Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

JAWAHEER CHAPTER 4

JAWAHEER CHAPTER 4

- - Post a Comment
JAWAHEER

CHAPTER 4Sai wajan karfe biyu jirginsu ya sauka a airport dake yola, fita sukayi, suka fara tafiya yayin da security dinshi ke zagaye dashi, nan mutane suka ganeshi musamman matasa nan aka fara ihu tare da daukanshi hoto, yana ta daga musu hannu,haka har suka samu suka fita, motoci ne makil a waje sodoji ne da yan sanda suka zo daukansu da motoci na alfarma, tare suka shiga mota daya shida jawaheer, sannan security dinshi suka shiga sauran, hotel aka kaishi kai tsaye dan sun so su fara kaishi government house yace a'a su kaishi inda zai sauka yana son hutu, hotel din gaba daya aka mishi booking babu kowa a ciki sai su kadai an zagaye hotel din da jami'an tsaro, domin kuwa kasar spain ta bada ajiyan m samir ga gwamnatin nigeria, shugaban kasa da kansa yasa governor din yola yayi mishi komai da komai, jawaheer kam abun mamaki yake ta bata koda yake ba abun mamaki bane dan he is a biggest celebrity in d world wannan ba komai bane, sai da yakai jawaheer har dakin da zata sauka sannan shima ya shiga nashi mai kallon nata dakin, yana shiga ya fada toilet dan yin wanka, koda ya fito daka wanka, yasa boxer tare da daura jallabiya yayi sallah, koda ya idar cire jallabiyan yayi, kwantawa yayi dan ya huta, bai dade ba bacci ya daukeshi.Ita ko jawaheer tunda ta shiga dakin take jinta wani iri na farko dai ba yunwa takeji ba dan taci abinci a jirgi, sannan ita ba rashin lafiya ba, gadai ta nan ne dai, wannan ne zuwanta yola na farko duk da ya kasance garin iyayenta ne shi, amma bata taba zuwa ba, sau da yawa takan rasa mai yasa iyayenta basa son koda firan garin yola ayi musu, musamman ma mum tafi tsanan mahaifar tata, lallai akwai wani abu amma kodai miye kiyayyar tayi yawa haka, dan murmushi tayi tare da fadin may be ma ba wani babban abu ya faru ba suka dauki karan tsana suka sama garin tare da watsar da danginsu gaba daya dama ance fulani nada riko, tashi tayi itama tayi toilet tayi wanka, sannan ta fito tasa kananan kaya riga da wando, tare dasa hijab dinta dan yin sallah azahar, bayan ta idar ta dauko wayanta tasa sim dinta na nigeria, kaman jira ake kiran mum dinta ya shigo wayan kin dauka tayi dan tasan indai ta dauka tasan tana yola sunanta sorry, amma da tayi tunanin rashin fadama mum din nata zai iya daga musu hankali suyi ta tunanin tana ina, dan haka kiran na tsinkewa ta tura ma mum message kamar haka..... *mum na dawo nigeria amma kiyi hakuri ina garin yola nida m samir muka zo, mum ki tayani da addu'a burina ya cika a kanshi duk da nasan kina min, tana gama rubutawa ta tura mata* koda saqon ya shiga wayan mum ihu ta saki tare da tafa hannu tana fadin lallai jawaheer yau ta wuce gonarta ta nunamin ban isa da ita ba, dad dake zaune kusa da ita yace haba bilkisu miye haka mai kuma ya faru? Kasa magana tayi sai miqa mai wayanta tayi amsa yayi shima ya karanta, salati yayi tayi tare da fadin mai yasa jawaheer zatai haka? Mum tace dole in tafi yola ina tsoran kar tarihi ya mai maita kansa, dad kallonta ya tsayayi tare da fadin koma dai miye kiyi mata addu'a sannan maganan zuwanki yola bai taso ba zanje da kaina in dauko ta, mum tace a'a tare zamu tafi, ganin yanda ta dage yasa dad fadin zasu tafi taren amma gobe da safe, mum badan taso ba dan taso su tafi yau din nan kar abunda take boyewa ya fito fili.
Washe gari tun karfe biyar su mum suka nufi airport dan mum ta matsa sosai,koda suka je airport din saida suka jira dan jirgin karfe 7 zai tashi, kallo daya zaka ma mum kasan tana cikin tashin hankali yau itace zata yola wanda a kalla shekara ishirin da wani abu da suka wuce rabonta da mahaifarta Wani irin hawaye mai zafi ne ya zubo mata a ido, shiga jirgi aka farayi suma suka tashi suka shiga, nan aka rufe jirgi ya daga zuwa garin yola.Jawaheer tunda tayi sallah asuba, tayi wanka tasa wata doguwar riga gaba daya tun jiya bata cikin yanayi mai dadi, ta rasa dalili ga gabanta dake ta faman fadi, jin nocking tayi dan haka ta tashi jiki a sanyaye ta bude kofar murmushi ya sakar mata yayin data lumshe ido dan kamshin turarenshi ya bugan mata hanci wanda yake kara sa taji ya narkar mata da zuciya, wani irin kyau taga ya karayi yi mata sosai, duk da bawai wani canji yayi ba hasali ma riga da wando ne jikinsa kaman kullum kananan kaya, duka babu wanda yayi ma dan uwansa magana sai itace tayi karfin halin fadin morning, bai amsa ba sai hannunta daya kama sukai dakinshi tare, bayan sun shiga ya zaunar da ita, ido ya kura mata tare da fadin jawaheer maike damunki? Daga kai tayi ta kalleshi taga shima din ita yake kallo dan haka tayi saurin yin kasa dakai tare da fadin babu komai kawai.... Sai kuma tayi shuru, jin muryanshi tayi yana fadin kawai me? Tace gabana keta fadi ban taba jin irin yanayin da nakeji yau ba, murmushi yayi tare da fadin ki yawaita fadin innalillahi wa inna'ilaihira jiun, kai ta daga alaman toh sannan ya kalleta tare da fadin zamu anguwan da dad dina ya fadamin tunda bakya jin dadi ki zauna muje mu dawo, kai ta girgiza tare da tashi tace a'a tare zamu duk inda zaka a cikin kasar nan ina tare dakai,murmushi yayi tare da jan hancinta sannan yace kinyi breakfast? Kai ta girgiza alaman a'a wayan dake dakin ya kira ya fadi abunda yake bukata, bai wani dade ba aka kawo abunda yace, tea da chips nd egg aka kawo, tare sukaci sannan suka fita, motocin da aka kawo su jiya nan suka shiga inda jawaheer ta fada musu inda zasu tace guyuk in anje kuma ace gidan liman, kai tsaye driver din suka nufi hanya, hannun jawaheer na rike dana m samir yana kallon garin yanayin garin ya mishi kyau in yaga abu bai gane ba saiya tambayi jawaheer ta fada mishi, da haka har suka iso anguwan, babu laifi anguwan nada kyau, da tambaya har suka isa kofar gidan, koda suka isa jawaheer ce ta fito tace bari ta fara shiga, yace a'a tare zasu, haka suka shiga cikin gidan,babu laifi gidan yana da kyau duk da ba wani girma gareshi ba, sallama jawaheer tayi, wata yar dattijuwa ta amsa tace waye? Ku shigo, bayan sun shiga jawaheer taga tsohuwar fuskanta dauke da glass dam taji gabanta ya buga da karfi domin sak fuskan mum dinta sai dai kuma wannan tsohuwa ce ita ta girmi mum dinta sosai lokaci daya ta shiga rudani.......


