Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

ABDULKADIR CHAPTER 5

ABDULKADIR CHAPTER 5

- - Post a Comment
ABDULKADIR
CHAPTER 5
Mutumin da kike so na tare da uniform din nan, ban san waye ni batare dasu ba, ban taba son kaina babu su ba, bana tunanin zaki iya" +

Kai ta girgiza mishi, hawaye ne cike da idanuwanta amman sunki zuba, in haka masu ciwon zuciya suke ji zasu kasance cikin addu'arta a ko da yaushe, saboda ciwo ne mai matukar radadi.

"Ba soyayyar nake tsoro ba Sadauki, ba mika maka dukkan zuciyata bane yake mun wahala, rashin tabbacin ka a rayuwa ta ne, bazan damu da raba soyayyarka da Uniform dinka ba, shi din da yafi ni muhimmanci ne matsalar"

Ta karasa maganar tana jin dacin son kan da take son yi a harshen ta, zabi take bashi, ita da take bakuwa a rayuwar shi ko Uniform dinshi daya girma da soyayyar shi? Tana jin idanuwan shi na yawo a fuskarta cike da son ta dago nata su sauka cikin su, amman taki yarda hakan ya faru.

"Waheeda..."

Ya kira sunanta, yana jan haruffan cikin sigar da shi kadai yake iya hakan.

"Karki ce mun in zaba... Ba zaki so amsar ba" 2

Runtsa idanuwanta tayi tana bude su da wani irin ciwo. Me yasa yaki ganin abubuwan data sadaukar saboda soyayyar shi.

"Duk abinda kike tunanin kin sadaukar saboda soyayyata bai kai uniform dina muhimmanci ba...karki so kanki da yawa haka" 1

**

"Adda! Addaa!!"

Idanuwanta da take ji sun mata nauyi ta bude, tana jin Amatullah ta kwashe da dariyar da ta sata jan karamin tsaki, dan mafarki take, kamar yanda a kwanakin nan mafarkan AbdulKadir din suke addabarta. A cikin daya daga mafarkan ta kira shi da Sadauki, tun bayan tashin ta tsinci kanta da kiran shi Sadaukin dan sunan ya dace dashi ta kowanne fanni. Batasan murmushi ya kwace mata ba saida taji Amatullah ta sake kwashewa da dariya 2

"Addaaaaa!"

Hararta Waheedah tayi da yasa Amatullah din sake yin dariya

"Jiba inda kike bacci fa, cikin kaya"

Miqa Waheedah tayi hadi da yin hamma tana miqa hannu ta dauki wayarta qirar Nokia Symbian E5 dake ajiye a gefe ta danna dan ta duba lokacin, karfe biyu harda kwata. Gabaki daya jikinta a gajiye take jinshi.

"Anata nemanki fa..."

Kai Waheedah ta dagama Amatullah din, tana kallo ta fice daga dakin. Zaune tayi a wajen tana tunanin ta inda zata fara miqewa, gajiyar da take ji har cikin tsoka da kasusuwan jikinta. Idanuwa ta lumshe, fuskar Abdulkadir na mata yawo, wata irin kewar shi take ji taban mamaki, zata alaqanta hakan da jimawa da tayi bata ganshi ba, tun hutun da yazo na sallah, shima ranar idi ne, tun da suka dawo daga masallacin idi bata sake sakashi a idanuwanta ba harya tafi. Satin da zata fara zuwa makaranta, Babban Yaya ya basu wayoyi, taga cikin mazan gidan ma kusan duk ya ba 'yan matasan. Matanne yace sai sun gama aji shidda.

Sosai taji dadin kyautar wayar har ranta. Yassar ya saka mata manhajar kafofin sada zumunta, ciki harda Whatsapp, har kati Yassar din ya saka mata. Lambar Abdulkadir ce ta farko da tazo sakawa taga Yassar duk ya saka mata lambobin su. Sunan kawai ta sake zuwa Sadauki. Shi kuma ta fara dubawa a whatsapp, sai lambar ta nuna bayayi. Sosai zuciyarta taji tai mata nauyi, lambar Yazid ta nema taga Yassar ya saka mata, shi kuwa yana Whatsapp. Sallama tayi mishi tana fada mishi itace. Shima tayi kewar shi ba kadan ba. Zata iya cewa shima tun bayan Sallah da canjin wajen aiki ya dauke shi zuwa Abuja.

Sai kwanaki da akace mata ya shigo, ita kuma taje gidan kanwar mahaifinta, kuma ba sosai take kwana ba, ranar dai rabon ba zata hadu dashi bane yasa ta kwana din, taji takaicin abin. Ta kuma yi mamakin da Yazid baije can din ya sameta sun gaisa ba, Yazid din data sani zai nemeta, bazai zo Kano bayan watanni masu yawa ya koma basu gaisa ba. Sai dai Zahra tace mata da Asuba ya wuce, a cewar shi ayyuka sun mishi yawa. Abdulkadir din kuwa text tai mishi tana fada mishi itace, tukunna ta sake tura mishi wani tana tambayar lafiyar shi. Kasa hakura tayi duk da bai amsa mata sauran sakkonin ba, ta tura mishi wani tana cewa bata ganshi a Whatsapp ba, ya bude. 2

STORY CONTINUES BELOW


Bata samu amsa ba sai bayan kwana wajen biyar tsakani, a kwanaki duk lokacin data samu tana duba wayar taga ko ya amsata bata gani bane. Sosai zuciyarta ta matse lokacin da take dubawa. Ba wata doguwar amsa bace. 'Na bude' kawai ya tura mata a taqaice. Amman zuciyarta ta mata wani irin sanyi. Tun lokacin suke magana ta WhatsApp din, ko tace take mishi magana, dan tana iya tura mishi sakonni sama da ashirin bai amsata ba, lokutta da dama zata ga ya bude ya karanta. Amsawar ce takan mishi wahala. Bai dameta ba a lokacin, har zuwa yanzun kuma baya damunta. Saboda bashi yake son magana da ita ba, itace take son magana dashi. 7

Indai yagani ya karanta, har kasan ranta ya wadace ta, duk rana zata bashi labarai kala-kala, abinda akai a makarantar su, me tayi a ranar, me ya faru da yan gida. Wani lokacin zai karanta ya turo mata Emoji din murmushi, randa ta wuni batai mishi magana ba zai sake turo mata da Emoji, idan yaga ta jima bata amsa shi ba zai kira sunanta. Zata rantse akwai yanayin yanda yake rubuta sunan da takan gane idan a gajiye yake ranar, idan ranshi a bace yake, ko idan yanajin fadan shi. Takan yi murmushi a dukkan yanayoyin tukunna ta bashi labari kamar ko da yaushe. 3

Bata taba gwada kiran shi ba ko sau daya. Takan tura mishi voice notes a whatsapp, a kasan zuciyarta tana fatan shima zai fahimci tana kewar muryar shi ya tura mata. Hakan bai taba faruwa ba. Sai dai lokacin da tayi wani zazzabi mai zafi, ta kwana biyu bata ko samu karfin duba waya ba. Kuma randa ta duba din bata da katin da zata siya data ta duba whatsapp din. Har washegari, tana kwance a daki ya kirata, tana dagawa ta kara a kunne, kafin tace wani abu muryar shi ta daki kunnenta

"Me ya sameki?" 2

Lumshe idanuwanta tayi, muryar shi na nutsar da wani abu cikin kirjinta da batasan a tashe yake ba. Kafin ta amsa ya dora da

"Meyasa ba zaki fadamun kina wani abu ba?"

Murmushi tayi

"Hamma..."

Bai bari ta karasa din ba

"Karki sake mun haka, bana so Waheedah" 3

Numfashi ta sauke a kunnen shi

"Bani da lafiya ne Hamma"

Ya kai dakika talatin kafin ya sake magana cikin wata irin murya da ta dinga shigarta har kwanya. Duk da hirar batai tsayi ba tai mata dadi. Satin saida ya jera kullum saiya kirata yana jin ya jikinta. Da zata iya mishi karya zata ce bata warke ba dan yaci gaba da kira. Amman ba zata iya ba, daga lokacin kuma idan harya kirata to ta dawo makaranta a gajiya tana bashi labari tace kanta na ciwo, yana kira yace mata tasha magani ta kashe waya ta kwanta. Amman ba zai amsa maganar tata a whatsapp ba. Mutane da yawa zasuyi mamakin badaudaden halin shi, ita kam babu wani abu a tattare dashi da bai mata ba, ko yake bata mamaki. 5

Numfashi ta sauke tana samu ta miqe dakyar, dan inta zauna tunane-tunane ba tashi zatayi ba. Kayan da tazo dauka ta saka cikin wata yar jakar biki da aka ba Mami wajen Walima, ta dauke. Ficewa tayi daga dakin, tana cin karo da Mami a falo

"Badai tun shigowar da kikai ba?"

Kai Waheedah ta langabar

"Wallahi Mami jikina ciwo yake... A gajiye nake jina"

Yar dariya Mami tayi

"Ai dole, tunda kune kirjin biki"

Dariyar itama Waheedah tayi, tana fadin

"Kirjin biki kam nashan wahaka Mami"

Ta karasa maganar tana ficewa daga dakin. Gidan su Nuriyya ta shiga da yake cike da mutane, tana samun Mama ta bata kayan da ta dauko. Tukunna ta sake komawa gidan nasu, wannan karin bangaren Anty. Tana shiga dakin da sallama. Idanuwanta na sauka kan Nuriyya da ake ma kunshi.

STORY CONTINUES BELOW


"Wai har yanzun ba'a gama ba?"

Waheedah ta fadi tana karasawa ta samu waje ta zauna. Nuriyyar bata amsata ba, ko dagowa batayi bama. Bata tsammaci amsa ba, ita kanta zuciyarta ta mata wani irin nauyi dan zata ce ita kadai tasan halin da aminiyarta take ciki. Dan a watannin nan biyu yanda take tashi ta gabatar da sallolin dare kan matsalar Nuriyya, ko ita da Nuriyyar bata tashi tayi addu'a kan matsalar irin haka. 4

Watannin su shidda da fara zuwa makaranta dukkan su, sunyi jarabawar zango na farko a cikin biyun da yake a shekara daya. Dan Nuriyya ma ta riga Waheedah gama jarabawarta ta farko. Duk da lokacin wata irin wayewa taban mamaki ta shigi Nuriyyar. Wasu irin samari take tarawa da Waheedah bata san daga inda ta kwasosu ba. Ko wayar hannunta Nokia C2, daya daga cikin samarin da tayi ne ya kawo mata. A gida tayi karyar cewar Anas ne. Waheedah kawai tasan asalin gaskiya, har fada sukayi akan wayar. Dan Waheedah taga rashin kyautawar abinda Nuriyyar takeyi.

Kowa yasanta da Anas, duk da tana tare dashi ne har lokacin saboda yana da yake wahala da ita. Tayi wasu samarin da suka fishi kudi, kyau, da komai, amman a cikinsu babu wanda yake dawainiyar da Anas din yake mata, shisa ta kasa rabuwa dashi. Duk da ya dameta da maganar aure, hakan yasa tayi kuskuren cewa ya gaida mahaifinta. Tasan Baba yasan da Anas, dan Mama kan nuna mishi inya siya mata kaya, koya kawo musu wani abin. Yakanyi hakan, idan lokacin doyane ko dankalin Hausa, da yawa yake siyowa ya kawo musu, haka kayan marmari. 1

Baba ya fara mata fada kan tara samari, duk da tsoron shi da take kamar ranta, dan Baba baya wasa. Tsayayyen mutum ne, bai hanata cigaba da tara samarin ba, sai dai takance suzo da yamma idan Baba bayanan. Tashin hankalin duniyarta ya farane randa Baba yazo ya sameta da wani dan makarantar su, da sai yayi magana ne zaka san bahaushene, idan kaji sunan shi kasan musulmine saboda yanayin shigar shi da kuma askin da yake kanshi. Ranar dukanta ne kawai Baba baiyi ba saboda fada. A ranar ne kuma yace tai ma Anas magana idan da gaske yake ya turo. 1

Tsaye duniyar tai mata waje daya, saboda ko kadan Anas baya cikin tsarin mazan da take son aure, a rikice da wuni ranar tana jiran Magriba tayi, Anas yazo ta bashi hakuri ta gaya mishi ba zata aure shiba, kafin ya jaza mata masifa. Magriba nayi kuwa sai gashi yazo, sai dai bata samu damar fada mishi ba, Baba ya fito ya same su yana gaya mata ta koma cikin gida. Da kanshi yaima Anas din magana. Abu kamar wasa washegari sai ga dangin Baban Anas din a gidansu aka tsayar da magana aka kuma saka biki wata uku kacal. Dan shi daman a shirye yake.

