Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

GIDAN SARAUTA CHAPTER 4

GIDAN SARAUTA CHAPTER 4

- - Post a Comment
GIDAN SARAUTA

CHARTER 4
Magajiya jitake kaman ta make Sulaiman ah lokacin addu'a tashigayi Allah yasa kada yakuma magana, Mai Martaba ne yace bangane me kake fada ba kanason kacemin duk laifin da ake tuhumarsa dashi Kai kayi?......
Gyada kai yayi,fuska babu annuri Mai Martaba yace what about the evidence da aka nunamin shikuma mezakace akai?...
Dagowa Sulaiman yayi yadubi mahaifin nashi kafin yace wannan bansaniba Abba amma inada tabbacin cewa Almustapha mutumin kirki ne bazai taba yin abunda aka tuhumeshi dashiba.......
Cikeda bacin rai Mai Martaba yace dakata Sulaiman banason shashanci kana jina,kasan me kake shirin sakanka aciki kuwa,tukunnan ma inakasanshi,miye alakarka dashi dahar kake goya mishi baya, kasan mema yayi lalata ya'yan mutane fa Sulaiman,dafe kai Mai Martaba yayi because shi atunanin shi Sulaiman nada hankali bazai taba yin abunda yake fada ba.............
Sulaiman dake zaune gaban Mai Martaba hawayenshi yaki tsayawa yace"he's my Brother Abba, your very own Son,miyasa bazaka iya tunawaba,miyasa kake hukunta 'Danka bayan baiyi laifiba",wannan karan Magajiya ne ta zabura zuciyar na dukan uku janyo Sulaiman tayi daga zaunen dayake kafin ta wankeshi da mari dafe kuncin shi yayi kafin kuma yasake ankara ta kara mishi daya,kallonta yayi sannan yace Mama marin ki cannot stop me from revealing the truth Mama, I'm tired! Almustapha dan Abba ne his very own flesh blood you cannot deny that......
Wani Marin takuma kaimai wannan karan idanunta sunyi jazir"baka da hankaline ko hankalinka daya,ko anfada maka shi Mai Martaban besan meyakeyiba?"....
Murmushi kawai Sulaiman yayi kafin yajuya bangaren Mai Martaba yana niyan sake assuring dinshi that Almustapha is his Son sede abun mamaki ganin Mai Martaba yayi zube kasa ya sume,cikin wani irin ihu yakarasa gurin Mai Martaba yana Abba!Abba!......
Magajiya ma cikin sauri takarasa tana kaga abunda kaja ba, Sulaiman bai damu da abunda Magajiyan kecewaba illa jijjiga mahaifinshi dayakeyi yana Abba katashi don Allah,don Allah katashi,dede nan dogarayen da sukazo fadama Magajiya sun kama su Amira suna shirin guduwa da Almustapha,ai tundaga bakin kofar dasuka ga meke faruwa sukayi saurin karasowa cikeda damuwa, Sulaiman ne yace sutaimaka sutayashi kaishi daki, Magajiya bakaramin tashin hankali tashiga ba dakin Mai Martaba suka kaishi yayinda Sulaiman yashiga kiran family doctor dinsu ba ajima ba segashi yataho...........
Zuwa yayi yaduba Mai Martaba din kafin yasaka mishi ruwa sannan yafito yasamu su Magajiya dake zaune ah parlour jigum jigum,dasauri Sulaiman yatashi yana"Doctor yajikin Abba?"......
Kallonshi Doctor din yayi kafin yace to dai alhamdulillah za ace amma mekuka fada mai daya tadamai da hankali haka?.....
Dafe kai Sulaiman yayi kafin yace yanzu dai he's fine Ina?......
Eh dukda bai farfadoba amma insha Allah ajima zai farfado,sede akwai abunda yakamata kudaina tunamai wanda shine yake sakashi cikin wannan halin,yayi losing memory dinshi nawasu yan dakiku dakuma wasu mutane dayayi hulda dasu wanda tun alokacin nace adaina tunamai because ze iya zama hadari ga rayuwarshi,nuna Magajiya doctor yayi kafin yace ita Hajiya tajima tana kiyaye hakan,inafatan kuma bazaku sake wannan kuskuren ba sabida shi babban mutum ne da mutane da dama sun dogara dashi sabida adalcinsa.......
Gyada Kai Sulaiman da Magajiya sukayi Sulaiman na in Sha Allah za a kiyaye Doctor, murmushi Doctor din yayi kafin yace anjima da dare zai dawo yasake duba Mai Martaba........
Fita Doctor din yayi yayinda Magajiya tadubi Sulaiman"yau da ka haukatar da Ubanka daka ji dadi ai,anya Sulaiman kayi hali kuwa?",tayi maganar tana kare masa kallo shidai baice mata komaiba......
Matsowa kusa dashi tayi kafin tace nafada maka likita yace kada ana tuna masa rayuwarshi da Khairiya dama duk wani abu daya shafeta inba hakaba ze iya zama hadari ah gareshi....
Tsaki Sulaiman yayi rai bace sannan yace"why only about Ummi za ace kada ah tuna mishi,miyasa ba ace yamanta kuba,miyasa ba ace yamanta su uncle Almustapha ba saiku?.....
Why?.....nishine abunda yake dauremin kai yayi maganar yana goge zufar dake keto mai kafin yatashi tsaye yace koma miyene nibazan daina fadama Abba cewa Almustapha danshi bane ba indai kema baki daina ci musu zarafi ba sannan when he wakes up I'll still tell him that nina yima bayin nan fyade bashiba juyawa yayi zai bar parlourn cikin sauri Magajiya tace Sulaiman dawo nan,dawowa yayi yayinda tace naji, I'll release him and bazan takura musu ba just kadaina batun fadama Mai Martaba wannan maganan sabida zai iya zama hadari gareka don Mai Martaba baya wasa gurin daukan hukunci sabida shi ah gurinshi rules apply to everyone inya tabbata you're behind this zeyimaka hukunci dede dawanda zaiyi ma kowa kuma wannan yana iya hanaka hawa karagar mulki Sulaiman,kayi hakuri ka tausaya min tayi maganar harda kwallarta.......
Kallonta yayi sannan yace,I regret what I did da 'ya'yan mutane wallahi kowani irin hukunci Abba zaiyi min zan iya karbanshi hannu bibbiyu sede zanyi shiru ne sabida rashin lafiyar Abba kuma kinyimin alkawari you'll release him....
Gyada kai kai tayi cikin sauri given him more assurance cewa zata yi release Almustapha,fita tayi yabi bayanta yayinda tasa akira mata Sarkin yanke hukunci sanda yazo tace ayi releasing Almustapha,yasha mamaki kwarai sede bazai iya ja da maganar taba bin bayanshi Sulaiman yayi harzuwa gurin...
Sanda yaga Amira da bakuwar fuska yasha mamaki don kuwa dogarayen basu samu isar da sakon ba kasancewar abunda yafaru da Mai Martaba.............
Since su aka shigayi Amira kukan farin ciki tashigayi ganin Sulaiman ana karasa since ta takarasa gareshi tareda rungumeshi cikeda murna,shafa bayanta yashigayi it's okay little Amira,since Almustapha akayi cikin sauri Sulaiman yakarasa gareshi idanunshi sunciko da kwallah yace I'm really sorry Yaya Almustapha I couldn't come on time,sa hannu Almustapha yayi yashiga goge ma Sulaiman din hawayenshi
kafin suka rungume juna dukda kuwa irin pain din dayakeji besashi yin complain ba,dakyar suka iya sakin juna yayinda Sulaiman yadan goge kwallarshi yace we've to get out of here anyi freeing dinka but what I don't understand here is miyakawo su Amira mallam Hudu cemin yayi Kai kadai......
Amira ne tace Yaya Sulaiman munzo rescuing Yaya Almustapha ne aka kama mu,Yar dariya Sulaiman yayi yana taya Almustapha tashi kafin yace"lallai irin ku brave girls dinnan ba,to kunyi kokari",yayi maganar cikeda zolaya,tabe baki Amira tayi tana aidai wallahi dabadan Yaya Almustapha yatsaya mana miskilanciba da babu mai kamamu kafin tadubi Asma'u sannan takara da kinga ko,dariya Yaya Sulaiman keyi mana dama bamuzo ba daman ke kika takura.......
Sunfita ah gidan suna tafiya ahankali sabida yanayin jikin Almustapha din Sulaiman yadubi Amira yace"is she your friend?".....
Dariya Amira tayi kafin tace to zan iyacewa friend dinace amma gawanda tafi kusa da donnima adalilinshi nasanta tayi maganar tana nuna Almustapha,sakan baki Sulaiman yayi yana don't tell me Amira,badai Antyn mu bace?......
Gyada kai Amira tayi tana mischievous smile, Sister in-law to be ba,kallon Asma'u Sulaiman yayi sannan yace "thank you Aunty mungode kwarai",itako Asma'u kunya kaman tanutse kasa jitake kaman ta dinke bakin Amira, Almustapha kuwa bakaramin baci ranshi yayiba jin abunda Amiran kefada ........
Seda suka isa bakin motan Sulaiman din Asma'u nashirin shiga Almustapha ya daga mata hannu kafin yace"Ina zakije,do we really know you?".....
daga Amira har Sulaiman mamakine yakamsu, Sulaiman ne yayi karfin halin cewa meye hakan Yaya Almustapha?...
Dakatar da Sulaiman Almustapha yayi sannan yace "i don't know her and keda kike cewa you know her because of me you're lying,tare naganku",dan shiru yayi nawasu dakiku kafin yayi karfin halin cewa"even if she's your friend,I suggest she's not a good companion",yana karasa fadan haka yashige mota abunsa.........
Asma'u dake gefe hawaye ne suka shiga bin kuncinta, she's speechless, Almustapha cewa yayi besantaba,me hakan ke nufi?"....
Jiki ah sanyaye Amira takarasa gareta sannan tashiga bata hakuri, Sulaiman ne yace kishiga mutafi I'm sorry for what he did dukda bansan dalilinsa nayin hakan ba......
Jijjiga ma Sulaiman kai tayi alamar bazataje ba,cikeda damuwa yace don Allah kizo muyi dropping dinki ah gida,cikin kuka tace kuje kawai zanhau machine,babu yanda Sulaiman baiyi da Asma'u ba amma taki binsu,shiko gogan ya hakimce agaban mota ya lumshe idanunsa ko kallon inda suke baiyi ba bare yadamu da zance dasukeyi da ita,haka Sulaiman da Amira suka shige mota suka tafi badan ransu yasoba dukda kuwa har kudin machine din yabata amma tace ita bazata karba ba.....
Haka tana kuka tanufi hanyar gate din masarautar don tana iya hangota daga inda take tsaye,dabadan danasani keyaba ce dasai tace datasani bata baro gidan iyayenta tazo taimakon Almustapha ba wanda ita take gani yazama part of her life sede tamanta cewa shidinfa ba abakin komai yadauketaba,dabadan taimakon datayi mishi don Allah tayiba datace tayi nadamar taimakon Almustapha,yanzu bata da wani tunani daya wuce yanda zata fuskanci su Ummi don tabbas tasan anacan anata nemanta.............

Story continues below

****
Gabadaya yau Ummi takasa tabuka komai tunaninta daya ina Asma'u taje,mezaisa tafita batareda ta fada ah gidaba har makwabta ta aika su Munira sudubo amma shiru babu ita babu labarinta.......
Gashi har azahar tayi,tana nan zaune cikin parlourn abun duniya yadame ta taji ana sallama,ansawa tayi cikin muryarta mai rauni yayinda Mommy takaraso cikin parlourn wanda ayanzu zuwanta na hudu kenan tunda tasamu labarin Asma'u tabar gida......
Zama tayi gefen Ummi tareda cewa Maryam haryanzu bata dawo ba?.....
cikeda damuwa Ummi tace batadawo ba Anty Zainab nikam abun yafara damuna sosai wayasanima ko ba gida ta kwanaba,kul Maryam,kul kidaina irin wannan kalamin don Allah ninasan Asma'u she'll never do something like that,bansan inataje ba but I've full faith in her kema nayi mamakin dakika biyema Abban su da yayunta wurin dauke yimata magana,ai inkaga yaro yana neman tabewa janshi zakayi ah jiki kaji miye damuwarsa sannan kadinga bashi shawarwari,guje musu bashine zaisa su gyaru ba Maryam, ya'yan mu basuda kamarmu, mu iyayensu inbamu jasu ah jikiba ta inazamuji matsalolinsu,dan numfasawa Mommy tayi sannan tace kinga Asiya wani irin rashin ji ne batayi amma nakan kirata daki inyi mata fada dukda kuwa ba koyaushe takejiba sekuma inbita da addu'a Allah yasa tagane sannan bantaba gujantaba......kinyi kuskure ba karamiba,barema kefa kikasan Asma'u da hankali gakuma sanin yakamata......
Cikin kuka Ummi tace ninasan Asma'u duk abunda yafaru da'ita coincidence ne kokuma wani ne yake niyan yimata sharri sede anawa ganin harda nata laifin shiyasa nayi mata horo tahanyar yin fushi da ita nawani lokaci ashe wani abun kuma naja gashi tafita tabar gida batareda sanin kowaba damuwana daya shine furucin Alhaji kafin tafita kan beyarda tashigo masa gida ba inta dawo ko bayanan takoma daga inda tafito Ummi takarashe maganar tana hawaye............
Mommy ne tace subhanallahi yaushe Alhaji ya yanke wannan hukuncin,anya yasan abunda yake shirin yi kuwa?....
Hmmm shine abunda Ummi tace kafin takara da shikuma ba a isa ah ja da zancenshiba.........
Tabbas shine abunda Mommyn tace,dama Hajja nanan ne kilan ita ta iyayi mashi magana dukda kuwa abune me kamar wuya ya canza raayi....
Humming kawai Ummi takuma yi yayinda azuciyarta kuwa cewa take dadai Asiya ce kilan tasaka baki amma Asma'u Kam komi zaisameta babu ruwanta indai Hajja ce.......
Mommy ne tace Allah gamu gareka, Allah ka kawo mana mafita cikin wannan lamari.......

***
Ah bakin gate me machine din yasauketa tabiyashi kudinshi,tun tana kan machine din zuciyarta ke dukan uku uku domin batasan mezata tarar ah gida ba hakanan batasan mezata ce musuba sede abu daya tasani batada gurin zuwa inba gidan ba hakanan mistake tariga tayi shi babu yanda zatayi,goge yar kwallarta tayi kafin ta doshi gate din megadinsu tasamu gaida shi tayi cikin ladabi yayinda ya amsa sannan yace Ya'ta kiyi hakuri kirufamin asiri don Allah kada kishiga gida don Alhaji yamin kashedi kan inkindawo kada inbarki kishiga inbahaka ba abakin aikina kuma kinga aikinnan shine kadai hanyar cin abincina nida iyalina,jikinta ne yashiga karkarwa yayinda takoma baya tana fadin innalillahi wainna ilaihir rajiun, Asma'u mekika jama kanki wannan wace irin rayuwa ce, samun jikin katanga tayi tajingina tana tunanin duniya yayinda hawaye bebar zuba daga idanunta ba tananan tsaye sega Musa yafito daga gida kallonta yayi sannan yabuga tsaki ze wuce cikin sauri tasha gabanshi tana Yaya Musa don Allah katayani bama su Ummi da Daddy hakuri wallahi nayi nadama........
Tureta yayi kafin yace seyanzu kikasan kinyi nadama,seyanzu kikasan laifin da kikayi to babu mai kulaki Asma'u kikoma inda kika fito inbaso kike Daddy yadawo yabata miki raiba,ina rayuwar dakika zaba kenan,to kije kiyi inshine mafi alkhairi gareki.........
Hakuri tacigaba da bashi tana rokonshi amma kinkulata yayi sannan daga karshe yace inabaki shawarar kibar kofar gidan nan inbasokike kijama mahaifiyarki ba sabida Daddy cewa yayi intabarki kika shiga gida to abakin aurenta sede ku tattara daga ke har ita kubar masa gida.....
Sa hannu tayi ah bakinta tana kokarin rike kukanta Musa kuwa tafiya yayi yabarta tsaye ah gurin kamar gunki,bata taba tunanin Daddy can do something like that ba sede koma wani irin mataki yadauka bazata taba yarda tazama silar raba iyayentaba don haka tabar kofar gidan tana tafiya ahankali kaman wanda kwai yafashema,batasan yazatayiba batasan inazatajeba, ita tukunnan ma wata sani acikin garin Zaria wanda zata iya kaimishi kukanta.......

