen na Sir", Mum ta wara ido duk da tasan nan ne wajen zuwan Ajiddeh duk lokacin da ranta ya b'aci tace "Ba nan aka ajiye matar nan ba da Daddy ya mask?", sukace "Nan ne Hajiya", tace "Kuje, Keh Sadiya ki tabbata kin kai mata abinci da duk abinda zata buk'ata snn ku zauna kuna lura da ita da duk motsinta", suka amsa kai da baki suka fita, suna fita ta janyo waya ta shiga neman layin mutum d'aya da tasan lallai zai samar mata mafita
         K'arfe hud'u Abu ya farka, har lokacin yana jin Zuciyarshi bata mishi dad'i, idonshine ya fad'a kan Batuul da yasashi jin wani sanyi cikin ranshi, ya lumshe ido ya bud'e snn ya gyara mata kwanciyarta kamin ya sauk'o da k'afafunshi a hankali dan bayason yayi motsin da zata farka ya mik'e ya shiga toilet, wanka yayi tareda yin alwala ya fito ya zira farar rigarsa ya shimfid'e abin Sallah ya hau, raka'a biyu yayi snn ya d'auko Qur'an kan shelf ya fara karantawa a nutse yadda bazai tasheta ba, saida ya karanta Rabin Suratul Tauba cikin kira'arsa mai dad'i snn ya dakata yayi addu'o'insa, jin ana k'iran Sallah ya tashi ya gabatar da raka'atanil fajr kamin ya koma kan gadon, bayason fita ya barta ita kad'ai a d'akin, shi zai jasu suyi Sallah tare , hannu yasa ya shafi gefen fuskarta a hankali ya shiga k'iran sunanta, "Fatima wake up, lokacin Sallah yayi", a hankali ta bud'e idon da ya cika da bacci snn ta mayar ta lumshesu, murmushi yayi yace "You sleep too much, Sleepy head", tashi kiyi Sallah, its time", sai a lokacin taji mey yake fad'i, zuciyantane ya fara pounding tunawa da jiya da tayi, words d'innan na ringing cikin kanta, sake rintse ido tayi ta kasa bud'ewa, tsoron bud'e ido takeyi kar daren jiya ya zame mata mafarki, She have longed to hear someone say he love her, duk da ba sani tayi tana son nashi ba  bataso wannan karon da ta samu taji ya zama mafarki, "Fatima", sulalewa tayi daga jikinshi tace "Toh kayi nima zanyi nawa anjima", mamakinta ne ya cikashi ganin taqi bud'e ido amma tana magana yace " Fatima Open your eyes", kamar baza ta bud'e ba a hankali ta bud'esu ta sauk'esu kanshi, cak ya d'auketa yayi toilet da ita, ya zaunar bakin bathtub d'in, brush d'inshi ya samata toothpaste ya mik'o mata, turo baki tayi ta ansa ta shiga wanke bakinta, tana gamawa ya jawo kan shower ya shiga tsiyaya mata ruwan, saida ta gama alwalan snn ya sake d'aukarta cak ya fito da ita  ya saka mata dogon Hijab d'inta dake ninke gefe, saida suka idar yace "Tashi kiyi rak'atainil fajr", mik'ewa rayi ta jero raka'a biyu snn ta bishi suka ci gaba da addu'a, Hannu yasa jikinta yaji temperature d'inta yace "Good morning", kallonshi tayi taga murmushi shimfid'e fuskarshi, bata tab'a ji ya gaidata ba sai yau, kuma from his look its sincere, a hankali cikin jin kunya tace "ina kwana", ya rik'o hannunta  yace "Baki amsa min ba", sunkuyar da kai tayi batace komai ba, "How you feeling right now?, kinajin wani ciwo?", kai ta girgiza mishi tace "Am fine", ya sauk'e ajiyar zuciya yace "Mai idon bacci, go back and sleep", mik'ewa tayi ta cire Hijabin ta ninke zata koma gadon taji ya rik'o mata hannu, yace "Hey, My princess, I couldn't say Hi to her", juyar da kai tayi tayi murmushi snn ta dake ta kalleshi tace "Its not like I care" ta k'wace hannunta ta koma kan gado, yayi dariya yace "Really?, well