Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

JAWAHEER CHAPTER 5

JAWAHEER CHAPTER 5

- - Post a Comment
JAWAHEER

CHAPTER 5Kallonshi tayi ya sakar mata murmushi tare da daga mata gira, yace jawaheer banso ana damunki sai yasa na canza miki sim nd kuma ban san any abu da zai daga miki hankali kin san abubuwan da suka faru na sanin basu mum bane iyayenki kin san tunda maganan nan ta fito kowa zaiji, nd kuma nasa wasu za suyi ta kiranki dan suji maike faruwa, banso wani koh wata su daga miki hankali har zuwa sanda zamu gano inda iyayenki suke, hannunta biyu ya kamo ya matse tare da fadin sai yasa na karya layin, murmushi tayi tare da fadin banyi fushi ba, kawai na dan damune akan mai yasa ka karya sim din ba tare da kamin bayani ba, amma yanzu da naji komai sai naji hankalina ya kwanta komai kuma ya wuce, yace dat my sister, yaushe zamu tafi abuja? Tace ba kace sai anyi kwana biyu ba,yace yes inaso in saba da kakanninmu gashi kuma bana jin yaranku, tace bari in fara koya maka, yace yauwa amma ba'a nan ba, kizo mu tafi waje, tace ok bari in canza kaya, yace ok ki sameni mota, daki ta shiga tasa wata jallabiya tare da yafa gyalen jallabiyan, ta nufi dakin adda taga tana bacci dan haka ta fita kawai tana shiga mota taga anja bata cemai komai ba har suka isa wani hadaddan restaurant babu kowa sai su kadai daka gani yasa an kama mai wajan ne duka, shiga sukayi suka zauna, kallonshi tayi tace mai za muyi a nan? Yace abinci zanci kin san ba komai na iya ciba, nd ke kuma baki damu damai naci ba, tayi narai narai da ido tace nifa kasan bani da lafiya ba yau na dawo gida bama, murmushi yayi yace hakane, my baby da sauri ta dago ta kalleshi hada ido sukayi ita tana mamakin sunan daya kirata dashi, shiko yana mamakin mai yasa kullum jawaheer take kara kyau, idan yaga ta mishi kyau yanzu anjima kuma sai tafi kyau,hura mata fuska yayi tayi firgit tasa hannunta ta rufe fuska tana dariya, dai dai lokacin masu saida abincin wajan suka zo suna tambaya mai za'a kawo musu, fada musu yayi ita tace tuwon semo miyan kuka, suka tafi, basu dade ba suka kawo abincin, sannan suka roqeshi akan su dauki hoto dashi, bai musa ba haka ya tashi suka dauka, suna ta murna, zama yayi yana kallon abunda jawaheer zata ci, lokaci daya kuma yayi dariya yace jawaheer miye haka? Tace mene? Yace wannan abun da zaki ci miye? Tace tuwo, kasa fadan sunan yayi, tace ka gwada ci akwai dadi sosai, kai ya girgiza alaman a'a, murmushi tayi ta fara ci, mai yakon yaci nashi saiya tsaya kallonta yanda take ci sai yaji abun ya burgeshi, dan haka shima yasa spoon cikin tuwan yaci ido ta kura mishi, taga ya cinye ya kara ci wasa wasa sai gashi ya cinye tuwan duka, saida ya gama yace ashe akwai dadi sosai dariya tayi tace abincin mu yana da dadi, murmushi yayi sannan ya fara cin farfesun kazan da aka hado mata dashi bai wani ci da yawa ba ya ajiye tare da kallonta yace ban taba cin abinci mai yawa irin haka ba, dariya tayi tace dan wannan abincin shine mai yawa? Yace eh mana, yace toh a fara koyamin hausa, tace mai kake so ka koya?? Yace komai amma nafi son in fara koyan gaisuwa, nan ta fara koya mai gaisuwa tana fada mai da turanci saita fassara mai, sannan ta koya mai tambayan abu, da wasu yan abubuwa, murmushi yayi tare da kunna wayanshi taji magananta ashe recording yayi, kokarin kwace wayan ta farayi wai zata goge garin haka ta fada jikinshi sukai qasa, wani irin yanayi dukansu suka shiga musamman ma shi, domin kirjinta ne ke kwance akan jikinshi, ganin irin kallon da yake mata yasa ta tashi da sauru tare da fadin kayi hakuri, baice mata komai ba harya tashi sannan yace baki ji ciwo ba? Kai ta daga mishi alaman eh, cikin sanyin murya tace muje gida dare ya farayi, tashi yayi yace muje, mota suka shiga aka sauketa kaman bazai fita ba komai ya tuna oho ya fito har kofan gidan ya kaita sannan yace mata saida safe, bata bashi amsaba ta shige, a falo ta tarar dasu mum harda dad, mum tana ganinta tace jawaheer daka ina kike maiya sami wayanki? Tace mum muna tare da m samir sannan na canza number ne, ido dad ya bita dashi yace saboda me kika canza number kuma baki bamu ba, tace dad m samir ya siya mana dazu nan ta fada musu number din suka saka, dad yace zai tafi hotel din daya sauka mum ta rakashi jawaheer kuma tayi dakin da take kwana ita da mum.
M samir koda ya isa an kira sallah isha'i dan haka saida yayi sallah sannan yayi wanka ya kwanta, amma kuma sai me?? Tunanin jawaheer ne cike a ranshi, musamman dazu data fado mishi jiki ido ya lumshe tare da fadin maike damuna? Kanwata ce da sauri yace no bazan iya ba kanwata ce kawai sabuwan da mukayi ne yasa nake jin wani abu but zanyi dan nesa da ita, duk yanda yaso ya cire tunanin jawaheer ya kasa daka karshe recording din da yayi ya kunna yana jin muryanta yana dariya har bacci ya daukeshi.


Itama ta gefen jawaheer tunanin nashi tai tayi ga wani irin azabban sonshi dake kara shiganta, Allah ya sani tana hakuri da irin son da take mishi amma ya kasa fahimta wani lokacin har tunani take inda zaice ta bashi jikinta zata iya bashi dan dai kawai yasan tana sonshi, duk da wani lokacin tana kokarin cire shi a ranta amma ina abun ya gagara sai dai kullum tayi sallah tana roqan Allah mafi alkhairi.