Story continues below

*****
Tunda suka isa gida Sulaiman yakira likita yace yazo yaduba Almustapha agida don yaki zuwa asibity,magunguna likitan yarubuta mishi bayan yaduba shi sannan yace yasamu yayi wanka da ruwan dumi ya huta,he need some rest.......
Godiya Sulaiman yayi ma likitan sannan yamusu sallama yatafi...........
Aisha da Amira ne suka shigo da abinci parlourn su,Sadiq ne yadubi Almustapha"gaskiya Yaya Almustapha baka kyauta ba abunda kayima yarinyan can banji dadiba wallahi"....
Shiru kawai yayi batareda yace musu komaiba, Amira ma tasaka baki "she was the one that wake me early morning kan muje muyi rescuing dinka, she's indeed a great friend,Amira takarashe maganar tana kyabe fuska".....
Tsaki Almustapha yayi ze tashi yabar gurin cikin sauri Sulaiman yariko hannunshi yace please kazauna,hararanshi yayi kafin yace "kudaina min maganarta to"......
Gyada masa kai Sulaiman din yayi yayinda Aisha dake gefe tana mamakin wace yarinya ce haka har namiji yake wani cewa adaina yimishi maganarta sede batasaka bakiba tunda bada ita akayiba...........
Seda suka fita Amira kebata labarin abunda yafaru kafin daga karshe tace"wallahi nayi tunanin Yaya Almustapha da Asma'u sun saba already barinma yanda tanuna tadamu yau dinnan ashe shiko sanintama baiyiba,Amma koma miyene ai baikamata yayi mata hakaba"....
Aisha da bakin ciki ya isheta tace Yayan naki cemaku yayi besanta ba?....
Gyada mata kai Amira tayi,rai bace Aisha tace lallai namiji Dan iska ne,batajira cewar Amiran ba takoma dakin su Almustapha din....
Sulaiman ne yadubeta yace lafiya Aisha kika shigo ko sallama babu?......
ba lafiya ba Yaya Sulaiman tunda ka ganni haka, I'm here to teach your Brother a lesson sannan tadubi bangaren Almustapha dake zaune yayi folding hannunshi ah kirji ko kallon inda take baiyiba cikeda masifa tace"cewa kayi baka san Asma'u ba komiye,eh lallai ka kyauta kuma kacika marar mutunci dasanin darajar wanda yayimaka, everyone hates you, everyone is running away from you,kowa yana kyamar ka hakanan kowa ko kallon ka baswason yi ahakan Asma'u tadubeka,taji tausayinka bata kuma kyamacekaba ana fadan laifinka amma itabata gani all she sees is the good side of you,all she says is "innocent Almustapha",tsaki Aisha tayi kafin tace is this how you're going to repay her kasan ma halin datake ciki kuwa?....
Sulaiman dake gefe yaji zafin kalaman Aisha don haka yayi kokarin tsaidata amma seta daga mai hannu kafin tace"let me talk today,inbanyi magana ba bazanji dadi arainaba,dayasan adalilinshi mijin dazata aura yafasa aurenta da bazaiyi magana ba,dayasan adalilinshi tasamu matsala da karatun ta har aka hanata zuwa makaranta dabazaiyi magana ba hakanan dayasan adalilinshi tasamu matsala da iyayentaba dabazaiyi mata abunda yayi mataba yau dukda kuwa iyayen nata na fushi da ita tasaci hanya don tayi rescuing dinshi tabaro gida amma beganiba,all that she gets from the Yaya Almustapha shine rashin mutunci da humiliation.......Dan numfasawa tayi sannan tace you'll never come across someone like her Almustapha and I promise you'll regret this tana kaiwa nan tajuya tafita tabar musu dakin don ta lura dan rainin wayau ne ko kallon inda take beyiba datana magana sede abu daya tasani no matter what,he get the information, damuwarta daya wani hali Asma'u take ciki yanzu batareda tayi wata wata ba tana fita tatari napep don zuwa gidansu Asma'u din dukda tanajin haushin Asma'u na abunda tayi.....
Bayan fitanta ne Sulaiman yadubi Almustapha yace"I'm confused Yaya Almustapha,wai meyake faruwane?".....
Ware hannu yayima Sulaiman cikeda rashin damuwa alamun baisani,kamo hannunshi Sulaiman yayi kafin yace please kafadamin Yaya Almustapha kasantane........
Harara Almustaphan yakaimai kafin yace "jarababbiyace,i don't even know her name believe me"......
Murmushi Sulaiman yayi sannan yace amma kasanta ai?.....
"Just her face", Almustapha yabawa kanin nashi amsa cikeda kosawa,then why will you do that to her,Sulaiman din yakuma tambayarshi...
"Look Sulaiman,i did not ask any help from her,bansan wayafada mata abunda yafaru daniba and what she did was wrong,bakaji me kawarta tacebane her parents are angry with her but still tabaro gida sabida tayi saving stranger",dan shiru yayi yana dafe kanshi sabida jidayayi kanshi yafara ciwo tsabar long maganar dayayi....
Kallonshi Sulaiman yacigaba dayi yanajiran more explanation,dakyar ya iya budan baki yace"she's not a decent girl,we don't know her motives so,just let her be"...
Murmushi Sulaiman yakumayi kafin yace,kwanta ka huta kafin ruwan zafinka yatafasa I'll be right back fita Sulaiman yayi yana tunanin samun Aisha only from her zaisamu details don yasan kozaiyi yaya bazai samu cikakken bayani gurin Almustapha ba yagode Allah ma dayasamu yayimishi long bayani haka............
Tambayar Amira yayi ina Aisha nan take cemasa aita fita ranta bace dan tsaki yayi sannan yace ina neighbor dinmu ce?...
Gyada masa kai Amira tayi kafin yace alright zantafi kaduna yanzu dauko su Afiya jirginsu yakusa sauka daganan zanwuce Masarauta wurin Abba I'll surely come back in the night and may be with baki so kigyara gidan,kitabbatar Ummi taci abinci...
Cikeda jin dadi tace in Sha Allah,wani farin cikine yadinga shigarta sabida yau zataga twin sister dinta finally.......
*****
Aisha kuwa tunda tahau napep hankalinta ah tashe yake har suka Isa titin unguwansu Asma'u,kaman ance tadaga kanta tahango Asma'u natafiya ta gefen titi sake lekawa tayi sosai don ta tabbatar itan ne,aikuwa itance babu tantama cikin sauri tacema mai napep din yatsaya dede gaban Asma'u din cikin sauri tasauka tana Asma'u,Ido jage jage Asma'u tadago tana kallon Aisha kafin Aishan takama hannunta suka shiga napep din sannan tacewa mai napep din sucigaba da tafiya cikin sauri Asma'u tace aa kadamuje gida please I'm from there.......
Babu musu Aisha tacema mai napep din sujuya zuwa unguwan daya daukota,har kofar gida yakaisu ya ajiyesu kama hannun Asma'u tayi suka shiga ciki Anty suwaiba batanan don daman nurse ce Kuma afternoon takeyi harta tafi..........

Seda tabar Asma'un tayi kukanta me isanta sannan tace kitashi kiyi sallah,jiki ah sanyaye tashiga bandaki tayo alwala kafin ta tada sallah seda ta idar sannan Aisha tace ga abinci kici, jijjiga mata kai tayi alamar aa,Aisha bata matsamata ba don tariga da tasan halin Asma'u kozatayi yaya baxataciba.........
Rufe abincin tayi kafin tace naji maiyafaru yau da safe Amira tafada mini dakika koma gida mai yafaru Kuma?.....
Take idanun Asma'u suka kuma cikowa da kwallah sannan tashiga bata labari seda takai aya sannan tayi shiru,Aisha ne tace Asma'u kinkyauta ma kanki abunda kikayi,kinmanta shwarar damuka baki nida Asiya,idanunki sun rufe bakya kallon komai se wannan yaron Almustapha,yaron da baya ganin darajarki,yaron dabai dauke ki abakin komaiba he's even claiming that besankiba wani irin rashin tunani ne wannan Asma'u?,nidai bahaka nasanki ba this's not the Asma'u that i knew, Asma'un danasani yarinyace me aji dasanin mutuncinta,yarinyace wanda tasan mutuncinta sannan tasan kiman iyayenta what you really did kinyi disappointing dina and babu abunda kikayi gaining illa rashin mutunci daga gurin wanda kikema wannan kokarin......you really disappoind me Asma'u Aisha takarashe maganar tana jijjiga kanta.....
Cikin kuka Asma'u tace I'm really sorry Aisha,nikaina bansan abunda nayi zan jama kaina wani abunba sai da na tsinci kaina ah irin wannan halin,nikaina bansan hauka nikeyiba seda Almustapha yafada min maganganu,nikaina bansan nazama daya daga irin matan da basusan mutuncin kansu ba se yau dana koma gida na iske kalaman Daddy akaina, nayi babban kuskure and I'm regretting it bansan ta ina zanfara gyara laifuffukana ba,bansan ta ina zan goge rashin fahimtar da iyayena sukayimin daga zukatansu ba,cikin kuka tadafe kanta tareda cewa dazan iya maida hannun agogo baya dana gyara laifuffukana sede bazai yuyuba,nariga na kwabsa yanzun mafita nike nema Aisha........
Goge mata kwallah Aisha tayi kafin tace kidaina kuka sometimes mukanyi mistakes and we learn from the mistakes damukayi besides nobody is perfect Asma'u, Allah yariga ya kaddara hakan zai faru sede mu kiyaye gaba and I hope you've learn from abunda yafaru dake bama ke kadai ba koni nakoyi wani abu daga wannan kaddarartaki,kinemi yafiyar ubangiji na saba ma iyayenki dakikayi sannan kirokeshi mafita don shikadai zai iya taimaka miki ah irin wannan situation din.....
Asma'u najan hanci tace in Sha Allah,damuwana su Ummi, murmushi Aisha tayi kafin tace Ummi munyi waya da ita i told her we're together gurina kikazo karkiga how worried she's amma tunda nace mata muna tare hankalinta yadan kwanta...........
Godiya Asma'u tashiga yima Aishan,shhhh babu godiya ah tsakaninmu cewar Aishan,yanzudai kici abinci kafin Anty suwaiba tadawo musan abunyi.........

******
Yana Isa kaduna jirginsu yasauka daukosu yayi daga airport se hira sukeyi cikin mota banda Dad dayayi shiru cikin motar ya lumshe idanunshi kawai he's just thinking of how to meet his family,his long lost family wanda yacire rai da ganinsu har abada,ana kiraye kirayen sallar maghrib suka shigo garin Zaria, straight Masarautar suka wuce da already
Sulaiman yasa agyara bangaren da aka warema Dad tun da jimawa wanda duk sanda aka tashi renovating gidan se an gyara da bangaren sannan ba a wuce wata ba ayi sanitation din gurinba dukda kuwa bakowa kezama acikin gidan ba wannan order ne daga Mai Martaba don akullum jiran dan uwanshi yakeyi shiyasa yasa sharadin gyara gurin,koda suka Isa Masarautar gaban bangaren Sulaiman yakaisu sannan yasa bayi suka shigar musu da kaya kafin yace su yi sallah tukunnan su huta, jijjiga kai Dad yayi sannan yace I'll not rest until I meet my Brother, murmushi Sulaiman yayi kafin yace to Dad amma muje muyi sallah ko,babu musu suka wuce masallaci Dad yanata karewa masarautar kallo anata kai kawo na shirye shiryen biki yayinda bayi na ayyukansu, everyone is so busy ahankali yafurta everything has changed.....
Seda sukayi sallah kafin suka rankaya bangaren Mai Martaba,dakinshi suka wuce direct yana kwance kan makeken royal bed dinshi yadan jingina kanshi da pillow yanzune tashin shi,tunda yatashi yake fadin anemo masa Sulaiman suna magana basu karasaba yatafi,aikuwa bekaiga rufe bakin nashiba yayi arba da idanun sulaiman din daga bakin kofa yana shirin yin magana yakuma arba da fuskar Almustapha,his very own Brother.......


