Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

TANTIRIN NAMIJI CHAPTER 4

TANTIRIN NAMIJI CHAPTER 4

- - Post a Comment
TANTIRIN NAMIJI

CHAPTER 4


Innalillahi wainna'ilaihir raji'un, Hajiya! Hajiya ta! girgiza ta yake iya karfin sa, ya sungume ta yai waje da gudu.


Haruna! Haruna! juya mota maza maza mu wuce.


Duka masu aikin sun fito hankalinsu a tashe, ganin Daddy yana wannan ihun abunda basu taba jiba.


Hankalinsu be gama tashi ba sai da suka ga Mommy a hannunsa, ga dukkan alamu babu rai a tare da ita.


Gaba dayansu suka yo kansu suna salati, wata tsawa ya watsa musu "ku matsa ku bani waje."


A sukwane ya shiga bayan motar dan tuni Haruna ya juya motar, ya fada ciki yaja suka bar gidan, suka nufi wani private hospital mafi kusa dasu.


Ko parking be gama bari yayi ba ya fito, kamar jaririya haka ya dauketa ko nauyin ta baya ji yai cikin asibitin da ita.


"Doctor dan Allah katemake ni, karta rasa rayuwarta dan Allah ka temaka mun" haka kawai yake furtawa.


Nan da nan Nurses suka amshe ta sukai emergency da ita, Doctor din na ciki nan da nan yai kanta ya fara bata temakon gaggawa, dan doguwar suma tayi ga dare ya farayi wajen 12.


Bayan awa daya karfe daya shaf, Doctor ya fito yace Alhaji yabi bayansa, bayan sun shiga office ya fara magana.


"Gaskiya Alhaji daba dan kunyi gaggawar kawota asibiti ba komai ze iya faruwa, dan jininta lokaci daya yai mugun hawa, saboda haka dole a kiyaye bacin ranta, idan ba haka ba zata iya rasa rayuwarta.


"Shikenan Doctor nagode, ayi duk abunda ya dace na kulawa da ita, zan iya ganinta yanzu.


Eh, "ba matsala zaka iya ganinta, amma bata bukatar hayaniya yanzu, san samu nema ace kaje gida ka dawo da safe, tunda bamu da bukatar masu jinya.


Fafur Daddy yaki tafiya yace anan shima ze kwana, haka ya kwana be rintsa ba.
****************


Maryam ce kwance rigingine akan kirjin Arfan, baccinsa yake hankali kwance ita ko saka da warwara kawai take.


A ranta sam babu wani namiji yanzu sai Arfan, amma tasa a ranta tunda ya gama lalata rayuwarta meyai saura, ai gwara kawai taci gaba da gashi tunda tasan ba ita ba aure a yanzu.


Amma a ranta tanajin ba wani namiji da zata iya bawa kanta sai shi Arfan din, duk da bata san maza ba, amma tabbas tasan cikakken namiji ne shi ta wajen saduwa.


Hakan shi yasa ta gwammace gwara ta tsaya a shi kadai din, amma kasan ranta tausayin Yar uwarta ne fal ranta da tausayin kanta, dan suna cikin tashin hankalin san abu guda a yanzu.


Musamman idan ta tuna Arfan mijin yayarta ne mafi soyuwa aranta, sai taji tai Masa tsana mafi muni a duniya, amma ba yadda ta iya, ya riga ya gama da ita, ya koya mata sansa a hankali.


"Tabbas zanyi rayuwa mara yanci, rayuwar bariki saboda haka mahaifina ya zabar min rayuwata,zanyi bariki zanyi suna amma bazan yarda wani namiji ya kara kusanta taba, Arfan Kai kadai zan cigaba da bawa kaina saboda kai ka lalatani."

Taci alwashin kodan ta koyawa Abbanta darasi akan san abun duniya, da abunda ya aikata musu, tasan dole yai nadama, tai wani murmushi me ciwo ta fashe da kuka.


Ya ilahi ta furta, jin haka ya farkar dashi ya kara rungumeta tsam.


Nan shedan ya samu dama ya fara kawata mata kyansa da surarsa, nan da nan taji wani abu ya soke ta aranta.


Haba Maryam meye na kukan, haka nifa nakine kema tawa ce, banga abun kuka haka ba, nasan kema kina sona,dan haka kiyi hakuri mu samu masalaha muyi auren mu.


Murmushi tayi ta boye kanta a kirjinsa, ya kara rungumeta, nan da nan salo yasanja ya samu hadin kanta sosai a wannan karon, ganin hakan ya kara sakankan cewa da ita.


Sai karfe goma da rabi suka farka, da sauri ta mike ta shiga bandaki tana ta astagfurullah, tai wanka tai sallah sannan ta dora abincin, tana kunna wayarta kiran Mama na shigowa.


Gabanta sai daya fadi, tana dagawa Mama tahau fada,"uban me kikeyi a gida har yanzu baki taho ba ."


Ummm gaba daya ta rikice, "Mama baya nan ne be kwana a gidan ba, yana ajiye ni ya tafi aiki, tun dazu na gama abinci ina jiransa yazo mu taho."


Hmmm! Wata ajiyar zuciya Mama ta saki, "to shikenan idan bezo ba ki hawo mota kawai kizo, dama banda rigima tayaya Alhaji zece kije gida ki kwana ke kadai."


"Wallahi ko Mama dakyar nai bacci dan gidan shiru ba kowa, bara na kira shi" a waya ta kashe wayar.


Ta saki wata nannauyar ajiyar zuciya, ta koma dakin yana kwance, amma ga dukkan alamu ya tashi yai wanka yai sallah, dan taga ga dadduma a shimfide kuma ta nade.


Da sauri ta matsa kusa da shi, ta rasama yaza tai ta tashe shi, a hankali ta matsa kusa dashi takai hannunta zata taba shi, jitai kawai ya fisgota jikinsa.


Kirjinsa ta fada nan ya fara hargitsa ta, yanai mata wani salo me tsayawa arai, wanda ya gama birkita mata lissafi, Allah ne ya temake ta wayarsa tai kara.


Idonsa yai jajur ya saki wani tsaki, ya jawo wayar ganin sunan Daddy yasa yai hanzari ya daga, yai masa sallama.


"Na'am, eh nine innalillahi wainna'ilaihir raji'un" ya saki wayar jikinsa yana rawa, kawai Maryam ya rungume ya fashe da kuka.


Itama rungume shi tai tsam tsam ta fashe da kukan, a hankali tana tambayarsa "lafiya meya faru?


