Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

TANTIRIN NAMIJI CHAPTER 7 KARSHE

TANTIRIN NAMIJI CHAPTER 7 KARSHE

- - Post a Comment
TANTIRIN NAMIJICHAPTER 7 KARSHE

Awansa biyu cir akan ta sannan ya fadi ragwaf kamar matacce yana nishi, sai sannan ya lura ashe suma tai cikin firgici ya dagota yaraf ta koma cikin tashin hankali ya fice.


Parlour ya nufa yama rasa ina zai sa kansa saboda tsananin tashin hankali, da sauri ya nufi parlour ya bude fridge ruwa ya dakko mai sanyi sosai ya tuttula mata wata ajiyar zuciya ta saki tana kukan azaba.


"Wayyo Allah na na shi ga uku na" idonta a rufe tama kasa budewa saboda azaba ki ta ke kamar bayanta ba a jikin ta ya ke ba, haka ta din ga rusar kuka lallabata ya ke amma kamar kara tunzura ta ya ke.


Hankalinsa ya tashi ga lokacin dawowar Alhaji Ghali ya kusa dabara ce ta fado masa ya daka mata tsawa "ke! dallah ki rufan baki ban miki kashedi ba, wallahi ko kiyi shiru ko na maimaita abun da nayi bana san iskancin banza kin jini ko?"


Gaba daya ta gigice ta toshe bakin ta saboda tsoro gaba daya bayan ta ciwo ya ke mata dan bazata iya motsawa ba sam saboda azaba, yaja tsaki "mtsww! raguwar banza raguwar wofi, saura naji nishin ki ko kuka kuma wallahi kika fito ni da ke nai."


Ya fice ya barta cikin tashin hankali kuka tasa mai cin zuciya, "ya Allah na tuba astagfurullah Allah ka yafe mun, Allah ni baiwarka ce makaskanciya Allah karka bawa wannan bawa naka damar cigaba da cutar dani, Allah na rokeka ka kawomun karshen wannan lamari, Allah ka shiryi mijina Allah ka dawo da shi hanya madaidaiciya, Allah na tuba astagfurullah!

Allah na rokeka ka saukaka kamun ka kawon silar da zan bar wannan gidan, saboda ba alkhairi sam a cikin sa Allah ka juyo da hankalin mahaifina kai na, Allah na rokeka ka yafemun ya Allah."


Haka ta din ga kuka tana addu'o'i tana rokon Allah amma sam ta kasa zama kuka ta ke ta mike kamar yar kaciya dan din kin da akai mata ma ga farke, ta nufi bandaki ta tara ruwan zafi ta shi ga ciki wani ihu ta saka ta fito haka ta daure ta kara ruwa ta dan gasa tai wanka ta dauro alwala.


A gicciye ta ke zama dan ta kasa zama sam haka tai sallar azahar ta kwanta tana lazimi cikin tana ta zil zil, ta shafa shi a hankali ta fashe da kuka, tabbas ciki nai da ita dan gashi yana ta zillo taci gaba da kukanta da addu'a.


Alhaji Ghali yau yai alkawarin kebewa da matarsa ko ta halin yaya saboda bacin ran da Baby Chakwai ya guma masa, hakan yasa yayo mata siyayya mai dumbin yawa ya kawo mata yayo mata shopping lodi guda ciye ciye da shaye-shaye sai magriba ya dawo gidan.


Hakan yasa bai fito da kayan ba ya shi ga Baby Chakwai yai masa banza har lokacin baccin su yai yai kwanciyarsa, Alhaji Ghali ya samu ya busa masa maganin nan bacci mai nauyi ya dauke shi sosai ya samu ya fice ya bude mota ya debo kayayyakin daya siyo mata ya nufi dakin cikin sa'a ya ji kofar a bude bai yi tunani ba.


Story continues below

Tana kwance a in da tai sallah anan bacci ya dauketa fitilar dakin ya kunna a kwance ya ganta a takure cikin hijjabi hannunta da carbi fuskar nan tayi fiyau, duk tayi baki ta fige ta lalace wani tausayinta nai ya kwaranyo a kirjinsa da tsananin soyayarta wani hawaye yaji ya taho masa.


A hankali ya karasa kusa da ita ya tabata ta farka a firgice tasa kuka, "dan Allah kayi hakuri kabarni na tuba" mamaki wa ta ke magana akai ko dai Baby Chakwai na gana mata azaba nai? Kawai ya basar dan ba mai amsa masa "ki nutsu Nauwara nine akwai mai cutar da ke nai?" sai sannan taji muryarsa sakin baki tai tana kallonsa yaushe rabo murza idon ta tai tabbas shi ne.


"Ni ne Nauwara ki kwantar da hankalinki insha Allah daga yau da ke zan din ga kwana, bazan kara guje miki ba na miki alkawari insha Allah!" ya din ga lallabata yana bata baki ta danji sanyi kadan addu'ar ta ta karbu kenan.


Yayi yayi ta zauna ta kasa dan bazata iya ba ganin haka ya rabu da ita yaci gaba da lallabata dan ma karta ga saboda ya kusanceta ya zo yasa ya rabu da ita, a nan ya dakko mata kayan bacci tasa anan ya lura da cikin jikinta cikin tashin hankali ya dumfarota "Nauwara wa yai miki ciki?"


Murmushi tai wako zai mun ciki ban da kai, cikin ka nai kai kai mun tun ranar daka kusanceni" gaba daya hankalinsa ya tashi "ba na son sa bana san ciki wa ya sa ki ciki ma tukun? an gaya miki neman yaya nake, wannan cikin shi nai zai kara gusar mun da dukkan farin cikina a duniya na tabbata."


Cikin kuka ta ce "haba Alhaji kai fa musulmi nai kuma hakika yaya rahama nai ga iyayensu, ka sani ko shi nai kadai kwan mu a duniya?" jikinsa yai sanyi ya rungumeta 'kin ga abun da banaso kenan matata ta fari garin haihuwa ta rasu, shi ya sa sam bana bukatarta musamman ga ke da na ke so a yanzu."


Nan ta din ga lallabashi tana kwantar masa da hankali haka yai hakuri ba dan ransa naso ba, suka kwanta sai karfe goma ya koma ya tarar Baby Chakwai nata bacci kamar gawa, murmushi yai ya cigaba da harkarsa sai da yaje yai mata sallama sannan ya tashe shi nan kuma ya lallabashi suka dai shirya ya fice.


Bayan wata uku cikinta ya fito sosai abun da ya daga hankalin Baby Chakwai kenan yana tambayarta wa yai mata ciki, sai tai masa karya ta ce wani nai ya ce kashe ta aka aiko shi yayi shi nai yai mata fyade sarai ya gane killer ta ke nufi yaronsa da yai batan dabo tun da ya aikoshi ya kasheta ashe fyade yai mata shi ne ya gudu.

Tabbas biri yai kama da mutum amma ya daga masa hankali ya ke ta yawon nemansa ya baza jama'a su nemoshi amma har yanzu shiru, murmushi yai har yaji sanyi a ransa dan yana mugun kishi akanta zai iya kashe ko waye, yayi abun da zai ya gama duk da ya lura duburarta ta zazzago amma haka ya ke zuwar mata tana ihu bai kuma fasa ba, dan yanzu har ta fara sabawa da azabar da ta ke sha.


Alhaji Ghali ya dawo ya manta sam da Baby Chakwai ashe yana kallon dawowarsa, shiru shiru yaji bai zo wajen sa ba ya fito a hankali ya din ga jiyo maganarsa a dakin ta, da sauri ya banka kofar dakin yana nishi kamar zaki a gigice suka mike......
*******************

Kallon kallo su kai shi da ita ba kowa bace face kawar ta Humaira, ta kalleshi ya kalleta ta gaishe shi ya amsa a cukule, "tana ciki nai?" "shi ga ki duba" haka kawai ya ce yaja motarsa ya bar gidan zuciyarsa na tafasa.


Sallama ta din ga dokawa shiru ba ita ba alamunta abun da ya bata mamaki ke nan ta shi ga dakin nata a kwance ta sameta ka shirban, HQ a wangale ga uban yaji a ciki wani ihu ta saka na tashin hankali tasa kuka mai tsuma rai.


Innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un! wannan wane rashin imani nai haka? ko mai ki kaiwa mutum bai kamata yai miki wannan azabar ba." Tana kuka ta din ga share mata yajin da sauri ta nufi kitchen ta dora ruwan zafi yai dumi ta juye a baf na toilet, duk da tafi karfinta haka ta din ga janta tasa ta a ciki tana kuka.


Wani ihun azaba ta saki saboda yadda duwaiwakanta suka dau zafi da radadi kuka ta ke kamar zata mutu saboda azaba, yaji a HQ ai masifa nai gaba daya ta gama fita hayyacinta, da ke Doctor ce akwai magunguna nan da nan Humaira ta bude first aid box ta bata magunguna pain relief dana bacci tasha tai mata allura.


Kuka Doctor saudat ta ke dan tama rasa mai za tai, "Tabbas nai wa rayuwata ganganci dana auri Lawan Humaira_ tabbas san zuciya bacinta tabbas komai ya sameni ni jawa kai na, hakkin baban su Amir ke bibiyata yadda naci amanarsa.


Da aurena da komai nake bin wani wanda ya zame mun karfen kafa a rayuwata, sandinsa na rasa aurena yanzu kuma a sanadinsa na ke shirin kara rasa auren nawa a karo na biyu, bayan wahala daya bani mai tarin yawa yai mun barazana da saki wanda bana fata a yanzu.


Tabbas Lawan ya cika cikakken dan iska wanda baya kunya bare shakkar kowa, ga shi yanzu yazo ya kamani da shi shi ma yana barazana ga rayuwarsa, kuka ta ke mai tsuma zuciya da rai Allah ka gafartamun Allah na tuba tana wannan sambatun bacci ya dauke ta.


