Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

GIDAN SARAUTA CHAPTER 12

GIDAN SARAUTA CHAPTER 12

- - Post a Comment
GIDAN SARAUTA 


CHAPTER 12Tare sukayi sallar maghrib da Isha kafin suka dunguma suka koma dakinsu Afiya din don Asma'u hanasu zaman parlour tayi tana zasu saka tsamin jikinsu bayan sunsan Mijinta zaizo da bako,Wanda dukdai maganar cikin zolaya akayita Afiya ne tasaki baki tana"mekike nufi Sis".....
Dariya Asma'u tayimata tareda cewa"ke wasa nike muku ammadai kinsan babu dadi yashigo da bako susame mun baje ah parlourn ko"........
Amiran e tace"kedai kawai kin hanamu zaman parlour yau sister in-law",nan suka shige daki suna mitar zolaya,dukwannan maganar dasu Afiya ake ita

dai Hamida se dariya datake binsu dashi.........
Karfe takwas saura Almustapha,Sulaiman da Dr Na'im suka shigo tare yayinda suka yada zango ah parlourn Sulaiman kam ko zama baiyiba yawuce ciki kai tsaye don ganin abun son sa Sumayya because yanzuma daga bangaren su yake batacan hakan ya tabbatar mai da nan din tazota,dakinsu Amiran yashiga inda yake kyautata zaton samun ta sede da mamakinsu bata dakin su hudu ne kawai baje kan gado kallon Asma'u yanayimata sign da hannu na Ina sumayyar tashiga wanda hakan yabama Yan uwansa dariya"tana bangarensu cewar Hamida".......
"She's not there", yakarashe maganar cikeda damuwa suma da mamaki suka kalleshi don ah tunaninsu can tayi sabida damunta dazukayi da tsokana ne tundazu yasata yin fushi tatashi tafice ah sashin nasu anan ne Hamida ke maida mishi yanda akayi cikin sauri yafice yana mamakin inatayi to?............
Koda yawuce su Almustapha ah parlour bekulasu ba jijjiga kai Almustaphan yayi in desbelief yayinda aranshi yake fadin"Yanzu haka sabida wannan karamar yarinyar yake wannan rawar jikin and yanada tabbacin ko fadama Asma'u isowarsu baiyiba wannan dalilin yasashi tashi tareda cewa Na'im din inazuwa".......
Dakinta yafara zuwa batanan don haka seya shiga kiran layinta kawai tananan zaune tareda kannen nashi taga call dinshi yashigo ahankali tatashi tafice zuwa dakinta don ko lura da Na'im dake parlour batayiba,tana shiga dakin tayi recieving call din yayinda shida yariga yaganta yayi hanging up tareda maida wayar aljihunshi dan tsaki tayi tana rufe kofar dakin"seyawani kira mutum amma bazaiyi magana ba don wulakanci,Ina zaman zamana yatasoni", takarashe maganar tareda juyowa tana kallon dakin sede da mamakinta taganshi dab da'ita bakaramin tsorata tayiba wanda hakan yasashi saurin riko hannunta yana"Dawa kike?"....
Kame kame tashigayi tana kokarin kwace hannunta amma yaki saki sema sa dayan hannun dayayi yatare kofar baki dayanta yanda bazata iya gudu ba kafin ya matsar da fuskarshi dede nata ah kasan makoshi yakuma cewa"tambayar ki nikeyi fa?",wannan karan hartanajin saukan numfashin sa akan fuskarta.........
Kaman zatayi kuka tace"bafa dakai nake ba Yaya am"......
Kallon dan karamin bakinta yayi yanajin kaman yayi kissing amma yasan tana iya yimashi rigima yanzu besides bashi kadai bane bare ya biyemata Yana tareda bako kawai se sakin yayi murmushi kafin yace"silly girl kawae",ware idanu tayi akanshi tana mamakin abunda yafada sede kafin ta ankara har yakai mata light kiss ah kumatun ta wanda yasata blushing batareda tashiryaba kafin yasaketa yafice yana "we're waiting for you",itadai tana tsaye gurin kamar sokuwa dakyar ta'iya neman mayafinta tasaka sannan tabi bayanshi Itama daukan trayn abincin tayi takai musu parlourn tareda komawa tadauko na drink data tanadar musu se tea agefe wanda ta'ajiyene don Dr Na'im din yazabi daya cikin tea da drinks din tunda batasan wanne yayi preferring ba.............
Zama tayi tana gaidashi"Ina wuni"...
Murmushi yasakar mata tareda ansawa"Lafiya Lau Amarya,yakike yafama da abokina?",yayi maganar yana kallon Almustapha cikeda zolaya.....
Itadai murmushi kawai tayi sannan tawuce ciki don barinsu suci abinci dukda talura yanaso su taba hira amma gabadaya Almustapha yayi kicin kicin da fuska, bayan tafiyarta ne Dr Na'im din yadubeshi yana...
"ka korarmin matar taka hankalinka yakwanta ai"......
Tabe baki yayi kafin yace"takori kanta dai,I didn't ask her to go right?".........
"From your face Imam,from your expression nagane komai bare itada take matar ka", Na'im din yayi maganar cikeda zolaya yayinda yakarada nimadai ba inyi zuciya inyi auren nan ko za adainamin gori Kuma nima inhana mutum hira da Matata,dariya Almustapha yayi kafin yace"kazo kaci abinci".......
Tsaki Dr Na'im din yayi tareda dan shafa kanshi"au dariya ma nabaka,dole kayimin dariya tunda i was stupid dana manta kai wayene wurin rashin kula mutane"........
Haka Dr Na'im din yasauko Almustapha yayu serving nashi calmly suka fara cin abincin tare don Na'im dagewa yayima saisun ci ah plate daya ahaka harsuka gama Asma'u tafito bayan Almustapha yasha kwaretete gun Na'im na cewa"nifa bagunka nazo ba gurin matarka nazo so, kabari mugaisa dakyau",hakan yasa yashiga yakira mishi ita sunkuwa taba hiran kadan sannan yace Ummi dasu Afiya fa?..........
Suna ciki, murmushi yayi sannan yace"su bazasu zo sugaida sabon Yayansu ba?".......
Dariya Asma'u tayi kafin tace"ba inyi musu magana Dr"......
Shima dariyar yayi yana"to shikenan",Ummi tafarayiwa magana tafito suka gaisa da fara'arta as usual hakanan bakaramin Jin dadin ganin abokin Almustapha din tayi ba for the first time in her life hakanan takoma daki tana ta sanya musu albarka"........
Ahaka su Afiya suka fito harda Hamida da Asma'u tasata fitowan dole tunda suka fito ah dakin yake kallonta,"she's very beautiful and matured ga yanda take tafiyar cikeda nutsuwa bakaramin tafiya da imaninsa yayi ba hakanan lokaci guda zuciyarsa tashiga raya masa"she's the girl Na'im,the right girl you've been waiting for"........
Hamida da taga yacika kallo gashi kallon dayake mata yanasata jin wani iri hakanan tunda tafito takejin gabanta na mugun faduwa dakyar tayi karfin halin dagowa ta kalli cikin idanunshi tareda galla mishi harara sannan tafaki idon mutane tana nuna mishi cikinta aranta tana fadin"daga gani zaiyi son mata, ammadai anji kunya godai godai dashi ko lura da cikin datake dauke dashima baiyiba".....
"Na'im daya ga abunda tayi bakaramin faduwa gabanshi yayiba shima hakanan lokaci guda kunya ta lullube shi wanda hakan yasashi kasa zama sema tashi dayayi aranshi yana"Ya ilahi, what have I done now?",don carab idanunshi sukamai kyakyawar gani ga Dan karamin cikin datake daukedashi dakyar ya'iya duban Almustapha yace"I'll be on my way Yarima".......
Da mamaki Asma'u da Almustapha suka dubeshi dondai basuji yace zaitafi dawuri hakaba besides shiya ce akira mishi su Afiya su gaisa,ganin kallon tuhuman da Almustapha keyi mashi ne yasashi sosa kanshi kafin yace"I'm really sorry Buddy yanzu akayi texting kan ana nemana ah gida".......
Almustapha dai kawai gyada mishi Kai yayi badon ya yarda ba don shidai baimaga sanda yadaga phone dinshiba bare har yayi recieving massage,su Amira suka gaidashi fuskarsu da fara'a banda Hamida daketa faman galla mai harara ansawa yayi nervously kafin yayi musu sallama yafice har mota Almustaphan ya rakashi kafin yadawo cikin gida..........
STORY CONTINUES BELOW

Wuraren goma da rabi Ummi taleko dakin nata inda tasamu duksunyi bacci kan makeken bed din hakanan sunbar wuta akunne gashi ko lullube jikinsu basu yiba,da murmushi tasaki tareda karasawa cikin dakin sannan tadauki blanket ta lulluba musu tana kallon fuskar Hamida cikeda tausayawa kafin tadan shafa fuskarta ahankali aranta tana hamdala da yarinyar tagane gaskiya cikin gaggawa and she's ready to get along with her siblings............
Bitayi kansu duka tayi kissing forehead dinsu wanda yazame mata al ada akullum indai har tazo dubasu harta iso kan Hamidan,itamma yimata tayi wanda hakan yasa Hamida farkawa don baccinta baiyi nisa ba murmushi Ummi tayi tareda tashi tana"I'm sorry na tasheki ko?".......
Girgiza matakai Hamidan tayi sannan tatashi tazauna tana"I'm sorry Aunty Khairiya".......
Ahankali Ummi tace "For what?"
Hamida sauke kanta kasa tayi kafin tace"for torturing your children and for everything that my Mother has done", takarashe maganar yayinda idanunta suka ciko da kwallah don haryanzu abun na matukar damunta and she really find it hard to believe cewa su Afiya sun yafemata so easily haka don koyau kawai kallonsu take da mamaki tun dazun.........
Dan shafa fuskarta Ummi tayi tana"Miyena zubda hawayen kuma ba ancemiki yariga yawuce ba?".....
Gyada kai Hamida tayi tana goge kwallarta kana tace"Thank you Aunty Khairiya"......
Jijjiga matakai Ummi tayi tana"Ummi dai ko,indai you're really sorry for everything kina kirana Ummi, I'm your Mother too"........
Murmushi Hamida tayi sannan tace"Thank you Ummi",Yar dariya Ummin tayi tana"kokefa,kwanta kiyi bacci abunki I'm going to my room too"......
To tace kafin takoma takwanta din tareda lullube jikinta haka Ummi tafice ah dakin bayan takashe musu wuta sannan taja kofar dakin tarufe........
Sulaiman kuwa tun fitan shi bangaren su Sumayyan yasake komawa aikuwa yayi sa'an samunta wannan karan don da alama sabani sukayi,Allah ma yataimakeshi su Dad baswa parlourn da alama sun shiga already.........
Zama yayi gefenta ah bakin gadonta tareda cewa"Sumyna",dukda yanda muryarshi tayi affecting dinta hakan besa ta kulashiba sema chat dinta data cigaba dayi fuskar tausayi yayi tareda kama duka kunnuwanshi"I'm sorry Dear kinsan dai bazan cigaba da jure fushinki agareni bako?"......
Batareda ta kalleshi ba tace"kana damuna fa"......
Dukda yaji haushin maganarta amma seya daure zuciyarshi tunda shikenama komai akamishi zai karba hannu bibbiyu don haka seyasa hannu yakarbi wayan hannunta cikin sauri tadago daniyar yi masa masifa amma idanunta nasauka cikin nashi tanemi duk wasu kalamanta tarasa ahankali yakuma cewa"I said I'm sorry ko?"........
Ganin tayi shiru ne hakan yabashi daman janyota yadaura kanta ah kafadunshi tareda cewa"I love you Sumyna kiyi hakuri kidaina fushi dani please",cikeda tausayinshi tace"yawuce".........
Murmushi yayi cikeda Jin dadi tareda dagota daga jikinshi yana fadin"Thanks Love".......
Itama murmushin tasakar mai daganan akashiga hirar soyayya kuma wanda inkagansu bazakace sune sukayi fada recently ba........
Yaukam Asma'u batama tsaya har Hajja takoreta ba tana gama shirinta tawuce dakinshi sede yaudin samunshi tayi kan sallaya yana sallah da alama baidamu yayi shafa'i da wuturinshi ah masallaci ba yataho gida karasawa tayi bakin gadon sannan takwanta tareda lullube jikinta kan kacemai bacci yayi awun gaba da'ita shima yana gama addu'o'inshi yataso yazo yakwanta tareda janyota jikinshi calmly,hakanan kwanan nan yakejin inba ajikinta yayi bacci bazaiji dadi ba,he always find comfort when he's with her,wrapping hannunshi yayi ajikinta hakanan zuciyarshi na raya mishi anya zai iya rabuwa da'ita kaman yanda takeso,don tariga tazama wani bangare na rayuwarshi.............
****
Bangaren Zaliha ganin Sulaiman dagaske yakeyi washegari tun safiyar Allah tayi bangaren su Sumayya don Lantana tace mata aitaxota gida...........
Sumayya daketa sharara bacci Mom tashigo tana tashinta,mika tayi ahankali tana...
"Mom kibarni inyi bacci bankwanta dawuri bafa jiya"........
Wani makan Mom takaimata tana"banason iskanci kinmasan karfe nawa ne tukunnan?"......
Jijjiga kai tayi tana murza idanunta alamun batasani ba cikeda bacin rai Mom tadubi Zaliha dake gefenta tana"kinganta ko batada aiki se shegen bacci kaman wata kasa,kafin tamaida kallonta da Sumayyan data bude idanunta yanzu tana"kitashi joor kinada bakuwa and it's pass 10 already".......
Tashi Sumayya tayi don ganin wayene yayinda Mom tafita tabasu guri don itadai batakawo komai aranta ba tunda tajima dasanin Zaliha nada hankali hakanan tana fatan zasuyi zaman lafiya koda Sumayyan ta ta auri Sulaiman din shiyasa ma da akayi zancen jiya bataji wani dar dar sosaiba...... ..
"Ina kwana",Zaliha tagaida Sumayyan badan ranta yasoba cikeda mamaki Sumayya ke kallonta yayinda batasan sanda ta galla mata wata uwar harara ba because batamanta abunda tayi mata ta waya ba hakanan kuma tanajin matukar kishin Sulaiman din haryanzu.........
Karshe ma sauka tayi daga kan gadon tareda yin hanyar bandaki dasauri Zaliha tabita tana...
"Sumayya kitsaya muyi magana please"........
Batareda Sumayyan tajuyo ba tace"You've nothing to tell me so,you better leave my room kafin ma nafito daga bandaki",babu abunda kakeji se karar rufe kofar toilet din Zaliha wani irin cizan lips dinta tayi cikeda takaici hakanan jitake kaman ta shake Sumayyan amma yata iya,dakyar ta'iya rarrashin kanta takoma tazauna,tananan zaune har Sumayyan tafito da mamaki tace"au dan jaraba baki tafi ba?", Sumayya tayi maganar tareda rike kugu kafin takarada"what do you want!"......
STORY CONTINUES BELOW

Ahankali Zaliha tataso takaraso inda Sumayyan take kamar wata mutumiyar kirki kafin tace...
"I'm here to say sorry for the other day,kiyi hakuri don Allah I said so many things to you cikin zafin kishi"........
Atakaice Sumayya tace"Yawuce",cikeda Jin dadi Zaliha tace"Thank you".......
Wani harara Sumayya ta dakamata kafin tace"that does not mean we'll be back to normal besides I can't trust you".........
Zaliha nashirin magana Sumayya tanuna mata kofar dakinta alamar tafice mata ah daki bata bukatan wani bayani cikeda takaici Zaliha tafice tana"lallai yarinyar nan senayi dagaske naga alama",daganan bangaren su Asma'u tawuce inda tagaida Ummi, Ummin ma cikeda fara'a ta amsa gaisuwar ta tana"Uwargidan Sulaiman ko?"....
Gyada kai kawai tayi tana murmushi kamar wata mutumiyar kirki kan kacemai Ummi da saurin sabo harsun barkeda hira hakanan su Hindatu suka kawo mata kayan motsa baki dukda suna mamakin wai Zaliha ce ah bangaren Ummin harma tazauna suna hira bayan basu manta abubuwan da tayima Asma'u ba hakanan basumanta complain din da bayi keyi akanta ba dabadan kada Asma'u tace sunyi gulma ba babu abunda zaihanasu zuwa su fada mata halin da ake ciki sede ko minti talatin ba akaraba Asma'un dasu Afiya suka fito parlour don yin breakfast because suma yau suna gida kasancewar weekend ne, bakaramin mamaki sukayiba ganin Zaliha ah bangarensu koda ta gaidasu sama sama suka amsa yayinda Amira da Afiya komawa ma daki sukayi suna sunkoshi.............
Itadai Asma'u tabe baki tayi aranta tana fadin...
"Gwanda dakika tuba hakan zaifi miki alheri".......
Ummi ne tatashi tafice don zuwa gunsu Afiya because kwata kwata bataji dadin abunda sukayima Zaliha dinba wanda duk ah tunaninta sabida Sumayya sukeyin hakan.......
Tana shiga tace"kudin miyene kuka wani dawo daki kaman wanda kukaga dodo?"....
Turo baki Afiya tayi"Ummi bakisan matarnan bane shiyasa kike hankilo",dakuwa Ummi tayi mata tareda nunata da yatsa"Afiya kifita idanuna inrufe,banason shashanci fa yarinya tazo har inda kuke sannan kuce zakumata wulakanci sabida kishin banza,to wallahi kushiga taitayinku banason wannan haukan kadama kuce zakusama Sumayyan ma arai barai har Sulaiman yakasa samun zaman lafiya ah tsakanin iyalinshi".....
Amira nashirin magana Ummi tace"inkikamin wani magana bugan bakin ki zanyi kutashi kukoma parlourn kuci abinci tunkafin raina yabaci, yarinyar kirki yar albarka tunbanda lafiya take zuwa gaidani sannan yanzu zakuzo Kuna kishi da'ita don hankali bai ishekuba?"cewar Ummin tana kallonsu harsuka fice ransu bace kafin tawuce dakinta tana mamakin abunda sukayi din wanda bakaramin batamata rai yayi ba because bata taba tsanmanin hakan daga garesu ba.........
Ah parlourn suka samu Asma'un da Zaliha nacin abinci don tun bayan fitan Ummin tayi mata bismillah itakuma babu musu tazauna suna ci don neman samun guri,sunata kumbure kumbure suka zauna suka shiga cin abincin itadai Asma'u abunma dariya yaso bata seda suka gama sannan Zaliha tadubesu kana tace"Asma'u nazo inbaku hakuri ne daman kan abubuwan dasuka faru abaya".........
Murmushi Asma'u tayi sannan tace"karki damu yawuce",kamar dagaske Zaliha tace"kiyi hakuri dai still kiyafemin,I know I've wronged you so many times"......
Kekam banace Miki yawuce ba,nayafe miki Allah yayafe mana baki daya and it's good that kingane laifuffukan ki sekuma kinemi tuban Bayin dakika cuta inaganin shine mafi mahimmanci ayanzu"....
Zaliha dakyar ta'iya daure zuciyarta kafin tace"hakane Kuma sede bansan dawani fuska zan kallesu ba kozaki tayani neman yafiyarsu?".......
Murmushi Asma'u tayi tana"zanrakakidai kinemi yafiyarsu dakanki inaganin zaifi".......
To cewar Zalihan tana murmushin yake hakanan duk yanda taso su Afiya subata fuska kisukayi donsu gabadaya Zalihan bata kwanta musu ba gani sukeyi dawani abun tazo kuma ahaka har suka fice tareda Asma'u zuwa bangaren Bayin nan tatarasu tanemi yafiyarsu kaman da gaske sukuwa sukace sun yafedin kafin tayima Asma'u godiya tana"zanshi anjima muyi hira inba damuwa".......
"You're always welcome Aunty Zaliha", Asma'u tayi maganar fuskarta daukeda murmushi ba'ita tabar gurin ba har saida Zalihan takule mata da kallo yayinda ahankali tasauke ajiyar zuciya tana gode ma Allah dakomai yake tafiya daidai yanda yadace ahaka harta koma bangaren su dakinsu Afiya tawuce tana"miyene kukayita wani huhhura hanci agabanta?",cikeda bacin rai Amira tace"yanzukai after all that she did kinyafe mata?"....
STORY CONTINUES BELOW

