Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

GIDAN SARAUTA CHAPTER 8

GIDAN SARAUTA CHAPTER 8

- - Post a Comment
GIDAN SARAUTA

CHAPTER 8


          

Haka akayima bafaden sutura akakaishi gidanshi na gaskiya hmm rayuwa kenan Allah  yasa muyi kyakyawar karshe..........
Tunda aka gama jana'izar Almustapha yafita yabar gidan don zuciyarsa bazata iya daukar abubuwan dayake faruwaba.....

                              

Bangaren Magajiya kuwa tunda taji labarin Almustapha nada rai tashiga damuwa dukda madai jiya ba a ambaci sunantaba to tabbas tasan tunda har wani yarasu ata dalilin haka Mai Martaba seyayi raising case din........
Zufa takeyi sosai jitayi antaba kafadanta cikin sauri tajuyo atsorace murmushi Zaliha tasakar mata sannan tace"Mama nine kikwantar da hankalinki don Allah"......
Lellekawa tayi taga babu kowa ah dakin sannan tace nasan Mai Martaba zaiyi raising maganar nan kada yarinyar nan tatona min asiri........
Zama Zaliha tayi sannan tace kinada tabbacin ba Laure bace taje tafada tunda kince agabanta kikayi waya don ni nafi suspecting dinta cikin sauri Magajiya tace"ba Laure bace ba don da itane tun jiya za a anbaci sunana kuma naji Mai Martaba yace gani tayi ko ana waya ah waje ko magana ne nigaskiya namanta but I'm certain sure ba Laure baceba"........
Okay then I'll find out koma wayene but promise me one thing Mama baxaki sake yunkurin kashe waniba sabida son Sulaiman yahau sarauta it might be a problem for you... Magajiya ce tace nasani shiyasa inba kasheshin mukayiba burinmu bazai taba cikaba.......

                              

Cikeda lallashi Zaliha tace kada kice haka Mama, I'm here for you babu kisa babu jima wani ciwo I assure you zamuyi achieving goal dinmu yanzudai mu tabbatar komai yatafi daidai zanje insa anemo min baiwar Matar can din I'll ask her zanji koma wani information ne daga gareta...........
Gyada kai Magajiyan tayi nervously yayinda Zalihan tafice cikin sauri............
Bayan la'asar Mai Martaba yasa aka tara kowa nacikin masarautar dukda kuwa Almustapha bayanan duban Hajiya Muniba yayi sannan yace Ina baiwar take?..........
Duban Surayya tayi sannan tace"tashi kije Surayya"......

                              

Nervously yarinyar tatashi tayi gaban Mai Martaba dukar dakanta kasa tayi tana mikamai gaisuwa ansawa yayi sannan yace fadamin waye kika gani yana waya acan bayan masarauta?.........

                              

Fans karkuso kuga fuskar mutumiyarkuanbi anrude#Madam M#

                              

Sunkuyar dakanta kasa tayi sannan tace"Allah yajada tsawon kwana mahaifina nadaya daga cikin masu kula da gonar Hajiya Muniba dake cikin masarautar nan to jiya sunyi aiki dasafe yamanta fartanyarsa agurin shine yace innagama aikina dawuri inje in daukemasa to sanda naje daukarne naga wata Mata tana bama wani kudi gabadaya jikinta arufe yake dawani katuwar bargo marar nauyi haka mutumin ma fuskarsa rufe shiyasa bansamu nagansuba don buya ma nayi shine harnasamu naji abunda suke fada wai yatabbatar yakira ah waya yasaka ansace tayar motar Almustapha shine hankalina yatashi narasa abunyi shiyasa nazo nasamu Hajiya Muniba nafada mata.......

                              

Galadima ne yace bawani karya takeyi babu yanda za ayi kice bakiga fuskar ba kode wani yahanaki fada ne?......
Kamar Surayya zata saki kuka tace wallahi iyakacin abunda nasani kenan yallabai....
Sarkin duka ne yace rankashi dade abani dama inhukuntata tukunnan kilan zata fadi gaskiya.........

                              

Girgiza kai Mai Martaba yayi sannan yace"bazan hukunta yarinya haka kawai ba tare da tayi laifi ba bazata taba fitowa hartayi magana ba,inyau bataga fuskar su ba inshallah wataran asirinsu zai tonu bazan dauki alhakinta akan abunda bata saniba sannan innayi haka kenan nangaba in rayuwarmu nacikin hadari koda bayin sunsani suna iya kinzuwa sufada sabida ana iyahukuntasu....
Duban Surayya Mai Martaba yayi sannan yace" jeki abunki".....
Godiya yarinyar tayi sannan takoma mazauninta dan murmushi Hajiya Muniba tayi tareda shafa kan Surayyan tana tuna yanda tayi convincing dinta takuma fada mata abunda zata fadawa duk wanda yatambayeta.......

                                              

                        

Hakanan bata manta zuwa datayi tasameta tace Zaliha tayi kiranta ba kuma koda tadawo seda tafada mata yanda sukayi yanzu abu daya takeson tafara ganowa shin bakin Magajiya da Zaliha dayane ko Yaya?....
Tunda ah iya saninta Zaliha is nice kuma akwaita da ladabi dubada yanda matan manyan fada ke fada.......

Waziri cikeda damuwa yadubi Mai Martaba bayan ansallami Surayyan yace"Amma dai yanzu yakamata asake sama Almustapha matakan tsaro kuma yarage fita tunda rayuwarshi nacikin hadari".....

Murmushi Mai Martaba yayi sannan yace maganarka gaskiyace waziri zansa asake samishi matakan tsaro amma maganar yarage fita baitaso ba tunda shi ne zaizama sarki nangaba inbaifita yaga matsalolin mutanensa ba tayaya zaiyi musu solving diinsu?..
kuma amatsayinshi na leader baikamata yazama yana jabayaba inyana tsoron rasa nasa rayuwar sabida silly things like that tayaya zai tsare nashi Al ummar?...
Gyadakai sukayi dukansu cikeda gamsuwa gameda abunda Mai Martaban yace........
Dismissing taron yayi bayan ya jaddada ma dogaraye dole sudinga duty dinsu squarely yanzu sannan yace yanason ayi torogh bincike da taimakon Surayya ko Allah zaisa asamu kayan da taga mutanen dashi by doing that may be asamu munafukan.........

Tunda sukabar fadan tayi shiru gabadaya tayi zurfi acikin tunani harsuka isa bangarenta kallonta Zaliha tayi sannan tace Mama lafiya naga you're so tensed?.......
Zama Magajiya tayi tana mammatsa hannunta sannan tadago tana kallon Zaliha....
"Zaliha I'm wondering why yarinyar can tayi karya bayan nasan tunda nafara maganar akashe Almustapha banhadu da wani ah waje ba yawanci ta waya muke magana da Matawalle kuma kinga cewa tayi nace akira ace a sace tayar mota and the truth is munjima da planing haka da Matawalle and wayama ah daki mukayishi"......
Shiru Zaliha tayi kafin tace.
"does that means the girl is hiding something?"....
"Sure, I'm very sure she's hiding something may be tasan gaskiya amma taboye taki fadan gaskiyar"....

Cikeda curiosity Zaliha tace....
"to meyesa zatayi hakan?".....
Jisukayi daga bakin kofa ance...
"to kukunsan wanda yayi aika aikan ne?"
Dasauri suka juya atare suna kallon mai maganar.....
Takawa Hajiya Muniba tashigayi ahankali harta iso gaban Magajiyan tana mata questioning look bakaramin rudewa Magajiya tayiba don  gani takeyi kamar Hajiya Muniban taji mesuke fada.........
Cikeda rudani tace...
"mekikazoyi ah bangarena?"....
Yar dariya Hajiya Muniba tayi sannan tace...
"banida right din zuwa ganin the whole Magajiya ne innayi niya?".....
Harara Magajiya tabita dashi kayataccen murmushi Hajiya Muniba tayi sannan tace"nice nasa Surayya tayima Mai Martaba karya sabida nafison Mai Martaban dakanshi yakama culprit din sabida kada ma meshi yasamu ko tasamu bakin depending din kanta,I know who ever it might be must be so cunning and intelligent hakanan nima kuma bazan bari asaka mijina cikin rudaniba ko ya kika gani?"tayiwa Magajiya maganarta tanasauke idanunta kanta........

Kinsan wanda yayi abun ne ke?...
Magajiya tayi maganar hankali tashe....

Murmushi Hajiya Muniba tayi sannan tace"banida wannan amsar tukunnan randa asirin maishi yatonu zakiji ah bakin Mai Martaba",sannan tajuya zata fita hartakai bakin kofa sekuma tayi saurin dawowa"and yes muhimmin abunda yakawoni shine intuna miki cewa duk abunda mutum yasa Allah aciki no matter how motives din makiyi yake bazai taba succeeding ba kamar jiya I told you Yarima will be home safe and sound  dayardar Allah to gashi kinga yazo gida lafiya alhamdulillah".......
Daganan tajuya tayi ficewarta,zama magajiya tayi zuciyarta na wani irin racing ahankali Zaliha tace kikwantar da hankalinki ninasan batajiba and I'm sure batasan wayebane behind this......
Cikeda damuwa Magajiya tace"Anya Zaliha?"....
Kamanfa tasani,batasaniba Zaliha tayi maganar encouragingly sannan tacigaba da bata baki har hankalin Magajiyan yadan kwanta...............

Dubanta tayi sannan tace kinyima Mai Martaba maganar household din?.....
Murmushin karfin hali tayi sannan tace nayi mishi and nasan zeyi tunani akai kuma duk tunanin shi dai bazai wuce yazabe kiba tunda you're the eldest Daughter in-law sannan kin girmi wancan tsinanniyar kinga koma miyene mulkin bayi na hannunmu kafin musamu mu kwato wancan dinma....

                

                        

Cikeda jin dadi Zaliha tace nagode Mama, murmushi Magajiya tayi tana inama Sulaiman mai tunani irinki ne danaji dadi ah rayuwana he's just so different duk acikin Ya'ya na bayataba bin magana na abunna matukar damuna.....

Cikeda tausayinta Zaliha tace he'll,zedawo gareki Mama I promise you that...
Murmushi Magajiya tayi tana dan sosa jikinta"I hope so"........

****
Tana tafiya tana tunani aranta don tabbas taso ace asirin wanda yayi niyar kashe mata Almustapha yatonu sede Allah beyi asirinsu zai tonu yau ba but one thing she's very sure of zatayi iya bakin kokarinta gurin gano koma wanene is behind all this dawannan tunanin ne takarasa bangarensu tundaga bakin kofa takejin surutu ah parlour wannan yabata clue cewa su Sumayya sun iso......
Aikuwa tana shiga parlourn dagudu Sumayya tayo kanta tareda rungumeta tana...
"Amaryar Yayanmu I missed you so much"......
Rungumeta tayi Itama"Nima nayi kewarki Sumayya infact I'm angry with you ko sallama babu kikayi tafiyarki"....
Sakinta Sumayya tayi tareda dan kama both kunnuwanta...
"I'm sorry Sister in-law"......
Murmushi Asma'u tayi sannan tace"nahakura tunda gashi kindawo garemu,how was your journey"..........

Alhamdulillah and you yagida,yakowa da kowa hope you're taking good care of my Brother?.....
Dariya Asma'u tayi tanadan girgiza kai...
"Sumayya you'll never change,surutun nan dai nanan"......

Haka suka zauna sunatashan hira da alama basusan meyafaru jiyan ba Itama kuma bata fada musuba tunda bawai wani good news baneba on top of that bata shirya tarban tsokanarsuba,se yanma tatashi tafice da Ummi zuwa lambu as usual koda suka dawo ana kiran maghrib leka dakin Almustapha tayi bayanan don haka tawuce kitchen tasamu anzuba mai abincinsu dauka tayi takai parlour don batason haduwa dashi kwata kwata don haryanzu kunyarshi takeji hakanan kuma takasa zuwa gaisheda Mom yauma haka su Mai Martaban ma to ma intaje dawani idon zata kallesu bayan abunda tayi jiyan shine abubuwan dake yawo ah kwanyarta......

Dakinta tawuce tayi sallah ba'ita tafito ba seda tayi sallar isha'i shima seda ta leko taga Almustaphan baya parlour sannan tashiga su Sumayya tasamu Sumayya nata mita wai miyasa ba a kunna Tv newai ah gidan nan......
Dariya Asma'u tayi sannan tace to ki kunna mana bagaki ga TVn ba......
Afiya ne tace ahto nimadai abunda nagani kenan babu wanda yarike hannunki fa mukawai kallon ne bamwasonyin anan baswa Korean films and that's my favorite..........
Kunna TV  din Sumayya tayi sannan tadauki remote takoma mazauninta tana caccanza chanels hartakai ZeeTv murmushi tayi sannan tace that's perfect ashema har Asian package ake biya amma kukayita bari kudin Abba natafiya ah banza.....
Tabe baki Amira tayi tana nidai don Allah ki aramin laptop dinki inkarasa kallon *Moon lovers* dinnan wallahi yahadu Korean film din inason Inga yaza akare.......
Dariya Sumayya tayi "zanbaki kikalla kodan kizubda hawaye kamar yanda nazubar ammadai mukalli *Qubool hai*,dinnan shima yahadu you'll start to like Indian series inkika gawannan".......
Cikeda jin dadi Amira tace thanks darling Sis shiyasa nikeson ki wallahi.......