A hankali ya bude baki, Mommy na Daddy na.........*Dedicated to: Mrs Ameenullah ina godiya sis Allah yabar zumunci ina jin dadin yadda kike mun comment nagode Allah yabar kauna**Nagaya muku so biyu zan dinga posting a sati dan Allah kuyi hakuri kudena yawan damuna private ina wasu books din guda biyu so dan Allah kuyi hakuri fans dana gama daya daga ciki zan dinga yi akan kari**Wallahi banjin dadi banyi editing ba idan kunga error kuyi hakuri**5-10*Ummi na shiga gidan ta fara ball da kayan da ta gani a tsakar gida na Laila tadinga zage zage tana kiran Laila ta fito su raba raini


Ta jika wanki ta daga kayan ta shekar a rijiya kayane masu tsada nata dana Lawan zata wanke ta dinga danne dannen ashar


Yaran ma korasu tai makota dan tasha alawa shin sai ta balla Laila yau a gidan gwara su zama saura su biyu a gidan


Jin shiru yasa ta haye sama dakin Laila ba sallama ba komai ta banka kanta dakin


Laila ce kwance a kasa laulayi take me mugun wahalarwa wanki ta jika amma ta kasa


Ko aiki bata jeba yau saboda wahala da cikin ke bata


Kawai ganin ummi tai tsaye akanta sai da hanjin cikin ta ya kada kamar cikin jikinta ze bare


Wuyanta ta damka ta shaketa a kwance ta haye kanta wallahi yau sai na kashe ki akan ki cigaba da zama da lawan


Ke nifa wallahi da kishiyar gida gwara ta waje nan ta fara dukanta ganin haka ta rarumo wata kwalba ta buga mata akanta wani mugun ihu ta saka ta dage wajen


Jini ne yake ta shatata ta kanta da gudu ta fice daga dakin itama ta rarrafa ta rufe kofar tana maida numfashi


Kuka ta rushe da shi wannan wane irin masifa ne wace irin rayuwace miji ba kwanciyar hankali kishiya babu ta kara rushewa da kuka


Lawan ne kwance dai dai a hotel shi da wata beb daya samu ana ce mata Yar gwal yarinyar ta gama tafiya da Lawan dan duk wata lugga ta bariki ta kware akanta


Lawan jiyai sam baze iya barin Yar gwal ba sai da yai sati biyu cif a wajen ta be leka gidan ba saboda gaba daya ya samu dai-dai dashi


Kwana suke suna diban juna bata gajiya itama gashi ta iya maganganun batsa yadda Lawan ke bukata


Gashi tana shan giya sosai shiyasa ta janye hankalinsa kwata kwata wayoyinsa ma a kashe suke yana dai lekawo office shima ba kullum ba kuma a makare ya kuma gudo da wuri ya tare rankata kaf a sabon gari gun karuwa Yar gwal


Laila kuma tana rasan ransa yanaso yasan halin data ciki musamman saboda cikin jikinta baya ganin ta a office anata tambayarsa yana bata da lafiya


Story continues below

Yau ta kama juma'at yau za'a daura auren Lawan da doctor Saudat auren da ba wanda ya sani ko matansa basu sani ba


An daura auren Lawan da saudat auren sirri sukai ba wanda yasan da wannan auren saboda saudat tace bata bukatar zama gidansa hakan ba karamin dadi yai masa ba


Momy kawar Saudat ce tazo tayata murna saboda ita kadai ta yarda tasan tayi aure sai kawarta data rakata gun malamin data kai ta ita ki bama ta kasar gaba daya


Yanzu Saudat kina ganin auren da kikai na sirri ze kai ki tudun muntsira kuwa wace irin rayuwace wannan kika daukarwa kanki


Dakata Momy bansan shishshigi saboda naga baki da surutu kinada amana na bari kika san maganar aurena


Aurena nayi shi ne da zuciya biyu na farko inasan nadau fansar wani cin mutunci da Lawan yai mun a asibiti na biyu kuma inasansa


Saboda haka dole Lawan yabi abunda nakeso saboda dorewar auren mu dashi wallahi sai na gasawa Lawan gyada a hannunsa badai shi Dan iskan namiji ba zan nuna masa shu'uman cin mu na yaya mata


Hmmm baki da wayo wannan ba hanyar daukar fansa bace kibar mutum kawai da halinsa musamman Lawan din nan da kinfi kowa sanin ainihin iskancin sa


Mtsww mubar wannan maganar kinsan har dinki nai masa yau ze fara zuwa yanzu ma me kunshi zata zo da kitso tai min kinsan amarya nake ayau


Bakin ciki kamar ze kashe Momy saboda haushin yadda Saudat tai auren sirri tana ganin abun ze bata matsala a gaba amma ita sam bata tunanin hakan
**************Buduri ake a gidan Alhaji Ghali na tashin hankali idan kaga yadda maza ke turuwar abun ze baka mamaki musamman yadda ya kasance manyan mutane ne wayanda ake mugun ganin girmansu a garin nan


Nauwara ce ta fito daga bandaki taga mutum a cikin dakinta fuskarsa a rufe ba abunda kake iya gani sai idonsa hannunsa wata sharbebiyar wuka ce


Ihu ta saka ta razana ta juya da gudu zata koma yasa kafa ya hardota jikake dam ta fadi a kan tiles ba karamar faduwa tai ba dan hakoran ta guda biyu sai da suka fita


Jini ya fara ambaliya ta hancin ta ta baki habu na labe sakon wadrobe ya rasa abunda ze dauka ya temaka mata dashi daga gefe ya hango butar jona ruwa dai dai kafarsa


A hankali yadauka shiko ya bita kasan ya haye kanta ya shaketa yana neman hallakata ya daga wukar ze daba mata habu yai kukan kura ya doka masa kettle a kansa


Tuni ya fadi warwas a kasa nan da nan jini ya fara ambaliya ta kunnensa amma saboda karfin hali ya daga wukar da niyyar sokawa Nauwara habu ya kara buga masa kettle akansa shike nan ya mutu a wajen


Nauwara tayi plat a kasa hakora biyu a waje kuka take me sauti tana nadamar auren me kudi datai da talaka ne da tuni tana rayuwarta hankali kwance


Hankalin Habu yai masifar tashi ganin yadda wannan me mask din baya numfashi yana daga mask din abun ya firgita shi saboda babban yaron Baby Chakwai ne yana mugun ji dashi