Da mamaki Asma'u tace"Why not,Allah ma mukanyi laifi yayafe mana bare mu bayinsa besides ku jiya bayafewa Aunty Hamida kukayi ba?".........
Dafe Kai Amira tayi tana"you'll never understand, Aunty Hamida and Zaliha sun banbanta".......
"Hmmm"shine abunda Asma'un tace kafin takarada"sabida itaba yar uwarku bace komi?"
"Wallahi bahaka baneba,kawaidai munaji ajikin mu she's not worthy of getting our Trust sister in-law", Amira takarashe maganar tana rike da hannun Asma'u just trying the best she can gurin sa Asma'u tagane......
Ahankali Asma'u tacire hannunta cikin na Amiran tana"kudai kawai kuna taya Yar uwarku kishi ne shiyasa bazaku taba ganewa ba", Afiya dake gefe tace"Amira kimadaina bata bakinki nidaman nasan dakyar inzata yarda itada Ummi halinsu daya,they're Soo softhearted shiyasa ake cutansu akullum",itadai Asma'u dariya tayi tareda ficewa daga dakin ah hanya suka haduda Iya Jamila da Hindatu cewa sukayi"Gimbiya daman munason muji in Yarima yafitane?".......
Murmushi tayi kafin tace"Baitashi ba tukun wani abun ne?"..........
iya Hindatu ne tace"Daman gyaran dakinshine zamu fara kafin muyi nasauran",cikeda mamaki Asma'u tace"gyaran dakinshi Kuma,dondai ah iya saninta itake gyara dakinshi kullum Kuma suma sunsani ranaku daidaiku takesa Jamilan ko Hindatu sabida dasubiyun kadai tayarda".....
"Eh Gimbiya daman ana gyaran gida baki daya bayan karshen ko farkon kowani wata wanda yazamanta al alda ah masarautar,za yi karkade karkade dakuma goge sosai", murmushi Asma'u tayi tana"oh sanitation?"......
Gyadamata Kai sukayi kafin tace"kuyina sauran guraren kawai inya tashi nizanyi na dakinshi dakaina"..........
"Ayi haka Gimbiya kada aikin yayi maki yawa",karku damu ainace zan iyako kuma in inaneman taimako zankiraku insha Allah,gyadakai sukayi tareda yimata godiya kafin sukawuce donyin nawasu bangare na gidan itakuwa dakin nashi tawuce"still yana kwance yana baccin shi hankali kwance don sai wurin takwas yakoma baccin tun bayan sallar asuba", ahankali takarasa bakin gadon nashi tareda zama tana karema kyakyawar fuskarshi kallo yayinda tasa hannunta cikin gashin kanshi aranta tana fadin "Sleepy head kawai",donta lura Almustapha mutum ne mebama bacci hakkinshi gashi wani irin kyau nadaban yakeyi mata inyana bacci,his face will look so innocent, simple,fresh and cute like a Baby hakanan ta tsinci kanta da ciro wayarta tashiga daukanshi hoto wanda hasken flash din yasashi yin motsi cikin sauri tatashi tana boye wayar abayanta kamar munafuka,bude idanunshi yayi tareda dorasu kanta dasauri tajuya tanayi kamar me neman abu cikin sauri yajanyota tafado jikinshi arude tace"Yaya Imam miye haka?", takarashe maganar tana kokarin tashi daga jikinshi sake matseta yayi ah jikin nashi yana"wakike dauka ah hoto?"..........
Kaman zatayi kuka tace"nina dauke ka ah hoto,badai niba sede in mafarki kayi",tayi maganar tana dauke kanta daga kallonshi sabida yanda idanunshi sukesata Jin wani iri.........
Murmushi yayi tareda dagata daga jikinshi kafin yamaida ta gefenshi tareda dora kanta kan kafadunshi yana"Just tell me you want snap with me basai kinmin satar hoton fuskataba", ashagwabe tace"nifa ban daukeka hotoba".........
Kallon fuskarta yayi wanda suke dab danashi kafin yayi kissing karan hancinta dayasata shivering batareda ta shirya ba cikin dabara yakarbi wayar hannunta kafin yamaida kanshi kan wayar yashiga dubawa aikuwa ga hotunan duk sunyi kyau hakanan sunkai su goma cikin rada yace"what's this?".......
Still cewa tayi"nifa bani na dauka ba",Yar dariya yayi cikeda mamakin ta sannan yabata wayan tareda cewa"to kidauka yanzu,fuskar Almustapha is yours kiyi yanda kikaga dama dashi"..........
Cikeda jin kunya da mamakin abunda yacedin tace"dagaske?",tana blushing ........
Gyada mata kai yayi ahankali yayinda tadaga wayar tana setawa daganan tashiga yi masu selfie seda tadauki yakai biyar ah position daya suke wanda dan gwanda ita tanama cuccuna baki tareda daga hannunta sama cewa tayi"Yaya Imam kana canza style mana", ahankali yace....
"I don't know how to",batareda tadamu ba tace"I'll teach you then", because bakaramin dadin moment din takeji ba ahankali tasakalo hannunta ta wuyanshi tareda daga fingers dinta biyu tana pouting mouth dinta"Yaya Imam dukyanda nayi haka zakayi",dariya abun yakusan bashi amma besan dalili ba seya tsinci kanshi dayin yanda tacedin yakai sau uku tana sashi suna canza style kafin tashiga gallery din suna kallon pictures din dan tsaki tayi tana"Not that bad but it should have been more romantic"..........
Cikeda mamakinta yadubeta don yasani tsaban excitement ne yasata fadin hakan batareda ma tasani ba,dan mischievous smile yayi sannan yace"oh really?"...
Juyowa tayi tana kallon fuskar shi dake kan pillown da nata yake hakanan suna facing juna ga numfashin juna dasuke iyaji saiyanzu tama gane baran baramar da tayi kanne mata ido daya yayi mischievously kafin yace"I think we should make it romantic tunda kinaso?".......
Yanda yayi maganar seda yasa tsikar jikinta tashi baki daya hakanan tasaka cewa komai se zuciyar ta dake aikin racing non stop ganin tayi shiru ne yasashi matso da fuskar shi kusa da tata sosai kafin yakai bakinshi kan cheeks dinta cikin rada yace"like this?"....
Wani irin ajiyan zuciya tasauke tareda lumshe idanunta batareda ta shirya ba shima dago fuskarshi yayi daga gefen fuskarta kafin yadaura ah goshinta yana sake yin kasa da murya"ko haka kike nufi?"yakarashe maganar yana sauke idanunshi kan pink lips dinta dayasha wet lips itama lips dinnashi take kallo adoringly tareda hadiyan wani abu ah makoshinta kawai jitayi yasaka bakinshi cikin nata yayinda yashiga kissing dinta gently Asma'u batasan sanda tashiga maida mai martani ba hakanan batamasan sanda wayartata tayi slipping daga hannunta ba aka shiga aikin lada, Almustapha wasa da ita yakeyi sosai batareda dukansu sun shirya ba abu daya suka sani,shine ruhi da gangar jikinsu ne kawai ke aiki awannan lokacin hakanan sunfi mintuna ashirin suna abu daya yayinda dakyar Almustapha ya iya controlling kanshi badon yagajiba sedan ganin yana kokarin wuce gona da iri Itama sannan yalura oganniyar ma batada niyan hanashi,janyeta yayi daga jikinshi jiki ah sanyaye kafin yatashi yashige bandaki donyin wanka Asma'u lumshe idanunta tayi cikeda kunyar abunda sukayi din hakanan zuciyarta nacigaba racing dukda kokadan batajin nadamar abunda yafaru ah yanzun sema dadi,wani irin feelings din da itakanta takasa fassarashi kallon riganta dake gefe tayi wanda shaddace akamata riga da skirt hakanan bakaramin kudi aka kashe wurin dinka kayan ba donyaunema rana tafarko datafara saka kayan ah kasalance tasa hannu ta janyo rigar duk ta cukuikuye tayi wani iri kaman ba rigan bane ke daukeda shatin guga dazu rufe fuskarta tayi da rigan cikeda Jin kunyar kanta kafin tatashi tana gyara hook din bra dinta hakanan tana tunanin tayaya ma zata iya fita dawannan kayan fisabilillahi, inta hadu dawani fa.yazatayi?"...........
Tana tunane tunanenta ahaka dai harta maida rigan jikinta yayinda tatashi tsaye tana gyara skirt din da duk ya cukuikuye shima,tafi minti biyar tana sakada warwaran yanda zata fita tabar dakin batareda tahadu da kowa ah hanyartaba kawai seji tayi yana shirin bude bandaki aidagudu takoma kan gadon talullube cikin bargo yanajin ta amma sebe kulataba sema wucewa dayayi gaban madubi yana daure da towel ajikinshi yayinda karamin towel din kekanshi yana kokarin tsane ruwan kannashi.........
Itadai kasa ciro kanta daga bargon ma tayi kwata kwata haryagama shirinshi cikin kananun kaya kasancewar weekend ne kuma bayida niyar fita yaudin koda kuwa fada ne.......
Zuwa yayi bedside din tareda daukan phone dinshi daniyar ficewa gun Ummi amma seya tsinci kanshi da yaye bargon daga kanta yana"Bacci kikeyi ne?",dukda kuwa yasan idanunta biyu neman magana ne kawai ......
Kaman zatayi kuka tajuya mai baya murmushi yayi don yasan dalilin dayasa haryanzu take dakin nashi kafin yace"Lemme bring you another cloth from your room"........
Aida sauri tatashi tana"aa Yaya karkaje don Allah",damamaki yace"Why?".......
Wannan karan har idanunta sunciko da kwallah tace"Hajja nananfa",in an I don't care manner yace"semenene to, kodai kinason kice yinimin zakiyi ah daki batareda kin fita ba?"........
Pouting bakinta tayi tana"nibance ba besides zanmaka gyaran dakinka ma daman se inyi yanzu kawai"..........
Da mamaki yace"bakinyi shara da safe ba?",don bai mantaba ba yashigo yasameta tana gyaramai gado yauda safe.........
Atakaice tace"Nayi, sanitation znyimaka as usual kaman yanda akeyi", takarashe maganar tareda tashi sabida irin kallon dayake mata yanasata jin wani iri janyota yayi jikinshi yana...
"you don't have to do that"......
Janyewa tayi daga jikinshi kafin takarasa gaban wardrobe dinshi tana karema gun kallo hakanan idanunta suka sauka kan drawer din dake rufe gam da padlock daga gefe wanda bayau tafara ganiba hakanan akullum tana mamakin miyasa bai rufe sauran ba se wannan in particular bayan shidinma wardrobe ne kamar sauran sede Allah baitaba bata ikon budan baki ta tambayeshi ba bude wardrobe din kayanshi tayi tareda daukan pjamis nasa da riga tawuce bathroom tana"Atleast dai kabarni ko kayanka ingyara maka ko?".....
Shidai duk yana kallonta harta fito sanye da kayan sannan tace"i can work with energy now"......
Girgiza kai kawai yayi ganin batada niyar bari din dukda yace tabaridin yayinda ahankali yace"I'm going out",to kawai tace mishi haryakai bakin kofa tace"Yaya imam"......
Kallonta yayi kafin ahankali tanuna mishi drawer din dake kulle da padlock din"the keys?".......
Cikeda kagara yace"kibarshi basaikin taba nanba"........
Batareda tadamu ba tace"miyasa zanbarshi bani nayi niya ba?"....
Dafe kanshi yayi aranshi yana"this girl bazata kasheniba",yayinda afili kuma yace"Because I don't actually know where the keys are",daganan bejira cewartaba yayi ficewarsa Itama tabe baki tayi sannan tashiga fito da kayan wardrobe dinnashi dukdama komai fa agyare yake fes fes amma hakanan takejin urge din tasake gyara mishi din........
Ahaka hartagama fidda na wurinda shaddodinshi yake sannan tadawo gun kananun kaya ananne taga keys ahankali tadaga tana"wayasani ma ko keys din drawern ne dayake cewa baisan inda yake ba",tayi maganar tareda karasawa gaban drawer din da niyar budeta..........
★★★
Mai Martaba tun ah jiyan yasa asanar da mutanen Fada kan cewa yau akwai zaman dayakeson suyi ah Fada karfe shadaya na safe shiyasa ma yau fadan yake acike babu wanda ake jira sai isowan Sarkin shima kuma baiyi wani African time ba don shadaya da yan mintuna yakaraso Fadan wanda aka bude taron da addu'a kafin yafada musu kudurorinsa na bude taron dabai wuce duk akan maganar nadin Sarautar Almustapha bane ba dakuma other post dayake tunanin xa'a bayar tunda waziri ma Allah yayi mishi rasuwa and Galadima betrayed them so they need some change now.............
Sosai sukayi na'am dazancen nashi yayinda sukayi suggesting Dad yazama waziri se abama Sulaiman Galadima tunda sudin ya yarda dasu kuma mutane da dama sungani sunkuma shaida cewa sudin mutanen kwarai ne, Mai Martaba bakaramin dadi yajiba jin kalaman daga bakin yan fadan yafito batareda shi yafara furtawa ba yayinda yayi hamdala ga ubangiji tareda cewa"shima daman abunda keranshi kenan amma yafison yafara jin raayinsu tukunnan tunda kuma sunyi na'am dazancen to alhamdulillahi".....
Dad dake gefe ne yace nidai daza abi tanawa da anbarni inji da tsufana ma tukunnan,dariya dagaci yayi yana"sokake kasake guduwa ko to wannan Karan baka isaba"......
Murmushi kawai Dad yayi yana hidin Allah yasa hakan shiyafi alkhairi to tunda kun takura,Amin suka amsa da yayinda daya daga cikin mutanen Fadan yace "Sarkin dawakai fa baida lafiya kuma jikinshi yayi tsanani sosai wannan dalilin yasa yace insanar muku cewa inda hali adaura wani akan wannan position din donshi baya tunanin zai iya yanzu",jiki ah sanyaye Mai Martaba yace"cuta aibayana nufin karshen duniya bane ba, insha Allahu zaisamu sauki kada yadamu".......
Wani ne yace"nidai bnsan dalilin dayasa yafadi hakan ba amma tunda yabukata din ayi hakan kawai besides zamubar abubuwan mu ne babu tsaro?".......
Jinjina kai sauran sukayi yayinda Mai Martaba yace toshikenan zanyi tunani akan zancen Dad ne yayi saurin cewa....
"why not abama Mallam Hudu wannan matsayin inma Sarkin dawakan yasamu sauki basai yakoma bakin aikinshi ba"......
Cikedajin dadin shawarar Dagaci yace"tabbas wannan ma shawarace mai kyau don Mallam Hudu mutum ne mai amana da sanin yakamata tuni najima dasanin haka",jinjina kai Mai Martaba yayi donshima bakaramin girman mutumin yake ganiba dubada yanda yarike masa amanar iyalinsa na shekaru da dama........
Ahankali yace"to shikenan sekuce Ina nemansa"......
Cewa sukayi to insha Allah kafin akadawo maganar saka date kuma wanda daga karshe suka saka wata daya wanda ranarne zaiyi dadaida date dinda akabama Almustapha na watanni biyar din yayi proving kansa the best choice to be the crown prince hakanan aka hada da batun auren Mai Martaban da Ummi sekuma Sulaiman da Sumayya da agurin akayi tambaya aka kuma bayar cikin amincin Allah kafin aka rufe taron da addu'a,atake Mai Martaba ya akai akira masa Sulaiman da Almustapha don basu aikin renovation na masarautar baki daya because it's going to be a very Grand celebration,sabida yanason ayi bikin da aka jima ba ayi irintaba bama ah masarautar Zaria kadai ba aa gabadaya masarautun Nigeria gabadaya..........Almustapha da fitowansa kenan daga dakin sa bayan yabaro Asma'u iya Hindatu ta tareshi tana ce mishi ai Mai Martaba na nemanshi ah Fada wannan dalilin yasama yawuce Fadan direct batareda yaje gun Ummin dayayi niyaba.........
Koda yaje yasamu Sulaiman agurin donshi yariga shi isa,dubansu Mai Martaban yayi sannan yafada masu kudurorinsa dakuma yanda sukayi da mutanen Fada adazun jinjina kai Almustapha yayi tareda yima Mai Martaban godiya ga irin karamcin da ake niyar yima Mallam Hudu din yayinda Sulaiman kuma ke korafin shibaison duk wani abu dazai dangantashi da mukami don Allah abama wani shikam ya yafe........
Hararanda Dad da Abba suka sakarmishi ne yasashi yin shiru batareda yashiryaba inda Mai Martaba kecewa"to baka isaba, this's our final decision and no one can change it inkuma anbaka mukamin kada kayi abunda yadace kacigaba da zama kara zube kaji?"......
Shidai shiru yayi don babu bakin magana sannan Mai Martaban yafara yimasu bayanin yanda abubuwa zasu kasance ko ince suka koma tattauna yanda abubuwan zasu kasance kama daga yanda za agyara gidan,bakin dazasu gayyata from different palaces across the country dama manya manyan yan kasuwan mu na kasa damakuma masu murzawa da gwamnati ayanzun,sunyi maganar IV ma dakuma abubuwan daza aci dadai sauransu wanda zancen yadaukesu lokaci mai tsawo suna tattauna ta..........
Inda daga karshe Mai Martaba yace maganar event na biki dasukeson yi Kuma suje su tattauna ah tsakaninsu komai suka shirya indai baifi karfinsuba zasu goya musu baya.......
Sulaiman murna kaman yayi yaya don daman tundazu yake rawar jikin cewa sunason suyi event na aurenshi da Sumayya sekuma na Asma'u da Almustapha da akace zaayi na lokacin bikin nadi Mai Martaba ne yadakatar dashi daman tahanyar cewa yabari zasuyi maganar daga karshe...........
*****
Bamu leka ma'u๐Ÿฅด +
Sa key din tayi tabude drawer din ahankali dukda hakanan batasan dalilin dayasa zuciyar ta ke bugawa ba unnecessarily, amma ahakan tayi karfin halin wangale drawer din because tariga da tafara aikin batason kuma ace bata karasashi ba,sauke idanunta tayi kan uban litattafan dake gurin hakanan duk wasunsu sunyi kura dasu yayinda aranta tana mamakin meyakeyi da wayannan litattafan be yarda suba tunda tanada tabbacin yariga yayi anfani dasu. dansa hannunta tayi jikin wani littafin tana lakuto kuran dake jiki yayinda kawai  taji tanason duba litattafan na menene don tanada tabbacin yafi ace na University ne kadai it might include his books tunna  secondary school harma da primary may be......
Sede kafin tadaga su dole seta dauke wata katuwar leda milk dake saman uban litattafan ah ajiye,ahankali takai hannunta tareda daukar ledar sede damamakinta taji ledan nada nauyin dabatayi tsanmaniba hakanan tanajin kaman karan kwalabe ajiyewa tayi ah kasa cikin sauri wanda hakan yasa kwalaban suka sakeyin kara,da mamaki tazauna gaban ledan tareda bude ta....
sakan baki tayi,lokaci daya kuma jitayi hannayenta sun shigayin karkarwa batareda ta shiryaba...........
Dakyar tayi karfin halin dauko daya daga cikin kwalaban giyan tana kare masa kallo take kuma idanunta suka ciko da kwalla tana furta " *Giya* ah dakin Yaya Imam?",kafin itadakanta kuma tashiga girgiza kanta tareda sa hannu ah bakinta tana kokarin hana kanta daga yin kukan dake shirin ballomata lokaci guda tana....
"No!,it can't be I'm just imagining things",takarashe maganar tareda sakin wani irin marayan kuka sabida dukyanda taso tahana kan nata daga yin kukan kasawa tayi hakanan lokaci guda farkon haduwarta dashi ke dawa mata"he was really drunk that very day sabida kwata kwata baya cikin hayyacinshi sannan ayanzu ma tana iya tuno yanda takejin mutane nafadin *mashayi ne shi*,amma ya akayi bata taba yarda ba tunda alokacin tagani da idanunta sekuma lokaci guda kalaman Dad suka shiga yimata yawo akwanyarta nacewa dayayi *duk abunda kikaji ance Almustapha yayi to sharri ne bawai yayin dagaske baneba,aikin Magajiya ne* lumshe idanunta tayi yayinda hawayenta baidaina zuba kan kuncinta ba,tayarda Magajiya was the one that trapped him in this situation hakanan she can clearly remember yanda Talatu tafada ranar agaban duniya kan cewa Magajiya ce tasa Almustapha yafara shaye shaye but she never take it seriously,duk ah tunaninta yadaina,duk ah tunaninta yajima da barin wannan rayuwar because koyau za'ace ta rantse kan Almustapha besake shan wani abun maye ba tun farin haduwarsu zata iya rantsewa tunda she spend most of her moments with him, she's always with him for more than three months now kuma haryau bazata iya cewa ga ranar da ta ganshi cikin maye ba,to me hakan ke nufi kenan?... ......
Me wayannan kwalaban sukeyi cikin kayanshi atake kuma wata zuciyar tashiga raya mata"were you with him twenty four hours each and everyday?"Kokuma acikin watannin dasuka wuce kullum tare kike kwana dashi bare ace kinsan meyakeyi sanda bakwa tare barema wanda ke shaye shaye always find it hard yadaina indai yafara,Magajiya might be the cause of his situation but she cannot deny the fact that her Husband is a drunkard kuka take sosai yayinda aranta tarasa matakin dazata dauka itakanta dukdama she's now blaming herself for being a very careless Wife aidai koba komai yakamata tunda tasani da ta bincikeshi taji shin still yanayi dinne ko bayayi haryanzu but batayi ba because she fully trust him,tafi mintuna talatin tana zubda hawayen da babu ranar tsayawansu kafin dakyar ta'iya tashi tashige bandaki tareda wanke fuskarta sannan tadauki mayafinta tasaka tareda ficewa ah dakin hakanan tana addu'ar Allah yasa kada ta hadu da kowa don muddin wani yaga fuskarta zaigane tayi kuka... koda takoma dakin Allah yataimaketa Hajja batanan wannan dalilin yasa tasamu bakin gado tazauna tana tunanin abunyi because she's really out of option,wata zuciyar tace tasameshi suyi magana yayinda wani bangare na zuciyartata ke raya mata kan cewa yimasa maganar ma bazata anfaneta da komai ba tunda tasan shi wanene yana ma iya kin bata hadin kai kokuma ya gwasaleta hakanan 70% na zuciyarta na kuma raya mata "what if it was a frank to trap him",to amma waye zaishigo dakinshi yayi hakan bayan itakanta tasan bakowa ke shigamai dakiba,inma hakane anshiga anyi trapping dinshine to muddin tanuna mishi cewa tana zargin yanashan giya yana iya fushi da'ita wanda itakuma kwata kwata batason hakan besides tanaso su rabu lafiya ne batareda wani issue ba and yakamata tasamu concrete evidences before concluding anything now sabida zuciyar ta tafi rayamata cewa Almustapha yadaina shaye shaye don koda kuwa yayi ah baya to sede in once in a blue moon,dawannan tunanin tayi concluding yin bincike kafin tadauki wani mataki ma'ana zata saka mishi Ido fiye da da don ganin take takenshi,goge dan guntun kwallarta tayi sannan tatashi cikin sauri tafice don komawa dakin nashi.............
Koda tashiga baidawo ba wannan dalilin yasata yin hamdala tareda daukan ledar tafice da'ita zuwa dakinta can saman wardrobe dinta ta ajiye kan intasamu lokaci zataje tazubar inda babu mai gani kafin takoma dakin nashi tacigaba dayi mashi gyaran kaya dukda ma kusan rabin hankalinta baya jikinta............ 1
STORY CONTINUES BELOW

