Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

GIDAN SARAUTA CHAPTER 6

GIDAN SARAUTA CHAPTER 6

- - Post a Comment
GIDAN SARAUTA

CHAPTER 6

Yana nan zaune sega Sulaiman yashigo cikin sauri"Yaya Almustapha mekama yar mutane take kuka?",donshi Sulaiman bawai yasan abunda yafaru baneba daya gama waya bangarensu Mubaraq yayi so, yafito ah bangarensu Mubaraq yaga wucewar Asma'u tana kuka shiyasa hankalinshi yatashi yataho gurin Yayan nashi don jin ba'asi............
Jin Almustapha yayi shiru yasashi kuma cewa "Yaya Almustapha mekayi mata please?"...
Wani harara Almustapha ya watsa mishi sannan yace we're going home right now.........
Riko hannunshi Sulaiman yayi calmly sannan yace alright zamu tafi ai semu tsaya mugaisa da iyayenta ko?....
Gyada kai kawai Almustapha yayi mishi yayinda Sulaiman yaciro wayarshi yakira Aliyu inda yake fada mishi su zasu tafi kuma sunason gaisawa da Daddy inyana gida dasu Ummi kuma......
Okay ganinan zuwa prince cewar Aliyun katse wayar Sulaiman yayi sannan yace"he's coming".........
Sunanan zaune har Aliyu yashigo nan yace sukarasa bangaren Daddy din atare suka fita zuwa parlourn Daddyn sallama sukayi,inda ya amsa,samunshi sukayi ah kwance kan three seater idanunshi sanye da medicated glasses yana karatun news paper.............
Tashi yayi yazauna calmly yana binsu da kallo,Almustapha kasa dagawa yayi ya kalli Daddy din don wani irin kwarjini yaji mutumin yayi masa samun guri sukayi suka zauna inda Sulaiman yafara gaida Daddyn blankly ya ansa yayinda Almustapha dinma ya gaidashi kanshi ah kasa kallonshi sosai Daddy yayi don yagane shine yaron da zai auri yartasa seyaji zuciyarshi na raya mishi "he's not that bad",and dubada yanda yaron yagaida shi cikeda ladabi seyaji hankalinshi yadan kwanta da Almustapha din,tambayoyi yashiga yi musu kan karatunsu dakuma aikin dasukeyi dukansu wanda mostly Sulaiman ne ke responding comfortably ana cikin haka sega Mommy tazo nan suka gaida ta cikeda ladabi, Aliyu yasamu Ummi ah dakin Asma'u tana lallashinta tana kuka sekawai yafasa fada mata kan tazo su gaisa da Almustapha din seya juya cikeda tausayin kanwartashi........ +

Sanda su Almustapha suka fito daga bangaren Daddy fadawan sukayi saurin bude musu mota suka shige harzasu rufe sega ikram dagudu hannunta rikeda phone din Almustapha tana"Uncle wait,your phone".....
Kallonta yayi adoringly sannan yadan saki murmushi,Mika mishi wayar tayi sannan tace"nagode".....
"You're welcome,shine abunda yafada mata",yayinda aka rufe motar suka wuce gida..........
Mommy dayanzu fitowarta daga bangaren Daddy tadubi Aliyu tace jeka kira Ummi inji Daddyn ku......
To Mommy yabata amsa sannan yajuya zuwa bangaren Ummi din yanda yabarsu dazun haka yasamesu yanzuma sede yanzu Ummin tambayar Asma'u takeyi meye dalilinta nayin kukan.......
Cikin kuka Asma'u tace"wai bayan dalilin dana sani kodai akwai abunda mukayima Hajja ne Ummi,kifadamin don Allah Asma'u tayi maganar zuciya ah karye.....
Riko hannunta Ummi tayi in a comforting manner tace"wani abun Hajja tayi miki?".....
Eh mana Ummi muna parlour kawai ta bankado kofa.nan Asma'u tashiga bama Ummi labarin abunda yafaru salallamin Ummi tashigayi cikeda mamaki yayinda nata idonma yacanza kala ita kanta tarasa yaushe ne Hajja zata sauke Kai ta hakura takarbeta amatsayin suruka ita babu abunda yafi damuntama irin yanda laifinta ya shafi Ya'yanta aiko bakomai Asma'u jikartace inma tana tunanin ita bata hada dangi da'ita ba......
Sa hannu Ummi tayi tana goge ma Asma'un kwalla sannan tace kiyi hakuri watarana zai zama labari in Sha Allahu Kuma ma kigode Allah da yaronnan bai biye maganarta ba and despite knowing all your flaws yayi accepting dinki hakan na nufin mutumin kirkine shi dear Ummi takarashe maganar in a comforting manner don ita kwata kwata batasan Almustapha bane mijin...........
Aliyu dake tsaye bakin kofa yanajin duk conversation dinsu ranshi bakaramin baci yayi ba dakyar ya iya controlling kanshi yayi sallama Ummi ce ta amsa mai sannan yadan saki murmushin yake yace Ummi Daddy nakira.......
Kace inazuwa cewar Ummi din,to yace sannan yafita yana tunanin matakin daya kamata yadauka kan Hajja because abunnata yayi yawa daya ma aka samu aka hanata zuwa yima Asma'u test din cutar kanjamau data sa jarabar sai anje yasan koya fada ma Daddy ba lallai ya iya taking action ba tunda shima danta ne don haka yasama ranshi tafiya Batagarawa washegari Kawu kadai zai iya maganin Hajja tadawo saitin ta..... 1

STORY CONTINUES BELOW


Sanda Ummi taje parlourn Daddy samun Mommy tayi ah zaune daga can gefe Daddy ne yace ya akayi bakizo kun gaisa da bakiba?..
Shiru tayi don tarasa mema zatacemishi because Allah yagani bazata iya budan baki tace mishi Asma'u ta tsaya lallashiba don seya nemi baasin kukan Asma'u din itakuma batason akai ga wannan gandun don haka setayi shiru ran Daddy yabaci "Maryam baki suzo sunason kugaisa amma kika ki fitowa batareda kinada wani kakkwarar daliliba,to inma fushi kikeyi don zan aura ma Almustapha Asma'u to kisani fushin ki bazaisa infasa ba", Ummi tunda Daddy ya ambaci Almustapha tadinga jin gabanta na faduwa don ita batasan wanene Daddyn ze aurama Asma'u dinba seyanzu dayake fada jitayi idanunta sun ciko da kwallah she has so much to say sede tasan kota fada basuda anfani don Daddy bazai canza raayiba sabida haka tayi Kim da bakinta,rai bace Daddy yace ba magana nike mikiba Maryam?......
Muryarta na stammering yace kayi hakuri tsaki yayi sannan yace to komadai miyene kidaina dora ma kanki damuwa akan Asma'u don komi yafaru ita tajama kanta and nakiraku sabida inji miye raayinku batun biki yarannan tun kwanaki nayima iyayen Aslam magana kan mujanyo bikin inason inhada dana Asma'u sede ban basu specific date ba shiyasa nakiraku inji ta bakin ki auren Asma'u da Asiya bazan jashi da nisa ba sabida daga ni harku munga abunda yafaru Kuma bamu fatan hakan yasake faruwa...........
Gyada Kai sukayi dukansu atare sannan yace daman inason inji ra'ayinkune kunason muhada bikin dana Mubaraq ne kokuma ayi separately.......
Mommy ne tayi gyaran murya sannan tace tabbas da da Hali gwanda ahada din kawai muna mu huta lokaci guda don biki akwai gajiya sede bamusan bangaren gidansu yarinyar ba if they're ready or not karya zama kaman mun takurasu....
Ummi ma cewa tayi hakane kam.....
Reasoning maganar tasu yayi sannan yace"kunyi magana mekyau zanyi magana da iyayen nata inji inma zasu takura in aka matsoda bikin zasu fada,duk yanda ake ciki zakusami...

Allah yazabi abunda yafi alkhairi cewar Mommy, Daddy na lura da yanayin Ummi don haka yace Maryam kibi abunnan da addu'a insha Allah Allah zai shige mana gaba......
Gyada mishi kai tayi kawai don itakadai tasan yanayin datakeji,damuwarta daya maganar mutane dama kuma halin da yarta zata shiga ..........

******
Tunda suka koma gida Sulaiman ke aikin tambayar shi dalilin dayasa Asma'u kuka amma ko kallo inda Sulaiman din yake beyiba yayi wucewarshi dakin shi don cire wannan nannauyar kayan daga jikinshi sannan yashige bandaki don watsa ruwa yakumayi alwalar maghrib sabida time yakusa..........
Ah masallaci suka hadu dasu Dad inda Dad ketambayanshi ya Daddy dakuma Asma'u dasauran yan gidan su.....
Lafiya Lau shine amsar da Almustapha yabama Dad din.......
Murmushi Dad yayi sannan yace in Sha Allah cikin satin nan zamuje tambaya maka aurenta....
Gyada Kai kawai Almustapha yayi donshi kanshi yarasa amsar dazai bashi alqur'ani Sulaiman yadauko musu nan suka shiga muraji'a seda akayi sallar Isha sannan suka wuce gida inda Mai Martaba yace yanason ganin Almustapha din washegari da safe.....
Suna shiga gida yawuce daki abunshi dukda kuwa yanda yaga sunata hira ah parlour wanda Mom,Afiya, Sumayya da Amira ne kezaune yaran nata hayaniya Mom na kallon TV ga Sulaiman da Daddy ma sun jona su dasuka shigo yanzu shiko bazai iya da surutunsu ba ciwon kai zai iya saka mishi shiyasa ma yayi wucewarsa daki.............

Dad ne yadubi Sumayya da taketa kumbure kumbure yace "Sumayyan Dad".....
Turo baki tayi tadubeshi yar murmushi yayi sannan yayi mata alama da datazo gurinshi babu musu takarasa gefenshi sede expression nafuskarta baicanza ba don tun ranarda aka hanata komawa school take musu irin wannan fuskar gabadaya tarage walwala wai ita adole fushi takeyi,rike hannunta yayi cikeda damuwa sannan yace"Sumayya don anfada miki gaskiya shine kike fushi?".....
Jijjiga kai tayi alamar aa,jan hancinta yayi "toki saki ranki no wasa nike miki kishirya xaki koma school cikin satinnan"....
Wani irin zare idanu tayi cikeda excitement tana"Dad dagaske kakeyi?"....
Gyada mata kai yayi wani irin rungume shi tayi cikeda murna "thank you
Thank you
Thank you Dad,I'm so happy"......
Seki fara shiri cewar Dad din Sulaiman dake gefe yana kallon yanda take murna seyaji dadi ah ranshi yanzu kam kobaiyi admitting yana son Sumayya ba to tabbas akwai burbushin sonta dakeson kamashi kwana kusa....

STORY CONTINUES BELOW


Afiya ne tace nidai banso kitafi we'll miss you,tabe fuska Sumayya tayi"I'll miss you more lovely Sisters dina sekuma yanayinsu yacanza baki daya Mom ne tace mezai hana suma anema musu makarantar tare acan.....
Ware idanu Sulaiman yayi sannan yace ai Ina su Afiya basuda wani foundation ss2 fa suke and karatun nasu bawai yazauna bane Mom so,I don't think this's a very good idea.....
Dad ne yace basuyi waec bane?....
Wallahi basuyi ba Dad karatun ma dayaya suka kawo ss2 din inason innema musu school mekyau sufara zuwa sabida susamu foundation mekyau da naso suyi waec this year sede nalura in mukayi hakan mun cucesu because abubuwa dayawa basu saniba insuka tafi University Kuma ahakan they'll suffer ......
Kayi magana mekyau Sulaiman seka duba musu in anshiga sati tunda kaga su mata ne kuma girma sukeyi babu lokaci ga Sumayya har tana aji uku ah jamia....
Ah to cewar Mom sannan takarada nikam daza abi nawa wallahi kawai suyi waec din yara sungirma kuma watarana aure zasuyifa dole dama namiji ne se ah bata mishi lokaci wannan na matsala baneba........
Dad ne yace aa Dear maganar sulaiman din akwai point ah ciki gaskiya we're in a situation whereby iyayen yara suna babban kuskure kowa kawai soyake yaga Danshi yagama karatu baswa tunanin shin yaran sunyi achieving abunda yakamata dakuma baswa tunanin how hard the studies will be for them don su Amira suna yanmata baza ace suyi jumping ba mutane nawa da girman nasu suke karatun sannan akwai masuyi ma ah gidan mazajensu Kuma hakan baisa sunyi failing ba baresu Amira dakeda karamin jikima kawai mubisu da addu'a zanyi magana da Abdulrahman din gobe Sulaiman Dad yakarashe maganar yana kallon Sulaiman sannan yace inyaso cikin sati seku fara process din nema musu makarantar tunda ana first term ne ma karatun beyi nisaba they can catch up......
Gyada kai Sulaiman din yayi.......
Dad ne yakuma duban Sumayya kishirya kekuma ranar Tuesday zaki tafi in Sha Allah......
To Dad cewar Sumayya din......

*****
Tunda tayi sallar isha takejin kanta nayi mata ciwo kuma tasan bazai wuce ciwon yayi tasiri daga kukan datasha bane tananan zaune kan sallaya Mubaraq yashigo dakin"Ma'u Lele?"....
Na'am Yaya Mubaraq Ina wuni?...
Lafiya Lau ya amsa gaisuwar tareda zama gefen gadon dakin observing fuskarta yayi sannan yace "kuka kikayi ne?"....
Murmushin yake tayi sannan tace"aa Yaya kaina ke ciwo"...
Sorry Allah yakara sauki don baiyi tunanin karya takeyiba sabida Aliyu beyimusu maganar abunda Hajjan tayiba........

Sa hannu yayi ah aljihunshi yaciro waya sannan yace ga wayar ki Daddy yace indawo miki da'ita and please make use of it properly kada insakejin wani abu dazaisa ah zargeki Asma'u kindai ga abubuwan daya faru...
Cikeda murna tace"insha Allah Yaya Mubaraq, thank you so much"...

Murmushi kawai yayi mata sannan yadinga mata nasiha tareda bata shawarwari kafin daga karshe yace yamusu subscription itada Asiya din yanzu zaibama Asiya nata, godiya takuma yimashi kafin yamata saida safe.ninke sallayar ta tayi sannan tarufe kofar dakin takunnan AC tareda kashe wutan dakin komawa tayi kan gadonta ta kwanta tanajin wani dadi aranta atleast yau tasamu abunda zai rage mata loneliness nata tayi kewar kawayenta dama kuma wayartata kanta kunna wayar tayi Allah yataimaketa akwai charging har 80% ma kunna data tayi inda massages suka shiga shigowa babu adadi wanda duk yawanci *Waiting for this massage* yake cemata tsaki tayi aranta tana matsalar kajima baka hau WhatsApp ba kenan massages na Aisha da Zahra ne suka fi daukar hankalinta don tafi kewarsu fiyeda kowa sede kayan haushi suma nasun waiting for this massage yake cemata shiga inbox dinsu tayi tamusu massage da " *resend your massages please* ".......

*****
Tunda ya shiga dakin cire jallabiyar jikinshi yayi yakwanta kan gado bayan ya kashe wutan dakin so yake yayi bacci amma gabadaya tunanin yarinyar yadameshi ko ya take ciki,is she still crying shine tambayar dayayi ma kanshi.....
Tsaki yayi ahankali sannan yacanza direction din kwanciyarshi tareda lumshe idanunshi amma still fuskar crying Asma'u yake gani sake juyawa yayi ta bangaren dama yakuma rufe idanun nashi sede abun mamaki itanne ke mishi gizo ah idanu still wannan karan tashi yayi yazauna cikin sauri yasan tabbas yanada tausayi and he hate seeing people crying most especially mace ma abun yakan dameshi sede bakaman yanda na Asma'un yadameshi yauba...........
Wata zuciyar ne tace mishi may be sabida you're the reason for her sadness ne,anyi involving nata ah case dinka bayan itabata da laifi furzar da iska yayi sannan ya furta"why is she involved in all this?",sekuma ya tabe bakinshi sannan ya tsinci kanshi da daukar wayarshi hakanan yau abunda bayayi kenan tunda Sulaiman din yamai setting komai na wayar.....

Apps din yashiga gani da Sulaiman yamai installing ahankali yadinga shiga daya bayan daya yana gani sede ya lura ba ayi registration na sauran ba daga Facebook se WhatsApp ne kawai Sulaiman din yabude mishi yanzu haka yanakan WhatsApp ne don yalura massages se shigowa yakeyi mamakine yakamashi bude inbox yashigayi ashe Sulaiman yabi all his contacts dasuke WhatsApp yatura musu hlo sannan yayi adding nashi ah groups sunkai uku wanda biyu na family ne daya kuma besan na menene ba yanakan bin contacts din ya iso kan wani suna da yadauki hankalinshi anyi saving da *Miss Unique*.........Yajima yana kallon contact din sekuma yaga anyi replying massage din da Sulaiman yatura da Hi........
Seda yayi like three minutes kafin yabude shiga display picture yayi inda yaga hoton ikram da wata wanda yake tunanin Yayarta ne don suna mugun kama lokaci daya ranshi yabashi Asma'u ce contemplating yashigayi ko yamata massage ne typing yashigayi ahankali....

_"kindaina kukan ne?_"
Wata zuciyar ne kuma tace mishi massage din beyiba,gogewa yayi sannan yasake fara typing kuma....

" _Natambayeki dazun bakibani ansaba?_"...

Shidinma gogewa yayi daya tuna zata ganeshi so easily which means that zata rainashi tace yadamu da'ita,wata zuciyar ne ta tambayeshi "why do you want to send her a massage to?",kasa samun ansa yayi don haka yayi wurgi dawayar can gefe ko minti uku ba ayiba kuma yasake daukar wayar yafara typing ah inbox dinta for the 3rd time......

