Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

BATUUL CHAPTER 20

BATUUL CHAPTER 20

- - Post a Comment
BATUUL
CHAPTER 20


Duk da batayi tsammanin fiyeda haka daga maganganunshi ba amma jikinta saida yayi sanyi, janye jikinta tayi daga nashi ta sauk'a ta zauna kan gadon, wani iri ta dinga ji ranta batasan lokacin da hawaye ya shiga zubo mata ba, a d'an tsorace ya kalleta ganin ta fara hawaye da sauri ya kamo hannunta yace "Not again, tashi muje malamin na k'asa.....", bata bari ya k'arasa ba ta warce hannunta daga nashi had'e da murgud'a d'an k'aramin bakinta, da serious expression shimfid'e kan fuskarshi yace "Hey watch out", yayi sauri ya sake rik'ota ganin yanda ta mike kamar zata tashi sama, hawaye ne ya cicciko idonta cikin b'acin rai ta tureshi tace "Let me be, I don't wanna talk to you", ta fizge jikinta hawayen dake fuskanta na k'arasa gangarowa, cikin zafin nama ya dad'a fizgota yana mata wani irin kallo yace "Fatima are you okay?, kinada hankali kuwa, na fad'a miki you should stop being rough okay?, you are carrying my baby, i cant risk anything happening to my baby, beside kema bakida lafiya, are you trying to hurt yourself?, mesa bakijin magana ne", ido ta lumshe snn ta bud'esu a hankali hawayen na ci gaba da zubowa, wani matsanancin kuka ta fashe dashi, baisan lokacin da ya furta "Yasalam", ba ya rungumota sosai jikinshi, zama yayi bakin gadon yana patting bayanta tareda d'an rocking d'inta, yanzu ne yake tabbatar da zancen da yayi da Ammah d'azu da ta ce ciwon Batuul ba normal ciwo bane da sa hannu, in ba haka ba she was jovial yanzun nan lokaci d'aya ta fara acting strangely, ajiyar zuciya ya sauke a hankali ya sunkuyo daidai kunnenta yace "Kinaso nima inyi kukan ko Fatima, I don't like you crying yana d'agamin hankali fiyeda komai, I can feel it a duka pulses d'ina in kina kukan nan, Dan Allah ki dena kinji?", bata d'ago ba
sai ma ci gaba da kukanta da takeyi, ido ya lumshe tareda sake matseta jikinshi yayi pecking goshinta snn yace "Tell me mey ya saki kukan", a hankali ta iya bud'e baki tace "zanje wajen Aunty?", kallonta ya tsaya yi for seconds snn yace "I thought we were done with that Fatima, haka kikeso Aunty ta ganki ba lafiya?, ko kinfiso hankalin Aunty ya tashi in taga yadda kika koma, kinga fa duk kin rame", ya fad'a yana d'aura hannunshi saman wuyanta, "I want you to get better kamin Aunty ta ganki kinji, she will b happy okay?", d'agota yayi yana share mata hawayen dake fuskarta, idanunshi gaba daya na exploring fuskarta kamar maison gano wani abun, Four months back da za a ce mishi akwai ran da zai zauna rarrashin mace kallon you are sick upstairs zai yiwa maishi, amma yau shi da kanshi ya zauna rarrashin yarinya k'arama har yakejin shima kamar zai biye mata suyi kukan tare, murmushi yayi ya jawo plate d'in Baby cucumbeya d'auki slice d'aya ya kai mata shi baki, batayi musu ba ta bud'e mishi baki ya saka mata, haka ya dinga bata har ta cinye slices uku tace mishi ya isheta snn ya d'auki cup d'in madaran nan ya fara bata, shima saida ta kusa shanyewa snn ta kauda kanta, zaiyi magana wayarta dake aljihunshi ta fara ringing, hannu yasa ya ciro wayar, ganin mai k'iran yasa ya mik'a mata
1

Tagumi tayi ta zubawa wayar dake hannunta idanu, yaushe ma ya zama mutum da har zai wani nemi ta dawo, Mummy ce ta fito daga bedroom dinta sai k'anshi take zubawa ta tsaya kallon Jainaba da tayi tagumi tana kallon wayar hannunta tana mata magana bata amsawa, a d'an tsawace Mum tace "Keee kinada hankali kuwa, tunanin uban wa kike tun d'azu na fito ina miki magana baki sani ba kuma koh shiryawar bakiyi ba bayan tun d'azu nace miki zamu fita", a firgice Jainaba ta juyo snn ta sauk'e Ajiyar zuciya tace "kinga ni banma jiki ba, wai wannan shasha shan ne yake son d'aga min hakali wai lallai lallai gobe in dawo", Mum tana kallonta tace "Waye kuma, shi Idrees d'inne yake ce miki sai kin dawo a goben?, sai