Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

BATUUL CHAPTER 12

BATUUL CHAPTER 12

- - Post a Comment
BATUUL
CHAPTER 12


Ba karamin rudewa Batuul tayi ba a lkcn, duk jikinta ya dau rawa sae tutturasa take tana neman kwace kanta amma ta kasa, gajiya tayi ta tsaya ganin ba saketa xae yi ba, banda hawaye babu abinda take, duk jikinta yayi sanyi, ko lura da halin da ta shiga bae yi ba don idonsa a lumshe suke, yakai minti biyar yana abu d'aya kmr wanda ya tuna abu ya xame bakinsa daga nata a hankali, sae dae ya kasa kallonta, kuka ta fashe da ta xame jikinta daga nasa tayi saurin janyo towel dinta ta rufe jikinta, bae bari sun hada ido ba ya mik'e ya fice daga d'akin da sauri, kuka sosai ta shiga yi bayan ya fita, takai minti goma tanayi daga baya ta mik'e da kyar ta koma toilet ta wanke fuskanta, vanity stool d'in ta jawo ta zauna jiki a sanyaye, kallon lips d'inta da ya koma ja ta tsaya yi jikin mirror, a hankali ta d'aura babban yatsan ta kai tare da lumshe ido hawayen dake makale idonta ya gangaro, bud'e ido tayi ta janyo man shafanta, jiki a sanyaye ta gama shafa man taje ta sako kaya, har ta gama ta kwanta jin lips d'inta take ba daidai ba, gashi bata daina jin taste din bakinsa a nata ba, lumshe ido kawai tayi ta kwanta.
+

Ajiddeh kam na xaune dakinta bayan ta watsar da kwalaye da ledan da ta shigo da, duk abun duniya ya taru yayi mata yawa, banda huci babu abinda take yi ita kadae, wannan wace irin jarabace aka turo mata gidan ta, anya ma kuwa zata iya ci gaba da yin wannan abinda Mummy ta fad'a mata, wai dan wulak'anci Aliyu har shi zai wani tashi ya zaga ya bud'ewa y'ar iskar nan k'ofa bayan ita ba yi mata yake ba, to me hakan ke nufi, fad'awa tayi kan gado tana maida numfarfashi, da tun farko tasan zuwansu Nigeria da Abutturab zai zama haka da bata barshi ya tafi ba, ko ita da taje ta dawo, wani hawayen bak'in ciki ne ya shiga zubowa daga idonta, ta mike xaune ta fashe da kukan takaici, ita kam ya xata yi da Batuul? wayanta ne ya shiga ringing, jawowa tayi da sauri ta kara a kunnenta, jin mai k'iran ya sata share hawayenta da sauri, daga d'aya b'angaren Mummy tace "Ajiddeh Jiddeh, jiddum fi khair ana, useki y'ar albarka, naga abin kirkin da kika turo, ba b'ata lokaci yanxu zan turawa su Zainab, daga can za a turo miki ba sai sun dawo gida ba, zamuyi maganan duka details d'in in suka iso", toh kawai ta iya cewa dan wani irin tuquqi da zuciyarta keyi mata, Mummy ce taci gaba da ce mata "kuma kici gaba da yi kamar kina son nata, dan komai yazo mana da sauk'i, ko meye ya sameta kinga baza ayi zarginki ba dan babu wanda yasan kina k'inta, shi kuma sai sun dawo d'in sai muji yadda nashi abun yake", tace "toh Mummy duk zanyi", da haka suka katse k'iran dan maganar ma wahala take bata, turo k'ofar d'akin yayi ya shigo, da ido yabi kwalayen da ice cream packs d'in dake zube a k'asa har wasu sun fara malalewa, tattarewa yayi yazo bakin gadon ya zauna, hannu yasa ya d'agota kanta yana kallon yadda idonta ya canja, "kina da lafiya kuwa, zaki d'ebo abincin kixo ki watsar dasu anan kamar a bola na tsinto kudin, kina ma da hankali kuwa?", zuciyarta ta shiga dannewa tasa hannu tana d'an murza kanta tace "Baby kaina ke min ciwo, har jiri jiri nake gani shiyasa ma kaga komai a k'asa, ba zubarwa nayi ba", kallonta yayi yana examining d'inta gabaki d'aya sannan yace "kin fad'amin? ko kuma kinada maganin sha ne", kai ta girgiza ta shige jikinshi tace "c'mon babe, kasan banso kana damuwa shiyasa ban fad'i maka ba, I will b fine, you don't worry", ta k'ara shige mishi jiki, hannu yasa kanta yana shafa gashinta mai d'an karan laushi ya lumshe ido sae dae ji yake kmr har lkcn bakinsa na cikin na Batuul, a hankali yace "tashi kici abinci sai ki kwanta", ba musu ta tashi ta janyo kwalin pizza, har ta bud'e ta d'au d'aya zata kai baki, ta kalleshi da wani irin murmushi fuskanta ta wara ido tace "babe", d'ago kai yayi ya kalleta tareda d'aga mata giranshi d'aya yana jiran jin mey zata ce mishi, "our Sister, bari inje in kai mata share d'inta, nasan she is famished, daga school ma take kaga dole taji yunwa", k'ok'arin mik'ewa tayi yasa hannu ya dawo da ita ta zauna tana kallonshi, murmushi yayi yace "rabu da ita, in tana jin yunwa zata sauk'o ta samarwa kanta abinci", kai ta shiga girgiza mishi zatayi magana ya sa hannu kan lips d'insa yace "shhhh, eat and get some rest, bakya jin dad'i you shouldn't bother, she will b okay", wani irin murmushi tayi murna fal ranta kamar tayi yaya, bata damu da ko yanaci ba, haka ta dinga tunkud'a abincinta, tunanin abinda ya faru tsakanin shi da Batuul kawai yakeyi yana kallonta don tun da yake kissing dinta bae taba samun natsuwa irin wanda ya samu gun Batuul yanxu ba, it was just amazing, lumshe ido yayi ya kwanta kan gadon Ajiddeh, gaba d'aya komai dawo mishi ya shiga yi a hankali, hotunan Ajiddeh dake kan wayar da ta goge ya tuna, baisan lokacin da wani slight murmushi yayi escaping lips d'inshi ba, then why did she delete the pictures ita da ba ma son shi take ba what made her jealous, wayanshi dake gefen Ajiddeh ne ya shiga ringing, zuciyanta ya bada sautin dam, ganin mey k'iran, jiki a sanyaye ta d'au wayan, wani zuciyan ke ce mata ta katse wayar dan ita tsoro takeji, kamin tayi abinda zuciyarta ke kissa mata ya bud'e lumsassun idonunshi, a tsorace ta mik'o mishi wayan ganin ya bud'e ido, tashi yayi daga kwance ya risina ganin mai k'iran ya karba wayar, a kunnenshi ya kara a nutse ya amsa da sallama yace "salamu alaikum, nda dubdo Ammah", amsa mishi sallamar tayi tace "Ya kuke Abu, yasu Hauwa'u", kallon