Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

GIDAN SARAUTA CHAPTER 2

GIDAN SARAUTA CHAPTER 2

- - Post a Comment
GIDAN SARAUTA

CHAPTER 2


Anacikin hakane sega securities sunfara zuwa aikuwa tuni daliban suka watse domin ah kaidar makarantar in dai akasame ku gurin rikici kokuma Kuna rabiyar fada muddin securities sukazo to dukan ku za'a diba ayi security office daku shiyasa kan kaceme babu daliban, kowa ya cigaba da harkokin gabansa...........
Se Asma'u dake zaune kusadashi tana kuka, security din daya karaso gabanta ne yace ke!meya sameshi?.....
Cikin kuka tace wasu ne suka mishi duka bansan meya musu ba.daya security dinne yakaraso yanacewa subhanallah kaman ko motsi baya yi taba Almustaphan yayi ya jijjiga shi sede baya motsi kwata kwata dasauri yaciro wayarshi yashiga Kiran ambulance din makaranta ba'a jima ba se gashi sunzo nan aka dibe shi akayi clinic dashi.......
Zahra seda ta tabbatar securities din sun tafi sannan tazo gurin Asma'un tarungume ta tana Asma'u agarin tausayin wani zaki jaza ma kanki!....
Goge kwallarta Asma'u tayi sannan tadubi Zahran don Allah kinsan clinic din school dinnan awani direction yake?.......
Zare idanu Zahra din tayi sannan tace mezakije kiyi?....
I've to make sure he's safe from those guys,I want to make sure yatashi yadawo normal and then I'll ask about his family in order to let them know his condition,riko hannun Zahra Asma'un tayi sannan tace baki ga abunda sukayi mishi bane ba,meya musu Zahra,how can someone be so heartless like this.nidai don Allah kirakani,ganin takiyin shirun ne yasa Zahran sa hannu ah bakinta tarufe tareda runtse idanunta "it's okay Asma'u he'll be fine please!".....

Dan shiru Asma'u din tayi sannan tace to muje,kamo hannunta Zahra din tayi sannan tajata zuwa wurin wani kujera suka zauna kamin tariko hannunta cikin nata"Asma'u kisaurareni dakyau please,shiwannan mutumin dakikeson taimako kinsanshi ne?"....
Jijjiga ma Zahra Kai Asma'un tayi alamun a'a,to bari kiji Asma'u he's a bad person duk abunda kika ga yafaru dashi laifinshine,nima bansanshiba tunda I'm new to the school kaman ke sede dazu dakikazo gurin shi naji yanmata na magananshi harcewa suke sun tausaya miki don rayuwarki na cikin hadari indai har taimakonshi kikeson yi,his name is Almustapha Asma'u.the illigitimate son of the king nasan dai inbaki sanshi by face ba tabbas kintaba jin labarinshi agarin nan koda kuwa kadan ne sabida haka nake shawartaki da daga yanzu kicire yaron nan cikin harkokin ki,agreed you helped him for the sake of humanity Allah yabaki lada amma yanzukam seki barshi da securities su sunsan yanda zasuyi dashi,sannnan inaganin zasu fiki sanin access to his family right?tunda ma shidin bawai *Boyayyen Mutum*(littafin maman abdushakur) bane agari,nan Zahra tashiga goge mata kwallarta tana kitashi mutafi lectures yanzu it's almost time kinji......

Kallonta Asma'un tayi da runannun idanunta don duk abunda take fada jinta kawai takeyi,kije kawai I'm not myself zanje gida segobe zanshigo ....
Bazaki jira Yayarta ki ba?......
Dan kama kanta tayi sabida yanda yake mata wani mugun ciwo sannan tace I'll just go zanfada mata awaya,nagode Zahra.......

Murmushi Zahra din tayi sannan tace Allah yabaki lafiya Asma'u, I'll call you later namiki saving number na.....
Murmushi Asma'un tamayar mata yayinda Zahran ta tashi tatafi tana mata waving seda ta tabbatar Zahran tabace mata dagani sannan ta tashi tafara tafiya wani student tahaduda ahanya nan ta tambayeshi inda school clinic yake nan yayi mata kwatance seda tabi ta cafeteria tayi take away din abinci sannan tawuce clinic din,itadai aganinta babu ruwanta dakoma wayeshi,she don't care about his identity she just want to help him no matter what sabida just because he's a bad person bekamata mutane suna treating nashi hakaba,to hakan dasukamai din shizaisa ya shiryu kokuma ah inane addini yayi koyi da hakan,sanda taisa clinic din gaisar da nurses din tayi sannan tace tazo duba Brother dinta ne cewa sukayi takarasa ciki nan tashiga babu kowa aciki se shikadai don yau babu patients ah kwance, ahankali tadinga takawa harta isa gaban gadon nashi yana kwance peacefully se bacci yakeyi yayinda goshinshi ke manne da bandage da alama anyi mishi treatment ne sekuma drip da akasaka mai, samun kujera tayi agaban gadon seta samu kanta dazama seyanzu take kare ma fuskarshi kallo setaga "he looks familiar, sede tarasa ah ina ta taba ganin fuskar,nan take Kuma yuuuiuu seyafado mata arai",dasauri taja baya tana hasbunallahu wani'imal wakil,zuciyarta tashiga bugu sekuma wata zuciyar tace mata ta Ina zaizama aljani tunda har mutane na dukansa sekuma tasake dawowa tazauna tareda dan taba jikinshi because she wants to be sure,karema features din fuskarshi kallo tashigayi yayinda zuciyarta tashiga raya mata he's very handsome,dogon fuska gareshi yayinda yakeda manyan idanu gwanin ban sha'awa pointed hancinshi dake tsaye kaman shiyakera ma kanshi lips din shi kuwa very cute and small gashi pink wanda mutum daga nesa zeyi tunanin pink lip stick yasaka,eye lashes dinshima kanshi abun kallo ne ahankali tafurta anya wannan dan Nigeria ne kuwa dubada yanayin gashin kanshi dama kuma yanayi halittunsa dukda kuwa bashida wani haske sosai gakuma karin wahala data kuma dushashe shi, tana cikin wannan tunanin ne nurse tashigo tana cemata bakida lecture ne?.....
Murmushi tasaki sannan tace nagama nayau......

Story continues below

Toshikenan amma dakin nemo abokinshi yazo yazauna dashi don bamwa barin Mata ah side din maza yanzunma don dubashi kikace zakiyi shiyasa muka barki da oganmu nanan ma bazai bari kijima hakaba...

Dan shiru tayi sannan tace toshikenan ga abincinan inya tashi yaci kafin yasha magani kafin abokin nashi yazo.....
Murmushi nurse din tayi sannan tace in Sha Allah, I'll make sure yacin.....
Haka Asma'u tatashi tafita jiki ah sanyaye,wayetasani acikin fadin ABU dazai zauna dashi babu fatan ta daya Allah yabashi lafiya cikin gaggawa....
bata tsayabin takan Asiya ba ta tari napep tawuce gida abunta.....

*****
Misalin karfe takwas na dare Talatun tashiga Shashin Magajiya tazube kasa tana mika gaisuwa, Uwargijiyata Audu feleken yana can baya yana jiran sallamar shi....
'dan tsaki Magajiyan tayi sannan tace matsalata da talaka kenan shegen nacin tsiya yanzu bazai iya hakuri harsai gobe ba.....
Wai yana bukatar kudin ne cewar Talatun kanta ah kasa, Magajiyan dakanta ta tashi tabude wani sif da aka garke shi da padlock taciro kudi tamika mata cikeda wulakanci tamika mata"seki bashi Kuma banason insake ganin shi agidan nan"......
Karba Talatun tayi tana godiya nan tafice.....

*****
Ahankali yadinga ji kaman baya jin dadin jikinshi,bude idanunsa yayi yayinda ya waresu yana karema 'dakin kallo ahankali abubuwan dasuka faru yadinga dawo masa tashi yayi cikin sauri wani sarawa da Kansa yayi seda yakoma yakwanta amma dukda haka bai daddaraba yakuma tashi yana kallon drip din da akasaka mishi pincikewa yayi sannnan yasaka takalminshi yafice ah ward din,tunda yafito nurse din ke aikin kiranshi kan yadawo amma ko kallo bai isheshiba dukda kuwa bawai yanajin dadin jikinshi bane ba amma ahaka yacigaba da daurewa yana tafiya har yabar cikin school din alokacin har anfara kiraye kirayen sallar isha,jiyayi anyi parking agefenshi amma hakan besa yadaina tafiyar dayakeyiba dasauri Sulaiman yafito daga cikin motar yana sanye da kananan kaya rikoshi yayi yana Yaya Almustapha inazaka je haka,you should have wait ina hanya fa danaje sallar maghrib ne natsaya sayamana abinci.......
Fizge hannunshi Almustaphan yashigayi yayinda Sulaiman din yaki saki sema janshi dayayi yashigardashi mota yafara driving babu yanda Almustaphan ya iya don bashi da karfin yin ja inja da 'dan uwan nasa.....
Sulaiman din bai tsaya ko inaba se cikin masarautar agaban gidan su Almustapha din. kamashi yayi yakaishi har cikin gidan zuwa dakinshi Amira dake waje tana tuka tuwo taga shigowarsu dasauri tatashi
tana Yaya Sulaiman lafiya meyake faruwa haka?....
Sa hannu Sulaiman din yayi kan lips dinsa yanayimata nuni da tayi magana ahankali,'dan sassauta murya tayi sannan tabi bayansu har zuwa dakin Almustaphan "Yaya Sulaiman kafadamin mana miye yasamu Yaya Almustapha?".....
Lil Amira it's nothing serious kidaina daga hankalinki....
Cikeda damuwa tace tayaya zandaina daga hankalina bayan kanaganin condition din dayakeciki takarashe maganar hawaye nashirin zuba daga idanunta bayan ya kwantarda Almustaphan yajuyo gareta.....
Amirah bakiyi trusting dina bane,cikin dan kuka tace I do Yaya Sulaiman but look at his forehead and he's looking weak takarashe maganar tana zama kusa da Almustaphan tareda riko hannayenshi....
Yaya Almustapha inake maka ciwo?.....
Jijjiga mata kai yayi alamun babu,tattaba jikinshi tayi taji temperature din is normal sannan hankalinta yadan kwanta,duban Sulaiman din takuma yi tayaya yaji ciwon nan Yaya?....
Murmushi yasaki ganin yanda tabi tadamu"minor accident ne yasamu little Amira nima kirana akayi aka fadamin yanzu kikawomana abinci muci tukunnan and please karki bari Ummi tasani kinsan hankalinta na iya tashi".....
To bazan bari tasani ba amma sede tuwon begamu ba, barima naje inadubawa daya yi zankawo muku....
Yauwa little Sis asaka man shanu please,dariya kawai tadanyi sannan tafice tabarsu su biyun ah daki......

Samun guri Sulaiman din yayi yazauna sannan yadubi Dan uwan nashi, I'm sorry Yaya Almustapha nasan you don't like me sede inason kasan abu daya I can't just look away,I saw it earlier on social media shine naje school clinic dinku don nasan definately can za a kaika,shiru yadanyi na dan dakiku kafin yacigaba......
Bansan miyasa kazama in this state ba amma I'll advise you please kana kiyayewa darana I don't want you to be hurt and please we should get this over shirun ka nadamuna,I know I'm not worthy of being a friend with whom you can share your problems with sabida mahaifiyata sede inason kasani cewa son da nake maka na tsakani da Allah ne please kadaina gaba dani though nasan bazan iya taimaka maka ba atleast zan na debe maka kewa ko,inkuma kana ganin hakan beyi makaba still I can have my way,yakarashe maganar ahankali tareda tashi yajuya zai fita har yakai bakin kofa seyaji muryar Almustaphan nakiranshi *Sulaiman*!,wani irin dadi ne yakamashi dasauri yajuyo yana kallon dan uwan nashi ware mishi hannu Almustaphan yayi alamun yazo gareshi dagudu yakarasa tareda rungumeshi........

Story continues below

Tapping bayanshi Almustaphan yashigayi kamin dakyar yace "I'm sorry for always being rude to you"......
Shhhhh, Yaya banga laifinka ba I'm sorry too.....yakarashe maganar tareda dagowa yana kallon Almustaphan fuska shabeshabe da hawaye sa hannu Almustaphan yayi yana goge masa kwallar "stop crying"..suna cikin hakane sega Amira tashigo hannunta rikeda trayn abinci nan ta dire musu....
Wai Ina little Angel ne Amira?...
Kasanta ai da shegen bacci harta kwanta tabawa Sulaiman din ansa....
Ayya, Ummi tasha magani,yakuma Kai mata wani tambayar..
Eh tasha Itama tayi bacci,tokema zauna muci abincin ko cewar Sulaiman din...
Zama tayi tana Aiko baka fadaba Yaya Sulaiman zan zauna inci da yan uwana......dariya sukayi atare don har Almustapha seda yadan murmusa dukda kuwa haryanzu abunda yafaru dasafe yana ranshi sede kaman su Amira basuda labari haka Sulaiman dinma Kuma daman hakan yafiso don bayason tayar musu da hankali...
Nan suka shiga cin abincin yayinda Sulaiman da Amira kedan taba hira shiko Almustapha yayi shiru se sauraronsu dayakeyi kawai,dukda kuwa Sulaiman sauro da zafi yadameshi ah dalilin rashin wuta amma ko alama bai nuna ba,se wurin goma nadare yabar gidan yatafi nashi bangaren dukda kuwa yanason zuwa gun Magajiya sede tabbas yasan akwai rigima inyaje don baza arasa magulmatan dasuka Kai mata labarin yazo da Almustapha ba....
*****
Tunda taje gida tashige daki ta kulle kanta harsaida Ummi tazo tabuga mata kofar dakin,zuwa tayi tabude karemata kallo Ummin tashigayi sannan tace lafiya kika garkame kanki acikin daki?....

Langabar dakai tayi sannan tace babu komai Ummi I was just tired shiyasa,to kinci abinci ne and how was the school inafatan komai yatafi lafiya dai ko?....
Riko hannun Ummin tayi ganin tadamu tace"Allah Ummi komai lafiya and abinci yanzu nike shirin fitowa inci".....
To kifito kici nayi azan wani abun ne yafaru don Sadiq yacemin Asiya tazo tana mitar kinyi tahowarki gida taje faculty dinku tayita nemanki bakyanan.....
Ummi batagama lecture ba shiyasa banjirata ba,dubanta Ummin tayi sannan tace ko bata gamaba kina jiranta tunda mahaifinku ne ya umarci hakan and besides koda wani abu yataso takama dole kidawo gidan aise ki kirata kiyimata bayani bawai kibari taje tana wahalar nemankiba....
Duban Ummi tayi cikeda damuwa don itakanta tasan bata kyauta ba sannan tace zangyara Ummi in Allah ya yarda...

Yadai fikam cewar Ummin,ga abinci nan kizauna kici nina tafi bangaren Babanku kafin ki kwanta kisamin yara suyi fitsari kada sumin ah gado....

To Ummi In Sha Allah,seda safe....
Allah yakaimu inji Ummin sannan tafice tabarta zaune kan dinning zata fara cin abinci........

Sanda Ummi tashigo taga abinci akan dinning tayi mamaki sosai dakin Asma'un tawuce dede lokacin tagama shiri kenan zata yafa gyalenta.....