Duk wani ta'addanci shi yake sawa ha aikata kuma tabbas kashe shin da yai ba karamin barazana bane ga rayuwarsa


Zama yai dabas zaman Yan bori shima ya fashe da kuka saboda tsananin tausayawa rayuwarsa da yake yasan yanzu shi dai sai ta Allah ba abunda ze hana baby Chakwai besa an kashe shi b akan wannan tantirin


Shi kuka Nauwara a hankali ta mike zaune bakin ta na zubar da jini ta kalleshi waye kai meyasa ka temake ni daka bari ya kashe ni na huta


Tayaya zan bari ya kashe ki Nauwara bayan Allah ya jarabceni da kaunar ki tun kallon farko danai miku naji ina masifar kaunar ki ya matso kusa da ita


Yanzu yazami da gawarsa Nauwara meye shawarar ki akan gawar nan kigaya min dan Allah


Ajiyar zuciya ta sauke banda wata shawara banda ita taunani na ya tsaya ta fashe da kuka


Baby Chakwai shagali kawai ake sha burinsa ya cika ze rayu shi kadai da Alhaji Ghali dama burinsu duniya tasan yayi aure tunda har an sheda yayi auren komai ya kare meye amfanin zaman yarinyar a gidan


Yasha giyarsa yayi tatul ya kalli Alhaji Ghali ya sheke da dariya my sweetheart kaje ka fito da waccen jakar ta gyara ragowar dakunan munada bakin kwana tunda munada wadatar waje base sunje ko ina ba


Jikinsa na rawa ya mike ya shiga gidan Dan cika umarnin Babyn sa saboda bayasan abunda ze bata ran baby Chakwai musamman yadda suke kara samun kyautuka daga kasashen duniya na kungiyarsu


Dole ya rike baby Chakwai yarinya Yar yayi wadda kowa keso shi yayi dace duk da ya fara tausayawa kwadayayyiyar yarinyar data nane masa


Alhaji Ghali ne ya shiga babban parlour din a hankali ya karasa bakin dakin nata saboda jin tashin kuka da magana kasa kasa


Ya kasa kunne yaji Habu na fadin yazama dole na kashe idan ban kashe shi ba tabbas keze kashe kiyi hakuri mu nemo mafita kawai


Kofar ya shiga bugawa iya karfinsa fitsari ne ya subucewa Nauwara jikin ta yanata rawa kamar mazari


Ki bude duk abunda kuke fada naji ku bude kashe ni kike son yi ko to wallahi ta Allah ba taki ba kaf danginku dan ubanki yau zaki san nizaki kashe


Tayaya wani ya shigo mun gida wallahi sai na kashe ku dukanku gaba daya Nauwara ta gama firgita ta fice hayyacinta


Ganin haka Habu yai shahada ya mike ya bude kofar shidewa tai ganin ze bude ga gawa yashe a kasa yana zuwa ya murza key daya biyu
Maryam! "Mommy na asibiti rai a hannun Allah, Daddy kuma ya yanke jiki ya fadi," ya kara rungumeta ya fashe da kuka.


Tsananin tausayin sa ya ƙara kamata, bata san sanda ta rugume shi ba, tana share masa hawayensa.


"Kayi sauri mu wuce kawai" tashi yayi da sauri jikinsa ba kwari haka ya miƙe yana share ƙwallar idonsa ya nufi ɗakinsa, gas ɗin ta kashe kawai tasa abaya har ya fito suka wuce asibitin.


Mama ta kira cikin kuka, take sheda mata cewa Mommy da Daddy suna asibiti ba lafiya, sun wuce can kawai, su kansu hankalinsu ya ƙara tashi sosai, a lokacin Abba da Umma sunzo.


Abba ne ya kira Arfan ya tambaye shi asibitin da suke, ya sanar masa yace gasu nan zuwa shi da Umma, ya kashe hankalin Mama da Nafeesat ya tashi, musamman Nafeesat tana mugun son iyayen mijin nata.


Suna zuwa suka tarar Mommy tama farka, dan tana zaune tana ta rusgar kuka, suna shiga suka tarar da ita a zaune tana ta kuka kamar ranta ze fita.


Da hanzari suka ƙarasa kusa da ita, Arfan ya rungumeta yana rarrashinta, "Mommy wai lafiya meya faru? kun gama samu a duhu naɗauka wani mummunan lamari ne ya faru daku."ɗago kan da za tai taga Maryam a gefe tana hawaye, wani kukan kura tai ta kamo Maryam tana jibgarta kamar jaka, tana ihu "gwara na kashe ki da naga wannan baƙin cikin da kike shirin ƙunsa mun."


Arfan ne yai kanta ya fisgeta, "gwara ki kashe ni da ki taɓa mun Maryam! itace rayuwata Mommy, me tai miki ?idan na rasata tabbas kun rasani."


Ihu Mommy ta kwarara, "wallahi kinyi ƙaɗan annamimiya ki haɗa ɗa da uba sanki, wallahi ba wanda zaki samu a cikinsu muguwa munafuka."


Banda kuka ba abunda Maryam keyi, saboda batasan me taiwa Mommy ba take mata wannan dukan, gashi taji tana wasu mugayen furuci masu barazanar tarwatsa mata kwanya.


"Mommm.....myyyy ban.. gane...me kike faɗa ba" ƙinƙinar dole ce ta kama Arfan, saboda ji yake kamar saukar aradu saukar maganar a kunnensa, ganin ya sake ta ta ƙara rufe Maryam da duka.


"Wallahi sai kin rasa rayuwarki, mijin yarki da babansa kika yaudara kika sasu a tarkon ki, to wallahi barin irinku a duniya masifa ce, gwara ace babu ke inyaso nima a kashe ni azzaluma."


Ya isa haka Mom! ko meye tsakaninki da Daddy be damen ba, saboda haka ki rabu da Maryam, kar nai abunda zaki fushi dani akan Maryam, bana gane kaina a kanta, ita ɗin rayuwata ce, ita kaɗai nakeso a duniya."


Kuka Mommy ta fashe da shi, "lallai Arfan akan mace kake gayan haka? macen da ta haramta a gareka, kasan cewa yayar ta kake aure amma kake gayan haka? to ka kyauta, amma inaso kasani babanka ma ita yake so shi ne sanadiyyar zuwan mu nan.


Ihu Maryam ta kurma ta zube a wajen, yayin da Arfan ya faɗi jagwab, innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, "Mommy what!" ya faɗa da ƙarfi.