Bangaren Zaliha kuwa gabadaya yau jiran zuwan Salma takeyi,sotake kawai yarinyar tazo matada labarin Almustapha da Asma'u sunsamu matsala amma shiru har azahar wannan dalilin yasa ta aika Lantana ta kiramata ita,koda tazo cemata tayi taji su Hindatu nacewa Asma'un ce zatayi gyaran dakinshi kuma kusan zatafito dinnan taga Asma'un tawuce da ledan dakin ta wanda tanada tabbacin tagani kenan.......
Da mamaki Zaliha tace"badai yarinyar nan bata yarda yana shabane ba?".......
Itadai Salma shiru tayi kanta na kasa yayinda Zaliha tayi kwafa tana "hmm Asma'u kenan inkinsan wata bakisan wataba, you've to believe it whether you like it or not because I'll surely make you believe that your husband is a drunkard".....
****
Wuraren karfe uku motocin sojoji suka kuma sauka cikin masarautar zazzau don diban su Magajiya akaisu prison kafin ashigar da maganar su kotu, Commander dinnasu ne yace ayi mashi iso gurin Mai Martaba aikuwa basuwani jima da tsayuwaba Mai Martaban yace akaraso dasu Fadan nashi cikin dan kankanin lokaci aka shigayi masu tarba ta alfarma seda suka sha ruwa suka setu kafin suka zauna magana da Sarki Abdulrahman din inda suka nuna masa dalilin zuwansu.........
Jinjina kai yayi ahankali yana nazarin zancen nasu kafin yace"Suyi hakuri bazai iya daukan Magajiya yabasu ba sabida duk abubuwan datayi ah masarautar tayishi hakanan he want her to be punished for her deeds agaban duk wanda tayi niyar gurbata ma rayuwarsu sannan yayi musu godiya sosai na goyon baya dasuka basu dakuma taimako dasuke niyar musu amatsayinsu na jami'an tsaro"........
Commander dinne yace bakomai ai aikinsu ne kuma yanda yafada din shima wani hikima ne sannan sunyarda da facilities dinsu,they can handle Magajiya very well tunda tariga tashiga hannu and if they need any help they shouldn't hesitate to call them sukuma insha Allah zasuzo"........
Bakaramin dadin kalaman Commander din Mai Martaba yajiba kafin sukayima juna sallama suka tafi,kokadan bejin zemika ma hukuma ita sabida yafison ta horu ah gabanshi horuwar dawani baitabayiba,she'll live all her life in prison that's his promise dukdama yasani muddin tashiga hannun hukuma aka kuma shiga kotu to tabbas hukuncin kisa za ayimata daga karshe tunda itama ta kashe wasu", she'll die when her time comes but he want her to suffer kamar yanda tasa iyalinshi suka wahala.seda aka kira sallar  la'asar sannan yawuce masallaci......
Wuraren karfe biyar da rabi Mai Martaba da Dad suka isa Gidan Horon inda Magajiya take yayinda suka sa ah fito da'ita because bazama su iya shiga wannan kazamammen gurin ba Allah yagani....
Tana kwance kan kasa dan bazance cement ba tunda duk ya gur gur je gurin wanda hakan yasa yakoma kaman yashi medauke da pebbles acikin shi,bude kofar dataji anyine yasata dagowa ahankali cikin sanyin jiki don ganin wanene gabadaya tayi baki ta rame, tazama kamar ba'ita ba don wallahi nikam dabadan nasan Magajiya agurin takeba ina iya cewa wata ce ba'ita ba......
Wani harara dogarin ya wurga mata tareda toshe hancinshi sabida wani irin doyi dayaji yana tashi agurin sakamakon warin da ciwuwwukan jikinta keyi because sunki healing kwata kwata sema cabewa dasuke sakeyi a kullum, sunwani zama abun kyama babu kyaun gani wanda hakan yakuma faruwane dalilin sosa jikinta datake yawanyi sabida masifar kaikayin dayake mata,wani sa'in intana kaikaya jikin nata zakayi tunanin ko tabin hankali ne da'ita,takicin abinci takuma ki karban treatment duk ita kadai,yananan tsaye hancin shi toshe wasu dogaraye biyun suka shigo suna toshe hancinsu suma don wallahi dabadan yazame musu dole bama babu abunda zaishigo dasu wurinnan,abincima yawanci daga bakin kofa suke garo mata shi wanda shidinma baci takeyi ba sema ball datakeyi dashi wanda inada yakinin hakan nadaya daga cikin abunda ke karasa dakin yin doyi tunda duk ga rubabbun abinci ah zube su basu kwashewa Itama kuma bata gajiya da zubarwa in an kawo din,zuwa sukayi suka kamata fuska ba walwala sannan sukayi waje da ita harzuwa inda Mai Martaban ke tsaye da dogarayensa abaya sekuma Dad dayayo mishi rakiya............
Kallon tsana da kyama yabita dashi hakanan yana mamakin yanda ta lalace cikin kwana uku,he never thought she could do all that she has done hakanan yana mamakin anya akwai wani abu waishi zuciyar Imani ah tattareda da kirjinta kaman yanda kowani dan uwa musulmi kedashi?...........
Ajiyeta sukayi ah gabanshi yayinda hannunta dake sakele ah bayanta yana daure da handcuff Mai Martaba yafi minti biyu baiyi magana ba hakanan be kalleta ba itakuwa dukda azaban datakeji ajikinta hakan behana ta wurga masa wawan harara ba,ayanzu ah duniyar nan babu wanda ta tsana irinshi hakanan tana ganin intasamu dama babu abunda zaihanata kasheshi kowama ya huta..............
Cikin kakkausar muryarsa yace"kincuceni da iyalina Magajiya cutar da ni kaina bazan iya misaltata ba,kin wahalarda ni kamar yanda kika wahalar da mutane na,me mukayi maki, have I ever wrong you in anyway or the other?",Mai Martaba yayi mata maganar murya ah raunane..............
Ganin batada amsar bashi sema mugun harara datakebinshi dashi yace"hmmm ni nasan banmiki komai ba hakanan ban yaudareki ba aduk zaman damukayi,akullum banida burin daya wuce incika miki hakkokin ki dake kaina but you,bakiyi ko daya ba and that's why you're like this and I promise you you'll end like this, aedaman Allah ba azzalimin bawansa bane se wanda ya zalinci kanshi", Mai Martaba yayi maganar ranshi na kuna kafin yayi mata wani irin kallon kyama yana nunata da hannu"sanda zanzo gurin nan I wanted to give you the punishment of your life, punishment dinda babu wanda nataba yiwa irinshi ah masarautar nan but by just looking at you nasan cewa you're already on punshment innabarki da wannan ma kadai ya isheki and kisani aurena dake babu nasake ki saki uku Kuma kisani duk cutana da kikayi nabarki da Allah, because it's unforgivable ko inason yafemiki ma zuciyata bazata barni ba infact I don't even want to think of that",daganan yacema dogarayen sudauketa sumaida gidan horon,karkuma suyarda susake wahalan nemo likita yadubata tunda ita tanuna bataso don tun zuwanshi suka sanar dashi kan Magajiya batason ganin likita sannan yace anabata abinci sabida shibazai yima mutum horo da yunwa ba dukdama yaso yasa adunga mata mugun bugu kullum wanda seta fita ah hayyacinta but by just looking at her wonds duk rashin imaninsa bazaice ayi mata wani illar akan wannan ba but it's a promise dasunyi healing za acigaba daga inda aka tsaya...........
Haka dogarayen suka dauketa zasu koma da'ita se mutsu mutsu takeyi tanama Mai Martaba wani irin kallo seda suka kai bakin kofa sannan cikin murya mai karfi tace...
"Don't even think this's the end, I'll make sure I destroy you and your family Abdulrahman"......
Yanda take maganar cikeda zafin rai harcikin dodon kunnensa yakeji hakanan besan sanda yatsaya cak ba daga tafiyan dayasomayi kafin yajuyo yana kallonta  dogarayen ma ayanzu sun tsaya,gyada mashi kai tayi yayinda tasaki wani mahaukacin dariya kuma tafi 3 minutes tanayi duk suna kallonta kafin tace...
Na kashe yan gidan Galadima baki daya seme?......
Nina rabaka da Khairiya nakumasa kamanta ko ita wacece hakanan nine dalilin dayasa Danka yashiga yanayin da ban taba ganin wani ya shigaba sabida kadaura son duniya akanshi,you wanted him to be the king bayan kamanta nine first wife dinka,I've a Son too and I wanted him to be the king not your filty Son,kaso ko kaki I rule this kingdom Abdulrahman for more than 20years now!"takarashe maganar tana nuna masarautar da hannunta sannan  tasake kwashewa dawani irin dariya,lokaci daya kuma tadaina dariya tareda bata rai tana"I might not achieve my goal of making him the King but still I'm proud na ajiye record,nayi abunda baza a manta dani ba ko bananan and i assure you I'll make all your lives miserable,I'll never let you live in peace ni Magajiya idan Dana bazaiyi rulling kingdom dinnan ba then I'll destroy it kowama ya huta", Mai Martaba daya zuciya hanyar inda take yayi yana huci cikin sauri Dad yarikoshi yana"Calm yourself Abdul inaganin haukane yafara damunta koso kake kabiyeta kuzama daya?".............
Mai Martaba na huci yace"bakaji metake fada bane, who is she,kakyaleni inkarasa ta kowama yahuta",cikin rarrashi Dad yace"babu abunda zata iyayi mana Abdul just look at her situation kawai frustration ne kedamunta bawani abu ba",daganan Dad yajuya yace ma dogarayen sutafi da'ita kafin ya lallabi Mai Martaban suka koma cikin masarautar yanata huci shikadai hakanan maganganun Magajiya nayi mashi yawo ah kwanyar shi.......
STORY CONTINUES BELOW

*10 days later*......
Shiri akeyi sosae ah masarautar zazzau wanda inka shigo cikinta dole kagane hakan domin tuni akafara gyare gyaren bangarurruka wanda ayanzu anyi nisa sosai hakanan koda akazo gyaran bangaren Mai Martaba Asma'u bata manta tuna ma Sulaiman batun layoyincan ba and alhamdulillah ancirosu tundaga lokacin Mai Martaba yaji rayuwarsu da Khairiya sun shiga dawomai daidai acikin kwanyarsa hakanan yana karajin wani irin sonta na ratsashi don ranar kasa runtsawa yayi seda yakira number  wayarta suka sha hira yana tuna mata each and every moment dasukayi spending ah baya sannan yake sake bata hakuri kan abubuwan dasuka faru tareda yimata alkawararruka dadama wanda akan zaicika rayuwarsu da farinciki daga ita har ya'yanta dakuma maganar zaikaita har chad washegarin aurensu gurin iyayenta da danginta,zaije yayimasu bayanin komai sannan yabasu hakuri kan abubuwan dasuka faru,bakaramin dadin kalamanshi taji ba haka Ummi takwana ranar tana kukan farin ciki tareda gode ma  Allah ........
Haka Mai Martaba yasaka agyara wani shashi ma Ummi acewarshi bekamata tazauna bangare daya da surukarta ba sannan yace su Afiya ma bayan auren sukoma bangaren da Hamida take don dama sashine babba da akayi na yaran shi 'ya'ya mata sannan haryau kowa tanada nata dakin da parlour da intazo anan zata sauka  shiyasa ma yace suma ah ware musu nasu daga cikin dakuna da parlourn na wannan sashin dukdama Ummi tanuna bataso dayazo mata da zancen because tafison Ya'yanta su zamanto suna kusa da'ita akoda yaushe amma seya dage kan hakkinsu ne dole yayimasu tunda sauran ya'yan ma anyi masu,in angama gyarawa anbasu sukuma suna iya deciding cewa gun mahaifiyar su zasu zauna to wannan shikuma bashida ja akai........
invitation cards ma jiya Sulaiman yakarbo daga gurin bugawa yakawo su Dad sugani,bakaramin kyau design din yayiba hakanan Dad da Abban sukayi ta yabawa sannan aka fara maganar yanda za ayi distributing nasu kaman yankin su katsina,kano,kaduna, Abuja,sokkoto,jigawa za'a iya kaimusu har gida sauran garuruwan kuma sede aturamusu sako tawaya inda Dad kecewa barema yanzu damuke cikin zamanin social media,shi Sulaiman yaso duka ma ayi hakan amma su Dad din sukace aa wayannan dindai akai musu kuma suma zasufi ganin ankarramasu, dawannan sukayi concluding washegari Sulaiman din zefara wannan aikin cikin ikon Allah yayinda Almustapha dinkuma zaicigaba sa gudanar dana cikin masarautar.......
Misalin karfe goma da rabi na dare Asma'u nakwance kan sofa din dake dakin Almustapha,daga kanta tayi ahankali tareda dorashi kan agogon dake jikin bangon dakin hakanan tana mamakin meyake tsayar dashi ah waje har tsawon lokacinnan haka don tun ranar da tasamu ledar giyan nan adakinshi bazata iya cewa ga ranar dayashigo yasameta idanunta biyu ba sede su hadu dasafe dukdama takan tashi taganta ah jikinshi kamar yanda yake mata kwanaki,inya dawo daga masallaci kuwa,da yayima su Amira karatu shima sama sama to shikenan kuma seyakoma daki yahau shiri,dayayi wanka yaci abinci yashirya yake fita shida dawowa kuma se Allah tunda itadai dasafen suke haduwa,gabadaya tarame tasama ranta damuwa da tunane tunane hakanan tarasa dawa zatayi sharing problems dinta gashi shi ba budan baki zaiyiba yace mata ga abunda yake tsaidashi itakuma batason tambayarshi don rasama mezata ce mishi takeyi, shin cemishi zatayi"miyasa baka dawowa da wuri?",kokuma "mekakeyi ah waje haryake sakayin dare haka!",gani takeyi intayi mashi irin wannan tambayar kamar zaiyi tunanin tana zarginshi ne bayan kuma zargin nashi takeyi tunda har tana son yin bincike akanshi dukdama haryau bata samu wani clue ba, lumshe idanunta tayi ahankali hakanan tanaji hawaye nason zubowa amma tayi kokarin rikesu, tasandai ana aiki acikin masarautar amma batasan cewa suke kan aikin ba se kwana uku da suka wuce da Sulaiman yashigo take mishi magana kan ya rage shigowa sashinsu shine yake cemata ayyuka ne yamasa yawa Mai Martaba yadanka musu duk wasu ayyuka na bikin akansu shiyasa tarage ganinshi,to jinwannan yasa tadanyi mashi uzuri to amma atleast  tana matsayin matarshi koba komai ae seyace mata"Asma'u kwanan nan ina da ayyuka sosai shiyasa kika ga bana dawowa dawuri",ko dai yayi mata wani bayani dazaisa ta gamsu amma baiyi ba infact he's acting normal as if nothing is happening bayan itakuma aranta abubuwa da dama suna faruwa besides ita batama tunanin aikin masarautace ke tsaidashi har dare haka tunda kullum insuna tareda da  Zaliha duk inda Isha tayi zatace mata zata koma bangarenta kar Sulaiman yadawo batanan,to tambayarta anan shine indai tare suke aiki da Sulaiman miyasa shi yake dawowa dawuri?(niidai azuciyata nace kinmanta waye Almustapha ne,katambayama Yaya bare kuma baka tambaya ba).........
Tananan kwance tana ta saka da warwara har bacci yayi awun gaba da'ita batareda tasani ba,wuraren shadaya da rabi  Almustapha da Sulaiman suka fito daga bangaren Mai Martaba bayan sungama lissafe lissafensu yayinda Sulaiman yayi sashin shi inda shima Almustaphan yayo nasu sashin dakinshi yawuto direct donkuwa kowa yayi bacci by that time. Samunta yayi kwance kan sofa kamar kullum amma se bebi takanta ba yau sema wucewa bandaki dayayi yayo wankanshi sannan yashirya cikin kayan baccinshi ahankali yakarasa jikin sofa din tareda tsugunawa agabanta yana karema kyakyawar fuskarta kallo cikeda tausaya wa,shikanshi yasan son da yarinyar takeyi mashi bana wasa bane ba hakanan akullum yanajin inama shima yana da urge din yimata irin wannan son because she deserve more from him............
Sa hannu yayi ahankali cikin nutsuwa yadaga ta kamar Baby dukdan kada yatada ta daga baccin da takeyi,zuwa yayi yakwantar da'ita tareda zama gefenta yana tsuramata manyan idanunsa gani yayi tayi rama tayi wani iri within 10days dinnan,she has changed so much bakamar Asma'un daya sani ada ba,bata mishi shagwaba yanzun inyayi mata abu, bata mai korafi sannan duksanda suke tare yakan lura da'ita tana yawan shiga duniyar tunani. Yanada labarai da dama dayakeson bata nakan ayyukan dayakeyi dakuma irin gajiyar dayake kwasowa but she never ask him on why he's coming late hakanan bata taba tambayarshi batun nadin sarautarshi ba dakuma bikinsu Ummi da akasaka danasu Sumayya bayan kuma yasan tanada masaniya akai tunda tana gani anata shirye shirye sannan yasa ran zata tambaya din tunda shi mutum ne da tasan baya fadan abu se an tambayeshi,in antambayeshin ma yaya tunda bakowa yake bude ma abunda keranshi ba. He's just very sure something is bothering her because she's not really Asma'un dayasani,he want to ask her meyake damunta but baisan ta'ina zai fara ba?..
Bai saba ba,baikuma taba yima wani irin wannan tambayar ba hakanan baya tunanin zaifara akanta he just hope that she'll open up soon because shirunta is really Killing him inside.........
Dan shafa kanta yayi ahankali yanayimata addu'ar bacci kafin daga karshe yayi bending kanshi tareda pecking cheeks dinta sannan yatashi yakoma ta dayan bangaren yahawo gadon tareda janyota jikinshi........
STORY CONTINUES BELOW