Yauma kinada 8:00am dinne?...
Juyowa tayi tareda gaishe da Ummin,sannan tace aa Ummi se karfe tara....
Oh yayi kyau to abincin miyene ah basket?....
Uhm uhm setafara kame kame don tama rasa mezata ce kafin daga karshe tasamu idea, yauwa Ummi kawata ce ah hostel take zama Kuma bata girki sayan abinci take ah school shine tace tanason cin paten dankali shine namata alkawari...

Kallonta Ummin tayi tanason tagano wani abu,sekuma tace to yayi kyau amma yaushema kikafara zuwa makarantar da har kinyi wata kawaa?.

Eh Ummi tun lokacin registration muka hadu, juyawa Ummin tayi tabar dakin tana kada dai kibar mini kwanuka ah makaranta...
In Sha Allah bazan bari ba Ummi..
Bayan Ummin tafita ne talumshe idanunata tana nanata astaghfirullah don abunda batayi ma Ummi shine karya,sede yau tafarayinshi and she's regretting it sede babu yanda zatayi bazata iya fitowa tacemata wani namiji zata kaimawa ba,karasa shirinta tayi sannan tafito taci nata abincin ah dinning table kafin tafice don tun dazu Asiya ke yo mata aike itafa zata tafi....
sanda tashiga motar da basket tsaki Asiyan tayi tana don gulma da iyayi har anfara rabon abincin gidan mu ah kawaye..

Dariya Asma'un tayi sannan tace Ina kwana?..
Lafiya Asiyan ta ansa ai tsaye cikeda manyance...
Sanda suka isa school tace Aseey kikaini clinic please inason inbama marar lafiya abincin nan......
In disbelief Asiyan tace marar lafiya Kuma,waye ba lafiya Asma'u?..
Kai tsaye Asma'un tace "a friend"....
Tabune baki Asiyan tayi sannan tace gaskiya to kiyi sauri because banason inyi latti ah dizgani gaban yara,to naji cewar Asma'un haka suka karasa gaban clinic din tasauka hannunta rikeda basket din Asiyan sebinta da kallo take tana mamakin yaushe har Asma'u tayi kawa daga zuwanta jiya.sanda Asma'u tashiga clinic din thesame nurse najiya tasamu murmushi tasakan mata tareda gaisheta ...

Ansawa nurse din tayi sama sama tana mata kallon tara saura kwata don jiya bayan fitan Almustapha tana kiranshi yaki amsawa dayan nurse din kebata labarin Almustaphan shiyasa yanzu dataga Asma'un taki sakin fuskarta....

Jiki ah sanyaye Asma'u tace don Allah patient din jiyafa yana cikine?..
Bayanan nurse din tabata amsa Kai tsaye....
Gyara tsayuwa Asma'un tayi tana"oh ansallameshi kenan?"...
Harara nurse din ta dakamata,bakince Dan uwanki bane inaganin zaki fini sanin halin dayake ciki ah yanzu sabida haka kifita kibani guri kina destracting dina Ina aiki"...
Take idanun Asma'u yaciko da kwalla don ta tsani wulakanci ah rayuwarta, I'm sorry tafurta ahankali sannan tafice daga clinic din sanda tashiga motar se alokacin hawayen yazubo, Asiya namata magana amma taki kulata don haka se Itama tayi shiru takaita bakin faculty dinsu ta ajiyeta...
Haka tabar mata abincin acikin mota dukda Asiyan tadamu da sanin halin da Yar uwartata take ciki kota samu na gulma sede batasamu fuskaba......

****
Tunkan yagama shiryawa Magajiya ta aiko tana neman shi dan tsaki yayi don yasani daman yau se an tsigale shi seda yayi breakfast dinshi ah nutse sannan yatafi bangarenta.....
Gaisheta yakeyi amma ko kallon inda yake batayiba,menayi kuma Mama...

Wani harara ta doka mishi cikeda bacin rai sannan tace"harma tambayana kakeyi?"....
Kai wani irin bunsurune dabazaka iya hakura da mata ba,so kake kajazamin abun magana acikin Masarautarnan,dan murmushi yasaki tareda dan sosa kanshi sorry Mama shiyasa nace miki bazan dawoba sabida nasan bazan iya hakura dasuba,tsaki tayi sannan tace auren kuma fa,mezai hana kayi aure Sulaiman?....

Kamo hannunta yayi sannan yace bazan iyaba Mama, I'm too young for that don Allah kibarma maganar nan,wabce hannunta tayi sakeni tukunnan ma abar wannan maganar meyakaika gidansu yaron can jiya,ban jamaka kunne ba?miyasa baka jin maganata ne wai Sulaiman?..

Yar dariya yayi I knew it dama,yan gulma sesun kwasa sunkai tonifa Yan uwana ne Kuma babu inda nake zuwa inji dadi inba gurinsu ba Mama inkuma kika takuramin kan wannan batun se in tatttara kayana inkoma london abina daman nagaji wallahi......

Cikeda takaici takai hannu zata make shi yayi saurin kaucewa yana "Wayyo Allah na"...
Kada Inkuma ji bakinka yafurta batun komawannan se na fafffasashi.....

Cikin dariya yace Allah nadaina amma nima kidaina takuramin batun Yan uwana they are my fleshy blood inbanyi hulda dasuba dawa zanyi?....
Baga Hamida ba,itan ba 'yar uwarka baneba?...
'dan sosa kai yayi yana ni Mama kindai san halinda da Bossy character dintan nan and besides she's always making phone call bama ta da time dina......

Tsaki Magajiyan tayi"Kai kasani dai koka ki kokasu sudin ba yan uwanka bane aide kana gani bayima sunfisu daraja ah gidan nan.....
Kallon Magajiyan yayi with full confidence yace "koma miyene Mama su yan uwana ne and ah idanuna sunfi bayi daraja dama mutane da dama cikin masarautar nan,bazan iya hanaki yin abunda kikaga dama ba amma nima kada kice zaki hanani hulda dasu"....
Yanzun umarni kake banine komi?.....
Karasowa yayi gabanta yana murmushi sannan yadan kwanto da kanshi jikinta "haba Mama na Isa inbaki Umarni kawai Ina neman alfarma ne".....
Tureshi tayi"dama yafi,ni inaganin mubar zancen nan ma mukoma batun aurenka Sulaiman"....
Tuni yaji duk wata fara ar fuskarshi ta gushe, haba Mama nikam bamunbar maganar nan bane tundazu....
Aa Sulaiman bamu bari ba ajiyeta mukayi gefe yanzu Kuma andawo kanta don bazai yuyu kana zubar min da mutunci cikin masarautar nan ba.....
Yar murmushi tareda lasan lips dinshi yayi ah zuciyarshi kuwa cewa yake wani mutuncine take dashi daman tunda kowa yariga yasan halin da take ciki dakuma muguntar da takema jama'a............

Abar maganar nan kawai Mama....
Dasauri tace baza abarta ba kawai kazabi daya cikin biyu,indai kanason inbarka kana ganin wayancan tsinannun to dole kayarda da maganar auren nan....
'dan shiru yayi na'yan dakiku sannan yace to nayarda amma Mama nigaskiya mace daya bazata isheniba.....
Cikeda takaici tace Allah dai yasauwaketo aidaman nibawai nahana ka bayin bane akwai concubines ai you can use them dukda kuwa awannan masarautar anhana wannan harka sede alokacinka adawo da ita kuma maganar aure munfara ta da Mai Martaba akwai 'yar Sarkin Borno Zaliha mahaifiyarta daman kawatace sosai kuma munyi magana da'ita karshen satinnan seka shirya kaje ka ganta don Mai Martaba yace bayason auren yawuce nan da wata uku....
Zare idanu Sulaiman din yayi sannan yace kai Mama wato tunkafin in amince har angama settling komai to da banyarda ba Kuma fa?....
Harararshi tayi sannan tace tunda ka yarda ai Kuma basai antaso da wancan maganar ba ko?.....
Turobaki yayi sannan yace no need basai naganta ba tunda daman auren dole za amin....
Dubanshi tayi "ah lallai wuyan ka yayi kauri yaron nan se in hadaka damai Martaba ina ruwana....
Yar dariya yayi sannan yace Allah ya huci zuciyarki Mamana nizan fita asa Talatu takawomin baiwa daya yau da daddare ko inje rumfarsu dakaina ....wani harara ta watsa mishi yayinda tabiyo don makanshi,yana dariya yafice ah guje marar kunya kawai......

Straight Mota yawuce don fita yakeson yi nan yayi arba da jacket din da nurse tabashi na Almustapha dakuma ledan abincin daya saya jiya da daddare ahankali yafurta subhanallah don kwata kwata yamanta dama yasai musu abinci daya fita dashi sunci ai,dauka yayi yabude daman jollof din shikafa ce da naman kaji kuma da alama babu abunda tayi don haka yadauka tareda jacket din yawuce gidansu Almustaphan dashi, sanda yaje jikin Almustaphan dasauki sosai babu laifi gaisawa sukayi sannan yace ga jacket din Yaya yakarashe maganar tareda ajiyeta gefen Almustaphan sannan yafita yashiga yaduba Ummi ma sannan yabama su Afiya abinci kan su dumama suci tareda yimusu bayanin yanda yasiyo yamanta ah mota.......

Tunda Sulaiman din ya ajiyemishi jacket din yashiga karema jacket din kallo, ahankali yadauka yarike ah hannunshi yana tuna sanda ta lulluba mai ajiki,shiyama manta kwata kwata da har wata yarinya tazo kusa dashi,dan tabe baki yayi sannan yafurta"I don't even know how her face look like bare inmayar mata"......

Story continues below

Tashi yayi ya lankayeta jikin wata kusa dake jikin bangon dakin dukda kuwa kamshin jacket din bakaramin dadi yayi mishiba ...
****
Yau kwata kwata batada lectures, Munira ne tashigo hannunta rikeda basket din jiya tace Adda Asmeey gashi Adda Asiya tace inkawo miki kinmanta ah mota,Ummi dake gefe tana kallon TV tajuyo tana karema basket din kallo karba Asma'un tayi dasauri sannan tashige kitchen don duk ah tunaninta abincin naciki batason Ummi tagani tayi mata fada......
Ajiye wa tayi akan drawer sannan tashiga bude food flask din sede to her own surprise babu komai aciki ancinye sede kwanukan ba'a wanke ba itakuwa wannan bedame taba tunda tasamu ancinye abinci ai atleast ba ayi asararshiba nan tawanke kwanukan tas sannan takifesu ah kwando,tun tana kitchen takejin kaman sunyi bako lekawa tayi nan tahango Mukhtar zaune suna gaisawa da Umminta Allah yataimaketa kanta da dan kwali don haka tafito tana yar murmushi"yau Yaya Mukhtar ne agidanmu"...
Yaron da aka Kira da Mukhtar dan kyaukyawa,dan gayu dashi da tunda Asma'un tafito yakafeta da idanu yace"tunda kinki kawoni nida na matsu ai gashi nazo"....
Sa hannu tayi ah bakinta tana yar dariya"Kai Yaya Mukhtar yaushe naki kawoka Kuma?".....

Duban Ummi yayi Adda Maryam kinji yarkin nan ko wai tambayata ma takeyi yaushe taki kawoni,tunfa suna registration nace insun gama zasu zo gida she should inform me amma shiru kake ji"....
Kyaleni da ita Mukhtar ainalura bakin cikin ganin Yan garin mu takeyimini Ummin tafada cikin zolaya,gwaliyo Mukhtar din yamata kaman zata yi Kuka tace to ai shikenan tunda kayi succeeding.....

Yi hakuri Asma'u wasa nikeyi kema kinsani Kuma Ummin nakima tasani,turo baki tayi a'a nikam ban hakura ba,cikeda zolaya yace sena saya miki ice cream kenan?...
Aa still ban hakura ba,kallon Ummin yayi yana gaskiya Adda Maryam an shagwaba min Mata yanzu inna aureta haka zanta fama?.....
Dariya Ummin tayi don duk awasa ta dauki maganar Asma'u kuwa dataji haka tashiga bubbuga kafa tana Ummi Kinga neman tsokanan nashi ko?, itadai Ummi babu abunda take se dariya don tasan halin Mukhtar da neman tsokana tun yana yaro gashi da raha....
Zare idanu yayi,wayafada miki wasa nikeyi barima kiga infara biyayya gun sirikata yakarashe maganar yana saukowa daga kan kujera cikin yar karamar muryarsa yace Adda Maryam za abani Asma'u don Allah?.....
Wannan karan Kam dagudu tashige cikin gida don bazata iya da halin Mukhtar ba, murmushi Ummi tayi sannan tace aiyanzukam katashi tunda ta tafiko...

Kin tashin yayi sannan yace"Ina naga ta tashi Adda Maryamu bayan bakice kinbaniba, nifa dagaske nikeyi Adda Maryam,it was love at first sight... believe me inason Asma'u and my intentions are good".....
Harara takai mishi tana lallai Mukhtar ashe zuwan ka da biyune bama ziyara kaxo minba.....
Yar dariya yayi still yana tsugunen, a'a na isa wallahi daman ni inada niyan zuwa itane bata kawoni dawuri ba,kaidai fadi gaskiya cewar Ummin...
To ayafemin Maman mu nidai ace anbani Asma'u se inji dadin shan ruwa agidan nan.....

Jijjiga Kai Ummin tayi kaifa baka da kunya Mukhtar gurin uwa kake neman izini?...
Sosa Kai yashigayi,Kai Adda Maryamu kemafa Uwace agareni wani kunya zanji nidai abani izini infara zuwa zance gurin Asma'una adaina min yanga....

Tashi Ummin tayi sannan tace nikam kaje kanemi yardarta banida matsala da wannan fatana Allah yazaba muku abinda yafi alkhairi,cikeda dajin dadi yace nagode Adda Maryam, I'm so happy today......
yadubi Sadiq dake dinning table yanacin abincin karya wanda duk gulma yatsaya ji don tun dazu yagama cin abincin....
Kanina kawomin abincin nima naci banason cin abinci akan dinning table, dariya Sadiq din yayi sannan yashiga zuba mishi yana auren likitoci zamusha kenan Uncle....
Ai kaidai bari har Doctors night se anyi dayardar ubangiji, Allah yanuna mana cewar Sadiq din sannan yakarasa zuba mishi yamikamai don sauri yake har jikinshi bari yakeyi tsabar gulma soyake yaje ya guntsama yayunsa Asma'u tayi saurayi finally.....
Aikuwa dukansu ukun yasamesu ah parlour suna kallon football, cikeda zumudi yace albishirinku!...