yayi himma yazo ya kinkime ki ai, in kinje can dinma uwar mey zai miki in banda jaraba, y'ay'ansa ai kin samo masu kula dasu toh meye zai wani ce ki koma", tab'e baki Jainaba tayi tace "jarababbe d'aya ko biyu, ni da kaina bansan mey zan mishi ba, ni Lagos dinnan ba sonshi nakeba, zama cikin k'abilu ba iyawa zanyi ba", "Mum tace rabu dashi tashi muje inda zamu, zamuyi maganinshi ne ai, so nake inyi maganin wannan sallamammiyar yarinyar nan da batasan mey takeyi ba, wai har ni take cewa babu ruwanta in wannan tsinanniyar ta mutu, kai nasan ba banxa ba har da sa hannu Ajiddeh da hankalinta baxa tayi haka ba", Jainaba tace "Nima haka nake gani wllh in banda haka yaushe ne Ajiddeh zataji tausayin wanna
yarinyar, tsanar da tayi mata koda wuk'a aka bata tsaf zata kasheta amma lokaci d'aya ta wanice ita ba haka ba, gaskiya da ayar tambaya", Mum tayi k'wafa tace "ni tashi muje inma yi mata akayi inma yin kanta ne duk zasuci uwar ubansu, badai ni Bilkisu tayi shirin tozartawa ba, ta Allah ba tata ba, ki taso muje kada raina ya kuma b'aci", Mik'ewa Jainaba tayi tace "muje", a parking lot suka had'u da Daddy zai fita, tsuru tsuru suka tsaya suna muzurai kamar wasu munafukai, har zai shiga motar ya fasa ya kallosu, a d'arare Mum ta k'arasa gurinshi tace "yanxu nakeson shiga wajenka, ashe har zaka fita", kallon shigar dake jikjnta yayi alamar fita zatayi yace mata "ki sameni a part d'ina", ya kalli driver da guard d'inshi yace musu "zaku iya tafiya", da haka ya juya ya koma ciki, gaban Mum na fad'uwa tabi bayan Dad, tasan shi ba mai magana bane kan abu koda yana damunshi amma inhar yayi magana toh lallai abin ya girmama, babban parlour shi ya koma ya shiga tana biye dashi a baya, waje ta samu ta zauna bayan ya zauna cikin nutsuwa yace "Ina Zainab ta tafi sati d'aya kenan rabona da ita", murmushi ta k'irk'iro tace "Laah ai tana gidansu Salma, ai inace ta fad'a maka kafin ta tafi tunda Salman tayi kwana biyu da zata koma shine suka tafi tare", kai ya kad'a yace "Zuwaira keh yanzu zaman yarinyar nan gabanki bai isheki ba har sai ta had'a da yawo", ido ta wara tace "Bafa yawo ta tafi ba, gidansu Salma taje ko nan dinma yawo ne", kallonta kawai ya tsayayi yama rasa mey zaice mata can yace "shirin ina kuma kikayi keh yanzun", tsuke fuska tayi ta had'e rai tace "Y'ar Sa'adatu da akayiwa aure kwanaki toh ta haihu kuma aiki aka mata shine zanje dubata a asibiti", d'an k'aramin tsaki yaja snn yace "in baki nutsu yanzu ba Zuwaira sai yaushe zaki nutsu, shekara kusan nawa da aure kin haifi yara har sunyi aure suma amma bakisan abinda ya kamata ba, ba dole a sako miki y'a ba tunda abinda taga kinayi shi zatayi a gidanta kuma su na tabbata da hankalinsu shiyasa suka dawo miki da y'ar, tunda abinda kike so kenan sai ki barta tayi ta shirme kina biyeta, aikinki kenan kullum bin k'awaye kamar wata yarinya k'arama? da girmanki bakisan kula da miji ba, gabaki dayanshi hakkin auren ma ba saninshi kikayi ba", had'e rai tayi tace "Nasani ai dama cin fuska zakamin, zumunci zaka hanani yinshine, menene a cikin auren da banayi maka masu aikine gasu nan kai kake biyansu, komai sunayi, so kake sai in riqa zuwa ina baka abincin a baki ina maka wanka, dududu ma sau nawa ake ganinka a wata, ni wlhy bazan
iya da zaman matsi kamar wata y'ar
k'auye ba, a matsayinka kamata yayi ina matar perm sect ace duk bayan sati biyu bana Nigeria, ka tsare ka hana kuma cikin gari ma ka hanani, wlhy bai yiwuwa, exposure ko wane irine yaci na ganshi amma duk kabi ka datse, toh ni ban iyawa", kallonta kawai yakeyi da mamaki, murmushi yayi yace "Tashi kije", dan yasan babu abinda zai fad'a taji tayi aiki dashi ta riga da tayi nisa, babu kunya ba tsoron Allah ta mik'e ta kad'a gyale ta fice daga

parlourn