Haka sukasa aka kawo musu abinci suka shiga ci hankali kwance sunaci har Sulaiman yashigo Asma'u kuwa tunda taji anataba kofa tayi saurin tashi tashige cikin dakinta don duk ahtunaninta tareda Almustapha Sulaiman din yashigo".....

Aikuwa tanashiga dakin sega call din Ummi yashigo cikeda jin dadi tadaga tana...
"Ummi na nayi kewarki"..........
Murmushi Ummi tayi daga daya bangaren kafin tace...
"Me too dear ya gidan hope everything is going well over there?".....
Dan shiru tayi tanadan tunani yayinda idanunta suka ciko da kwallah kafin ahankali tace"everything is fine Ummi and they're all nice".....
Murmushin dayafi kuka ciwo Ummi tayi because from her Daughters voice take gane damuwarta, ahankali tace "komai na duniyar nan hakuri akeyi Asma'u bakomai kakeso kake samu ba at that right instant you must be patient sannan kidinga addu'a babu ruwanki dashiga abunda bai shafekiba as you know *GIDAN SARAUTA* ba gurine damutum zaita zuba babu control ba,sannan kibi mijinki sauda kafa kimishi biyayya kinji".....
Gyada kai Asma'u tayi kamar wanda tana gaban Ummin ne haka tacigaba dabata shawarari kafin sukayi sallama kan kacemai har bacci yayi awun gaba da Asma'u.........

Around 12:00am yashigo gidan abuge gabadaya yagaji dakyar ma yake tafiya tangal tangal kamar zai fadi babu inda zuciyar shi keson kaishi irin gurin Ummin shi ahankali yacigaba da tafiya harya isa dakinta...........
Wutan dakin akunne sannan su Jamila baswa ciki itakadai ce kwance idanunta lumshe da alama ma bacci takeyi karasawa yayi bakin gadon yazauna gabanta yana kallon fuskar ta sa hannu yayi ahankali yana taba temperature na jikinta kafin idanunshi suka ciko da kwallah kaman bashine yashigo yana bugeba sa hannunta yayi cikin nashi sannan yace"Ummi I need you,kitashi hakanan kiyi magana please i need to hear your voice inason inji kinrungumeni cikin jikin ki kaman yanda kikeyi abaya"........
Dan sake tabata yayi kamar mejin tsoro sannan cikin murya me girgiza yace"let me be blessed in that way before i leave this world, Ummina they're after my life sunason rabani dake,sunason haramtamin sake jin dadin uwa don Allah kitashi,prove them wrong fulfil my dreams Ummi",yakarashe maganar wannan Karan kuka yakeyi kaman rashi zai fita sake damke hannunta yayi cikin nashi yana"I'm a good child,I never disrespect you Ummi bansan mena musuba hakanan bansan memuka tare musuba Ummi, they're after my life Ummi, they're...af...ter..my life yadinga maimaita maganar muryarshi na cracking"

Ummi dakejin kukan Dan nata harcikin ranta batasan sanda tabude idanunta ba daman ba bacci takeyiba kawai idanunne ta lumshe su tanajin yanda yake kuka ajikinta hakanan tanajin yanda hawayenshi ke ratsa jikinta Itama batasan sanda hawayen suka fara bin kuncinta ba hakanan batasan ya akayiba sesamun kanta tayi da daga dayan hannunta tadorasu kan Almustapha din tanashafawa ahankali cikin sigar lallashi hakanan batasan ya akayi bakinta yashiga furta"Hassanan ya walaad,laa tabkee, ana huuna amamaka.Ummi huuna maaka, satakuna alaa ma yaaraam insha Allah.(it's okay Son,stop crying I'm here Imam,Ummi is with you)"..........
Komai nashi tsayawa yayi cak lokaci guda yayinda yadago ahankali....                      

Tareda duban direction din da Ummin take don ah iya saninshi wannan muryar Ummi ne,muryar dayajima yana begen ji muryar datafi kowani murya yimasa dadi and on top of that she's the only one datake kiranshi da *Imam* se sometimes Mai Martaba............

                      

Yunkurin tashi yayi amma yakasa sabida wani irin lulu da kanshi keyi mishi besan ya akayiba se samun kanshi dayayi yakwanta ajikin hannunta nan take wani nannauyan bacci yayi awun gaba dashi tsabar giyan dayasha din tafara masa aiki...........
Ummi batadaina shafa kan nashiba cikeda so da kaunar Dan nata hakanan bata daina zubda kwalla ba batasan dawani bakin zatayiwa Allah godiya ba dayabata ikon daga hannunta harta iya lallashin Danta bayan shekaru masu yawa haka,hakanan batasan da bakin dazata gode mishi ba daya bata ikon yin magana bayan shekaru masu dama yanda taga rana haka taga dare don ko kadan batajin zata iya rufe idanunta don gani take inta yi bacci tatashi all that happened will turn out to be a dream dukda tayi attempting tashi dakanta harwajen sau uku amma takasa.......
Wujajen karfe biyar da rabi na asuba Jamila tashigo dakin Ummin don taimaka mata tayi sallah tunda taji su Amira na complain Almustapha bekwana gida ba don koda suka fito karatu bayanan dakinsu suka koma.......
Bakaramin mamakine yakama Jamila ba ganin Almustapha datayi kwance gefen Ummin dukawa tayi tana shirin tashin shi amma setaji zuciyar ta tashiga bugu sakamakon warin giya dataji innalillahi wainna ilaihir rajiun shine abunda tadinga maimaitawa aranta tareda addu'ar Allah yasa Ummin bataji warinba donkuwa tasani tabbas hankalinta zaitashi dukda ba iya magana zatayiba bare motsi itakuwa duk abunda zai tada hankalin Ummin baso takeba gashi tausayin uwar dakin nasu takeji sosai akullum tayi sallar bata manta sanya baiwar Allahn cikin addu'ar ta sabida ita mutum ce meshiga rai......
Kiran sunan Almustaphan tashigayi ahankali jitayi yayi motsi kadan kara kiran sunan nashi tayi wannan karan bude idanunshi yayi yadaurasu kanta......
Hamdala tayi aranta sannan tace lokacin sallah harya wuce.....
Almustapha dakanshi ke sarawa kadan kadan yatashi dakyar yafice zuwa dakinshi direct bandaki yawuce donyin alwala don ganin yanda gari yafara haske yasan an idar da sallah ah masallaci and on top of that ma kanshi ciwo yake mishi wanda baisan dalili ba.........
Alwala yashigayi harya idar sannan yadubi mirror din dake bandakin yana diban ruwa kadan yana watsama kanshi at thesame time kuma yana kallon kanshi acikin madubin soyake kanshi yadaina sarawa gashi jiyake kaman wani abu yafaru last night"something very special"daya kasa tunawa.......

                      

Dafe kanshi yayi yanason tunawa amma yakasa giving up yayi sannan yafara takawa don barin bathroom din atake kuma yafara tuno Ummi dayanda ta taba shi hartamayi mashi magana.......
Sa hannu yayi yadan taba kanshi yana shafawa kaman yanda Ummin tayi jiya kaman wanda zesamu clue agurin........
Fita yayi yashimfida sallaya yatada sallah seda ya idar sannan yafice zuwa dakin Ummin donkuwa ko addu'a betsaya yayiba yaudin samun Jamila yayi zaune gefen Ummin tana bata ruwa tanasha don shine abunda suke bata first thing in the morning kullum........
Cikin sauri yakaraso cikin dakin ganin yanda Ummin ke kallonshi babu ko kiftawa zama yayi gabanta cikeda rudani yace....
"Ummi na,you said something yesterday kinmin magana ko?"......
Yakarashe maganar yayinda hawayen farin ciki suka fara ziraro mishi tunkan yasamu ansa daga gareta........
"Talk to me Ummi I'm yearning to hear your voice again please!",yakarashe maganar tareda sa hannunshi cikin nata yana dan mammatsawa soothingly..........

                      

Jamila ne tace"Anya Yarima Ummi ce tayi magana kuwa ? Kodai mafarki kayine?"takarashe maganar tana kallonshi don aganinta giyan dayasha ne yasashi yin tunani haka..........
Ko kallon Iya Jamila beyiba sema rokon Ummin dayakeyi tayi magana please ganin yanda Dan nata yadamu yasa ta daga hannunta ah hankali takai fuskarshi tareda sa thumb dinta tana goge masa kwalla Itama hawayen takeyi rungume hannunnata yayi like his life depend on it"I miss your voice Ummi,say something please".....
Murmushin dayafi kuka ciwo Ummi tayi sannan tace...
"and i miss talking to my little Imam"......
Wannan karan Almustapha rasa inda zaisa kansa yayi tsabar farinciki hakanan hawaye basu daina ambaliya ah fuskarsa ba dan sakin hannunnata yayi cikeda so sannan yayi kissing dinsu kafin yarungumeta......
"I'm so very happy Ummina,bakina bazai iya furta how happy I'm right now ba muryarshi na cracking yace"Ummi",i'm feeling like I'm the most happiest Son on earth right now,i love you Ummina"yakarashe maganar tareda dagowa yayi kissing forehead dinta sannan yasake komawa cikin jikinta......
Murmushi tayi tana dan tapping bayanshi ahankali cikin sigar lallashi
"i love you more Son"...........

                                      

                        

Jamila dake gefe ko motsi takasayi tsabar mamaki se Hindatu ne datashigo taji Ummin na magana yasata kasa yin murnar ita kadai sujudu shukur tayi sannan tafice cikin sauri tayi dakinsu Afiya tana "Oh ni Hindatu bantaba ganin safiyar datafimin kowanne ba irin nayau kufito don Allah,kufito kuzo kuga baiwar da Allah yayi mana yau da sanyin safiyar nan",takarashe maganar tanayimasu Afiya alama da hannu kan suzo don daman basu koma bacci ba......

Kallon Afiya Amira tayi irin meya farun nan....
Turo baki Amira tayi tana"yaza ayi insani sede kitashi muje mugani don iya Jamila inba important magana baneba bazama tazoba Amira takarashe maganar tareda tashi tafice bin bayanta Afiya tayi lokacin kuma Jamila da Asma'u suka bullo daga hanyar dakin Asmau din bakin Jamila dai yaki rufuwa kamar wanda aka bata gonar auduga dakin Ummi tayi suka bi bayanta har suka shiga ganin Almustapha na jikin Ummin dukansu biyun nakuka gakuma Ummi se tapping bayan Almustaphan take in a comforting manner yasa su Afiya mutuwar tsaye...........
Jin Ummi tace"it's okay kadaina kuka please"yanda take maganar ahankali zakagane cewa she's not that okay because muryartama bawai yana fita sosai baneba.....

Wani irin ihun murna Afiya tayi "Ummin mu"kafin taruga aguje zuwa jikin gadon tarungumeta haka Amiran ma dukansu se kuka ba bakin magana..........
Wanda suke tsaye suna kallonsu ma tayasu hawayen tausayi da murnar sukeyi sunfi minti goma ahaka kafin dakyar Almustapha yadan ja da baya yana kallon Ummin sannan yashiga goge mata hawayenta"Ummi babu inda yake miki ciwo",yayi maganar ahankali murmushi tayi tana bin ya'yan nata da kallo cikeda so da kauna sannan tace"I'm okay"......
Afiya ne tace hartafiya zaki iyayi Ummi?......
Dan shiru Ummi tayi kafin tajijiga mata kai alamar aa cikeda damuwa Amira tace dayardar Allah Ummi tafiyar ma zakizo kifara yinta kwana kusa..........

Amsawa sukayi da Amin baki dayansu dubansu Jamila da Hindatu tayi cikeda sonsu suma don bata taba ganin mutane masu amana irinsuba they're always loyal to her and she'll never forget that........
Dakyar Hindatu ta'iya cewa namiki murna Aunty ya jikin naki.......
Murmushin dayafi kuka ciwo Ummi tayi sannan tace"dasauki Jamila,nagode kwarai da kaunarku gareni infact bansan tayaya zangode muku inji dadi arainaba", takarashe maganar wani hawayen nazuba.......
Jijjiga mata kai Jamila tayi Itama tana matsar kwallah"don Allah kidaina samu jin kunya yakamata kihuta hakanan kada jikin ki yayi ciwo",Jamila takarashe maganar tareda zummar tashi ta taimaka mata ta kwanta sede ta lura Ummin se kallon bakin kofa takeyi.........
Kai direction dinta tayi bakin kofar itama"Asma'u ce rakube jikin kofa kaman zata shige cikinta se murmushi takeyi at thesame time kuma tana goge kwallarta"she's just so happy jin muryar Ummi datayi hakanan she's just so happy seeing them all happy like this sehakan yatuna mata da nasu gidan gidan iyayenta......
Dagowa tayi ahankali sekuma idanunta suka sauka cikin na Ummin cikin sauri tasauke kanta kasa cikeda kunya sannan tashiga wasa da fingers dinta........
Murmushi Ummi tayi sannan tace...
"Habibty come here"....
Dagowa Asma'u tayi ahankali tana kallon Ummi irin tanason ta tabbatar da'itan ake magana koba da itaba........
Gyada mata kai Ummi tayi tareda karacewa"zo abinki kinji".....