Ajiddeh yayi sannan yace "suna lafiya Ammah, ya gida ya k'arfin jiki?", tace "Alhamdulillah, kana jina, kayan Batuul da aka turo yau zasu iso, dan haka in suka iso kaje ka karb'o su sannan sai inyi magana da ita, inaso in mata explaining abubuwan dake ciki da yadda amfaninsu yake, mik'amin Hauwa'u inyi magana da ita in tana kusa", Ajiddeh ya mik'awa wayan sai muzurai takeyi da ido don gaba daya hankalinsa ya tashi don bae san me Ammah xata ce mata ba, jiki a sanyaye ta karb'i wayan tasa a kunne, xuciyanta sai double flip yakeyi, sai da Ammah ta k'ira sunanta sannan ta amsa, a daburce kamar mara gaskiya tace "Na'am Ammah ina wuni", sau d'aya Ammah taji muryarta tun bayan aurensu da Abu, ba yabo babu fallasa Ammah ta amsa mata da "kuna lafiya Hauwa, ya y'ar uwarki", har cikin ranta take jin yadda Ammah ta k'ira Batuul y'ar uwarta, kamar munafika tace "muna lafiya", Ammah tace "yayi kyau, ki kula da ita kamar yadda zaki kula da taki k'anwar kin ji, nasan Batuul batada Matsala, nasan abin yazo miki bazata, ki d'auka kaddara ce, tun can da rubutacce ne, ki barwa Allah komai sai kiga yazo miki da sauk'i, Allah yayi muku albarka, ya kad'e duk wata fitina cikin zamanku, kuyi zaman lafiya keda Y'ar uwarki, Allah ya baku zuri'a d'ayyiba ya baku zaman lafiya, Allah yayi muku albarka", har Ammah ta gama maganan da zatayi k'wak'walwarta ta kasa processing maganganun da takeji, gaba d'aya kanta ya gama d'aurewa, suyi zaman lafiya ita da y'ar uwarta, wannan magana ai kishiyoyi ake fad'awa, maza tayi ta cire tunanin daga ranta tace "Toh Ammah mungode", daga haka ta mik'awa Abu wayan tana kallonsa, bayan sun gama maganan da zasuyi da Ammah sukayi sallama, kallon Ajiddeh yayi, she wasn't looking herself anymore dan abincin ma ta denaci, yana bud'e baki zaiyi mata magana wayarshi ta sake ringing, bai d'auka ba har ya katse dan lamba ce bak'uwa, sai da aka sake k'ira a karo na biyu ya dauka, muryan namiji yaji yace "This is Daniel speaking from Birmingham port authority, we call to notify you d arrival of your cointainer, we would like you to come and claim your property", ajiyar zuciya yayi, kayan da Ammah ta fad'i kenan, cewa yayi "Aiit, I will be there surely soon", "Thank you", mutumin yace mishi sannan suka katse wayan, Ajiddeh dae ta kafa mishi k'ananan idanuwanta ko kifta wa bata yi, iska ya hura mata yace "what are you thinking about wife, obviously me", a hankali ta kalleshi har lokacin hankalinta tashe tayi murmushi tace "Ba komai", ta juya taci gaba da cin pizza ta, ba wai dan ya yadda ba ya k'yaleta, mik'ewa yayi yana kallonta yace "I will b back soon, take care", da haka ya fita daga d'akin da ido kawai ta bishi dan ba daidai take jinta ba, sai da ya kalli kofar d'akin Batuul kamin ya sauk'a k'asa, d'akinshi yaje ya d'auko key ya fita, tafiyar minti 25 ya isa gun port authority, container number ya fad'a musu bayan ya k'ira Ammah ta sanar dashi number, da mamaki yake kallon kayan, bai tab'a tunanin haka kayan keda yawa ba, ta ina ma zai kai kayan nan gidanshi, kana gani kasan lefe ne na aure, idea ne ya fad'o mishi kawai yasa akayi loading kayan a babban mota, yana gaba babban mota na biye a baya, gaban wani gida da rabinshi duk glass ne suka tsaya, nan aka sauk'e kayayyakin, mutanen ne suka shigar da komai ciki, sai da suka gama ya sallamesu suka tafi, shiga yayi ciki ya kwanta kan sofar parlour, wayanshi ne ya shiga ringing, Ammah ce take k'ira , yana recieving tace "Ka amso kayan?", hannu yasa cikin gashin shi a hankali yace "Ehhh Ammah, but ban k'arasa gida ba", yasan tunda Ammah tace zatayiwa Batuul magana yau d'innan sai tayi, ya lumshe ido yace "In sha Allah Ammah, ina komawa zan bata wayan ", bata tsaya jin komai ba ta katse wayan, bai bar gidan ba sai bayan 30mins,

Kai tsaye d'akin Batuul yaje da ya koma gida, kwance ya tadda ta tana bacci abinta hankali kwance, daga ita sai d'an bum short da crop top ta takure waje daya ga xanin ta a gefenta, yafi minti biyu tsaye yana kallonta daga baya ya janye idonshi ya bud'e closet d'inta ya Ciro mata dogon hijab, hannu yasa cak ya d'auketa, baki ta bud'e zata sa ihu ya matseta jikinshi, ajiyar zuciya ta sauk'e jin k'anshin turarenshi tayi lamo jikinshi sae dae gabanta faduwa yake, har sai da ya kaita mota sannan ya bud'e ya direta ya jefa mata hijab d'in da ya d'auko mata shima ya zaga ya shiga daga gefen driver ya tada ya bar compound d'in, kallonsa take a tsorace sae dae ta kasa cewa komae, a hankali ta saka Hijab dinta da ya jefa mata.Driving yake ba tare da yace mata komai ba, duk ta takure cikin motar a tsorace, ga sanyi da takeji dan gaba d'aya wajen sai traces d'in snow ake, a hankali ta juyo kanta daga kallon waje ta kalleshi, wani irin kallo da ya sakar mata yasa tayi saurin d'auke kanta, idonta har ya cicciko, kanta ta kifa kan k'afarta ta sake k'ank'ame jikinta sabida sanyi, bata d'ago ba har sai da taji yayi parking tukunna ta d'ago kanta a hankali, inda ya kawo su tabi da ido tana kallo, xaro ido tayi ganin irin gidan dake gabansu, bud'e k'ofar motan yayi ya fita ya fara tafiya, bata yi yunk'urin fita daga motan ba har saida ya juyo yaganta zaune har lkcn, wani irin kallo ya watsa mata, sannan ya dawo ya bud'e motan, bata jira yace komae ba ta fito, ya kama hannunta, yana tafe tana binshi a baya, kalle kalle Batuul ta shiga yi ganin irin gidan da ya kawo su, don rabin gidan duk glass ne, sosai gidan ya mata kyau, duk wanda yayi designing gidan yayi k'ok'ari, baki ta tab'e da ta tuna shima d'in architect ne fa, amma gaba d'ayanta a tsorace take, stairs yabi da ita ya nufi