Lumshe idanunshi yayi yasake bude su but still arba yasakeyi da fuskar Yayanshi Almustapha,yakasa yarda da idanunshi still don haka yashiga murza su ahankali amma still fuskar Dan Uwan nanan abakin kofa dukda kuwa tsufa dayayi hakan bazai taba sashi manta fuskar tilon 'Dan uwanshiba.........
Ahankali Dad yashiga takawa zuwa bakin gadon idanun shi suncika fal da hawaye,daga hannu Mai Martaba yayi yana son taba dan uwannanshi,yanason sake tabbatarwa dagaske shidin yake gani ba illusion ba zama Dad yayi gefenshi tareda cewa Abdulrahman kaine haka,kaine agabana,ashe darabon zamu sake haduwa,kaine kagirma haka?......
Mai Martaba jin muryar Dad yasashi saurin janshi zuwa jikinshi se hawaye,kuka yake me tsuma zuciya yana miyasa kajune for this long,miyasa katafi kabar tilon kanin ka,baka taba tunanin halin dazan shiga bane Yaya?......
Cikin kuka Dad dinma yace, I'm really sorry Abdulrahman nayi kewarka sosai......
Dan bugun bayanshi Mai Martaba yayi kafin yace dakayi kewana dazaka dawo, murmushi Dad yayi kafin yadago ya kalli kanin nashi daya manyanta yazama babban mutum,aziciyarshi ya furta rayuwa kenan.......
Allah baiyi haduwarmu ba sai yau,dan ka nason ka da alkhairi tabbas Sulaiman yaron kirki ne shine sanadiyar sake haduwarmu in sha Allah bazan manta da hallaccinsa gareniba yakarashe maganar yana duban bangaren da Sulaiman din yake,Dad da jikinshi bawani kwari yace so this's the surprise?..........
Yar dariya Sulaiman yayi yana goge kwallarsa sannan yace "yes Abba,I hope you like it".....
alama Abba yayi masa da hannu kan yazo, ahankali Sulaiman yakaraso gaban mahaifin nashi ya tsuguna,kamo hannunshi Mai Martaba yayi kafin yayi kissing forehead dinshi, Sulaiman na iyacewa this's the very first time da mahaifinnasa yayi masa sumba ah goshi don haka besan sanda hawayen farin ciki yafara zuba ba"Allah yayi maka albarka Yarima, Allah ubangiji yabaka ya'ya nagari wanda zasuyi maka abunda yafi wanda kayimin yau,bazan iya fadamaka irin farin cikin danake cikiba yau kuma duk ta dalilin efforts dinka, murmushi yayi tareda shafa fuskar dan nashi sannan yace I feel blessed to have my Son,mutanen Zaria bazasu taba nadamar samunka amatsayin shugaba ba, this's how much I like your surprise Son......
Sulaiman kama hannun Abban yayi yana hawaye shikadai yasan irin farin cikin dayake ciki ayanzu,yaji dadi matuka da kalaman Abban how he wished his mother is like his Father,how he wish Itama mutumiyar kirkice wanda zatadinga samishi albarka kullum batareda ta kuntata ma wasuba babu abunda yake damunshi ah yanzu daya wuce dazu ganin Magajiya dayayi tareda Doctor dincan yayi mamaki matuka shiyasa yabi bayansu and that was when yaji shocking news of his life.............
Gani yayi Magajiya taciro kudi tabama Doctor din, godiya likitan yashigayi yayinda Magajiya tace"nine da godiya likita kamin taimako na dukkanin shekarun nan hakana yau ma ka taimakeni da Sulaiman yafada ma Mai Martaba komai,daya rusa min duka plans dina,sede abu daya daban ganeba shine sumar da Mai Martaba yayi menene dalilinshi?".....
Murmushi likitan yayi kafin yace he was shocked by the news wanda yakaishi ga suma kuma bahakan yana nufin yatuna Almustapha bane da mahaifiyarsa kawai labarin ne yazomai ah bazata, indai you have faith in your Boka dakuma aikin dayayi miki kikwantarda hankalinki don bana tunanin Mai Martaba zai iya tuna Matarsa da Ya'yansa bayan wayannan shekarun da suka shude inbadai wani bane ya tada masa da zancen shima din he might just believe it inya yarda dasu bawai don ya yarda har zuciyarsa bane.......
Murmushi Magajiya tayi sannan tace nagode likita,zuwa anjima seka koma ka dubashi ko,insha Allah ranki shi dade ayi biki lafiya......
Nan yatafi,lumshe idanu Sulaiman yayi yana fadin innalillahi wainna ilaihir rajiun,so wannan duk yin Mahaifiyarsa ne,shimadai abun yabashi mamaki ace wai specifically Ummi kawai dasu Almustapha Mai Martaba yamanta, indeed something is fishy daman,yana ganin mahaifiyarsa ta wuce takoma cikin gida shikuma dedenan Dad yafito ah massallaci don haka yasamo shi suka wuce bangaren Abban....
Rungume Abban yayi, murmushi Abba yayi yana dan tapping bayanshi yayi yana miyena kukan kuma Yarima?......
Dagowa Sulaiman yayi sannan yace Abba I don't deserve the throne, Yaya Almustapha yakamata abama baniba........
Cikin sauri Mai Martaba yadubi Sulaiman din sannan yace "yauwa dazu muna magana bamu karasa ba Son, you were saying something about Almustapha".....
Gyada kai Sulaiman yayi kafin yace eh Abba hakane.....
Dad dake gefene yace ma Sulaiman,Son inaganin abar maganar nan se gobe zamuyita he should get some rest now........
Girgiza kai Mai Martaba yayi kafin yace inason sani Yaya,don Allah kufadamin meyake faruwa,riko hannunshi Dad yayi kafin yace"you've another family wanda kayi loosing memory dinka ka manta dasu and that time likita yace kada afada maka sabida ze iya putting life dinka in danger Abdulrahman shiyasa ba afada makaba,cikeda confusion Abba yace my family?...
You mean I've another wife and children?........
Gyada masa kai Dad yayi ahankali cikeda damuwa yace ya akayi bansan suba,shiru yayi nayan dakiku trying to remember something amma babu abunda yake iya tunawa abudaya yasani matarshi daya Magajiya se Yayanshi mata uku da Sulaiman.......
Dafashi Dad yayi kafin yace"kakasa tunasu ko?".....
Gyada masa kai yayi, ahankali Dad yace just keep praying and you'll remember them in Sha Allah.......
Duban Dad Mai Martaba yayi kafin yace"I'm confused Brother, explain it in details yaza acemin inada iyalin daban sandasuba?.......

Story continues below

Murmushi Dad yayi kafin yace bawai bakasan dasuba kamanta dasu ne,you can't remember them,you can't remember the moments you shared with them but zanmabaka labari may be you'll remember something.........
Shiru yayi yana kallon Yayannashi nan Dad yashiga bashi labari kaman yanda Sulaiman yafada mishi shima yanda yaji labarin Abba da Khairiya,seda yakai karshe sannan yadubi Mai Martaba sannan yace baka iya tuna komai har yanzu?......
Murmushin dayafi kuka ciwo Mai Martaba yayi don sometimes yakanyi tunanin shima yataba aure, sometimes yakanyi mafarkin wata mata tana kuka asking for his help sede betaba ganin fuskarta ba shiyasa sometimes inyaji feelings din kaman yataba rayuwa da wata mata bayan Magajiya seya ke daukan abun kaman tsabar yawan mafarkin dayakeyi ne,seyanzu dayaji labarin da Dad kefada mishine yasa shi jin ashe ba mafarki bane,ashe yafaru agaske kallon Dad din yayi kafin yace yea natuna sede I've nothing to do with her she betrayed me remember?...... .
Jijjiga kai Dad yayi sannan yace don't say that tunda you actually don't know the truth......
Cikeda bacin rai antuno mishi da abunda yariga ya gushe ah kwakwalwar shi,antuno mishi da abunda yayi believing befarubama,beji dadiba because now it'll disturb him, it'll affect him cewa yanada wanda tataba cutanshi,da ace wani ne yafada mishi bazai yarda da maganarba ze cigaba da dauka amatsayin mafarkin ne kawai sede of all people yasan Yayanshi bazai taba yimai karyaba,he can't remember anything about their life,he can't remember how suka hadu kawai dai yasan yataba aure da ita don haka yace,you said it yourself tayaudareni Yaya inaganin mubar magananta please........
Cikeda damuwa Dad yace"inmunbar maganarta Ya'yanta fa,hakkinsu dayake kanka amatsayinka na ubansufa?"......
Cikin idon Yayan nashi ya kalla sannan yace bana tunanin inada wasu Ya'ya tare da ita,they are not my children taje tasamo su awaje please kada tazo talakabin Ya'yan data rasa yanda zatayi dasu ......
Tashi daga zaune Dad yayi kafin yace"dakana cikin hankalinka kayi wannan maganar zanga laifinka but banyi blaming dinkaba but believe me one day you'll realize everything in Sha Allah, I'm here I'll help you remember everything sede bazai yuyu mucigaba da ganin namu ah waje suna wulakanta ba, it's high time you accept them as your children sabida Khairiya tatafi da ciki daman and Allah yabata Yan biyu,sun girma yanzu they need you and their family"......
Shidai shiru Abba yayi batareda yace komai don maganar Dad ko kadan baishigeshiba.......
Duban Sulaiman Dad yayi kafin yace kaje gida kadauko su Almustapha sudawo cikin masarauta yau dinnan sannan gobe dasafe without anyone knowing inason azo ayi musu DNA TEST inaga only then mahaifin ku zai cire zargin dake ranshi and only then zeyarda yakarbesu amatsayin Ya'yan shi yakuma basu equal right agidan nan.......
Gyada kai Sulaiman yayi sannan yafita cikeda jin dadi because he's fully sure Abba bazai taba going against Yayan shiba koda kuwa ranshi bayaso and bazaiyi wasa da opportunity dinnan ba straight gidansu Amira yawuce don daukosu.......
Bangaren Abba da Dad kuwa bayan fitar Sulaiman Dad yayi niyar bin bayanshi dasauri Mai Martaba yariko hannunshi, I'm really sorry Yaya Almustapha karka tafi"......
Dawowa Dad yayi yazauna sannan yace bafushi nayiba,gyada kai Mai Martaba yayi sannan yace to amma still kazauna i don't want you to leave my side se inga kaman tafiya zakayi kabarni and maganarsu yaran bawai banyarda dakai bane kawai inason kasan cewa i witnessed everything with my own eyes shiyasa nakasa yarda sudinma ya'ya na ne anma indai akayi DNA din duk abunda result yace I'll accept it......
Shhhhh it's okay have some rest now, Allah yakaimu goben......
Amin ya amsa kafin suka fara hiran yaushe rabo cikeda kewar juna inda yake bashi labarin bayan barin shi gida Indonesia yayi direct sabida yasan ba lallai ataba tunanin can din yayiba and beyi wahalar samun aiki ba sabida akwai Baban abokinshi alokacin yana da company babba acan wanda asalinsu yan can ne kuma musulmai bakaramin rikeshi sukayi kaman nasuba har Allah yasa soyayya yashiga tsakaninsu da kanwar abokin nashi nan yanuna yanasonta akayi masu aure,sunyi kusan shakara goma shadaya Allah baibasu haihuwa ba hakan kuma betaba sa Dad ya guji Mom ba don aganinshi haihuwa na Allah ne,insuna da rabo zasu samu dukda kuwa sunyi yawace yawacen asibity daga karshe suka hakura,segashi sanda suka fidda rai har suna shirin abducting yarinya Allah yaba ma Mom ciki,murna kaman zasuyi yaya nan aka shiga renon ciki har Allah yasauketa lafiya suka samu mace"Sumayya", bakaramin gata suke nuna mataba sabida she's their only happiness duk wani abuda takeso anayimata shi hakanan iyayen baswason ganinta cikin damuwa shiyasa ta taso shahwababbiya, murmushi Abba yayi sannan yace I'll like to meet her now?...
Dariya Dad yayi sannan yace indai Sumayya ce harsai ka gaji da ganinta, she'll surely come by herself akwai wanda yakaita zumudin son ganinka ne.....
Murmushi Mai Martaba yayi sannan yace, inason in sanar da zuwanku masarautar nan ah daren yau,aa Abdulrahman kabari se gobe ko bayan biki.....
Murmushi Mai Martaba yayi sannan yace nida inatunanin daga bikin ma tsabar farin ciki, murmushi Dad yayi sannan yace niko dabazan taba yafema kaina ba bazanso yanke farin cikin ya'ya na ba, I'll be part of the wedding kuma za ayishi jibi dayardar ubangiji ....
As you say cewar Mai Martaba din sannan yace amma bikin na'da Sulaiman as the crown prince zandaga shi zuwa wani watan se ah hada dana tarban ku wannan Karan Dad beyi musuba sabida aganinshi wannan opportunity ne na convincing Abba kan maganar Almustapha.......

Story continues below

*****
Mommy nata damuwa da rashin ji daga Asma'u,sanda su Mubaraq, Aliyu da Musa suka shigo tace wai haryanzu babu labarin yarinyar nan fisabilillahi.......
Musa ne yace Mommy kuncika damuwa akan abunda bai shafekuba,ita data tashi tafiya ta tuna halin dazaku shigane tukunnan, Asiya dake gefene tace amma dai koma miyene yakamata kuje kunemota.....
Wani harara yadaka mata yayinda Aliyu yace"kedin har yaushe kikayi hankalin da zakibama wasu shawara?"..
Tsaki Mommy tayi sannan tace kufitar min ah gida in bakar magana ce tattareda bakinku marasa kunya kawai,kuma wallahi inbakuje kun nemo Asma'u ba kafin dare babu wanda zanbama abincin dare,cikeda damuwa Musa yace haba Mommy mukuma miye laifin mu komun samota ma Daddy yace bazata shigo gidan nan ba to babu anfanima shiyasa dazu dana ganta nace takoma daga inda tafito,ba Mommy ba gabadaya su Aliyu da Mubaraq suka saki baki suna kallonshi.....
Mommy ne tace ah Ina kaganta Musa?....
Cikeda rashin damuwa yace tazo bakin gate mai gadi yahanata shigowa shine nima nace bazata shigoba...
Wani wawan mari Mubaraq ya wanka ma Musa kafin yace amma seyau nasan bakada hankali Musa, dafe kuncinshi yayi cikeda bacin rai yace"menayi dazaka mareni ba order din Daddy nabiba",wannan karan Mommy ne takuma makanshi tana Innalillahi wainna ilaihir rajiun amma dai Musa sai yau nasan bakada hankali kanwartaka zaka kora akuma kofar gidansu fisabilillahi......
Ranshi bace yace Mommy kinamin fada kaman nikadai ne bandamu da al amurantaba,inace suma duk ransu bace yake da'ita yakarashe maganar yana nuna yayun nashi, Mubaraq ne yace kayimin shiru shashasha kawai don muna fushi da'ita bazamu ganta tazo kofar gida mukoretaba,don muna fushi da'ita tayi laifi bazamu barta takoma inda tafito ba in Daddy hankalinshi ya gushe yakasayin meya kamata mu miye amfanin mu Musa?,agreed Daddy yace kada azo da ita gida couldn't you atleast come and inform Mommy ko Ummi su zasusan yanda zasuyi tunda bawai mutanen arziki suka rasa agarin nan ba wanda zasu iya ajiyeta gidansu for few days kafin bacin ran Daddy ya lafa, gaskiya kabani mamaki Musa cewar Mubaraq din sannan yafice rai bace because he cannot stand it,yana fushi da'ita amma that does not mean ze juya mata baya ah irin wannan situation din, Aliyu dai baice komaiba yabi bayan Yayan shi yafita, Mommy ne tace sekaje kanemeta ai,fita yayi zuciyarshi namai zafi donshi haryanzu baiga laifinsaba.......
Fitarsu be jimaba sega Ummi dakanta tazo tana fadama Mommyn ansamu labarin Asma'u ashe gidansu Aisha ma tajeta bawani guba.......
Allah sarki baiwar Allah may be tagaji dazaman gida and tagaji da juya mata baya da kowa yayi shiyasa tayi hakan,tunda tana gidan nasu bana tamtama yanzu cewar Ummi din, Asiya ne tace tabbas Ummi don Aisha akwai hankali ga sanin yakamata, murmushi Ummi tayi bawai haryakai zuciyaba kafin tace yanzu matsalar mahaifin kune gashi yace gobe zaije *Batagarawa* ganin su kawu da Yan Uwa daganan zasu dawo da Hajja jibi in Allah ya yarda...........
Allah yakaimu jibin kafin nan za asan abunyi tacigaba da zama acan din kuyi magana da ita Antyn nata cewar Mommy.....
Munyi magana da'ita dazun......
To yayi kyau, Allah yakawo mana mafita....
Amin cewar Ummin......