"Tabbas wannan babbar masiface da ta shigo rayuwar mu Mommy, amma Maryam bata da lefi, mune muka shiga rayuwarta, nine mutuɓ na farko da Maryam ta fara so, na tabbata bazato Daddy ba ni zata so, saboda haka karki nunawa Daddy nasan maganar zan."


Story continues below

Itama rushewa tai da kuka me tsuma zuciya, "tabbas Arfan hakane, banso naiwa Maryam haka ba, ni kaina yarinyar ta shiga raina, amma sheɗan yai tasiri a zuciyata, abun ya ƙara taɓani nasan cewa ƙaddarace wannan ta faɗawa ahalina, bata da wani magani a duniya sama da addu'a."


Wallahi baze yiwu ba ni kaɗai nake da Maryam, dan ni Allah Ya halicceta, wallahi koda san Maryam ze kashe Daddy ba zan bar masa ita ba, nima ita ce rayuwata." ya fashe da kuka.


"Haba Arfan idan rai ya ɓaci hankali baya gushewa, sai babanka ma ya aureta kai baka aureta ba, ko ka manta yayarta kake aure?" "haba Mommy ai ba uwarsu ɗaya ba ubane ɗaya."


"Banda baka da hankali a wane nassi akace ka auri yaya da ƙanwa? babu shari'a ta haramta ma, saboda mu musulmai ne ko a garin kafirai ban taɓa jiba, saboda haka addu'a itace kawai abunyi." ta miƙe ta ɗakko ruwan sanyi ta zubawa Maryam.


Duk da a cikin fushi take amma sam tana jin tausayin yarinyar, tai atishawa tana buɗe idonta ta gansu kamar yadda suke, "Allah na roƙeka karka ƙara maimaita mun wannan mummunan mafarkin da nayi, ina zan kai wannan abun kunyar?"


"Ba mafarki kike ba Maryam, ki nutsu miyi magana, kiyi haƙuri da abunda nai miki da farko, ke ƴar cikin cikina ce amma fushi yasa ni faɗa dake saboda kishi, tabbas dana samu haihuwa da wuri da nayi jika dake, musamman idan ya kasance cewa mace na fara haifa."


"Eh nasani Mommy, amma naji kina ta maganganu ko zafin ciwo ne, wallahi dukan be dame niba." Hmmmm! tabbas Alhaji ne ke sanki da ɗansa Arfan mijin yayarki ba mafarki bane." bata bari ta ƙarasa ba ta zura da gudu tana ihu, da mahaukacin gudu Arfan ya rufa mata baya.
 *****************Tunda Malam ya samu aka gama bikin Maimuna ya tattara kayansa ya koma gidan Indo. 


Ganin haka ya ɗaga hankalin Indo, ta dinga roƙonsa tana kuka tana hawaye akan yayi haƙuri ya koma gidan Haule, saboda bakin duniya yanzu za'a kafata a unguwa, amma fafur yace wallahi baze koma ba, tayi tayi yaƙi komawa.


Ƙarshe yai fushi yace "Indo zan bar maki gidan ki, tunda saboda kinga ina zama a gidan kine yasa kike mun haka, da ace gidana nane bazaki takura mun na fita na koma gidan da nake jinsa kamar maƙabarta ba. 


Hankalinta yai mugum tashi jin wannan furucin Malam, ta rushe da kuka "haba Malam meyasa  zakai mun haka? ina gujema fushin ubangiji ne akanka, ina guje ma surutun mutane akan ka."


Hmmm! Indo kenan, ke a karan kanki kinsan cewa ni ba jahili bane, ni nasan hakkokin Allah bazan bari na take suba, tunda kika ga na aikata haka akwai dalili kuma da kaina zan koma. 


Tsakanin mace da mijinta sai Allah, nan suka koma kamar basu yi ba, taiwa kanta karatun ta nutsu dan ta fuskanci tanada shigar ciki, shiyasa ta maifa hankali kan mijinta tunda ita Haulen bata damu ba.


Tun bayan biki Haule ta shiga bakin ciki da ɓacin rai, saboda ba abunda ta tsira dashi kuɗin data samu na biki ansace saboda rashin lafiyarta.


Gaba ƙafa duk yadda takesan ta taka ta fita abun ya gagara, ƴan gulma ne kawai ke sanar mata Malam fa yai aure ya tare a gindin Indo, dan asiri tai masa ba haka ta bar shi ba, saboda haka itama ta miƙe.


Ga ba ƙafa ba kuɗi, ƴan kayan da ta samu daga gun Nauwara duk ta bayar asiyar ai mata asirin itama, amma shiru kake ji ba wani bayani.


Maimuna suna zaune lafiya da Ustaz, zamansu gwanin sha'awa, dan harta fara lemo da kunun aya, ga ɗinkin ta tanayi shi ko yana ƙofar gida da tiredar sa yana chaji, Alhamdulillah sun samu cigaba me yawa.


A yaune suka wayi gari jikin Inna me koko yayi tsanani bata ko motsi, hankalinsu yai mugun tashi suka kwashe ta sai asibiti. 


Kwanan su uku jikin inna ba wani sauki sai a wajen Allah, gashi yanzu haka aiki zasi mata wai wani ruwa ne ya taru a cikinta, ga affendix aiki biyu kuɗin aikin kansa yafi dubu ɗari da hamsin.


Duk yadda suka so abun ya faskara, saboda basu da waƴannan kuɗin a halin yanzu, Maimuna ta gama yanke shawarar sai da firinjin ta ɗaya da keke ɗaya saboda ceto lafiyar Inna, saboda tsohuwar ta shiga ranta sosai, zama suke na amana ƴa da uwa haka suke bazaka ce surukai bane.


A yau ne taɗan samu damar magana kaɗan, suna zaune akayi baƙi masu bada tallafi a asibiti, har wata nurse  ta sanar musu su roƙe shi meyi ne ze musu, badan ran Maimuna yaso ba ta amince saboda Ustaz yai na'am da hakan. 


A hankali suna ɗan magana da Inna yau sama sama, mutumin da iyalensa suka ƙaraso, har ya miƙa musu temakon ya ya gifta, Ustaz ya bishi yai masa bayani, ya dawo da baya dan ya ƙara ganinta, waro ido yai  ya sulale a wajen a sume..........
Innalillahi wainna'ilaihir raji'un! dan Allah Alhaji ka rufan asiri ka tashi ka temaki rayuwata, dame zanji a wannan lokacin?


