Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

BATUUL CHAPTER 11

BATUUL CHAPTER 11

- - Post a Comment
BATUUL

CHAPTER 11

A dinning d'in ta ganshi zaune yayi serving kanshi breakfast din da ta yi yana ci, Ajiddeh na daga gefenshi tana ta kumbure kumbure, tana ganin Batuul ta watso mata wani mugun harara, ko kallonta Batuul batayi ba ta karaso cikin falon ba tare da tace musu komai ba ta wuce, har ta kai bakin kofa idon shi na akanta, sai da yaga fitanta snn ya maido da hankalinshi kan Ajiddeh da ta zuba mishi ido rai a b'ace tana kallon yadda yake kallon Batuul, yasan driver bazai tafi ba sai ya jirashi ya fito dan yana son bata wayanshi in ta tashi a k'ira a d'auketa kuma ya bata kud'i, yi yayi kamar bai San kallon da take mishi ba yace "so you ain't eating har yanzu, kilan zaki dafa ne ko kuma sai na tafi zaki faraci ta shigo ta ganki kinaci kije kina amai koh", ya karashe maganan yana murmushi, sake hade rai tayi tace "kaga nifa wulakancinka ne banaso Aliyu, koh jiya a gabanta ka dinga min dariya, ko ta rainani ai kai ka jamin, bare ma bata isa tayi hkn a gidana ba", bai ce mata komai ba yaci gaba da cin abincinsa yana murmushi, sai had'iyar miyau take tana kallon yadda yake cin abincin, duk yadda akayi abincin nada dadi ganin yadda yake ci sannan ga k'anshi duk ya gama bad'e ta a gun, kallonshi tayi rai a b'ace tace "magana fa nayi maka amma kaqi kulani sai tunkud'a abinci kakeyi kamar wanda bai tab'a ci ba", kallonta yayi da idanunwanshi dake piercing zuciyarta yace "ko kin taba dafa irin wannan ne a gidannan da kike cewa inaci kamar ban tab'a ba", baki ta turo tace "nifa duk ba wannan ba, ai abinci ga ka gashi, baby ni abinda na tambaya tun jiya, I urgently need it, gashi har ka shirya bakace komai ba fa", cike da shagwaba ta kare maganar, shi kam har ta gama maganan bai ce mata komai ba, da alama santin chips d'in Batuul yasashi kasa magana, ran Ajiddeh ne ya fara b'aci, tashi tayi a fusace zata tafi ya riko hannunta da sauri, ya dawo da ita ya zaunar kan dinning chair din, kallonta yayi da murmushi a fuskanshi yace "keh bakisan in mutum na cin abinci bai son damuwa ba, da kinci abincin kema nasan all your worries will b cleared away" wani irin kallo ta mishi yace mata "tunda bakici je d'auko min cheque d'ina a sama", da murna ta mike ta haura sama, bata jima ba ta sauko rike da cheque book dinshi a hannunta, har saida ya gama cin abincin tukunna ya janyo ya rubuta mata amount din da take bukata, murna ta dinga yi kamar mey, har bakin kofa ta rakoshi tareda yi mishi peck a kumatu sannan yayi mata sallama ya tafi.+

Inda Batuul taga driver na tsaye nan ta nufa, da kanshi yazo ya bud'e mata k'ofa tareda ce mata "Morning Ma'am" kai ta gyad'a mishi ta shiga ta zauna ba tareda ta iya ce mishi komai ba, ganin bai tada motar ba yasa tace mishi "am getting late, let's get going" babu musu ya tada ya d'au hanya, har suka isa school ranta b'ace yake, tasan ta riga da tayi missing first lecture, har gaban department dinsu ya kaita, kamin ya fito ya bude mata kofa ta bude ta fito, wucewa tayi lecture hall ta tadda ana lecture , shiga tayi ta zauna ba tareda ta cewa Kowa komai ba, Aisha dake gaba sai kallonta takeyi haka ma Samantha, sai da ta zauna tukunna suka juyo suka ci gaba da sauraren lecturer, batafi 45mins da shiga ba lecturer ya gama ya fita, a tare Samantha da Aisha suka yo wajenta, Aisha ce ta fara ce mata "don't tell me har kin fara latti daga farawa", kamin tayi magana Samantha ta karb'e da cewa "Hey love you were late today, and you missed almost two lectures today, you okay?" , hawayen da take ta kokarin maidawa ne ya shiga zubomata, a tsorace su Samantha ke kallonta ganin yadda take hawaye, janyota Aisha tayi ta rungume, Samantha ce tayi mata alama da ta jata suyi waje, sai da sukaje inda babu mutane tukunna suka zaunar da ita, kuka sosai ta shiga, babu abunda sukeyi sai rarrashinta, har suka gaji suka rabu da ita, sai da tayi mai isarta tukunna tayi shiru dan kanta, hawayenta tashiga gogewa da hannu sannan ta dubesu tace "what were we thought, I mean d topic", Aisha dan haushi ko kallonta batayi ba, Samantha ce tana kallonta tace "It seems you are hungry, let's go and get something to eat, am also famished" kallon Aisha tayi taga ta had'e rai, jiki a sanyaye tace "Aisha cikina ke ciwo", cikin sanyi Aisha tace "toh Fatima koh baki d'aukemu komai ba ai kinsan bazamu cutar dake ba, ciwon ciki dai ko clinic ai sai muje a baki magani, amma kinzo late we were worried sannan kuma kiyita kuka kiki bamu ansa", Samantha dai baki ta bud'e tana kallonsu, sai da taji sunyi shiru sannan ta dubi Aisha tace "She said what, what's d problem?", a takaice Aisha tace "stomach ache", ido Samantha ta xaro tace "then?, we should be in the clinic, let's rush her", kai Batuul dake zaune ta girgiza tana kallon yadda Samantha ta rud'e tace "I will b fine dear, you shouldn't worry, it usually does, I will take my medication when am back home", da rashin gamsuwan abinda ta fad'a musu Aisha ta girgiza kai tace "Fatima bafa cutar dake zamuyi ba, nanfa kika zauna kina kuka amma kice wani wai you are okay, how does that even makes sense", ta k'arashe maganan ranta b'ace, a hankali Batuul ta kamo hannunta ta zaunar gefenta tace "dagaske nake ya daina, kinga Kuma inada magani na a gida, ba lallai school clinic suyi min prescribing irinshi ba" sai yanxu Aisha ta yadda ta fad'awa Samantha yadda sukayi, littafin dake hannun Samantha Batuul ta ansa tana Kallo tace "Did I miss so much", Kai Samantha ta girgiza tace "you got no worry, I will explain everything", giranta d'aya Batuul ta d'aga, Samantha na kallonta ta fashe da dariya tace "yeah you gat my back" tanayi tana kad'a kai, dariya su dukan suka sa, Samantha tace " SHIT!,But girl you scared me, you shouldn't cry again when am there, I have this terrible phobia of tear, it doesn't even have a name", dariya ta basu, Batuul tace, "not in my weirdest dream, its not happening again I promise" ta k'arashe maganan tareda mik'ewa dan taga duk jikinsu yayi sanyi, sai da ta mik'e ta fara tafiya tukunna ta juyo ta dubesu tace "who is joining me for a cup of frapuccino", a tare suka mik'e suka biyota, suna isa wajen taji cikinta ya k'ulle, a hankali ta fara d'aga k'afarta ba tare da ta bari sun gane, har suka samu waje suka zauna cikin bai barta ba, k'aryan da tayiwa su Aisha ne ya dawo mata, dama ance babu kyau k'aryan ciwo, d'an k'aramin tsaki taja dan tasan period d'inta can come anytime tunda har cikinta ya fara ciwo, waiter dake aiki a wajen ne ya iso wajensu, ya tambayasu abunda xa a kawo musu, Samantha tace "Serve me caramel", juyawa yayi ya kalli Aisha yace "Ma'am what would you like to have?" , kallonshi tayi tace "Hazel nut sugar free and and chicken lasagne", daga haka ya juya yana kallon Batuul da taketa tunani hankalinta ma baya wajen, sai da Aisha ta d'an tab'ota tukunna ta d'ago tana kallonsu, tambayanta yayi itama me take so, tunda har cikinta ya fara ciwo in tasha abu mai zak'i wahala ne zai k'aru mata gashi batada magani, ita pad d'inma bata dashi, tunanin hakan yasa ta hawaye da tayi k'ok'arin maidawa, jiki a sanyaye tace mishi "peppermint sugar free", da haka ya tafi yaje kawo musu, baifi minti biyar da tafia ba ya dawo riqe da tray, ajiyewa kowa abinda yayi ordering yayi sannan ya bar wajen, sai da suka kusa gamawa kanta a k'asa taji anyi musu sallama, bata d'ago ta Kali mai sallaman ba amma tasan