"Hope you're doing alright now?".....
Yakai sau uku yana gogewa yanasake rubuta thesame senstence kafin daga karshe yayi jihadi yatura dukda kuwa rabin zuciyarshi na tuhumarsa da miyasa yatura matan........Wani bakuwar number tagani da akayi mata sending Hlo dashi sekuma taga meshi nata kokarin typing na tsayin lokaci se tamayi tunanin meshi na son introducing kanshi ne kokuma yaturo mata sako sede da mamakinta taga yaturo short massage........
"Hope you're doing alright now?"....
To me hakan ke nufi don kuwa indai mutum zai turo mata massage irin haka tabbas yasanta setayi reply da "I'm okay,can I know you please?"......
Daman Almustapha befita daga inbox dinba don haka yakaranta yafi minti biyar yana kallon massage din kafin daga karshe yakashe data din ya ajiye wayar gefe tareda lumshe idanunshi sannan yafurta"atleast she's okay now"....
Bangaren Asma'u tayita jira maishi yayi mata responding amma shiru sema daga baya data duba taga yasauka tabbas bataji dadin hakanba sabida tanason tasan wayene haka ita kanta batasan dalilin dayasa she's so attracted to the number ba normal massages ne suka shiga shigo mata don haka tafita ah WhatsApp dinta sannan tatafi massage box mostly from MTN ne sena Zahra sunfi biyar duk kan yatake ne,tajita shiru dakuma meya hanata zuwa makaranta..........
Reply tayimata da she'll call her in the morning sabida talura dare yayi yanzu din batason takira Zahra tayi bacci........
Tana cikin wannan tunanin ne sega Ummi tashigo tashi tayi tazauna tana analyzing fuskar Ummin don rabonta da ita tun sanda Aliyu yazo yace mata Daddy nakiranta,zama Ummin tayi gefen Asma'u din tareda taba temperature din jikin 'yartata.....
"Kinci abinci?"...
Shine tambayar da Ummi tayimata... +

Naci tareda su Munira Ummi.....
Gyada kai Ummi tayi alamun gamsuwa sannan tace daman kinsan yaron can ne Daddy ke niyan aura miki...

Asma'u jitayi lokaci guda kanta nasarawa don Ummi tatabo mata tabon datake kokarin healing dinshi by force by fire,bansaniba wallahi Ummi seda naje nima naganshi dago kai tayi da jajayen idanunta tadubi Ummi din tareda cewa "Ummi Allah bana son shi kiroki Daddy yacanza dawani", Asma'u takarashe maganar hawaye na zuba kallonta sosai Ummi tayi talura dagaske Asma'u din takeyi"is he that Bad?".....
Turo baki Asma'u tayi "he's not Ummi infact he's so gentle and nice amma somewhat arrogant"......
Ummi sa thumb dinta tayi tana gogema Asma'u kwallarta Itama batajin dadin abun amma she's being strong for the sake of Asma'u din......
"Bakasamun 100% ae Asma'u,just keep praying inba mijinki bane ba sekiga anfasa batareda anga laifinkiba kwata kwata nasan he's not a good guy sede yazamuyi Daddynki bazai taba canza raayinshiba kinsani ko?.....
Gyada kai tayi jiki ah sanyaye don tabbas Ummin gaskiya take fada....
seda Ummi ta tabbatar hankalin Asma'u din yakwanta sannan tafice zuwa dakinta Itama abun yadameta sede kawai tana boye damuwartane don kada takarama Asma'u din fear amma dai koma miye ne aganinta Daddy bekyauta ba tunda yasan wanene Almustapha kuma ahakan yakeson aurama 'Yarsa though she's impressed by abunda Almustapha din yafada ma Hajja dazun hakan yanuna mata he's willing to marry her Daughter ba forcing dinshi akayiba bare ya wulakanta ta.....
*****
Gimbiya Zaliha daman takanyi excercise dasafe don tun ah gidansu itada yayunta yazame musu kaman al ada ma shiyasa koda tazo nan masarautar Zaria aka kebe mata daki daya tacan waje for this purpose intaje tacanza kaya agurin tayi excercising kafin tamaida normal clothes dinta tadawo bangarenta intayi wanka tazagaya duka matan gidan tagaidasu.....
To yauma tagama excercise din kenan tafito daga gurin tana tafiya yayinda kuyangunta ke biye da ita ah baya,suna cikin tafiya sukaji kaman ana hayaniya awani guri tsayawa tayi sannan tadubi daya daga cikin kuyangunta tace"jeki dubo ihun miyene wannan keyi?"....
Jikina bari yarinyar tajuya tatafi batafi minti uku ba segata tadawo kai akasa tace "Gimbiya dogaraye ne ke fama dawani dattijo yadage seyaga Mai Martaba yanzu"....
Dan tsaki Zaliha tayi sannan tace"seyaga Mai Martaba kuma da sassafen nan,don Itama abun yabata mamaki sosai", ahankali kuma tace sudin miyasa bazasu fada mishiba kilan sakon yanada anfani ne shiyasa dattijon yadamu........

STORY CONTINUES BELOW


Hakane kam cewar kuyangar kafin daya daga cikinsu tace"bazasu taba barinshiba sabida Magajiya tace duk wani sako da akeson isarwa Mai Martaba ita za afara samu kuma yanzu batanan inaga shiyasa suka hanashi".....
Gimbiya Zaliha juyawa tayi tabi hanyar datakejin surutun yayinda suka bita ah baya har suka isa gurin wani dattijo nahango that looks very familiar sede namanta ah ina nataba ganinshi, dogaraye sun zagayeshi suna shirin daga shi su fitar dashi don kuwa
sunyi sunyi yatafi ta sanyi yaki shiyasa suke niyan yimashi
ta karfi yanzun......

Zaliha ne tace kubarshi,dagowa duka dogarayen sukayi suna kallonta kafin suka shiga mika mata gaisuwa ansawa tayi sannan ta sallamesu kallon tsohon tayi sannan tace"Baba lafiya kakeson ganin Mai Martaba da sassafen nan?".........
Folding hannunsa mutumin yayi alamun roko cikeda damuwa yace"don Allah 'yata kitaimaka min inga Mai Martaba mana wallahi abunda zanfada mishi yanada matukar mahimmanci"...

Dan shiru Zaliha tayi nadan dakiku kafin tace"kayi hakuri ba aganinshi da safe se anjima shima inya zama dolene kokuma kabari ranar laraba tunda shine ranar dayake zama da mutanensa privately yaji matsalolinsu......

Marairaice fuska tsohon yayi"Yata bazaki gane matsanancin halin danake ciki bane shiyasa nidai inda hali kitaimakamin",ajiyar zuciya Zaliha tayi don tagaji da lallaba wannan mutumin don haka tace"tsarin gidan kenan sokake ni inkarya doka kenan?"....
Jijjiga mata kai yayi alamun a'a kafin tace "to kagani,inzaka fadi sakon infada mishi to inbadai na sirri bane inkuma bahaka ba kayi hakuri seranar laraba din"........
Nan Gimbiya Zaliha tajuya tayi tafiyarta yayinda kuyangunta suka bi bayanta cikin sauri mutumin yasha gabanta don ya lura she's kind kuma kamar ma 'yar sarkince bayason yayi missing wannan opportunity din sabida yasan samun yaganta akaro na biyuma wuya zaiyi mishi yanzu ma sa a yaci don yafi sati yana zuwa dogarayen na koranshi.........
kallon shi Zaliha tayi yayinda yayi fuskar tausayi yana wallahi 'yata ina tsaka mai wuya yafiya nazo ni nema gurin Mai Martaba kar in mutu da alhakin yaro akaina.......

Laifin me kayi Mallam?....

Cikin sauri mutumin yace babban laifi mukayi akwai yaron damuka yima sharri wanda watane tasaka mu sunana Mallam Audu nakasance inasaida kaji nida iyalina don shine hanyar cin abincin mu kwatsam sega wani mutumi yazo yasameni kan yana naiman intaimaka masa zebani makudan kudi kinsan Dan Adam da kudi yar uwata baremu talakawa damuke tsananan bukatanshi shiyasa ake cutanmu batareda mun ankareba alokacin ma amince masa nayi nace masa zanyi koma miyene aka sakani din nan yafada min yanda zanyi ko alokacin dana tunkari Mai dakina daya seda tayitamin nasiha amma nakiji haka mukazo mukabada labarin karya aka bamu kudi muka tafi...
Gyara tsuguno Mallam Aundu yayi sannan yace"billahil azim 'Yata tunda na tafka wannan kuskuren haryau nake ganin ba daidaiba ah rayuwata karshema kaji na guda goma suka mutum ah dare daya shabiyar sukayita rashin lafiya daga nan nakaisu kasuwa amma akaki sayansu da daraja naki saidawa nadawo dasu gida danaga biyar sunsake mutuwa daga baya shine naje nasayar da goman biyar Kuma babusu babu labarin don sun bata agasken..........
Cikin kuka Mallam Audu yace na talauce yanzu narasa meye yakemin dadi don kuwa tun wancan lokacin da abun yafaru bandamu ba tunda inada sauran kudin da aka bani na cin hanci shimukayi ta anfani dashi harya kare daganan kuma hanyar samu tarufe ko Ina naje neman aiki kaman asiri se aki daukana yanzu haryakai gabar da zamutashi nida iyalaina murasa abunda zamu sakama bakin salatinmu tun wancan satin nadinga bin wanda mukayi aikin dasu amma su sunki zuwa neman yafiyar don inaganin su tukunnan iftila'in be iso kansuba shiyasa nazo masarautar nan don insamu Mai Martaba innemi yafiyarshi dana yaron nan kona samu Inga daidai ah rayuwa na don nikam inaganin hakkinsu ne akaina dan shiru yayi sannan yayi folding hannunsa alamar roko"don Allah kitaimaka min kaman yanda Allah yataimakeki"............
Zaliha cikeda mamakin waye yayi wannan aika aikan tace"bakasan sunan wanda tasaka ka bane?"...........

Cikin sauri yace bansani ba wallahi nasandai sunce macece sabida wani tasaka yanemo mu nikuma bansake haduwa dashi ba tun bayan daya sallame mu amma dai tabbas anan take ......
Dan shiru Zaliha tayi kafin aziciyar ta take raya dole tanemi wanene wannan how could someone stoop so low haka tasan dai ana irin wayannan munafurce munafurcen ah masarautar su sede wannan din kaman yayi yawa.....

STORY CONTINUES BELOW


Duban Mallam Audu tayi sannan tace kaje gida yanzu zuwa yanma seka dawo kafin nan za ayima Mai Martaba magana ko?..
Gyada Mata kai yayi sannan yashiga yi mata godiya tareda sa mata albarka sannan yace kada indawo kuma su hanani shigowa..
Bazasu hanakaba zan fada musu,cikeda jin dadi mutumin yace nagode sosai 'Yata sannan yatafi abunsa......

Bangarenta takoma cikeda al ajabin abun samun guri tayi tazauna sannan tasa aka kira mata safara'u daya daga cikin kuyangunta wanda tasan bazata boye mata komai ba kuma ta lura daman tanason kawo mata gulman Masarautar always..........
Zubewa Safara'u tayi gaban Gimbiya Zaliha tana ranki shi dade Ina kwana.....
Lafiya Lau alhamdulillahi Safara'u tambayar ki zanyi wani abu inafatan zaki bani amsa yanda yakamata banason boye boye......
To ranki shi dade,nan Zaliha tafada mata labarin da Mallam Audu yafada mata sannan tace wakike tunanin zaiyi wannan aikin?....
Cikeda tsoro Safara'u tace"Topha nidai anya nasani"....
Wani harara Gimbiya Zaliha tasakar mata tana"menace miki kafin infara magana?"..
Muryar Safara'u na stammering tace"cewa kikayi banda tsoro infada miki gaskiya".....
Gyara zama Zaliha tayi tareda dora kafa daya kan doya..."ah to seki fadamin kokuma insaba miki yanzunnan"......

Cikin sauri Safara'u tace"nidai nasan ah masarautar babu wanda ya'isa yayi wannan abun se Magajiya donkuwa itake mulkan kowa dukda ma munsa Almustapha ba mutumin kirki bane amma tabbas zata iya yimishi sharri sabida ta muzanta shi ah idanun Mai Martaba"....

Cikeda mamaki Zaliha tace"Almustapha kuma,kina nufin kanin Yarima Sulaiman?...
Gyada mata kai Safara'u tayi sannan tace Yayaanshi dai yayinda zuciyar Zaliha kedauke da dumbin mamaki don ah iya saninta Sulaiman na yawan ambaton Almustapha acikin hirarsu tabbas yana cewa Yaya Almustapha amma gabadaya tayi tunanin inkiyace ta suna tunda ah iya saninta dai babba shike gajan sarauta tunda ance mata Sulaiman zai gaji sarauta to tabbas shine babban 'da namiji kenan kuma tamayi tunanin mahaifiyarsu daya da Sulaiman din sabida sonda yake mishin yayi yawa.............
Ganin tafada duniyar tunanin Safara'u tace shikenan ranki shidade?...
Dawo da attention dinta kan Safara'u tayi sannan tace "bangane ba miyasa Mama zataso bata Almustapha ah idon Mai Martaba bayan 'Danta na cikinta ne'.....
Yar dariya Safara'u tayi"bafa danta bane Gimbiya inaganin bakisan labarin Masarautar nan sosai ba ammadai kowani irin cikakken bayani kikeso zakifi samu gurin Talatu".....
Ahankali tace"Talatu",tanason tuna ah ina taji sunan atake kuma tafado mata arai 'yar hannun daman Magajiya kenan.........
Shiru tayi nadan dakiku kafin tace ah je ah kira mata Talatu din ba afi mintina goma ba segasu sunzo tareda Safara'u din gabadaya Talatu tayi baki tarame zubewa tayi ah kasa tashiga gaisheda Gimbiya Zaliha din nan ta amsa tana kallonta kafin tace Safara'u tashi kitafi......
To Gimbiya cewar Safara'u din kafin tafice, ahankali Gimbiya tace kinsan Mallam Audu me kaji?......
Cikin sauri Talatu tadago zuciyar ta na bugu tace nasanshi zuwa yayi Gimbiya?.....
Yanda taga Talatu tarude tabbas something is fishy sabida haka ta gyada mata kai sannan tace kifada min mekika sani game dashi sabida dazu yazo yanason ganin Mai Martaba yanason fada masa komai dayafaru tsakanin shi da Mama nine nace yatafi yadawo da yanma ....
Talatu kaman zatayi kuka tadafe kirji tareda cewa munshiga uku mukam bamu fita daga wannan ba zamu shiga wani fisabilillahi.........
Gimbiya Zaliha ne tace kikwantar da hankalinki kifada min mana se insan abunyi ko ah tunanin ki nizan bari wani abu yasamu Mama ne?..........
Dan shiru Talatu tayi kafin tafara zayyano mata komai daga karshe kuma tace kinga laifin Uwargijiyata anan Gimbiya?,tayi hakan ne sabida Sulaiman yasamu sarauta tabbas inbata muzanta Almustapha ah idanun Mai Martaba ba Sulaiman bazai taba zama sarkiba ah anyi hakan ma yaya nidai don Allah kisan yanda zakiyi da mutumin nan kada yasamu ganin Mai Martaba don inya fada mishi Uwargijiyata bazata samu fitowa daga inda aka sakataba gashi takicin wani abincin kirki Talatu takarashe maganar tana kuka....
Gimbiya kekanki nasan kinason mijinki yazama sarki, nasan kinason kizama matar saki sabida haka don Allah kirufa mana asiri har mu cinmma burinmmu.....
Gimbiya zaliha ne tayi gyaran murya sannan tace tabbas Sulaiman shizai zama sarki kuma sabida wannan dalilin ne yasa na aureshi sabida ah tsarin gidan mu bamwa auren wanda bazai gaji sarauta ba so kikwantar da hankalinki nima bazan taba supporting Yayanshi yazama sarkiba don nima downfall zezame min ace kaf ya'yan gidanmu sun auri sarki nikuma ace na auri kanin sarki bazai yuyuba cewar zalihi din tana bata rai.......
Cikeda jin dadi Talatu tace nagode Gimbiya.....
Murmushi kawai Gimbiya Zaliha tayi mata sannan tace kikwantar da hankalinki Maman ma inason ganinta amma bazai yuyu ba tunda sun hana....
Godiya Talatu tayi sannan tatashi tafice jiki sanyaye don bakaramin kewar Uwargijiyata tayiba shiyasa gabadaya ta lalace gashi bayi ma batasamun wani fuska daga garesu donkuwa dukkansu gani suke ita wawiyace after abunda Magajiya tayi mata bekamata tacigaba dayi mata irin wannan kaunarba abunda basu saniba shine ita aganinta bedace tacuci Magajiya ba she'll always remain loyal to her..............

STORY CONTINUES BELOW


Bayin kuwa sunsamu Freedom na'yan kwanakin nan wanda shiyasa ma kullum addu'ar su Allah yasa kada Magajiya tafito.......

****
Cikin shigansu mekyau irinta sarauta yashigo parlourn Mai Martaba din sewani kamshi yakeyi nadaban tundaga nesa mahaifin nashi ke kallonshi wanda hakan yasashi feeling uncomfortable samun guri yayi gefenshi can nesa yazauna kanshi ah kasa sannan yace"Ina kwana".......
Murmushi Mai Martaba yayi sannan yace kamatso mana yakazauna daga can Almustapha.......

Bai iya mishi musuba sabida kwarjinin Mai Martaba din don haka yakarasa gaban shi yasake gaishe shi akaro na biyu amsawa Mai Martaba yayi tareda shafa kanshi yanadan smilling nature din Almustapha na burgeshi don yafara lura yanada nutsuwa......

Kaga nasaka zuwa da safennan ko?....
Gyada Kai kawai yayi analyzing dinshi Mai Martaba yayi nadan dakiku kafin yace Dad dinku yazomin da maganar aurenka shine nakeson inji ta bakinka..
kanason yarinyar ne Almustapha?
Yanda Mai Martaba yayi masa tambayar abazato seda kirjinshi yadan buga sannan yarasa amsan dazai bashi shidai yasan bazai iya mishi karya yanason Asma'u ba tunda bason nata yakeyiba........
Jin yayi shiru se Mai Martaba yayi tunanin ko kunyarshi yakeji murmushi yayi sannan yace it's okay amma ka amince da auren ko?.....
Yafi minti uku kafin Almustapha yace "eh",to madallah cewar Mai Martaba din yayinda Almustapha ke feeling somehow yasan cewa this's the best solution indai zaiyima Dad biyayya sannan nabiyu yaga yanda Hajja tayi treating Asma'u jiya so he can't just turn his back on her bayan shine silar wahalarta yakamata yaga komai yakoma normal tukunnan.....