her Papa cares, Say Hi to her for me  pls and tell her that Papa Loves her so much ", murmushi tayi ta shige cikin bargo tanajin kamar moment d'innan yayi ta zama haka, kada komai ya canja mata, cikin baccinta taji an rungumeta ta baya, gyara kwanciyarta tayi suka koma bacci, k'arfe goma ya farka itama ya tasheta, wanka ta farayi snn ya k'ira Farida a waya ta kawo mata kaya ta saka, bacci ma takeyi kasancewar yau weekend, idonta cikeda bacci ta taso ta kawo mata kayan, sai wani irin kallo take bin Batuul dashi tana dariya k'asa k'asa, Hararta Batuul tayi ta anshi kayanta tace "Kyaji dashi dai", bakin gadon ta zauna tace "Keh ni mey nace miki toh, kawai dan nayi dariya", Abu ya fito daga toilet, ya kalleta yace "kayan fa?", nuni tayi mishi dasu tace "gasu nan", yace "zaman na meye toh?", ta zumb'uro baki ta mik'e zata fita tace "Ammah tace ince muku breakfast is ready" kallonta kawai yayi ta fice Batuul na murmurshi, suna gama shirayawa ya rik'ota hannunta suka fito, tun tana qi har ta hakura, suna sauk'a downstairs ta fakaici idonshi ta warce hannunta tayi gaba abinta, kowa na kan dinning su biyune basa nan, Ammah da Abui da Sadiq ta gaida sukayi mata ya k'arfin jiki, a kunyace ta amsa da Alhamdulillah snn ya ja mata kujera ta zauna sukayi breakfast tare
      Da yamma suna zaune itada Farida a main parlour, kamar daga sama ta jiyo muryar su Ahmad, rabonta da jin muryarsu watanni kenan in ba a waya ba, da wani irin murna ta tashi t isa inda take jiyo muryar, da gudu ta isa ta rungumeshi hawaye na k'ok'arin zubowa idonta ganin duka kannenta a gabanta, d'aya bayan y'ata ta dinga rungumarsu snn ta karb'i Aabid dake hannun Sayyid tayi pecking d'inshi, sam ya manta da ita sai kallonta yake kamar yaga sabon mutum, jiki a sanyaye ta kallesu tace "Aunty fa?, batace zata zo bako?", Ahmad ya dubeta yace "ita tace muxo, zasu zo tareda Baba su dubaki wai", kai kawai ta gyad'a tana k'ok'arin maida hawayenta da bataso su gani tace "Ku shiga ku zauna, duk kunyi wani tsayi, Sayyid gashin meye haka ka tara kanka kamr wani black cotton?", dariya kawai ya mata ya sunkuyar da kanshi suka karaso ciki, Farida ta d'auki Hafiz tace "muje ka rakani sweet boy", basu jima ba ta sauk'o tareda Ammah, Ammah tace "Ashe manya bak'i ke tafe bamu sani ba, ya kuka baro gida, Ya Auntyn Ku?", Duk suka gaisheta snn suka amsa mata da tana lafiya, nan tasa aka cika musu gabansu da kayan abinci iri iri, suna nan zaune Abu da Sadiq suka shigo a tare, tausayinta yaji ganin yanda take farin ciki ganin yaran, bama yadda take yiwa Aabid wasa ba, ya k'araso wajenta batareda tasan ya shigo ba ya sunkuya daidai kunnenta yace "Hey am happy to see you happy", a d'an tsorace ta juyo ta dubeshi tayi mirmushi tace "Thank you", ya girgiza mata kai yace "You look cute holding the baby, can't wait to see you babysitting my princess", wara ido tayi tana kallon koda wanda yaji, ganin babu mai kallonsu ta sauk'e ajiyar Zuciya ta d'an bugeshi cikin wasa, dariya yayi ya mik'e ya anshi Aabid hannunta yana cakud'a mishi gashi yace "Hey Champ", dariya Aabid yayi mishi cute dimples d'inshi na appearing, da maamki ta bishi da kallo, gaba d'aya ba shine Abutturab d'in da ta sani ba months back, murmushi kawai tayi tana jin wani farin ciki a ranta da takeson ya d'ore a