namiji from his voice, kujeran dake gefenta taga yaja ya zauna, ji tayi yana cewa "This isn't fair, you girls enjoying without an invitation?", Samantha ce tace "Hey lemme order one for you, ta juya zata k'ira waiter, hannu ya d'aga mata alamar surrender yace "Hey No Thank you, am okay", kallonshi Aisha tayi da mamaki ganin baya tab'a kula matan dake binshi ma amma yanzu shi da kanshi yake zuwa inda suke, a hankali Aisha tace "You sure?", kai ya gyad'a mata tareda da yi mata murmushin shi mai kyau, kallon Batuul yayi yace "Sai dai in wannan da bata magana xata bani nata, I will gladly take it", Batuul batasan ma sunayi ba dan hankalinta ma baya kansu, kud'in frapuccino da zata biya ma bata dashi a yanzu haka da take zaune, tunaninta sam bai kawo bata da kud'i ba har sai da ta tuna ba da jakan jiya ta fito ba kuma yau bai bata kud'i ba, d'an tab'a table d'in yayi yace "y'ar uwa tunanin mey kikeyi, you are too young for that", sai a lokacin ta d'ago ta kalleshi da murmushinshi mai kyau a fuskanshi, ajiyar zuciya tayi tace "Ba tunani nakeyi ba", tsareta yayi da ido yace "okay tell me what we just said", shiru tayi ta d'auke kanta, murmushi yayi yace "you see you can't say, ki dena its not good for you at such a tender age", batace mishi komai ba itadai, dan tama manta da sunanshi ko jiya da ya fad'a musu, alama yayiwa waiter yaxo, ce mishi yayi ya bashi bill d'insu, shi ya biya musu duka kud'in abunda sukaci, duk da suna ya bari bai sauraresu ba, Samantha ce ta mik'e tace "okay Mr Shaheed, we got class now, hope to see you ltr, and thank you for all" murmushi yayi mata kawai yana kallon Batuul dake Zaune, ciwon cikinta na dad'a k'aruwa, a hankali ta mik'e tana kallonshi taga shima ita yake kallo suka had'a ido, maza tayi ta d'auke idonta tace mishi "mun gode" murmushin sa na nan fuskanshi har lkcn yace "its okay", daga haka suka mishi Sallama suka wuce, bayansu yabi da kallo har sai da ya dena kallonsu ya juya tareda murmushi, suna tafiya Samantha tace "He is such a gentle man, am already crushing babes", Aisha kawai ta biye mata Batuul kam shiru tayi tana jin abinda ke damunta har suka isa class
Abuturrab na fitowa ya shiga Duddubawa ko zai ga motar driver amma wayam, da mamaki ya ciro waya ya k'irashi, yana d'agawa yace "I didn't say you should leave, where are you guys", a daburce driver yace "Sir Ma'am insisted we should leave, and am by d office now, av already dropped her", rai a b'ace ya katse k'iran ba tare da ya jira driver ya k'arasa magana ba, he wanted giving her money, kuma inma ta gama lecture ya za ayi tasan anzo d'aukanta, d'an tsaki yaja ya fad'a motarsa, awa biyu sukayi suka fito daga class d'in, gumi sosai takeyi tsabar azaban ciwo amma ta daure dan bataso su Aisha su sani, Aisha ce ta fara yi musu sallama ta wuce yau da yayarta zasu tafi, bayan minti kamar Sha biyar Samantha ma ta wuce, sai lokacin tayi tunanin bata fad'awa driver ya dawo lokacin ya d'auketa ba ya fad'o mata, waje ta nema ta zauna ta kifa kanta kan gwiwa ta fashe da kuka, sunan Aunty kawai take k'ira, ita Yanzu ya zatayi ga ciwon ciki da zai hanata takawa ta tafi da k'afa tunda ba nisa sosai, gashi bata da kud'i bare tayi karambanin hawa Bus ko Taxi tunda ba lallai ma ta gane ba, kuma batada number Yaa Abu bare ta k'irashi tace ta gama lectures azo a d'auketa, to in ma tana da shi iya kiransa xata yi, kuka sosai takeyi kamar wacce ake zanewa, tafi awa d'aya zaune a wajen, kamar daga sama taga mota yaja ya tsaya gabanta, a hankali ta d'ago rinannun idanuwanta dai dai lokacin da ya fito daga motan, tsayawa yyi ya hade rae yana kallonta, sunkuyar da kai tayi ta mike a hnkli tana jan kafa ta xaga xuwa seat din gaba, tana shiga motar shi ma ya shiga ya rufe, ya juya yana kallonta fuskarsa daure sae dae fa har da borin kunyan daxu da safe yace "How dare yhu xan ba driver na order ki sa ya ketare? Kin yi employing driver ne garin nn?" D'ago kai tayi tana kallonsa, sae a snn ya lura da idonta da yyi ja, kana ganinta kasan kuka tayi, d'an kyabe baki yyi ya tada motar ya ja ya nufi gida, jinginar da kanta tayi jikin kujeran motar ta lumshe ido tana jin ynda ciwon cikinta ke karuwa ba kadan ba, yana gama parking a garage ya bude motar ya fita ba tare da ya bi ta kanta ba, da kyar ta bude motar ta fito, bata jira ya kulle motar ba ta nufi cikin gida, bin ta yyi da kallo yana mamakin halinta, komai kuka kmr wata 'yar goye, tsaki yyi ya rufe motar ya nufi cikin gidan shi ma. Bbu kowa falon Batuul ta haura sama da sauri ta shige dakinta ta sa key ta fada kan gado ta cusa kanta cikin pillow ta dinga rusa kuka kamar ranta zae fita, juye juye ta shiga yi ta sauko k'asa ganin kwanciyar ma ya gagareta, kan kace me duk ta fita hayyacinta. Abuturrab kam bedroom dinsa ya shiga, ya nufi toilet yyi wanka, xaune ya samu Ajiddeh dakin da ya fito, ta mike tace "Babe wllh na mance ban gaya maka ba, lotions dina sun kare, gashi akwae wani turare don nake son siya, xan kuma sake kayan make up" wani kallo ya shiga mata yace "Wae ke wace irin mace ce Ajiddeh, how on earth mijin ki xae dawo daga aiki bbu sannu da xuwa, baki bari ya huta ba, baki kawo masa ko ruwa ba ki xo kina masa lissafe lissafen banxa, to bani da kudin siyan komae ynxu" sakin baki Ajiddeh tayi tana kallonsa, sae kuma ta ja tsaki tana hararansa cike da fitina tace "Toh idan ban maka lissafe lissafe ba Aliyu wa xan ma, ko ina da su xan xo ince maka bbu, ubana xan kira ince yyi min bayan kana da halin min" kayansa ya sa ya fice daga dakin ya bar ta nan tsaye, downstairs ya sauka ya kwanta dogon kujera ya lumshe ido, to ita kuma wancan kukan me take a sch, tsaki yyi ya mike xaune ya jinginar da kansa jikin kujera, shi kam kawae wahala aka hadasa da, mikewa yyi ya koma sama ya nufi dakin Batuul, kwance ya sameta kasan dakin tana juye juye tana kuka, tsayawa kallonta yyi da mamaki, shi dae ya shiga uku, karasawa dakin yyi ya durkusa gabanta ya dagota yana kallonta yace "Wae ke kina da hankali kuwa?" Kuka take tana yarfe hannu tana neman kwace kanta daga rikon da yyi mata, jawota yyi jikinsa don xuwa ynxu ta d'aga masa hankali yace "Wae wats wrong with yhu, me ya faru ki gaya min? Talk to me plss, What happen" rufe fuskarta tayi jikinsa tana kuka, ya dago kanta yana kallonta yace "Fateema!" Da kyar tace "Cikina ke man ciwo" yace "Ciki kuma? What did yhu eat at sch" girgixa masa kai tayi ta runtse ido tace "Nothing!" Sae kuma ta fashe da kuka, duk ta rikitasa yace "Wait yana maki haka a gida ne, wani irin magani ake siya maki?" Boye fuskarta tayi jikinsa taki cewa komae sae kuka don ita kadae tasan axaban da take ji, murda kofar dakin aka yi, ae da sauri ya turata ya mike ya koma baya, Ajiddeh ta shigo ta tsaya daga bakin kofar fuskar nan nata daure tana kallonsu, kame kame ya shiga yi yace "Kinga babe wae cikinta ke ciwo kuma taki fadin cause din, nd nd... Wat are we going to do to her then, ko mu tafi clinic?" Ajiddeh ta yatsine fuska tace "Cikinta ke ciwo ko kuma tana Al'ada?" Kallon Ajiddeh ya tsaya yi kafin ya juya ya kalli Batuul da tayi k'asa da kai tana hawaye, Ajiddeh ta watsa mata harara tace "Ko ba jini bane?" Ae Batuul k'asa dagowa tayi, Ajiddeh ta ja tsaki ta fice daga dakin, kallonta Abuturrab ya tsaya yi, ta ki bari su hada ido.K'arasowa yayi gabanta ya d'agota yana kallon yadda gumi yasa front hair d'inta kwanciya, sae kuma ya hade rae yace "dama haka yake yi miki can gida" jin taki cewa komae ya jawota jikinsa, ya rasa