Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

KE NAKESO CHAPTER 4KE

KE NAKESO CHAPTER 4KE

- - Post a Comment
KE NAKESO
CHAPTER 4
Tun randa Alhaji Yusuf ya bar gidan su, ba ta sake zuwa wurin aiki ba, hakan ya sa ran laraba da yamma, sai ga Walida ta zo.

    

"Mai-jidda lafiya kuwa kwana biyu muka jiki shiru?"

                              

"Ke dai kin faye damuwa. Yaya Mai-gidan? Ina Dan hutawa ne, ko ke ma za ki shiga layi?"

                              

"Lafiya kalau. Maganar gaskiya na ke miki, me ya faru?"

                              

Nan ne Mai-jidda ta fada mata duk abin da ake ciki.  

                              

"To don kin rabu da Alhaji Yusuf, shi ne za ki daina zuwa aiki, mu ma ki watsar da mu? Aikin ki fa wa ki ka barwa? Kin san dai ni ba zan miki ba, don haka ki shirya gobe, daman ki dawo".

                              

"Me zan dawo na yi? Oh na manta kin san ran Asabar daurin aurena?"

                              

Walida ta dubi Mai-jidda, sannan ta dafa kafadarta cikin kulawa. "Ki kwantar da hanakalinki, tunda dai ana addu'a. Insha-Allahu alkhairi ne."

                              

"Yaya na iya idan ban kwantar da hankalina ba? Jiya suka kawo lefe, ga shi can a dakin Umma, ya dauka wani abin sa zai burgeni, bayan na san duk karya ne ya tsane ni".

                              

"Allah ya ganar dake kawai, zan iya cewa, ni tashi mu je ki nuna min na gani."

                              

"Wa ni? Allah ya sawwaka ko kalan akwatunan, ban sani ba, ki yi sallama dakin Umma ki duba."

                              

"Tunda na zo kam, ai sai mu kalla tare idan kunyan su Umma ki ke ji."

                              

****

                              

Ranar Juma'a sai ga Yaya Maryam da yaranta su, a dole sun zo aure, kallon su kawai take yi, don duk abinda ake yi tana kwance. Sai sallah ke tada ita. A daki ta shigo ta sameta. 

                              

"Wai ke Mai-jidda me yake damunki ne haka? Ace mutum ya rinka daukar zafi da rayuwa haka idan za ki warware ki shiga jama'a gwamma kin shiga, me ki ke son mutane su yi tunani idan suka ga wannen bakin halin da ki ke yi?"

                              

"Yaya Maryam me za su yi tunani kuwa, banda ina alhinin rashin mijina da ya rasu, wanda kuma hakan ne."

                              

Yaya Maryam ta zauna a gefen gadon Mai-jidda, sannan ta-ce. "Ni da ke mun san cewa wannan ba shi da sauran amfani a wajenki, kwarai ba zan hana ki tunanin Dokta ba, amma ya kamata ki rinka boye damuwarki, sabuwar rayuwa za ki soma.

                                              

                        

 Ta Yaya za ki zauna da mijinki, bayan ki na kwance kamar tsumma cikin tunanin mijinki da ya rasu?"

"Yaya Maryam ko ban yi tunanin Rayyan ba, dole ne ya zo min, saboda ba yadda za ayi duk wayewar gari ina ganin Abdul-Aali, ban tuna Dan-uwansa ba. Ki fada min ta inda za ayi zaman wannan auren?"

Yaya Maryam ta yi murmushi, sannan ta-ce. "Na fahimce ki, amma kuma ina son ki dubi Abdul-Aali a wata fuskar daban, shi za ki aura, ke yake so, kuma don me ya sa za ki tauye wannan a tsakanin ku?

 Shin kin san halin da shi yake ciki? Kin san daurewar da ya yi ya fada miki bukatarsa, duk da ya san ba za ki karbe bakuncin hakan da kyau ba. Yana son matar sa, amma haka suka samu sabani da ita.

 Saboda zai kawo ki gidan sa. Ki na tsammanin baya fuskantar matsalolin da ke ki ke fuskanta ne? Sannan wannan auren, sai dai jama'a su ki shi, amma ba an haramta miki shi bane a addini."

Mai-jidda shiru ta yi tana jin Yaya Maryam, yaya za ayi ta manta wannan ranar a rayuwarta...

Bakinsa ya bushe sosai, sai na'urar jikinsa ke wani kara da sauri da sauri ta juya ta dubi Mama dake tsaye jikin gadon Rayyaan, sannan ta-ce. 

"Mama zai mutu ko?" Cikin karyewar zuciya. Mama ta ja ta jikinta ta rungume, sai kuka suke yi. Abdul-Aali daya ke zaune a gefe bai hana Jidda kuka ba ranar, saboda shi ma da zai samu da zai yi domin a kan idanunsa yana kallo dan -uwansa yana wahala, ba yadda za ayi ya cire masa wannan wuyar. Sannan ransa a hannun mai duka yake.

Kamar yadda ya saka masu kaunar Rayyaan a zukatansu. Haka nan Shi yake rike da ran abinsa, duk kuma lokacin da ya ga dama, zai iya karbar kayan sa ko kuma cikin rahamarsa ya ba shi waraka.

 A hankali ya daga hannu ya rike na Mai-jidda, yayin da ya numfasa, sunan Muhammad, da sauri ta bude kofar ta shigo da Muhammad, a hannunta wanda yake zaune da su Mukhtaar a waje. 

Shafa kan yaron ya yi domin a lokacin magana yana ba shi wahala. Runtse idanunta ta yi cikin jin radadin da yake ji a zuciyarta, ta fita ta kira su Mukhtaar da su Suwaiba hade da ce masu "Ku shigo Dokta..."

 A sanyaye ta koma dakin, tana ganin yadda 'yan-uwan suke masa addu'o'i, idanunta cikin nasa ya yi mata murmushi. Dansa na gefen sa, ya yi wani numfashi, nan take Mama ta fita da yaron a hannunta, amma Mai-jidda tana tsaye ki kam, sai da ta ji murdadden harshensa yana salati ne, ta yanki jiki ta yi kasa kafin a tare ta...

Nan ta fashewa Yaya Maryam da kuka, sannan ta-ce. "Na gode Yaya Maryam, na amince Dokta ya bar ni kuma lokaci ya yi da zan fuskanci rayuwata, na yi sabon gini na kuma inganta rayuwar Muhammad, koda kuwa ya kama na zauna da mutumin da na fi tsana a duniya ne."

Murmushi Yaya Maryam ta yi, ta san Mai-jidda tana yaudarar kanta ne, amma tabbas tana son Abdul-Aali. 

*******

Babu rikicin da ba su yi ba da Hamamatu kan tafiya Kano. "Kai ne za ka yi aure, ni kuma me zan je na maku a can. Ku sha bikin ku lafiya, ko so ka ke yi na je na yi ta maku aikin bauta, ku na shan amarcin ku?"

Kallonta kawai ya yi cikin tausaya mata, tabbas ya san yadda Hamamatu take son sa, wannan ya sa ma ya ba ta waje a zuciyarsa, bayan haduwarsu da ita, abu kamar wasa daga gidan abokinsa suka saba.

 Kullum idan ya je gidan cin abinci, sai ta zauna a falon wai ya faye tsumewa, yana bukatar abin da zai sa shi farin ciki a rayuwa, kanwar matar abokinsa ce. Ba a dau lokaci mai tsawo ba, ya fahimci son da take masa mai tarin yawa. Wannan ya sa a hankali ya sabarwa kansa da Hamamatu, dole ya san halin da take ciki yanzu. 

Don haka ya rabu da ita. Maganar tafiya Kano, shi din ma ana daura aure zai koma PH. Haka ya gama shirin sa, ya kama hanya. Hamama ta ci kuka randa Abdul-Aali ya tafi, don sai da ta yi zazzabi. Yana zuwa gidansa, ya fara zuwa ya ga aikin da ake yi kafin, ya wuce gidan Abba.

                

                        

Nan ya zauna a falo a gajiye. Mama ta shigo ta-ce. "Ina su Mimie kuma na ganka kai kadai, ko gida ka bar su?"

"Mama ai ba su taho ba, ganin ba dadewa za mu yi ba, daga daura auren, ni ma zan juya, hakan ya sa nace su yi zamansu".

Mama ta dube shi, ta san dai da wani bayanin, bayan wannan, don haka ta-ce "To shi kenan, Allah ya sa a gama lafiya. Da safe ne za ka wuce Dutsen ko kuwa yau za ka tafi?"

"Sai da safe Insha-Allahu, saboda akwai bakin da za mu wuce tare." 

"To, Abdul-Aali yanzu ka ga za ka kara iyali, abu guda da zan fada maka shi ne sai ka yi takatsantsan sosai, don sha'anin hada mata sai a hankali.

Dole ka kasance mai hakuri da rashin gaggawar yanke hukunci. Ka kamanta adalci tsakanin matanka, sai ka ga kansu ya hadu. Amma da zaran ka fidda wani bambanci, to ka kawo wa kanka damuwa kenan. Ka ji tsoron Allah. Allah ya taya ka riko, ya hada kawunanku."

"Na gode Mama. Insha-Allahu zan kiyaye. Ku yi ta samu a addu'a".

******

Mai-jidda tana zaune a dakinta cikin gidan, sai hayaniyar bakin kusa da 'yan-uwa ke tashi, ta rasa ma wanda duk ya gayyace su a cikin kankanin lokaci. Ga su nan dai sun cika gidan. Walida ce kawai a cikin kawayenta ta zo, don ba wanda ta fadawa batun auren.

 Mabruka ma a waya ta fada mata, don sun riga sun koma. Har take mata tsiya. "Wai wannan auren na ku na rowa.

 Sai da ku ka bari mun koma za ku sa rana ko?" Ta ji mamaki kwarai yadda har aka sa auren kusa-kusa, ganin suna tunanin Mai-jidda ta-ce ta fasa kafin ayi. Don haka fatan alkhairi kawai ta bi-ta da shi. 

A safiyar ranar ta daure ta kira Dan Kano, saboda yanzu lokacin rabuwarsu ya yi a karo na biyu. Suna magana ba ta san lokacin da hawaye suka zubo mata ba. Yaya aka yi take son mutumin da ba ta taba gani ba?

Sannan take kin mutumin da ta sani ciki da bai. Kwarai Allah bai kaddari haduwarta da Dan Kano ba, wannan ba karamin ciwo yake haddasa mata ba. Tana jin muryarta, ya fara rawa a sanadiyyar kukan da idanunta suke yi, ta yi saurin kashe wayar.

Sako ne ya shigo wayarta. "Why, Hauwa me ya sa za ki aure shi, bayan ba kya son sa, har cikin ranki?"

Wane amsa za ta ba shi yanzu? KAI NAKE SO. Ba mijin da za a daura min aure da shi ba nan da awa daya? Ai da kunya ma. Don haka ta-ce. "Saboda ina addu'a kamar yadda ka fada min, tunda kuma na ga abin da yake faruwa na qudurtawa raina zabin Allah kenan a tare da ni.