d'akin da aka zuba kayanta, da mamaki tabi kayan da ido, ta d'ago kai tana kallonsa, kallonta yayi shima snn ya d'auke ido ya xauna ya fixgota ita ma ta xauna daga gefensa, wayarsa dake hannunsa ya kunna yayi danne danne snn ya mika mata, sai da ta kalli fuskanshi taga shima ita yake kallo sannan ta karb'i wayan a sanyaye ta kara a kunnenta, muryan Ammah taji tana cewa "Bitti ya gida?", a kunyace tace "Alhamdulillah Ammah, ina yini?", Ammah tace "Alhamdulillah Bitti, kinga kayanki sun iso ko?", sai da ta kalli Abu, taga kallonta yake sannan ta gyad'a kai kamar Ammah na gabanta tace "Ehhh Ammah, gasu nan na gani", Ammah tace "Yawwa akwai wani kwali a ciki anyi packaging, ki bud'e yanzu in miki bayanin abubuwan ciki da yadda zakiyi amfani dasu", "toh tace" sannan ta mik"e ta isa wajen da kayan ke ajiye, a hankali tace "Ammah kwalin ba d'aya bane, suna da yawa", Ammah tace "Ehhh k'aramin ciki zaki bud'e, manyan duk turarrarukanki ne ciki", tace "toh Ammah", karasawa tayi inda k'aramin kwalin yake ta shiga k'ok'arin bud'e kwalin, kasa bud'ewa tayi harda sauk'e numfashi, a hankali ta juyo ta dubi Abu dake zaune, kallonta shima yayi yaga tayi rau rau da ido, ganin yaqi cewa komai ta juya taci gaba da kiciniyar bud'e kwalin, d'an murmushi yayi ya mik'e ya isa inda take, k'anshin turarenshi da taji yasa tayi Saurin juyowa, kamin ta tashi yazo ta bayanta ya mik'o hannayenshi daga gaba kan kwalin, sama sama ta rik'a jin numfashinta jin sauk'ar numfashinshi kan wuyanta, still tayi har ya gama bud'e kwalin, bai bar bayan nata ba sai ma sake kwantowa da yayi, jiki a sanyaye ta d'auki wayan ta maida wayan kunnenta, sai da Ammah ta gama mata bayanin komai sannan sukayi sallama, wasu ma duk ba fahimta tayi ba jin numfashinshi na sauk'a jikinta yana sending shivers to her spine, a hankali ta shiga k'ok'arin tashi daga wajen, hannayenshi yasa ya zagaye waist d'inta ya sake matseta jikinshi, babu abinda zuciyanta keyi sae double flips lkci daya jikinta ya dau rawa, bakinshi ya kawo daidai kunnenta, a hankali kamar me rad'a yace "nan zaki bar kayan naki har sai ranan da matata ta yadda ki zama co_wife d'inta, batace mishi komai ba sai ma hawayen dake dad'a taruwa idonta, jin tayi shiru yasa ya juyo da ita, hawayen da ya gani idonta yasashi yin murmushi yace "kukan meye zakiyi kuma?", lumshe idonta tayi hawayen dake tare ciki ya shiga gangarowa, murmushi yayi yasa hannu yana goge mata hawayen da ya zubo mata, hannunshi ne ya kai kan lips d'inta masu d'umi, wani irin shock taji yabi spine d'inta kuma har lokacin bata bud'e ido ba, a hankali ya shiga zagaye lips d'in nata da hannunshi, har ya sunkuyo ya kaj bakinshi dai dai nata har tana iya jiyo sauk'ar numfashinshi kan fuskanta, kirjinta sai heaving yake, ta kuma ki bude ido, ko me ya tuna sai kuma ya mike ya kamo hannunta, sai a lokacin ta iya bud'e idanuwanta ta ganshi tsaye, mik'ar da ita yayi, ba musu tabi bayanshi har sai da suka sauk'o k'asa, sai da suka shiga kitchen ya sake mata hannu, wani irin breath taking view ta gani ta glass d'in kitchen d'in, a hankali ta shiga k'arewa kitchen din kallo, babba ne sosai, komai na aiki akwai ciki sai kitchen island daga tsakiya, wani smile ne da bata shirya yi ba yayi escaping lips d'inta, babu abinda tafiso rayuwarta irin kitchen mai kyau da girma, yana kallon fuskanta yace " You like it?", bata san lokacin da ta shiga gyad'a mishi kai ba, murmushi yayi yace mata "cook something light, am famished", bata ce mishi komai ba ta shiga matsawa daga gabanshi, farin ciki fal ranta ganinta cikin dream kitchen d'inta, dogon hijabin jikinta ta take ta kusa fad'uwa yayi saurin rik'eta, k'ok'arin cire mata hijab d'in ya shiga yi, sai lokacin ta tuna da kayan dake jikinta, maza tayi ta rik'e hijabin, tace "No pls" kallonta yayi da lumsassun idonshi da yasata saurin sadda kai k'asa, a hankali ta bud'e baki tace "Yaa Abu kayan are too small ka bar min", bai bi ta kan maganan da take fad'amishi yaci gaba da abinda yake, kai ta shiga girgizawa zata fara hawayen nata tace "Yaaa Abuuu akwai sanyi wllh", har sai da ya janye hijabin jikinta, gaba d'aya jikin nata yabi da kallo daga ita sai d'an bumshort fari da sky blue crop top, lumshe ido yayi ya bud'e ganinta haka tsaye gabanshi, a hankali ta d'ago kai suna had'a ido tayi saurin sadda nata k'asa cike da kunya ganin irin kallon da yake mata, kasa motsawa tayi daga wajen, wani abu yaje ya danna ya k'ara temperature kitchen d'in to a higher degree, dawowa yayi gabanta ya daga mata kafada yace "you can start now, na rage sanyin", kasa motsi tayi ta tsaya, sai da ya sake mata magana tukunna ta juya jiki a sanyaye tayi hanyan fridge, waje ya samu ya zauna kan kujerun island d'in kitchen d'in, babu wani abun amfani na girki cikin fridge d'in daga fruits sai fresh milk da su cheese da kayan lashelashe, rufewa tayi ta koma gun cabinets d'in kitchen d'in, tuna fish ta fiddo da pasta da duk abubuwan da zata buk'ata ta shiga had'a Tuna spaghetti, duk inda tayi idonshi na kanta, a takure take aikin gaba d'aya, ga sanyi da takeji har yanxu, duk da bai kai na d'azu ba, lura yayi da yadda take shivering tana aiki, tsam ya mik'e ya shiga unbuttoning rigarshi, batasan ma me yake ba tana ta aikinta har ya gama sai jin mutum tayi ya rungumeta ta baya, a tsorace ta sauk'e ajiyar zuciya har sai da ya jiyo hakan, anya Abuturrab din da ta sani ne wannan kuwa, what is he doing haka, a kunne ya rad'a mata a kunne "this will help control d cold, I will keep you warm, don't you worry" bbu yabo bbu fallasa yayi maganar, lamo tayi jikinshi tana jiyo k'anshinshi me ddi da dumin jikinsa, ido ta lumshe sannan ta bud'e a hankali, fuskanshi ya d'aura kan gashin kanta da ke ta k'anshi, tana manne jikinshi a tare suka gama girkin, duk kamshin girkinta da na jikinta ya sauke masa kasala, Batuul kam k'asa gaskata cewar Abuturrab din da ta sani ne wannan a jikinta, is he this caring dama ko kawae yana da wata manufa ne a kanta, she just can't tell. +