Musa ne kawai ya amsa da goro,don haka Sadiq yace tunda kai kadai ka ansa kai kadai zan fadamawa, harararshi Aliyun yayi yana kai labarin ka har wata tsiyace da mutum ze so ji......
Turo baki Sadiq din yayi sannan yace toshikenan, Musa kuwa daya kosa yaji miyene cikeda kalaman yaudara yace zo 'dan kani na,zo kafada min kaji, murmushi Sadiq din yayi sannan yakarasa gun Musa acikin kunnensa yace Adda Asmeey tayi saurayi yanama cikin gidan nan yanzu. .....
Wani tsalle Musa yayi tareda zare idanu,dagaske kake ko wasa?.....
Allah dagaske Yaya Musa kaje kagani in karyane aikuwa nan gogunanku suka juyo suma sunason jin zance cikeda manyance Mubaraq yace ku bamason haukafa miyene zakuwani zo Kuna mana ihu muna kallo miyene yafaru?....
Dariya Musa yayi sannan yace a'a badamunku mukeyiba kuyi hakuri yanzuma zamu fita nan yakama hannun Sadiq din yace muje Sadiq, Aliyu ne yace"kut kudawo nan, miyene yafaru kufada mana,zaku wani tafi don munafurci"....
Yayinda Mubaraq yace kyale yan rainin wayau mana banason rainifa,dariya Sadiq yashiga yi yayinda Musa yace nawa zaku biya?...
Dakuwa Mubaraq din yamishi yayinda Aliyu yataso afusace zeyi kansu cikeda tsoro Sadiq din yace yi hakuri don Allah karka tabani Adda Asma'u ne tayi saurayi bawani abu bane ba... sololo Aliyu yatsaya baki sake,sekuma yasaki dariya wai dagaske?..
Yana Ina, Mubaraq ne yace wai wace Asma'un?, Ma'u dai danasani ...
Eh Yaya Mubaraq mujema kaganshi dan gayu dashi wallahi cewar Sadiq din, a'a baza ayi hakaba badadi muje kanshi tunda yana nan za a hadu ai wataran nidai Ma'ulelen nikeson gani inzolaye ta cewar Mubaraq...

Story continues below

****
Yana kwance ah daki yaji sallamar Mallam hudu,Afiya ne taje ta amsa shi sannan suka shigo har dakin Almustaphan yashiga yaduba jikinshi sannan yace"naji mummunar labari Yarima amma banji dadin abunda kayiba,fisabilillahi Allah ya horema bakin magana don miyene?"...
Badon kayi magana bane,kasan bakayi abu ba miyasa bazakace baka yinba nina baka kudi da hannu na kaje kasayi maganin nan amma sukayi maka sharri Kuma kayi shiru"....
Tunda yake magana kan Almustaphan akasa yake,seda yakai aya sannan yakara da nikam wannan bayibane ba ranar litinin din zanzo inbada shaida tunda ninasan gaskiya ....
Ajiyar zuciya Almustaphan yayi sannan yace "karka damu Mallam Hudu".....
Cikeda bacin rai Mallam Hudu yace"Ya kar indamu Yarima,sokake inyi shiru inga ana wulakanta ka...
Jijjiga Kai Almustaphan yayi alamun a'a kaman Kuma bazaiyi magana ba seyace"banason rikici ne I'll just pay them back".....
Dukda Mallam Hudun bawai yana wani jin turanci bane amma tabbas yagane meyake cewa don haka yace"Allah yayi mutum inagani ikon Allah nikam,toh!tunda haka kace bazan takurakaba haka kawai mutum ya anshi laifin da banashiba gaskiya Allah yazuba ma ruwan hakuri".....
Murmushi kawai Almustaphan yayi yayinda Mallam Hudun yace zanbaka kudin seka basu kawai inaganin shine mafita.....
"Nagode"shine abunda Almustaphan yafadama Mallam Hudu,nan yayi masa sallama kan ze tafi dukda seda yabi yaduba Ummi kamin ya wuce gida abunsa......

*****
Yau gabadaya hanata sakat sukayi sunbi sunsata ah gaba wai tayi saurayi,kuka tashigayima Ummi kantace musu subarta ita bahaka bane fa,dariya Ummin tayi sannan tace kinga tafiyata nikam don kunfi kusa, dariya Mubaraq yayi sannan yace ai Ummi gwanda kidawo mufara zancen biki kinga se ahada danawa tunda karshen watan nan za aje tambaya....
Itadai Asma'u haushi kaman tayi yaya,sema yanzu tagane wanda yahada abun dasauri tayi kanshi tana Allah Sadiq yau me rabani dakai cikin gidan nan seyayi dagaske....
dagudu yafita yabar parlourn yana wayyo Allah Ummi kizo kitaimakeni....
Sukuwa su Aliyu inbanda dariya babu abunda sukeyi wayarta dake gefen Musa ne yayi ringing aikuwa sunan Mukhtar ne yayi appearing ah screan din, dariya Musa ya kece da kunga har masoyin yakira yakasa hakuri yadaga wayar yana nuna musu screan din cikin sauri takarbi wayar tareda amsawa tasaka ah handsfree....
Daga can bangaren Mukhtar yace Matas laifin me nayi akaki daga wayata tundazu?.......
Ae tanajin haka dasauri tacire ah handsfree din kuma tagudu daki tanajinsu suna mata dariya, Allah Yaya Mukhtar kabari kaga kasa anata tsokana na agida,'yar dariya yayi sannan yace kice nasamu shiga har haka?...
Dole inzo in kwashi gaisuwa cikin weekend dinnan....
Turo baki tayi, Allah nikam kabar wasan nan banaso....
Ganin batadau abun da serious ba yasashi sassauta murya yace "Asma'u I'm serious bawasa nike ba,I love you"....
yanda yayi maganar seda yasa tsikan jikinta yatashi,cikin nutsuwa yacigaba da magana"tun randa naganki naji kinyimini and it was love at first sight believe me"....
Shiru tayi don tama rasa mai zata cemishi,kina jina Asma'u na?yayi maganar ahankali....
Uhm kawai ta iyacewa, murmushi yasaki sannan yace kibani dama innuna miki irin son da nike miki please,I really love you!....
Kai tsaye tace mishi I'll think about it Yaya Mukhtar....
Cikeda jindadi yace zuwa yaushe kenan?....
Murza yan yatsunta tashigayi sannan tace kaidai kabani lokaci.....
To Asma'u na, I'll wait for your answer, don't make me wait for a very long time please.....
to kawai tace mishi yayinda tayi mishi sallama ta katse wayar,lumshe idanunta tayi ahankali don batamasan nayi ba abunda kawai tasani shine she need to give him a chance atleast dubada yanda yan gidansu suka dame ta........
*****
Washegari kuwa Almustapha bakaramin dadin jikinshi yajiba don yanzu yasamu sauki sosai shiyasa yana wanka yashirya yashiga duba Ummi, yau se kallonshi takeyi wanda yakula sabida bandage din dayake kan goshin shine murmushi yasakar mata dayaga akwai alamar damuwa ah fuskarta,how are you feeling Mother?.....
Jijjiga mashi kai tayi alamar dasauki,taba goshinshi yayi yana nuna mata don yasan abunda keran ta kenan "a minor accident Mother, but I'm fine now"......
Murmushi tadanyi mai kawai sannan yadan shafa fuskar ta yanajin temperature din jikinta.....
Babu laifi don temperature din is normal,ahaka yafita yabarsu tareda su Afiya bayan yafitan ne Amira tace Allah nikam miskilancin Yaya Almustapha yafara damuna takarashe maganar tana yatsine fuska....
Yar dariya Afiya tayi tana ayyyahya,seyau yafara damunki aini tun ba yauba tunanina ma daya Matarsa wallahi don kuwa akwai aiki ah gabanta....
Hummm,I pity her,cewar Amiran.....
Dayafita straight shagon Mallam Hudu yawuce bayan sun gaisa ne Mallam Hudun yabashi dubu sittin din yace ya ajiye gurinshi kafin Monday, godiya yayi masa sannan yakoma gida ya ajiye kudin sannan yashiga school dukda bawani serious abu yake dashi ba acikin makarantar.......
....
Bangaren Asma'u kuwa tun ranar Mukhtar yashiga takura mata don kuwa baya kwana biyu bezo mataba harma yafara sabawa da 'yan gidansu barin ma samarin tun tana kin fitowa harta fara bashi fuska,don ayanzu kam har Daddynsu yasan da maganar Mukhtar dukda kuwa bawai tana wani yinshi bane ba sede masu it's magana sukace ita zuciya tanason me kyautata mata Mukhtar kuwa kullum cikin kyautata mata yake ta hanyar nuna mata kauna daga ita har familynta,yawan rahan shi dason mutane yajawo mishi soyayya cikin gidan don kowa yinshi yakeyi harta Hajja ma don tun tana mai bakin hali harta daina donta lura bemasan tanayiba,akwai ranar datace nikam Zainabu saurayin Asma'un nan bashida zuciya ne kullum yagaisheni sena ki amsawa haka kuma bazai hanashi dawowa ba inyasake zuwa...

Murmushi Mommy tayi,Hajja Mukhtar yaron kirki ne babu ruwanshi kina amsa gaisuwarshi don Allah don babu abunda yakeson mu dashi ah gidan nan se alheri,harara Hajjan tasakar mata sannan tace ke kika sani dai,don da yabon Ansar kikayi zanfi jin dadi....
Shima ai Ina yabonshi Hajja cewar Mommyn, Allah yazaba musu abunda yafi alkhairi duka,Amin Hajjan tace kawai....
Zuwa makaranta kuwa sunayinshi sannan kowaccensu tamaida hankalinta sosai kan karatun ta dukda kuwa Asiya ananan da rawar kai don kuwa duk wani party da gargajiga baya wuceta setayi attending sede haryanzu Asma'un batasan da haka ba tunda bawai suna yawan haduwa bane acikin school bare tasan halin da Yar uwartata take ciki.....
Akarshen watan aka Kai tambayar auren Mubaraq acikin kaduna Kuma anbasu alhamdulillah sannan babu bata lokaci akasa lokacin biki nanda wata biyar......
******
Sulaiman kuwa kamar yanda Magajiya ta umarceshi yaje Borno haka ya shirya cikin weekend yanata kunkuni yatafi,babu laifi Gimbiya Zaliha tayi mishi don akwai Body kam gata kuma da kwainane shikuma abunda yake burgeshi kenan becika son mace me kunya ba shiyasa yana dawowa yayi na'am da zancen nan aka kawo tambayar auren Hamida babban 'dan Sarkin sokoto yanason kara aure shine yanemi ita Hamidan Kuma anbashi yayinda aka hada da maganar nasu Sulaiman din aka tsaida biki nanda wata Uku, Magajiya murna kaman tayi yaya dukda kuwa itafa ba haka tasoba taso ayi bikin cikin gaggawa batason ana bata lokaci sede babu yanda taiya don Mai Martaba yace shibazai je yace ah matso da bikiba don ba mutuncin shi baneba

***
Almustapha tunranar daya karbi kudi gurin Mallam Hudu ya ajiyeshi safely seda sati yazagayo yabada kudi da aka taru ah kotu, Mai Martaba yayi mamaki kwarai da Almustapha be guduba don anashi judgement din da ace yadauka din bazai bari har sati yazagayo yakawo kudin ba to amma sebeyi magana ba kawai yasa akabama Mai kaji kudinshi sannan yace ma Almustaphan kada yakaraji an tuhumeshi da maganar sata don kuwa inhakan tasake faruwa baza amishi sassauciba yanzunma sabida yace magani yasai ma mahaifiyarsa.........

Tundaga ranar Almustapha yacigaba da harkokin gabansa basosai yake shiga school ba seranar da sukeda specific course din da zai gyara din shima se in practical aspects zeyi mostly yake zuwa sekuma yanma intayi yatafi shagon Mallam Hudu,su Afiya ma babu canji daga gurin Hamida sema abunda yakaru don yanzu haushin kowa takeji anrabata da masoyinta abunnranta za ayi mata auren dole shiyasa duk wani haushinta akansu take saukewa .......

★★★
*TWO MONTHS LATER*...

Shirye shiryen biki akeyi sosai acikin Masarautar babu kama hannun yaro, Sulaiman tundaga bakin kofa yake kwalawa Almustaphan Kira, Yaya Almustapha kana inane?...

Almustapha dake daki yana kwance yadafe kanshi ahankali shibayason damuwa amma yalura Sulaiman yasashi agaba,dede lokacin Sulaiman din yashigo cikin dakin yana nikam gaskiya Yaya yakamata kasayi waya kullum mutum yayi ta nemanka baya samunka Kuma babu halin communication...
Murmushi Almustaphan yayi yana bin Sulaiman din da kallo,turo baki yayi Allah Yaya kasandai you've to do something during my wedding bawai kayita shirunkan nan ba......
Jan kumatunshi Almustaphan yayi"naughty Boy,baxaka barni inhuta ba?".....
I won't Yaya, Mama tace senaje naga Zaliha cikin satinnan tunda naje sau daya bankara zuwa ba and she told me senatafi mata da gift narasa mezan saya.....
Jijjiga Kai Almustaphan yayi irin unbelievable dinnan donshi aganinshi Sulaiman besan meyake yiba tunda har yarasa wazai tambaya shawarar sayan gift seshi....
Magana fa nikeyi Yaya Almustapha!....
Tashi Almustaphan yayi don Sulaiman din yadame shi gwanda yabar mishi dakin kilan ya kyale shi,zuwa yayi jikin hanga tareda daukar shirt dinshi yana sakawa, Sulaiman ne yace"kut Yaya fitama zakayi inamagana,yayi maganar rai bace tareda tashi fuuu ze fice wai shi ah dole yayi zuciya, murmushi Almustapha yayi tareda janyoshi ya dawo dashi sannan yace"I've no idea, I'm sorry",sannan yasakeshi fita Sulaiman din yayi don shima seyanzu yakejin haushin kanshi dayazo gurin Almustapha din dama samunsu Afiya yayi kilan su taimaka mishi......

Karasa sa rigarshi yayi sannan yasa hannu don mayar da hanger din karap idanunshi yasauka kan katuwar rigar sanyin Asma'u sa hannu yayi yadauko ta yana Kare mata kallo sannan wata zuciyar tashiga raya mishi "Anya Almustapha ka kyauta kuwa,yakamata kamayar ma yarinyar nan rigar sanyinta"....
Sekuma yayi tsaki ahankali,don shi ko fuskarta bazai iya ganewa ba amma ai rigar sanyi ce mekyau Kuma yanada tabbacin tanason abunta don haka yayi deciding zetafi dashi school gobe and he'll make an announcement ajikin notice board may be tagani and then she can get her cardigan back....
dawannan idea din yakarasa shirin shi sannan yafita don yanzu sun fara test sosai exams yagabato yakamata yafara shiga school sosai don yana dan karatu against exams ...


Dan write-up yayi jikin paper sannan yafita dashi don ayimishi photocopy,seda yabi akamishi sannan yawuce cikin makarantar....

*****
Kai,Ya Allah Zahra Malamin nan yagama damu cewar Asma'u,dariya Zahra tayi aikedai bari kawata bantaba tunanin irin question din dazaiyiba kenan Basma dake gefensu tace"hehe yanmata that's Medicine for you wai danma aji daya muke tukunnan".....
Hmmm to Allah yabamu sa'a kawai,Amin Basma da Zahra suka amsa ah tare......