Lawan na fita bai zame ko ina ba sai hotel nan yai kwanciyarsa yana hutawa, sai dare sannan ya tashi ya shirya saboda yadda aka dame shi da waya, city star suka kama anan a kai dinner din, matane zafaffu hadaddu manyan mata masu ido masu ji da naira, kowacce ta yaba da Lawan saboda ba karya ya hadu dan fari nai tas.


Laila na kwance wani abokin aikin su ya kirata "Hajiya Laila to meye duniya ko duk kishin nai dan za'ai miki kishiya ki kasa gaya mana sai a gari mukaji" abun taji bambarakwai ta sheke da dariya "haba dai yallabai wane irin kishiya kuma? ai dama ina da ita."


"Haba Laila wallahi da gaske yanzu haka dinner ma zan tafi" wata zabura tai "dan Allah da gaske?" "wallahi da gaske na ke ba da wasa ba" "dan Allah biyo mu tafi" mikewa tai jiki na rawa ta zura abaya ta fito sai gashi ya dauke ta suka wuce wajen dinner din.


Bai gama parking ba ta bude ta fice yana kiranta amma ina tayi gaba hall yayi hall ana cashewa ta shi ga, can ta hangosu tsakiyar jama'a ana ta barin naira a hankali ta taka ta din ga ratsa mutane ta isa har gabansa hannu tasa ta wanka masa mari


Wanda gaba daya attention din mutane ya dawo kanta Hajiya Santalous tayo kanta a haukace, amma ya daga mata hannu ta fashe da kuka "lallai kai cikakken dan iska ne lawan.


Wato ni kaci moriyar mangwaro ka yada kwallo ko? yai mata banza yana kallonta dan yama rasa wane kalar hukunci zai mata cin mutinci da bakaken maganganu ta din ga yi masa wanda gaba daya bikin ya tsaya cak, "ke kuma wallahi yadda ya ke dukana agaban kowa nida matarsa ya ke wulakanta mu, kema zaki biyo sahu dan bala'i da masifa zaki tarar a gidan sa mara yankewa."


Cikin fushi tai kansa ganin yaki kulata ta damki wuyan rigarsa sai da ta kai kasa, cikin tsananin fusata ya shaketa ya fara duka nan da nan maza suka shi ga tsakani aka kwaceta, ihu ta ke tana kuka kamar mahaukaciya tana zaginsa yana zaginta.


"Wallahi Laila sai na ci ubanki ni nai ajalinki idan baki wasa ba, banza jahila baki da baki sai a kai na haukanki ke ta shi, wallahi darajar cikin jikin ki na kyaleki da sai nai miki dukan mutuwa" nan aka samu mata suka fitar da ita suna bata hakuri amma kowa mamaki ya ke yadda suke zagin junansu suna dure duren ashar har da fasa kwalba.


Hajiya Santalous jikin ta duk yai sanyi ba yadda bai ba ta bishi su wuce hotel amma taki, haka bikin ya watse kowa na fadar albarkacin bakinsa wayanda suka san halin karnancin su suka din ga bada labari, kowa mamaki ya ke wai matarsa ce wannan cab di jan akwai kallo a gidansu cewar wasu.


Hajiya Santalous ko tunani ta tafi tabbas bazata iya auren duka ba, ga dukkan alamu halinsa nai dan gashi sun nuna a filin jama'a, mijin da ta ke takama dashi shi ne mai wannan aikin tabbas akwai matsala sosai, Hajiya Lubna ce ta tabota figigit ta juyo.Daddy ya ce "subhahanallah zaka je ka kashe kan ka a baza a wofi akan abun da ka san gaibu nai ba samu zakai ba, idan ban da baka da hankali tayaya kana auren ya zaka auri kanwa shashasha kawai."


Momy ce ta shigo da sauri ta tallafe shi ta dinga masa fifita har ya samu sa'ida sai da ya lafa yana haki, ya kalli Daddy ya fashe da kuka "tabbas Daddy baka kaunata baka kaunar ganin farin cikina a duniya.

Mikewa yai ya fice daga dakin bai ce komai ba dan gaba daya abun ya gama fice masa arai, mugun tausayin yaransa yakeji a yanzu kawai daurewa yake dan ya nuna masa kuskurensa da abun da ya aikata saboda ya hankalta a gaba.


Hankalinta ya tashi ganin Daddy yai masa banza yama fice, cigaba da rarrashinsa tai tana kwantar masa da hankali a haka bacci ya fara daukarsa ta kamashi ta kai shi dakinsa.


Watan ta biyar a kwance a asibiti duk wani mai imani sai yaiwa Nafeesat kuka ta rame ta jeme sai uban ciki, baci ba sha sai ruwa da ake sa mata masu magunguna alhamdulillah jikin nata yai sauki sosai zuciyarta ce ta kumbura sosai.


Amma ta dan sabe a yau aka mai da ita ainihin dakin da aka kwantar da ita dan bazasu sallameta ba sai lokacinta yayi Edd din ta ya cika sannan zasi mata operations su ciro jaririn saboda bazata iya haihuwa ba a yadda ta ke.


Cikin watan sa bakwai cif a yanzu Maryam ko cikin ta ya kai wata biyar dan tana gidan kanwar Umma saboda mutane sun fara zargin wani abu akanta jikin nata dai alhamdulillah yau tana magana sosai ba laifi.


Bayan ya farka daga baccin ya mike ya dakko takarda da biro ya rubuta mata saki daidai har guda uku saboda sai ya sake ta tabbas zai samu damar auren kanwarta da ta kasance rayuwarsa a halin yanzu, dan wanda yai tunanin rabashi da ita tabbas ya raba shi da duniya nai.


Ya ninke ta ya fito ga bawa driver "ungo ka kai asibitin da matata Nafeesat ta ke ka ce a bata wannan in jini" shi kuma bai kawo komai ba ya hau mota ya tafi yana zuwa su kai kicibus da Abba ya rarrafo ya taho yau saboda yanaso ya duba jikin Nafeesat duk da shi ma sai a hankali.


Suka gaisa ya gaya masa aiken da Arfan yai masa da takkadar gabansa sai da ya yanke ya fadi saboda tashin hankalin ganin takadda, to mai ta kunsa amma ya dake ya amsa yace "bari na shiga na dubata duk da dazu muka dawo da Hajiya jikin nata da sauki ba kamar da ba."


Suka shi ga tare ya dubata tana murmushi ya fito ransa duk a jagule saboda yadda duk ta kare abun tausayi, ba abun da kake gani sai kashi Abba ya zauna suka gaishe shi sannan ya mikawa Mama takardar "karanta mana muji."Ta karba ta fara warwarewa ta soma karantawa kamar haka._Ni Arfan hakika ina tsananin san kanwarki Maryam wadda ta sanadinta na bar duk wasu halayena saboda tsananin san da nake mata wanda rasata daidai ya ke da rasa tawa rayuwar gaba daya a doron duniya, kuma tabbas Nafeesat idan ina auran ki bazan samu damar mallakar muradin raina ba duk da Maryam ta kasance masifa ga rayuwata, ina santa mahaifina na Santa amma tabbas ni zan mallaketa saboda haka na yanke..._


Story continues below

Kasa karasawa tai ta fashe da kuka wanda gaba dayansu jikinsu ya fara rawa, Nafeesat ko jikin ta nai ya fara rawa dan ko bata karasa ba tasan mai takardar ta kunsa cikin kidima ta ce .


"Mama ki sanar dani saki nawa yai mun dan Allah Mama ki sanar dani? innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un! tabbas na san Mama Arfan ya rabu dani bai tsaya a abun da yai mun ba nida kanwata daku iyayena sai ya sakeni.


Ya barni na mutu cikin sittira mana, ya bar ni na mutu da hijabin aure mana, amma ya gaza yimun wannan alafarmar" sai kuma ta shide gaba daya ta fita daga hayyacinta abun da ya daga hankalinsu ke nan.


Cikin kidima aka kirawo likita nan da nan aka shi ga da ita emergency dan dubata, ina haihuwa tazo gadan gadan nan da nan aka ce sai dai ai mata cs bazata iya haihuwa da kan ta ba gaba daya kuka suke dukansu.


Abba kuka yake kamar ransa zai fita yayi nadama mara amfani ta yadda ya fifita kudi akan yaransa, ga shi yanzu abun da san kudin nasa ya haifar masa shi ya sa hannu aka shi ga da ita, anyi nasarar ciro mata diyarta mace mai kama da ita sak amma karama ce dole sai an sata a kwalba.


Amma kuma Allah yai ikonsa akan mahaifiyar inda kafin ma agama ta cika, tashin hankali wanda ba'a sa masa rana wannan ahali suka tsinci kansu a ciki.


Inda Abba ya yanke jiki ya fadi Mama tayi tawakalli hawaye kawai ta ke ita ta koma tana rarrashin Umma, ta ke ta kira Daddy ta sanar masa da abun da ke faruwa a gigice ya sanarwa Momy suka taho asibitin kota kan Arfan basu bi ba.


Suna shi ga asibitin suka kara rikicewa ganin ta akwance sambal kamar kai mata magana ta amsa, Daddy nai ya tsaya yai duk wasu cike cike da suka da ce aka basu gawar saboda ta dade tana jinya a asibitin ya bukaci su wuce da ita gidanta ai mata suttura a can.


Mama ce cikin fushi ta ce "me zata koma tayi a gidan wanda bai san kara ba ko yakanah, wallahi dan ku yayi asara bata da hurumi da wannan gidan tun da ya aiko mata da takaddarta saki uku rigis, wanda yai sanadiyyar rasa rayuwarta ai ya huta ko kuma mun bar shi da Allah."