Da murnarta ta kara wayar a kunnenta tace "Hello Aunty ina wuni", sai kuma ta fashe da kuka, "Yasalam", kawai Abu ya iya furtawa snn ya rungumeta yana kad'a mata kai alamun tayi shiru ta bar kukan da takeyi, daga d'aya b'angaren Aunty tace "Kukan na meye kuma Batuul sai kace wata Yusra, ya jikinki", cikin sheshek'a tace "Aunty naji sauk'i, Aunty inaso inzo in ganki", ji tayi Abutturab ya sassauta rik'on da yayi mata ya saketa ya ja baya, kallonshi tayi idonta cikeda hawaye, maganan Aunty ya katseta daga kallon da take mishi Aunty tace "keda bakida lafiya yawon mey zakiyi, kiyi zamanki har sai kinji sauk'i sai kizo kinji", kamar Auntyn na gabanta ta kad'a kai a hankali tace "Toh", Aunty tace "yawwa maza goge hawayenki bana so a ganki kina kuka kinji, ga Yayya nan za a kai mata wayan kuyi magana da ita", muryan Yayya taji tana cewa "Kaji ja'irar yarinya kukan na meye kikeyi, yaro na zaman zamanshi kinsa ya baro aikinshi, laulayin cikin kikewa wannan rakin, maga yadda zakiyi idan lokacin haihuwar tayi", Zumb'uro baki Batuul tayi tace "keh ina ruwanki, wama ya fad'a miki hakane", Yayya tayi dariya tace "zauna can, ina uwargida har sai an fad'amin, maigidan naki da kanshi duk sati sai ya kiran a waya kuma duk ya fad'a min tab'arar da kike mishi, ai nace mishi ma had'ani dake zaiyi in wuce dake Yerwa, maga ta fad'i", Batuul tace "keh Yayyan nan ko, babu inda zan biki, wajen Aunty kawai zanje", Yayya tayi shewa tace "Aunty taki ma basai in tafi da ita Maidugurin ba, dama naji tana wani rarrashinki dan lalacewa, ita ke dad'a tunzuraki nasani", "Ni kinga tunda ba abun arziki zaki fad'amin ba sai anjima", Yayya tace "gantalallu duk halinku d'aya da y'an uwan naki, ku masu uwa ba'a fad'in lafinta koh, in Baban naku ya dawo ya kawoni gun naki dan ni na raba kaina da tuk'in gantalallun k'annenki, wataran sai nasa shi Baban naku ya tasa su su d'auki tasu uwar suyi gudun da sukeyi dani akan titi, mugaye kawai", dariya Batuul tasa tace "toh keh ki koyi tuqin mana nan gaba basai ana gudu dake ba", Yayya tace "Ina nan tafe ne badai dariya kike min ba", haka sukayita hira, saida suka gama wayan ta kalli Abu dake daddana wayarsa, saida gabanta ya fad'i ganin irin kallon da ya jefeta dashi, zatayi magana yace "tashi ki shirya in kaiki", kallonshi tayi tace in shirya? Ina zaka kaini?", mik'ewa yayi ba tareda ya kalleta ba yace "inda kika gama cewa zaki yanzu", raurau tayi da ido ganin he is so serious, hawaye ne ya cika idonta, a hankali ta tako gabanshi tace ta fad'a jikinshi ta fashe da kuka, cikin shesheka tace "Yaa Abu nifa kawai na fad'a ne, am sorry toh na fasa, kaji bazan sake cewa Zani ba dagaske", hannu yasa ya zagayeta, hakan da yayi ya sata sauk'e ajiyar zuciya, ya d'aura fuska kan gashin kanta tareda lumshe yana shaka'ar kanshinta mai dad'i yace "Its
okay, bana son kukan nan", da sauri ta d'ago tace "kayi hakuri dagaske?", kai ya gyad'a mata yana murmushi yace "I can't be angry with you Fatima, bana so kina tadawa Aunty Hankaline, in taji kina kuka she might think wani abun ke damunki", sake k'ank'ameshi tayi tana girgiza kai tace "nace bazan sake ba", ya sunkuyo yayi pecking lips d'inta yace "that's my princess, muje Malamin na jiranmu", Hijab d'in da ya gani kan gadon ya janyo yasaka mata ya riqe hannunta sukayi waje. Suna fitowa corridors ta kallesa a hankali tace " Ya Abu ina take?" Ya d'ago kanta yace "Wa?" Ta d'an yi shiru sai kuma tace "Ita" sai a sannan ya tuno da Ajiddeh ya d'an bude ido yace "Ohh Ajiddeh? She might be at the parlor" daga haka ya ja ta suka sauko parlor, janye jikinta ta shiga kokarin yi daga nasa jin muryar Ammah da Anty Amnah a parlon da alama shigowarta kenan don gaisawa suke da Ammah Bayan Mum ta bar parlour rai b'ace ta fito ta dawo parking lot, da k'arfi ta shiga k'walawa driver k'ira, a guje ya taho yace "Hajiya gani", kallonshi Kawai tayi ya ciro makulli daga Aljihu ya bud'e motar ya fad'a, daga ganin yanayin yayar tata tasan ba lafiya ba, batace komai ba saida ta Shiga ta zauna tace "Yaa Zuwaira mey ya sameki naga kin canza daga shiga ki fito, wani abun ne ya