haka,d'aya bayan yaran suka gaisheshi yana amsawa, ya kalllesu yace "Maybe we should go out for ice cream ko, Movie or anything? am offering the treat, who wants to join?", Yusra da kamar jira take tace "Ni zanje, muje Blue cabana, they got the best ice cream and Chapman, yafi na ko ina and their Kebab, omg its so yummy, kasan ko Aunty sai ince mata akaini weekends wai saitace saidai a siyomin, am happy you are taking me.....", bata k'arsa ba Khalil ya sakar mata da wani harara, shiru tayi zata koma ta zauna ganin an harareta Abutturab da tunda ta fara magana yake murmushi ya kamo hannunta yace "Then you will get us all in munje ko" kai ta kad'a mishi, Batuul da mamaki take kallonta ganin yanda yarinyar ta k'ara tsayi, Abu yayi dariya yace ku fad'awa Ammah we are going tunda yamma tayi, Farida ta mik'e tareda Batuul zasuje su shirya, Abu yace "Farida ki sauk'o mata da Hijab in kinje sama", kallonshi tayi idonta yayi rau rau har hawaye ya ciko jin yace a kawo mata Hijab ta dawo kusa dashi a hankali tace "Hijab kuma?, dashi zanje?", ya kad'a kai yana wasa da Aabid ba tareda ya kalleta ba yace "Yeah, anything?", matsawa tayi daga kusa dashi ta zumb'uro baki ta zauna kan sofa, Farida ta sauk'o tareda Amamh riqeda Hijab d'in Batuul ita kuma ta d'aura veil kan cape top da skirt d'in dake jikinta, ta mik'awa Batuul hijab din, duk suka mik'e Ammah tayi musu Allah ya kiyaye sai sun dawo, Batuul ce kad'ai bata tashi ba tana fushin da babu wanda ya lura da ita, Ammah ce tace "Bitti tashi ki bisu kema ki warware jikinki kinji, zaman gidan ai babu dad'i, tashi kije", batason yiwa Ammah musu, mike we a tayi ta zura Hijab d'inta ta fita, koda taje k'in shiga motar Abu tayi dukda taga ya bud'e mata front seat, zagayawa tayi ta shiga ta Sadiq tayi zamanta batareda ta kalleshi ba, baima lura da Fishin da takeyi ba, bayan kowa ya shiga yaja mota suka fita tasu Sadiq ta biyosu a baya.Har suka Isa Blue Cabana duk surutun da akeyi a motar batace komai ba, Sadiq ma duk tsokanarshi haka ya gaji ya kyaleta, bayan anyi parking da kamar bazata fito ba ganin kowa ya fito itama ta fito sai b'ata fuska takeyi, Abu na gama parking shima bayan yaran sun sauk'a ya rufe motar yacewa Farida ta karb'i Aabid hannun yaran nan ta rik'eshi snn ya zagaya ta wajen Side d'in da Batuul take, cikin wasa ya harareta ya kamo hannunta yace "Keh wa yace miki ana shiga motar Sadiq, he drives roughly, bare keda kike carrying baby na", ya d'aura hannunshi kan cikinta, da sauri ta wara ido ta kalleshi jin hannunshi a jikinta tayi maza ta ture hannun tana kalle kallen ko wani ya gansu, ko a jikinshi saima tsareta da yayi da ido, kauda kanta tayi ta matsa baya, yaci gaba "Kina ganin irin gudun da ya riqa shararawa kamar mai shirin barin garin, plss kar ki sake shiga driving d'inshi, I will be there for you always, In sha Allah kinji, Let's get going", d'an k'aramin bakinta ta tsuke tareda murgud'ashi tana janye hannunta, daidai kan idonshi, ido ya lumshe ya bud'e su kanta a ranshi yace "Damn, komai tayi kyau yake mata koda kukane, shi bai tab'a ganin wanda kuka keyiwa kyau ba kamar ita, badan bayason ganin kukanta ba yana damunshi yana sashi jin wani iri da kullum sai tayi mishi ya gani sbd in tanayi face d'inta na zama cute, ainihinta yake gani batareda k'arin