Jikin Daddy har rawa ya ke saboda tashin hankali "haba Hajiya wasa kike Arfan din da duka yaushe ya fito daga asibitin yana gida ma fa shi ba lafiya" murmushi kawai tai ta mika masa takardar ya karanta fashewa yai da kuka duk dakiya irin ta namiji.


Ya din ga kuka duk sai da jikinsu yai sanyi "tabbas ka haifi da baka haifi halinsa ba, amma dan Allah kuyi mun alfarma idan har mun zama daya a sallaceta a gidana" Umma ce ta ce ba komai su tafi.


Yana kwance a daki yana ta tunani anya ko yaiwa Nafeesat adalci bai kamata ba sam abun da ya aikata, dan yana san kanwarta bai kamata ya rabu da ita ba tun da tana masa tsananin biyayya, bai mata adalci ba tabbas kafin dan aiken ya risketa gwara ya janye dan tabbas yana san Nafeesat amma Maryam fa?


Nata mai sauki nai gwara su rabu da Nafeesat cikin salama, yadda zai Dora mata lefi yadda iyayensu bazasi jayayya wajen bashi auren Maryam ba, da wannan shawarar ya samu karfin gwiywar mikewa ya fice.


Haka ya mike yana layi ya nufi gate ya tarar driver ya dawo ya ke tambayarsa yaya ya kai ya ce eh, cikin tashin hankali ya koma dakin sai kuma yaji fitar su Daddy, yana nan kwance yana karanta wasikar jaki ya kira Maryam missed call bakwai yai mata sannan ta daga.


Fashewa tai da kuka "Arfan ka cuceni ka gama da rayuwata ciki wata biyar na shege ni Maryam? Wallahi ka gama zaluntata saboda wannan abun yar uwata ta ke halin mutuwa da rayuwa, tun ranar data samu labari bata kuma rayuwa mai dadi ba a duniya.


Zabura yai kina nufin dama ba rainon ciki Nafeesat ke ba lalura ce tasa har yanzu bata dawo ba, kina nufin kice ciki ne da ke? alhamdulillah! naji dadi amma zan je duba Nafeesat, nasan kodan cikin jikin ki zan mallake ki cikin ruwan sanyi" "bansani ba munafiki kana nufin bama kasan halin da iyalinka ke ciki ba ke nan, to karka kuma nai ma na dan ni yanzu uwace a gareka dan mahaifinka zan aura" tana kuka ta kashe wayar.


Story continues below

What! ya furta da karfi ta kashe wayar gaba daya ta fashe da kuka duk duniya bata da makiyi kamar Arfan ta tsaneshi tsana mai yawa, tabbas sai ta rama bakin cikin da ya tusa mata ita da iyayenta kodan yaji dacin da suke ji, ba abun da zai hanata auren mahaifinsa sai mutuwa koda ko shi ne aikin da za tai na karshe a duniya.


Shi ko mikewa yai jikinsa na rawa ko gani bayayi sosai yana fita yaga motoci na shigowa har da ambulance, yai mamaki da aka shi go kowa kuka ya ke nan aka dakko gawarta hannunta nai ya leko zoben hannunta ya gani tabbas ita ce ba sai an fada masa ba ta mutu.


Ni ne? ni na kashe ta wallahi! wayyo Allah na! innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un! ya Allah! wani gigitaccen mari Daddy yai masa "kukan me kake? ka kashe ta ka huta sai ka zuba ruwa a kasa kasha, amma inaso ka sani ko mutuwa zakai wallahi bazaka auri Maryam ba ko bayan raina ka aureta ban yafeba.


Gaba daya ya susuce wasu surutai ya ke abun tausayi yana bin gawar har aka shi ga da ita aka ajiye a tsakar gidan dan ai mata sittira, jikin ta ya tafi gadan gadan ana rikishi amma ina rukunkumeta yai, jini sai zuba ya ke da kyar aka bambare shi ji kake yif ya fadi.

*******************
Amarya ta lakadawa Zubaida uban duka da kyar Malam Mato ya kwace ta a hannunta, gaba daya ta hada mata jini da majina Zubaida ta daku shi ya sa yana kwatar ta tai hanyar waje ko mayafi bata dauka ba gidan Kulu ta fada tana haki.


Kuka tasa sai da tai mai isarta sannan ta fara zagin Kulu tana tsine mata, "wallahi Kulu kin cuceni dan duk ke ce kike kara tunzura ni, ga shi yanzu kun mana sanadin mutuwar aurena, wallahi sai naga bayan Haule ko zan yawo tsirara har gida taje ta kashen aure."


Hhhhh! ta sheke da dariya "kin ga shi ke nan dan ni ko ta kyauta mun munyi ragas gaba dayan mu duk mu zauna a haka ba kare bin damo ke babu ni babu ita babu kin ga babun badilahu ke nan."


Cikin tsananin fushi Zubaida ta mike "lallai baki da mutunci dole ki furta haka tun da ke dama ba mijin gareki ba sai yawon na dandi dole mu da mukasan muhimmancin mazajen namu dole hankalinmu ya tashi."


Habawa tuni suka kaure da fada kamar kaji suka din ga tone tone, "ni sai dai ki ce mun uwar tuggu Zubaida amma waya kai ki bin malamai kaf lokon nan ke kika koya mana bin Malamai, kuma dandi ai ba karya bane tun da tsohuwa ma tayi a haka a samo mutum, saboda haka karshen ki nai yazo yanzu."


Habawa kukan kura tayi tai kan ta ta fara jibga ta huce fushin dukan da ta sha akan ta nan suka din ga fada sai da makota suka shi go jin ihu suka rabasu.


Haule ko tana fitowa asibiti ta nufa ta sha wahala kafin a kai ta gunsu yana ganin ta ya hade fuska tamau jikin ta a matukar sanyaye ta shi ga dakin daga shi sai ita yana bare mata ayaba yana bata.


Wani kallo yai mata da wata muguwar harara "nan ma kin biyomu nai ki karasa kashe ta da abun da ke cikin nata ko yaya? to maza tun kafin na bude idanuwana ki fice daga dakin nan kafin raina ya baci na yanke miki mummunan hukunci dan ko ganin ki bana san yi."


"Haba Malam kayi hakuri mana ko gaisawa ka bari muyi kaji me ya kawota kasan fa tana da hakki ita ma akan ka, yadda nake matarka haka ta ke matarka itama, saboda haka bai kamata kai mata haka ba kayi hakuri ka saurareta kaji uzurinta."


"Wacece matata? ki ma daina wannan maganar kawai gaya miki nai banba amma ai mun dade da rabuwa shi ya sa duk san da kika ce na koma gidanta na kiya, na bar mata gidan nai saboda in rufa mata asiri saboda lalurar data samu, amma yanzu ta warke bana bukatar sake ganin ta kafin mu dawo ki tattara kayan ki koma kauye."


Kuka ta rushe da shi ta durkushe a wajen "dan girman Allah kayi hakuri ka mun rai ka tausayamun wallahi bazan iya komawa kauye ba, kasan ban da kowa ban da komai sai kai ka temakeni ka maida ni dakina dan girman Allah na tuba wallahi, ki sa baki Indo dan Allah ki yafemun kice ya yafemun."


Indo ta din ga lallabashi da kyar ya ce "shi ke nan wallahi kinci darajar farar mace mai farar zuciya baiwar Allah, wallahi da nagama zama da ke" murna ta din ga yi tana ta godiya ga Indo dan ita yanzu taga rayuwa wanda ka yarda da shi dan yaci amanarka ba wani abun wahala ba ne.


Nan ta saki zancen Nauwara amma ya dakatar da ita yama fice tasa kuka ta sanarwa da Indo komai dan dama can ita ce mai bata shawara ta gari kuka tasa saboda tausayin Nauwara hankalinsu ya tashi sosai da sosai.


Bayan wata uku indo ta warke ciki ya kai wata bakwai tuni an sallamesu, kullum cikin bashi hakuri ta ke kan lamarin Nauwara duk da abun na damunsa amma ya da ke, amma yau mummunan mafarkin da yai ne yasa ya mike ya wuce police station dan ya jarraba zuwa gidan basu sani ba, an hana shi shi ga wai ba kowa kuma yana yawan ganin maza ma shi ga gidan, Alhaji Ghali ko har a kasuwa yana ganinsa bayan ganin da ya ke yana fitowa.


Ba bata lokaci suka bashi yan sanda ya debi Malamai yan uwansa suka dau hanyar gidan ta dan tabbas mafarkin da yai Allah zai iya kamashi zuwa yanzu tayi nadama mai matukar yawa.
Cikin tashin hankali suka mike tsaye suna kallonsa gaba dayansu a firgice suke, "lallai Alhaji ni zaka yaudara? ni zaka rainawa hankali? Alhaji ni zaku munafunta ni zaku yaudara? ke kuma wallahi sai kin dandana shi ga gonata da ki kai, sai kun dan dana cin amanata da ku kai gaba dayanku."


Ya fice ya bar su a dakin jikin Alhaji Ghali yai sanyi shi fa ya gaji da wannan masifar ya gaji da wannan danyen aikin da suke aikatawa, wannan wace kalar rayuwace ya tsunduma kansa a ciki dan yanzu dubararsa har ta fara fitar da wasu tsutsotsi ya rasa wa zai gayawa.


Dole ya ajiye wannan dabi'ar ya kula da matarsa ya zame masa dole idan ya daka ta Baby Chakwai wallahi ba zai bar shi ya huta ba, gwara ya yiwa tufkar hanci kamata yai ya zaunar aiko ta saki wani ihu sai da ya razana.


