Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

BATUUL CHAPTER 18

BATUUL CHAPTER 18

- - Post a Comment
BATUUL

CHAPTER 18


Har jirginsu Aunty Jainaba ya sauk'a Nigeria hankalinta yaqi kwanciya kan abinda Ajiddeh ta fad'a mata, inko gaskiya ne ai da sun kad'e dan kishiya ba abar so bace ko cikin mafarki, bazai ma yiwu bane, Aliyu ya raina musu hankali, amma koma menene zasuyi maganinshi maci amana kawai, so take kawai ta isa gida ta fesawa Mummy lbrn cin amanan da d'an matsiyatan nan yayi musu, Dan ba Ajiddeh kad'ai yayiwa ba, ko jiran driver batayi ba ta tari Taxi tayi hanyar gida, suna isa tacewa driver taxi ya jirata a kawo mishi kud'inshi ta shige cikin gida jikinta sai b'ari yakeyi kamar ita aka yiwa kishiyar, a hakimce ta tadda Mum d'in Ajiddeh zaune a parlour, da mamaki Mum ke duban Jainaba da ta fad'o cikin d'akin ko sallama babu tace "Keh kuma daga ina haka kamar ana tunkud'oki, mey ya faru kika dawo da wuri haka keda zakiyi har sati biyu", waje ta nema ta zauna jiki na b'ari, Mummy ta gyara zama tace "Keh ko lafiya haka, Ya Ajiddehn take?", gumin da takeyi ta goge snn ta shiga korowa Mummy bayanin duk abinda ya faru tun zuwanta har zuwa zancen cikin dake jikin Batuul da kuma abinda Ajiddeh ta fad'a mata kan cewa Batuul matar Aliyu ce, wani irin zabura Mummy tayi daga kan kujerar da take zaune ta dafe k'irji tana rafka salati tareda cire d'ankwalin kanta da ya bayyana gashin kanta mai tsawo da shek'i tana fifita dashi dan wani irin zafi takeji duk da Acn dake aiki, tace "Jainaba bana son zancen banza, wane Aliyun ne yayi aure?, ba dai na Hawwa ta ba, ina ba Aliyun Ajiddeh bane ya k'ara aure" Jainaba dake zaune ta mik'e tace "Shi d'in ne kuma ma dan wulak'anci irin nasa har ciki ke gareta yanzun, wannan tsinanniyar yarinyar wai itace matarsa duk ba a sani ba", Cikin d"aki Mummy ta shiga sai gata rik'e da gyale da jaka tana ta sababi tace "Ni Bilkisu zata wulak'anta, duk burin da naci kan Ajiddeh? Su da zaman lafiya saida su ga wasu nayi, shima munafikin Aliyun shine harda dukar min y'a ko?, toh duk sai sunci ubansu gabaki d'ayansu dan sai nasa sunyi kuka da idanunsu munafukai kawai, wannan ciki sai ya zama sanadin rushewar farin cikinsu baki d'ayansu, sai na nuna musu kan kishiya babu abinda bamayi, munfi k'arfin zama da ita koda tadda ta mukayi bare kuma an kawo mana ita a munafurce" ta fad'a tareda wani d'an guntun murmushin takaici ta kalli Jainaba da ta koma ta zube kan kujera tsabar gajiya tace "Yaya ina kuma zamu? Ni wlhy duk na gaji, in na huta sai mu tafi", ta watsa mata wani irin kallo tace "bakida hankali inaga, ace miki anyiwa Ajiddeh kishiya keh har lokacin hutu ke gareki?, ai in kinga mun huta to sai naga na d'agawa Bilkisu hankali itada Zuri'arta baki d'aya naga sun wulak'anta sun d'and'ani bakin cikin da suka jefa y'ata snn zaki samu damar hutawa, kan y'ay'ana biyun nan babu abinda bazanyiwa mutane ba, bare ma Ajiddeh wacce tafi komai soyuwa a gareni, duk burina yana kanta, sun jawowa kansu, maza ki tashi muje", Rai b'ace Jainaba ta mik'e da k'yar dan duk jikinta ciwo yake mata ga gajiya suka fita waje, Sadi driver na ganin Mummy ya washe baki tareda k'arasowa wajenta yace "Hajiya fita zamuyi kenan?", tace "Ehhh maza d'auko mota, Kuje zamu yanzun nan", Jainaba batace komai ba sai bin Mummy da takeyi a baya kamar wata doluwa, saida ya fita da motar bayan sun shiga sun zauna ta dubi Mummy tace "wai gun wa zamu a Kuje?" Mummy ta kad'a kai tace "wajen wani Malamin zamu mana, wannan ma yafi kowa iya aiki danshi baima San Allah ba, Matsafine sosai na bugawa ma a Jarida snn shi ba kowa yakewa aiki ba sai in kanada connection, kin dai San y'an cikin k'auyen garin Abujan nan da basu San wani Addini ba, toh gunshi zamu, Hajiya Ramatu ta dad'e da cemin zata kaini gunshi ban samu munje ba sai kwanaki ne dana rakata kuma naga aikinta ya kammalu in no time kinga har ta samu ta auri wannan Ambassador, matanshi kuma sun shiga gari yanzu daga ita sai y'ay'anta da ta kawo suke zama a can, y'ay'an mijin nata ma ta koresu kuma mijin bai isa cewa komai ba , yanzunma can d'in zamu, dan ni na tabbata banida mak'iyi kamar wanda zai tab'amin y'ay'a", a bakin gate suka tadda driver d'in taxi shida Mangal yanata mishi zuba, Sadi Aunty Jainaba tacewa ya bada kud'in motar ya ciro ya mik'a suka d'au hanyar Kuje, saida suka shiga can cikin k'auyen snn tacewa Sadi sun kawo, nan yayi parking suka fito suka isa y'ar bukkar hatsabibin bokan nasu mai suna Namurje
+

STORY CONTINUES BELOW


Hawaye kawai Farida keyi dan ita Sam bata shirya tafiya ba yanzu, Abu kam driving yakeyi hankali kwance ko kallonta baiyi ba, a hankali ta bud'e baki tace "toh Yaa Abu kaga bari in k'ira Ammah in fad'a mata ina zuwa kar taga nayi dawowan baza....", wani irin kallo da ya wurga mata yasa ta saurin sunkuyar da Kai, bata sake d'agowa ba saida taji yaja ya tsaya da motar, jiki a sanyaye ta d'ago kai tanace airport suka zo, duk ranta ba dad'i batayi sallama da Batuul ba, ganin ba airport bane yasata sauk'e ajiyar zuciya tareda murmushi, fita yayi daga motan yayi gaba itakam tana nan zaune dan baice ta fito ba, saida yaje bakin k'ofar shiga yaganta zaune cikin mota ya daka mata harara yace "kin fito cikin motar nan ko sai nazo na fidda ki mara kunya", ba shiri ta fito tana zumb'uro mishi baki tabi bayanshi, numfashinta ne ya kusa d'aukewa ganin irin tsaruwar gidan, tasha ganin gidaje masu kyau ko designs d'in Yaa Abu amma wannan