***
*Same night*
Daddy ne yadubi Mommy dake serving nashi dinner yace"Hajjan bata dawo ba haryanzu?".......
Batareda Mommyn tabar zuba abincin datakeyi din ba tace"Bata dawo ba Dear".......
Dan tsaki yayi kafin yace"Daman kucema su Aliyu suje sudauko ta gobe ina anfanin zuwa tazauna ah gidan surukai ba haihuwa Asma'un tayi ba bakomai ba dama ace bamwa gari ne mu is understandable".......
Jinjina kai Mommy tayi don Itama abun yajima yana damunta kawai shiru tayi bare abunka da uwar miji kada kayi magana yazama wani laifin kuma,to amma  tunda shi yasan rashin dacewar hakan dasukayi hakuri daga ita har Ummin ai yau yabudi baki yayi magana dukdama Ummin bata fito fili tayi complain ba amma tabbas tasan abun naranta kawai fadane batayiba,ahaka dai takarasa zuba mishi abincin yashiga ci kafin daga karshe tatashi tayi bangarenta don fada ma su Aliyun sakon Daddynsu because batason ma tazo tamanta goben,koda tafada musu cewa sukayi to don kuwa daman sunjima suna planning zasuje gidan Asma'un Allah nedai baiyiba to yanzu sunsamu great opportunity.........
Sadiq ne yace"Nima zanbiku Yaya Aliyu",wani harara Aliyun yayi mashi tareda cewa"Babu inda zakaje yanzu seyaje yanamana kauyanci",Aliyu yakarashe maganar yana kallon Musa.....
Mommy ne tace"Uwar kauyanci zaiyi muku kubar yaro yaje yaga yar uwarsa shine zakuwani ce zaije yamuku kauyanci dan iskanci".......
To Mommy inaga Nadin Yaya Almustaphan ma yakusa zuwa zaije ai,tashi Mommy tayi don komawa bangaren mijinta tana"nidai nace seyaje goben kuma inga uban dazai hanashi",daganan tayi ficewarta Sadiq dayasan yana iya samun rabonsa yayi saurin tashi don wucewa Boysqusters dinsu don dama ah bangaren Mommy suke tun dazu binshi Musa yayi yana"matsoraci kawai daka tsayamana".............
*****
*Early morning*.....
"Sis kinkira matar ne?",Afiya tayima Sumayya tambayar tana kallonta gyada matakai Sumayyan tayi tareda cewa"Amma bani nakirata ba da Mom ne zasuyi magana daman ai",Sumayya tayi maganar tana karawa da"Ummin Asma'u ne tahada su da matar,ita tayi masu Asma'un gyaran jiki lokacin bikinsu inda tace ta'iya sosai don haka tabama Mom contact dinta sukayi communicating daita kan komai da komai inda suka karashe zancen zatazo kusan two weeks to the wedding,to jiyane ma naji suna magana da Mom kan yau zata kamo hanya"..............
Cikeda Jin dadi Afiya tace"yaeyyyy  Allah yakawota lafiya".....
Harara Amira tayi mata tana"kekuma murnar na menene?"...
Itama Afiyan maida mata hararantayi playfully tareda cewa"akan mi bazanyi murnar ba".......
"Naga kina rawar jiki ne bayan ke ba Amarya ba bakomai ba",dariya Sumayya tayi tana"kukam baku da dama. miyene in anyi matan Amira kema inkinaso basai amiki ba tunda bakudin ki bane zaiyi ciwo"......
Ahto nima dai abunda nagani kenan cewar Afiya,nidai don Allah ku taimaka kukarasa raba ankon nan laziness dinku yayi yawa ga biki se matsowa yakeyi Sumayya tayi maganar tareda tashi tsaye,sakan baki Amira tayi tana 'yar dariya....
"Amma nidai bantaba ganin marar kunyar Amarya irinki ba".......
"Lol,kifadi abunda keranki Amira don kinga bani da kawaye ne agarin nan shiyasa", Sumayya tayi maganar tareda ficewa daga dakin don leka Asma'u tatambayeta ko ta  aikamasu Aisha da Zahra ankonsu da ta bayar tunda na dinner din harda kawayen Asma'u ne ayanda suka tsara......
Aikuwa samunta tayi tafito ah wanka kenan jikinta daure da towel,murmushi tasakar ma Sumayyan sanda taga tashigo dakin kafin tace"Amarya Amarya".......
Dariya Sumayya tayi tana"kema wata amaryar ce ae".......
Zama Asma'u tayi tana goge jikinta da dan karamin towel kafin tace...
"aa kam ni ae ba sabuwa kal ah leda baceba"........
"Lol,bawani nan",inji Sumayya din kafin tace kinsamu kin aikama su Zahra ankon ne?...
Salati Asma'u tasaki tareda cewa"wallahi namanta kwata kwata Sumayya inba yanzu dakikayi maganar ba,amma ba inkira Zahra tazo gida takarbi nata inta taso daga school Aisha kuma tana kaduna I was even thinking ko inbayar mata dinkin ah garinnan ne kawai duk kinga na manta",Asma'u takarashe maganar tareda janyo wayarta don kiran Zahra din kallonta sosai Sumayya keyi kafin tasaka hannu takarbi wayar,dagowa Asma'un tayi dasauri tana"Kiran Zahra din zanyi dai"............
Batareda Sumayyan tamayar mata da wayan ba tace"wai what's wrong with you ne Sis,I've been noticing you kaman kina cikin damuwa kwanan nan"...........
Asma'u da take idanunta suka canza launi tasaki murmushi kafin tace"me kika gani?"...
"Nifa babu abunda kedamuna",no karyane Asma'u gashi kinrame duk kin canza,kinyi wani iri and tunda ake maganar bikin nan baki zama ayi dake bayan nasan ke bahaka kike ba,you always interact.......
Dariya kawai tayi dukda idanunta sunciko da kwalla kafin tatashi tsaye tareda karasawa gaban mirror tana kokarin boye hawayenta"wai meyake samun yan gidan nan ne tun wurin kwana uku kenan kowa seyana tambayata meyake damuna haka, Ummi kusan kullum seta tambayeni, Afiya da Amira shekaranjiya sunmin same tambaya, Aunty Hamida ma dazu damuke girki seda tamin tambayar nan kema gashi kina neman isata,kumafa dukdan kunga na rame ne to slimming nafara", takarashe maganar murya ah karye jijjiga kai Sumayya tayi in desbelief kafin tace....
"you can pretend to be okay but no one will believe you sabida muryarki ma kadai ya'isa yatona miki asiri".........
Asma'u kasa cewa komai tayi se jan man shafawanta datayi tafara shafawa jikin ta tana hawayen data rasa dalilinsu duk Sumayyan na kallonta tacikin mirror,ahankali tace"kunyi fada da Yaya Almustapha ne?"......
Cikin sauri Asma'un ta jijiga mata kai,to ko bakida lafiya ne, Sumayya tayi mata tambayar ah karo na biyu shima jijjiga kai tayi yayinda takife kanta agurin tana kuka me tsuma zuciya cikeda tausayinta Sumayya tataso tana rarrashinta kafin daga karshe tace"shurunki won't solve problems, you've to speak out Sis inma bazaki fadamin ba you can call Umminki kokuma kikira Asiya kuyi magana I'm very sure she'll advice you akan koma menene kinji?"......
Gyada kai kawae Asma'un tayi yayinda Sumayyan seda tayi kokarin lightening mood dinta kafin suka kira Zahra din batun ankon inda tacemusu zata biyo  takarba inta taso daga school........
Aikuwa batazo tasamu zuwanba shiyasa ma dayanma dasu Aliyu sukazo daukar Hajja dako ah lokacin suna tareda Ummi, Asma'u tabashi kayan yamika ma Zahra inzasu wuce gida tunda gidansu baida wuyan ganewa,sunjima suna hira da Asma'un don  itakadai ne duk yan matan sunfita gari hakanan Aliyun nata lura da yanayin Asma'un gakuma  raman da tayi compared to sanda tazo gida yaso su kebe suyi magana amma babu hali dubada yanda Bayi keta kai kawo kuma Musa da Sadiq ma sunanan she might not like to speak up probably ahaka harsuka tashi tafiya inda Ummi keta mitan miyasa za azo daukan Hajja bayan gashi sun saba abunsu gama kuma biki dake karado kai amma se Hajjan tace bakomai zatadawo bikin ai Itama tanason taje tadan kintsa ne... ..
To kawai Ummin tace badon ranta yasoba don bakaramin sabo sukayi da Hajjan ba shiyasa ma gabadaya taji batason tafiyar tata to amma yazatayi tunda Hajjan ma tanuna tanason zuwa gidan abunda Ummi batasani ba shine Hajja nashiga mota tashiga yimasu Aliyu surutu"Yan bakin ciki kawai,dan kayan itatuwan dana keci kullum dakuma zama danakeyi ah muhalli mekyau shine akeyimin bakin ciki".........
Dariya Aliyu yayi yana"to Hajja yanzun dawa kike?"......
Harara tabuga mishi tana"Wanda ya tsargu kuma ko anki ko anso sena dawo bikin nan".......Shidai Aliyu dariya kawai yayi don yasan inya biyema Hajja se suyitayi ne babu tsayawa and daga karshe shine ah ruwa don zuwa zatayi tahada mishi bomb gurin Daddynsu,koda suka koma gida maghrib ta gabato shiyasa ma baiyi tunanin kiran Asma'un ba seda yazo kwanciya aranshi yana addu'ar Allah yasa batayi bacci ba kokuma baswa tareda Almustapha don dukyanda yaso yabari se washegari kasawa yayi don gabadaya gani yakeyi kanwar tashi nacikin tsananin damuwa........
Asma'u nakan sallaya ta'idar da sallar isha wayarta tayi kara,tashi tayi tadauko cikin sauri don kada call din ya yanke ganin Aliyu yasata dagawa cikin sauri.....
"Ina wuni Yaya Aliyu?"......
"Dazuba mun gaisaba Sis",yayi maganar ahankali yar dariya tayi sannan tace "aiyanzu da dazu ba daya bane ba Yaya Aliyu sannan tashiga tambayarshi yanda suka isa gida"yakun isa gida lafiya yakuma kuka samu su Mommy da Ummi,I hope kowa lafya?"......
Kowa alhamdulillah Sis except one person,cikeda damuwa tace"subhanallah waye ba lafiya?".......
Gyara zama shi yayi sannan yace"tsaya kada kitada hankalinki kuma,kowa lafiya ah gida I'm talking about you Asma'u, what's wrong with Sis,bakida lafiya ne ko akwai wani me takura miki acan din?"............
Cikin tsananin damuwa Asma'u taji gabanta yashiga faduwa itakam tashigesu wai miyake faruwa ne,miyasa kowa yake gane halin da take ciki so easily while she's trying so hard to hide it,jin tayi shiru ne yasa Aliyun cewa"Asma'u,are you there?"....
Gyada mishi kai tayi kaman wanda tana gabanshi kafin dakyar ta'iya cewa....
"Eh Yaya nifa babu abunda yake damuna believe me",bebari tarufe baki bama yace"karya kikeyi Sis you better tell me what's bothering you inbaki fadamin ba wazaki fadamawa,are you going to let it disturb your peace of mind?",sannan yayi kasa da murya "Feel free Sis,Yaya Aliyu is here for you",ah take taji zuciyarta ta karye hakanan idanunta suka ciko da kwallah lokaci guda ita kanta tasan she really need someone to talk to kozata dan ji sauki aranta and surely tasan Aliyu is the right person,shi mutum ne dabaidamu da baza sirrin wasu ba and most importantly akwai shakuwa sosai ah tsakaninsu,he might understand her and may be yabata shawara ma sede tasan maganar bana waya baneba don haka tace"we cannot talk on phone dole semun zauna Yaya".........
Cikin sauri yace"okay then I'll come home tomorrow evening semuyi maganar kinji,but before that kikwantar da hankalinki please"....
Gyada kai tayi kamar wanda tana gabanshi jin tayi shirune yasashi sake cewa"kinji sis?"....
Sa hannun tayi tashiga goge yar kwallarta kafin tace"To Yaya Aliyuna", murmushi yake yayi yana"that's my girl, I'm hanging up now kigaida mijinki kinji".......
To kawai tace mishi kafin ta ajiye wayarta ah gefenta,haka tacigaba dazama agurin tana hawaye ita kadai har wuraren shadaya kafin dakyar tatashi tasauya kayanta zuwa na bacci kafin tahau gadonta ta kwanta sede gabadaya bacci yaki daukanta........
Yau Almustapha da wuri yadawo gida, shiyasa ma dabai samu Asma'u kwance ah dakin ba seyayi tunanin ko agaba zatazo ta wannan dalilin yasashi yin wanka yashirya cikin kayan baccinshi sannan yadauki laptop dinshi yana dube dube dukdama rabin hankalinshi nakan kofa ko Allah zaisa tashigo amma shiru har shadaya da rabi,dan tsaki yayi sannan yakashe laptop din tareda rufeta yana mamakin rashin zuwan nata tunda bawai sunyi sallama da Hajjan baneba bare yasan tatafi........ +
Kwanciya yayi tareda jan bargonshi amma gabadaya yakasa bacci duk rufe idon dazaiyi ita yake gani hakanan kawai soyake yaga,"her very beautiful soul sleeping next to him as usual",yacanza position din kwanciya yafi ah irga amma babu alamar zai iya baccin wannan dalilin yasashi tashi cidok yafice zuwa parlour da tunanin ko anan tayi bacci sede koda yaje nanma batanan jiki ah sanyaye yakoma dakinshi yakwanta don bayason zuwa dakinta kuma Hajja nanan,bashi yasamu yayi bacci ba se wuraren biyun dare hakanan asuba nayi yafarka feeling as if some part of him is missing ahaka yatafi masallaci yayi sallah yadawo,samun su Amira yayi suna zazzaune suna jiran yazo yayi masu karatu,wucesu yayi batareda ya amsa gaisuwar subama don gabadaya mamakin rashin ganinta agurin yakeyi bayan kuma da'ita ake karatun, ah hanyar dinning  suka ci karo dan kara tasaki sakamakon gwaruwan da goshinsu yayi wanda hakan yajanyo attention dinsu Amira dake parlour harda yar dariyarsu shikuwa kallonta yakeyi cikeda jin dadi don bakaramin relief yajiba infact bemaji zafin buguwarba don koyajima baidamu ba kama hannunta datake sosa goshin nata dashi yayi sannan yajata sukayi daki,rufe kofar dakin yayi tareda jingunuwa jikin kofar yanajin wani kwanciyar hankalin daya rasa adaren jiya sunfara dawowa daya bayan daya, ahankali yataka zuwa inda take tsaye,rungume ta yayi hakanan lokaci guda yalumshe idanunshi tareda sauke ajiyar zuciyar dabaisan dalilin shi ba,itadai mamaki da kidima ne suka kamata lokaci guda gashi tanason kwace jikinta amma gabadaya ta kasa sabida wani irin wawan runguma yayi mata jitayi yace"Don't move please",sakamakon motsin da takeyi ajikinsa itama kuma seta tsinci kanta dadaina motsin sannan ahankali tasa hannunta ah gadon bayanshi tana lumshe idanu............
Sunfi minti biyar yanatason yayi magana amma yakasa,dakyar kuma yayi karfin halin cewa"do you know?"....
Jijjiga mai kai tayi ahankali tanajiran jin maizaice amma shiru,sema sake cewa dayayi"do you k..n..o..w that",wannan karan har muryanshi na cracking amma gabadaya yakasa karasa sentence din ahankali tazare jikinta daga nashi cikeda damuwa tasa hannunta tariko fuskarshi tana kallon cikin idanunshi"Yaya imam"........
Kallonta yakeyi kawai batareda yace komaiba, calmly tacigaba da magana"what where you saying,what do you want me to know?"..........
Cire hannunta yayi ajikin fuskarshi sannan ya sarkesu cikin nashi yana kallon hannayennasu dake sarkeda na juna kafin yace...
"I couldn't sleep early without you by my side yesternight".......
Lokaci dayi taji heart dinta yayi melting,she couldn't sleep without him too and ita tasan dalili but shifa? what's the reason behind it,has he by any chance fall for her?goge kwallar dayayi slipping agefen kuncinta tayi kafin tacanza maganarda"Su Amira najiranmu Yaya"because batason ayi furthering maganar ma she might end up getting hurt sabida tunanin Almustapha ze sota ma is a false hope,a very great one ma kuwa sede da mamakinta taji yadagata sama kamar Baby bedire ko'ina ba sekan gado,kwanciya yayi ajikinta kafin in a whisper yace...
"I want to sleep now".....  
Gyada mishi kai kawai tayi tana kokarin danne kukanta,she couldn't just say no to him besides she need it too,his warmth,his breath,his scent infact everything about him ma don Itama dakyar ta'iya tayi baccin jiya............
Yarigata yin baccin yayinda itakuma taketa sake sake aranta harma batasan sanda baccin yayi awun gaba da'ita ba.......
Bangaren su Amira kuwa haka sukayita jiran fitowarsu amma shiru,wannan dalilin yasa Afiya tashi tana tattara littafanta"tonikam kunga tafiyata".........
Sumayya ne tace "kujira mana sufito kada Yaya Almustapha yafito baisamemuba kunsan ranshi zai baci",don ita haryanzu bakaramin tsoron Almustapha takejiba shiyasa take dar dar dashi.......
"To indai jiran wayannan ma'auratan zakiyi kinada aiki,Afiya jirani mutafi daki baxan zauna bakin ciki ya kasheni ba don nasan yama manta da existence dinmu anan",wannan karan Amira ce tayi magana.....
Dariya Afiya tayi tana"ah to",daganan sukayi daki itama Sumayyan binsu tayi dukda ranta baisoba sede kuma talura maganar tasu akwai kamshin gaskiya acikinta shiyasa ma tayi giving up tareda mamakin Yaya Almustaphan,so he could be lovely like this๐Ÿฅด........
STORY CONTINUES BELOW