"Lafiya Nauwara me ya sameki kike wannan ihun?" "cikina nai ya motsa" ta fada da kyar saboda yadda duburarta ke tsirinta, cikin murmushi ya shafa cikin "gaskiya munyi sake kin ga cikin nan naki ya kai kusan wata shida fa, ya kamata jibi Monday na kai ki asibiti daga nan sai na kai ki gida ki wuni ko?"


Wani farin ciki taji ta a ciki wanda tun da Allah ya halicceta ma bata taba kasancewa a cikinsa ba, dama zata kara fita daga wannan gidan? dama zata kara ganin Innarta da Malam da kawarta Maimuna a duniya? kuka tasa na farin ciki ta rungumeshi "nagode nagode Allah ya biyaka ya kara bamu zaman lafiya, Allah ya kara karkato mun da hankalinka gaba daya ka dena duk wasu abun da ya sabawa Allah."


Ya tausaya mata har hawaye yai cikin jin kunya da nauyi wanda tun da Allah ya halicce shi bai taba jin kwatankwacin wannan kunyar ba, ya rumgumeta "insha Allah na miki alkawari daga yau daga yanzu na bar wannan mummunar dabi'ar tawa bari na har abada, ina rokon Allah ya gafarta mun zunuban dana dade ina aikawata."


Rumgume shi tai cikin farin ciki suna ta murmushi haka suka kwana cikin farin ciki, washe gari lahadi da wuri yake dawowa dama karfe hudu amma ya ce sha biyu zai dawo kawai zai wani aiki nai kar ta damu cikin matukar kewar juna suka rabu ya fito ya tunkari dakin su zai dau wasu takardu.


Baby Chakwai cikin bakin ciki da bacin rai ya kwana, tashin sa kenan yaiwa abokan iskancin sa waya su kawo masa maganin da zai sha yai awa biyar cir akan namiji, wanda sai ya kusa mutuwa idan ya hau shi saboda yai alkawarin sai ya hukuntata, "sannan ina so ku kawon maganin da zan zubawa Alhaji a abun sha wanda ba mai ganewa na kashe shi kowa ya huta."


Daidai lokacin da Alhaji zai shi ga dakin yaji ana zancen kashe shi gabansa na faduwa ya juya ya fita, dakin da bai shi ga ba ke nan, to dole sai ya san abun yi dole sai ya dau kwakwkwaran mataki, gaskiya Baby Chakwai ya bashi mamaki fiye sa tunaninsa, da kyar yanke tukin da kyar yaje kasuwar hankalinsa na kan Nauwara haka kawai yaji gabansa na faduwa.


Story continues below

Yana fita minti talatin abokan shashancin nasa suka karaso su biyar suka kawo masa maganin, wanda zai zama kamar doki zai fita daga hayyacinsa nai kawai ya fara aiki ba bata lokaci ya afa kayansa,da kuma na kashe Alhaji Ghali suka din ga iskanci suna ihu.


Nauwara na kwance tana bacci cikin farin ciki saboda tsanin farin cikin da Alhaji Ghali ya sa ta na zata ganin iyayenta, tana mafarkin sun hadu dasu cikin farin ciki sun kuma gafarta mata kamar a mafarki taji an dalla mata mari ta bude idonta fes akansa suna kallon kallo.


Tuni ya daka mata tsawa ta juya taki ganin haka ya kira abon nasa suka daureta da igiyoyi, dayan ya ce "Anty Chakwai barni na dana" ya kece dariya "ai kowa zai yi ku kwantar da hankalinku yau cin mutan da zami mata" tana kuka tana ihu ya kifata ga ciki da sauri tai goho, "hhhhhh! shegiya ita ma so ta ke" tana kuka ya hau ta sai da yai awa biyu cur.


Tun tana kuka sai da ta dena kuka har sai da ta suma yana kanta yana wannan aikin, sun manta basu rufe kofar parlour da key ba bare ta dakin da take han hai, ganin tayi laushi yaran suka koma parlour suna fita Alhaji Ghali ya shi go da yan sanda, "yauwa ku fara da su" ihun da yake ji a dakinta kuma na Baby Chakwai nai yasa ya nufa da gudu, abun da ya gani nai yasa ya saki wani ihu wanda ya janyo hankalin ragowar police din.


*******************

"Tabbas Hajiya sai dai ki hakuri duk tsuntsun daya ja ruwa shi ruwa kan doka, amma abun da nakeso ki sani tunani bai aure ki ba sai kin shi ga gidan dan ina da tarihin gidan Lawan mai yai Mazauna mai yai Tal'udu ina da labarinsa kaf.


Wallahi baki ga komai ba duk barikin da kike yi wallahi na gidansa karshe ne dan ba abun da ake sai bariki a gidan nan, dukansu ya ke kamar jakai shan giya ko kamar ruwa a wajensa dan ita ce ruwansa, kin bi kyansa kin aure shi yadda kika dau lamarin yasa nakasa gaya miki amma idanuwanki sun gane miki karnanncin da suke.Wallahi wannan ba komai bane a gidan Lawan saboda haka ki shirya zaman hakuri ki kuma kau da kai kar ki biye musu, tun da kin san kina da manyan yaya a wani gidan saboda haka kar ki biye musu kuyi ta karnanci."


"Chab di jan ca zaki abun namu daidai ke nan, ko kin manta saboda dukan da nakewa tsohon mijina idan mutanen boyena suka tashi yadda yake jibguwa, saboda yadda basa san bacin raina ca zaki lokacin gyara musu zama ne gaba daya yayi."


Suka sheke da dariya suka tafa "lallai kam namanta kema Boss ce ashe na manta" suka tafa daidai lokacin driver ya tsaya suka shi ga gidan yaranta zazzaune bakin ciki kamar ya kashe su babar ce ta fara magana.


"Haba Hajiya yanzu tun da Abban mu ya mutu shi ke nan kin auri aure aure? aure na uku ke nan kuma ba iya zama kike ba, kowa kice ga matsalarsa to mu dai gsky mun gaji Hajiya! kin san ko irin mijin da kika aura? mijin da ko ya girmeki kadan nai tantirin dan iska cikakken dan iska na bugawa a jarida, cikakken dan giya manemin mat....."


Bata karasa ba ta dauke ta da mari "fitsararriya mara kunya ni kike tara akan nayi aure na raya sunna, da dana ke zaune haka ba ca kukai ana yi da ku ba ina zaman kai na, dan tsanbar iskanci nayi auren ma bazaku barni na huta ba zaku fara bina da bita da kulli.


Work out all of you stupid!" jikinsu gaba daya rawa ya kama suka wuce sum-sum suka bar dakin kar suje mutanen nata su motsa ta nasa musu na jaki, su kuma suka zube a parlour din ana maida yadda akai kowa da abun da ya ke fada kowa da abun da yake fada suna ta shakiyanci irin nasu na manyan mata yan duniya.


Bayan sati guda duk wani gyara Lawan yinsa ya ke ka'in da na'in ya gyara mata saman Laila duk da bai komai ba amma saboda sabuwar amarya aka sake sabon fenti aka gyara aka fitar mata da kitchen a barandar saman ba abun da zai hadasu da ke nan.


Ummi ko tashin hankali ta shi ge shi inda iyayenta suka zo su kai mata jan kunne idan ta sake ta daga masa hankali ko ta dagawa yan kawo amarya basu ba ita har abada, ko ta sake ta fashe auren ta to ta nemi wasu iyayen amma basu ba, sun mata nasihohi sun kuma shi ge ta sai dai tsananin kishi da ta ke ciki amma ta da ke.


An kawo amarya lafiya yan kai amarya sun watse ango ya shi go bai bi takan Ummi ba ma dan kar tai masa hauka ta hanashi jin dadin sa yau, suka nufi bangaren amarya Ummi tai bakin ciki tasha kuka kayan da ya aika mata ko kallonsu ba tai ba saboda bakin ciki.


Laila ko bayan ta koma gida ta din ga kuka kamar ranta zai fita saboda bakin ciki tana kallo yana kiranta taki dagawa, dan yasan shi ne bashi da gaskiya yai mata lefi sosai amma ya zai yi yasan halin haukanta shi ya sa ya boye mata, haka ta din ga kuka bata boyewa kawunta komai ba ta sanar masa addu'a kawai yai dan bai da ta cewa.


Satin amarya uku Lawan ya shi go gidan saboda yanzu da ita yake yi yadda take tattalinsa ko yawon ya rage, sai yau ya zama mashaya, ya dawo tsakar dare a maken sa ya tashe ta "ke tashi zan yi" cikin bacin rai ta kalleshi "mai za kai kenan?" "kin fini sani zan kusanceki" cikin bacin rai ta mike.


"Kayi kadan ka sadu dani cikin maye wallahi, ban san iskancin naka ya kai haka ba har zaka din ga shigowa gidan ka unguwarku a make, ka manta cewa kana da yara ko ka manta haihuwa kake har yanzu baka dena ba, to bazan iya ba ni bazan taba bawa sakarai sauna kai na ba a banza a wofi ba cikin maye."


Cikin bacin rai ya gaura mata mari sai da ta kife saboda marin ya shi ge ta mari nai na bazata, ya fara dukanta ihu ta ke tana kuka yana cikin dukan yaji an shake shi an daga shi sama an buga da kasa, wani ihu ya saka saboda azaba nan ta din ga dukansa yana ihu sai da tai masa lilis sannan ta kwanta itama a wajen sai bacci shi ko suma yai a wajen.


Doctor Saudat abun yaki sai da aka kai ga asibiti inda ta samu Doctor dan Fulani ma an kwantar da shi saboda ruwan ya dan taba gabansa, amma yafi karfi a cinyarsa kowa mamaki ya ke me ya kawo masa wannan kunar? amma ance wai ruwa ya sauke shi ne ya kone matarsa kuma ta ce ba a gidan sa bane dan bata san zancen ba.