Washe gari da safe jawaheer ta tashi da wuri, ita ta share tsakar gidan tare da hada kayan wanke wanke ta wanke su tas, adda ta fito tace jawaheer keda baki da lafiya inake ina aiki? Mai makon ta bata amsa saita gaidata da fadin ina kwana adda, murmushi adda tayi tace lfya ya karfin jikin naki? Tace alhmdlh naji sauki, adda tace haka akeso Allah ya kara mana lfya, tace ameen yar tsohuwa, dariya adda tayi tace aina fiki kyan jiki, jawaheer tace wa tab aida ban sami samari ba, adda tace ina samarin tunda kika zo banji anyi sallama ba, niko sanda ina budurwa zo kiga layi, jawaheer dariya take tayi tana fadin ba wani layi kakana kadai ke zuwa inna aureshi nasa ya sallameki dan kin mai tsufa, mum ce ta fito tana dariya tare da fadin ina kwana adda, adda ta amsa cikin fara'a tare da fadin kinga yar nema sauki ya samu zata damemu da surutu, mum dariya tayi dan harga Allah taji dadin yanda jawaheer ta sake yau har take ta fira, wanda rabonta data sake irin haka tunda tasan basu bane iyayenta amma yau gashi tana ta surutu, mum tace adda ina zan sami waina shi nake son ci yau, adda tace shine tun jiya baki magana ba aida anyi yau,kira abubakar ya siyo miki, tace toh daki ta koma ta dauko wayanta ta kira abubakar, sannan ta dawo tsakar gida inna adda da jawaheer keta kulla alale, suna fira, ita hannu tasa ta taya su, har suka gama jawaheer ta daura akan murhu, har alalan yayi suka faraci amma banda mum dan tana jiran waina, sallaman abubakar ne yasa su duka suka daga kai, amsawa sukayi sannan ya shigo ya ajiye cooler din tare da gaida adda, itama mum gaidashi tayi sannan itama jawaheer, bayan ya amsa yake tambayan jawaheer ina m samir bai zo bane? Tace eh bai zo ba uncle, murmushi yayi tare da fadin bari inje in shirya yau yace yawo zamu tare, mum tace yadai kamata shima yaga gari da irin al'adunsu, harya tashi zai fita ya dawi tare da tambayan ina mlm mahaifinsu kenan, adda tace yana bacci, yace mai gari jiya ya ganni yake tambaya na wai dagaske khausar ta dawo gari, nace mishi eh yace shine mlm bai fada mishi ba, nace toh nima ban san dalilin hakan ba nayi tafiya ta, mum tayi dan murmushin takaici tare da fadin naga kasar nan ta kowa ce kuma kowa zai iya zuwa inda yake so, koda can baya rashin sanin yanci nane yasa akamin haka, adda tace Allah dai ya kyauta suka amsa da ameen, sannan abubakar ya fita, jawaheer kam bayan ta tattare kayan da suka ci abinci ta wanke daki ta koma tayi kwanciyanta tare da tunanin m samir, haka taita zama a daki har wajan karfe daya ta fito tayi alwala ta koma tayi sallah, bayan ta idar taji mum na kiranta fita tayi tace mum gani, mum tace kije kici abinci mana, kin shige daki ko dai jikin ne? Tace a'a mum tashi tayi taje ta zuba abinci kadan ta zauna kusa da mum tana ci tana tunanin ina ma mum ce mamanta ta gaskiya da tafi kowa farin ciki, ajiye abincin tayi dan taji yana mata daci, mum tace badai wai har kin koshi ba? Tace eh mum bana jin yunwa sosai, shuru mum tayi dan tasan halin jawaheer ba'a matsa mata akan abu yanzu ta fara kuka, jawaheer damuwa ya mata yawa na rashin ganin m samir haka taita zama har yamma amma shuru bai leqo gidan ba, har mum da dad suka fita koda dad yazo yace ta bisu taki yarda ta bisu tace suje, tana zaune a falo adda ta zauna kusa da ita, duk tana lura da jawaheer tace jawaheer nikam wani irin so kikema wannan yaron haka? Jawaheer tayi dan murmushi tare da fadin adda niwa nake so? Adda tayi dariyan manya tace kaji ja'ira, bayan keda bakinki kin fada munji ko kin manta ne? Jawaheer tace kai ku tsofaffin nan bakwa mantuwa wlh, adda tace jawaheer naga kaman shi bawai yana sonki bane, irin yanda ke kike sonshi, amma zan baki shawara duk da nasan miye so ya kuma akeji dan nima auran so nayi duk da a lokacin ba'ayi, hada ku akeyi sai akaci sa'a muna son juna, ya kamata kibama wani namiji dama dan ya shiga cikin rayuwanki sannan ki nunama samir kema a matsayin dan uwa yake a wajanki yanda shima yake nunawa, ji jaraba wannan abun guda biyu idan kikayi zan kara miki wasu, jawaheer tayi dariya tace zan gwada yar tsohuwa suna zaune kam sai gashi wani yaro yayi sallama, wai ana kiran jawaheer, kallon juna sukayi ita da adda, sannan adda tace kaje kace tana zuwa, yaron ya fita jawaheer tace adda taya zani bayan ban san ko waye bane? Adda tace sai yasa nace kije ki gani, tashi tayi daka ita sai dogon wando da top amma yakai mata giwa sai wani dan shara sharan gyale ta yane kanta dashi, fita tayi taga wata mota kiran matrix tsayawa tayi sai taga an bude motar wannan dr din ta gani wanda ya dubata a asibiti, da murmushi akan fuskanshi yace bismillah ki shigo ciki mana, tace nan ma ya isa ai yace ba mutunci bane mu tsaya a waje...... Hasken mota ne ya hasko su, motocin m samir ne da security dinshi tun daka nesa ya hangosu suna tsaye, bayan motar ta tsaya ya fito zai wuce dr yace m samir tsayawa yayi tare da fadin dr ya aiki? Dr yace lfya tare da miga mai hannu suka gaisa hada ido sukayi da jawaheer wani irin kallo ya mata mai kama da harara, sannan ya shige ciki, dr yace shigo muyi magana, jiki a sanyaye ta shiga ciki,yace nazo inji ya jikin ki? Tace na warke nan ya fara mata surutai wanda gaba daya bama jinsa take ba, shiko m samir yana shiga yaga babu kowa sai adda ya gaidata da hausa tana ta mamaki tare sa fadin sai anjima kallo ta bishi dashi dan mamaki harya fice bata ce komai ba, koda ya fita yaga sun shige mota tsaki yayi tare da kawar da kanshi gefe ya shige mota akaja suka bar wajan.......Jawaheer kam bata Jin komai na abunda dr yake fada mata, shima kaman ya lura da hakan yasa yace mata bari ya barta yaga kaman ta gaji, hakan ya mata dadi yace ta bashi number dinta, bashi tayi sannan ya bata ledoji manya guda biyu daya kawo mata, amsa tayi tare dayi mishi godiya sannan ta fita tayi gida, a falo ta tarar da adda tana cin danwake, zama tayi kusa da adda tace adda samir yazo naga bai dade ba ya fita, adda tace hmm aini yau yaban mamaki, kinji hausa gaidani yayi da hausa harda cemin saida safe, jawaheer kam shuru tayi tana tunanin mai yasa ya tafi bai bari ta shigo ba, jin adda tayi ta katse mata tunani da fadin nasan ya ganki keda wani koh? Tace eh adda wannan dr din nanne yazo dubani, kinga yanda ya sakar min harara nan taba adda labarin abunda ya faru, adda tayi murmushi tace jawaheer inaso ki nutsu ki bama wannan dr din lokacinki dan ki nuna ma m samir kema fah akwai masu sonki, jawaheer tace adda shifa dr gaidani yazo yi ba sona yace yakeyi ba, adda tace aida haka zai fada miki, kedai kawai kiyi abunda nace..... Sallaman mum ne ya katse musu firan da sukeyi, jawaheer da fara'a tace mum har kun dawo sannu da zuwa, mum ta amsa tare da fadin dad dinki yace kije yana waje, tashi tayi ta fita ta sami dad a mota, dad yace jawaheer gobe ni zan koma ko akwai abunda kike bukata? Tace a'a dad babu komai sai dai ina son ka canza masu adda gida inda hali, dad yayi murmushi yace naso nayi hakan amma m samir ya rigani dan dazu abubakar yake fadamin fitan da sukayi gida yaje ya siyan musu cikin adamawa, abubakar yace gidan babba ne akwai komai da komai domin gidan wani barawon gwamnati ne wanda ya saci kudi shine gwamnati ta kama gidan ta saida, jawaheer tace kai Allah ya saka mishi da alkhairi, dad ya amsa da ameen, sannan yace an fara biyan kudin aikin haji, zan biya musu sai yasa zan koma ma gobe, sannan ina aiyuka, jawaheer tace Allah ya saka maka da alkhairi dad, murmushi yayi tare da kara son yar tashi ba ita yama abu ba amma tana ta godiya, kudi ya dauko ya bata ta amsa tare da fadin dad nida transfer kamin ma da yafi, dad yace toh riqe wannan din bari in miki transfer din ma, nan ya mata transfer tace kai dad kudin yayi yawa, yace jawaheer kudin da nayi ta sanadinki ne in baki ciba wa zaici, sannan million dari din da mum dinki ta bani lokacin data miqa mana ke, dasu na fara sana'a har nayi mugun arziki inada kalan kudin wajan sau million, na ware miki million dari na ajiye duk sanda naga mahaifiyarki zan bata kudin, wani hawaye ne ya zubo ma jawaheer tare da fadin dad idan na tuna baku kuka haifeni ba ina shiga cikin wani hali, wlh dad zuciya na yana zafi inna tuna hakan dan Allah dad kubar tunamin, ta karasa zancen cikin kuka, ya janyota jikinshi yana bata hakuri tare da fadin jawaheer ke yata ce har gobe, murmushi tayi tare da fadin ngd dad, yace bari inzo in tafi bacci nake ji, tace toh saida safe dad, gida ta koma inda ta sami adda ta fiffito da kayan da dr ya kawo kayan tea ne manyan gwangwani dasu milo sugar kwali dasu biscuit chocolate, mum tace ashe dr yazo dubaki? Tace eh mum, mum tace wannan hidima haka Allah dai ya saka mai, adda ta amsa da ameen, jawaheer kam haushin kayan ma taji tana yi, dan me yasa zai kawo mata suma, tashi tayi ta nufi daki, bata dade da shiga ba mum ta shigo, tace mum ashe samir ya siyama su adda gida? Mum tace eh wlh gobe zamu gidan ma muga in akwai abunda yake bugata duk da abubakar yace basai ansa komai ba, amma gobe zamu mu gani, jawaheer tace Allah ya kaimu, jawaheer ta kasa bacci babu abunda take son ji sai muryan m samir tashi tayi ta fita ta kira number dinshi amma taji ance switch off, tsaki tayi ta koma daki ta kwanta sai juyi take tayi.