Baba kuma yana dan tanadi, tunda yasan auren Nuriyyan zai iya zuwa kowanne lokaci, duk abinda ya samo yakan ba Mama ta ajiye, ita kuma adashi ta shiga irin na talakawa dan a taru a rufama kai asiri. Har da Abba aka karbi kayan sa ranar Nuriyyan aka kuma tsaida magana. Babu kalar tashin hankalin da bai faru a watannin ba, da kukan ta shabe-shabe, da duk yanda take tsoron Baba ta same shi tana tsugunnawa kan gwiwoyinta akan cewar ita bata son Anas. Baba yace ta makara, dan shi bazai zama karamin mutum ba, idan bata san shi meyasa tasa yaje ya gaishe shi. Me yasa ta dinga karbar mishi kaya?

Tabbatar mata Baba yayi idan an fasa auren sai dai idan shine ya kwanta dama, ko Anas yazo gidan da kanshi yace ya fasa aurenta. Tun daga ranar tashin hankalinta ya fara, a watannin babu kalar wulakancin da batayiwa Anas, duk da har fada mata yayi zata cigaba da karatunta, shi zaiyi kokari ya biya mata komai, duk dan hankalinta ya kwanta. Amman kamar duk wani abu dazai dan kyautata mata yana kara tunzurata ne. Haka zasu zauna ita da Waheedah susha kuka. Ita kanta Waheedah din saida tai zuru-zuru a yan lokuttan. 2

Tayi-tayi da Nuriyya ta kwantar da hankalinta, taci gaba da addu'a, batasan abinda Allah ya boye a auren ba, amman taqi. Kullum Anas cikin kiran Waheedah yake ya kawo mata karar Nuriyyan, amman ko maganar takan kasa yima Nuriyya saboda halin da take ciki. Abin harya fara bama Waheedah tsoro dan wayar karshe kan karar Waheedah da Anas ya kawo mata, maganganun shi sun tsaya mata

STORY CONTINUES BELOW


'Nima akwai zuciya a kirjina Waheedah, nima na iya fushi. Wulakancin da Nuriyya taimun jiya yasa naji kamar in samu Baba a fasa auren nan. Sai dai kinsan me? Wallahi bata isa ba, bata isa ta mayar dani dan iska ba, har gardama nayi da Mamana akanta da tace mun ita auren bai kwanta mata ba.

Ta hakura saboda na nuna mata bazan iya barin Nuriyya ba. Zaman wulakancin take so muyi aiko? Ki fada mata a shirye nake da ita, wanda duk ya gaji saiya sauko ayi zaman lafiya. Amman ko zata mutu sai an daura auren nan' 7

Sosai maganganun shi suke ma Waheedah yawo, bata gani ba, amman takan karanta wulakancin da namiji a litattafan Hausa, takan kuma ganina fina-finai. Shisa take gujema wulakanta mutane ko yaya suke kuwa. Musulunci ma yai hani da hakan, duk mazan dakan bita a makaranta takan fada musu an mata miji, dan bata son fara abinda ba zata iya karasawa ba. Tana jin yanda bata da wani wajen saka kowa a zuciyarta, Abdulkadir ya cike ko ina

"Ina son shi Nuriyya, ina son Hamma, wani irin so da bana tunanin inda zai kaini, saboda bansan ko zuciyar shi zata dokamun yanda tawa take doka mishi ba, amman ina son shi, ban damu ko zai soni ba shima..." 1

Dariya Nuriyyar tai mata lokacin tana tambayarta ko a film din Hausa taji kalaman, to a watannin nan ma sam bata ma Nuriyya zancen Abdulkadir din. Dan hankalinsu ba'a kwance yake ba. Tunda satin bikin ya kama, Nuriyyar ma tayi wani irin sanyi naban mamaki, ko magana batayi sosai. Kamu kadai zasuyi washegarin ranar juma'a, ran asabar a daura aure hadi da yinin biki, kawayensu na islamiyya duk sunzo, harda kawayen Nuriyya na FCE dinsu duk sunzo suma yin lallen da Anty ce ta dauki nauyin shi. Abba kam Allah kadai yasan me yayi musu, dan data shiga gidan Mama na mata godiya sosai.

Mami ta siyi kayan kitchen masu yawan gaske, tunda aka saka ranar take siya tana ajiyewa a hankali a hankali. Duk da a yanayin da auren yazo ma Nuriyya bai hana Waheedah jin dadin yanda danginta suka hidimtawa Nuriyyar ba. Kusan duka hidimar bikin Waheedah ce tsaye akai. Daga kan dinkunan da Nuriyya zata saka, itace mai zirga-zirga wajen tela, haka sauran hidindimun da za'ayi. Tunda satin ya kama kuma rabon da suyi magana da Abdulkadir. Har wayar shi ta kira a karo na farko, tajita a kashe. Duk sakkonin data tura mishi a whatsapp basu je ba. Tana fada mishi hidimar bikin da sukeyi.

Yanzun ma Whatsapp din ta sake budewa tana bashi labarin zirga-zirgar da tayi, da kunshin da za'ayi musu, da yanda take tunanin zaman kunshin. Saida ta ajiye wayar tukunna take tunanin saida satin bikin ya kama tukunna take fada mishi. Yazid ne ta fadama da suka gaisa kamar yanda sukanyi lokaci zuwa lokaci. Sai taga kamar Abdulkadir din. A kasan zuciyarta take addu'ar Allah yasa lafiyar shi, shirun nashi ya fara mata yawa, inda tana ganin sakkoninta sun tafi ya karanta, tasan yana lafiya, amsata ne kawai baiyi ba. 1

Kunshin akai mata itama, suna dan hira da kawayen Nuriyya, dan ita ta lafe a gefe daya tana kallon kunshin dake hannunta, tana jin kamar bata cikin gangar jikinta, kamar ruhinta ya fita daga jikin ya koma gefe yana kallon abinda yake faruwa da ita, abin yana mata kamar mugun mafarkin da zata iya farkawa daga shi kowanne lokaci. Bata hango ma kanta auren Anas ba kona minti daya, inda tasan hakan zai faru da ta jima da sallamar shi ta hakura da kwadayin hidimar da yake mata. Tasan Baba fiye da kowa, idan ba mutuwa tayi ba baza'a fasa auren ba. Amman tana jin da gaske mutuwar zatayi idan aka daura auren. 2

Ba zata iya zama da Anas ba, bata hango rayuwar aure dashi ba, ko bikinta ba haka ta hasasoshi ba. Saboda ta hango auren hamshaqin maikudi, biki irin na alfarma, gida tanqameme da iyayenta ba zasuyi tunanin kayan daki ba. Duk da taji Baba na fadawa Mama cewar Abban su Waheedah ya siyi kayan daki, katifa kawai zasu siya. Tana kuma da tabbacin masu kyaune, za'a saka mata kayanta a gidan da bai cancanta ba. Gyara zama Nuriyya ta sake yi, sosai takejin abin kamar a mafarki. Waheedah da take ta hira da kawayenta suna dariya take kallo, tana jin wani nauyi a kirjinta. 1

Yanda kawayenta na FCE da basu taba ganin Waheedah ba suke zancenta yai mata zafi, yanda take shiga zuciyar duk wanda yaganta lokaci daya na tsayama Nuriyya a makoshi. Yanzun yanda take dariya na kara hada mata zafi, babu abinda take tunani sai kanta, da za'a daureta a auren Anas cikin kwanaki biyu, Waheedah zata ci gaba da hidimarta babu nauyin auren kowanne talaka akanta. Zata iya samun maikudi ta aura, karshen abinda take si ya faru kenan. Zata karasa mutuwa idan Waheedah ta samu Abdulkadir, shisa take addu'ar karya taba kallon Waheedah din da wannan niyyar. 6

STORY CONTINUES BELOW


Bazai taba yiwuwa a liqa mata auren Anas, Waheedah kuma ta samu Abdulkadir ba. Sai dai ko bata same shiba, tasan zata samu wani wanda yafi Anas din kudi, zata samu abinda ita bata samu ba kamar koda yaushe. Hakan kadai idan tayi tunani tanajin kamar zatayi hauka. Ko kadan rayuwa batai mata adalci, Waheedah ta zama kamar kaddara ta shigo da su rayuwar junan su dan ta nuna ma Nuriyya abinda duk take son zama amman yai mata nisa. Idanuwanta ta lumshe, alkawari taima kanta ta gama zubda hawaye akan abinda yake faruwa, tunda Anas yace yaji yagani, zata ga ko zai iya jure zaman aure da ita. Dan ta gama shirya mishi wulakancin da zaisaka shi dana sanin aurenta. 6

*

NDA KADUNA

Wanka ya fito, daga shi sai gajeran wando, da towel rataye a wuyan shi. Ahmad da shi kadaine abokin shi a zaman shi makarantar horar da sojojin tunda yazo ta shekaru hudu da wani abu, har yana shirin fita kuma, dan watannin daya rage musu bashida yawa. Suna shekararsu ta karshe kenan. Babu ruwan shi da kowa, in baka shiga lamarin shiba, sai abinda bazai iya kaucewa bane kawai zai hadaku. Ko wajen motsa jiki, ko training, ko a aji, wani abu dai daya zama mishi dole, saboda akwai masu saurin daukar zafi irin shi. Saidai bakowa yake jurewa hukuncin manyansu idan fada ya kaure ba.

Tun suna mamakin taurin zuciya irin na Abdulkadir harsun bari, shisa zuwa yanzun babu mai shiga sabgarshi sai ta kama, a yan Terma five kenan, balle kuma wanda suke kasan shi, har basaso wani abu ya hadasu da Abdulkadir din. Zai dakeka kamar ya samu ganga, musamman idan ya tashi yana jin bacin rai, in ya samu wani ya huce a kan shi yakanji ya dawowa dai-dai.

"A. Bugaje"

Ahmad yace kamar yanda kowa yake kiranshi a NDA din.

"Baka gyara wayar nan ba ashe?"

Screen dinshi ya fashe, a kwana biyu yana dan samu ya amsa kira idan ya shigo, saita kara faduwa, yaje ya gyara dinne baije ba. Yassar ma a wayar Ahmad din yake kira su gaisa.

"Zan gyara"

Ya fadi a takaici yana karasawa kan gadon ya kwanta. System dinshi ya janyo da take ajiye kan tebir din da yake dakin, budewa yayi, hannuwan Waheedah da kunshinta na cika screen din. Har yau baiga kunshin da yai mishi kyau kamarshi ba 2

"Hannuwan nan namun kyau wallahi, ina ma in gano yarinyar da take da shi"

Ahmad ya fadi yana miqa kanshi dan yaga hango sosai. AbdulKadir yakai hannu ya latse system din yana kasheta gabaki daya.

"Au dan bakin ciki kar ingani?"

Yai maganar yana dariya. Har duba system din yayi baiga hoton ba, ya rasa kalar boyan da Abdulkadir yai ma hoton, idan zai mutu yana tambaya ko yasan mai hannun ne, ko yana da alaqa da ita kamar yanda yai zato da farko bazai kulashi ba ballantana ya samu amsa. Kamar yanda yanzun ma bai kulashi ba. A gidansu Abdulkadir banda Yassar baisan kowa ba, sai Hajja dan sukan gaisa idan ta kira Abdulkadir din koshi ya kira, sai Zahra da itama suna waya, itace ma daya tambayi AbdulKadir din ko kanwarshi ce ya samu amsar

"Ban damu da ka kusa zama cikakken soja ba, zan karyaka Ahmad, da gaske zan karyaka..." 1

Yayi dariya sosai, kuma hakan ya tabbatar mishi da cewa kanwar Abdulkadir din ce. Akwai yarinyar da yake yawo da hotonta a wallet din shi. Wasu lokuttan kuma yakan cire hoton ya saka a aljihun shi, duk idan aka bata mishi rai Ahmad na kula yakan saka hannun shi a aljihun shi, kamar hoton nada wani sihiri da zai hutar da fushin shi. Duk yanda yake so ya tambayeshi alaqar shi da yarinyar hoton saiya kasa, saboda a bayyane yake. Tana da muhimmanci na gaske a rayuwar shi. Bai dai taba nuna alamar yana da budurwa ko yana son wata ba. Idan har hirarsu ta tsawaita to ta dangancin aikin da suke gab da fuskanta ne na kare kasarsu. 1

Sai dai watanni kusan bakwai da suka wuce, yakanga Abdulkadir din manne da wayarshi duk dare, ba daddanawa yake ba, da alama dai yana karanta wani abinne, yakan kuma ga yana murmushi shi kadai inya zauna da wayar a hannun shi. Gashi ya bude whatsapp din da babu yanda baiyi dashi ya bude ba, yaki. In kuma ya dauki wayar Abdulkadir din dan yai kira ko wani abu, banda yan gidansu da zaiga Hamma wanne, ko Adda wance, sai su Zahra, baya ganin kiranshi da kowa sai lambar daya sakama 'Wahee'. Yakan kuma ga saqoninta na shigowa wasu lokuttan. Baida tabbas, amman yana alaqanta hotonta ne Abdulkadir yake yawo dashi.