Yayinda Basma ke kallon pictures cikin wayar Asma'u,lura tayi da pictures din Asiya sosai acikin wayar seta cema Asma'u.. ....
"wainikam Asmeey inakikasan wannan yarinyar?"....
Mugani Asma'un takarba don kallon hoton da Basma ke tambaya,Yar dariya tayi sannan tace miyasa kika tambaya?....
Tabe baki Basma tayi"Naga she's not decent ne, she's the new girlfriend of Ahmad Dj"......
Zare ido Zahra tayi tace wani Ahmad Dj din gayen danakejin labarinshi?...
Gyada Kai Basma din tayi yayinda Zahra tace muga hoton yarinyar gaskiya tabata wayonta,uhmm kekam irinsu da saninsu suke wani abun wallahi,they just want to be popular and ah tunaninsu this's the best way,abunda basu sani ba shina kana 'ya mace kana yawo da irin wayannan Mazan ai babu wanda zaiso ya aureka ma don ko wani abu baitaba shiga tsakanin kuba mutane baza su yardaba.
Asma'u datunda suka fara maganar taji kanta namata wani irin sarawa, Zahra ne tace Asmeey bani Inga hoton yarinyar tadauki wayar Asma'un tareda kurama screen din wayar ido,jiki ah sanyaye ta dago tana kallon Asma'un wanda ah yanzu kwalla yafara zubowa ah idanunta.....
Dasauri Zahra tace Basma are you really sure this's the girl?.....
Harara Basma takai mata sannan tace ke zanmiki karyane,I even have evidence sunje birthday party dinshi this weekend she was there with him barima kiga video din,so disgusting and annoying jijjiga Kai Basma tayi tana karawa da"Kai duniya inazaki damu"kamin tashiga videos dinta tamika musu bayaan tayi playing aikuwa sega Asiya carab ajikin maza tasha straight skirt se tikan rawa takeyi wanda duka mazan daka gansu kasan they're not decent,haka akazo gun bada cake ma tabama Ahmad din abaki Basma tace ai yanzukam kunyarda ko?...
Last week fa har dambe sukayi da ex dinshi akanshi,akayita posting,kekam Zahra bakyajin labarin komai ah school dinnan daga ke har Asma'un inaga sabida ba a hostel kuke zamaba....
Dakyar Asma'u tayi controlling tears dinta don batason Basma tagani sannan tace please send me the video,nan Basma tatura mata sannan tace musu itazataje hostel yunwa takeji don dama ba 'Yar garibace so ah hostel take zama ...

Bayan Basma ta tafinne Zahra tadubi Asma'u"don Allah kada kitada hankalinki Asma'u akan abunnan,wani irin duba Asma'un tamata sannan tace yakike tunanin kar intada hankalina, Asiya yayata ce,my blood sister Zahra and look at what she's doing yabazan damuba, inacikin makarantar nan bansan halin da take cikiba,miye anfanina fisabilillahi wannan karan kukanta karuwa yayi,goge mata kwalla Zahra tayi sannan tace kisameta kuyi magana kiyimata fada inbata dainaba seki fada ah gida.....

Goge kwallarta tashigayi sannan tace, Allah yasa taji maganata bakisan Aseey ba yanzu seta hayayyakomini....
To yazakiyi you've to tell her the truth aide kinji abunda Basma tace game da yaron nan and I know him and his group too well, he's capable of doing anything Asma'u,daddaikune basu san Ahmad Dj ah cikin ABU ba.....Dan Jan numfashi Asma'un tayi sannan tace
I'll talk to her yanzuma inaganin gurinta zanje kawai muyi magana,yauwa yamafi kuyi acikin school kada kuje gida har ajiku just call her now sekiji inda take kije kisameta.....
Aikuwa nan take tashiga dialling number din Asiya din bejima yana ringing ba tayi picking,"miyene kike kirana"cewar Asiya din...

Sorry Aseey inaso inganki ne akwai maganar danikeson muyi,kina inane I'll come and meet you ..
Dan tsaki Asiya tayi sannan tace wace irin maganace dabazaki bari semunje gidaba zaki damu rayuwana?..
Dan numfasawa Asma'un tayi sannan tace kede it's important kifadamin inda kike....
To jarabbabba Ina cafeteria kizo kisameni cewar Asiyan sannan tayi disconnecting call din batareda ta jira jin mezata ceba.....

Story continues below

Duban Zahra Asma'u tayi sannan tace I've to go meet her,zamuyi magana later.....
Murmushi Zahran tamata giving her more courage "all the best friend"..
Thank you,Nan ta tashi tatafi cafeteria din,sede zuwanta to her own surprise tasamu Asiya zaune da gayen datagani ah video din suna cin abinci suna dariya abunsu,har yana wani bata ah baki takaici ne ya ishi Asma'u wanda yasa takasa karasawa seta juya kawai tabar gurin yayinda hawaye ke sulala ah idanunta,tafiya take batareda tasan inda zatajeba wani lungu tasamu tazauna nan tashiga rera kuka kaman wanda akayimata mutuwa harda sheshekar ta.....
Almustapha dake zaune can gefe wanda gurin yazame masa gurin isolating kanshi inyagama abubuwan dayakeyi don kuwa bayason zama cikin mutane bare su bata mishi rai,yanzuma yafito daga cafe ne yagama karatunshi shine yaxo yadan huta seyaje yayi placing write-up dayayi yakuma kai jacket din security office may be yarinyar inta gani tabi bayan abunta....

Sosai yakejin kukan ta wanda abun kaman gabama yakeyi,shidai tunda yake zuwa nan betaba haduwa da kowaba gurin that is isolated and always quiet shiyasama yake zuwa gurin don yazame masa habits,dan tsaki yayi don kukan ta na damunshi seyatashi yadauki jacket din ah hannunshi don tafiya,haryafara barin gurin sewata zuciyar tace mishi what if wanine is trying to harm her kokuma wani snake ne tahadu dashi atleast he should check....
Ahankali yajuya yakoma inda takedin,kanta na kife kan cinyarta se sheshekar kuka takeyi abunta,ganin babu abunda yacijeta Kuma babu wani agurin seya zauna gefenta tareda lumshe idanunshi,yafi minti goma ahaka yayinda tadan dago kanta arba tayi da mutum ah gefenta dasauri ta tashi zata gudu,bude idanunshi yayi jin motsinta tashinta idanunsa data Kira da manya ranar yasaukesu kanta shima tashin yayi yatsaya tareda dauke kanshi daga kallonta, nan yajuya zai tafi.....

Dasauri tasha gabanshi,tana kallon shi you!and here?....
Rabawa yayi tagefen ta zewuce amma seta sake saurin tareshi don yabata haushi atleast he should say thank you for the other day Kuma ma har yawo yake Mata da jacket watonma yamaidashi nashi....

Wani kallo ya watsa mata wanda seda gabanta yafadi yakuma rabawa tagefenta zewuce,cikeda karfin hali tasake shan gabanshi dukda kuwa idanunta sunyi luhu luhu dashi,rike kugu tayi"you don't have manners at all,nataimake ka the other day bakaneme ni kacemin ko thank you ba bare har kayi tunanin dawomin da jacket dina,sannan tadan kalli jacket din kafin tamaida kallonta gareshi it even seems like kamaida shi naka,may be i should have believe what people were saying about you".......
Kallonta yayi ahankali,from the start datayi maganar ita ta taimakeshi yaji dadin ganinta atleast he will thank her sede dayaji zafafan kalamanta seyaga ashe she's also like the others ,there is no difference between her dasu...
Harararshi takeyi don yabata haushi tabbas,mika mata jacket din dake hannunshi yayi ahankali takarba jiki ah sanyaye ganin yanda furkarshi tayi wani iri seta fara regretting abunda tayi mishi Kuma,itakanta batasan ya akayi tafadi wasu kalaman ba may be harda haushin Asiya ne yasata hucewa akanshi......
Kanshi ah kasa yace "thank you and I'm...sorry", Yana kai aya yatafi yabarta tsaye agurin kaman gunki,dasauri kuma tabishi tana wait please!.....
Shan gabanshi takuma yi sede wannan karan janyeta yayi ya wurgar agefe sannan yacigaba da tafiyarshi dukda haka bataji haushin abunda yamataba dakyar takuma tashi zata bishi sede yabace mata da gani tanemeshi kas da bus tarasa......
Yanzu inazata ganshi tabashi hakuri,shine tambayar da tayima kanta....
....
Sunada lectures by 12:00pm don haka takoma medical college din,ahanya tahadu da Mukhtar ganin tana tafiya not normal yatambayeta lafiya,nan yace lafiya Lau kawai tadan fadine cikeda damuwa yace suje clinic mana....
Jijjiga mishi Kai tayi ahankali "no need Yaya Mukhtar I'm fine"...
Cikeda damuwa yace no sweetheart, you're not fine kizo muje I'll take you to the clinic,barina dauko motata, murmushi tasakar mishi sannan tace you're overprotective,nace maka babu komai kaikam karka damu Kuma bama kanada practicals ba yanzu?....
Kallonta yayi sannan yace inadashi amma your health comes first Asma'u......
Sa hannu tayi ah both kumatunta,so I've such a caring husband to be?....

Story continues below

Yar dariya yayi sannan yace,kina nema kidauke zancen ne kuma baza a fasaba,dede lokacin Zahra takaraso gurin gaisar da Mukhtar din tayi sannan tace what's going on here?..

Yauwa Zahra zokicema Yaya Mukhtar zaki kaini clinic shiyatafi practical dinshi, murmushi Zahra tayi sannan tace I'll take her though bansan meke damuntaba just know that you can count on me....
Murmushi yayi sannan yace thank you Zahra, I'll have to go now....
Duban Asma'un yayi sannan yace ki kula da kanki I'll come home anjima....
To kawai tace mishi yayinda yawuce yabarsu agurin,dubanta Zahran tayi don tasan she's just faking a smile, yakuka kareda Asiya,sad look tayi sannan tace bamuyi maganar ba naje nasamesu tareda yaron kawai se ah mota zanmata maganar......
To shikenn Allah yakaimu lokacin, nan Zahra tashiga daga kafar tana ya akayi kikaji ciwo Kuma,turo baki tayi sannan tace "bashine ba yabuge ni nafadi?"
Kallonta Zahran tayi sannan tace wayene Kuma, Yaya Mukhtar?...
Dasauri tace a'a kekam it's just a minor accident,muje cikin lecture rooms din kinsan munada lecture yanzu.....
Tabe baki Zahra tayi sannan ta
gyada mata kai sannan tace after that we've practicals ma na chemistry.....
Haka suka tashi suka tafi cikin collage din don attending lectures se 4 suka gama duk wani activities dinsu na school haka Zahra ta tafi gida tabar Asma'u tana jiran Asiya tazo daukarta ba ita tazo ba se biyar da rabi haka suka kama hanyar gida Asiyan ne tafara magana"kikace zakizo kisamoni ah cafeteria nayita jiranki bakizoba?"......
Nazo kawai kin karasawa nayi gunki because you were with someone,harararta Asiya tayi sannan tace sabida inatareda wani shine bazaki iya karasowaba,okay fine amma aidasaiki Kira kicemin kinfasa zuwa bawai ki ajiyeni kamar itace inata jirankiba you have no idea how much time I've wasted waiting for you,kin kyauta gobema rana ne ai.....
Hmmm Aseey yanzu abunda kikayima kanki kin kyauta kenan?,do you think abunda kika jefa life dinki aciki shizai fisheki, you're there to learn my sister bawai kije kina hulda dawa yanda basu dace da rayuwarkiba, I'm sorry nasan I'm your younger sister sede hakan bazai hana ni fada miki gaskiya ba,I saw the video and everything and naji labarin komai though I couldn't believe it seda nakuma gane ma idanuna, folding hannunta tayi tadubi Asiyan sannan tace don Allah Asiya kirabu da Ahmad dinnan he's a bad person
Okay.......
Parking Asiya tayi ah gefen titi sannan tadubi kanwartata kafin ta sheke dawata dariya"to sannu Ustazu iye,kiyimin waza azi kinji Yar malamai jikan malamai,who do you think you're dazakina fadamin irin wayannan maganganun,Ina karatu Asma'u and I know what I'm doing kinajina inkin ganni dasu Ahmad Dj tokisani bawai hakan na nufin inabata rayuwana baneba.....
Kallonta Asma'u keyi in desbelive sannan tace koda ke azuciyarki babu komai mutane bazasu gane hakan ba Asiya bakiji me bature yace ba"show me your friend and I'll tell you who exactly you're"...
Barema bana tunanin video din dana gani zesa incire ma raina kinzama kamarsu, Asiya kiji tsoron Allah kirike martabar gidanmu dama mutuncin ki me Yaya Aslam ya rageki dashi,the poor guy loves you so much amma kiga inda kike neman jefa rayuwarki Asiya, gaskiya inbaki bar abunda kikeyi ba I won't help it dolene infada ah gida don bazan zuba miki idanuba....
Murmushi Asiya tayi sannan tace you should go ahead and tell them bazai dameniba and kema dakike pretending to be inocent I know everything and nasan gayen dakika taimaka din har akayita yada ki ah social media,kinyi tunanin bangani bane ba?..
Kawai fa nayi shirune don kowa yayi minding ways nashi atleast kowa yarufa ma Dan uwansa asiri amma tunda kikace haka kina nunawa nima zan nuna naki.....
Wannan karan Asma'u hawaye ne yagangaro fuskarta,don tasan tabbas ranar antayin video amma batasan yayita yawo ba,cikin sauri tace my situation is different from yours Asiya sabida haka kada ma kifara wannan tunanin.....
Dariya Asiya tayi sannan tace whatever,nidai nafada miki,shiru Asma'un tayi yayinda Asiyan ta tada motar suka wuce gida Asma'u kuwa aranta tadauki alwashin muddin Asiya bata canza ways dintaba seta fada ahgida tunda ai ita Allah yaga zuciyarta batayi da niyan komai bane ba and it was a coincidence....

******

Mai Martaba yatara duka iyalinsa ah babban parlourn sa ah daren yau wanda hardasu Gimbiya Humaira da Halima dakuma 'ya'yansu dasuka zo bikin Hamida da Sulaiman,bude taron akayi da addu'a kafin Mai Martaba yayi gyaran murya sannan yafara da"tabbas nayi farin cikin ganin iyalaina baki dayansu ah wannan gurin, Allah yacigaba da rayamin ku yakuma yi muku albarka daga ku har ya'yan ku",dukansu suka amsa da amin sannan Mai Martaba yacigaba da magana"bawani abu bane yasa natara ku anan baki dayan ku sedan wani abu dayataso dakuma wata decision dana yanke,bikin Hamida da Sulaiman yazo alhamdulillah so alokacin wannan taron inason inrada Sulaiman amatsayin Yarima wanda shine zai gaje ni bayan na sauka daga mulki dukda kuwa mahaifiyarku taso ayi hakan tun adacan baya amma naki sabida dalilin rashin ganin Dan Uwana Almustapha naso ace yadawo in yanada 'Da babba to tabbas yafi kowa cancanta abashi sabida asali shine yakamata yahau sarautarma sede Allah beyiba yanzu wurin kimanin shekaru talatin Ina nemanshi sede har yau babu labarinshi, ahankali yadubi ahalinnashi sannan yakarasa da nasare inaganin babu kaddarar sake haduwarmu sannan kilan zaman Sulaiman magaji na shine mafi alkhairi ga mutanen Zaria dama kowa baki daya shiyasa nayanke wannan shawarar kuma gobe zan tattaunata da mutanen fada in Sha Allah......

Story continues below

Tunda sarki yafara magana Magajiya takejin ranta yayi wani irin fes yayinda ah bangaren Sulaiman bahaka baneba sabida shi bahaka yakeson jiba,tunaninshi daya yazaiyi yahana faruwar wannan abun,sosai yan uwanshi suka shiga tayashi murna murmushi kawai yake ah fili wanda bawai yakai har zuci bane ba.......
Rufe taron akayi da addu'a yayinda kowa ya watse,tunda yaje shashinshi yarasa nazama dakuma abunyi sekai kawo yakeyi daga karshe
ya yanke shawarar zuwa yasamu Magajiya kilan ta taimaka mishi dukda kuwa hope dinshi na ta taimaka mishi is 1% out of 100% dasauri yake tafiya dogaraye nata zubewa suna mika mishi gaisuwa amma ko kallon inda suke beyiba bare ya ansa musu,sashin mahaifiyartasa yashiga inda tundaga bakin kofa yakejin muryarta tana Humaira idan ba hakan nayiba shi kanin naku babu abunda zai samu sede yazama kaman bawa ko dan kallo,muddin hakn tafaru nikuma nazama ba komaiba acikin Masarautar nan,tsayawa yayi don yakarasa jin metake fada.......
Inda Magajiya tashiga Jero ma Manyan 'Ya'yanta abubuwan ta aikata ....