Mai Martaba ne yafito dashi daga trance dinshi tahanyar cewa"Dad dinka zasuje tambaya jibi insha Allah"......
Allah yakaimu cewar Almustapha din ......
Mai Martaba ne yakarada "munason ayi simple biki Son hope you don't mind?....
Nan ma gyada masa kai kawai yayi se Mai Martaba din yaji wani iri seyake ganin kaman Almustapha din zeyi tunanin bayason shi ne shiyasa bayason nuna bikinshi ah duniya shikuma bahaka bane sunyi shawara ne da Daddy kan se Almustapha yazama victorious se suyi bikin crown prince dinshi dama kuma na auren dukda kuwa ahakan ma za a gayyaci jama'a amma daurin aure kawai za ayi don haka yace inkanason ayi wasu events da bukukuwa babu matsala ai se ayi....
Cikin sauri Almustapha yace"aa",donshi daman bawai meson hayaniya baneba....

Allah yayi muku albarka cewar Mai Martaba din kafin yace da anyi bikinka zanfara assigning dinka zuwa gurare kafara aiki dama kuma aiki ah fada kaji sabida mutane susan dakai dakuma capability dinka......
Gyada kai kawai Almustapha yayi sannan yace to...
Sallama yayima Mai Martaba din zuciyarshi dauke da tunani kala kala.......

****
Tun karfe goman safe kawu ya diro garin Zaria wanda Aliyu dakanshi yaje yadaukoshi batareda kowa yasani ba sannan yazayyane masa duk abubuwan da Hajjan tayi donkuwa yasan daya fadama wani ah gidan ba lallai abarshi yakai kara gurin kawun ba kuma shidai aganinshi kawu ne kadai daidai da Hajja don abunnata yayi yawa............

Sanda suka isa gida akacema Daddy Kawu yazo yasha mamaki anma seyace su karaso dashi parlourn shi yana zaune ah parlourn suka gaisa da Daddy sannan yatambayeshi ya mutanen *Batagarawa* duk lafiyansu kalau cewar kawun kafin yace Hajja fa?......

Tana nan kawu sannan Daddy yace kataho baka fadamin ba dakace kanason ganina zanzo har inda kake Kawu kasandai matsalar ciwon kafan ka inkayi tafiya mai nisa zai iya tashi......
Murmushi kawu yayi sannan yace"Muhammadu kada kadamu dakai nike nema har inda nake nasan zakazo kasameni inna nemeka sede gurin Hajja nazoni inason muzanta da itane kan wasu abubuwa dasuke faruwa"...
Cikeda damuwa Daddy yace"Hajja kuma inafatan lafiya dai ko?"....
Lafiya Lau Muhammadu sannan yadubi Aliyu dake can gefe yace jeka cema Hajja nazo inanan bangaren...
Gyada kai Aliyu yayi sannan yafice don zuwa kai sakon kawun ba ajimaba segasu Ummi da Mommy sunzo sun gaisheshi cikeda ladabi sannan suka tafi sannan aka kawoma kawun kayan motsa baki.......
Tunda Aliyu yasanar da Hajja zuwan Kawu taji ta dan rude don tasan haka kawai baxai zo nemanta ba hararan Aliyu daketa hade rai tayi"Wani abunne yafaru zai diroma mutane da sassafen nan?"...

STORY CONTINUES BELOW


Nima bansaniba Hajja yadaice inkiraki ince miki yazo,tsaki tayi sannan ta tashi tana neman mayafinta"munafuki kawai aiko kasan meya kawoshi ma ba fada zakayiba tunda anriga angama asirceka kunyi nisa bakwajin kira",shidai Aliyu bece komaiba yayi ficewarsa daga dakin Hajja din Itama yafa mayafinta tayi tabi bayanshi.ah parlourn Daddy tasamu Kawu din kafin tasamu guri tazauna gaisa wa sukayi fuskarshi babu walwala sannan yace "Yanzu Hajja abunda kikayi kin kyauta kenan?".....
Menayi kuma tayi tambayar ah tsarge......
Hmmm shine abunda Kawu yace kafin yakarada"kinsan mekikayi ai basaina maimaita ba amma dai inason kisani cewa girma yafadi wallahi dagirman ki da komai kidiba kije gaban siriki kina barar baki kuma ma akan jikarki Hajja? Kawu yayi maganar cikeda mamaki don kuwa haryanzu abun na matukar bata mai rai tareda bashi mamaki sosai.......
Daddy dake gefene besan zancen da akeyiba yace"wai maiya farune kawu nifa kunsani ah duhu?'....
Murmushin takaici Kawu yayi sannan yace kada kadamu Muhammadu wannan tsakanina da mahaifiyarka ne zancen....
Hajja dake gefe tayi tsumi tsumi da Ido tana muzurai tace"babu ruwanka ai gaskiya nafada ko ita Asma'un bakasan abubuwan datayi baneba,kakirashi yaron yamaimaita abunda nafada inma karya nayi mata zakaji tunda dai nan daga ni harkai dama kuma uban nata babu wanda baisan abunda tayiba"...........
Girgiza kai kawu yayi "kekam bazaki taba canzawa ba ai kumani mai zai kaini yin wannan aikin yara kananan dakikayi,abunda nakeson kisani shine shi yaron dakike ikirarin kina fada masa laifin Asma'u din shine same Yaron da kike zargi tareda intadin,shine Almustapha dan Sarkin dakikecewa yabata Asma'u din.....
Hajja tunda yafadi haka taji kanta nawani irin sarawa ga tasaki baki because she really can't believe it wai Almustapha shine dan iskan yaron da akefada ya bata Asma'u kuma wai shine yaron da ake gulmanshi agari sabida itadai babu abunda tagani tattareda wannan matashin saurayin illa nagarta dakuma haiba,babu kuma wani abu datagani tattare dashi marar kyau sema nutsuwarshi dama iya magana tana stammering tace"w...a...i da...ga..ske kake ko wasaaa Kawu?.....
"Iyi shidinne dai wanda kike zagin kuma kikeson shalelen jikarki ta aureshiba sabida kisamu shiga,to kisani Hajja babu wanda ya'isa yahana auren Asma'u da Almustapha indai ina raye sede in Allah beyiba kuma indai bawai iyayenshi ne suka fasa ba,inanan dake wataran zakizo kiyi nadamar abubuwan da kika fada hakanan inanan dake zakizo kiyi danasani abunda kikema Maryam da Ya'yanta dan tsaki kawu yayi sannan yakarada tunda nake Maryam bata taba bata min ba bareta batama Yan uwana hakanan cikin garin Batagarawa duk wani danginmu yabonta yake amma ke kin rufe idanunki kin ki karban gaskiya bayan kiri kiri kinsan cewa babu laifin datayi miki"Allah Hajja kituba kikarbi jokokinki in Maryam tayi miki laifi su miye nasu laifin", baffa yakarashe maganar yana kallon Hajja....

Ranta bace tatashi tace"kayi ka gama babu abunda zai canza araina daga xargin danakeyi musu aini danasan shine wallahi ko inda suke bazan kalla ba kuma kasani Asiya ma ba sa'ar yin shi baneba tafi karfinshi wallahi tana kaiwa karshe tafice tabar Kawu zaune gurin....
Murmushin takaici yayi sannan yabita da kallo yasan tasan gaskiya she just don't want to accept the truth ne ........
Duban Daddy yayi dayake zaune speechless donshi yarasa gane kan zancen yanason karin bayani amma yasani kawun bazai fada mishi ba don haka yace kawu dazun suka kirani ma kan zasu kawo tambaya jibi in Allah ya yarda............
To alhamdulillahi cewar Kawun kafin yace nima banga takomawa ba se in tsaya in angama komai se inkoma don na lura Hajja nada matsala.....
Kawu babu matsala zaka zauna anan din batareda wata damuwa ba?....
Gyada masa kai Kawun yayi don yasan halin Hajja intayi niyar bata abu setayi dangwanda shidin tana shakkunshi tunda koda take matar Yayanshi yagirmeta sosai daman............
Haka aka gyarama Kawu guest room aka saukeshi anan......

Bangaren Asma'u kuwa batasan daliliba duksanda tahau WhatsApp dinta tadinga duba mewancan number din koya hau online amma shiru hakanan kuma babu ko display picture bare tasan ko wanene hakanan baya cikin duk wani group datasan tana ciki she don't know why amma dai tanada strong feeling nacewa they somehow have some connection!a very close connection! tunda ma har yake tambayar yatake,jiya da dare tajima batayi bacci ba tana kissima wayene wannan din sede duk tunanin ta bata kawo kowa ba seyanzu nema taji tafara tunanin kodai Sulaiman ne tunda jiya yaganta tana kuka donkuwa tasan dai ko giyar wake tasha Almustapha bazai yi mata magana ba bare har yatambayi wayene ita dawannan tunanin ne tayi saurin daukar wayarta ta kunna data sannan tasake tura massage kamar haka...

STORY CONTINUES BELOW


" _Yaya Sulaiman ne?_"

Sede koda ta tura baya online sekawai tasauka abunta....
Daman tunsafe Zahra takirata dataga massage dinta cikeda kewan juna sukayita hira yayinda Zahran tace in anbarta zatazo cikin sati su zanta.....
To kawai Asma'u tace mata donta gaji da tambayar da Zahra kemata na dalilin daya hanata zuwa makarantar

*****
Gabadaya Sulaiman yashiga damuwa dubada yanda Magajiya ke shunning dinshi down don tunda akasakata ah under house arrest babu garin da zai waye baije gareta ba amma kullum ansa daya ce batason ganinshi abun yadameshi yakuma sakashi ah gaba no matter what she's his Mother and he has to atleast show some care tunda yadamu da ita din agaske dukda kuwa yasan halinta da abubuwan datakeyidin yanzuma yazo inda taken ne amma tacema guards dinma in Sulaiman yaxo batason ganinshi kwata kwata dasuka fada mishi bakaramin sanyi jikinshi yayiba yayinda cikeda damuwa yajuya yafita.....
Karkuso kuga Magajiya duk ta rame tazama wata iri don ko wanka takiyi barecin abincin kirki wai ita adole tana fushi da Mai Martaba abunda batasaniba shiyama manta da kashinta ayanzu tunda haryau babu wanda yaje yafada mishi halin da take ciki.......
Bayan tafiyar Sulaiman dinne sega Talatu taxo tasamu daya daga cikin dogarayen wanda shidin na hannun daman Magajiya ne sannan tace mishi tanason kallon Magajiya don Allah important sako zata fada mata......
Dan shiru yayi sannan yace"bazai yi kigantaba Talatu sede infada mata don kinga anhana kowa ganinta inba Yarima Sulaiman ba.....
Cikeda damuwa Talatu tace yanzu yaxanyi don Allah rayuwarmu nacikin hadarine inason in isar da sakon nan gareta don nasan Gimbiya Zaliha ba lallai ta iya daukan mataki daidaiba.......
Dogarin ne yace kifadamin sakon manato?.....
Dan shiru tayi kafin tace kuma hakane fa don ta yarda da Sama'ila yana daya daga cikin na hannun daman Magajiya don haka tafada mishi sakon jinjina kai yayi cikeda damuwa sannan yace to kibarnan kada kowa yaganki zanfada mata nasan zata fadamin abunda zanyi...........
Godiya tayi masa sannan ta tafi koda Sama'ila yaje befada ma Magajiya cewa Talatu bace takawo sakon kawai yanuna as in yasan abunda yafaru dinne cikeda tsoro Magajiya tace"kana nufin Audu yazoshi yau?...
Gyada kai Sama'ila yayi sannan yace amma Gimbiya Zaliha tace yadawo dayanma.......
Gabadaya Magajiya tarude don tasan indai Mallam Audu yasamu ganin Mai Martaba to kashinta ya bushe yanzuma tana neman hanya tafita awannan kurkukun ne inakuma a ga ansake kai wani karan nata itakam tarasa miyasa kwanan nan batada luck ne cikeda damuwa tace"Sama'ila dayanma zaidawo ko?"....
Eh Uwargijiyata...
Ahankali tace kusan yanda zakuyi kaidasu inusa ku kawar dashi banason inga Mallam Audu na numfashi cikin doron kasarnan daga yau...
Angama Uwargijiyata cewar Sama'ila din sallamarshi tayi yatafi yayinda tashiga fifita donkuwa bakaramin gumi bane yashiga keto mata lokaci guda dukda kuwa sanyin tiles din gurin dama kuma fan din dake gudu ah dakin ga zuciyarta wani irin bugu yakeyi bana wasaba...

Inusa da Sama'ila tun bayan sallar laa'sar suke leke leke kozasuga Mallam Hudu yashigo don daukeshi su cinma burinsu amma shiru.....
***
Se wuraren biyar Mallam Audu yasamu yataho masarautar se sauri yake bugawa ko Allah zaisa yayi sa an samun ganin Mai Martaba yau don shikam talaucin nan ta isheshi gaskiya gashi da iyali hakkin mutane nata binshi yana cikin wannan tunanin ne yaji anjefa mai mayafi akai tareda rufe mishi baki sannan aka sakashi cikin mota yanason yayi ihu babu hali sabida toshemai baki da akayi basu jima da shiga dashi cikin motar ba yaji yafara jin hajijiya sekuma bacci yadaukeshi lokaci guda..........

Zaliha tajima tana jiran taji ancemata Mallam Audu ya'iso amma shiru kakeji babu wani labari don haka setayi tunanin koma ya hakura da kawo karar ne sekawai tacigaba da harkokin gabanta..........

***
*TWO DAYS LATER*....

Yau aka kai tambayar auren Almustapha gidan su Asma'u wanda manya manyan maza na dangi daga Batagarawa sunzo tarban baki daman
kuma kawu nanan bekomaba dama wasu aminan Daddy dake cikin garin Zaria anyima su Dad da waziri tarba mekyau don bakaramin dadin yanda aka karramasu sukayiba sannan akayi tambaya cikin mutunci anbasu Asma'u sannan atake akasa biki nanda sati biyu tunda bothside na families din baswason aja maganar kuma sunyi akan sunason ayi simple wedding daga bangaren *Gidansu Almustapha* din Daddy yace bakomai sudai albarkan auren sukeso bawai wasu didimaba kuma daman kosu basuce hakan ba yariga ya sama ranshi auren Asma'u da Asiya kam bazai barsu suyi wata didimaba bayan abubuwan dasuka faru Mubaraq kuwa namijine daman bawani event zeyiba sede inwanda dangin gidan Matar dazai aura zasuyi zeje shima insun bukata........

Haka su Daddy suka koma gida cikeda santin irin tarbar da akayimasu don sunji dadi sosai sannan sunsan yar gidan mutunci zasu auro koba komai.........
Koda Sulaiman yazo yanama Almustapha congratulations anbashi mata bewani damuba donshi daman yasan zasu bashi din tunda Dad yariga yayi magana besides bawannan bane agabanshi yanzu.......
Adaren ranar Sumayya tagama hada kayanta don washegari zata koma *Jakarta* suna zaune ah parlour anata hira Sulaiman yashigo gaida Mom yayi sannan yace zancen me ake bani?....
Afiya ne tace"Yaya Sulaiman muna jajen za ayi auren Yaya Almustapha Sumayya batanan ne".......
Dan satan kallon inda Sumayyan take yayi tawani turo baki kaman zata fashe da kuka don yanzu tagama mita wai ansan tana makaranta miyasa za asa biki sati biyu.......
Mom ne tace "kecefa kika dage xaki koma miyena damuwan kuma Sumayya,inbaki samu bikinshiba aizaki dawo kisamu matarsa wannan ba matsala bane"....
Wannan Karan hawayene yashiga tiltiloma Sumayya din cikeda takaici ta tashi tayi daki tana kuka furzar da iska Sulaiman yayi sannan cikin sauri yabi bayanta tana shirin rufe kofar yayi saurin rikewa tareda karasawa cikin dakin zama yayi bakin gadonta yana ganin yanda take tsaye tana kuka kamar yar yaye sosai yakejin zafin kukan nata ganin taki dainawa yace"so kike ki karamin pain bayan wanda nike ciki ne Sumy?"......
Magananshi yashigeta sede hakan behanata cigaba da kukan datakeyiba.......
Ahankali yataso ya iso inda take tareda cire hannayenta daga fuskarta still tana kukan harda majina warce hannunta tayi tana shirin juya mishi baya cikin sauri yasake riko hannu wani irin electric shock sukaji dukansu"ni miye laifina Sumayya konine nasa ranar bikin dazaki huce akaina?".......
Nika ka kyaleni Yaya Sulaiman kai kaja komai don nasan da hadin bakinka akayi hakan don ah muzanta min bansan miyasa ka tsaneni ba hakanan bansan dalililin dayasa baka so.......
Cikin sauri yadaura yatsanshi kan lips dinta yana kallonta don bakaramin suka maganarta tayima ranshi ba cikin karyayyar murya cikeda nuna damuwa tareda wata irin muryar dabaisan yanada itaba yace"kul! Sumayya kidaina fadin irin wannan maganan because you don't know how special you're to me don dakin sani bazaki taba fadin wa yannan magan ganunba"......
Kallonshi take ahankali sabida tanason gaskata maganarsa she's busy looking into his eyes sede babu abunda tagani illa pure truth acikinsu and sincerity dan gyada mata kai yayi ahankali tareda karya wuya gefe daya...
kidaina fushi dani Sumayya I'm not at fault please "believe me,I care for you"....
Batasan sanda wasu butterflies keyawo acikin taba dukda kuwa kukan da takeyi hartake ganin kaman Sulaiman din zai gane halin da take ciki sake riko hannunta yayi cikin nashi sannan suka karasa gaban gado suka zauna kallonta yayi sannan yace kingama shirin ne?...
Gyada mishi kai tayi, murmushi yadanyi sannan yace"I'll miss you kidaina fushi dani don Allah, I've so many problems agabana kibari agurinki indinga samun farin ciki koda kadan ne Sumayya"....
Yanda yayi maganar seda tsikar jikinta yatashi gawani irin tausayinshi dataji yashigeshi lokaci daya tabbas he must be going through alot because of his Mother sabida uwa uwace dole yadamu da al amarinta....