 Amma kafin nan, wannan lokaci gudan zan fada maka cewa na yarda zan iya bawa wani gurbi a zuciyata, wata kila kuma na riga na bayar. 

Allah ya baka sa'a a rayuwarka. Abu daya da na ke son kayi min, shine don Allah ka manta da ni, tunda haka qaddarar mu take, mu ba masu haduwa bane, may be HAR GABAN ABADA!"

Dan Kano ya yi murmushi, ya juya ya ga jama'ar da suke tuttudowa, don daurin auren Hauwansa. Ajiyar zuciya yayi, ya rubuta mata. "Na bar ki lafiya, kuma Insha-Allahu za ki yi farin ciki da zabin Allah a gareki."

Tana kuka ta ke kallon Screen din wayar, wannan wane irin abu ne yake faruwa da ita? Tana son Dan Kano tuntuni take tunanin ko Alhaji Yusuf take so, sannan ita ba ta auri Alhaji Yusuf ba, ba ta auri Dan Kano ba, ta buge da auren mutumin da ya fi kowa tsanarta.

 Tsabar ya gwada mata hakan ma, don ya sa ta dole ta aure shi, jingina mata sharadin auren ya yi da zaba mata miji da kansa, ko kuwa daukar Muhammad daga gareta. Wane mutum ne, zai so raba uwa da Danta, don kawai wani abu nasa da ya ke son cimmawa? 

Walida ce ta shirya mata kayayyakinta tsab! Don ana daura aure za su tafi Kano. Muhammad na manne jikin Mamansa, saboda yadda ya ga ta sha kuka, sai ya zaci ko ba ta da lafiya ne gaba daya ya ki ya saki jikinsa. Umma ce ta shigo ta-ce A'isha ta fita da shi ya yi wasa. "Idan kin gama shiryawa. Babanku yana so ya miki magana".  

                

                        

Ita tunda ta ji an shafa Fatiha, zuciyarta take ta faman bugawa uku-uku, bare da Baba ya sa ta a gaba da nasiha, sai ta ji gaba daya ta tumurmushe ta zama tamkar wata karkashi. Karfe biyu motoci suka iso, saboda daukar amarya.

 Don mugunta ko ma ya-ce zai bari ta kimtsa a tsanake, ganin anyi auren ba shiri, amma kuma Yaya Hamza yake ce mata Baba ne ya-ce ta tafi, duk wani shirin da ba ayi ba, za ayi shi daga baya. 

Haushin komai take ji, amma ba yadda ta iya, su Anty Fauziyya da Walida ne suka yi mata rakiya zuwa Kano. Rabonta da Abdul-Aali tun randa ya kawo katunan daurin aure. 

Gidan Abba aka kai ta tukun, gaba ki daya ji take yi kamar wani mummunar mafarki take yi, wanda za ta farka, ko wane lokaci ta yi Isti'aza, amma ina, gadan-gadan. Mafarki dai ya ki karewa, hakan ya sa ta yarda cewa komai da gaske ne.

Dakin da ke gefen na Mama aka saukesu, daman nan ake kawo amare idan anyi aure a gidan, kafin a kai su gidan mazajen su. 

Tana nan dai, ba yabo, ba fallasa. Abin mamaki, ta nemi kuka ma ta rasa shi, ashe sukuni ne samun yin kuka, don abin da take ji a zuciyarta, ya fi karfin duk wani tunaninta. Nan su Walida suka kwana. Washegari ta bi su Anty Fauziyya suka tafi. Ta yi wanka da safe, tana sake da wani lace mai laushi mai kalan ruwan madara, fuskarta ba kwalliya, bayan hodar da ta shafa. 

Sai man baki. Ta na dai cikin halinta na kullum, musamman da su Walida suka tafi sai ta ji ta takura, tunda sassafe da ta gayar da su Mama da Abba, ba ta sake fita ba nan ta zauna. Karfe goma ya shigo dakin da take. Kamar yadda yake tsammani ko kallo bai isheta ba, bai zauna ba shi ma.

"Kin tashi lafiya?"

Da kyar ta amsa masa. "Ki shirya anjima za mu tafi can gida, sai ki karasa kimtse-kimtsen ki, don gobe za mu tafi Insha-Allahu".

Wani kallo ta dallara masa, wanda ya so ya ba shi dariya, amma ya matse yana jiran abin da za ta ce "Mu tafi ina? Ai ni yadda ka gannin nan albarkacin su Mama ka ci har aka shafa Fatiha, don haka a nan zan zauna, ba inda zan je".

"Na ji na samu albarkacin su Mama, amma dai kin san da Abdul-Aali aka daura miki aure ko? Kuma duk inda yake son ya ajiye ki, nan zai kai ki. Don haka ki shirya anjima za mu tafi. It's an order". 

Ya fada tare da juyawa ya fice a dakin, yana ji ta wurgar da wani abu, ya bugi jikin bango. Murmushi ya yi ya-ce. "Ai sai kiyi kuma dai." Mama ya samu a daki suka gaisa, sannan ya-ce yana son abin karyawa.

"Ai kuwa ga shi nan na ajiye maku tun dazu. Hauwan ma tun safe da ta fito ta koma ba ta sake lekowa ba." Nan ta sa baki ta kira Yahanasu. "Yahanasu kira min Anty Hauwa".

Yayi shiru bai ce komai ba, har ta shigo falon. "Hauwa ga abin karyawarki, har ya fara sanyi, ki zauna ku karya."

Ba dama ta-ce ta koshi, don asalin yunwa take ji, amma kuma ganin Abdul-Aali a wurin, ya sa ta ji kamar ta manta da yunwar cikinta. Dan kadan ta deba har ta matsa gefe za ta fara ci, ya-ce "Hada min Tea, kar ki cika Sugar sosai".

A hankali ta mike ta dau (Mug) din kamar ta fasa masa a kai take ji, ta hada komai. Tsabar isa ga komai da komai, ya sa hannu ya hada ne, ba zai iya ba, sai anyi masa. Don matarsa ta saba shagwaba shi, zai yi tunanin ita ma haka za tayi masa, lallai yana da aiki.  

Yana gama cin abincin, ya fita zuwa wurin Abba. 

Ta shirya kamar yadda ya bukata, kasancewar ba yadda ta iya ya fadawa su Mama za ta koma gidanta, amma kam ran na tan nan bakikkirin! 

Sai da dare suka tafi, ko a mota bai ce mata komai ba, saboda ya san idan ya yi magana, to fada zai janyo, tana ta tunani, wai yau ita-ce za ta shiga gidan Abdul-Aali a matsayin matarsa.

                

                        

 Daman kayanta kam sun rigata isa. Yaya Hamza ne ya hado sosai. Baba ma ya mika, wanda zai iya suka tattara suka kawo mata, ita da ma sun hakura sun yi wani abu mai amfanin da kudinsu, don ita kam wannan duk ba a gabanta suke ba.  

Kayan da ta taho da su jiya ne kawai a motar. Za ta iya kirga sau nawa ta je gidan nasa, sai dai yanzun da suka shiga gate din, ta ga fasalin ya canza, da alama anyi gyara ne. Shi a dole zai yi amarya. Hmmm!

 Shi ya yi mata jagora har cikin gidan, ya sa makulli a kofar da take tunanin nan ne sashinta, don gidan a hade yake, amma ta tsakar gida kowane side yana da back door dinsa. Mai-gadin gidan ne ya shigo mata da jakunkunanta. Falon babba ne sai kuma kofa daya da ya kai ta zuwa corridor mai dauke da dakuna biyu.

 Kowanne da bandakin sa a ciki, sai daya kofar dake falon, kuma na kicin ne. Bayan ya nuna mata dakin ne, ya bi dayan kofar inda take tsammanini sashinsa zai kai ta. Kwafa ta yi, sannan ta ajiye mayafinta ta shiga alwala. 

Tana addu'a, ta ji shigowar sa, sai da ta idar ya-ce. "Idan kin gama, ga abinci a falo". Daman Mama tayi masu guzurin abinci, sannan suka taho.

"To" kawai ta ce masa, ta kula wani kama kai yake yi. Sai dai ya karata, amma tunda ya sa ta yin wannan auren, to shi ma dole ya ga abinda bai masa ba. Key ta sa a kofar, sannan ta shiga wanka, ta sa wata doguwar riga Ja.

 Ta yafa siririn gyalen Pashmina a kanta. Daman can ita ma'abociyar kamshi ce, duk da kayanta da kamshinsu, sai da ta sake sa turare mai sanyin kamshi, saboda Allergy dinta. Sannan ta fita zuwa falon. 

Ba ta same shi ba, wannan ya ba ta damar sakewa ta ci abincinta a tsanake, ko a wane hali Mamin Mimie take, sai Allah. Ya baro ta can cike da damuwa, bayan ya san ba abinda zai amfana da ita Mai-jidda.

 Tunani kala-kala take yi, tana gama cin abinci, wanda ba sosai ta ci ba, kasancewar cikinta ya toshe. Ta kai Plate din kicin, fitowarta ne ta same shi a falon, yana sake da T-shirt da Jeans. 

Don haka kanta ta daga ta wuce hanyar dakinta, amma sai ji ta yi Abdul-Aali ya tare mata hanya, yana duban idanunta ya-ce. "Ina za ki je?"

"Ina ka ajiye ni, da ka kawo ni gidanka?"

Kada idanunsa ya yi ya-ce. "Jidda me ya sa ba ki da sassauci ne?"

"Sassauci? Daman ka na tunanin samun sassauci bayan abin da kayi min? Lallai kana son kanka da yawa."

Hannayenta ya rike ya-ce. "Jidda..."

Idanunta a rufe ta-ce. "Kar ka fara tunanin komai a ranka."

"Ba tunanin komai na ke yi ba, faruwa yake yi, kuma ke ma kin sani, KE NA KE SO".

"Tun wane zamani?" Ta tambaya cikin bacin rai.

Kawar da kansa gefe ya yi, ya sake mata hannayenta, ya bude baki zai yi magana. Sai kuma ya rufe, da kyar ya iya ce mata. "Ba na tsammanin kin shirya jin duka labarin tukunna."

"Ka yi daidai da ka fadi haka".

"Ina son ki fahimce ni, kafin mu koma PH, ya kamata mu zauna mu yi magana".

"Me zai hana mu fara yanzu? Me ka ke zaton Dokta zai ce idan ya ganka kusa da ni haka?"

Murmushi ya yi, amma iya baki, sannan ya-ce. "Dokta ya rasu, sweetheart. Mu kuma muna raye." Mai-jidda ta runtse idanunta, tana fatan kunnuwanta su toshe ta huta.

"Kuma ina ga zai so da ni dake duk mu kasance cikin farin ciki."

"Wa ya-ce maka ina bukatar na kasance cikin farin-ciki, ko kuwa ina bukatar farin-cikinka? Rayuwata yanzu ta ta'allaka ne akan Dana da kuma aiki na, ba farin-ciki a lissafina..."