komai ba sai lips d'inta da suke sake komawa pink, matsowa ya dad'a yi gabanta yace "Hey mey ke damunki", yasan wani abin ne ya sameta wannan attitude d'in da ta fara displaying, kamar jira takeyi ya tambayeta hawaye ya fara bin kuncinta, wani abin yaji har cikin ranshi, wlhy ko kad'an baya son ganin hawayenta, "Ya salam" ya furta snn da sauri ya jawota ya rungumeta sosai a jikinshi, duk da hijabin dake jikinta hakan bai hanashi jiyo d'uminta dake soothing d'inshi ba, Su Sadiq suka k'araso ganin basu taho ba, "Bro, for real?, a nan d'inma?", ya fad'a muryarshi cikeda tsokana, wani kallo Abu ya jefa mishi da yasashi fashewa da dariya, sai a lokacin ya lura da Batuul dake hawaye yace "Subhanallah, mey ya sameta haka?", ya juya yana tambayan su Farida da su Ahmad da suka tsaya cirko cirko suna kallonsu, kafad'a Farida ta d'aga mishi alamun she has no idea, muryan Abu yaji yace "You guys should get going, make sure kowa ya sami abinda yakeso, anything okay?", ya mik'o mishi ATM card d'inshi da ya ciro cikin aljihu yace "We will join you shortly", Sadiq da damuwa duk ya cikashi yace "Yeah okay....but then is she fine?, like babu matsala", Kai Abu ya kad'a mishi yace "Bakomai, Farida ki kula da yaran nan, let them have all they want", Farida ta kad'a kai ta kama hannunsu suka fara tafiya, suna tafiya ya jasu suka jingina jikin mota a hankali yake patting bayanta yace "Hayat meye kuma?, what is it now, kukanki yafi komai tada min hankali, you should please stop it and tell me mey ya sameki, mey kikeso?", ajiyar zuciya takeyi har lokacin, sassauta rik'on yayi snn ya d'ago kanta yana kallon fuskarta da ta b'aci duk da hawaye, sauk'e idonta tayi k'asa bata bari sun had'a ido ba, yasa hannu ya share mata hawayen yayi cupping fuskarta da duka hannayenshi yace "Okay now tell me, mey kikeso", kamar baza tayi magana ba a hankali tace "Ko ba kaine ba", jin tace shine ya wara ido ya kalli fuskanta da kyau yace "Huh?, Really?, Ni na saki kukan?, Me nayi toh, tell me please , I will rectify it right away kinji", ya k'arashe maganan kamar zaiyi kukan shima jin shi ya sata kuka, cikeda shagwab'a kamar zata sa wani sabon kukan tace "Ko ba kai bane ba kace sai in saka hijab bayan zafi akeyi kuma fa its an evening outing sai kowa ya rik'a ganina kamar matar aure fa", sosai magananta ya bashi dariya da mamaki, bai san shirmen nata har ya kai haka ba, d'ago kanta yayi yana kallonta tareda sa hannu yana zagaye shape d'in da Hijabin yace "Fatima Hijab din ne baki so?", bata d'ago ta kalleshi ba tace "Ni ai bance banaso ba, kawai fa Kaine, kowa sai yace ni matar aure ce", ta sake fashewa da wani kukan, rungumeta ya sakeyi yanzu kam dariya yayi da kyau yace "And that's exactly dalilin da yasa nace ki saka Hijab, banason ana kallemin keh, bazan saurarawa duk wanda yayi miki wani irin kallo ba, you are married Fatima, married to me, you are just mine", ajiyar Zuciya ta sauk'e jin maganunshi tace "Ba toh zan iya saka Abaya ba or any gown", yayi murmushi yace "Yeah hakane but then, hijab zaifi rufemin keh all, nafison ganin ki so modest da kowa na ganinki yasan yes you are married, don't you know immodest dressing shike attracting filth, shike janyo duk wata musiba ta yanzu da ake facing tsakanin opposite gender", dogon numfashi taja