daban yake, ya tafi da ita ba kad'an ba, binshi kawai takeyi har suka k'arasa hawa sama ya bud'e wani d'aki ya shige ciki, bayanshi tabi itama ta shiga, Batuul ta hango kwance kan gado tana bacci hankalinta kwance, batasan lokacin da ta fasa wani ihu tana fad'in "Sweetheart ashe kina nan shine kika barni so lonely inata Nemanki....", tana yi tana nufar gadon da niyyar hawa, da hanzari ya fizgota yana mata mugun kallo yace "bakida hankali ko? Tashinta zakiyi daga baccin", ta zumb'uro mishi baki tace "toh aini ban sani ba" , yaja tsaki ya jefar da ita ya koma gaban computer da alama tunda ya fita baccinta takeyi hankali kwance, d'an murmushi yayi ya dawo bakin gadon tareda hawa yana kallon kyakyawar fuskarta, hannu yasa ya gyara mata gashinta da ya bazar tun d'azu snn ya gyara mata duvet, a hankali ta bud'e lumsassun idanunta dake cike da bacci ta sauk'esu kanshi, murmushinta mai kyau tayi mishi ta sake maida idanun ta rufesu, shima har lokacin murmushin ne a fuskanshi, Farida ikon Allah ta tsaya gani, a hankali ya sunkuya yayi kissing goshinta snn ya sauk'o daga kan gadon, Farida ya gani duk ta wara ido tana kallon Abunda yake, harara ya sakar mata yace "kallon na lafiya ne, mara kunya kawai saura ki tada ta, kuma if you try something stupid sai nayi maganinki dan yanzun ma ba k'yaleki nayi ba" daga haka ya fita, itakam yana fita ta murgud'a bakinta tace "masifaffe" tayi windown d'akin tana kallon yadda tsarin gidan mai kyau yake

Mummy zaune gaban boka Namurje bayan ta gama zayyano mishi abinda ke tafe dasu tana haki, saida ya gama jin bayanansu snn ya d'ago kanshi tare da janye abunda ke kife akan nashi mai kamada hood, innalillahi wa inna illaihi rajiun, wani irin mutum ne zaune gabansu da ko kad'an bashida kyan gani, bak'i ne k'irin snn ga wani shafteten maki shimfid'e a fuskanshi, irin mazan nan ne murd'ad'u, Su Mum hankali kwance ko tsoron halittarsa basuji ba, magana ya fara da wata irin razananniyar murya yace "duk naji bayananku kuma zaku sami aiki daidai bud'ewar jakarku, Mummy tayi caraf tace "ai In kud'i ne bakada matsalarsu, ranka shi dad'e munason wannan yarinyar a fara ta kanta, ba abinda ke cikinta kad'ai za a halaka ba har itama in san samune munaso tabishi inyaso daga baya sai musan yadda za ayi da sauran matsiyatan, dan ni har iyayen yarinyar sai naso ganin bayansu tunda suma ganin bayanmu sukeson yi", ya saki wata shegiyar dariya da gama jin maganganunta yace "Aikinki ya gama, a mik'osu tukunna sai kiji kanun bayanin", jiki na rawa Mummy ta janyo jakarta ta shiga zazzage mishi mak'udan kud'in dake cikin jakar masu uban yawa, kai kace ita akayiwa kishiyar sabida yadda jikinta ke b'ari, sai da ta juye tas snn tace "gasu nan ranka shi dad'e, inma da k'ari za a biyoka dasu", baice komai ba ya d'auko wata jaka ya ciro wani abu shi ba nama ba snn ba jini ba k'ulle a leda ya mik'o mata yace "wannan abin da na baki zaki jefa cikin kogi, bazaki bud'i baki ba har sai kin gama aiwatarwa , yadda zai b'ace cikin ruwan nan haka nan cikin jikinta zai b'ace itama tabi sahu", Mummy jiki na rawa tasa hannu biyu ta amsa kamar wacce aka mik'owa abin kirki ta shiga ce mishi "Nagode ranka shi dad'e", Aunty Jainaba tace "muna nan dawowa bada dad'ewa ba", shidai baice musu komai ba har suka gama b'ab'atunsu suka fita, Aunty Jainaba tace "Yaya kinga wannan mutumin da gani bana wasa bane dan har firgitani yayi da farko", Mummy tayi murmushi tace "Ai Bilkisu da zauri'arta wasa suke dani basu san wacece Zuwaira ba har yanzun, sunana kawai sukeji", suka sa shewa gaba dukkansu biyun sukaci gaba da hiran abubuwan sharrin da zasu jefi Zuri'ar Ammah dasu har suka iso inda motar Sadi take, a firgice ya tashi daga baccin da yakeyi jin an bud'e motar ya Shiga 
mitsike ido yace "Hajiya ashe har an fito" basuce mishi komai ba tunawa dasukayi da gargad'in da bokansu yayi musu kawai suka fad'a mota, tab'a baki yayi ganin babu wanda ya kulashi yaja k'ofar ya tada mota suka tafi, wajen sha d'ayan dare suka iso garin Abuja, saida suka zo dab Jabi lake snn Mummy ta shiga tab'a Aunty Jainaba ta tsaida Sadi a wajen, hakan kuwa akayi yayi parking suka fito suka gama tsafe tsafensu suka dawo mota sunata murna tareda fatan samun Nasara har suka isa gida
1

STORY CONTINUES BELOW


          Kanshi ya kifa jikin steering motar yana tunano stress d'in da ya shiga kwanakin nan, sam hankalinshi yaqi kwanciya da barin Batuul, ga wannan sarkin y'an rawan kan tazo zata k'ara mishi akan na da, iska ya furzar bakinshi ya tada motar yayi hanyar gida yana tunanin yanda zai shawo kan Ajiddeh ya bata hak'uri, parking yayi ya fito daga mota ya shiga gidan, kamar kullum tana nan kwance idonta a kumbure, tana ganinshi ta fashe da wani kukan, yasan hakan zai faru shiyasa ya shigo a shirye, rarrashinta ya shigayi da bata baki as usual don aikin kenan kullum, itakam murna cike fal ranta jin bayanin dasu Mummy sukayi mata a waya, sai da ta gama bashi wahala snn ta sauk'o kamar ko da yaushe, daga nan suka fad'a wata duniyar, ko masallaci bai fita ba nan gida yayi Magrib da Isha itakam tana kwance har saida yayi dagaske tukunna ta tashi tayo alwala ta had'e sallolin da duk ma babu nutsuwa cikinsu, tana idarwa ta dawo jikinshi ta shiga yi mishi wasu abubuwan amma gaba d'aya hankalinshi na wajen Batuul, so yake yaje ya ganta dan yasan ba kowanne abincin takeci ba sai kayan kwad'ayi amma fir Ajiddeh taqi kyaleshi, ita ko tambayar inda ya kai ta ma bata yi.