****
Tunda Talatu taga ana gyaran bangaren su uncle Almustapha tashiga tambayar bayin waya sasu kuma miyasa,sede bata samu ansa me karfi ba don ansar daya ce Yarima ne yasaka su kuma basu san daliliba sekawai tayi tunanin kilan Sulaiman din nada special baki dazai saukar ah gidan shiyasa,sede fa gulmarta bata tsayanan ba sabida sanda taga Yarima yashigo da motar sa zuwa bangaren tayi tashiga leke leken suwa ye wayannan bakin,idanunta yagane mata namiji da mata dakuma kyakyawar mace datayi shigen turawa setayi tunanin bakin Sulaiman dinne sukazo daga inda yayi karatu wannan dalilin ya hanata sanar da Magajiya harda karin ma itakanta tayi mata wuyar gani don kuwa she's very busy cikin jama'a koda zataje gurin Doctor ma dakyar tasameta ta fada mata isowarshi nan tasata yin wani aikin itakuma taje dakanta don acewarta inbataje dakantaba ana iya samun matsala.......
****
Cikeda tsoro tace kiyi hakuri ranki ya dade sabida ni tsarin mu tasake rugujewa Laure takarashe maganar kanta ah kasa don kuwa tun ranar da aikinsu yakasa aikuwa takasa tunkarar Hajiyartata don tsoro takeji harsai da ita Matar da kanta tanemeta......
Sabida aikin baiyiba shine kika ki zuwa kifada min cewar matar tana kallon Laure dake zaune gabanta........
Kiyi hakuri ranki shi dade Lauren tayi magana kaman zata fashe da kuka,babu komai Laure kuma batun aiki baiyiba ninaga zaija mana cikas sabida anriga anga macijin shiyasa nayi saurin daukeshi kada kidamu,cikeda rashin fahimta Laure tace ranki shi dade kina gurin ne?........
Aa bana gurin Laure kede yanzu kitashi kikoma gida in akwai wani bayani dazanyi miki zansake neman ki......
Gyada kai Laure tayi sannan tayima matar godiya sannan tatafi cikeda mamakin yanda macijin ya bace donko taji labarin abakin sauran bayi yan uwanta.......

****
Koda yaje gidansu Almustapha din samunsu yayi ah parlour dukansu yayinda Ummi na daki,dubansu yayi sannan yace nifa bazama nazo yiba Dad yace inzo indaukeku mutafi gida,wani kallo Almustapha yayi mishi don baigane inda yadosa ba, murmushi yayi sannan yakarasa gaban Almustaphan "Yaya Almustapha insha Allah daga yau wahalarku takare, we're going home now,I mean you people are going to be like us and we're going to live as a family from now on", Sulaiman yakarashe maganar fuskarshi na nuna tsantsan farin cikin dayake ciki.......
Amira dake gefene tace dagaske kake Yaya Sulaiman,kana nufin Mai Martaba ya karbe mu ah matsayin ya'yanshi?.....
Gyada mata kai kawai yayi don ganin yanda tayi maganar with so much hope shikuma bazaiso ya ruguza mata hope dinba,wani irin dadi taji har cikin ranta kafin tashiga tsalle harda hawaye wani harara da Almustapha yayi mata shiyasakata nutsuwa kallon Almustapha Sulaiman yayi sannan yace "if you can stop her from jubilating ah fili bazaka iya hanata ba azuci Yaya Almustapha",katashi mutafi gida everyone is waiting for you, Afiya can't wait to see you......
kai tsaye Almustapha yace"I'm not going anywhere",sabida shi babu wata farin ciki dayayi da zancen don azuciyarshi cewa yake after all this years seyau ya tuna dasu,after all the humiliation seyau yasan su Ya'yansa ne,babu abunda yahanashi rayuwa da babushi dinma dukda kuwa walakanci dayadinga sha behanashi surviving ba and he believes that he'll always move on dayar dar Allah.......
Bata rai Sulaiman yayi jin kalaman Yayan nashi"haba Yaya yazakayi irin maganar nan don Allah,koma miya faru he's your Father besides inbakaje donshiba aiyakamata kaje don Uncle Almustapha.......
Hmmm kawai yace kafin yashiga tambayar kanshi wanene Uncle Almustapha ma, kwakwalwar shi tashiga tunomishi dacan baya tun yana cikin gatansa,tun lokacin da kullum yake makale da mahaifinsa yakan ji labarinsa abakin Mai Martaba donkuwa babu ranar da zatazo ba a ambaci uncle Almustapha dinba,kallon Sulaiman din yayi yana tunanin yaushe shi uncle Almustapha din yadawo,sede besamu ansa ba sema tashida Sulaiman yayi yawuce dakin Ummi yana inbazakaje ba mukaga tafiyar mu aikoba komai kayi biyayya ga nagaba dakai,ko kula Sulaiman din baiyiba sesanda suka fitar da Ummi din zuwa mota Amira ma tadawo tadauki yar bag dinta tafice,duk yana ganinsu yariga yayi making mind dinshi and no one can change it,batun mahaifiyarsa da kannensa kuma he'll surely come for them............
Seda ya tabbatar kanin nashi yayi bacci sannan yakoma bangaren nasu,ah parlour yasamu Afiya da Sumayya suna sanye da hijabi Sumayya nata damun Afiya kan suje sugurin Mai Martaba, Afiya kuwa tsoro takeji don haka tacemata tabari se Dad yazo.......
Aikuwa ba ajima ba segashi yashigo dagudu Sumayya ta tashi tayi gurinshi tana Dad kaga Afiya ba tundazu nace ta tashi muje mugaida Uncle Abdulrahman taki, Sulaiman dayanzu shigowanshi yana turo wheel chair din da Ummi kekai yace "point of correction,Abba akecewa"....
Dariya Dad da Afiya sukayi yayinda Afiya tatashi aguje tayi gurin Ummi, Ummi dake kan kujera dataga yartata Itama zakaga canji ah fuskarta alamun she's so relieved.....
Sumayya ne tace Yaya Sulaiman ramawa kayi ko?, murmushin kawai yamata yayinda yajuya gun Amira yana miyene kike rakubewa kamar munafuka,lekowa tayi ahankali cikeda nervousness wannan karan Sumayya ne taganta dariya tayi mata yayinda takarasa gabanta tareda kamo hannunta"Amira miyena buya kuma?"....
Jijjiga ma Sumayya kai Amira tayi yayinda hawaye suka fara bin kuncinta ita kanta tarasa na menene,she just can't believe zata kwana acikin wannan makeken gidan me dauke da daular kaya kala kala,goge mata kwalla Sumayya tayi yayinda Afiya tazo ta rungumeta tana hawayen Itama"nayi kewarki Amira,I missed you so much!",takarashi maganar cikin muryarta dake rawa.........
Dad dake gefe ne yace to sad moment ya isa aidai kyabarta tazo ta gaisa da Dad ko?....
Murmushi kawai Afiya tayi kafin takamo hannun Amiran suka karaso gaban Dad, Afiya tace wannan Dad ne Amira Yayan Mai Martaba, i stayed in his house for this long and yanzu yadawo gida baki daya.........
Murmushi Amira tayi yayinda Dad yace bazakiyi hugging Dad dinki ba,dariya tashigayi cikeda jin kunyarshi shafa kanta yayi sannan yace Allah yayi miki albarka......
Amin ta amsa, Sumayya da Afiya ne suka tabuke fuska yayinda ah tare sukace Dad mufa?......
Wannan karan harda Mom dayanzu take shigowa aka yi dariyar.......
Dad ne yace to Allah yayi muku albarka dukanku.....
Atare sukace Amin, sannan yace to kuje kuhuta ko....
Gyada kai sukamai yayinda Amira taja wheel chair din Ummi sukayi ciki...

Hardakin Mom Sumayya takaita tana Mom nayi sabuwar kawa, she's so beautiful tazo tagaida ki......
Murmushi Mom tayi yayinda Asma'u tashiga gaidata,amsa gaisuwar Mom tayi azuciyarta tana yaba kyaun yarinyar don already daman Dad yace mata sunzo da yarinya zemata bayani daga baya zata kwana anan......
Bayan sun gaisa da Mom ne Mom din tace kinkaita gurin Ummin ku?......
Aa yanzu zamuje,to kaita tagaidata sekuje daki tahuta ko kafin anjima......
Kama hannunta Sumayya tayi sukayi dakin da aka tanadar ma Ummi,dakin fes fes yake agyare gawani kamshi dake tashi sede batasan dalili ba tunda suka doshi hanyar dakin takejin zuciyarta na dukan uku uku, Ummi nakwance kan royal bed, Amira ne kezaune gefenta tana bata ruwa tana sha,karasawa Sumayya da Asma'u sukayi yayinda Asma'u ke kallon fuskar Matar setaga tanayi mata kama da Almustapha sosai,riko hannun Ummi Sumayya tayi tana dan daga dayan hannunta "hello Ummi,nakawo miki new friend dina I hope you'll like her",Sumayyan takarashe maganar idanunta sun ciko da kwallah don sosai takejin tausayin Matar ace mutum na kwance ba lafiya tsawon shekaru haka.......
Kissing hannunta Sumayya tayi sannan tace"I hope you get well soon,I cannot wait to hear your beautiful voice kaman nasu Amira"......
Amira dake gefe ne tace Asma'u she's our Mom,Ina wuni Asma'u tagaida ta,jin shiru takuma sake gaidata wannan karan Amira ne tace"Bata magana amma nasan tajiki,zan iya ansawa on her behalf?", Amiran tayi maganar cikeda zolaya yayinda idanunta na zubar da kwallah, murmushi Asma'u tayi Itama nata idanun suna shirin tara kwalla tacema Amira eh.....
To lafiya cewar Amiran tana kokarin rike hawayenta......

*****
Dayanma Anty suwaiba tadawo gida agajiye,Aisha dake zaune tana kallo tace sannu da dawowa Anty suwaiba.....
Yauwa Aisha sannu,ina Asma'un badai tana nan tana aikin kukan nataba?.....
Murmushi Aisha tayi sannan tace a'a Aunty Suwaiba aima takoma gida yanzu nikeson fita insiyo kati inkira Ummi inji inta Isa gidan....
Cikeda mamaki Anty suwaiba tace,ta tafi kuma shine batayimin sallama ba,kenan baban nasu yasauko?.....
Aa Anty suwaiba su Yaya Sulaiman ne da Uncle dinsu suka dauketa kan zasuje subama Daddy hakuri.......
Sakan baki Anty suwaiba tayi sannan tace da izinin wa,agidan nasu ansan zasuje ne.....
Aa cewar Aisha din,tsaki Anty suwaiba tayi sannan tace yanzu ke kina da tabbacin can din sukaje miyasa kuna abu ba tunanine aiko kirana kyayi Aisha kifada min.....
Riko hannun Anty suwaiba Aisha tayi sannan tace kada kidamu Anty ninasan tana hannun kirki I trust Yaya Sulaiman Kuma hardasu Amira fa...
Janye hannunta Anty suwaiba tayi sannan tace nikam tashi kisiyomin kati inkira Ummin natan ban isa ba amanan yarinya aka banifa.......
Dariya Aisha tayi sannan takarbi kudin kati tafice don zuwa siyo recharge card din..........Dubawa yashigayi cikin nutsuwa yayinda lokaci daya fuskarshi tacika da annuri yana kuma hamdala azuciyarshi, Sulaiman dake gefe ganin Dad din yayi murmushi seyaji hankalinshi ya kwanta don shima daman beduba ba yafison yakawoma su Abban tukunnan ayi komai agabansu, Dad ne yamika ma Abba envelope din sannan yace it's now clearly written that su 'ya'yanka ne so,anawa tunanin wannan enough prove ne basai ankuma wani bincike ba.......
Karba Abba yayi yagani sannan yayi shiru nawasu dakiku don bemasan wani irin feelings yakeji aranshiba bare har yasama abun fadama su Dad din,abu dayane yasani ya yarda da Sulaiman da Yayanshi bazasu taba yimasa karya akan abu mai mahimmanci hakaba..........

Maidama Dad envelope din yayi sannan yace keep it with you and alhamdulillah with you nayi realizing wasu daga cikin zuria na dasuka dade baswa taredani,yaran dasuka jima basu samu gatanaba dakuma soyayyataba,I really feel blessed to have you Yaya Almustapha and in Sha Allahu daga yau zanbasu hakkinsu kaman sauran yan uwansu bazan nuna musu banbanciba dukda kuwa abunda mahaifiyarsu tayi mini,I believe it's not their fault laifin wani baya shafan wani,don haka zanrikesu dakyau and I'll give them the love they deserve.........
Ahankali Mai Martaba yadubi Sulaiman dake gefe yana ta murmushi yarasa inazaisa kanshi don farin ciki"mobbu honduko(rufe bakin) Babana",cewar Mai Martaba yana smiling dariya Sulaiman yayi sannan yace Abba Allah kadai yasan irin farin cikin danake ciki yau.........
Murmushi kawai Mai Martaba yayi sannan yace kaje kasamu Sarkin gida kace masa inason asanar da duk wani ahali nacikin masarautar nan kama daga kan bayi har sauransu kowa asanar mishi cewa inason yin sanarwa karfe takwas nadare..........
Gyadakai Sulaiman yayi sannan yatashi yafice, Dad ne yadubi kanin nashi sannan yace sanarwan miyene haka?......
Gyara zama Abba yayi sannan yace batun samun ya'yana I want to ensure that sunsamu equal right like the others......
Cikeda jin dadi uncle Almustapha yace naji dadin wannan decision din naka, I'm so proud of you sede bakayi maganar crown prince ba,yanzu kaga Almustapha ne babba.....
Murmushi Mai Martaba yayi sannan yace ba girman muke dubawaba yanzu Yaya, capability muke dubawa tukunnan shi Almustapha din ina yasan kan gidan sarauta daduk wani aiki daya kamata ayishi,sannan na biyu Almustapha is not a good boy for my people countless times ankawomin karansa anan Yaya,taina kakeson infara zaban shi ah matsayin shugaba fisabilillahi,innayi haka banyi adalci ma mutane na ba sannan abuna karshe danake dubawa shine Sulaiman anriga anjima da kwadaita mishi sarautarnan banason abinda zaikawo gaba tsakanin Ya'yana ni kaga dalilaina,so inaga mubar maganar nan we should focus on how to make that boy a better person tukunnan sabida mahaifiyarsu tariga ta lalatasu...........
Gyara zama Dad yayi sannan yace koma miyene shine yakamata yakarbi sarauta bayan kai and believe me he's capable enough,just give him a chance batun Sulaiman kuma shidakanshi yanuna bayaso......
Dan shiru Mai Martaba yayi kafin yace to shikenan amma se bayan bikin yaran nan zamuyi zama da mutanen fada bana yanke hukunci direct senaji opinion dinsu.......
Murmushi Dad yayi sannan yace Allah yakaimu lokacin,su waziri naji suntafi Maiduguri ko?...
Eh suntafi bayan laasar dinnan sune zasu halarci daurin auren su Sulaiman acan din cewar Abba yayinda Dad yace Allah yasanya alkhairi yakaisu lafiya yakuma dawo dasu lafiya.......
Amin ya Allah, daganan Abba yace i want to meet them now, kaini gurinsu Yaya.....
Kama hannunshi yayi yatayashi tashi yana "Abdulrahman tunanin me kake sama ranka haka duk kabi ka tsofe",dariya Mai Martaba yayi sannan yace kaidin naga Saurayine ai Yaya.....
Rankwashi Dad yake niyar kaimishi Mai Martaba yayi saurin kaucewa yana yar dariya kafin Dad din yace"zancen gaskiya kafini tsufa"....
Ah ido ba amma ai kafini shekaru Yaya kuma wahalar mulki ma kadai ta Isa ta tsofar dani, murmushi Dad yayi sannan yace to tsoho Abdulrahman.....
Murmushi kawai Abba yayi don yalura Yayannashi neman tsokanarshi yake son yi.......
Haka suka shiga takawa harzuwa bangaren dasu Dad din suke dukda kuwa dogaraye sunyi niyar binsu Abba yace suyi zamansu he's going alone......
Tunda ga waje Abba yalura babu dogaraye dakuma bayi ah bangaren,cikeda mamaki yadubi Yayan nashi, Yaya yahaka Sulaiman befadama bayi akwai baki anan bane ba, I'm not seeing any of the slaves here meyasa?.....
Cikeda rashin damuwa Dad yace kamanta ni ne Abdulrahman,I want a free life banason takura shiyasa nacema Sulaiman banaso koda yaturosu.....
Tsayawa Mai Martaba yayi sannan yace"to ai yanzu ah gidan nan kake wani free life ne Yaya,taya Madam ayyuka zasuyi sekuma masu gadinku tako ina for security reasons,don Allah kayarda da wannan abun in ansake turo su kada ka koresu please"......
Murmushi kawai Dad yayi sannan ya gyada ma kaninnashi kai dede nan suka isa cikin parlour din...
Guje guje sukeyi ah tsakiyar parlourn kaman wasu yara kanana,Sumayya narikeda apple ahannunta tana gutsura tana musu gwaliyo,"duk maiso yaje yadauko,ni banbadawa"......
Amira ne data gaji dabin Sumayya tace"koni mayyace na hakura wallahi,takarashe maganar tana zama kam kujera"......
Afiya ne tayi sa an kamo Sumayyan nan tashigayi mata cakulkuli suna dariya bashiri Sumayya tasaki apple din yafadi ah kasa yashiga gangarawa dagudu Afiya tasaketa tabi apple din tana tonikam yau nacika mayya dansainaci, daukar apple din tayi ahankali sakamakon ganin kafafun mutane biyu datayi gabanta wanda dayan kafanshi na sanye da takalmin sarauta me tsada da kyau wanda ko tantama babu na sarki ne inko banashiba tona Yarima Sulaiman ne sede shidin tariga da tayimishi sani inba occasionally ba baicika saka kayan sarauta ba,jitayi gabanta na dukan uku uku yayinda ahankali tatashi daga sunkuyon datake, Dad da Mai Martaba tagani dasuka tsaya kallonta suma fuskar Dad dauke da murmushi yayinda na Mai Martaba takasa fassara expression na fuskarsa,jatayi da baya ahankali sannan tashiga gaidasu cikin rudani....
Amsawa Dad yayi yayinda take idanun Mai Martaba yaciko da kwalla,koyanaso bazai iya denying cewa Afiya ba yarsa bace, she's his Daughter one single look yayi mata yagane hakan sabida kaman datakeyi da Sulaiman dama shikanshi hannunshi na shaking yariko hannunta"My Daughter?"....
Itama idanunta suncika da kwalla tashiga gyada masa kai, ahankali yarike hannunta kamkam suka karasa cikin parlourn don daga nesa yake hango twin sister dinta donkuwa ga kama nan already yasan Sumayya don dazu taje gurinshi sun jima tare,hada Amira da Afiya yayi ya rungumesu ahankali yakejin wani irin son su nashiganshi tareda tausayin yasukayi rayuwa without him,mesukayi going through without his support tunda shiba jiyau bane shi ganau ne na shari'ar da akayi da Almustapha kan yayi sata,what does that means suna rayuwar talauci kenan shiyasa yashiga harkar sata,anya ze iya forgiving kanshi for living them all alone kokuma Khairiya ne bazai yafemaba na abunda tayi mishi wanda hakan yasashi rabuwa da yayanshi.......
Sakinsu yayi ahankali cikin murya me rauni yace"forgive your Father please"........