Humaira nine sanadiyar barin Yayan Babanku gidan nan tunda jimawa sabida tun ina karama Allah yadauramin son mahaifinku sannan nakudurtama raina sena aureshi kota halin yaya, sede on the other hand mahaifinku ne karami and wanshi ne zezama sarki alokacin na lura Abdulrahman nason sarauta and shida kawunku suna matukar son juna don zasu iya sadaukarwa juna koma miyene adalilin kaunar dasuke ma junansu sannan abunda nakara lura shine shi kawun naku bayason sarauta dawannan makamin nashiga rayuwar mahaifinku nasashi abaya yazamanto meyawan rubuce rubuce duk abunda yafaru dashi wanda inada tabbacin shi kawun naku zai gani wanda har burina yacika nasamu nakawar dashi ah idanuna....
Sake duban Humaira da Halima Magajiya tayi sannan tace
Humaira nine sanadiyar gushewan kwakwalwar Mai Martaba harya manta dawaye Khairiya dama 'ya'yanta ah gidan nan wanda kuma inada tabbacin har abada bazai taba tuna kowacece itaba sabida wanda yayimin aiki banawasa bane ba sannan nine sanadiyar halin da Khairiya keciki sabida nagaji da ganin idanunta acikin Masarautar nan nagaji da yabata da Mai Martaba yakeyi dukda kuwa tafita ah rayuwarshi sabida ko bayan narabasu nasa yamanta da'ita namayar da Khairiya baiwa na cikin masu dafa abinci wanda aboye nayi hakan kada Waziri yasani sede kash bansan wani abun najama kainaba don tunda Mai Martaba yaci Masan da Khairiya tayi sau daya yace shifa kullum wannan Masan da miyar ganye yakeso anamishi dasafe washegari nasa wata tayi yakici dole se itan ne tacigaba dayimishi dukda bawai raina yanaso bane haryakai ga Mai Martaba yace yanason ganin wanda takeyi mishi masa yayi mata godiya Kuma yanason tanamishi duk wani abincinshi nanfa hankalina yatashi sosai shine nasa akayi mata illar da har yau tana kwance kuma bazata sake tashiba dasunan dafawa Mai Martaba masa bare har tayi tunanin ze yafe mata ko ya tuna da ita watarana,ahaka zata Kare har abada dukdama banyi tunanin zata Kai har yanzu ba...
Halima ne ta jinjina Kai sannan tace gaskiya Mama kinyi daidai sabida ah *GIDAN SARAUTA* in mutum be tashiba yama kanshi hobbasa ba to sede yazama dan kallo ko bawa,gwanda ace Kaine shugaba shiyasa kikaga nima tunda nasamu 'da namiji nadaina ragama sauran kishiyoyina....
Murmushin mugunta Humaira tayi sannan tace ayyayya wato shine dalilin dayasa Abba bayacin masa da miya?....
Hmmm wannan shine dalili Humaira don cemasa nayi meyimasa masar Allah yayi mata rasuwa ranar yini yayi bashida walwala sannan tundaga ranar in anyi masa baya ci sema yayita fada ko inyaci yayi amai.....

Lallai kam,Anya wannan matar Itama ba tsafin tayima Abba ba Mama,cewar Humaira din,oho mata koma shi tayi to tasamu wanda tafita don aduniyarnan bana tunanin akwai mehana ni cinma burina,shiyasa koda nasamu labarin kawun ku naboyema mahaifinku batun.......
Cikeda mamaki Humaira tace Mama kinsamu labarinshi yana Ina?....
Indonesia Humaira,najima dasamun labarinshi sede bansan taka maimai inda yakeba sejiya me aikin nawa yazo yakefadamin,wai yana Indonesia da iyalinsa.....
Hmmm yakarata can basai yadawoba kilan ma yanada 'da namiji cewar Gimbiya Humaira.
nima abunda nagani kenan,shiyasa duk abunda nafada muku kuyi Kim da bakinku kada kowa yaji koda kuwa Sulaiman ne don yaroncan bashida hankali da tunani wataran innazauna inatunani se ince anya 'Dana ne Sulaiman don gaskiya beyi gadoba.....

Dariya Humaira tayi sannan tace kyale Dan banza anayi sabida shi amma bayagani in sha Allah bazamu fada masaba,haka suka cigaba da hirarsu duk akan makircinsu harda batun ah yanzu bata da wani buri daya wuce taga Mai Martaba yatsani Almustapha,tsana irin sosai dinnan domin matakin daya dauka kan abunda yafaru wata biyu dasuka wuce baiyimata ba kuma bahaka tasoba. .. Sulaiman kuwa kafarsa kasa daukarsa tayi don kuwa bakaramin mamaki yaji ba,yasan Mamanshi is someone who is not nice at all sede betaba tunanin muguntan nata yakai har hakaba,tunda yafita ah shashinta yasamu guri yazauna tunanin duniya ya isheshi,mezaiyi, *MENENE MAFITA*,ta ina zaifara neman uncle din ah Indonesia tunda shibawai yasan address din bane kuma ah iya tunanin shi kawo kawunsan ne kadai zai tsayarda rada shi as the crown prince da ake niyar yi din sannan daga nan ne Kuma zasu fara tunanin neman mafita gameda rashin lafiyar Ummin,Dafe kanshi yayi all he knows is bazai taba tonawa uwarsa asiriba sede he can do whatever he can to stop her from doing all the evil things datakeyi......
Yana cikin wannan tunanin ne yaji kamar magana kasa kasa,se yayi shiru yana saurare to his own surprise seyaji muryar Magajiya tana"kasamu duk wani bayani?"...
Bawan ne yace eh Uwargijiyata a adireshin shine anan dakuma duk wani bayani akan ahalinsa.....

Yar dariya tayi sannan tace to nagode,nan tacema Talatun tasallameshi sannan suka juya zasu tafi jin suna tahowa ta direction dinshine yasashi saurin tashi yadan buya abayan wani katanga seda ya tabbatar sunbar gurin sannan yafito yana hamdala sannan yawuce sashinshi atleast yanzu yanada hope he'll surely come and look for the details.......

****

Tunda takoma gida tashige daki tarufo kofarta,koda Mukhtar yazo cewa Munira tayi tace masa tana bacci don yau batajin hiran shima Kuma dashike yasan batajin dadi yaudin seyace kada su tasheta hira yayi dasu Mubaraq sannan yawuce gidansa dake cikin garin Zaria din don ba a hostel yake zamaba.....

Juyi tadingayi akan gadon ta tarasa meyake mata dadi,batasan yazatayi da Asiya ba tabar abunda takeyi din,daukar wayarta tayi takunna data dinta tana dudduba chats kozata danji Dadi aranta aikuwa sega friend dinta Aisha online,mamaki tasha kawarai don tajima bata chat fita tayi ah whatsapp din sannan tashiga dialling number dinta aikuwa yayi ringing nan ta daga, Asma'u tafara haba Aisha miye duniya?.....
Dariya Aisha tayi sannan tace kwalin cabin Asmeey,kadama kifara mitar dazu aka kawomin wayar hawana WhatsApp kenan don nasan korafin dazakiyi kenan dariya Asma'un tayi sannan tace "tona maida wukar kawata,yakike it's been long nayi kewarki sosai wallahi"....
Nima nayi kewarki Asma'u,tunfa damuka gama school bamuyi communication ba gashi ba halin ziyartar juna ba gari daya muke ba but I'm back now harsai kingaji dani cewar Aishan......
Hahaha,yanmata kozan gaji dakowa bazan gaji da keba, you're special to me you know that,ya mutanen gida?..
Duk lafiyansu kalau wallahi,tokigaida minsu please kuma namiki murna Allah yasa akashe waya lafiya....
Aisha tace Amin Asma'u nagode sosai semun hadu ta chat,to shikenan nan sukayi sallama Aisha nashirin katsewa Asma'un tace yauwa nikam Aisha yama full name din Sarkin Zaria?....
Yar dariya Aisha tayi sannan tace kinji kunya wallahi Sarkin garin kuma bakisan sunanshiba,pity face Asma'u tayi kaman tana gabanta sannan tace sorry mana kifadamin please naga ke bakya manta irin sunayen nan ne and besides abunda yayi Zaria shiyayi kaduna ai so yakamata kinsani....
To uwar iyayi sunan shi sarki Abdulrahman Sulaiman i guess.....
cikeda jin dadi Asma'u tace nagode to kigaida su Mama,nan ta katse call din lumshe idanunta tayi ahankali sannan tasake bude su duban wayartata tayi kafin tashiga Facebook if she could remember ranar Zahra cemata tayi sunan gayen Almustapha and he's the illigitimate son of the king,tokoma illigitimate son ne yakamata yana bearing sunan mahaifinshi ne donhaka tashiga searching Almustapha Abdulrahman setaga babu don duk sunayen dayake nuna mata is not exact sede similar names,dan tsaki tayi sannan tace"what name could he be using?"....
Can wata idea tafado mata nan tasa Almustapha A Sulaiman suma duk babu wasu sufficient names haushi ne yakamata tayi wulli da wayar sannan tace"he's different from the others,so sunan dayake using ma might be different,komadai miyene I need to apologise to him",dawannan tunanin takwanta bacci...Washegari bayan Mai Martaba yayi magana da mutanen fada aka yi announcing bikin rada Sulaiman amatsayin the crown prince wanda za a hada tareda bikinshi dana Hamida,Yan fada damutanen gari kadai ke murna don kuwa bayi bakaramin tashin hankali suka shiga ba sabida sunada tabbacin indai Sulaiman yahau sarauta to tabbas abunda aka daina shekarun baya dasuka wuce za adawo dashi wato zamansu wulakantattu da anfani dasu batareda anbasu wata daraja ba,dukda kuwa Magajiya na tunanin bayin basu san Sulaiman ke wannan aika aikan ba iyakacin wanda yayimadin ne kawai suka sani sede abunda batasani ba labari yariga ya yadu ah tsakaninsu kawai tsoron fada akeyi sabida sanin wacece Magajiya acikin Masarautar......

Tunda aka tashi daga babbar fada yawuce dakinshi yasa dogarayensa suka fitar mishi da kayanshi don tafiya Maiduguri kaman yanda yayima Magajiya alkawari zeje yaga Zaliha....
haka yakama hanya batareda yayima kowa sallama ba.....

****

Afiya nayima Hamida tausa, Hamidan tadube ta tace ke tashi kije kicema Laure Ina Dan waken danace tayimin tundazu jiranta nikeyi.....
Cikeda takaici Afiya tafita tayi kitchen din masarautar wanda kace anguwane guda tsabar girmansa yayinda yake  daukeda masu aikin girke girke kowa is busy yana portion din aikin da aka basa,masu yankan albasa dana masu gyara kayan miya daban haka masu duba wuta ma daban,sedacan gefe kuma masu wanke kwanuka nayi,masuyin tuwo ma daban wanda suke afili dayane Kuma nanne ake dafa abincin jama'ar masarautar baki dayanta......
Afiya tagefen su tazo tawuce yayinda tashige wani gu wanda shima dai kaman kitchen dinne sedai bekai wancan din girmaba sannan mutane basufi goma acikinta ba dasukeyin aikin yayinda jakadiya guda daya dake tsaye kansu tana supervising ayyukan dasukeyi da alama nanne ake dafa abincin su Magajiya dakuma Mai Martaba....
Daga can nesa tahango Laure karasawa tayi gurinta sannan tace

 "kekam Gimbiya Hamida nata jiran kinzo kinyi zamanki".....
Tsaki Lauren tayi sannan tace bakiga ina jiran ruwan ya tafasa bane,tunda ma kinzo kijefa mata danwaken kawai daman Magajiya na nemana,hararanta Afiya tashigayi tana dashike aini akasaka yin danwanke ko,nidai sako ta aikoni in isar kuma nafada miki sabida haka Kinga tafiyata,dariya Lauren tayi sannan tace kitafi mana barinaje infada ma Magajiya ita zatasan yanda zatayi dake,take kuwa laure tatashi tabar Afiya tsaye gurin kamar gunki,tabe baki tayi sannan takoma tazauna tana jiran ruwan ya tafasa tajefa danwaken don already ankwaba garin danwaken.......
Seda ya tafasa sannan tajefe kwabin tas cikin ruwan, wutan naci sosai don haka tuni yafara kumfa nan tashiga neman matsami sede babushi ah gurin don Lauren bata tanadeshi kusa ba,tashi tayi dasauri  don dauko matsamin data hango kan wani dan tebiri, daukan matsamin tayi harzata tafi se idanunta sukayi arba da funkasau da miyar ganye acikin cooler wanda marfinshi is transparent,jitayi ya burgeta kuma harga Allah son ci takeyi batareda tayi wani tunani ba tashiga bude coolern tadauki funkasau daya zata kai baki Talatu dayanzu shigowarta kitchen din tadaka mata wani uban tsawa.....
"Ke mekikeyi agurin abincin su Magajiya?"....
Iye mekikeyi ah gurin tsabar tsoro Afiya seda tasaki matsamin da funkasau din yafadi ah kasa she never thought this was coming kan kace me gabadaya attention yadawo kanta harma da wayanda suke waje suka fara lekowa don gulma,janta Talatun tayi sannan tace mekikeyi anan?.....
Kwace hannunta Afiya tayi sannan tace babu matsami nazo dauka zankwashe abinci.....
Wani harara Talatun ta watsa mata tareda sake damkar hannunta,nafa ganki da idanuna sabida haka kidaina min karya,mekikasa musu acikin abincin?"....
Cikeda firgita tace babu abunda nasaka musu nikam kiduba kigani mana,suna cikin wannan rikicin ne jakadiya ta karaso tana tambayar meyafaru......
Nan Talatu tashiga bayani" jakadiya tundaga can waje nake hango mutum kaman yana barbada abu acikin abinci amma ban tabbatar ba seda nashigo naga tana sake garwaya miyar shine nayi ihu"....

Story continues below

Duban Afiya jakadiya tayi sannan tacema Talatun tayi searching dinta,nan tashiga tattabamata jiki amma babu komai sake kallon jakadiyan tayi sannan tace wallahi jakadiya kiyarda dani naganta,kafin Talatu tarufe bakinta wata baiwa tace gacan wani leda ah karkashin teburin awurge,dasauri kowa hankalinshi yakoma kan ledar dasauri Talatu ta tsuguna tadauko ledar wani irin bakin garine aciki,karba jakadiya tayi sannan tace miye wannan?....
Tuni Afiya idanunta sukayi jage jage da hawaye tace nima bansaniba babu abunda nayi Talatu kiji tsoron Allah dakuma ranar haduwarki dashi..