       Kamar yadda yace kar ta tada ta batayi karambanin tada ta ba, k'asa ta sauk'o tana zagaye gidan tana yaba kyan da yayi mata, sai da ta gaji dan kanta ta hawo sama, bata dad'e da dawowa ba Batuul ta farka da mamaki take kallon Farida ta wara tace "Laaah yaushe kikazo, wa ya kawoki?" Farida tayi dariya tace "wannan baccin naki ai har a saceki baki sani ba, tun d'azufa kike kwance", "Wanne irin tun d'azu? Bai jima bafa da na kwanta" inji Batuul tana k'ok'arin sauk'owa, Sallah azahar ta d'auro alwala tayi daga nan suka sauk'a k'asa sukayi kitchen Farida sai santin gidan takeyi, Farida ce ta shiga had'a musu lunch Batuul kuma na zaune kan island d'in kitchen d'in, in no time Farida ta had'a musu spaghetti lasagne tanayi sunata shan hira, saida ta gama snn tayi musu serving a bowl d'aya, tana tunkaro Batuul dashi dariyar dake fuskarta ta d'auke ta toshe bakinta, Farida tace "A'a meye hakan" da k'yar ta samu ta iya bud'e baki tace "kin saka cheese bana so", da mamaki Farida ta tsaya kallonta Dan tasanta da son cheese, sabida itama ta zuba tace "Cheese d'in ne ya saki kamar zakiyi kuka?", ta bud'e baki kenan zata yi magana taji amai na yunk'uro mata, da gudu ta sauk'o tayi sama, Faridan ma a guje ta ajiye fork d'in hannunta tabita a baya tana tambayarta ko lafiya?, saida ta gama kwarara amanta a toilet snn ta d'ago a galabaice duk batada k'arfi, Farida duk ta rud'e sai hawaye take  ta rasa yanda zatayi gashi ta baro wayoyinsu wancan gidan sabida tsabar masifan shi, kamo Batuul tayi daga toilet d'in ta wanke mata fuska snn suka fito, kan gado ta kwantar da Ita sai maida numfashi take, tashi tayi ta fita ta dafo mata noodles cikin lokaci kad'an, nanma Batuul turewa tayi tace batason kamshinshi, Farida duk ta damu tace "Besty wai mey ke damunki?, dama yana miki haka kuma yaushe kika zama allergic to cheese da har zai na saki amai",Batuul dai shiru tayi mata tana maida numfashi, a hankali kamar mai rad'a tace "Orange Juice zansha da Toast", da sauri Farida ta mik'e bata dad'e ba ta dawo riqe da abinda Batuul d'in ta fad'a mata, kad'an taci ta ture tace ta k'oshi, ta kwanta bacci, Farida kam kallonta kawai takeyi jikinta duk yayi sanyi, saida ta tabbatar baccin Batuul keyi sannan ta tashi ta sauk'a k'asa dan ta fara jin yunwa, sai a snn ta tuna da girkin da tayi musu, warming tayi ta tsiyayo juice tayi sama dashi, duk bayan seconds sai ta kalli Batuul ta tabbatar tana lafiya, Batuul kam Bacci takeyi sosai, lokaci lokaci takan bud'e ido suna had'a ido da Farida zata sakar mata murmushi taci gaba da baccinta abin har tsoro ya fara bawa Faridan, Har magrib Batuul bata tashi ba sai da Farida taga gari yayi duhu snn ta tada ta suyi sllh magrib, tana farkawa tace "Yaa Abu fa?, bai dawo ba?", Farida tace mata "Ehh", take mood d'inta ya canja ta had'e rai tayi toilet abinta, koda ta fito kin yin magana tayi, Farida har saida ta gaji dan kanta tayi shiru, Kallonta Farida tayi tana murmushi dan ta kasa daurewa da sudden behavior nan nata tace "uhnnm Besty ko dai Baby za a samawa Yayana ne wannan rashin lafiya haka?", kunya duk ya rufe Batuul tayi kicin kicin da fuska tace "Baby kuma, wani irin baby, Malaria nake ya kama ni", dariya maganan ya bawa Farida tace "Ko ba Malaria ba, ai 9ja muke dole kice Malaria kikeyi", bata kulata ba dan ita rashin zuwan Abu ke damunta, itama Faridan badan ta yadda ta k'yaleta ba, haka ta zama wata shiru shiru har goman dare tana tsammanin dawowanshi amma baizo ba har sha d'aya har saida Farida ta gane, shima Abu gaba d'aya hankalinshi na kan Batuul, gashi ta zama so choosy akan abinci duk hankalinshi ya tashi

        Washe gari da  sassafe ya fito lokacin Ajiddeh na bacci ya tafi can gidan, a d'aki ya tadda Batuul kwance, kallo takeyi amma gaba d'aya hankalinta baya wajen, da k'yar ta samu bacci ya d'auketa jiyan nan, gaba d'aya haushinshi takeji, d'auke kai tayi kamar bata ganshi ba taci gaba da abinda takeyi, hawowa yayi kan gadon ya d'agata cak yace "Wannan shariyan haka kuma fa? How is my baby?, ya fad'a yana shafa cikinta daidai nan Farida ta shigo riqe da d'an tray da glass cup a kai, had'e rai tayi ta k'araso ciki tareda gaisheshi, bai amsa mata ba saima harara da ya bita dashi, zumb'uro baki tayi tacewa  Batuul "Ga lemonade d'in" ta juya zata fita, kai Batuul ta kad'a mata kawai dan kunyan yadda tazo ta samesu ta ji" Farida na fita ya juyo da Batuul yace "Hey bana son wannan silent treatment d'in mana, shout and yell yafi min da wannan shirun da kikemin", kamar ba da ita yayi maganan ba ta sake d'auke Kanta, a hankali ya fara mata magana yace "Hear me out, kinga Ajiddeh ce fa batajin dad'i shiyasa ban dawo ba jiya", kuka ta fashe mishi da ta shiga turashi daga jikinta tace "ai ni lafiyar ce dani, ka koma wajenta tunda nata lafiyan yafi damunka", dariya ne ya k'ufce mishi ganowa da yayi kishi ke damunta, nan ta k'ara k'arfin kukanta, janyota yayi jikinshi ya rungume ya shiga lallashinta, da k'yar ya samu tayi shiru, sai wajen 10 d'in safe ya fita siyo mata abubuwan da ta lissafa mishi zataci ya fita ya samo mata, lokacin da ya dawo gida a parlourn k'asa ya tadda Farida zaune tana kallon Tv yace mata "Ammah tace min Monday zakiyi resuming school dan haka nanda kwana hud'u zaki koma", tace "Ehhh", har ya fara tafiya tace "Yaa Abu wayoyinmu a gidanka, dan Allah ka kawo mana, koh jiya haka Batuul tayi ta amai kuma na rasa wanda zan fad'awa dan babu waya", har ranshi yaji aman da Batuul tayi dan yasan tana wahala sosai amma yaqi nunawa ya dake yace "anqi a kawo d'in, da uban wani ne ya saki bari can?", ya haura sama ya barta nan zaune, kullum haka yakeyi da sassafe zai zo ya dubata har sai ya sata yin bacci yake komawa wajen Ajiddeh, Ajiddeh ma bata sake mishi maganan Batuul ba, ko tambayanshi Ina take batayi ba, Dan Mummy tace mata ta kwantarda hankalinta cikin kwana biyu za ayi maganin Batuul, Farida kuma ce mata yayi ta koma Nigeria.