Wajajen goma na safe Sulaiman yashigo bangaren su Asma'u din yana tambayar ina Almustapha amma sece mishi Afiya tayi yana bacci da mamaki yace"Bacci kuma?"....
Are you really serious.....
Yar dariya tayi sannan tace"Allah dagaske nakeyi Yaya",dan tsaki yayi sannan yayi hanyar dakin Almustapha din yana"lallai ma Yayan nan yasan munada ayyuka shine ze kwanta bacci fisabilillahi?"...........
Cikin sauri ta tare gabanshi tana dariya kafin tace"yanada kai ai you can do the work yau hutu yakeyi',wani harara ya daka mata yana"Bani hanya ni kiga I don't have your time" sannan yakarada"I was supposed to go to Kaduna tun sassafe amma natsaya jira yafito sabida banason ana aiki one of us baya gurin thinking he'll come out soon amma shiru shiyasa nabiyo baya"........
Batareda ta matsa agaban nashi ba tace"zaifito ai Yaya Sulaiman",dukdai wai tanason yagane dakanshi kan cewa yana tareda matarshi amma Ina shigabadaya ma wannan tunanin baizomai bai ganin ya matsa ne akafule tace"Yaya Sulaiman ta'ina zaka fara shiga dakin mai iyali newai tukun"........
Lokaci daya Sulaiman yaji abun yafado masa don shadaf yamanta yadaina shiga dakin Almustapha tunda yayi aure,dan shafa suman kanshi yayi yana"Damn it",kafin yadago ya kalleta"kinsan I totally forgot", sekuma yakwashe da dariya dukda takaicin dayakeji na abunda Yayan nashi yayi yana"lallai ma mutumin nan,zan rama wallahi badai inyi auren yagani...........
Afiya ma dariya tayi tana aigwanda kai ganin sa nema bakayiba kwata kwata muda ko ansa gaisuwarmu baiyiba bare musa ran za ayi karatu yau yanazuwa corridor yaja Matarsa sukayi daki...........
Dariya sosae Sulaiman keyi yana cize yatsan shi,daman he was worried ganin Asma'u kaman tanada damuwa but after hearing this today seyake tunanin they might resolve their differences,dawannan yafice yana "Shikenan yau ba batun zuwa Kaduna amma Yaya yasani ana gama biki innakwashi amaryata muka tafi honeymoon bazaku sake ganinmu semun samo muku tsarabar Baby",dariya sosai Afiya tayi tana jijjiga kai da mamakin rashin kunyar Sulaiman din.......
Asma'u kuwa itata fara farkawa ahankali ta dago kanta daga physique chest dinshi tareda daurawa kan wall clock din dake dakin ai batasan sanda ta zabura ba ganin har karfe shabiyu da mintuna arba'in da uku wanda zaburan nata ne yafarkar da Almustapha daga baccin dayakeyi yana tambayarta lafiya..........
Kaman zatayi kuka tace"kaga time fa",bedamu da abunda tace dinba hakanan baiduba wall clock din data bukata yayiba sema kallonta dayakeyi cikeda adoration,ganin kallon dayake mata yayi yawa gashi yana sata feeling wani iri seta sake pouting bakinta cikeda shagwaba tace"niwai miyene kaketa kallona?", murmushi kawai yasakar mata because he's really enjoying the moment,it's been 11 days now rabon dayaga tayi mashi shagwaba shiyasa dayaga tayi ayanzu taburgeshi hakanan yakejin kaman all his problems are gone...........
Ganin yaki magana ne yasata tashi cikeda tsarguwa,cikin sauri yatashi yazauna shima tareda janyota kan cinyarshi in a whisper yace"where are you going Wife?",harara ta buga mishi wanda hakan yasashi sake janta jikinshi cikeda zolaya yace"ko ruwan wanka baki hadamin bafa?"....
Wannan karan kan 
dan bugun kirjinshi tayi sannan tatashi cikin sauri tasauka daga kan gadon tsabar tama rasa mezata cemishi,sekace daman ita take hada mishi ruwan wanka ada din,wai what's wrong with him ne yau,miyasa bai tafi inda yasaba zuwa ba ita tana tunanin yanda zata fita tabar dakin nema dakuma yanda zata fuskanci yan gidan.......
Yana ganinta tsaye tanata saka da warwara itakadai,intayi bakin kofa kaman zata fita sekuma tadawo hakadai, shidai baicemata komai ba baikuma tashi daga kwance dayake ba se yar dariya dayakeyi mata kasa kasa can kuma seyaga ta sake nufar kofan Yar dariya yakumayi yana jiran ganin tadawo amma wannan karan setayi ficewarta abunta...........
Jijjiga kai yayi yana mamakin hali irin nata sannan yatashi yashige bandaki donyin wanka, Asma'un ma tanazuwa daki wankan tashiga don gabadaya tarasa abunyi,wannan abun kunya damai yayi kama kana bangare daya da suruka kakasa tashi daga bacci sai azahar that too adakin miji fisabilillahi?....
Itadai Almustapha bai kyauta mataba yau gaskiya.........
Seda tayi wanka tashirya sannan tadauki wayarta dake kan bedside drawer tun jiya, bakaramin mamaki tayiba ganin 10 missed calls from Yaya Aliyu cikin sauri tashiga kiranshi Allah yataimaketa yashiga, ringing daya yadaga muryarshi daukeda damuwa yace"nayi ta kiranki baki daukaba,inafatan dai lafiya?".........
Dan murmushi tayi sannan tace"wayar na silent ne Yaya Aliyu seyanzu nagani, I'm sorry",shima cewa yayi "I'm sorry too baxan samu zuwa yauba munama kaduna 2 jirginmu zai tashi zuwa Lagos kinsan Daddy bayawa mutum alert inza ayi tafiya sede kajishi kwatsam, I'm really sorry innazauna I'll call you semuyi magana"......
Karka damu Yaya, Allah yasaukeku lafiya kagaida min Daddy please......
Ahankali yace"insha Allah nan sukayi sallama ya katse call din",ajiyewa tayi agefenta taredayin hamdala don itakanta daman kawai tace mishi to dinne bawai dan tasan ta'ina zatafara bashi labarin abubuwan dasuka farun ba ....
STORY CONTINUES BELOW

Almustapha kuwa yana gama shirinshi gun Ummi yayi suka sha hiransu don cewa yayi yau hutawa zaiyi babu inda zashi awurin Ummin nema yakejin Hajja tatafi, murmushi yayi aranshi yace"so that old woman was helpful"........
Ganin har 3 Asma'u bata fito ba Ummi tadubi Almustapha da tuhuma"Anya Imam kana damuwa da al amuran matarka yanda yadace kuwa?".....
Da mamakin meya kawo maganar yace"wani abunne yafaru Ummi?"......
Ajiyar zuciya Ummi tayi sannan tariko hannunshi cikin nata"I'm not sure if kaine cause din damuwarta but I'm sure something is bothering her for the past two weeks I guess,nayi nayi tafada min bata fadaba she always says that she's okay while she's not,kai bakaga yanda tarame bane ko bakasan yanda ake kula da Mata bane sena koya maka?",yanda Ummi keyi mai maganar seyake ganin kaman tamaidashi wani karamin yaro ne,dan cire hannunshi yayi cikin nata sannan yashafa suman kanshi gabadaya yarasa mema zaice ma Ummin,da ace tasan yanda yadamu yaji matsalar yarinyar shima dabazama tafara mai maganar ba yanzu........
Jin yayi shiru yasata cewa"Did you ask her?"....
Ahankali ya jijjiga mata kai alamar a'a,jiki ah sanyaye Ummi tace tokodai kasan mekayi mata ne kakeyimin shiru inatada magana nikadai.....
Cikin sauri yace...
"I did nothing Ummi".......
Try and ask her dukdama ba lallai tafada ma ba kokuma kazauna kayi tunanin abunda kasan kayi mata yabata mata rai ko abunda kasan zai iyasata cikin damuwa because I've the feelings that it's something connected to you Imam......
Gyadama Ummin Kai kawai yayi yayinda tatashi tafice don zuwa gun Asma'un bayan tacema su Rukayya sukai abinci dakinta......
Almustapha ba irin tunanin dabaiyi ba don tuna maiyayi mata amma shibaiga yayi komaiba,abu dayane kemai yawo akanshi na....
"kodai don taga rabuwarsu takusa ne shiyasa tashiga cikin damuwa",dawannan yatashi yafice zuwa masallaci yana mamakin abun donshidai yasan tana sonshi hakanan in mutum na sonka bazaiso rabuwa dakaiba ya kuma fa cemata bayason rabuwa da itan shima amma yarinyar nan tadubi kwayar idanunshi tace itaba haka ba,harda yimashi kukan munafurci gashi kuma yanzu ita abun yake damu,dan murmushi yayi aranshi yana"zanyi maganinki yarinya"..............
Ummi har daki taje tasamu Asma'u nan tasata dole taci abinci agabanta tana ta janta da hira dukdan tasaki jikinta don tasan Asma'u da shegen kunyar tsiya yanzu seta fara wasan boye boye da'ita akan abunda yafaru yaudin kafin daga karshe tajata sukayi lambu bayan sunyi sallar la'asar....
****....
Daman Mai Martaba da Dad sun tsara cewa Hajiya Muniba da Matar waziri sune zasuje sayan kayan lefe dama kuma kayan daki da kitchen ah duk kasar dasukaga zaifi musu sauki ko inda suke ganin zasu samu kaya masu kyau sede koda Dad yazoma Mom da maganar jiya take fada mishi ai Hajiya Muniba batajin dadi kwanannan, she's always sick da mamaki Dad din yakecemata baiji Mai Martaba din na complain ba infact shiyace da'ita ma za'aje.. ....
Dan shiru Mom tayi kafin tace"to besani bane komi?"......
"Probably",cewar Dad din kafin yace zai tuntunbeshi yaji shiyasa ma yau dasuka hadu yake sanar dashi,da mamaki Mai Martaban yace wallahi baisani ba and tana zuwa gunshi fa baiga alamar batada lafiya ba.........
Dad dinne yace"may be she's hidding it ne,kaje kasameta kuyi magana zaifi"....
"Sure",cewar Mai Martaba din kafin yatashi atake yayo bangaren nata,tana kwance ah dakinta gabadaya batajin dadin jikinta kwananan kawai daurewa takeyi,zama yayi abakin gadon cikeda damuwa sannan yataba temperature din jikinta yana
"what's wrong with you Dear?"......
Kokarin tashi zaune tayi tana"Nothing,Ina kwana Dear,hope lafiya kayi tattaki dakanka har bangarena you should have send for me zanzo immediately", takarashe maganar cikeda karfin hali, she's just trying so hard to prove that she's okay while she's not......
da mamakinta Mai Martaba yadaura hannunshi kan lips dinta yana...
"why do you want to force yourself to be okay when you're not Muniba?",shiru tayi tana kallon shi kafin yasake matsowa kusa da'ita tareda doro kanta ah kafadunshi"I'm here to see you tunda kinkoyi boyema mijinki damuwarki",yanda yayi maganar ya tabbatar mata da baiji dadin abunda tayi din ba seta tsinci kanta da sakin murmushi kafin tace...
"I'm okay fa kawai zazzabi ne kedan damuna"...........
Shiru yayi baice mata komai ba har likita yakaraso cikin sauri tace"I'm okay really"........
Cewa yayi with serious look"You're not Muniba kibari likita yaganki,i don't like seeing you this way",yanda yayi maganar bazata iya jadashi ba wannan dalilin yasata tsayawa likitan yaduba ta,seda yagama examining dinta sannan yace"kinada ulcer ko?".........
Gyada mishi kai tayi ahankali kafin likitan yacigaba da magana"you've to avoid spicy food sannan kirage cin mai and try and be eating your meals on time inbahaka ba zaicigaba da damunki"......
Mai Martaba ne yadubi likitan kana yace"kana nufin ulcer kedamunta?"......
"Eh ranka shidade" cewar likitan kafin yakarada"but is not that chronic intana avoiding abubuwan dana lissafa she won't have any problem in Sha Allah"........
Godiya Mai Martaba yayima likitan kafin yayi mata prescribing drugs yatafi, atake Mai Martaban yasa aje ah siyo kafin yadawo dakin yana"tunda kinzama stubborn girl I'll start feeding you myself"........
Kai Dear yaushe nazama girl tsofai tsofai dani, janta yayi jikinshi cikeda so yana"you might be old to the world Muniba but not in my eyes,kaman Baby nike ganinki kullum believe me".....
Itadai dariya kawai takedanyi ahankali don tasan kawai yana fadan hakan ne don ya faranta mata,itakanta tasan she's very lucky data auri Mai Martaba,he might not have feelings for her na soyayyar aure yanda yakamata but she's sure yana respecting dinta and despite she knowing cewa Khairiya yakeso betaba nuna mata hakan ba and koyaushe in suna tare nuna mata yakeyi she's the most special being in the whole world and it makes her feel good even though tasan bawai hakan bane ba,ita tunda tafara rashin lafiya ma tayi tunanin ciki gareta shiyasa ma tayita boyemai don aganinta abun kunya ne ace tsofai tsofai da'ita tana da ciki ashema ulcer ce ke damunta ba wani abuba,yes tasan tanason yara wanda zata haifa da cikinta but at her age itakanta tasan it'll be something difficult...........
Yajima ah bangaren nata donseda yatabbatar taci abincin kaman yanda yayi alkawari sannan yabata drugs tasha kafin yafice don komawa fada kan susake sabon decision na wanda zasuje sayayyar.........
***
Kwanan nan gabadaya Magajiya batajin dadin jikinta dukda irin daurewan datakeyi wurin ganin she's strong amma ina,kaikayin jiki yadameta,ga ciwukan jikinta gaba sukeyi ba baya ba itakanta kyaman jikinta take ji ah yanzu bare wasu, she's so weak don sau uku tana suma acikin satinnan ana zuwa asamata drip ajikinta don Mai Martaba cewa yayi baza akaimasa annoba clinic dinsaba wayasani ma cutan jikinta is communicable kada taje tayada ma mutane diseases because likitan kanshi cewa yayi yarasa dalilin dayasa kurajen jikinta suka ki healing drip dinma dayake bata na taimaka mata tasamu karfin jikinta ne kawai sabida kin cin abincin da takeyi din...........
Sede yaufa jikinnata yayi tsanani sosai don yanda jikinta ke karkarwa dakuma yanda take sosa jikinta kamar mahaukaciya tsabar kaikayin dayakeyi mata seda tabama dogaraye tsoro,tana sosa jikin tana fame ciwukanta wanda hakan bakaramin azaba yakesata jiba sede gani takeyi sosawan yafi mata dadi akan barinshi yana mata kaikayi don yafi wannan din azaba.......Sunanan tsaye suna kallon halin da take cikin batareda kowannensu yace komaiba,can kuma seta saki jiki tafadi sume,daya daga cikin Dogarin ne yayi karfin halin yin magana "subhanallahi ta sume fa",kafin kuma dagudu suka shiga kokarin bude kofar don dama arufe take ta raga raga suke kallonta daman.........
Shiga dakin sukayi suna toshe hanci baki dayansu tsabagen warin dake tashi agurin kafin suka karasa gareta daniyar daukanta amma ina don dukyanda sukaso taimaka mata kasawa sukayi dubada yanayin jikinnata,gabadaya ya cabe gani sukeyi dasun tabata fatan jikinnata zai sabulewa zeyi,sky blue kayan prisoners dake jikinta ma duk yafita ah hayyacinshi yatashi daga blue yakoma brown gashi daman sleeveless ne rigan shiyasa ake iya ganin ciwuwwukan dake jikinta.............
Ganin sun kasa aiwatar da komai akanta ne yasa daya daga cikinsu yace"muje mukira Doctor din mana don ko munfada ma Mai Martaba abunda zaice ayi kenan?"..........
Jinjina kai sukayi cikeda gamsuwa da maganar tashi kafin sukace toshi yaje yakira likitan mana, haka yafice cikin sauri yayi gidan likitan daya zamanto yana cikin masarautar daman sukuwa komawa waje sukayi don daman numfashima  dakyar sukeyi acikin gurin,ba afi 30 minutes ba saiga dogarin yadawo tareda likitan.......
Tsayawa yayi daga bakin kofa sannan yace sushiga su fito da'ita nan don Allah yagani shibazai iya shiga gurin ba don bemanta wahalar dayasha ba kwanaki dayayita zuwa yana samata drip bakaramin fama yayi da tashin zuciya ba hakanan kusan kwana biyu inyaci abinci daya tuno yanayin warin dayaji adakin da Magajiyan take seyaji amai yazo mishi lokaci guda ko inyatuna yanayin ciwon jikintan,shi babban likita ne dayajima yana aiki ah masarautar nan. kai bama ah masarautar nan ba kadai tunda yakanyi aiki ah wasu hospitals hakanan yasha encountering patients masu cuttutukan dazaisa shi jin kyama amma hakan baitaba sashi jin wani iriba kaman yanda na Magajiyan yadameshi,her situation is so worst dashikanshi yarasa wani irin cuta ne gareta dabada badan ba cewama zaiyi shibazai dubata ba sede it's part of his work,as a Doctor he can't just ignore his patients batareda wani kwakwaran hujja ba bayan yasan she really need him.......
Yana nan tsaye har suka fito da Magajiyan,sawa yayi suka kwantar da'ita kan tabarmar dake gurin kafin ahankali ya tsuguna gabanta yana mamakin rayuwa dakuma duniyar kanta baki daya,kamarfa jiyane matan nan ke Mulki acikin Masarautar nan,kaman jiyane takeji da izza take kuma wulakanta mutane yanda taga dama don babu inda zaka shiga cikin masarautar zazzau kace *MAGAJIYA* ba ace maka ansantaba kama daga kan Bayi,Yan fada, dogaraye harma Matan manyan fadan don dukansu sara mata sukeyi tareda bata daraja hakanan suke tsananin tsoronta........
Yau ina Sarautar tata,Ina izzar,Ina kuma wannan mulkin da takeji dashi ada,she's just here laying infront of him helplessly and in need of his help as a Doctor wanda shikanshi bashida tabbacin kozai iya taimaka mata ayau din dubada yanayin ciwukan jikinta because yanada tabbacin yau drip dinma dakyar inze shiga jikinta...........
Tashi yayi ahankali jiki sanyaye don haka kawai yakejin tsoron Allah yana kara shiganshi sakamakon abunda yake ganin kafin yadubi dogarayen yace"bana tunanin zan iya taimaka mata yau Kam inaganin zaifi akaita asibiti don jikinta tsanani yake karayi"............
Jiki ah sanyaye daya daga cikinsu yace"to kafada ma Mai Martaba din mana"....
Gyada mishi kai kawai yayi kafin yafice,straight fada yawuce koda yasamu Mai Martaba din cewa yayi shiba ruwanshi kuma baiyarda kowa yafitar da'ita daga masarautar nan ba duk abunda za ayi mata ayishi within nan",to kawai likitan yace kafin yayi ficewarsa donshima yanayine don Mai Martaba din anma tunda yanuna yacire al amuranshi cikin maganar to shima miye nashi?...
Shiyasa ma yana fita ah fadan yayi wucewarsa gidansa batareda yasake waiwayar inda Magajiyan take ba..........
Dad dake zaune tareda Mai Martaban ne yadubeshi bayan Doctor din yafita sannan yace"bekamata kace hakaba Abdulrahman",dasauri Mai Martaban yakalli Dad din yana mamakin jin haka daga gareshi kafin yace"Yaya badai kanason kacemin inji tausayin wannan matar baneba?".........
Jijjiga kai Dad yayi sannan yace"nibance kaji tausayinta ba Abdul but", Mai Martaba baibari Dad din yakarasa ba yace"But what Yaya,ah tunanina kafi kowa sanin who she's and kafi sanin abubuwan da tayimana inanan dakai mukaje gurinta kwanan nan after abubuwan dasuka faru batada sign of regret ko kadan ah tattare da'ita sema zuciyar ta dake cikeda bakin hali dakuma neman hanyar daukan vengeance akanmu",jinjina kai Dad din yayi cikeda gamsuwa da maganar kanin nashi,ajiyar zuciya Mai Martaba yayi sannan yace"then why do you expect me to pity such a person,why do you want me to care Yaya!bayan mutumin dakakeson intaimaka ma din babu abunda takawo ma family na inbanda badluck dakuma tragedies", yakarashe maganar ranshi ah bace ahankali Dad yadaura hannunshi kan kafadun Mai Martaban sannan yace"Calm down Abdulrahman,ba abunda tada hankali baneba,I know Magajiya has wronged you in everyway sede kaida ita akwai banbanci you're a Muslim Brother and a leader as well besides she's in a situation datake tsananin bukatar taimako so baikamata kajuya mata baya ba,kai don Allah zakayi badon halinta ba kuma aidon ka taimaka mata bahakan na nufin anyafe matabane ba, when she gets better zata cigaba da zama ah prison din ina........
Shidai Mai Martaba maganar Dad ko kadan bai shigeshiba don wallahi ko kadan bayajin zai ji tausayin Magajiya,tariga ta cuce shi and he cannot forget that shine kawai,ganin baice komai ba sekawai Dad din yaja bakinshi yayi shiru sunanan zaune har wani daga cikin Dogarin yasake zuwa yana sake fadama Dad din halin da Magajiya ke ciki,don harcemasa yayi yanzu ko motsi batayi cikeda tashin hankali Dad din yatashi yafice zuwa gidan horon nan yaga halin da take ciki sawa yayi aka sake kira mishi Doctor din daga gidanshi,koda yazo cewa yayi he cannot do anything kaman yanda yafada ma Mai Martaba dazun advisebely sukaita hospital shine kawai shawarar dazai iya basu atake Dad din yasa akawo ambulance ............ +
STORY CONTINUES BELOW