Plate daban daban ta xuba masu abincin taga ya hade su a plate daya, ta juya tana kallonsa, daukar abincin yyi yana rike da ita jikinsa suka fita daga kitchen din, duk yanda taso ya kyaleta tayi xamanta kin saketa yayi, ya hade rae ya fixgo ta jikinsa, kamar xata yi kuka a hankali tace "Ya Abuu meye haka" bakinsa ya kai saitin kunnenta murya can kasa yace "ohh baki ji ddi ma ina baki hakkin ki na matata yanxu ba koh? Kinsan ni din me jin maganar mahaifiyata ne don haka am doing all this for her sake," shiru Batuul tayi bata ce komae ba, ya dauki fork ya fara cin abincin, lumshe ido yayi jin sweet taste din abincin as he expected, kallon kyakkyawan fuskarsa ta tsaya yi ko kiftawa bata yi, a hankali ya bude ido suka yi ido hudu tayi saurin sunkuyar da kanta, murmushi yayi ya jawota jikinsa sosae kamar zae maida ta ciki yace "Kina kalle ma Ajiddeh miji ko?" Hade rai tayi ta shiga kokarin kwace kanta amma ya ki saketa, hakura tayi tai lamo jikinsa, ya ci gaba da cin abincinsa, ganin yaki ce mata ta ci yasa ta dauki fork din ta fara ci a hankali ita ma, yayi murmushi yana kallonta, "Are yhu still on ur period?" Ya jefo mata tambayar idonsa a kanta, question din ya xo mata a ba xata ga kunya da taji ya rufeta, sharesa tayi ta ci gaba da cin abincin ta, ya juyo da fuskarta yana kallonta yace "Answer me" ta hade rae tace "Y did yhu ask?"Murmushi yayi ya d'auke idonshi daga kanta, abincin dake gabanshi yaci gaba da ci, sae kuma ya ajiye fork d'in hannunshi ya juyo da wani irin smirk a fuskanshi ya sake matso da ita jikinshi yace "you didn't tell me, are you still on your period", tsoron tambayar ne ya kamata amma ta dake ta tsuke d'an k'aramin bakinta tace "nima ban sani ba", yanda tayi maganan ne ya bashi dariya, hannunshi ya d'aura kan mararta yace "Lemme check to see if you are still on it tunda kince keh baki sani ba", a razane ta yar da fork d'in dake hannunta ta zaro ido ta d'aura k'aramin hannunta kan nashi ta rik'e tace "Yaa Abu am still on it, kayi hak'uri, bai bi takanta ba yaci gaba da abinda yakeyi, kallon kyakyawan fuskanta da ya jik'e da hawaye yayi, yayi murmushi yace "Toh ai kema ba sani kikayi ba, kinga I should check for us both", babu abinda jikinta keyi in ba rawa ba, rintse ido tayi tana hawaye jikinta ya dau rawa jin yadda hannunshi ke yawo kan mararta, gaba d'aya jikinta ya saki, a hankali ya shiga daddana mata mara, hannu tasa ta sake rik'e mishi hannu, ido a rintse tace "Yaa Abu dan girman Allah ka bari, nace maka am still on it, yana min ciwo", murmushi yayi yace "dama doctor yace ayi massaging lower abdomen if it hurts, shi nake miki to reduce d pain", a hankali hawayen suka ci gaba da kwararowa, ji tayi kawai ya d'auketa cak, wara ido tayi ta shiga wutsil wutsil, wani irin kallo ya sakar mata yace "I will slap yhu in baki tsaya ba, da kinsan you are on it kika ce min baki sani ba, yanzun nan zan sake ki ki fad'i k'asa", shiru tayi jin yace zai saketa, bata bud'e ido ba saida taji ya direta kan lallausan gado, a hankali ta bude idonta tana kallon fuskanshi, tashi tayi da sauri ta zauna tana goge hawayen dake fuskanta da bayan hannu, muryarta na rawa tace "Yaa Abu nace kayi hak'uri fa, ", ta fad'a tana marairaice fuska, dariya ta bashi yanda tayi maganan ya zauna daga gefenta ya hade rai yana kallon fuskanta yace "kukan meye kike min", kin cewa komae tayi ya fixgota ta fad'a jikinshi, wani sabon kukan ta fashe da tace "ni wllh zan fad'awa Ammah", dariya sosai yayi yace "da kika nace aka aura min keh, sai kicewa Ammah meye"?, sadda kanta tayi k'asa ta mayar kan cinyarta, dabara ne ya fad'o mata ta d'ago kai ta kalleshi, suna had'a ido ta d'auke nata tareda juya kanta ta hade rai tace "toh zan fad'awa Ajiddeh ni dae", baisan lokacin da ya tuntsire da dariya ba ya juyo da kanta tana kallonshi, yana rik'e da hab'arta da ta kasa yadda su had'a ido, har lokacin murmushin nan na fuskanshi yace "da kinbar gidanta a yau ba sae gobe ba kuwa", bata kulashi ba yace "ko don kinga har ta fara kulaki", jin yayi shiru ta d'ago ta kalleshi taga ita yake kallo, ya daga kafada yaci gaba "in kin shirya barin gidanta sai ki fad'a mata in kin k'oma" mik'ewa yayi ya isa wani k'ofa, a jikin bangon ya danna abu k'ofan ya bud'e, shigewa yayi ciki, sai lokacin Batuul ta d'ago rinannun idanuwanta, d'akin ta shiga k'arewa kallo, Babba ne sosai da makeken walk-in closet d'in distressed raw wood da ya cinye side d'aya, daga gefe shelf d'in takaddu ne, sae wani sculptural rope lamp da ya sauk'o daga gefen shelf d'in, sai lokacin ta juya ta kalli gadon da take, traditional bed ne, makekene sosai da wasu brass lamps da suka bada wani irin unified look, da extra reading light, sai wasu faux leather headboard kujeru biyu daga gefe suna facing juna, hankali idonta ya fad'a kan crispy curtains, da glass d'in dake bayan curtains d'in, tab'e baki tayi snn a hankali ta mik'e ta isa wajen tare da yaye curtains d'in, numfashinta ne ya kusa d'auke ganin yadda wajen yake, sai a lokacin tasan sama ya hawo da ita, gaba d'aya filin grass ne shimfid'e da ya sha gyara, sai pond d'an madaidaici da swan farare a ciki suna ta shawagi, sai k'ananun kifi duk cikin pond d'in, daga can