Ke dallah can rufemin baki,ke yar shegiya dake har kinada bakin cewa wani yaji tsoron Allah cewar Talatun sannan ta zungure ta kibari a tabbatar da abunda kikayi mana tukunnan nan ne za aga waye baya tsoron Allah....
Jakadiya ne tadubi Talatu,ya Isa haka don Allah, Afiya kuwa se kuka takeyi tana ita wallahi batayikomai ba ah duba abincin.....
Wata cikin bayin ne  tace to agwada bama mage abincin agani mana,aikuwa nan aka dauki shawararta akasamo mage cikin masarautar nan take sannan aka gutsuri funkasau da yar miya akasaka mishi nan yashiga ci,Amira dake dakin Hamida taji Laure tazo tana kawo gulma dagudu tayi hanyar kitchen,zuwa tayi tarike Afiya tanacewa kada kidamu tunda anbawa magen ai gaskiya zai bayyana ....
Cikin kuka Afiya tace Amira sekace bakisan halin mutanen nan ba ni inada tabbacin da biyu akayi abunnan.....
Goge mata hawaye Amiran tashigayi tana Allah yafisu in Allah ya yardama ba hakan bane ba .......
Jisukayi bayin na ihu ai mage tafara amai daganan kuma tafadi luuu shikenan babu rai,salati akafara da salallami...
Talatu tace aidama nafada amma anaganin kaman karya nakeyi,ga yarinya nashirin yin kisa kiri kiri,kisanma na masu gida,nan fa bayin suka fara yowa kan Afiya kaman zasu rufeta da duka,kankame yar uwarta tayi suna kuka, jakadiya ne tace duk su tsaya basuda right din yanke hukunci sabida duk wani abu daya danganci harkan bangaren bayi mata dakuma dangane da kitchen Magajiya ce zata yanke hukunci sabida haka kowa takoma bakin aikinta, hakan kuwa akayi yayinda jakadiya tasa dogaraye biyu suzo sutafi da..
ita bangaren Magajiya, Magajiya na zaune ah parlourn ta akazo kiranta kan ga wata tayi laifi,yatsuna fuska tayi sannan tace tana zuwa.....
Cikin takun kasaita tafita gaban parlourn nata Afiya ce zube kasa dogare biyu natsaye akanta.....
Kallonta Magajiya tayi sannan tace kekuma me kikayi,bana ce ko kallonki banason inayiba akusa dani?...
Cikin kuka Afiya tace don Allah Magajiya kiyimin rai wallahi nibanyi komaiba, bansan komai ba sharri akayi mini ....
Daga mata hannu Magajiyan tayi alamun batason hayaniya,shiru tayi dukda kukan zucin datakeyi Amira kuwa nacan gefe ta rakube Itama hawayen takeyi tarasa ta Ina zata taimaki Yar uwarta...
Jakadiya ne tadubi Magajiya tace Uwargijiyata kamata mukayi tazuba guba acikin abincin ku kuma har Mage munbama yamutu ah take,dafe kirji Magajiya tayi lokaci  daya taji zuciyarta na dukan uku uku,kafin tazare idanu kamar wata zararriya tayi kan Afiya....
Kasheni kikeson yi nida 'ya'yana don ubanki?.....waya turoki,kifadamin maza waya turoki Magajiyan takarashe maganar tareda kaima Afiya naushi,kuka Afiya keyi tana"banibane wallahi,bansan ya akayiba sharri akayimini".....
wani naushin Magajiya tasake kaimata,tana bazaki fadamin ba?....
Itadai Afiya secewa take batasan wayene ba daga karshe Magajiya tace aje da ita gidan yari ayita bata kashi harsaita fada.....kuka Afiya da Amira sukeyi sosai suna Afiya batasan komaiba anma Ina babu wanda yakulasu sema hankade Amira da dogarayen sukayi sannan suka dauki Afiya sukayi gaba da ita,dagudu Amiran tayi gidansu tana kuka dakin Almustapha ta leka bayanan don haka tazari hijabinta tana faman toshe bakinta don kada Ummi taji kukan datakeyidin......
Tundaga masarautar take gudu harta isa kasuwa bata tsayaba seda ta iso gaban shagon Mallam Hudu ta tsaya tana haki gakuma hawaye dake zuba ah idanunta shabe shabe......
Mudi ne ke fadama Mallam Hudun ga kanwar Almustapha tazo tana kuka dasauri yafito don yasan bawai su Amira suncika fitowa daga masarautar bane Kuma tun da har akace tana kuka to ba lafiya ba......
Samunta yayi zube bakin kofar shagon tana kuka tsabar gudun datayi gabadaya tagaji shiyasa takasa karasawa cikima,tsugunawa yayi ah gabanta,"Amira,tashi?"...
Nan yakama hannunta suka shiga shagon dubada yanda jama'a suka fara taruwa suna kallonsu daman acikin shagon akwai wani store don haka yakaita ciki,kidaina kuka kifada min meyafaru?.....
Kasa daina kukan tayi se Afiya datake ta kira,me Afiya tayi kifadamin Amira.....
Mallam Hudu sharri akayi mata,suntafi da'ita ina Yaya Almustapha don Allah kafadamin inda yake?".....
Cikeda tausayi yace yana makaranta bezo nanba seda yanma zaizo......
Kikwantar da hankalinki kikoma gida nasan daya taso ah makaranta nan zezo daganan semuzo gida inji meya faru don na lura yanzu ko magana mekyau bakya iya yi,shikuma ba wayane dashiba bare inkirashi kinji.....
Gyada mishi Kai tayi alamar to dukda bawai maganar tashigeta bane gani takeyi inbataga Almustaphan ba tafada mishi hankalinta bazaitaba kwanciya ba gashi Sulaiman bayanan don taji Hamida namaganan ya tafi Maiduguri....

Story continues below

Kudin machine Mallam Hudu yabata sannan yace taje gida,haka tafita ah kasuwan ta tari machine nantace mai yakaita Samaru,aikuwa har bakin gate din main campus din ya ajiyeta nan tashiga datambayan mutane har
tasamu ta isa Medical college din,daka ga idanunta zakagane taci uban kuka agaban gurin tahango yan mata na zaune su biyu suna hira abunsu,karasawa tayi gurinsu tareda yi musu sallama, Zahra ne ta ansa yayinda Asma'u tashiga kare mata kallo dubada irin kodaddun kayan dake jikinta gata kuma kyakyawa abunta, astaghfirullah shine abunda Asma'un tafurta tareda dauke kanta gareta...
Amiran talura da kallon da Asma'u tayimata amma bata damuba don abunda yakawota shine agabanta,cikin dashashiyar muryarta tace don Allah kunsan wani yana Medicine sunanshi Almustapha.....
kai tsaye Zahra tace gaskiya bamusanshi ba,sede kitambayi wasu daga can don mu sabbin dalibai ne ah makarantar bakowa muka saniba tafada tana nuna mata bangaren da wasu samari kezaune agurin,godiya Amira tamasu sannan tabar gurin takarasa gurin samarin tayi musu thesame tambaya,dariya sukayi sannan daya daga cikinsu yace yanzu ke fisabilillahi Yan mata inazamusan wakike nufi, Almustapha ae badaya bane ah faculty dinnan dadai kinsan sunan babanshine kilan mu iya taimaka miki....
Cikin sauri tace nasani sunanshi Almustapha A Sulaiman,babban Dan Sarkin garin nan...
Tsaki sukayi ah tare sannan wani yace kudubeta don Allah wai Dan Sarki,ke dallah tafi kibamu guri bamason hauka.....
Dariya wani yayi sannan yace Abokaina kumata ahankali mana zataji da cikin dayamata ne kilan kokuma da naku zataji.....
Tsaki Ibrahim yayi sannan yace baka ganta bane ah haukace kamanshi dukyanda akayi ita takai kanta ma,sannan ya zare idanu tareda nunata da yatsa,ke kibarnan tun bankai hannuna jikinki ba tunda ke bakida hankali.tunda suke maganan Amira kam sewasu sabbin hawayen,mehakan ke nufi?is this the humiliation that her brother is going through?....
To ya akayi basu saniba,shaidar da akayi mishi kenan,juyawa tayi ahankali jikinta har rawa yakeyi tana hawaye ah yanzukam tama manta damuwar data kawota sena son sanin meyafaru akema Yayanta wayannan accusations din.... Asma'u dake gefe tareda Zahra duk sunajin abunda ke faruwa,jitayi tanason sanin yarinyar,she wants to know if what people are saying is true because even though he's a stranger bata taba yarda he's a bad person ba don haka tabi zuciyarta dasauri ta tashi tabi bayan Amiran, Zahra nakiranta tace "Zahra inazuwa I need to meet that lady".....
Jijjiga Kai Zahra tayi in desbelief tana"kekam Asma'u inaruwanki da harkartanewai"....
Asma'u bata kulataba sema sauri data karayi don ta isko Amiran,shan gabanta tayi sannan tace sorry na tsaidake amma inason intambayeki.....

Kallonta Amiran tayi tana goge kwallarta,sannan tace inajinki,kema kinzo kicimin mutuncine ta hanyar zagin Yaya na?.....
Jijjiga kai Asma'un tayi dukda kuwa bakaramin dadi tajiba dataji cewa Amiran kanwar Almustapha ne atleast she'll get the chance to meet him tabashi hakuri tahanyarta ...
Amiran ne tace,sauri nikeyi miye zaki tambayeni?....

Riko hannunta Asma'u tayi sannan tace dagaske Yayanki ne?
..
Jijjiga mata kai tayi alamar eh,se alokacin Asma'u talura da kamar da Amiran keyida Almustapha din, murmushi tayi sannan tace miyasa kike nemanshi to?....
Wani kallo Amiran tayi mata,sannan tace it's personal..
Oh I'm sorry bahaka nike nufiba,ina nufin tunda kina kanwarshi you can call him kisan inda yake  basai kinzo kina tambayar mutaneba.....
Cikeda takaici Amira tace da inada halin kiranshi dabazaki ganni ananba,tayi tsaki tawuce zata tafi dasauri Asma'u tace kitsaya zankaiki gurinshi......
Cak Amiran ta tsaya sannan tajuyo tadubi Asma'u din,gyada mata kai Asma'un tayi sannan tace akwai inda naganshi jiya kilan yanacan amma I'm not sure tunda sau biyu inazuwa nemanshi nima bansameshiba sede mugwada dubawa....
To kawai Amiran tace mata yayinda tashiga bin bayan Asma'un suna tafiya babu maice ma dan uwansa komai secan Asma'u tace ashe MBBS yakeyi shima?.....
Uhum kawai Amiran tace mata, murmushi Asma'u tayi sannan azuciyarta tace"she's like her Brother too".....
Gurinda suka hadu jiya takaita,dukda kuwa batayi tsanmanin samumshi ba sede to her own surprise yana zaune abunshi yakurama wata bishiya idanu......
Amira naganshi dagudu tayi inda yake tana Yaya Almustapha jin muryartane yajuyo fadawa tayi jikinshi tashiga rera kuka,dasauri Asma'u tajuya musu baya dan jidatayi kaman an soki zuciyarta dawani abu sakamakon rungumar da Amiran tayima Yayanta.....
****
Tun bayan da aka tafida Afiya gidan yari Magajiya takasa zaune takasa tsaye
sabida takasa yardar ma kanta cewa har Almustapha da kannensa zasu taba tunanin kasheta sabida abubuwan datayi musu,Kai kawotake cikin dakinta yayinda Talatu nazaune gefe kanta ah kasa,akaro na uku Magajiya tace kintabbata Kinga sanda takesa guban acikin abincin?......
Nanda nan Talatu tashiga rantsuwa,wallahi Uwargijiyata naganta da idanuna tundaga waje nahango mutum na barbada abu acikin abincin bayan angamasawa kuma se aka shiga garwayawa niban taba tunanin Afiya bace seda nashigo naganta,nima nayi mamakin abun Uwargijiyata......

Hummm shine abunda Magajiya tace kenan tareda dafe hannu ah kirjinta don abun yadameta"harni zasuyi tunanin kashewa?"....
Lallai insunsan wata basu san wataba,shegen yaron nan nawasadani kije kicema Sarkin gidan yari sucimin uban yarinyarnan harsaita fadi gaskiya...

To uwargijiyata, nan Talatu tafita jikina bari, Gimbiya Humaira ne tace nifa Mama duk nayi tunanin ke kika hada abun dafari?....
Hmmm Humaira banibane,bansan komaiba akan wannan al amarin wannan shirine nasu daman sunyi niya,niban kashesuba su suna shirin kasheni nida 'ya'yana zankawo  karshen komai dayardar Allah......
Yafikam Mama,cewar Humaira din sede kada kiyi abunda zai tona mana asiri, dariya Magajiya tayi sannan tace ni inadaidai dakowa 'yata sannan ina abu da tunani bawai cikin gaggawa ba......

*****

Hugging nata back yayi yana jin kukanta harcikin ranshi,seda tayi mai isarta don kanta sannan tadago tadubeshi,Yaya Almustapha,zata kuma fashewa dawani kukan yasa hannunshi kan lips dinta shhhhh! Amira it's okay kifadamin meyake faruwa,yanda yayi maganar zaka tabbatar bakaramin damuwa yayi da al amarinba,riko hannunshi tayi cikin nata sannan tace "for how long have you been enduring this Yaya,kowa yana zaginka,kowa na doramaka laifin dabakayiba muduk ah tunanin mu acikin Masarauta  ne kawai Yaya ashe har acikin makarantar ku?.....
haka sukeyimaka Yaya,tayi masa tambayar tana hawaye,kafadamin don Allah,harfa cewa suke kai dan iska ne,miyasa mutane basu da Imani Yaya,miyasa mutane bazasuyi bincikeba sekawai sudinga anfani da abunda waninsu yafada koda kuwa ba gaskiya bane ba,numfasawa tayi ahankali sannan tace mukam munshiga ukunmu ah rayuwarmu,laifinme mukayine muke ganin irin wannan jarabawar, yaushe ne zamuyi farinciki ah rayuwarmu,dasauri  Almustapha  yakuma sa hannu kan bakinta sannan yace kada kiyi sabo Amira, besides why are you here,ya akayi kikasan inanan?.....

Kallonshi kawai tayi don tagane yanason kawar dazancen ne, Asma'u dataji yana tambayar Amiran ya akayi tasan yana nan dasauri tabuya don batason Amiran ta nunata,aikuwa Amiran cewa tayi wata takawoni gurinka nazo nemankane nahadu da ita shine tace tasan kana nan....
Dan shiru yayi sannan yace"meya faru kike nemana?"don yariga yagane wa Amiran kenufi tunda itakadaine tasan yana zama anan.....

Yaya Almustapha Afiya,anyimata sharri Yaya Almustapha,sunkaita prison she's there now suffering shine nazo infada maka....
Cikeda tashin hankali yace prison,you mean Afiya is in prison now?.....
Jijjiga mishi kai tayi dasauri yatashi sannan yayi gaba yabarta agurin yana cewa mutafi gidan,that means Ummi is alone in the house?.....
Eh tace mishi sannan suka shiga tafiya sauri sauri......
seda ta tabbatar suntafi sannan tafito tana dan goge kwallarta,what are they going through,miyene acikin rayuwarsu dahar Amira takeshirin yin sabo batareda tayi realising ba ....she need to know sede itakanta batasan dalilin dayasa takeson saniba hakana batasan miyasa take ingiza kanta ga bawan Allahn nan ba abu daya tasani tanabin zuciyarta da gangan jikinta ne kawai........


★*★
Tunda suka isa Masarautar hankalin shi ah matukar tashe yake first gurin Ummi ya wuce seda ya tabbatar she's fine sannan yacema Amiran tazauna shizaije cikin gidan dukda kuwa zuciyarshi naraya mishi kada yaje saboda rabonda yayi ga da ga da Magajiya yana ganin tun sanda mahaifiyarsa tarabu da Mai Martaba sede me he's the only Brother to Afiya bezai yuyu yatsaya yana ganin abunda suke mataba batareda yadau action ba....