Karar siren din ambulance dinne yajawo attention din mutane da dama dake cikin masarautar,nan aka shiga neman ba'asin abunda yafaru don duk randa akaji abu irin haka to tabbas rashin lafiyar me tsanani ne da likitocin masarautar kansu bazasu iya handling ba se anfitar da marar lafiyar asibitin gari........... 
Kan kaceme rashin lafiyar Magajiya ya gama karada masarautar barin ma tsakanin Bayi da Dogaraye dasuka fi kowa iya gutsiri tsoma da gulma, Zaliha ganin masu aikinta sunata kus kus yasata kiran Lantana tana tambayarta lafiya,jikina bari lantana tashiga fada mata rashin lafiyar Magajiya din don daman Itama neman hanyar fadan take tun dazu sede tsoron karta fada ba atambayeta ba yazama wani laifin yasata yin shiru.........
Cikeda tashin hankali Zaliha tace"kikace antafi da Mama asibiti?"......
Gyada kai Lantana tayi sannan tace"Gimbiya harcewa fa akayi naman jikinta fita sukeyi dakansu",wani maka Zaliha takai mata tana"hankalinki daya kuwa,matsala na daku Bayi kunada jahilci wallahi tayaya naman mutum zena fita",cewar Zalihan ranta ah matukar bace itadai Lantana yin kasa dakai tayi kamar munafuka tana karacewa"Allah kau haka naji anacewa Gimbiya" ........
"Yimin shiru dallah inkuma bahaka ba kitashi kifitar min ah dakin",cewar Zalihan hakuri Lantana tashiga bata sannan Zalihan take tambayarta ko Sulaiman din nada labari........
Nan tace mata gaskiya dakyar in yasani,cikeda tashin hankali tafice zuwa bangaren su Asma'u don tanada tabbacin anan zatasamo Hamida don ta fada mata at thesame time kuma tashiga trying number din Sulaiman din............
Sede kwata kwata baya dagawa,yarfa hannunta take tana sauri har kaman zata fadi yayinda tacigaba da kiran number nashi tana fadin"pick the call Sulaiman, pick up the call please!".....
Ana biyar dinne yadauka batareda ta amsa sallamar dayayiba tace"where are you Dear?".......
Jin muryarta wani iri yasashi cewa"what's wrong Zaliha,wani abunne yafaru?"........
Rasa abunda zatace masa tayi kawai seta saki kuka tana fadin...
"Mama Sulaiman,come home now please", bakaramin bugawa kirjinshi yashiga yiba tunda har Zaliha takirashi da Sulaiman ayaudin yasan tabbas ba lafiya ba hakanan yanda yaji muryarta ma kadai ya'isa yafada mishi cewa something is very wrong.........
Yanason ya tambayeta meya samu Mama sede gabadaya yakasa ma sabida tsoron ansar dazata bashima yakeji cikin sauri yabar site din da ake gyaran donkuwa yana cikin masarautar daman ba nisa yayi ba hakanan yataho bangaren shi hankali tashe sede batanan,clinic din masarautar yaje nan ma baswanan cikeda tashin hankali yaciro wayarshi da niyar kiranta sega call dinta yashigo kuma dagawa yayi cikin sauri yana tambayar ta inatake,murya araunane Hamida tace suna bangaren su Almustapha amma zasu tafi asibiti yanzu don ance antafi da Magajiya din asibiti already........
Goge zufan dake keto mai yayi sannan ya katsewayar. ah parking lord suka hadu harda Asma'u donsu Afiya kinzuwa sukayi wanda hakan bakaramin kona ran Zaliha yayiba itakuma Sumayya ana mata gyaran jiki babu yanda ta'iya dukda koda ta biyosun ma ba sabida Magajiya bane ba but for her Yaya Sulaiman,she wants to be with him and console him..........
Sharara gudu Sulaiman din yadingayi harsuka isa asibitin shika wanda Allah ne kadai yakaisu lafiya, ahaka harsuka Isa emergency sede da mamakinsu haryanzu ba'a karbi Magajiya dinba, tana nan kwance akan gadon da ake tura marasa lafiya da mamaki yadubi driver da nurse din da suka kawota yana"why are you still here ko basu ganin ankawo patient ne?".......
Jiki ah sanyaye nurse din tace"sunce bazasu karbeta ba", Sulaiman da ranshi keyi mashi kuna yace"why?"......
Shiru sukayi dukansu,buga table din yayi cikeda bacin rai yana kallon nurse da driver din sannan yace"I'm asking you something for goodness sake?".....
Jikina bari nurse din  tace"Because she's Magajiya".......
Wani irin look Sulaiman yamata sannan ahankali yakuma furta kalmar wai"because she's Magajiya?"......
Asma'u daranta yabaci tace"is she a devil ko itan ba mutum baceba da baza aji tausayinta adubata ba ah arin wannan condition din,tukunnan ma ya akayi sukasan itace",tayi maganar ah kafule dasauri Nurse din tace munzo da file dinta ne and  Doctor din yaga sunanta, Asma'u dasauri tayi hanyar da take tsanmanin nanne office din doctor din amma sai Sulaiman yayi saurin shan gabanta cikeda bacin rai tace"kabarni Yaya Sulaiman i need to bring them back to their right senses, patients dinma harsai sunzabi wanda zasu duba don wulakanci?"..........
Jijjiga kai Sulaiman yayi jiki ah sanyaye sannan yace"inkikaje mezaki ce musu?"...
STORY CONTINUES BELOW

Da mamaki tace"mezan cemusu fa kace?"...
Gyada mata kai yayi sannan yace"they're right Asma'u,Mama tayi abunda is unforgivable and she's paying for what she did now, I can't blame them nor you so, it's better we just leave"......
Zatayi magana yajijiga mata kai sannann yajuya yafice ah gurin gabadaya yama rasa abunyi,to yanzu insukaje wani asibitin ma may be thesame thing za afada musu komi?..... 
binshi 
sukayi inda yace sumaida Magajiya din cikin mota haka sukaje wani private hospital acikin Zarian dukda yaso suwuce gida kawai amma Asma'u ta matsa sede alhamdulillahi su sunkarbeta amma fa sunkasa bata attention koda kadan ne se magun guna dasuka rubuta wai asaya abata and advisibly su fitar da ita waje kawai don su basu taba ganin cuta irin wannan ba Allah yagani............
To kawai Sulaiman din yace don dama abunda yayi planing kenan bayan anki karbansu ah dayan asibitin dasuka jedin,dukyanda kakai ga rashin imani inkaga Hamida da Sulaiman saisunbaka tausayi,dafa gadon datake yayi ahankali aranshi yana fadin to kenan ayanda take sume zasu barta har lokacin tafiyarsun yayi komi?........
Aedai koba komai ayimata taimakon gaggawa dazaisa tafarfardo daga suman datayi wanda hakan ne zebasu hope din cewa she'll wake up soon,dafashi da Hamidan tayi ne yasashi juyowa yana kallonta ahankali tace"mukoma gida kawai Sulaiman".........
Gyada mata kai yayi jiki ah sanyaye hakanan yana mamakin yaushe jikin mahaifiyar tasu yakoma haka tunda shiba zuwa ganinta yakeyi ba,anhana su kai bama shikadai bama babu wanda kezuwa mata ziyara asanda take gidan horon,he was busy preparing for his wedding while his Mother is suffering,he was busy jubilating wanda hakan yasa yamanta da al amuranta nawasu lokaci,ahaka suka kwasheta suka koma gida da'ita Sulaiman baiyi tunanin komai ba yace akaita bangarenta babu musu kuwa sukayi abunda yace din straight bandaki yashiga yadebo ruwa ah rubber sannan yazo yazauna gefenta dukda warin da jikinta yakeyi hakan baisa yadamuba sema diban ruwan dake rubber dayayi yashiga yayyafa mata ahankali aikuwa segashi tafara motsi da jikinta bashi kadai ba har Hamida wani irin wawan ajiyan zuciya sukayi tareda hamdala....... 
Kuka Hamida keyi sosai harda shesheka yayinda sautin kukan nata ne yasa Magajiya tafara bude idanunta dasuke mata dishi dishi dakyar tasamu suka budu sannan tadaura su kan Hamidan, bakaramin mamakin ganin yartata tayi ba amma batada bakin magana don ayanda takejin jikinta ko A dakyar inzata iya cewa,matsowa Hamidan tayi tana sannu Mama yayinda haryanzu batabar kukan datakeyi dinba.. ..
Shima Sulaiman din sannu yashiga yimata haka Zaliha ma dake can tsaye Asma'u kuwa tunda suka dawo take bangaren su daman batareda ita sukazo bangaren Magajiya dinba......
Itadai se binsu da'idanu kawai takeyi dukda ita kadai tasan yatakeji aranta game da kowannensu ganin shirun yayi yawane yasa Zaliha cewa bari taje tasa ahado kayan abinci intaci setasha maganin may be tasamu taji dadin jikinta.....
Gyada mata Kai Sulaiman din yayi inda tafice cikin sauri.........
Koda Zaliha tadawo bayinta na biyeda ita da kulolin abinci nan akashiga zuba ma Magajiya din,amma gabadaya kinci tayi don ko sun saka mata abakima dawowa dashi takeyi haka sukayita rokonta taci amma taki hakanan babu yanda suka iya suka hakura,Sulaiman dinne yashiga ballo maganin daya bayan daya kaman yanda likitan yayi prescribing sannan ya bude bottle of water yazuba ah cup tareda mika mata amma shidinma kin sha tayi don dukyanda yaso tabude bakinma ki tayi sema matsesu da take sakeyi besan sanda hawaye suka shiga running ah cheeks dinshiba,it hurts seeing her like this amma yazaiyi?......
Hakanan inbata taimaka musu wurin shan maganin ba ta'ina zata samu lafiya fisabilillahi.......
Tashi yayi jiki ah sanyaye yabar dakin yana share kwallarshi don yasan inyacigaba da zama daga shi har Hamidan za arasa mai rarrashin wani bayan kuma shine namiji,he should be strong if not for himself then for his Sister and her unborn child,shiyasa ma yanzun yakoma parlour yazauna inda yabar Zaliha da Hamidan ah daki .......
Bangaren Almustapha kuwa tun bayan da yabar dakin Ummi masallaci yawuce yayi sallah sannan yadawo dakinshi yacigaba da ayyukanshi cikin system dinshi dukda yaso Asma'un tazamanto tana kusa dashi amma kwata kwata batasake shigowaba shima kuma dake yanada abunyi sebe damu dabinta ba,ahaka har sallar maghrib tayi,bakaramin mamakin rashin ganin Sulaiman dayayi ah masallaci yayiba don ko la'asar ma baiganshi ba sede baiyi wani tunani ba may be baya masarautar ne amma yanzu kuma seyakejin kaman something is wrong don haka yaciro wayarshi yashiga kiranshi sede haka yayita ringing bedauka ba,jiyayi andafa kafadunshi ahankali yajuya don ganin wanene..........
Dad ne murmushi yasakar mai tareda cewa"Son wakake jira tundazu.",don yajima cikin masallaci yana hangen Almustapha na tsaye,cikeda damuwa Almustaphan yace"I'm trying to call Sulaiman banganshi ba tunsafe" ......
"His Mother is sick",shine kawai abunda ya'iya cewa da mamaki Almustapha yace"you mean Mama?"....
STORY CONTINUES BELOW

Gyada mishi kai yayi cikeda damuwa Almustaphan yace suna Ina?.....
"Bangarenta" cewar Dad din nan kuma yamasa bayanin da Sulaiman din yamishi bayan sundawo daga hospital din hankali tashe yayi bangaren Magajiya din because he's fully sure Sulaiman hankalinshi atashe yake and he really needs someone to be with him.........
Aikuwa samunshi yayi ah parlourn ya'idar da sallah kenan zama yayi kan daya daga cikin kujerun dake parlourn yana iya cewa this's the very first time daya shigo bangaren Magajiya not because he wanted to but only because of Sulaiman din wanda gani yakeyi bashida kamarshi aduniyar nan and he can proudly say that he's the best Brother ever.......
Yananan zaune har Sulaiman din yagama addu'o'inshi kafin yataso yazo gefenshi yazauna batareda yace komaiba dafashi Almustapha yayi sannan yace"yajikin nata?"........
Dasauki kawai Sulaiman din yace yayinda yake mamakin ganin Almustapha din don ah tunaninshi he'll be the last person to have some pity akan Magajiya,cireshi yayi daga trance dinshi tahanyar cewa...
"Dad yace kana planing fitar da'ita waje so,how are the preparations?"....
"I don't know either",shine abunda Sulaiman din yace mishi don ko tunanin wani kasa zaikai Magajiyan ma baiyiba bare har azo ga batun booking flights dadai sauransu donshi gabadaya kanshi ah daure ma yake hakanan yanaji gabanshi na faduwa akai akai batareda yasan dalili ba.........
Batareda Almustapha yakuma cemishi komai ba yaciro wayarshi ah aljihu nan yashiga kiran Dr Na'im ba ajima ba kuwa ya dauka nan yake fada mishi sunada patient ne agida inba matsala yazo gida yanzu akwai maganar dayakeson suyi ........
Daga daya bangaren Murmushi Na'im yayi sannan yace"I'll only come if za abar Amarya tayimin wannan hadaddiyar jollof din dankalin".........
Jijjiga kai Almustaphan yayi yana"Na'im baka da matsala fa"....
Shima dariyar Na'im yayi kafin yace"I'm just kidding, I'll be on my way insha Allah",godiya Almustapha yayi masa kafin yayi hanging up call din yasan Na'im will be of help tunda shiyanada interaction da Doctors da dama from other countries hakanan yafishi sani sosai so,he might advice them inma bazai iyaba zai iya hadasu dawanda zai iya taimakonsu........
Aikuwa ana idar da sallar isha Na'im din ya'iso wannan dalilin yasa suka karasa bangaren Magajiya din tareda su Almustapha din donsuma daga masallaci suka fito, straight dakin da Magajiya din take suka shiga da sallama.........
Hamida na sallah kan sallaya yayinda hawaye kebin kuncinta tana ta aikin nemawa mahaifiyarta yafiya da sauki gurin ubangiji Na'im bakaramin faduwa gabanshi yayiba ganin yanda fuskarta ke dauke da damuwa gashi uwa uba hawayen dake bin kuncinta dayake jinsu kaman anwatsa mai ruwan dalma ah zuciyarshi dakyar yayi karfin halin dauke kanshi daga gareta yana istingifari aranshi don Allah yagani bemasan ta'ina zaifara cire abunda yakeji gameda ita daga ranshi ba bayan kuma itan matar aure ce...........
Duba jikin Magajiya yashiga yi jiki ah sanyaye wanda one look yayi mata yasan"her condition is really critical and chance din survival dinta is really low",amma mi yabudi baki yace musu hakane bayan bashi ke iko da duniyar ba bare abun cikinta hakanan bayason yafurta abunda zaizo yadameshi daga baya don haka yace"kunkaita asibiti ne?"....
Gyada kai Sulaiman din yayi sannan yashiga fada mishi yanda sukayi da Doctor din,jinjina kai yayi sannan yace Skin Doctor yakamata tagani, this's not my field nor Almustapha's so,inaganin kawai kufitar da'ita wajen kaman yanda suka cemuku don likitocin nan ma ba lallai suyi muku abunda nawajen zasuyi ba besides her condition is really critical yakamata kuyi making nashi quick..........
Wannan karan Almustapha ne yace"do you know any Skin Doctor dazaka iya hadasu dashi kokuma wani hospital kake tunanin zasu kaita?"....
Kai tsaye Na'im yace"I know someone, *Dr. AS Kumar.* He's the best Dermatologist in India yana aiki in one of their hospitals " *Gleneagles Global hospital, L.B Nagar,Hyderabad*, he's very talented infact nataba hadasu da wasu da Yarsu keda skin problem,yayimata aiki and it was successful karkaso kaga yanda iyayen sukazo suna yimin godiya daga baya,so inba damuwa zan iya hadaku dashi but I've to talk to him first".........
Cikin sauri Sulaiman din yace"kayi mashi magana don Allah",to Na'im din yace kafin yadago wayarshi yashiga kiran number din mutumin aikuwa sunci sa'a yadaga haka sukayi magana and alhamdulillah yace yana gari so they can come nan Na'im yayi musu bayanin yanda sukayi da mutumin inda Sulaiman yace"we're living tomorrow insha Allah,ta private plane din Abba dukdama bansani ba kozai bari".....
Cikeda tausayin kanin nashi Almustapha yace"I'll talk to him", Sulaiman baisan sanda ya rungumi Almustapha dinba yana masa godiya don yasan bakowane zai iya yin abunda Almustapha din yakeyi mashi ayanzu ba,sunjima suna tareda Na'im din don har complain din rashin cin abinci da Magajiya din keyi Sulaiman din yayimasa amma Still abunda likitan masarautar yace shima yace"itane yakamata ta taimaka ma kanta taci abinci,the only help we can give her is drip dinnan and nothing else shikuma yanzu bazai zauna ajikinta ba so,kawai lallabata zakuyi tanacin abincin inzai yuyu"......
STORY CONTINUES BELOW