d'aya side d'in Lazy S-shaped pool ne, da toskana brown lounge kujeru biyu daga gefensu, bataji fitowanshi ba sai jin k'anshin shower gels da sabulun da yayi amfani dasu taji, juyowa tayi suka hada ido, da sauri ta d'auke kanta ganinshi daga shi sai d'an towel, kamin ta matsa daga wajen ya k'araso yasa hannayenshi ya zagayo waist d'inta, a hankali ya sauk'e fuskanshi kan wuyanta, sanyin ruwan dake jikinshi da sauk'ar numfashin shi wuyanta yasata shivering, a hankali yace mata "kina son gidan?" da k'yar ta iya gyad'a mishi jikinta na rawa, kafad'unta ya kama ya juyo da ita tana fuskantarshi, kasa d'ago ido tayi ta kalleshi, hannu yasa ya d'ago hab'arta yace "hmmmm well I built it for my love, my wife, kin santa?" ya tambayeta yana kallon cute face d'inta, batasan lokacin da ta murgud'a d'an k'aramin bakinta ba ta tsuke fuska ta dauke kai, murmushi yayi ya kuma juyo da fuskarta, d'aura d'an yatsanshi kan lips d'inta yayi yace "I like it when you twist your lips", a hankali ya sunkuyo ya lumshe ido yayi wa lips d'inta light kiss, lumshe ido tayi ita ma jin lips d'inshi kan nata, sai da ya d'ago yana kallonta yace "zaki sani sabon wanka ko", a hankali ta d'ago idanuwanta jin abinda yace eyes d'insu yayi locking, da sauri tayi k'asa da Kai, saketa yayi ya juya ya isa inda closet d'in yake, bayanshi tabi da kallo a xuciyarta tace is this the Abuturrab she knw, lallai namiji bashi da kunya, tab'e baki tayi tana kallon broad figure d'inshi, jiki a sanyaye ta sake curtains d'in ta dawo kan gadon ta zauna, kanta a k'asa har ya gama sa kayanshi ya tada sallah, tana nan zaune har ya idar, sai da ya mik'e daga kan abin sallah yace mata "Let's get going, nasan matata na nan tana jirana", tsuke fuska tayi ta mike ta nufi kofa, bin bayanta yayi yana murmushi, da mamaki ta dubeshi ganin kwanukan da suka bari gun basa nan, tab'e baki tayi taci gaba da tafiya abunta jin baice mata komai ba, Hijab d'inta dake kan sofa ta d'auka ta zira tabi bayanshi har suka fito inda yayi parking, da kanta ta bud'e gidan gaba ta shiga, takurewa tayi jin sanyin ACn dake kunne, observing d'inta da yayi yasa shi controlling temperature, hannunta na hagu ya kamo a hankali ya shiga murzawa, ta fixge hannunta don ta gama gano sa yanxu, jikinta kawae yake so kuma baxata bashi ba.+

Sai da suka shigo gida hankalinta ya fara tashi, Abu kam ko a jikinshi kai tsaye ya shiga cikin gidan ta bi bayansa kamar munafuka, Ajiyar zuciya ta sauk'e ganin Ajiddeh bata palon ta nufi sama da gudu, murmushi yayi dan yasan gudun mey takeyi shima ya haura sama, dakinsa ya shiga ya fada kan gado ya lumshe ido, murmushi kawae yake ba tare da yasan dalili ba.Da mamaki Ajiddeh ke dubanshi daga bakin k'ofa ganin ya dawo da wani kayan ba da wanda ya fita ba, kuma tun biyar ya fita yace mata yanzun nan zaije ya dawo amma sai Yanzu yake shigowa, ga shegiyar nan ma tun d'azu take mata knocking taqi bud'e mata k'ofa, tsaki tayi ta k'arasa shigowa d'akin, kai tsaye gadon da yake kai ta nufa ta zauna daidai kanshi ta shiga tashin shi, a hankali ya bud'e lumsassun idanuwanshi ya d'aura kanta, had'e rai tayi a dole ya b'ata mata rai tace "Aliyu tun yaushe ka fita ka barni gidan nan, daga cewa yanzu zakaje ka dawo shine ka shanya ni nan", murmushin shi mai narkar mata da zuciya yayi ya riqo hannunta ya janyota jikinshi, a hankali ya d'aura bakinshi daidai kunnenta cikin rad'a yace mata "keh wai baki iya kula da miji ba?, ba girki, ba gyaran gida, babu tsaftace ko ina sai kanki kawae, amma kinfi kowa iya mita, a haka ake nuna son?", jikin tane yayi sanyi jin abinda ya fad'a mata, toh me kuma ya kawo wannan maganan, d'ago kanta tayi ta kalli fuskanshi taga idonshi na lumshe ne har lkcn, rolling idanunta tayi a ranta tace kai ka sani, har lokacin idonshi lumshe ya sake jawota ta fad'o jikinshi yaci gaba da cewa "ko kinaso in samo wacce zata na yi min dukka wannan abun kinga kema sai ki koya gunta?", a firgice ta d'ago tana kallonshi tace "mey kake nufi Aliyu", sai a lokacin ya bud'e lumsassun idanunshi ya zuba mata su, murmushi yayi ganin expression d'in dake fuskanta ba tare da ya damu ba yace "sai in qara aure mana, kinga kin samu mai koya miki nima na samu mai bani abinci ba sai ina zuwa restaurants ba", gaba d'aya ji tayi iskan d'akin yayi mata kad'an, hannu tasa ta warware dogon gashinta mai tsayi da laushi tana mishi wani matsiyacin kallo cike da masifa tace "A ina d'in wai zakayi aure, ba dai ina gidan nan ba, wlhy Allah indai da raina baka k'ara aure, sai ina maka girki sannan zaka san ina sonka?, tun farko daga gidanmu ni ban saba da wahala ba shiyasa aka nema min masu aiki kace baka sonsu ka koresu to ya kake son inyi da kai? sai yanxu kuma kace min wani ban Iya komai ba, dama can meye auren, abun da yake ciki ai ina yi maka, shine yanzu zaka tsiro da zancen aure, duk shegiyar ma da tayi gigin aurenka sai na lahanta ta ta rasa mai aurenta wllh", tana huci ta kare maganar, da mamaki yake kallonta, dariya maganarta ya bashi sosae, wai in tans raye bai k'ara aure", kanshi ya kad'a yace "calm down, wannan hargowa tun banyi auren ba, ki bari in nayi sai kiyi using energy d'inki sai kiyi fad'an dagaske", idonta ne ya cicciko da hawaye jin abinda Aliyu ke fad'a mata, a fusace ta mik'e zata bar d'akin yasa hannu ya fizgota ta fad'o kanshi, kokawa ta shigayi dashi a kan ya k'yaleta amma yaqi, ta fashe da wani matsanancin kuka,  a hankali ya d'aura bakinshi kan wuyanta ya fara kissing har ya gangaro kan lips d'inta, kasa resisting d'inshi tayi da kokawar da takeyi dashi, lkci daya ta hadiye kukan ta bada Kai.