A hankali Abdul-Aali ya sa hannu a wuyan Pashminan dake jikinta yana ja har sai da zaren gezan ya iso wuyanta, yana gogan fatar wurin, idanunta a rufe, saura kadan wani sauti ya fito a bakinta, amma ta danne. "Ba na son farin-ciki, idan dai daga gareka ne".

 Mai-jidda ta furta a hankali, wanda shi ne babban karyar da ta taba yi a rayuwarta. Ta tunzura da gyalen da yake ja a hankali, wanda take Allah-Allah ya janye shi, ta huta ko kuwa ya matsa daga gefenta.

Abdul-Aali ya rike mayafin a hannunsa, tamkar wani kwai yake lailayawa, idanunsa a lumshe, ya manna hancinsa yana shakar kamshin dake jiki, yana bude idanunsa, yayi mata kazafin da ya fi kowane girma, kai tsaye cewa ya yi "Makaryaciya!" Fuskarsa kunshe da wani murmushi, mai dauke da manufofi kala-kala.

Ta daga kanta sama tana kallon gefe ta hadiyi wani abu, sannan da sauri ta-ce. "Sai da safe."

Ta wuce dakinta cikin sauri, ta turo kofar, "Yau ni Mai-jidda na ga ta kaina, me yake damuna har na bari Abdul-Aali ya kai hannunsa gareni? Subhanallah! Tabbas ba yadda za ayi na bi-shi PH.

 Domin kuwa ban yarda da kaina ba. Abdul-Aali maye ne, ba zai dau wani dogon lokaci ba wajen wargaza min shiri na. Kuma ni ba zan bari ya yi nasara ba."

Sai wajen takwas da rabi Abdul-Aali ya fito. Ya ji Mai-jidda shiru, don haka ya bude kofar dakinta ya samu tana kwance, amma kuma idanunta biyu. 

"Jidda yaya na ga ba ki shirya ba?"

"Ina kwana." Ta fada hade da zama sosai a kan gadon.

"Lafiya, karfe sha daya ne Flight din mu ya kamata mu fita fa". Ya fada yana duba fuskar agogon da yake hannun sa.

"Oh, na manta ban fada maka ba, ni a nan zan zauna".

Ya bude idanu yana kallonta. "Ya kamata ki san da wa ki ke magana. Yaya zan ce miki ki shirya mu tafi, sannan ki ce min ke anan za ki zauna?"

"Ka manta ina da aikin yi, ka aure ni? Saboda haka zan koma wajen aiki na."

"Aiki? Aiki a kamfanin wannan mutumin? Kin san me ki ke ma fada kuwa?"

"Na sani mana, ban rubuta masu akan zan yi tafiya ba, ka ga kuwa karshen wata za su biyani kudi, idan na ci, ka na ga na kyauta? Tunda ban yi masu aikin su ba?"

"Resign, ki rubuta masu takardar barin aiki, ba shi kenan ba."

Mai-jidda ta mike daga kan gadon, tana gyara shimfidar ta-ce. "Ni ban san yaushe muka yi yarjejeniya da kai akan zan bar aikina idan na aureka ba. Oh right saboda bamu yi zancen aure da kai ba. Don haka ni ba zan bar aiki na ba. Saboda na san muhimmancinsa a gareni."

Yana kallon yadda take magana cikin zafin rai, da rashin kulawa da me hakan yake masa. "Za ka rasa Flight dinka, ka san babu wani kuma, sai bayan kwana biyu, don haka kar kasa Hamama ta zaci ni na rike ka."

Numfashi ya ajiye, ba abinda yake gani a lokacin sai kyaun Jiddan sa, ko da kwalliya ko babu, ko murmushi take yi ko masifa take yi. Jiddansa tana da kyau. Sai dai ta faye taurin kai. 

                      

"Na ji yana da muhimmanci a gareki, amma yanzu ke matata ce, kuma dukkan wasu bukatunki sun rataya a wuyana, kuma zan iya sauke miki su da naki da na Muhammad, so, ban ga amfanin aikin ba, don haka kafin na dawo, ina so ki je, ki kai takardar barin aikin ki, ina fata kin fahimta?"

                      

Shiru ta yi tana kallon sa, saboda sigar da yake mata magana da ita ta bambanta da na kullum.  Tana kallo ya tafi, ba tare da ta ba shi ko abin karyawa ba. Sulaiman ne ya kai shi (Airport), da ya dawo mata da makulli ne, ya-ce. Yaya Abdul-Aali ya ba shi kudi ya kawo mata. Sannan duk abin da take so, ta kira shi a waya, sai ya kawo mata. 

                      

"Akwai wani abu Anty Hauwa?"

                      

"A'a, sai dai gobe Insha-Allahu, ina son na je Dutse maganar wurin aiki, ban san yaya za ayi ba."

                      

"Ba damuwa ba ni da Lectures gobe, sai na zo na kai ki Insha-Allahu".

                      

"To na gode Sulaiman. Mutanen Final year".

                      

"Sai a hankali, sai goben dai". Nan ta dauki kudi a cikin kudaden da Abdul-Aali ya bar mata, ta ba shi ta-ce ya hau mashin.

                      

Wuni ta yi ranan tana shirya kayanta, ta kimtsa kicin. Da dare kuma sai gidan yayi mata shiru da yawa, ga shi ita ba ma'abociyar kallo ba, hakan ya sa ta dau wayarta ta kira Umma suka gaisa. "Yaya Muhammad bai tambayi inda na ke ba?"

                      

"Ga shi nan, yau ne ki ka soma tafiya, kina barin sa? Lafiyarsa kalau."

                      

Mai-jidda ta yi dariya hade da goge kwallar da ta fito a idanunta. "Ba shi wayar mu gaisa".

                      

Nan Muhammad ya karba, yana ta zuba mata surutu, tun suna waya, take jin shigowar wata wayar. Sai da ta ajiye ne, ta ga (Missed calls) din Abdul-Aali. 

                      

Bayan minti biyar ya sake kiranta. "Assalamu-alaikum." Ta fada muryarta kasa-kasa. 

                      

Abdul-Aali ya amsa mata sannan ya-ce. "Kin wuni lafiya?"

                      

Yanzu ta san zai cika ta da surutu ne kawai. "Lafiya kalau. Yaya su Ramla?"

                      

"Lafiyansu, wato su kadai ki ka damu da su ko? Shi ne ko ki kira, ki ji isa ta".

                      

"Kai ka na da mai kula da kai, me zai sa na damu da kai? Kuma tunda ga shi ka kira, na san lafiya ka isa".

                      

"Hmm! Akwai alkhairi a cikin kyautatawa, ya kamata ki sani".

                      

"Uhmm! Inji wanda ya yi kwas a kuntatawa mutane ba".

                      

Dariya ya yi har sai da ta ji dirin muryarsa a cikin kunnenta, wanda ya wuce kai tsaye har cikin jikinta ya sa, zuciyarta na bugawa da sauri, nan ya tuna mata da wani abu da ta yi saurin kawarwa a ranta. "Da fatan dai ba wata matsala a gida? Ki kulle ko ina fa, kan ki kwanta".

                      

"Na ji, ba mai sace maka komai dai a gidanka."

                      

"Ni ba komai bane damuwata, ke ce, don haka take care."

                      

Ta rasa wannan hira ta ba gaira ba dalili da ba ayi ba da, sai yanzu. "To sai da safe, yawwa na fadawa Sulaiman ya zo gobe mu tafi Dutse".

                      

"To ba damuwa. Allah ya kiyaye hanya, goben za ku juyo kenan?"

                      

Murmushi ta yi, don ita kadai ta san me take shirin yi. "Eh to it depends".

                      

"Akan me fa?" Ya tambaya cikin rashin fahimta. "Meye abin dadewa a cikin mika wasika, kar ki ce za ki je ko ina dama, gidan Umma kawai na amince ki je".

                      

Yau tana ganin ikon Allah. "Kai dai ba ka bada izinin tafiya ba? Sai ka yi addu'ar isa lafiya, shi kenan abin da na ke bukata". Ta fada a hankali, hakan ya sa Abdul-Aali ya ji wata kasala na sauko masa, ya-ce. "To shi kenan. Allah ya tashe mu lafiya."

                                      

                        

Yana kashe wayar, ya dubi fuskar wayar yana wata 'yar gajeruwar murmushi, nan Hamamatu ta shigo falon, ya san yaran ta zo dauka, don sun yi barci a falon. 


Ta  kwantar da karamar kenan, ta kashe masu wutan dakin, ta bar na corridor, saboda koda za su tashi fitsari. 


Tana jan kofar ne, ta ji Abdul-Aali a bayanta ta gane sarai me yake nufi ta matsa da sauri tana masa wani irin kallo, dakinsu ta wuce, bai daddara ba, ya bi-ta, ya-ce "Me ya faru ne Sweety?'


Harara ta zuba masa ta-ce. "Ka fi-ni sanin wannan amsar, don haka kar ma ka dago maganar".


Ya matsa kusa da ita ya-ce. "Haba har yanzu duk kishin ne bai kare ba?"


Bai samu amsar wannan ba. "Ki yi hakuri, ni ban ga meye abin zafi ba anan, kin tsaya za ki hana mu jin dadin rayuwa."


Harara ta kwada masa. "Jin dadi rayuwa ya wuce wanda ka jiyo a Kano." Ta fada tana juya idanunta cikin fushi. "Allah ya huci zuciyarki, ke ma kin san ke daban ce ko amare goma na yi, ke special ce."


"Sai ka fadawa na goye kenan, don Allah ka fita barci na ke ji, kuma ka takura ni, ban son ina kwance ana tsaye a kaina."


Zama ya yi a bakin gadon ya-ce. "Ni kuma na je ina? Ke ma kin san ba na raba daki dake."


"Gwamma ka saba, tunda kwanan za ka kawo matarka, ka ga kuwa ni za ka bari da wahala, na kai maka kayanka can dakin, idan ka yanke shawarar yanayin zaman, sai ka ajiyeta a can. Wannan ba damuwata bace".


Jan ta ya yi jikinsa ya-ce. "Ni kuma damuwata ce."


Da sauri ta fizge jikinta, hade da daukar mayafi da filo ta bar masa dakin. Kansa ya shafo cikin damuwa, haka ranar ya kwana cikin juyi.


*******


Ko a jikinta, ta shirga kaya a boot din mota, ta kula da kallon da Sulaiman yake mata, don haka ta-ce. "Ban san yaushe zan kammala ba, shi ya sa zan tafi da shiri na, ka san sha'anin tafiya".


Yake ya yi kawai, shi dai ya san yadda ta jidi akwatunan nan, ba yanzu take da niyyar dawowa ba. Bai ce mata komai ba.


 Gidan Abba ya kai ta, tai masu sallama, ce masu ta yi za ta je wurin aiki ta fara shirin rubuta barin aikin, tunda yanzu ta dawo Kano. Hakan ya sa su Mama ba su dau wani haske ba, har suka dau hanya.