Muryan matan ne ya katse jawaheer daka duniyar tunanin data fada, tace sannunku ku karaso mana, wani karamin falo ta kaisu wanda daka gani an ware shine dan ajiye baki, falon sai kamshin turaren wuta yakeyi, jawaheer dai bin matar take tayi da ido, domin abubuwa ne fal a cikin ranta, fita tsohuwar tayi jim kadan sai gata da ruwa ta kawo musu, pure water mai sanyi, sannan ta zauna tare da fadin bismillah, m samir kallon jawaheer yayi wacce idonta nakan wannan tsohuwar,kafin yayi magana yaji matar na fadin sai dai ban shaida ku ba, cikin harshen hausa take magana, m samir bai san mai take fada ba dan haka ya kalli jawaheer tare da fadin tayi mata bayani, jawaheer tace da fatan mun sameki lfya hjy, amsawa tayi da fadin lfya qlau, sannan jawaheer tace dama mun zo neman khausar ne, da sauri matar ta tashi tare da kallon jawaheer lokaci daya kuma ta fashe da kuka tana fadin maiya kawo ku, waya turoku, mai kuka zoyi nan? Mai yasa zaku tunamin da ciwon da yake zuciya ta wanda ya kasa warkewa, kodai ku yan uwan muhd ne wanda ya bata min rayuwan yarinya, baxan taba yafe mai ba shine mutum na farko daya tarwatsa min a halina, ku tashi ku fita, m samir da bai san abunda ke faruwa ba sai kallon jawaheer yake amma yaga kaman matar fada take dan yanda take magana kadai ya isa ya nuna mishi hakan, jawaheer tace kiyi hakuri hjy wlh bada wata manufa muka zo miki ba, hasalima....... Dakata yar nan bana son jin duk wani abu da kuka zo dashi ku tafi kawai ku barni, jawaheer tace dan Allah ki saurare ni wannan da kike gani dan khausar ne kuma jikanki, gaba daya tsayawa tayi tana kallon jawaheer alaman ban san yaudara, kai jawaheer ta daga mata tare da fadin yaron muhd ne wannan a gabanki sai dai baya jin hausa, sai yaren kasar su spanish ko turanci, da sauri ta rungume m samir tana kuka tare da fadin ina kaje wajan shekaru ishirin da suka wuce a ina ka rayu, m samir farin ciki ne fal cikinsa tunda yaga ta rungumeshi alaman sunyi nasara kenan, kuma ya tabbata zaiga mum dinshi yanzu, sakin m samir tayi sannan ta kalli jawaheer tace yar nan fadamin a ina ya taso, nan jawaheer ta fara bata labarin abunda ya faru wanda dad din m samir din ya fada mishi da yanda abubuwa suka faru a baya tare da satoshi da yayi har ya girma a wajanshi, kuka ta kuma saki tare da fadin lallai muhd shine silan tarwatsa min dangina, amma babu komai munyi imani da kaddara wanda a wancan lokacin muka kasa fahimta, shigowan su mum gidan yasa jawaheer da tsohuwar suka fita shima m samir ya rufa musu baya, jawaheer tace mum dad mai kuka zoyi nan? Mum kam kuka takeyi yayin da matar itama take kuka tana fadin bilkisu dama kina raye, gaba daya jawaheer ta shiga rudani sosai dan haka ta matsa wajan dad dinta tana fadin dad maike faruwa ne? Dama sun san juna ne? Dad bai iya magana ba balle ya iya bata amsa, matar ta kamo hannun m samir ta hada dana hjy bilkisu tace ga danki nan bilkisu, jawaheer wani irin duhu ta gani ya rufe mata ido hannu ta daga tana fadin dama yaya nane kai jini nane kai mum dinmu daya ash..... Tif tayi kasa sumamma da sauri sukayi kanta suna fadin jawaheer musamman ma m samir da yafi kowa rudewa lokaci daya domin duk maganan da sukeyi babu abunda ya fahimta dan da hausa sukeyi sai dai ya gane mum itace mum dinshi, ruwa tsohuwar ta dibo ta fara yayyafa ma jawaheer amma ko motsi batayi ba, dan haka hankalinsu ya kuma tashi sosai dad ne yayi karfin halin fadin mu kaita hspt, jin an fadi hspt yasa m samir ya fahimta dan haka ya dauketa cak sukai mota ya shigar da ita yace ma security dinshi suje hspt mafi kusa, tafiya kadan sukayi suka isa wani asibiti inda akai emergency da ita domin ceto rayuwanta, mum babu abunda take sai kuka tare da fadin jawaheer insha Allan babu abunda zai sameki kuka take sosai gaba daya ta kasa zama, shiko m samir gaba daya ya rasa maike mishi dadi, ganin irin kukan da mum take yasa ya nufeta yana bata hakuri lokaci daya ta janyo m samir ta rungumeshi tana kuka mai cin rai, yau ya kamata ace ranan farin ciki ne a rayuwanta amma kash abubuwa sun jagule, ga danta Allah ya hadasu, ga jawaheer a asibiti rai a hannun Allah, sunyi wajan awa daya kafin dr ya fito da sauri m samir ya nufeshi yana tambayan ya jikin nata, yace suje office dinshi, binshi sukayi har office dr din sai kallon m samir yake yana mamaki kaman ya sanshi m samir ne ya katseshi da fadin dr ya jikin nata? Dr yace munyi iya kokarin mu sauran sai a barma Allah, dan harta farka tana fadin ashe yayana ne shikenan burina bazai cika ba, nono daya muka sha...... Tana cikin fadin haka ta kara suma ko numfashi baya fita amma yanzu mun sa mata oxygen numfashin ya fara fita, gaskiya tana cikin mugun damuwa wanda ba'a so mutum yakai irinshi domin sai anyi sa'an gaske mutum yake tashi idan yayi irin wannan abun, dayan biyu ne ko ka tashi da ciwon barin jiki ko kuma zuciyarka ta buga ka mutu, yanzu dai sai mu jira ta farka mu gani, hankalinsu gaba daya ya tashi m samir wani irin son jawaheer yaji yana shiganshi wanda bai taba jin irinshi ba sai a yanzu amma yana ganin hakan a matsayin dan tana kanwarsa ne jininsa wanda saida dr yayi bayani ya fahimta dan da turanci yayi, ashe duk son da take mai ashe yayanta ne shi lallai Allah mai iko ne, mai kuma yanda yaso, mum zuciyarta cike take da damuwa dad ma kam ba'a magana dan yafi kowa shiga cikin damuwa domin yar lelenshi wacce yafi so kaf yaranshi itace yau a kwance a gadon asibiti tana cikin yanayin rayuwa ko mutuwa gashi dr yace babu tabbaci, lokaci daya ya kalli mum yace anya ba zamu fitar da ita waje ba? Idan wani abu ya sami jawaheer bazan iya juran gani ba,mum tace nima haka nake tunani muyi magana da dr din. Koda aka fadama dr shawara ya basu akan suyi hakuri har zuwa gobe su gani sannan koda wajan suka kaita babu abunda zai canza, tare da fadin gwara ma suyi hakuri su barta a nan, dad yace bari dai suga zuwa goben tare da tambayan dr zasu iya ganinta? Yace eh su shiga amma karsu dameta da hayaniya, shiga sukayi dakin gaba dayansu, tana kwance akan gadon dakin ansa mata oxygen baka jin karan komai saina oxygen din da karan ac duk da ac a kunne yake jikinta babu abunda yake sai zufa, lokaci daya fuskanta yayi fayau tayi rama kaman wacce tayi ciwon kwana biyu bakinta yayi fari, mum ta kalli dad cikin kuka tana fadin kalli yanda ta koma yanzu2 anya jawaheer ba mutuwa za tayi ba, na shiga uku ni bilkisu....... Kuka yaci karfinta sosai dad ya jata suka fita m samir shima kukan yake tare da share mata zufan dake goshinta jikinta yayi wani irin dumi gashi kuma kaman babu jini yanda yaji jikin nata yayi wani irin tashin hankali ya kuma shiga tare da fadin wani irin ciwo ne haka lokaci daya?kallan fuskanta yayi yaga tayi haske tayi fayau gabanshi yaji ya fadi tare da fadin no zaki rayuwa my sister kuka ya saki sosai......