Story continues below

Washe gari tunda jawaheer tayi sallah asuba take ta kallon wayanta tana tunanin kota kira m samir ne, amma tana tunanin kaman bai dace ta kirashi yanzu ba, dan safiya ne, haka ta zauna akan dadduma harta fara bacci, bata farka ba sai wajan 9 ta ganta akan gado, murmushi tayi dan tasan mum ce ta kawota gadon, fita tayi ta nufi toilet, tana fitowa taga adda tace ga ruwan wanka nan dama yanzu zan kiraki, jawaheer tace toh yar tsohuwa, ansan ruwan tayi ta shiga toilet din, wanka tayi sannan ta fito ta shirya cikin atamfa riga da skirt ya mata bala'in kyau kaman ba itaba, adda tace kai jawaheer atamfan nan ta miki kyau amma na lura dake kaman ke bakya son irin wannan kayan kin fison kiyi ta shiga kaman ba musulma ba, dariya jawaheer tayi tace lah nice ba musulma ba? To a kunnen mai gidan, dai2 lokacin mlm ya fito yace kyaleta amarya ta kishi takeyi dariya adda tayi tace ni na yafe mata kai, jawaheer tace kaji kishin koh kaman dagaske take, dariya duka sukayi mlm yace yaushe zaku gidan? Mum tace anjima kadan abubakar muke jir..... Bata rufe baki ba saiga sallaman abubakar da m samir sun shigo, gaban jawaheer ne ya fadi kallo daya ya mata ya kawar da kanshi, gaida su mum yayi, itama jawaheer ta gaida uncle dinta, ya amsa sannan ta gaida m samir wanda ya amsa a dakile ba tare daya ko kalleta ba, mum tace ma m samir yaci abinci kuwa? Yace a'a tace ai naga alama murmushi yayi mum ta kalli jawaheer tace kema kije kici abinci kafin mu tafi, sannan ki dauko m samir kayan tea tace to, kitchen din adda ta nufa ta hada mishi kayan tea tare da soya mai akwai, falo takai mai shi daya ne a falon su mum na waje suna fira, ajiye mai tayi tare da fara kokarin hada mishi yace no leave it zanyi da kaina, sororo tayi tare da ajiye spoon din jiki a sanyaye, tana son yin magana taji yana fadin gobe zamu tafi abuja, da sauri ta dago tana kallonshi amma shi ba ita yake kallo ba, tace da wuri haka, bana tunanin zan biku gaskiya wani irin kallo ya mata da yasa tayi saurin yin qasa da kai, adda ce ta shigo tace jawaheer kuyi sauri mana, fada mishi dan Allah tunda baji nama yake ba, cikin sanyin murya tace ance kayi sauri muje, kai ya daga alaman yaji, tashi tayi itama ta fita waje da ido ya bita harta bace mai sannan ya lumshe ido, tana tafiya yaji abincin ya isheshi dan haka tashi yayi ya fita shima, uncle abubakar yace zaije kasuwa bada shi zasu ba, mum da adda suka shiga mota daya jawaheer da m samir kuma mota daya, sai security din dake mara musu baya, sai sharara gudu mota takeyi amma babu mai cewa komai, wayan jawaheer ne ya fara kara dan haka ta duba taga number ne, mamaki tayi toh wa yasan number dinta ita dai tasan bata kira kowa ba, har kiran ya tsinke wani kiran ya kara shigowa ta kalli m samir taga ba ita yake kallo ba dan haka ta dauka, tana dauka taji anyi mata sallama ta amsa yace nasan baki ganeni ba koh? Tace eh, yace dr ne, harga Allah ta manta ta bashi number dinta, tace eyya yaka koma gida? Yace lafiya qalau sai dai na tafi da tunaninki, tayi dan murmushi wanda a dai2 lokacin m samir ya waigo suka hada ido, wani irin kallo ya mata wanda yasa tayi saurin juyar sa kanta gefe, ci gaba tayi da wayan taji an fisge, da sauri ta waigo taga yana watsa mata wani irin kallo, yace dawa kike waya? Tace friend dina, yace ok daka yanzu in zakiyi waya a gabana karki karayin wani yare sai english, bata ce mai komai ba ya jefa mata wayan tare dayin tsaki kadan, bai kara ko kallonta ba balle ya mata magana wayanta ne ya fara kara, ganin number din dr yasa ta kashe wayan gaba daya, tafiya suke har suka karasa wani dangareren gida sukai horn mai gadi ya bude, suka shiga ciki bayan an faka suka fito, m samir yana fita baiko bi takan jawaheer ba ya nufi wajan su mum, jawaheer kam canjin da yake nuna mata ya fara damunta domin taga yana nuna halin ko in kula da ita tun jiya, amma koma dai miye yau sai taji miye dalili, shiga gidan sukayi wani dangareren falo suka shiga wanda yaji kayan more rayuwa, adda salati ta fara tana fadin ina zamu kai wannan gida? Dariya su mum suke ta mata suna fadin adda an zama yan gayu, gidan yayi bala'in haduwa gashi gidan sama, falo biyu ne a 'kasa sai daki daya a kasan, sama kuma falo daya ne sai daki uku a saman, fadin tsaruwan gidan bata bakine, adda harda hawaye tana ta sama m samir albarka tare dasu mum, tace jiba abunda muke ta kyama gashi yazo duniya ya bamu babban kyauta, haja taita mai godiya shidai murmushi yake tayi dan bai san mai take fada ba, adda tace babu abunda za'a sa a gidan hakan ya isa, mum tace shikenan dan itama taga babu abunda gidan yake bukata, haka suka fito da fadin zasu sa ranan dawowa, shiga mota sukayi dan tafiya gida, suna cikin tafiya jawaheer ta kalli m samir tace Allah ya biyaka gidan yayi kyau sosai, banza da ita yayi, ji tayi kaman tayi ihu dan takaici, ta bude baki zata kara magana taji yace mai adda take fada dazu? Dadi taji koba komai ya mata magana, tace godiya take maka tare da addu'a, dan murmushi yayi sannan yace ok, ya ciro wayanshi ya danna wasu numbers jim kadan yace dad yakake, shuru yayi sannan yace dad komai normal nan ya fara bashi labari dad din yaji dadi sosai tare da fadin ina jawaheer baice komai ba taga ya mika mata waya, amsa tayi tare da fadin hello dad yace yarinya ta yakike? Amsawa tayi tare da gaidashi nan suka taba fira tana ta dariya daka karshe sukai sallama, ta mika mai wayan sawa yayi a kunne ban san mai dad din ke fada mishi ba naji yace ok dad ba damuwa gobe zamu koma abuja muma, yana fadin haka sukai sallama, kallon jawaheer yayi suka hada ido murmushi ta sakar mai tare da fadin wai mai nayi maka kake shareni? Dan tsaki yayi tare da fadin babu komai, tace toh mai yasa kake shareni? Yace haka kawai bana son damuwa, sakan baki tayi tana kallonshi wato nice damuwa ma, dan tsaki tayi wanda bata san ya fito ba jin hannunshi tayi a bakinta yaja tare da fadin wa kike ma tsaki? Kasa magana tayi dan ya riqe mata lebe, ganin yanda tayi da ido kaman zatai kuka yasa ya sakan mata bakin tare da fadin karki kara min tsaki i hate it, bata ko kalleshi ba balle yasa ran zata bashi amsa, yau ce rana ta farko daya taba bata haushi, danme zai dinga wani shareta ba tare da tamai komai ba, inda yasan yanda ta shiga cikin damuwa aida bai mata haka ba, ido ta lumshe kaman mai bacci, bini bini ya kalleta ganin kaman tayi bacci yasa ya kura mata ido tare da fadin slp beauty, tafiya mota keyi tana sharara gudu, jin tsayuwar motar ne yasa ta bude ido mai yakon ta ganta a gidan adda saita ganta a hotel din da yake kwana, kallonshi tayi suka hada ido, kawar da kanshi yayi tare da fadin muje, kaman ba zata fita ba, komai ta tuna kuma ta fito suka shiga tana biye dashi a baya, dakin da ta sauka tai niyan nufa taji ya janyota sukai dakinshi akan gadon dakin ya ajiyeta, toilet ya nufa yayi wanka jim kadan sai gashi daka shi sai towel ga kuma wani karami yana goge kanshi dashi, kallonshi tayi, tayi saurin kawar da kai, murmushi yayi tare da matsawa kusa da ita ya mika mata karamin towel din yace gashi ki gogemin, kin amsa tayi ganin haka ya kamo hannunta ya mika mata towel din, yace tashi kimin, bata tashi ba sannan bata mai komai ba, yace saboda niba saurayinki bane? Da sauri ta dago kai ganin yanda ya kafeta da ido yasa tayi saurin tashi tare da fadin zan wuce gida, kafada ya daga alaman ke kika sani, ganin yanda ya mata yasa ta fara kokarin fita har takai bakin kofa taji ya riqota tare da fadin wa yace ki tafi? Tace na gaji da zama a nan ne, yace ok to babu inda zaki yau tare zamu kwana ni dake cikin wannan dakin.......