+

        Batuul na shiga d'aki ta fad'a gado, lumshe ido tayi tana tunanin abinda ya faru yau gaba d'aya, tunda ya sauk'e ta makaranta ya bata kud'i, bud'e mata k'ofa da kuma tafiyansu gidanshi mai kyau da abunda ya dinga yi mata yau, lumshe ido tayi tana tariyo duk event d'in da ya faru yau, wani iri ta dinga jin kanta, gaba daya ta k'asa daina tunawa, jiki a sanyaye ta mik'e ta cire Hijabin jikinta da kayan dake jikinta, jin k'anshin turarenshi jikin kayan yasa ta d'aura rigan kan fuskanta, wani irin weakness taji k'afanta ya fara, a hankali ta koma kan gadon ta zauna har lokacin rigan na fuskanta, a hankali ta cire ta ajiyeshi gefe, da kyar ta mik'e ta janyo towel ta d'aura ta fad'a toilet, nanma tafi 15mins cikin bathtub d'in da ta cika da ruwan zafi, sai da ta gaji da zama dan kanta ta mik'e ta fito daga ciki, alwala tayi ta canja pad d'inta sannan ta fito, gaban vanity table d'inta ta zauna ta shafa mai ta fesa turarukanta masu sanyin kanshi sannan taje closet d'inta ta ciro kayan bacci, short sleeping gown fari da fuskan Panda daga gabanshi ta saka, sai da ta karanta Qur'an a wayarta sannan ta kwanta bacci, ta dde kwance sae juye juye ta ke, da ta bude ido Abuturrab take tunawa, ta rasa dalili, sae kusan midnyt bacci ya d'auketa, washegari kamar yadda ta tashi jiya haka yau ma tayi, da kayan baccin nata ta sauk'o kitchen ta shiga had'a musu breakfast dan 8 take da lecture, pancake paste ta kwab'a sannan tayi strawberry syrup ta tafasa musu fresh milk ta juye a flask, a jikinta taji kamar ana kallonta daga bakin k'ofa, a d'arare ta juyo ta kalli k'ofan, wani irin k'ara ta saki zata bi k'ofan baya ta fita ganinshi tsaye bakin kofar yayi folding arms d'inshi yana kallonta, cikin hanzari ya k'araso cikin kitchen d'in yayi maza ya kamota, babu abinda jikinta yakeyi sai rawa gashi ta kasa barin su hada ido, a hankali ya jawota jikinshi ya rungumeta tsam ganin ta tsorata, patting bayanta ya shiga yi yana rad'a mata subhanallah kunnenta, har sai da yaga b'arin da jikinta keyi ya ragu sannan ya sassauta rik'on da yayi mata yana kallon kyakkyawan fuskarta da hawaye ya ziraro yace "sarkin tsoro, ni d'in kike tsoro, ina zakije da kika sa gudu, ko kamanni na ne ya canja maki?", ya sa yatsanshi yana share mata hawayen, d'an k'aramin bakinta ta turo snn ta d'ago kanta ta kalleshi tace "ni ba tsoro ka bani ba, meye xa ka tsaya a bakin k'ofa kana kallona", dariya maganarta ta bashi amma ya dake ya d'ago fuskarta da ta sauk'ar yace "jiya ma by this time kika tashi?", kanta kawai ta gyad'a mishi, saketa yayi ya koma inda burners d'in suke, pancakes d'in da ta fara soyawa ya tsaya yana kallo,  "did you make all this?", ya fad'a tareda juyowa yana kallon fuskanta, a hankali ta gyad'a mishi Kai, d'ayan tukunyar dake kan wutan ya bud'e, aroma d'in ne ya sashi yaja d'an baya yana kallonta yace "wannan ya sunanshi?", wara ido tayi a hankali tace "cream in chicken soup", kai ya gyad'a yana murmushi don ji yayi ta burgesa ba kadan ba, dawowa yayi gabanta yana kallon fuskanta yace "who taught you all this", a tak'aice tace "Aunty", ya daga kafada don yasan amsan kenan, "What time do you have lecture today?", ya tambayeta yana kallonta, tace  "8:00", waje ya samu ya zauna kan kujeran island din yana duba kitchen timer yace "and its 6:30 now" "kin iya kunu", mamaki tambayan ya bata a hankali tace mishi " Yeah na iya,wane iri?", murmushi yayi yace "any type", kai ta gyad'a mishi tace "Na iya kunun gyad'a, Mard'om, tsamiya, kanwa, alkama sai Kunun Accha", kai ya gyada alamun he is impressed yace mata "Na gyad'a nake son sha yanxu, zaki iya yi", d'an karyar da kai tayi tace "toh ai babu gyad'an yin kunun", bai ce mata komai ba ya tashi ya isa cabinet d'in ya bud'eshi sannan ya Ciro bucket d'in nik'akk'en gyad'a, da mamaki ta tsaya kallonshi, smiling yayi ganin irin kallon da take mishi  yace "Ammah packed everything for me, I love traditional food yhu knw", tab'e baki tayi ta isa Inda bucket d'in yake ta bud'e tare da d'an duk'awa tana duba gyad'an, a hankali bayan ta d'ago ba tare da ta bari sun had'a ido ba tace mishi "zanyi", yana zaune yana kallonta cikin 25mins ta had'a kunun gyad'a mai scrippers, sai da yaga ta gama ta fara kaiwa dinning shima ya fito daga kitchen d'in ya koma Palo, shi yace basai ta share gidan ba yau tunda time ya k'ure, bata ce komae ba ta koma kitchen din don tsaftace ko ina. 
    Ajiddeh kam K'aran wayanta ne ya tasheta daga bacci, tsaki tayi ta jawo wayar, time ta fara gani taga k'arfe shida da rabi na safe, juyawa tayi taga Abutturab baya d'akin sannan ta d'aga wayan a tsorace ganin mai k'iranta at wannan lokacin, a d'arare tace "Hello Mummy" tana jin tsoron kar ace wani abun ne ya faru a gida, daga d'aya b'angaren Mum tace "kina jina, Malamin nan yace aiki fa bazai yiwu ba sai kina nan kuma yace Cikin kwanaki uku in baki zo ba komai zai iya faruwa da shi kansa bae gano ba, dan haka duk yadda za ayi kisan yadda zaki yi ki iso yau d'innan ba sai gobe ba", a tsorace da jin abinda Mum ta fad'a mata tace "Mum ban san ko zai bari inzo ba", inji Ajiddeh, "kina ma da hankali kuwa, nace miki komai zai Iya faruwa shine kike cemin bazai barki ba, toh koh bai bari ba bazaki taho ba inyaso a San abin yi daga baya", maganganun Abuturrab na jiya ta tuna, hankalinta a tashe tace "toh toh naji Mummy, yanzu zanje in sameshi ince mishi an min waya ance bakida lafiya kuma kinason ganina, nasan in yaji haka zai bari, sai kiyi all things possible yadda bazai gane ba", da haka sukayi sallama akan zata k'irata duk yadda akayi, tashi tayi tana matsar k'walla yadda zatayi pretending wa Abu.

  
Batuul ta d'auko flask d'in fresh milk d'in kenan zata fito daga kitchen taga Ajiddeh na sauk'owa hankali tashe, duk gashin nan an baje shi, ae fa nan gabanta ya shiga faduwa ta k'asa karasawa dinning,
a tsorace take kallonta ganin yanayin da take, wani irin mugun kallo tabi Batuul dashi ganin irin kayan dake jikinta, har sai da tazo zata wuce ta dinning d'in a hankali Batuul tace  "INA kwana", wani kallo ta watso mata tareda hararanta, tab'e baki Batuul tayi ta d'auke kanta, dama ita kirkin da Ajiddeh ke mata ba yadda tayi dashi ba, gara tana masifan da ta Saba kawae, tana dire flask d'in hannunta ta haura sama abinta da sauri.