Jawaheer kam ko motsi batayi, m samir iya tashin hankali ya shiga gaba daya ya fita cikin hayyacinsa, mum ce ta shigo dakin domin a lokacin anata kiran sallah la'asar, kama hannunshi tayi wanda ya rike na jawaheer dashi, dagowa yayi da sauri wanda yake zargin jawaheer dince amma sai yaga sabanin hakan, mum ce cikin kuka take mai magana cikin harshen turanci tace kaje kayi sallah,baiyi magana ba sai tashi da yayi ya fita dan yin sallah, haka su mum sukai ta zama amma shuru bata farka ba, abun ya damesu sosai gashi har wajan karfe biyar yanzu gaba daya hankalinsu a tashe yake, mahaifiyar mum ce tace nikam bilkisu itama wannan din yarinyar kice? Mum zatai magana taga kaman jawaheer tana motsi da sauri ta nufeta tana kiran sunanta tare da fadin jawaheer ganin idon jawaheer din a bude yasa ta furta alhmdlh da sauri ta fita lokacin su dad na waje da m samir dad na ganinta yace bilkisu lfya kuwa? Tace ta farka zan kira dr ne, dad yace bari in kira shi, m samir da mum suka koma dakin, m samir suna shiga ya nufeta ganinshi yasa ta sakar mishi murmushi amma ta kasa magana, shima ya kasa furta mata komai sai murmushi da yake ta sakar mata shima, dr ne ya shigo dakin wanda yasa m samir niyan barin wajan amma ta rike mai hannun alaman ya tsaya, dr ganin haka yayi murmushi tare da fadin lovers, matsawa dr din yayi ya fara dubata tambayanta ya farayi amma bata bashi amsa da baki sai dai ta daga mishi kai kota girgiza mai kai, hankalinsu ya tashi sosai ganin taki magana dad yace dr mai yasa bata magana? Dr yace nima abunda nake son sani kenan amma karku damu zatayi, dr yace amma alhmdlh jikin da sauki nayi mamaki ta tashi ba tare da wani matsala ba, gskya ku kara godema Allah, dad yace toh dr ni yanzu magana kawai nakeso tayi, dr yace madam kice wani abu plz, ido ta lumshe alaman karma ya dameta, mum ta matso kusa da ita, tana fadin jawaheer plz kiyi magana, bude ido tayi ta kalli mum lokaci daya hawaye ya zubo mata sannan bakinta ya fara rawa tace mum, kowa ya kura mata ido ta kara matse hannun m samir sannan taci gaba da fadin mum m samir danki ne na cikin ki? Mum dan Allah ina son sani ance sunan mum dinshi khausar ba sunanku daya ba mum dan Allah ki fadamin maike faruwa wlh mum ban san mai yasa na tashi ba amma haka Allah ya tsara dan Allah mum ki fadamin miye tsakaninku ko zuciyata zata samu salama daka radadin da takeyi a halin yanzu, mum kuka ta farayi tare da fadin jawaheer zan fada miki komai kaman yanda kike son ji duk da banso fada miki ba, amma inason in kinsan gskya karki juyamin baya karki gujemu duk rintsi duk wuya.......
TUNA BAYA.....

Garin yola garine na fulani mu uku iyayena suka haifa a duniya ni daya ce mace a wajansu, yayyina maza ya abubakar sai ya abdullahi saini bilkisu wacce naci sunan kakata ake cemin khausar, mahaifina mlm kabiru shine limamin anguwanmu mutane suna girmamashi mahaifiyata kuma nafisa, muna kiranta da adda, ita daya ce wajan mahaifinmu duk wani gata da dan gata yake samu suna nuna mana duk da alokacin ba'a karatun boko bawai ba'ayi bane a'a anayi sai dai ba'a bashi muhimmanci, mahaifina koda haiyuwa akayi kasancewan shine liman shine yake radama yaro suna, sannan komai mai gari zaiyi saida saninshi, tunda na taso nake tallan nono domin wannan dabi'an fulani ne musamman wanda suke kauye, akwai dan mai gari wanda yake sona bayaji sosai gashi kashe mutum a wajanshi ba komai bane, sannan iyayena tun ina karama suka bashi ni dan haka irin tasu al'adan yake ana haifanki za'ayi kamunki, a bama wani ke ma'ana anyi miki miji tun kina karama, gashi kuma koda bakwa son juna baku isa ku karya alkawari ba, tunda na taso na tsani auwal, gashi yana bala'in sona, ko yazo wajena bana wani bashi fuska, akwai wani ma'aikata da nake kai nono inda na hadu da muhd mahaifin samir lokaci daya muka saba harya fara koyamin turanci daka baya ya fara sona, ya sami mahaifina akan yana sona, inda ya nuna mishi bazai hada zuri'a da farin fata ba wato bature bai fito ya fada mishi anyi min miji ba, babu yanda baiyi ba amma mahaifina yaki, irin son da muke ma junanmu wata rana naje wajanshi dan saboda shi gaba daya aka hanani tallan nono, na sata jiki naje, inda mukaci kukanmu har yakai daya fara ban hakuri yana sharemin hawaye sanadin da shaidan ya rinjayemu kuka ta saki sosai sannan taci gaba mun aikata sabon Allah, tunda na tafi ban kara fitowa ba har saida aka gano inada ciki hankalin iyayena ya tashi sosai nan sukai ta buguna tare da yayyina inda sukace in ban fadi wanda yamin ba sai sun kasheni, jin naki magana sukace wlh zuwa dare in ban fadaba sai an jefeni gashi kowa a gidan lokacin ya shareni babu maijin tausayi na, haka na sata jiki na samu muhd nake fada mishi abunda ya faru, mai makon inga yayi fada sai daga hannu yayi yana godiya tare da fadin rabo rabo lallai koba ta hanyar aure ba inda rabo sai an samu, kuka na fara mishi akan yabar garin dan wlh zasu iya kasheshi da farko yaki yarda sai dakyar ya amince dan saida na mishi alkawarin baza'a zubar da cikin ba sannan yabar kasar gaba daya, haka na koma gida iyayena suka kara rufeni da duka kaman zasu kasheni waina dauko musu abun kunya, in ban fadi wa yayi min ba sai sun kasheni, da naji wuya tare da tunanin muhd yabar kasar ma yasa na fada musu wanda yamin sun shiga tashin hankali sosai, gashi anje inda yake aiki ance yabar kasar, haka iyayena sukace a zubar da cikin naki yarda babu irin abunda ba'ayi ba amma cikin yaki zubewa, har yan gari suka san labarin abun kunyan dana aikata ko waje bana fita dan gori da zaki abun bama ni daya ba harta iyayena ana musu gori wanda hakan yasa aka cire mahaifina daka liman akaba wani, abun yama mahaifina ciwo wanda hakan yasa kaf yan gidanmu suka kara tsanata har gwara adda tana tausayamin in babana baya gida, ana haka har na haiyu cikin rashin gata, har nayi arba'in cikin dakin datti nake kwana da yarona, kwananshi arba'in da daya a duniya na nemeshi na rasa, nan aka dauka mahaifina ya kashe yaron ya boye, aka tsanemu a garin da kyara zagi wanda mahaifina yayi zuciya tare da fadin inbar gidan sannan inna kara zuwa mai gida Allah ya isa bai yafe min ba, babu irin hakurin da adda bata bashi ba amma yace inta kara magana a bakin aurenta, haka tana gani na tafi yayyina sune masu kara zugawa waina dauko musu abun kunya basa iya shiga cikin mutane, haka nabar gidan cikin dare banda kudi banda kowa, duk wannan abunda akamin ban damuba kaman rashin yarona wanda nake gani kaman mahaifin nawa ne ya daukeshi dagaske din, gaba daya na kara tsanan zaman kauyen ma tare da fadin gwara da aka koreni