faru?", Mum taja wani dogon tsaki cike da masifa tace "Dan uwarka kai jahilin ina ne iyye?, ina zaka kaini da ka karyo kwanan nan", Driver da duk ya rikice yace "Hajiya ranki shi dad'e ca nake kasuwa za....", bai gama rufe baki ba a hasale tace "bukkar uwarka zaka kaini ba kasuwa ba, shasha Kuje zamu, jahili", shidai baice komai ba dan inda sabo ya saba indai ran Mum b'ace yake a rana toh sam bai son ya zama shike duty, jiki a sanyaye yace "Ayi min afuwa Hajiya, kuskure aka samu", daga haka ya d'auki hanyar Kuje, Jainaba da ta gama tabbatarwa babban abune ya tab'a Mummy ta tab'a baki tace "Wai Daddy ne ya bata miki rai", Mum tayi k'wafa tace "Abun nayi ne Jainaba, wato ina saka ban sani ba warwara nakeyi, bamuga ta zama ba, wannan karan da zafi zamu shigi kowa, da zafi zafi akan daki k'arfe, bazanyi sanya ba wannan karon, sai naci uban kowama, baza a d'aga min hankali ina zamana ba wlh sai nayiwa abun tufkar hanci", wayarta ta d'auko daga gefenta ta shiga dialling number tasa a kunne, har ya katse ba a d'aga ba, Jainaba taja d'an siririn tsaki tace "Yaa Zuwaira nifa bakice min komai ba har yanzu, mey ya faru kuma banda matsalar Ajiddeh", Mum ta sauk'e wani nannauyan ajiyar zuciya tace "Shifa wannan baban nasu ne ya sani gaba da surutunshi na banza da wofi, akan mene zai dameni nida rayuwata, kinji wai wa'azi ya zauna zai min wai ina abubuwan da basu dace ba", Jainaba tayi dariya tace "baki mik'a mishi microphone ba dan kifi jin wa'azin da kyau", Mum tace "birki na taka mishi, inji da abinda shashashar yarinyar ta Sani ko kuma in biye mishi ya dad'a bata min rai, kuma fa duk sai nayi maganinsu, in banda taurin kanshi ma na jaraba duk abinda akayi kwana biyu yake barin jikinshi amma dai wannan karon alwashi naci sai na samu komai yadda nakeso", Jainaba tace "Yaya wai ina laifin wannan karan ayimana yadda Daddy kullum komai nashi zai koma naki, a badda hankalinshi da tunani ya zama komai a hannunki", Mum tayi k'wafa tace "Dan ubanki wace makarantar nayi da zan iya riqe wadannan abubuwan, ai sai yanxu nake takaicin kin zuwa makarantar da nayi ina Karama, da yanzu komai nashi nasan takansu", Jainaba tace "Ai ba sai Lallai ke din ba, dama su Zee ne zasuyi ai", "kinga fa dad'a tunzurani kikeyi kina b'atan rai, wadanne yaran marasa wayo ne zasuyi min abin kirki, kiga kayan takaicin da Ajiddeh ke k'unsa min, itakuma Zainab in banda yawo kamar wata hadari a cikin gari babu abinda takeyi, kedai bari duk na kusa kawo k'arshen komai", Jainaba tace "Toh Allah yasa", Mum taci gaba da k'iran wayan Zee da har lokacin taqi d'auka, Driver dake gaba yana jin komai Addu'a ya riqa Allah ya rabashi da masu irin halin Mum, kamar kullum yauma tafiya mai nisa sukayi kamin su isa gurin bokan nasu, da zuwansu Mum ta gama zayyane mishi duk abinda ke tafe dasu, k'asar dake gabanshi ya buga yace "itafa wannan yarinyar abinda muka tura Mata yana nan jikinta har yanzu kuma yana kan aiki saidai bansan mey ya hana aikin ci ta mutu ba, dan yaci ace ta mutu tun bayan kwana biyu", Mum tace "gaskiya ne yana aiki dan y'ar tawa da nayi maka bayani tanason kawo mana matsala tace min mutuwa zatayi, in da yadda za ayi ranka shi dad'e ta mutu a huta, kaga in ta mutun, ta wajen nawa zata dawo hankalinta sai musan nayi akanta itama", haka dai Mum ta dinga Zayyanowa boka abinda za ayi tun daga kan Daddy, Ammah, Abu da kuma Batuul, boka yace indai jaka a bud'e take zasuga aiki da cikawa, nan ya duk'ufa ya fara da na Batuul, Suna zaune a wajen wayar Jainaba ta shiga ringing, saida aka kira wajen sau shida snn ta d'aga, shiru tayi tana sauraren mai magana a wayan, sai da yayi shiru tace "Toh naji", ta katse wayar, boka ya gama masu tsubbe tsubbensu yace "kuje, kamin ku k'arasa gida zaku ci karo da lbrn mutuwarta" da murna fal ransu suka zube mishi kudi suka tashi akan zasu dawo in da wata matsalar, sai da suka fita zasu gun mota Mum tace "Wane d'an iskan ne yake damunki a waya, yaga baki d'au na farko ba ai sai ya rabu dake koma wani jarababben ne", Ajiyar Zuciya Jainaba ta sauk'e ta tab'e baki tace "Idrees ne", Mum taja tsaki tace "Shifa wannan k'aramin mara kunya ne, ko ba d'azun nan ya k'iraki ba", Jainaba tace "Shine ya k'irani, wai tuna min zai sakeyi indai ban dawo gobe lallai lallai ba toh inyi zamana a inda nake ba sai na dawo ba", Mum taja tsaki tace "Karamin mara kunya, sai yazo ya kinkimeki ya maidaki", da haka har suka isa mota Driver ya tada sukayi gaba suna ci gaba da hiran abinda zai faru+