Story continues below

Amira dake hawayene tace"wai yau nine mahaifina yake rungumata haryana neman yafiya na,maizai hanani yafe maka Abba,i really need you bansan miye dadin uwa ba bare na uba tunda na taso,tunda nayi wayau I always have the urge of being loved by a Father and Mother sede bansamuba,goge kwallarta tayi ahankali sannan tace Abba inban yafe maka ba ta ina zansamu wannan gatan barema by Allah bantaba rikeka a raina ba ko Inyi fushi dakai kullum tunanina shine wannan jarabawa ce garemu and in Allah ya yarda watarana zezama labari, Amira takarashe maganar tareda sake rungumar Mai Martaba tapping bayanta yashigayi yana lallashinta ahankali haka Afiya ma....

Sumayya ma karasawa tayi gabansu sannan tayi pouting mouth dinta"Abba nifa baza'a rungumeniba"......
Dad dake gefene yace"when will you grow up komai ke wasa kika dauke shi?"...
Amira da Afiya ne suka dan buda mata yayinda Mai Martaba yace"dagaskiyarta kyaleta Yaya,inbata rungume niba wazata runguma?".......
Cikeda jin dadi tashiga click din rungumar tana I love you Abba.......
Shafa gashin kanta yayi sannan yace "I love you more my darling Daughters".......
Asma'u dake gefe tana zaune tun su Sumayya na wasa harzuwa yanzu tatashi ahankali dan seyanzu tagane bekamata tana zaune cikin suba, family talk sukeyi and she should not be involved tashi tayi ahankali tafita ah parlourn dukda batasan meyake faruwa ba tayima su Afiya murna atleast they're reuniting with their Father,goge kwallarta tayi yayinda ta tuna kalaman Amira na tataso batasan gatan iyayeba, atleast ita tagode Allah ma tayi nata rayuwar cikin gata da iyayenta yanzu ne kadai tasamu misunderstanding dasu and tana fatan yazo karshe in Sha Allahu wata zuciyar kuma tace mata that means Ummin su Afiya is sick for this long,meke damunta kenan dede lokacin ta iso kofar dakin Ummin jitayi ta bugu da mutum dasauri takoma baya tana subhanallahi, I'm really sorry kasa rufe bakinta tayi ganin wanda ke gabanta saurin dauke kanta tayi sannan ta raba ta gefenshi zata wuce janyota yayi yadawo da'ita gabanshi yana binta dawani mugun kallo janye hannunta tayi daga rikon dayamata cikin sauri zata sake tafiya yasake fizgota"why do you keep following me?"........
Wani harara ta daka mishi azuciyarta tana lallai wannan yacika dan rainin wayau,afili kuma tace "inma nabiyo wasu aibakai nabiyo bako?"......
Cikeda rashin damuwa yace"they're my family don't you even think of hurting them"......
Batareda tacemai komaiba tawuce tashige dakin Ummin don ita tarasa suitable answer dazata bashi taji dadi aranta,meke damunshi why will he even think that she'll hurt his family......
Shiko yaji haushin shariyar datayi masa don haka yajuya zaibita seyaji Dad yakira sunansa, ahankali yajuya bangaren Dad din sannan yace na'am,arba yayi da fuskar Mai Martaba.......
Kallonshi Mai Martaba yayi sannan ya ware mishi hannu alamun yaje gareshi,dauke kanshi yayi sannan yajuya ahankali yabi ta back door batareda yace musu komaiba cikeda defeet Mai Martaba yace"he's different from them, he's older than them daman nasan it'll be difficult for him to forgive me,sede nima I'm just trying to accept him sabida yazame min dolene amatsayina na ubanshi bawai don Ina alfahari da halawayensa bane,duban Dad Mai Martaba yayi sannan yace I'll introduce them tonight convince him to come to the venue please Yaya",yana karashe maganar yajuya yatafi, jijjiga kai Dad din yayi sannan yabi bayan kanin nashi......
Tanaganin abunda Almustapha din yayi sede kwata kwata bataji dadin abunda yayima mahaifin nasa ba koda kuwa meyamasa, ahankali takarasa jikin gadon da Ummin ke kwance idanunta bude tana kallon silling sede takan dan kyafta idanun, murmushi Asma'u tayi sannan takalli wheel chair din Ummi dake can gefe ahankali tajanyo shi sannan cikin dabara ta daga Ummi tadaurata kan wheel chair din dawowa tayi gabanta tareda cewa"Ummi zamuje musha fresh air awaje I hope you don't mind?".....
Tsayawa tayi kozata samu ansa daga Ummi din amma shiru ko motsi Ummin batayiba,jiki ah sanyaye taja wheel chair din harsuka bar dakin ta backdoor tabi don dazu taleka tahango wani guri kaman lambu daga wani bangare and gurin is so silent,tura wheel chair din tadingayi har suka isa lambun shiga sukayi sannan ta samu wani karkashin bishiya dataji yanada sanyi gakuma iska me dadi dake kadawa tsaida wheel chair din tayi sannan taciro dankwalinta tashimfida agaban Ummi tazauna tana sauraron yanda tsuntsaye ke shawagi dakuma kuka ko ina agurin fes yake,kallon fuskar Ummi tayi ahankali sannan cikin kakkausar muryarta tace"I hope you're feeling okay here Ummi,naga dakin is so silent and you were all alone shiyasa nayi deciding infito dake kisha iskan duniya,I know you're sick and can't walk on your own but we're here for you right?,kinada right din yin yanda kowa keyi,you should know what's going on in the world as well, inafatan banyi laifiba tayi maganar tana sunkuyar da kanta dukda kuwa tasan ba ansa zata samuba"...... ...
Sunfi minti goma shabiyar shiru ahaka can ta tashi tsaye tana dan karema lambun kallo daga tsaye idanunta ne suka gano mata bishiyoyin tangerine da Guava duk sun nuna wanda tundaga inda take take hango yanda suka canza kala.....
Cikeda jin dadi ta kalli Ummin"Ummi barina kawo mana abun motsa baki,batajira cewartaba tayi gaba seda taciro da dan yawa sannan tadawo tawanke bakin wani tiyo dataga ansa ma wata bishiya ruwa na zuba,zubasu tayi cikin hijabinta sannan tazauna gaban Ummin....
tashiga bare tangerine din tana bama Ummi din da tayi tunanin bazatasha ba setaga tana sha kuma,yafi rabi tabata tanasha kafin tadaina tauna kuma seta hakura tacanza mata da gwava din shima half taci taki cigaba da cidin,nan Asma'u tashiga ci itama bakaramin dadin tangerine din tajiba sabida tsabar zakinsa,seda ta gama sha sannan tadubi Ummin tana dan taba cikinta"nakoshi wallahi Ummi amma jinake kaman inkara, tangerine din zaki Masha Allah".......
Batadamu da rashin maganar Ummi ba all that she believes is Ummi najinta and tasan me take fada don haka tace"Ummi barinayi miki tarihin Annabawa,I don't know which one you'll like to here amma yaudai zanyi miki na annabi Sulaiman and next time semuyi na wani Annabin,dan shiru kuma tayi tunawa datayi gobe zata tafi gidama, murmushi kawai tayi tana shirin fara yimata tarihin taji ana kiran sallar maghrib,sakan baki tayi sannan tace ikon Allah, Allah babban sarki har lokacin sallah yayi......
Dauke dankwalinta tayi akasa sannan tawuce bakin tiyo din tayi alwala abunta kafin tadauko wani kettle data hango very clean tadibi wani ruwa aciki takarasa gurin Ummin tashiga yi mata alwalan.........
Almustapha da tun da yabar cikin gida yarasa inazaisa kanshi sekawai yayo cikin lambun yasamu guri yazauna yana tunanin duniya cikeda haushin Mai Martaba din na wato seyau yatuna dasu, seyau yasan su Ya'yansa ne,shiyasan he's not a toy daza aringa playing da,years back mahaifinsa yakoresu yakuma ciresu cikin life dinshi and now all of a sudden yace yadawo yanason su, this's impossible bazai yarda yafara believing his Dad is back ba wataran asake breaking heart dinshi,yana cikin wannan tunanin ne yadinga jin kaman motsin mutane acikin lambu bayan wasu dakiku kuma seyadinga jin magana jefi jefi anayi,sede bedamuba tunda yasan akanzo ayi bayin lambu dayanma don bazaice daya daga cikin Ya'yan Mai Martaba bane sukazo lambun don yasan sunacan suna shagalin biki don haka yacigaba da zamansa gurin idanunsa lumshe har aka kira sallar maghrib......
Tashi yayi don tafiya masallaci yana cikin tafiya ya hango kaman Umminsa donkuwa kayan dake jikinta kenan,cigaba da matsowa yayi gurin ya tabbatar itance yayinda Asma'u nayi mata alwala fuskarta daukeda murmushi........
Wani irin shock yaji ajikinshi atake kuma jikinshi yayi sanyi sabida yaga abunda su basu taba yima Ummin ba tunda kuwa rashin lafiyar ta tayi tsanani,kasa tafiya yayi yacigaba da kallon Asma'u din yanda takeyimata cikeda kwarewa harta gama taja wheel chair din sukayi cikin gida tana"muje muyi sallah Ummi".......
Binsu yayi abaya jiki ah sanyaye seda ya tabbatar tashige gida da Ummin sannan yawuce masallaci gabadaya abun naransa.......

Story continues below

"****
Nikam gaskiya Aisha baki kyautaminba tun dazu nike Kiran layin matarnan akashe,nidamuwanbewuce inji in yarinyar nan ta Isa gida lafiya ba, Aisha dayanzu tafito ah bandaki tace Anty kiyi hakuri don Allah in Sha Allah Asma'u ta isa gida lafiya"....
Allah yasa cewar Anty suwaiba kafin ta tashi don shigewa bayin Itama tana mita"ai gobe da yardar Allah zanje gidan nasu indubo dakaina"...
Itadai Aisha tada sallah tayi don ta gaji da mitar yayartata mistake dinta daya tamanta bata karbi number din Sulaiman dinba gashi Amira ba wayane dasuba.......

*****
Tunda aka idar da sallar maghrib yashigo gida yayinda bayi biyu ke biye dashi ah baya hannunsu rikeda kaya,Amira, Asma'u da Sumayya na zaune ah parlour sunata haukansu duk suncika koina da surutu.......
Karasowa yayi cikin parlour yana toshe kunnenshi "Kai! Kai! wannan ai seku fasama mutum dodon kunne".....
Amira ne ta taso tana Yaya Sulaiman ango......
Cire hannun yayi ah kunnenshi sannan yace mekikace,yayi maganar yana satan kallon Sumayya don yau tayi shigar mutunci batasa kananan kayaba doguwar riga tasa har kasa,cewa nayi Yaya Sulaiman ango,hope za aje dauko amarya damu......
Jan kumatun Amiran yayi sannan yace,aidole aje dake lil Sis watanedai ko ah tayan mota baza ajeda itaba.......
Cikeda tsarguwa Sumayya tace "nidaman bance zanjeniba",dariya sukayi duka yayinda yace"kujimin tsarguwa,dadin abunma ni ban ambaci sunaba".....
Turo baki tayi kaman zatayi kuka sannan tazari wayarta zata bar parlourn cikin sauri yariko hannunta tafado jikinshi cikin muryar dabaisan yanada itaba yace"I'm sorry kanwata wasa nake miki fa,inbakije ba wazai je Sumayya?"......
Tureshi tayi da karfi sannan tace nidai bazanjeba daman koka fada ko baka fadaba, besides ina ruwana ma da bikin ka takarashe maganar murya akarye sannan tawuce cikin gida,binta yayi da kallo seda ta bacemai da gani sannan yakalli bayin yace kushiga dakincan kujirasu kunji abunda nafada muku ai......
Cikeda ladabi bayin sukace eh, yayinda ah zuciyarsu suna mamaki waza asa suyima shirin sarauta sude sunsan anbasu alkyabba uku.......
Kallonsu Afiya yayi sannan yace Abba yace kushirya kuje zasu shirya ku inmun fito ah sallah zandawo.....
Gyada masa kai sukayi,yayinda yace Yaya Almustapha fa?..
Amira ne tace bedawo daga sallah ba, okay sena dawo yakarashe maganar yana fita yayinda wayarsa tashiga ringing,tsaki yayi gabadaya yarasa Kashi nawa zeraba kansa friends dinsa dasukazo daga london se kiransa sukeyi he knows that yakamata yana taredasu dukda anyi musu providing komai ah masaukinsu sede dole yatabbatar everything is alright ananma,yana cikin tunanin nan ne yaji Dad yace go and attend to your friends I'll talk to him......
Dagowa yayi yakalli Dad din sannan yasaki lallausar murmushi kafin yadaga call din yanacema me wayar gashinan zuwa..........