Har bangaren Magajiyan yaje yatsaya ah waje,yasan basai yaje yafada mataba tana yan kai mata gulma already aikuwa bejima da tsayuwaba segata tafito tana mamakin ganinshi kuma don tasan halin Almustapha......
Cikeda bacin rai tace "kaima kazo ka hallakanin ne?"....
 Kallonta kawai yayi kafin ya dauke kanshi sannan yadan matsa kusada ita, I'm here to deliver a massage kafin ya mikama daya daga cikin dogareyen wata paper sannan yajuya yatafi don anashi ganin bazai tsaya yana jayayya da wannan sakaryar matar ba bare harta fada mishi maganar banza, Magajiya kuwa bakaramin baci ranta yayi ba don Almustapha karshen raini ya rainata tunda har bazai iya fadamata meyakawoshiba sede ya rubuta ah rubuce cikeda takaici tacema dogarin ya karanta......
Cikin sauri dogarin yabude takardar kafin yashiga karanta babu ko sallama babu komai se yar rubutun dayayi.....

" _inaganin yakamata kisaki kanwata hakanan, she's not at fault duk wani abu dakike ganin zakiyi you should put me amma kada kihada da kannena please!_ "...

Tsaki Magajiya tayi sannan tace banida lokacinsa, yacigaba da aikomin later yaga inban hada dashiba nan tajuya tashige abunta.....
tunda yabar gurin shagon Mallam Hudu yawuce nan yake fada masa ai Amira tazo, Almustapha kawai cemishi yayi munhadu daganan bai kuma magana ba Mallam Hudu ma besake tankawaba sukacigaba da harkokin gabansu......
Tundaga lokacin Almustapha besamu ansa daga Magajiya ba haka shima kuma be koma ba sede sau biyu suna zuwa gurin Afiyan ah gidan yari don dubata,kuka tadinga mishi tana itabatasan komaiba bata kuma yi abunda ake tuhumarta dashiba, Almustapha yaji tausayin kanwarshi sosai kuma bakaramin tashin hankali yashiga ba wanda yahanashi shiga makaranta har sati yakare he's always trying to think of a way out sede babu mafita shikuma bazai iya kaskantar da kanshi ga matan nan ba because he's fully aware koya kaskantar din to babu abunda zaisamu ma sema ta tusa sabon wulakanci,acikin weekend Sulaiman yadawo daga Maiduguri seda ya huta sannan yayi gidansu Almustapha din, Amira kadai yasamu da Ummi inda yake tambayar Ina Afiya da Almustapha nan takwashe komai tafada mishi bayan sun fito don batason Ummi taji dukda kuwa tanada tabbacin Ummi tasan ba lafiya ba tunda bataganin Afiya din.....
Innalilahi wainna ilaihir rajiun shine kawai abunda Sulaiman din ke nanata wa,dafe kanshi yayi sannan yace duk haka yafaru bansaniba?......
Cikin kuka Amira tace kaine kadai hope dina Yaya Sulaiman please save my sister,hakuri yashiga bata sannan yace kada tadamu zeyi abunda zai iya yagani sannan yafice zuwa gurin Magajiya......
Murmushi tayi da ganinshi sannan yace kaddai harka huta kenan?.....
Gyada mata kai yayi sannan yace Mama inada maganar dazamuyi.....
Dubanshi tayi sannan tace zauna nima daman inason inji labarin mutanen Maiduguri.....
Zama yayi gefenta sannan ya riko hannunta cikin nashi"don Allah Mama alfarma nikenema agurinki kan maganar Afiya tuni Magajiya tayi kicin kicin da fuska"abunda yakawoka kenan,daman zuwa kayi ka bata min rai takarashe maganar tana cire hannunta cikin nashi,to bazan lamuntaba gwandama katashi katafi", cikin sauri yace bahaka bane Mama kema kinsan Afiya bazata taba sakamiki guba ah abinciba you and I know that......
Zare idanu Magajiya tayi sannan tace oh hakama zakace,sokake kace ninasama kaina guba nida Yayana kenan.gashi ankama yarinya kiri kiri tanasa guba a abinci sannan kace bazata iyaba,to ai tayi kagani tunda har tana gidan yari,dafe kanshi yayi sannan yacigaba dayi mata magiya amma sam taki yarda haka yatashi yatafi hankali tashe,besan yazaiyi ba hakanan besan ta ina ze bullo ma maganar ba sede kuma yana mamakin yanda Magajiyan ta hakikance kan cewa Afiya tasa mata guba,if she was the one that planned it bazatayi reacting this way ba ah tunaninshi sede wata zuciyar kuma tace  mishi "sekace bakasan Mama ba, she's good at pretending",tsaki tadanyi yasan Amira nada hope sosai akanshi gameda Afiya sede babu yanda zeyi don Magajiya dagaske take kan batun bazata bar Afiyanba tunda dai gashi babu irin magiyar da baiyi mata ba,bangaren su Afiyan yawuce sede yanzun dakin Almustapha yaje straight yasame shi yajingina pillow ah jikin bango yana duba wani littafi,inkaga Almustaphan zakayi tunanin dagaske karanta littafin dake gabanshin yakeyi,sede bahaka bane kwata kwata donkuwa yafada wata duniyar tunani ne kawai, Sulaiman dinma jona dan uwansa yayi don shima duniyar tayi mishi zafi ayanzu.....
Sosai Almustapha yayi mamakin Sulaiman din don Sulaiman yakasance mutum mai yawan surutu dakuma damunshi indai yaxo gurinsa don haka seya juya gareshi tareda cewa  "what's wrong with you?".....
Murmushin dayafi kuka ciwo kawai Sulaiman din yayi batareda yace komai ba don yau kaman shine yakoma miskilin Almustapha ma besake cemishi komai ba haka suka karashi zaman su babu maicema dan uwansa komai sedaga baya ne Sulaiman din yatashi yafita, bejima da fita ba segashi yadawo da leda ah hannunshi zama yayi sannan yace Yaya Almustapha katashi don Allah.....
Tashi Almustaphan yayi yana kallon dan uwan nashi,ajiye mishi ledar Sulaiman yayi sannan yace ..."I bought you a cell phone,don Allah kada kace bazaka karba ba".......
Murmushi kawai Almustapha yayi sannan yadauki wayar yabudeta wayace mai kyau Android phone betsaya bude kwalin ba ya ajiyeta gefe sannan yakoma ya kwanta shima Sulaiman din tashi yayi yafita hoping that Almustapha yayi accepting wayar  don yanason yaje Indonesia yayi bincike gameda kawun nasu kafin bikinsu sabida yana da tabbacin shine kadai zai iya taimakonshi ah yanzu don ya lura Magajiya tagama birkicewa duba time yayi sannan yashiga addu'ar Allah yasa Magajiya tayi bacci by now don haka yawuce bangarenta,ko ina shiru kam se dogaraye dasuka zagaye cikin masarautar suna gadi,ahankali yayi sanda yashiga dakin tayi bacci don haka cikin nutsuwa yashiga bincike cikin drawers dinta yanayi yana dubata har Allah yataimakeshi yasamu file din paper din, rufe drawer din yayi sannan yafita ah dakin Magajiya kuwa cikin bacci tadunga ji kaman motsi don haka tabude idanunta amma babu kowa don haka takoma sharar baccinta.......
seda yakoma dakinshi sannan yabude file din takardan yadauka yashiga karantawa wanda duk information ne cikinta....
Sunan kawunshi yagani wanda take tattareda shekarunsa,gurin aikinsa dakuma garin dayake zama, ahankali yafurta *jakarta*, don shine city din da kawun nasu kezama acan Indonesia din,dan tsaki yayi sannan yashiga tunanin ta Ina zai fara neman kawun nasu ah wannan babban garin dayake capital city dinsu,lumshe idanunsa yayi sannan yasake dorasu kan paper din seyaga sunan bank din da uncle Almustapha ke aiki ah garin *CIM bank*, murmushi yadan saki sannan ya ajiye paper din safely cikin drawer kafin ya kwanta yana kimtsa abunda zai fadama Mai Martaba goben don yabarshi yatafi atleast bank ba boyayyen guri bane ah gari so zai iya samun address dinshi cikin sauki.......
****
Tun ranar data hadu dashi da kanwarsa tajikuma some part of them hankalinta ya kasa kwanciya kwata kwata,duk sanda zata kwanta  dasu take kwanciya aranta kuma dasu take tashi hakana zuwa gurin da Almustapha yasaba zama yazame mata jiki dukda kuwa bata nasarar samun sa.....
Ayauma Zahra ta tafi gida tabarta tana aikin jiran Asiya wanda yariga ya zame mata jiki,tsaki tayi tareda duba wristwatch din hannunta 6:30pm,yanzu tasani Asiya bazatazo su tafi ba se gurin tara na dare don sunkusan fara exams shine Asiya tasamu excuse wai suna karatu ah school ne,itakuma bawai wani karatu ta iya ah school ba sabida tafi jin dadin yi ah gida ah dakinta inta tashi cikin dare,bayan ta idar da sallah ne tawuce wurin cin abinci because she's so hungry seda tayi nak da cikinta sannan takoma massallaci har akayi sallar Isha,tun ana sallah takejin wayarta na vibration alamun kira hakanan aka cigaba da kira babu sassautawa....
seda aka sallame sannan tadauki wayarta ta duba me kiran Yaya Mubaraq ne,dauka tayi ahankali daga daya bangaren yashiga fada"mekikeyi inata kira bakya dauka"......
Ina Sallah ne Yaya Mubaraq,okay to ki dafa min indomie please I'm on my way home.....
Dan numfasawa tayi sannan tace bamu tafi gidaba tukunnan muna cikin school,cikin sauri yace cikin school kuma?...
mekikeyi acikin school haryanzu dabaku tafi gidaba yaushe kuka fara kaiwa dare?.....
Ganin yadamu sosai tace bawani abubane Yaya kasan munkusa fara exams so mukan zauna muyi karatu ne se 9 mudawo,cikeda bacin rai Mubaraq yace wani irin karatu ne dabazakuyishi tunda ranaba  tunda dai ai ba lectures kukeyiba inkunzo gida kuma bazaku iya karatun bane?......
Cikin in Ina tace we're sorry bazamu sakeba,Ina kuke, kifadamin inda kuke   I'll come banfita ah school ba semu wuce gida tare,inagaban mosque,cewa yayi I'm coming now wait for me there bejira amsarta ba ya katse call din......
Dafe kai tayi cikeda damuwa sannan tashiga kiran Asiya amma sai ringing yake bata daukaba ita gaskiya batasan yazatayi ba,batasan mezata cema Yaya Mubaraq ba inya tambayeta ina Asiyan cigaba da kiran Asiya tayi amma har sau biyar bata dauka ba sega Kuma Kiran Mubaraq din nan yace mata gashinan yazo suzo su tafi,tana katse wayanshin takuma Kiran Asiya seda yakusa katsewa sannan aka dauka sede muryar namiji ne,cikeda tashin hankali tace who are you and where is my sister?.....
Bar Man din daya dauki wayar yace she's drunk naga kinata kirane shiyasa nayi picking, innalillahi wainna ilaihir rajiun shine abunda Asma'u tashiga furtawa yayinda wani irin hawaye masu zafi suka shiga zubo mata dakyar tayi karfin halin cewa inane gurin please?....
fada mata address din yayi sannan ta katse wayar,dakyar takarasa gurin motar Yaya Mubaraq din sai yashiga tambayar ta" Ina  kika Bari Asiya Kuma?"...
Cikin kuka tace muje musamota,rai bace yace amma bancemiki inazuwa ba baki fada mata bane?....
Kayi hakuri shine kawai abunda ta iya furtawa kafin tashiga motar,seda yatada motar sannan yace tana inane yanzu?....
Address din da bar man din yabata tafada mishi,kallonta yayi sai yanzuma yalura kuka takeyi, ahankali yace kinsan inda kike fada kuwa,"Are you sure she's there?"....
Jijjiga mai kai tayi kafin tace haka akafadamin yanzu tawaya,besake cewa komai ba har suka isa gurin because yayi tunanin may be she's nearby dagurin ne sede to his own surprise Asma'u cikin gurin tashiga binta yayi se kide kide da rawa yanmata da samari keyi yayinda wasu na badalarsu innalillahi wainna ilaihir rajiun shine kawai abunda Mubaraq yake furtawa har suka isa gurin Bar man din,tana zaune kan kujera jikinta sanye da English wears doguwar riga yayinda tayi rolling gyale ah kanta,tagama shan beer din dake gabanta kenan takuma mika ma Bar man din wai yakara mata, tana nuna kanta cikin maye,ina ni ya yaudara, I'll kill him, I'll finish him sannan tadubi bar Man din daya tsaya yana kallonta tace cikin tsawa "wai bazaka karamin baneba?"......
Dubansu Asma'u yayi"tundazu tazo nan ranta abace tace inbata tasha,inaganin sunsamu matsala da saurayinta ne don duk zuwansu gurinnnan dasukeyi bantaba ganin tasha giyaba sai yau", Mubaraq dake gefenta yadaga hannu yadaga ta cak sannan yace Asma'u tadauko Jakarta da car key din,zille zille tashiga yi tana yasake ta bekulataba seda yakaita mota tukunnan tana shirin mishi hauka ya wanketa da wawan mari tukunnan yarife kofar duban Asma'u yayi rai baci drive the other car muje gida...............
Jiki ah sanyaye tashiga dayar motar yana gaba tanabinsu abaya har suka isa gida.......
Parking yayi ah filin gidan sannan yafito da Asiya din yace Asma'u tabiyoshi betsaya ko inaba se bangaren Daddynsu,ah parlour ya zubar da ita sannan ya shiga dukanta, Daddy da Mommy dake cin abinci ah dinning table suka taso cikin sauri...
Mubaraq meyake faruwa?.....
bebar dukan nataba yace,yarinyar nan tana neman tabata mana suna ah garin nan,tana neman tabata rayuwar ta,nan yashiga basu labarin abunda yafaru kuka Mommy tashiga yi yayinda Daddy yace kadaina dukanta because she's not in her right senses I'll deal with her inta tashi,barta agurin haka Mubaraq yajuya yafita Asma'u na kuka tabi bayanshi seda suka fita sannan yace"kinbani mamaki and don't think I'll ever forgive you for this,kinsan abunda yar uwarki takeyi Amma bakizo kinfada ah gidaba?".....
Cikin kuka tace I'm sorry Yaya Mubaraq,kobi takanta beyiba yabar ta tsaye agurin......
Kuka tashigayi sannan tawuce bangarensu ranar kasa bacci tayi kwata kwata gabadaya tashiga damuwa,washegari dasafe Asiya tatashi taganta ah parlourn Daddy, mamaki ne yakamata yayinda abubuwan dasuka faru suka shiga dawo mata dafe kirji tayi tana furta yau tashiga uku sannan ta tashi cikin sauri don guduwa hartakai bakin kofa taji muryar Daddy yanacewa where do you think you're going?......
Juyowa tayi idonta yataru da kwallah,ahankali yace kidawo kizauna komawa tayi tazauna tareda gaisar dashi amma ko kallon inda take baiyiba,Kiran Mommy yayi sannan yace takira kowa ah gidan yazo,aikuwa cikin minti ishirin kowa ya hallara ah parlourn,da addu'a Daddy yabude taron kafin yadubi Asma'u yace what do you know about this,nan tashiga zayyano mishi komai sannan tafada mishi har fada tayima Asiya sanda tasani kuma tayi tunanin tabari ne sekuma tabashi labarin yanda akayi jiya......
Babu abunda kowa keyi ah parlourn se sallallami, Hajja ne tace cikin kuka menake fada miki Zainabu?,nasan wataran se matarnan tahada miki makirci keda 'ya'yanki gashi ya tabbata,inba sharri ba mezaisa yarinya mai hankali kaman Asiya tasha giya takarashe maganar tana goge kwalla da kasan zaninta,dafe Kai Daddy yayi sannan yace Hajja da idonmu munga state din da Asiya takeciki jiya saboda haka kidaina tunanin wani neyayi mata sharri....
Cikin tsawa Hajja tace kai dallah rufemn baki,Kai daman ai bakason afadi laifinta kwata kwata,shiru Daddy yayima Hajja seda tagama mitarta tatashi tatafi sannan Daddyn yadubi Asiya...
rayuwar dakika zaba ma kanki kenan,karatun dana tura ki kiyi shine laifina ko?.....
Jijjiga Kai tashiga yi tana kuka, Allah Daddy bahaka bane kuma Itama munafukar data jamin meye batayi ina ita da illigitimate son din sarki take soyayya ma,babu wanda baisaniba cikin makarantar Mubaraq ne cikin tsawa yace inbakiyi shiru ba Asiya zanzo inmiki dukan tsiya agurin,kinyi laifi accept it bawai kizo kina wa wani sharriba,Asiya bata daddara ba tace I even have the video kabarni innuna mana to prove you wrong.....
Daddy ne yace Ina video din yake?...
Tashi tayi zataje tadauko wayarta Mubaraq yace you don't have to I've it in my phone and munyi magana da ita Asma'u din dajimawa she told me everything and natambaya naji gaskiyar magana nan Mubaraq yashigama Daddy bayanin abunda yafaru sannan yace batasan wayeshiba kawai she was trying to help Kuma tun lokacin nace mata babu ruwanta dashiga harkar daba nataba tunda ba itakadai bane agurin  tunda taga wani baitaimakeshiba that means something is wrong......
Jijjiga Kai Daddy yayi alamar gamsuwa sannan yace koma miyenevKuma koma wayene dalaifi dawanda yayi dakuma wanda baiyiba I've finally made my decision,dukkansu zan aurar dasu because wannan abunda yafaru yazamemin darasi sannan yakuma dubansu kushirya aurenku tareda Mubaraq zan hada,nakira Aslam da Mukhtar din anjima insunzo zanyi magana da kowannensu sannan yadubi Asiya kekuma daga yau babuke babu zuwa makaranta indai kina cikin gidan nan inshi mijin naki yaga zai barki daga baya kiyi karatun wannan tsakaninkune sannan yakalli Asma'u nabarki kije makaranta but that does not mean kiyi duk abunda kikaga dama,if anything goes wrong kema thesame punishment zanbaki,your punishment na kinfada mana abunda Yayarki tayi shine auren dazanyi miki batareda kinshiryaba and duk wata mace data ke tasowa ah gidannan tasaka ma ranta cewa babu ita babu zuwa jami'a ah gidana data gama secondary school zanyimata sure in mijinta yaga dama shiyasata ah makaranta, this's my final decision and no one can change it....
Nan Daddy yatashi yafita yabarsu da jimami,Ummi da Mommy ne suka dubi juna yayinda Ummi tace yanzu yaza ayi Anty Zainab?......
Dafe Kai Mommy tayi sannan tace addu'a shine mafita Allah yasa auren shine mafi alkhairi garesu don kuwa babu mai iya canzama Babansu ra ayi nina rigada nasani.....
Gyada Kai Ummi tayi sanin halin Mai gidan nasu sannan ta tashi don tafiya don tasan gaskiya Mommyn ke fadi,Daddy mutum ne mai tsatsaurar ra'ayi inya fadi abu yazauna kenan, Mubaraq ne yace Ummi matakin daya dauka shine daidai dasu kowa taje gidan mijinta shine mutuncinta ni inabayan Daddy they should even thank God wanda sukeso ze aura musu if I were in his shoes wasu tsofi daban zan nema inhadasu dasu yanakaiwa karshe yatashi yafice Aliyu da Musa bin Yayansu suma sukayi batareda sunce komaiba haka Mommy tafice don raka Daddyn zefita,duban Asiya Asma'u tayi Ido cikeda kwallah tamatsa kusa da ita"I'm sorry Aseey,bantaba tunanin it'll turn out this way ba"......
Daga mata hannu Asiya tayi sannan tace don't touch me,ya isheki haka you've finally succeeded kinji dadi ai tunda an rabani da abunda raina keson yi,kinji dadi ai tunda ke zaki cika burinki ke kadai daman ah gidannan kene who's always right inni nayi abu I'm always wrong,tafa hannu tayi you should celebrate now Asma'u,sannan tanunata da dan yatsanta but believe me yanda kikasa nayi bakin jini ah gidan nan senasa kema kinyi,infact senasa duka yan gidannan sunyi maki tsanar daba'a taba yimawani ah duniyar nanba, I'll make your own mother to hate you to the point that zata yafeki Asma'u,I promise you that inadani kikeja......
kuka Asma'u tashigayi metsuma rai yayinda Asiya tafita tabarta ah gurin Itama kukan takeyi.......
Innalilahi wainna ilaihir rajiun,shine kawai abunda Asma'u ke furtawa,itakam wannan wace irin jarabawa ne yasameta,kuka tadingayi kaman ranta zaifita haka ranar bata tafi school ba don bakaramin ciwo kanta yashiga yiba.....