jin abinda yace kuma tasan gaskiya ya fad'i, a hankali ta janye daga jikinshi tace "toh shikenan, am sorry", kamota yayi yayi pecking goshinta yace "I love you", wani irin rumbles taji a cikinta kamar jiya jin ya sake maimaita mata I love you, yace "Let's help you ki cire Hijabinki sai muyi zamanmu cikin mota tunda kinga zafi kikeji, I will order duk abinda kike so here", ya fad'a yana ciro wayarsa daga aljihu, da sauri ta riqe mishi hannu ta girgiza kai tace "No am fine, ai na dena jin zafin", murmushi yayi yace "Sure?", ta kad'a mishi kai tace "Yeah", da haka ya riqe hannunta suka isa wajen dasu Sadiq suke, lokacin har kowa yayi ordering abinda yakeso, ido suka zuba musu su dukan suna jira suji mey ya sameta , kujera Abu Abu ya ja mata ta zauna snn shima ya zauna, raurau tayi da ido ganin duk ita suke kallo ta kalli Abu, murmushi yayi ya kallesu ya d'aga musu gira yace "She is fine, babu abinda ke damunta, y'all should relax", explanation d'in abinda ya sata kuka suke jira yayi musu amma ganin kamar bazai yi ba sukayi shiru kowa yaci gaba da abinda yakeyi, waiter ya k'ira ya bashi order abinda za a kawo mishi snn ya ce Batuul ta fad'i abinda take so, tace "Chicken wings in marinated sauce with plenty garlic, Large Lasagne, cream in chicken soup with emm french bread... ", tsayawa kowa yayi ya zuba mata ido jin taqi dena ordering, a hankali Farida tasa hannu ta d'an tab'a ta tace "kee ina zaki zuba duka wannan abinda kike ordering, mey zakiyi dasu?, k'asa k'asa tayi maganar, murgud'a mata baki tayi tace "Keh kam ina ruwanki, inma zubdawa zanyi", ta juya taci gaba da bashi order "With spicy lamb kebab, sour cream sauce, butter scotch ice cream with some toppings, just any and strawberry shake", Abu kam danna wayarsa yakeyi har saida ta gama ya kalleta yace shikenan?, kai ta kad'a mishi yace "Okay you can go", ganin Expressions dake shimfid'e fuskarsu ta d'aga musu kafad'a tace "Wai meye nayine, nifa zanci kayana", Sadiq ya saka wani irin dariya da yasa Abu ya d'ago yana neman mey yakewa dariya, cikin dariyar yace "Do you eat this much ko kuma dai da wani abun, am not getting this seriously", ya sake saka dariya, Farida ma tasa dariya, wara ido tayi snn tayi raurau dashi ta kalli Abu kamar zatayi kuka, kujerarshi ya ya matsar kusa da nata with stern voice yace "Saaadiqq", snn ya watsawa Farida dake k'ok'arin had'iye dariyarta harara, "don't mind them, shiyasa kikaga basuda lafiya, Eat as much as you want, babu ruwanki dasu", ta tsuke baki tace "Bafa dayawa ma nayi ordering ba, kad'an ne fa dan inajin kwad'ayinsu ne duka", ya jawota jikinshi yace "Shhh don't worry, ya kwantar da kanta kan kafad'arshi, suna zaune har aka kawo mata duk abinda tayi orderingSTORY CONTINUES BELOW


Tunda Ajiddeh ta shiga d'aki bata fito ba sai washegari da safe, tasha kuka har ta godewa Allah, da yamman ranan ta fito daga d'akin da ta kwanta ta taga masu aiki sai kai kawo suke wani d'aki, k'arasawa tayi taga waye cikin d'akin, ta manta da sam Mummy tace mata akwai matar da Daddy ya kawo gidan, wata mata ta gani da bandage d'aure jikinta, sai kuma a kanta, sosai ta tsaya tana kallon matar snn ta tab'e baki ta juya ta koma d'akin da ta kwana ciki ta ci gaba da zamanta, ko sau d'aya Mum bata lek'o ta ganta ba sai masu aiki da take