Umma dai ta kalli Mai-jidda, ta kalli himilin kayanta ta kasa iya furta komai, can sai cewa ta yi. "Yayan ku zai zo gidan nan ya yi maganinki, wane irin rashin hankali ne haka? A kanki aka fara aiki, da ana aurenki da kwana biyu, kin dawo wai ke aiki?"


"Umma kin san aikin kamfani daban da na gwamnati ba kalula, kuma ga yadda na tafi ba sallama, shi ya sa na zo don komai ya daidaita, kuma shi din ne ma ya sa aka kawo ni, ba kin ga Sulaiman ba kanin sa?"


Wannan fada ya fi karfin Umma, haka ta yi shiru sai mita take yi. Muhammad kuwa yana dawowa daga makaranta ya ga Maman sa, sai murna yake yi.


Da dare ma bayanin da ta yiwa Baba kenan, ya yi shiru, amma ya-ce. "Bari Abdul-Aalin ya zo, sai mu yi magana, har yaushe za ki ta sa shi jigila? Sam wannan tsarin bai yi ba."


Nan dai ta sha zamanta abin ta, ba takardar da ta bayar, yana rubuce a takarda a jaka. kullum tana zuwa aikinta. Walida ta-ce. "Ba ki da M, yanzu don Allah kin tafiya kika yi, saboda wannan aikin da in ba dole ba, ba abinda zai sa mutum ya yi, don wuyarsa."


"Ke rabu da ni, hakan ya fi min, yanzu kin ga Abdul-Aali ya damu da tafiyata ne? Yana PH, duk lokacin da zai zo, sai na tafi Kano shi kenan."


"Kuma haka ki ke tunanin ba zai gane ba ko meye? Tunda ya-ce ki ajiye aikin, ba sai ki ajiye ba?"


                

                        

"Na ajiye aiki na, na sha Mamaki kenan, ke dai bari sai a zo a cika ka da bayanin za a kula da kai, ba ka bukatar aiki, ina ajiyewa zan ga hali, daman ya tsaneni, sai na rasa inda zan shiga na samu na kashewa."

"Ni dai wannan ba hujja bace, za ku yi daru, muddin ya gane ba ki mika wasikar nan ba".

"Idan na yi niyya kenan. Ni tun daga can dama ba wai na yi niyyar mika takardar bane."

"To idan ya tambaya a gidan su fa, ko kin koma?"

"Na yi magana da Mama."

Walida tana girgiza kai ta-ce. "Allah ya shirye ki Wallahi, ni banda Injiniya ma da neman wa kai damuwa ba, ban san me ya sa bai kyaleki ba, ya aurawa kansa matsala".

"Koma dai me ki fada, ba zan yi resigning ba."

Haka ta kwashe sati biyu, kullum sai ya kirata da dare, kusan karfe tara yake kiranta kuma daga maganganun sa ta fahimci cewa Hamamatu ba ta wurin yake wayar.

*********

 Ranar ta tashi a aiki kenan, ta fito don tafiya gida, sai ga motar Abdul-Aali a gaban ginin ofis dinsu. Wani mummunar faduwar gaba ta ji. Yaya aka yi ya zo a tsakiyar sati? Me za ta ce masa? 

Ta rude cikin tambayoyin da suka addabeta, amma haka ta daure ta zagaya ta bangaren da ba kowa, ta bude motar ta shiga, ita kanta ta san karfin hali ta yi. "Ina takardar take?"

Ba musu, ta bude jakarta ta dauko wasikar barin aikinta. "Ki shiga ki bayar, ki zo mu tafi."

Kallon sa ta tsaya yi, za ta yi gardama, amma rabon da ta ga ya sha mur, irin haka tun zamanin da Dokta ke raye. Don haka ta-ce masa "Zan kawo da safe, yanzu wanda zan bawa, baya nan ya yi tafiya, amma yau zai dawo."

Bai ce mata komai ba. Ya suri motarsa, tana jira ta ga sun yi hanyar gida, kawai sai gani ta yi sun dauki hanyar Kano. Ita dai tana tantamar hankalin Abdul-Aali a yau.

 Abin da ba ta sani ba, gidan ya fara zuwa aka ce masa tana wurin aiki, da alama dai ce masu ta yi ya amince, don haka bai ga laifin su Umma ba, kai tsaye ya wuce zuwa ofis din. 

Hannunta duk ya jike da zufa, duk da AC din da ya kunna a motar, saboda yau ta san Allah ne kawai zai ceceta daga Abdul-Aali. Bai bi gidan Abba ba, kai tsaye gida suka wuce, sai da suka zo shiga ne, ta tuna da kayanta. 

"Ina kayana?"

Kallonta ya yi ya wuce ciki, hade da ajiye makulli a kan (Dining table). Yau tata ta sameta, ita da aka sace a wurin aiki ne ya kamata ta yi fushi, ko shi da ya sato ta? 

"Yaya za ayi ka daukoni babu shiri, sannan kuma na tambayeka kayana, ka ki ka kulani."

Juyowa ya yi cikin fusata. Yatsarsa manuniya yana kan fuskarta. "Jidda, kar ki ga kin saba yin abin da ki ke so a baya, ina shiru, yanzu ki na karkashi na ne, idan nace ayi abu a gidana shi ake yi, ranki zai yi masifar baci.

 Idan har na sake sa doka a gidan nan ki ka take shi. Ashe ban yi dake akan za ki je ki mika takardar barin aikin ki bane, ki dawo. Shi ne za ki raina min hankali, ki je ki yi zaman ki a can ko? Ba ki dauki umarni na a bakin komai ba ko?"

Yadda yake kururuwa tamkar zai hadiyeta ne, ya sa ta tsorata tamkar ta shige cikin bangon falon jikinta na rawa ta-ce. "A'a ka yi hakuri, ba haka bane."

"To yaya ne? Ko kuwa haka ki ka yi da tsohon bazawarinki, saboda ku samu damar haduwa, tunda ba na nan?" 

Kwarai Mai-jidda ta tunzura da kalamansa, don haka ta nemi mutuwar bakinta, ta rasa. Nan da nan ta samu muryarta.

 "Dalilina na rashin barin aiki na daban, amma idan abinda ka ke son ka fahimta kenan, shi kenan, ni ba zan hanaka ba, sai dai kar ka kara fadar abinda za ka zo ka yi da-na-sanin fadin sa."

                

                        

Ta wuce daki ta zauna, ba zato kawai ta ji hawaye a fuskarta. Abdul-Aali kuwa ya rasa me yake masa dadi, ta bata masa rai da yawa, ya tsani mutum mai taurin kai. 

Bayan issha, ta ji yunwa na damunta, don haka ta fito kitchen dinta, saboda ta dan dafa wani abin, tana fere Dankali ne. Ya shigo ya sameta a kitchen din. "Ki bar abincin, ga shi na karbo Tuwo wurin Mama".

Haushi ne ya kara kamata ta-ce. "Zuwa ka yi ka cewa Mama na ki yin girki ko meye? Ka ci, ni ba na jin cin tuwo."

Kafadarta ya rike yana duban cikin idanunta. "Sorry, na yi kuskure da na fadi maganar dazu, amma ki kiyaye bata min rai."

"Na ji, kai ma ka daina taba ni, ba na so." Ta kwace kafadunta daga rikon sa. Murmushi ya yi ya-ce. "Sai dai ki fadawa wani ba ni ba, ni kam na san sirrin". Ya fada yana lumshe mata idanu.

Hararar sa ta yi, sannan ta koma firar Dankalinta. "Tuwon da yawa fa, are you sure ba za ki ci ba?" Kai ta daga masa. "Miyar kubewa ce". 

Ya san ta fi son Kubewa, don haka da sauri ta juyo, amma kuma ganin murmushin fuskarsa ta-ce. "Ka bawa Malam Danlami (Mai-gadi)".

"Shi kenan, kar ki ce ban yi miki tayi ba."

Ya fita ya bar mata kicin din, tana gama fira, ta dauraye Dankalin, ta sa ruwa a kai ta diga vinegar, sannan ta ajiye shi a fridge. A kasan kafet ta samu yana cin abincin Plate ta dauka ita ma ta je ta diba. Tana jinsa, ya yi waya da matarsa. Ba ta ce masa komai ba. Kafin ya gama ta dauke Plate dinta ta wuce daki.

 Ya samu tana kade gado cikin shirin kwanciya. "Har kin shiga ne?" Ya fada hade da tura kofar dakin, nan da nan ta bar abin da take yi, domin kuwa tsayuwarsa a dakin ba abin da zai haddasa, sai damuwa a gareta. "Eh."

"Da wannan kayan za ki kwanta?"

"Kamar ka bar min wani zabi, ina ce a gida kasa na taho na bar duka kayana."

"Daman guduwa ki ka yi kenan? Har da kwashe duka kayanki". Tana tsume, ba ta ba shi amsa ba ya-ce. "Idan ki na son aro, ki zo ki karba."

"Ba fataran kaya na ke yi ba, da zan karbi naka ai, ka gama maganar ne? Zan kwanta".

Ajiyar zuciya ya yi ya-ce. "Allah ya ba mu alheri."

A hanyarsa ta fita ne, ya kashe mata wutan dakin. Ta yi waya da su Umma, ta fada masu ta dawo Kano, saboda kar hankalin su ya tashi, sai da ta ajiye, ta rinka jin haushin kanta, yanzu shi kenan su Umma za su dauka ita ga me dadi miji, daga zuwa ya sure ta sun tafi, ba tare da sallama ba. Ta tsani Abdul-Aali da nuna isarsa. 

Da sassafe yau kam ta tashi ta shiga aiki a kicin. Dankalinta na jiya ta fitar daga fridge, sannan ta dora (Pepper Soup). Buruntun ta ya jiyo a kicin ya samu ta shirya cikin wata bakar atamfa mai digo-digon ruwan goro.

Kayan sun mata kyau sosai, ba ta san yana bakin kofar ba, don hankalinta ya yi nisa kan aikin da ta ke yi. Ta juyo za ta sa abu a dustbin ne, ta gan shi, sai da ta dafe kirji cikin tsoro.  

Sai da ta mayar da numfashinta, sannan ta gaishe shi, ta kara da cewa. "Jiya ka sa ni jin kunyar su Umma, saboda dole ya sa na ce masu na taho Kano tare da kai, kar su ji ni shiru."

"To meye abin jin kunya? Ba mijin ki ki ka biyo ba? Dama tafiyar ta satar hanya ce, don haka dawowarki shi ne daidai".

Karar Dankali a cikin mai ne, ya sa ta juya don ta duba girkinta. Tana gamawa, ta sa a (Food Flask) a falonta ta ajiye. 

Sun fara karyawa ne, yake ce mata. "Ki shirya za mu je gidan Abba, zan masu sallama don yau zan koma."

Ba ta san dalilin da ya sa ta ji bacin rai ba, daya dauko ta da ya yi, ya raba ta da aikinta ko kuwa tafiyar da zai yi, ya bar ta, ba abin yi?. 

"Daman ka san yau za ka koma, ka dauko ni daga Dutse?"