        Da wani irin kuka ta fad'a jikin Abutturab dake kwance kan sofa da remote hannunshi yana kallon TV, don yi yayi kamar bae san ta sakko falon ba da farko, a rikice ya d'agota ya shiga tambayanta lafiya, tana kuka kamar zata had'iyi rai tace "Mummy", tashi yayi yana kallonta yace "What happened to her", cikin sheshek'a kamar dagaske ta kasa ce mishi komai, a d'an tsawace ya d'ago fuskarta yace "talk to me Ajiddeh, what happened to Mum", a sanyaye tace mishi "Yanzu Yaa Zee ta k'irani, wai Mummy ba lafiya kuma tana son ganina", ajiyar zuciya ya sauk'e ya jawota jikinshi ya rungume yace "shhhhh, its okay , she will be alright, okay?, gobe zamuje gida", da hanzari ta d'ago tana kallonshi tace "baby bazan iya ba, inason inje inganta yau, bazan Iya ba", ta k'arashe maganar da kuka sosai, tashi yayi ya kamata suka haura sama, sai da ya shiga d'akin ya zaunar da ita kan gado yace mata tashi ki shirya kayan da zakiyi amfani dashi, yanzu zamuje muyi booking flight ko na evening ne sai mu bi", rinannun idanuwanta ta d'ago tana tana kallonshi tace "Baby ai kana da aiki, ba komai ba sai kaje ba, you should stay back ka kula da abubuwan da kakeyi, In sha Allah she will b fine", haka tayi ta insisting har sai da ta samu tayi convincing d'inshi ya fasa bin ta, bakwai da arba'in da biyar daidai suka sauk'o shida Ajiddeh tana riqe da trolley d'inta a hannu, Batuul na palo suka sauk'o tare, mik'ewa tayi tsaye har suka k'araso inda take, Ajiddeh sai hararta takeyi ta gefen ido, sai lokacin ma ya tuna da ita, kud'i ya ciro daga aljihunshi ya mik'a mata sannan yace "David ya kaiki school", da haka suka fita suka barta nan tsaye ko wayanma bai samu ya bata ba yau. Haka kawae taji ranta ya baci ta bi bayan Ajiddeh da harara, suna fita ta ja tsaki ta haura sama don xuwa dauko jakarta ta bar gidan ita ma.A bakin mota ta tarar da David tsaye yana jiranta, hannu tasa ta bud'e motan ta fad'a sannan shima ya shiga, sau biyu David na maimaita gaisuwarshi, sai a na ukun ta amsa mishi, zuciyanta ne taji yana mata xafi ta rasa dalili, ta ja tsaki yafi sau biyar zamanta cikin motan, hawaye ne mai d'umi ya shiga sirarowa daga idonta, hannu tasa ta shafo hawayen ta tsaya tana kallo da mamaki, kifa kanta tayi tsakanin cinyoyinta ta fara kukan da batasan dalilinshi ba, daga sama taji David na fad'in "We ve arrived", a hankali ta d'ago kanta ta k'arewa wajen kallo, batace mishi komai ba ta d'auki jakanta ta fita daga motan, department d'insu ta nufa taga Su Samantha da Aisha da wasu students d'in na tsaye hall way d'in, agogonta ta duba taga saura 15mins su fara lecture, tana juyawa zata bar wajen suka had'a ido da Aisha, d'auke kai Batuul tayi kamar bata ganta ba, can bayan faculty d'insu ta nufa ta zauna taci gaba da kukanta, k'anshin turare mai dad'i ne ya bugi hancinta amma bata d'ago taga daga ina k'anshin yake ba, cikin wani irin masculine voice mai dad'i da nutsuwa taji ance "Here, take this",  ta d'ago rinannun idanuwanta ta sauk'e kanshi, da sauri ta d'auke idonta ta juyar da kai gefe ta hade rae, har lokacin bai bar wajen da yake tsayen ba, juyowa ta kuma yi ta ga har lokacin hannunshi na mik'a mata farin handkerchief d'inshi, a sanyaye tasa hannu ta karb'a, wani k'anshi mai dad'i ne ya bugi hancinta da takai fuskanta, ido ta lumshe ta shiga goge hawayen dake fuskanta, daga d'an nesa da ita ya zauna, bai ce mata komai ba har sai da ta juyo ta dubeshi sannan yayi mata murmushin shi mai kyau, kau da kai tayi ta fara wasa da biron da ta ciro cikin Jakarta, a hankali ya fara magana "if you don't mind, may I know d reason behind those tears, I might help", sai lokacin ta sake tunowa da yadda taga Abu ya riqe Ajiddeh, wani siririn tsaki ne yayi escaping lips d'inta ta fara k'ok'arin maida hawayen dake shirin dawowa, jin tayi shiru batace komai ba yasa ya sake kallonta, suna had'a ido ya d'aga mata girarshi d'aya yana jiran jin mey zatace, agogon hannunta ta duba taga lokacin lecture yayi, da hanzari ta mik'e ba tareda ta bari sun had'a ido ba ta miqa mishi handki d'inshi, ganin bai amsa ba ta ajiye mishi  tace "Thank you, I need to go right away", bata jira jin cewarshi ba ta tafi cikin sauri ta bar wajen", murmushi yayi yabi bayanta da kallo tare da lumshe ido, tana isa taga har an fara shiga class itama taje ta zauna, waje d'aya suka zauna itada Aisha, bayan sun zauna ne Aisha tace "Fatima wai meye problem d'inki, ko yau you look pale, in bakida lafiya dolene sai kinzo school", had'e rai Batuul tayi tace "wa yace miki banida lafiya", dan bata jin yin magana da kowa, murmushi Aisha tayi tace "ai ba sai an fad'i ba, you look sick, red eyes, plump lips, pale face, nasan inda zan tab'a temperature d'inki nasan yayi sama", yak'e Batuul tayi tace "Am totally fine, bacci ne kawai ban samu nayi ba jiya", ta d'auke kanta tana sauraron maganan da lecturer d'insu ya fara, baki Aisha ta tab'e bawai dan ta yadda da abinda Batuul ta fad'a mata ba itama tayi concentrating da jin lecturer d'insu, Batuul dai na zaune ajin ne amma gaba d'aya mind d'inta is off, batasan ma dalilin da yake sata damuwa ba, har suka gama lecture l batayi grabbing komai ba, jiki a sanyaye ta mik'e suka fito daga lecture hall d'in, Samantha ce tace "Let's go and get some food, am hungry just as the glutton I'm, then we go home after then, no any other class, done for d day",ta fad'a tareda d'an tsalle, dariya sauran suka sa amma Batuul was absent minded bata ma san mey suke cewa ba, sai da Samantha ta sa hannu fuskanta ta fara waving sannan tace "Hello, you there", sannan ta dawo daga tunanin da take tace musu, "You carry on, I will b there right away, I need to clear somethings over here", Aisha dai batace komai ba tayi gaba abinta haka ma Samantha tare suka tafi, suna tafiya itama ta juya ba tare da tasan inda zata ba, wani guri ta hango duk bishiyoyi ne, wajen very serene, ba tareda wani tunani ba taje ta zauna abinta ta fiddo littafi kamar me shirin karatu sae dae ita kanta tasan ba karatun xata yi ba.