Kallon soft hannunshi tayi dake cikin dayan nata sannan tasake daura dayan nata kan hannunsu tace"I'll miss you too Yayana,don Allah kadaina sama ranka damuwa"......
Murmushi yasakar mata tareda gyada mata kai ahankali dukda kuwa yanda idanunshi sukayi ja, sunjima suna zaune ahaka babu mai iya cema dan uwansa wani abu se tunanin zuci dasukeyi dukansu biyu din.......
Se wurin shadaya yaga shirun yayi yawa yace barina barki kikwanta kada kitashi late gobe....
Good night Yayana tayi maganar cikeda tausayinshi....
Good night Sumy na yayimata magana cikin cool voice dinshi sannan yafice ah dakin......
Binshi tayi da kallo tana murmushi kamar wata sokuwa......

*****
Sallama Hajiya iklima ketayi ah parlourn Wazirin amma ina yatafi duniyar tunani tafi minti biyar tana doka sallama bai ansaba don baka tashige parlourn kai tsaye cikeda damuwa don tasan bazai wuce yana nan yanata tunane tunanen 'Yarshi dake neman samishi hawan jini tunba yauba .....

Zama tayi gefenshi sannan tace Babansu Faisal miyasa kakeson daurama kanka cuta sabida Magajiya kamanta cewa ba ita kadai bane yarka kanada wasu responsibilities akanka atleast you should be healthier for our sake dakuma sauran Ya'yanka......
Kallon Hajiya iklima waziri yayi sannan yace bazaki gane meyasa nake shiga damuwaba tunda Magajiya ba yarki baneba,bazaki gane yanda nakejin tausayin taba dakuma tunanin halin dazata shiga inta cigaba da halayenta.......
Cikeda damuwa Hajiya iklima tace ammadai kasan itaba yarinya baceko sannan tanada hankali tasan maiya dace amma dukda haka son zuciya ya rude ta takeyin yanda taga dama shidai Waziri jin Hajijiya iklima kawai yakeyi don gani yakeyi laifin shi ne koma miyeda Magajiya takeyi da ace be kyaletaba yahadata da hukuma an hukunta ta da may be bazata cigaba da abubuwan datakeyi yaudinba......
He's regretting all his actions and blaming himself for everything don kuwa abun na hunting dinshi for years now sannan haryau beyi sharing labarin dakowa ba...Sede kash yanzu abun is too late komai ya tabarbare babu halin gyarawa dama ace ze iya maida hannun agogo bayane daya gyara abubuwan daya bata acan baya, Hajiya iklima ne tace kadaina tunanin nan don Allah yanzu tun dazu niketa zuba kaman ya'yan kurna ashe kai kwata kwatama hankalinka baya gurina........
Cikeda tausayin Matar yariko hannunta sannan yace Iklima kiyi hakuri abunne yadame ni gakuma Mai Martaba haryanzu yaki sakin Magajiya aiko ba komai yaduba daraja ta dakuma tarayyarmu yayima Matar sa afuwa ko?....
Hmmm shine abunda Hajiya iklima tace don kuwa tanajin labarin abubuwan da Magajiya take cikin masarautar shiyasa koda wasa bataga laifin Mai Martaba ba dayasa ta underhouse arrest sede kuma tawani bangaren ma tayi reasoning maganar Wazirin amma seta ce mishi"ni inaganin kafini ma sanin wanene Mai Martaba acikin Masarautar nan dama kuma irin adalcinsa yau da ace Sulaiman ne yayi laifi babu abunda zai hana Mai Martaba yabashi irin wannan punshment din dadina dashi akwai adalci so,inaganin Inka tuna wannan hali nashi bekamata karinka damuwa ba.........
Gyada kai Waziri yayi sannan yace"kuma hakane fa"....
Eh mana and na tabbata bemanta da Magajiya ba kwata kwata dole zai waiwayeta kwana kusan kilan yafison ta horu ne............
Gyada kai waziri yakumayi cikeda gamsuwa yana tuna yanda yayi watsi da laifin yarsa ya rufeshi kirif yaki fadama kowa bayan laifin datayi ba kadan bane kashe mutane at her tender age is the worst crime da mutum zaiyi haushin kanshi yakeji da bai fada ah lokacinba sannan yanajin haushin kanshi dabaiyi tunanin inya barta haka zata iya zama masifa ga jama'a ba hakanan kuma yake kara jin haushin kanshi har yanzu don ya lura baida courage din fada din kuma bayajin ze iya exposing yarshi for what she did( Nidai nace baka tuba bama kenan)...... +

Bangaren Asma'u kuwa tunda akace mata bikin ta sauran two weeks bakaramin tashin hankali tashiga ba don gabadaya lissafin yanda zata zauna da wannan arrogant mutumin ku takeyi under thesame roof,taci kuka kamar ba gobe haka Asiya tayita rarrashinta tana bata hakuri Ummi kuwa kinbin takanta tayi don Itama tana iya yin kukan seta buge da kiran Yayarta ah Gombe don sunyi magana kwanaki kan me gyaran jiki daga Maiduguri zatazo tun lokacin da akasa auren Asma'u da Mukhtar sekuma Allah baiyiba shiyasa yaudin takuma kiran ta suka sake zantawa nan Adda Rukayya(Wanda su Asma'u Mommyn Gombe suke kiranta dashi) tace in sha Allah zata kirata suyi magana kilan ma tace gobe zata kamo hanya don bata wasa damaganar kudi ita........

....
Tunda Sulaiman yabar bangaren su Mom bayan ya jaddada masu Amira cewa gobe zaikaisu school ayi musu interview yadawo suwuce kaduna da Sumayya,cewa sukayi muma zamu rakata dariya yayi sannan yace babu maibin mu dagani sai Sumy na zamu tafi.....
Dariya Amira tayi sannan tace yaukuma Sumynka takoma Yaya Sulaiman........
Kedai barsu ba a shiga tsakaninsu gobe zakiji an tabarbare kuma daga baya azo ah shirya cewar Afiya....
Jan hancin Afiya dake kusa dashi yayi sannan yace"silly girl,to barima kiji wannan karan mun dinke nida Sumayya bazamu sake fada ba"...
Allah yasa suka fada atare sannan ya amsa musu da amin yakuma karada wasa nakeyi muku na'isa intafi babu ku aisai Sumayya takumayin fushi dani kuma wannan karan kam for life nasani....
Hakan ma bazata faruba Yaya Sulaiman cewar Amira...
Allah ya yarda cewarsa sannan yayi musu saida safe yafice already yayi sallama dasu Mom daman.....
bangarenshi yawuce cikeda dokin Matarsa don kuwa yanzu yagama rikicewa gun Sumayya kuma babu inda yake tsanmanin samun nutsuwa se gurin Gimbiyarsa Zaliha da murmushi ya isa dakin nasu samunta yayi kwance dawasu nighties hadaddu wanda dasu da babu duk dayane don gabadaya sirrikan jikinta suna nunawa........
Karasawa yayi jikin gadon sannan yazauna gefenta tareda karban wayar dake hannunta cikin rada yace"Hubby is back ah ajiye wayar akulani,you know i miss you right?",yakarashe maganar tareda dan shafa lallausar gashin kanta don babu dankwali ko hula akanta.....
Bata rai tayi sannan tace"bawani missing dina dakayi ina kullum se kagama hirarka sannan kake tunawa dani"........
Analyzing fuskarta yayi seyaga kaman ranta abace donkuwa bata taba yimashi hakaba tun xamansu ahankali yace"Zaliha?".....
Miyene tayi masa tambayar ah murtuke.....
"Tashi kizauna muyi magana mana"....
Babu musu ta tashi tazauna riko hannunta yayi cikin nashi sannan yace"look at me please?",kin kallonshi tayi matso da fuskarshi yayi kusada tata cikin lallashi yace "inma laifi nayi miki kiyi hakuri don Allah",yakarashe maganar tareda brushing fuskarshi gefen tata......
Saurin tureshi tayi"nibanason irin haka kadaina tabani kuma kasani tricks dinka bazasu shigeniba"............

STORY CONTINUES BELOW


Cikeda damuwa yace"wai maiya farune Zaliha stop keeping me in the dark"......
Directly tace ashema dagaske kakeyi bason sarauta kakeyiba,ashe dagaske kakeyi bakason Yarima wato kai good samaritan ko to wallahi nidai bazai yuyuba inazama dakai lafiya lau bazakamin irin wannan yaudarar ba......
Cikeda desbelief Sulaiman yace"is this the reason dakike ta shunning dina down Zaliha?"....
Gyada masa kai tayi sannan tace yakakeson inyi to kanason mayar dakanka bawa dole indamu Dear gaskiyar ni I want you to be the Crown prince kaman yanda Mama takeso aikobadan niba itan yakamata kabi Umarninta amma Kai sai abunda kaga dama zakayi........
Sulaiman wannan karan ranshi abace yace"Shut up Zaliha,ya isahaka,ya isheki! kidaina sako Mama cikin wannan maganar because you know nothing about her kedai kawai kice daman you never love me abunda zansamu kikeso baniba"........
Nidai bance makaba tayi maganar tana hararanshi......
To miyene inba hakaba, why can't you stay with me the way I'm sekice sena karbi sarauta sa yatsa yayi yana nunata sannan yace "to barima kiji infada miki inzaki cirema ranki wannan tunanin gwanda kicireshi aranki tun wuri sabida I'm not going to be the crown prince but my Brother Almustapha, I'm Sulaiman Zaliha, Sulaiman! Yayi emphasizing word din sannan yakarada gwandama kiyi putting dinshi at the back of your mind tun yanzun........
Yana karashe fadin haka yatashi yafita yabar mata dakin yarasa dalilin dayasa Zaliha tacanza suddenly, he's very sure duk yanda akayi wani ne yazuga ta waye kenan shine tambayar daya shiga yima ranshi.........

****
Seda ya tabbatar sauran dogarayen da akasa suyi gadin Magajiya hankalinsu baya kansa sannan ya shige cikin dakin idanunta biyu yasameta tana zaune ah kasa ta rakube guri guda jin shigowar mutum ne yasata dago dakanta tana ganin Sama'ilan tayi saurin tashi tana "kun kawar dashi ko?"......
Dan shiru Sama'ila yayi don yarasa abun fada mata cikeda kaguwa taji sun kasheshi tace ba magana nake makaba Sama'ila?.....
Kai akasa yace"kiyi hakuri Uwargijiyata bedawo cikin masarautar nan ba kwata kwata kuma har gidanshi munje ah daren nan bayanan iyalanshi ma jajen rashin dawowarshi sukeyi"......
Sa hannu tayi tabuga ah jikin bango cikeda damuwa tace"kodai yasamu yakalli Mai Martaba ne,kodai yasamu yafada mishi abunda nayi takarashe maganar zufa na keto mata cikin sauri kuma tashiga jijjiga kai"bazai yuyuba Mai Martaba bazai tabajin labarin nanba because inyaji kashina yabushe takarashe maganar idanunta sun kada sunyi ja dakyar ta iya komawa tazauna ah inda take don kafafunta bazasu iya daukartaba tarasa dalilin dayasan she's not lucky this days"....
Gashi Ya'yanta na hannun daman nata dukkansu babu wanda yasan abunda ke faruwa da ita jitayi Sama'ila yace kiyi hakuri Uwargijiyata bazasu samu ganinshiba muzamu cigaba da nemansa se lokacin ma ta tuna yana gurin tsabar tension don haka tace yatafi yabata guri...............

****

Ahankali yadinga bude idanunsa yayinda kanshi kedanyi mishi zogi kadan kadan har ya budesu waral karema dakin kallo yashiga yi,dakine madaidaice medauke da karamin gado wanda yake kwance akai sekuma yar taburma dake shimfide can gefe mamakine yakamashi na tayama akayi yazo wannan unknown place din yayinda ahankali yaji komai yafara dawo mishi filla fillah.........
Subhanallahi shine abunda yashiga furtawa kafin yatashi cikin sauri ya leka window din fili yagani wanda duk datti yacika gurin na busassun ganyayyaki komawa yayi jikin kofa yashiga bubbuga wa ahankali yana"waye akusa don Allah,azo ataimakeni wasune suka sato ni!"...
Yafi awa daya yana maimaita thesame thing anma babu wanda yakawo mishi dauki don haka yakoma bakin gadon yazauna gabaki daya yarasa yazaiyi don yasan yanzu iyalanshi nacan hankalinsu tashe suna nemanshi gashi shidai baisain iya awannin daya dauka yana zaune ananba yana cikin wannan tunanin ne yaji antaba kofar ba ajimaba kuma akabude ta wata mata yagani tashigo wanda zatayi shekaru arba'in da takwas zuwa hamsin dai bayanta kuma wata yar budurwace wanda bazatafi shekaru shatakwas ba hannunta rikeda kwanon abinci tsorone matuka yakamashi don kuwa duk atunanin shi Magajiya ce dafari,cikeda rudani yace ku kuka satoni?........
Dariya Laure tayi don yanda yayi maganar bakaramin dariya yabata ba Hajiya Muniba ma daurewa kawai tayi sannan Laure ta ajiye kwanon kusa dashi......
Ina tambayar ki kina dariya yarinya?.....
Wannan Karan Hajiya Muniban ne tace"kayi hakuri Mallam bamu muka satoka ba amma ninasa ah daukoka".?.....
Cikeda damuwa yace"danayi muku me,don Allah nikam kusa amaidani inda kuka daukoni wallahi iyalaina na jirana kuma suna matukar bukatata"......
Ka kwantar da hankalinka sunsan kana nan kuma nan yafi maka don acan waje ana nemanka
Inkuma kanason sukama ka to zan iya barinka ka tafi cewar Hajiya Muniba din,cikeda damuwa yadube ta yana neman karin bayani gyada masa kai tayi ahankali sannan tace"a masarautar Zaria nikeda zama wannan baiwa tace ita taji sanda wasu keshirya yanda zasu kama ka su kasheka sabida wani sirri daka sani akan Magajiya shine tazo tafada min nikuma nasa akayi saving dinka from them and iyalanka ma naje har gida nasanar dasu halin da akeciki don nasan zasu shiga damuwa suyita nemanka........

STORY CONTINUES BELOW


Dagaske kike ba cutar dani zakiyiba yayi mata tambayar cikeda tsoro, murmushi tayi sannan tace danayi niyar cutar dakai dabaka kawo yanzuba Mallam taimakon ka zanyi kaman yanda nakeson kataimakeni.....
Cikin sauri yace wani irin taimako ni koma miyene yanzu damuwa na bewuce inje ga iyalinaba suna matukar bukatata yayi maganar kamar me shirin yi kuka....
Tausayi yadan bata sannan tace nasan matsalarka cinsu da shansu ne ko?
Gyada matakai yayi ahankali kafin tace to kada ma kadamu da wannan sabida nasai musu kayan abinci nakai musu tun ranar godiya yashiga yi mata sosai cewa tayi"Babu komai karka damu aiyiwa kaine",don data taimakesu setakejin kaman wanda ta taimaki danginta ne aduk sanda tayima wasu taimako to tabbas takanji wani farin ciki tattareda ita she has no one to spend money for inba yan uwanta musulmai mabukata ba....

Duban Laure tayi dake gefe rikeda kwano tace ajiye mishi abincin mana yaci semuyi magana, ajiye wa laure tayi cikin sauri yajanyo kwanon batareda second tunaniba yashiga ci donkuwa bakaramin yunwa ne ke nukurkusanshiba seda yacinye tas sannan yace Laure tabashi ruwan daya gani ah hannunta mika mishi tayi cikeda mamakin yanda yacinye wannan uban abinci don kuwa Itama tanada ci amma gaskiya bekai nashiba,yana gama shanye ruwan yadubeta sannan yace"nagama ci wace magana ce zamuyi"...
Jijjiga kai Hajiya Muniba tayi sannan tace kafada min meya hada ka da Magajiya ko ince meka sani game da ita harkakeson exposing dinta?....
Dan shiru yayi kafin yafara bata labari dallah dallah har yakai karshe jinjina kai tayi sannan tace"Kai wannan matar inason Inga karshen makircinta"......
Shidai Mallam Audu shirun yayi sannan yace nidai kitaimaka min inga Mai Martaban inban fada mishi abunnan ba hankalina bazai taba kwanciya ba...

Indai don ta wannan ne kada kadamu amma inason kabani lokaci nanda sati uku sabida inason sudaina nemanka tukunnan don rayuwarka nacikin hadari sannan nabiyu inason kasani cewa Magajiya bawannan ne kadai laifuffukan datayiba inason mutara evidence against her kafin muyi exposing dinta......
To shikenn shine abunda Mallam Audun yafada sannan yakara jaddada mata cewa shifa damuwarshi iyalanshi ne kuma tacemai she'll take care of them for now shikuma yacigaba da zama acikin wannan gida za anakawo mishi abinci kullum godiya yayi mata sannan suka tafi abunsu......