Kallonshi tayi da sauri tare da zare ido, hada ido sukayi yayi saurin kawar dakai tare da tamke fuska, dan murmushin takaici tayi tare da kokarin jan hannunta daka nashi amma ta kasa danya riqeta tam, ganin tana son ya saketa yasa ya kara janyota jikinshi ta fado kanshi, zama sukai akan gado ya kura mata ido na wani lokaci sannan yace miye tsakaninki da dr din nan?? Da sauri ta kalleshi, ganin babu wasa a tare dashi yasa tace babu komai, yace toh mai yazo yi wajanki? Tace yazo ya gaisheni ne kawai, kai ya daga alaman yaji, sannan ya tashi tare da fadin muje muci abinci sai a kaiki gida, da sauri ta tashi kallonta yayi tare da fadin saurin me kikeyi haka? Tace inaso ne inje gida na gaji, baice mata komai ba yayi gaba itama ta bishi, fadama security din inda zasu kaishi yayi, wajan wani hadaddan cin abinci suka nufa, bayan sun zauna a private waje ta kalleshi tace mai yasa baya cin abincin hotel din? Yace hakanan, masu kawo abincin ne suka zo suka tsaya suna jiran su fadi abunda suke so, kallonta yayi yace kalan abincin da kika ci rannan nake so, dariya tayi tace ma mai kawo abincin ya kawo tuwon semo, da farfesun kaza, ita kuma ya kawo mata rice nd stew da garden salad, tafiya yayi jim kadan saiga abincin ko wanne fara cin nashi yayi, ita kam ci take sosai dan sai yanzu ta tuna tun safe babu abunda taci suka fita, har suka gama ta tashi zasu fita ta riqe cikinta tare dayin yar kara, da sauri ya karasa wajanta tare da riqeta yana tambayanta lfya? Tace cikina ke murda min, cikin tashin hankali yace bari muje hspt, tace a'a zai daina bari in huta kad..... Bai gama sauraranta ba ya dagata cak ya fita da ita har mota yace suje hspt wani asibiti suka nufa, nan akai emergency da ita ganin yanda ya daukota yasa suka zata ko emergency ne, dr ne ya shigo dakin ya fara dubata, yace baki ci abinci da wuri ba da kika tashi ci kuma sai kika ci wani abun mai yakon ki fara shan tea, magani dr ya bata tasha, tana sha ko minti biyar batai ba cikin ya daina, sannan dr din ya sallamesu, suna mota ya kalleta yace ya cikin? Tace naji sauki sosai, ido ya kura mata can yace maganan tafiyan mu gobe saiki shirya dan da wuri zamu wuce, tace daka bari mun dan kara kwana biyu a nan, kuma banji mum tayi maganan tafiyan ba, yace dazu mukayi da ita so dan haka tace babu damuwa saiki shirya, shuru tayi ba tare data kara cewa komai ba, ita inda so samu ne ta zauna ta kara kwanaki a nan, suna karasawa kofar gida ta hango dr yana zaune akan motarshi yana danna wayanshi, m samir ya ganshi kallo daya ya mishi ya kawar dakai tare da kallonta yace sai yanzu nasan abunda yasa bakya son tafiya, nd kin dameni zaki tafi gida ashe shike jiranki, tace wlh ni ban san zai...... Shut up ya daka mata tsawa inma kin sani in baki sani ba wannan ba damuwa na bane, the only thing i hate shine karya, kince babu komai tsakaninku mai yazo yi yanzu??? Tace nima ban sani ba kuma bai cemin zaizo ba, yace bani phone dinki, mika mai tayi da sauri ya amsa ya duba yaga wayan a kashe, kallonta yayi tare da miqa mata wayan amma taki amsa ya ajiye mata a jiki tare da fadin mai yasa kika kashe wayan?? Tace hakanan kawai, yace ok tambaya na karshe miye tsakaninki da wancan dr din?? Tace babu komai yazo gaida nine ran nan, yace yanzu kuma mai yazo yi?? Tace nima ban sani ba, janyota yayi jikinshi tare da bude kofar gefenshi ya fito ita ya janyota ta fito ta kofar daya fita daura hannunshi yayi akan kafadanta tare da janyo dayan hannunta yana wasa dashi yajata suka fara tafiya, dr dake zaune m samir yace dr yakake? Dr ya dago yaga jawaheer maqale a jikin m samir nan idanshi ya canza launi dan tsabagen kishi, dakyar ya iya amsa ma m samir, sannan yaja jawaheer sukai ciki, dr kam wani irin takaici ne ya cika shi, suna shiga gidan ya saketa tare da tureta yayi ciki, binshi tayi da ido tana mamakin mai yasa yayi mata haka? Miye dan dr yazo wajanta, shiga itama tayi jiki a sanyaye ta samesu a falo har dashi, suna magana da mum ita kuma adda tana taba mlm labarin gidan, jawaheer gaidasu tayi bayan sun amsa adda tace dr yazo nemanki tun dazu, tace eh na ganshi, wani yaro ne ya shigo da kaya wai gashi a bama jawaheer inji dr, m samir jin an kira sunan jawaheer kuma ance dr ya gane sakon daka dr dinne, dan haka ya tashi da sauri ya amshi ledan, chocolate ne dasu biscuit tsaki yayi tare da bama yaron yace ya tafi dashi, yaron duk da baiji abunda yace ba ya gane ance yaje an bashi ne, mum tace ya zaka bashi bayan na jawaheer ne, yace mum kayan zaki ne kuma ita tana fama da ciwon ciki,so naga babu amfanin amsa, in kuma tana so sai in siya mata wasu, mum wani irin kallo tamai tare da fadin waya gaya maka cikinta na ciwo? Nan yaba mum labarin abunda ya faru da taci abinci, mum tace ai wannan ba komai bane kuma zata iya shan chocolate din, yanzu idan dr yaga yaron ya fito da kayan baziji dadi ba, yace mum wannan ba damuwan mu bane, ita kam jawaheer tana kwance akan cinyar adda ta daura akanta a kai, duk tana jin abunda suke fada tadai yi shuru ne, tana tunanin irin wannan sabon salon na samir, adda tace jawaheer abinci na kitchen fah, tace na koshi adda, mlm yace mai kika ci? Tace munci abinci kafin mu zo nan, nan mum ta basu labarin abunda ya faru da jawaheer cikin harshen hausa, nan suka fara mata sannu, shidai da ido yake ta kallonsu, dan baji yake ba amma ya dan fahimta ya gane mum ta fada musu abunda ya faru da jawaheer dinne, tashi tayi ta zauna tare da rungumo adda tace zanyi kewarki addata, banso tafiya gobe ba, adda tayi dariya tace nima haka idan aka tafi sai kuma yaushe? Ido suka hada da m samir ya sakar mata wani irin mugun kallo, tayi saurin kawar dakai tare da fadin bazan dade ba zan dawo adda ta, haka sukai ta fira daka sun hada ido dashi ya watsa mata mugun kallo, daka karshe dai tashi tayi ta shiga ciki, bata dade da shiga ba shima ya wuce, hada kayanta tayi tayi, lokaci kadan ta gama hada kayan sannan ta kwanta dan ta huta, tunawa tayi da wayanta dake kashe ta tashi ta dauko ta kunna tana kunnawa saqo ya shigo cikin wayan, budewa tayi dan taga dr ne ya mata saqon ga abunda yace nan *haba jawaheer keda nake daukanki mai hankali da nutsuwa mai yasa zaki biyema wannan farin fatan bayan kin san irin tamu tarbiyan ba irin tasu bace kalli yanda yake wani riqeki kaman wani maharraminki haba jawaheer, tunda na fara ganinki nake sonki kuma soyayyan aure nake miki bawai na wasa ba, inaso ki bani dama mu fahimci juna sannan iyaye su shiga ciki, ina fatan zaki amsa bukata ta ngd daka dr nazir* tana gama karantawa ta lumshe ido lallai dr nazir namiji ne da duk wata mace zatai burin samu a matsayin namiji sai dai ita kash m samir ya sace mata zuciyarta tare da ruhinta bata ganin kowa sai shi, ya kamata ta fadama dr nazir gaskiya.... Dan shuru tayi lokaci daya ta tashi ta fita mum ce kawai a falo, tace mum ina adda? Mum tace tana kitchen fita tayi ta nufi kitchen din inda ta sami adda na zuba dan wake a tukunya wanke hannu itama tayi tazo tana taya adda jefawa tare da fadin adda kina son danwake sosai, dariya adda tayi tace ai akwai dadi ne, jawaheer tace lallai nikam bai cika damuna ba, adda tace kin bar dadi, tace ya akayi keda mutumin naga kaman dazu yana ta miki mugun kallo sannan an aiko miki da kaya daka dr ya kyautar, nan jawaheer ta bata labarin abunda ya faru bata boye mata komai ba, adda tayi dan murmushi tace jawaheer kici gaba da kula dr tunda har yace yana sonki, tace adda shifa m samir din fa? Adda tace yace yana sonki ne?? Shuru jawaheer tayi adda tace kiban amsa mana, tace a'a bai ceba amma ina fatan yace min haka, adda tayi dan murmushi tare da fadin jawaheer ke yarinya ce har yanzu baki san mai duniya take ciki ba, kawai inason kiyi duk wani abu da nace miki indai kina son ki tabbatar da zaki sami m samir ko bazaki sameshi ba, kar ki zauna zaman jiranshi kiyi biyu babu, idan m samir yana sonki dole yayi kishin ki, inko baya sonki komai za kiyi babu ruwanshi, dan haka ji shigo da dr cikin rayuwanki sannan koda kun koma wani abu ya faru ki dinga fadamin tace toh adda ta, haka sukai ta jefa danwaken har adda ta tsame tasa musu suna fira suna ci.