Takawa tashigayi ahankali harta isa gun Ummin ta tsuguna sabida gabadaya kasa tsayuwa kansu tayi ga kunyar Ummi da Almustapha da takeji shikuma se kallonta yakeyi fuskarshi daukeda murmushi........
Kamo hannunta Ummi tayi sannan tace..
"tashi zauna gefena"......
Cikin Yar siririyar muryarta tace...
"Nan ma yayi"...
Yar karamar dariya Ummi tayi wanda dakyar ma yafito tace"yau kunya na kikeji?"......
Still kanta nakasa ta jijjiga kanta alamar aa......
Sake riko hannunta Ummi tayi sannan tace"to tashi kizauna"......
Babu yanda ta'iya haka tatashi tazauna gefen Ummi gashi tana daf da Almustapha gabadaya she's feeling uncomfortable sa hannu Ummi tayi tareda dago fuskarta sannan tace"you're a very beautiful girl with a very beautiful heart".......
Itadai Asma'u sakeyin kasa dakanta tayi tana smilling Ummi ne takuma cewa "kinjima kina son jin nayi magana amma yau gashi bakin nawa yabudu kinkasa cemin komai this's not fair you know?"....
Babu abunda Asma'u ta'iya cewa sai"sorry".......
Ummi na niyar magana Almustapha yace"you should rest now Ummi kada jikinki yayi ciwo"......
Dukda she has alot to say seta samu kanta da gyada ma Dan nata kai gyara zaman shi yayi tareda kwantar dakan Ummin akan cinyarshi yana murmushi dan satan kallon shi Asma'u tayi"he look so very happy wanda hakan yakara ma fuskarshi kyau sosai",tashi tayi ahankali sannan tafice don gani take they need some space itada yaranta it's been long dasukayi magana......

                

                        

Kitchen tawuce tasamu jamila zasu fara aiki gabadayansu suna cikin farin ciki.......
Murmushi Asma'u tayi sannan tace...
"yau mun makara kaman".......
Wallahi fa cewar Jamila kafin Asma'un tace miye favorite food din Ummi inason inyi matada kaina.......

Dan shiru Jamila tayi kafin tace"Ae Auntyn ne meyema batason cine don ita agaskiya kafin ayi abinci kaji tayi complain dawuya komai ci take sede na lura tanason Gurasarsu na chadi chadin nan dakuma pepper soup din kayan ciki...........
Turo baki Asma'u tayi"to ae ban san ya akeyinsaba Iya Jamila"......
Dariya Jamila tayi sannan tace...
"Kai Gimbiya miye abun tada hankalin basai ingwada miki yanda akeyi dinba"......
Dan murmushi Asma'u tayi sannan tace"to nagode",nan Jamila tafara ciro ingredients suka shiga kwabawa kafin suka koma kan pepper soup dinma nan Asma'u tace itakadai takeson tahada murmushi iya Jamila tayi sannan tace"to Gimbiya"......

Cikin awa daya da rabi angama kammala abincin duka gidan baki daya haka na Ummin ma sannan aka zuzzuba duban Rukayya Asma'u tayi sannan tace"dauki abincin Ummin nan kikai dakinta"......
To Gimbiya.Hindatu ne tace dakin kai din dakanki zefi jijjiga mata kai tayi alamar aa kafin tasake duban Rukayya"kikai kawai".......
Haka Rukayya tafice da abincin wucewa daki Asma'u tayi tayi wanka sannan tayi shirinta cikin simple gown na material dakin Almustapha tawuce straight because she's very sure yana tareda Ummi dagashi har su Afiyan haka su Sumayya da Sulaiman ma duk sun shigo haka Mom ma se murna akeyi itakuma takasa shiga cikinsu kwata kwata don gani take she does not belong there aranta kuwa tana inama Mai Martaba is in his right senses inama zai iya tuna Ummi datasan babu wanda zaikaishi farin ciki yau sede Allah baiyiba and tanaji ajikinta yanzu Ummi tafara samun lafiya to inshallah Dad din ma will remember his wife one day one time dawannan tunanin ne tashiga kallon dakin it's very neat and tidy dukda haka seta shiga sake gyarawa harma da canza bedsheet bayan tagama sharar dakin tas sannan tasaka turaren wuta ga room freshner medan karen dadi data saka kankace me dakin yasake bada wani scent medan karen dadi..........
Murmushi tasaki sannan tajuya don fita ah dakin abakin kofa sukayi karo dagowa yayi cikin sauri yana kare mata kallo jitayi zuciyar ta tashiga dukan uku uku lokaci guda sunkuyar dakanta tayi dasauri tana shirin rabawa ta gefenshi tawuce yayi saurin riko hannunta da soft hand dinshi............

Juyowa tayi dasauri tana kallonshi murmushi yasakar mata wanda bakaramin tafiya da imaninta yayiba sannan yadan kalli dakin nashi kafin yakara maido da kanshi kanta cikin soft and cool voice dinshi yace..
"Thanks"
Kasa dagowa tayi takalle shi sabida ynda bugun zuciyarta ke karuwa ga kunyarshi da takeji hakanan batasan sanda muryarta tafurta "for what?"...........
Directly yace...
"for cleaning my room"...
Bakaramin mamaki ne yakamata ba dagowa tayi tanason ta tabbatar shin Almustapha ne kobashi ba amma seta sake arba dawannan Smilling face din nashi mai tsada da bata taba ganiba saiyau dayakema Ummi don wannan smile din nadaban ne because one look tayi mishi tagane daga bottom of his heart yazo......
Cikin sauri tacire hannunta cikin nashi sabida wasu sabbin al amari datakeji kafin tajuya tafice aguje......

Yana nan tsaye harta bace mai dagani kafin yakarasa cikin dakin don shirin yin wanka..........
Bangaren Asma'u kuwa koda takoma daki bakin gado tazauna tana sauke ajiyar zucuya
"what does that mean, Almustapha namata murmushi yau?"duk tunanin duniya tayi amna takasa figuring komai out she's just out of words it seems like a dream to her duk lumshe idon dazatayi Smilling face dinshi take gani ahaka har Sumayya tashigo dakin tana"Sister in-law  Yaya Almustapha yafara saki yin kulle ne?".....
Dariya Asma'u tayi dukda baikai har zuciba sannan tace"wai yaushe kika iya hausa harma kikasan wayannan kalaman"......

Zama gefenta Sumayya tayi tana"kina wasa dani se ma inkaiki inbaro ki indai ah yaren hausa ne, I'm so fund of the language tun Ina karama sabida naji ance shine yaren arewancin nigeria koda yaushe and Dad ma yanayimin sosai Mom ma kuma ta'iya so kinga bayanda za ayi bazan iyayiba dukdama mostly turanci mukeyi acan din"........

                

                        

Wasa da kafa Asma'u tafarayi tana gaba dashi tana baya sannan tace"yafi miki ai gashi yanzu basai kinsha wahalar koyaba'".....
Dariya Sumayya tayi tana"yes, it's true but Yaya Sulaiman yasani agaba yanason hanani sa outfit din danasaba sawa acan I don't know what's his problem with me dukdama nace mishi bazamu sake fada ba but dawowana dinnan daga jiya nafara gajiya da lecturing dina dayakeyi"....
Murmushi Asma'u tayi tana kallon Sumayyan yanda taketa mita itakadai akan Sulaiman seda tayi shiru sannan tace"to ke miyasa bazaki daina sa wayan can kayan dinba tunda kinga anan bashine usual dress damuke sawaba infact kabilunmu akasani dasaka irin wayannan kayan".....
Tashi Sumayya tayi tana batarai"to kema Yaya Sulaiman din kika koma Sister Inlaw?"...
Takarashe maganar tanadan tura baki riko hannunta Asma'u tayi"dawo kizauna shawarace fa Sumayya"....

Kai tsaye Sumayyan tace "to banaso nagadai inzan fita yanzu bancika sa wayancan dinba acikin gidane kawai shima se in Yaya Almustapha bayanan don banason wannan hararar nashi me yawan shirin sani fitsari ah wando"......
Dariya Asma'u tayi sosai sannan tace"bazan sake ba to yi hakuri kizauna".....
Tanason Sumayya sosai because she's so funny and free duksanda tazauna dakai setasamu yanda tayi tasaka dariya......
Dakyar tabama Sumayyan hakuri sannan tazauna nan suka cigaba da hira abunsu har aka kira sallar azahar nan suka tashi sukayi sallar tare kafin Sumayyan tafice don komawa bangarensu tasan by now Mom takoma and batason barinta ita kadai.............
Asma'u abakin su Afiya takejin Dad da Almustapha sunyi deciding za akai Ummi hospital sabida suduba jikinta sukuma ga ga improvement da akasamu ah jikinta may be sunada wani advice dazasu bayar or any suggestion aranta taji dadi donkuwa shawara ne mekyau..........

Bayan la'asar Sulaiman da Daddy suka shigo tareda babban Malamin da Sulaiman yace zai kawo iso yayi mishi ah parlour sannan yashigo yana kiran Almustapha dake dakin Ummi don yau manne mata sukayi gabadaya shikam yaki fita koina ma...........
To Almustapha din yace kafin Sulaiman yace "yace afito da Ummin yanason ganinta"......
Gyada mishi kai Almustapha yayi tareda tashi shida Amira suka tamaika mata tazauna akan wheel chair din kafin suka fice zuwa parlourn Asma'u dake kitchen suna aikin dinner Sulaiman yashigo yana akwae bako akawo masa kayan motsa baki sannan yadubi Asma'u yace Sis kizo don Allah......
Tsame hannunta tayi daga ruwan wanke shikafar ta wanke hannun da clean ruwa sannan tabi bayanshi har zuwa parlourn zama yayi hakanan Itama tasamu guri tazauna can gefe tareda gaishe da mutumin ........

Ansawa yayi kafin yadubi Ummi dake kan wheel chair yatambayeta ya jiki amsawa tayi da dasauki sannan Sulaiman yace "Mallam itace wanda nayimaka bayani kwanaki harkake bamu ruwan dazatana sha to alhamdulillahi yau seta tashi Allah yanufeta dayin magana sannan tana iya motsa hannunta sede tafiya ne da tashi daga kwance bata iyawa se an taimaka mata".........
Masha Allah cewar Mallamin sannan yace wannan ma wani baiwane daga Allah alhamdulillah domin ni yanda kafadamin condition dinta banyi tunanin za asamu improvement kwana kusaba dubada yanda kukayi sakaci da addu'a tun baya bayan kunsan cewa sihiri ne sede kuma  alhamdulillah babu abunda yafi Allah hakanan babu abunda ya gagaresa semu gode mishi da hakan......
Gyada kai sukayi duka suna furta alhamdulillah kafin Mallamin yace Hajiya ruwan da nake baki na addu'o'i kikesha yanzunma bazaki daina shaba zaki cigaba da Sha sabida shima wani tsarine dazai taimaka sannan yana karya sihiri sosai da ikon ubangiji se acigaba da addu'a duban Sulaiman yayi sannan yace batun rashin tafiyarta da tashinta kuma wannan bazance komaiba kasan komai da hakuri ake samunshi mucigaba da addu'a insha Allah with time dayardar Allah kuma zamuzo muga tafara tafiyar dakanta don inaaganin sihirin ne be ida karyewaba.........
"Mungode to Mallam amma da muna tunanin kaita asibiti taga likita ne",wannan karan Dad ne yayi magana.........

Gyaran murya Malamin yayi sannan yace"wannan ma shawara mekyau ne kujedin kuyi masu bayani in akwai abunda zasu iya zasuyi",canza magana Malamin yayi da "ya maganar Mai Martaban kuma kasan innatafi kuma kara zuwana zaiyi wuya gaskiya kasanni I'm a very Busy Man".......
Duban Dad Sulaiman yayi yayinda Dad din yace"Sulaiman din yayimaka bayanin komai ko?"......
Gyada kai Malamin yayi sannan yace yamin sede tun alokacin nace masa babu abunda zan iya bashi sede intayashi da addu'a don irin mutane kamar Mai Martaba anamusu sihiri mekarfine inkuma yakamasu kafin ashawo kan abun da wahala gashi kuma kunyi wasa da addu'a shidinma bamusaniba koyanayi ko bayayi amma dai baza ace komaiba indai mukacigaba da addu'a ah wurin mu kuma kudinga tayashi anan tunda babu abunda ya gagari Allah ae dayardarsa kuma zewarke yatuna komai sede daso samune asamu ah karya sihirin tahanyar sanin mesukayi zefi sede hakan dakamar wuya ko?.....
Gyada kai Dad yayi sannan yace mudai kutayamu da addu'a kawai muma zamu tayashin daman matsalar ai yanzu narashin tuna matarshi dayayine dakuma kinyarda da'ita dayayi wanda munada tabbacin daace yanacikin right sense dinshi bazai taba zargintaba kuma ni inaji ajikina insha Allah komai yakusa zuwa karshe........
Murmushi Malamin yayi sannan yace inshallahu rabbi haka suka yi addu'a sannan Sulaiman da Dad  suka fita raka Malamin shidai Almustapha yanazaune gefen Ummi his genuine problem is Ummi tayi recovering gabadaya tunda tanadasu he's sure bazata wanidamu da Abba ba dukda yasan tanason mahaifin nashi sosai sede me shima Abban yariga yayi auri better wife yanzu and from a mare look yasan yanajin dadin zamada sabuwar matar tasa....

Asma'u dake can gefe tanazaune har sukafice sannan tatashi sumui sumui tawuce su Afiya zatafice ah parlourn Ummi tace "Habibty"......
Juyowa Asma'u tayi kanta akasa tanadan murmushi tace"na'am",cikeda kunya don tarasa dalilin dayasa Matar ke kiranta da wannan sunan haka.......
Karasawa tayi gaban Ummin sannan ta tsuguna she can feel yanda idanun Almustapha kekanta........
Murmushi Ummi tayi sannan tace...
"yau bazamu je lambu bane?"..
cikin yar karamar murya Asma'u tace"inkinaso zamuje Ummi"......