          Bayan kwana uku ana gobe Farida zata koma da yamma Batuul na baccinta a d'aki ita kuma Farida na gefenta tana chatting da Affan d'inta sai murmushi takeyi abinta, a firgice Batuul ta farka tareda sakin k'ara, Farida dake gefenta ta mik'e a rude ta rik'ota tana tambayarta ko lafiya, kasa yi mata magana tayi sai riqe cikinta da tayi ta sulale k'asa tana yarfe hannu, hankali tashe Farida ta shiga neman layin Abutturab dan ko 2hrs baiyi da barin gidan ba, baccin ma da takeyi ajikinshi tayi snn ya kwantar da ita ya fita, kullum a rana yakan shigo sau biyar kuma da sassafe yake shigowa, watarana sai dai ta farka ta ganta a jikinshi, kwana ne kawai bayayi, kuka Farida ta fashe da ganin har ya katse bai d'auka ba, a karo na biyu ne da ta k'ira yana fara ringing ya d'aga, cikin kuka ta fad'a mishi abinda ke damun Batuul, bata gama ba ya katse wayan cikin tashin hankali, in few minutes ya iso kamar dama can yana area, a guje a ya hawo sama, ganin Batuul riqe da cikinta tanata murk'usu ya sake tada mishi hankali, nan ya rungumota ya shiga tambayarta mey ke damunta taqi cewa komai sai kukan da takeyi tana riqe da cikinta duk yanda yaso tyi magana batayi ba sai juye juye da takeyi, Shida Faridan duk hankalinsu tashe yake sosai, ganin sae gaba abun yakeyi duk ya rud'e, Farida daketa hawaye tayi k'arfin halin cewa Yaa Abu mu kaita asibiti Dan Allah kar wani abin ya sameta, sai lokacin tunanin Hospital ya fad'o mishi,  ko second d'aya bai k'ara ba ya d'auke ta cak yayi waje da ita, mota ya sata shima ya shiga yaja motar duk hankalinsa tashe, a gurguje doctors suka karb'eta suka shiga dubata, duk iya kwarewarsu sun nuna amma basuga komai ba, haka suka hak'ura suka yi mata allurar pain reliever suka k'ara mata ruwa Dan ganin yanda taji jiki ta jigata, har ta fad'a daga d'an lokacin nan, likitocin na fita ya taso ya rungumeta yana sake tambayanta ta fad'a mishi inda ke mata ciwo, duk yanda yayi da ita k'in cewa komai tayi sai kukan da take tana juye juye, iyakar rudewa ya rude, Farida har fuskarta ya kumbura tsabar kukan da tasha, shikam ji yakeyi kamar ya cire mata ciwon ya dawo dashi jikinsa, Farida ce ta matso gaban gadon ta riqe hannunta d'aya ta shiga tofa mata addu'a a hankali, ta kusa minti sha biyar tana mata addu'a, ko Abutturab baisan abinda takeyi ba, a hankali ta fara tsaida kukan da takeyi jin ta fara samun relieve har dai tayi shiru tayi lamo jikinsa tana sauk'e numfashi, a hankali ya d'ago kanta yana kallon idonta da ya kumbura tsabar kukan da tasha, cikin sanyin Murya yace "Fatima don Allah tell me mey ke damunki, ina ke maki ciwo?",  kyar ta iya bud'e baki tana nuna masa cikinta tace "cikina kemin wani iri", rungumeta yayi tsam jikinshi kamar wacce za a k'wace ya dinga rad'a mata sannu a hankali.Tana nan rungume jikinshi har tayi bacci, a hankali yaji numfashinta na sauk'a kad'an kad'an alamun baccin nata ya fara nauyi, ajiyar zuciya ya sauk'e amma har lokacin tana nan kwance jikinshi bai kwantar da ita ba, sai bayan 15mins snn a hankali ya d'an d'agota daga jikinshi ya kwantar da ita kan gadon, kallon k'aramin cute face d'inta ya tsaya yi yana lumshe ido, ciwon rana d'aya amma duk ta fad'a ta rame, dama can ba wani jikin bane da ita, sai haske da ta k'ara, yafi five minutes idonshi na kanta daga baya ya d'auke idanunshi ya sauk'esu kan Farida dake tsaye gefe duk tayi sanyi yace "Taci wani abune bayan na fita?", kai ta girgiza mishi a hankali tace "Babu abinda taci, ko baccin daka sa tayi ma fa bata tashi ba, kawai ina kwance naga ta mik'e ta riqe cikinta, shine tace yana mata ciwo ne", kallon Farida kawai yakeyi har tayi shiru snn yasa hannu cikin gashin kanshi masu santsi  ya bajesu yace "take care I will b right back", daga haka yayi exiting d'akin, har ya dawo bacci Batuul keyi, Farida na zaune kan kujera ta jingina kai ta baya ta tsura ma Batuul idanu, tausayinta kawai take cikin ranta, ji takeyi kamar ta fasa komawan gobe ko kuma su tafi tare, motsin k'ofan da taji ne yasata duban wajen, Abuturrab ne ya shigo riqe da paper bags a hannyenshi har ya k'araso cikin d'akin snn Farida ta miqe tana mishi sannu da zuwa ta anshi kayan dake hannun nashi, zama yayi daga kan kujeran idonshi nan kan Batuul d'in, sai da Farida tace mishi sannu da zuwa yaya snn ya dubeta ba tareda ya amsa ba ya jeho mata tambayar "Ta tashi bayan na fita?", kai ta kad'a mishi tace "No! Bata tashi ba, baccinta takeyi tun d'azu" bai ce komai ba ya juya ga kallon Batuul d'in da yakeji kamar ya cire mata ciwon gaba d'ayanshi ta huta, hannunta da babu drip ya kamo cikin nashi ya rik'e gam yana jin wani feeling na circulating dukkanin nerves d'inshi, a hankali ya juyo ya dubi Faridan yace "Kinci abinci ne?", ta kad'a mishi kai alamar a'a, yace "gashi nan ki duba packs d'innan", yayi mata nuni da bags d'in da ya shigo dasu, bags d'in ta janyo ta shiga bubbud'esu, tab'e baki tayi ganin irin abincin da ya siyo musu, ita