Bala'i ake sosai tsakaninsa da matarsa sai kuma ga Doctor Saudat an kawo itama, nan fa wayanda suka san alakarsu gulma ta barke a tsananin mutane ita ma daki guda aka bata ta ke jinyar Humaira ta kira iyayenta amma fafur sun ki zuwa sai ita ke jinyarta.


Lawan ko kememe yama ki daga wayarta satin ta biyu a asibiti da ke bata da kan jiki ta dan ji sauki sosai, a ranar ta dau alwashin bawa Lawan last lesson a rayuwarsa koda ko karshen zamansu yazo kenan tsakaninta da shi, duk da bazata so hakan ba amma azabar daya gana mata tabbas sai ta rama.


Nan da nan Nurse din da suka taho da gawar su kai kansa amma ina numfashi ya gagareshi fita gaba daya ya fita hayyacinsa, kowa haushi ya ke ba shi to duk wannan na meye abun da ya ke bukata nai kuma ya samu, suka dauke shi sai asibiti saboda zuciyarsa ce tai mugun bugawa.


A ambulance din suka juya da shi ba wanda yabi bayansa saboda bacin rai kowa kuka ya ke su Mama da Umma nai da Momy su kai mata wanka, su nayi suna kuka saboda yadda take ta zubar da jini suka hadata duk da yamma tayi amma haka akai mata sallah aka kaita saboda jinin.


Masha Allah ta samu jama'a tayi mutane fiye da tunanin mutum sai sannan Umma ta kira kanwarta ta sanar mata halin da ake ciki na rasuwar Nafeesat, ihu ta saka ta saki wayar kasa saboda tashin hankali "Maryam! Maryam!"da gudu ta taho cikin tashin hankali "lafiya Anty?"


Ta fashe da kuka "Maryam Allah yayi ikonsa duk abun da Allah yai, bawa ba zai wucewa kaddararsa ba bata baya wuce lokacinsa" cikin kuka ta ce "Anty menene?" girgiza kai ta ke "sai dai miyi hakuri Maryam Allah ya karbi ran Nafeesat! sai wancen dan iskan ya zuba ruwa a kasa ya sha zabi ya rage gareki yanzu ko uba ko da?dan kin san dole a nemi ki maye gurbin yar uwarki, amma zanfiso ki mana alfarmar auren uban ko dan Arfan ya gane kurensa."


Wata kara ta saka ta zube a wajen take jini ya fara bin ta cikin tashin hankali Anty tai kan ta da sauri ta kira mijinta tana kuka ta gaya masa, da sauri ya dakko shatar taxi suka tafi asibiti suna zuwa aka kai ta dakin yan bari saboda bari za tai wata biyar.


Haka ta kira Umma ta sanar mata tai mata addu'a kuma tai mata fatan alkhairi Allah ya rabata da cikin lafiya tasha wahala sannan cikin ya fadi, ba bata lokaci su kai mata wankin ciki kwananta daya tai normal suka sallameta a ranar suka wuce gidan makokin duk wanda ya ganta sai ya tausaya mata halin da ta ke ciki.


Abba na gadon asibiti ya gamu da cutar paralyse saboda wannan faduwar da yai a karo na biyu Sulaiman ke jinyar sa saboda su Mama na karbar gaisuwa ba um ba um um Abba ya zama kamar gawa a asibiti, ga Arfan a kwance shi ma zuciyarsa ta buga ana tunanin fita da shi ma waje saboda halin da ya ke ciki me wuyar fassaruwa amma Daddy yaki yarda.


A yau akai sadakar uku suna zazzaune a dakin da suke Umma da Mama da Anty sai Maryam da ke kwance Mama ta gyara zama "lokaci yayi da zamu rama zalincin da Arfan yayi mana, lokaci yayi da bakin cikin da ke ranmu zai ragu."


Umma ta gyara zama "tayaya ke nan?" "yauwa ta hanyar auren mahaifinsa da Maryam za tai, kar muce zamu hana wannan auren Umman yara saboda daukar fansa" Anty ta gyara zama "ai idan kun ga ba'ai wannan auren ba to Maryam ce ta rasu amma aure ba fashi Allah nai ya halatta bamu ba."


Story continues below

Umma ta ce "ku fuskanci wani abu komai kaddarane a ratuwa bai kamata ace zamu dauki fansa ba, ana barin halak ko dan kunya ko dan yadda uwarsa ke mana ya kamata miyi hakuri muyi mata addu'a Allah ya bata wanda ya fishi, amma ni yanzu gaba daya duniyar ta ban tsoro yanzu Nafeesat ku duba babu, shi ma yana can kwance a asibiti rai a hannun Allah zuciya ance har aman jini ya ke, ko zai tashi ko akasin haka waya sani to meye amfanin auren da zai zamo saboda cutar da wash?


Ko wannan ya ishe shi ishara Allah ya jarabce shi da san Yaya da kanwa a lokacin da ya rasa yayar kanwar ma kuma ba zai sameta ba, mu bar shi da wannan jarabawar ta ishe shi ishara a duniya ku kwantar da hankalinku amma gaskiya bansan wannan auren, musamman yadda matar nan ke mana ace mun aurawa mijinta yar cikinta akwai cin fuska."


Maryam ta mike zaune "Umma!" cikin kuka "wallahi wallahi ni Daddy na ke so! Allah ya jarrabi zuciya da kaunarsa! a yanzu babban burina na aure shi ba dan daukar fansa ba sai dan na raya sunna" jikin ta yai sanyi kalau Mama ta ce "kwantar da hankalin ki diyata baza'a tauye miki hakki yadda aka saba ba, saboda haka na gama magana in dai na isa da ke ranar sadakar bakwan yar uwarki ranar daurin auren ki."


Jikin Umma yai sanyi bata san magana Mama ta ce dan ba ita ta haifetaba amma lamarin yayi tsauri gaskiya, ita ko murna ta kama yi a ranta burin ta zai cika zata nunawa Arfan kurensa zata auri ubansa ta tashi kai daya da uwarsa kuma dole yai mata biyayya a matsayinta na matar babansa uwa a gareshi.


Mama ta sa aka kira Daddy tai masa bayani duk da yaso ya hakura amma jin yarinyar ma nasansa sai hankalinsa ya kwanta, tun da ba kowa yasan anyi ba sai na gida gida kuma har ga Allah kullum ya kwanta sai yai wanka saboda mafarkin Maryam da yadda ta ke haifa masa kyawawan yara masu kama da shi, "shi ke nan Hajiya ba matsala Allah ya kai mu ranar sai ai daurin auren bayan arba'in sai ta tare ko?" "eh hakan yayi Allah ya nuna mana, sai anyi hakuri kaga yarinya ce ga kuma abun da ya faru" "haba ba komai, komai ya wuce ai" sukai sallama ta koma gida.


Abba na gadon asibiti bai san wainar da ake toyawa ba amma yau ya danyi magana amma bata fita a harharde ta ke, Umma da Mama da Maryam sun je duba shi inda Mama ta ke shaida masa auren Maryam da Daddy, hawaye kawai ya ke saboda ko yai maganar bazasu gane ba amma baya san auren sam, "ka kwantar da hankalinka Alhaji sai ka warke za'ai biki kawai daurin aure za ai, Sulaiman zai daura tun da shi ne a madadin ubansu ga kuma kawu na nan shi ke nan ai."


Yau ta kama ranar bakwai bayan gama addu'ar sadakar bakwai aka gabatar da daurin auren, abokan Daddy sun sha mamaki jin Alhaji Kamal nai zai aure tun da kuruciya bai ba sai yanzu da furfura, ba damar suyi magana ya riga ya gama yanke hukunci, sadaki dubu hamsin ya bayar aka daura auren Momy na daki ta samu labari sai da ta yanke jiki ta fadi saboda tashin hankali.


"Dama Alhaji bai hakura ba da gaske yake? Tabbas ya gama ci mun fuska da wulakantani a zaman makokin surukata zai mun wannan tozarcin?" yan uwanta nai suka din ga tausarta komai ya wuce, a ranar su Umma suka hada komai nasu suka koma gida gudun fitina ita dai bataso ba wallahi cin fusakar yai yawa.


Arfan jiki yaki sam kullum ba shi da zance sai na Nafeesat da Maryam, Doctor nai ya shi go duba shi "sannu Arfan kayi hakuri ka dangana har anyi bakwai baka zauna a wajen makokin ba, yanzu muka dawo daga sadakar bakwai, gashi babanka ya daura aure yau da kanwar matarka naji ana cewa" "what doctor?" ya fusgo maganar cikin murmushi "ashe zaka iya magana eh yayi aure kanwar matarka ya aura kayi kokari ka karfafa mana gwiywa ka cire damuwa sai mu sallameka" wani tari ya fara "Maryam! Maryam! no ba ita ba ce!"


Tuni ya fice daga hayyacinsa Doctor yai nadamar gaya masa saboda bai san cewa abun na shi zai worst har haka ba da bai sanar masa ba wallahi, to meye ruwansa ma da auren mahaifinsa jikin nasa ya rikice dole ya kira mahaifinsa farin cikin da yake ciki yasa ya bada umarnin fita da shi waje sati daya a tsakani suka daga shi da Momy.


Story continues below

An sallami Abba ya koma gida amma komai yi masa ake ya nuna baya san auren amma Mama tai masa jan ido ya kulle bakinsa saboda yanzu yayi nadama sosai, anyi arba'in kwana uku a tsakani Maryam ta tare a gidan Daddy tana kuka aka kai ta ta sha gyara ciki da waje kamar ka latsa jini ya fito Daddy ya ce sai taje zai bata lefenta.


