Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

BATUUL CHAPTER 16

BATUUL CHAPTER 16

- - Post a Comment
BATUUL
CHAPTER 16


Wani mugun kallo yake yi ma Farida yace "kin wuce kin bar nan ko sai na zo na sameki, are you stupid ku ke min ihu haka a gida", duk da tsoron da taji hakan bai hanata dakewa tayi kamar ba da ita yake kamar ba, ta d'aga kai ta kalli su Ajiddeh da ido ya k'ank'ance da masifa, harara ta galla mata daga haka ta kuma maida dubanta kan Batuul tana washe baki tace "keh kin ga gashinki kuwa yadda ya wani dad'a cika yayi tsawo, meye sirrin 'yan mata, sea foods da salads kike ci ne? Kai Amma gaskiya gidan Yayana ya......", bata k'arasa ba taga yana tunkarosu, hanjin cikinta ne suka kad'a ganin haka, Batuul kam ko a jikinta sai dariya take, yana zuwa yasa hannu ya fincikosu a tare yayi hanyan stairs yana rik'e da hannunsu, ko lura da Ajiddeh da yayarta bai yi ba a sama, Batuul ta finciketa nata hannun daga rik'on da yayi mata ta tsaya cike da masifa tace "meye haka kake wani jana kamar igiya, ni nace maka inason zuwa sama ne?", da mamaki ya tsaya kallonta da har bai san lokacin da ya sake hannun Farida ba ta sulale a guje tayi sama abinta tana 'yar dariya, abubuwane kawai ke mishi yawo a kai, badai har yarinyar nan ta raina shi ba, ita kanta Ajiddeh da yayarta sakin baki suka yi suna kallonsu, juyawa Batuul tayi zata tafi ya fizgota gabanshi yana kallon fuskanta yace "Are you stupid?, ni kike ma magana haka, are you out of ur senses?" sauk'owa Ajiddeh ta shiga k'ok'arin yi daga saman da take tsaye dan bataji zuciyarta zata iya jure wannan abinda take gani gabanta, Aunty Jainaba ce tayi saurin riketa a hankali tace mata "keh shashasha tsaya, ki bari muga iya gudun ruwansu, ai inaga ma lokacin maganinta yayi a gidan, kema dai kinyi sakaci, meye na barin budurwa haka a gidanki", da mugun kallo "Ajiddeh ta dubi Jainaba tace "dalla can toh da duk abinda nake gaya muku Kun zata wasa nakeyi, toh yau koma menene, k'arshen xamanta yazo wllh" Batuul kam turashi ta shiga yi tana murgud'a d'an k'aramin bakinta tace "Ni ka rabu dani", duk wannan abinda sukeyi baisan su Ajiddeh na sama ba, matseta yayi jikinshi ya murd'a mata hannu yace "sai kin fad'a min sudden change of behavior nan naki, wato na fara miki wasa shine zaki rainani", had'e rai tayi hawaye taf idonta ta turashi daga jikinta tace "Ni kam ka sakeni", sauk'owan da yaji ana yi daga stairs ya sa ya daga ido da sauri, Ajiddeh ya gani tana sauk'owa furiously, with full rage a fuskanta, tura Batuul d'in yayi yana mata mugun kallo yace "b'ace min daga nan", juyawa tayi a fusace ta nufi stairs, karo suka kusa yi da Ajiddeh ta koma baya da sauri ta raba ta gefenta xata wuce, a zuciye Ajiddeh ta fincikota ta hade ta da bango tana huci tace "Keh dan ubanki nayi miki kama da sa'ar uwarki da har zaki dinga min isa a gidana, to wllh xaman ki ya kare yau a gidana yanxun nan kuma ba sai anjima ba" turata Batuul tayi tace "kar ki sake ki sake gigin tab'ani wllh, zagi kuma wannan training din da aka maki kenan gidan ku, banida time d'inki", da haka ta juya ta haura sama ta bar ta nan tsaye, kwalalo ido jainaba tayi, Ajiddeh kam mutuwar tsaye tayi gun ta kasa kwakkwaran motsi, bata tab'a tunanin Batuul zata iya yin abu kamar wannan ba, a zuciye ta k'araso wajen Abu har wani rawa jikinta ya shiga yi sai hargowa take tace "Aliyu wlhy wlhy, kadai ji na rantse koh, toh yarinyar nan sai ta bar gidan nan yanxun nan, in kuma bata bari ba ni zan bar maka gidanka, ai dama nasan wannan kareta da kakeyi duk sabida kana samun wani abun gunta ne, wa ya sani ma ko zagayawa kakeyi gunta da daddare zaman dadiro kakeyi da ita, in ba haka ba, yaushe har zata rainaka ta rainani, dubi yanda ka wani rungumeta yanxu, ni za a rainawa hankali a wani ce karatu tazo yi, toh koma meye ta zo yi ni bazan zauna da ita gidan nan ba , kuma in ba karuwanci takeyi ba Meye ma'anar aman da naga tana kwararawa jiya kamar mai ciki, ko daxu sai da naji kakarin amanta har sau biyu a daki, ohh wato karuwa ka kawo min gida ka.....", bata k'arashe maganan ba ya