STORY CONTINUES BELOW


Juya mishi baya Abdulkadir yayi, yana jan pillow ya dora hannuwan shi akai, dan baya sakawa a kanshi, koya kwanta yasa pillow daya fara bacci yake zarowa ya dora hannunshi akai. Gashi har yanzun kwanciyar jarirai yake, jikin shi a dunqule haka yake bacci. Idanuwan shi ya lumshe, hoton Nuriyya na mishi yawo kamar koda yaushe, tun yana kokarin danne shi harya haqura yabarshi. Ya daina kokawa da zuciyarshi akanta, zuwa yanzun ya fahimci zuciyar shi na doka mata. Zai wani abu akai, saiya fita daga NDA ya dan samu nutsuwa, yanzun koma menene yake ji dole ya jirashi ya nutsuwa tukunna. 4

Lokaci irin wannan hirar Waheedah yakan karanta, har tai mishi saida safe, yakan koma baya yaita sake karantawa har saiya fara jin bacci. Amman kwana biyu hakan baya samuwa saboda bai gyaro wayarba. Yana kewar hirarrakinta, dan takan hana mishi tunanin Nuriyya irin haka, takan debe mishi kewar gida da gujema ganin Nuriyya ya hanashi zuwa. Sosai surutun ta yake mishi dadi 1

'Hamma kasan me ya faru yau'

Yakan karanta sakkoninta da sanyin muryarta, har yanayin idanuwanta yakan gani, kamar tana cikin dakin tare dashi. Idan an bata mishi rai yakan lumshe idanuwan shi yaji muryarta cikin kanshi 1

'Banda saurin fushi Hamma, dan Allah banda saurin fushi kaji'

Takan fada mishi haka a sakkoninta, tana saka murmushi kwace mishi. Inba ita ba, babu wanda ya isa yana bashi umarni haka, ko abinci takan mishi magana yaci, karya zauna da yunwa, wata rana sunanta kawai zai rubuta, zata ce mishi ya ajiye wayar ya kwanta. Yanda take karantarshi har mamaki yake bashi, tashi yayi ya dauko wallet dinshi ya ajiyeta gefen kanshi yana gyara kwanciyarshi. Hotonta yai amfani dashi ya danne na Nuriyya da zai sakashi tunanin abubuwan da zasu addabeshi. Baccin ya fara jin yana fisgarshi

'Hamma kayi addu'a'

Yaji muryar Waheedah na fadi cikin kanshi, batare daya bude idanuwanshi ba yayi addu'a, ko tofawa baiyi ba, bacci ya dauke shi.

*

Washegari da yake ya fada asabar, Ahmad ya dame shi, suka shiga kasuwar wayoyi ya gyara screen din wayarshi tukunna suka dawo. Suna dawowa charge ya saka wayar dan yaga yayi kasa sosai. Yai sallar azahar yazo ya zauna ya fara cin abinci, wayar ya ciro daga chargy ya bude data dinshi yana ci gaba dacin abincin, text dinshi ya shiga ganin wajen sakonnin ashirin, ya kuma san Waheedah ce. Dubawa yayi duka na jin ko yana lafiyane. Zuciyar shi na daukar wani irin dumi da sakonninta ne kadai kan haifar. Tana bashi kulawar da yake so, kulawar da babu wanda yake bashi ita sai Hajja, itama bakowanne lokaci ba.

Whatsapp din ya shiga, sakkoninta ne da yawa, zaice ita kadai take turo mishi sakkoni haka, su Nawaf gaisuwace, sai kuma zagi idan ya karanta bai amsa ba. Yassar ma hakan ne, yafi jin dadin nata fiye da nakowa, ita kadaice bata taba magana akan halayyarshi ba, asalima tana saka shi jin babu wani abu marar kyau a abinda yakeyi din. Bata damu dako ya amsata ko bai amsata ba, idan tazo takan sake mishi magana ta kuma bashi labari, Waheedah daban take da kowa na rayuwar shi.

Daga farko ya fara karanta sakon, da gaisuwa ce, hirar makaranta. Sai kuma ta fara bashi labarin suna hidimar biki. Karanta sakkonin yake yana cin abinci, kafin yaji shinkafar ta bimishi ta hanyar da bai kamata ba, tari ya kuwa sarqe shi, ruwa ya dauka babu shiri yana kwankwada, amman tarin bai daina ba, ga kirjinshi da yakeji kamar an fara hada wuta a ciki, idanuwan shi harsun kawo ruwan wahalar shaqewar da yayi, hakan yasa shi kankance su yana sake duba sakon Waheedah

'Nikam nagaji sosai Hamma, daman haka hidimar bikin kawa yake? Allah nafi Nuriyya gajiya'

Kasa yayi babu shiri yana isa sakonta na karshe

'Hamma har an daura auren Nuriyya fa' 1

Karanta sakon yake yana son fahimtar asalin ma'anar shi, kafin yaji numfashin shi na barazanar daukewa. Kanshi yake girgizawa yana sake danna wayar ko zaiga wani sabon sakon Waheedah din da zai karyata na karshe.

"No... No... Wasa ne wannan"

Ya furta yana jin zuciyarshi kamar tana rabewa biyu, kullum Waheedah na mishi hira, me yasa bata taba ce mishi Nuriyya zatayi aure ba, sai yanzun ne zata fada mishi an daura mata aure. 1

"Haka nace ki jirani, in nutsuwa waje daya Nuriyya. Nace ki jirani" 3

Yake fadi kamar wanda ya samu tabin kwakwalwa, ji yake gabaki daya duniyar ta hade mishi waje daya. Wayar ya cilla kan gado yana ture abincin, mikewa yayi ya fice daga dakin kwanan nasu. Wajen motsa jiki ya nufa, yana addu'ar kar wani ya tare mishi hanya, dan ko gani bayayi sosai, wani abu yake son duka, idan ba punching bag ba, to fuskar duk wanda tsautsayi ta gifto dashi. Allah ya taimake shi harya karasa wajen motsa jikin baici karo da kowa ba, bai kuma kula ko ana kaucewa bane idan an hangoshi

"A. Bugaje..."

Ahmad dake wajen ya kira ganin yanayin Abdulkadir din

"Ka matsamun Ahmad..."

Abdulkadir ya fadi yana karasawa ya dauki abin nade hannu ya fara nannadawa a hannun shi. Ahmad na karasawa wajen shi

"Me ya faru? Lafiya? Kaimun magana dan Allah..."

Dayan hannun Abdulkadir yake nadewa

'Hamma har an daura auren Nuriyya fa'

Shine maganar dake mishi yawo a ko ina na jikin shi tana kara saka kirjinshi wani irin radadi, yasan bacin rai, yasan fushi, yasan abubuwa da dama. Amman yanayin da yakeji yanzun daban ne a rayuwarshi, yanayine da baya fatan ya sake jin shi har abada, dan haka bazai bari ya dame shi ba, zai daki wani abu har saiya daina jin kirjinshi na mishi kamar zai bude.

"A. Bugaje..."

Ahmad ya kira cike da damuwa a muryarshi, Allah ne shaida yana jin Abdulkadir din kamar dan uwanshi. Bai kuma taba ganin yanayin da yake gani a fuskarshi ba, bai kula shi ba, punching bag din ya soma duka kamar zai jijjigota, da dukkan karfin shi yake dukanta, amman ji yake kamar yanayin da yakeji na karuwa da duk dukan, kamar da tunanin Nuriyya a matsayin matar wani zuciyarshi na kara budewa. Saida yaji numfashin shi na barazanar daukewa tukunna ya daina dukan yana dora hannuwan shi gwiwoyin shi hadi da wani irin sauke numfashi, tukunna ya dago ya hada wata irin zufa. 1

Kankance idanuwan shi yayi yana kallon Ahmad, muryarshi can kasan makoshi yace

"Tayi aure. Ahmad tayi aure..." 1

Kai Ahmad ya jinjina mishi yana fahimtar dalilin da yasa Abdulkadir din shiga yanayi, bai magana na ba, dan yaune karo na farko da Abdulkadir din yake fada mishi wani abu mai girma haka

"Ta jirani fa in nutsu ne... Shine tayi aure. Ni nace banyi tunanin aurenta bane? Me yasa zatayi aure?" 14

Ya karasa yana sauke numfashi, hannu Ahmad yakai ya taba kafadar shi cikin son nuna mishi yana tare dashi, ya fahimta. Abdulkadir din ya kauce yana fadin

"Don't... Kabarni"

Ya juya yana ficewa daga wajen motsa jikin, dan iskar da take wajen ta mishi kadan, kanshi kamar zai bude saboda bacin ran da yakeji a cike dashi. Har wani ja-ja yake gani yana gilmawa ta cikin idanuwan shi. Tayi aure bata jira shi ba, shine tunanin da yake cike dashi, yana jin wani yanayi na maye gurbin koma meye yake ji akan Nuriyya...!
Sadauki dan Allah... Ka saukake mun auren nan" 1

Muryar Waheedah ta daki kunnuwan shi tana dawo dashi daga dogon tunanin daya tafi, runtsa idanuwan shi yayi yana sake budesu akanta. Dubawa yake ko zaiga alamar wasa a tata fuskar, ko zaiga hijabin da ta saka tsakanin su ta yaye. Kan hannun kujerar dake kusa dashi ya zauna yana maida numfashi, sosai ya girgiza, bazai tuna ranar karshe da wani abu ya girgiza shi haka ba. Kallon Waheedah ya sake yi da yaji kamar kafafuwan shi na rawa saboda tashin hankali. Hannu yaga tasa tana share kwallar da ta tsiyayo kan kuncinta. Kirjin shi yaji yana zafi, gani yake yau din gabaki daya duk wani abu da tasan bayaso takeyi, kamar kuma tana yi dinne dan ta bata mishi rai.

"Wahee..."

Ya kira muryarshi can kasan makoshi, bata dago ba, taji shi, ta saurara ne ko tsikar jikinta zata tashi kamar ko da yaushe, tsayin shekaru baisa ta daina jin yanayin soyayyar shi ta daban da take taso mata duk idan ya kira sunanta. Wannan karin babu abinda taji banda gajiya da komai, duniyar take ji ta hade da ita a waje daya, kamar tana cikin dakin da babu ko da window ballantana kofa, ji take fitarta daga dakin zata zo da saukake mata auren shi da zaiyi.

"Wahee magana nake miki"

Abdulkadir ya fadi, yana kokarin danne bacin ran da yake ciki, yanayin da yazo mishi a wahalce, saboda Waheedah ce, bai taba boye wani yanayi nashi ba a tare dashi. Bai taba tsoron bude mata komai nashi ba, tare da ita bai taba jin akwai wannan bukatar ba, idan ranshi a bace yake yana nuna mata saboda tasan yanda zatayi dashi, idan farin ciki yake takan gani. A gabanta yake dariya sosai dan yasan bazata taba raina shi ba, a yar karamar duniyar shi daga ita sai Yassar yake tsokana sosai. Ita fiye da kowa, ko Yassar kanyi shakkar mishi wani wasan, amman cikin ido Waheedah kan kalle shi ta tsokane shi.

Ganin tayi shiru har lokacin yasa shi saukowa daga kan kujerar yana tsugunnawa kusa da ita. Hannuwanta ya kamo duka yana rikewa cikin nashi. Kusancin shi bai taba kinyin tasiri akanta ba, yasani, lokutta da dama ko damun shi tayi da surutunta, matsawa zai ya rike hannunta bakinta zai shiru. Idan wani abu yai mata daya riketa a jikin shi yaji ta zagaya hannuwanta a bayanshi yasan ta karbi hakurin shi batare daya furta ba. Yanzun ma hakan yake so yayi amfani dashi kafin komai ya karasa kubce mishi.