STORY CONTINUES BELOW


Shiko m samir ya rasa dalilin da yasa ya tsani dr, shidai abu daya ya sani bawai yana son jawaheer bane, kawai yana tausaya nata ne, dan shuru yayi lokaci daya kuma yace ba haka bane, kawai bana sonta da dr dinne dan ban yarda da hankalinsa ba, daukan wayanshi yayi ya doka mata kira, ringing biyu ta dauka, yace mata kin gama shirin mamaki tambayar tashi ya bata tasan dai dazu yana ta nuna mata halin ko in kula, yanzu kuma yana tambaya waiko ta shirya, tace eh na shirya komai duk da basan komawa nake gobe ba, yace saboda wannan dan iskan dr din koh?? Jawaheer ina tunaninki yake wai yaushe ma kika fara sonshi ne?? Shuru tamai tana jin ikon Allah daka cewa bata son komawa ya hakikance yana ta zagin mutum wanda baisan maike faruwa ba, tace kana cin hakkinsa domin shi bai san maike faruw....... Wani irin tsawa ya mata tare da fadin yimin shuru ban san haka kike ba, da tun farko ban daukeki a matsayin friend ba, wani irin takaici taji lokaci daya maganan da bata zata, zata fito ba taji ta fada nima fa budurwanka bace kace ni kawarka ce ina da right in kula duk wanda naga dama, jin ya kashe wayan yasa ta fara tunanin maita fada mishi haka, daura hannu tayi akai tana kuka tare da fadin Allah yasa ba fushi yayi da ita ba, daukan wayan ta tayi ta kirashi amma saiya saka mata busy alaman ya kashe wayan, daka karshe ma data kara kira sai taji switch off, kuka ta saki mai karfi mum dake kwance kusa da ita tana bacci ta farka tare da tanbayan lfya jawaheer? Tace mum wlh ina son m samir ban son in rasa shi, mum ta janyota jikinta tana fadin kiyi hakuri jawaheer idan Allah yasa shi zaki aura dole ya zama mijinki ance matar mutum kabarinshi, tace hakane mum, in ban sami m samir ba zan iya shiga cikin wani hal...... Toshe mata baki mum tayi tana ta rarrashinta, dakyar tayi shuru amma maganan bacci kam babu shi, dan ya gudu yanda taga dare haka taga safiya, tunda tayi sallah asuba, ta nufi dakin adda, adda tace jawaheer lafiya naga kaman idanki a kumbure? Kuka ta fara tare daba adda labarin abunda ya faru, adda tace ai gaskiya kika fada mishi baki Karya ba, aishi ba saurayinki bane, dan haka dole ji tsaya da wasu, jawaheer tace haba adda nifa shi nake so, adda tayi tsaki tare da fadin ai sai kiyi ta son nashi, kina son mutum yana miki wulakanci dan yaga ya hadu, shima yanda ya hadu haka kema kika hadu, babu namijin da zai ganki yaji bai sha'awar ya mallakeki, dan haka wlh kima cireshi a ranki tun kafin ya sa miki ciwon zuciya, gwara ki nemi mai sonki kibar wanda baya sonki, jawaheer cikin kuka tace adda bana son wannan magan ganun naki basu da dadin ji wlh, adda dariya tayi tare da fadin kaji ja'ira gaskiyan ne baki so? Tace adda taya zan cirshi a raina bayan kin san ba abu bane mai yihuwa? Adda tace ina zaune zanji kince kin cireshi a ranki amma fah kar kice na miki baki, kallon adda tayi sororo tace kaman ya adda? Adda tace nan gaba zaki gani badai namiji bane shi, jawaheer tashi tayi ta fita alaman taji haushin maganan adda, dariya adda tayi tace kai Allah ya yaye miki yarinya sai kace a kanfa aka fara soyayya ita ko zuciya ma taki yi, shiba sonta yake ba amma ta like mai, dakinsu jawaheer ta shiga taga mum na hada kaya mum tace yauwa jirgin 8 za mubi kizo ki shirya, jiki a sanyaye tace toh fita tayi ta nufi toilet tayi wanka da ruwan sanyi dan garin ana dan zafi, fitowa tayi ta fara shiri cikin wata doguwar riga na less yayi mata mugun kyau, duk da batai makeup ba, ta daura dankwali irin ture kaga tsiya ta yafa wani karamin gyale, sannan ta fita falo, inda adda tasa musu abinci kunu da alale da farfesun kayan ciki, zama sukai suna ci amma ita kam jawaheer tunani take saida mun ta lura da ita tace jawaheer tayi firgit mum ta girgiza kai tare da fadin kici abinci mana, bata ce komai ba ta fara ci, bata wani ci da yawa ba ta ajiye, adda tace zo muje ki rakani can gidan, tashi tayi suka fita ita kuma mum ta fara shiri itama, bayan sun fita tafiya sukai mai dan nisa jawaheer tace kai adda na gaji, adda tace muje mun kusa, kan wani dutse suka je suka zauna, jawaheer tace ina gidan? Adda tace jawaheer babu inda zamu nace muzo nan ne saboda mu sami daman magana ni dake, inaso kiji kuma ki duba ki gani, jawaheer idan kika duba rayuwa yanzu ya canza a baya kinyi kuskure kin nuna ma samir kina sonshi yaki yarda ya soki kaman yanda kike sonshi, idan kika duba zaki gane tun daka sanda kika furta kina sonshi zaiga bazaki iya rayuwa ba tare dashi ba, sannan namiji yace yana sonki yata kaya balle kece kika furta mishi kalman so, aikin bani, wlh indai kika bi yanda na fada miki zai fito yace miki yana sonki, jawaheer tace me kenan? Tace matso kiji, magana ta mata a kunne, jawaheer tace amma kina ganin hakan zaiyi? Adda tace insha Allah ki gwada, tashi mu koma ma dan nasan yanzu ke ake jira, kallon agogon hannunta tayi taga 8:30 tace adda lokaci ya wuce gashi wayana yana gida, adda tace kai muyi sauri toh, suna karasawa kofar gidan taga motocin m samir a kofar gidan, gabanta taji ya fadi ance jirgin 8 za subi gashi yanzu 9 ya kusa, tana shiga ta ganshi a tsakar gidan yana kaiwa da komowa,waigowa yayi ya ganta a tsaye wani irin kallo ya mata tare da fadin daka ina kike?? Tace mun fita ne da adda, yace karfe nawa yanzu?? Tace 8:49 yace what time zamu tafi? Tace 8 yace gud tawo muje fita sukayi suka hadu da adda, ya kira security dinshi ya mishi magana yace ya fadama adda, yace adda yace in fada miki mum ta wuce saboda jawaheer ta bata lokaci suma yanzu zasu tafi a mota, nan adda taita musu addu'an sauka lfya, jawaheer tace bari in dauko kayana, riqota yayi tare da turata mota suka tafi, tace mishi kayana fah? Yace keep quite karki dameni plz, shuru tayi tana kallon sa, lokaci daya tasa kuka waigowa yayi yana kallonta, yace driver ya faka, bayan driver ya tsaya yace mishi ya dan fita, driver na fita ya janyota jikinshi tare da rungumeta ido ya lumshe yace miye haka jawaheer? Tace haka aboki ya kamata yama kawarshi mai yasa kake fushi dani? Sakinta yayi da sauri kana kallonshi zaka gane ranshi a bace yake, nanata sunan yayi aboki wato yanzu bata sona, aboki ta daukeni...........