"I want to spend sometime with you Dear muje kinji".....
Gyada mata kai tayi ahankali sannan tatashi tana shirin tura wheelchair din Ummi ne tadubi Almustapha tace "join us Imam"......
Ware idanu yayi yana kallonta gyada mishi kai tayi ahankali tareda sakar mishi murmushi........

Bazai iyacema Ummi no ba most especially on this special day of his life don haka yatashi yabi bayansu.....
                              

Tura wheelchair din Asma'u tadingayi har suka isa lambun samun spot tayi karkashin wata bishiyar gwava ta tsaida wheel chair din sannan tasamu guri ta gefen gurin tazauna.......
Murmushi Ummi tayi sannan tace Imam yakamata kashiga maganar nan kodai kai ka hana Asma'u yimin magana ne?......
Cikin sauri ya tsuguna gabanta sannan yace"nikuma Ummi?"......
Eh mana tonaga yau se guduna takeyi inma baka hanataba nasandai sabida kai akejin kunyata......
Asma'u dakanta ke kasa tace...
"aa Ummi bahaka bane".....
Yar dariya Ummi tayi sannan tace zonan Habibty jiki ah sanyaye Asma'u takaraso gaban Ummin kamo hannunta Ummi tayi tanadan wasa dashi sannan tace"look at me Dear".....
Jiki ah sanyaye Asma'u tadago tana kallon Ummin dukda takasa dora idanunta cikin na Matar riko cheeks dinta Ummi tayi calmly sannan tace"gaskiya I don't like your behaviour yau kwata kwata Asma'u,da kinamin magana freely da banida lafiya and yanzu that I'm fine kunyana kikeji?"......
Girgiza kai Asma'u tayi alamar aa, murmushi Ummi tayi mata sannan tace"please feel free with me I'm like a Mother to you,akullum naganki sanda banda lafiya banida burin dayawuce in iya budan baki infada miki how beautiful you're,how kindhearted you're,how intelligent you're and most especially yanda kike karama amma halin manya gareki i most say we're very lucky to have you as a family member infact from the first day dakika kawoni nan nasan my son is very lucky sannan lokacin hankalina yadan kwanta because I know from that very day yanada shoulder to cry on...........
Thank you Asma'u....
Asma'u dake hawayen farin ciki kanta akasa tace"please Ummi kidaina min godiya you're making me feel somehow"....
Zandaina miki amma kema saikinyimin alkawari daya Ummi takarashe maganar tana kallon Asma'u din .......
Cikin sauri Asma'u ta gyada mata kai.....
Sannan Ummin tace "kimin alkawari xaki saki jikinki dani yanzu I'm your Mother kidaina kunya ta please".....
Gyada kai kawai Asma'u tayi don harga Allah bata tunanin zata daina jin kunyar Matar sede tarage tadan saki jiki da'ita.........

                              

Sakin hannunta Ummi tayi sannan tace.."yau babu fruits ne"......
Murmushi Asma'u tayi sannan tatashi tana"barina tsinko mana Ummi"....
Wucewa tayi yayinda Ummi tace bazakaje kataya taba!......
Kallon Ummin yayi ahankali sannan yace"I don't want to leave you alone Ummi yanzu zata dawo ai" ......
Kaidai bi Matarka I'm fine here.....
Zesake magana tace"nace kajeko I'm okay kaji".....
Babu yanda ya'iya haka yabi bayan Asma'u din yana bin bishiyoyin da kallo daya bayan daya harya iso inda take din tsalle tsalle takeyi tana kadan bishiyan tangerine amma haryanzu takasa ciro ko daya because yanzu babu ya'ya nunnannu akasa sosai duk sunyi sama se nishi takeyi itakadai dukda haka kuma bata gaji da kadan bishiyar ba............
Yana tsaye yana kallonta aranshi yana"kamar jaraba sekace shikadai ne fruit anandin".......
Ganin takasa ciro ko daya ne kuma da alama bata da niyar giving up yasashi karasawa bayanta ahankali kamar bazaiyi magana ba sekuma yace..
"give me the stick"......
Seda ta tsorata jinshi datayi kusa da'ita ga kamshin turarenshi daya mamaye mata hanci lokaci guda seda tayi gaba kadan sannan tajuyo gudun kada ta bugu da kirjinshi ga zuciyarta sewani irin racing yakeyi........

                              

Mika mishi karan tayi kanta ah kasa ahankali yakarba yana mamakin rashin maganar ta yanzu kuma da alama ma kaman gudun shi takeyi this days bata taba yarda su hada idanu yalura da hakan tun jiya......
Tabe baki yayi tareda karban stick din yayi wulli dashi don gani yakeyi shi bawani anfani zaiyi masa ba sannan yasaka hannun shi yaciro tangerine sunkai hudu lokaci guda juyowa yayi don mika mata amma wayam batanan............
Batareda yadamu ba yaciri wanda zai iya sannan yakoma gurin Ummi samu yayi Ummi natayima Asma'un hira Asma'u kuwa harda dan darawa yayinda take mika ma Ummi gwava dasu grapes daddaya tanaci.......
Zama yayi gaban Ummin shima sannan yace Ummi ga tangerine zakisha?.....
Gyada mishi kaitayi tana Smilling mika mata yayi without thinking twice amma taki karba sema cemishi datayi..
"ka baremin min to Son"....
Kallon tangerine din yayi donshi baicika son barewa ba yana bata masa hannu dawani irin stain.........
Asma'u data lura dashine tace kawo inbare......
Ko kallonta baiyiba yashiga barewa murmushi Ummi tayi sannan tace"ya'iya ae"......
Haka yabare tas sannan yamika ma Ummin tanasha haka suka kai har kusan maghrib agurin yayinda Ummin da Asma'u sukayi cikin gida shikuma yawuce masallaci abunshi.............

                                              

                        

Around 10:30pm yashigo gida don yatsaya hira da Mai Martaba yau din ko dakinshi beshiga ba yawuce dakin Ummin donyi mata saida safe samunsu Amira yayi harda Sumayya don batakai ga tafiya bangarensu ba se zubama Ummi surutu takeyi wanda yawanci labarin Indonesia ne dakuma makarantar su nacan........
Tunda ya shigo Sumayyan tayi tsit kaman wanda taga malaikan mutuwa.......
Gaisar da Ummin yayi sannan yasamu guri yazauna suma gaidashi sukayi kafin Sumayyan tace Ummi seda safe.......
Haba Daughter muna hirar mu, murmushi kawai tayi kafin tace...
"zanzo gobema harsai kin gaji da surutuna"......
Afiya ne tace"Zaki gajikam indai Sumayya ne Ummi"....
Ummi na murmushi tace"aa kam tayaya ma zangaji da hirada 'Yata kizo duksanda you're free nima zanbaki labarin garin mu".....
Cikeda murna Sumayya tace thanks Ummi sannan takarasa gabanta tayi kissing forehead din Ummin tana"good night kiss ne Ummina".....
Murmushi Ummi tayi yayinda su Sumayyan suka fice 
tanama su Amira gwaliyo donsuma zasu rakata sesu dawo suwuce nasu dakin..........
Seda yaran suka fice sannan ta dubi Almustapha tace....
"nadauka kun kwanta fa".....
Girgiza mata kai yayi alamar aa sannan yace yanzu shigowana ma Ummi........
Dubanshi tayi cikeda damuwa sannan tace and you're not wearing cardigan gashi sanyi yafara shigowa...........
I'm okay Ummi kayan jikina nada nauyi ae and acikin parloun Abba nake babu sanyi........
Kallonshi ta tsaya yi cikeda jin dadin yau Almustapha yakira mahaifin shi da Abba which means that yayi accepting dinshi as a Father she hope that bangaren Mai Martaban ma all is well haryau bata manta yanda yayi watsi da'ita dakuma Ya'yanta hakanan yajuya mata baya... those days were one of the most terrible days of her life......
Ganin tana kallonshi dawani irin emotion ne yasashi cewa...
"I'm sorry I shouldn't have call his name".........
Hawaye suncika idanunta tasaki murmushi tace"I'm so happy Imam finally you're addressing Abdulrahman as your Father"..........
Matsowa yayi kusa da'ita in a comforting manner yashiga goge mata kwalla tareda rungume ta sannan yace"Ummi yanzu kike samun sauki I don't want you to think about him,banason kidaga hankalin you've us and we'll always make you happy kinji"......
Gyada mishi kai kawai tayi don batajin kona rana dayane zata iya manta masoyinta abun ranta dagowa tayi daga jikin Almustapha din sannan tace...
"Asma'u tayi bacci ne?"......
Besan ya akayi yagyada mata  kaiba donshima bashida suitable answer dazai bata riko hannunshi tayi sannan tace "Imam I want you to promise me one thing "....
Kallonta yayi sannan yace Okay Ummi cikin sanyi tafara magana
"Asma'u is so nice and innocent girl inason kayimin alkawarin you'll always stand by her,inason kamin alkawarin you'll never hurt her feelings no matter the circumstances,she deserve to be loved Son! promise me please?".......
Kallonta yake ko kiftawa bayayi don yama rasa ansar dazai bata how sure is he zairike amanan Asma'u,how sure is he zai iya kasa hurting dinta bayan yasan yarinyar batada aiki se kuka she's so fragile and weak ta'ina zai iya fara daukan wannan alkawarin ma tukunnan..........
Dakyar ya'iya cewa Ummi it's very late now kikwanta yakarashe maganar yana niyan tashi yataimaka mata takwanta cikin murya me tattareda daci tace"nasan kasha wani abun maye jiya Imam,i know you Drank something to which you were out of you mind", takarashe maganar yayinda idanunta suka ciko da kwalla don abun bakaramin damunta yake ba tunsanda yake zuwa mata wataran abuge dabatada lafiya.......

Cikeda damuwa yasa hannu yatare hawayen dake shirin zubo mata tareda jijjiga mata kai shima idanunshi sunyi jazir yana...
"not anymore Ummi, please kada kizubar da hawayenki sabida ni".......
Cikeda damuwa tace"why will you drink something my Boy,miyasa zakasha abunda zai fidda ka cikin hayyacinka bayan kasan ya haramta,miyasa zakasa rayuwarka cikin irin wannan hadarin Imam?"takarashe maganar wannan karan hawayen suna zuba donko Almustapha yakasa hanasu zubowan sakamakon wani irin sanyi da jikinsa yayi lokaci guda.......
Cikin muryame daukeda damuwa tace"kana tunanin wannan shizai sama maka sauki aranka ko kana tunanin shan giya shizai sa al amuranka su daidaita,then if you're thinking this way you're very wrong My Son babu abunda shan giya zeyi maka Illa it'll only destroy you, your life,your health,your dignity, your future and most importantly your family dama al umma baki daya because if I'm correct you're going to be a leader Imam,Imam shugaba zaka zama inkana shaye shaye mezaka koyama subjects dinka try to remember leadership is an example abunda kayi shizasuyi koyi dashi bare yanzu da ake fama da youth masu bata rayuwarsu batareda sunyi realizing ba and on top of that your wife Son ninasan babu Matar da zataso tazauna da namiji meshan giya barema Asma'u she doesn't deserve someone like you when it comes to this situation my Son....dan numfasawa tayi sannan takarada try and change please niba tarbiyar danayi makaba kenan atleast su Afiya I was not with them harsukayi wayau but you we spent so much time together I know you well Imam bantaba tsanmani induniya tayi maka zafi you'll turn out this way ba takarashe maganar tana goge kwallarta.............
Shima hawayen yakeyi don gabadaya yarasa ta'ina zaifara ma Ummi bayani tagane shikanshi besan ya akayi yafara shan giyaba all he could remember was ranar he was very frustrated and someone took him to the bar bemasan waye baneba and he don't even know why ya yarda yabishi har yabashi yasha and from that very day dukranda aka bata mishi rai sosai inbeje yasha dinva bayatabajin hankalinshi yakwanta shikanshi abunna matukar damunshi yanason canzawa sede yakasa wani abunda daya kasa hana zuciyarshi don ita kanta zuciyar baso takeba forcing kanta takeyi..........
"I'm very sorry Ummi,kisani ah addu'a please nima bansan ya akeyi nakesha ba inraina yabaci ne nakeji invanshaba banajin dadi"........
Gyada mishi kai tayi ahankali cikeda tausayinshi sannan tace"go to sleep now and whenever you're angry just come to me first I'll surely make you better if I'm not around recite the holy book babu abunda yafishi Imam you also have your wife"....
gyada mata kai yayi tareda hugging dinta lightly sannan yataimaka mata takwanta seda ya tabbatar tayi bacci sannan yawuce dakinshi shima......