An kai amarya cikin kwanciyar hankali dakinta, Abba ya share komai a ransa ya cire batun dansa yai amfani da ita ya din ga addu'a komai ya ragu a ransa a daren mai afkuwa ta afku, Abba ya kusanci Maryam cikin aminci inda ya din ga kuka tana kuka saboda tasha gyara wajen (Feedyn Bash mai maganin mata original mai gyaran amare da zawarawa har da iyayen mata) ji yai tamkar ba'a taba fasata ba yadda yajita gata yarinya danya sharaf.


Daddy ya debi ganima kasa kyaleta yai kawai kashe arna yake gaba daya ya rikice bai san ta'asar daya tafka ba sai da asuba, tunani ya ke anya ko Maryam ta taba sanin wani namiji koma dai meye matarsa yar baiwa ce kuma yai alkawarin riketa amana, yadda yaga ya taba ta shiru hankali sa ya tashi sosai ashe suma tai ya dauka bacci ta ke, da gudu yai waje neman taimako saboda gigicewa.
*******************

Maimuna suna Malaysia abun su karatu suke ka'in da na'in ita da mijinta, matsalar tun auren su ta ke fama da ciwon mara, sunyi magani sunyi amma shiru har yanzu ba bayanin haihuwa, duk inda suka je sai ace lafiyarsu kalau ba abun da ke damunsu, sun mika lamarin su ga Allah mai kowa mai komai sun san shi ne mai yi kuma zai musu da izinin sa.


Abun da yake daga mata hankali mafarkin Nauwara da ta ke kullum tana kuka tana neman gafararta, kullum ta tashi sai tai sadaka tai mata addu'a saboda mafarkin na daga hankalinta sosai tama rasa yaza tai saboda tashin hankali idan ta kira gida ace kowa lafiya.*******************
Cikin tashin hankali yai kansa ya fara duka kamar Allah ya aikoshi yan sandan nai suka rike shi, suka makawa Baby Chakwai ankwa a tsirararsa, ita ko tuni ta sume a sume ta ke kuka yake yana tsine masa albarka, ana haka Malam suka shi go suma abun ya basu mamaki mai yawa yadda ya kasance sun tarar da motar police a gidan.


Ihun da suka ji yasa su kai cikin gidan sun yi mamaki da suka ga mutane police sun kakkamasu, kukan Alhaji Ghali nai ya janyo hankalinsu amma police din da suka tarar suka hanasu shi ga kwata kwata da kyar suka zura masa wandonsa suka fito daga dakin, Alhaji Ghali ya kinkimo Nauwara tana ta zubar jini.


Salati Malam yasa ya nufosu lafiya wallahi yata ta mutu sai nai shari'a da kai, kuka ya ke ya kasa magana da sauri aka fita da ita ya sata a bayan mota su kai asibiti, suna zuwa dake da police ka akarbe ta su kuma akai police station da su.


Awa biyu tsakani doctor ya fito yake sanar musu result din duburarta ta Riga ta zazzago ta lalace dan har tsutsotsi ta ke daga ciki, ga ciki wata shida da sati biyu ga shi ta kamu da hawan jini mai tsanani da ciwon zuciya dole za'ai mata aikin a maida duburar, amma dole sai ta haihu ko an mayar tazo haihuwa zata kara zazzagowa.


Yanke jiki Malam  yai ya fadi saboda tashin hankali, shi ko Alhaji Ghali kuka ya ke yana tausayawa Nauwara yana nadamar abun da ya aikata, anan aka samu Malam ya farfado amma yai rantsuwar sai ya maka Alhaji Ghali a kotu, ba wanda ya hanashi hatta shi kansa Alhajin, yana fita ya wuce police station aka shigar da kara sai kotu, inda aka aikawa da Alhaji Ghali sammaci, Malam yayi dana sanin kai shi kotu saboda yadda yai nadama da yadda Nauwara ke gaya masa yadda ya tuba ta silarta amma ya Riga ya shigar gobe ne ma zaman kotun.


Sunje kotu inda Alhaji Ghali bai boye komai ba kama daga auren su da yadda su kai aure da Baby Chakwai da tuban da yai  inda kotu ta sassauta masa saboda yadda yayi nadama anan aka yanke masa hukuncin shekara biyar a gidan yari da tara mai yawa, a ta ke ya biya tarar yai rubutu ya mallaka mata manyan company raba dukiyarsa yai kashi uku ya mallaka mata kaso guda yayi kuka da nadama sosai.Baby Chakwai ko shekara ashirin da biyar aka yanke masa saboda yadda ya din ga mata fyade har aka kamashi, ban da yadda iyayen yara suka din ga zuwa yadda ya din ga bata yaransu maza, an fito da su za a tafi dasu prison shi Baby Chakwai gwauron dutse, Alhaji Ghali kurmawa amma rabasu kuma ko wanne  ance a killace shi, saboda karsu lalata wasu ma a can Baby Chakwai ya kalli Alhaji Ghali da Malam ya ce......
****************
Lawan jarumin maza bai farfado ba sai sanyin asuba inda ya mike a gigicewa ya  runtuma ihu ya sakko a sukawane, Ummi ta fito sallah ta tare shi "anya ko lafiyarka? tabbas zargina ya tabbata gamo kayi tabbas Lawan, tun jiya tsakar dare kake ihu na dauka na jin dadi nai ka samu yadda kake so gona tayi kyau, sai naga sabanin haka ko dai tafi karfinka nai?" Ta sheke da dariya ganin yadda yake wiki wiki da ido, "anya ko lafiyarka?"


"Boyeni Ummi wallahi kashe ni za tai karfi nai da ita kamar doki buga ni ta din ga yi da kasa" hhhhhhhh! ta bushe da wata dariya "ayyiriyiri alhamdulillallah! yau ka auro daidai da kai wadda zata sai ta mana kai, ai ni abun yai mun dadi yanzu nasan kayi aure, maza koma ba inda zaka Hajiya! Hajiya! sakko gashi zai gudu da ya fita sai yai sati bai dawo ba wallahi" cikin bacci taji kira ta sakko da sauri har tana tuntube.


Ya aika ta fito kememe taki ya rasa yadda zai yana tsaye kawu yazo ya tsuguna har kasa ya gaida shi, ya amsa ya dakko tabarma ya shimfida masa a zaure cikin kunya suka kara gaisawa, rabonsa da kawu tun ran daurin aure nan ya shi ga bada hakuri ya nemi ganin Laila, shi dai yai masa fada na gaskiya yai masa nasiha mai ratsa zukata ya dan shi ge shi ba laifi.


Laila ce ya fito da uban ciki a gaba dan wata takwas yanzu nan ya sata a gaba ya lallabata, tsakanin Laila da Lawan sai Allah ba wanda zai iya rabuwa da kowa a cikinsu, nan da nan suka daidaita kwana uku tsakani ta koma gidanta suka Dora daga inda suka tsaya kullum sai sun yi fada saboda kishin Laila shi kuma yawo. 


 A hankali ta ke binsa a baya har Prince hotel inda ta samu dama ta gana da waiter na reception din ta ba shi kudi ya bata spare key din dakin, yan sanda ta kira tai musu kwatancen dakin minti sha biyar sai gasu tana gaba suna binta a baya Lawan na cire wando Babyn sa ko tai tsirara tana jiransa su kacame. 


Kawai ji yai ana murza key din abun da y bashi mamaki ke nan, "yauwa yallabai ga shi nan gaba daya ku hada ku kamasu" abun ya daure masa kai kafin kace kwabo sun buga musu ankwa.......Iya mai aiki ya gani ta tare shi "lafiya Alhaji?" "Iya ba lafiya ki taimaka mun mu kai ta asibiti" murmushi tayi "ka nutsu Alhaji ka kwantar da hankalinka bara naje na ganta kasan mata sai hakuri" da sauri yayi gaba ta bishi a baya "yauwa dan bamu waje" kamar zai kuka ya fita ta saki murmushi ta debo ruwa ta yayyafa mata ta saki attishawa ta fashe da kuka saboda azaba tun da duk wanda Arfan ya ke mata ba ta cikin hayyacinta.) 


"Ya isa haka Maryam kamar ba mace ba ki kwantar da hankalinki mana" nan ta taimaka mata ta gyarata ta sanja zanin gadon duk da ba jini amma taji jiki sosai, kunya duk ta gama lullube Maryam ji ta ke kamar a mafarki wai yau ita tai aure ta auri baban Arfan wanda ya kassara rayuwarta a duniya. 


Da sauri Iya ta nufi kitchen Daddy yai sauri ya fado dakin tana zaune tana kokarin saka kaya, kunya duk ta lullubeta da hanzari ya rungumeta "Babyna ya jikin naki da fatan dai kina lafiya bansan haka ba nai gaggawa amma kiyi hakuri kinji Baby."


Kunya ta lullubeta ta kasa ce masa komai murmushi yai saboda ya fuskanci haka, "shi ke nan me kikeso yanzu?" tayi shiru da kyar ta ce "ina san saka kaya nai" dariya yai "bari na sa miki" ba yadda ba tai ba amma yaki tana ji tana gani ya sa mata kaya ya dorata a cinyarsa, kiyi hakuri Babyna nayi alkawarin zan rike ki amana kinji kidena jin nauyina komai Allah nai ke kaddarawa Allah ya kaddara ke mata ta ce wannan kaddara ce.


Kuma nagodewa Allah da ba da aurena dana ya kusanceki ba abun zai fi mun ciwo dan ana yi sosai, kiyi hakuri ki yafemasa lalurar data ke damunsa ma ta ishe shi yanzu, abun da na ke so dake shi ne ki manta da komai ni mijinki nai miyi rayuwarmu mai inaganci ki haifa mun kyawawan yara masu kama dake sak."