Se after ten sannan Na'im yabar gidan har mota Almustapha ya rakashi kafin yadawo yayima Sulaiman din saida safe tareda mishi nasihan yakwantar da hankalinshi sannan yawuce nasu bangaren,wanka yayi yayishirin bacci yana mamakin rayuwar kanta bakidaya, kaman fa jiyane Magajiya ta addabi rayuwarsu but look at what she has turn into now, Allah kenan,Shiba azzalimin bawansa bane ba hakanan baya bacci sannan dukwanda ka cuta to tabbas zaibi maka hakkin ka koda kuwa ba'anan bane ba but Magajiya kam he's very sure tundaga nan tafara ripping abunda ta shuka dukdama baijimata dadi ba because despite everything that happens Allah yagani baitaba yimata irin wannan fatan ba donshi da yau zata shiryu ma babu abunda zaihanashi yafemata yakuma nema mata yafiya gurin iyayenshi ma besides koyaki koyaso  tariga tahada dangi dashi tunda she's a Mother to his siblings..........
dawadannan tunane tunanen yagama shirinshi cikin pjamis dinshi da riga sannan yayi hanyar dakin Asma'un don yanada tabbacin ita bazuwa zatayiba tunda yanzu Hajjan tatafi shikuma yariga dayasani he'll find it difficult to sleep indai bata taredashi shiyasa ma bai yaudari kanshi ba...........
Koda yashiga dakin tana bandaki kawai seya zauna kan gadon yana karema dakin nata kallo dayake fes fes dashi,ko'ina very neat and tidy gakuma sanyayyar permanent kamshin jikinta dana turaren wutan datasaka suka hade guri daya suka bada wani scent me dan karen dadi,yananan kwance yana tunanin duniya harta fito daga wanka baima saniba,Itama tunda suka dawo daga asibiti Ummi tasata agaba wai Itama sai anmata gyaran jikin nan sannan yakamata tarage fita daga bangarensu hakanan tunda bikin auren su yakusa inma ayyuka ne ai akwai wanda zasu iya kula dashi basaida itaba dan Ummin kwata kwata batada labarin rashin lafiyar Magajiya din don bai isotaba itakam hakanan su Afiyan ma basu fada mataba shiyasa ma tazauna akaita tsuma ta dayanman nan din hakanan matar tadinga shafa mata wasu abubuwan da itakanta batasan menene ba wanda se yanzu akabarta tazo tawanke jikinta.......  
Tunda tagama wankan takejin wani irin sauyi na daban ah fatanta,yayi laushi,yayi fresh sosai hakanan wani kamshi na daban yashiga fita ah duka illahirin jikinta wanda itakanta hakan bakaramin shauki yake sataba dakyar ma ta'iya baro bandakin tafito dan kasa gajiya da kallon fuskar ta da skin dinta ah madubin bandakin tayi, straight gaban wordrobe dinta tayi inda tabude tadauko kayan baccin dazata saka don kwata kwata ma bata lura dashiba seda ta dauko kayan data tajuyo sannan taganshi, bakaramin mamaki da razana tayiba sede ganin hankalinshi baya kanta ma yasata yin sanda takoma bandakin,seda tagoge jikinta sannan tasaka kayan baccinta tafito still idanunshi na kafe ah wani bangare na bangon dakin aranta cewa tayi"to tunanin me yakeyi haka?",don tanada tabbacin da yaganta bazai barta hakanan ba seyayi yanda yayi yajata zuwa jikinshi ko yakafeta da mayun idanunshi koda kuwa bazaice mata komai ba wannan dalilin yasata karasawa kan gadon zaman datayi ne yasashi dawowa daga trance dinshi fuskarta dauke da damuwa tace...
"Yaya imam tunanin me kakeyi?"............
Batareda yacemata komai ba yatashi daga kwancen dayake wanda daman yayi pillow da hannunshi ne kafin yamaida kanshi kan cinyarta yana kallon kananan Calabar din dake kanta wanda shekaran jiya Sumayya tayimata  su sama sama don daman bawai ta kware baneba...........
Dan turo baki tayi tana"kanka nauyi Yaya", murmushi yayi yanasake gyara kwanciyar shi harda dan bugun cikinta da kanshi dukwai neman magana yakeyi,ture kanshi takesonyii amma takasa sema sonjin meke damunshi dake ranta haryanzu din don haka takuma cewa"tunanin me kakeyi tundazu?".....
Kamo hannunta yayi sannan yasaka cikin lallausar gashin kanshi tareda lumshe idanunshi,kobai fadaba tasan massaging kanshi yakeson tayi don haka setashiga yimashi batareda takumayi mashi tambayar dazun ba donta lura kamar bayason maganar ne. Bayan kusan mintuna uku kuma setaji yace"I was just thinking about life"...........
Dan tsayar da massage din datake mishi tayi wanda hakan yasashi bude idanunshi yadaura cikin nata kafin yacigaba da magana"I never thought things will turn out this way Wife,the fact that we're now happy and Magajiya is behind boss abunna matukar bani mamaki".......
Itama jiki ah sanyaye tace"yea rayuwar kenan Yaya Imam hakanan kuma babu abunda Allah baya iyayi,you just have to trust him and I assure you he'll never let you down, mahakurci mawadaci gashi yau hakurin ku dakuma addu'o'inku yadawo muku da farin cikin ku wanda har hakan yakansa kuma manta irin hardships dinda kukayi going through abaya,so ni aganina baikamata kayi mamaki ba shi Allah akoda yaushe yana bayan maigaiskiyane".....
Jinjina mata kai yayi tareda sake riko hannunta yanasake cusawa cikin lallausar gashin kanshi alamar tacigaba dayi masa tausar data fara ta bari din, murmushi kawai tayi aranta tana fadin"Uban miskilaye",kafin tatashi tadauko man gashi ah kan mirror dinta tadawo tamaida kannashi kan cinyarta shidai baice mata komai ba haka tashiga lakuta tana shafawa tana massaging kan nashi jitayi yace"And do you know that despite all that she has done I'm really feeling bad for her bayan kamata yayi inji dadi ma", tayaya ma zakaji dadi Yaya imam?.....
You're not like her, you're a great Muslim kanada zuciyar Imani hakanan you've gone through alot of pains din da ko ah mafarki bazakaso koda makiyinka ne yayi going through ba,she might have hurt you likewise she might have make your life miserable but nariga nasani you'll never wish to see her in pain Yaya,I trust you with that", takarashe maganar ahankali shikuwa lumshe idanun yakumayi yanasake jin kalamanta nashiganshi,babu wanda maganarshi dama kuma muryarshi ke tabamai jiki da bargo irin Asma'u,komai tafada jinshi yakeyi nadaban ne wani sa'in yakan alakanta hakan dacewa dondai shibaiyi hulda da mata bane ba hakanan she's the first lady dinda daba muharramin shiba data fara Hulda dashi kafin aurensu,lokaci daya kuma maganarsu da Ummin na ranan yaudin yafado masa arai wannan dalilin yasashi sa hannunshi duka biyu yakamo hanneyenta dake cikin gashin kanshi sannan yatashi ya yazauna ah tsakiyar gadon tareda folding legs dinshi dasuke gogan nata ah yanzun hakanan suna facing juna,kallon hannunsu dake sarke dana juna yayi sannan ahankali yadago yakalleta...
"I want us to talk about something"..............
gyada mishi kai kawai tayi yayinda zuciyarta kuma ke aikin bugawa akai akai,shiru yayi nadan wasu dakiku don ya rasa ta'ina ma zaifara maganar,dakyar dai can yayi karfin halin cewa"Don't you think zaman mu akwai gyara?".......
Wara idanu tayi da mamaki,baijira cewartaba yacigaba...
"I mean we're married for more than 4months now amma dagani harke babu wanda yasan inda relationship din yadosa,we need to make a change Asma'u,we need to make a decision",yakarashe maganar almost in a whisper...........
Kallonshi takeyi babu ko kiftawa hakanan idanunta suka canza launi lokaci guda muryarta na cracking tace"dec..isi...on kuma,ni ka...m b...amun rig...a munyi shiba tun kwanaki?".........
Batareda yasaki hannunta ba yasaki murmushi tareda dan janyota yajuyata inda bayanta yake kallo yanzu sannan yadaurata kan cinyarshi tareda sakalo da wuyanshi ta kafadunta hakanan yasaka hannayenshi yazagaye tiny cikinta yana dan matsawa wanda hakan yasata shiga wani irin yanayi,lumshe idanunshi yayi tareda kai bakinshi daidai kunnenta"wani irin decision ne muka yanke",yayi maganar cikin rada dukdama sarai yasan decision din kawai yanason tasake fadane shikuma seya bata ansa yanda yadace,turo baki tayi gaba hakanan taji takasa tashi daga jikin nashi yau, "uhmm tell me",yasake maganar ahankali wannan karan har shivering seda jikinta yayi dakyar tayi karfin halin cewa"Kai kace you'll free me from this relationship,that was our agreement Yaya imam So, nibanga abun sake tada maganar ba infact I'm just waiting for the right time,I mean kace after your turbaning ceremony you'll let me go".....
"Can you really live without me?",yayi mata maganar tareda juyo da'ita tana kallon cikin idanunshi wannan karan dukdama haryanzu tana zaune kan cinyar tashi,jitayi idanunta sunciko da kwallah sakamakon kalaman da taji yayimata din,can she really live without him kaman yanda yatambaya din,tabbas tasan it'll be difficult hakanan batada ansar bashi sede meyake nufi?.... 
intace bazata iya rayuwa babushi dinma cewa zaiyi yana sonta komi?.......
Ganin tana shirin yimai kukan data saba akullum yasashi dora fuskarshi kan nata tareda saka bakinshi cikin nata seda yayi kissing nata mai isarshi sannan yabude idanunshi yadaura cikin nata still fuskarsu na gab dana juna In a whisper yace... 2
_"when you're in love with someone,you stick to them Asma'u"_
Nasan kina Sona...
_So, Love me like you care,I won't stop you!_
_Kiss me like you dont.I won't say No_
_"Hug me forever, I'll never turn my back on you_"
_"Crush me forever Asma'u,Tell me you love me and never let me go_"......
_"Because I'm yours, hakanan I've nothing to pay you in return for all your favours than this_"...
Yayi maganar ah raunane wanda hakan yakara speed din hawayenta dake zuba non stop. For a moment tayi tunanin she's getting her love in return ashe bahaka baneba,ashe shi tausayinta yakeji, asheshi he's trying to pay her ne for all that she's done for him ne and nothing else bayan kuma besani ba hakan dayayin yafi hurting feelings nata, batasan sanda tashiga bugun kirjinshi ba dadan karfi kafin tace cikin kuka"Banaso ni,I just want you to let me go bazan iya zama dakai ba Yaya imam"........
Bakaramin zafin maganarta yajiba don jiyayi kaman tacaka mai kibiya ah kirji dakyar ya'iya cewa"Why,miyasa bazaki zauna daniba?"....
Am I not worthy of being your husband?.......
Cikin sauri tashiga jijjiga masa kai kafin cikin muryar kuka tace"because you don't love me,nikuma bazan iya zama dawanda baya sona ba" ....
Lumshe idanunshi yayi yanajin kukanta har cikin ranshi kafin yakuma duban cikin idanunta....
"Indai wannan ne dalilin ki then,i'm not letting you go Asma'u you better put this at the back of your mind", yakarashe maganar tareda kwantar dakanta jikinshi hakanan yana tapping bayanta in order to calm her down ko Allah zaisa tadaina kukan....
Itakuwa Jin abunda yace din yasata kuma bugun kirjinshi tana"Why are you so selfish Yaya Imam?".......
Dan ajiyan zuciya yayi sannan Ahankali yace"By Allah,I don't know Asma'u,nima bansan daliliba,abu daya nasani".....
"You're now part of my family So, I'll never let you go shiyasa ma gwanda kikwantar da hankalinki mu fahimci juna",dakin yayi shiru sosai inbanda sautin kukanta babu abunda kakeji karawa yayi da"to inma nasake ki laifin me zance kinyimin bayan babu abunda kika cika rayuwata dashi sai alkhairi"...
"Inna sake ki dawani idanu zandubi iyayenmu bayan su gani suke zaman lafiya mukeyi tunda,bakya tunanin inmukayi yunkurin rabuwa batareda wani kwakkwaran daliliba zamu iya hurting iyayenmu dama kuma wanda muke tareda su?",wannan shine tambayar da Almustapha yayi mata,itadai kasa cewa komai tayi don tasan kotayi maganar ma ba anfanarta zatayi ba tunda ya dage kuma tariga da taga yarda sakin tan ne bazaiyiba tunda har yayita mata kwana kwana,to gashi yau yafito fili yafada ma besides batadama strength din yin magana hakanan tana tunanin kenan yana nufin auren su babu rabuwa har abada hakanan yana nufin yanzu itan matarshi ce tahar karshen rayuwarshi komi?......
Can she really accept him as her husband harma suyi rayuwar aure kamar kowani ma aurata despite knowing ba sonta yakeyi ba tunda everything he's doing now is out of pity and nothing else. Sannan
What of those issues,the issue of drinking da haryanzu batasan miye asalin abunba,itakam tashiga uku she's so confused and in a dilemma hakanan itakanta tarasa matakin dazata dauka. Bangaren Almustapha kuwa baifasa rarrashinta ba hartayi baccin wahala ajikinshi ahankali yakwantar da'ita kan gadon tareda lulluba mata blanket yana kallon kyakyawar fuskarta,shidai yasan this's the best decision and yanagani hakan ne kadai zaisa takwantar da hankalinta ta karbi aurensu hannu bibbiyu kamar yanda yakeda niyar yi tadaina ramar da takeyi dinnan,atunaninshi bema kamata tana tunanin whether he loves her or he does not ba tunda he's ready to fulfil all her needs hakanan bashida burin daya wuce ya faranta mata akoda yaushe to mekuma take bukata bayan wannan?......
Aiko shi butulune baya bakanta mata ba don seyanzu yake gane how important she's to his life, dawannan tunanin yatashi yashige bandaki don dauro alwala sannan yazo yatada sallah tunda bawai bacci yakejiba hakanan kuma dare yayi sosai........Asma'u koda tatashi da asuba Almustapha yafice masallaci wannan dalilin yasata rufe kofar dakinta da makulli sannan tawuce bandaki don yin alawala. Koda ta'idar da sallar kasa kwantar da hankalin ta tayi guri daya bare hartasamu strength dinyin addu'a,tabbas she's in a dilemma hakanan tarasa wani mataki zata dauka ayanzun gashi Yaya Aliyun datace zasuyi shawarar ma baya gari kuma babu ranar dawowansa besides ko yananan ma batada strength din fadamasa komai dallah dallah kaman yanda zatayi da mace Yar uwarta......
Ahankali kuma setaji Asiya yar uwarta tafado mata,yes Asiya can be a good companion and she's sure zata bata shawara maikyau gameda abunda kefaruwa hakanan she can keep it to herself batareda kowa yasani ba,sede mi?
Asiyan ai bata gari tana kaduna itakuma tafison suyi magana face to face bata waya ba,daga karshe dai deciding zata kira Asiyan in anjima tayi kafin tatashi taninke sallayar sannan takoma takwanta don Ummi tace tadaina shiga kitchen yanzu tabari harsai bayan bikin aurensu besides yanzu gyaran jiki akeyi masu..  ......
shikuwa koda yadawo sukayi karatu dasu Afiya dakinshi yawuce don shirya wa yafice gun Sulaiman din daganan kuma yawuce gun ayyukan dake kansu tunda Sulaiman dinma balokacine dashiba yanzu sakamakon rashin lafiyar da Magajiya  keyi......... +
Bangaren su Sulaiman kuwa tun wuraren hudun asuba jikin Magajiya ya matso sosai donkuwa lokaci guda idanunta suka canza launi gawani irin numfashi datakeyi da sukansu sunrasa gane dalilinsa addu'o'i yakeyi mata hakanan yana fadan wasu afili tareda rokonta tana maimaitawa amma takasayin koda guda dayane sebinsu da idanu da takeyi,ahaka yaje yayi sallar yadawo bangaren nata, zama yayi gefenta tareda riko hannunta yanadan mammatsa cikinsa hakanan yana tayimata addu'o'i aransa yayinda Hamida ke zaune kan sallaya tana sallah haryanzu.......
Sulaiman still narike da hannun Magajiya kawai jiyayi tadamke hannun dakarfi wanda hakan bakaramin tsoratashi yayiba,kirjinshi na bugawa yadubeta sekuma yaji tasaki hannun ahankali hakanan idanunta dayake kallo ah yanzun sun kafe guri daya, innalillahi wainna ilaihir rajiun shine abunda yashiga furtawa hakanan bugun zuciyarshi nacigaba da karuwa, addu'a yake aranshi Allah yasa kada abunda yake tunani yazama gaskiya,wani irin zufa ne yashiga keto mishi lokaci guda hakanan yakasa aiwatar da komai sema zaune dayake agurin kaman gunki har Hamida ta gama addu'o'inta. bayan tanade sallayar sannan tazo da niyar duba jikin mahaifiyar tasu sede da mamaki taga idanunta ah kafe gefe daya,cikin raunanniyar murya tace"Mamah?".. .....
Amma shiru ....
Kara cewa tayi"Mama?",Wannan karan harda dan tabata amma thesame thing sakin kuka tayi me sauti sannan tadubi Sulaiman"Sulaiman,meya samu Mama?"...
Dago jajayen idanunshi yayi ya daura kan Yayartasa da tundazu yakasa daukesu daga kan Magajiya din dake kwance,kuma tambayarshi tayi"meya samu Mama Sulaiman, kafadamun please".........
"I don't know Yaya Hamida,I don't know really", yakarashe maganar tareda sakin wani marayan kuka,harga Allah begama yarda ta rasu ba but the chance of she being alive is really low shiyasa ma ya tsinci kanshi ah irin wannan yanayin,koke kokensu ne yatado Zaliha daga baccin da takeyi don daga Hamidan har Sulaiman din anrasa mai rarrashin wani dasauri ta karaso tana tambayarsu ko lafiya amma babu mai bata amsa, kallon fuskar Magajiyan tayi hakanan itama tashiga kukan dukda nata yafi nasu don Dora hannu tayi aka tana ihu,"Nashigesu Mama ta mutu" .......
Ihun tanne yajanyo attention din Bayin dake bangaren wannan dalilin yasa suka fara taruwa,ganin abun na neman komawa hauka tsabar yanda Zaliha ke exaggerating yasa Sulaiman karfin halin ciro wayarshi yashiga kiran layin likitan masarautar,ba'ajima ba saigashi yazo don bema koma gida daga masallaci ba. Kallo daya yayima Magajiya yagane rai yayi halinsa,cikeda tausayawa yasa hannu yarufe mata idanu tareda  daukan zanin dake gefe ya lulluba mata , Sulaiman kallon likitan yatsayi galau lau lau kaman wani tababbe ganin hakan ne yasa likitan yadafa kafadar Sulaiman din ahankali tareda cewa...
"indeed every soul shall taste death Sulaiman,your Mother is no more babu abunda tafi bukata ayanzu daya wuce addu'arku".......
Shiru Sulaiman din yayi hakanan yanzu hawayen basa zuba sede kallo daya zaka mishi kagane yana cikin matsanancin damuwa hakana rayuwarshi da Mahaifiyar shi ke dawo mishi daya bayan daya tun yana dan yaro, despite her being wicked to others she was really a loving Mother don shikanshi yasani daga sama saman nan ne tafara nuna masa hali,shidinma sabida yaki bata hadin kai ne tuna best kalamanta akanshi yayi"Son yaushe zaka dawo daga London dinnan ne,mahaifinka na bukatar ka akusa dakai and you know I want you to be the crown prince ko,Kuma bazaka taba samun hakan ba harsai kazamo mai taimaka masa akoda yaushe"......
That was her advice always wanda hartakoma yin karfi dayaji wanda hakan yasa ya tattaro kayanshi yadawo gida batareda ranshi yaso ba,ahakan ma tayita lallaba shi but what he always give her was nothing but a pure pain, ahankali yasa hannunshi ya goge hawayen dake bin kuncinshi ah yanzu yayinda likitan ganin arude yake yasa yafice don sanar dasu Dad abunda yafaru........
STORY CONTINUES BELOW