                

                        

Washegari aka kai Ummi hospital wurin likitan da take gani sannan akayi mishi bayani dalla dalla bakaramin dadi yajiba jin Ummi tafara magana donshi harga Allah yajima da cirema Matar hope din rayuwama bakidaya dubada irin wahalar dayaga tanasha acan baya...
Hamdala yayi ga ubangiji sannan yace congratulations Ma'am Ummi dake kan wheelchair tasaki murmushi tareda cewa thank you.......
Duban Almustapha yayi sannan yace tanasha wayancan drugs dinne haryanzu?..
Gyada mishi Kai yayi ahankali sannan doctor din yace to zamuyi mata test semuga in akwai problem ajikin nata but still tacigaba da shan magungunan zuwa nanda one month kafin muga abunda Allah zaiyi kuma......
Godiya Almustapha din yayi masa yayinda yarubuta musu test din dazasuyi sukaje sukayi akace washegari suzo ku karbi rasult aikuwa washegari Almustapha da Sulaiman ne sukazo su kadai...
 tabbatar musu likitan yayi kan komai is normal kawai tacigaba da shan drugs din Sulaiman ne yadubi likitan sannan yace"are you sure doctor,if akwai matsala ko wajema zamu fidda ta mukam so advisibly mezaka ce?".....
Murmushi likitan yayi sannan yace"I guess you'll get thesame answer ko kunje can din sabida duk wasu facilities munadasu anan and we did all that we can bamuga komaiba so kaga this's the only taimakon dazan iyayi kenan shiyasa nabata magun gunan tun acan baya and alhamdulillah tafara samun sauki inaga mubari nan da one month to two months dai haka inbabu wasu improvement din nidakaina zanyi referring dinku to can din I've connection with so many hospitals outside the country"........
Mika masa hannu Almustapha da Sulaiman sukayi suka masa godiya sannan suka fice don komawa gida.......

Cikin sati biyu jikin Ummi yayi sauki sosai don yanzu muryarta nafita clearly gakuma wani karfi da sauyi datakeji acikin jikinta hakanan Asma'u dukyanda take gudun Ummi tanajin kunyarta dole seda ta rage don kullum Ummin sake janta jikinta takeyi Itama kuma hakan nasata sake sakewa da Matar.......
Bangaren Almustapha kuwa har anyi convocation dinsu amma baisamu yajeba sedaga bayane yaje yakarbo certificate dinsa he's now fully a Medical Doctor ranar da Asma'u taga certificate din agurin Ummi bakaramin farin ciki ta tayashiba don harjitake kamar nata ne even though other part na zucuyarta natuna mata burin datasha kan zama medical doctor amma yanzu yatafi invein sede intayi laakari da mu mutane muna planning life dinmu ne without knowing what  Allah has install for us, indeed he's the best of planners and she's sure yayi mata wani tanadine shiyasa komai yayi turning out this way intayi irin wayannan tunanin takanji dan sanyi aranta.........
Acikin sati buyunnan kuma fuskar Almustapha tayi bye bye da kallon na Asma'u don haryanzu gudunshi takeyi she always find a way to get away from him inyashigo tayi bacci sanda zaifita kuma tana aiki ah kitchen dakinshima tayi bye bye dashiga don baya taba fita batareda yagyara koina ah dakinba hakan yasa Itama tadaina zuwa abinci kuwa Iya Jamila kekaimusu shida Sulaiman inkuma shi kadai zaici takai mishi daki...........

Acikin wayannan kwanakin ne kuma Hajiya Muniba tatare abangaren da akayi mata kusa da nashi amatsayin Matar Mai Martaba hakanan dataji labarin jikin Ummi gurin Mom har gida tazo taduba Ummi din cikeda tausayinta.......
Ummi ma batayi mata wani haliba don kuwa ance bakonka annabinka and besides dan tana matar mahaifinsu Almustapha bazata wulakantataba tunda ita tanada mutunci kuma daman ita mutumce me hakuri dasaukin kai.......
★*★

Yautakama laraba kuma yaune Mai Martaba yabashi wani nannauyar aiki na boreholes da za ayi ah unguwannin talakawa beso aka bashi wannan task dinba sede Mai Martaban cewa yayi this's one of the things that will make you close to your people Son katuna 5 month aka baka kayi proving kanka innocent and a month has passed now you've to be punctual.......
Gyada ma Mai Martaban kai kawai yayi sannan Mai Martaba yasa  Galadima da yayimasa bayanin unguwannin dazaiyi aiki na tonon boreholes din dakuma kudin da aka bayar don already kudin nagurin Galadiman.........

Godiya yayima Mai Martaba din sannan yajuya yafice don komawa bangarensu yasauya kayan sarautarnan because becika son fita dasu ajikinsaba kuma yanason leka Mallam Hudu yau din shiyasa ma yayi deciding komawa yacanza kaya kafin yafice tunda seda yanma ne zasu zauna magana da Galadima din.............
Straight dakinshi yawuce bude kofar dakin yayi yashiga tareda wucewa gaban wardrobe dinshi yabude yana neman kayan sawa jiyayi kaman motsin mutum ah bandaki mamakine yakamashi donshidai yasan masu aiki baswa yimasa wankin toilet dakansa yakeyi don tuni yacire rai da aikin Asma'u ma tunda gudunshi takeyi yanzu...............
Amma sebai damuba acewarshi koma wayene zefito ai dauko kayan dazai saka yayi yashiga canzawa haryagama sannan yakarasa gaban mirror yana gyara lallausar gashin kanshi jiyayi anbude kofar bandakin don haka seyakalli direction din toilet din tacikin mirror din ido hudu sukayi da Asma'u dake daure da towel dako gwiwarta batakaiba ga gashinta ma ah tsefe duk jikeda ruwa da alama wankesu tayi yanzun.............

                

                        

Mutuwar tsaye tayi agurin gabadaya takasa motsi ma shikuwa saurin dauke kanshi yayi sakamakon jin yanda gabadaya jikinshi yayi wani irin yarrr.............
Cigaba da gyara gashin shi yayi batareda yasake duban inda takeba ganin tarasa nayine sekawai tafashe da kuka ah gurin.........
Mamakine yakamashi aranshi yana"itakuma wannan me akayi mata,saka cumb din yayi cikin drawer sannan yakoma kan gadon shi yakwanta tareda lumshe ido don jiyayi lokaci daya yafasa fitan ma baki daya daman yana nemanta suyi magana to opportunity yasamu yanzu he can't just waste it.......
Jin takiyin shiru ne yasashi cewa...
"wanine yadake ki?".....
Kaman wanda yana kallonta tashiga jijjiga kai sannan tace "bakaine kaki mikomin hijab dinaba".......
Tashi yayi yazauna tareda kallonta yana jijiga kai unbelievable donshi bemasan ina hijab dinta yakeba why is she trying to accuse him kuma.........

Kuka takuma saki cikeda shagwaba tana kara kakkare jikinta takasa kallonshi tace"kadaina kallona please kunyanka nikeji"......
Wannan karan seda yadan saki dariya dukda batajiba da kaman bazaiyi magana ba sekuma yace...
 "narike kafanki ne konace kizo dakina kiyi wanka?".......
Sake kokarin daga kafarta tayi amma takasa don gani take intasake wani step towel dinma fadi zaiyi gabadaya gawani kunyarshi datakeji itakam yau su Afiya sun cuceta dasuka ce tazonan tayi wanka don zasuje gaida Hajiya Muniba ne dukansu Amira tashiga bandakinta Afiya tashiga na dakinsu don suyi sauri itakuma sukace tazonan tunda dakin mijintane ae abunda yasa tazodin sabida talura kwanannan becika zamaba around this time ba amma se Allah yakawo shi kuma at the wrong time...........

Jin tayi shiru batace komaiba yasashi maida kanshi yakwanta tareda sake lumshe idanunshi yana"inkin gama kukan kizo muyi magana".....
Wani harara ta daka mashi wanda shi baimasa tanayiba don ba kallonta yakeyiba cikeda takaici ga hawaye nabin kuncinta tace"to kazo kabani hijab dina".....
Batareda ya kalleta ba in a serious tune yace..
"bandauka ba Asma'u"...yanda yakira sunanta sedayasata jin wani iri kafin ahankali tace "nasani ai nakasa daga kafana  ne please kamiko min yana kan bedside dinka",batareda yakalli inda takeba yadubi bedside din nashi aikuwa hijabin na ajiye dukda aranshi yanajin taraina mishi wayau nema da tace takasa tafiya hakan kuma behanashi wurga mata hijab dinba aikuwa kan jikinta yafada cikin sauri tarungume hijab din jikina karkarwa tafara neman yanda zatayi tasaka aikuwa Allah yataimaketa tasadin sede gaba abaya......
Hanyar kofa tayi cikin sauri zatafice yayi saurin tashi tareda binta cikin zafin nama yatsaya abayanta ya danne kofar wanda hakan yasa takasa budewa dukda ba key yasaka ma kofar ba hakanan kuma tanajin inuwarsa abayanta cikin sauri tajuyo yayinda hawaye suka fara zuba tana kabude min don Allah inta..  kasa karasa maganar tayi sakamakon arba datayi da kyakyawar fuskarshi ga gashinan yasha gyara sewani glowing yakeyi gashi dab da'ita yake ko numfashi kwakwara takasayi sema kamshin turarenshi daya addabeta don closeness din yayi yawa harsuna iya jin numfashin juna..........
Sa hannu yayi ahankali tabayan kugunta yasa key akofar sannan yace cikin cool voice dinshi...
"wipe those tears away"......
Goge kwallar tashigayi bashiri amma still wasu nazuba non stop samun kanshi yayi dasa hannu yana tayata goge kwallar aikuwa segashi tadaina cikin muryar dabaisan yana da'ita ba yace"magana zamuyi ba wani abu zanmikiba"......
Kaman zata kuma fashemai da kuka tace kabarni don Allah inje insaka kaya zandawo yasan karya takeyi inta tafi bazai sake ganinta ba don haka yace..
"no you're not going anywhere besides kinrufe jikinki ai kuma ma cemiki akayi kallon ki zantayi?"yayi maganar cikeda rashin damuwa......

Tayi mamakin yanda ya sake yana mata magana kuma talura shima baida niyar barinta ta tafin inbata tsaya taji mezaice dinba ga closeness dinsu na damunta dakyar take iya numfashi ma and talura shibaima wani damuba(araina naje Jan ajin kike ji yarinya)......

"Miyene maganar to?",takarashe maganar tana turo karamin cute pink lips nata shiru yayi yana kallonta wanda yasata saurin sauke kanta abunda bata saniba shi tunanin yanda zaiyi putting words din yakeyi.......
Sunfi three minutes ahaka kafin dakyar ya'iya cewa...
 "you requested something the other day"...
Cikeda mamaki tana nuna kanta tace"me?".....
Seda yaja mata aji sannan yagyada mata kai kadan......
"Meyene abun nikam namanta", tayi maganar innocently"........
Dan sa hannun yayi ya wargaza gashin kanshi yarasa tayaya zaiyi mata bayani tagane shikuma yakasa fitowa directly........

Cikeda kaguwa tace"Yaya Almustapha miyene nifa namanta".......
Dan jada baya yayi kadan sannan yace "inbaki tuna ba shikenan"....
Bakaramin mamaki yabataba itakuma harga Allah takasa tunawa kwata kwata..........
Pouting lips dinta tayi"intafi kenan?".....

Sa hannu yayi cikin aljihun wandonshi yana kallon ta sannan yagyada mata kai ahankali juyawa tayi tabude kofar harzata fice yayi saurin cewa...
"you said something about being my friend"..........
Tsayawa tayi cak gurin yayinda zuciyarta tashiga bugu so fast"so,he wants to be her friend?"...

 Hello Dearies nasan Kuna kewar Magajiya dayawa....to tell you the truth nima nayi kewarta but soon zakuji daga gareta tace ingaisheku duka and she's waiting for your replies......
Kuyi hakurifasako nakawo nima....

                      

Juyowa tayi ahankali tana kallonshi sabida tanason kara tabbatar wa maganar daga bakinshi tafito ko aa sede da mamakinta babushi ah gurin da alama yakoma can cikin dakin kokuma yashige toilet...........
Jiki ah sanyaye tawuce dakinta samun Amira tayi harta gama shiri tanata mita wai tashiga wanka kaman me canza fata.....
Itadai Asma'u batace mata komaiba don haushinsu takeji ayanzuma gabadaya gani takeyi su suka jamata komai ma daya faru karasawa tayi gaban wardrobe dinta don neman kayan dazata saka................

                      

★*★

                      

Mama haryanzu naji shiru Mai Martaba beyi taking decision ba kodai yabama wani ne bamusani ba?, Zaliha takarashe maganar ta fuskarta daukeda damuwa..........
Magajiya ne tadan dafa kafadarta sannan tace"mekikeci nabaka na zuba ne babu yanda za ayi ya dauki matakinnan batareda nasaniba kumama inatunanin yamanta da zancen ne dubada yanda abubuwa sukayi mashi yawa kwanan nan amma zan sakeyi masa magana kikwantar da hankalinki.....
Dan ajiyan zuciya tayi tana"Allah yasa to"....
Amin Magajiya ta ansa sunanan zaune Sulaiman yashigo fuskarshi daukeda fake smile don kwata kwata yakasa gane kan matarshi tunda tafara yawan ziyartar mahaifiyartasa and it seems like bakinsu daya yanzu shidai yazuba musu ido ne yaga karshen gudun ruwansu dukda yakanyima Zaliha nasiha in directly kullum babuma abunda yafi daga mishi hankali ayanzu irin yanda tayi fatali dashi batama da lokacinshi kwata kwata acewarta inbaidawo yafara fighting for the throne ba to yayi bye bye da zaman lafiya tsakaninsu gashi shi mutum mai karfin sha'awa da bukatar mace akodayaushe tareda shi but it seems like she's turning her back on him ma gabadaya".........