Tunda ta ajiye wheel chair din Ummin yana kallon gabar tacema Ummin tagabatar da sallahnta,yayinda Itama tashimfida darduma ta tada tata sallar har ta idar seda tagama addu'o'inta sannan tadan jingina kanta da jikin gadon tana kallon Ummin tana dan motsi dakanta wanda hakan yayi mata dadi don gani tayi kamar sallahn Ummi keyi, murmushi tadan saki kafin afili tace"Allah yabaki lafiya Ummi".......
Komawa tayi tasake jingine kanta tareda lumshe idanunta haka kawai taji tanason tayi karatun alqur'ani sede bataga qur'ani akusaba kawai seta shiga rera suratul rahman cikin muryarta medan karen dadi cikin nutsuwa kuma bawai tadaga muryar sosai bane don inbakana kusa da dakin ba bazakaji karatun da takeyidin ba..........

Tunda yashigo gidan yawuce dakin Ummin don dubata,sede tunda ya iso kofar dakin yakejin kaman ana karatu,bude kofar dakin yayi batada kara wanda hakan yasa Asma'u bataji shigowanshiba,ajikin kofa yatsaya yana jin karatun nata harcikin ranshi,hakanan yaji yakasa karasawa cikin dakin hartakai karshen suran yananan tsaye,jira yake yaji kozata cigaba tadauko wata surar amma shiru daga kafanshi yayi yana shirin juyawa carab sukayi ido hudu dauke kanshi yayi cikin sauri sannan yakarasa cikin dakin.........
Gaban Ummin yaje yana karema wheel chair din kallo sannan yashiga shirin maidata ta kwanta........
Cikin sauri Asma'u tace dakabarta azaunen tafi jin dadi,wani harara yadaka mata batareda yace komaiba .......
Dan tabune baki tayi don bataji dadin abunda yayiba takuma cewa"Allah daka barta intayi sallahn isha se inmaidata kwanta"......
Bayan ya kwantar da Ummin ne yace kebakiga condition dinta bane dazaki zaunar da ita,bazata gaji dazama bane akace miki...........
Dan bata rai tayi sannan tace"is not as if I want to hurt your Mother Yaya Almustapha,I'm just trying to help and nothing else".......
Cikeda bacin rai Almustapha yace"what do you mean,did we ask for your help?".....
Shiru tayi nadan dakiku sannan tace"I'm sorry it's not your fault it's mine danashiga hurumin da banawaba amma we should talk outside karmu dameta,hararanta yayi batareda yadamu da maganar da takeyiba sannan yazauna gefen Ummin,fita tayi ah dakin tana dan share kwallarta ah corridor din dakin tazauna har yafito sannan tatashi tatsaya gabanshi takuma cewa "I'm sorry kawai naga she's all alone in the room ne,I know how it feels to be lonely shiyasa nazo mudaukema juna kewa sekuma batun sallah dana taimaka mata tayi naga tunda nazo gidan nan yau babu wanda yayi tunanin taimaka mata wurin yin alwala in lokacin sallah yayi bare azo ga batun sallah,I don't know kodan su Amira were busy inside the house ne shiyasa basu samu sunzo suntaimaka mata tayiba Kuma naga sallarna it's important for her as she's sick,koda mutum baida lafiya sallarnan dai tana kanshi it's obligatory sede Allah bai tsawallataba inmutum baida lafiya zai iya yinta ah kwance hakana zai iya yinta azaune kaman yanda Allah yafada acikin suratul An nisaa aya ta dari da Uku,inada tabbacin kanada masaniya da hakan Inkuma baka dashi kana iya zuwa ka duba Yaya Almustapha sabida samun karin ilimi...........dan numfasawa tayi sannan tace,komu no matter how busy we're we should never miss prayer because"A busy life makes prayer harder, but prayer makes a busy life easier", besides we never know when our last prayer would be bare Ummi dake kwance babu lafiya and we all want her to be healthy kuma hakan zaifaru ne only da rahamar ubangiji,mumata addu'a Itama muyi assuming tanayi anata ran,shaaa why am I even saying all this things I know it sounds weird but I'm sorry kawai nafadi abunda keraina ne tana karashe maganar tashige daki abunta,binta yayi da kallo ahankali kuma yaji antaba shi cikin sauri yajuya Dad ne fuskarsa daukeda murmushi yace"Zo Son"....
Babu musu yabi bayan Dad din harzuwa dakinshi nan Dad yace ga kayanan kasaka we're going somewhere I'll be waiting for you at the parlour........
Kallon kayan Almustapha yayi badan ranshi yasoba yagyada ma Dad din Kai,fita Dad yayi yayinda yashiga daga kayan yana kare musu kallo"arayuwanshi na yanzu he has only 4sets nakaya wanda suyake cuccudawa yacanza
dukda kuwa irin kodewan dasukayi tsabar sunci duniya,he don't want to wear those clothes sede yana ganin girman Dad he cannot just keep him waiting,batareda yadamu dayin wanka ba yadauki kayan yasaka sannan yasaka takalmin ma kallon mirror yayi lokaci daya yaga yacanza kaman bashiba,lokaci daya yaga yakoma his old little Almustapha (The prince),saurin dauke kanshi yayi daga madubin don bayason yacigaba da yaudaran kanshi,if he can see the old him through the mirror bazaisa yafara regaining old feelings dayake dashiba ada shiyasa yayi saurin dauke kanshi sannan yafito ah dakin yayi hanyar parlour nan yasamu Dad zaune,tashi Dad yayi yana karema Almustaphan kallo babu abunda yake furtawa inbanda Masha Allah.......
Riko kafadun Almustapha yayi sannan yace"yanzu naga Yarima",Dad din yakarashe maganar yana murmushi lokacinne kuma su Amira ma suka shigo sanye cikin kayan sarauta bakaramin kyau yamusuba sannan lokaci daya suka canza kama, Sumayya ma na sanye da kayan ajikinta,dan fakan idanunsu tayi sannan dakin Ummi....
Asma'u dake zaune bakin gado takamo ta dasauri tana kekam kinfison zaman daki friend,to kizo kiga Yaya Almustapha yanda yakoma"oh my god Sumayya tayi maganar tana sa both hands dinta ah both side of her cheek sannan tace dabadan kinrigani ba wallahi se ince ina crushing gayen nan,tayi maganar dreamingly",buge hannunta Asma'u tayi sannan tace Sumayya you're impossible wayace miki haka,yar dariya Sumayya tayi sannan tace"I already know basai kinmin boye boyeba,don Allah muje kiganshi".....
Nibazanje ba Asma'un tayi magana stobbornly tana shirin komawa tazauna.....
Fuskar tausayi Sumayya tayi sannan tace tomuje kigasu Twins suma tunda ni ko compliment bakiyi nayi kyauba takarashe maganar tana hararan Asma'un wanda hakan yasa Asma'u dariya sosai kafin taja kumatun Sumayya,inama kika bani chance din complimenting naki Sumayya, believe you really look gorgeous.......
Cikeda jin dadi Sumayya tace"thank you",sannan taja hannunta suka fita tana kizo muje kigansu babu yanda taiya haka suka tafi........
Sanda suka Isa parlourn duk suna zazzaune yayinda Almustapha ke sallar isha akan wata darduma kuma direction din datake tsaye nan ne gabar wannan yabata access din kare mishi kallo, bakaramin kyau yayi bakam setaga kuma yacanza mata hartafara tunanin anya wannan"Mr Taciturn dinta ne kuwa",karasawa tayi gurin su Amira tace kunmin kyau da wayana na nan dana muku hoto ......
Sumayya ne tace I've my phone gashi kiyimana, murmushi kawai tayi sannan takarbi wayar nan tashiga yimasu hotuna .......
Daga karshe sukace ayi selfie da'ita....
Dad de yana gefe yanata kallonsu yana dariya,sanda Almustapha ya idar Dad yaduba time yace mutafi........
Seda suka fita sannan takoma ciki fuskarta daukeda annuri.......
****
Tarone akayi ah filin Masarautar sosai wanda duk tarone na bayi, dogaraye dakuma duk wasu daga ciki ahalin masarautar yayinda kowa da portion din inda suka tsaya, Mai Martaba na sama gefenshi yan fada ne wanda suka fi kusanci dashi duk da kuwa badukansu bane ke gari sabida halartar daurin auren Sulaiman da Zaliha dasuka tafi ah Maiduguri.........
Bude taron akayi da addu'a yayinda Mai Martaba yafara magana cikin nutsuwa"nasan kuna mamakin taraku danayi ah cikin daren nan dukda kuwa bikin da ake gudanarwa acikin gidan nan wanda I must say almost all of us are busy with the preparations,sede inason kusani cewa shi wannan taron danasa ayi yanada matukar mahimmanci gareni damaku baki daya sabida inason ingabatar muku dawasu daga cikin ahalina dana jima Ina begensu nakuma Jima inanemansu wanda inada tabbacin wasu daga cikin ku sunsan da hakan,to alhamdulillah Allah yayi dawowansu alokacin dana fidda rai daganinsu shiyasa nahada wannan taron don insanar daku, ahankali yadubi Sulaiman dake gefensa alamun yashigo dasu,fita Sulaiman yayi sannan ba ajimaba saigashi yadawo tareda su............
Kallonsu Abba yayi sannan yariko hannun Abba dana Sumayya yayinda Mom kegefensu yace wannan shine Yayana Almustapha wanda yajima baya tareda mu ayanzu yadawo gida alhamdulillah tareda iyalinsa.......
Zubewa dogaraye da bayin suka shigayi suna mika gaisuwa murmushi kawai Dad yakeyi musu yana daga musu hannu,kafin Abba yakamo hannun Almustapha yasakashi gabanshi yana kallonshi still bai saki hannun ba"This my very own Son, Almustapha tareda my two princesses Afiya and Amira da recently nagane cewa su jininane kuma Ya'yana da Allah yamani baiwa yabani su..........
Nanma bayin da dogaraye suka shiga zubewa suna mika gaisuwa yayinda kowannensu zuciyarsu na bugun uku uku da abunda suke gani barinma wayanda abuyataba shiga tsakaninsu da Amira ko Afiya da Almustapha din don sunsan yanzu kam kashin su ya bushe..
Abba ne yanuna strictly they need to be respected kaman yanda akema sauran yayanshi sannan duk wanda yabata musu koyayi musu abunda bashibane zehadu da consequences,bayan dogon bayanai dayayi sannan aka rufe taron seda suka bar filin sannan kowa yashiga watsewa.....
Amira da Afiya harda hawayen farin ciki........


Jijjiga ta Talatu tashigayi gabadaya ta rude yayinda wasu daga cikin bakin ke aikin yi mata fifita cewa akayi akawo ruwa cikin sauri jiki na bari Talatu tafita da gudu batajimaba tadawo da ruwa ah kofin silver mikawa Hajiya Salima ruwan tayi yayinda matar tasa ruwan ah hannunta sannan tashiga shafa ma Magajiya ah fuskarta..........
Motsi tafara yi ahankali sannan tabude idanunta yayinda lokaci daya abunda yafaru yashiga dawo mata,dasauri tatashi a rikice sannan ta makuro Talatu"don ubanki me kikace?".....
Mekika fadamin, cikeda tashin hankali Talatu tafara kuka tana kokarin kwatan kanta,ganin Magajiya nashirin yima Talatun rauni yasa Hajiya Salima data fi kusanci da ita ta riko Magajiyan sannan tayi mata rada cikin kunne,mutane na ganinki Magajiya zaki tonama kanki asiri kikwantar da hankalinki kicikata tukunnan.......
Se lokacin Magajiya tama tuna biki akeyi ah gidan kuma da jama'a ah dakin nata, ahankali tasaki Talatu dake shesheka kuka kaman ranta zai fita donta lura yau agarin neman kyauta me tsoka ankusa aikata lahira,zaunar da Magajiya Hajiya Salima tayi yayinda hakurinta yakasa tsayawa nan don haka tatashi tafice tana huci,bangaren Mai Martaba tayi direct yau ko jiran dogaraye su sanar dashi isowanta batayiba ta banka cikin dakinnashi...............
Yana tsaye yayinda hannunshi sarke ah bayanshi yana tunane tunane shikadai,cakumo rigarshi tabaya tayi yayinda yayi saurin juyowa idanunta dasukayi jazir tadubeshi da su kafin tafara bugun kirjinshi"meyesa zaka cuceni,mahimmanci na kenan agurinka, Abdulrahman ka kyautamin kenan abunda kayi takareshi maganar tana kuka still tana bugunshi akirji,cikin sauri yadan tureta yana"meyene kuma Magajiya,yakina behaving kamar yarinya laifin me nayi yayi mata tambayar innocently don shikanshi yarasa meyayi".......
Sake cakumo rigarshi tayi tana zazzare idanu"au bakamasan mekayiba,cikin tsawa tace kanason kacemin bakamasan mekayiba?"......
Maimartaba dai dakyar yake numfashi tsabar cakumar da Magajiya tayi mishi........
Dad dayanzu shigowarshi dakin yazo yima Abban saida safe yaga Magajiyan ta makure Mai Martaba tura kofan yayi dasauri sannan yaje yajanyota ta baya,yana baki da hankaline,miye hakan cikin sauri Itama tajuyo tana kallonshi "Babu ruwanka,meyezaisa kashiga abunda ba nakaba,kafita kabar dakinnan yanzu tayi maganar tana nuna mishi kofa"......
Cikeda bacin rai Dad yace"kode ke kifita ba jahila kawai wanda batasan mutuncin kantaba barena dan Adam,daga hannu tayi cikeda bacin rai zata kaima Dad mari yayinda cikin sauri Mai Martaba yariko hannunta sannan yadaga hannu yakai mata wani wawan marin,bakida hankali ne "he's my very own Brother and kina tunanin daga hannu kimare shi,wai Magajiya miye yake damunki ne wai?".........
What's all this for goodness sake, Mai Martaba yayi maganar rai bace har jijiyoyin wuyanshi natashi, Magajiya daharyanzu bata dawo daga shock din Marin ba hannunta kan kuncinta tatsaya tana kallon Mai Martaba, kafin tafara kuka"ka mareni Abdulrahman sabida Yayanka yadawo,ka mareni sabida kasamu Ya'yanka,ka mareni sabida kasamu wanda sukafi maka mahimmanci ah rayuwarka mudama option ne agareka nasan dahaka shiyasa baka damu da sanar dani komaiba sede inji ah bakin wasu"........
Cikeda da bacin rai Mai Martaba yace"oh abunda yasa kikazo kina haukar nan kenan,don banfada miki dawowarsu ba, yaushe ma kikazo gurina Magajiya,Ina kinsan banida lafiya amma tunda kikazo sau daya bakisake neman inda nake ba inma mutuwa nayi baki damuba you only care about the wedding and yourself,ta inazan ganki har infada miki nasa ayi taro shima bakizoba yakikeso inyi miki yakarashe maganar yana nunata da yatsa,I don't want any disturbance now kifita kibarmin daki tunkafin raina yasake baci".........
Cikin kuka Magajiya tace aidaman nasani ta inda zaka bullo kenan,samun guri Mai Martaba yayi yazauna yana huci sannan yace Allah tunda mutuncin ki kifita inbahakaba zansa guards suzo su fiddamin ke banida time din all your nonsense..............
Jiki ah sanyaye tana hawaye ta harari Dad tafice tana huci.......
Ahankali Dad yazo gefenshi yazauna tareda tapping shoulder dinshi"are you alright?"......
Gyada masa kai Mai Martaba yayi sannan yace I'm sorry on Magajiyas behalf nasan rantane yabaci daban gaya mataba shiyasa tayi behaving this way when she calms down zatadawo daidai"......
Cikeda mamaki Dad yace,is this how she behaves when she's angry,gyadama Dad kai Abba yayi for the second time kafin yakara da but bayakaiwa nayau sede ina mamakin don banfada mataba bai kamata tayi reacting this way ba and it's all her fault bata bani daman fada mataba inama naganta Abba yayi maganar rai bace sannan ahankali yadago ya kalli Dad din"amma kamata yayi ta tayani farin ciki ko tunda tasan how important you're to me bawai tayi behaving this way ba,so what if banfada mataba ai yanzu tasani",yayi maganar murya karye cikeda tausayinshi Dad yace"kahuta yanzu we'll talk about this about it after the wedding",gyada kai Mai Martaba yayi kafin yakwanta kan gadonshi nan Dad yamishi saida safe yafita yana kissima halayen Magajiya yakamata asirinta ya tonu,yakamata kaninshi yagane cewa wacece real Magajiya sede bazasu iyayin hakan ba harsai sun hada kai sun tona mata asiri yanda kowa zaisan asalinta,bama yan masarautar ba yan gari baki daya sabida tayi succeeding in her act kuma tasama ran mutane cewa Almustapha is not the real child but illigitimate sannan tasamusu wrong impression akanshi he knows that it's going to be a tough ride gashi dama ahalinshi baki daya sede no matter what,they have to expose her with Allah's help,tunowa yayi dawani abu kafin ahankali yawuce bangarensu .......