****
Tun 8:00am Sulaiman yashiga bangaren su Dad nan yasamu su Afiya harsun shirya don sunsan shi da azalzala shiyasa ma kwata kwata basu koma bacci ba dasukayi sallar asuba..........
Seda yagaida Mom da Dad sannan suka tafi koda sukaje school din anyi musu interview kuma alhamdulillah sundanyi kokari though not that perfectly se principal din tayi deciding barinsu ah ss2 din tunda ta lura sunada kwalkwalwa mekyau may be in aka hada musu da lesson teacher zasuyi catching up.......
Aikuwa shawarar data bama Sulaiman din kenan nan yake tambayar ta inda zasu samu lesson teacher shine tace cikin corpers dinsu baza arasa wanda keda interest nayin extra lesson ba zata bincika in ansamu she'll call him...
Godiya yamata sannan suka koma gida nan yasamu Sumayya harta shirya murmushi yasakar mata mai shiga rai don ita kanta batasan sanda tamayar masa da murmushin ba karasawa yayi gabanta sannan cikin rada yace"watoma har saurin tafiya kikeyi ke bakidamu ma zamuyi kewarkiba".....
Shagwabe fuska tayi cikin yar siririyar muryarta tace"waya fada maka bazanyi kewarku ba?"...
"Gashi actions dinku sunnnuna sewani zumudin tafiya kikeyi",yakarashe maganar yana karema karamar pink lips dinta kallo.....
Dan bubbuga kafa tayi tareda dauke kanta"kallon fa na menene?".....
Dariya yayi tareda dan sosa lallausar gashin kanshi sannan yawance dacewa "barinaje nayima Madam sallama zakimin bayani ah mota wazakifi missing?"......
Afiya datana ankare dasu tundazu ashe bata shige cikiba tace"zatafi kewana of all people".....
Hararanta Sulaiman yayi sannan yace "ke awa?".....
Ni ah kanwarta kaman yanda kake Yayanta....
Binta yayi zai rankwasheta dasauri tagudu tayi dakin Ummi shikuma yasaki murmushi yafice daga bangaren koda yaje yima Zaliha sallama dukda kuwa abunda tayi masa jiyan be mantaba sede shi mutum ne meson zaman lafiya shiyasa yakeson nuna kaman komai bai faruba cemasa tayi"ita Sumayya din dole kai zaka rakata Dear?".....
Nizan rakata Zaliha akwai magana ne?.....
Tsuke baki tayi sannan tace"nidai gaskiya nagaji komai Sumayya komai Sumayya Yarima,wai nikam kafadamin meke tsakaninku ne?"....
Murmushi yayi yana dan shafa sajen sa sannan yakaraso wurunta tareda riko kugunta yana karema kyakyawar fuskarta kallo tareda kai bakinshi kunnenta"what's your problem girl?".....
Turo baki tayi tana shirin tureshi sede takasa don bakaramin riko yayimata ba ga kamshin turarenshi dake rikitata mutsu mutsu tashigayi sake riketa yayi dakyau tareda daura fuskarshi kan nata cikin rada yace"Zaliha".....
Yanda yayi maganar seda tsikar jikinta yatashi don jiya bakaramin kewarshi tayiba because Sulaiman yakoya mata jaraba karfi da yaji lumshe idanunta tayi tareda sake budesu tadaura kan nashi"Baki yarda dani bane,koko baki yarda da son da nake miki bane?".....
Niiii...fa bance hakaba tayi maganar uncomfortably don Allah kadai yasan abunda takeji murmushin nasara Sulaiman yayi sannan yayi kissing cheeks dinta batareda ya matsa ba yace"believe me Sulaiman dinki nasonki sabida haka kidaina damuwa da irin wayannan tunanin",baibari tayi magana ba ya hade bakinsu guri guda sunfi 2minutes ahaka kafin yasake ta yace"I'm going now kiyimin addu'a indawo lafiya kinji Wifey?"bejira mezatace ba yafice cikin sauri don yasan akwai magana bakinta.........
Daga hannu tayi tana Yarima wait mana amma ina baimajitaba don ahankali tayi maganar,jijjiga kai tayi ahankali tareda dan sakin murmushi"he's such a loving husband",duk bacin da ranta zaiyi yasan yanda zaiyi yayi calming nata down tanada magana dashi sannan bawai yacire mata zarginda take mishi bane amma dai atleast yayi easing pain dinta for a moment and she's sure hakan dayayi na nufin bazai taba barinta ba...........

STORY CONTINUES BELOW


Haka Sulaiman dasu Afiya suka kama hanyar kaduna don karfe biyar jirginsu Sumayya zai daga zuwa Indonesia koda suka isa gidan abokin Sulaiman mai suna Idriss suka sauka matarshi tayimusu tarba maikyau as usual se bayan la'asar sannan suka tafi airport din suna jiran time din tashin jirgin yayi sanda Sumayya zata wuce harda hawayenta dakyar Sulaiman ya rarrasheta don su Amira ma hawayen suka fara koba komai ai sunsaba yanzu Kuma inta koma can she'll be alone dabadan badan ba setace zata hakura da karatun ma amma sedai tasan how important karatun yake agareta shiyasa ta daure zuciyarta...
Haka kowannensu rai ba dadi suka juyo zuwa Zaria...........

****
Isowar dare me gyaran jikin tayi aikuwa adaren tafara gudanar da aikinta daga Asiya har Asma'u din babu wanda aka bari nan aka shiga yimasu gyare gyare kullum.......
Asiya kuwa dadin abun takeji don ita batada damuwa tunda masoyinta takeso don tuni tamanta dawani Ahmad Dj seyanzune ma take realizing summer love ne kawai tama Ahmad din koko tace hauka donkuwa bata dauki abun ah matsayin abu mai mahimmanci ba, Aslam is her first love kuma dashi takejin zata iya rayuwa don yariga yazama wani bangarena gangan jikinta dama zuciyarta baki daya yayinda ah bangaren mutumiyar ku Asma'u kam babu abunda ya canza don babu ranar da bazata zubar da hawayeba wanda itakanta batasan daliliba don bazata iya cewa actually ta tsani Almustapha ba and bata jin haushin shi ko kadan dukda kuwa tanason taji haushin nashi amma zuciyarta takasa amincewa da hakan....
Acikin satin ne Zahra tazo mata ziyara zokuga murna dalewa tayi jikinta tana"I'm so so happy to see you Zahra"...
Zahra dinma thesame thing tace mata kafin tasamu guri tazauna akan gadon tana karema Asma'u kallo don tawani irin ramewa at thesame time kuma tayi fresh abunta gawani haske tada kara gakuma kamshin da jikinta yakeyi tako Ina....
My best ❤️ kina jin dadi fa dariyar yake Asma'u tayi tana dan bugun kafadar Zahra din"wani jin dadi Zahra?" ...
Kai tsaye Zahra tace naga kinyi fresh abun ki ne....

Nadai rame Asma'un tabata amsa, Allah kinyi fresh Asma'u dukda Kin rame din Zahran tayi magana seriously..........
Murmushi kawai Asma'u tayi mata tana tambayarta Auntynta dama mutanen gida daganan kuma suka koma hirar school inda Zahra kecemata zasuyi resuming next week.....
Atake mood din Asma'u yacanza Zahra talura da hakan seta riko hannunta ahankali murya karye tace"Asma'u miyasa kikadaina zuwa school?"....
Tunkan Zahra tarufe baki har idanun Asma'u sunfara zubda kwallah .........
Hakuri Zahra tashiga bata yayinda Asma'u tarungume kawartata tana I'm not destined to be a medical doctor Zahra,haka Allah yayi daman kinsan ance kana naka Allah yana nashi...

Cikeda damuwa Zahra tace miyasa kike fadin haka tell me exactly meyake faruwa ko baki yarda dani bane Asma'u......
Cikin sheshekar kuka Asma'u tace"I'm getting married Zahra",tayi maganar muryarta na cracking sannan takara da" ne...x..t weekkk"....
Dan shiru Zahra tayi because she's so speechless sannan tace to ai aure baya hana karatu Asma'u inbadai mijin bane ya hanaki,wannan karan Asma'u tarege kukan ahankali tashiga bata labarin abunda yafaru harzuwa yau Zahra saida tazubar ma kawarta kwallah dakyar ta iya controlling kanta sannan tashiga gogema Asma'u hawayenta encouragingly tace"kicigaba da addu'a bakisan wani alheri bane behind this Asma'u, you're prayerful and a very nice person may be Allah yayi miki planning something better ne don Allah kidaina damun kanki and keep Smilling because you look good when you smile", Zahra takarashe maganar tana goge nata kwallar don tarasa mezata cema Asma'u din batason tazama silar sakar mata da gwiwa tunyanzu dukda kuwa tasan kawartata nacikin hali mai wuya sede mezasuyi?...
Basuda mafita daya wuce addu'a din dakyar ta iya chearing mood din Asma'u din sannan suka shiga hira har tasa Asma'u takira Aisha atake tafada mata bikinta don da cewa tayi bawanda zata fadama wa....
Aranar Aisha tazo suka fara shirye shiryensu wai zasu fidda anko, Asma'u ne tace bawani anko daza ah fidda kosun fitar ma babu maisaya sabida it's too late ahakan sukace sudai zasu fidda wanda keda niya zai saya babu yanda ta iya hakanan tabarsu bayan ta jaddada musu cewa babufa event din daza ayi nan sukacemata sunji kafin Aisha tace bamu number Yaya Almustapha din to mukira shi batun anko din?..

STORY CONTINUES BELOW


Wani harara Asma'u tayi mata irin bakida hankalinnan.....
Dariya Aisha tayi sannan tace bafa wasa nake ba kibani don Allah kinga har ana kiran laasar sonike muje kasuwa da Zahra yanzu mufidda ankon inyabamu kudin semu saya kawai muraba ma close friends dinmu aidai kowacce in ansaya mata atamfa baza tayi complain din dinki ba nanda sati daya kam bazasu rasa mai dinka musuba....
Tsaki Asma'u tayi tana Allah Aisha kindaina damuwa dani ke damuwarkima ankone ba irin mijin dazan auraba......
Jan hancinta Aisha tayi tanadan murmushi sannan tace"I know you love him and Almustapha will never hurt you dan kallon shi danayi bayan namishi masifan nan he's so cool baida hayaniya besides inya miki wani abunma nikadai na isheshi tundaga KD zanzo ingyara mai zama nidai ynxu damuwarmu kibamu numbersa it's urgent.....

Hararanta Asma'u tayi"cemuku yayi yanada kudi Aisha?"....
To sannu me miji cewar Zahra harkina kakkareshi,dariya tayi tana Allah bahaka bane amma kuma dai kunsan baidace bako...
Aisha ne tadaga hannu tana mudai kibarmu ah to waya fada miki ana tausayin namiji yanzu kede kawai kibamu inkinada niya inbaki da niya kuma basai inkira Yaya Sulaiman yaturomin koya mishi magana kawai......
Ya ilahi cewar Asma'u sannan tace Aisha Allah banda numbersa wani harara Aishan tayi mata fada ma wasu badai niba......
Shiru tayi takyaleta tanajin Aisha takira Sulaiman ba ajimaba kuwa yadaga call din ah handsfree ma tasaka.....
Ina wuni Yaya Sulaiman.....
Dariya yayi sannan cikin barkwanci yace kibari ingaidaki dai don kune Aunties dinmu yanzu......
Lol oh haka abun yakoma yanzu cewar Aishan tana dariya Itama......
Eh mana,to ya shirin biki Aunty Aisha wai mekuke shirya mana ne?....
Kai zamu tambaya ai cewar Aishan, murmushi Sulaiman yayi tareda shafa sajenshi yana"aa kam ai mata keda biki bamuba"....
Allah ko Yaya?....
Allah kuwa Aunty Aisha,dariya tayi nidai kadaina dauramin girman dole tunban tsufa ba.....
To nadaina Aishatu.....
Yauwa kokaifa Aishan tayi magana tana gyara zama kafin tacire ah handsfree kuma tace yauwa daman maganar ankon kawayen amarya ne inatabin Asma'u taban number ango taki shine nace barina maka magana kokai zaka bani.......
Lol Asma'un tahana ki numbersa?...
Gyada kai tayi kamar tana gabansa, cikeda zolaya yace kodai kishine irinnaku na mata batason kiji muryar angonta dariya Aisha tayi sannan tace to wayasani dai nimadai inada nawa baby boo din....
Lol toshikenan nawa kuke bukata kudin ankon yanzu dai Sulaiman yatambayi Aisha don yasan koyafada ma Almustapha cemasa zaiyi shi yayi taking care of abun koma yaki kulashi don bakaramin aikinsa bane yadauki abun amatsayin shirme..........

Aisha ne tace koma nawa yanda ya sauwaka dai ae abunma is too late kawai dai munason mubama close friends dinmu ne ...
Haka Sulaiman yayi yayi tafadi nawane amman taki don haka yace taturo account number dinta nansukayi sallama ba ajimaba kuwa sega alert na 200k yaturo wara idanu tayi tace 200k fa Asma'u..
Itadai Asma'u batace komaiba se murmushi datayi kawai dukda aranta bataso suka tambaya ba ahankan Sulaiman yakirasu yana tambayarsu kudin yayi sukace masa eh sannan sukayi godiya nan Aisha tace dubu darima yayi daman tanada account number din Asma'u din atake tatura mata 100k tace ki ajiye inkina bukata kiyi anfani dashi don nasan yana iya turo wani kudin ma na entertainment or anything else atamfa kuwa zamu samo masu kyau mukawo akaima friends ko gobe ma,gyada mata kai kawai Asma'un tayi sannan suka fice ita da Zahra bayan sunyi sallar laasar......
Kallon alert din tayi na 100k din setake ganin kaman takura ne miyasa za ace sukawo kudin anko bayan bikinda babu wani event daza ayi..........

Wani idea ne yafado mata atake na takira Sulaiman din tamishi godiya sannan tace masa kudin yayi yawa yaturo account number tarage seta mayarmai da 100k din tunanin inda zata samu number sa tayi sekuma take tatuno da number da akayi mata magana ta WhatsApp shiga tayi ta dauko number din sannan tayi dialing......

Almustapha dake zaune gefen Ummi yana bata abinci tanaci ahankali yaji wayarsa tashiga ringing amma bedaukaba sabida bayason abunda zaiyi distracting dinsa sau biyu ana kira yana tsinkewa batareda ya daga ba seda yagama bama Ummin abincin tasha ruwa sannan yakoma kasa yazaune tareda daga wayar jin tana sake ringing yasashi kallon sunan da Sulaiman yamasa saving da sunanta ahankali harya katse bedauka ba kamar jaraba kuma tashiga sake kira tashi yayi ahankali yana kallon Ummi sannan yafice yabar dakin harya kusa tsinkewa yadaga dasauri......

Assalamualaikum tayi masa sallama cikin lallausar muryarta datasashi jin wani yaarrr lokaci guda besan sanda yasamu daya daga cikin lumsassun kujerun parlourn yazaunaba tareda jingina jikinshi kadan jin anyi shiru ne yasata sake cewa"Ina wuni?".......
Nanma shiru yayi tareda lumshe idanunshi dago wayar tayi tana karema screen din kallo ganin ba ayi mata responding ba mayarda wayar tayi kunnenta ganin she's still on the call......
"Are you there,kana jina?".....
Kamar bazai kulataba cankuma cikin muryarsa medan karen amo yace"who's on the line?"( Kai jama'a Almustapha ya iya rainin wayau walhi)..
Yanda yayi maganar seda taji kirjinta yabuga don kuwa tabbas ko cikin bacci taji muryar Almustapha zata ganeshi dakyar ta iya controlling kanta kafin tayi karfin halin cewa"Yaya Sulaiman?"because she want to be sure.........
Almustapha kuwa katse call yayi hakanan yaji ranshi lokaci guda yabaci jin ta ambaci Sulaiman din wanda shikanshi besan daliliba gashidai sunan kaninshi takira kuma da alama bata gane shidin baneba.....

Kallon wayar tayi cikeda mamaki jin yayi hanging up tareda tabe bakinta "he's very arrogant and he'll never change", takarashe maganar tana wurgar da wayar kan gado dukda kuwa she really can't believe her ears and she's hundred percent sure shine...
Fadawa tayi kan gadon kuma tareda sake daukar wayarta tashiga dial calls tana karema number din kallo tafi minti uku ahaka kafin tayi deciding saving number din nashi....
Da *Mr Taciturn* tayi mishi saving sannan ta wurgar da wayar tafice ah dakin rai bace sakamakon kiran dataji Ummi nayi mata don tasan bewuce bata tsumin da ake bata kullum za ayiba ita gabaya tagaji wallahi ita bada son miji ba amma sewani gata ake mishi bata isa kuma tace bazata shaba don tasan se ankusan yin kuli kulin kubura da'ita donkuwa Mommyn Gombe ma kadai ta isheta.....*****
Satin biki yakama anata shirin biki sosai from both gidajen amare dana angwaye.yau takama laraba kuma yaune akeshirin kawo kayan lefen Asma'u wanda Mom da daya daga cikin matan Galadima sukaje Dubai sukayo siyayyar wasu kuma ah Lagos suka karasa sayan kayan.....
Dayanma akaje kai kayan bangaren Ummi zaa tarbesu shiyasa duk su Mommyn Gombe dama wasu daga cikin close kawayen Ummi sunzo su don tarbansu sanda suka iso tarba akayi masu na mutunci sosai sannan akafara shigo da kaya karkuso kuga yanda akwatinan kansu sukayi kyau, setin akwati dai dai dai har seti biyar na Asma'u sekuma kayan uwa shima seti daya sekuma akwatina guda biyu babba da karami sukayima Mommy amatsayinta na yaddikonta.......
Guda ake sosai acikin gidan ana kallon kaya suma su Ummi dasu Hajiya Iklima da suka tashi tafiya sunyi musu tukwici mekyau kuma sunji dadin hakan dubada yanda akayi musu tarba ta mutunci... +

Har Maghrib anata shigowa duba kayan Asma'u donkuwa kowa tafita seta guntsa ma makociyarta ganin abun bana kare bane Mommyn Gombe tace akai bangaren Daddy aedaman kayan aure ranar biki ake kawowa yawanci abari ranar bikin se afito dashi kowa yagani kafin akaima yarinya gidanta.......
Haka kuwa akayi sannan suka samu sa'ida inbahaka ba baza arasa har masu sataba ahakan ma.........
Hajja tunda yan Batagarawa suka shiga suna koda irin kayan da aka kawoma Asma'u din seda kirjinta ya fadi don haka taki zuwa don intaje tagani tana iya samun heart attack kayan seti biyar wasa ne kuma ace harda na uwa daban dakuma na kishiyar uwa......
Haushinta daya ita miyasa ba ayimataba wata zuciyar ne tace daman basu dauketa da mahimmanci ba hakanan basu dauketa abakin komai ba........