                      

Magajiya ne takalleshi tareda tabe baki zama yayi gefenta cikeda kulawa sannan yace"Ina wuni Mama"......
Batareda ta kalli inda yakeba tace...
"lafiya lau".....
Murmushin dayafi kuka ciwo yayi sannan yace...
"dazun nashigo kina bacci ai"....
"Oh"...
Shine kawai abunda tace mishi bangaren Zaliha kuwa ko gaisuwar ma baisamu ba yafi minti goma zauna kafin yayimusu sallama yafice Allah yagani shidai yana sauke hakkinshi amatsayinshi na Danta straight bangaren Mom yayi batanan tana bangarensu Almustapha don haka yasamu guri yazauna ah parlourn tareda jingine kanshi ahaka har daya daga cikin bayin takawo mai ruwa ta ajiye tafice abunta ba ajimaba kuma sega Sumayya tafito daga dakinta jikinta sanye da riga da alama ma rigar bacci ce iya gwiwa se hannunma siririya dukdama rugar nada dan fadi bata nuna shape din jikinta sosai ba kiran daya daga cikin bayin tashigayi don harga Allah batama lura da mutum ah parlourn ba shikuwa jin muryartata ne yasashi dagowa seda zuciyarshi ta buga sakamakon kallonta dayayi cikin wannan yanayin saurin dauke kanshi yashigayi yana istingifari aranshi........

                      

Baiwar ne takaraso gabanta tareda sunkuyar dakai tace"gani Yaya Sumayya"......
Oat zaki hadamin in sha Sakeena I'm somewhat peckish.......

                      

Cikeda ladabi yarinyar da aka kira da sakina ta sunkuyar dakai sannan tace to kafin tayi hanyar kitchen don aiwatar da abunda Sumayyan tasakata yi din......
Sumayya kuwa juyawa tayi don komawa dakinta se idanunta sukayi carab kan Sulaiman fuska daukeda murmushi tayo hanyar parlourn tana...
"laa Yaya Sulaiman kananan dama miyasa bakayimin magana ba?".......
Ganin tana yowa direction din dayake yasashi saurin cewa "Sumayya just go back to your room Inbazaki iya sa something matured ba karkizo kusa dani please"yakarashe maganar hankali tashe donshi kadai yasan meyakeji kuma wallahi intayi tazi gurin shi ahaka yasan zai iyayin abunda zasuzo suna nadama dagashi har ita".........
Tabe baki tayi sannan tajuya don komawa daki don itadai Allah yagani bataga abun tada hankali anan ba ina ruwanshi tunda ba jikinshi baneba...........
Komawa tayi daki tadale gado abunta don batama jin sake komawa gunshi bare yasake bata kusa sede me dukyanda taso tacigaba da kallon da takeyi ah laptop din dake gabanta kasawa tayi sabida gabadaya tunaninshi ya mamaye zuciyarta gashi kaman ma yana cikin damuwa ne tashi tayi ahankali kamar wata marar lafiya tana contemplating taje gunshi ne ko aa daga karshe dai tanemi zani tadaura tareda saka hijab tafice still yana parlourn kanshi na kallon sama idanunshi ah lumshe karasawa tayi tazauna gefenshi sannan tace"I'm sorry"........

                                      

                        

Dago da lumsasun idanunshi yayi ahankali yadaurasu kanta sannan yace...
"For what Sumy?".....
Dan turo baki tayi don Itama batasan dalili ba shiru yayi nadan dakiku kafin yace..
"yanzu fisabilillahi kowani namiji ma yazo haka zakifito agabansa?"........
Kaman zatayi kuka tace"Kai Yaya Sulaiman kacika mita wallahi yama za ayi infito gaban wani namiji haka ku ai yayuna ne shiyasa"......
Girgiza matakai yashigayi ahankali sannan yace..
"still baidace ba Sumayya niba muharraminki baneba besides ko blood Brother dinki baidace kifita haka gabanshiba at this your age sabida shaidan you don't know what he's capable of".......
Kallon he's very serious tace to naji zangyara.......
"Kimin alkawari Sumayya,because inada matukar kishi akan abunda nake so"yakarashe maganar murya akarye.......
Dan ware idanu tayi don she's very confused murmushi yasakar mata tareda dan riko hannunta yana kallon cikin idanunta sannan yace..
"Yes Sumayya, I'm in love with you,I love you Sumyna" yakarashe maganar gabadaya white teeth dinshi bude daya karama fuskarshi kyau hakanan kuma yasata sake fadawa cikin duniyar lumsassun idanunshi they're busy looking into each others eyes shi damuwarshi shine taga irin son da yakemata ko Allah zaisa ta agaza mishi while on her side kuma gabadaya she's so shocked and out of words tama rasa mezata cemashi sede all she knows that shine she feels thesame way.......
Sunfi minti uku ahaka gyaran murya sukaji anayi akansu Amira ne da Afiya cikin sauri Sumayya tadauke kanta cikeda jin kunyarsa dariya su Afiya suka kwashe da tana niyan tashi yayi saurin sake riko hannunta yadawo da'ita tazauna bedamu da presence din kannen nashiba cikin kakkausar murya yace"baki bani amsa ba Sumyna,I said I love you I want to spend the rest of my life with you will you mind doing thesame?"yakarase maganar kamar wani maraya..........
Murmushi kawai Sumayya tayi yayinda tatashi wannan Karan tayi daki aguje shima murmushin yayi yanabinta da kallo harta kule masa yes bata furta masa da baki ba but he's very sure she feels thesame way......
Afiya da Amira kuwa se ihun murna suke Amira na nidaman nasani there is something between you two.....
Tashi Sulaiman yayi yana to yan sa Ido ana ruwa kuna irgawa nidai atayani campaign......
Amira ne tace ae dolema Yaya Sulaiman cikin sauri Afiya tace"kinmanta yanada sweetheart ne nidai babu wata campaign dazanyi banason Sumayya taje gidan dazata hadu da kishiya".....

Dan shiru Amira tayi cikeda zolaya tace kumafa hakane Yar uwa,yasan zolayanshi sukeyi amma seyayi kansu yana..
"nalura yarannnan kunraina ni
dayawa".....
Hakuri suka shiga bashi suna wasafa mukeyi Yaya Sulaiman, murmushi yayi sannan yace I know amma please kada ku birkita min ita akan maganar kishiryannan tazo tace tafasa........
Bazamuyi ba Allah Amira takarashe maganar tana dariya mischievously.......
"Better yakarashe maganar tareda barin bangaren don Almustapha yace masa yanason suyi magana da yanma akwai abunda zaiyi mishi".......
Sede koda yaje baisameshi ba donhaka seya zauna gun Ummi suna hira abunsu harlokacin sallar maghrib yayi.....
****
Around 9:30pm Magajiya ta'isa bangaren Mai Martaba don tasan by now yana side dinshi sannan bekai ga kwantawa bacci ba.......
Koda tashiga dakin yafito daga wanka kenan yana tsane jikinshi karasawa tayi cikin sauri tareda karban karamin towel din daga hannunsa tashiga taimaka masa dukda ransa besoba amma bai hanataba don aganinshi inyana yawan shunning nata down bawai tana kyauta mata baneba....
Seda yasauya kaya zuwa na bacci ganin haryanzu batace komaiba yace..
"lafiya Magajiya akwai magana ne because ni I'm going to bed now".....
Cikin sauri tace daman ranar nayimaka magana kan rike household kuma haryanzu banji kacemin komaiba zama yayi gefenta sannan yace"kinsan Allah namanta kwata kwata gwanda ma dakika tunamim"....

Murmushi tasakar Mai kamar wata mutumiyar arziki sannan yace"inshallah Allah I'll see what I can do by tomorrow morning jikin naki yana damunki sosai be dakika damu har haka? Yakarashe maganar yana kare mata kallo...... ....
"Dasauki Mai Martaba kawai dai nagaji kasan shaanin tsufa",shidai gyada mata Kai kawai yayi dukda yana mamakin ta haryau nawai tanason adora wani in her place bayan yariga yasan Magajiya dason mulki tunda"......
Saida safe tayi mishi sannan takoma bangarenta....

                

                        

Bangaren Almustapha yana zaune ah parlourn yana jiran isowar Sulaiman yayi shiru gabadaya yana lissafe lissafe shikadai har Sulaiman din yashigo. .......
Hararanshi Almustapha yayi sannan yace...
"where have you been?"......
Ziyara naje Sulaiman yabashi amsa kai tsaye dukda ran Almustapha yabaci najiranshi dayasa yayitayi besa yakuma tanka mishi ba......
Seda Sulaiman din yagaji da shirun sannan yace ......
"kace kana nemana nazo kuma bakace komaiba".....
Batareda ya kalleshi ba Almustaphan yace...
"do you know any good geologist dayake aikin boreholes?"......
Dan shiru Sulaiman din yayi na dakiku kafin yace sede in bincika maka dai Yaya.......
Rufe files din dake gabanshi yayi sannan yace"okay then, please kabincikamin before end of this week"daga haka yayi wucewarshi dakinshi.....
Tabe baki Sulaiman ma yayi sannan yaciro wayarshi yashiga kiran Sumayya bejima yana ringing ba tadauka...
 "Babygirl bakiyi bacci ba?"...
Cikeda shagwaba tace Yaya Sulaiman nice nakoma Babygirl yaukuma?......
Yar dariya yayi sannan yace...
"audama bakisaniba you're my Sweetest Babygirl dazu shine kika gudu abunki koki bani ansa"......
Murya can kasa kasa tace...
"you know my answer already ae".......
Tashi yayi daga kujerar yafice ah parlourn don komawa bangarensu yana nidai bansani ba kifada bakini inji......
Make kafada Sumayya tayi kaman wanda tana gabanshi tace...
"naqi wayon,kasani ai kawai kanason infada ne"........
Yar dariya yayi sannan yace"okay love nakyaleki but when you feel like saying it out kifadamin kinji".......
Haka suka cigaba da wayarsu cikeda so da kaunar juna don dukansu babu wanda yalurama time yagudu harhaka don se gurin daya nadare sannan sukayi sallama su Hajiya zaliha anacan anata shatata bacci miji nanan yana soyewa da wata.......

Washegari dasafe Mai Martaba ya aika akira mashi Hajiya Muniba babu bata lokaci tasamoshi ah sashin shi bayan sungaisane yace shawara nike nema Muniba dan murmushi tasaki sannan tace inajinka Dear........

Gyara zama yayi sannan yace Magajiya tasameni maganar household kinsan ita take controlling komai daya danganci bangaren abinci dama kuma baki daya bayi Mata......
Gyada Kai Hajiya Muniba tayi cikeda gamsuwa sannan yacigaba"she's somewhat sick this days so tasameni kan tanason ta ajiye wannan responsibility din and age requested that I give this task to one of our Daughter in-laws so I'm somehow confused kungane Zaliha is the eldest but Asma'u itace Matar Almustapha Kuma yagirmi Sulaiman gabadaya narasa figuring out waye zanbamawa banason nayi rashin adalci aciki .............
Dan shiru Hajiya Muniba tayi kafin tadan numfasa"ae abun ba agirma bane Dear kaduba cikin su waye kayarda dashi wayekuma kakeda tabbacin inkata wannan damar bazata zuba ma kasa ah Ido ba,the most important thing shine wanda zaasa agurin atabbata ya cancanta,so yanzu Kai wakake ganin you trust so much"........
Shiru Mai Martaba yayi because in his heart yayarda da Asma'u dari bisa dari sede Zalihan ma bazaice wani abu akanta ba tunda tanazuwa gaida kuma tanada ladabi don haka seyace I trust them both..........
Murmushi Hajiya Muniba tayi sannan tace then seka basu duka kowacce kayi mata handling responsibility daya dace da'ita and hakan ma zaifi don babu wanda zaice kayi sonkai..........
Godiya yayi mata sannan yace thank you Muniba......
You're welcome Dear barina barka kashirya yanzu nasan nanbada jimawaba zaka shiga fada ko?...

Gyada mata Kai yayi ahankali kafin tamishi sallama tafice tana tunanin Allah yasa kada yabama Zaliha aikin dazaisa tana wulakanta bayi bangarenta takoma direct.............

Yau Asma'u tareda ita akayi karatun asuba donkuwa gani take Itama zata karu koba komai daganan tawuce Kitchen sukayi breakfast dakanta takaima Almustapha abinci daki don Sulaiman beshigo ba yau......
Yayi mamaki donshikam har yayi wanka abunsa yashirya cikin bakar hadaddiyar shadda data kara fito da kyawunsa........
Ajiye abincin tayi sannan tace...
"Good morning Yaya Almustapha"
Morning ya ansa mata ajiye abincin tayi sannan tashiga serving dinshi calmly duka baihanata ba harta gama sede yaki faraci itakuma taki tafiya..........
Ganin kamar da magana abakinta ne yasashi cewa...
"do you need anything?"......
Girgiza maikai tayi alamar aa kafin tace..
"bakacemin ka gode ba"......
Cikeda mamaki yace"name fa!"..
Turo baki tayi"for accepting your friendship mana"....
Kallonta yayi blankly aranshi yana"so we're now friends shiyasa tadawo dayimin wayannan hidimar", ahankali kuma yasakar mata
Lallausar murmushi  dayayi melting heart dinta kafin yadubeta  yana...
"Do friends have to thank each other?"......
Tashi tayi tafice tana "kaidai bakason cewa ka goden ne kawai"...
Jijiga kai kawai yayi sannan yafara cin abincin calmly........