"Ke ki ka zabi zaman Kano, ni ban ce lallai ki zauna ba, gidana wadatacce ne a PH. Idan za ki shirya mu tafi, shi kenan, amma idan Kano ki ke son zama, to sai ki zauna a gidanki, ayyuka na suna da yawa a can, ba zan raba hankali na ba koyaushe ina hanya. Ina fatan kin fahimta?"

Wani munduku ne ya taso mata. "Kai kanka ka san ba son ka na ke yi ba, bare na damu da zama kusa da kai ko nesa da kai ba, idan ka ga dama kar ka sake zuwa.

 Wannan kai ya dama, amma ni ma ba zan zauna a gidan nan ba ni kadai, kamar wata mayya, gidan Abba zan koma. Ka aika a taho min da kayana kuma".

Kallonta yake yi har ta gama maganarta, "Idan kin gama, ki zo mu tafi gidan Abba".

Yana ma jin me ta fada kuwa? Kuka kawai ta sa, sannan ta tashi ta bar falon. Ita ba ta ga me auren Abdul-Aali ya tsinana mata ba, sai bakin-ciki. Tana zaman zamanta, ya wargaza mata rayuwa, ko Muhammad yanzu hannun Umma yake, wai sai ya gama wannan Term din, sai ta dauke shi a canza masa makaranta.

 Idanunta sun yi ja. Lokacin da ta fito don tafiya gidan Abba. "Haka za ki je gidan Abban, duk idanunki ja? Me ki ke so su ce?"

"Koma me suka ce, ai daidai ne, tunda ba abinda ka ke min, sai kuntata min da sa ni kunci, daman ba wanda ka fi tsana kamata, ka kawo ni gidanka kam, sai yadda ka yi da ni, gwamma su san komai, ko za su raba ni da kai."

Da sauri ya dubeta, jin maganar da ta fada. "Ki wuce ki gyara fuskarki."

Yana zaune a motar, ta dawo, bayan ta gyara fuskarta. Bai ce komai ba, ya ja motar suka tafi.

Mama dai sai ganin Mai-jidda ta yi da Abdul-Aali, batun ta tambayi yadda aka yi ma ba ta taso ba, ko da Abdul-Aali ya-ce mata yau zai koma, sai ta-ce. "Za ka tafi da Hauwan ne?"

Abdul-Aali ya rasa amsar da zai bawa Mama, don ba abinda zai sa ta zauna, amma kuma ya san Jidda sarai, don haka ya-ce. "A'a tana nan tukun, may be idan yara suka yi hutu suka zo, idan mun tashi komawa, mu koma gaba daya".

"To Allah ya nuna mana lafiya."

Mai-jidda ta koma falo, koda zai tattauna da Mama, can sai ga shi ya fito. "To Jidda ni zan wuce kenan, tunda an ki ayi min rakiya. Sulaiman sai ya kai ki, ki dauko kayanki, ki dawo nan din."

A hankali ta dago idanunta tana kallon sa, ba tare da ta-ce komai ba. "Magana na ke miki, ko ba ki ji ni bane?" Ya fada cikin daga murya kadan.

"Allah ya sauke ka lafiya". Ta fada cikin rashin kulawa.

"Me ya sa ki ka faye son rigima ne ke? Ko ma ki ce bari na raka ka mota, bare ma zuwa (Airport)?"

"Allah ya sawwake, sai dai a mafarkinka, idan ka ga dama kuma ka tabbata a PH".

Ya kula da wani abu ne ya kara ba ta haushi, don yau fushin nata na daban ne. "Shi kenan, tunda haka ne." Ya mike ya fita daga falon. Abdul-Aali na fita. Mama ta shigo falon ta-ce. "Hauwa, tashi ki je ki raka mijinki, an taba yin haka ne?"

Yau ta ga ta kanta Mama ta ji abin da ta fadawa Abdul-Aali, dolenta ya sa ta sa mayafinta ta bi bayansa. 


                                              

Yau ta ga ta kanta Mama ta ji abin da ta fadawa Abdul-Aali, dolenta ya sa ta sa mayafinta ta bi bayansa. Ya sa hannu zai bude kofar motar ne, ya ganta, tuni Sulaiman yana zaune a mazaunin direba. "Lafiya dai? Ko kin canza ra'ayin ki ne?"

                      

"Babu, ka yi hakuri, raina ne yake bace. Allah ya kiyaye hanya".

                      

Murmushi ya yi sannan ya-ce. "Ameen, na gode Jidda". Za ta koma ne, ya-ce "Me ya bata miki rai?"

                      

"Ka bar shi kawai, za mu yi maganar daga baya".

                      

"To shi kenan, sai kin kira, sau dayan nan dai a daure a kirani ni ma".

                      

Kanta na kasa ta gyada masa shi, ta wuce cikin gida, bai san sallamar ma albarkacin Mama ya sameta ba. Ita wataran tana ganin karfin halin sa ma, duk abin da take mashin nan, ya kasa hakura da ita. Tana komawa cikin gida ta samu Mama a daki, nan take ce mata.

                      

 "Nan gaba ki daina haka, wa ya-ce miki ana wasa da al'amarin miji, ko ba tafiya zai yi ba, idan ma cikin gari zai fita, ki nuna kulawarki gare shi. Bare kuma sha'anin hanya, ai bai dace ku rabu da mutum cikin fushi ba."

                      

Mai-jidda kuka take yi, wanda ita kanta ba ta san dalili daya na yinsa ba, shin don Mama tana mata magana tamkar Ummanta ne, ko kuwa don tana tuna irin zaman da suka yi da ita lokacin da Dokta ke da rai ne? "Assha meye kuma na kuka? Haka za ki zauna da mijinki, kullum cikin kunci?"

                      

"Mama ban san yadda zan yi ba, marigayi na raina har yau, ba zan iya manta shi ba".

                      

"Hauwa, ba wanda ya-ce ki manta shi, asali ma yana da kyau ki rinka masa addu'a, amma kuma hakan ba shi zai hanaki rayuwa ba."

                      

Mama ta mike ta bude wardrobe dinta, dake jikin bango, can ta dawo da wata takarda a hannunta, ta mikawa Mai-jidda, ita kuwa ta dubi Mama cikin alamar tambaya. "Mene ne wannan Mama?"

                      

"Takarda ce." Idanun Mama suka ciko da hawaye sannan ta-ce. "Daga wurinsa."

                      

Mai-jidda ta firgita, tamkar wacce ta ga 'yan fashi "Meye?"

                      

"Shi ya rubuta watanni uku kafin rasuwarsa, yana so a ba ki idan lokaci ya yi." Mama ta dan yi shiru sannan ta-ce. "Kuma ina ga wannan lokacin ya zo, shi ya sa na ba ki".

                      

"Meye..." Mai-jidda ta kasa fito da sautin da ya taso a makogwaronta. "Me ya rubuta?"

                      

Mama ta yi murmushi, ta mika mata takardar. "Ki karanta mana."

                      

Mai-jidda ta sa hannu ta karbi wasikar, tana kallo. Mama za ta tashi ne. Mai-jidda ta yi saurin rike mata hannu, saboda ba ta tsammanin ta shirya fuskantar koma meye yake cikin wasikar nan, ita kadai. 

                      

Tana bude wasikar, ta ga rubutun Dokta, wanda ya fara birkicewa a lokacin saboda ciwon ya fara kwace masa ikon yin rubutunsa. 

                      

Hauwa!

                      

"Lokacina yana karatowa. Dukkan mu mun sani, duk da ba mu barin haka ya bayyana ko kuwa mu yi magana akai, raina a hannun Allah yake, shi kadai ya san lokacin da zai karbe ni.

                      

 Muhammad yana hannun ki, na san za ki kula da shi, saboda ki na daya daga cikin matan da na sani masu juriya, don haka na san ba zai samu matsala ba.

                      

 Ke kuma fa? Shin wa zai kula da ke? Na san za ki ci gaba da rayuwa, saboda Muhammad, amma kuma ina son ki kasance cikin farin-ciki.

                      

wannan ya sa na ke rubuta wannan wasikar.

                      

Idan Mama ta ba ki wannan wasikar, to zai kasance saboda alaqa ta shiga tsakaninki da Abdul-Aali ne, na san zai zo dominki. Na sani, na san Abdul-Aali sosai ciki da bai.

                      

Da ba yadda za ayi na kasa gane cewa yana sonki. Ba zai iya kiyaye kallon da yake miki ba, tunda ni kaina ina sonki na fahimci ko menene ma'anar kallonsa gareki. Na fahimci alamomin..."

                                      

                        

"Ya Allah!" Mai-jidda ta fashe da kuka.

Mama ta yi saurin shafa bayanta. "Yi shiru, ba komai ci-gaba da karantawa".

Mai-jidda ta share hawayenta ta ci-gaba.

"...Ga abinda zance. Hauwa kar ki damu, ba komai, kar ki ji tsarguwa ko kuwa bakin-ciki a tare dake. Ki kasance cikin farin-ciki. Idan Abdul-Aali ya saki farin-ciki, ki kasance tare da shi, idan baya sonki, ki rabu da shi.

 Ki samu wanda zai sa ki murmushi. Ko ba za ki yi don kanki ba, ki yi domina, kin ji? Ba na son rayuwarki ta kare, don kawai tawa ta kare.

Mijinki mai kaunar ki.

Dr. Rayyaan S.

A hankali takardar ta sulale daga hannun Mai-jidda, da ya rasa karfin sa zuwa kasa. Cikin tunanin Dokta ta sa fuskarta a hannunta tana kuka mai tsuma rai, cikin kunci da son da take yiwa mijinta Marigayi hade da wani abu da ya shige ta, wanda ba ta san menene ba.

"Hauwa na dauke ki tamkar yadda na dauki Suwaiba. Abdul-Aali Dana ne kuma na san yana sonki, idan har ke ba za ki iya mayar masa da makamancin son da yake miki ba, ko kasa da haka, to ina ga kawai ki rabu da shi, ki samu wanda zai sa ki farin-ciki."

Mai-jidda ta samu kanta da matukar jin nauyin Mama, duk yadda take da ita, ko take sonta, ta san ita-ce ta haifi Abdul-Aali, ko da kuwa don Danta Rayyaan take kin Abdul-Aali, amma hakan yana mata zafi.  

Sai bayan azahar. Sulaiman ya kai ta gida, don dauko abubuwan da za ta bukata, jikinta duk ba kwari. Yanzu daman tun Rayyaan na da rai.  Abdul-Aali yake sonta? Yaya za ayi ya so matar Dan-uwansa? Abin yana daure mata kai ainun!

Tana kwance a daki banda tunani ba abin da take yi, wajen karfe hudu na yamma, ta kira lambar Abdul-Aali a karo na farko da ta kira, ba cikin fushi ba kenan, ta kira don ta ji isarsa, kamar yadda ya bukata. 

"Hello". Muryar Hamama ta ji, nan take ta ji kamar ta ajiye wayar, saboda ba ta san me za ta-ce ba, cewa za ta yi ta bawa mijinta waya ko me? 