dalilin da yasa tausayinta ke shigansa hka, ko don amanarta Ammah ta basa ne yasa hakan, k'asa yyi da murya yace "Tambayan ki nake, talk to me" sake shigewa tayi jikinshi tana riqe cikinta, kuka ta shiga yi mishi tana ta mutsu mutsu, gaba daya ta rikitashi da kukanta, kokarin tashi takeyi daga jikinshi ganin amai na shirin zuwa mata, ya riketa yana kallon fuskanta da ya gama jikewa da hawaye yace "kina da magani ne" kai ta shiga girgiza mishi, wani karfi taji yazo mata ta janye jikinta daga rikon da yayi mata xata mike ya rikota yace "ina zakije", yana mata mugun kallo dan ranshi ya fara b'aci, bakinta ta toshe tana girgiza mishi kai, ce mata yayi "amai zakiyi", kai ta gyad'a mishi sauran hawayen idonta na k'arasa zubowa, k'arasawa yayi da ita toilet d'in, tun kan su shiga ta shiga kwarara amai nan bakin kofar, har ta gama yana riqe da ita, da k'yar ta samu ta miqe, jiri ne taji yana kwasanta ta sulale k'asa a wajen, binta yayi ya kamota jikinshi tare da miqar da ita, babu abinda takeyi sai hawaye, d'ago kanta yayi yana kallonta yace "are you done", kai ta gyad'a mishi ta maida kanta ta kwanatar jikinshi dan rashin k'arfi, ji takeyi kamar zata fad'i in ba a riqeta ba, gaban sink ya dawo da ita har lokacin tana jikinshi, sai maida numfashi takeyi, tap din sink din ya kunna, ya sata wanke baki da fuskanta, har ta gama. Idonta na rufe, bata ankara ba sai ji taji ya sunkuceta a hannunshi, ta bud'e ido da sauri tana kallonshi, harara ya sakar mata ya wani hade rae, maza tayi  ta rintse ido har saida taji ya sauk'e ta kan gado tukunna ta budesu a hankali, bayanshi kawai ta iya gani har ya kai bakin k'ofa, rintse ido tayi hawayen azabar take ji yaci gaba da zubowa, pad d'in da zatayi amfani da ma ita batasan ina zata samu ba tukunna, kuma tunda har tayi amai, ya kusa zuwa kenan, yana fita d'akinshi ya wuce, zaune kan gado ya tadda Ajiddeh, da alama waya ta gama, bai bi ta kanta ba ya wuce ya d'au keyn motan shi yayi hanyan fita, a guje ta diro daga kan gadon ta sha gabanshi tace "yaushe ka dawo ne da har zaka kuma fita Aliyu, kuma ina zakaje da yamman nan hka", bae tanka ta ba ya bi gefenta ya fita, ganin yayi hanyan d'akin Batuul yasa ta k'ara hasala ta sha gabansa tsabar masifa har idonta ya kankance tace "Aliyu ba dai gun wannan yarinyar zaka ba, wannan ai iskanci ne, period dinne takewa iskancin nan kamar yau ta farashi, ko kuma sabon salon karuwancin nata ne hakan", wani mugun kallo ya bita dashi ya sa hannu ya matsar da ita gefe ya ci gaba da tafiyarsa, biyoshi tayi a baya tana ta mishi surutun da baima san mey take fad'a ba, k'ofan d'akin Batuul ya tura ya shiga, tana kwance kan gadon nan inda ya barta, k'arasawa yayi bakin gadon daga tsayen da yake yace "zaki iya tashi?", a hankali ta bud'e lumsassun idonta ta kalleshi, hade rae yyi ya sake nanata mata tambayan, k'ok'arin tashi ta shiga yi, da k'yar ta samu ta mik'e xaune, hijab dinta dake gefe ya mik'o mata ta saka, Ajiddeh dake bakin k'ofa baki ta sake tana kallonshi tana huci, da k'yar Batuul ta mik'e yana kallonta yace "can you walk?", a hankali ta gyad'a masa kai,  ita ta fara wucewa gaba yana binta a baya, ja tayi ta tsaya ganin Ajiddeh bakin k'ofa, a d'an tsawace yace "muje mana", a hankali ta juyo idonta yayi raurau tana kallonshi, hannu yasa ya rik'ota, har bakin k'ofar ya isa da ita, wani mugun kallo yayi wa Ajiddeh cikin kakkausar murya yace "give me way", ganin yanayin da yayi magana ya sata tsorata, bata tsaya musu ba ta matsa daga bakin k'ofa, tana yi ma Batuul wani mugun kallo da yasata saurin d'auke kanta, a hankali yake tafiya tana biye dashi har suka isa bakin stair case, ji tayi cikinta yayi wani irin kullewa, ae bata san lkcn da ta sulale ta zube wajen ba tace "Ya salam" ya salam
d'in da ta ambata ne ya sashi juyowa da sauri durkusawa gabanta yyi ya shiga tamabayanta baza ta iya tafiya bane, a wahalce ta gyad'a mishi Kai, hannu yasa ya d'auketa cak, Ajiddeh dake tsaye a bakin k'ofa, a tsorace take kallonsu, sosai zuciyanta yake bugu kamar zai fito, idonta har ya cicciko, har cikin mota ya sakata sannan ya zaga shima ya shiga ya tada suka bar gidan, driving yakeyi lokaci lokaci yake juyowa yaganta tana ta murk'ususu, wayanshi ya d'auka ya sanar da doctorn shi gasu nan zuwa, har suka isa asibitin idonta rufe yake tana hawaye, shi ya taimaka mata ta fito, tana riqe jikinshi suka isa cikin asibitin, direct office d'in consultant d'inshi ya wuce da ita, sai da ta zauna shima ya zauna, bayan sun gaisa ya juya yana kallon Batuul yace "Hello young lady , what's d problem", shiru tayi ta kasa ce mishi komai, Abutturab ne ya kalleta yace "baza ki bud'e baki ki fad'a mishi abinda ke damunki ba", kanta ta kauda gefe, likitan ne da kanshi ya mike yace "its okay, let me examine", tashi yayi ya matsa gaban computer shi sannan yace mata ta taso ta kwanta kan gadon dake office din, a hankali ta mike ta isa kan gadon, kallonsu kawai Abutturab keyi ganin yadda take ta gyara hijabin jikinta bataso a d'age, sai da likitan yayi y'an gwaje gwajenshi sannan ya dawo kujeranshi ya zauna yana kallon Abu yace "Is she married?" Kai kawae Abuturrab ya gyada masa, likitan yace "Alryt! she is having menstrual cramps which is caused by the condition of the reproductive tract, such as the endometriosis, uterine tissue that appears outside the uterus, it also happens because the contradictions in the uterus or womb, which is a muscle, if it contracts too strongly during her menstrual cycle, it can press against nearby vessels. This briefly cuts off the supply of oxygen to the uterus, it's this lack of oxygen that causes the pain or cramping", har saida yayi shiru tukunna Abutturab yace "But can it be avoided or controlled?, I mean the pain", murmushi likitan yayi yace "well yeah it can, the pain usually stops when they get married or even after delivery, so maybe when she delivers as you say she is married and she still encounters d pain, If its a mild menstrual cramp, she should take aspirin or another pain reliever, such as ibuprofen, naproxen or acetaminophen, its for d best relief  as soon as bleeding cramps start", kallon inda take kwance yayi yaga idonta na lumshe, sannan ya juyo  yana jin sharhin da likitan ke mishi, Kowa da inda kwarewarsa take, ya kalli doctor yace "Doctor but is there any home remedy for it, like first aid treatment", kai likitan ya gyad'a yace, "Heat can also help, placing a hot pad or a hot water bottle on her back or lower tummy, taking a hot water bath may also provide some relief, rest when needed, avoid food that contain caffeine and salt, not use tobacco or drink alcohol, too much sugar also should b avoided and chocolates also, massaging of the lower back and abdomen, women who exercise regularly often have less pain also", ajiyar zuciya Abu yayi, murmushi likitan yayi yace "its normal you should not worry, just that others experience more pain, I will b giving her an aspirin injection now, she will b okay", mik'ewa yayi ya isa inda take kwance ya shiga had'a alluran da zaiyi mata, ji tayi kamar mutum na tsaye a kanta, a hankali ta bud'e idonta, kan Alluran dake hannun likitan idonta ya fad'a, a zabure ta mik'e tana girgiza kai, da murmushi a fuskanshi yace "It won't hurt much young lady" hawaye kawai takeyi tana kallon Abu, tasowa yayi shima ya dawo gaban gadon yana mata wani irin kallo, kuka ta fashe da tace "Yaa Abu allura zaimin, banaso xae daina min da kanshi after