Around 10:30am Asma'u taje gurin Talatu tana kince kina nemana?......
Gyada mata kai Talatu tayi ahankali sannan tace"abunda kikayimin bakowa bane zai iya yimin arayuwa dukda anfada miki cewa niba mutumiyar kirki bace amma hakan besa kinjuyamin bayaba dan zamana dake nagane cewa baku cancanci inki taimakon ku ba kamar yanda kika taimakeni Magajiya kuma ita tayi watsi dani inaganin lokaci yayi daya kamata tafuskanci gaskiya bayan duk abubuwan damukayi", folding hannu Talatu tayi hawaye nabin kuncinta tace hankalina ba akwance yakeba gabadaya nafara nadamar abubuwan danayi kifada min duk abunda kikeso inyi miki na taimako  gurin tona asirin Magajiya nikuma zanyi miki bayan nan kuma inason inmika kaina ga hukuma sabida suyimin hukuncin daya dace dani"........
Asma'u har ranta taji dadin maganar Talatun yayinda afili kuma tace"niban daukoki don kutayamu tonama Magajiya asiriba munyi miki don Allah ne so basai kin takura kanki ba please"......
Jijjiga matakai Talatu tayi tana nariga nayanke shawara zan taimakeku don Allah kada kice aa,gyada Kai Asma'u tayi sannan tace"are you sure?".....
Eh cewar Talatun kafin Asma'u tace to kibari zamuyi magana anjima yanzu zanje fada ne Mai Martaba yana nemana kikwantar da hankalinki don Allah ......
Gyada mata Kai Talatu tayi yayinda Asma'u tafice zuwa bangaren Mai Martaba don fitowarta zata gun Talatu Rukayya kece mata an aikomata sakon kira koda ta'isa samun Zaliha tayi da Magajiya zaune saida zuciyar ta tabuga dakyar ta'iya daurewa tazauna can gefe tareda gaida Mai Martaba din......
Amsawa yayi yana murmushi kafin tagaida Magajiyan.....
Yitayi kamar batajiba seda Mai Martaba yace Magajiya bakiji ana gaidaki bane cikeda takaici ta ansa tana hararar Asma'u din itadai Asma'u kanta nakasa donta rasa dalilin wannan Kiran that too tareda wayannan ko me suka hada mata Allah kadai yasani....

Mai Martaba ne yace"nakiraku ne sabida indaura wani nauyi wanda mahaifiyarku ta bukaci ayi hakan".......
Shiru sukayi dukansu dukda kirjin Zaliha sai dukan uku uku yake tun shigowar Asma'u domtarasa dalilin dayasa za ayi involving Asma'u cikin wannan zancen badai Mai Martaba yanason bata wani abun bane haka tayita tunane tunane ita kadai dakyar ta'iya maida attention nataga abunda yakecewa bayani yayi musu na yanda sukayi da Magajiya din sannan yace "shiyasa kukaga nataraku duka biyu kowa inbata portion din aikinta sabida befi experience ba because one day one time kune zaku zama manyan and the responsibility will be all yours"......
Gyada kai sukayi jiki ah sanyaye sannan yace ke Zaliha daga yau zakina kula da bangaren hukunci na bayi insunyi laifi kokuma ansamu sabani ah tsakaninsu kece zakina solving problems nasu inkuma yagagareki kina iya samun Magajiya she'll help you out or kizo direct kisame ni kinji........
Gyada kai kawai tayi dukda jitake kamar zuciyar ta zatayi boasting wato wannan ne kadai aikin daza abata?......
Jitayi Abban yadubi Asma'u sannan yace Daughter kezakina kula da bangaren abincin bayi dakuma suturarsawan su duk inkinada matsala kisameta kokuma just come to me directly sannan ke Asma'u kisamu jakadiya zatayi maki bayanin komai gameda abincin masarautar nan daduk wani abu dayakamata kisani sannan yadubi Zaliha itama yace kekuma ga Magajiya she'll explain everything to you inafatan ban takura wanin ku ba?....

Gyada Kai sukayi ahankali dukda ma Asma'u har ranta itakam bason abunnan takeba sede dawani bakin zata dubi Mai Martaba tace masa bataso?...
Intayi haka tayi masa adalci kuwa wayannan sune tambayoyin da takeyima kanta albarka yadinga saka musu sannan yasallamesu.........
Zaliha da Asma'u ne sukafara fita yayinda Magajiya tadubi Mai Martaba tana  amma dai rankashidade baka kyau.......
Batakai ga karasawa ba yadaga mata hannu alamar ya Isa sannan yace"I did what I felt was right kuma kene kika ce ah tsakanin su biyu nikuma bazan iya hakan ba so please Magajiya just watch over them and pray Allah yasa hakan shiyafi alkhairi gobe za ayi introducing nasu to Bayin su susan  cewa sune sabbin shuwagabanninsu I've somewhere to go to right now sena dawo yana karasa fadin haka yafice yabarta tsaye tanabinshi da kallo baki sake".........Lallai Mai Martaba wuyanshi yayi kwari bata taba tunanin zeyi taking wannan step dinba don atunaninta ai Zalihan ce babba so bazai taba bama Asma'u ba sede gashi he end up giving her some of the responsibilities wanda shine ma yafi mahimmanci da girma ah idanun bayin........... +

Bin bayanshi tayi tafice fuuuu kamar wanda zata tashi sama zuwa bangarenta.........

Zaliha kuwa koda suka fice tareda Asma'u din sebinta da mugun harara takeyi ganin Asma'un batamasan tanayiba yasata saurin jawo riganta wanda har hakan yatsoratar da ita cikin sauri tajuyo tana..
"miye hakan kuma?".....
Sakin rigarta Zaliha tayi tareda daga hannu tana nunata da yatsa daya"wallahi karkiyarda kice zaki shiga harkata bawai kinga anbaki matsayin dayafi nawa ba kice zaki raina ni,don da alama ma roka kikayi don ah iya sanina Mai Martaba bazai taba daukan wannan matsayin yaba ma wanda ba jinin sarauta ba irinki,nina rasa ke wace irin mayya cema tukunnan dahar kikasamu wannan matsayin ah gidan nan".....
Asma'u daranta yagama baci dukda tanajin hawaye sun taru mata tayi kokarin makesu kadama Zalihan taga weakness dinta ahankali tace"yanzu sabida matsayi kike zubar da girmanki har kikemin magana haka?"...
Zaliha kamar zata maketa tace ..
"karki fadamin maganar banza"......
Murmushin dayafi kuka ciwo Asma'u tayi sannan tace"nibazan tsaya ina fada dake akan abunda baikai yakawo ba Aunty Zaliha sede inason kisani shi position din da kiketa fifiko akaima basonshi nakeyiba don gani nakeyi kamarma wani nauyi aka dauramin da'ace zakiyimin hanyar daza a saukemin ita ma bakaramin gode miki zanyiba abunda yasa kikaga nayi shiruma sabida Abba ne,bazan taba bari yabani aikiba inkiyi ince zan zuba masa kasa ah idanu shiyasa kikaga haka so do whatever you want to take it back bazan damuba... takarashe maganar tareda juyawa don tafiya sekuma tatuna wani abu tadawo"and yes,kada kisake zagina kokice zaki zagi identity na atleast I'm proud of the fact that niba Yar Gidan Sarauta baceba hakanan ban hada dangi dasuba koba komai mu bamu fada da yan uwanmu na jini sabida position,koba komai bama wargaza zumuncin mu sabida abin duniya hakanan koba komai we stays like a family and we're true to one another bamwa stabbing yan uwan mu behind their back. atleast it's prestige!, Asma'u takarashe maganar tanayima Zaliha wani irin kallo kafin tajuya tayi tafiyarta tabarta tsaye gurin kamar gunki tana hucin takaici.......

Zaliha jitakeyi kaman tabita ta bugi yarbanza amma tayi controlling anger dinta tawuce bangaren Magajiya aranta tana"harni yarinyar nan zata fada ma magana,aiko zanyi maganinta"
Asma'u ma tayi nasu bangaren ah parlour tasamu Ummi tana kallon CNN jingine jikin kujera da alama ma taimaka mata akayi tazauna din......
Fake smile tasaki don gabadaya ranta ajagule yake game da wannan babban nauyi da aka daura mata gashi har Zaliha naneman tafada mata magana tunma ba aje koina ba abun bakaramin damunta yayiba.......
Zama tayi gefen Ummi tareda gaisheta sannan tace yajikin Ummi?.......
"Dasauki alhamdulillah Habibty yanaganki wani iri,Is everything alright?",Ummi takarashe maganar tana observing fuskar Asma'u din gyada mata kai Asma'u tayi tana kokarin danne damuwarta kafin tace...
"babu komai Ummi everything is fine"......
Cikin sauri Ummi tace a'a kam kifada min damuwarki please it's evident on your face that kinada damuwa, inbaki yi sharing damuwarki daniba dawa zakiyi sharing Asma'u?.........
Hakanan se Asma'u taji she's free with Ummi din and she can share her problems with her indai tawannan fannin ne ahankali tafada mata yanda sukayi da Mai Martaba din dakuma yanda sukayi da Zaliha awaje kafin daga karshe tace"Ummi I'm too young for that ta'ina zan iya rike wannan nauyin banason inzo inyi failing Abba and kinga sabida haka ma munfara samun matsala da Zaliha koba komai Matar Yaya Sulaiman ce bazanso fada irin haka yashiga tsakanin mu ba kumama kaman zatafi dacewa da aikin tunda ita ranta naso", takarashe maganar cikeda damuwa.......
Murmushi Ummi tayi sannan tace...
"wannan shine damuwarki Asma'u?".....
Gyada mata kai tayi ahankali kafin Ummin tace bazan ki taimaka miki wurin sawa adauke miki wannan matsayin ba indai kina ganin bazaki iyaba but before that Dear inason kizagaya cikin bayin nan fannin inda suke zama,abincin dasukeci dakuma suturun dasuke sakawa dama sauransu kiga yanda suke rayuwa seki dawo kifada min opinion dinki"......
Dagowa Asma'u tayi tana kallon Ummin murmushi Ummi takumayi mata encouragingly tana"I'll support you whatever your decision might be kinji"......
Gyadama Ummi kai tayi don hakanan taji hankalinta yadan kwanta sannan tace zanjeni da dayanma Ummi.........
Allah yakaimu Ummin tabata ansa ahankali nan tazauna gefen Ummi tana tayi mata hira don ganin tayi Lightening mood dinta cankuwa sega Asma'u se dariya takeyi har Almustapha da Sulaiman suka shigo gaidasu tayi suka amsa tananan zaune.........
Sulaiman ne yadubi Almustapha din sannan yace...
"nasama maka maiyin aikin and he's willing to do it yacemin ma zaka iya zuwa kasameshi da yanma kokuma shizaizo gida dakansa kuyi magana"......
"Thank you shine abunda Almustapha din yace"......
"You're welcome Bro amma zakaje kasameshi ne koshi zaizo don yace I should get back to him on time Sulaiman yayima Almustapha maganar yana kallonshi?".....

STORY CONTINUES BELOW


Dan ware hannun yayi alamar baisaniba shima jijiga kai Sulaiman yayi in desbelief sannan yace"Allah Yaya you'll never change".....
Murmushi kawai yayi bece komaiba sema daga wayarshi dayayi yashiga danne danne Sulaiman kuwa duban Ummi yayi yace"Ummi yakamata akai Yaya hospital ko akwai aikin daza su iyayima bakinshi wanda zaisa yafarama mutane magana sosai ta hanyar basu details mekyau ba short short maganaba, hawa mulki zakayi Yaya yakamata ace kana interaction da mutane yanzun sosai"....
Dariya Ummi tayi tana"Kai Sulaiman ba a rabaka da abun dariya wallahi yanzu daman ana sa mutum yakoyi magana dole ne ah asibiti?"....
Dariya Sulaiman dinma yayi yace"ahto Ummi nagadai sune suke bada taimako inmutum nada problem na rashin lafiya may be they can help"........
Lol that's how your Brother is naturally you can't change that Ummi takarashe maganar tana yar dariya sannan takara da but kaga ni mukanyi hira sometime and he's open to me so with time inya hau mulkin dole yayi maganar ai tunda yazame masa dole.......
Shidai Almustapha yanajin su bece komaiba Asma'u kuwa se satan kallonshi take tana mamakin shi wai ace mutum magana ma wahala takeyi masa.ikon Allah kenan dan murmushi yayi jin sundameshi da same magana sannan yadubi Ummin yace...
"Ummi fura nikeson sha".....
Kallonshi Ummi tayi da mamaki tana...
"Daman haryanzu kananan da jarabar shan fura Imam?",shidai shiru yayi bece mata komaiba yayinda Ummi tadubi Asma'u tana"Daman yana yawan shan fura haryanzu?"....
cikin sauri Asma'u ta girgiza kai alamar aa don tama rasa mezata ce yar murmushi Ummi tayi"cab lokacin da Imam na karami bana iya rabuwa da fura da Nono to kullum seyasha kamar jaraba inko babu yadinga kuka kenan haka zaihanamu bacci ranar"......
Asma'u batasan sanda dariya ya kubce mata ba she's just imagining him crying like a baby yayinda dayan bangaren na zuciyarta ke tambayarta miyasa to bata taba ganin yasha fura ba tunzuwanta gidan hakanan kuma bata taba gani su Jamila na hada mishiba......
Abunda basu saniba shine Almustapha haryanzu yanason shan fura da Nono sede tunda Ummi takwanta rashin lafiya besake sha ba don duksanda yakalli fura da nono ko ah kasuwa ne seyadinga tuna yanda Ummi ke dama mai ada lovingly toko ya siya baya iya sha yadinga tunanin mahaifiyartasa kenan dukda kuwa ranshi naso toyau kuma seyaji yanason shan furar data dama da hannunta amma seya lura yajama kanshi raini ne tunda Ummi ended up gisting his wife about his childhood............
Hararar Asma'un yayi dayaga tana mai dariya sannan yayi wucewarsa daki Sulaiman ne yace"I text him zezo gida in the evening"......
To kawai Almustapha din yace mishi sannan yayi wucewarsa daki dariya Ummi tayi kafin tace"Da akwai wata mata ta'iya fura sosai harcikin masarautarnan take kawo mana kullum Nono kuma akan tatsa daga jikin shanayen masarautar ne so fresh sekin gani lokacin gwanin ban shaawa ",koina Matar take yanzu oho.....
Ummi tayi maganar ahankali......
Asma'u ne tace rayuwarkenan Ummi inda rabon kisake ganinta zaki sake ganinta insha Allah nima kakata ta'iya fura haryau bansake shan fura maidadi irin nataba.........
Kallonta Ummi tayi sannan tace"you must be missing her I know?'.....
Murmushin dayafi kuka ciwo kawae tayi don harga Allah tanason ace Itama tanada kaka mesonta me goya mata baya hakanan tana pampering dinta kaman yanda taga anayima wasu yaran sede ita Allah baibata wannan gatan ba tunda kakkaninta na bangaren Uwa duk Allah yayi musu rasuwa se Hajjan ne dama itakuma tadauki karan tsana ta daura musu gashi tayi aure ma koneman inda take batayiba........