d'aga hannu ya sharara mata mari da ya gigitata, har Aunty Jainaba saida taji tsoron jin irin marin, Aunty Jainaba ce tayi saurin saukowa ta rufe mata baki tace "ke don uwar ki Meye haka kike yi, yaushe ne zakiyi hankali Ajiddeh, jibi fa irin maganganun dake fitowa bakinki, mijin naki kike yiwa magana haka?, dama bakida hankali ashe", tana yi tana k'iftawa Ajiddeh ido tayi shiru, fincike hannunta tayi daga rik'on da yayi mata, idonta har ya canza kala duk ya k'ank'ance hawaye na xuba idonta tace "ai ka mari aurenka Aliyu, akan gantalalliyar y'ar iskar nan kake mari na, ai ba sai ka mareni ba zansan mey ke tsakaninku, kuma yau zan bar maka gidanka", ta juya fuuuu tayi sama, Aunty Jainaba ce ta kwantar da murya tace "Aliyu ashe haka kake fama, ai ni ban tab'a sanin haka yarinyar nan take mara hankali ba, Dan Allah kayi hak'uri ba sai ka daka ta tata ba, kasan hankalinmu ba d'aya da naku ba, kayi hak'uri kaji?, zanje yanzu in ci uwarta, Allah ya k'ara maka hak'uri", kasa cewa komai yayi tunda yaji abinda Ajiddeh tace "wai cikine jikin Batuul, ciki kuma? toh wane irin ciki", a hankali ya maida dubanshi kan Aunty Jainaba yace "Ba komai", da haka ya barta nan tsaye ya haura sams, d'akin Batuul ya wuce kai tsaye, bud'e k'ofan d'akin yayi ya shiga rai a had'e, Farida dake zaune tana ta zuba bata san lokacin da ta fasa ihu ta mik'e tsaye daga kan gadon ba tana yarfe hannaye, sau d'aya Batuul ta kalleshi ta d'auke kanta tana kallon Farida tace "Keh wai meye haka kika hau gado kina wani tsalle, ko ce miki akayi bouncing castle ne?", kallonta Farida tayi sannan tayi mata nuni da Abu dake k'arasowa cikin d'akin da baki, kallonshi tayi ta tab'e baki tace "toh mey zai miki?", fuska a daure yana kallon Farida yace "get down", sake matsawa tayi jikin gadon tace "Dan Allah kayi hak'uri Yaa Abu, bazan sake ba", k'arasawa yayi bakin gadon ya fizgota yana mata mugun kallo, ihu ta fasa ta rintse ido tana jiran jin sauk'ar mari, "ni nayi kama da sa'an ko koh? all those warning I made clear to you basu shigeki ba?", a hankali ta bud'e idon jin bataji sauk'ar mari ba, kamar munafuka tace "Yaa Abu nifa bance komai ba, kawai cewa nayi ai ka Iya reno, Batuul tayi kyau", tsaki yayi ya hankad'ata har sai da ta fado daga kan gadon yace "Baxa ki kwana min a gida ba yau"+

STORY CONTINUES BELOW


Ajiyar zuciya Jainaba ta sauk'e a fili ta furta "Lallai da aiki a gabanmu", sannan ta juya ta haura saman itama, a bakin k'ofa sukaci karo da Ajiddeh janye da akwati, da mamaki take kallon Ajiddeh sannan ta riqe akwatin tace "Keh meye hakan?, ina zaki da akwati", Ajiddeh tace "kema in zaki tattaro naki ki d'auko kizo mu wuce dan ni na gama zaman gidan nan indai wannan bak'ar yarinyar tana nan, ni wlhy right from day one ba santa nakeyi ba, bare yanzu da tazo ta tare take zama min a gida, gashi har wata suka k'aro mishi dan munafurci da sa ido", kuka sosai ta fashe da, Aunty Jainaba ta ja ta suka koma dakim ta zaunar da ita, Fridge ta bud'e ta mik'o mata ruwa, ta sha sannan ta karb'a ta ajiye tace "ashe keh bakida hankali ban sani ba Ajiddeh, ashe ba da kai kike tunani ba?", kallonta Ajiddeh tayi hawaye na sakko mata tace "ban gane ba", zama itama Jainaban tayi daga gefenta tace "Gashi ko kin nunamin alamu, in banda rashin hankalinki ina kika kinkimi akwati zaki da?, wa yace miki ana yiwa namiji haka bare wannan mijin naki d'an isa da kallo ma mutane basu isheshi ba, kina gani fa ko kunyata baiji ba ya sharara miki mari, toh ina ga in kin bar gidan, ai sai abinda yaci gaba, duk danginmu kaf cikinmu babu wanda ya tab'a auren mai irin kud'in mijinki kin sani, duk da kema naki uban nada kud'i amma ko k'afar nashi uban bai kamo, gashi shima yaro dashi amma arzik'inshi yafi k'arfinshi gashi komai kikace kinaso sai ma ya miki dad'i badai ragi ba, zancen zaki bar mishi gida bai zo ba, Allah ne yayi zanzo inga rashin hankalin da kike kwab'awa, duk da nazo da shiri amma dai nasan sai mun sake akan nada, wannan duk yadda akayi ya riqe ibadarsa sosai shi yake hana aikinmu ya kamashi, kuma ina jin iyayensa ma basu bar shi