A hankali ya miƙe ya ɗebo ruwa me mugun sanyi a firij ɗin ɗakin, ya watsawa Alhaji Ghali da Nauwara lokaci guda suka dawo hayyacin su, banda kyarma ba abunda jikin Nauwara keyi shi kansa Habu a tsorace yake dakiya ce kawai irin ta maza.


Ganin sun dawo hayyacinsu yasa Habu yai maza yaje ya ƙara garƙame ƙofa, saboda kar wani ya sawo kai, hankalin Alhaji Ghali ya gama tashi, duk iskancin sa baya kisa bema taɓa ba, duk wanda ze iya kisa ma tsoronsa yake.


A hankali ya haɗiye wani mugun yawu me ɗaci da ciwo, "waya kashe shi a cikin ku? meyasa zaku kashe shi? ko kunsan babban na hannun daman Baby Chakwai ne?"


"Eh nasani Alhaji" cewar Habu "amma tabbas dabe mutu ba matarka ce zata mutu, nafi kowa sanin halin Baby Chakwai da mummunar aƙida ta tsanar kishiya, baya san a haɗa shi da kowa, wannan shine dalilin dayasa ya turo a kashe matar ka, saboda ya zauna shi kaɗai da kai alhali shi baze iya haka ba.


Kuka Nauwara take da nadamar mugun ƙwaɗayi irin nata wanda ya kai ta ga halaka, da taiwa babanta biyayya da tuni tana nan hankalin ta kwance, amma ga abunda san zuciyarta ya ja mata da zugar uwarta.


Habu ya kwashe duk abunda ya faru ya sanarwa da Alhaji Ghali, amma ya ɓoye masa cewar dashi aka kulle ƙofa, sai ya nuna jinsu yai suna tattaunawa, shi ne ya shigo ya ceceta tunda basu sawa ƙofar mukulli ba.


Jikin Alhaji Ghali yai sanyi ainun, a hankali yace "tabbas Habu wannan ƙullin Baby na ne, amma meyasa zatai haka? meyasa zatai mun haka? kashe Nauwara ai ta sani a bala'i da masifa, mezance da iyayenta? me mutanen gari zasu ɗaukeni? ai har gwara yasa na sake ta.


Haka zalika kashe masa babban yaronsa da kukai kun ƙara samu a masifa, baya yafiya baya haƙuri, yana matuƙar ƙaunar sa bansan dalili ba, kunsan da yaya na same shi? naci wahala sanar har yarda mukai auren jinsi."


_(Duniya ina zaki damu? har alfahari yake yaci wahala kafin ya saɓu ubangijinsa, wannan wace irin masifa ce muke cikin ta, Allah kasa mufi ƙarfin zuciyoyinmu, ka tsare mu ka tsare imanin mu ya rabb.)_


Jin Nauwara tai abun gingirin gim, kamar a kiyama gaban ubangiji ranar da kowa ze faɗi abunda ya aikata yake faɗar wannan mummunar maganar, da kansa yake faɗar kalar ta'addancin da suke aikatawa, kuka ta ƙara rushewa dashi.


"Kiyi haƙuri Nauwara nine na jaza miki, amma kema ke kika jawa kanki,mugun kwaɗayinki na masifa, kinsan cewa bake naso ba amma kika shiga kika fita, ba malamin ku yasa na aureki ba, kwaɗayinki ne yasa na aure ki, dan duk motsin ku a tafin hannuna kuke, kin san duk sammakon mutum wani a tafe ya kwana.


Story continues below

Amma duk da haka na riga na aureki, komai ya sameki ni za'a tuhuma, saboda haka yanzu ni zan magance wannan matsalar, Habu dole zaka bar gidan nan yanzu saboda gudun tonuwar asiri, akwai wata mota ta a bayan gidan nan, akwai wani gate wanda ba kowa yasan dashi ba.


Gareji ne wanda ƙofa akai ta cikin wani ɗaki a gidan nan, wanda iya hangenka bazaka gane ba, yadda kasan gini haka gate ɗin yake, kamar bayan gida haka yake da mota a ciki, amma hanyace saboda tsaro, ba wanda ya sani sai ni sai Allah sai maginan dana ɗakko daga asar ƙetare.


Kuma idan kabi bayan hanyace wadda ba mutane, hanyace da zata kai ka chan bayan unguwar nan kasna daji ne, zamusa wannan gawar a ciki da komai nasa har bindigar, idan kai tafiya me nisa zaka ga wani ruwa ka wullar ciki sai ka dawo, kaji maza ku tashi muyi komai akan lokaci kar Baby Chakwai yazo."


Cikin sauri suka sa gawar a chan surkukin bayan,  zakai zaton ɗaki ne ashe hanyace da ƙaton garage da komai, a hanyar ya kwashi gudu da motar ya nutsa daji saboda unguwar har yanzu ta baya ba mutane.


Nan da nan suka gyare wajen kamar ba'ai komai ba, a lokacin gaba ɗaya Alhaji Ghali ji yake jikinsa yai masa nauyi, mugu mugun tsoron Baby Chakwai ya ƙara ratsa shi.


Alhaji Ghali yaje yace wa Baby Chakwai ya buga taƙi buɗewa, ya sheƙe da dariyar murna da farin ciki, "bar jakar banza zata buɗe ne, koma kai ta bugawa akwai aikin da zatai mun yanzu." Ya koma ciki yana ta duba ko ina dan kar aga wata sheda, yasan Baby Chakwai ba mutunci, ga muguwar sha'awar Nauwara ta kama shi, amma shi sam baya san amfani da gaba, duk da wani lokacin yana sha'awar wajen. 


Lokacin matarsa ta fari yana saduwa da ita sosai yana gamsuwa, wajen haihuwa ta rasu, yana mugu mugun santa, tun daga lokacin ya tsani haihuwa, shi yasa baya yarda a haihu a gidansa, ya gwammace yai ta saduwa ta dubura ya nemi maza ƴan'uwansa, dama dokar da malaminsa ya bashi ce tunda yaje neman arziki da suna a duniya, kuma gashi ya bi dokar ya samu, yayi duk abunda yake buƙata a duniya saura lahira.


Minti arba'in da biyar Habu ya dawo, tuni Alhaji Ghali na gun bikin su duk da hankalinsa ba a kwance yake ba, kawai yaƙe yake Baby Chakwai ko abun nema ya samu, dan tasan buƙata ta biya, giya yake ta ɗibgawa cikin sa saboda murna da farin ciki.