Dago dakai tayi ta kalleshi sannan tace plz ka daina fushi dani, dan murmushi yayi tare da fadin komai ya wuce rungumeshi tayi tare da shafa mishi gashin kanshi, dariya yayi yace karki bata min gashin kai, tace sai in gyara maka, kiran driver yayi yaja suka wuce, tafiya suke kowa da abunda yake tunani, ita ta gefenta tana tunanin yaushe zai sota, yaushe zai fahinci irin son da take mishi, shiko ta gefenshi yana tunanin tunda sun bar yola babu ita babu ganin dr dama shine damuwanshi ya rasa mai yasa ya tsani dr din, dan waigowa yayi ya kalleta bacci yaga tanayi dan jiya batai bacci ba tunani ya hanata, ido ya kura mata yanda take bacci hankali kwance, yana cikin kallonta yaji ta fado jikinshi, murmushi yayi tare da kara gyarata ya mikar mata da kafa tare dasa kanta akan kafanshi, tafiya suke mota nata sharara gudu, bai taba long journey ba a mota sai yau, dan haka shima ya gaji sosai, amma yana jin dadin tafiyan, bude ido tayi taga anata gudu, tashi tayi daka jikinshi da sauri tana murmurza ido, murmushi ya sakar mata, tace har yanzu bamu kai ba? Kai ya daga mata alaman eh, tace kai wlh na gaji gaskiya da nisa, murmushi yayi tare da fadin matso nan, matsawa tayi kusa dashi yasa hannunshi akan kafadanta yace kefa kinyi bacci bai kamata kiga nisan wajan ba, tace ni nasha ina tashi zan ganni a gida, dariya yayi yace oh i see sai yasa kikai bacci, kai ta girgiza alaman a'a, yace toh miye? Tace jiya banyi bacci ba sai yasa nayi yanzu, kallonta yayi yace maiya hanaki bacci?tace babu komai kawai dai bana jine, shuru yayi tare da aiya nawa cikin ransa kodai tana tunanin wannan dr din ne? Tsaki yayi mara sauti amma duk da haka taji, dago kai tayi da sauri ta kalleshi ganin ya tamke fuska yasa tasa hannunta tana shafa mishi fuskan tare da fadin miye kuma? Hannunta ya cire daka fuskan nashi tare da fadin babu komai, bata kara cewa komai ba har suka zo wani kauye da ake ta siyar da abubuwa, tace driver dan faka, driver tsayawa yayi a gefen titi, kallonta yayi yace mai za kiyi tace yunwa nake ji abu zan siya, yace nop ki bashi ya amso miki, tace ai ban san mai zan siya ba saina fita na gani, kallon wajan ya farayi yana dubawa, tsaki yayi tare da cema driver yaja motar su wuce, driver ya tada motar suka tafi, tace ya zamu tafi ban siya komai ba, yace saboda abun wajan bai min ba, tace nifa yunwa nake ji, yace sorry in naga wajan da yayi min sai a tsaya kici, kai ta daga alaman toh, tafiya suke tayi babu wanda ya kara magana, har suka shiga cikin wani gari yace driver ya tsaya, bashi kudi yayi yace ya siyo mata kaza da drinks, amsa yayi ya fita jim kadan sai gashi ya kawo kaji har guda biyar, da drinks da yawa, amsa tayi ta fara budewa kudi ya kara ma driver yace kuma kuje kuci abinci tare da sauran security din, yace ok, bude kazan tayi tace kai yayi yawa, fara ci tayi tare da miqa mai kai ya girgiza tare da fadin nop bana ci, bata fuska tayi tace in baka ciba nima zan daina ci, kafada ya daga alaman bai dameni ba, ganin haka yasa ta ajiye naman wai tayi fushi, murmushi yayi tare da daukan naman yasa mata a baki ta kawar dakai yace plz kici ban san taurin kai, daukan naman tayi shima takai mai wajan baki ya kawar dakai ta kara matsawa kusa dashi zata bashi ya janyota jikinshi wanda yasa bakinta ya mannu a nashi, dukansu tsayawa sukai cak, sunyi wajan minti daya kafin ya danja baya, da sauri itama ta matsa tare dajin wani iri, shuru dukansu sukayi na wani lokaci sannan taji muryanshi yana fadin muci, bata musa ba suka fara ci, har driver ya dawo suka tafi baka jin karan komai sai wakan nicki minaj, sai wajan karfe hudu suka karaso garin abuja, tana ganin sun shigo taji wani irin dadi, gida suka nufa da sauri ta fita suka ci karo da khalil wani irin runguma sukai ma juna na murnan ganin juna, khalil yace sis sake ni mana inje inga samir, tace babu ruwana dakai dariya yayi yace sorry sis ai nafi jin dadin ganinki akanshi, dariya tayi tace mai wayau, sakinshi tayi ya nufi m samir dake tsaye yana kallonsu yana dariya hugging dinshi yayi tare da fadin bros u r wlcm, m samir yace thanks, ya umar ne ya fito shima cikin murna yayi hugging m samir sannan suka shiga ciki, jawaheer dakinta ta nufa tana shiga tayi toilet dan tayi wanka, bayan tayi wanka ta fito tasa wani wando 3quater da wata top mai bala'in kyau ta fito falo ta gansu su duka suna ta fira hawaye ne ya zubo mata tunawa da tayi bata hada komai dasu ba, wani irin zafi takeji daka zuciyarta, juyawa tayi zata koma daki dad ya kirata tsayawa tayi cak dan haka ya tashi ya nufi inda take, ya janyota jikinshi tare da fadin ina zaki, tace zani daki ne dad, yace no muje, kaita yayi har wajansu ta zauna kowa idanshi na kanta, tausayinta suke ji sosai, ga hawayen da take son boyewa ya kara zubowa, khalil yace sis miye haka? Bata bashi amsa ba sai kuka data saki tare da fadin mum plz muga kwalin da aka baku ni, kowa ya tausaya mata da turanci take magana kowa dake falon yaji mugun tausayinta, mum cikin sanyin jiki ta tashi ta nufi dakinta sai gata da kwali, miqa ma jawaheer tayi ta riqe kwalin tana kuka, budewa tayi taga international passport, dauka tayi taga wasu abubuwa akai budewa tayi tana kuka wani dan karamin passport ne ya fito, da sauri ta dauka tana kallon hotan fuskan matan sak mata da sauri ta nuna ma mum tana fadin mum kalla ki gani da sauri mum ta amsa tace wlh itace ta bamu ke jawaheer itace kuma duk yanda akayi mahaifiyarki ce dan ga kaman ku nan, ci gaba tayi da duba kayan ta dauko wasu riga da wando masu kyan gaske tana kallo, mum tace wannan sune kayan data bamu ke sune lokacin a jikin ki, rungume kayan tayi tana kuka mai ban tausayi m samir dake zaune yana kallonta cike da tausayi ya tashi ya nufeta tare da goge mata hawayen yace jawaheer kiyi hakuri ki daina wannan kukan nayi miki alkawarin haduwa da mum dinki bada dadewa ba wannan nauyin yana kaina, kuka ta kuma saki tare dayin hugging dinshi duk wanda ke falon saida tausayin jawaheer ya tsargo mai cikin zuciya, musamman khalil da sukafi sabawa dashi lokacin da yaji ba kanwar shi bace yayi takaici sosai dan yana son jawaheer, m samir amsan kwalin yayi tare da fadin mum a nan zan zauna ina daki na? Mum ta kalli jawaheer tace jawaheer kaishi dakin kusa dana khalil, mum tayi hakan ne dan jawaheer ta daina kukan, tashi tayi ta fara tafiya yana biye da ita a baya, bayan sunje kofar dakin taja jiki ta tsaya tare da nuna mai kofar da hannu alaman ga dakin nan, murmushi yayi tare da fadin tare zamu shiga, batai magana ba ta bude kofar ta shiga shima ya shigo, dakin akwai komai a ciki ga kamshi dake tashi daka ganin mum dazu tasa akasa komai dan tasan da babu komai a dakin, kallonta yayi yace wow dakin yayi kyau bari inyi wanka ki zauna ki jirani, kai ta daga mai alaman toh, yana shiga ta fita waje dakinta ta nufa ta kwanta tana kuka mai cin rai, yanzu basu mum bane suka haifeta ji take abun ya dawo mata sabo, musamman da taga bros umar khalil ga mum ga dad ga samir, amma ita bata hada komai dasu ba, mai yasa haka ya faru da ita mai yasa mum dinta ta bada ita, lallai tana bukatar jin amsa ada bata da burib haduwa da mum dinta amma a yanzu tana so, tashi tayi da sauri ta dauko wasu takardu tasa a jaka tare da daukan key din mota, har zata fita ta tsaya ta koma ta nufi wardrobe dinta ta dauko wata doguwar rigan atamfa tasa tare da yafa gyale akanta karami fita tayi ta nufi dakin m samir tare da fatan Allah yasa bai fito daka wanka ba, shiga tayi tako ci sa'a bai fito ba wajan kwalin ta nufa ta bude tare da kwashe kayan dake ciki tana kokarin fita taji ya kira sunanta da jawaheer tsayawa tayi cak, ba tare data waigo ba, ganin bata waigo ba yasa ya fara matsowa kusa da ita ji tayi ya riqota ta baya tare da juyo da ita, kallonta ya tsaya yi sannan yace wannan kayan fah? Mai zaki dasu? Kallonta ya kumayi daka sama har qasa sannn yace ina kuma kikë shrin zuwa? Wani irin hawaye ne ya gangaro mata sannan tace zan tafi zan tafi gaba daya zanje neman mahaifiyata lokacin da nake yola banji ina son ganinta ba, amma dawowa na nan gidan yau yasa naji ina son haduwa da ita, yau nasan miye iyaye bazan iya zama a nan ba dole in tafi in nemot..... Janyota yayi jikinshi tare da toshe mata baki yace ya isa haka jawaheer ya isa haka, karki kara tunanin barin nan gidan, kina tunanin kinyi adalci kenan yasu mum za suji in suka ga bakya nan?? Kinyi tunanin haka? Tace karka dakatar dani ka barni dan Allah yace jawaheer mai kike tunani kin san halin da kowa zai shiga kuwa? Nima kaina kin taba tunanin wani hali zan shiga idan aka nemeki aka rasa? Da sauri ta dago dakai suka hada ido lokaci daya kuma ta fashe da kuka tare da fadin koda na tafi kuna raina har abad......... Shhhhhhhhh ya dakatar da ita tare da fadin okey na fahimta amma kafin ki tafi inaso ki fadamin wani irin so kike min dahar kike tunanin barina gaba daya saboda wani dalili?? Zaki iya nesa da abunda kike so ba tare da kin sameshi ba?? Kasa magana tayi sai kuka da take tayi, shima shurun yayi tare dayin hugging dinta sosai yana mai jin kukan nata har cikin ranshi, ido ya lumshe ya rasa mai yasa yake jin abubuwa da dama akan jawaheer wanda baya ji akan ko wata mace, ko sonia da sukai zama tare na lokaci mai tsawo baya jinta kaman yanda yake jin jawaheer a halin yanzu sakinta yayi tare da janyota suka zauna akan gadon dakin yace jawaheer kiyi shuru kibar wannan kukan, nayi miki alkawarin neman miki mum dinki jibi zan koma spain muna da wasa bazan dawo kasar nan ba har sai na nemo miki mum dinki, inaso kimin alkawari ba zaki kara tunanin barin gidan nan ba, kai ta daga cikin kuka alaman eh, tare da rungumeshi tana fadin nagode sosai Allah ya baka abunda kake so, a hankali yace ke nake so jawaheer..........