somedayz", rik'ota yayi jikinshi yace "shhhh, he said it, it won't, close your eyes", rintse ido tayi, shi ya janye hijabin dake jikinta, k'ank'ameshi tayi idonta rufe har aka tsikara mata alluran, sai da aka gama ya d'agota , drugs likitan yayi musu prescribing daga nan sukayi mishi sallama suka wuce, shi ya taimaka mata har wajen mota sannan ya zaga ya shiga shima, a wajen wani saida abinci ya tsaida motanshi, juyawa yayi suka had'a ido tayi maza ta janye nata, "I will b right back", ya fad'a mata sannan ya wuce, kafin ya dawo harta yi bacci dan ciwon ya fara saketa,  ganin tana bacci yasashi murmushin da baisan dalilinshi ba ya shiga motan, k'ok'arin gyara mata kwanciya yayi, a hankali ta bud'e idon baccinta ta kalleshi, yana kallonta yace "sleep back", gyara kwanciyarta tayi taci gaba da baccinta har suka isa gida, a hankali ya shiga tashinta bayan ya gama parking, lumsassun idanunta ta bud'e, yace mata "we are home", jiki ba k'wari ta sako k'afa waje ta fito, shi ya d'auko ledan magani da abincin da ya siyo ya biyota dashi a baya, d'akinta ta wuce kai tsaye ta fad'a gado taci gaba da baccinta. Ajiddeh kam suna barin gidan dama ta shige dakinta da gudu tana rusa kuka ta dauki wayarta ta shiga kiran layin uwarta, sae da ya kusa katsewa aka d'aga, ta fashe da wani matsanancin kuka daga daya bangaren uwartata a rude ta shiga cewa "subhanallahi, lafiya Ajiddeh me ya faru?" Cikin kuka tace "Wayyo Mumy ni na gaji da wnn wahala da nake yi kan Aliyu, Mumy ina cikin tashin hankali don ga dukkan alama wllh aiki ya lalace gaba daya, sae kin ga abinda yake min ynxu, walakancin yau daban na gobe daban, ga shegiyar da ya dawo tare da ma na rasa yanda xan yi da ita a gidan, yanxu haka fa tare suka fita don iskanci wae tana al'ada ta ishe mu da kuka a gida, sae kin ga walakancin da yayi min da na tambayesa inda xa su, wayyo ni Mumy kar ta kwace min miji ya ji yana sha'awar aurenta don wallahi sae kin ga yanda ta iya girki yarinya" cikin matsanancin kuka ta kare maganar, Mumy tace "Ke dae shashasha ce wllh Ajiddeh, ina ruwan ki da wata yar iska can ke da xa ki turo kudi mu koma gun bawan Allahn can a san abun yi, da yyi niyyar aurenta ae ba ke xae aura ba ita xae aura tunda sun fi kusa can munafukae, kawae dae an hado shi da ita ne don take maki lekan asiri ke kuma wawuya baki gane ba, har xaki wani d'aga hankali ke da xaki saita ma shegiyar xama ta ji xaman gidan ma ya isheta, yarinyar da ba ma wani kyau gareta ba in ban manta ba sae wani dogon hanci kmr tsiya, meye kuma xaki damu kan ki, yana da kamar ki fara doguwa siririya kyakkyawa ga diri, g'ashi har gadon baya, yanxu dae ko kudinsa ya kama ki dauka kawae ki dauke ki turo mu san abun yi, ita kuma shegiyar ki daina d'aga hankali kanta baxa ta dade maki a gida ba nasan abinda xan yi" Ajiddeh na share hawayen idonta tace "Toh shknn Mumy xan turo ko xuwa gobe" nan Momy ta dinga mata hudubar tsiya tana digesting har  taji tsayawar motar Abuturrab, ko kan ta fito har Batuul ta shige daki dama, hakan yasa ta nufi stairs, suka kusa cin karo da shi, kallo daya yyi mata ya ga ynda idonta ya kumbura saboda kuka, ya bi gefenta xae wuce ta sha gabansa tana masa kallon raini tace "Wllh yau sae dae ka xaba ko ni ko wancan karuwar a gidan nn, idan ba karuwanci ba don tana jini har sae ta so ka sani tana wani murkushe murkushe kana daukar ta? Ta ina ta xama muharramar ka, to Allah baxa ta kwanan min a gida ba yau, ka je ka biya mata hostel" banda tafasa bbu abinda xuciyarsa ke yi, acting gently yace "Bani hanya in wuce" tana masa matsiyacin kallo tace "Naki sae ka xabi ko ni ko karuwan can" cikin kakkausar murya yace "Xa ki sa na maki abinda ban taba maki ba Ajiddeh" wani shewa ta saki tace "Ka Dade baka yi ba Aliyu, uwar meye baka min ba daga cikin walakancin ka har...." Bata rufe baki ba taji saukan lafiyayyun mari har biyu ya shaketa ya ja ta tun daga sama har suka sauko k'asa ya jefar da ita falo yyi wani irin ball da ita, ae daina gani tayi na 'yan dakiku, bin ta yyi yana huci ya kuma fixgota yace "Don kaza kazan ki ke kika koya mata karuwancin?" Cikin tsawa yace "Answer me kar in sumar da ke a nn, kin san matsayin ta a gidan nn kike kiranta da karuwa?" Jefar da ita ya kuma yi ya nufi sama yana huci.D'akinshi ya shiga bayan ya kwashe ledojin da ya zubar corridor tun lokacin da Ajiddeh ta fara mishi shirmenta, babu abinda yake buk'ata irin ya watsa ruwa a lokacin, toilet ya wuce ya sakarwa kanshi hot shower, har saida yaji ya fara komawa daidai sannan ya fito daga cikin cubicle d'in wankan, alwala yayi a sink sannan ya fito cikin toilet d'in, gaban vanity table ya tsaya ya shafa mai sannan ya fesa turarukanshi masu k'anshi, closet d'inshi ya bud'e ya ciro farar jallabiya cikin jerin jallabiyoyin dake a ciki, xirawa yayi har xai fita idonshi ya fad'a kan ledojin dake ajiye a k'asan d'akin, d'an tsaki yaja ya kwashi wasu daga ciki ya fice waje, d'akin Batuul ya wuce kai tsaye ya tura k'ofan ya shiga, tana kwance kan gado ta kifa cikinta, rabin k'afanta duk ya sauk'o daga kan gadon, d'an tsaki yaja ganin bacci takeyi ya ajiye ledojin dake hannunshi ya fita, makulli ya sa ma kofar dakin ya rufe, snn ya sauk'o kasa don tafiya masallaci, bai tarar da Ajiddeh a palon ba ya fice masallaci, sai da akayi isha sannan ya shigo gidan, wutan palon ya kashe ya haura sama, har lokacin Batuul na bacci, a hankali ya d'an tab'a  ta alamun ta tashi, a hankali ta bud'e idonta daga nannauyan baccin da take yi, ganinshi a tsaye yasa tayi maza ta mike zaune, had'e rai yayi yace "tashi kici abinci kisha maganinki", baki ta bud'e zatace mishi ita bata jin yunwa, wani kallo da ya bita dashine ya sata zumb'uro baki ta miqe a hankali, yana tsaye ta shiga toilet tayi brush ta fito, kamar zatayi kuka lokacin da ta fito daga toilet d'in dan har ta fara bleeding kuma bata san inda xata samu pad ba, har lokacin da hijab a jikinta, kan gadon ta koma ta zauna a d'arare, tana tsoron b'ata bedspread d'in, "Ni zan tashi in kawo miki abincin", ya tambayeta yana jifanta da wani irin kallo, jiki a sanyaye ta mik'e zata sauk'o daga kan gadon ta take dogon hijabin dake jikinta, fad'uwa tayi k'asa ji kake tim, y'ar k'ara ta saki da yasa Abu saurin k'arasowa wajenta, d'agota yayi yana kallon idonta da ya cicciko yace " c'mon kin cire hijabin nan ko sai na b'ata miki rai yanxun nan, yhu are bothering me fa a gidan nan", raurau tayi da idonta tana tsoron ta cire hijabin dake jikinta ko tayi staining kayanta, ganin ta tsaya taqi yin abunda ya sata ya sa ya d'age hijab d'in da take qin cirewan, y'ar k'ara ta saki ta d'urk'ushe a wajen, binta yayi ya kamota yace "ina miki wasa ko", kai ta shiga girgiza mishi tana hawaye, yace "Au kuka ma kika sami daman yi?", sulalewa ta shiga yi daga rik'on da yayi mata zatayi k'asa, ya wani fixgota yana mata mugun kallo yace, "I will slap you right now, meke damunki?", shiru tayi ta kasa mishi magana, tsaki yayi ya turata "tashi ki d'auki abincin nan" ya fad'a mata a tsawace, jiki a sanyaye ta tashi ta isa inda ledojin suke tana hawaye, a hankali ta shiga bud'e ledan, pad ta fara cin karo da, ajiyar zuciya ta sauk'e ganin pad d'in a ciki, a hankali ta d'ago idonta taga ita yake kallo a tsayen, harara ya sakar mata da yasa tayi saurin d'auke kanta, maza tayi ta ciro pad d'in daga cikin Leda ta miked da sauri ta shige toilet ta banko k'ofar, bin inda tabi yayi da kallo, tsaki yayi tareda girgiza kai, sae kuma yyi murmushi ya fita daga d'akin.