Story continues below

Tunda Magajiya tafito ah bangaren Mai Martaba bata wuce koina ba se bangaren su Humaira da Halima don tasan nanne kadai babu wasu baki donsu kadai ne se yaransu,tunda tashiga dakin Halima tayi saurin riko hannunta tazaunar bakin gado,Mama kiyi ahankali kada kijima kanki ciwo........
Ture hannun Halima tayi sannan tace amma Allah yahadani da gabayen Ya'ya bansaniba,yanzu harkuma ayi irin wannan aika aika ni bansaniba?........
Cikeda damuwa Gimbiya Humaira tace"kiyi hakuri Mama wallahi bamusaniba Kuma ni aganina duk wannan tada hankalin dakikeyi bashine mafitaba,mafita shine mutaru munemi solution inkina behaving haka se asirin dakika jima kina boyewa ya tonu don mutane zasufara suspecting wani abu barema gida da jama'a, tabbas nasan labarin yazo miki ah bazata kamar yanda yazo mana sedefa ba hakan yana nufin gwiwar mu tasace bane don muddin su Almustapha suka samu gurbi aziciyar Mai Martaba shikenan mu zamu zama yan kallo.........
Cikeda gamsuwa Magajiya ta kalli yartata tanajin bayanin datakeyi dukda kuwa ranta na tafarfasa seda takai aya sannan tace yakikeso muyi inban nuna bacin rainaba Humaira......
Murmushi Humaira tayi sannan tace nima bansan yaxa ayiba yanzu amma inason kikwantar da hankalinki agama bikin nan lafiya jama'a su watse kafin mukoma namu gidajen semusan mezamuyi,don Allah Mama kidaure kada kice zakiyi wani abu..
Dan shiru Magajiya tayi sannan tace"toshikenan,zanyi iya kokarina"....
Yauwa cewar Humaira din kafin tace Abba ma kije kibashi hakuri inya sauko kudawo normal don inkun samu matsala kaman aikin mu yarugujene don zaifi kusanci dasu wayancan din........
To kawai Magajiya tace bawai don ranta yanasoba.......
Haka suka cigaba da tattaunawa............

****

Washegari asabar karfe shadaya na safe aka daura auren Humaira da mijinta Sadiq wanda shima dan wata Masarauta ne,anhalarci taron daurin auren sosai don kuwa cikin masarautar babu masaka tsinke ancika makil yayinda motaci kuwa sunjeru daga waje duk na manya manyan mutane kama daga kan masu gwamnati,yan siyasa,manya manyan yan kasuwa sannan kuma sarakuna daga different masarauta sun halarci taron daurin auren...................
Yayinda acan garin Maiduguri ma andaura auren Zaliha da Sulaiman wanda suma anyi taro sosai..........
Tunda aka gama daurin auren aka tafi inda aka tanadar donyin reception wanda shima duk acikin Masarautar ne,yayinda kide kide na ganga dakuma algeta shike tashi cikin masarautar hakanan masu kirarima nayi da maroka,karkuso kuga Sulaiman yanda yahade cikin kayan sarauta bakaramin kyau yayiba don kayan daya sama na daban ne bakaramin aiki akayi akantaba sewani sheki yakeyi daka ganshi kaga ango
Dukda kirarin da morokan keyi mishi baidamuba sabida shi gabadaya hankalinshi ma ba akansu yakeba he's busy looking for his one and only Brother dazu suna tare besan ya akayi ya bace mishiba,juye juye yashigayi yana neman shi can yahango shi tsaye jikin wata mota yayi folding hannunshi ah kirji tareda dan lumshe idanunshi kadan, murmushi Sulaiman yayi sannan cikin sauri yakarasa gabanshi"Allah Yaya Matarka ta haduda aiki,innayinan seka zille kayican se gudu kakeyi kana barina nikadai and i always want you by my side"Sulaiman yakarashe maganar yana pouting bakinshi murmushi Almustapha yayi wanda yafidda white teeth dinshi tareda sa dimple dinshi lotsawa kadan"Congratulations Ango"......
Playfully Sulaiman yace "so Yaya Almustapha can tease someone, tundazu inka zille nasamoka maganarka daya"congratulations ango", Sulaiman yayi maganar yana immitating yanda Almustapha din kefadi.....
Sannan yasa hannunshi ah aljihun wandonshi yana"don't worry soon zamu nema maka mata, this's what I'll be doing on your wedding day as well"......
Jijjiga kai kawai Almustapha din yayi batareda yace komaiba yayinda Sulaiman din yakarema Almustapha din kallo from head to toe"oh my god Yaya tundazu nidanake namiji ma nakasa daina admiring kyaun da kayi barekuma ace kashiga school yanzu"I promise wasu matan sesun saki baki yawu yana zuba"........
Hmmm kawai Almustapha yace sannan yatafi yabarshi agurin binshi Sulaiman din yayi cikin sauri"I'm sorry don Allah kada kasake guduwa yanxu muje gida gurinsu Mom da Ummi".......
Kaje gurin Mama ne Almustapha yayima Sulaiman tambayar batareda ya kalli inda yakeba......
Jijjiga kai Sulaiman yayi jiki ah sanyaye sannan yace"i won't".....
shiru Almustapha yayi don har Sulaiman yafidda ran zaiyi magana yace"why?".....
Tsayawa Sulaiman yayi sannan yace"kasanta she'll start lecturing me barema nasan she's angry with me ga abunda yafaru"......
Kallonshi Almustapha yayi cikeda tausayinshi sabida ganin how different he's from his Mother kokadan bedauko halintaba,yau in akacemishi Magajiya ba mahaifiyar Sulaiman bane bazai musa ba because they're two different people with two different perspectives......
Ahankali yadanyi tapping shoulder din Sulaiman din sannan yace"you've to go and see her,you need her blessings",yana karasa fadi yayi gaba yabar Sulaiman tsaye gurin cikin sauri Sulaiman din yakamo shi yana"okay zanjeni amma first muje gunsu Ummi,shidai Almustapha bece masa komaiba har suka Isa sashin nasu wanda yanzu take kewaye da dogaraye yayinda bayi kuma aciki sunata harkokinsu don daga Sumayya zuwa Afiya kowa ankawo mata baiwa biyu wanda zata kula da needs dinta haka Ummi ma Sulaiman yasa ankawo Uku masu kula da lafiyarta haka Mom sunkai hudu wanda zasuna kula da harkokin cikin gidan........
Tundaga bakin parlourn yake kwala ma Sumayya kira,tanajinshi taki ansawa dan murmushi yayi sannan yabar Almustapha ah parlour yawuce dakinta tana kwance kan bed tana chatting abunta,tunda yashigo kamshi turarenshi tadingaji  medan karen dadi tareda kwantar mata da hankali.......
Gaban gadon yakarasa ta inda take kallo,inata kiranshi shine kika ki ansani Sumayya?......
Dagowa tayi takalleshi sannan tamaida kanta kan wayar banji baneba......
Wabce wayar yayi yawurgar kan gadon sannan yakamota tatashi tsaye"meye damuwanki Baby girl yayi maganar yana kanne mata Ido daya,kokarin kwace kanta takeyi amma takasa,sassauta rikon dayayi mata yayi sannan yace ahankali"why are you behaving so strange this days,yes nasan we always tease each other still muna hira ai ko but now abu kadan sekiyi fushi dani I don't know why"......
Feel free Sumayya,nayimiki wani abune yayi maganar yana kallon kwayar idonta,dan rufe idanunta tayi don Itama batasan daliliba ahankali tace babu komai....
cikin sigar lallashi yace kalleni to,bude idanunta tayi tadaurasu akanshi don ta damu yatafi yabarta sabida kamshin turaren shi firgitata yakeyi and his presence as well....
"Are you sure?".....
Gyada masa kai tayi, murmushi yayi sannan yace "to daga yau adaina min rashin kunya inbahakaba zan ballah bakin",dariya kawai tayi yayinda yasaketa sannan shi ya kwanta kan gadon nata tana tsaye"washhh nagaji wallahi,yau tun safe banzauna ba infact tun jiyama"......
Cikeda damuwa tace"sorry"..
"Thanks",zokimin massage yayi maganar cikeda zolaya,hararanshi tayi tana"Anty Zaliha tayi maka badainiba"......
Yatsina fuska yayi sannan yace wannan ashe zan mutu in ita zatamin massage Sumayya"Yar *Gidan sarauta* cefa gaba da baya,kinga kuwa tako ina tadebo"......
To ai nima Yar sarautarce cewar Sumayya tana yatsina fuska,dariya yayi yana kinga expression din fuskarki kuwa kaman wanda na yabi  kishiyarki,shaaa nasan ke yar sarauta ce amma ai baki tashi cikinsu ba dukda ma cikin gata kika tashi sede zakiyi abunda ita bazatayiba".......
Nidai katashimin agado bacci nikeji,zare idanu yayi tareda tashi yazauna tsakiyar gadon seyanzu ma talura da takalmi yadale mata gado.......
"Bacci fa kikace Sis,aibaki isaba yau auren yayankine tukunnan ma inasauran suke yakarashe maganar yana tashi daga kan gadon sannan yakama hannunta yana muje waje inmuku assembly ma........
Ah parlour yasaki hannunta yana kiransu Afiya da Amira ba ajima ba segasu sunfito daga kitchen tareda Mom,sakan baki Sulaiman yayi ganin kayan dake jikinsu"lallai yaran nan aurena guda kitchen ma kuka shige abunku ko,kallon Mom yayi sannan yace Mom kigansu kayan bacci ne fa ajikinsu".......
Dariya Mom tayi sannan tace koyan girkin Indonesia sukeyi,wai sena koya musu tunda zun nikebinsu suje suyi wanka sunki......

Story continues below

Amira ne takaraso parlourn tana"Yaya Sulaiman Allah bamuda kayane,kasa karashe maganar tayi ganin Almustapha datayi zaune sanye cikin sabuwar shadda fara kal wanda bakaramin kyau yayi mashiba gashi gashinnan yasha gyara ga wata hadaddiyar hula dayasaka,tsalle tayi tana Afiya zokiga Yaya Almustapha don Allah,dagudu Sumayya da Afiya suka karaso suna gamu,woow shine abunda Sumayya tace"Allah Yaya me shiru shiru dukda bakason min magana yaukam semunyi hoto",dariya sukayi dukansu harda Mom dake tsaye ah can baya........
Zama Sumayya tayi gefenshi sannan tace Yaya Sulaiman daukemu,babu musu ya daukesu,another one please tayi maganar tana canza style kafin tadubi Almustapha din Yaya don Allah kayi smiling.......
Murmushi yayi don yarinyar dariya take bashi, she's so open minded seda akamusu yakai biyar yaga batada niyar tsayawa  yaja karan hancinta ahankali fuskarshi daukeda annuri"it's okay naughty girl",sannan yatashi yabarta gurin zaune binshi tayi da kallo tana"Ya Allah, Afiya yayankun nan baya kasheniba, he's so lovely ah swear".......
Hararanta Sulaiman yayi"zoki tura hotunan ko in goge yanzunnan", dagudu tayi gurinshi tana bashi hakuri riko ta yayi sannan yace"I need a selfie too",sannan yayi whispering ah kunnenta"with you"......
Daukarsu yayi sannan su Afiya ma akayi dasu hotuna sunyi kyau yanata mita waishi yazaiyi yadaura hotunan shi da kannenshi with sleeping dress Kuma ranar aurenshi for that matter..........
Alkawari yayi musu kan zai bada dinkinsu ma wani tailor din friend dinshi inyasamu fita and yasan zaiyi musu express kona gobe susamu kafin agama sauran don already yasiyo kayan dajimawa ya ajiye don specifically na aurensa yasaya musu sebezo yasamu yabada dinki ba kuma ma babu na Sumayya ciki so zai squeezing ayi musu duka susamu nasawa ah events din daza ayi agaba............
Seda yakarasa gun Mom suka gaisa sosai tanata tsokanan shi ango ango sannan yakarasa dakin Ummi don duba jikinta,samun Asma'u yayi kwance jikin gadon Ummin tayi shiru alamun tunani takeyi, murmushi yayi sannan yace Asma'u kekam tunda kikazo kina kunshe ah daki abunki,yar dariya tayi tareda tashi daga kwancen datake tana Ina wuni Yaya Sulaiman......
Amsawa yayi sannan yace"memakon kije parlour ko dakinsu Amira kuyi hira abunku",nafi jin dadin hakan nedai.........
Toshikenan kinga banji Daddy yana maganar zamuje gidan kunba yau ma kodai se gobe ne.....
Cikeda damuwa tace he's busy ko?....
Gyada mata kai yayi ahankali sannan yace,kozaki kira kifada ma Ummi kilan tayi understanding.....
Jijjiga Kai tayi cikin sauri alamun a'a don batasan ta inama zata farama Ummi bayaniba don haka tace kozaka maidani gidansu Aisha din kawai inyaso inkum tashi sekubi tacan kudaukeni........
Dan shiru yayi nawasu dakiku sannan yace"to amma kibari se anjima don yanzu inada gurin zuwa koma inshi Dad din baya komai inna tambayeshi basai mujeba kawai".......
Godiya tayi mashi sannan yaduba jikin Ummi yafita ah dakin don zuwa gurin Magajiya........
Ah daki yasameta ya gaggaisa da baki se Allah sanya alkhairi akeyi mishi yayinda wasu ke guda,harkasa ya tsuguna ya gaida Magajiya dukda kuwa yanda takejin haushin shi haka ta daure zuciyarta bata nunaba suka gaisa lafiya lau........
Yasha mamaki sosai dabata bata rai koyimai fada ba sekuma dayayi la'akari da gurin akwai dumbin jama'a sannan no matter what yasan yau is a special day for her.......