Koda aka Kira Asma'u taje ganin kaya kitayi don aganinta ai rashin kunya nema itakam bazata iyaba Ummi kuwa hamdala tadingayi tareda yima Allah godiya sekuma fatanta Allah yasa mijin Asma'u mutumin kirki ne bawai ganin kaya dayawaba ita babban damuwanta shine farin cikin yarta...
****

Yau takama Friday kuma yau yana daya daga cikin ranakun murna da farin ciki ga both families din Almustapha da Asma'u dama kuma yayunta dasukayi aure suma,biki akeyi sosai acikin gidan Alhaji Muhammad donkuwa gida yacika makil da jama'a kama daga mutanen Batagarawa har kuma mutanen Gombe both dangin Daddyn, Mommy dama kuma Ummi dai duka sekuma abokaganan arziki dasuka halarci taron,kunsandai bikin fari dole kowa zeso yazo, ciki kuwa harda lovely fans na Gidan Sarauta don kuwa babu exception kama daga Zeeneert novels,Sadeeyer novels,Gidan Sarauta Fans,Miemiebee novels,Zauren biebieisah, Zauren karatu,High class ladies,Zauren rahama novels,Taskar khadeeja candy dama dai sauransu duka kowa taci anko sunyi kyau abunsu har Ma'u takecemin nikam Zeeneert bakin nan sun burgeni ga ankonsu yayi kyau sosai jinake kaman insace su intafi dasu *GIDAN SARAUTA*....
Dariya nayi sannan nace "ai kina iya sacesu kuwa don kuwa babu abunda sukafiso kamar sugansu acikin GIDAN SARAUTA donkuwa kobaki tafi dasuba zasuje da kafafunsu ganin angonki dama mutanen arzikin gidan baki daya ammafa banda Magajiya nayi emphasizing word din har raina naji yabaci lokaci guda,murmushi tayi cikeda jin dadi hakanan taji sun kwanta mata(su fans ansamu shiga) sannan tace Magajiya meta musu kuma?........
Ware idanu nayi cikin sauri sannan nace zakiji labari amma bayanzu ba,gyadamin kai tayi sannan tace bari zancema Ummi akwai baki anema musu masauki ni wanka zanshiga yanzu.....
Bakomai Amarya, murmushin yake tayimin tashige donzuwa gun Umminta.....

Karfe biyu dot bayan an idar da sallar juma'a aka daura auren *Asiya* da *Aslam* sannan aka daura na *Asma'u Muhammad* da *Almustapha Abdulrahman Sulaiman* Mubaraq da amaryarsa kuwa acan gidansu amaryar aka daura auren babu laifi jama'a suntaru sosai dukda kuwa sunce simple wedding za ayi sede bangaren Daddy ya gayyaci mutane da dama daga bangaren su Almustapha dinne yawanci close relatives ne kawai se wayanda suka sani kuma bayan daurin auren ne akayi reception...
Can nahango Almustapha se glowing yakeyi tundaga nesa don kuwa babu wanda zaiso dora idanunshi akanshi batareda yasake daurawa ba yana sanye cikin kayan
Sarauta dayasha aiki yayi kyau sosai sekuma wannan rawanin dake kara mai wani irin haiba dakuma kwarjini ah idanun mutane Sulaiman ma yayi kyau cikin normal atire dinshi cikin wanda suka halarci taron harda Mallam Hudu dom kuwa shima cewa yayi bazaiso yayi missing daurin auren Almustaphan shiba,Mai Martaba ma ya halarci taron wanda hakan bawai yabama mutane wani mamaki sosai bane dafari sabida akan gayyaci sarki zuwa daurin aure kuma yazo sannan dubada yanda Daddyn shima bawai wani karamin mutm baneba seda aka daura auren sukaji an ambaci Almustapha Abdulrahman Sulaiman kowa mamaki yakamashi yayinda suke bidan jin wani information amma babu hali don masu gulmar sede suyitayi ah tsakaninsu......
Sulaiman yawanci abokanansa ya gayyato amatsayin Almustaphas friends,suna tsattsaye Sulaiman yazo yasamu Almustapha yana"Contulations ango"......
Murmushi Almustapha yayi wanda yakarama kyakyawar fuskarsa kyau da annuri batareda yace komai ba don yalura Sulaiman rama abunda yayi masa ranar daurin aurensa yakeson yi yanzu don tundazu yake damunshi............

STORY CONTINUES BELOW


Jin Almustapha baice komai ba yasa yasake taba kafadarshi cikeda tsokana yace "Yaya Almustapha tun dazu nake cewa congratulations ango amma kaki kulani",yayi maganar ashagwabe jan hancinshi Almustapha yayi cikeda mugunta yace"silly Boy"....

Sulaiman kaman zaiyi kuka yace"dazafi fa Yaya!"....
Serves you right Almustaphan yafada yana tafiya yabarshi agurin tsaye........
Binshi yayi cikin sauri sannan yace zamuje gaisheda mahaifiyar Asma'u kakarta da Antynta fa.........
Not today Almustapha yabashi amsa yana cigaba da tafiya cikin sauri Sulaiman yace "to ai Dad ne yafada baniba?"......
Tsayawa yayi cak sannan yadubi Sulaiman din irin he wants to be sure dinnan gyada masa kai Sulaiman yayi sannan yace suje bangaren su Aliyu sauran abokansu nanan sesu shiga tare.........
Binshi Almustapha yayi dukda shidai aganinshi is too early yadauka se washegari ne ake zuwa gaisuwar amma tunda Dad ne yace hakan babu yanda ya'iya...........

Sanda suka Isa sunsamu friends din nacin abinci haryanxu seda suka gama sannan suka tashi suka fice Aliyu ke directing dinsu harzuwa bangaren Mommy don sunfison sugaisa da Hajja tukunnan tunda suka isa bangaren Mata keta guda"aiyirrrrrrrrrrrrririiii!" ana ga angon Asma'u yazo gaisuwa da abokanansa........

Ah parlourn Mommy aka saukesu sannan aka shiga kiran Hajja ah dakinta dake cikeda tsofi kamanta dasuka halarci taron cewa tayi itafa bazata zoba indai mijin Asma'u ne dama Aslam ne......
Hankalin Mommy yatashi don tarasa ta'ina zata fara convincing dinta ma dakyar tayi karfin halin cewa don Allah Hajja kiyi hakuri musamman sukazo gaida ki cikeda bacin rai Hajja tace Ina ruwana to,inbanda tsugudidi ninasasu suzo ne?...
Rarrashinta aka shigayi ana tayi hakuri kobadon su ba kodan bakin dake gurin kada yazama abun magana dakyar Hajja tayarda tana wallahi indon tashine ko ganin idona bazaiyi ba amma yaci albarkacin wanda yazo dasu damakuma bakin dake gidan nan ajiyar zuciya Mommy tayi don bakaramin relief taji ba jin Hajjan tayarda
haka Hajja ta sabi mayafinta tafice tareda yan rakiyanta abaya ah parlourn tasame su zuwa tayi ta hakimce kan three seater murmushi Sulaiman yayi ganin Hajja din don ya lura irinsu xa ayi rigimammun tsofi don haka yace"Ina wuni Matar mu?"....
Hararanshi tayi sannan tace Matar ku nacan badainiba dariya Sulaiman yayi sannan yace kai tsohuwa kishi trun yanzu inaga ankaita gwanda kidaura damara tun hanzu yayi maganar cikeda zolaya hararanshi tayi itadai kafin abokanan suka shiga gaida ta tana amsawa rai adagule shidai Almustapha yaji muryar sounds so familiar amma seya kasa dagowa don nauyinta yakeji sosai tareda kunyan dabaisan dalili ba.....

Seda yaji kaf abokanan sun gaidata sannan yadago ahankali yadubeta tareda cewa "ina wuni",duk da kuwa mamakin daya tsinci kanshi ah ciki ansawa tayi adakile sannan tatashi ta tafi kowa yana mamakin halin Hajja din"So she's her grandmother yafurta maganar ahankali batareda kowa yajiba".......
Mommy ne tazo suka gaisa tareda sauran mutane sannan suka nufi bangaren Ummi.......
Nanma ah parlour aka saukesu anata guda har Ummi tashigo parlourn da mutanenta cikin shiga ta alfarma Almustapha kasa dagowa yayi ya kalleta sabida wani irin kunyarta dayaji ya lullubeshi lokaci guda kanshi akasa yagaidata Ummi babu laifi tadan yaba da yanayinshi aranta tana addu'ar Allah yasa he's good at heart bawai pretending kawai yakeyi ba nan suka fice bayan Mommyn Gombe tace su zauna ah guests parlourn sujira Amarya da kawayenta suzo suyi hotuna donkuwa Sulaiman yakira Aisha yafada mata zasuzo damai hoto ayi bayan daurin aure su shirya Asma'u, kuma tafada ma wani babba inza a bari shine tafada ma Mommyn Gombe donta lura she's socialize gakuma saukin kai ne da'ita.........
bude kofar dakin Mommyn Gombe tayi sannan tace Ina kuke ne"Aisha?"...
Aisha dake daurawa Basma dankwali tace na'am Mommy gani takarashe maganar tareda tasowa takaraso gaban Mommyn....
Sunafa jiranku ah guest parlour nacan waje kokun fasa hotunan ne?...
Cikin sauri Aisha tace zamuyi Mommy anayiwa Asma'un kwalliya ne kuma kinsanta tana iyacewa bazata jeba.......
Karasa banko kofar dakin Mommyn Gombe tayi sannan tace tana ina?...
Nuna mata wani daki Aishan tayi nan
Mommyn Gombe tashige dakin, Asma'u ne zaune gaban mirror se makeup artist dake tsantsara mata kwalliya wanda tunkan agama Mommyn talura yartata bakaramin kyau zatayiba......
Duban makeup artist din tayi sannan tace kunkusa gamawa ne?.....
Eh Hajiya budurwar tabata amsa,gyada kai Mommyn Gombe tayi sannan tace abokanan mijinki da shi kanshi sunajiranku zakuyi hotuna Asma'u sauran inji kince bazakije ba kinsan halina nikam juyawa tayi tadubi Aishan tace if she misbehaves let me know kinji.......
Gyada kai Aisha tayi, Asma'u dai takaici kaman tayi yaya ahaka aka karasa kwalliyar sannan aka mata shiri cikin wata hadaddiyar lace coffee brown da touchoff na golden colour yasha dinki mekyau sannan aka daura mata gyale golden akai suka fice kowa yaganta seya yaba kyaunda tayi hakanan anata guda har suka fice daga bangaren zuwa parlourn bakin........
Suma kawayen amarya sunsha anko sosai sunyi kyau abunsu,Aisha ne tafara shiga tasanar musu da isowansu Asma'u zuciyar ta bugu yakeyi kaman ze bulluko haka suka shiga parlourn ita da kawayenta wanda tundaga bakin kofa camera man yashiga kashesu da hotuna haka abokanan angoma shidai Almustapha yana hakimce kan three seater kanshi ah kasa..........
Har kujerar suka rakata tazauna gefenshi yayinda bugun zuciyar ta yakaru, Aisha ne tayima Zahra rada"kinga lovebirds ba har kayan ma iri daya suka saka"....
Yar dariya Zahra tayi sannan tace tabbas shima gashi kayan jikinshi coffee brown da golden colour dinne kaman wanda suka hada baki......
Kikasani kosun hada din,dariya suka kumayi Aisha nakarawa da Allah kau mutum baya taba gane kan Ma'un nan.......

STORY CONTINUES BELOW


Sulaiman ne yacema camera man din yafara ma Amarya da ango separately se ayimasu general gyada kai yayi sannan yadauke su ah position din da suke kafin yace sucanza style shidai Almustapha still yayi ko motsi baiyiba haka Asma'u ma don ita tunanin daya isheta ma ya isheta........
Camera Man dinne yace kudan gyara ma as in more romantic zaifi kyau......
Mischievous smile Sulaiman yayi don ya lura camera man is making his work more easier ma karasawa yayi gabansu sannan yace ma Almustapha yamatso kusa da Asma'u Itama ta matso haka babu yanda suka iya suka matso din sannan camera Man din yadaga hannun Almustapha yadaura kan na Asmau bakaramin shock sukaji ba dukansu biyun sannan yakoma baya yana"smile a little"......
Asma'u ne kadai tayi faking smile yadauka sannan yace"yauwa amarya to ki dan kwantar dakanki ah jikinshi",cikin sauri Almustapha da Asma'u suka kalli juna wanda yabada wani style din kuma dasauri me hoton yadauka gashi suna dab da dab har suna iyajin numfashin juna ga kamshin turarrukansu daya garwayu yabada wani special scent tareda sasu feeling wani iri dariya sukaji yan parlourn nayi wanda yasa Asma'u jin kunya don kasa dagowa ma tayi ta kallesu seta tsinci kanta da sunne kanta cikin physique chest din Almustapha donkuwa gani take ananne kadai she'll be safe from them daukansu me hoton yakuma yi ahankan sannan suka fita suka basu guri donsun lura they need privacy..........
Lumshe idanunta tayi sosai tunda ta sunne kanta ah kirjinshi sabida wani irin feelings datake ji tundaga gangan jikinta dama zuciyarta baki daya,wani irin special feelings dabata taba jiba tunda take ah rayuwarta wanda har hakan kesa bugun zuciyarta karuwa tareda tsoron kada yayi exploding har Almustaphan yagane halin da take ciki,fatan ta daya sufita subasu guri tasamu tagudu don bayan abun kunyar datayinnan bata tunanin sake hada idanu da abokanansa........
Abunda bata saniba shine sun jima da fita sukam Almustapha kuma yakasa cireta daga jikinshi sabida ko tabata bayasonyi because bemanta wannan electrification shock dayakejiba duksanda jikinsu yayi colliding ganin bata da niyar barin jikin nashi yasashi karfin halin cewa"they're gone,kitashimin ajiki".......
Saurin tashi tayi daga jikinshi batareda ta kalleshiba zata gudu yayi saurin riko hannunta takoma tazauna......
"Kabarni don Allah cikin gida zan tafi".......
Analyzing fuskarta yayi don taki kallonshi kwata kwata sema wasa da fingers dinta data shiga yi.......
Dan tsaki yayi sannan cikin cool voice dinshi yace"So, she's your grandmother?".....

Batasan sanda tadago ta kalleshiba jin abunda yafada din atake kuma taji idanunta sunciko da kwallah tagane wayeke nufi amma seta tsinci kanta da cemishi"Who?".......
Dan shiru yayi na dakiku kafin yace"That old lady".......
Wannan karan kasa holding tears dinta tayi seda suka zubo don bazata taba manta abubuwan da Hajjan tayi mata ba data tuna takejin inbatayi kukaba hankalinta bazai taba kwanciya ba, hawayen nazuba ahankali kuma ta gyada masa kai alamun eh........
Bayason yaga mace na kuka kwata kwata barin ma ace shine sanadi don haka yaciro hankerchief yamika mata cikeda command tace "wipe away your tears right now".....
Babu musu ta karbi hanky din tashiga goge kwallarta ita kanta batasan daliliba bata iya bijire maganar Almustapha indai he's serious seda ta goge hawayen tas wanda har yabata mata kwalliya amma baidamu ba......
Mika masa hankyn tayi seyaki karba kafin directly yace"it seems like she's giving you a hard time because of me?"yakarashe maganar idanunshi nakanta.......
Ji tayi wasu kwallar na shirin zubowa amma setayi kokarin holding nasu,itakam tana iya cemishi Hajja ta tsaneta ya karyatata donkuwa tasan bakowa bane zai yarda kaka zata tsani her very own granddaughter without a genuine reason atleast gwanda tace mishi sabida shidinne kawai kilan ya yarda din don haka tace eh......
Cikeda tausayinta yace"and the rest of your family?",yakuma mata tambayar idanunshi nakanta wanda kesata feeling uncomfortable......
Wasa takeyi da fingers dinta sannan tace"farkon da abun yafaru sunji haushina har suka gujeni amma yanzu nasan sun sauko sede nasan ba lallai bane su cire zargin dasukemin gabadaya ah zukatansu", takarashe maganar murya ah karye irin abun na matukar damuntan nan......
Yafi five minutes baiyi maganaba kafin dakyar ya'iya cewa"I'm sorry".....
saurin kallonshi tayi in desbelief don bata taba tsanmanin wayannan words din daga gareshiba......
Gyada mata kai yayi ahankali alamar eh he mean it kafin yamaida hankalinshi kan wayarshi yashiga inbox dinta don tura mata massage because bazai iya long magana ba tundazu yake analyzing yanda zaimata bayani dayayi yunkurin magana se yakasa shiyasa yayi deciding mata text kawai....
nan
yafara mat typing kamar haka...

STORY CONTINUES BELOW


_Because of me you went through alot Asma'u,I'm sorry and I promise you that"I'll prove to your family cewa babu komai tsakaninmu, I'll prove to them that I'm a good person and we never did what they were thinking,zan cire zargin da family din ki keyi miki ah zukatansu insha Allah,but I need sometime to do that and as soon as everything is back into its right place I'll free you from this relationship"I PROMISE!"_.....