Story continues below

*****
Tunda yadawo daga masallacin sallar asuba yawuce prison din masarautar, dogarayen nazubewa kasa suna mika mishi gaisuwa suka mishi iso,cell din da akarufe Afiya aciki yakarasa sannan yasa suka bude mashi...
Tana kwance jikin gini ta rakube kanta dakaganta kasan ah tsorace take baccin,karasawa yayi gabanta wanda jin motsinsa yasata firgita ta tashi cikin sauri"don Allah kada ku dukeni wallahi banyi komai ba"tayi maganar cikin firgita tareda folding two hands dinta guri daya alamar roko takeyi.......
Cikeda tausayawa Sulaiman din idanunshi yaciko da kwallah,kamo hannun nata yayi sannan yace little Angel it's me kidaina tsorata Sulaiman ne,your Brother.....
Dagowa tayi ta kalleshi idanunta jage jage da hawaye harsun kumbura gawani baki datayi kwana biyun datayi ah prison din,cikin kuka tace Yaya Sulaiman!kafin tafada jikinshi cikin sauri kuma tajanye tana auchhhh tana dan taba jikinta,cikin sauri Sulaiman yace what's wrong?.....
cikin kuka tace don Allah kataimakeni ka fidda ni agurin nan kullum dukana sukeyi,'yar goge kwallarsa yayi sannan yace stop crying my dearest Sis,I promise I'll get you out of here as soon as possible kidaina kuka......
Dan shiru tayi tana shesheka tareda ajiyar zuciya seda yatabbatar tadaina kukan sannan yatashi yatafi cewa guards din yayi sukira mishi Sarkin yari, sanda yazo yace adaina dukanta and anabata abinci mekyau,gyada kai Sarkin yari yayi yayinda Sulaiman yafice agurin yana tunanin mafita, straight gurin Mai Martaba yawuce yana dakin shi bai fito fadaba don haka yazauna ah parlour yana jiranshi yafito,sanda yafita karasawa yayi gabanshu ya zauna sannan cikin girmamawa yagaidashi..........
Murmushi Mai Martaba yayi sannan yace,Babana Kaine da safennan?.
Eh Abba nazo infada maka ana nemana ah makarantar mu ne urgently......
Murmushi Mai Martaba yayi sannan yace auren naka bayazoba kabari in anyi sekatafi mana,sauran sati biyu kuma ga shirye shiryen da akeyi......
Dan gyara zama Sulaiman din yayi sannan yace bajimawa zanyiba nafada musu amma sunmatsamin intafi ne....
Dan shiru Mai Martaba yayi sannan yace toshikenan, Allah yakaika lafiya yadawo dakai lafiya.....
Amin ya Allah, godiya yayima Mai Martaban sannan yace da daddare in Allah ya yarda zamu tashi.....
Safe journey cewar Mai Martaban godiya yakuma yi sannan yafice ah parlourn........

****
tana kwance wuraren la'asar Ummi tashigo tana kallonta kafin tasamu zama gefen gado sannan tadubi 'yartata"yanzu ke anfada miki kuka shizaisa Babanku yacanza ra'ayinshi komi?".....
Jijjiga ma Ummin Kai tayi alamun aa batareda tace komaiba,fada Ummi tashigayi mata,inma zaki tashi gwanda kitashi kidaina wannan langabewar don ba sawa zaiyi acanza abunda akayi niyaba kinadai gani jarabawa ne agabanki gwanda kikwantar da hankalinki kiyi karatunki banason Ina ganinki haka......
To Ummi in sha Allah,taba jikinta Ummi tayi sannan tace ko kefa,bakida abunda yafi addu'a kilan wannan shine mafi alkhairi gareki,kicigaba da addu'a nima zantayaki kuma ma tunda Mukhtar ne nibana wani fargaba besides kunason junanku,so nibanga abun tada hankaliba.....
Ummi ni damuwa na Asiya she's blaming me for everything and on the other hand Yaya Mubaraq ma haushina yakeji sabida wai banfada ah gidaba....
Cikin rarrashi Ummi tace kada kidamu Mubaraq ze sauko Asiyan ma haushin naki for the mean time ne she'll calm down,kuma tayi laifi ai dole kifada ko?.....
Hakane cewar Asma'u din yayinda Ummin tace kitashi kiyi sallan laasar kifito kici abinci banason kunshewan dakike ah dakinnan don gobe dolenki kishiga makaranta.....
To Ummi,ta ansama Ummi din yayinda Ummi tafita itakuma tashige bandaki don dauro alwala,tun tana bandaki phone dinta ke ringing seda ta idar da alwalan sannan tafito tadauka Allah yataimaketa be katseba call din.Zahra ce ahankali tace"Zahra yakike?"...
Ah daya bangaren Zahra tace I'm fine,hope lafiya naga baki shigo school bayau.....
Murmushin dayafi kuka ciwo Asma'u tayi sannan tace kaina ke ciwo Zahra amma naji sauki in sha Allah gobe zanshigo....
Cikeda damuwa Zahra tace"alright then, Allah yabaki lafiya Asma'u sekin shigo goben".....
Thank you Zahra...
You're welcome,take care kigaidamin su Ummi....
Murmushi Asma'u takumayi tana dan goge ruwan fuskarta tace zasuji in Sha Allah kafin tayi hanging up call din,she wants to share her problems with someone sede batajin zata iya fadama Zahra bawai don bata yarda da itabane kawai dai she just don't feel like it's okay, lumshe idanunta tayi tana tuno kalaman Ummi data kecewa "besides kunama son junanku", tambayar kanta tashiga yi does she really love Mukhtar,kodai kawai she's just giving him a chance ne?....
She just know that she respect him very much and she trust him kuma tadaukeshi ah matsayin wanda yan gidan su sukeso  besides she always feel okay and happy when she's around him,may be this's the feeling da mutane ke Kira da love din, ahankali tafurta"that means I love Yaya Mukhtar?"....
Kasa bama kanta ansa tayi don haka seta tashi tadauki hijab dinta tashimfida sallaya ta tada sallah......

***
Daddy kuwa tunda yakira Mukhtar ajiya da daddare hankalin Mukhtar bakaramin tashi yayi ba don besan me Daddyn zece mishiba don haka tunda gari ya waye yashirya kan daya fito ah test zewuce office din Daddyn Asma'u din yasameshi,aikuwa yana fita ah test din yawuce gurin Daddy din,bayan sun gaisane Daddy yacemishi kaga nakiraka ko?...
Kan Mukhtar nakasa yace eh Daddy, murmushi Daddy yayi yace I'm sorry to announce this nayi deciding zan hada auren Asma'u da Asiya dana Yayansu sabida wani dalilina shiyasa nace barina kiraka infada maka if you're ready katuro parents dinka tunda naga kun fahimci juna and you've something doing......

Wani dadi ne yakama Mukhtar don kuwa yajima yana jiran wannan ranar, eh Kam he's not ready for the wedding as in betaba tunanin abun will be this soon ba hakana Kuma bashida matsala koda kuwa za ayi kwana kusanne tunda ba aikinyi yarasa ba because bawai karatun kadai yasaka ah gabansa ba yana business sosai.....
Murmushi yayi sannan yace babu komai in sha Allah zanyi magana da mutanen gida....
Dan numfasawa Daddyn yayi sannan yace hope dai ban takuramaka ba? ...
Eh Daddy babu takura wallahi, Allah yasanya alkhairi aciki, nagode kwarai.....
Murmushi Daddyn yayi sannan tace to Masha Allah,yayi kyau,sundan yi hira duk akan business dakuma karatun Mukhtar din kafin yayi ma Daddyn sallama yatafi...
Aslam kuwa dake ah kaduna yake besamu shigowaba se yanma don haka ah gida yasamu Daddyn yanda sukayi da Mukhtar haka yayima Aslam din sede yafadamishi duk abubuwan da Asiya tayi amma dukda haka Aslam yace ya yarda zeyiwa mahaifinsa magana don bakaramin so yakema Asiya ba tunda daman yakeson turo iyayenshi itanedai tahanashi, mahaifin Aslam da Daddy business partners ne wanda tsabar shakuwarsu sunzama kaman family.........
***
Tunda safe dayabar parlourn Mai Martaba yakoma bangarenshi yasaka  kuyangunsa suka shiga hada mishi kaya,seda aka hada tas aka ajiye gefe daya sannan yafice yabar gidan bashi yadawoba se karfe tara na dare,shima saka dogarinshi Isah yayi wanda sun saba yafitar mishi da kaya zuwa mota shikuma yashiiga wanka,seda yayi wanka yashirya tsaf cikin kananan kayanshi sannan yaci abincin da aka kawo mishi,duba time yayi karfe goma darabi,lumshe idanunshi yayi sannan yafice straight gidan yari yawuce nan yasa guards din suka bude masa cell din da Afiyan ke ciki idanunta biyu bakaman dasafe daya sameta tana bacciba, murmushi yasakar mata wanda bawai yakai har zuci bane kawai dai just to give her courage,gaidashi tayi ahankali sekuma ga hawaye,kama hannunta yayi sannan yace taso zaman ki anan yakare Afiya...
Cikin sauri ta tashi tasa hannunta cikin nashi tarike kakam haka suka fito daga cell din,duban guards din sukayi du kansu ah kasa dukda kuwa wani irin tsoro ne ah tattare dasu sede babu halin magana don basu Isa suyi questioning din Yarima guda ba,cikin sauri yace kibiyoni nan sukabi tawata kofa inda ba mutane sosai harsuka isa Mota cewa yayi tashiga,kallonshi tayi sannan tace "where are we going daman bagurin su Ummi zaka kainiba?"....
Ahankali yace,"I'm sorry you can't meet them now, I've to take you somewhere far kafin musamu solution Afiya just trust me.....
Goge kwallarta tayi sannan tashige motar,driving yafarayi har suka bar masarautar fatanshi daya  Allah yasa har yabar garin Zaria kada Magajiya tasamu labari...


Post a Comment for "GIDAN SARAUTA CHAPTER 2"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...