Aunty Amna dake tsaye tana magana ta hango Abu rik'e da Batuul suna sauk'owa downstairs, juyawa tayi ta dubi Ammah snn ta juya tayi stairs d'in, tana zuwa ta rungumo Batuul jikinta tace "Ayyyyy Batuul Habibty, bakiji dad'i ba ashe, Allahumma yashfiki, Allah yasa Kaffara ne Allah ya k'ara miki lafiya, baiwar Allah kina zamanki mutane na binki da sharri, kiyita Addu'a kinji, In sha Allahu duk wani mugun nufinsu akanki bazai tabbata ba da izini Allah", murmushi Batuul tayi tana tunanin maganganun da Aunty Amna ta gama fad'a mata yanzu, ita bata gane ma zancen mey takeyi ba", lumshe ido tayi ta bud'e snn tace "Namafa ji sauki Alhamdulillah Anty", Aunty Amna tace "Zaki warke kinji, Allah ya rabaki da sharrin masharranta", daidai nan Ajiddeh ta fito d'akin Abu zata sauk'o down stairs itama, jin maganan da Aunty Amna keyi yasa ta kasa d'aga k'afarta kuma, ta tsaya tana kallonsu, Aunty Amna ta dubi Abutturab da ya had'e rai tace "kai kuma yarinya batada lafiya kaje ka ajiyeta baka fadawa mutane ba", hannun Batuul ya janye ya dawo da ita gabanshi yace "Bata fa jin dad'i, she is weak", wara ido Aunty Amna tayi tace "Iyye, kaji mara kunya, da kasan she is weak ka barta tana shan wuya a can, kai a dole mai mata ko, ai sai ka kinkimeta tunda she is weak" sunkuyar da kai Batuul tayi dan kunya, kamar jira yakeyi ko sai gani sukayi yasa hannayenshi duka biyu zai d'auketa, wara ido Batuul tayi tareda matsawa baya tana girgiza mishi kai alamun kar ya mata haka, kamar bai gane mey take nufi ba ya sa hannu ya kamota zai d'agata taji kamar ana kulle mata ciki ta fasa wani razanannen k'ara da yafi na ko yaushe had'e ta rike cikin tana kiran Anty da kyar, lkci daya ta sulale yayi maza ya bita ya kamata a rikice yace "Ya salam, Not again baby, you will get well soon", Aunty Amna da ta tsaya kallon tsiyar Abutturab a tsorace da jin karan ta tsuguna itama ta kamo Batuul duk ta rud'e tace "Abu ciwon nata ne", kasa bata amsa yayi sai d'aukarta da yayi cak yayi k'asa da ita yana k'iran sunan Ammah, Ajiddeh da ke tsaye har lokacin tana kallonsu idonta ciccike da hawaye ta kasa d'aga k'afarta, ta rasa me ke mata dadi a duniylar, ganin yayi k'asa da Batuul ta fashe da kuka ta koma d'akin da take da sauri, a rikice Ammah ta fito tana tambayan mey ya faru, Farida da Sadiq dake side d'in Abui tare suka fito suna tambayan mey ya faru, Aunty Amna ma na tambayarshi ko ciwon nata amma ya kasa ce mata komai sai sunan Ammah da yake k'ira yana girgiza Batuul d'in ta tashi, Gaba daya duk sun rud'e kowa ya rasa abinda zaiyi ganin jikin Batuul d'in duk ya saki, Farida na kuka tace "Ammah ni kam nace ku kaita wajen Dr Zakaa zai dubata ya fad'a mana abinda ke damunta," hawayen dake idonta ta goge tace "Sadiq Abui na Guest room tareda bak'onshi, kace ciwon nata ya dawo", a rud'e Sadiq d'in ya amsa ya fita amsa aiken da Ammah ta mishi, da k'yar Ammah tayi k'arfin hali ta kamo Abun dake riqe da Batuul ya kasa cewa komai tace "Babana kawota ka kwantar da ita, zataji sauk'i In sha Allah, yanzu za ayi mata magani", ta fad'a tana k'ok'arin karb'an Batuul daga hannunshi, girgiza kanshi yakeyi hawaye na gangarowa idonshi, zama yayi kan kujerar Batuul na rungume jikinshi, gefenshi Ammah ta dawo ta zauna zatayi magana kenan Abui yayi sallama shida Ashiekh da Sadiq, Abui yace "Subhanallahi, jikin nata ne kenan", Abu bai iya cewa komai