★*★

Koda Magajiya tashiga dakin nata samun Zaliha tayi azaune se kumbure kumbure takeyi itakanta oganniyar afusace tashigo...........
Dasauri Zaliha tatashi tana......
"Mama kinga abunda Mai Martaba yayi ko?"....

Zama Magajiyan tayi tana sosa jikinta gabadaya yanzu jikinta yadameta da kaikayi fiyeda nadama donta lura kaman abunma gaba yakeyi gawasu kuraje dake fito mata ah skin dinta yanzuma data rasa na menene kuma bawani kyaun gani Allah yataimaketa acikin jikine ma dakyar ta'iya barin susan jikin kafin tace"bantaba tunanin zeyimin hakaba wallahi all I was thinking shine ke zaibamawa tunda ke babba ce amma tunda yayi haka to bazata sabuba don bazan taba bari wata data keda dangantaka dasu tayi taking hold of this responsibility ba,tayi kadan wallahi", Magajiya takarashe maganar tana huci.......
Nima bantaba tunanin hakanba Mama amma tunda yabatan babu matsala nalura shiru shiruce kumama dabakinta tacemin bataso dazu damuka fita daga bangaren Mai Martaba din wai sabida bazata iya dubanshi tace bataso bane yasata karban responsibility din so, ni aganina zan kula da komai zannuna nafi zakewa harma shi Mai Martaban dakanshi yadawo yabani bakidaya"....
wani kallo Magajiya tayima Zaliha don itadai bata tunanin Asma'u bazatayi wani abuba donta lura Asma'u is naive and cunning tun ranar datazo takwaci Talatu ah hannunta so bazata taba bari tahada hulda da'ita bama ita abunda tayi deciding shine tafasa yarda da sharawan databama Mai Martaba din ita zatacigaba dayidin kawai har susamu mulki yadawo hannunsu baki daya seta mayar da aikin ma Zaliha din............
"Ninasan abunda zanyi goben so kada kidamu kuma dukyanda kikaga nayi kigoyamin baya because it's the best for you".......
Gyada kai Zaliha tayi dukda kuwa tana mamakin me Magajiyan zatayi kuma wani mataki zata dauka sede koma meyene she has full faith in her...........

STORY CONTINUES BELOW


**★**

Bayan la'asar Jamila tashigo hannunta rikeda kwaryan Nono dakuma ledan fura wanda Ummi ne tasata tasamo mata don tanason dama ma Almustapha din tunda yace ranshi naso......
Ajiyewa tayi sannnan tace Aunty ga fura da Nonon murmushi Ummi tayi kafin tace bude mugani Jamila Allah dai yasa fresh Nono ne beyi tsamiba kinsan Imam da zabe.......
Bude kwaryar Jamila tayi yayinda Ummi tasa hannu tadan taba Nonon cewa tayi"yauwa babu tsami se ah tace shi ajuye ah roba kusaka shi ah fridge indare yayi zandama mishi kafinnan yayi sanyi".......
To Aunty nima nayi kewar damunki wallahi,dariya Ummi tayi tana yau zakisha ai karki damu daukan kwaryar Jamila tayi har zata fice Ummi tace yauwa Jamila inkin gama tace Nonon keda Hindatu zaku raka Asma'u bangaren da bayi ke rayuwa dakuma inda suke aiki cewa tayi To Aunty barina gama semuje kafin tafice don aiwatar da abunda aka saka tadin........
Asma'u kuwa tana idar da sallar laasar Talatu tafado mata arai don haka tana gama addu'o'inta tafice zuwa gurinta........
Samunta tayi zaune kan sallaya taidar da sallah itama murmushi Asma'u tayi mata kafin tace "Ya zaman kadaici?"....
Murmushi kawai Talatu tayi kafin Asma'u tace kinci abincin rana kuwa?.....
Naci Gimbiya Talatun tayi maganar ahankali kafin tace dazu muna magana bamu karasa ba kika tafi.........
Eh wallahi Abba kenema na shiyasa kinga kuma babu dadi inbarshi yana jirana tunda ke ai kinanan zamu iya karasa maganar koyaushe ma shiyasa ma yanzu nazoni tunda babu abunda nikeyi", Asma'u takarashe maganar tana gyara zamanta Talatu ne tace hakane kuma.........
Dan kallonta Asma'u tayi kafin tace nibanason ace kintonamata asiri nafison itada kanta tatona makanta asiri takuma fadama duniya abunda tayi sannan in akwai shaida dazaki bayar sekema kibayar kinji..........
Cikeda damuwa Talatu tace...
"to kina tunanin zata tona makanta asirin ne Gimbiya, lallai bakisan waye Magajiya ba".......
Cikeda confidence Asma'u tace"time will tell,babu yanda za ayi ace kacuci mutane da dama haka sannan ace asirinka bazai taba tonuwa ba Talatu nidai taimako daya zakiyimin ayanzu"...........
To Gimbiya cewar Talatun kafin tayi shiru tana sauraren Asma'un cikin sanyi Asma'u tafara magana.....
"Nasan kinada masaniya akan duk wani al amura na tsakanin Mai Martaba da Mahaifiyar Yarima,nasan kinada masaniya akan sharri akayimata koba sharri akayimata ba",cikin sauri Talatu tace"sharri ne wallahi Gimbiya ni shaidace,wayene zai aibata wannan baiwar Allahn acikin gidan nan,wayene besan halinta nagariba sede in aki fadin gaskiyar kokuma sede in kowa yayi shiru sabida tsoron kada ya tsoma kansa ah halaka amma Sarauniya Khairiya mutumiyar kirkice,macece mai kamala dasanin darajar dan Adam......
Magajiya tayi makirci dayawa don ganin taraba Mai Martaba da matarnan amma takasa sabida tsananin shakuwar dasukayi da juna gakuma yarda dasukayi da juna don duk gulmar dazaka kaima matarnan akan mijinta kowa shaidana bazata taba yarda ba hakanan shima sunsan abunda kowannensu zai iya dawanda bazai iya ba shiyasa Magajiya dataga babu halin hadasu fada tahanyar makirci yasata komawa gun boka yataimaka mata harta aiwatar da niyarta.........
Asma'u da itanunta suka canza launi lokaci guda tace...
"ikon Allah me bokan yayi don Allah?"....
Murmushin takaici Talatu tayi sannan tace"Magajiya bata zuwa gurin bokanta da kowa Gimbiya shine gaskiyar magana koni danake kusanci da'ita sede inra kata injirata daga can nesa harta gama abunda zatayi mu dawo gida kuma dai yakai sau biyar yana bata laya wanda duk bansan namenene ba kuma gaskiya ba a lokaci daya yabayar ba guda uku nasan dai awajen gari narakata ta binne su bayan wata bishiyar kuka wanda nikaina bansaniba kozan iya ganeta yanzu kokuma ma bishiyar nanan ko batanan kingadai abun yajima gaskiya..........
Innalillahi wainna ilaihir rajiun shine abunda Asma'un ke fada yayinda idanunta ke zubar da kwalla babu control sannan cikin kuka tace alokaci daya ta binne laya guda ukun ne?........
Jijjiga Mata kai Talatu tayi alamun a'a kafin tace..
"akwai ratan shekaruma ah tsakani sede inada tabbacin aguri daya ta binne".....
Kinga nafarkon daya bata tacemin ah dakin Mai Martaba zata binne shi dukda bansan tawani bangare bane tunda badani tajeba........
Se dayan kuma ah fada inda yake zama karkashin kujerar dayake zama.......
To sauran ne duk take sawa ah wajen gari din karkashin bishiyar kuka to matsalar yanzu bamusan wannene na sihirin da akayiwa Mai Martaba ba tunda shine babban matsalarmu yanzu Gimbiya......

Goge kwalla Asma'u tayi kafin tace"zezama na dakin nashi ne Talatu insha Allah zan bincika"....

Cikin sauri Talatu tace ta'ina zaki fara wannan garajen dakin da anyi masa gyara yafi ah irga yanzu terazo nema akasan kuma nasan cikin kasa ta binne.........
Murmushin dayafi kuka ciwo Asma'u tayi kafin tace"wannan bashine damuwana ba Talatu damuwana shine inga Ummi tasamu right dinta,Inga Ummi tafita daga zargin da aka jima anayimata tunda yanzu tafara samun lafiya with time zata fara fita and that's when people will start talking gwanda ayita ta kare,gwanda mahaifiyar Yarima sunanta yawanku ah idanun jama'a wanda hakan yasa akeyima Yarima kallon mutumin dabaida da'a,mutumin da baya kallon mutuncin mata,mutumin da bedauki darajarsu abakin komaiba bayan ni in my eyes he's the best person I've ever known sabida Mijina mutum ne da namijima bai isheshi kallo ba bare azo kan mace, I'm a witness Talatu I've seen it with my very own eyes nazauna da Almustapha fiye da wata yanzu amma ni haryau banga yayi abunda mutanen Zaria ke zarginshi ba haka Ummi she's the purest soul I've ever known,cikin kuka Asma'u tace tomiyasa za a cuci mutane irin wannan?.....
Laifin me sukayi,why will they be punished for someone's mistake please?......
Magana takeyi tana kuka mai tsuma zuciya se yau take ganin bata taba ganin cruel mutum like Magajiya ba and she'll pay for her sins for sure, azuciyarta tana raya laya har biyar?....
Kenan tayima wasu asiri bayan Ummi da Abba komi hakan ke nufi?,tokomadai miyene she'll try her very best taga ta karya wayannan sihirurrukan......
Talatu dake kallon Asma'un cikeda tausayawa don seyanzu tagane sun cuci mutane da dama wanda basumayi deserving ba tsabar selfishness irin nasu da rashin tunani jitayi Asma'un tace zansamu lokaci zaki rakani bayan garin don Allah muje mucire layoyin nan sabida bamusan har mutane nawa bane suka cutu sabida hakan na dakin Mai Martaba dana fada kuma ninasan yanda zanyi insha Allah.............
Girgiza mata kai Talatu tayi ahankali sannan tace basai kinjeba Gimbiya nizan je dakaina......
Cikin sauri Asma'u tace aa Talatu bazakije kekadai ba bazansaki kidauki wannan risk dinba murya ah karye Talatu tace wannan na daya daga cikin hukuncina Gimbiya kibarni inyi don Allah nayimiki alkawari bazan dawo cikin masarautar nanba harsai nacire wayannan layoyin ........ 1

Gyada matakai kawai Asma'u din tayi donta lura bazata hakura ba kafin Talatun takuma cewa"sede zaki taimakamin wurin fita daga masarautar nan batareda kowa yasaniba sabida Magajiya tanada wayau sosai kuma tanada mutane masukai mata duk wasu labarai sannan kema kiyi ahankali bako inazakina fadar magana ba kamar yanda nafada miki tako ina tana da mutanenta".....
Gyada kai Asma'u tayi sannan tace"nagode sede fitar nakine bansan yazaayiba?"......
'koda asubama in dogaraye sunshiga sallah zamusan yanda za ayi",cewar Talatun.......
Godiya Asma'u tayi mata kafin tace barina koma cikin gida akwai inda zanje yanzu......
"To Gimbiya",tashi Asma'un tayi tafice jiki ah sanyaye........ 1

Kicibis sukayi da jamila tafito daga kitchen hannunta rikeda robar dake dauke da Nono cikinta tagama tacewa xata saka ah fridge don yayi sanyi...........
Cewa tayi yauwa Gimbiya dama yanzu zanshiga gurin ki nagama tace Nonon Aunty tace zamuyi maki rakiya nida Hindatu.........
Asma'u da idanunta suke jazur tsabar kukan datasha tayi faking smile sannan tace to Iya Jamila ba indauko mayafina semuje ko aikuwa hakan akayi bata jima ah dakin ba tadauko mayafinta tafito suma samunsu tayi ah parlour suna jiranta nan sukayi gaba seda sukayi tafiya mai nisa kafin suka iso kitchen din masarautar tundaga bakin kofa Hindatu tace barimu fara daganan Gimbiya......
Gyada musu kai kawai tayi kafin suka kutsa suka shiga kitchen din......

Post a Comment for "GIDAN SARAUTA CHAPTER 8"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...