Ita kanta Waheedah mamaki takeyi, dan tasan abinda yake kokarin yi din, lokuttan duk da yayi tasani, amman hakan bai taba hanashi tasiri akanta ba, wannan karin zuciyarta ta gama bushewa. Hawayen da ke shirin zubo mata taji sun tsaye cik, kamar tabatan da yayi ya kara busar mata da zuciya. Hannuwanta ta zame daga cikin nashi, tana yawata idanuwanta akan fuskar Abdulkadir din

"Ka kwashi yaranka, ka bani takardata..." 7

Tai maganar muryarta na mata baqunta cikin kunnuwanta, balle Abdulkadir da yake kallonta idanuwanshi na kankancewa da bacin rai. Kallon shi take, yanayin da take gani a fuskarshi a da zai tsoratata, sosai zuciyarta zata fara rawa da abinda zai faru, amman yau ko a jikinta take ji. Itama ranta a bacen yake, karo na farko da takejin son dora bukatarta sama da tashi. Wani murmushi yayi mai sauti yana mikewa, bin shi da kallo Waheedah tayi ganin ya soma tafiya, amman ba kofa ya nufa ba, hanyar da zata kaishi dakin Anty. Wani sabon zazzabi take ji yana lullubeta, da gaske Abdulkadir yakeyi yaranta zai dauka. Hawayen da suka bushe mata take jin sun fara farfadowa. 1

Tana kallon shi harya bace mata, dakin Anty ya nufa kanshi tsaye. Ko kwankwasawa baiyi ba ya tura kofar yana samunta a tsaye.

"Ikram zaki bani"

Kallon shi Anty takeyi, tasan taurin kanshi tun yarinta, amman nayau da take gani daban ne, musamman Waheedah, bata taba ganin ran yarinyar a bace irin nayau ba, ko menene Abdulkadir din yai mata mai girma ne. Amman hakan baya nufin tana son ganin mutuwar auren nasu, kodan yara dake tsakani

STORY CONTINUES BELOW


"Abdulkadir karkayi haka, karka yanke hukunci cikin fushi dan Allah. Ka duba yarinyar nan duka watanta nawa a duniyar? Idan zaka tafin ne ma, ka dauki Fajr shi. Kabarta ta huta idan an kwana biyu saika dawo kuyi magana, itama tahau dokin zuciya ne"

Kankance idanuwan shi Abdulkadir yayi, yana wani irin sauke numfashin bacin rai, Waheedah ita taja mishi tonon sililin nan. Da ta saka kowa yazo yana tsoma mishi baki a cikin maganar iyalin shi 1

"Kiban yarinyata Anty..."

Abdulkadir din ya fadi yana kokarin danne sauran maganganun da suke kan harshen shi. Itama Antyn ranta take ji yana kara baci

"Ba zakaji magana ba kenan ko? Ba zaka ji ba ko Abdulkadir..." 2

Runtsa idanuwan shi yayi yana budesu

"Idan da naso jin ra'ayinki kan abinda yake faruwa ina da bakin dazan bukaci hakan...kiban yarinyata" 3

Hannu Anty ta saka tana kwance goyon Ikram din, mika mishi ita tayi tana furta

"Allah ya shirya"

Karbar yarinyar yayi da taketa bacci kamar komai bai faru ba, nutsuwar da take ciki na sakashi sauke numfashi, saida ya gyarata cikin hannun shi tukunna ya kalli Anty

"Amin"

Ya juya yana ficewa daga dakin, yanda ya doko kofar na saka Anty yin dana sanin marin da taki daukeshi dashi. Sai dai tasan Abdulkadir idan bai rama ba, sai ya gaya mata maganganun da zatayi satika tana juyi dan kunar rai. Wani abin da zai maka koda an samu igiya an kulle shi a baka kulki ka jibgeshi bazaka huce ba. Kan gado ta koma ta zauna, zuciyarta na tafasa. Shikam falon ya karasa yana kallon yanda Waheedah take kallon shi cikin sabon tashin hankali. Hakan ya mishi dadi, gara taga da gaske yaranshi zai dauke, saita tashi su koma gida gabaki daya. 2

Idan rigima takeji zai bata dai-dai wadda zata isheta harda kari idan bukatar hakan ta taso. Waheedah batasan ta mike ba saida taga kallon da Abdulkadir din yake mata. Ta dauka zuciyarta ta bushe, ta dauka babu wani abu dazai sake taba ta, saida taga yarinyarta a hannun shi tukunna takejin yanda yake son rabata da sauran nutsuwar da ta rage mata, muryarta a karye ta soma magana

"Me kake so dani? Sadauki me kake so dani haka? Meye ban baka ba? Lokacin da sukazo saura suka samu daga zuciyata, saboda kaso mafi girma na tare dakai..." 2

Shiru tayi tana mayar da numfashin daya taso mata mai hade da kukan da yasa ta kasa karasa maganar data fara

"Ki biyoni mu tafi gida, koma menene zamu gyara shi mu biyu..."

Abdulkadir ya fadi yana rokonta da duka zuciyarshi da ta amince, saidai a fuskarta yake ganin hijabin da baisan daga inda ta samota ta saka a tsakaninsu ba, hannu tasa ta share hawayenta tana girgiza mishi kai, yanayin daya kara mishi zafin da kirjin shi yakeyi. Kai ya jinjina yana fadin

"Kiyi abinda kike so Waheedah..."

Ganin ya juya yana shirin barin dakin ya sata furta

"Takardata Sadauki..."

AbdulKadir bai nuna alamun yajita ba ya fice daga dakin. Aurenta a hannun shi yake, yara nashi ne, zai dauka duk sanda yaga dama. Ya dauka idan yayi amfani dasu zata hakura ta dawo hayyacinta daga rashin hankalin da take ciki. Hakan bai faru ba, zai dauki yaran yanzun, zai tafi dasu. Zai kuma ga wanda ya isa yasa shi sakinta, tonon asirine ta gama yi mishi, abinda bai taba tunanin zata tabayi ba, sosai ta girgiza shi, dan harya shiga bangaren Mami yana mamakinta, yana kuma duba cikin kanshi ko zai tuna asalin laifin dayai mata banda na ranar amman ya rasa.

Bai samu Mami a falon ba, Aminu ne zaune da Fajr da hankalin shi gabaki daya akan tom and jerry din da yake kallo a babbar talabijin din dakin. Batare da yayi magana ba ya karasa yana saka hannun shi daya ya dago da Fajr din da a shagwabe yace

STORY CONTINUES BELOW


"Paapi..."

Gyara mishi tsayuwa Abdulkadir din yayi yana fadin

"Wuce mu tafi..."

Da rashin fahimta yaron yake kallon shi da idanuwan shi irin na Waheedah din

"Omma fa?"

Saida Abdulkadir ya sauke numfashi tukunna yace

"Banda ita..."

Maqale kafada Fajr yayi, yana shagwabe fuskarshi sosai

"Zan zaneka Fajr... Ka wuce nace"

Wucewar Fajr yayi dan duk karancin shekarun shi yasan cewa Abdulkadir din zane shi zaiyi kamar yanda ya fadi, kukan shi ma bai bari ya fito ba, dan yana bala'in tsoron duka, ko tsintsiyar kwakwa yaga Waheedah ta fito da ita ta ajiye waje daya zai nutsu. Abdulkadir kuwa ya taba saka charge ya zane shi, sosai yake tsoron yin wani abu a gaban shi. Sai lokacin Aminu yace

"Tunda ba zashi ba ka kyaleshi"

Kallon shi Abdulkadir yayi yana kafe shi da idanuwa, bai manta maganganun daya fada mishi a asibiti ba dazun, kawai ya kyalene baice komai ba saboda a lokacin yana cikin jin kunyar Mami

"Ka mantani ko? Aminu ka manta wanene ni" 1

Kai Aminu ya sauke kasa yana jin zuciyarshi na dokawa cike da tsoro. Bai manta ko waye Abdulkadir ba, haushin shi da yakeji dinma a yanzun ya nemeshi ya rasa

"Zan dakeka, zan fasa maka bakin da saikayi sati magana da kowa na maka wahala balle kayi tunanin mun rashin kunya..." 1

Abdulkadir ya karasa yana directing bacin ran nashi kan Aminu. Sosai yake jiran yaron yai motsin da bai mishi ba, ya ajiye Ikram kan kujera ya dake shi kamar ganga. Zuciyarshi zatai mishi sanyi ko yaya ne idan ya zane wani, tunda bazai iya zane Waheedah da ta bata mishi ran ba. Amman Aminu ko dago dakai baiyi ba ballantana yai kokarin cewa wani abu. Kai Abdulkadir din ya jinjina ya juya ya kama hannun Fajr yana janshi suka nufi hanyar da zata kaisu harabar gidan inda motarshi take a ajiye.

*

Yassar ya hango ya bude motar shi ya fito, cikin shigar manya kaya da hula da suka kara mishi wani irin kwarjini. Tsaye Abdulkadir din yayi batare daya san dalili ba, yana nan har Yassar din ya karaso ya same shi

"Ina kuma zakaje da yara?"

Yassar ya bukata, yana kai hannu ya dafa kan Fajr daya fada jikin shi yana fadin

"Uncle..."

Yana gidan shi a kwance yaga wayar Hajja. Saida zuciyar shi ta doka, dan yasan ba lafiya ba, indai Hajja zata daga waya ta kirashi sai da wani babban dalili. Baiyi mamakin jin dalilin Abdulkadir bane ba.

"Bakaimun sallama ba Hamma..."

Abdulkadir ya fadi yana kankance idanuwan shi, dan yaga yanayin Yassar din shima yasan abinda yake faruwa. Wani irin kallo Yassar ya watsa mishi

"Yaran ka dauko? Ka sake tan?"

Kai Abdulkadir ya girgiza mishi, hannu Yassar ya mika yana karbar Fajr da Abdulkadir din ya kasa hanashi

"Nasan baka da hankali ko kadan, amman banyi tunanin yakai haka ba. Gidan ubanka zakaje da jaririya? Ko Nuriyyar ce zata shayar maka da ita?" 2

Sosai Abdulkadir ya dakuna fuskarshi

"Karkai mun fada Hamma, idan zaka dauki sides saika tsaya kaji nawa bangaren tukunna"

Tsaki Yassar yaja, da yace bazai sake shiga matsalar Abdulkadir din ba, yanzun ma dan Hajja ta kirashi shisa ya dauko kafarshi yazo. Hannun Fajr ya kama yana shirin raba Abdulkadir din da nufin wucewa

STORY CONTINUES BELOW


"Hamma ina zakaje mun da yara?"

Kallon shi Yassar yayi

"Idan ka biyoni saina watsa maka mari, mahaukacin banza..." 6

Murya can kasa Abdulkadir yace

"Yarana, a gaban yarana Hamma..." 4

Tsakin Yassar ya sake ja yana wucewa abin shi, yanajin Abdulkadir din na biye dashi. Baiko juya ba harya karasa bangaren Anty, tunda Hajja tace mishi suna can data kira. Waheedah ya samu ta hada kanta da kujera, yanayin ta nasa wani abu tsaya mishi a rai, dagowa tayi fuskarta harta tara jini saboda kuka. Sosai Yassar yaji kirjinshi yayi nauyi. Karasawa yayi ya zauna kan kujerar yana mika mata Ikram. Da sauri ta karbi yarinyar tana riketa a jikinta, duminta na saukar mata da wata irin nutsuwa taban mamaki

"Nagode Hamma..."

Ta fadi cikin wata irin murya da tasa Yassar sake kallon Abdulkadir din yana watsa mishi wani kallo. Kankance mishi idanuwa Abdulkadir din yayi, ya dauka Yassar na bayanshi, kamar ko yaushe akan abubuwa da dama. Tun a watanni baya yagane cewa shima bayan Waheedah yake, bashida matsala dan Yassar yaso Waheedah, ko bakomai kanwarshi ce, amman shima kaninshi ne, kuma yana da kishin da bayaso a fifita soyayyarshi akan ta kowa. Ko Hajja bayason yaga tana nuna ma su Yazid soyayya fiye da wadda take nuna mishi.

"Kiyi hakuri Waheedah..."

Kai Waheedah ta girgiza ma Yassar da takejin maganar shi kamar ya watsa mata ruwan zafi. Shima kan yake girgiza mata yana saurin dorawa da

"Ba ina nufin kiyi hakuri da koma menene yai miki ba..."

Da mamaki Abdulkadir yake kallon Yassar

"Hamma?" 1

Ya kira, ko kallon shi Yassar baiba, asalima maganar da yakeyi yaci gaba

"Idan nan din zasu dameki ki tashi mu tafi gidana..."

Wani murmushi mai sauti Abdulkadir yayi da bashida alaqa da nishadi

"Kana magana kamar izinin fitarta yana hannun ka" 1

Zama Waheedah ta gyara tana daga Ikram ta mike, towel dinta ta zame ta sakata a bayanta. Goya yarinyar tayi a bayanta. Kamar yanda Yassar din ya fadi, tana bukatar hutu, bataso kowa ya dameta ko yayi kokarin bata hakuri, tana kuma da tabbacin Yassar bazai bar kowa yazo ya dameta ba. Zata jira takardarta a gidan shi. In yaso daga baya ta dawo gida. Dan daman batayi niyyar zama bangarensu ba, balle Mami ta tambayeta meya faru. Batasan ta inda zata fara ba, ya saukake mata shine abinda tafi bukata.