Story continues below

Kunya ce ta lullubeta ta boye kan ta a kirjinsa yana ta kwantar mata hankali da maganganu masu dadi da ratsa zukata, mamaki nai ya kamata Daddy dama ashe dan love nai haka da girmansa amma ya ajiye a gefe kawai love yake zuba mata, awa daya Iya tai nocking ya bude kofar "yauwa Alhaji na hada muku abincin yana dining" "mungode Iya Allah ya kara girma" murmushi tayi ta tafi wajen dining din tana jiransu.


Da kyar ya jata suka je dinning farfesu Iya ta zuba mata na kan rago mai zafi, ta ce "maza kici shi da zafinsa" haka ko ta din ga cinsa da zafin nasa da kyar saboda kunya ga Iya ta tsaya akanta ta, hada shayi mai kauri sosai ta bata, murna Daddy ya ke sai da ta tabbatar ta ko shi ta barta Daddy ma yayi break fast din sa suka koma daki. 


Bayan wata daya zamansu suke lafiya lau dukansu sun saki jiki da juna bata taba sanin haka rayuwar aure ta ke da dadi ba sai da ta auri Alhaji Kamal, dama haka auren babba ya ke da dadi da kulawa da tarairaya gaskiya da mata zasu gane in dai kai sa'a gwara babban wanda zai rike ka amana da tattali, zamansu suke cikin kwanciyar hankali da kulawa abun da ya bashi mamaki ya lura da yanayinta gaba daya ya sanja tun tana sati biyu a gidansa, abun na bashi mamaki yadda ta ke yawan bacci ga zubar da miyau.


Arfan ya sha wahala sosai kullum Momy kuka ta ke tana addu'a dan ba komai a bakinsa sai Maryam, tabbas abun na daga mata hankali yadda yake zancen cikin sa na jikinta ga shi likitoci sun ce in dai bai dena tunani ba bazai warke ba yanzu zuciyarsa ta kai matakin karshe dole ai masa aiki, kuka Momy ta ke tana karawa ta yanke hukuncin samunsa ta sanar masa gaskiya dan mai afkuwa ta riga ta afku, mahaifinsa yai masa shigar sauri da yayi hakuri ya barwa dan nasa ko dan rayuwarsa.


Yana kwance yana hawaye ya rungume wayarsa a kirji yana kallon hoton Maryam da Nafeesat kirjinsa na masa zugi da radadi a hankali ta zare wayar daga hannunsa, "Arfan ina so ka zama mutum mai tawakkali mai yarda da kaddara mai kyau da akasinta, ka cire damuwa a ranka ko dan yarka da matarka ta barma wadda ke cikin kwalba yanzu, idan ka kashe kanka zaka barta cikin damuwa mai tsanani zata tashi cikin maraici muma iyayenka zaka samu a wani hali musamman ni.


Karka manta cewa ni kai kadai gareni mahaifinka ya kara aure yana da damar sake samun wasu yaran, kuma wadda kake kulafuci ita ya aura to ka cire damuwa a ranka ka manta da komai ka fuskanci rayuwarka ta gaba, ka bar komai dan Allah ka lura da tarbiyyar yarinyarka mai sunan mahaifiyarta Nafeesat! haka babanka ya rada mata suna dan Allah ka kwantar da hankalinka kaji, Maryam ta zama matar mahaifinka a yanzu, cikin ka kuma ya bare yanzu tana zaman aure da mahaifinka, suna nan zaune lafiya kalau ina samun labari sosai daga gidan."


Kuka ya fashe da shi kamar karamin yaro "tabbas shan giya masifa nai bala'in da ke cikin giya yafi kisan kai muni, idan ka sha giya ba abun da bazaka aikata ba, giya ce ta din ga kawata mun kanwar matata Momy har ta kai ina sa mata kwayar birkita kwakwalwa mai sa sha'awa a drinks, wanda hakan ya ban dama na din ga sheke aya da ita ba tare da tana cikin hayyacinta ba, tabbas giya masiface ta sanadin abun da nai mata Allah ya jarrabceni da tsananin soyayyarta wanda na rasa ya zan da rayuwata." 


Yana kuka yana gaya mata abubuwan daya shuka itama kuka ta ke ciwonsa nai ya tashi likitoci su kai masa allurai a ranar akai masa aiki, satin su uku ya warware ras aka sallamesu suka shirya dan komawa Nigeria sun sauka airport Daddy ba zai samu damar zuwa dakkosu ba saboda Maryam bata jin dadi ko office dai na fita yai, yana gida a zaune ita ko sai shagwaba ta ke kala-kala da iskanci san ranta.


A hankali su Momy suka shi go da sauri Daddy ya mike ta fashe da kuka "wayyo cikina!" ai bai san sanda ya nemi waje ya zauna ba ya fara lallabata yana rungumeta, cak ya maida ta kan cinyarsa, abun ya bawa Momy mamaki ganin yarinya karama ta burkitashi wato duk mace macece duk kankantar mace sai ta birkita namiji komai girmansa, hawaye taji sun taho mata ta matse suka shi ga Arfan bakin ciki ya cika masa zuciya ganin yadda lokaci daya yarinya karama ke juya mahaifinsa.


Story continues below

A hankali suka zauna Arfan ya ce "Daddy ina wuni" "lafiya lau ya jikin" "alhamdulillah!" da kyar ta ce 'Hajiya ina wuni" sunan taji bambarakwai kamar dirar mikiya amma ta maze, "lafiya lau Maryam ya gida?" "lafiya" haka kawai ta ce, harara ta zabgawa Arfan "Alhaji na! shi wancen yaron bai iya gaisuwa ba nai?" Daddy ya hade rai "baka ga Antynka bane bazaka gaisheta ba? A matsayin Uwa ta ke a wajen ka yanzu" wani abu nai ya cake shi a zuciyarsa amma ya dake "ina wuni Anty" "lafiya yarona ya jikin naka hope ka samu lafiya?"


Kasa magana yai sai hawaye wadda yafiso fiye da kansa ita ke mulki a gidan su yanzu, ita ce matar mahaifinsa mafisoyuwa a ransa, ficewa yai daga dakin ba dan ransa yaso ba Momy ta bishi da kallon tausayawa, mikewa tai dan taga abun nasu nayi nai yafi karfinta ita ko sai iskanci ta ke da cikin wata biyu  a ranar suka dakko yar Arfan wadda Momy ta riketa tana bata madara Maryam gwara kan Momy ta ke da Daddy a gidan.Bayan shekara uku.

 Abubuwa da dama sun faru Arfan yai hakuri ya fawwalawa Allah lamarinsa ya samu wata yarinya mai hankali zai aura, ita ko Maryam ta bar duk wasu halaye da ta ke a gidan saboda yadda Ummanta ke mata fada da nasiha, Abba ko ya ga izina tun a duniya komai nashi sai da ya kare wajen neman Magani fafur Maryam ta hana Daddy taimaka masa sai da ya gwabzu sannan ta taimaka masa.


Maryam haihuwar fari ta haifi dan ta namiji yanzu ma ta sake haihuwar yan uku biyu maza daya mace, ta cika gida da yara a  shekara uku, Nafeesat tai wayo tana yawonta ko ina zaman lafiya ya wanzu tsakanin Momy da Maryam Abba ya shiryu ya cire kwadayi a ransa Daddy yana masifar kaunar yaransa da matarsa.A karshe Arfan ya shiryu yayi nadamar abun da ya aikata a rayuwarsa dan kullum yaga yarsa sai yai kwallar san matarsa, sai yanzu ya lura tsantsar sha'awa yakewa Maryam ba tsananin so ba a karshe rayuwar kowa tayi inganci.


*******************Watan Nauwara uku a asibiti tana jinya ta tashi da nakuda wadda ta din ga wahala tun safe har dare ana kokarin shi ga da ita tearter Allah ya taimaketa ta haifo yaranta tagwaye mace da namiji, tana haifarsu ta ce a kira mata iyayenta suka zo har da Indo wadda ita ma ciki yai nauyi ta kallesu ta fashe da kuka.


"Hakika duk abun da ya sameni ni najawa kaina kwadayi mabudin wahala bani ya ce yanaso ba Maimuna ya ce yana so amma saboda san zuciya irin nawa muka shi ga muka fita muka rabasu na aure shi, wanda tun da na aure shi nake nadama da danasani kudin da naso tarawa bamu mori komai ba daga ni har Inna ta, Inna ki duba yadda Allah yai dani ki duba rayuwar da nake ciki ga shi har zan koma ga ubangijina ban ga Maimuna ba bare na nemi gafararta."


Gaba daya kuka suke Malam nai kawai ya dake "haba Nauwara cuta bata san inda rai ya ke ba kowa da kaddararsa, ana yin fiye da haka ma a tashi mu dai mun yafe miki Allah ya yafe mana gaba daya, Maimuna ma na ari bakinta baki mata komai ba dama rabo nai a tsakaninku da mijinki ina za'a kai wayannan yaran har biyu kiyi hakuri ki shiru kinji Allah na tare da ke 


"Malam ba zan ta shi ba labarina ya zama izna ga masu kwadayi da masu auren kudi, ba komai a cikin sa sai tarin na dama da dana sani tabbas Baby Chakwai ya cuceni ko a tarihi ban taba ganin (Dan Iskan Namiji) ba kamar sa, na bar shi da bullowar rana da faduwarta, alhamdulillah! na godewa Allah dana tuba kafin na koma gareshi, dukiyar dana samu daga mijina Malam a din ga hidimtawa marasa karfi da marayu dasu, ga yarana nan amana a bawa Maimuna su ta rike mun tabbas duk wanda ya hau motar kwadayi zai sauka a tashar wulakanci."