haka ba, yanzu watanmu uku muna abu d'aya amma bama tab'a cin nasara, wannan karan kuwa ba da wasa zamu shigeshi ba, itama wannan yarinyar gaba d'aya b'atar da ita zamu sa ayi tunda har a dalilinta yake marinki, dan haka dole ne abi ta kanta a magance matsala, sati d'ayan da nazo yi na fasashi, jibin nan zan koma in fad'awa Yaya duk abinda ake ciki, sosai zamu tashi tsaye akanshi, sai mun sa ya gwammace kid'a da karatu", kamar wata wawiya tana nan zaune har sai da junaiba ta gama sannan tace "Toh yanxu ya zanyi, dan ni duk matar da ta rab'eshi ko tace zata shigo rayuwarshi wlhy Allah sai na hallaka koma wacece, sai dai nima a kasheni, Anty baxa ki gane irin son da nake ma Aliyu ba" cikin matsanancin kuka ta kare maganar, junaiba ta sauke ajiyar xuciya tace "Ai babu wani zancen wata matar in ba ke zakiyi sake ki bashi dama ba, yanzu ki tashi ki kintsa kije ki bashi hak'uri daga nan sai kiyi mishi zancen tafiyata dan ya bamu d'an tsoka mu samu na aikin, suma Malaman na yanzu ba abin yadda bane sai kaga da k'yar ake samun na gaske, dubi fa abinda wannan d'an isakan mutumin yayi mana", mikewa Ajiddeh tayi har lkcn xuciyarta na tafarfasa don da xa a bata wuka a lkcn babu abinda xae hanata caka ma Batuul, Allah sa ma cikin ne jikinta kamar yanda take xargi, shikenan xamanta ya xo karshe gidan cikin ruwan sanyi, kwafa tayi ta mik'e ta shiga cire kayan jikinta tana naxarin abinda Anty jainaba tace.
Ficewa Farida tayi daga dakin tana xumbura baki a xuciyarta tace "Ae ko da na kira maka Ammah yanxun nan, kuma in fita in fasa gaskiyan komai" bin ta yayi da harara sannan ya dawo daga gefen Batuul fuskarsa daure, kamar bata ganshi ba ta mik'e k'afafuwa zata kwanta ya rik'ota cikin kaushin murya yace "I will slap you idan baki tsaya kin saurareni ba", kuka ta fashe masa da, nan da nan ya rude ya dago kanta yace "me ya faru kuma, me nayi maki" kin cewa komai tayi sai kukan da take, nan ya shiga rarrashinta kamar wata jaririya, da kyar ya samu tayi shiru, ya rungumota jikinsa ya lumshe ido yayi shiru, mamakin kansa kawai yake, ya rasa gane dalilin da yasa yake behaving haka, maganar Ajiddeh ne ya fado masa, ya bude idonsa a hankali yace "Are you noticing some changes a jikinki?, I mean do you feel anything unusual?", had'e rai tayi ta dago kai tana kallonshi tace "Meye toh kake tambayata", yanda ta had'e ran ne ya kusa bashi dariya amma ya dake yace "wai yaushe kika koyi rashin kunya ne, ina miki magana kina had'e min rai, ehhn tell me", ya k'arashe maganan tareda zame mata hular dake kanta, tsuke mishi baki tayi tace "Ina ruwanka da hulata da zaka ciremin, ni ka maida min abuna", yace "bazan mayar ba har sai kin fad'a min mey ya canja ki lokaci d'aya", sake had'e fuska tayi tace "wai wani canjawa, ni dama can haka nake kaine baka sani ba", dariya yayi yace "d'azu fa naga har my wi.....", sai ya tuna alk'awarin da yayi mata na cewa bai sake k'iran Ajiddeh da my wife gabanta, kwana biyu bata yi kuka ba har wani dad'i yakeji, kallonta yayi yaga ta tsareshi da ido yace " I meant Ajiddeh, d'azu har gani nayi kin kare kanki gunta, hmmm I lyk that courage, d new you, but banda wannan sabon attitude d'in towards me, kuma idan xaki mata fitsaran ki tabbatar ina gida", kallonshi tayi ta d'an tabe baki tace "ni ka tafi bacci zanyi", yace "bacci? mey ke damunki ne, we have to see a doctor, dan baccin nan naki ba na lafiya bane", zumb'uro mishi baki tayi tace "inji waye banida lafiya, am fit and fine", yace "ina wani fit and fine, bakida aiki sai amai da bacci, ko breakfast ma bakiyi ba yanzu, ko jiya ma bakici dinner ba", kamar jira takeyi ya gama magana tace "Yawwa kaga ma ko, ice cream nakeso in sha yau ma, amma ba na Gelatorino ba yau, na Cold stone nakeso, sai ka siyo ma farida breakfast", kallonta kawai ya tsaya yi yadda cute lips d'inta ke moving, ganin baice komai ba ta tsuke baki tace "I knew it dama baza kayi min ba, toh kaje zanyi da kaina", lumshe ido yayi ya janyota ya had'ata da jikinshi ya shiga kissing d'inta passionately, ita kam sai tutturashi takeyi amma yaqi saketa, Farida ce ta