Tura mata massage din yayi tana zaune gefenshi taji wayarta tayi kara alamar massage yashigo daga wayar tayi daga cinyarta atleast shigowar massage dinma zeyo freeing dinta from this akwardness don duk atunaninta bewuce massage din MTN bane ba sede to her own surprise taga "Mr Taciturn".....
Dagowa tayi tadube shi cikin sauri still idanunshi nakanta mayarda idanunta tayi kan wayar sannan tashiga karanta massage din seda ta gama tas sannan ta kife wayar tama rasa abun fada sabida bata taba tsanmanin haka daga Almustapha ba she never thought he'll be simple like this,so "he cares?" shine tambayar datayima kanta dukda kuwa his last sentence namata yawo ah kwanyarta na"he'll free her from this relationship",hakan na nufin ze saketa kenan zata zama bazawara in the future kenan wasu hawayene suka taru ah idanunta kunsan Asma'u da yawan kuka amma setayi saurin rikesu jin wata zuciyar nace mata"this's the best Asma'u atleast Almustapha care for you harma yana yakinin clearing mind din iyayen ki what could be better than this?..
Tasan tanason Almustapha sede bezama dole shi yayi reciprocating love dintaba bakowani so bane yake zama successfull tama gode Allah tasamu chance din zama dashi for some time and zata danyi rayuwa da Ummin dataji tana kaunar matar tun day one din haduwarsu may be ma intazauna dashi tagano yanda aka cutar da Ummi tunda Dad yace babu irin asibitin da ba aje ba amma ance anrasa gane meke damunta voice din zuciyarta ne kecemata "this's a great chance Asma'u,accept it the way it's"............

Kakalo murmushi tayi sannan tadube shi tace"thank you",don ita bazata iya harkar text ba yanzu tunda Allah yabata bakin magana.........
Gyada mata kai kawai yayi sannan yatashi zai fita har ya isa bakin kofa tayi karfin halin cewa"Yaya Almustapha?"......
Tsayawa yayi cak jinta ambaci sunanshi batareda yajuyoba....

Tashi tayi daga zaunen da take sannan tahadiyi yawun bakinta takumayin karfin halin cewa"Can we be friends?".....
Wannan karan juyowa yayi yana kallonta blankly dan kwantar da kanta tayi gefen kafadanta cikeda shagwaba tace"pleaseee",tayi maganar cikin siririyar muryarta tasan she need to be close to him sabida tasan matsalolinshi dama kuma na masarautar bakidaya shiyasa tayi requesting friendship dinsa......
"No",yabata ansa shortly sannan yajuya yatafi he don't need a friend ah rayuwarshi anashi gaanin his family members ma kadai sun isheshi rayuwa suma don yazama masa dolene bayason zama ma mutane matsala ne kwata kwata tunda gashi itada taita shige mishin ma yanata gudunta abaya dukda hakan besa ta tsiraba harta tashiga wani hali sabida shi......
Gani yakeyi dukwanda zaice zai kusanceshi zai shiga hali mai wuya shikuma shiyasa bayason hakan kwata kwata gwanda shi yariga yasaba da irin wannan rayuwar daman...........

Asma'u kuwa bakaramin sosuwa ranta yayi ba ga ansan dayabata aiko ba komai seyayi kara ita gwanda yaki kulatama sau dubu da "No" dinnan dayace mata......
Tsuke baki tayi sannan tace"he'll never change"......
Tana cikin wannan tunanin ne Aisha da Zahra suka shigo suna dariya"halan kunma manta da existence dinmu ko?".....
Sukayi maganar atare harararsu Asma'u tayi sannan tace"kufa baku da matsala wallahi".....
Dariya Zahra tayi"inako mukaga ta matsala kuda kuke da ita kunyi solving dinta ae"....
Rankwashi Asma'u takai mata kaman zatayi kuka hakuri Zahra tashiga bata kafin Asma'u tace suntafi ne?.......
Aisha ne tace mata munsha hotuna kam yau dinnan dukda naso muyi dake amma mijinki yawani zo ya boyeki anan takarashe maganar tana tabune baki.....
Kuma daya fito koya kalli inda muke bare yabamu hakuri cewar Zahra...
Dariya Asma'u tayi sannan tace kukuka sani dai nidai kuzo mukoma cikin gida..........
Haka suka tafi cikin gida abun su sunata tsokanarta itadai bata kulasuba tunda tasan babu abunda tayi........

STORY CONTINUES BELOW


******
Gudu Talatu takeyi kamar wanda zata tashi sama dukda kuwa irin mahaukacin nishin da takeyi ba ita ta tsayaba seda ta isa gurin Sama'ila dubanshi tayi tana haki tace"Sama'ila nashiga uku Ina Magajiya?"...........
Tana inda take mana Talatu yayi maganar ranshi bace donshi ta tsoratar dashi ma dagari........
Don Allah kaje kace mata Almustapha yayi aure,sarki yayima Almustapha aure yau dinnan kuma wancan yarinyar takarashe maganar muryarta na stammering don bakaramin damunta abun yayiba.....
Hararanta Sama'ila yayi sannan yace badole se an fada mata ba kibarta da abunda yadameta yanzu,ke Talatun nan nalura kin iya tada zaune tsaye wallahi yakarashe maganar yana cigaba da shan rakenshi.......

Cikeda damuwa tace"Haba Sama'ila don Allah kafada mata koda yanda zatayi tafito daga wannan kurkukun wallahi bakasan yanda nakeji bane shiyasa
nikam gani nake karshenmu yazo ah masarautar nan.......

Sama'ila daya gama shan raken bakinshi yana shirin kutsiran wata yace"karshen kudai amma banda ni nikam,aiki akasani nayi nabi umarni babu komai nawa aciki".....
Sakan baki Talatu tayi cikeda mamaki tace"yanzu fisabilillahi abunda xakace kenan Sama'ila,amma gaskiya kaban mamaki?"...
Ahhhhh! Ah to mekikeso ince,kefa abunnan takai takai ne inzakisan inda dare yayi miki gwanda kisani tun wuri don wallahi nalura matan nan dakyar inzata kai labari......
Wannan karan kuka Talatu tasaki "Amma dai baka da amana Sama'ila".....
Dariya ya shekeda sannan yace"amana fa kikace Talatu?"....
Gyada masa kai tayi tana kuka kuma fashewa yayi da dariya yana"kehar kinada bakin cewa banda amana akwai wanda yaci amanar masarautar nan ma irin ku keda Magajiyan baki daya ware hannunshi yayi sannan yakarada aimu fa yan abi yarima asha kidine wanda yake cashe shi zamuyi yayi sabida mutsira dakanmu amma ke tsabar dakikanci duk abunda matarnan tayi miki wai kina tareda ita....
Goge kwallarta tayi sannan tace nidai kafada mata sakona don Alllah don tasan tagurin shi ne kawai zatasamu sakon ya isa ga Magajiyan......

Tashi yayi daga zaunen dayake sannan yace zanfada mata anmafa sede inza abani na kashewa cikin sauri Talatu tace wallahi za abaka kaidai kaje ka fada mata......
Murmushi yayi sannan yace angama Talatun Magajiya yanzu zanje infada mata to...........
Haka yatafi tana hamdala tajuya takoma cikin masarautar shiko Sama'ila koda yaje becema Magajiya Talatu ne taturo shiba kawai cemata yayi yakawo mata labari......
Duk tayi baki tafita ah kamanninta sabida kin cin abinci da takeyi ga wanka ma batasonyi yasa duk kwanannan kaikayi kedamun ta sosai ajikinta haka tadinga soshe soshen jikin kenan.......
Labarin miyene Sama'ila tayi maganar ahankali sabida rashin karfin jiki datakeji ......

Yarima Almustapha yayi aure Uwargijiyata,yau se biki akeyi a masarautar nan karkiso kiga farin cikin da Mai Martaba yakeciki yasake gutsirar rake yana sha sannan yakarada"ankashe kudi fa,abu yayi kyau gaskiya".......
Tunda yake maganar tadingajin wani irin hajijiya na dibanta,dakyar ta iya rike jikin bango kozatayi retaining kanta amma ina sede jiyayi tafadi ah kasa sume.........
Ihu yasaki wanda yakira attention din sauran dogarayen sukazo cikin sauri nan yake cemusu suma tayi daya daga cikinsu ne yatafi cikin gida don kiran bayi mata suzo sudaurata kan gado ba ajima ba segasu jikina bari suka daga ta suka kwantar kan gado........
Sama'ila ne yatafi sanar da Mai Martaba amma baisamu ganinshi ba haka Sulaiman ma don haka yawuce straight gidan likitan wanda acikin Masarautar yake daman matarshi ce ke gida shi bayanan rokonta yayi takira likitan tafada mishi aikuwa hakan akayi ba ajima ba yace yana zuwa inda Magajiyan take.......

Komawa yayi still tana kwance ah sume daya daga cikin bayin tana shafa mata ruwa ah fuska amma ko motsi batayi suna cikin hakan ne sega
Likitan yakaraso dubata yashigayi cikin gaggawa sannan yasakamata drip tareda yi mata allura nan yace zuwa anjima zata tashi but they've to transfer her to another room don nan yayi datti dayawa gawani tsami dake tashi agurin Sama'ila ne yace "dole seda izinin Mai Martaba"....

Zanyiwa Mai Martaban magana innasamu ganinshi cewar likitan sannan yayi musu sallama yafice...

****

Dayanma akazo daukar Asiya don kaduna za akaita bakaramin kuka tayiba haka suka kankame juna itada Asma'u dakyar aka rabasu suna kuka haka aka tafi da'ita bayan Daddy yahadasu dukkansu biyun yayi musu nasiha me ratsa jiki haka iyayensu mata ma...........

Hajja kam anacikin yan rakiyan Asiya ita ah dole me jika dukda kuwa tanason zuwa taga gidan Asma'u din amma girman kai yahanata..........

Bayan maghrib akazo daukar Asma'u ma dakyar aka banbareta jikin Ummi tana kuka me tsuma zuciya Ummin ma seda tayi hawaye because takasa controlling tears dinta Matar Waziri da Matar Galadima dama wasu manya manyan matan cikin masarautar ne sukazo daukarta haka aka tafi da ita Masarautar Zaria....
Bangaren Mom aka ajiyeta Mom tashi tayi tarungume ta tana 'Yata tadawo,I missed you so much.....
Asma'u dai batace komai ba se hawaye........
Sedare Mom tamata nasiha sosai sannan tarakata har sabuwar bangaren Ummi nada da aka gyara wanda already su Afiya, Amira,Ummi da Almustapha sunkoma ciki tun a week to bikin suda masuyi musu aiki

Har dakin Ummi takaita tazaunar da'ita sannan tadubi Ummin dake sanye cikin sabuwar shadda hadaddiya tasha dinki don Itama ado akayi mata sosai na bikin Danta tace Khairiya yauga sirikarki nakawo miki ita har dakinki,i hope you'll get well soon we really need you, we've alot to talk about Mom takarashe maganar idanunta sunciko da kwalla donba karamin tausayin matar takejiba.......
Asma'u dake hawaye takarasa gaban Ummin tayi kissing forehead dinta sannan tace"Ummi na nayi kewar ki",takarashe maganar tana kallon fuskar Ummin data lura akwai alamun excitement ah fuskarta data ganta.....
Murmushi Asma'u tayi tana rikeda hannun Ummi don jitakeyi har cikin ranta kamar Umminta ne na asali tabiyota gidan mijinta.......
Tajima tana zaune tanayima Ummin addu'a na Allah yabata lafiya kafin Mom tace muje inkai ki dakin ki gyada mata kai tayi sannan sukaje har dakin ta ajiyeta kan gado kafin tayi mata saida safe tafice Asma'u jitayi hawaye sunfara zuba tunawa datayi da furicin Daddy nacewa dayayi babu mai kwanan gidan amare da ankaisu kowa yadawo gida ita yanzu shikenan kwana zatayi ita kadai gashi bataga su Afiya anan ba tunda aka kawota.........
Tana cikin wannan tunanin ne taji anbude kofar dakin Almustapha ne yashigo ya na "Sulaiman stop disturbing my life circle nagaji bacci nikeji",yakarashe maganar tareda rufe kofar dakin gam harda sa key bayan yashigo yalura inba haka yayi ma Sulaiman dinba bazai barshi da zancen rakiyar ango zuwa gun amaryaba.......
Bubbuga kofar Sulaiman yayi yana"aikatsaya ko good night inyi maka ko Yaya?".....
Jijjiga kai yayi yana Smilling "Sulaiman baida matsala wallahi"yakarashe maganar tareda juyowa yana kallon cikin dakin yanzu arba yayi da figure dinta dake zaune tsakiyar gado tana lullube cikin alkyabba gawani gyara dayaga anyima dakin nashi sewani kamshi na musamman dayake tashi tako ina gadon ma ansaka tend me dan shara shara anrufe kowani side seta gaba ne ah dan bude wanda hakan yabashi daman ganinta mamaki yakeyi miyasa za akawo mishi ita dakinsa fisabilillahi what do they think?..........
Jiyayi Sulaiman dake bakin kofa yace "toshikenan tunda bazaka kulaniba aci amarci lafiya".....
Wannan karan ba Almustapha ba har Asma'u seda maganar ta doki kunnenta........Saurin yaye alkyabbar tayi daga jikinta sannan tataso daga tsakiyar gadon tadawo bakin gadon tasauko da kafafunta kasa tana niyar tashi setaga yafara taku ahankali zuwa direction din da take kirjinta ne yashiga dukan uku uku,the more he comes closer the more heart dinta yake beating so fast har ya iso gabanta wani tsoro ne yakuma shiganta ganin yana shirin dukowa kusa da ita rumtse idanunta kawai tayi tanajiran jin mezai mata amma saitaji shiru harna kusan three minutes bude idanunta tayi setaga babushi agurin abunda bata saniba shine Almustapha phone dinshi yadauka akan bedside drawer sannan yafice........... +

Zagaya bangaren nasu yayi baki daya kozai samu empty room dinta da akayi mata jere amma duka three extra rooms din arufe suke dayan na Mai Martaba ne sekuma biyun ne daya nata wanda baisan wannene cikiba.........

Tsaki yadanyi shifa bayason disturbance kwata kwata arayuwanshi yama za ayi akawo masa ita dakinsa fisabilillahi.......
Dialing number din Sulaiman yayi amma yayita ringing bedauka ba hakanan yawuce dakin su Afiya shima Afiya hartayi bacci se Amira dake waya jin anbude kofar ne yasata saurin sa wayar ah karkashin pillow tareda dagowa don ganin waye ne........
Hararanta Almustapha yayi don tabbas by looking at her yasan bata da gaskiya......
Daurewa tayi tace"Ina wuni Yaya Almustapha?"...
Batareda ya amsa mata gaisuwa ba yace"ita wannan yarinyar iyayen ta basu kawota da kayan daki bane?".......

Cikeda mamaki tace"sunkawo ta dasu mana meka gani?".....
Wannene dakinta?....
Nakusa da dakin Ummi tabashi amsa ranta bace don bataji dadin abunda yafada dinba.......
"Arufe ne".....
Yaya Sulaiman ya rufe dazun and yatafi da keys din,tsaki yayi sannan yafice ah dakin yana"zanyi maganin yaron nan ah swear"......
Itadai Amira komawa tayi tayi kwanciyarta tareda sake zaro wayarta daga karkashin pillow tacigaba da harkan gabanta.....

Yafi 10 minutes kafin yayi deciding komawa dakin koda yabude samunta yayi still tanazaune agurin daya barta ganin yashigo dinne yasata saurin tasowa tace"Yauwa Yaya Almustapha don Allah ina kayana suke,I need to change".......
"I don't know", yabata amsar rai bace donkuwa shima bawai yasan inda kayan nata yakeba to miyasa zata tambayeshi"....
Turo baki tayi sannan takarasa gaban wardrobe din data gani budewa tayi ahankali amma sedai duka kayan namiji ne ah ciki wanda suke jere neatly kai kace wardrobe din macene gashi kowani samfarin kaya an ajiyeshi bangare guda seda tagama kallemai wardrobe sannan takoma bakin gado tazauna tareda daukan wayarta tashiga kiran Aisha ba ajimaba tadauka........
Amarya Amarya!
Ayya Aisha banason wasa yanzu I called to ask you"where are my belongings?".....
Suna dakin ki mana Aisha tabata amsa kai tsaye,are you sure Asma'u tayi mata tambayar tanason ta tabbatar....
Yes, I'm very sure Asma'u,saida safe Asma'u tayi mata sannan ta katse call din duban nannauyan kayan jikinta tayi itadai Allah yagani bazata iya kwana dasuba duban bangaren da Almustapha yake tayi sede to her own surprise ashe har ya kwanta akan carpet ya lullubu da blanket da alama ma har yayi bacci abunshi........
Turo baki tayi"yanzu anason indinga kwana da katon gardinnan ah daki daya kenan?"......
Kasa bama kanta ansa tayi don haka tatashi takoma bakin wardrobe din nashi wani t shirt dinshi tasamu fari sekuma pjamis nashi dauka tayi tawuce bathroom tana wallahi sakawa zanyi don bazan iya kwana da wayannan kayan ba.........
Yana kallon ta don bawai baccin yayiba dukda yana mamakin yarinyar yazata dauki kayan namiji tace zatasa yana cikin wannan tunanin ne segata tafito sanye da kayan jikinta sewani yawo take cikin rigar don bakaramin yawa yayi mata ba dan gwanda wandonma yazauna sewani turo baki takeyi kaman zata fashe da kuka murmushi yasaki tareda jan blanket din yarufe kansa aransa yana fadin"she's so silly".......
Bakin gadon takarasa tadauki mayafinta tayafa sannan tahau kan gadon ta lullube cikin blanket ba ajima ba wani nannauyan bacci yayi awun gaba da ita without any fear........

STORY CONTINUES BELOW


******

Likitan besamu ganin Mai Martaba ba seda aka fito daga sallar maghrib donkuwa yini yayi very busy yana karban baki tareda gaisawa da jama'a......
Gaida Mai Martaba yayi cikeda girmamawa sannan yace "Madam babu lafiya fa nayita nemanka infada maka bansamu ganin ka ba"..........