Ta ƙofar baya Habu ya fice yabar gidan zuciyarsa fal tausayin Nauwara, da santa fal ransa yabar gidan, dan ba gidan zama bane wannan, baze zuba ido yaga ana wannan abun ba, yaso shima yayi amfani da ita amma yaji sam baze iya ba.


Ana wannan hidimar yace masa zeje yaga malaminsu, saboda harkar kasuwancin sa sunyi alƙawari yau, murna ya kama shi dan dama neman hanyar daze keɓe da wani tsohon saurayinsa yake, suna matuƙar jin daɗin juna da gamsar da juna.


Nan da nan ya amince masa ya bashi key ɗin sabuwar motar da aka bashi yanzu, duk dan karya shirya wani abu koya fita da gawar Nauwara, ya fice zuwa gidan bokansu za'a ce dan ba Malam bane.


Yana zuwa ya zayyano masa komai ya kuma sanar masa cewa tabbas Baby Chakwai yana cin amanarsa, abun yai wa Alhaji Ghali ciwo matuƙa, saboda shi a ganinsa ai aure sukai, saboda bashi da hankali.


Boka ya gyara zama ai ba abun ɓacim rai bane, tunda kaima kana da mace a gidan kaje kadinga saduwa da ita, ta dubura sannan ka dinga saduwa da ita ta gaba, idan tana al'ada kadinga yawan zuwar mata, shine zaka samu duk wani burinka ya cika, kuma kaga bakai ba haihuwa abunda bakaso kenan nasani.


Suka bushe da dariya ya ajiye masa damun kuɗi, bayan yasa aiwa Baby Chakawai ɗaurin baki game da lamarinsa da Nauwara, tama dena shiga lamarinsu dan ya tsorata sosai ne.

         ***************Laila ce take tsugune tana ta sheƙa amai kamar ta kwaranyar da kayan cikin ta, Ummi na daga ɗaki ta fito tana zaro ido ta ɗora hannu aka tana ta rusa ihu, "yau na shiga uku mezan Gani ni Ummi a gidana."


Ta ƙaraso ta ƙara duba ta ta duba idanuwanta, ta kuma sakin ihu "lallai nayi sake mugun sake, wato ni zaku munafunta, lallai Lawan ya cika munafikin maza cikakken ɗan duniya, ciki! ciki! a gidan nan wallahi ƙarya kike.


Ta fara dukan Laila iya ƙarfinta, "wallahi sai na kashe ki keda abunda ke cikin ki yau ɗin nan" gashi mugun laulayi take fama dashi, magana ma da ƙyar take balle ta iya bala'i harta kai ta ga dambe.


Ummi tafi Laila baki tafita masifa da bala'i, dan ba ƙaramar ƴar masifa bace, Ummi na da mugun kishi, dan tace gwara yaje yai barikinsa dama bata gani ba, amma kishiya fa baƙin cikin ta ze iya kashe ta, saboda tana kallonta akoda yaushe.


Laila kuma dama shashasha ce, bata da wayo kasancewar ta ƴar fari, hakan shi yasa Lawan ya sami galaba akanta, tun a waje ya koya mata kalolin iskancin sa, sunwa juna mugun sabo wanda bazasu iya rabuwa ba, sunfi shekara goma tare yana koya mata iskanci tana biye masa saboda so.


Dukan ta take tana ihu, kamar an wullo shi ya shigo gidan, daya shaƙi Ummi ya fara dukanta kamar baze barta da rai ba, da ƙyar ta samu ta kufce tai ɗaki ta saka sakata, suka dinga zage-zage  yadda kika san manyan maguzawa.


Laila kuka take me ciwo yadda Ummi ta maidata kamar jaka, sai da suka gaji da ɗure ɗuren ashar ɗin ya juyo kanta, "muje na kaiki asibiti mudawo naci uwarku gaba ɗaya, akan me zaku dingayi mun iskanci a gida, ke kuma jaka ki zauna tai ta dukanki, ya tallafeta suka je asibiti. 


Doctor ya dubata yace su jira result, bayan result ya fito ya tabbatar musu tana da ciki na wata biyu, kuma dan sunzo asibiti da wuri, daze iya fita saboda haka zata zauna tai rainon ciki a asibitin, saboda gudun wata matsalar.


Kuka take sosai shi kansa ya tausaya mata, "gaskiya Lawan baka da adalci, kasan baka fi ƙarfin gidan kaba zaka auroni, wallahi sai ka sakeni mugu azzalumi, wato ka tafi yawon karuwancin ka shiyasa ka manta dani gaba ɗaya, kuma kasan banda lafiya wannan jarabbiyar ta dawo kullum sai ta naɗeni kamar jakar ta, wallahi nima bazan yarda ba to.


"Ke ni kike gayawa maganganu san ranki? dan kinga ina tausaya miki, baki ga duk abunda nai mata ba ni da ke waya maƙalewa wani? harda zaki gayan magana haka, sa'anki ne ni?"


Ranta itama a ɓace "an gaya ma ɗin, kai abunda zakai, nima angayama tsoronka nake, banza ɗan tasha ɗan iska kawai."


Maza suka haɗu suna bashi haƙuri, cikin kuka tace 'kubar shi ya kashe ni mana, banza ɗan iska kawai, ko yanzu ka nunawa duniya cewa kai ne Lawan ɗan iskan namiji, cikakken ɗan bariki haihuwar kwalta.


Yayo kanta aka rirriƙe shi, "shi ke nan tunda kince haka, kije na sake ki saki ɗaya." Ya juya yai tafiyarsa ko gezau batai ba, kuka kawai take ana ta bata haƙuri, kowa ita yake bawa lefi, daga fannin maza, yayin da mata suke ɗora masa lefi.Caraf ta fada kirjin sa yai sauri ya rungumeta, daidai lokacin da Abba da Umma suka shi go, luuuu ta sume a jikin sa, daidai lokacin Arfan ya iso wajen.


Wata muguwar kutufo yai wa likitan, ya wafceta da karfi daga jikin sa ga rungume ta ana sa jikin yana huci, Abba suman tsaye yai saboda mamaki, Umma ko kuka ta fara shabe-shabe da hawaye.


Abba ne ya karaso yace "menene haka kukeyi? me yake faruwa?" cikin bala'i Abba ya fara fada, likitan ne yai karfin halin magana bakinsa har ya fashe, "wallahi Alhaji ina tsaye anan ina jiran nurse zan shiga tearter, naji kamar an wurgo abu jikina, sai da na duba naga macece ban ma san taba wallahi.