Da sauri ta dago kai ta kalle shi, murmushi yayi tare da fadin yes jawaheer u r my sister bani da wata yar uwa mace sai ke, so kinga dole in soki, ajiye ajiyan zuciya tayi tare da lumshe ido dan ba haja tai zatan jiba, tashi tayi tare da fadin saida safe, shima tashin yayi yace sis bacci yanzu miye time? Tace na gaji ne sosai, yace ok good night, fita tayi ya bita da ido harta rufe mai kofar sannan ya lumshe ido tare da buga hannunshi akan dayan hannun yace damn, shima kwanciyan yayi tare da tunanin jawaheer din tare da alkawarin neman mata mum dinta a duk inda take a fadin kasar nan.

Koda ta shiga daki kuka ta fashe dashi tare da fadin lallai na yarda m samir bazai taba sona ba, Allah ka jarabceni da son wanda baya sona amma ina roqanka kasa in cinye wannan jarabawan, shuru tayi tare da fadin lallai wannan shine maganin matsalata, wannan ne karo na farko data taba tunanin tayi aure ko zata cire m samir a ranta, lallai shine mafita amma komai zanyi sai naga mum dina zanyi aure inyi nesa dashi gaba daya da wannan tunanin bacci yayi gaba da ita.
Washe gari m samir tun karfe 7 ya fita shida khalil da security dinshi, direct wajan hukumar shiga da fice suka nufa, inda suka basu international passport din mum din jawaheer, tare da kudi masu yawa akan su nemo bayanai akanta, ce musu sukayi su dawo nan da sati daya, hakan akayi suka tafi bayan yawan mutanen da suke ta cincirindon son daukan hoto da samir dakyar dai suka shiga mota suka bar wajan akan nanda sati daya zasu dawo ko kuma su zasu nemeshi sun daiyi exchanging number, yawo suka dinga yi ranan.

Jawaheer kam tunda ta tashi tayi wanka, tasa wata atamfa mai ruwan ja da ash yayi kyau atamfar anyi dinkin riga da skirt saiya fito mata da surarta das a jikin kayan tayi bala'in kyau duk da ba makeup a fuskanta, wani karamin gyale ta yafa ta fito ta sami mum ita daya a falo, tace ina kwana mum? Amsawa mum tayi cikin sakin fuska tare da tambayanta ya gajiyan hanya, tace alhmdlh mum hanya babu dadi, mum tace ina zaki naga kaman fita za kiyi, tace eh mum yau zan shiga skul mun koma tun last week, mum tace kai jawaheer kina wasa da karatu tun last week kuka koma shine kikai shuru baki fara zuwa ba, yanzu kin san lecture nawa kikai missing? Tace mum karki damu attendance ne matsalan kuma nasa ana daukan min, mum tace toh shikenan dan Allah ki daina wasa kije kici wani abu kafin ki tafi, tace mum zanci a skul, babu yanda mum batayi ba amma taki ci tace bata jin yunwa, fita tayi ta wuce daya daka cikin motar gidan ta shiga mai kiran prado, ita da kanta take tukin har cikin makarantar,faka motarta tayi sannan ta nufi department dinsu, tun daka nesa ta hango yan class din nasu daka gani akwai lecturer a ciki domin duk sun bada hankalinsu wajan kallon waje daya, tana isa kam taga lecturer ne a ciki, dan haka ta shiga cikin sanyin jiki, kallonta lecturer din yayi kaman zaiyi mata magana sai kuma ya fasa, ji yayi tace mishi morning amsawa yayi sannan ta nemi waje ta zauna, kowa yayi mamakin dabai koreta ba dan yau kwananshi uku da fara basu darasi sannan duk wanda yazo idan ya shiga baya bari ya zauna, bayan jawaheer ta zauna ya kuma kallonta tare da sakin murmushin dashi kanshi bai san yayi ba, ganin itama ta mayar mai da martani yasa ya gane abun da yayi, da yake ya iya duniyanci saiya basar yaci gaba da lecture har lokacinsa yayi, sannan ya kalli jawaheer yace daka yau karki kara shigo min class indai na rigaki shigowa, kai ta daga alaman naji, sannan ya fita, tsaki tayi tare da dauko wayanta tana dan dannawa, kiran dr ne ya shigo kaman ba zata dauka ba, komai ta tuna kuma ta dauka tare da fadin hello, ajiyan zuciya ya sauke tare da fadin jawaheer wai nayi laifi ne aka daina daukan waya ta? Uhm kawai tace yaci gaba da fadin jawaheer naje adda tace min wai kin koma jiya, shine ko sallama babu, tace kayi hakuri tafiyan ne yazo a bazata, yace bakomai da fatan anga sako na, dan shuru tayi kafin tace uhm, murmushi yayi sannan yace ina fatan za'a bani dama? Tace Allah ya taimaka ya shige mana gaba, wani irin dadi yaji tare da fadin kenan an bani dama, kai yau ina farin ciki Allah ya dai daita mu, bata ce komai ba sai murmushi da tayi, wani lecturer ne ya shigo tace ina zuwa zamu fara lecture yace ok tare da kashe wayan, sai lecture ake musu amma ita sam bata san mai ake fada ba, domin tayi nisa cikin duniyar tunani ba komai take tunani ba sai na amince ma dr akan yaci gaba da nemanta har Allah yasa su fahimci juna tayi hakan ne da zuciya daya domin tana da burin ta sami miji tayi aure dan ta cire m samir a ranta duk da tun jiya take ta kokarin tusa ma kanta kin shi amma hakan ya faskara, lallai koda banga mum dina ba indai muka fahimci juna dole inyi aure in huta, ji tayi ana mata magana, wata yarinya ce kana ganinta kasan suma suna da arziki, jawaheer firgit tayi taga lecturer din ya fita tace kai ashe har an gama, yarinyar tayi murmushi tare da fadin sunana zarah, yau na fara zuwa lecture saboda nayi ciwo sai nayi differing da yanzu ina 3lv amma yanzu ina 2lv, jawaheer tace Allah sarki Allah ya baki lfya, murmushi zarah tayi tare da fadin baki fadamin sunanki ba, tace jawaheer murmushi zarah tayi tace suna mai dadi zarah ta amshi no din jawaheer tare da fadin in akwai lecture zata dinga fada mata, sannan tace duk abunda jawaheer bata gane ba ita zata dinga nuna mata, nan jawaheer tayi godiya tare da fadin an gama lecture din yanzu? Zarah tace a'a akwai wanda zai zo karfe hudu, jawaheer tace kai bari inje inci wani abu yunwa nake ji, zarah tace muje tare toh, fita sukayi tare suka je wani restaurant a cikin skul din, fried rice jawaheer tace a bata, ita kam zarah snacks ta amsa da drinks suna ci suna fira har suka gama, fita sukayi suka zauna wajan wata bishiya ko wacce na danna wayarta, wayan jawaheer aka fisge daka hannunta da sauri ta dago taga ko waye khalil ta gani dariya tayi tare da fadin bros mai kazo yi? Yace zo muje ki gani, zarah ta dago kai tare da kallon khalil gaidashi tayi jawaheer tace bros dina ne, tace ashe yayanmu ne, dariya yayi sannan yace ma jawaheer ga mota can kije ana jiranki ni bari in zauna a nan muyi fira da zarah, dariya tayi sannan ta nufi motar dan a zaton ta dad ne, tana budewa taga m samir zama tayi a cikin motar tare da rufewa shine a mazaunin driver daka gani shine ya tuka motar, kallonta yayi tare da fadin baki so gani na ba koh? Tace a'a , yace mai yasa kika daure fuska? Tace babu komai, murmushi yayi