ma, haka naita tafiya cikin dare harna bar anguwanmu ina cikin tafiya ne cikin sauri saboda tashin hankali ko gajiya banyi ba, wata mota ta rugo a guje saura kadan ta bugeni, Allah ya taimaka, mutumin ya fito yana fadin haba baiwar Allah miye hka bakya duba hanya gashi cikin dare ina zaki, nace duniya zan shiga, yace subhanallah, haba baiwar Allah mai yayi zafi haka, kuka na saki tre da bashi labarin abunda ya faru ya tausayamin sosai inda yace in shiga motarshi muje ban musa ba na shiga sai naga ya nufi anguwarmu, direct gidan mai gari mukaje inda yayi2 in fito naki, haka ya shiga jim kadan saiga mai gari da mutane sun fito inda akasa na fito dole, mai gari yace wannan yar iskan zaka aura bawan Allah ko dai kaine ka mata ciki? Yace wlh ko daya, nan aka tura aka kira mahaifina bayan yazo ya ganni yace baya kaunar ganina, mai gari yace ya nutsu nan aka mishi bayani inda yace shiba mahaifina bane ya sallamani zan iya yin duk abunda naga dama tare da fadin har abada baya bukatar ganina,haka mai gari ya daura mana aure da mutumin da ba'asan ko waye ba......Babu abunda nake sai kuka, bayan an gama daurin auren mai gari ya kalleni yace daka yau kar in kara shigowa wannan garin domin kar in lalata musu yara, haka muka tafi muka bar garin cikin dare, babu komai a raina sai tsanar garin da yan garin tare da mahaifina, haka muka shiga cikin garin yalo inda anan gidan mijina yake duk da bamai karfi bane sosai amma yana da rufin asiri yana da mota golf guda biyu daya ana mishi haya daya kuma shi yakeyi da kansa, yayi karatun boko rashin aikin yine yasa ya fara jan mota, iyayenshi sunyi mamakin auren da yayi amma da yake suna da tawakkali duk da abun ya bata musu rai ace yayi aure bada saninsu ba, haka suka hakura dan mamanshi ta dade da rasuwa wajan matar babanshi ya taso, suna nunamin gata sosai haka shima duk da yasan labari na, ina mamakin mai yasa ya yarda ya aureni, wata rana muna fira yake fadamin wai ya taba ganina ina tallan nono tun daka lokacin yaji yana sona, amma sanin al'adun mu na fulani yasa ya boye komai dan yasan kauyenmu kana jariri ake maka miji, sai kuma gashi yanzu kin zama matata, ina kokarin kyautata ma mijina, domin kaf duniya banda kamanshi dan ina ganin yafi kowa kaunata, shekara daya da aurenmu na haifi dana namiji santalele inda aka sa mishi sunan baban mijina wato umar, lokacin daya cika arba'in matar data riqe mijina ta rasu, munyi kuka sosai, tun bayan rasuwanta baba shima ya fara ciwo sosai, tsakaninsu wata uku shima ya rasu, kai munji mutuwar baba sosai, inda gaba daya zaman garin yalo ya ishemu dan dama ni bana son garin ina dai zama ne kawai, haka muka tattara muka koma kaduna muka sami gida muna haya, shekara biyu tsakani na kuma haifan da namiji muka sa mishi khalil, a lokacin mijina ya sami aiki a banki, lokaci kadan rayuwanmu ta fara canzawa, daka wajan aiki aka dawo dashi abuja inda aka bamu gida karami za'a dinga cirewa cikin kudin aikinshi, haka muketa rayuwa cikin kwanciyan hankali tunda na haifi khalil ban kuma samin ciki ba, abun yana damuna dan ina son samun yarinya mace, su umar har sun fara zuwa makaranta, wata rana munje anguwa nida mijina, motarmu tayi faci, nan ya fara kwance taya yana gyarawa ni kuma ina tsaye kusa dashi saiga wata mata tana ta gudu da alaman wasu ne suka biyota, tana zuwa wajanmu ta mika ma mijina kwali tana fadin dan Allah gashi akwai komai da komai a ciki ka ceci rayuwar yata daka fadawa halaka, tana fadin haka tabar wajan ta wuce da wajan minti biyar lokacin har mun shiga mota muna jimami tare da fargaban maita bamu, saiga wasu mutane da makamai sunzo sun wuce da gudu suna fadin miyi sauri karta bace mana, jin haka yasa muka gane kasheta suke son yi, haka muka karasa gida muka shiga da kwalin budewan da zamuyi muka ganki kina bacci abunki tare da magudan kudade dollars na amurka, mun tsora sosai wata takarda muka gani anyi rubutu kaman haka..... *salam ga duk wanda ya tsinci wannan yarinyar inaso ya riqemin ita amana wlh yar sunna ce bata hanyar zina aka sameta ba banda lokacin yin bayani sosai kar lokaci ya kure min, sunanta jawaheer duk wanda ya dauketa yayi amfani da wannan kudin na bashi halak malak, idan na rayu zan dawo neman yata wata rana in kuma sun kashe ni, shikenan* kallon juna muka fara nida mijina yace bazai dauki kudin ba zai kaiki wajan police dan yana tsoro ni nayi ta nuna mishi yayi hakuri mu taimakeki mu riqeki amanace mahaifiyarki ta bamu, da farko kaman taso ta ajiye kine sai Allah ya hadamu ta bamu, dakyar ya yarda lokacin da mukaje canzo kudin naira million dari ne kudin dai2 wlh munyi mugun firgita da yawan kudin, tun daka lokacin ya fara business da kudin yabar aikin banki rayuwa ya canza mana sosai, wlh jawaheer ina masifar sonki na dauki son duniya na daura miki haka mijina da nake ganin yafi kowa sonki domin yace tunda ya sameki Allah ya bude mishi kofofin arziki baya son ganin fushinki ko kadan munsha yin fada akanki nida shi, idan kikai abu na miki fada to in raina yayi dubu saiya baci sai yasa kika fi sabawa dashi dan yana yawan tafiya dake wlh ina takaicin fada miki bamu bane muka haifeki..... Kuka jawaheer take sosai lokaci daya ta fara fadin yanzu ba'asan inda iyayena suke ba, na shiga uku shikenan bani da wani gata a duniya mai yasa mum dina bata tafi dani ba, anya ma ta auren aka sameni kuwa kaman yanda ta rubut.... Mum ce ta toshe mata baki duk wanda ke wajan saida ya tausaya mata m samir shima hawaye yake amma bai bari sun gani ba dan da turanci mum ta fada mata komai, wani irin tausayin jawaheer yaji yana shiganshi sosai, shi gashi yaga mahaifiyarshi tare da taimakonta lallai shima ya zama hakki a kansa ya neman mata iyayenta, lokaci daya ya kalli mum yace mum babu wani shaida da za'a gane inda iyayenta suke? Mum tayi shuru can tace akwai international password da hotan mamanta a jiki, da sauri yace yana ina?? Mum tace yana gida abuja, yace mum plz mu koma yau can abuja din, mum tace dare yayi sai dai gobe, jawaheer kam bata komai sai kuka, adda itama fa fara rarrashinta tare da fadin yakamata tayi tawakkali insha Allah zaki ga iyayenki, dakyar jawaheer tayi shuru amma babu komai a ranta sai tarin bakin ciki da takaici yanzu basu dad banr iyayenta inta tuna hakan sai taji kaman tai ihu dan baki ciki, muryanta su mum sukaji tana fadin international password din wani kasa ne? Mum tace saudiya sannan ina tunanin itama yar can ne dan balarabiya ce ita, jawaheer bata kuma cewa komai ba, inda mum take tambayan adda ina mahaifinta adda tace hmmm labari mai tsawo amma bari in baki.......