tura k'ofan d'akin ta shigo riqe da waya, turasa Batuul tayi da sauri ta koma baya, ganin condition d'in da suke ciki yasa tayi maza ta juya ta riqe bakinta tace "Oooops, am sorry, Ammah ke son yin magana da Batuul", Batuul dai kasa d'agowa tayi ta kalleta sai shine da ya bita da harara yace "out", da sauri taja musu k'ofar ta fita tana kyalkyala dariya.D'ago kai tayi ta kalleshi bayan Farida ta fita, suna had'a ido tayi maza ta dauke nata tace " kagani ko, ni dai ka tafi daga d'akina", hannu yasa ya d'ago hab'arta yace "ita tace gidanta (Ajiddeh) keh kice d'akinki, kamar kun ma san sanda aka yishi", yana murmushi ya kare maganar, janye hannunshi tayi tace "toh ba d'akina ba, d'akinka, ka tashi ka tafi ni dai" ta k'arashe maganan tana zumb'uro mishi baki, ya buda ido yace "You are totally changing from what you were, kin koyi fad'a da rashin kunya, korata fa kikeyi, I can decide to stay with you for a whole year if you didn't change, beside I lyk being with you all d time, I can't get enough of you, your warmth, body texture, scent everything, next time bakin ki ya sake ce min in tafi sai na dawo d'akinki gaba d'aya da xama, ko kuma keh in maidaki nawa d'akin da zama", zumb'uro mishi k'aramin bakinta tayi tace "toh ba turarenka bane kullum sai ya rik'a min yawo akai, ni bana sonsu yanxu", ta fadi tana kauda kanta, kalllonta yakeyi har ta gama maganan snn yace "baki sonsu?", kai ta gyad'a mishi da sauri, yace "toh wanne kikeso in na amfani da? nuni tayi mishi da kan vanity table d'inta tace "ba ga nawa ba, kaita using ni bazan hana ka ba ai", dariya ta bashi yace "yanzu keh sai ki yadda in shafa turarenki, toh su meye ma naki turaren in banda humra, ni kuma mey ya had'ani da shafa humra", had'e rai tayi tace "ai akwai wasu ba Humra bane kawai", yace "naji toh, yanzu zaki rakani in sai wasu sabbin turaren wanda basa damunki", da sauri ta kad'a mishi kai tace "Ni babu inda zani", girarshi ya d'age mata yace "woooh , fine I will go by myself, but in na kawo wani karki ce min shima na
damunki tunda kece kika qi zuwa kiyi selecting", murgud'a Mishi bakinta tayi tace "Na yadda", mamakin kanshi yake gaba d'aya, shi kanshi baisan mey ke damunshi ba, wai shine yayi stooping to Batuul's level har yake biyewa shirmenta, har wani murgud'a mishi baki takeyi amma he couldn't do a thing sai ma burgeshi da take, kallonta yayi yace "Okay, now tell me mey zakici, I will get it right away", ya had'e rai yace "don't tell me bakijin yunwa ko kuma ice cream zakisha, solid abinci nakeson kici", kallonshi tayi tace "Toh sai ka had'o min ice cream d'in da Burger na burger kings, kada a samin cheese, sai pizza shima na pizza hut amma fa beef, da chips d'in KFC sai kace su baka spice d'in da yawa, sai daga gefen school d'inmu akwai wani road side food vendor, shi kuma sai ka siyamin Tacos da chicken rolls a wajenshi, shima ya samin spice da cream dayawa", shikam kallonta ya tsaya yi tana magana tana lumshe ido, har wani tsayawa tunanin abinda zatacin takeyi , tace "Yawwa sai kuma Raffaello, a pack of twix and what keeps me moving Nutella", ta k'arashe maganan da dariya abinta tana wara ido, shi kam kasa cewa komai yayi sai kallonta yake ko kiftawa bai yi, ganin irin kallon ta had'e rai tace "Kaji?", d'an tab'e baki yayi ya kalleta yace "Naji, amma wai ke zakici duka wannan abinda kika lissafo?", kai ta gyad'a mishi tareda d'age girarta tace "toh zance ka siyo ne in baxan ci ba?, duka nikeson ci", yace "Fine", tareda da d'age mata hannayenshi, yace "wannan lissafin naki its better we order it, kowanne fa venue d'inshi daban", da sauri tace "Ah ah, nikam its better you go by yourself, kar suje sumin mistake", mik'ewa kawai yayi dan yasan rigima take jin yi, ta kalleshi tace "sai ka tambayi Farida ma abinda zataci", har ya kai bakin k'ofa tace mishi "kaga ko, baka maidamin hulata ba", sai ta fashe mishi da kuka, da har bazai juyo ba jin ta fashe da kuka yasashi dawowa da sauri ya wara ido ya sa mata hularta ya gyara mata kwanciya murmushi dauke fuskarsa yace "I've done that" mikewa yayi yana kallonta