+

      Palo ya koma ya kwanta, remote ya d'auka yayi powering TVn, yunwa yakeji amma bazai iya tashi ba, he is too stressed, kitchen ya koma ya had'a coffee, snn ya dawo parlour ya jinginar da kanshi kan sofa yana kurb'an coffee d'inshi a hankali, tasha ya canja daga TLC zuwa NATgeo Gold, don Ajiddeh ke kallon TLC, d'an tsaki yaja tunawa da yayi da ita da shirmen da ta gama yi mishi d'azun, ko kadan bae yi nadamar abinda yyi mata ba don ta kai sa bango, iska ya furzar daga bakinshi yaci gaba da shan coffeensa a hankali, ta baya yaji an rungumeshi, ko ba k'anshin turarenta ba yasan ita ce, ya b'ata rai, a hankali cikin rad'a tace mishi, "baby fushi kayi", k'in kulata yayi kamar baisan tana wajen ba sae dae he was so surprise bae yi tunanin xata sakko da wuri haka ba, kai it's vry unusual of her ma kawae, sae dae if she's up to something, zagayowa tayi ta gabanshi ta zauna kan cinyarshi tareda sak'alo hannayenta duka biyun wuyanshi tace "babe, am am sorry", ci gaba yayi da kallonshi kamar baiji mey take cewa ba, fuskanta ta kawo daidai nashi tace "talk to me mana babe, am truely remorseful wllh, sae daga baya naga ban kyauta ba forgive me plss, in dae akan....." Kasa ambaton sunan tayi, cije leb'enta tayi daga baya ta d'anyi murmushi ta kalleshi tace "indae akan Sister Batuul ne I promise baxa mu sake samun matsala ba", rintse ido tayi jin sunan Batuul ya fito daga bakinta, da mamaki shi kam yake kallota jin ta ambaci Batuul as her sister, anya Ajiddeh bata da brain disorder ma kuwa, k'ara shigewa jikinshi tayi tace "Yes our sister, I mean it, I was so stupid da na dinga yin abubuwan da nayi maka, I don't know what came over me that I reacted that way calling her names, but babe I promise bazan sake ba, kayi hak'uri kaji, I was just being pessimistic about her , thinking zaka sota if she stays here, but yanxu I have realised my mistake, she is like a sister to me also, I will gladly keep her in my house, I promise" a hankali ta kare maganar ta d'ago kanta tana kallon kyakkyawan fuskanshi, lumshe idonshi yayi sannan ya bud'esu, rungume shi ta sake yi murya can kasa tace "Trust me babe" rungume ta shi ma yyi sosae, ya lumshe ido yace "why didn't you realise it since then, but anyway am happy that you finally realised it, kinga yarinyar nan bata da matsala, nasan she will b obedient to you indai har kika kwantar da hankalinki kika jata a jiki, zakiji dad'in zama da ita, am also sorry for everything Honey" kai ta gyad'a mishi tace "nima nasan bata da matsala baby, kasan sharrin shaid'an kuma da irin son da nakeyi maka, I can't risk seeing you with another woman, zan Iya mutuw....", hannu yasa a bakinta yace "shhhh, I will always be yours alone" kallonshi tayi tace "promise", bakinshi ya d'aura kan nata tare da janyota jikinshi, sai da ya gaji dan kanshi ya saketa, k'ank'ameshi tayi jikinta ta saki wani mugun murmushi, hiran da suka gama da Mummy d'azu ta tuna, da kuka dama ta shiga d'aki bayan  Abu ya haura sama ya bar ta falo, waya ta d'auka ta shiga neman layin Mum, bugu biyu ta d'aga, wani irin razanannnen k'ara Ajiddeh ta saki da har ya tsorata Mum d'in ya sata janye wayar daga kunnenta tana tabbatarwa ko da Ajjideh take waya, a rikice ta maida wayan kunnenta ta shiga tace "keh daina shirmen nan kiyi min magana, mey ya faru kuma", Cikin sheshek'a ta gama zayyanewa Mum yadda akayi, da mamaki da tsoron jin abinda Ajiddeh ta gama fad'a mata ta sauk'e ajiyar zuciya tace, "wane rashin hankalin ne ya kaiki zagar mishi y'ar uwa harda ce mata karuwa a gabanshi, keh kinsan halinshi mey ya kaiki yin abunda har zai dakeki, wama yace kije ki tafka wannan haukan wai", cikin sheshek'a tace "Mum ni bansan ya zanyi bane, I was furious a lokacin, raina duk ya gama b'aci, bazan iya jurewa ba shiyasa nayi mishi wannan haukan, ko ba komai dai ai shima ranshi ya b'aci, sai ita wannan y'ar iskar, da na samu nayi laying hannuna kanta wlhy da sai yadda Allah yayi da ita dan tsanar da nake mata baya misaltuwa", katseta Mummy tayi da cewa, "naji ya isa, d'azun nan su Zainab suka wuce Tchad, kuma duk kan aikin namu na turasu dan ni Daddynku ya hanani zuwa, toh yanzu abinda nakeso dake, siyasa zaki shiga yi masa ki nuna masa kinyi kuskure kuma kin gane laifinki amma hakan bazai sake faruwa, ki nuna mishi kina k'aunar ita yarinyar har sai ya aminta da hakan, itama ki nuna mata k'auna har sai mun samu munyi maganinsu shi da itan dukkansu da ma duk wani munafiki dake gefe, ni yanxu haka ba kud'i hannu na kuma Dad d'inku rabon da ya bani kud'i har na manta dan cewa yayi baisan mey nakeyi dasu ba, wai har sai na nuna mishi abu d'aya da na tsinana mai amfani da nayi da kud'in, yanzu haka nayi niyyan k'iranki in miki bayani akan tafiyansu Zainab d'in sai kika rigani, kud'i kawai xaki turo har Zainab d'inma wani senator da yazo wajen Babanku ya ganta yace yana sonta amma kuma yanada mata sannan Babanku yace ya turo dan ya bashi ita shine mukeso musan yadda za ayi da Matan nashi dan bazan yadda da kishiya ba, kinga kina turo kud'in sai ayi komai a gama, an jefi tsuntsu da dutse d'aya", Hankalin Ajiddeh ne ya fara kwanciya jin bayanin da Mummy ta gama yi mata tace "Mummy wannan kud'i duk ba matsala bane, yau da safen nan ya rubuta min cheque d'in miliyan uku da nace mishi ina buk'ata, banmaje nayi cashing d'insu ba a bank, xan turo sai ayi abinda ya kamata, amma Mummy d'ayan ne ban iyawa, wlhy na tsaneta yadda baki zato, bazan iya nuna ina sonta ba, Kawai in ansamu anyi abinda za ayi ta tattara nata ta barmin gida", tsaki Mummy taja tace "ai kinji ki, toh kije kiyi abinda kika ga dama tunda baza ki  d'auki abinda na fad'a miki ba", cewa tayi "Mum ba hakane bane, kawai ni kallonta ma bana son yi ne", Mummy tace "na fahimceki, amma kowane mutum yana son a so d'an uwanshi, da hakan sai ya dad'a kyautata miki, kinga ko ta dalilin ta zaki moreshi bare shi dake son y'an uwanshi, lokaci d'aya zai Iya rabuwa dake ya maida wata gurbinki, amma y'an uwanshi bai tab'a iya canja su, shiyasa nakeso ki nuna mata so", cikin hanzari Ajiddeh tace, "Mummy abar wannan maganan, ni yanzu xan turo komai a gama", ta tsorata da jin da tayi za a iya canja ta, Mummy tace "toh shikenan yanxu ki tashi ki shirya kije ki bashi hak'uri ki nuna kinyi nadaman duk abubuwan da kikayi", wani munafikin murmushi tayi ta sake shigewa jikinshi da ta dawo daga tunaninta, shi kam Abutturab tunani yadda zaiyi da Batuul Kawai yakeyi duk randa Ajiddeh ta gano ita d'in matarsa ce yasan gidan nn sae yayi musu kadan, tunanin Batuul kawai yakeyi zamansu a wajen, Ajiddeh ta kalleshi tace "baby na fara jin bacci muje mu kwanta", kallonta yayi dan shi sam bayajin bacci, Batuul ma kawai yakeson gani yaga halin da take, yace Mata "I will b coming dear, bari in gama program d'innan its interesting, I will meet you up there", peck yayi mata daga haka ta mik'e tayi hanyan stairs, har ta fara tafiya ta juyo ta kalleshi tace "Baby, I will check on my Sister before leaving", da wani munafikin wide smile shimfid'e fuskanta da kana gani kasan yak'e take, kallonta kawai yayi har ta juya ta tafi, ya sauke ajiyar xuciya cikin ransa yace Allah sa har cikin ranki Ajiddeh.