tura mata, wayarta da Mum ta bada a kawo mata ta d'auk'a ajiye nan kan gadon, samun kanta tayi da logging wajen calls da neman sunanshi, a hankali ta shafa sunan hawaye na zubowa idonta, tana son Aliyu amma abinda tayi mishi bata tunanin zai yafe mata shi, dialling number tayi, tun kamin yayi ringing tayi maza ta katse k'irar, gallery ta shiga tana kallon hotunansu da sukayi a tare, tana jin inama ya saurareta ko sau d'aya ya bata chance d'in nuna mishi she has changed for good, koda bazai sota ba ita zata soshi, tana cikin tunanin nan ta jiyo tafiyar Dad, sai a lokacin gabanta ya shiga fad'uwa, batasan mey zata ce mishi ya dawo da ita, tashi tai zata shige toilet ta b'oye daidai nan ya hangota, da mamaki k'arara a fuskarshi yake kallonta da ta k'ame waje d'aya hannunta rik'e da knob d'in k'ofar, da mamaki a muryarshi yace "Hauwa, yaushe kika dawo gida?", a hankali ta shiga takowa gabanshi hawayen da take k'ok'arin maidawa na zubowa, a hankali ta k'araso tace "Daddy ina wuni", kallonta kawai yakeyi da ganin yanayinta snn mey take nema side d'in nan, "lafiya", abinda yace kenan snn yace "Tun yaushe kike gida haka, tareda Aliyun kuka dawo?", kai ta shiga girgizawa ta fashe da kuka mai tsanani da k'yar ya lallasheta tayi shiru snn ta da kyar tace, "jiya muka zo shine banajin dad'i nazo gida", kallonta kawai Dad keyi yasan there is more to wannan maganan ba abinda ya faru kenan ba, yace "Shine da shirme da bakida lafiya zaki taho gida, mu lafiyan zamu baki anan gidan d'in kome?", jiki a sanyaye ta rik'o hannun Dad tace "Dad kuma ina missing d'inku shiyasa fa nazo, kayi hak'uri zan koma gobe", tanayi hawaye na ci gaba da zubowa, yace "Its okay, bar kukan, but next time kar ki sake wannan wautar, bakida inda yafi gidan mijinki daraja, yaron kirki mai mutunci ma da yasan darajar mutane, he calls me every two weeks and kowane Sallah da previous azumi in zai bada Sadaka, sai ya k'aramin da wanda zan bawa mutane, he is a good son really, ki kula dashi sosai Hauwa kinji, I don't want you to be like your Sister da ta zama kamar itace k'anwarki, kiyi hak'uri kiyi zamanki gidanki, Allah ya miki albarka", wani kuka taji yaxo mata da batasan yana shirin zuwa ba ta rungume Dad, murmushi yayi ya d'agota yace "Karki damu, my prayers are always with you", ya kamo hannunta yace "I got a patient a wannan d'akin, muje ki gaisheta", suna tafiya yana bata labarin yanda accident d'in nasu ya faru, har suka k'arasa d'akin, ko da sukaje zaune suka tarar da matar da Qur'an gefenta alamar karatu ta gama yanzu, bayan sun gaisa yayi mata ya jiki yace "Ajiddeh wannan itace Kulthum, Kulthum ga d'ayar y'ar tawa sunan ta Hauwa", da murmushi matar tace "Masha Allah, Allah ya rayata, d'azu naga ta lek'o banma san itace ba", Dad yace "Toh ni zan koma inda matsala sai a nemini, Ajiddeh stay here with her for today, keep her company", kai ta kad'a ya fita daga d'akin, kallon Kulthum Ajiddeh ta tsayi, mata mai kyau da ita ko ina y'an uwanta suke, baki ta tab'e ta nemi guri ta zauna dan tunanin nata matsalar