Tunda Sulaiman yafita yakoma gun abokanshi dakuma wasu hidindimu  yama manta da batun maida Asma'u don gabadaya ya shafa'a......

Aranar ana gama daurin aure mutanen Borno suka dauko Amarya suka taho da'ita aikuwa sunyi isowar dare sosai don kusan dayan dare suka iso cikin masarautar dukda kuwa irin daren daya tsala hakan behana anyimisu tarba mai kyau ba don already angyara bangaren Sulaiman din dayake makeke ne don yanzu zezama nasu shida ita,sosai suka yaba da karamci irinna masarautar Mai Martaba Abdulrahman..... 
Hakanan washegari akafara events da aka shirya komai yatafi cikin tsari hakan su Amira ma baa barsu abayaba sunyi sunyi suja Asma'u amma taki zuwa don ko ajiyan dayanma seda tafita da Ummi wanda ayanzu tafi jin dadin zama da'ita fiyeda kowama dukda kuwa bawai magana sukeba........
Itama she's lonely,gani take bataga ta murna da farin cikiba tafison zama guri shiruma gashi damuwarta yanzu shine har yau Sulaiman bedubeta ba hakanan Dad don sanda suke shigowa ma tayi bacci damuwarta daya kada hankalinsu Ummi yatashi.....

Story continues below

Ranar litinin angama biki yayinda baki sunfara watsewa sannan duk wasu programs daza ayi angama shi don Gimbiya Hamida ma antafi da ita gidan mijinta.........

****

Tun ranar asabar Anty suwaiba kafin tawuce office ma taje gidansu Asma'u din bayan sun gaisa da Ummin take tambayarta ko Asma'u tazo gida...........
Cikeda mamaki Ummi tace tazo gida kuma,basuna tareda Aisha gurinkiba?......
Cikeda damuwa Anty Suwaiba tashiga bata labarin abunda yafaru,Ummi tace ikram ce tajefamin wayar aruwa ankaita gurin gyara yabaci shiyasa baki sameni ba amma Asma'u kam batazo gida ba kwata kwata wallahi.......
Shiru Anty suwaiba tayi don tana blaming kanta for everything don ah iya saninta ita ga abunda Aisha tace mata,to in Asma'u batazo gidaba inataje kiran Aisha tayi take sannan tace tazo tasameta gidan su Asma'u din, Aisha tunjin muryar Anty suwaiba tasan babu lafiya don haka tazari hijabinta abakin kofa sega Mallam Hudu yana shirin bude gidansu Amira don Sulaiman yaje hargidansa yamasa bayanin komai sannan shima yace zezo har gida yagasu Almustapha din yamusu murna inya samu sarari don shigan shi masarauta ba abu maisauki bane tun sanda Magajiya ta kori su Almustapha din.....
Gaishe shi tayi dayake tasan fuskarshi sannan ta tambayeshi number Sulaiman nankuwa yabata take tashiga Kira amma yayita ringing ba adauka ba ahaka harta isa gidansu Asma'u agaban Ummi tatsuguna tana gaisuwa yayinda Anty suwaiba tarufe ta da fada tana"kimai maita abunda kika fada min jiya bayan na dawo?".......
Jiki ah sanyaye tashiga bayani yayinda daga karshe tace ga number Yaya Sulaiman din nakarba yanzu barina sake kira,sake kira tayi still ba a daukaba cikeda damuwa Ummi tace"ikon Allah, Allah yasadai lafiya",Amin cewar Aisha din kafin tace Allah Ummi kilan sunzo bakunan nan ne I'm sure nansukayo.....
buge bakinta Anty suwaiba tayi"dallah rufemin baki,kuna abu kaman hankalinku baya jikinku,aidakin kirani da duk hakabai faruba".......
Ummi ne tace kiyi hakuri Suwaiba kuskure anriga anyishi fatanmu inda Asma'u take yanzu shine kawai..........
Anty suwaiba sunfi awa ah gidan kafin daga karshe Ummin tace kada tadamu tatafi aikinta zasu cigaba da kiran number din itada Aisha haka suka rakota har bakin gate nanne Aisha tayi tunanin tambayar me gadi ko wasu sunzo neman Daddy......
Cikin sauri yace"tabbas sunzo harda yarinyar wurinki yayi maganar yana nuna Ummi,sede nace musu mai gidan bayanan amma zai dawo yau kuma sunce xasu dawo in Sha Allahu".....
Murmushi Ummi tayi taredayin hamdala atleast tanada hope yanzu,may be zuwa anjima suzosu nan tacema Aisha dinma takoma gida babu komai bayan tafiyansu bejimaba sega Daddy ma yadawo,zuwa sukayi tayi mishi sannu da zuwa inda yake cemata yajima da shigowa gari yatsaya daurin aurene ah masarauta da aka gayyace shi,shiyasa koda dare yayi taga basuzoba setayi musu uzuri da kilan shagalin bikin ne yahanasu zuwa.....
Hakanan har yau Monday shiru sedefa yaudin hankalinta yadan fara tashi gashi ita bata tunkari Daddy da maganar ba shima kuma beyimata ba dukda daman tasan bayi mata maganar zeyiba kozata yi yaya tunda shiya bukaci ko ambaton Asma'u din bayason ayi mashi ah gidanshi.......
*****...
Dayanma likis tana zaune cikin lambu karkashin bishiyar mangoro data saba zama kullum sede yaudin bata fito da Ummi ba sakamakon baccin databarta tanayi ah dakin,lumshe idanunta tayi ahankali yayinda hawaye suka fara zuba ah idanunta tagaji she want to go back home,tana missing gidansu dama kowa ah gida, tadaukar ma kanta alkawari yaukam in Dad ko Sulaiman basuyi mata maganar tafiyaba komawa gidansu Aisha zatayi gobe sabida koba komai zamanta acan yafi ma ana akan zamanta anan gida daba saninsu tayiba............
Sa hannu tayi tana goge kwallarta yayinda takebin bishiyoyin tangerine da kallo duk maitarta dasu yaukam batada appetite din shansu......
Tananan zaune taji kaman ana taku kadan kadan sekuma can taji ankusa isowa inda take, tsoro ne yakamata donkuwa tunda take zuwa lambun bata taba sa'an haduwa dawaniba shiyasa take zuwa kullum freely without any fair,kallon gefe da gefenta tayi yayinda take tsoron kada masu maganar su kamata,ahankali ta tashi dayake bishiyar mangoron ba irin me tsayin da mutum zesha wahalar hawa bane setayi saurin dalewa bishiyaan ahankali sannan tayi likimo jikin wata reshe jitayi mutane biyun sunsake matsowa kusada bishiyar don daga inda takema tana iya hangosu.......
Jitayi daya Matar dake tsaye gaban yar budurwa taciro wani abu ah leda tace inji Magajiya kisaka wannan acikin shayin  Almustapha inzaisha da dare kafin ya kwanta ina kince yakansha shayi?...
Gyada kai yarinyar tayi,Asma'u jitayi gabanta yashiga dukan uku uku sede fatanta taga fuskar yarinya amma bata iya gani daga inda take ......
Karban ledan yar budurwar tayi sannan tace zanyi yanda akace inyi sede yana iyakin sha don yanada ra'ayi wallahi.......
Tsaki Matar tayi sannan tace kekika sani kisan yanda zakiyi yasha in bahakaba keda Uwargijiyata nidai sakone na kawo miki,tana karashe fadin haka tajuya tatafi.........
Nan budurwarma tabar gurin, innalillahi wainna ilaihir rajiun shine abunda Asma'u ke furtawa "wannan din wani irin mugunta ne,mekuma akeshirin yima Almustapha lallai wanda akabama wannan abun tabbas acikin sashin da take yake,seda ta tabbatar suntafi sannan tasauko ah bishiyar tayi cikin gida tana kissima yanda zatayi handling abun"........

Story continues below

***
Zaliha yarinya ce kyakyawa son kowa kin wanda yarasa don bazaka ganta kace mata mummuna ba duk hassadarka,yau yan gidansu suka komai yayinda dayanma tabi duk wani bangare na gidan daya zamanto na surukanta tagaidasu cikeda ladabi,kowa seyabawa yake da halinta dakuma biyayyarta don sunji dadin mutuntasu datayi barinma Magajiya baki harnan tayi inlaw me hankali.......
Sanda taje bangarensu Mom ah parlour tazauna aka kawo mata kayan motsa baki sannan tagaisa da Mom din, Afiya ne gulma nacinta tayi daki tana kiransu Sumayya waisuzo suga Matar Sulaiman......
Oh my god kinga kyawunta ga body Afiya takarashe maganar tana yar dariya, Amira ne tace haba kinsanni bansamu naganta ba duk event din da akayi sabida mutane......
Aikuwa xoki ganta tasowa sukayi itada Sumayya suka leko ahankali suna gulma,komawa Amira tayi tareda Sumayyan...
shiyasa Yaya yaketa rawar  jiki,gaskiyakam babu laifi masha Allah......
Sumayya ne tace"Ina kyau anan nikam batamin kyau ba",takarashe maganar tana yatsine fuska....
Kallonta duka sukayi suna mamaki,yayinda takoma ta kwanta Afiya ne tace wallahi ba laifi Sumayya tanada kyau kam babu hassada...
Ku dama inakukasan kyau daga ganima bakar munafuka za ayi,dariya su Afiya sukayi ah tare suna nikam Sumayya kodai son Yaya kikeyine, fadamana man please....
Cumbune baki tayi"Allah yasauwake wallahi,mezanyi da wancan abun",dariya suka dinga mata suna tsokanarta daga karshe tatashi ta tafi gurin Asma'u tana"kukam zaku iyasamin hawan jini wallahi"....

***
Talatu bayan takoma gurin Magajiya tace"Uwargijiyata nabata takarba kuma"......
Murmushin mugunta Magajiya tayi sannan tace, Almustapha taka takare, you'll never be successful indai ina numfashi ah doron kasan nan.......
Duban Talatu takuma yi sannan tace,banason asamu matsala kitabbatar yarinyarnan tasaka abunnan acikin shayin kinajina?....
gyada kai Talatu tayi sannan tayi godiya tafice......

Wuraren karfe takwas nadare ta daidaici dawowan Mai Martaba daga masallaci kafin yakoma fada tana wani tunaninta, ahankali kuma tatashi tafita bayi nabinta donyimata rakiya harzuwa bangaren Mai Martaba yayinda su suka tsaya daga waje......

Yana tsaye yana shirin cire riganshi na sama tayi saurin karasowa tashiga ciremishi cikeda kisisina,yagane ta don yaga zoben hannunta don haka yadan tureta,cikin sauri takuma sa hannu sannan tafada jikinshi tareda rungumeshi ta baya"kayi hakuri don Allah Mai gidana kadaina fushi dani"....
Sa hannu yayi yakuma tabuketa daga jikinshi sannan yajuyo yana kallonta"I'm not in the mood to talk to you gwandama kikwashi kafafuwanki kitafi".....
Kukan munafurci tafara sannan takwantar dakanta ah kirjinshi"don Allah fa nace,nasan nayi kuskure kuma gashi nayi nadama kayafemin don Allah bazan iya jure fushin kaba"..
Batareda yadamuba yace seyanzu kikasan bakiyi daidai ba?....
Goge kwallarta tayi tana kisisina"Allah tunranar nagane laifina sede naga you're always busy shiyasa banzo nasame kaba nace barina bari agama bikin nan dai"..
Dagata yakuma yi ajikinshi yana"kinbaridai seda kika sallami bakin ki badai niba so stop acting"....
Marairaicewa tayi"Allah dagaske nike kayi hakuri bazan kumaba",jinta dameshine yace nifa yawuce daman bam rike kida komaiba Magajiya...
sa hannu tayi takamo fuskarshi tana kallon cikin idanunshi"Amma ai gashi idanunta sunnuna bakayi farin ciki da abunda nayiba"......
Yes banyi farin cikiba because nayi tunanin keme sona ne kuma meson abunda nikeso koban fada mikiba yakamata kitayani murna ai.......
Hawayene suka shiga shatata ah fuskarta tana kallonshi tareda sake bashi hakuri wai bazata sakeba,rantane yabaci ranar and kasan in raina yabaci daman haka nikeyi but I'll correct my mistakes zaka gani and you'll be pleased with me...
Murmushi yayi sannan yashiga goge mata kwallarta"it's okay  Magajiya yawuce",cikeda jin dadin tasamo kanshi ta rungumeshi tanayi mashi godiya.....
****
Tunda tashigo gida take leka kitchen minti minti kozata ga sanda za a hada tea din amma shiru don ta lura bayin ma
 wasu harkokin suke baki dayansu,abunda bata saniba shine akan kawo musu abinci daga kitchen din masarauta ne sekuma sometimes insu sunaso se Mom tadafa dakanta kokuma tayi directing bayin suyi mata tana monitoring dinsu sabida wani sa'in abincin da ake kawowa baswa ci...
Yanzu zaryanta zuwa kitchen yafi saugoma, Sumayya ne tace yau lafiyarki Asma'u kinata fita kina dawowa,do you need anything?..

Jijjiga Mata kai Asma'u tayi sannan tace babu kekam,don Allah ta ina dakin Yaya Almustapha yake?....
Mischievous kallo Sumayya tayi mata tana"ehhhhhn dama abunda kikeson tambaya kenan shine tundazu kike wahalar da kanki?".....
Allah bahaka bane Sumayya, I'm just asking,dariya Sumayya tayi sannan tace yana gefen na Dad by the right.......
Godiya tayi mata sannan tasamu guri tazauna tana wasa da hannunta itakadai tana contemplating tajene ko kada taje......
Yana kwance ah dakin yadan jingina da pillown shi yana dan dube dube cikin littafin dake rike ah hannunshi dukda kuwa he's ready for the exams bayason wani abunda zaiyi going wrong this time around gashi 8:00am ne exams din........
Jiyayi anyi knocking ah jikin kofar shi seda meshi takuma knocking wajen sau uku sannan yace"come in",shima dakyar ......
Afiya ne dataketa kumbure kumbure tashigo hannunta rikeda tray dauke da black tea akai ta ajiye mai kan yar karamar table tana gashi Yaya Almustapha.....
Ko kallon inda take beyiba kuma daman batayi expecting wani serious answer daga gareshiba,seda tafita tashiga mita ita kadai"yanzu shi yanaji inata knocking daman idanunshi biyu amma yaki cewa inshigo,haushinta daya yace bayason bayi suna shigar mai daki so koma miye za akawomai abasu su sukawo yanzu they've to be enduring this tunda agidansu nadakam baya rufe kofar dakin ma don koya rufe zafi zai addabeshi tunda babu arzikin fan nanko ga AC dole yamusu kinibibi,tana cikin mitarne suka gwaru da Asma'u...

Post a Comment for "GIDAN SARAUTA CHAPTER 4"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...