"Hello, ina wuni?"

"Mtsss! Ke yanzu ko kunya ba kya ji, bayan kin ji muryata ma, hakan bai sa ki ajiye wayar ba, to bari na fada miki, don kin auri mijina, ba shi zai ba ki damar ki shige mana rayuwa ba. Sai ki jira, idan yana tare dake, ki yi masa magana ko kuwa idan ya fita ya kiraki, amma ba a gidana ba".

Ran Mai-jidda ya baci, me ya sa Hamamatu za ta fadi irin wannan maganar? Duk da Abdul-Aali baya gabanta, ai shi mijinta ne, kuma tana da damar kiransa a duk lokacin da ta so, sai dai idan shi yayi mata iyaka.

"Allah ya ba ki hakuri, daman na kira na ji isarsa ne, amma tunda kin amsa. Hakan ma ya wadatar, ki gaida 'yar..."

Kafin ta karasa magana. Hamama ta tsinke wayar. Mai-jidda ta kufula, zuciyarta ta kawo, don me ya sa za a wulakanta ta, akan abin da ba ma so take yi ba, in dai miji ne, ta je ta bar mata.

******

Da dare bayan sun gama hira da su Mama da su Kasim a falo, kowa ya watse. Mai-jidda tana daki, sai ga Abdul-Aali na kiranta a waya, tana gani har wayar ta tsinke ba ta dauka ba, sai da ya sake kira, sannan ta dauka. 

"Shi ne har yanzu ban ji wayarki ba?"

"Hmm! Idan ka san za ka sa mutum ya yi maka waya, sannan ka na da doka akan yin hakan, ina ga tun farko gwamma ka ce kar na kira, sai lokacin da ka ke da sararin yin hakan, kai ka nemeni". 

"Ban gane ba, doka kamar Yaya?'

"Ban san idan ka na cikin gidan ka, bai dace na kira wayarka ba, amma tunda yanzu na sani, gaba zan kiyaye."

                

                        

Ta fada ranta na kuna.

"I'm sorry about that. Amma ban sa wata doka ba. Duk lokacin da wani abu ya taso za ki iya kirana, lokutan da ba na son amsa waya, za ki samu wayar a kashe, amma ki tura Message."

"Sai ka fadawa matarka, don fahimtar ta daban da taka."

Abdul-Aali ya yi shiru, wato Hamama ce ta amsa wayar Mai-jidda. No wonder take ta hada rai, tun da yamma. 

"Ki yi hakuri, mu bar wannan maganar, hakan ba zai sake faruwa ba Insha-Allahu. Kin koma gidan Abban ne, ko ki na gida?"

"Na dawo tun da rana."

"To ya yi kyau, akwai isassun kudi a hannunki ko? Idan babu akwai a daki na a durowa, duk sanda ki ke da bukatar su, za ki iya zuwa ki dauka".

"Na gode. Amma ba na bukatar komai".

"To shi kenan." Bayan ya dan yi shiru ne, ya-ce mata. "Yanzu za ki iya fada min abin da ya bata miki rai dazu?"

"A'a, sai dai wani lokacin, don ya wuce. Besides ka bawa Madam time, kafin a kara dora min laifin rike miji."

Murmushi ya yi mai wannan sautin dake tayar mata da tsikar jiki, sannan ya-ce. "Jidda kenan, to shi kenan. Mun yi magana da Abbakar ya-ce, idan zai shigo Kano, zai taho miki da kayanki."

"To, na gode".

"Sai da safe". Ya fada a takaice. 

"Allah ya tashe mu lafiya."

Ta kashe wayar a sanyaye, haka kawai ta rasa abin da yake mata dadi. A bangare guda ba abin da ta fi so, irin ta ji ta tsani Abdul-Aali. A bangare guda kuma al'amarin sa na ba ta al'ajabi, jira take yi sai randa ya zo tukun, tayi masa duk tambayoyin da suke ranta.

 Haka sati biyu suka yi, suka wuce ba ta gan shi ba, abin dai yana damunta, amma kuma ba damar tayi masa magana a waya. Kullum da dare, sai ya kirata sun gaisa koda na minti daya ne. Wataran ta kan ji kamar ta tambaye shi lokacin zuwan sa.

 Amma kuma sai ta fasa, saboda kar ma ya yi tunanin ko son ganin sa take yi. Ita akwai abin da ba ta so su yi magana ne akai a waya, don haka ta yi shiru. 

Ran Asabar ta je gidan Yaya Maryam, nan take ba ta labarin wasikar da Dokta ya bari. Yaya Maryam ba ta ce komai ba, sai kallon Mai-jidda take yi. 

"Don Allah ki ce wani abu, na rasa me zan yi, kaina ya kulle".

"Mai-jidda kenan, lamarinki akwai abin ban dariya, meye kuma abin kulle kai a nan? Ina ce don Rayyaan ki ke kin Abdul-Aali? To ya bar miki wasiyya, ki manta da shi, ki kuma so Dan-uwansa, idan yana sa ki farin-ciki, dadin karawa, shi da kansa ya-ce kar ki ji guilt na son Abdul-Aali, don haka ya gama cewa komai saura ya rage naki."

"Yaya Maryam ba za ki gane bane, ban san yadda aka yi Dokta yake tunanin so-na Abdul-Aali yake yi ba, ya iya mugunta da gangan yake yi, ya tsane ni. Ki na ga tun da ya tafi yau fiye da sati uku kenan, amma ko maganar zuwa baya yi?"

"Ki na so ya zo kenan?"

Mai-jidda ta gyara zamanta kan gadon, tana wasa da yatsun hannunta. "Zaman wa na ke yi, ni ba na son ganin sa. Amma dai ya kamata ya san ya ajiye mutum a nan, ni ya hana ni aiki na, sannan kuma ya bar ni ba abin yi, ya koma wajen iyalin sa."

"Mai-jidda sha'aninki da Abdul-Aali sai idanu, ba abin cewa, ni dai ina nan dake har zuwa lokacin da zai bude miki idanu, ki san me ki ke ciki, wai a tunaninki duk wannan meye idan ba so ba? Ki na son Abdul-Aali Mai-jidda".

Mai-jidda ta dubi Yaya Maryam a razane. Yaya za ayi ta so mutane biyu a tare? Kai Yaya Maryam ba ta gane ba dai, ba yadda za ayi ta ma so Abdul-Aali fa? Ina! "Ni kuma na so Abdul-Aali. Hmm! Lallai ranar jaki zai fidda kaho. Allah ya sawwaka, na gama soyayya a duniya, sai dai zaman aure."

                

                        

"To Allah ya bada sa'a."

Ko da ta zo tafiya, sai da ta bi gidanta tukun, ta duba komai lafiya. Ta dan yi share-share, a karo na farko ta shiga sashen Mai-gidan. Babban falo ne mai dauke da (Dining Area) da dakinsa a ciki, sai madaidaicin bandaki daga ciki. 

Komai gwanin sha'awa, nan ta shiga ta wanke (Toilet) din, ta duba ma'ajiyin komai a dakin, tana taba kayayyakin tana tunanin, hala Hamamatu ce ta shirya masa su.

 Shirmammiya, wa zai shirya masa da to. Ta fada wa kanta. Dakinta ta koma ta dauko turaren wuta ta kunna a dakin. Sai wajen karfe biyar, ta gama kimtsa ko ina, sannan ta kulle ta fito. 

A wannan daren zama ta yi kusa da wayarta, amma shiru Abdul-Aali bai kira ba, hakan ya ba ta mamaki kwarai, ganin tun aurensu kullum sai yayi mata waya a wannan lokacin, sai dai idan yana gari. Tun tana jira wayar, ta yi kara har dai ta hakura. Barci ya dauketa. 

Sai washegari da safe ta samu wayarsa, ita ma haka ta bari ta yi ta ringing, sannan ta daga. "Ina ki ka shiga haka, tun dazu na ke neman ki a waya".

Mai-jidda ta-ce. "Ba na kusa ne. Ina su Mimie?"

Nan ya-ce. "Bari na ba su ku gaisa". Mai-jidda ta hadiyi wani abu, saboda tsoron abin da zai biyo baya idan Hamama ta san ta yi waya da yaranta, sai dai hakan bai hana ta yi magana da su ba daya bayan daya. Sai murna suke yi sun ji muryar Anty Hauwa.

Baban su ya karbi wayar yana dariya ya-ce. "Kin ji yara ma suna marmarin jin muryarki."

"Hmm! Hakan ya sa na ga jiya ba ka kira ba."

Ya karanci fushi a cikin muryarta. "Da ki ka ji shiru, ke me ya hana ki kira?"

"Ban san dalilin rashin kiran ba, wannan ya sa na ga zan saurara zuwa yau, idan na ji shiru, sai na nemeka."

"Uhmm! Wallahi aiki ne ya min yawa jiya har yamma ina ofis, duk da kasancewar Asabar ce. Ina sallar issha, barci ya daukeni, da na farka kuwa dare ya yi sosai, shi ya sa na kyale ki."

"Yau na je gidan Yaya Maryam, ta can na duba gida."

Ji ta yi ya yi shiru kafin ya-ce. "Haka aka ce miki ake fita ba tambayar izini?"

"Na fada maka, ni ba zan kira wayarka ba, kuma ba ka kira ba, ni kuma ban ga abin kin zuwa ba a duka inda na je ba, shi ya sa na yi tafiyata".

"Gaba nan ko gidan Umma za ki je, sai kin fada min, saboda ba amfanin fita haka ba izini, ki na ji na ko?"

Ta hada rai, yanzu zai fara nuna mata isarsa na shi Mai-gida. "To."

"Sannan ran Alhamis ki shirya, ki koma gida. Insha-Allahu muna tahowa."

Muna tahowa? Abin da ta fi dauka daga zancen sa kenan, wannan yana nufin da su Hamama zai zo, tun da aka yi biki, ba su hada idanu ba, yanzu ga shi za su taho, ko da wane idanu za ta dubeta? Oho.

"To, Allah ya kawo ku lafiya. Makarantar su Mimie fa?"

"Ai za ayi (Public holiday), wannan ya sa za mu taho gaba daya. Sannan akwai Sister din Hamama da ta haihu, duk dai za mu hada tafiyar."

"Allah ya kai mu, sai kun zo".

"Ana maraba da ni kenan."

"Kai ma dai ka fiye rudan kanka wasu lokutan, sai anjima".

Yana dariya ya-ce. "Mu jima da yawa."

Tana kashe wayar, ta shiga tunanin yadda za ta kasance tsakaninta da Hamama, tunda ta san yadda ta dauki zafin abin kawai za ta bi-ta a hankali ne, har ta sauko. 

Don batun gaskiya, ko ita-ce hakan ya faru da ita, to ba za ta dau abin da sauki ba. To ma me zai daga mata hankali? 

Tun ran laraba ta koma gidanta, ta kara kimtsa ko ina, kasuwa ta shiga ta sayi abubuwan da za ta bukata na aiki. Tun safe ta fara rage ayyuka, saboda ya zamana daidai isowarsu, ta kammala ta kimtsa. 