bata cika son jagwalgwalon turawa ba, daga k'arshe dai pasta with Lamb ragu da cauli flower crisp ta ciro ta ajiye gefe, kallon Abu tayi tace "Yaa Abu in ciro maka?", kamar me  nazari yake kallonta snn ya girgiza mata yace "No am okay", batayi mishi musu ba ta koma kan kujera ta shiga cin abincinta, sai da ta gama tayi disposing packs d'in yace mata ta mik'o mishi ruwa, Fridge d'in d'akin ta bud'e ta mik'o mishi bottle d'aya bayan ta bud'e, har lokacin hannunshi na cikin na Batuul, yana jin yadda pulses d'inta ke kaiwa da komowa, basu fi thirty minutes ba bayan nan ta bud'e lumsassun idanunta a hankali, kanshi tafara sauk'esu, ido ya wara shima ya matso kan gadon ya d'agota sai ji tayi ya rungumeta jikinshi, ya kai minti biyu rungume da ita bata yi k'ok'arin k'wace kanta ba har saida ya saketa ya d'ago hab'arta yace "Ina ke miki ciwo yanxu Fatima?", murmushi tayi mishi kawai ta shiga k'ok'arin tashi ta zauna, da kanshi ya d'agata ta zauna yana making sure bata takura ba, ganin yanda Farida ta tsaya tsuru tana kallonta ya bawa Batuul dariya, tace "Hey what's up duk kin zama wata iri, am okay fa", murna ne ya cika Faridan tayi maza ta dawo kan gadon ta zauna, tace "Don't get sick pls, you scared d hell out ta me pls kinji?" murmushi tayi kamar ba ita ke ciwo ba d'azu snn ta kalli Abu da yake lumshe ido yana bud'esu yana kallonta ta d'an shagwab'e fuska tace "Mu tafi gida Yaa Abu, ni bana son asibitin nan", kai ya girgiza mata yace "No sai kin fad'amin mey ke damunki, baza mu tafi ba bamusan mey ke damunki ba", had'e rai tayi tace "Yaa Abu nifa na warke, mu tafi gida", ta fad'a tana k'ok'arin sauk'owa kan gadon, hannunta ya rik'o ya k'ura  mata hazel brown idanunshi, cikin wani irin murya yace "Fatima mana, I want you to fully get better, bana son kina shan wahala kamar na yau, nafiso ki zama under medication, under proper care kinji?", zumb'uro mishi baki tayi tace "Toh fa na warke ni, bazan sake yin rashin lafiyan ba", Ido kawai ya zuba mata yanason ta gano abinda yake hange amma baya son stressing d'inta tunda ba isasshen lafiya bane da ita, a sanyaye yace mata "ina zaki yanzun?", ta zumb'uro mishi baki tace "toilet", da  sauri Farida ta mik'e ta riqota tace muje in rakaki, kai ta kad'a tace "zanfa Iya da kaina na warke", kamar jira yake ta rufe baki ya sunkuceta yayi toilet da ita itako sai wuntsila k'afa takeyi ya sauk'eta, bai bi ta kanta ba har saida ya Isa toilet snn ya ajiyeta a hankali, d'an murgud'a mishi bakin tayi snn ta kalleshi tace "Toh ka tafi", wani irin kallon da yayi mata yasata yin shiru ta kasa motsi, ganin ta nemi waje ta tsaya yasashi k'arasawa gabanta ya shiga k'ok'arin d'age mata skirt d'inta, ihu ta fasa ta riqe skirt d'in da k'arfi tace "Bafa komai zanyi ba, alwala nakeson yi", kallonta kawai yakeyi snn ya kamata suka koma gaban hand wash basin d'in, kamar wata yarinya shi yayi mata alwalan, bags d'in da ya shigo dasu ya janyo bayan ya sata ta zauna kan gadon, pack d'aya ya Ciro mai d'auke da malted custard roast da Lamb Kebab salad, da kanshi ya bata abinci har saida tace ta k'oshi snn yace tayi sllhn shi kuma ya fita wajen doctor yayi maganan discharging d'inta, bai jima ya shigo lokacin har ta idar da sllh suna hiransu da Farida, ce musu yayi zasu tafi, murna Batuul ta shiga yi dan ta tsani asibiti ita kam, da murnarta ta shige gaba kamar ba ita aka kawo a galabaice ba, driving yakeyi amma duk bayan seconds biyar sai ya juyo ya dubeta, cikin lokaci kad'an suka isa gida lokacin ana k'iran Magrib,saida sukayi sllh snn suka kafa hira ita da Farida, ganin ya shigo d'akin yasa Farida fita, daidai tazo wuceshi yace " You should Get ready gobe flight d'in by 8 ne", sai a lokacin Batuul ta tuna da tafiyan Farida, jiki a sanyaye ta amsa da "toh", sam hankalinta bai kwanta da barin Batuul ba gashi shi bama zama yakeyi ba, cikin d'akin ya k'araso ya zauna bakin gadon yana kallon Batuul da har idonta ya cicciko yace "How you feeling now?", baki ta bud'e zatayi magana hawayen dake tare idonta ya shiga gangarowa, har ranshi ya ji zubowansu da hanzari ya gyara zamanshi kan gadon ya rungumota tareda cewa "Yasalam, Fatima what is it again?, I told you mu zauna asibitin amma kikayi insisting mu dawo gashi nan yana damunki kuma koh", ji yayi ta sake lafewa jikinshi a hankali tace "Does she have to leave tomorrow?", sai da ya tsaya for some seconds snn ya gano abinda take nufi, ajiyar zuciya ya sauk'e jin ba ciwon cikin nata bane ta d'ago kanta yace "School zata koma, dama mid semester break ta zo", a hankali ta d'ago ta dubeshi tace "toh ni yaushe zaka kaini gidan, I want to go home" muryarta na rawa ta kare maganar, rungumota ya sakeyi jikinshi yana shafa kanta yace "very soon, ko har kin manta deal d'inmune?, ba nace zan kaiki gida da kaina ba in kika haifa min baby na", d'an zumb'uro baki tayi jin ya ambaci Babyn shi ta kauda kanta, murmushi yayi tareda juyo da kan nata, idonshi kan