yace "I will send in Farida", da haka ya juya ya fita, a corridor ya tadda Farida na waya, harara ya bita dashi ya sauk'a batareda ce mata komai ba, dariya tayi ta juya ta shige d'akin, da sauri Batuul dake kwance ta juya mata baya, zuwa tayi ta fad'a kan gadon ta yaye bargon da Batuul d'in ke rufa da tace "Hey c'mon get up, ya tafi shine zaki wani kwanta, toh ga Affan nan, he is on the line", d'an tsaki taja tace "Riri you will never change wlhy", lumshe Ido tayi ta fad'a da baya snn ta d'ago tace "Ohhh how I missed this name, babe I missed you sooo much baza ki ganeba", dariya ta bawa Batuul, jin muryar Affan cikin wayan tayi maza ta mik'a mata tace "he is on the line", ture wayan tayi tace "ba ruwana dashi ai ni, ba ya manta dani ba, I don't want to talk to him nima, he promised to call me back rannan but he never did", ta k'arashe maganan tareda lank'washe hannayenta a k'irjinta, Farida ce ta maida wayan kunnenta tace "Mine", da sauri Batuul ta d'ago ta kalleta jin sunan da ta k'ira Affan dashi, a ranta tace "Sabon salo", "Mine kaji ko, kayi mata lefi, ita fushi take dakai", tace "Baby mine ina jinta, samin wayar speaker muyi maganan da ita", speaker ta danna snn ta ajiye wayan, yace "Hey sweetheart best friend, am so sorry for not calling back, these days kullum busy nake sabida shirin exams dake gabanmu, nayi miki alk'awari I will come immediately after my exams, not even before going home", da sauri ta d'auki wayan jin yace zaizo tace "Yaay that's my best friend", haka dai sukaci gaba da hirarrakinsu har ta gama ta mik'awa Farida wayar sukaci gaba da hirarsu ta soyayya, saida suka gama sannan Batuul tace "wai ke yanzu Farida dagaske kike son Affan dinnan?, he just 3yrs older than us fa", Farida tace "of course I do know, shiyasa ma nake son nashi, ni wlhy na tsani saurayina ya fini koda five yrs bazan iya auren babba ba, ni kunyanshi ma zan rik'aji, Affan is d perfect guy for me, I soooo much love him to d extent da in akace za a rabani dashi I can jump through d window", dariya sukasa dukkansu biyun, Batuul tace "kin manta from d terrace dai", suka sake sa dariyan, Farida tace "Kinsan I had a crush on Affan tun farkon ganina dashi, I always get jealous yadda kuke, I tot ma soyayya kukeyi yadda naga you guys are so close, saida kikace min wai he wants to ask me out, wai inja mishi aji, ai ba Iya zan ba, wlhy ranan I couldn't sleep, Allah na rik'a yiwa godiya, dan dama kullum sai na rokeshi, I was just happy", dariya Batuul tasa tace "We have been best friends tun childhood d'inmu, His Mom and Aunty were cousins, kuma best friends, Aunty tana fad'a min lokacin suna Uk tareda su Ammah, she have been married for nine years amma bata samu haihuwa ba, Shekaran da akayi aurenta shekaran aka haifi Yaa Abu da Massa, kuma lokacin Ammah da Yaa Mera suna aiki, gidansu a Jere yake su ukun, dama mazajensu abokai ne sosai tun yarinta, Baba, Abui sai shehu, toh Aunty ce kad'ai bata aiki, kinsan Fulani tana gama secondary school akayi mata aure, Baba kuma yace yafi son saita haihu taci gaba da zuwa makaranta, toh a lokacin nefa sai su Ammah su rik'a kawo mata su Yaa Abu gunta in zasu aiki, ita tayi rainonsu, daga baya ma sai komai nasu ya dawo wajen Aunty, har lokacin da suka shiga school, lokacin da suka cika Nine years, lokacin
Aunty ta samu cikina, kowa yayi murna sosai, cikin Aunty nada wata shida aka yiwa Baba transfer ya koma Nigeria, lokacin yace zai tafi da Aunty, su Abui sukayita insisting ya bar Aunty dan its risky tana yawo at this stage of pregnancy, gara ya riqa zuwa yana dawowa, yace hankalinshi bazai tab'a kwanciya ba, gara ya tafi da matarshi, lokacin su Yaa Abu sun gama year 6 dinsu na makaranta shida Massa, sunsha kuka da Aunty zata tafi, especially Yaa Abu, dan komai da Uwa zatayiwa d'anta tayi musu, tacema su suka sa mata sunan Aunty har yabita muma muke k'iranta dashi,dan shi Yaa Abu cewa ma yayi zai bita, da k'yar aka samu Baba ya rarrasheshi yace anytime sukayi hutu zai turo a d'aukesu, Da haka ya tattara suka koma Nigeria, dama lokacin Maman Affan(Sakina) ta