"Karya yake Abba dan iska ne kawai, tayaya zaka rungume mace haka ka sata a cikin kirjin ka, ba wani kunya ko tsoron Allah to wallahi sai munyi shari'a da kai, wallahi bazan bar abun da kai ya tafi a banza ba."


"Haba bawan Allah idan ni ban kararka bisa dukana da kai banji ba ban gani ba, ai kai baka da bakin da zaka ce za kai karata." 


"Ya ishe ni kai Arfan ka cika ta mana haka ka rungumeta haka, baka san asibiti bane," sai sannan Momy ta karaso jin shiru basu dawo ba har yanzu, ita ko Umma kuka kawai take saboda sam bata yarda da Arfan ba.


Ita taga lokacin da take gudu ta fada jikin likitan, hankalinta yai mugun tashi, doctor ne yace "Alhaji yarinyar nan fa ba'a hayyacinta take ba." Jin haka Umma ta karasa ta mika hannu ya bata ita.


Shiru yai musu abun da ya bawa kowa mamaki, ya basu yarsu yaki sai nishsi yake kamar wanda yai tsere,  ganin haka Abba ya matsa ya karbeta, luuu ta tafi "innalillahi wainna'ilaihir raji'un!" abunda kawai suka furta kenan.


Doctor yace "koda ta fado jikina ba numfashi a tare da ita, ya bari ma asan abunyi yazo yana haukan kishi akanta, tun da matarka ce ai kayi hakuri a ceci lafiyar ta, tun da a asibiti kake kuma kaga cikin halin da take ciki."


Umma ce tai karfin halin magana "dan Allah likita ka ceto rayuwarta karta mutu." "Kiyi hakuri Hajiya bazan taba masa mata ba yai mun wani sharrin, yanzu kina kallo daga fadowar ta jikina bisa kuskure abun da yake yi."


"Ba matarsa bace kanwar matarsa ce." Cewar Momy  "shakuwa ce a tsakaninsu shi ya sa." Abun yai matukar bawa doctor mamaki amma ya maze, "shi ke nan muje na dubata" shi ko bakin ciki ya cika Arfan, saboda ganinta da yai a kirjin wani shi ne babbar damuwarsa.


Story continues below

Wajen ya bari ya koma dakin da aka kwantar da Momy, ya hada kai da gwiywa ya din ga kuka kamar karamin yaro, a hankali a ka turo kofar aka shi go.


Momy ce ta zauna a gefen sa ta rungume shi, ta fashe da kuka ita ma, "wannan wace irin masifa ce ta shi go rayuwar gidana? ga babanka can rai a hannun Allah, saboda san da ya kewa wannan yarinyar, kuma likita ya tabbatar da cewa in dai be samu abuda yake so ba zuciyar sa zata iya bugawa."


Da wanne zan ji? kai kuma ga kalar taka masifar ta san kanwar matar ka, to na gama yanke hukunci wallahi ko yai wa kowa dadi ko a kasin haka, amma bazan zuba ido rayuwar gidana ta salwan ta ba." Ta rungume shi tana rarrashin sa suna kuka dukan su.


Duk maganar da suke a kunnen Umma tazo wajen Momy, saboda Abba na wajen Daddy ya farka yace a kirata, amma har yanzu jikin sai godiyar Allah, taji wannan batu fasa shi ga tai ta koma da baya tana rusa kuka. 


Ji tai ance "kiyi hakuri Hajiya zata warke, mun shawo kan matsalar firgita tai, akwai abun da ya firgita ta saboda haka yanzu sai dai kuyi hakuri har ta farko, amma karku tuna mata da abun da ya faru, ze iya kara jefa ta cikin wani halin."


Ana haka taga Momy ta fito a fusace tayi dakin da aka kwantar da Daddy, da sauri ta rufa mata baya, tana shi ga ta bita ta zubawa Daddy ido cike da tausayi da zallar so, "Alhaji in dai saboda ni ce na yarda na amince da bukatar ka, saboda haka ni zan nemi wannan alfarmar da kai na."


Wani zafin nama ne ya zowa Umma ta toshe mata baki, "kiyi wa Allah kiyi hakuri ki rufa maganar nan," tana maganar tana hawaye, ta bambare hannun nata da karfi, a she kin ma san komai, to wallahi abun da baze yiwu bane ko a mafarki.


Kiyi hakuri nasan kece mahaifiyar Maryam ga mahaifinta, ina rokon alfarma ku temaka ku aurawa mijina, baban Arfan mijin yar ku Nafeesat auren kanwar Nafeesat, ga baban Arfan ma'ana mijina Alhaji Kamal. 


Wata zabura Abba yayi ya mike, "me kika ce Hajiya?" "abun da na fada haka ne alhaji a rai na, ina so ka yarda ka amince da bukatar mu." Da gudu Umma ta fice tai dakin da Maryam ta ke, tana kuka kamar ranta ze fita.


"Maryam kin tarwatsa farin cikin mutane da dama, meyasa zaki mun haka ba kalar tarbiyyar dana baki ba kenan, dole akwai lauje cikin nadi game da zaman ki gidan Nafeesat, har ga Allah ba'a san rai na kike zaune ba, dan dai mahaifin ku yafi karfina ne ga kwadayi da san abun duniya da yai masa yawa."


"Hajiya kin san me kike cewa kuwa? "na sani Alhaji wannan shi ne dalilin daya kwantar da mijina a gadon asibiti da ni kai na, saboda haka muke rokon ka ni da shi akan wannan batun."


Yai shiru yana tunani "ka dena tunani Alhaji komai mun dauke ma a wannan auren, zaka samu manyan kyaututtuka daga wajen Alhaji ka kwantar da hankalin ka, kawai yardar ka muke nema kai ne mahaifin ta.


Jikin sa har rawa yake saboda san abun duniya, "Hajiya in dai ku kun amince ai ni me sauki ne a wajena, tun da ku kuka nema." wani kakkai fan abu ne kamar mashi ya soke Momy a zuciyarta, jin furucin Abba amma ta danne saboda tasan kishi ne.


"To mungode Alhaji sai a ta shi daga gado haka, na amince mahaifin yarinya ya amince, bukata ta biya sai ka mike." A hankali ya ta shi zaune fuskarsa cike da walwala, "nagode sosai Hajiya Allah ya biya ki jihadin da ki kai, ban da bakin godiya a agareki." "Ba komai" ta juya ta fice da sauri saboda hawayen da ya zubo mata.