Mum tace maiya faru adda?? Adda tace bayan kin tafi na bujire ma mahaifinki akan bazan yarda ba dole a dawo dake gida yace sai dai in biki in kuma na biki a bakin aurena, muna zaune aka kirashi mai gari, bai dawo ba sai can cikin dare yazo yana fadin an miki aure kuka nasa ina fadin haba mlm kai yanzu baka san kaddara ba? Wlh abunda ka aikata ko wanda baije islamiya ba bazai aikata ba, kaine limamin wannan garin mlm mai yasa bazaka dauki kaddara ba? Mai yasa zaka yanke wannan danyan hukuncin wlh mlm ka manta da nauyin dake kanka na amanar da Allah ya baka na yaranka, yanzu da kuka mata aure kasan wata aura?? Miye sana'an mijin?? Dan gidan mutunci ne?? Duk baka saniba, kai dai burinka tabar inda kake saboda kunyar data dauko mata wanda bai wuce ya fada kan kowa ba, mlm ina iliminka?? Da har zaka bari wai magan ganun mutane suyi tasiri akanka harka manta da kaddara bayan Allah yace muyi imani da kaddara khairan wa shairan, Kai ka sani ko wannan jarabawan da Allah ya maka inka jure shine silan shiganka aljanna, amma saika kasa jurewa....... Kuka mlm ya saki yana fadin kaico na kaico na lallai yau na yarda da manzon Allah yace gwara ka auri mace mai addini, yau gashi matata ta tunasar dani abunda na manta saboda kunyar duniya , yau idan Allah ya dauki rayuwa na mai zance mishi, lallai ban kyauta ma bilkisu ba, ban mata adalci ba, yanzu ina zan ganta?? Adda cikin kuka tace nasan ganinta zaiyi mana wuya amma ni burina ka gane ka kuma fahimta amma alhmdlh tunda ka gane, nasan ko mu dade ko mu juma wata rana zata dawo garemu insha Allah kawai mu tayata da addu'a duk inda take Allah ya kareta, abun ya mata yawa ga batan yaronta ga koranta da akayi kai wannan wani irin ibtila'i ne, mlm yace wlh koni inayi mata duk abunda nayi bada son raina ba, lallai nayi dana sani wanda bashi da amfani a yanzu Allah yasa mijin data aura ya riqemin ita da amana, adda tace ameen ,mlm yace zanyi ta bincike har in gano inda take, adda tace Allah yasa a dace, tun daka wannan ranan mlm yake ta tunaninki kullum burinshi ya ganki yaga wani hali kike ciki, abubakar yayi aure yana da yara biyu, maryam da abdullahi sunan yayanki aka samai suna kiranshi da hamman, shi kuma abdullahi ya sami aikin mota yana zuwa gari2 yayi hatsari ya rasu munji mutuwarshi sosai, abubakar yake mana komai na rayuwa duk da shima bawai yana da wani karfi bane, mahaifinku ya saida shanayenshi ya gyara gidan nan tare da fara sana'a a kasuwa yana saida su hatsi wanda shida abubakar suke zaune suke saidawa tunda babban shago ne, duk da mahaifinki ba wani lfya gareshi ba kullum burinshi ya ganki ko ya sami labarinki amma shuru har yanzu, kinji abunda ya faru bayan tafiyanki, amma bilkisu ban taba tunanin zaki rabu damu ba tsawon wannan lokaci, tace adda kiyi hakuri wlh ina son inzo duk da nasan har yanzu baba yana fushi dani, amma inna tuna shida kanshi ya koreni sai inji bana son zuwa amma kullum kuna raina kuma kuna cikin addu'a na koda yaushe, Allah sarki ya abdullahi lokaci yayi Allah yaji qanka ashe bazamu sake haduwa ba, adda ta kalli dady tace Allah ya biyaka yanda ka riqe min yarinya tsakani da Allah kaima Allah ya baka abunda kake nema duniya da lahira, dady ya amsa da ameen.
Jawaheer kam kallonsu take Amma ita daya tasan abunda take saqawa a ranta, shiko m samir idonshi na kanta gaba daya tausayinta yake ji, ya rasa dalili mai yasa yake jinta a ranshi yanzu, amma ta wani gefen yana ganin kaman tausaya mata yake dan shima ya taba shiga irin halinta na rashin mahaifiya lokacin da yasan mum dinshi na raye ba karamin ciwo yaji abu, itace ta zauna kusa dashi tare da kwantar mai da hankali wanda gashi yau sun hadu da mum dinshi duk ta sanadin jawaheer din, gashi kuma sanadin haduwanshi da mum dinshi yasa jawaheer tasan basu bane iyayenta, ido ya lumshe tare da fadin no matter what i will stay by ur side, jawaheer matsawa yayi kusa da ita, kallonshi tayi ta sakar mishi murmushi wanda bata san ya fito ba, shima murmushin ya sakar mata tare da fadin ya jikin naki? Tace naji sauki sai dai bana jin dadin zama a nan, inaso in koma abuja, yace kiyi hakuri gobe zamu tafi, kai ta daga mai alaman toh, adda tace bari inje gida dare yayi kar mlm ya dawo yaga bana nan,nama san yana gidan yanzu inna koma a kawo abinci, dady yace ki bari adda zamu siyo yanzu, nima inaso inga mlm ya kalli mum yace bari muje, jawaheer tace dad, cikin sauri duka suka kalleta, tace kuje da mum itama nasan tana bukatar ganin kakana, kowa dake dakin saida yaji tausayinta, mum tace a'a babu inda zani dawa zaki zauna, tace mum naji sauki kuma m samir zai zauna dani kije kiga kakana, mum wani hawaye ne ya zubo mata tare da zuwa wajan jawaheer ta rungumota tana fadin dan Allah duk wuya karki barni jawaheer ban taba banbantaki da yaran dana haifa ba, jawaheer ina sonki haiyuwanki ne kawai banyi ba amma wlh baki da banbanci da yarana, jawaheer itama cikin kuka tace insha Allah mum bazan taba gudunki ba, bani da wata uwa saike.... Kuka yaci karfinta dakyar ta seta kanta tace mum kije dare nayi, mum kallon m samir tayi tace ka kula da ita nima anjima zan dawo tare zamu kwana da ita, yace ok, sannan suka fita.
Bayan sun fita m samir ya zauna kusa da ita, ido ya kura mata tare da fadin jawaheer kibar kukan nan haka, ya isa, murmushi tayi tare da fadin yana da amfani domin shine kawai nakeyi inji dadi, ido ya kura mata ganin irin kallon da yake mata yasa ta juyar dakai gefe, kirjinta yana buga mata da karfi duk sanda suka hada ido jin muryanshi tayi yana fadin bakya jin dadi in kina tare dani?? Da sauri ta waigo suka kara hada ido wani tambayan ya kuma jefo mata yace jawaheer mai kikeji in kina tare dani?.......