haifeshi shekaranshi biyu da wata goma, da zai cika shekara uku Aunty ta had'a mishi birthday party a gidanmu, wai zatayi compensating rashin zuwa sunanshi da batayi ba, ana cikin shagalin party Aunty ta fara labour, nan akayi rushing d'inta asibiti, bata sha wani wahala ba ta haifeni, toh kinji wannan shine yasa I became close with Affan, mun shak'u sosai, he became d elder brother I never had, He is my birthday mate, kullum tare ake mana celebrating, kuma shi gidansu Affan sai sun sauk'e Qur'an suke shiga school, su Yaa Abbass duk saida sukayi sauk'a kamin suyi joining school, Affan ne kad'ai ya shiga school lokacin yanada haddar izu sittin, kinsan yadda kan mutumin naki yake, yanaja sosai, shiyasa aka turashi makaranta akace zai iya hada duka biyun, lokacin da nake shekara biyu, lokacin Kakan Massa ya rasu aka nad'a Baban Massa sabon sarki, Amma ma tacewa Abui itama baza ta zauna ba tunda duk y'an uwan nata basa nan, shima haka suka tattaro suka dawo, su Yaa abu kuma nan aka barsu sabida school, kin dai ji how I became close with Affan", Farida tace "Wow, so you know this much shine baki tab'a fad'amin ba", dariya Batuul tayi tace "komai da lokacinshi, gashi nan yanzu da lokaci yayi kin sani", Farida tace "Tell me, how does it feel to b married, like how do you feel, ya kikeji duk lokacin da kika tuna kinyi aure?", bata amsa ba sai ma tambayar da ta jefa mata itama tace "How does it feel to b in love, ya kikeji?, wara ido Farida tayi tace "Lallai ma, keh zan tambaya wannan ma ai, ko zakice min you are not in love ne har yanzu, I just saw it da idanuwa kina nunawa Yayana soyayya", ta k'arashe maganan tareda kashe mata ido d'aya, dariya Batuul tayi ta mik'e tace "You are not serious", daidai lokacin Yaa Abu ya shigo d'akin, Farida ya kalla yace "abincin suna k'asa go and arrange them", simi simi kamar munafuka ta mik'e ta fita, Batuul ya kalla yace "nan zakici abinci ko k'asa?", cewa tayi "Ni na tab'a cin abinci a k'asa ne, a d'akina zanci, ko dan kaga Farida?", kai ya kad'a, baya ji da rigimarta yace "sai ki sauk'a ki kwashi abubuwan naki" da haka ya fita
+

STORY CONTINUES BELOW


D'akin da ya zama nashi ya koma, a bakin gado ya tarar da Ajiddeh zaune da wata irin shiga, d'auke kanshi yayi kamar bai ganta ba ya shiga cire kayan jikinshi, tasowa tayi ta shige jikinshi, had'e rai yayi ya turata daga jikinshi, sosai ranta ya b'aci amma da yake nema take su shirya haka ta koma gun nashi, ta sake mannewa a jikinshi, hannu yasa zai janyeta tace "Haba babe meye ne haka kake min, indan abinda nayi d'azu ne am sorry, I promise you bazan sakeba, d'azun ma sharrin shaid'an ne da kuma irin son da nake maka, bana iya jure ganin wata mace kusa da Kai, amma kayi hak'uri kaji babyna", cire hannayenta yayi daga jikinshi yace "Ai this is not your first time na bani hak'uri, kinsha bani kuma kike sake aikata laifin, abinda kikaga yafi dacewa dakene kikeyi, keep on with it", marairaice mishi fuska tayi kamar dagaske tayi nadama tace "Am serious this time, bazan sakeba kaji?, in kanaso har ita zanje in bawa hak'uri", ajiyar zuciya ya sauk'e yace "Ban aike ki ba", tace "toh ka hak'uran?, tsakanin mata da mijinta sai Allah, kai kawai ya gyad'a mata ya juya yayi toilet, biyoshi tayi tana cewa "Let me help you", tare sukayi wankan, shi ya d'aukota a hannunshi suka fita, bayan sun kintsa take ce mishi "Baby jibi fa Aunty na zata koma", ya kalleta yace "Soon?, mey tazo yi dama?", shiryayyar k'aryar da zatayi mishi ta rasa, batasan lokacin da tace "kasan dama d'an mijinta anan yake karatu, toh wai zasuyi convocation d'insu shine tazo tayashi murna", kai kawai ya gyad'a yace "Okay Allah ya kaimu, gobe kamin in fita you remind me", saida suka gama shiryawa yace "Food is downstairs, sai ki d'ebi na Aunty ki kai mata", da haka ta fita shi kuma yayi shirin fita, washe gari ma haka yaje ya samo musu abinda zasuci, da yamma Batuul take ce mishi Farida zata kai wa wata k'awarta da tayi aure ziyara a Birmingham saida ya gama musu tambaye tambayenshi tukunna ya yadda sannan ya had'ata da David suka tafi.