Har yanzu kuka yake ta koma ta same shi a kwance lakadan yana hawaye, "dama ka hakura da kukan nan Arfan ka rungumi matar ka, saboda a halin yanzu an riga an bawa mahaifin ka Maryam." "What?" ya fada da karfi ji kake tim ya fadi.  
       *********************
Innalillahi wainna'ilaihir raji'un! shi ne abun da mutanen dake wajen suke fada, kafin kace meye wannan likitoci sun dauke shi zuwa emergency, iyalansa kuka suke suna cewa su Maimuna mayu ne, wallahi idan ya mutu sai sun yi shari'a dasu, suma sai sun kashe su sun bi hakkin babansu.


Tashin hankali ba irin wanda basu shi ga ba, saboda wannan sharrin da akai musu, kafin kace kwabo Yan sanda sun zagaye su da duk wanda ke dakin, dan sun ce binkicen ya shafi kowa.


Kuka Maimuna ta ke tana addu'a a ranta,  ta kalli Ustaz Bello "sai da nace ma ka bari na sai da keke na daya da fridge amma kaki, ga shi yanzu bamu ji ba bamu gani ba kaddara ta fada mana, da ace mun siyar da yanzu an mata aikin." ta kara rushewa da kuka me tsuma zuciya. 


Kiyi hakuri matata, tabbas ke Yar aljanna ce, wannan kaddara ce ta bakin naki, amma ba komai Allah shi ne gatan mara gata, shi ze fitar mu daga wannan mummunan zargin.


Duk wanda ke wajen ya tausaya masu ainun, amma wasu mutanen sai tsine musu suke suna mayune su, Allah ne ya tonu asirin su dama wannan kyan nasa shi da mahaifiyar tasa ai daga gani mayu ne. 


Kusan awa uku sannan wannan Alhajin ya farfado, yana farfado wa ya fara kiran 'Tata! Tata!" likitoci su kai kansa, ya tsai dasu "ku kai ni wajen yar uwa ta, ku kai ni naganta." Ya fashe da kuka kamar karamin yaro.


Nan da nan aka kira matarsa da yaransa, suka shi go suna kuka "Amina ki tayani yiwa Allah godiya, yau Allah ya nuna min Yar uwata Tata, wadda nake baki labari ita kadai ce ta rage mun a duniya." 


"Wacce kake nufi Alhaji? kad dai  wadda ka yanke jiki ka fadi a wajen da suke?" "eh ita ce, ita ce ku kai ni naga yayata." 


"Innalillahi wainna'ilaihir raji'un! Alhaji rashin sani yafi dare duhu, ai mu mun dauka mayu ne, mun kai Yan sanda suna gadin su saboda kar su gudu, ganin lokaci daya daga ganin su ka suma haka." 


"Yasalam muje dan Allah kar wani abu ya samu yayata, muje Amina." Da hanzari ya sakko daga gadon suka nufi dakin, daidai lokacin jikin yadan lafawa Inna me Koko, ta dan farfado tana ta bawa Maimuna baki, ta dauka saboda lalurar ta take kuka.


Suka karaso wajen kowa kallon su yake cike da mamaki, yana zuwa ya rungume Inna me Koko, abun da ya bawa kowa mamaki kenan! "Yaya Tata dama zan kara ganin ki a duniya baki rasu ba?" duk dakin mamaki su kai karma Bello da Maimuna suji labari, sun zama kamar gumaka.


A hankali ya daga ta murna fal fuskarta, "Ahmad maza daga ni zaune yau na ganka" da sauri Bello ya temaka masa suka dagata, ta kara rungume shi suka din ga kuka, "Ahmad ina su Addar mu? da Baffana? da Yan uwana?" ya share kwallar sa "Yaya kowa ya rasu a wannan lokacin, ni kadai nai saura da dukiyar mu, nida Baffa munzo garin nan neman ki bamu same ki ba.


Haka mu kai ta garari ga kadarorin mu na gwalagwalai da lu'u lu'u, mun neme ki mun rasa, har Allah ya hada mu da mahaifin Amina, shi ya temaka mana aka seda su suka zama kudade, wanda bansan adadin yawan su ba a lokacin, babanmu ya raba kaso biyu yace ni daya, daya na kine in ajiye har Allah ya hadamu, shi yasa nake yawo dasu duk inda zani, mu kadai muka rage ko bayan ransa.


Mahaifin Amina shi ya tsaya mun nai karatu na, ya bude mun kamfanoni wanda suke aiki a yanzu, Baffa ya rasu da dadewa yaso ya ganki Allah beba, amma Alhamdulillah! yau zan sauke nayin dake kai na, duk wata dukiya taki tana nan a hannuna sisi ban taba ci ba, kullum juyawa ake ana adana miki.


Amina ki zama sheda yau zan cika tsohon alkawarin mahaifina na bawa yaya ta dukiyar ta, dakkon jakata a mota." Ana kawowa ya zaro wani file ya mika mata, tana kuka tana bata so ita ta bar masa, ga dan ta nan ya kula mata dashi, amma dole suka sa ta karba. 


Ta rungume yaransa da matarsa, ta damka file din ga Bello, na baka halak malak wannan naka ne dana me biyayya, Allah ya saka ma da gidan aljanna kai da matarka, burina ya gama cika naga ahalina ko yanzu na mutu Bello baka da matsala, kana da gata a duniya ga kanina nan shi ne a matsayin mahaifinka.


Ta rungume su dukkan su sannan ta kankame dan uwanta tana hawaye, kunsan minti biyar bata cika shi ba, ya zare jikinsa ya ga ta tafi ragwaf, ya taba ta ba wani bayani, nan da nan ya kira doctor yana zuwa ya dubata sosai, kawai yaja zani ya rufe ta ruf gaba daya dakin ya kaure da salati.


Wani kallo maimuna ke musu kamar almara, wai me kuke nufi ne bangane ba? yayana me hakan ke nufi naga an rufe Inna kowa na kuka?"


Alhaji Ahmad ne yai zaman Yan bori a kasa ya fashe da wani gurshekan kuka, Allah ya jikanki Tata, Allah yai miki rahma, jiri ne ya kwashe ta ya buga ta da kasa, da gudu su kai kanta anma taje kasa.

Post a Comment for "TANTIRIN NAMIJI CHAPTER 4"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...