"Ina zakije?"

Abdulkadir ya bukata yana kallon ta cike da sabon mamaki

"Ka aikomun takarda ta gidan Hamma, ko kabama Abba, duk wanda yafi maka sauki dai"

Tai maganar tana kallon Yassar da fadin

"Hamma muje..."

Ta kama hannun Fajr, bai cika yawan magana ba, amman bai taba tunanin zai rasa abin cewa gabaki daya ba sai yanzun, dan ba kalaman shi bane kadai suka kubce mishi, harda abinda ya kamata yai tunanin da ya wuce tsananin mamaki.

"Waheedah tsinuwar mala'iku da duk takun da zakiyi batare da izinina ba..."

Ya tsinci kanshi da furtawa ganin ta saka kafarta daya wajen dakin. Juyowa tayi da wani irin yanayi a fuskarta

"Tunda safiyar yau nake zubar da hawaye, kuma kaine sila, tsinuwar zatai balance Sadauki... Ina jiran takardata" 6

Ta karasa tana ficewa daga dakin. Wani murmushi Yassar yayi, tunda ya san yarinyar bai tana tunanin tana da kwarin gwiwar karbarma kanta 'yanci ba sai yau. Lokutta da dama yakanji kamar harda laifin shi a abinda take fuskata na zama da Abdulkadir, yakanji a kaso dari ma aurenta da Abdulkadir yana da hannu cikin kashi tamanin harda doriya. Musamman watannin baya haka yakejin duk laifin shine, amman yanzun ta fara rage mishi nauyi. Duk da can kasan zuciyarshi bazaiso mutuwar aurenta ba, amman hakan bazai hanashi goyon bayan gaskiya ba. Wannan karin son Abdulkadir baizai rufe mishi idanuwa ba. Batare dayace komai ba yabi bayanta. 1

STORY CONTINUES BELOW


**

Bazai ce ga yanda yakai gida ba, nutsuwar shi bata taba kwacewa akan tuqi ba sai wannan karin. Bangaren Waheedah ya wuce yana shiga har dakin baccin su, wannan karin takalman shi ya cire bayan ya zauna kan gadon tukunna ya kwanta. Pillow dinta ya dauka yana rikewa a jikin shi, kamshin turarukan ta ya shaka yana lumshe idanuwan shi. Yakanyi kewarta duk idan yazo ya koma wajen aikin shi. Bai taba tunanin zai kewarta yana gida ba, amman ya fara, cikin kasa da awa biyu komai ya birkice musu. 1

'Sadauki zaka karyani...'

Yaji muryarta cikin kanshi data saka shi bude kananun idanuwan shi, kafin ya sake mayarwa ya rufe su yana kara matse pillow din a jikin shi, sanyin shi na sake tunasar dashi cewa ba ita bace ba

"Ba zakimun haka ba, Waheedah ba zakimun haka ba..."

Ya furta a hankali yanajin an kwankwasa kofar dakin, wata irin dirowa yayi daga kan gadon

"Nasani, nasan ba zaki iya nisa dani ba... Nasani"

Yake fadi yana karasawa ya bude kofar, Nuriyya yagani, a karo na farko da yaji baiso ta kasance a bakin kofar ba. Rigarshi ce a jikinta sai wandon da ko cinyoyinta bai rufe ba. Ta kama gashinta da yake a kwance ta kulle shi a tsakiyar kan nata. Kwalliya ce a fuskarta sosai, da alama tayi wanka bayan fitar shi. Sosai yake kallonta yana neman samun nutsuwa koya take daga hakan.

"Naji motar ka..."

Nuriyya ta fadi, tana jin zuciyarta tayo tsalle zuwa wuyanta da yanayin dake fuskar shi, zatai karya idan tace bataji tsoro ba daya bude kofar, saboda taga wani abu kamar disappointment shimfide kan fuskar shi, kamar ba ita ya tsammaci gani a tsaye a gaban shi ba, sosai hakan ya tsoratata. Ganin ya kankance idanuwan shi yana kallonta har lokacin yasata fadin

"Ya jikin Waheedah din?"

Tanajin dacin dora sunan nata kan harshenta, wani irin tuquqin kishi na danne kirjinta da yanda zai kasance sunan Waheedah zatai amfani dashi yau dan tai nasara kanshi

"Da sauqi"

Ya furta can kasan makoshi, kai tadan jinjina tana shagwabe mishi fuska

"Abinci fa?"

Saida ta kira abinci tukunna yaji cikin shi ya murda mishi da yunwar da yakeji, numfashi ya sauke, duk ranar baici komai ba, Waheedah ko damuwa da cikin shi batayi ba. Yanda baya jure yunwa idan yana tare da ita har mamaki yake bashi.

"Ki dafa koma menene"

Yai maganar yana shirin rufe kofar a fuskarta, kallon shi Nuriyya takeyi tanajin cikinta ya murda mata da yunwar da takeji itama. Ba zatace ga rana daya datai wani girki kwakkwara ba tunda tazo gidan. Da tace mishi

'Abinci fa?'

Batana nufin me zata dafa bane, tana nufin me zasuci ya fita ya siyo musu dan ita yunwa takeji ta fitar hankali, biscuit ne kawai a cikinta duk yinin ranar. Saurin dafe kofar tayi

"Masoyi..."

Ta fadi tana tattaro duk wata kissa da zata iya ta nade muryarta da ita. Numfashi Abdulkadir ya sauke, bacin ran da yakeji a kusa yake. Da Waheedah ce data gane gab yake da fashewa, ko bata bashi space din da yake bukata ba zata kama hannun shi ta zaunar dashi, zata dora kanta a kafadarshi su zauna shiru har sai yadan nutsu. Amman da alama Nuriyya bata karanci ranshi a bace yake ba. 2

"Naga yamma tayi, na dauka ma ka siyo mana..."

Tai maganar tana kallen shi fuskarta a shagwabe. Numfashi ya sake saukewa yana dorawa da

"Idan ba zaki dafa ba ki barshi..."

Da mamaki a fuskarta take kallon Abdulkadir, bai taba mata magana cikin yanayin dayai mata ba yanzun

STORY CONTINUES BELOW


"Masoyi..."

Ta kira

"Kinjini ai"

Ya fadi yana rufe kofar a fuskarta ya koma kan gadon ya kwanta. Wani bacin ran na sake danne shi. Dan yasan ba laifinta bane ba, ba ita ta bata mishi rai ba, bai kuma kamata ace ya sauke akanta ba. Yagani a fuskarta yanda hakan ya tabata, ba Waheedah bace ba, ita kadai ce a duniyar shi yake saukewa bacin ranshi ko da ba tada alaqa da hakan, saboda tabarshi, saboda ta nuna mishi bakomai dan yayi hakan, ta fahimta yana son saukewa a wani waje, dan ya zabeta bai dameta ba. Karamin tsaki yaja. Ko kadan bayason yawan tunane-tunane, Waheedah tasan hakan ta zabi ta sakashi cikin tunani. 4

Nuriyya ta kai mintina biyar a tsaye a bakin kofar, ranta idan yayi dubu a bace kowanne yake. A rayuwarta batason wulakanci koya yake, idan akai matashi takanji kamar an mata hakanne dan a nuna mata ita din bakomai bace, amman tunda can idan wulakancin ya kasance daga bangaren shine takanji kamar zata hadiye zuciya ta mutu. Yanzun ma haka takeji, kirjinta har zafi yake mata. Batasan me akai mishi a waje ya bato mishi rai ba, dan ita tasan batai mishi komai ba. Yunwar da takeji na karasa bacin ran ya hade mata, wucewa tayi ta koma bangarenta tana nufar kitchen.

Fridge ta bude tana rasa abinda zata dafa, akwai kaza a ciki danya. Abdulkadir na kokari sosai wajen kula dasu tasani, kajine da yawa a nata fridge din, Waheedah kanzo har bangarenta ta kawo mata, bata cika amfani dasu bane shisa suka taru, randa taji kwadayi ya kamatane take daukowa ta soya. Yanzun ma kulli daya ta fito da ita duk tayi kankara, ta rufe fridge din tana sakata cikin abin wanke-wanke ta bude fanfo. Tukunya ta fito da ita tana ajiye, kazar da take a yayyanke ta kwashe ta zuba cikin tukunyar, ruwa ta zuba a ciki ta dora kan gas tana kunnawa.

Wajen fridge din ta karasa tana dubawa taga ko tana da cefane. Gani tayi babu, tunda ba girkin takeyi ba, bata kula ba. Fita tayi zuwa bangaren Waheedah ta shiga kitchen din nata tana bude fridge, akwai kayan miya a cikin robobi a ajiye wajen roba biyar. Na farkon ta fara dauka ta wuce ta koma, diba tayi ta zuba cikin kazar, sosai take ganin ya mata yawa, dan robar nada girma,a fridge dinta ta saka dan ba mayarwa zatai ba, koda zata sake amfani dashi. Maggi tazo ta bare ta watsa, taliya zatayi jalof. Tana gama zuba maggin taji kiran sallar la'asar. Daki ta koma tayi alwala, zani kawai ta daura saman kayan jikinta ta saka hijab ta gabatar da sallar. 2

Ko dardumar bata linke ba ta cire hijab din da zanin tana watsa su kan gado ta koma kitchen din, yunwa takeji ta fitar hankali, budewa tayi taga ya tafaso, amman wani karni ya daki hancinta dan kazar ko wankuwa batai ba, kuma kayan miyar babu albasar kirki a markaden su. Dauka tayi ko dan bata karasa dahuwa bane ba, ludayi tasa taji ko kazar tadan yi laushi, rufewa tayi ta tsaya kamar minti biyar a kitchen din, har lokacin ranta a bace yake, tukunna ta bude daya daga cikin locker din dakin ta dauko taliya guda daya. Kakkaryawa tayi ya zuba cikin tukunyar tana jujjuyawa tukunna ta koma falo ta zauna. Gara ko kallo ne tayi ta rage zafi.

Tana kunnawa ta dauki remote suna dauke wutar su, wani dogon tsaki taja

"Tsinannu..." 1

Ta furta a fili tana mikewa. Kitchen din ta koma taga tsaliyar harta fara laushi dan kanana ce, da tana gidan su takan jima bataci taliyar turawa ba, filawa Babansu yakan siyo a kado musu taliyar Hausa, ita ko lokacin sai tayi sati biyu bata dora tukunya ba, tun Mama na mata fada harta gaji ta hakura, idan ta matsa mata abincin ba za'a ga dai-dai ba, garama idan da mai da yaji ne, ko wake da shinkafa ce wani lokacin waken a tsai-tsaye za'aci shi. Bai gama dahuwa ba, shisa ta daina sakata, tunda ba wadatar abincin suke dashi ba da za'a dinga barnar shi.

Taga alamar taliyar ta kusan dahuwa, amman sosai ruwan yayi yawa. Abin kama tukunya da bangaren Waheedah ta dauko shi bata mayar mata ba ta saka tana dauke tukunyar daga kan gas din, rage ruwan tayi cikin abin wanke-wanke tukunna ta sake mayar da tukunyar kan gas. Tunawa tayi bata zuba mai ba, shisa taga taliyar ta mata wani iri, dubawa tayi ta dauko man a cikin roba, da yake na 'ya'yan itatuwa ne suke amfani dashi. Tana ma da man gyada da Waheedah ta bata yakai kwalba biyu, a cewarta kanwar babanta ce ta kawo mata da tazo gidan. A ludayi ta tara man tana zuba ludayi biyu ta cakuda, gani tayi kamar bazai wadata ba, ta kara ludayi daya tukunna ta rufe tana mayarwa. 14

STORY CONTINUES BELOW


Jujjuya taliyar ta sakeyi, ta daddaga ludayin a hannunta ta dan-dana. Gishiri ta dauko ta zazzaga dan taji kamar bai mata ba, hannunta ya kubce kuwa, cikin hanzari tai kokarin saka ludayi ta kwashe amman duk ya narke dan abincin nata tafasa, tsaki ta sake ja, komai baya tafar mata dai-dai. Dabara ce tazo mata, ta dinga kwaso romon da ludayi tana zubawa cikin wajen wanke-wanke tukunna tadan dibi ruwa ta kara ciki, gani tayi cefanen naso yai mata kadan, ta zaro taliya daya ta saka a bakinta, duk da hakan gishirin nason mata yawa, kuma bataji cefane kamar yanda ta Waheedah kanyi ba. Robar ta dauko ta kara dibar wani ta zuba ta cakuda, sai taga tadan mata kyau a ido. Kamshine kawai baya tashi. 7

Faranti ta dauka tana zuba musu ita dashi a hade, kusan duka naman ta kwashe ta saka musu a ciki. Dauka tayi zuwa falon ta ajiye ta koma ta dauko cokulla masu yatsu ta saka a ciki, tukunna ta taka zuwa bangaren Waheedah da batasan me yake acan din ba tunda bata nan, a falo ta same shi zaune.