Washe garin ranan da Aunty Jainaba zata tafi, da safe Batuul ta sauk'o, wainar fulawa kawai takejin ci tunda asuba, tana kitchen tana y'an aike aikenta taji su Ajiddeh sun sauk'o, bata bi ta kansu ba ta tab'e baki taci gaba da aikinta, zama sukayi a parlour suna cin abincin da sukayi ordering, a guje sukaga Batuul ta fito toshe da bakinta, bata bar parlour ta tsuguna ta dinga kwarara amai a wajen, da ido suka kalli juna, Aunty Jainaba ta xaro ido tayi kasa da murya tace "Keh anya wannan shegiyar yarinyar ba ciki gareta ba kuwa, kullum sai tayi amai, toh na menene?", Ajiddeh dake ta kallon Batuul ita ma murya can kasa tace "Ai ni so nake ma hakan ya kasance ta tattara ta barmin gida, nasan in har ya tabbatar cikine toh ba yadda za ayi ta zauna, maidata gidansu zaiyi, ya Allah ka tabbatar da hakan", dai dai nan Abutturab ya sauk'o don shima ya ji k'ak'arin aman nata, da sauri ya k'araso ya d'agota ya rungume yana k'iran sunanta, suna ganinshi suka mik'e, gaba d'ayansu sai da zuciyarsu ta doka ganin yadda ya rungumeta, ita kam Ajiddeh ma sai gani tayi sun mata kama, Aunty Jainaba ce ta wayance da cewa "yi sauri ki mik'a mata ruwan Ajiddeh, sannu kinji", Batuul kam bata ma san mey suke cewa ba, haka shi ma don duk hankalinsa ya tashi ganin yanda take aman, k'arasawa wajensu Aunty Jainaba tayi damuwa dauke fuskarta kamar gaske tace "Aliyu bai kamata a barta haka tana ta ciwo ba a gida, akai ta asibiti dan aman nan nata yayi yawa, kar aje ba a saniba wani ciwon ne yake damunta har yayi mata illa, ku kaita asibiti yanzu gskya, dubi yanda duk ta galabaita" sai da ya tabbatar ta gama aman snn ya d'auketayayi sama da ita, Ajiddeh ta bi su da harara xuciyarta na tafarfasa, jikinta ya gyara mata ya canja mata kaya snn ya sauk'o da ita, numfashi kawai take mayarwa duk jikinta yayi laushi, David ne ya shigo daidai lokacin, Abu ya kalli Ajiddeh yace "Tunda ga david ku tafi airport kawae ni xan kai ta asibiti" caraf Jainaba ta anshe tace "Kai haba mu tafi asibitin gaba daya kawae Aliyu babu komai" yace "Xa ki iya missing flight kuma, kawae ku je bbu damuwa" bata so haka ba amma bbu yanda ta iya tace "toh shikenan, bari muje in d'auko kayana, Allah ya kara miki lafiya y'ar nan" ta ja hannun Ajiddeh sukayi sama, suna shiga d'aki tace "kina jina, kada ki sake ki wani bini airport, kije asibitin ayi komai kan idonki, sai muga ta fad'i, shegiyar yarinya mai kama da y'an Ethiopia ni na tabbata ba komai bane wannan banda ciki, ni kaina yanzu tsanarta k'aruwa yakeyi a raina wllh", Ajiddeh tace "toh", suka janyo akwatin suka sauk'o, inda tayi aman ya gama gyarawa snn ya koma ya d'auki Batuul d'in zasu fita, daidai nan suka sauk'o, har ranta takejin yadda ya rungume Batuul a jikinshi, danne zuciyarta tayi tace "Baby kaga why not mu tafi tare, kaga jikinta is very critical, you might need help, I will go with you, Anty xata tafi airport din ita kadai, she will understand", kallonta yayi yace "No ki tafi Airport din da ita its okay I will manage", Aunty Jainaba ce tace "Ah ah Aliyu ba komai ai, ba sai ta bini ba, ga mara lafiya nan, ita tafi buk'atarta ai, kuje kawai, Allah ya bata lafiya" ganin suna b'ata mishi lokaci kawai ya d'auki Batuul yacewa Jainaba, "Allah ya kiyaye hanya ya fita", Jainaba tace "maxa Bishi", da sauri Ajiddeh ta bishi ta shiga gaban mota, badan yaso ta bishi ba, a baya ya kwantar da Batuul snn ya dawo gaba ya seta rear mirror d'inshi daidai yadda zaina monitoring d'inta, motar su Jainaba ce ta fara fita sai nasu daga baya, kowa yayi nasa hanyan, suna isa asibitin ko reception bai tsaya an duba mishi file ba ya shiga office d'in doctor d'inshi kai tsaye, Ajiddeh ma jiki na rawa tazo zata kutsa kai cikin office d'in ya kalleta rai a had'e yace "stay outside, ki tsaya daga waje, bbu amfanin shigan ki", ba dan taso ba haka ta koma daga baya ta zauna kan d'aya daga cikin kujerun wajen rai b'ace, da sauri likitan ya taso ya karb'eta suka kwantar da ita kan gadon office d'in, gaba d'aya abin nan da akeyi batasani ba dan bacci takeyi abinta tun mota, hannu kawai Abu ya kalmashe sai rocking yake kan kujera yana ganin likitan na aikinshi cikeda k'warewa, saida ya ya gama gwaje gwajensa sannan ya dawo ya zauna kan kujera, Hannu ya mik'a mishi da murmushi a fuskanshi yace "congratulations, you are going to be a Father, your wife is one month and few days pregnant", gaba d'aya jin maganar yayi wani iri, ya kasa daina kallon likitan, he wasn't expecting it, Batuul is pregnant?, bai janye hannunshi ba har saida likitan ya janye nashi snn yayi maza ya janye hannunshi, ganin irin kallon da likitan ke mishi yyi saurin k'irk'iro murmurshi, take ya nunawa likitan yaji dad'i sosai, a kanshi kuwa Ajiddeh yake hangowa idan