lips d'inta yace "I like them when you pout, I miss them so much", kamin ta ankara har kai nashi lips d'in kan nata, passionately yake kissing d'inta kamar yau ya fara kissing d'in nata idonsa lumshe, haka yayita tarairayarta har wajen sha d'aya bayan yayi mata wanka ya jasu Sllh Isha ya kwantar da ita ya shiga sata bacci, a jikinshi tayi baccin wajen 11:30, saida ya tabbatar tayi nisa a baccin tukunna ya saka mata temperature d'in d'akin ya koma moderate, ya tabbatar she is fine snn ya fita, a parlourn k'asa ya tadda Farida ta kashe wutan ko ina tana kallon CBS, Ce mata yayi ta koma d'aki gun Batuul snn yayi mata sai da safe ya fita akan gobe da safe zaizo kaita airport ta zama cikin shiri, sai da ya shiga mota tukunna ya tuna da wayoyinsa, missed calls ya gani babu  adadi daga mutane daban daban amma duk na Ajiddeh yafi yawa, d'an murza goshinshi yayi snn yayi igniting motar ya d'au hanyan gida, lokacin da ya isa Ajiddeh na kwance parlour tayi bacci  da alama tasha kuka ba kad'an, tausayinta yaji Sosai har cikin ranshi yasan bai kyauta mata ba, kashe appliances d'in yayi snn ya dawo ya d'auketa yayi sama da ita+

       Washegari kamar kullum da ya tashi sllh saida ya tashi Ajiddeh amma bata tashi ba, shi kam daga masallaci d'ayan gidan ya wuce, a kitchen ya taddasu su biyun duka Farida har ta shirya, k'arasowa yayi cikin kitchen d'in yana amsa gaisuwan Farida ya isa inda Batuul ke jingine jinkin Fridge, yana zuwa ya jawota jikinshi ya d'aura hannunshi kan mararta a hankali, da sauri ta d'aga ido taga ko Farida na kallonsu, ai kuwa ido hud'u sukayi da Faridan, maza tayi ta d'auke idonta cike da kunya snn ta riqe mishi hannu, rankwafowa yayi daidai wuyanta da muryan shagwab'a da ya sauqe mata kasala gaba d'aya yace "Ina duba Baby na", cike da jin kunya a hankali tace "Yaa Abu Farida fa na nan" kallon Faridan yayi, suna had'a ido ya sakar mata wani irin kallo, babu shiri ta bar abinda takeyi ta rage wutan stove d'in tayi waje da sauri, tana fita ya juyo da Batuul d'in, y'ar rigar dake jikinta ya d'age ya shiga making circles a flat tummy d'inta da yasata jin wani sabon feeling na daban na ratsata, a hankali yace mata "Meh zaki bawa Farida?", sai lokacin abin ya fad'o mata d'ago kai tace "Nima ban sani bafa, kawai zan bata kosu bracelets d'ina ko?", ta tambayeshi, murmushi yayi ya janye hannunshi cikin rigan nata ya kamota yace "muje ki gani sai ki duba ki ga In yayi a bata", babu musu ta bishi a baya suka fita waje, Farida na ganin fitansu ta koma kitchen taci gaba da abinda takeyi tana murmushi cike da jin dadin irin xaman Bestyn nata da yayanta, suna shigowa daidai nan Faridan ma ta fito riqe da bowl d'in oat a hannuta tana jujjuyashi, a nan ya bar Batuul ya haura sama, ba a jima ba ya sauko yace su wuce, cikin y'an minutes suka isa airport, sai lokacin Batuul ta dad'a tabbatar da tafiyan Farida, kamar kar su rabu harda k'wallanta, k'ok'arin fitowa ta shigayi daga motan zata raka Farida yayi maza ya rik'ota yana kallonta yace "Ina zakije haka?" , zumb'uro mishi baki tayi cike da shagwab'a tace "zan rakata mana", kai ya girgiza yace "kinada hankali zaki fita a haka ko mayafi babu?, dubi kayan dake jikinki?", kallon kanta tayi taga koh kayanta are, wandone jikinta sai jacket iya gwiwa da hood amma yake fad'a mata wai kada ta fita a haka, rai b'ace ta koma ta kwanta sai Faridan ce ta zagayo tayi hugging d'inta, dan takaici kasa magana tayi sai hawaye da ta dinga yi, shi ya d'auki jakan tsaraban ya rakata dashi yace mata inji Batuul, ya k'ara mata da kud'i masu yawa, har saida yaga ta shiga jirgi sannan ya juyo, a mota ya tadda Batuul har tayi kukanta ta gode Allah, ko sau d'aya bata kalleshi ba bayan ya dawo, haka ya k'arashi surutunshi suka isa gida, yana parking ta bud'e mota ta fita a guje, a gujen shima ya bita dan har ranshi yakejin gudun nata snn gashi ba lafiyane da ita isasshe ba,  daidai takai k'afanta kan 5th stair case ya cimmata, wani razanannen k'ara ta saki da yasata durk'ushewa k'asa, binta yayi ya kamota jikinshi yana mata wani irin kallo yace "Fatima ban hanaki tsalle ba?, bakida hankali koh?, next time you try this shit I will slap you", gaba d'aya bata sanma mey yake fad'i ba sai yarfe hannu da takeyi, kuka sosai ta shiga yi tana k'iran sunan Auny tana riqe da cikinta, rud'ewa yayi ganin da gaske take ya d'agota yace "Batuul talk to me, cikin ne?", a hankali ta shiga gyad'a mishi kai a wahalce, duk ya rasa mey ma zaiyi dan duk ya rud'e, cak ya d'auketa sukayi asibiti, ikon Allah ne kawai ya kaisu lafiya dan baisan irin driving d'in da yayi ba, likitocin this time ma cikin gaggawa suka amsheta, sai kukan wahala take tana k'iran sunan Aunty, har dare likitocin na kan Batuul sun kasa gano Ina matsalar take gashi duk wani taimako da zasuyi sun mata shi amma babu wani ci gaba, Abu kam tsayawa kawai yayi yana kallonsu ya kasa cewa komai, kamar shi ke ciwon har fad'awa yayi daga yini