Koda aka kawo musu abincin, babu wanda tayiwa ci biyu, shake d'in nema tasha da d'an yawa, sudai da mamaki kawai suke kallonta, Su Yusra ne sukace sunason a kaisu XD cinema, Farida da Sadiq sukace su tashi su kaisu, Batuul dake shan shake d'inta Farida ta duba tace "You going?", d'auke kanta tayi tace "Kuje, kaina zaimin ciwo in na shiga wajen nan, harara Farida ta sakar mata tace "Kedai kyaji dashi, you and your unending problems", had'e rai tayi ta kalli Abu snn ta kalli Farida zatayi magana Abu yace "Farida!!!, ta zumb'uro baki ta kama hannun yaran tace "Kunga kuzo mu tafi, mulki take ji dashi yau d'innan", daga haka suka k'ara gaba abunsu, Abu ya kalleta yayi murmushi yaci gaba da danna wayarsa, sau biyu tana kallonshi taga danna waya kawai yakeyi yana murmushi, yana zaune bai lura da lokacin da ta tashi daga kujerar ta bar wajen ba, wasu mata ne suka zo suka zauna kan kujerun, da mamaki ya d'ago yana kallonsu jin wasu muryoyi daban, kallonsu ya tsaya yi yana so ya tuno inda ya sansu, they look familiar, d'ayar ce yaji tace "AAK, ashe ana ganinku a gari, tun daga makaranta shikenan kun b'uya ba a jinku, though kwanaki naje ance ka auri wannan yarinyar Ajiddeh, ya kk ya kwana biyu", sai a lokacin yayi recalling faces d'insu amma bazai ce ga sunayensu ba, kallonsu yake d'aya bayan d'aya snn yace "Excuse me Dan Allah, baku had'u da wata zaune nan kujerar ba?", tab'e baki sukayi sukace, "No we didn't meet anybody gaskiya, ya kk toh ya matar taka?", gaba d'aya hankalinshi baya kansu yace "Yeah she is fine, sorry excuse me, I need to go now", daga haka ya mik'e ya barsu nan zaune, ransu duk ya b'aci amma inda sabo sun san halinshi ne hakan, wayar Batuul ya shiga k'ira amma bata d'auka daga baya ma kasheta akayi, hankakinshi gaba d'aya ya gama tashi, su Sadiq ya k'ira yaji ko tana tare dasu sukace mishi bata zo ba, ya ma rasa ina zai fara nemanta, itakam bakin wani pond taje ta zauna tana kallon swans d'in dake cikin ruwan, sosai suke birgeta, tana daga zaune lokaci lokaci take kallon shi taga yana zaune abunshi, ita da kanta bata san haushin mey take ji ba, wani irin fad'uwa gabanta yayi lokacin da ta hango matanan nan zaune wajenshi, da sauri ta d'auke idonta daga kansu amma curiosity ya sata juyawa ta sake kallonsu, dariya taga sunayi, da sauri ta sake juyawa sbd yadda taji zuciyanta na bugawa, hawaye ne taji ya tarar mata a ido, tana ganin kiranshi tasa wayar a silent, daga baya ta kasheshi gaba d'aya, duk inda yasan zai ganta sai da ya zaga, duk abin nan da yakeyi idonta na kanshi, yana d'aga ido ya fad'a kanta, tana zaune tana kallonshi, da wani irin hazari ya k'araso wajenta tareda fizgota yana k'are mata kallo ya tabbatar if she is fine, wani irin kallo ya bita dashi yace "kinada hankali kuwa?, mey ya tadaki daga wajen da kike, are you even okay wai?, mey ke damunki, tell me now", d'auke kai tayi ta ki yadda ta had'a ido dashi sai da ya sake dad'a k'arfin rik'on yace "I will slap you right away, ina miki magana kina d'aukemin kai, what's wrong with you?", wani irin kuka tasa da yasa jikinshi yayi sanyi, d'an tsaki yaja yasa hannayenshi duka cikin gashinshi ya bajesu, d'aukarta yayi cak ya nufi hanyar mota da ita, lamo tayi jikinshi gabanta na fad'uwa, sai da ya bud'e mota ya sakata ciki snn ya kira Sadiq a waya yace "Sadiq you can take the kids home when they are done, daga nan sai a kaisu gida", bai jira mey Sadiq zaice ba ya kashe wayan

Post a Comment for "BATUUL CHAPTER 22"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...