Idonshi nakan nata yana jiran yaji mai zata ce, yayin da ita kuma tambayan yazo mata a bazata, dan haka yasa ta kasa koda motsa baki balle ta bashi amsa, ganin irin yanayin data shiga yasa ya hura mata iska a fuska wanda yasa ta lumshe ido da sauri, ido ya kara kura mata yana dan murmushi tare da fadin jawaheer kina da kyau sosai, da sauri ta bude ido dan ta gani ko shi dinne dagaske yake fada mata haka, ido ya kashe guda daya kaman yasan abunda yake ranta, yace kina mamaki koh? Gaskiya nake fada miki, kina da kyau mai daukan hankali jawaheer tun sanda na ganki naji kina min kama da larabara ina mai kyautata zaton kina da jini da larabawa, duk namijin daya sameki zaiji dadi sosai, sannan duk wanda ya aureki zanja mishi kunne ya riqemin ke da kyau, wani iri taji domin magananshi ta karshe ya nuna mata bawai yana sonta bane, jin tayi shuru yasa yaja hancinta tare da fadin jawaheer kin sani cikin farin ciki sosai ta sanadinki yau gani ga mum dina, kema Allah ya nuna miki iyayenki, kai ta girgiza tare da fadin bana bukatar ganinsu har abada zanyi rayuwa na ni daya ba tare dasu ba, ido ya kura mata ganin irin kallon da yake mata yasa ta juyar da kanta gefe, yace har cikin zuciyarki kike fadan wannan maganan?? Shuru tayi ba tare da tace komai ba, yace ki bani amsa, kuka ta saki tare da fadin mai zance da yafi wannan? A da ina farin ciki sosai tare da iyayena, amma lokaci daya komai ya canza min tunda nasan basu bane iyayena, ina mamakin mai yasa mum dina ta bada ni, ta tafi ta barni...... kuka yaci karfinta sosai janyota yayi jikinta ya rungumeta yana bata hakuri akan tayi shuru, dakyar ya samu tayi shuru, yace jawaheer inaso koda yaushe ki kasance maiyi ma kowa uzuri, karki yanke hukunci akan abunda baki san miye asalin faruwanshi ba, haka kawai mahaifiyarki ba zata bada keba, lallai akwai wani abu a labarinki, wanda hakan ya zama dole mu nemi mum dinki, jan jikinta tayi a nashi tace nemanta bashi da amfani bani da wani buri daya wuce in sami namijin da nake so, shima yana so na, wanda za muyi rayuwa cikin jin dadi sai sai kash, hakan bamai yihuwa bane, ina tunanin barin kasar nan gaba daya inyi nesa da kowa na wani lokaci, ido ya kura mata yana kallonta harta gama, yace har dani za kiyi nesa dani? Shuru tamai ba tare data bashi amsa ba, yace ina jinki jawaheer? Tace ni kawai so nake in huta, yace ba amsan da nake son jiba kenan, satan kallonshi tayi amma sai akayi rashin sa'a shima din ita yake kallo caraf suka hada ido, ya daga mata akai alaman ina jinki, tace nifa bance zanyi nesa dakai ba, murmushi yayi yace gashi kince za kiyi nesa da kowa, tace ni banda kai nake nufi, wannan karan dariya yayi tare da fadin jawaheer bazan taba barinki ba har sai na sadaki da mum dinki wannan shine alkawarin dana daukan miki, wani hawaye ne ya zubo mata tace mai yasa zaka min haka? Yace saboda u r my sister my best friend, ke kawata ce daka yanzu, wani irin murmushi ta saki lokaci daya tare dayin hugging dinshi tana fadin thanks alot.
Bayan su mum sunje gida dad yaba driver kudi yace yasai abinci yakai masu jawaheer, sannan suka shiga cikin gidan, koda suka shiga falon baki suka zauna, basu dade da zama ba saiga mlm ya shigo falon yana fadin kai yau na gaj..... Bai kai da karasa maganan ba idanshi ya sauka akan bilkisu duk da tayi dan jiki kadan da kuma haske, hakan baisa mlm yaki ganeta ba, da hannu ya fara nunata yana fadin bilkisu, kece? Sai kuma ya daga hannu sama yana ma Allah godiya tare da hawaye wanda kana gani kasan na farin ciki ne, yace khausar matso kusa dani, da sauri mum ta karasa wajanshi itama tana kukan rungumeta yayi yana fadin dan Allah ki yafeni khausar nasan nayi miki ba dai dai ba, ki gafarce..... Tace haba baba ka daina neman gafara na kaifa mahaifina ne, komai kayi a kaina kayi dai dai, mlm yace Allah ya miki albarka khausar sai a sannan ya lura da dady, yace jibrin sannu, nan dady ya gaida mlm cikin girmamawa, mlm ya fara mishi godia akan irin riqon da yayi ma yarshi dan daka gani bama sai an tambaya ba kasan tana cikin kwanciyan hankali, adda ce ta shigo dauke da tray ruwa ne akai da zobo da kofuna, ta ajiye a falon, mlm yace yau ina cikin farin ciki sosai adda tayi dariya tace ina abubakar? Mlm yace yanzu zai shigo yaje anso mi..... Kafin ya karasa sukaji sallamanshi amsawa sukayi su duka ya shigo shima dai ba karamin farin ciki yayi ba na ganin kanwar tashi, nan adda tahau bama mlm labarin abubuwan da suka faru mlm yasha mamaki, yayi shuru can yace ita yarinyar tana asibiti ne da yaron naki? Mum tace eh amma yanzu zan koma dan inaso in kwana da ita gobe wai take son ma mu koma abuja, mlm yace kai da wuri haka muje asibtin tare nima inga yaron da kuma ita mai jikin, haka suka fita harda abubakar adda kawai suka bari a gida.Koda suka isa asibitin, suka karasa dakin inda suka iske jawaheer na sallah shi kuma m samir na danna wayanshi ba komai yakeyi ba sai game, dan bashi da sim card din nigeria bai samu ya siya bama, ganin sun shigo yasa ya tashi da sauri yana fadin sannu da zuwa mum, cikin harshen turanci amsawa tayi cikin sakin fuska, sannan tace mai jiki anji sauki kenan, yace eh alhmdlh, sai a sannan ya gaida su mlm da abubakar, mlm murmushi yayi tare da mika mai hannu danshi baya jin turanci, amma abubakar naji, mlm yace ni wannan yaran naku ban iyashi ba, duka suka saka dariya, mum tace ma m samir ga kakanshi shine babanta, ga kuma yayanta ta nuna abubakar, nan m samir ya kara gaidashi tare da fadin uncle ina farin cikin haduwa daku, abubakar yace nima haka uncle dinka yana cikin masoyanka danni dan barcelona ne, kuma kai nake so, dariya m samir yayi tare da fadin thanks my uncle, dai dai lokacin jawaheer ta idar da sallah, itama gaida mlm tayi cikin harshen hausa, amsawa yayi tare da fadin ya jikin naki? Tace da sauki alhmdlh, sannan ta gaida abubakar shima ya amsa cikin sakin fuska, nan mlm ya zauna kusa da jawaheer suna ta fira yana ta janta da surutu tana ta dariya m samir kuma ya matsa kusa da uncle dinshi yana fadin wai mai yasa take dariya mai ake fada mata haka? Dariya abubakar yayi yace wasa yake mata yana fadin shine zai aureta amma itace zata biya sadaki dan taimaka mata zaiyi, shima m samir din dariya ya farayi yi, tare da fadin uncle nima ina son koyan wannan yaran naku, abubakar yace ai babu wuya sai in fara koya maka, gashi naji ance gobe zaku tafi, kallon jawaheer yayi yace sis mu dan zauna a nan na kwana biyu mana, murmushi tayi tace ok duk yanda kace bani da zabi, yaji dadin