d'aya. Sai karfe takwas da wani abu na daren bacci ya dauketa shi ma sai juye juye take, Abuturrab dake xaune gefenta ya tsura mata ido cike da tausayinta ganin yanda ta wani rame daga safen xuwa dare, mikewa yayi da kyar ya nufi office din likita, nan ya shaida ma likitan in dai cikin xai bada matsala kawai a cire sa, ficewa yayi daga office din ya nufi gida kafin ta tashi don dauko wayarsa, Ajiddeh na xaune parlor kamar ko da yaushe, yau dai sai ya gaya mata ma'anar fitar da yake da asuba ko sallama babu baxa kuma ta kara ganinsa ba sai dare, bin sa da kallo tayi ganin ko kallonta bai yi ba ya haura sama, mikewa tayi ta bi bayansa, xaune ta samesa gefen gado, da ganinsa kasan akwai matsala, ta karaso da sauri ta xauna gefensa tace "Me ya faru babe? What's wrong?" Rike kansa yayi bai ce komai ba, ta dago kansa tace "Talk to me mana, me ya faru" Da kyar ya iya bude baki yace "Batuul!" Ji tayi kamar ya soka mata mashi, lokaci daya xuciyarta ya shiga tafarfasa, ta dake tace "What about her?" Cike da confusion yace "I just don't know, tana asibiti" wani farin ciki ya lullube Ajiddeh, sai dai cike da damuwa kamar gaske tace "Ayya, Allah ya bata lafiya" mikewa yayi da kyar ya dau wayarsa xai fita, tace "plss xan bi ka muje in dubata babe" bai tanka ta ba ya fita, ta mike cike da murna ta dau hijab ta sa ta bi bayansa da sauri, har ta shiga motar bai ce mata komai ba ya tada suka kama hanyar asibitin, ba karamin tashi hankalinsa ya kuma yi ba ganin likitoci a kanta, su Ajiddeh kamar na kirki ta dinga kwantar masa da hankali wai she will be fine. Likitocin na fita ya shiga Ajiddeh na biye da shi a baya, rungumeta yayi ta kankamesa tana kiran sunansa cikin kuka, a rikice yace "Don't worry Fatima xa a cire babyn ki huta kin ji" girgixa masa kai kawai take tana kuka sosai, Ajiddeh ta xauna gefenta tana mata sannu, rike hannunta Batuul tayi ta fada kanta tace "Wayyo Mutuwa xan yi Anty ki taimake ni cikina" shiru Ajiddeh tayi tana kallonta lokaci daya jikinta yayi sanyi jin ta ambaci mutuwa.A hankali Ajiddeh ta shiga girgixa kai da kyar tace "No! Baxa ki mutu ba, Allah xai baki lafiya kin ji" Abuturrab da ya gama rudewa jin abinda tace ya rike hannayenta yace "Noo no baxa ki mutu ba Fatima, don't worry xa a cire babyn ki huta, bana so kuma, xa a cire soon kin ji, kar ki kuma cewa xa ki mutu plss" ko kadan Batuul bata san abinda suke cewa ba don ita kadai tasan abinda take ji a lokacin, tayi wani kara da ya kuma rudar da Abuturrab da Ajiddeh tace "Don Allah Anty ki ce ya kai ni gun Antyna nasan mutuwa xan yi, wayyo cikina" Abuturrab ya rungumeta a rikice yace "Stop this Fatima, ki daina kiran mutuwa plss" hawaye ne ya ciko idonsa yace "No! Baxa ki mutu ba wife, baxa ki mutu" Ajiddeh da duk jikinta yayi sanyi ita ma ta shiga hawayen a hankali tace "Baxa ki mutu ba, Allah xai baki lafiya" mikewa tayi da kyar ta fice daga dakin, ta tafi nesa da ward din, layin Mum dinta ta shiga kira, bugu uku aka daga, bangaren Mum tace "yauwa 'yar gari dama yanxu nake kokarin kiran ki, ya ake ciki kin ga alamar...." A sanyaye Ajiddeh ta katse ta tace "Mum kinsan me? don Allah kice a dakatar da aikin nan tukun....." Cike da mamaki Mum tace "A dakatar da aiki? Saboda me?" Da kyar Ajiddeh muryarta na rawa tace "Mum kinga fa kila mutuwa xata yi, kuma..." Sai ta fashe da kuka tace "Mum ni dai a dakata tukunna....." Wani uban ashar mum ta kunduma mata a fusace tace "Shegiya sallamammiya, kin san nawa na kashe 'yar abu kaza kaza, a dakatar da aiki??? Wani irin zagi Mum ta kuma k'undumo mata da har saida ya tsorata ta, a fusace ta diro daga kan gadon da take cikeda masifa tace "Keh kinsan mey kike cewa? to kinyi kadan Ajiddeh, a xuri'armu bbu warce ta taba zama da kishiya, baxa kuma a fara a kan 'yar cikina ba,  Aliyu naki ne ke daya don ubanki, Ajiddeh cikin kuka tace "Mum nifa bance zan zauna da ita ba, kawai dai  bana son ta mutune", Fusata Mummy ta sakeyi har wani gumin masifa ke tsattsafo mata a goshi, rai a b'ace tace "keh don ubanki ki fita idona kinaji, shegiyar yarinya da bata san abinda takeyi ba, zur'armu kaf babu wacce ta zauna da kishiya, mey ma za ayi da zama da kishiya, Allah bai d'aura mana ba kema kuma baki zama da ita, ita da take gantalalliyar kishiya ma har aka munafurce ki akayi komai shine kike tausayinta, indai ni haifeki kika kuma tausayin yarinyar nan sai. na tsine dan haka in zaki dawo hankalinki tun wuri ki dawo kisan inda dare yayi miki, wawiyar yarinya kawai, kina abu sai kace bani na haifeki ba, K'anwar uwarki ce yarinyar da zakice mituwa zatayi ko kuma in ta mutun asara ne dake,   mutuwa kuma kamar tayi shi daga ita har shegen dake cikinta, kaji min wahalalliya mara wayo, to kin yi k'adan yanxu ma shiri nake xan koma kauyen don ba a gama aikin ba" Ajiddeh ta fashe da kuka sosai tace "Allah mum ni dai ba ruwana, kar ta je ta mutu...." Wani raxanannen tsawa Mum ta daka mata ta dinga kunduma mata zagi  