va don shi kadai yasan mey yakeji cikin ranshi, bayason kowa ya tab'ata sbd fargaban abinda za a ce mishi ya biyo baya, bayajin ko d'aya daga cikin nerves da pulses d'in jikinta na aiki, Ammah ce ta kawo hannunta ta rik'o na Batuul d'in, gabanta ne ya rik'a fad'i ganin hannun Batuul d'in ya saki, d'agowa tayi tana kallom Abu da idanunshi suka kad'a, lumshe ido yayi snn ya bud'e yace "Ammah babu abinda ya sameta ko?, I know she will be alright, nasani Fatima zakiji sauk'i i know you won't leave me just like that isn't it Batuul, you have to get up", Aunty Amna Abui ya kalla yayi mata alamun taja Farida da Ammah da ta matsa baya tana girgiza Kai, hakan ko tayi ta kama hannun Ammah tace "Ammah zataji sauk'i fa, ba dama haka yakeyi mata ba, yanzun nan zata farfad'o, muje muyi mata addu'an samun sauk'i", Itama Aunty Amna k'arfin hali kawai takeyi gaba d'aya jikinta yayi sanyi sai hawaye da takeyi, Farida ce ta karb'e hannunta daga rik'on da Aunty Amna tayi mata ta dawo gaban Abu ta tsuguna dab fuskar Batuul d'in tana kallonsa hawaye na sakko mata tace "Yaaa Abu saida nace maka a kaita asibiti fa, don Allah mu tafi", ta kalli Abui dake tsaye ta mike ta isa kusa da shi cikin kuka tace "Abui don Allah nace mu kaita asibiti da yanzu ta warke, ka ganta yanxu kwance ko motsi batayi, Dan Allah muje a kaita", Hannu Abui ya d'aura kanta ya shafa snn yace "Babu abinda ya sameta kinji, zataji sauki" yacewa Sadiq " *Sadiq tai sha samiro Leno*, Sadiq kamata ka kaita sama", tana girgiza kai tana kuka haka Sadiq ya jata yayi sama da ita ya rage daga Abui sai Abu dake riqe da Batuul snn Asheikh, Asheik ya dubi Abui yace "Alanguro akwai Zamzam a kusa?" Abui yace "Ehh bari a d'auko",Wani nannauyan ajiyan Zuciya Aunty ta sauke lokacin da Yusra ta mik'o mata wayanta tace "Mama ga wayan inji Yayya wai ta gama", karb'an wayan Aunty tayi tace "Kuje ku shirya, its getting late, kice wa Fa'eezah a gama sa muku kaya ku tafi", kai Yusra ta kad'a tace "Toh Mama", daga haka ta fice tana tsalle, wayar ta sake janyowa ta dialling number Baba, ringing biyu ya d'aga, jin muryan Aunty a sanyaye ya sashi saurin cewa "mey ya samu muryanki haka, its so weakening", kamar jira takeyi taji muryan Baba hawayen dake cike idonta ya gangaro, ido ta bud'e ta lumshe snn tace "Uncle ashe Batuul ce bataji dadi ba saida aka dawo da ita d'azu Ammah tamin waya tana fad'amin wai sun dawo da ita tana can gidansu, shine nakeso in ganta koma mu taho gidan tare, we should treat her here a gida hankalina sam yaqi kwanciya, inason ganinta Uncle", "Maryam", Baba ya kirata daga d'aya b'angaren, kasa amsawa tayi har saida ya sake cewa "Maryam", kuka ta fasheda ta kasa amsa kiran da yakeyi mata, Baba dake zaune office yace "Subhanallahi Maryam kuka kuma, mey kikeso?", cikin sheshekar kuka tace "Uncle gida nakeso ta dawo, hankalina zaifi kwanciya in ina ganinta, kaga fa cewa Ammah tayi batasan mey ke damun Batuul d'in ba, toh haka zatayi ta zama da ciwo ba'a nema mata magani ba Uncle", D'an Murmusawa Baba yayi yace "Haba Maryam, kada son y'arki ya rufe miki ido ki manta da cewa tanada aure, kinfi kowa sanin yanzu duk wani nauyi da responsiblity d'inta na kan mijinta, in kikace zaki dawo da ita gabanki bakya tunanin kin musu shishigi har ma suyi tunanin gazawar su muka gani, am very sure kin san su masu kula da Batuul ne dama duk sauran yaran nan ko bama nan", tana share hawayen dake zubo mata tace "Uncle nifa bawai gani nayi sun kasa ba, rashin sanin takamaimai abinda ke damunta da ba ayi bane yafi d'aga min hankali", Abui yace "Duk naji wannan, ki kwantar da hankalinki da izinin Allah zata samu sauk'i, tunda shi Aliyun ya sanar dani rashin lafiyarta, yanzu haka sun d'auko masu magani ana dubata, kiyi mata add'ua sosai kinji, sai kiga ta samu lafiya kamar da, amma in taga kina tada hankalinki itama nata hankalin kinsa tashi zaiyi", kamar Baban na gabanta ta shiga gyad'a kai tana share hawayen fuskarta, da haka ya samu ya rarrasheta ya kwantar mata da hankali+