taji wannan lbrin da yake ji, likitan ne ya katse mishi tunani tareda prescribing mata magunguna da advises kan abinda zata riqaci, da kuma wad'anda are not good to her health, ita dai har lokacin baccinta takeyi, mik'ewa likitan yayi zai bar office d'in yace "Mr Kyaree, I will be right back" a hankali ya mik'e ya isa bakin gadon yana kallonta ko kiftawa bai yi, likitan na fita a bakin k'ofa ya kusa cin karo da Ajiddeh, da sauri ta koma baya tana yak'e, murmushi yayi mata yayi gaba abinshi, a guje ta biyo bayanshi da damuwa kamar gaske fuskarta tace "Excuse me doctor" juyowa yayi yana kallonta, tace "Hope she will be okay, I don't want anything to happen to her, she is my only Sister, tell me what is wrong with her Doc", murmushi yayi yana girgiza mata kai yace "Yeah she is okay, she will b fine surely, congratulation your sister is pregnant", kwalalo ido tayi waje da dafe k'irji tace "What?", ganin irin kallon da yake mata yasa tayi maza ta kirkiro murmushi tace "Omg, Am happy, Thank you sooo much Doctor", ya mayar mata da murmushin yace "you are welcome" ya juya ya tafi, wani irin farin ciki da ta dad'e bataji irinshi bane taji yana ratsa ta, tana zama ta k'ira Aunty Jainaba dake airport ta sanar da ita komai, Anty junaiba tace "Wayyo ni da ban tafi yau ba" nan dai sukayi ta murnan k'arshen zaman Batuul gidan yazo karshe cikin ruwan sanyi tunda cikin shege ke jikinta, Abutturab kam jikinshi duk yayi sanyi, daidai kanta ya tsaya yana kare mata kallo, yasan yana da son yara, yanada burin ganin yayanshi amma bai taba sa damuwa ranshi ba na Ajiddeh bata haihu ba, tunda yasan Allah ke badawa a lokacin da ya dace but with Batuul, its totally out of it, yana d'aura ido kan cute face d'inta yaji wani courage yazo mishi na son ganin babyn da Batuul zata haifa mishi, wani abu da bai tab'a ji bane yau ke mishi yawo gaba d'aya jikinshi, d'an murmushi ya saki ya d'an sunkuya yayi kissing y'an cute lips d'inta da bai iya resisting, cak ya d'auketa ya rungemata tsam jikinshi yana jin abin nan na mishi yawo a jiki, barin office din yayi yana rike da ita ya fito, a zaune ya tadda Ajiddeh tana waya da sauri ta katse ganinsu, kamar ta samu wuk'a ta cakawa Batuul takeji amma ai k'arshen zamanta ma yazo, fuskarta d'auke da murmurshi ko tambayarshi abinda ke damun Batuul batayi ba sai murmushinta takeyi, shima d'in baice mata komai ba, kallonta yayi yace "muje", tasa kai gaba suka tafi, ganin gaba d'aya mood d'insa ya canja a ranta sai cewa takeyi, "wato so yake ya rufa mata asiri ko, toh ai ta Allah ba taku ba, Allah ya toni asirinta yau", mota ya bud'e ya kwantar da Batuul ya gyara mata kwanciyar kallonsa take tana lullumshe ido sbda irin baccin da take ji, ya zaga ya shiga ya tada suka fita, suna isa gida Ajiddeh ce ta fara fita daga motan ta shige cikin gida ya bi ta da kallo, da sauri ta haura sama ta shige d'akin Batuul ta shiga fiffido mata akwatinanta, kafin su Abu su shigo har ta sauk'o downstairs dasu, yana rike da hannun Batuul suka shigo parlon, da mamaki duk suka tsaya kallon ikon Allah, shewa ta saki tana tafa hannaye tace "In kana tunanin ni xa ayi ma wasa da hankali kayi karya Aliyu, don zaman karuwan nan ya k'are gidan nan," ta juya tana kallon Batuul tace "Munafuka algunguma, ashe karuwanci kike yi dama, toh yau Allah ya toni asirinki, iskanci ba a gidana za ayishi ba dan ban gada ba, a tafi can inda aka saba aci gaba dayi, Dan ni dai kam ban zama da mai cikin shege a gidana", kallonta kawai Abu yake da mugun mamaki don baisan ya akayi ta sani ba, Batuul kam d'aurewa kanta yayi ga jirin da ke d'ibarta, Jiki na rawa Ajiddeh tayo kanta ta fizgota da kargi tayi k'ofa da ita ta hankad'ata waje tana hakki tace "k'arshen karuwanci dai yau ya k'are gidana, aje gaba aci gaba daga inda aka tsaya," da sauri Abu ya k'araso ya d'ago Batuul duk ya gama rud'ewa ya shiga dubata ko taji ciwo, ita ko banda kuka babu abinda take, ganin komai normal babu abinda ya sameta ya mik'e, cikin zafin rai ya fixgo Ajiddeh ya wanka mata lafiyayyun mari har biyu ta both sides, ya shaketa cikin tsawa yace "kika kuskura ki sake tab'ata ko kika yi gigin k'iranta da karuwa sai na hallaka ki wllh, don matsayinta d'aya yake da naki a gidan nan" ranshine ya dad'a baci cikin kaushin murya yana mata wani irin kallo yace "Let me tell you what you don't know jiddah, kamar yadda kike matata a gidan nan, toh haka Batuul ma take matata ta sunna, snn cikin dake jikinta ba na kowa bane, nawane", yana kai wa nan ya Kama Batuul da komai ya tsaya mata yayi sama da ita, nan yabar Aunty Ajiddeh da numfashinta ke neman barin jikinta, idanunta sun firfito.

Post a Comment for "BATUUL CHAPTER 16"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...