"Ka taso muci abinci"

Ta fadi tana kallon shi harya mike ya taka ya wuce ta batare dayace komai ba. Yunwa ke cin shi sosai da sosai. Bayanshi Nuriyya tabi har falonta. Kan kafet suka zauna, cokali AbdulKadir ya saka cikin abincin yana jujjuyashi, yanayin taliyar bai mishi ba sam, yakanci kome Waheedah ta dafa ta bashi, bai saba fada mata ga abinda yake son yaci ba, idan unguwa taje ma saita gama mishi girki take fita indai yana nan. Zubawar kan zame mishi aiki, da lokacin cin abincin yayi zata kirashi a waya taji ko yaci.

Lokutta da dama zai saka mata rigima saita baro duk inda take ta dawo sunci tare, ko yace shi baisan yanda zai zuba ya isheshi ba, haka zata fada mishi ludayin dazai amfani dashi, ko guda nawa zai zuba, miya tasa ya samo wajen zubawa ya zuba tace ya dinga diba yana sakawa a abincin inya rage saura ya saka mata a fridge. Sai dai Waheedah ce, tasan abinda yake son ci, tasan abinda bayaso, taliya na daya daga cikin abincin da bawai ya dameshi bane, gara da miya, amman jalof haka tsuranta bata dameshi ba.

Idan Waheedah tayi tana hada mishi salad sai yaci, idan yace ta dafa taliya, takance mishi tana son ya dinga cin komai saboda inya koma wajen aiki bata kusa. Sosai yake cakuda taliyar yana tunanin sakata a bakin shi, naman ma ko kadan bai mishi ba, idan a wajene babu yanda zaiyi saiyaci, amman cikin gidanshi bai saba da abinci irin hakan ba. Bayason yin wani dogon nazari ya nannado taliyar yana sakata a bakin shi. Nuriyya yake kallo da take cin abincin hankalinta a kwance, kamar yana mata dadi, abinda baisani ba, bawai abincin ya mata dadi bane, ita kanta taji yanda gishiri yadanyi yawa. Sai dai yunwa takeji ta fitar hankali, inda baya nan ma zataje ta hada shayi. Amman batason nuna mishi yanda abincin bai mata ba.

Dakyar Abdulkadir ya hadiye taliyar dake bakinshi yana dubawa danya dauki ruwa, bata kawo mishi ba

"Baki bani ruwa ba..."

Ya furta, sai lokacin ta dago tana kallon shi, mikewa tayi ta dauko mishi ruwa a fridge tazo tana kawo mishi. Ganin ya kalleta yasa ta komawa ta dauko kofi tazo ta ajiye, budewa ruwan tayi tana zuba mishi, dauka yayi yasha, ruwan ya kulle mishi ciki lokacin daya dira cikin hanjin shi, ko kadan bazai iya cin taliyar nan ba, ganin ya bai dauki cokalin ba yasa Nuriyya fadin

"Har kayi me?"

Daquna mata fuska yayi

"Bana son taliya Nuriyya..."

Da rashin fahimta take kallon shi

"Idan Waheedah ta dafa kana ci" 1

Kai ya jinjina mata da taji kamar ya watsa mata garwashin wuta, tabbatar mata yake tata ce bazai ci ba, amman yanacin ta Waheedah, magana zatayi ya dora da

"Ba irin wannan bace" 1

Cokalinta ta ajiye itama, tana danne kishi da tuquqin bakin cikin daya taso mata tayi mishi wani murmushi

"Kaci naman to" 1

Baiyi musu ba, cokalinshi ya dauka yana kokarin sabulo tsokar naman, amman yaji abu ya gagara, idan abincin Waheedah ne yana saka cokali a jikin naman yake raboshi da kashin shi saboda ya dahu. Ajiye cokalin yayi yasa yatsun shi ya tsamo cinyar yana kaiwa bakin shi ya kafa hakori a ciki, qiri-qiri yaji naman, kona waje yafi shi dahuwa, gutsura yayi yana taunawa, ruwan naman na sauka bakin shi da wani dandano marar dadi, gashi ko maggin kirki bai kamashi ba. Ajiye na hannun shi yayi yana dakuna fuska

"Wanne irin nama ne wannan? Bai dahu ba..." 5

Abdulkadir ya fadi yana ciro na kora wanda ya gutsura da ruwa

"Bangane bai dahu ba..."

Nuriyya tai maganar a kufule, kankance idanuwan shi yayi yana kallon ta

"Kici a bakinki..."

Naman ta sa hannu ta dauka ta gutsura, ita kanta taji bai dahu ba, ajiyewa tayi kunya na kamata, tasan bata iya girke-girken nan ba, girman kanta kuma bazai taba barinta tace Waheedah ta koya mata ba, shisa take ta damun shi daya dauko mata 'yar aiki, kuma ko da ta iya ma, Allah ya dora mata ganda, ba zata iya girke-girken da Waheedah ke yini tana yi ba. Duk ranar girkinta takanja jiki, kota jashi tace suje bangaren Waheedah din su tayata hira, dan suci abinci acan din. Farko-farko ta dauka Waheedah din kan basu saboda Abdulkadir din ne kawai.

Saida taga ko baya nan taje bata hanata, wani lokacin takan aika Fajr ya kirata tazo ta dibi abinci. Yanda Abdulkadir din bai taba kula tana gujema girki ba har mamaki yake bata. Addu'a take Waheedah karta jima a asibitin, dan taga alamar zasu samu matsala da Abdulkadir kan abinci. Mikewa yayi da alama ranshi a bace yake, yana sawa ta mike itama 3

"Dan Allah Masoyi kayi hakuri, cikin sauri nayi girkinne dan naga yamma tayi..."

Baice mata komai ba ya rabata ya wuce, ranshi a bace yake, kuma yunwa yakeji, idan yai magana baida tabbacin abinda zai fito daga bakin shi, addu'a yake kartai kokarin binshi dan baisan me zai faru ba...!Tunda suka shiga gidan Yassar ta gaisa da matar shi Hawwa da yar kanin Abba ce ya aura, ta samu kujera a falon ta zauna. Batasan me Yassar din yace mata ba, taga dai tazo tace mata ta tashi taje ta huta, daya daga cikin bedrooms din dakin ta rakata. Fajr kin binta yayi saboda yana kallon cartoon, da yake Yassar din ma yakan je ya dauko shi yai hutun karshen mako a gidanshi wasu lokuttan, yaron ya saba dasu. Tana shiga ta kwantar da Ikram, bandaki ta shiga ta daura alwala dan ko sallar azahar batayi ba. Ta fito ta gabatar da sallah, zaune tayi akan kafet din tana dora kanta a jikin gadon, kanta a cunkushe take jin shi, ta rasa abinda yake mata dadi a gabaki daya duniyar. 1

Tunani ne ya dauketa yana watsata shekaru Shida da wasu yan watanni da suka wuce, kafin rayuwa ta kawota inda take.

*

Tun bayan bikin Nuriyya, sai ya zamana babu abinda Waheedah ta saka a gaba banda karatunta, takanyi kwana biyu bata leqa gidan Nuriyyar ba, duk da ba wani nisan kirki ne a tsakanin su ba, ita tana cikin Naira da kwabo, su kuma su Waheedah din a kofar ruwa, ko da kafa zata gangara. Amman suna yawan waya, kusan kullum zasuyi chatting, wani lokacin kuma inta riga Nuriyya tashi daga makaranta takan biya ta FCE dinsu sai su gaisa. A yanayinta take fuskantar yanda har lokacin taqi kwantar da hankalinta da auren Anas din. 1

Sai dai fadan da Waheedah take mata yasa ta daina gaya mata komai, inta tambaya ma sai dai Nuriyyan tayi murmushi tace mata lafiya kalau, duk da tasan karya take, bata takurata, kullum Nuriyyar na cikin addu'o'inta akan ta samu kwanciyar hankalin da kowacce mata take samu a dakin aurenta, tare da mata addu'ar nutsar da hankalinta da auren Anas din. A bangaren samarin da suke kawoma Waheedah tayin soyayya ma babu abinda ya canza, dan bata fasa gaya musu cewar an mata miji ba, kamar yanda bata fasa bama AbdulKadir labarin yanda ranarta ta kasance a kullum ba. Duk da yanzun saqqonin nata na zuwa, suna kuma nuna alamar an karanta. Amman tun kafin bikin Nuriyya rabon da ta samu amsar shi. 2

Batasan ya akai ba, amman a shirunshi take karantar akwai abinda yake damun shi, tana kuma jin hakan har kasan zuciyarta, kuma koma menene yake damun shi din, tare suke cikin damuwar, dan itama nata hankalin ba'a kwance yake ba. Daina kirga kwanakin zuwan shi tayi, zasu fi mata sauri idan bata kirga ba, sosai ma tayi mamakin kanta da bata taba tambayarshi yaushe zaizo ba. Tana alaqanta rashin yin hakan da yanda jikinta yake bata ba lafiyar shi ba. Haka rayuwa taci gaba da tafiyar mata har bayan shekara daya, shekarar da tayi dai-dai da lokacin fitar AbdulKadir daga NDA. 1

Lokacin da har a fuskar Mami takan karanci damuwar da ta kasa furta mata akan rashin wani da za'a nuna ace yau yazo zance wajenta. Musamman da aka sa bikin Zahra, dan wannan karin yara uku Hajja zata aurar, Zahra, Mubarak da kuma Yazid da sai yanzun da alama surutun kowa ya ishe shi ya fito da matar aure, duk da sukan jima basu sakashi a idanuwansu ba, da alama yabar Kano din kenan kuma sai dai ziyara. Duk da gidan nasu Allah yai musu fahimta kan cewa shi aure lokaci yake dashi.

Duk yanda kaso ka kawar da yaro, idan lokacin shi baiyi ba dole zaka hakura, shisa sam Abba baya jira, wanda duk Allah ya fitowa da miji aurar dashi yakeyi, ko Nusaiba akwai wanda ya fito cikin yan uwa da nufin aurenta, takiya da cewar ita karatu take so tayi, tunda ko sakandire bata kammala ba, babu yanda basuyi akan a tsayar da magana ba, Abba ne yaki, cewar shi su dai jira in zasu iya, yarinyar ta kara mallakar hankalin da zata yarda da auren dan su, karya yanke hukunci da zai zamana kowa baiji dadinshi a gaba ba. Ita kanta Waheedah zuwa lokacin tana so ace ta fara kula wasu, tasha fadama kanta daga yau duk wanda yazo mata da tayin soyayya zata amsa shi, amman saita tsinci kanta da kasa yin hakan. 2

Ko wani ta tsaya dashi takanji kamar tana cin amanar AbdulKadir ne, tanajin rashin hankalin dake cikin hakan, tunda bai furta mata kalmar so ba, asalima bai san tana haukanta ba, amman haka take ji. Zuwa yanzun azumi ta fara da tsayuwar dare akan neman zabin Allah, sai take jin da duk rana kamar ana kara rura mata wutar son AbdulKadir dinne a zuciyarta. Yau ma a gajiye ta dawo daga makaranta, dan bata dawo ba sai yammaci liqis, har a kasusuwan jikinta take jin gajiya. 1

STORY CONTINUES BELOW


Da sallama ta shiga dakin tana zare takalmanta a kofa.

"Mami..."

Ta kira tana cilla jakar hannunta kan kujera, da hijabin ta nufi hanyar kitchen inda ta samu Mami tana tace zobo. Kanta ta dora a bayan Mami din tana fadin

"Mami kashina kaman zai fito waje..." 1

Dariya Mami tayi tana ture Waheedah din

"Dagani nikam... Kashin ne kaman zai fito waje?"

Kai Waheedah ta daga mata, cikinta take jin ya tattaru waje daya saboda yunwa.

"Nagaji sosai, gashi yunwa nakeji"

Robar sugar Mami ta dauko tana zubawa cikin bokitin zobon.

"Kije kici abinci..."

Dakuna fuska Waheedah tayi 3

"Mami baki dafa mana komai ba?"

Murmushi kawai Mami tayi, kamar Waheedah zatayi kuka ta baro kitchen din tana zira takalmanta ta fice daga gidan. Ta manta girkin Mama ne ranar da taci wani abu a makaranta, yunwar da takeji kuma ba zata barta ta tsaya koda indomie ta dafa ba. Zataje taga ko abinda Mama din ta dafa zai ciyu. Bangarenta ta wuce tana shiga da sallama, bata samu kowa a dakin ba, dan haka ta wuce kitchen din, kulolin da ake zuba abinci ta bude, tana cin karo da malmalolin tuwon shinkafa da suke kulle a fararen ledoji. Plate ta dauka, tasaka malmala daya a ciki, lumshe idanuwanta tayi tana addu'a a cikin zuciyarta miyar ta kasance ta taushe ce, ko ya aka watsal-tsala zata iya daurewa taci kodan yunwar da takeji.