abunda tace yana son biyayyan jawaheer tana son abunda yake so, mum ce tace au nama manta taci abincin kuwa?? M samir yace eh taci amma bada wani yawa ba, mum tace jawaheer kin taba ganin ana ciwo babu cin abinci?? Tace mum nafa ci kadan na rage, murmushi mum tayi dai dai lokacin dad ya shigo dauke da ledoji a hannunshi, mum ta tashi ta amsa tare da ajiyewa kayam fruit ne dasu kaji gassasu, mum taba jawaheer kaza daya ta mika ma mlm da abubakar mlm yace a'a shi tare da matarshi zaici dariya duka sukayi m samir shima yaci kazan yana ta fadin kazan akwai dadi suna tamai dariya yanda yake ta santi, dad yace jawaheer kinji sauki koh? Tace eh dad sai dai bana jin dadin komai amma ganin mum da kakana yasa naji dadi sosai, kowa ya fahimta abunda take nufi wato shiryawan mum dinta da mahaifinta yasa taji dadi sosai, kowa dake dakin saida yaji tausayinta tare dayi mata fatan itama Allah ya hadata da iyayenta, dad yayi murmushi tare da fadin Allah ya kara miki lafiya bari muje mu kwanta dare yayi, duka kowa ya fita amma banda m samir da mum, m samir yana son yi mata magana amma bazai iyaba dan mum na wajan haka ya fita tare da fadin good night, ji tayi kaman ta bishi, koda ya fita ya tarar dasu a waje, abubakar yace ma m samir a gidanshi zai kwana, security dinshi sukace ma abubakar dan Allah yayi hakuri an basu tsaronshi ne idan wani abu ya faru dashi zasu shiga matsala, duk yanda abubakar yaso m samir ya kwana a gidanshi haka ya hakura akan gobe zasu hadu, koda m samir ya koma hotel din daya sauka wanka yayi ya kwanta amma bacci yaki zuwa, sai juyi yake tayi gaba daya tunanin jawaheer yake tayi wanda ya hanashi sakat, ya rasa dalilin da yasa yake tunaninta har yake kokarin hanashi bacci abunda bai tabayi ba kenan ko sonia da yake so baya jinta kaman yanda yake jin jawaheer a yanzu, dan tsaki yayi tare da fadin tausayinta nake ji sai yasa nake tunaninta.....Haka yaita tunani kala2 yayinda yake ta tursasa ma zuciyarshi akan tausayinta yake kawai, wasa2 har wajan karfe biyu amma babu alaman bacci a idonsa sai tunanin jawaheer gaba daya ma kanshi ya kulle yama rasa mai yake ji a kanta, ganin babu baccin a idonsa ga tunanin yaki barinsa yasa ya tashi ya shiga toilet yayi alwala, sallah yazo yayi tare da roqan Allah akan ya zaba mishi abu mafi alkhairi a rayuwanshi, ya dauki lokaci mai tsawo yana roqan Allah akan ya zaba mishi abu mafi alkhairi, kafin ya tashi ya koma gado yana kwanciya bacci ya daukeshi.Ta gefen jawaheer ma haka abun yake bata so m samir ya tafi ba, ita inda so samu nema dashi ya kwana da ita amma sai dai hakan bamai yihuwa bane, babu abunda take sai tunaninshi tare dason qara ganinshi, duk da sau da yawa zuciyarta tana kara nuna mata tayi baya dashi dan ba sonta yake ba, amma ta kasa, a yanda takeji inda tana da halin cireshi a ranta data dade da cireshi, itama haka taita tunani har bacci barawo yayi awon gaba da ita.Jawaheer tunda ta farka tayi sallah asuba, bata koma bacci ba, har adda tazo da kayan abinci ita da mlm, jawaheer ta gaidasu cikin girmamawa inda suka tambayeta ya jiki ta basu amsa da fadin da sauki, dad dinta ne ya shigo cikin dakin yana fadin mai jiki anji sauki kenan? Murmushi tayi tare da fadin alhmdlh dad, dai dai lokacin dr ya shigo dakin tare da wata nurse, jawaheer na ganin dr ta tashi tare da fadin dr yau zani gida koh? Dariya dr din yayi daya kafeta da ido yace a'a ai kya bari ki dan kara jin sauki koda nanda sati biyu ne, ido ta zare tare da fadin ni kam yau gida zan tafi dan na warke sosai, dr yace shikenan zaki iya tafiya amma ki dinga kiyaye wa ki rage yawan tunani, tace insha Allah, murmushi yayi tare da kallon dad yace alhaji Allah ya kara mata lfya, jiki yayi sauki komai yayi normal, dad yace hakane mun godema Allah komai yayi kyau, dr ya kuma waigawa wajan jawaheer yace zanzo gida inji mai kike tunani haka har ya miki yawa kika fadi lokaci daya, mlm yace likita ni take tunani amm zanyi hakuri in aureta haka, duka suka sa dariya, jawaheer sai tunanin maiya hana m samir zuwa take tayi, haka suka fara shirya kaya har suka fitar da komai aka bama jawaheer magani Suka shiga mota, direct gidan adda suka nufa, koda suka isa jawaheer dakin adda ta shiga ta kwanta dan bata son wata fira a halin yanzu tafi jin dadi ta ganta tayi shuru, tunawa tayi da wayanta dan haka ta fito ta dauki hand bag dinta dake falo, mum tace mata yauwa jawaheer maza kizo kiyi wanka saiki kwanta gaba daya, tace to mum, dan shuru tayi can tace mum kayana basa nan suna hotel din da muka sauka, mum tace bude akwatina ki dauki zani anjima ko gobe kyaje ki kwaso kayan bata kara magana ba ta nufi dakin da kayan mum suke ta dauki zani ta nufi bayi dan tayi wanka, bayan ta fito daka wanka daka ita sai saurin kirji sai kayan data cire a hannu, kasancewan bayin gidan a waje yake, tana saurin ta shige ciki sukaci karo wanda shima a dai2 lokacin ya shigo gidan kuma bayin daka shi sai kofar gidan, tsayawa tayi taga dawa ta buge ganinshi tayi yana mata murmushi itama bata san lokacin data sake murmushin ba, sai taji kaman tayi hugging dinshi, a hankali ya furta mata ya jikin ki? Tace da sauki, yace naje hspt akace min kin dawo gida, ban tashi da wuri ba yau jiya banyi bacci da wuri ba ina ta tunani, tace tunani kuma? Yace eh, shuru tayi tana dan nazari shi kuma idanshi na kanta, katseta yayi da fadin ina mum? Tace tana ciki shiga yayi itama binshi tayi a baya tana shiga tayi daki, mai ta shafa cikin kayan mum ta dauko jallabiya tasa duk da ya mata yawa amma haka tasa, tana zaune tana jiyo firan mum da dan nata, uncle abubakar ya shigo, nan firan ta canza zuwa na ball, mum tace bada ita ba, jawaheer kwanciya tayi amma ba bacci takeyi ba, kawai tana tunani ne, tunda tasan basu mum bane iyayenta take jin wani iri saita tsinta kanta da rashin sakewa kusa dasu, harta dad bata sakewa in yana wajan sabanin da, wani zubin in abun nata ya tashi haka zatai ta shagwabe ma dad dinta wanda a yanzu bata jin zata iyama fira dashi kaman da, wani guntun hawaye ne ya zubo mata, babu komai a ranta sai bakin ciki tare da takaicin mai yasa basu kasance iyayenta na gaskiya ba, mum ce ta shigo dakin hannuta dauke da tray, ganin tana kuka yasa mum tayi saurin karasawa wajanta tana fadin jawaheer mai ya sameki?? Tayi saurin goge hawayen tare da fadin babu komai mum, ido mum ta kura mata tare da fadin jawaheer nasan abunda kike tunani bazai wuce kice bamu bane iyayenki, tun ranan da kika san haka kika rage yin magana damu, kika daina sakewa