      Batuul kam bayan ta saka pad d'in sai da ta leqo kanta taga ya bar d'akin sannan ta sauk'e ajiyar zuciya ta fito dan mugun yunwa takeji, direct wajen ledojin ta nufa ta tsugunna wajen ta shiga bubbud'esu, na farkon drugs d'inta ne ciki, matsar dasu gefe tayi ta bud'e sauran, da murna ta shiga bud'ewa ganin abincin favorite restaurant d'inta Gordon Ramsay, pack d'in ta bud'e taga roast chicken, lavender, apricot, honey, d'ayan bowl d'in ta duba taga starter ne green apples, turnips sai watercress, wani irin farin ciki kawai takeyi, d'ayan pack ta sake dubawa pasta ne with shrimps kebab, babu b'ata lokaci ta tashi ta wanko hannunta, ko using spoon d'inma baza ta iya ba, sai da taci ta k'oshi ta maida ledojin gefe ta tashi ta cire kayan jikinta ta fad'a toilet, ko ta kan Maganin ma bata bi ta shiga tayi wanka abinta, ta fito kenan d'aure da towel taji an turo k'ofan d'akin, a razane ta d'ago kanta warce ta gani tsaye bakin kofa yasa hanjin cikinta mugun k'adawa, Ajiddeh ta karaso tana murmushi tace "Sannu sister ya jikin?" K'asa cewa komae Batuul tayi sae kallonta take, kuma da ganinta kasan a tsorace take, Ajiddeh bata damu da hakan ba sae ma murmushi da take tace "Amma kina da pad kuwa ko in dauko maki a daki" Batuul ta sunkuyar da kanta da kyar tace "Ina da shi" Ajiddeh tace "Toh Allah ya sauwake, kin sha magani kuwa?" Batuul tace "Ynxu xan sha," Ajiddeh tace "Toh sannu, ni na tafi in kwanta sae da safe" Batuul ta kalleta don har lkcn ta k'asa yarda Ajiddeh ce, a hnkli tace "Toh sae da safe na gode" Ajiddeh tace "Yauwa" sannan ta fice, Batuul ta sauke ajiyar xuciya ta isa inda kayanta yake cike da mamakin Ajiddeh, lotion ta shafa, snn ta shafa turarrukanta masu sanyi kamshi ta fiddo wani sabon sleeping gown dinta  mara nauyi me d'an karamin hannu ta sa, ta xura gashinta cikin net, ledan maganinta ta bude ta fiddo magungunan ta sha snn ta ajiye su gaban mirror, ta nufi switch din dakin ta kashe wuta kenan don kwanciya xata yi aka bude kofar dakin, kin kunna wutan tayi don bata son ya ganta ba hijab kuma ta k'asa barin wajen, ya shigo dakin ya rufe kofar, da sauri ta nufi inda hijab dinta yake xata dauka yyi saurin fixgota yana mata wani irin kallo cikin duhun yace "Wae me kike boye min da ban sani ba a jikin ki, baki sanin muhimmancin Hijab sae na shigo dakin ki don rainin wayo koh?" Kokarin kwace kanta ta shiga yi a hannunsa yace "Stay still kar in mareki" sunkuyar da kanta tayi bata ce komae ba, a hankali yace "Ya cikin?" Kin cewa komae tayi ya D'ago kanta yace "Am talking" ta rufe ido kmr yana ganinta murya can k'asa tace "da sauki" yace "Sure?" Shiru tayi bata ce komae ba, yace "ko kina son a maki massaging Abdomen..." Da sauri tace "No na samu sauki" murmushi yyi yana kallon d'an karamin bakinta dake motsi a hankali, yace "Sure?" Runtse ido tayi ta janye hannunta xata bar wajen, ya fixgota jikinsa, wani irin faduwar gaba taji jinta a jikinsa, suka ji an bude kofa can corridor, saketa yyi da sauri ya juya ya nufi kofa.Yana fita d'akin Batuul a corridor ya tarar da Ajiddeh a tsaye, wani irin kallo ta bishi dashi ganin ya fito d'akin Batuul, bak'in cikinta ta shiga dannewa dan batason tayi anything stupid, murmushin yak'e tayi tace "Baby naga har na fara bacci baka shigo ba shine nace bari in fito in dubaka, ashe kana d'akin Sis dinmu", ta fad'i da wani irin expression shimfid'e fuskarta ta sake kallon d'akin, hannunta ya kamo yace "Yeah ita na shiga dubawa, kinsan batajin dad'i", tace "hakane, nima saida na shiga na dubata before in shiga ciki", yace "kin kyauta", ya rungumota jikinshi suka shiga ciki. Batuul kam yana fita ta tabe baki ta fad'a gado, ko yunk'urin rufe k'ofarta batayi ba tayi kwanciyarta dan ko ta rufe in ya tashi bud'ewa yakeyi, addu'ar bacci tayi ta tofe jikinta da d'akin taja duvet ta kwanta, bata fi minti goma a kwance ba bacci ya d'auketa, k'arfe biyar daidai ta tashi da addu'a bakinta, tana zaune kan gadon har biyar da rabi, sai da taji an idar da sallah ta mik'e ta shige toilet, wanke toilet d'in ta farayi tukunna tayi wanka, mayukanta ta shafa ta gyara gashinta ta tufke da ribbon sannan ta isa closet d'in kayanta, tsayawa tunani tayi na kayan da zata saka, wani gown d'in atampa ta ciro ta saka, ta fesa turarruka sannan ta d'au vacuum cleaner ta tsaftace d'akin tsaf, ta gyara gadonta ta kunna electric burner ta saka turaren wutan, lokaci d'aya d'akin ya d'au k'anshi, sakkowa tayi k'asa ta shiga kitchen, wutan ta kunna taga kitchen d'in na nan yanda ta barshi, shiga tayi ta gama examining komai taga mey zata dafa, fridge ta bud'e , nama ta ciro ta shiga had'a lasagne, tayi peanut butter smoothie, Garlic egg Muffins, sannan tayi offals pepper soup, Abuturrab na dawowa masallaci yaga wutan kitchen a kunne sai dae bai bi ta kan kitchen din ba ya wuce sama dan a tunaninshi Ajiddeh ta sauk'o tayi wani abin, 7:30 Batuul ta gama duk abubuwan da zatayi ta jera komai kan dinning, gyara gidan tayi, takwas dai dai ta gama ta saka turaren wuta gidan ya bade da kamshi me ddi, tea ta hada jin cikinta ya fara ciwo don ta samu ta sha magani, tana gama sha ta haura sama ta dauki magungunan ta sha snn tayi kwanciyarta don sae goma take da lectures, abinda zatayi ne ta rasa  kawai ta janyo macbook d'inta ta shiga kallon Boss Baby.

    8:30 Abuturrab ya fito sanye da pyjamas d'inshi, tun daga bakin kofa yake jin k'anshin masu dad'i sun had'e gidan, kanshin turaren wuta da na abincin da ta dafa, sauk'owa kan stairs d'in yayi, yadda gidan ke shining ya bi da ido har ya k'araso dining, da mamaki yake kallon kan dinning d'in ganin anyi arranging abinci Kai, k'arasowa yayi ya bubbud'esu, aroma din abincin ya bugi hancinshi, maidawa yayi ya rufe, for the first yaji Batuul ta birgeshi, yasan training d'in Aunty ce ita din, murmushi yayi ya haura sama, d'akinta ya nufa ya tura kofar ya shiga, kwance ya ganta kan gado a kife, bayanta kawai yake gani sai screen din computer, ya karasa cikin d'akin don ganin abinda take kallo, har yazo bakin gadon bata sani ba sai tuntsirar dariyar da take ta faman yi, jin mutum ya zauna kan gadon yasa ta saurin mik'ewa zaune, matsawa tayi daga kusa dashi ta koma can k'arshen gadon, kallonta kawai yake, haka kawae ya samu kansa da murmushi, a hankali ta d'ago idonta taga ita yake kallo, maza tayi ta d'auke nata idon cikin sanyi tace mishi "ina kwana" ya bude ido yace "Morning! Ashe kin iya tashi da wuri?" Kauda kai tayi tace "Eh!" Yyi shiru yana kallonta, satan kallonsa tayi jin shiru suna hada ido ta dauke nata da sauri, ya d'aga kafada yace "Ya dysmenorrhea, ko dama na kwana daya yake maki?" D'an turo baki tayi ta juya masa baya, yyi murmushin da bae san dalilinsa ba, bae kuma ce mata komae ba ita ma bata juyo ba sae dae addu'a kawae take ya tashi ya tafi, wayarta ne dake gaban mirror ya shiga ring, ta mike a hankali ya bita da kallo har ta isa gaban madubin ta dauki wayar, wara ido tayi tana murmushi ta d'aga, sae kuma ta hade rai tace "Kin ban mamaki farida friendship din kenan dama sae yau kika san za ki kira ni koh?" D'aga daya bangaren farida tace "Wayyo Afuwan Besty, kusan kullum sae nayi xancen ki gun Ammah I just don't want to call ki fara min kuka ne wllh, waow hope you are enjoying ur new home, tell me how it is over there, have you made friends? Ina jarababbiyar matar ya Abu, how are you coping with her, hope she isn't giving u tough time...." Batuul ta xaro ido tace "Kai farida spare me those questions, hakuri ya kamata ki fara bani da yawa" Farida ta fashe da dariya tace "Ohhh yhu need to see how happy I am besty, ur voice is so lively, from all indication I guess u are enjoying it over there...." Batuul tayi murmushi a xuciyarta tace uhm lallai kam, ko ba enjoy ba, a fili tace "Ni dae ina Ammah fa?" Farida tace "Tana daki wllh let me put her on the line" Batuul tayi murmushi tace "Alryt!" Juyawa tayi tana kallon Abuturrab da ya kafa mata ido tayi maza ta dauke kanta, muryan Ammah ta ji da fara'a tace "Bitti?" Batuul tayi murmushi ta sulale nan k'asa ta xauna a hankali tace "Na'am Ammah ina kwana?" Ammah tace "Lfya lau Bitti ya gida? In ji ba matsala dae koh? Kar fa ki boye min don Allah" Batuul tace "Babu Ammah ya su Abui?" Ammah tace "Lfya lau suke, ya karatu kina xuwa dae koh?" Batuul tace "Ehh ina xuwa Ammah" Ammah tace "Ma'sha Allah! Ina Abuturrab din" kallonsa tayi taga ita yake kallo, a hankali tace "Ga shi nan, in bashi?" Ammah tace "Bashi!" Hade rae yyi yana kallonta, ta sunkuyar da kanta ta mike a hankali ta isa gabansa ta mika masa wayar, karba yyi ya fixgota lkci daya ta fado jikinsa tun kan tayi k'aran da take shirin yi ya rufe fuskarta a kirjinsa, tayi lamo tana shakan kamshin jikinsa me dadi, wayar ya kai kunne yayi ma Ammah sallama sannan ya gaisheta, da fara'a ta amsa masa don ba karamin dadi taji ba jin suna ma tare, tambayarsa Ajiddeh tayi yace tana dakinta, nan dae ta dinga masa nasiha kamar yanda ta saba a kan yaji tsoron Allah ya xama me adalci tsakanin matansa, dama irin abinda yake gudu kenan shi, don jikinsa sanyi yake, lumshe ido yyi yana sauraranta, ta kusa minti goma tana nasihan nata har lkcn kuma Batuul na jikinsa yaki saketa gabanta sae faduwa yake don she's not use to that, daga karshe ce masa tayi ya ba Batuul wayar, mika mata wayar yyi ta karba ta shiga kkrin kwace jikinta amma ya ki saketa, k'ara wayar a kunne tayi, Ammah tace "Kina jina Batuul" a hankali tace "Eh Ammah" Ammah tace "Kiyi ta hakuri kin ji Bitti, bbu ruwan ki da Abokiyar xaman ki tsakanin ki da ita sae girmamawa, ki kula da ibadun ki, ki xama me tsafta duk da nasan kina da  amma ki kara kan na da, ko da yaushe dakin ki da jikin ki ya kasance cikin kamshi kin ji, Farida na nn xuwa idan sun yi hutu" Batuul ta wara ido cike da murna tace "Toh Ammah nagode, Allah kara girma" Ammah tace "Ameen Bitti sae mun kuma waya" nan suka yi sallama Batuul ta d'aga kai tana kallonsa ta ga idonsa lumshe, kokarin xame jikinta ta shiga yi ya bude ido yana kallonta, ta hade rae tace "Makaranta xan tafi ni" saketa yyi ya mike sanin lkcn tashin Ajiddeh yyi, ya fice daga dakin, bin sa da kallo tayi kafin ta lumshe ido ta kwanta kan gado. 