tare da fadin jawaheer yau baki damu da inda na shiga ba, baki kira niba, tace bani da abunda zance maka ne, yace ok toh bari in tafi, bata bude kofar ba sannan bata motsa ba, ya kuma cewa zan tafi, kallonshi tayi da idonta daya rine kadan kawai take jira tayi kuka, janyota yayi jikinsa yace karki sake kice zaki fito da wannan hawayen, jawaheer na rasa mai yasa ko kadan bana son ganinki cikin damuwa, bana son inyi nesa dake na saba dake cikin lokaci kadan, gobe zan tafi inaso plz koda na tafi kici gaba da riqemin kanki karki bama kowa daman shiga rayuwanki, dagowa tayi ta kalleshi dan bata gane mai yake nufi ba, murmushi yayi tare da fadin nan gaba kadan zaki fahimta abunda nake nufi, but yanzu ina son ki riqemin kanki ban son ko wani namiji ya shigo cikin rayuwanki, naso mu tafi tare sai naga koda munje banda tym nd ban son in barki cikin kadaici, shuru tayi tana tunani toh mai yake nufi kar inbar wani ya shiga rayuwa na? So yake in zauna banyi aure ba..... Katseta yayi da fadin zanyi missing dinki sosai, murmushi tayi tare da fadin nima haka, yace taya zan gane? Murmushi tayi tare da fadin komai kaji na fada a kanka dagaske nake kuma hakan nake ji, a musulunce mace zata iya fadama namiji tana son shi, amma a al'adance abun kunya ne, samir a kasar ku na fada maka ina sonka, amma ka nunamin inyi hakuri naji kuma nayi duk da ban cire raiba, amma a yanz..... Shuru tayi yace yanzu me?? Na hakura dakai ina son nima in sami mai sona inyi aure bada dadewa ba, kallonta yayi yana dan nazari kafin yace zaki iya auran namijin da baya sonki? Tace zan iya indai ni ina sonshi, murmushi yayi tare da fadin mai kike tunanin zai faru bayan auren? Tace zaman hakuri, yace har zuwa wani lokaci zaki ta zaman hakuri dashi, tace bazan iya sani ba, amma idan hakan ya faru zuciyata zata yanke a lokacin, yace ok naji zaki iya aurena bayan kin san bana sonki? Wani irin hawaye ga zubo mata, tace zan iya burina a kullum in kasance dakai a koda yaushe, yace jawaheer shikenan nayi miki alkawarin zan aureki amma inaso ki sani ban taba kallonki a matsayin budurwa taba, sai yar uwata, inaso kiyi tunani akai indai kin amince nanda wata biyu za muyi aure in kuma baki aminceba shikenan kiyi tunani akai, shuru tayi na wani lokaci sannan tace bana tunani akan sonka a kullum tunani na shine in sameka a matsayin miji dan haka na amince, yace ok zan fadama dad yau sai a fara komai duk abunda kike bukata sai ki fadamin, amma ina so ki sani indai kika shigo babu saki kar nan gaba kice baki son zaman, murmushi tayi tare da fadin bana tunanin baki na zai iya fadin haka,yace good zamu koma gida anjima sai mu karasa magana dama ke nazo in gani, tace ok sannan ta fara kokarin bude kofar amma yaki buduwa, kallonshi tayi alaman ya bude mata, yace haka zaki faramin babu wani abu sai kawai ki fita, rufe ido tayi tana dariya sannan ta matsa kusa dashi ta mishi peck a goshi, dariya yayi sannan ya bude mata motar ta fita, da ido ya bita har ta karasa wajan su khalil da suke ta fira shida zarah, tace toh saika tashi ku tafi dariya yayi tare da cema zarah sai munyi waya, tace ok, sannan ya tafi, jawaheer kallon zarah tayi tace badai har an kulla luv ba? Zarah tace haba luv a minti nawa, dariya suka sa dai2 lokacin wannan lecturer din yazo yace ma jawaheer tazo yana son ganinta, bayan ta matsa kusa dashi yace ga no dinshi yana son ta kirashi, bata yayi tasa sannan ta koma wajan zarah tana fada mata abunda yace mata, zarah tace haba nayi mamakin dabai koreki ba, ashe ya kamo fish, dariya sukayi har 4 yayi suka shiga lecture basu fitoba sai 6 gida ta nufa direct a gajiye ta shiga gida babu kowa a falo dan haka tayi dakinta, tana shiga toilet ta nufa tayi wanka wardrobe dinta a kusa da toilet dinta yake kaya tasa sannan ta fito tana fitowa taga mutum a dakin yana kalle kalle, kallonta yayi rai a bace sannan yace jawaheer jiba dakin ki duka pics dina ne harta carpet dinki, indai kina sona mai yasa kike kula wasu mazan?? Ido ta dan zaro alaman wana kula..... Tace ni yaushe kum...... Ya isa ban son jinki dazu waye naga yana baki number kina sawa?? Shuru tayi kaman ba zatayi magana ba, can tace lecturer dinmu ne fah, yace lecturer number din mai yake baki?? Tace yace in kirashi ne zai mun magana, ido ya lumshe ji yake kanshi na mishi wani irin tafarfasa lokaci daya idanshi ya kade yace mai zaki mishi idan kin kira shi? Tace nima ban sani ba, kallonta yayi kaman zaiyi magana sai kuma ya fasa ya fita fuuuuuuuu, dakinshi ya nufa zama yayi akan gadon dakin shidai yasan bawai son jawaheer yake ba, kawai yana tausaya mata sai yasa yake son ya aureta sannan baya son tana nesa dashi, to mai yasa nake kishi idan wani yana mata magana?? Wata zuciyar tace saboda kana sonta da sauri yace nop, kawai dai dan zan aureta ne dole kuma inyi kishi a kanta,karan wayanshi ne yasa ya dauka yaga dad din su khalil ne dauka yayi dad din yace mishi samir gani na dawo ina falo, yace ok dad ga ninan, tashi yayi ya fita ya nufi falon, samun dad yayi da mum akan dinning dad yace samir ya gida gobe ne tafiyan koh? Yace eh dad, dad yace masha Allah, Allah ya taimaka, yace ameen, yace dad dama inaso inyi maka magana nida jawaheer mun fahimci juna, kuma...... Dan shuru yayi dad yace inaji, yace muna son muyi aure in kun amince, dad cikin murmushi yace alhmdlh alhmdlh abu yayi kyau, mum tace toh yanzu ya za'ayi, amma inaga da an jira an duba iyayenta koh? Dad yace a'a in ba'a gansu ba fah, haka zatai ta zama? Kinga dole kuwa tayi aure, mum tace hakane, m samir yace dad plz ban son bikin ya wuce wata daya, mum harara ta sakar mai tare da fadin toh mara kunya, kai ya sosa tare da tashi yabar wajan suka bishi da dariya, dakinshi ya koma ya kwanta haka kawai yake jinshi cikin farin ciki da annashuwa, haka har bacci ya daukeshi,.

Washe gari jawaheer nada lecture karfe 8, dan haka da wuri ta shirya duk da ranta a jagule yake, dan tasan m samir yana fushi da ita, gashi yau zai tafi, ji tayi ba zata iya tafiya ba har sai ta ganshi, dakinshi ta nufa taga baya nan, fita tayi ta nufi falo taga mum na gyara kayan abinci akan dinning, tace morning mum, mum tace har kin fito? Tace eh mum gashi har na kusa makara, na tafi sai na dawo, mum tace ok samir yace in fada miki ya tafi, sannan ga sako ya bayar a baki, dam taji kirjinta ya buga wato tafiya yayi shine bai mata sallama ba......

Post a Comment for "JAWAHEER CHAPTER 5"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...