a gaban mu, jawaheer wlh dai dai da rana daya ban taba cireki a raina ba, har gobe ina miki kallon yar dana haifa a ciki na, mai yasa kema ba zaki daukemu a matsayin iyaye ba jawaheer?? Kuka jawaheer ta kara fashewa dashi tare da rungume mum tana fadin ba haka bane mum har gobe kune iyayena kawai ina takaicin daya kasance baku kuka haifeni ba, amma ban taba canzaku daka matsayin da kuke ba, mum tace toh kiyi shuru ga abinci kici sai kizo muje falo ayi fira dake, bata musa ba ta dauki cup din tea da white rice ns stew ta fara ci, mum tana zaune harta gama ci, duk da ba wani da yawa taci ba, amma tasha tea din da yawa, mum ta dauko mata magani tasha, sannan suka fita falo, tunda ta fito idanshi na kanta harta zauna, akan kujeran dake kallon nashi, gaida uncle abubakar tayi ya amsa tare da tambayanta ya jikin nata? Tace da sauki alhmdlh, murmushi yayi tare da fadin badai ciwon bane yasa kika rame kayan naga ya miki yawa, itama murmushin tayi wanda ya kara fito mata da kyanta, tace a'a kayan mum ne nawa yana hotel din da muka sauka, adda ce ta shigo da kayan jawaheer tana fadin ga wasu da kika canza a asibti na wanke miki su, tace lah adda wanki kuma, keda kanki? Adda tace gasu maza kije kisa sai kuje ki dauko sauran, bata musa ba ta tashi ta nufi daki dan canza kaya, jim kadan sai gata ta fito cikin hijab, ido m samir ya bita dashi dan ba karamin kyau hijab din ya mata ba, mum tayi murmushi tace jawaheer hijab na miki kyau amma bakya son sawa, murmushi tayi, tana kokarin zama taji muryan m samir na fadin muje mu dawo, dan haka bata karasa zaman ba suka fita, security din na ganinsu suka bude musu baya suka shige, kai tsaye hotel din suka nufa har suka karasa babu mai ma dan uwanshi magana, har suka shiga ciki ta nufi dakin data sauka ta fara hada kayanta tana cikin hadawa ya shigo dakin ya hade hannunshi biyu a kirjinshi ido ta dago suka hada murmushi ya sakan mata tare da nufanta ya zauna kusa da ita, ita dai bata cemai komai ba tana ta hada kayanta, hannunta ya kamo tare da janyota jikinshi kirjinta ya fara bugawa da karfi fuskanta ya dago suna kallon juna ido ta rufe da sauri amma tana jin saukan numfashin shi, jin muryanshi tayi yana fadin kina fushi dani ne? Ido ta bude da sauri ganin har yanzu ita yake kallo yasa ta kara rufe idonta murmushi yayi tare da fadin sunanta jawaheer bata amsa ba haka bata bude ido ba, yace mai yasa kike fushi dani, ido ta bude tare dayin kasa da kanta, ganin haka ya kara janyota jikinshi yace fadamin, tace niba fushi nake dakai ba, yace to mai yasa bakya son yin magana dani yau? Tace ba haka bane , yace toh miye? Dariya ta saki tare da fadin babu komai kawai bana son yin magana ne yau, yace har dani bakya son yin magana? Kai ta daga alaman eh, murmushi yayi tare da sakinta ya tashi tsaye yace ok kiyi hakuri da takura miki da nayi akan saina miki magana, in kin gama ki sameni a mota, da sauri tace to wazai fito min da kayan? Yace keda kanki mana tunda baki son a dameki, murmushi tayi tare da tashi tayi hugging dinshi ta baya tace sorry ba haka nake nufi ba, kana daya daka cikin mutane masu muhimmanci a rayuwa na, koda zan zauna daka ni sai kai bazaka taba gundura na ba, waigowa yayi tare da fadin really? Kai ta daga mai alaman eh, hancinta yaja tare da fadin zo in tayaki hada kayan, zama yayi suna ta hada kayan har suka gama, ya kira masu aikin hotel din suka fara fitar sa kayan zuwa mota, suma fita sukayi ya kalleta yace yau kinyi kyau, tace nagode, bayan sun shiga mota yace ma jawaheer ina ake saida sim? Dariya tayi tace nima ban taba zuwa state din nan ba, amma muje mtn office, tace ma driver suje mtn office yace ok, hannunta ya kamo tare da fadin kema zaki canza naki sim din, da sauri ta dago tana kallonshi tare da fadin saboda me?? Shuru ya mata ba tare daya bata amsa ba, har suka karasa mtn office, fita sukayi suka shiga wani office aka kaisu daka shi sai jawaheer, jim kadan sai ga wani ya shigo yana bama m samir hannu tare da fadin ban taba tunanin zan ganka ba a rayuwa yau gani gaka, m samir yayi murmushi mutumin yace plz zamu iya daukan hoto? M samir yace ok nan mutumin ya fara daukansu, sannan ya tambayi m samir mai yake so yace sim card guda biyu sannan yana son number shigen iri daya, mutumin ya dauko sim biyu ya bashi, special number karshen ne kawai ya ban banta, daya 7 daya 8, nan aka mishi register dayan ma da sunanshi akayi, har aka gama suka fito, nan mutane suka fara ihu tare da daukanshi hoto, dakyar security dinshi suka fitar dashi sukai mota, suna cikin tafiya ya kalli jawaheer yace bani wayanki? Kallonshi tayi ba tare da tace mishi komai ba kota miqa mai, hannu ya miqa mata ganin haka yasa ta bashi wayan, hannu yasa a kunnenta ya ciro dan kunnenta ya ciro abun sim din, ya cire nata yasa mata sabon daya, shima yasa daya a nashi, sai daya gama ya miqa mata wayanta tare da karya sim dinta, da ido ta bishi tana son yi mishi magana amma taga ya daure fuska ganin haka yasa tayi shuru tare da mamakin mai yasa ya mata haka, bai karayi mata magana ba har suka karasa gida, security dinshi suka fara shigar mata da kayan, itama ko kallonshi batai ba tayi cikin gida dan karya mata sim da yayi ba tare da wani dalili ba abun ya bata haushi, yana kallonta ya bita da murmushi dan yasan taji haushi, amma shi daya yasan dalilin da yasa yayi hakan, koda ta shiga a tsakar gida taga adda ita da mlm, bayan ta musu sannu da gida, tace ina mum? Adda tace ta fita ita da babanki basu dade da fita ba, m samir shima ya shigi gidan, tana ganinshi tayi ciki, adda tace toh ni yanzu bajin yaranka nake ba, ta kwada ma jawaheer kira tazo da sauri, adda tace taya zaki shige ciki bayan kin san mu bama jin turanci, fada mishi ya tayaki shigar da kayan, kallonshi tayi wanda shima itama din yake kallo yana mamakin fushin da takeyi dan an karya mata sim, tace ance wai ka tayani shigar da kaya, murmushi yayi tare da daukan akwati itama ta dauki wasu suka shigar dasu haka har suka gama kwashewa mlm ya fita daka gidan dan komawa kasuwa, itama adda ta nufi dakinta, ya rage daka m samir sai jawaheer a falo wanda sukai shuru su dukansu, tashi yayi ya matso kusa da ita, yace mai yasa kike fushi? Mai akayi miki? Tana son ta tambayeshi mai yasa ya karya mata sim amma saita kasa dan ya mata wani irin kwarjini, ganin tayi shuru yace saboda na karya miki sim kike fushi koh? Toh idan na kwace wayan fah????........

Post a Comment for "JAWAHEER CHAPTER 4"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...