Zuciyarta taji tayi wani irin tsalle da yasata bude idanuwanta tana dafa dayan hannunta jikin kantar kitchen din, batasan me tagane nashi ba, takun tafiyar shi, kusan shi, ba zatace ga asalin abinda taji ba, amman ba saita juya ba, tasan shi dinne ya shigo kitchen din, AbdulKadir ne, sosai take jin shi gab da ita, jikinta yai mutuwar da ta kasa juyawa ne kawai, tana kallon shi ya mika hannu ya dauki plate ta saman kanta, ta gefe ya zira hannu yana dauko tuwon guda daya, ya saka a plate din yana karo wani guda dayan. Tunda la'asar ya dawo gidan, yana daki a kwance ne saboda bayason surutu, bayason magana da kowa. 6

Ko passing out da akanyi shagali a gida, ayi su calender su menene ya fadama Yassar ya gayama su Hajja bayaso, suyi mishi addu'a kawai, kar wanda ya tara mishi mutane, in sunyi koda yazo zai juya. Sanin halin shi yasa basuyi komai din ba, duk da haka Hajja tasa ya daukar mata hoton shi guda daya, tayi babban agogo ta kafe a falonta. Tunda can bayason mutane, saboda suna bashi haushi, yanzun abinne ya karu, ko kadan bayason jin shi cikin mutane. Yana jiran list din sunaye ya fito zuwa inda za'a kaishi ya hada jakarshi yayi gaba. Tun da yazo yunwa ke cin shi, bai fadama kowa yana hanya ba, a cikin abokan shi wani zaizo Kaduna ya biyoshi.

Dan haka bai samu kowa a gidan ba, yaran gidan wasu na boko, wasu na islamiyya, Hajja kuma ta fita, har kitchen ya shiga bai samu wani abinda zaici ba, Nazir kadai yagani yace mishi girkin Mama ne, hakan yasa yunwar tashi bacewa na wani lokaci, kafin yanzun ta sake taso mishi tana fito dashi babu shiri. Hijabin jikinta ya sanar dashi ita dince, bayajin akwai mai saka dogayen hijabai har suna share hanya a gidan nasu banda ita. Ba zaice ga asalin abinda tai mishi take bashi haushi ba, duk da haushin kowa da komai yake ji. Amman nata yai yawa, yanajin inda ta fada mishi Nuriyya ta fara kula wasu da yayi wani abu akai kafin lokaci ya kure mishi. 8

Duk da tun daga ranar da aka daura mata aure, bai sake bari tunaninta ya dame shi ba, ya riga ya faru, babu abinda zai iya akai, amman ya tabashi ta fannin dashi kanshi bai taba tunani ba. Ganinta yanzun din yana saka wani abu matsewa a kirjin shi. Wajen tukunya yadan matsa yana budewa, wata irin miyar kuka tai mishi sallama, tunda yake bai taba ganin miyar kuka mai muninta ba, yana ganin ruwan daban, kukar daban, man da yake a sama kamar daga baya akai tunanin zubashi yana gefe shima. 3

STORY CONTINUES BELOW


"Mama!"

Ya kira yana saka Waheedah sake lumshe idanuwanta da yanda muryarshi ta sauka cikin kunnuwanta tana saka tsikar jikinta tashi. Sai lokacin ta samu karfin juyowa tana sauke idanuwanta akan shi, rigar sojoji ce a jikinshi mai dogon hannu, sai gajeran wando, ya kara mata wani irin girma naban mamaki, sai taganta yar kararrama a gaban shi. Wani yawu ta hadiye ko zuciyarta zata rage gudun da take a kirjinta

"Mamaa!!"

Ya sake kira a karo na biyu, dai-dai lokacin da Mama ta karaso kitchen din a rikice, dan ko bataji muryarshi ba tasan babu wanda zai mata wannan kiran saishi, bata dai tsammace shi a lokacin bane saboda tasan baya garin 1

"Wacce irin miya ce wannan?" 2

Ya bukata yana tsareta da idanuwa, Kallon shi Mama tayi girman shi na bata mamaki, kaf gidan batajin akwai mai tsayin shi. 1

"AbdulKadir... Saukar yaushe?"

Ta tambaya maimakon amsar tambayar dayai mata

"Wacce irin miya ce wannan?" 3

Ya sake maimaitawa yana yin kamar baiji maganar datai mishi ba, hadi da dorawa da

"Ya mutum zai saka wannan miyar a bakin shi? Meyasa za'ai mana tuwon shinkafa da wannan miyar? Me yasa kike mana girki kamar Abba baya bada kudin da za'ai mana me dadi?" 2

Numfashi Waheedah ta sauke ganin yanayin dake fuskar Mama yasata fadin

"Hamma..."

Sai lokacin ya juya yana sauke mata kananun idanuwan shi da suke cike da rikici, kai tadan girgiza mishi alamar yabari, kome yake shirin sake fada karya fada, yai shiru kawai. Wani irin tsaki yaja yana ajiye plate din ya fice daga kitchen din, itama Waheedah nata plate din ta ajiye tana rufa mishi baya, Mama tabisu da kallo kawai, dan AbdulKadir ya dade da daina bata mamaki.

"Hamma..."

Waheedah ta kira tana mayar da numfashi saboda gudu-gudun da tayi wajen binshi, juyowa yayi gabaki daya yana sata runtsa idanuwanta tukunna ta bude su

"Meye?"

Ya bukata yana tsareta da idanuwan shi da suke birkita mata lissafi, akwai kwarjini na musamman dashi kadaine yake mata

"Me zaka ci?" 1

Ta bukata, kai AbdulKadir ya girgiza mata, yana sake juyawa. Yanajin idanuwanta nabin shi harya sha kwana. Numfashi ta sauke tana kai hannu a kirjinta inda zuciyarta take doka mata, takai mintina biyu a wajen tukunna ta wuce tana komawa bangarensu, sam ta manta da wata yunwa da takeji, tana shiga ta wuce daki, tana samun Amatullah ta fito daga bandaki da alamar alwalar magriba tayi dan ana gab da kira, hijab ta cire itama tana shiga bandakin ta gabatar da alwala. 5

*

Sanda ya dawo daga sallar isha'i ya samu abinci a dakinshi an ajiye. Tunanin farko da yazo mishi shine Waheedah ce, zama yayi yana daukar plate din ya bude, dankaline da kwai, sai karamin flask din da yasan shayine a ciki, budewa yayi yana zubawa, kamshin shayin yasa shi sanin ba Waheedah bace ba, Hajja ce, ita kadai take saka Na'a'na'a a shayinta. Haka kawai a kasan zuciyarshi sai yaji yaso ace ya fito daga hannun Waheedah ne, daya girgiza mata kai bayana nufin bazaici komai bane ba, yana nufin baisan me zaici ba, amman bata kawo mishi komai ba. 3

A cup ya zuba shayin ya soma hadawa da soyayyen dankalin da kwai yana ci, lokacin yaji an turo dakin da sallamar da kafin ya amsa Yassar ya dora da

"Ba zaka iya cemun zaka zo ba?"

Kafadu yadan daga ma Yassar din bayan ya amsa sallamar da yayi, gefen shi Yassar ya zauna yana daukar cokalin dake cikin plate din ya cako dankalin yasa a bakin shi yana soma taunawa tukunna ya ajiye cokalin

STORY CONTINUES BELOW


"Kafadu zaka dagamun?"

A kasalance AbdulKadir yace

"Me kake so inyi to? Na riga nazo, komawa zanyi in kiraka ince maka zan taho?" 3

Kai Yassar ya jinjina, sosai rashin kunyar AbdulKadir ta karu tun shekarar data wuce, wani abu ya same shi da baisan menene ba, bakomai yake fada mishi ba, amman baya rufe shi har haka, ko kiranshi yayi a waya da cewar zaije Kaduna ya dubashi sai yace mishi babu lokacin da zai ganshi, tun yana zuciya yaqi zuwa harya kula AbdulKadir din na boye mishi ne, saiya dinga share shi baya kiranshi saiya shiga Kaduna tukunna. To har yanzun kuma boye mishi yake, wannan ba kanin shi bane ba.

Wayarshi da take a hannun shi Yassar ya danna dan yaga ko karfe nawa, hakan yasa AbdulKadir cewa

"Nasan yarinyar nan..."

Yana dakuna fuska, danna wayar Yassar yayi haskenta ya dauke, da sauri AbdulKadir din yakai hannu yana fisge wayar Yassar din ya sake dannawa

"Kaban wayata AbdulKadir..."

Sosai yake kallon hoton fuskar wayar Yassar din

"Hawwa ce ko?"

Ya tambaya yana mika ma Yassar din wayar daya karba yana fadin

"Ban sani ba"

Kai AbdulKadir ya jinjina yana ajiye plate din dankalin ya dauki kofin shayin shi daya rike da hannuwa biyu yana kurba

"Tun yaushe?"

Shiru Yassar yayi ya kyaleshi

"Hamma magana fa nake maka... Tun yaushe? Zaka fara dating baka fadamun ba ashe?" 1

Kallon shi Yassar din yayi

"Kamar yanda wani abu ya sameka baka fadamun ba kake nufi?" 1

Numfashi AbdulKadir ya sauke dan bashi da abinda zai fada, wani abu ya same shi da gaske, amman kuma ya riga ya wuce, fadar bashida amfani tunda ba wani abune zai canza ba idan yayi hakan.

"Me yasa ba za'a hada dana su Hamma Yazid ba?"

AbdulKadir ya bukata yana son sake akalar zancen. Yassar yagane hakan, bazai takura shi sai yasan meya same shi ba

"Bamu dade ba, ba mufi wata biyu ba, kar wani abu ya canza a gaba..."

Kallon shi AbdulKadir yayi

"In har kasata a fuskar wayarka kana jinta a ranka Hamma, bana tunanin akwai abinda zai canza..."

Murmushi Yassar yayi, wata biyu da fadama Hawwa yana sonta, amman ya dan jima yana yin haka daga nesa-nesa daman, duk sanda zasu zo gidan, kuma suna dan chatting kadan a WhatsApp. Bayaso abinda ya faru da Yazid akan Waheedah ya faru dashi, shisa bai kwauron baki ba, kuma da dukkan alamu itama ta jima tana jinshi din, duk da haka bayason yin gaggawa, duk da zaifi so suyi shagalin bikin nasu tare da Yasir, amman sam Yasir yace mishi shi bai shirya yin aure dan lokacin ba, da alama zai rigashi.

"Kayi magana kawai ayi bikin nan duk mu huta"

AbdulKadir ya fadi cikin sigar tsokana. Yar dariya Yassar yayi

"Lallai yaron nan, to kaima kayi auren mana"

Girarshi duka biyun AbdulKadir ya daga ma Yassar

"Da wa?"

Ya tambaya yana kurbar shayin daya kware shi dajin amsar Yassar din

"Waheedah..."

Tari yake sosai dan shayin yabi mishi ta hanyar da bai kamata ba, sosai yake kara kurbar shayin ko zai samu sauki, muryarshi a dishe ta fito daga kasan makoshin shi

STORY CONTINUES BELOW


"Wanne irin wasa ne wannan?"

Ya bukata yana sa Yassar din hararshi

"Karka rainamun hankali AbdulKadir, shekara nawa kana yawo da hotonta a wallet? Dan banyi magana ba baya nufin ban kula ba, itama kuma ina kallonta, bata kula kowa, ban tana ganin ta fita zance da wani ba..." 1

Kallon Yassar yake da dukkan alamu Hausa yake mishi, amman da wani yare daban yakejin maganganun Yassar din na dira kunnuwanshi saboda yanda ya kasa fahimtarsu, yanayin fuskar AbdulKadir din Yassar yake kallo, mamaki na bayyana akan tashi fuskar

"Tsaya... Me kake son ce mun?" 1

Ya tambaya yana kasa gasgata abinda yake gani a fuskar AbdulKadir din, kai Yassar yake girgizawa

"AbdulKadir..."

Ya kira yana cigaba da girgiza kai, AbdulKadir din bai magana ba har lokacin, kallon Yassar din kawai yake kamar qaho ya fito mishi a tsakiyar kai

"AbdulKadir..."