     Sadiq ne ya d'auko Zamzam d'in da ake buk'ata a side d'in Abui, a cup Asheikh ya d'an tsiyaya snn ya samu waje ya zauna ya fara tofi cikin ruwa, Abu dai har lokacin ya kasa cewa komai sai ido da ya zuba mata idonshi duk ya kad'a, motsin kirki ya kasa yi, he is so freaked, gani yakeyi duk wanda ya tab'ata ce mishi za ai ta bar rayuwa, Asheikh da ya gama tofin shi ya miqe ya dawo gaban kujerar da Abu ke riqe da ita, Abui yace "Aliyu ko zaka samu a gyarata tasha maganin", kamar badashi akayi maganan ba, saida Asheikh ya sake maimatawa snn ya d'ago rinannun idanunshi dake cike taf da hawaye kamar wani yaro, kai Abui ya kad'a mishi alamun he should be strong tare da zuwa kusa dashi ya zauna ya dafa mishi kafad'a yace "Abutturab you have to be strong okay?, zata samu lafiya In sha Allah kaci gaba da yi mata addu'a, ido ya lumshe snn yace "Abui bata mutu bako, baza ta mutu ba In San Allah", sosai Abui ya tausaya mishi yace "ciwo ai ba mutuwa bane Aliyu, zataji sauki da yardar Allah, kayi yadda yace d'in ka kwantar da ita a nema mata lafiya", gani yakeyi kamar in ya sauketa daga jikinshi wani abun zai sameta, kallonta yayi for some seconds snn jiki a sanyaye ya shimfid'eta kan doguwar kujerar amma har lokacin hannunta na cikin nashi, Asheikh ya karaso gaban kujeran ya tsuguna daidai kan Batuul snn ya mik'awa Abu ruwan yace "amshi ka shafa mata a fuskarta", hannu Abu ya mik'o ya tsiyaya mishi ruwan snn ya shafa mata shi a fuska, bayan ya gama ya sa a mik'o k'aramin spoon yace Abu yana sa mata droplet a baki, jiki a sanyaye ya anshi cup d'in ya d'ebi kad'an ya d'iga mata shi a baki, wani irin dogon numfashi taja da ya sa Abu saurin kamota yace "Batuul am glad you are alive, don't leave me again kinji, don't plsss", sai ga hawaye nan idonshi, bata bud'e ido ba haka nan batasan abinda akeyi ba, kamar ba ita tayi wannan numfashin ba ta koma yadda take d'azu, Asheikh yayi gyaran muryan yace "Alhamdulillah, wannan ruwa da ta sha ya dad'a tabbatar mana da lallai asiri akayi mata kuma yana nan cikin jikinta, yawo yakeyi gaba d'aya jikin nata dan a ruwa aka  jefa sihirin da akayi mata, yadda yake yawo cikin ruwa haka itama yake yawo cikin jikin nata snn gaba d'aya rayuwar aka so ta bari da ita da abinda ke cikinta amma da yake Allah yayi tana da saurin numfashi bata mutu ba sai dai za a ci gaba da magunguna snn anayi mata sauk'ar Qur'ani da kuma tofi kullum, In sha Allah da yardar Allah zata samu sauk'i", Abui yace "Subhanallahi, La hawla wala quwata illa billahil aliyyil Azim", Sadiq dake tsaye shi ma tun d'azu ya rasa ma abin fad'a, yanzu har Batuul abar ayi ma asirice, duniyan nan is so cruel, Allah ya bata lafiya su kuma Allah ya toni asirinsu koma su waye sukayi mata", kamar wanda aka tsikara haka Abu ya mik'e ya isa gaban  Asheikh yace "Asheikh inaso in san su waye sukeson cutar da ita da dalilinsu na cutarta, yanzun nan bama sai anjima ba, Ko su waye su sai nasa sun gane kuaransu na cutar min mata da sukayi", Asheikh yayi murmushi yace "Toh mu dai baza muce ga wadanda sukayi mata ba har sai ta samu sauk'i, in akwai likita sai a samoshi ya riqa dubata da abinda ke jikinta, snn tunda ba abinci zata ci ba, su sai su duba suga yadda za ayi tana samu, mu kuma a namu b'angaren  zamuyi kok'arin ganin mun taimaka da addu'a", Jinshi kawai Abu yayi amma ba wai ya aminta da zancen ba, Abui yace "Toh Asheikh mun gode sosai", yace a k'ira mishi Aunty Amna ko Ammah yayi musu bayanin sauran magungunan nata da yadda za ayi amfani dasu, Aunty Amna ce tazo amma Abu sam ya kasa ya tsare sai shi aka bawa magungunan yace "Zaitun d'in za a riqa shafa mata shi a dukkan jikinta, Ma'ul ward d'in kuma ana d'iga mata shi a baki, kad'an kuma a saka a wool a kai mata hanci ta shak'a, Habbatus saudanma jikinta za a riqa shafewa dashi kamin ta kwanta, Abu ne ya anshi komai.