Sai dai har ta ji shigowar mota cikin gate, zuciyarta bai bar bugun uku-uku ba. Dogon numfashi ta ja ta sauke, sannan ta dan samu natsuwa.

 Gefenta ta bude, suka fara shiga, don Mai-jidda ta ji hayaniyar yaran. Falon Abdul-Aali ta shirya masu komai daman, tana daki ne, ya shigo. Ta dago fuskarta suka hada idanu. "Sannun ku da isowa".

"Yauwa, sannunki da gida." Shiru ta yi saboda ta rasa abin cewa. "Yaya ki ka zauna a ciki, kun gaisa da Hamama ne?"

"Ina jira tukun, sai sun dan kimtsa, zan shiga mu gaisa."

"To ba laifi." Mai-jidda ta mike ta-ce. "Na ajiye abinci a falonka, akwai drinks kuma a fridge. Idan da wani abu, ina nan".

Kallo ya bi-ta da shi. "Don Hamamatu ta zo, shi ne za ki kunshe kanki a daki?" Kanta na kasa, ba ta amsa masa ba. "Ki fito mu ci abincin tare".

Za ta yi magana ne ya-ce. "Bari na yi sallah kafin nan."

Ba daman ta musa, don bai ba ta filin yin hakan ba. Shigowarsu da kusan minti talatin. Sannan Mai-jidda ta yi sallama a sashin Hamamatu, su Mimie ta samu a falo, nan suka yi kanta a guje, suna murna. Musamman Mimie da ta fi wayo. "A'a Mimie, kin zo ne? Lallai sannunki da zuwa. Me ki ka kawo min?"

"Anty Hauwa, me zan kawo miki?"

"Ina tsaraba ta?"

"Ni ban san inda ake sayarwa ba, sai dai ki tambayi Mami na."

Dariya Mai-jidda ta yi ta-ce. "To lallai, ni kuma ga shi na ajiye maku wani abin dadi, ina Mamin naku?"

"Tana daki, ina abin dadin nawa?"

"Zan ba ki anjima, je ki mata magana, ki ce Anty Hauwa ta zo su gaisa."

Sai dai kafin Mimie ta shiga daki, sai ga Hamamatu ta fito daga ciki. "Mimie ke da wa na ke jinki?"

"Anty Hauwa ce ta zo gaisheki. Mami kin san ta ajiye min abin dadi?"

Hamamatu ta kufula, ita ba ta son rainin hankali, wane gaisheta za ta zo yi,  neman gindin zama ko?.

"Sannun ku da hanya." Mai-jidda ta fada ganin fitowarta. 

"Meye haka za ki shigo wa mutum ba notice, ba na son wannan kinibibin, bayan abin da ki ka yi, har za ki iya nuna min fuskarki?"

Mai-jidda ta dubi yaran da suke zaune suna kallon Maminsu. "Ba abinda ya yi zafi Mamin Mimie, ki yi hakuri."

"Ko ba ki fada ba kam, hakuri ya zama min dole, tunda kin samu abinda ki ke so, sannan magana ta karshe, ba ruwanki da shiga jikin yarana. Ba ke ki ka haifar min su ba bare ki yi Pretending ki na sonsu, kowa ya yi sabgar gaban sa, tun farko. Ba na son Munafurci, ehe!"

Maganar ta bawa Mai-jidda mamaki, don ita ba ta zaci abin ya yi zafi haka ba. Ba ta kara tankawa ba, ta fita a sashin. 

Ko da Abdul-Aali ya nemeta cin abinci, sai ta ji kamar kar ta je, sai dai kuma ba ta son yawan yi masa gardama, hakan ya sa, ta dauki mayafin da ya shiga da atamfarta ta sa a jikinta, sannan ta yi sallama (Side) dinsa. Ya amsa mata fuska a cike da fara'a.

 Ita ko kallon sa ma ba ta yi sosai ba, hankalinta duk yana kan maganar Hamama, ai kuwa idan za su yi zaman tare, ba yadda za ayi ta-ce ba za ta kula yara ba, tunda dai 'ya'yan mijinta ne, randa ta haihu a gidan, idan ba ta kula su.

 Yaya za ayi su shaku da kannensu, su so juna? Sai a lokacin ta tsaya ta daga ido, ta dubi Abdul-Aali. Subhaanallah! Me ya kai ni tunanin haihuwa da Abdul-Aali? 

"Lafiya, Jidda? Me ya faru?'

Ta tabbata razanar fuskarta ya gani a dalilin tunanin da ke ranta. "Babu komai".

Nan suka jira sai da yaran suka shigo, sannan ta zuba masu abincin, ta fiddo Jugs na abin sha kala-kala daga fridge, wanda duk ta hada da kanta. (Mango juice) ne da su zobo. 

Ta gama zubawa ne. Hamamatu ta shigo falon, ba abinda take ji, sai kuna, musamman da ta samu Mai-jidda tana zubawa Abdul-Aali drink a kofinsa. Haka dai ta daure ta zauna. Mai-jidda ta mika mata (Serving spoon), saboda ta sa abin da take so.

Haka aka yi zaman cin abincin cikin shiru, sai yaran da suke hira da Baban su. Tana gamawa, ta mike ta bar falon. Abdul-Aali yana ganin yadda suka yi, ya san ya samu babban matsala a hannu, idan bai dau mataki ba.
Mai-jidda ta karasa bawa Ramla abinci, sannan ta tattara, falon ta bar su anan, ba ta sake leka su ba har aka yi sallar issha. Wayarsa ta gani yana nemanta a Side dinsa. Ko da ta shiga, ta san 'Nasiha' Zai  masu, domin ta samu Hamama a zaune a falon.

                      

"Wai Hamama Sarautar ta ki, kika barwa Jidda ne? Na ga ta fi kowa iya latti."

                      

Mai-jidda ta yi murmushi ta-ce. "Ku yi hakuri, na zaunar da ku."

                      

Hamamatu ta daga kanta, ba ta ga abin ban dariya anan ba, idan zai fadi abin da zai fada, ya fada su tashi, bazata iya ganin wannan kayan haushin ba.

                      

"Sweety, muna saurarenka". Ta fada tana duban Abdul-Aali.

                      

"Bismillah! Mu fara da yiwa Annabi Salati." Nan Abdul-Aali ya yi masu addu'o'i sosai.  Fuskarsa ba alamun wasa ya-ce. "Ba komai bane ya sa na taraku a nan, illa don mu fuskanci juna, mu kuma san irin zaman da za mu yi tare.

                      

 Kasancewar wannan ne karo na farko da ku ka hadu tun bayan aure. Ya kamata na yi (Setting ground rules), gindaya wasu dokoki. Na farko dai dukkan mu zaman ibada muke yi.

                      

 Domin aure ibada ce, hakan ya sa kamar yadda ko wace irin ibada za mu yi, tsoron Allah shi ne a gaba, domin kuwa duk wani abu da za ku yi, wanda zai sabawa umarnina ko kuwa sabawa hakkin zamantakewa.

                      

To tamkar kun sabi Allah ne. Tunda shi ya umurceku da ku min biyayya a matsayina na mijinku. 

                      

Wannan ya kawoni ga magana ta biyu, wato shi ne hadin kanku. Lallai ne wannan yana da muhimmanci a zaman mu, domin kuwa idan ku ka daga hankulanku. To ni ma nawa hankalin ba zai kwanta ba, bare har na samu na gudanar da al'amuranku cikin sauki da adalci ba.

                      

Ina addu'ar Allah ya hada kawunan mu baki daya, ya sanya albarka a cikin wannan gida. Ya albarkaci zuri'ar mu, ya kuma karo mana zuri'a masu albarka. 

                      

Dukkan ku ba yara bane, kowacce ta mallaki hankalin kanta, wannan ya sa zan ce maku ku san yadda za ku yi maganin Differences dinku, ba zan zauna da ku duka ba, alhali ku na gaba a karkashin shugabancina, wannan ya sa ya zama lallai ku kulla mu'amala kyakkyawa a tsakaninku. Cikinku akwai wacce take da magana ko tambaya?"

                      

Hamama ta gyara zama, sannan ta dubi Mai-jidda, dukkan su ba wacce ta-ce wani abu, ganin haka Abdul-Aali ya-ce.

                      

 "To sai maganar raba lokaci tsakanin ku, zuwa lokacin da Jidda za ta koma PH, tunda yanzu tana Kano, wannan ba matsala bane, sai dai idan ya kasance duka ku na gari daya. Wannan zan bari, sai ku yi shawara tsakanin ku, yadda ku ka ga ya dace maku."

                                      

                        

Hamama ta-ce. "Duk abin da ka ce."

Ya dubi Jidda, ita ma ta yi na'am. "Tunda duk kun yarda da hakan, shi kenan, duk lokacin da tafiya ta kamani, idan na dawo, wacce ta yi girki kafin na tafi, za ta ajiye, dayan ce za ta karba. Sannan idan da daya na yi tafiya, to wacce ba ta tafi ba, ita za ta karbi girki ranar, ina fatan kun fahimci bayani na?"

Mai-jidda dai tana jinsa, har ya gama bayaninsa, ganin ba su da tambaya ya-ce. "Shi kenan. Allah ya ba mu zaman lafiya. Ya kuma kade fitina, ni ma kuma ku tayani addu'ar Allah ya ba ni ikon yin adalci a tsakanin ku."

Duka suka amsa da Ameen. Sannan ya sallamesu.

Tana komawa daki, wanka ta yi, sannan ta yi shirin kwanciya, duk da dare bai yi ba sosai, tana ta tunanin bayanan Abdul-Aali. Allah dai ya taimaketa, ta samu Maman Mimie ta sauko daga fushinta, don haka ne kawai zai iya ba ta damar sakewa, su yi mu'amala.

Saukin abin ma dai ba tare suke zaune ba. Don haka ba wata damuwa. Tana cikin tunani ne, ya turo kofar dakin nata, ya shigo.  

Da sauri ta mike ta zauna. "Abdul-Aali?"

"Na ba ki tsoro ne?"

Kada kai tayi a hankali "A'a kawai dai ban tsammanci shigowarka bane, shi ya sa."

Ya samu gefen gadonta ya zauna hade da tankwasa kafarsa daya. "Yaya za ki ce ba ki tsammanci shigowata ba, bayan kin san ke ce da ni yau". Ya fada yana murmushi.

Mai-jidda ji ta yi kamar an dana mata wani abu a cikin hanjinta. "Mamin Mimie fa tana nan, ni kuma yaushe ka taba shiga daki na?"

"Don Mamin Mimie tana nan. Na ga alama ba ki ma saurari bayani na ba dazu."

"Ka bada speech mai kyau, kuma na saurara sosai, sai dai kai ma ka san makwancinka ba anan yake ba."

"Wai ni tun ana ce min Ango-Ango har an daina, bayan ma ba asan ko Angwancin ban yi ba." Ya fada cikin zolaya.