+

        Abutturab da Ajiddeh kam tunda suka fita airport suke abu d'aya, da k'yar ta samu kujera shima d'in ba first class amma tace taji ta gani zatayi managing, ai Uwa tafi komi, haka dai tayi convincing d'in Abu, wayanshi da ya ciro cikin aljihu don duba karfe nawa ya tuno mishi da Batuul, ba b'ata lokaci ya shiga neman number David ganin zai kai yamma bai dawo ba kuma bai bata wayan ba, David na d'agawa Abutturab yace mishi "Where are you?", David yace Sir av dropped her at school, am at the construction site now to give out d documents", d'an iska ya furzar yace "Did she tell you when she will be done?, i mean for today?", "David yace "No Sir, she didn't", Abu ya gyad'a kai yace "okay, you should leave d site now and b there at her school, make sure you wait for her to finish and take her back home", David ya amsa da "okay Sir", daga nan ya kama hanya ya koma makarantar su Batuul, inda ya sauk'eta nan yaje ya kafa motarsa, tunda yaje yake zuba ido ko zai ganta amma shiru, tun 10:30 yake makarantar gashi har 1 tayi babu Batuul, har lecture halls d'insu sai da ya riqa bi yana yi musu describing d'inta bata nan kuma an tabbatar mishi da sun gama lecture d'insu na yau, ba tare da b'ata lokaci ya ba ya kira Abutturab yace yaje bai ganta ba, calmly yace mishi ya koma yaje ya sake dubota, sau biyu yana komawa amma bata nan har wajen 4, sai lokacin hankalin Abuturrab ya fara tashi, Ajiddeh na lura da shi sae dae bata ce komae ba, Sallama yayi mata daga karshe yace xae tafi sae sun yi waya, ta wani hade rae tace " Ban gane ba Aliyu, a kan wata can xaka tafi ka bar ni jirginmu bae tashi ba, ita din yarinya ce da baxa ta iya kula da kanta ba duk xa ka wani tada hankali haka" ya daga kafada don bai son su rabu da fada yace "Chill babe, wani takardu xae kai min office to suna gida kuma wae ta kulle gidan da makulli shi yasa kika ga na takurasa ya nemota" tsaki Ajiddeh tayi tace "Toh gidanta ne xata wani kulle da makulli kuma wa ma ya bata makullin" peck ya manna mata a lip yace "Yi hakuri mai gida" turo baki tayi, yayi dariya yace "Don't worry babe, i promise to be back soon" bin sa da kallo tayi har ya bace mata kafin ta lumshe ido ta sauke ajiyar xuciya, Allah kadae yasan irin son da take ma Aliyu, kuma In'sha Allah nata ne shi din ita kadae.
Abuturrab kam direct makarantar ya wuce daga airport din, har ya gama zagaye makarantar babu Batuul, a gajiye ya dawo gida lokacin biyar da rabi, ido ya lumshe ganin  abincin da ta jera tun safe kan dinning ba a tab'a ba,sai lokacin ya tuna da zancen abinci, yasan dae baxa ta bata ba amma haka kawae ya kasa samun natsuwa. 
       Batuul kam Na zaune wannan gurin har 4:15, sosai wajen ya mata dad'i har yasa ta manta damuwar dake ranta, sai kallon tsuntsaye takeyi suna shawaginsu kan bishiyoyi da water fountain d'in dake tsakiyar wajen, agogon dake hannunta ta duba taga 4:15, a razane ta miqe ta tattare kayanta ta fito daga gun, tasan dan bata sallah ne shiyasa time ya qure har haka bata sani ba, rana har ya kusa fad'i lokacin, tafiya kawai ta shiga yi har ta iso dpt dinsu ta tsaya tana kalle kalle, bataga kowa da ta sani ba, haka kawae taji hawaye sun cicciko mata ta nufi hanyan gate a sanyaye zataje ta tari cab ya kaita gida, tafiya takeyi tana ta share hawaye, har wani blur take gani, dab bakin gate taji mota na mata horn, matsawa tayi ta bashi hanya ta koma gefe taci gaba da tafiya, ji tayi horn d'in na dad'a k'aruwa, "Fatima", a tsorace ta juyo tana kallon mai k'iranta, parking yayi ya fito yazo ya sameta inda take tsaye, fuskanta ya gama examining sannan yace mata "do you always cry?", d'ago idonta tayi ta kalle shi tace "Are you stalking me?", dariya tambayarshi ya bata yace , "Mey ya faru baki tafi gida ba tun d'azu and you finished your lecture for d day tun 10", shiru tayi bata ce mishi komai ba, tambayanta ya sakeyi jin tayi shiru yace  "ina zaki yanzu?", a hankali tace mishi "gida" ido ya wara yace "by yourself, do you normally go by yourself, mey kika zauna yi a school d'in har kika kai this time?",  kai kawae ta girgiza mishi, ya juya zai koma mota yace "let's go, I will drop", ba musu ta shiga gaba yana biye da ita a baya, shi da kanshi ya zaga ya bud'e mata k'ofa, wani kanshi ne mai dad'i yayi mata sallama, ido ta lumshe ta jinginar da kanta jikin kujera, Hamdala ta dinga yi a ranta dan dama tsoron shiga cab d'in takeyi, sai da ya fita gate d'in ya juyo ya dubeta yace "yace where are we heading to?", sai a lokacin ta bud'e idonta tace mishi ST.Georges No 15, daga nan bai sake cewa komai ba ya d'au hanya.
       Waya Abuturrab ya bugawa Mr Steven akan ayi enquiring abt Batuul dan har yanzu bata dawo gida ba kuma school d'inma bata can, daga nan ya shiga yayi wanka ya canja kayan dake jikinshi, ko mai bai shafa ba ya sake d'aukan key yayi waje, yana zuwa bakin k'ofa yaga wata bak'ar Rolls Royce ta shigo compound d'in, sai da motan yayi wajen two minutes da parkin tukunna maishi ya bud'e ya fito, ajiyar zuciya ya sauk'e ganin Batuul ta fito cikin motar yayi tucking hannuwanshi cikin aljihu yana kallonta, "Thank you" tace da Shaheed tana kallonsa, Sam bata lura da mutum na tsaye ba sai da ta juyo zata shiga gida, gabanta ne ya bada sautin dam ganin Abu tsaye bakin k'ofa ya zuba mata lumsassun idanunshi ko kifta wa bae yi gashi ya wani hade rai, dakewa tayi ita a dole tana fushi taci gaba da k'arasowa, Sai da tazo dab dashi ta kasa d'aga k'afa ganin yadda idonshi ya canja kala yana kallonta dasu, shi kam Shaheed tuni ya bar compound din ba tare da ya lura da Abuturrab ba ma, a hankali Batuul tace "Ina yini" bae amsa ta ba ya kama hannunta suka nufi cikin gida fuskarsa a daure, gabanta ya dinga faduwa har suka shiga Palo, kulle kofar yayi ya juya yana facing dinta yace "Daga ina kike?" Sunkuyar da kai tayi ganin he's serious, murya can kasa tace "School" wani tsawa ya daka mata yace "I will slap you idan kika ce min school, I repeat my self where are yhu coming from, kuma waye yayi dropping din ki yanxu" hawaye ne ya xubo idonta har lkcn bata d'ago kanta ba.

Post a Comment for "BATUUL CHAPTER 12"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...