        Tuk'i sukeyi hanyar Jere, Driver sai dariya lbr raha yake yi yana kyakyatawa, yana son fita irin wannan da Dad keyi ba tareda entourage d'inshi ba,  kamar daga sama sai ganin mata sukayi sanye da Hijab d'inta ta shigo titin a guje, ji kake k'iiii ammma ina saida suka buge ta, daga nan sukayi losing control d'in tasu motar, Babu abinda Daddy yake fad'i sai "Innalillahi wa inna illaihi rajiun", abinda ya dinga nanatawa kenan har motar taje ta bugi wata bishiya snn motar ta tsaya, kan kace meye mutane har sun cika wajen wasu suna wajen matar da aka buge wasu kuma sunyi wajen motar, jin surutun mutane yasa Dad sanin lallai da sauran ransu, a hankali ya d'aga hannunshi da yakeji kamar ba nashi ba ya tura  k'ofar motar, Driver dake gaba sai faman kokuwa yakeyi da airbag da ya rufe mishi fuska, mutanen dake wajen ne suka taimaka musu suka fito daga cikin motar, daga can Side d'in sukaji ana ihun "ta mutu", wasu suna "ba mutuwa tayi ba ayi saurin kaita asibiti", da sauri Daddy ya karasa gurinsu, ganin matar taji ciwo sosai yasa cikin hanzari yace "Dan Allah bayin Allah akwai wani wanda ya santa cikinku sai muje dashi asibiti dake cikin gari", duk mutanen dake gurin kowa yace su gaskiya basu tab'a ganinta ba, haka duk suka riqa zuwa suna kallonta suna basu santa ba, ganin ana b'ata lokaci yasa Dad yace musu "Toh koh zaku had'a mu da wani da kuka yarda dashi mu tafi asibitin dashi, sai yaje ya gano inda muke ko daga bayane in Allah yasa an samu y'an uwanta sai mu dawo da ita", duk yawan mutanen dake gurin nan kowa mak'e kafad'a yayi yace shi baxa shi ba, Mutumin birni ba abun yadda bane", d'an k'aramin tsaki Dad yaja yace "Ado zo mu taimaka mu sata mota, mutanen nan ba lafiya ne dasu ba", Ba b'ata lokaci Ado yazo suka kamata suka sata mota, mutanen ganin dagaske suke tafiya zasuyi da ita yasa suka kama surutu, kota Kansu Daddy baibi ba yacewa Ado yaja motar su tafi, Abuja suka karaso direct suka wuce asibiti lokacin ana kiraye kirayen Sallar Magrib, suna zuwa aka karb'eta aka fara bata taimakon gaggawa
        Bayan Asheikh ya koma guest side ne Abu ya d'auki Batuul yayi d'akin Ammah da ita ya kwantar da ita kan gado, ya jima yana yi mata addu'a da fatan samun lafiya kamin Ammah tace yaje ya watsa ruwa yayi Sallah dan ko azahar da la'asar d'inma duk a gida yayisu, sam yaqi barin wajenta, abinci kam har lokacin ba a samu ya shiga cikinshi ba, tunda ya dawo sai yanzu ya shiga d'akinshi, gaba d'aya ya manta da zancen wata Ajiddeh a gidan, ajiyar zuciya ya sauke ganinta zaune bakin gadon kamar mai jiran ace cas ta sa gudu, K'araswa yayi cikin d'akin ya zauna kan gadon tareda riqe kan da duka hannayenshi, a hankali ta dawo gefenshi ta zauna ta d'an dafashi tace "Sannu, how is she feeling now?", bai bata amsa ba sai rungumeta da yayi tsam a jikinshi, har saida ta tsorata jin irin force d'in da yasa a hug d'in, kok'arin kwace kanta takeyi amma sam bai saketa ba, maganganun Asheikh kawai yake tunawa da yace da abinda akayiwa Batuul ta fara wannan ciwon, a hankali ya d'aura fuskarshi kan wuyanta ya fara magana a hankali "I can't risk losing her for anyone, they were trying to hurt her, so suke su rabata da rayuwarta, Mey tayi musu zasu maka haka?", kyarma jikin Ajiddeh ya fara bugun zuciyarta ya tsananta har wani danshi takeji yana bin jikinta, saketa yayi ya rik'o kafad'unta yace "Hauwa do you know they wanted killing her?, an encounter with them will have to b their worst nightmare, I will make them pay for each pain they caused her", da sauri Ajiddeh ta d'ago itama idonta duk ya cicciko da kyar  tace "Its okay babe, they will surely pay for it, amma kasan su waye?", kai ya girgiza mata alamun No, ta saka hannayenta cikin gashinshi tace "Everything will b fine kaji,  kaje kayi wanka, you need rest", mikewa yayi ya shirya ya shige toilet, baki Ajiddeh ta toshe ta saki wani irin kuka, tausayin rayuwarta ta fara, in dai Abu ya gano she is behind komai tasan zamansu ya xo karshe, har ya fito daga wanka tana nan inda ya bar ta, cikin few minutes ya shirya cikin kananun kaya ya dawo kusa da ita ya xauna yace " You also need some rest, ki tafi kiyi wanka, farida will get you something to eat sai ki kwanta" mikewa yayi ya fiddo mata da towel ya mika mata ta karba a sanyaye ta mike ta shiga bathroom din, kwanciya yayi ya lumshe ido ya dafe kansa da yayi masa nauyi, ji yake kamar ciwon Batuul ya dawo jikinsa kawai, da yake a gajiye yake gashi tun jiya rabonsa da bacci, lokaci daya baccin ya daukesa. 
       Washegari Aunty Jainaba bata koma gida ba sai da ta k'ara kwana har biyu snn ta shirya Mum ta had'ata da kulle kullensu da suka koma gun boka suka amso bayan sun gama planning irin wulakancin da za ayiwa Idrees, shi da kanshi yaje ya d'aukota a airport, tun daga airport d'in taga yadda yanayin shi suka canza, ganin yana wani shan kanshi itama ta watsar da kashinshi a ranta tana ayyana yadda zataci ubanshi har suka isa gida, Babu kowa a gidan tasan duk yaran na  makaranta masu aiki na b'angarensu, d'akin ta bud'e ta shiga, turus tayi ta tsaya ganin komai na d'akin an canja shi snn ga jerin sabbin akwatuna an a d'akin har set uku, juyowa tayi zata mishi magana cikeda bala'i, dama kan wannan surprise d'in nashi ne ya sata baro aikin da takeyi can Abuja ta taho amma ganin ba fuska ta kasa bud'e baki

Post a Comment for "BATUUL CHAPTER 20"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...