Wace Madam din Mai Martaba yayi maganar cikeda mamaki......
Uwargida ranka shidade, kana nufin Magajiya?Mai Martaban yayi maganar yana duban likitan,gyada masa kai yayi ahankali....
Subhanallah meke damunta and yaushe tafara rashin lafiyar yayi maganar cikeda damuwa.....
Nan likitan yashiga yimasa bayani sannan yakarada nace sumaida ta guri mai tsafda se one of the guards yacemin seda izininka dole so,nayita nemanka alokacin kuma bansamu ganin ka ba because you were very busy........
Ayya kasan jama'a se ahankali yaudin dole nayi attending to them but zansa ayi transferring nata to her side harzuwa sanda zata samu lafiya.........
Gyada kai likitan yayi harzai tafi sekuma yadawo sannan yakara sunne kanshi kasa yana dan wasa da fingers dinsa alamar he's feeling nervous yace"inba damuwa nikam inason muuyi wata magana ranka shi dade"......
Murmushi Mai Martaba yayi sannan yace "feel free Doctor kafadamin abunda ke ranka".......
To shikenan sannan yace"Daman maganar Madam dinne anawa ganin by now kam aeta horu inaganin yakamata kayafe mata hakanan we do make mistakes and learn from them abunda kayi matama kadai ya isheta ishara gobe koda wasa nasan bazata sake yimaka ba,amma innayi shishigi ah al amarinka kayi hakuri ranka shidade likitan yayi magana kanshi ah kasa..................

Dan numfasawa Mai Martaba yayi tareda jinjina kai sannan yace babu komai Doctor kuma nagode da shawararka kwarai zanyi tunani akai.....
Godiya likitan ma yayi sannan yayimasa saida safe yatafi..........
Koda Mai Martaba yakoma bangarensa jakadiya(head na kitchen dama kuma bayi baki daya)yasaka aka kira masa sannan ya umarce ta da taje tasa amaida Magajiya bangarenta yanzu aikuwa babu bata lokaci ta aiwatar da hakan sannan tazo tafada ma Mai Martaba komai ya auku successfully.........
Mai Martaba har bangaren Magajiya yaje yadubata sede tana bacci don haka bema jimaba yakoma nashi bangaren dukda yana mamakin ramewar da Magajiyan tayi sabida shidai ah iya saninshi ana bata ishashen abinci.........

*****

Karfe 4:30am alarm dinta yashiga bugawa wanda yafarkar da'ita daga nannauyar baccin da takeyi don kuwa tanada tabbacin dabadan alarm dinba babu abunda zai hanata makara yaudinnan tunda daman da gajiyarta takwanta,juyi tayi ah gadon tareda yin mika kadan sannan tayi kokarin tashi daga kwancen datake tana addu'ar tashi daga bacci......
Karema gadon kallo tashigayi jin wani kamshi na daban dake ziyartar hancinta seyanzu nema tatuna cewa ba agidansu takeba dan tabune baki tayi kaman zatayi kuka kafin tasaukar da kafanta kan lallausar kafet din,bandaki tashige tadauro alwala sannan tafito hasken wutan bandakin ne ya haska mata direction din da Almustapha yake still baccin shi yake hankali kwance mamakine yakamata don itadai ah gidansu duk inda hudu tayi to duka samarin gidansu sun tashi daga bacci kenan don ko ranka bayaso se Daddy yasa antakura maka katashi tun baswaso har yariga yazame musu jiki yanzuma.......
Wata zuciyar ne kuma tace kiyimasa uzuri mana Asma'u kowafa yagaji jiyan nan.......
Dawannan tunanin ne takarasa gaban gadonta sekuma alokacin ta tuna batada hijab ma kwata kwata sannan mayafinta ba lallai yarufe mata jiki sosai ba har tasamu tayi sallah......
Dan tsuka tayi kafin takoma bakin gadonta takwanta tana jin takaici har cikin ranta hakanan kuma takasa komawa bacci har aka shiga kiraye kirayen sallar asuba tana nan kwance.......
Lokacin ne kuma taga Almustapha yatashi daga kwancen dayake yashige bandaki yadauro alwala, harya fito zetafi masallaci tayi saurin tashi tasha gabanshi wanda seda tasa ya tsorota yadan koma baya cikin sauri.........
Ganin itane yasashi cewa"miye hakan?".....
Marairaice murya tayi"aiya banida hijabin dazanyi sallah kanunamin inda kayana suke"......
"Bansan inda suke ba",yabata ansa kai tsaye yanashirin fita amma taki bashi hanya dafe kai yayi rai bace azuciyarshi yana"what's all this nonesense da Sulaiman yajamishi, he'll surely deal with him inya hadu dashi dasafe"......
"Get out of my way",yayi maganar cikin cool voice dinshi.......
Make kafada tayi"naqi nikam nima se kafadamin inda hijabi na yake bafina sonyin sallah kayiba ae".....
Sakan baki yayi yana kallonta cikeda mamaki donshi yalura kaf duniyan nan babu mai gaya mishi magana son ranshi haka kawai irin Asma'u abunda baisaniba itanma tana shakkunshi kawai karfin haline takeyin wani sa'in,yana cikin wannan tunanin ne yaji ana shirin tada sallah ah masallaci don haka besauraretaba yadaga ta cidok kaman baby ya dire ah gefen kofan yafice abunshi binshi tayi tana don Allah kafada min lokacin sallah zai wuce.........
Kojuyowa baiyiba barema tasan koyaji metake fada yayi wucewarsa masallaci,tsaki tayi sannan tawuce dakinsu Amira amma suma arufe da alama ko tashi basuyiba haka dakin Ummi ma su Hindatu basu bude ba .......
Komawa tayi dakin Almustapha din tazauna bakin gado tareda rafka uban tagumi kusan sau uku tana tashi tana duba ko mutanen gidan sun tashi amma shiru dakin Mom ne kawai bata lekaba Itama don tasan adakin Dad take kwana shiyasa haka tacigaba da zama kamar wata marainiya har gari yafara haske,wuraren shida segashi yadawo kuma don wulakanci bebi takanta ba yakoma yayi kwanciyarsa abunsa batasan sanda tafara kukan takaiciba yanajinta tanata sheshekar kuka amma yaki kulata sede duk juyin dazaiyi yanajin kukan nata harcikin dodon kunnen sa...........
Tsaki yayi yana shikam Allah an hadashi da jaraba yau dinnan daukar wayarshi yayi tareda tura mata massage.....
"and what's the crying for?"...
Tanajin wayarta tayi kara jikinta yabata shine don haka tadauka tunanin kozai fada mata inda hijabanta sukene amma to her own surprise setaga wannan massage din wani kututun bakin ciki ne yakuma shiganta azuciyarta tana"inkasan wata bakasan wataba"......
Kara sautin kukan tayi wannan karan harda shikewa tashi yayi yazauna daram yana kallonta tareda sakin tsaki........
"Will you keep your mouth shut?".......
Goge kwallarta tashigayi lokaci guda batareda tadaina kukan ba"I'll kick you out of my room fa,nace miyasameki kinyi shiru what do you want me to do?",yayi maganar rai bace.......
Cikin kuka tace"Ina banyi sallah bane ba kuma kaki kabani hijab dina"........
Wani wawan harara yadaka mata sannan yatashi yafita ah dakin ba ajima ba segashi yadawo da hijab ah hannunshi ya wurga mata cikin sauri tatashi tadauka don ita damuwarta bewuce tasauke sallar dake kantaba bandaki tashige don sake dauro alwala yayinda shikuma ficewa yayi don zuwa yagyara ma su Amira zama don dakyar suka iya tashi suka bude masa dakin ma kuma ya tabbatar basu yi sallar asuban ba suma...........

STORY CONTINUES BELOW


Koda tayi sallar seda tagama addu'o'inta sannan taninke sallayarta tafice adakin kuma harlokacin baidawo ba dakin Ummi taje Hindatu kawai tasamu tana karatun alqur'ani kasa kasa se Ummi dake kwance kan gadon...
Murmushi Asma'u tayi sannan tasamu guri tazauna seda Hindatu takarasa surar da takeyi sannan ta rufe alqur'anin ta ajiye gefe tareda gaida Asma'u din...
Lafiya lau Iya Hindatu yakike?.....
Lafiya Lau Gimbiya .....
Ummi tayi sallah ko, Asma'u tayi tambayar cikeda curiosity.....

Murmushi Hindatu tayi sannan tace "tayi Gimbiya don kullum Yarima Almustapha dakanshi yake zuwa yataimaka mata inlokacin sallah yayi tayi karatun alqur'anin dakikaga inayima shikeyi kullum har gari ya waye bansan miyasa yaudin beyiba shine nima nace barinayi kawai tunda ansabayi tanaji"....
Allah sarki cewar Asma'u din dukda kuwa tana mamakin maganar Hindatu din aranta tana"kenan yaji maganata tun ranar?",kasa bama kanta ansa tayi and besides what matters is Ummi tasamu lafiya shine damuwarta"yajikin Ummin?"....
Dasauki alhamdulillah tunda tanacin abinci sosai yanxu bakamar da ba........
To Allah yatashi kafadunta,Amin ya Allah cewar Hindatu din kafin Jamila ma tashigo nan suka gaisa da Asma'u din......
Kafin tace"Gimbiya ance inkawo miki bayi guda goma su zasuna kula daduk wasu harkokin ki".......
murmushi Asma'u tayi"nagode amma nibana bukatan su"....
Ware idanu Jamila tayi sannan tace"dolene ai Gimbiya Mai Martaba ne ya umarci da ayi hakan "......
Jin Jamila ta ambaci Mai Martaba se Asma'u batayi musuba tace to shikenan suzo din amma meye da meyene zasuna yimin dama?......

Gyara zama Jamila tayi sannan tashiga lissafa ma Asma'u.....
Kinga kezaki zabi duk abubuwan dazasunayi miki kama daga kan gyaran jiki,firfita,wanke kaya,baki abinci dakuma gyara miki muhallinki dana Yarima..........
Girkifa su sukeyi?.....
Jijjiga kai Jamila tayi alamun a'a sannan Hindatu tace"abinci daga babban kitchen ake kaiwa kowa nacikin masarautar nan Gimbiya".........
Dan shiru Asma'u tayi sannan tace akwai kitchen ah bangaren nan ne?.......
Gyada mata kai Jamila tayi, murmushi Asma'u takumayi sannan tace"tonikam abincin mu anan zan nayi mana nida iyalina sabida haka kije kitchen din kisamo min kayan hadin abun kari yanzu"...
Cikeda mamaki Hindatu tace"bazaki wahalaba dakin barshi acan dinma jakadiya nakula dakomai inkuma akwai abincin dabai miki ba duk zatasa agyara"...
Kekam karki damu nayi niyane Hindatu.......
Murmushi Jamila tayi sannan tace akwai wasu kayan abinci anan dinma sede ba komai bane akwai...........
Miye da miyene akwai?...
Akwai doya,dankalin hausa dana turawa,akwai kwai da plantain sekuma akwai kayan miya acikin fridge,akwai danyen kifi da kaji gyararru duka se fannin shayi ma da kunu akwai kayan hadi irin kayan abincin gargajiya ne daman ba'a kai ga kawowa ba kilan se anjima Yarima Sulaiman zaisa ah shigo dasu.......
To ai shikenan tunda akwai wayannan zeyimin aiki for now batun aiki kuma na girki kukadai nayarda da sabida Dad yafada min kunjima tareda Ummi sauran duk kawai sunamin share share dawasu ayyukan dabaza a rasa ba shidinma banda dakin Ummi dana Yaya Almustapha.........

Cikeda jin dadin zancenta sukace in Sha Allahu za a kiyeye kuma dukda haka zan nema miki bayin damuka yarda dasu wanda zasu zama kuna tare koda yaushe koda guda biyune...
Godiya Asma'u tayi sannan tace suje kitchen din haka suka kama girki su ukun babu kama hannun yaro soyayyen doya sukayi seda farfesun kifi dakuma haddadiyar kunun gyada ko ina nagidan tashi yake da kamshi se yaba aikinta su Jamilan sukeyi kowacce aranta tana alhamdulillah Almustapha yayi dacen mata seda suka gama tas sannan tasa suka sauko da sabbin hadaddun kulolin da aka kawota dasu tasaka abincin kashi uku daya na Mai Martaba da Dad sekuma na Ummi daban hakana Mom ma daban daukan wani set din food flask din tayi bayan anwanke tasaka na Almustapha sauran kuma tace abarshi acikin cooler din dayake su Afiya da Amira zasuzo su diba Itama intayi wanka zatazo taci suma su Jamilan su tabbatar ankai na Mai Martaba da Dad din inyaso sesu dawo su diba.........
Murmushi sukayi suna sannu Gimbiya,itadai bajin dadin sunan take ba kwata kwata amma babu yanda ta'iya haka tadauki na Mai gidanta tawuce daki still hijabi ne sanye akanta tunda tabude dakin ni imtaccen kamshin turarenshi ke ziyartar hancinta..........
Hangoshi tayi zaune bakin gadon haryayi shirin shi cikin hadaddiyar sky blue shadda wanda bakaramin amsarshi tayiba sewani glowing yake abunshi murmushi tadan saki sannan ta ajiye abincin gabanshi"your breakfast Yaya".......

Ko kallonta baiyiba sema cigaba da danne dannen wayarshi dayayi dukda aranshi yana mamakin shin itace tayi kokuma wanda aka saba kawo musu ne tunda ah iya saninshi inma kawowan ne she's not responsible ah wurin kawomai abincin.......
Bata damu da shariyar shiba tafice abunta takoma tadauki abincin Ummi takai daki taimaka ma Ummin tayi tayi brush sannan tashiga bata abincin politely harta gama ci, batasan prescription na drugs datakeshaba don haka tafita daga dakin tunda tanada tabbacin insu Hindatu sunzo zasu bata tasha samu tayi already bayin sunyi kel kel da ko Ina na sashin sede banda dakunan data lissafa babu su ga kamshin turaren wuta take tashi me kwantar da hankali........
Batamayi tunanin Sulaiman na parlourn ba seji tayi yana santin abinci"nikam na shaida yau naxo gidan Amarya, Yaya kaji wani asirtaccen kamshi dake tashi agidan nan ga delicious abinci daniketa nausa tun dazu".......
Yanda yayi maganar seda yabata dariya,gaidashi tayi ya ansa sannan yashiga tsokanarta amma setaki bi takanshi tashige dakin Almustaphan tagyara tasaka turaren wutan nan ma..........
Sanda tafito ah dakin Sulaiman yafice se Almustapha dake zaune kan three seater idanunshi lumshe only god knows tunanin dayakeyi..........
Karasowa tayi tsakiyar parlourn jitayi yace"here are the keys to your room",yayi maganar yana pointing hannunshi kan keys din dukda tana mamakin ya akayi yasan tashigo parlourn behanata sa hannu tadauki keys dinba tawuce dakin don Hindatu tanuna mata dazu shima tashi yayi yawuce dakin Ummi nan bayin sukazo sukayi clearing kwanukan dasukayi breakfast dasu..........

Dakin tashiga tana karema ko Ina kallo tabbas iyayenta sunyi kokari don bakaramin tafiya da hankalinta kayan dakin sukayiba.....
Komai anjerashi perfectly,towel tadauka tashiga wanka abunta dukda tana ganin wani abu kaman swimming pool ah bandakin besata bi takanshi ba...
Sanda tafito tana daure da towel tazauna kan royal bed din tana goge jikinta ahankali jitayi wayarta tayi kara alaman text yashigo.......
Turo baki tayi tareda yin tsaki, da batadamu da duba text ba amma tunda talura Almustapha nason yi mata massage daganan duksanda taji wayarta tayi karar text koba daga shi bane setadinga jin urge din taduba.....
Yanzuma daga wayar tayi sede wannan dinkam shiya turo budewa tayi ahankali sannan tashiga karantawa........

" _kishirya zamuje gaidasu Abba?_ ".....

Ajiye wayar tayi jiki ah sanyaye tashiga shiri tafi awa daya batagama shirinba don tsayawa tayi contemplating mezata saka kafin daga karshe tayi deciding saka wata atamfar super tareda yin laffaya bakaramin kyau tayiba sannan tafito ah parlour tasameshi......
"Nashirya",tayi maganar shortly..
Batareda ya dubeta ba yayi gaba binshi tayi ah baya bangaren su Mom suka fara zuwa suka gaidata kafin sukayi bangaren Mai Martaba don kuwa Dad ma yanacan......
Ah parlourn shi suka samesu tunda suka shigo Dad da Abba ke kallonsu cikeda sha'awa........
Zama yayi kusa da Dad Itama ahankali tazauna gefenshi donba karamin nauyinsu taji tanajiba shiya fara gaidasu sannan ita"Ina kwananku"
Murmushi Dad yayi sannan yace lafiya Lau Daughter yaukuma nauyina akejine?.....
Murmushi kawai tayi tana sake cusa kanta cikin mayafi babu abun da Mai Martaba yakeyi se murmushi sake gaidashi tayi jin be amsataba dazun....
Inakwana Abba
"Lafiya Lau 'yata,ya bakunta?".....
Alhamdulillah tabashi amsa ahankali, murmushi yayi haka kawai yaji kunyar yarinyar yaburgeshi"munga breakfast mungode"wannan Karan Dad ne yayi magana kafin Abba yace"dabaki wahalar dakankiba 'yata feel free akwai masuyi kinji don't take the trouble next time".........
"Allah bakomai Abba".....
Allah yayi muku albarka yayi maganar yana kallonta.....
Amin ya Allah suka amsa duka kafin Mai Martaban yadubi Almustapha yace kasan yaddikon ka bata da lafiya kuwa?
Girgiza kai yayi alamar aa.......
Dan shiru Mai Martaba yayi sannan yace"kubi kudubata ansaka mata drip ma jiya,kuje da Asma'un taganta"......
Almustapha jiyayi wani irin kututun bakin ciki ya tokareshi arasa waza ace yaje yaduba batada lafiya se Magajiya his very own worst enemy.........
Jin yayi shiru Abban yace yaya dai Son,akwai matsala ne?....
Cikin sauri Almustaphan yace aa, toshikenan cewar Abba din sannan yasallamesu shidai Dad bece komaiba haka suka fita sukayi hanyar bangaren Magajiya gabadaya ranshi ajagule.........
Suna tafiya dogaraye nata zubewa kasa suna mika gaisuwa amma ko kallon inda suke baiyiba bare yasan sunayi Asma'u kuwa bataji dadin abunda yayiba setake ganin kaman wulakanci ne.........

Post a Comment for "GIDAN SARAUTA CHAPTER 6"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...