Yassar ya sake kira a karo na babu adadi, yana jinjina abinda yake gani a fuskar kanin nashi, har ranshi, duk tsayin shekarun nan ya dauka soyayya suke da Waheedah din, yana kuma da tabbacin bashi kadai bane yake zaton hakan. Wani zafi yaji kirjinshi nayi, ya hana Yazid furta mata yana sonta saboda a tunanin shi AbdulKadir din nasonta, yana kuma da tabbacin idan shi baya sonta ita tana son shi, dan yanda take tambayarshi akan AbdulKadir din kawai ya tabbatar mishi da haka daga nata bangaren. 2

"Me yasa?"

Yassar ya tambaya, sai lokacin AbdulKadir yace

"Me yasa me?"

Kai Yassar ya jinjina

"Tana sonka AbdulKadir..."

Yassar yai maganar can kasan makoshin shi, tausayin yarinyar na cika zuciyarshi, plate din dankalin shi AbdulKadir ya dauka yana diba ya cika bakin shi dashi taf yana cigaba da taunawa, maganar Yassar din na mishi yawo a duk ilahirin jikin shi 4

'Tana sonka AbdulKadir'

Ko a mafarki mai nisa bai taba hango soyayya da Waheedah ba, ko kadan, soyayya fa, da Waheedah, tana da muhimmancin dashi kanshi baisan iyakarshi ba a rayuwarshi, amman soyayya da ita, shine karshen abinda yake hangowa. Sai dai soyayya da kowama a yanzun ba abu bane da yake tunanin zai faru, bayajin yana da wannan lokacin. 1

"AbdulKadir..."

Yassar ya kira ganin yanda yake cin abincin

"Karka kware..."

Bai kulashi ba, dankalin kawai yake zubawa a bakin shi yana taunawa. Hakan yasa Yassar mikewa ya fice daga dakin da tunani kala-kala a ranshi. Tari AbdulKadir ya somayi yana fita, babu shiri ya dauki shayi yana kora dankalin bakin shi dashi, hadiyewa yayi yana sauke numfashi. Kafafuwan shi ya ja yana dorasu kan gadon hadi da kwanciya yaja bargo ya rufe jikin shi. Pillow din daya dora kan shi yaji ya soma isar shi, dan ba haka yake kwanciya da pillow ba, dagawa yayi yana dora pillow din akan hannun shi tukunna ya dora kan shi a sama, yadanji dai-daito a kwanciyar.

Yassar yasa kashi abinda bayason yi, idan akwai abu na biyu da bayason bayan raini, tunani ne, ko kadan bayason ya zauna yana tunani, taya Yassar zaice Waheedah na son shi, ita Waheedah din bata da bakin da zata fada mishi kome yake faruwa, kanshi ya bala'in daurewa cikin yanayin da bai taba tsintar kanshi a ciki ba, komai yake ji ya cakude mishi haka kawai. Tun ran daurin auren Nuriyya rabon dayai tunanin wani aure, yanzun kuwa gabaki daya tunanin ne a ranshi.

Ta ina zai fara? Wacce yarinya zai fara tunkara? Yaushe ma zai ganta? Duk da yasan indai yana da rai da lafiya aure abune da ya zame mishi dole, ko dan gujin fadawa halaka, tare da Waheedah yana da tabbacin ba zata taba raina shi ba. Asalima raini na daya daga cikin abinda yasan bazai taba shiga tsakanin su ba. Kuma a yanda yakeji bazai iya kallon idanuwan kowacce yarinya da sunan soyayya ba a yanzun, bashida ma da wannan lokacin, da anyi posting dinshi zuwa inda zai fara aiki kuma zai kara samun karancin lokacin duk wannan abubuwan.

STORY CONTINUES BELOW


Tashi yayi zaune, karo na farko a tsayin lokaci da yaji zuciyarshi na dokawa da abinda yake shirinyi. Wayarshi ya dauko yana kunna data din, WhatsApp dinshi ya bude, sunan Waheedah ne farko da saqonninta da suketa shigowa, sosai bugun zuciyarshi yake karuwa, bude sakkonin yayi:

'Me kaci?'

'Karka kwanta da yunwa Hamma'

'In dafa maka indomie? Ko zaka sha Tea?'

'Shine baka fadamun zaka zo ba ko?'

Dubawa yayi yaga tana online, rubutu ma takeyi, jikinshi yakeji har kyarma yake mishi, a hankali ya soma rubutu yana tura mata:

'Waheedah...'

Rubutun da take yaga ta tsayar, hakan yasa shi cigaba:

'Waheedah...'

Runtsa idanuwan shi yayi yana sake budesu kan screen din wayar

'Hamma'

Ta amsa, ya karanta sunan nashi da muryarta, bayason yin abinda zai dana sani, sanin ba zata taba raina shi bane abinda yabashi kwarin gwiwar rubuta

'Kina so na?' 5

Karanta tambayar tashi yayi, ganin bata fara ko typing ba, ba lallai ma tagane kan tambayar tashi ba

'Ba so na yan uwa ba Waheedah... So na aure. Kina so na?'

Tana online har lokacin, amman bata ko fara rubutu ba, kuma yaga ta karanta, zuciyarshi yakeji har cikin makoshin shi saboda dokawar da take mishi.

'Ki amsani, zan kirga daya zuwa goma. Karki amsa sai kina da tabbaci, idan bakida shi karki amsa, nida ke zamuyi kamar ban tambaya ba, maganar ba zata sake hadamu ba har abada' 2

Ya fadi yanajin yanda maganganun nashi suka zauna mishi, ita dashi suna da daqiqan da zasu dauke shi ya kirga daya zuwa goma, amman zai karya idan yace baya tsoron shirunta. 1

'Daya...'

'Biyu...'

'Uku..."

Rubutu yaga ta soma, hakan yasa shi barin kirgar da yake, can kuma yaga ta daina

'Hudu...'

'Biyar...'

'Shidda...'

Rubutun ta sake cigaba dashi, tana sake dakatawa bayan wani lokaci

"Ki kasheni kawai Waheedah" 6

AbdulKadir ya furta a fili, yana jin alamar zufa a goshin shi da bayan wuyan shi 1

'Bakwai...'

Zuwa lokacin hannuwan shi kansu zufa suke fitarwa, shi baima taba tunanin soyayya da ita ba, yanzun hakan baisan rashin hankalin daya kaishi yin abinda yayi ba, baisani ba, gashi yazo yanajin bugun zuciyar da bai taba tunanin zai iyaji bama akan jiran amsarta, Yassar bai tabbatar ba, hasashe yakeyi, bai tabbatar da Waheedah nason shi ba, kilama tana da wanda take so, yai tunanin yanajin wani tuquqi na tokare mishi makoshi. 1

'Takwas...'

Ya tura, yana jin yanda zaibar garin Kano da sassafe, yanajin yanda yaima kanshi karya da tunanin amsarta ko rashin amsarta bazai canza komai ba, da gaske baya tunanin zai iya hada idanuwa da ita idan bata amsashi ba. Duk da bayajin yana dana sanin tambayarta din, Yassar yasa shi son sanin ko tana son shi ko bata son shi.

'Tara...'

Ya tura yana gyara zaman shi hadi da fitar da wani irin numfashi mai nauyin gaske, idanuwan shi ya runtsa a hankali ya bude su kan screen din wayar.

STORY CONTINUES BELOW


'Ina son ka, ina son ka da aure Hamma AbdulKadir' 17

Sake karantawa yayi yana sauke numfashin da baisan yana rike dashi ba. Wayar ya ajiye gefe yana dafe kanshi da hannuwanshi duka biyun, wani irin numfashi yake saukewa mai nauyin gaske, kafin ya mike yana zira takalman Yassar dake bakin kofa ya fice daga dakin yanayin hanyar wajen bangaren nasu. Takawa yake zuwa bangaren Abba yanajin shi kamar wanda yake tafiya a gajimare, jinshi yake kamar yana yawo a wata duniya da batashi ba, kamar yana gefe yana kallon wani mafarki dashi a ciki.

*

Dakin Abba ya shiga da sallama, ya same shi a tsakiyar falon a zaune, Mama nakan kujera

"AbdulKadir..."

Abba ya fadi da fara'a yanajin dadin ganin dan nashi.

"Abba..."

AbdulKadir yace yana karasawa ya zauna gefen shi.

"Abba zanyi magana dakai" 1

Murmushi Abba yayi

"Soja manyan kasa, ina saurarenka ai" 1

Daga kai AbdulKadir yayi yana kallon Mama dake zaune, yana saka Abba kara fadada murmushin shi, mikewa Mama tayi, batason sake shiga hancin AbdulKadir din kafin ya tona mata asiri wajen Abba. 3

"Bari in baku waje kuyi sirrinku" 2

Cewar Mama tana dora murmushi kan fuskarta, lokacin daga fice daga dakin. Kallon Abba yakeyi a nutse yace

"Aure zanyi Abba... Kafin in koma nake so a daura" 12

Da mamaki bayyane a fuskar Abba yake kallon AbdulKadir din, kafin ya numfasa da fadin

"Aure AbdulKadir?"

Kai AbdulKadir ya daga mishi, yana jin maganganun na fitowa daga zuciyarshi

"Eh Abba..."

Wannan karin Abba ne ya jinjina kai, maganar na dirar mishi da wani yanayi, yana kuma son karbarta da budaddiyar zuciya, idan har AbdulKadir din zai bude baki da maganar aure to yana kokarin ganin ya gujema fadawa halaka ne, kuma yanzun yana da sana'ar da Abban yake da tabbacin zata riqe mishi mata, sai dai shi bayason yin abu cikin gaggawa, musamman magana ta aure.

"Yaushe zaka koma?"

Jim AbdulKadir yayi kafin ya amsa

"Sati biyu in na dade"

Numfashi Abba ya sake saukewa

"Maganar aure a sati biyu AbdulKadir, abune da bazance bazai yiwu ba, amman gaggawa ba abu bane mai kyau. Aure kuma yana bukatar shiri. Nasan kana da aikin dazai rike maka mata, amman wajen zama fa? Lefe da sauran hidindimun biki" 2

Dakuna fuska AbdulKadir yayi shi baiyi wannan tunanin ba kwata-kwata. Yama manta ana wani abu waishi lefe a maganar aure, ya kuma manta ana neman wajen zama. Magana Abba yaci gaba dayi

"Ana iya maganar auren, idan kana ganin zaka iya shiryawa nan da watanni shidda sai a hada dana su Yazid duk ayi..."

Kai AbdulKadir ya jinjina, hakan ya mishi, zai tara kudin da zasu ishe shi yin lefe, wajen zama zasu iya farawa da barikin sojoji tunda yasan za'a bashi muhalli, amman ko kadan ba dadewa zai ba, kafin ya tara kudin dazai mallaki nashi ne zasu zauna. Baya son yaranshi su tashi cikin bariki, badan wani dalili ba, ra'ayin shine kawai hakan. Dariya maidan sauti yaji ta kubce mishi, yadan girgiza kai. Da gaske ya samu matsala, shine da maganar aure harda tunanin rayuwar yaranshi da yanda yake son ta kasance. 1

"Hakan yayi Abba... Zan tara kudin sai in bama Hajja ta siyo abinda ya kamata..."

Murmushi Abba yayi, AbdulKadir din ya kalle shi yana fadin

"Waheedah ce Abba... Waheedah zan aura" 1

Kallon shi Abba yake da mamaki shimfide akan fuskar shi

"Waheedah? Waheedah ta nan gidan?"

Ya karasa tambayar da alamar rashin yarda a muryarshi da fuskarshi gabaki daya. Akance sai halayya tazo daya ake zama guri dayama har a qulla alaqa, Abba na ganin karyar zancen a abinda AbdulKadir yake fada mishi, dan ta kowacce fuska AbdulKadir bai dace da Waheedah ba, halayyarsu da komai nasu ya banbanta, bai kuma hango ta yanda akai suka fara soyayyar ba.

"AbdulKadir ka tabbata? Ita Waheedah din ita tace tana sonka?"

Kai AbdulKadir ya dagama Abba, inda batace tana son shi ba, bazai taba zuwa ya furta ma Abba zancen aurenta ba. 1

"Allah mai iko... Oh Allah" 5

Abba yake fadi har lokacin da AbdulKadir din ya mike jinjina maganar yake, dan kai kawai ya iya daga ma AbdulKadir batare da yaji kome yace ba, harya fice daga dakin. Sosai yake jinjina al'amarin auren Waheedah da AbdulKadir, shikam zai kira Waheedah ya tabbatar daga wajenta kafin ya yanke kowanne hukunci, dan jikin shi na mishi wani iri akan auren, sanyin Waheedah yai yawa, zafin AbdulKadir ko su da suka haifeshi addu'a suke binshi da ita, yana kaunar su biyun duka, yana jin Waheedah har kasan zuciyarshi, zai komai dan ganin ba'a cutar da marainiya da sa hannun shi ba...!

Post a Comment for "ABDULKADIR CHAPTER 5"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...