Karfe Tara da wani abu ta sakko da shirin tafiya makaranta, xaune ta same su shi da matar tasa kan dinning suna breakfast, Ajiddeh na ganinta ta sunnar da kai don bata so ta sakko ta sameta tana cin girkin ta ba, idon Abuturrab na kanta har ta karaso falon kanta a k'asa ta ce "Ina kwana Anty" Ajiddeh ta kirkiri murmushi tace "Lfya lau sister, ashe kin tashi, nace Aliyu ya shigo ya dubo ki muyi breakfast yace wae ba kya tashi da wuri" Batuul dae bata ce komae ba sae kofa da take kallo, Ajiddeh tace "Toh ki karaso ki karya mana" girgixa kai Batuul tayi tace "A'a na sha tea tun daxu" Ajiddeh tace "Ohk," kofa Batuul ta nufa jin Abuturrab bae ce komae ba, yana ganin hka yace "Ki jira ni gun mota, na aiki driver" toh kawae tace ta fita, Ajiddeh da mood dinta ya canxa lkci daya ta sunkuyar da kai kar ya lura, da sauri ta D'ago tace "Honey ko kuma in kai ta kawae tunda motar biyu ne kar ka makara" ba tare da ya kalleta ba yace "Ae ita ma ta iya driving din, Akwae kudin da xan bata ne shi yasa nace ta jira" Ajiddeh taji kmr ta kwala ihu, wato har kudi xae bata, murmushi ta kirkira tace "C'mon babe nima ae kanwata ce, nawa xaka bata in bata kawae?" Ajiye cup din coffeen hannunsa yyi yace "Don't bother suna da yawa kudin" mikewa yayi yana goge bakin sa da tissue yace "Na tafi babe, sae na dawo take care of ur self for me" yana kai wa nan ya nufi kofa, bin sa da kallo tayi xuciyarta na tafarfasa, tana ganin fitansa ta mike da sauri har tana neman faduwa ta nufi kitchen don lekawa ta window ta ga inda Batuul xata xauna a motar, ae ko dai dai lkcn da Batuul ta bude front seat ta shiga, shi ma ya xaga ya shiga maxaunin driver, ta fashe da kuka da karfi wani mugun tsanar Batuul na k'aruwa a xuciyarta, anya xata iya ci gaba da yin abinda momy tace tayi kan Batuul kuwa, ynxu idan Abuturrab ya ji tana burgesa d'an girkin nan da ta iya ya xata yi da rayuwarta ita da ko indomie ba lallai ta dafa shi ruwa bae yi masa yawa ba, tunanin hakan yasa ta rushe da kuka ta fito kitchen din tana rerawa.Har suka isa makarantar, Abuturrab bae ce ma Batuul komae ba ita ma window kawae take kallo abun ta, sae da yyi parking sannan ta dauki jakarta dake kafarta xata fita yace "Ki na da hankali kuwa, wa ya baki izinin fita" komawa tayi ta xauna ta jinginar da kanta jikin kujerar da take xaune, kallonta kawae yake, ita kam bata ma san yana yi ba, ya wani daure fuska yace "Kin yi breakfast ma kuwa" ba tare da ta kallesa ba tace "Na sha tea" a d'an tsawa ce yace "Hey look at me!" Juyawa tayi tana kallonsa yace "Yaushe na fara wasa da ke xaki wani dinga dauke min kai ina magana" tagumi tayi tana kallonsa ko kifta wa bata yi, dariya ta basa ganin yanda ta tsuke baki, yace "Ayt, naga alama don kin ga na fara bi ta kan ki ne ynxu, ina kare ki gun matata shi yasa kike son ki raina ni koh?" Ita dae bata ce komae ba kuma bata fasa kallonsa ba, kayan jikinta ya kalla da d'an karamin bakin gyalen da tayi rolling a kai yace "Wae ma kina matar aure xaki dinga irin wannan shigar kina xuwa makaranta kina da hankali kuwa" kallonsa take har lkcn kuma bata ce komae ba, kafin ya kara cewa komae ta kalli agogon wrist dinta tace "Its almost time for lecture" tana fadin hka ta dauki jakarta ta bude motar ta fice, bin ta yyi da kallo cike da mamakin ta, bae san lkcn da yyi murmushi yana shafa kansa ba, kamar wanda ya tuna abu ya bude motar ya fita ya kulle sannan ya bi bayanta, tafiya take kamar me tausayin kasa tana rataye da jakarta, ko kai ka ganta sae ta burge ka don a nutse take tafiyar, kamar ance ta waiga taga yana biye da ita a baya, ae bata san lkcn da ta tsaya ba gabanta na faduwa sosai, ya karaso ya xaga gabanta yana facing dinta, sunkuyar da kai tayi, yana mata wani irin kallo yace "Are yhu stupid? Yhu walked me out ina maki magana?" K'in cewa komae tayi, ya gyada kai yace "Gud nasan maganin ki?" Kudi ya ciro aljihunsa ya mika mata ba musu ta risina ta karba murya can kasa tace "Thank yhu" wayarsa ya mika mata fuskarsa daure yace "driver xae kira ki" ta karba tace "Toh" tafiya yayi ya bar ta nan tsaye ta bi sa da kallo snn ta ci gaba da tafiyarta ita ma, sae taji for the first Abuturrab ya burgeta, "Upon all, he is kind at heart kmr yanda farida ta gaya mata, he always care and show concern" murmushi tayi ta karasa Dept da sauri ganin few minute ya rage a fara lecture.