tace ", Ajiddeh ta katse wayar ta jingina da bango hawaye na sakko mata, da kyar ta ja kafa ta koma ward din, hankalin ta ya kuma tashi ganin halin da Batuul ke ciki, likitoci biyu a kanta, karasawa tayi da sauri ta xauna kusa da ita jin abinda take ta cewa, ta rike hannunta hawaye na sakko mata tace "Baxa ki mutu ba, sai lokacin ki yayi" Abuturrab dake xaune ya rike kai ya d'ago da kyar yana kallonsu da idanuwansa da suka kada, ya karbi wayar Ajiddeh don bai ma san inda nasa yake ba, ya fita don kira Ammah shi da likitocin xa su ji ta nasa da an cire cikin a nn take kawai amma sun ki wai sai bayan awanni idan suka gama binciken da suke, rungume Batuul Ajiddeh tayi, sai ce mata take cikinta, dubara ne ya fado ma Ajiddeh ta shiga tofa mata addu'a a hankali, Abuturrab na fita ya kira Ammah, tana d'agawa ya kasa ce mata komai, tayi sallama yayi uku kafin da kyar yace "Ammah, Batuul...." Jin muryarsa Ammah tace "Abuturrab, lafiya me ya faru" da kyar ya kuma cewa "Batuul..." Nan hankalin Ammah ya tashi ba kadan ba tace "Kayi min magana mana Aliyu, me ya samu Batuul din" k'asa bata amsa yayi hawaye na sakko masa, nan hankalin Ammah ya kuma tashi barin da taji yayi shiru kuma tasan hawaye yake shirun nan, don ita ta haifi abunta, tsawa tayi masa tace "Kana da hankali kuwa Aliyu, baxa ka fadi abinda ya samu Batuul din ba" da kyar ya bude baki yace "Bata da lafiya ne" tayi kokarin boye tashin hankalinta tace "Subhanallah! Tun yaushe?" Yace "jiya" sosai hankalinta ya tashi don tasan ba abu kadan bane Abuturrab xai ma hawaye, tace "Me ya sameta?" Ya girgixa kai bai ce komai ba, Ammah tace "ka bude baki ka min magana Aliyu, farida fa?" Da kyar ya iya cewa 'Daxu na Kai ta airport " Ammah tace "Dawo min da ita immediately" "toh" kawai ya iya ce mata ta katse wayar hankali tashe tayi part din Abui. Juyawa yayi ya koma ward din, har lokacin Batuul na jikin Ajiddeh idonta lumshe, sai dai a hankali take kukan yanxu sai ajiyar xuciya da take saukewa jin kamar an xare mata ciwon, ita ko Ajiddeh bata fasa to fa mata addu'a ba, don bata ma san Abuturrab ya shigo dakin ba, tsaye yayi jikin bango yana kallonsu hankalinsa ya d'an kwanta ganin Batuul ta nutsu, karasawa yayi gun gadon ya xauna gefensu ya kamo hannun Batuul yana kallonta, a hankali ta bude rinannun idonta tana kallonsa, Ajiddeh ma ta juya tana kallonsa, kauda kai Batuul tayi, murya can kasa tace ma Ajiddeh xata je bayi, Ajiddeh ta mike ta d'agata ya bi su da kallo har suka isa bayin, a nan bakin kofa Ajiddeh ta jira ta tafito ta kuma kama hannunta suka koma kan gadon, A hankali Abuturrab na kallon Batuul yace "Ya daina cikin?" Kai kawai ta gyada masa, ya kalli Ajiddeh yace "We are leaving for Nigeria gobe" ita ma ta gyada masa kai kawai. Wayarta ne ya shiga ring a hannunsa ya mika mata ta karba ta ga Jainaba ce, gabanta ya fadi ba kadan ba taki d'agawa ta ajiye, ta juya tana kallon Batuul da ta rufe ido har bacci ya fara daukanta ta ci gaba da mata addu'a a xuciyarta, Abuturrab ya mike ya fita, ba a dau lokaci ba ya dawo, yana kallon Ajiddeh yace "Xa a cire cikin yanxu, it's time" Ajiddeh tayi shiru tana kallonsa sai kuma tace "saboda me?" A hankali yace "She's suffering babe" girgixa masa kai tayi duk da wani abu da taji ya tokare xuciyarta tace "No! Allah xai bata lafiya a bar mata" a sanyaye yace "A'a gwara a cire mu samu rest of mind" da kyar Ajiddeh tana kokarin maida hawayenta tace "if dat's ur only child or hers a duniya fa," d'an murmushin karfin hali yayi yace "baxan iya jure ganin tana wahala haka ba, ke kya haifa min masu yawa idan Allah ya yrda" duk yanda Ajiddeh ta so convincing dinsa a bar cikin kin yarda  yayi, mikewa tayi daga karshe ganin da gaske cire cikin xa ayi, ta dau wayarta ta fita, Ammah ta kira yana fara ringing ta d'aga, sama sama Ammah ta amsa gaisuwarta don tun kiran Abuturrab bata da nutsuwa barin da ta kira can Maiduguri taji ciwon Batuul har da sa hannu, Ajiddeh da ta ma rasa abinda xata ce a hankali daga karshe tace "Ammah dama wai Batuul ce ba lafiya kuma laulayi take, shine Aliyu wai a cire cikin nayi masa magana ya ki saurarata" tana maganan ne da kyar don wani tukuki take ji a xuciyarta ta rasa dalili, a dakile Ammah tace "Toh don uwarsa tunda bashi da hankali ba sai yasa a cire ba muga, wawa da shi ba xai rike addu'a ba an tasa shi da iyalinsa a gaba sai haukan banxa shi d'an boko, ni ban taba gani soko mara wayau kamar Aliyu ba, kuma yana tare da wahala in har baxai rike addu'a ba, Batuul kuma ta Allah ba ta mutane ba, bbu abinda xai sameta sai Wanda Allah ya rubuto mata, babu abinda aka isa ayi mata, ciki kuma sai ta haifesa lafiya idan Allah ya yrda, ki bani gantalallen" jikin Ajiddeh yayi sanyi ba kadan ba lokaci daya hawaye ya cika idonta ta ja kafa da kyar ta koma ward din ta mika ma Abuturrab wayar, hannu yasa ya karb'a batareda yasan ko waye ba ya kara wayan  a kunnenshi

Post a Comment for "BATUUL CHAPTER 18"