"Wannan kuma kai ya dama, dama ka fito fili ka ce ka ba ta kwanakin duka, saboda kai ma ka san da gangan ka yi, me za ka yi da matar da ka tsana?"

Shareta ya yi ya-ce. "Tashi ki yi alwala ki zo." Gabanta ne ya shiga faduwa, amma ta daure ta yi alwalar, sai da suka yi nafila, yai masu addu'a, sannan ya juyo ya dubeta.

"Game da amsarki ta dazu, ni ban taba tsanarki ba." Ya fada hade da kura mata idanu. "Yau kam zan fada miki me na ke ji game dake.

 Idan ki na so ki amince to, idan kuma ba ki amince ba, ya rage naki." Tabbas Mai-jidda ta san me yake ji game da ita. Abdul-Aali ya kula da canjin dake tare da ita.

"Ba ka taba tsanata ba ko? Wannan shi zai sa duk lokacin da na shiga wuri, ka ke saurin fita, sannan kuma hakan ne ya sa ba ka taba min murmushi ba, ko kai min magana, kai yi ma ka ke yi.

Kamar ba na Existing a rayuwa, duk iya lokacin da Dokta ke raye. Haihuwa fa na yi, amma ko gaisheni ba ka yi ba, bayan ka ga irin halin da na shiga. That's a real trick".

Mai-jidda ta yi wata gajeruwar busassheyar dariya. "Kai amma ni ma na rasa ina na samo dalilin cewa ka tsaneni, za ka iya min afuwa?" Ta fada cikin gatse, mikewa ta yi ta nade abin sallarta, sannan ta zauna a kan gado.

A take zuciyarsa ta kamu da ciwo da kuma mamaki, dalilin mamakin kuwa, bai taba tsammanin ta damu a kansa da har zai sa ta kula da halin ko in kulan shi gareta ba, ciwon da ya ji kuwa.

 Shi ne ya gwammaci ya mutu da ya cutar da Jidda. Zama ya yi a gefenta sannan ya-ce. "Me ki ke son na yi?" Ya fada cikin murya kasa-kasa. "Akan abin da na ke ji game da matar Dan-uwana?"

Baki ta bude tana kallon sa. Abdul-Aali kuwa ya yi amfani da wannan damar ya-ce. "Sai na samu Rayyaan nace masa Dan-uwa, ka san matarkan nan ko?

 Ina so na fada maka cewa ba abin da na ke so, duk duniya kamarta, ban taba son wata 'ya mace kamar yadda na ke sonta ba. Ina fatan ba za ka damu ba?' Ina tsammanin idan na yi haka, ba za a kwashe lafiya ba Jidda, ko kuwa?"

                

                        

Mai-jidda ba ta motsa ba, sai ma wani tsuma da take yi, da wani abu a cikin jikinta.

"So? Shin kam maza, ba abinda za su samu suka fi so ba?"

Zuba mata idanunsa yayi "Kar ki min haka Jidda, kar ki kawar da maganar nan, ba abinki da baida muhimmanci a tare da ni, shin kin san da hannuna na kirga lambobi, saboda lokaci ya yi saurin tafiya, a sanda ki ke nakudar Muhammad, saboda ba zan iya jure ganinki cikin wuya ba? Ko kuwa kin san a satin da ya kamata, ina angwancewa, kwana nake yi ba na barci. Saboda da zarar na rufe ido, kukan ki na ke ji cikin jin ciwon nakuda?"

Mai-jidda ta kai hannu baki ta rufe cikin mamaki, tare da hadiye wani sautin da ya taso mata a makoshi.  "Sannan duk lokacin da na bude ido, na ga kallon da ki ke yiwa Yaya Rayyaan... Yaa salaam! ...kin san yadda na ke fatan da ace ni ki ke yiwa wannan kallon?"

"Abdul-Aali..." Ta fada tana girgiza kanta idanunta cike taf! Da hawaye.

Bai kula ta ba ya ci gaba da fadin "Kin san da cewa har yanzu sakon ta'aziyyar ki yana adane a wayata? Za ki iya tuna me ki ka rubuta? 'Ina fatan a ranakun da za su zo, za ka daure ka kula da amanarka cikin tuno kyawawan lokutan da ka debe tare da Dan-uwanka, mun yi rashi sosai, amma Allah shi ya dauki abin sa.Ya tafi ya bar mu a hannunka, da fatan za ka rike amanar da ka dauka. Allah Ya bashi mafificin makoma, Hauwa'. " Ya yi shiru, muryar sa na neman ta gagare shi fita. "Ki na fahimtar zance na kuwa?"

Yana ga kamar ta fahimta saboda hawayen dake idanunta ya-ce "Ki na da ilimi, ki na da juriya, kin kula da Rayyaan a cikin rashin lafiyarsa ba tare da nuna gajiyawarki ba.

 Ki na kula da Muhammad tamkar ba komai bane me wuya duka ke kadai. Sannan ki na saka zuciyata ta tsaya cak! a duk lokacin da na daga ido na kalleki, Jidda!"

"Ya Allah, Dokta gaskiya ya fada, ya gane komai me ya sa ni ban gane ba? Me ya sa sai yanzu?"

A hankali ya sa hannu ya riko nata ya ware mata su sannan ya kai  hannun bakin sa ya sumbata. 

"Saboda na baki shekaru biyu ki yi makoki, kin kuma gama tunda kin fara kula wasu da niyyar aure ba zan iya nesantar ki ba ko da na dakika daya ne." Shiru ne ya ratsa su kadan sannan ya sauke ajiyar zuci, hannunta har yanzu cikin nasa ya murza yatsunta  hade da duban idanunta  "Kin san kece dalilin tafiyata UK a karo na biyu?

Saboda na nisance ki na baki daman yin makoki don ban yarda da kaina ba a kanki Jidda, ko yaushe ina samun labarinki da na Muhammad a wurin Mama. Wannan ya sa na samu labarin kina shirin sake wani auren."

Ta dube shi da lumsasshun idanunta, wadanda suke tamkar sun gaji. "Kar ki yi tunanin sa Jidda." Ya rike fuskarta a tafukan hannun sa, sannan ya duka har sanda ya kusa taba labbanta. "Just think of us." Yana fadin haka, ya ida niyyarsa.

*******

Mai-jidda ba ta san duniya ma kala-kala ba ce, sai da Abdul-Aali ya kai ta wanda ba ta taba ziyarta ba, ta fahimci hakan. 

Da sassafe ta shirya ta tafi kicin, don gida da yara. Nan da nan ta shiga shirya Breakfast. Zuwa karfe takwas ta gama komai ta shirya a falon sa. 

Dispenser ta kunna saboda ruwan zafi, sannan ta shiga bangaren Hamamatu, ganin kofar a bude. A falo ta sameta tana yi wa su Ramla tsifa, ta gaisheta, yau dai ta amsa ba laifi, hala nasihar jiya ce ta shige ta?

"Mamin Mimie, idan kun gama, na sa Breakfast a falon Dadin Mimie."

"To". Ta-ce mata.

"Mimie za ku sha Corn-flakes?"

Da wuri ta-ce eh, don haka Mai-jidda da ta koma ta sa kwalin Cornflakes da su kayan Tea a falon. A dakinta ne ta samu Abdul-Aali ya shirya cikin kananan kaya, nan take ta rasa me za ta yi. Wani irin nauyi ta ji saboda Allah kadai ya san me ta fada jiya da ba ta cikin hayyacinta.

Ita dai daman ba ta yarda da kanta ba, amma ba ta taba tsammanin dan bayanin da ya mata na cewa ya dade yana sonta, ko kuwa ba wanda ya kai shi sonta duk duniya ba,  zai sa ta sakar masa komai ba.

 Don haka ne da ya zo kusa da ita zai shafa fuskarta, cikin gaisuwa ta yi saurin kawar da kanta ta-ce. "Ina kwana?"

"Hmm! (This is not fair), gaisuwar da na cancanta kenan? Bayan sai da aka gaida kowa a gidan nan, kafin a gaisheni?"

Nan ta shiga in ina, tana cewa. "A... abin karyawa na falo, su Mimie suna can".

Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya-ce. "Jiddah!" Wannan kiran da ya yi, ta yi kuskuren daga idanu ta dube shi. Nan take wani abu ya narke a cikinta. 

"Dadin Mimie, don Allah ka manta duk abin da ya faru, kuskure na ne, kuma hakan ba zai sake faruwa ba, don haka, don't get any ideas." ta fada tana juya idanunta.


"uhumm. Amma kuwa ba haka na ji kin ce jiya ba". Ya fada yana dubanta da kyau.

Ta yi saurin zare idanu. Yau ta shiga uku me ta ce? "Koma dai menene, ina son ka san cewa ba na cikin (right state of mind) na, ba ni cikin hankalina, don haka, ka manta da na fada".

Murmushi ta gani kawai a makale a fuskarsa duk da bai ce komai ba yace komai.


Oh he's loving this!

Ta sa kai za ta fita daga dakin, ya riko hannunta ya hada ta da bango, tana jin hucin numfashinsa a fuskarta.

 Ji take yi tamkar a cikin jikinta yake tsabar kusancin sa, rufe idanu ta yi tana jira ta ga ikon Allah. Numfashinta kuwa tamkar na aro, wanda yake sauri ya komawa mai shi.

 "Ki na so ki ce min ba kya son wannan?" A hankali labbansa suka taba gefen kunnenta, wanda ya sa ta ji tamkar wani wutan shocking aka sa mata, haka ta narke kamar roba.

 "Ko wannan?" Ya sauko a hankali zuwa habarta, kafin ta ankara da abin da yake shirin mata, don haka nan da nan ta yi saurin matsawa ta gyara muryarta, sannan ta-ce. 

"Ba na so." Sannan ta fita daga dakin. Abdul-Aali ya dade a tsaye a wurin, kafin ya fita zuwa Side din sa, can ya same su da yara, tana ta faman biye masu.

Da gudu Ramla ta dare shi tana cewa. "Daddy ina kwana?"

Mimie ma ta bi sahu, duk suka makale uban. Mai-jidda ta ji sun burgeta, suna komawa wajen zamansu. Mamin su ta shigo, kai tsaye ta rankwafa daidai kujerar Abdul-Aali ta sumbace shi a kunci, tana ce masa.

 "Ina kwana." A take Mai-jidda ta kawar da kai cikin runtse idanu, ta tuna lokaci kankani da ya wuce. Yayi mata shigen wannan, sai dai nasa ya fi birkita kwakwalwa.

 Amma wanda Hamamatu ta yi, sai ya rufe mata idanu da haushi. Me ya sa ba za ta bari sai suna su biyu ba? Wata zuciyar ta-ce, ki ka san ko haka ya saba gaisawa da matarsa? 

Daga idanun da za ta yi, suka yi ido hudu da Abdul-Aali, wani murmushi yayi mata tamkar mai mika sakon idan ke ba za ki yi ba, ina da mai min. 


"Hmm! Ba sai ku yi ta yi ba".

Post a Comment for "KE NAKESO CHAPTER 4KE"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...