+

     Karfe sha biyu saura suka fito daga lecture, Batuul tace "Lets get something to eat frnd am hungry" Aisha tace "It's ok, same with me here" suna tafe ne bbu me cewa komae cikinsu har suka iso wani guri da Shaheed ke xaune da abokansa kusan su biyar, biyu bakake kmr sa uku kuma turawa, hiran su kawae suke shi kuma yana duba wani textbook dake hannunsa" Batuul ta hade rae ganin yanda suke kallonsu tun kan ma su karaso, suna Karasowa wani dake xaune gefen Shaheed yace "Hey Aysha!" Aysha ta tsaya tana murmushi tace "Hei Usman how you, how's lecture?" Usman yace "Alhmdllh, dat gal! Is she ur frnd? So haughty of her!" Sae a sannan Shaheed ya d'aga kai yana kallonsu, Batuul ya bi da kallo don ko tsayawa bata yi ba ta ci gaba da tafiyarta, ya lumshe ido ya bude ya ci gaba da karatunsa, Aysha tayi dariya tace "No, no, not at all, she's not! just dat ba ku saba bane, Well! We'll chat later Usman, bye for now" yace "Ayt! Take care of ur self bae" dariya tayi ta bi bayan Batuul da sauri. Xaune ta sameta waiter dake aiki a wajen yana tsaye kusa da ita yana tambayar me xae kawo mata, tace "Just caramel bun and frapuccino" mutumin ya juya yana kallon Aysha yace "yhu ma'am?" Tace "Same also!" Juyawa yayi ya tafi kawo masu. Aysha tace "Shine kika tafi kika bar ni koh?" Batuul ta kalleta murmushi dauke fuskarta tace "Yea naga yhu were busy ne" Aysha tace "Ayt, amma ko gaisawa ne ki dinga yi da mutane don ku saba mana" Batuul bata ce komae ba sae juya wayar Abuturrab dake hannunta take, Aysha ta ce "Kawo in sa maki digit dina, it's gud ace mun yi exchanging" mika mata wayar Batuul tayi ta karba ta kunna, "Woaww is this ur sister on the screen, kai she's so beautiful wallahi, ya aka yi ke baki yi hasken ta ba" hade rae Batuul tayi ba tare da tasan ta ma yi hakan ba, don ko lura da hoton screen din ma bata yi ba kawae ta fito da wayar daga jaka ne don ta duba agogo, Aysha bata damu da shirun da Batuul tayi mata ba tayi ta koda kyan Ajiddeh, daga karshe ta sa mata nmbrta tayi mata saving ta mika mata, Batuul na karban wayar ta maida jakarta snn ta maida hankalinta kan abincin da aka dire masu gabansu, ta riga Aysha gamawa snn ta fiddo wayar don hoton ya tsaya mata a rai haka kawae, kare ma hoton kallo kawae take, bata san lkcn da ta ja tsaki ba Aysha ta kalleta tace "Ya dae" yake tayi tace "Naga time ya wuce ne, baxa kiyi sllh ba?" Aysha tace "No bana yi" Batuul bata ce komae ba ta shiga gallery duk tayi mark din hotunan Ajiddeh dake wayar har na screen din ta watsa su a kwandon delete. Tana gama hakan ta ja tsaki ta fiddo kudi jakarta tace "Tambayar mana bill Aysha" ita ta biya kudin duk yanda Aysha ta so biya bata yrda ba, suka mike don komawa Dept.


     Karfe hudu da wani abu suka fito daga lecture, Aysha tace "kinga tare da aunt dina xa mu wuce tana jirana, Bus xa ki hau ko taxi?" Batuul tace "No xa a  xo daukana ne daga gida" Aysha tace "Ayt sae gobe, don't forget Karfe 8 muke da lecture fa" Batuul tayi murmushi tace "Insha Allah ki gaida aunt din ki" Aysha tace "Xata ji, nima ki gaidar min da pretty aunt din ki, so fyn da ita ga gashi, ina nan xuwa wataran in ganta" dauke kai Batuul tayi kmr bata ji ba har Aysha ta bar wajen, waje Batuul ta samu ta xauna, ko minti goma bata yi a gun ba wayar jakarta ya shiga vibrate ta ciro, d'agawa tayi daga daya bangaren yace "Are yhu done for today?" Mikewa tayi tace "Yea!" Ya katse wayar, ta nufi inda tasan xata gansa. Sauke glass Abuturrab yayi yana kallonta, sae kuma ya fito ya bude mata back door sanin gaba xata taho kuma Ajiddeh na ciki, Ajiddeh ta bi sa da kallon mamaki baki bude taji kamar ta rusa ihu, don da kawae so tayi Batuul ta zagayo ta bude ta ganta a xaune sae ta ga ynda xata yi, meye haka Aliyu ke yi, abinda bae taba yi mata ba wae bude mata mota ta shiga, shine yake bude ma shegiyar nan, what have come over him haka, ita kanta Batuul tayi mugun mamakin abinda Abuturrab yyi sae kallonsa take, infact shi kansa sae da ya ji wani iri a lkcn, don bae taba yi ma wata 'ya mace haka ba apart from Ammahn sa, what's he doing, A hankali Batuul ta raba ta gefensa kanta a kasa ta shiga motar, k'asa komawa seat dinsa yyi ba tare da ya kulle mata motar ba duk da hakan ya so yi don ganin irin kallon da Ajiddeh ke yi masa, samun kansa yyi da rufe motar a hankali, snn ya juya ya koma seat dinsa, banda xufa babu abinda Ajiddeh ke yi cikin motar duk da Ac'n da ke kunne, Batuul tayi mamakin ganinta cikin motar sae a sannan ta gane me yasa yayi hakan sae ta ji ddi da bae bar ta taje gaban ba, does he really care haka dama, d'an murmushi tayi tana kallon Ajiddeh tace "ina yini?" Da kyar Ajiddeh ta Hadiye wani abu da ya tsaya mata a makogwaro tace "Lfya!" Abuturrab ya d'an sata kallonta kafin ya tada motar suka bar wajen, sae da ya fara biyawa domino's, yana isa yyi parking ya fito, Ajiddeh da ke cika har lkcn tana batsewa ta bude motar ta fito ita ma, Batuul dae ta bi su da kallo, kallonta Abuturrab yyi yace "No no ba sae kin fito ba kiyi xaman ki a mota" da sauri Batuul ta dauke kai tana kallon window ta gefenta tana danne dariyar da ke shirin taho mata, bae damu da halin da Ajiddeh ta shiga a lkcn ba na kunya ya bar ta nan yyi gaba abun sa ya shiga domino's din, bayan kusan 10 mins ya fito rike da kwalayen pepperoni pizza da ledoji har biyu me dauke da cold stone ice cream, yayi mamakin ganin Ajiddeh tsaye har lkcn kmr warce ruwa ya ci, ya bude back seat ya ajiye kwalayen hannunsa da ledoji snn yana kallon Ajiddeh yace "Shiga toh mu je" Batuul dae har lkcn waje take kallo tana murmushi. Da kyar Ajiddeh ta iya bude motar kamar mara laka ta shiga, shi ma ya shiga ya tada motar suka bar wajen, tafiyar minti goma yayi suka iso gida, yana gama parkin Ajiddeh ta fice tayi cikin gida kmr xata tashi sama, Batuul ta fito ta kwashi kwalayen, fitowa yyi shima ya fito da ledan ice cream din snn ya rufe motar ya fara tafiya, bin bayansa tayi har suka shiga falon, Ajiddeh na tsaye tsakar falon, Batuul ta ajiye kwalayen pizzan hannunta shi ma ya ajiye ice cream din hannunsa, kwashe kwalin da ice cream din gaba daya Ajiddeh tayi ta nufi sama don dama shi take jira a falon, Abuturrab ya bi ta da kallo yace "Hey! Guda daya fa kadae ne naki a wajen nan babe" ko kallonsa bata yi ba ta haura sama fuu, Batuul ta kauda kai tana murmushi, Abuturrab ya juya yana kallonta yace "Ohh dariya ma kike koh, ae ko xa ki tsaya da yunwa ko kuma ki shiga kitchen kiyi girki" yana kai wa nan ya haura sama, Batuul ta tabe baki ita ma ta haura sama, dakinta ta shiga ta cire kayan jikinta ta shiga bayi ta sakar ma kanta warm shower, ta jima a bayin kafin ta fito daure da towel tana goge dogon gashinta da karamin towel, bude kofar aka yi ta kwalalo ido ta tsaya cak gabanta na faduwa, Abuturrab ya shigo dakin, kauda kai yyi da sauri suna hada ido yace "Erm my.. my phone, ina wayata?" kmr munafuka ta nuna masa jakarta, ba tare da ya kalleta ba ya nufi jakar ya bude ya fiddo wayar, kunna wa yyi yaga blank screen sae wall paper bbu photon dake gaban screen din, kallonta yayi kafin ya shiga gallery, mamaki ya cika sa ganin wayam sae few photos dinsa da ya rage bbu na Ajiddeh ko daya, hade rae Batuul tayi sanin abinda yasa yayi still a wajen, ta ci gaba da goge gashinta ta nufi gaban mirror, bin ta yyi da kallon mamaki, ta ja kujera ta xauna tana ci gaba da goge gashinta, karasawa gun mirrorn yyi ya fixgota ya juyo da ita yana mata wani irin kallo yace "Yhu deleted my wife's pics from my phone" ta wani hade rae tace "Toh na sani ne, ko ba mistake bane" bude baki yyi yana kallonta, ta turo baki ta kauda kai, bae san lkcn da murmushi ya subce masa ba, yana kallonta a hankali yace "Me ya shigar dake gallery nah?" Ta bude ido tace "Mistake I said!" Kallonta ya shiga yi daga kasa xuwa sama, ta dauke kai fuskarta daure, bata ankara ba sae ji tayi ya fixge towel din jikinta, ta rike gam ta xaro ido a tsorace Tace "meye haka ya Abu" yana mata wani irin kallo yace "Mistake" ta bude baki xata yi magana sae gani tayi ya kuma fixge towel din, a rikice tayi kasa tace "Nashiga uku don Allah stop this" bin ta yyi kasan yace "Sae kin gaya min me hoton matata ya tsare maki a waya da kika goge" a rude tace "No plss, Don Allah kayi hakuri ban san...." Janye towel din yyi gaba daya ta kwala ihu yyi saurin jawota jikinsa ya hade bakinsu, daukewa ne kawae numfashinta bae yi ba lkcn, shi kansa sae da yaji wani shock a lkcn, ya lumshe ido a hankali ya shiga kissing dinta kamar xae hadiyeta.

Post a Comment for "BATUUL CHAPTER 11"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...