Daga wannan maganar ta fara shakuwa nan Malam ya tafi kiran likitoci amma kafin suzo har rai yayi halinsa, mutuwar da ta girgiza mutane da dama lokacin marar indo ta murda in da akai labour room da ita Alla iu.  h cikin ikonsa ba taiu.  doguwar nakuda ba ta haifo danta namiji, kafin agama cike cike har an sallameta dake lafiyarta lau haka akai mata sallah aka kaita makwancinta na gaskiya Nauwara tayi jama'a mijinta na prison aka kawo shi ya sallaceta yai kuka kamar zai rasa rayuwarsa yaiwa yaran huduba Ghali da Nauwara. 


Story continues below

Ranar bakwai Malam ya kara jaddada hudubar Ghali da Nauwara yaronsa kuma Ahmad, Indo ta hada yaran tana shayar dasu dukansu amma ana hada musu da madara ba'a sanarwa da Maimuna ba dan kar a daga mata hankali. 


Bayan shekara uku. 


Abubuwa da yawa sun faru ciki ko har da mutuwar Baby Chakwai ya haikewa wani a prison yai masa fyade yan prison sukai masa dukan mutuwa dukan huce haushi sukai masa laga laga kafin gandirobobi suzo har ya mutu sun masa fata fata, Alhaji Ghali ko ya sha jinya ta tsutsotsin da ya ke futurwa ta duburarsa amma cikin ikon Allah ya kwanta asibiti da ke yana da kudi ya samu kulawa daga waje aka dakko masa likita amma ya riga ya samu matsala ba zai kara haihuwa ba.


Ya shi ga tashin hankali yai godiya ga Allah da bai zubar da yaransa biyu ba ya warke saura shekara biyu ya fito daga prison, ya mika lamarinsa ga Allah duk da kasuwancin nasa yai baya sai da ya nemi Malam ya nemi mutanen arziki sannan suka ci gaba da juyawa, abun ba laifi ana kai masa yaransa sun saba da shi sosai kullum sai yai kuka idan yaga yaran musamman macen zam Nauwara.


Maimuna sun dawo an gama gina musu gidansu a Lamido crescent sun dawo sun sanja sun yi kyau abun su, Bello ya hada degree din sa a business studies ita kuma tayi accounting a gidan su suka sauka gida aljannar duniya, bayan sun nutsu Malam ya sanar mata rasuwar Nauwara da neman gafararta da kuma amanar yaranta da suke hannunsu dan dama Indo wani cikin gareta yanzu.


Maimuna tayi kuka Bello ma yaji mutuwar ta daga masa hankali haka ya din ga rarrashinta haka Malam ya bar mata yaran duka uku sun ci gaba da rayuwarsu cikin kwanciyar hankali, cigaba yazo musu sosai yaran gaba daya madina ya kai su su uku kanin Maimuna Ahmad da Ghali da Nauwara, shi ma ya koma yayi masters nasa a lokacin Maimuna ta samu ciki farin ciki ba a cewa komai sun yi hamdala sun yi godiya ga Allah, a karshe rayuwar Maimuna da iyayenta da yayanta tayi inganci Haule ta shiryu kunya ka dai ta isheta yadda Maimuna ke dawainiya da ita tun mutuwar Nauwara ta kara saduda da duniya.


Karshen labarin su Nauwara da Maimuna da Alhaji Ghali da Baby Chakwai kenan, kowa ya girbi abun da ya shuka tun a duniya wayanda suka tuba Allah maji rokon bawa ya gafarta musu.


*******************Suka tasa keyar Lawan da budurwarsa zuwa police station tana binsu a motarta sai da sukai parking sannan suka shi ga ta nemi waje ta zauna, dpo yazo "ya dai lafiya Doctor meyafaru? wannan ba Lawan bane Dan iskan Namiji?" "eh shi ne yallabai mijina ne ina so a tara masa gajiya ai masa laga laga kamar yadda yai min, shi nai wanda nake maka magana akansa."


"Ai baki da matsala wannan dan iska nai na gaske muna da case nashi dayawa sosai anan karki damu" tai murmushi ta fice "yanzu muka fara wasan" Lawan ya jibgu daga shi har Baby kuwa satin su daya ana lakadarsu sannan tazo tasa aka saki Baby ta zauna dan ai musu sulhu, Laila hankalinta ya tashi sosai anan ta shirya taje gidan inda ta tarar Ummi da Hajiya Santalous na fada aljanun Hajiya sun tashi ta lakadawa Ummi dan banzan duka abun da ya daga hankalinta ke nan. 


Ta fito da gudu dan neman dauki tana fitowa suka hadu da abokinsa ya ke sanar mata Lawan na police station, nan ita ma ta sanar masa halin da ta tarar dasu a ciki da sauri ya kai musu dauki sai da yai mata rukiyya sannan ta zube tana bacci a wajen, Ummi ko jikin ta duk yai tsami ta gaya mata abun da ke faruwa da Lawan, hijabi ta dakko suka bishi police station din suna zuwa suka tarar da Doctor Saudat Lawan duk ya sauya kamanni.


Suka zazzauna "yallabai nazo kai mana sulhu ni da mijina Lawan" gaba dayansu mikewa sukai Ummi da baki a fashe fuska duk a kumbure ita ma "waye mijin naki? amma dai baki da hankali ko?" cewar Laila wani murmushi tai "tabbas Laila nasan baki gane niba? Doctor Saudat ce wadda tai jinyar ki a asibiti ranar aurenku da Lawan." 


Mamaki nai ya kamata matuka "ku zauna muyi magana ayi sulhu" bayan sun zauna "yallabai mijina ne ya kamani da abokin aikina a dakina, wallahi bamu aikata komai ba amma yai mun izaya" nan ta din ga basu labari tana kuka duk sun tausayamata "saboda haka shi ya sa shi ma na yanke shawarar a hukunta shi kamar yadda na sanar da kai dpo a baya, saboda haka ina neman gafararka na tuba na ajiye aikina na hakura na ajiye aikina saboda zaman aurena." 


Jikinsu yai sanyi gaba daya lallai Lawan ya cika dan iskan namiji amma bashi da lefi lefin matan yafi yawa, anan shima ya nemi gafarar matan nasa yai alkawarin daina dukansu ya yafewa Saudat ya amince ta cigaba da aikinta kawai, tai masa godiya akai sulhu suka taho gaba dayansu gidan suka nufa anan suka tarar da Hajiya a tsakar gida, anan Ummi ta sheda masa ta ce sai ta kasheta ko ta bar mata gidan saboda Lawan nata nai ita ka dai.


"Karya kike wallahi Lawan namune mu hudu" cewar Saudat habawa nan ta fara zagin Lawan taci kwalarsa ya zabga mata mari ya fara dukanta, nan ta rikide ta fara jibgarsa sai da ta sumar da shi ta juya kan matan aiko ganin abun nata hauka nai suka rufar mata suma ashe Laila ma gang nai da ita, tai mata dukan tsiya da kyar aka rabasu Lawan ya farfado take yai mata saki uku a wajen saboda ya ce wataran kashe shi za tai.


Laila ta fara nakuda Doctor Saudat ta karbi haihuwar ta haifi yarta mace kyakykyawa anyi suna lafiya, Lawan ya nutsu ya rike matansa tsakani da Allah amma kowacce gidanta daban ya dena shan giya sai dai dan yawo wannan kuma sai a hankali za'a dena. Bayan shekara goma sha bakwai.


Yayan Laila uku yayan Doctor Saudat biyu duk mata yayan Ummi bakwai, amma suna cikin tashin hankali na lalacewar yaransu abun duk yafi karewa akan Laila saboda abun da suka kasance suna shukawa ita da Lawan, dan har wannan lokacin idan bala'in ya tashi suna yi Ummi ce da Doctor Saudat suka daina biye masa kuma ko a jikinsa lalacewar yaran nasa.


Yaran Ummi mata uku Babbar rons din ta ta ke ta biyun lesbian ta ke mazan ko duk nutsatstsu nai, yayan Doctor Saudat ko macen shekararta shida akai mata fyade wanda abun ya daga mata hankali, ta samu sun daidaita da iyayenta yanzu komai ya daidaita ta koma ga Allah.


Laila ko matan duk yawansu suke ma karuwanci yara kanana abun tausayi, sune manya dama namijin ko shekararsa sha biyu amma shaye shaye yake abun ya daga mata hankali sosai, tayi nadamar aikata abun da ta aikata ga yaransu duk sunki auruwa saboda abun da ubansu ya aikata, tun abun baya damun Lawan amma yanzu abun da mun sa yake.


Lawan ya zama babban mutum yanzu duk ya watsar da halayensa sai wanda ba'a rasaba dan har yanzu yaga mata yana lallabawa, ga Yaya a gabansa sun girma kullum a addu'a suke Allah ya shirya suna istigfari. (Allah kasa muyi kyakykyawan karshe Allah yasa mufi karfin zuciyarmu)


Karshe! Lawan ya shiryu shi da matansa amma Allah ya jarabcesu da yara fitinannu saboda abun da mahaifinsu ya aikata, suna nadama dukansu saboda yadda suka biyewa san zuciya wajen zabar san zuciyarsu basu zabarwa yayensu Uba nagari ba, gashi suna dana sani abun daya aikata na bibiyar yaransu duk da sun hade kansu musamman Ummi da Laila Doctor Saudat bata shi ga cikinsu, a karshe suna cikin tarin nadamar zabin da sukaiwa rayuwar su da ta yaransu.
*To fans alhamdulillah nazo karshe na ajiye alkalamina

Post a Comment for "TANTIRIN NAMIJI CHAPTER 7 KARSHE"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...