Kan kacemai labarin rasuwar Magajiya yagama karada masarautar zazzau kowa nata 
jimamin abun sede fa babu wanda yayi yunkurin zuwa bangaren inbanda wanda tafi zalinta arayuwarta,don Dad was the first dayaje sekuma Almustapha next wanda kusan tare suka isa dasu Asma'u, Mom da Sumayya harma da Ummi don kuwa duk fushin dasu Afiya keyi da magajiyan behana sunjesu ba domin mutuwa ba wasa bane ba. suna shiga Almustapha yakarasa ga Sulaiman din tareda rungumarshi yanayi masa ta'aziyar rashin mahaifiya dayayi ayaudin shidai Sulaiman babu abunda yake furtawa inbanda"kuyafewa Mama please,inanema mata afuwa agurinku ko Allah zaisa tasamu rahamar ubangiji",Almustapha da idanunshi suka canza launi tsabar tausayin kanin nashi yace"Shhhhhh,nayafe mata Sulaiman believe me tunda jimawa na yafewa Mama. Allah yajikanta Allah yasa mutuwa hutu ce agareta"..........
Amin duka yan dakin suka amsa da inda Sulaiman yadinga binsu kaman zaucacce yana aikin nemawa Magajiya gafara,duk sun yafe mata suke cewa koda ya'iso gurin Ummi shafa kanshi tayi tana hawaye cikeda tausayinshi tace"Sulaiman nayafewa Magajiya tunda jimawa,kasani duk laifin da tayimin dawanda nasani dawanda bansani ba duk na yafe mata,dawanda nagani dawanda bangani ba na yafemata hakanan da wanda naji dawanda banji ba duk nayafe mata Allah ubangiji ya yafemana baki day",rungume Ummin yayi yana"nagode Ummi,nagode sosai I don't even know how to thank you keda Ya'yanki, my Mother has given you nothing but a pain amma ku dukanku zuciyoyinku are so pure and clean"......
Rarrashin shi Ummi tadingayi tana shafa bayanshi lallai Sulaiman abun ah tausaya mishi ne haka ma Hamida dakyar Ummi ta lallaba shi aka fara shirin yima Magajiya din wanka ..........
Bangaren Mai Martaba kinzuwa yayi har akayi mata sutura ana shirin yi mata sallah, Ummi dakanta ne taje tasameshi tareda nuna bacin ranta karara"mahaifiyar ya'yan naka ne kake son kin zuwa jana'izar ta komi Abdulrahman?"........
Da mamaki yakalleta sabida aganinshi kowani zaifadi haka itan bazata fadaba,yana shirin cewa wani abu tatari numfashin shi tahanyar cewa"Magajiya ta cuce mu but you cannot deny the fact that tabar mana duniyar ma baki dayanta so,ni aganina kamata yayi kamanta baya kayafe mata,ai koba komai she's a Mother to your children hakanan kana tunanin zasu ji dadine inka yi ignoring jana'izar mahaifiyar su?"...
Kallonta yatsaya yi shikam don yama kasa cewa komai,karawa tayi da"inta cuce ka abaya Allah ya yariga da yabi maka hakkinka you should be grateful for that Abdulrahman and to tell you the truth am highly disappointed wllahi,Ina addinin naka inakuma tausayinka na mutanenka da sanin yakamatanka ah matsayin na shugaba?",cewar Ummin sannan tajuya tafice tana "I hope you'll let go of your ego komai yawuce if not it'll keep hunting you kuma kaine zakazo kana dana sani daga baya".............
Binta yayi da kallo harta bacemai dagani kafin yasauke ajiyar zuciya yana kissima kalamanta,dakyar ya'iya tashi yafice daga bangaren nashi inda Dogarayen dake bakin kofa suka shuga binshi ah baya har ya'isa bangaren Magajiya din lokacin har su Almustapha sundaukota ah makara zasu kaita masallacin masarautar ayi mata sallah hakanan babu wasu mutane agurin inbanda sudin, dasaurai Sulaiman din yazo yafada jikin Mai Martaba tareda sakin wani kukan yana"Abba kayafema Mama don Allah,nasan tacuceku nasan kuma laifuffukanta is unforgivable but believe me indai harbanji kunyafe mataba hankali na bazai taba kwanciya ba"...........
Tapping bayanshi Mai Martaba yashigagi yana....
"na yafe mata Sulaiman, Allah yajikanta be strong please"....
Ahaka harsuka karasa masallacin
Kankacemai mazan masarautar sun cika masallacin sakamakon ganin Mai Martaba dasukayi yaje don da wasunsu kin zuwa sukayi sabida shi din yayinda wasu kuma sunyi niyar zuwa kodan albarkacin  Sulaiman because koba komai she gave birth to a kind person like him wanda suna iya cewa he's one of their life saviour.........
Ahaka akayima Magajiya sallah akakaita gidan ta na gaskiya,rayuwa kenan kowa mamakin abun yakeyi matuka hakanan tsoron Allah yana kara shiga jikin masu tunani acikinsu,haka aka zauna zaman makoki dukdama tsararrun mutane ne wanda duk yawanci yan masarautar ne sekuma dan dogaraye kadan don sauran duksun koma bakin aikinsu,Dr Na'im ma tareda shi akayi jana'izan hakanan yashiga yimasu Hamidan ta'aziya harcikin gida,tsakanin jiya da yau harta rame ta canza kama cikeda damuwa cewa yayi"Addu'a zakiyi mata ba kuka da tada hankali ba please".......
Yanda yayi maganar seda taji wani iri dukda kuwa halin da take ciki hakanan tsinci kanta da daga idanu tadubeshi,damuwa karara tagani ah furskarshi se kawai ta gyada masa kai kan zatayi abunda yacedin, addu'a yayima Magajiya tareda yimasu Ummi ta'aziya sannan yatashi yafice yakoma gun zaman makokin,haka ranar Sulaiman yatara bayi da dogaraye yana ta aikin nema ma Magajiya yafiya gurun su don gani yakeyi yimata addu'a da nema mata gafara sune kawai gatan dazai iya yimata.........
Asma'u daman takirasu Mubaraq dasu Musa kan suzo su halarci jana'izan dukdama basu iso da wuriba don ah makabarta suka iskesu seda suka dawo sannan sukayi musu ta'aziya tareda fadima Mai Martaba ai Daddy da Aliyu ma baswa gari shiyasa basu zoba sunjima ah gidan don se bayan azahar sannan suka fara haramar tafiya dukdama seda suka shiga sukayima matan ta'aziya........
Dayanma Driver yakawo su Mommy da Ummi gaisuwa suma saikusan maghrib suka koma gida.............
Bangaren Zaliha kuwa gabadaya ganin mutuwar Magajiyan take kamar ah mafarki hakanan kalaman Magajiya na"she should take over",sunata yimata yawo akai gakuma auren da Sulaiman zaisake na matukar damunta she's just trying so hard wurin pretending to be okay with it bayan bahakan bane aranta.........
STORY CONTINUES BELOW

Yau kwana uku da rasuwar Magajiya gabadaya Sulaiman ya rame yakuma koma wani iri hakanan babu inda yake zuwa daga masallaci se gurin zaman makoki wanda ko babu kowa haka zaizauna yayita addu'a wannan dalilin yasa Almustapha ke taredashi akoda yaushe hakanan preparation na biki ya tsaya cak dukdama masu gyaran gine gine sunakan yi sukam basu bariba,Dad yasamu Mai Martaba yayimasa maganar kozasu daga bikin amma yace ina babu fa dagawan daza'ayi bikine za ayishi ranarda akasaka insha Allah wannan dalilin yasa Dad yaja bakinshi yayi shiru haka Abba take yakira Almustapha din yayi masa maganar cigaba da preparation inda yace masa shiya karasa distributing invitation cards din tunda Sulaiman is not himself right now sannan shima daman ayanzu bazai taba sashi yin wani wahalarba,wannan dalilin yasaka Almustapha komawa bakin aiki washegari cikin kwana biyu Sulaiman dinma yajona shi don yalura zama da dorama kai damuwa ba anfanarsa zaiyiba, bakaramin mamaki Almustapha din yayiba hakanan yace masa he don't have to do that yazauna agida he'll handle everything, what if akayi baki masu zuwa ta'aziya fa......
Murmushin karfin hali kawai Sulaiman din yayi tareda cewa"innazauna ina tunanin shizai dawomin da Mama?","she only need our prayers Yaya and inayimata,life goes on now and wanda yatafi ya tafi"........
Murmushi Almustapha yayi don yaji dadin yanda Sulaiman din ke kokarin kwantarda hankalinshi dukda yasan it'll be very difficult for him, bangaren Sumayya ma gabadaya tashiga damuwa because seeing Sulaiman in pain nasata shiga wani damuwane Itama hakanan duk zumudin datakeyi na bikin taji yafita ranta ma bakidaya,kawai sai tadaina participating sesu Afiya daketa haukansu su kadai........
Asma'u ma tunda akayi rasuwar bata samu zama ba hakanan tashiga wasan boye boye da Almustapha din don yanzu kwata kwata ma batason suna haduwa,tarasa decision dukdama takira Asiya kan yaushe zasu zo Zaria inda take cemata ana sauran sati bikin nadin Almustapha din wannan dalilin yasata kin fadamata damuwarta kan zatabari setazo sesuyi maganar shiyasa ma tayi deciding dena kusantar shi harzuwa wannan lokacin tunda shi yariga yazama jarababbe itakuma indai yananiyan tabata bazata taba iya hanashiba sabida tsananin son da takemishi,ita haka take indai tanason mutum she can sacrifice everything koda kuwa hakan na nufin itazata cutune bare Almustapha da inyafara mata wani abunma manta duniyar da takema takey sede takasa yarde ma kanta cewa waishi yana son zama da'ita har abada bayan ba sonta yakeyiba,she really want to hear those three letter words from him,words dinda kowani gender ke muradin partner dinshi yadubeshi yafada mishi lovingly,she might not have deserve him but she deserve to be loved ai,Itama Yar Adam ce hakanan tanada nata burukan rayuwar,tunda su Gimiya Humaira dasauran Ya'yan Magajiya sukazo suka tafi Hamida tafara rashin lafiya  don haryanzu shock din rasuwar mahaifiyar tasu bai bartaba hakanan abunda mazajen yayunta sukayi bataji dadin shiba, ace rasuwar mahaifiyar guda suce kwana uku kawai matansu zasuyi sannan suma sunayin ta'aziya suka juya abunsu, aiko sati swabarsu suyi gashi suntafi sunbarta da kewa abunda yafi bata mata raima shine kaman wanda mazajen nasu suka hada baki........
Zazzabi take sosai kwanan nan din wannan dalilin yasa Asma'un da Zaliha ke tareda ita akoda yaushe dukda Asma'un tafi zama dubada yanda suka shaku da juna ah dan zamansun na kwanaki hakanan kuma Hamidan  bakaramin tausayi take bama Asma'un ba moreover tafi jin maganarta ma na ta sha drugs dadai sauransu haka zatayita lallabata taci abinci dukda bataci din kuma kotacin  ma baiwuce tayi loma uku ko hudu ba shima wataran hararwa takeyi,dukranda Asma'un taga jikin Hamidan yayi tsanani se kawai takwana gurinta .........
Ummi ma ganin Asma'un tadamu da al'amarin Hamidan yasa take tura mai gyaran jikin har bangaren Hamidan tayi mata acan dukdama Asma'un baso takeba amma yata iya?........
****
Sumayya! Sumayya su Afiya keta kwalama Sumayya kira ayayinda suke shiga bangarensu,yatsine fuska tayi ahankali sabida ita gabadaya komaima yafita aranta batamaki ace anfasa duk wani shiri da akeyiba,shigowa sukayi cikin sauri suna....
"munata kiranki baki ansaba"...........
"Inajinku ai kuma nasan zakushigo kusamoni",Sumayyan tabasu ansa zama Afiya tayi tanacewa.....
"Tailor din Abuja yakira wai yasaka kayan mun ah mota probably zuwa azahar kayan zasu iso"......
"Allah yakaimu",shine abunda Sumayyan tace tareda gyara kwanciyarta cikeda damuwa Amira tace"wai Sis meyake damunki ne "......
Sumayya batasan sanda hawaye suka yi slipping ah cheeks dintaba, ahankali tace"nibanason duk wannan shiryen shiryen da kukeyi da za'abi nawama afasa events din kawai".........
Sakan baki sukayi da mamaki suna tambayarta meya faru don daman sunjima da gane tadena zumudin bikin wanda ah tunaninsu sabida rasuwar ne with time she'll overcome it amma kuma sema gashi tana maganar afasa events!....
For what!
Bayan duk uban shirin dasuke tayi,ga kawayen su dasuka rabama anko everyone is just waiting for the day..........
Jin tayi shiru ne yasaka Amira dagota tanakara tambayarta meya faru,cikeda takaici Sumayya tace"ku bakuga halin da Yaya Sulaiman yake bane ba wai,why will I be happy when he's not,miyasa zanyi ta murnar shagalin bikin mu bayan shi yanacikin damuwa,he lost his Mother remember,jinjina kai sukayi don suma sunsan maganarta gaskiya ne don suna ganin yanda Yayan nasu yakoma cikin kwanakin nan ga Hamida ma babu lafiya moreover Asma'u ma is not even interested,jiki ah sanyaye Amiran tace to basai afasa ba kawai......
Da mamaki Afiya ta kalleta, ahankali tace"to yazamuyi Afiya wanda zeyi organising abubuwan ma kilan yamanta mune dai muketa haukanmu daman"........
Sulaiman dake bakin kofa yanajinsu yasaki murmushi tareda cewa"Waye yafada muku na manta?"......
"Bikina da Sumy guda ace na manta da preparations to ashema zan iya manta kaina", yakarashe maganar tareda zama kusa da'ita yana kanne mata Ido daya,itadai sakan baki tayi tana kallonshi da mamaki don rabon da taga fuskarshi with this Charming smile harta manta don tun bayan rasuwar kullum da dare suna tare dashi,haka zatayita lallashin shi tana fadamishi kalamai masu dadi rashin ganin progress daga gareshine ma yasa gabadaya jikinta yayi sanyi dukdama jiya basu haduba wanda hakan ne yakara tada hankalinta ayaudin......
Hura mata iska yayi sakamakon kafeshi da idanun da tayi, dasauri tadawo daga duniyar tunanin data fada,Yar dariya yayi yana"Mobbu honduko Sumyn Sulaiman"(Rufe bakin Sumyn Sulaiman).........
Yanda yayi maganar seda yasakata sakin murmushi batareda ta shirya ba hakanan kuma tarufe bakin nata dake bude tundazu, she's just out of words Afiya ne tace"dagaske Yaya Sulaiman baza afasa event ba?"......
Gyada musu kai yayi sannan yace"friends dinmu nata preparing ai tun tuni daman miyasa za afasa?" .......
Tsalle suka shigayi akan gadon suna ihun murna shidai dariya kawai yakeyimasu yanabinsu da kallo cikeda amusement ahaka harsuka tashi suka fice,dawo da kallonshi kan Sumayya yayi tareda kanne mata Ido daya yana"kallon na menene?",don yalura tundazu se kallonshi take da mamaki.........
Kamo hannunshi tayi cikeda damuwa batareda ta amsa tambayarshi ba tace"Are you okay?"......
Dan jan karan hancinta yayi yana"I'm very okay My Dear"tana kallom idanunshi takuma cewa"really?"....
Gyada matakai yayi yana smilling wanda yayi melting heart dinta lokaci guda because it's really from the bottom of his heart amma se tace"you don't have to pretend to be okay kaji?"....
"Tell me when you're in pain,inkanada damuwa share it with me and I'll always be there".........
Dan matso da fuskarshi yayi kusa da tata ahankali yace"I'm very lucky"........
Turo baki tayi tana shirin turashi ganin closeness dinsu yayi yawa amma seya damke hannunta cikin nashi cikeda zolaya yace"bazaki tambayeni why I'm very lucky ba?"......
Ashagwabe tace ayya am Yaya Sulaiman kada wani yashigo dai...........
Murmushi yasaki tareda sakin hannunta sannan yadaura thumb dinshi kan lips dinta yana dan shafawa wanda hakan kesata jin wani iri,ture hannunshi tayi tana turo baki,yar dariya yayi tareda cewa.....
"believe me Dear I'll not cross my limit now but the moment you become mine Sumayya,I'll make sure i make you believe that I'm the best husband in the whole world".........
Sauke kanta tayi cikeda kunya " Kai Yayana banason maganar nan,katashi kaje nikam bama aiki kakeyi ba?".........
Dariya yayi
"Oh korana ma kikeyi yanzu?",kafin dakyar ya tsagaita dariyan "Yarinya gwandama ki ajiye kunyarnan agefe don nikam cireshi zanyi inma baki dainaba,tukunnan ma fada min inakikeson muje Honeymoon",yayimata tambayar yana kara gyara zamanshi........
Tashi tayi dasauri tayi hanyar kofa tana mai shagwaba tahanyar bubbuga kafarta ah kasa,dariya yakeyi sosae harda dan rike ciki sannan yabita ah bayaa yana"haba Sumyna tsaya ki fadamin mana,ina kikeso muje?"......
Nan yashiga irgo mata da hannunshi dukda kuwa ba kallonshi take ba sema tafiya datacigaba dayi
"Paris?"...
"Satorini?"...
"Bali?"....
"Thailand,Phuket?"
Ko muje "British Virgin island",yayi maganar yana sake kwashewa da dariya don Allah kadai yasan abunda yake kissimawa ranshi ganin tana niyar yin dakin Mom ne yasashi saurin kamota yana"Baki fadamin ba zaki gudu?".......
Mutsu mutsu tafarayi tana"Yaya Sulaiman yaushe ka koma marar kunya newai?".......
Wara idanu yayi mischievously"yanzuke duk zamana dake me kunya kike daukana,to lallai bakisan waye Sulaiman ba Baby"..........
"Tonidai barni intafi inada abunyi"....
Kinsakinta yayi sema sake matseta dayayi ajikinshi yana"ba inda zakije harsai kin fadamin inda zamuje musamo little Sumayya"...........
STORY CONTINUES BELOW

Bugun kirjinshi tayi tana yar dariya cikeda kunya"Kai Yayana"........ kwaikwayon muryarta yayi shima"KaiSumyna"..
Jijjiga kai tayi da mamakinshi, kafin in a whisper yace "ko guraren dana lissafo  basu miki bane ba?".....
Shiru tayi tana kallonshi so lovingly,ganin tayi shirun ne yasashi cewa"then we should make a new suggestions,we can go to Maldives if you want to,yatsina fuska tayi kamar wata karamar yarinyar hakan yasa yayi tunanin ko bai mata bane ba cewa yayi....
"Saint bartherlemy fa?",shima yatsina furkar tayi wara idanunshi yayi yana dariya"ah lallai yarnan kinada buri,shaa I like that what of "Mauritius?"........
Shima yatsina fuska tayi,turo baki yayi tareda yin fuskar tausayi don gabadaya idea ta karemai kaman zaiyi kuka yace"to ke kizaba kawai tunda basu miki ba".......
Dariya tayima expression din fuskarshi tareda barinshi tsaye gun tayi dakin Mom seda ta isa kofar dakin sannan tajuyo tana kallonshi ahankali tace"Let's go to *Fiji resort* Yaya Sulaiman,I really want to go there nan zaka kaini",daganan tayi saurin bude kofar dakin tashige da gudu jijjiga kai yayi yana murmushi aranshi yana"zanyi maganinki ne Yarinya",afili kuma seya furta kalmar "Fiji",hakanan Kuma yana tambayar kanshi "what's so special about that place donshidai baitaba zuwaba yasandai *Fiji* ah under Asia take hakanan baisan abubuwa game da gurin ba,ficewa yayi daga bangaren kaman soko yana ta murmushi tareda niyar inyazauna zaiyi bincike akan gurin data fadadin..............
Tun daga ranar Sumayya tajona su Afiya suka cigaba da shirye shiryen bikin abunsu.......
*****
Angama gyaran masarautar baki dayanta,koina yayi kel kel dashi gwanin ban sha'awa hakanan babu wanda zaizo wucewa koda ta wajen masarautar ne batareda ya yaba kyaun da masarautar ta karayiba,su Sulaiman sungama rabon invitation card biki nata matsowa hakanan baki nata isowa gakuma shirye shirye da aketakan yi babu kama hannun yaro, Almustapha gabadaya ya damu da hide and sick din da Asma'un keyi dashi don ba karamin kewanta yakeyi ba,haka zaigama kwaso gajiyar shi ah waje kullum seyadawo yanemeta ya rasa inyakira layinta kuma akashe,inyaje dakinta ma samu yakeyi batanan kullum haka dakinsu Afiya ma sekawai yafara tunanin ko tareda Ummi suke kwana shiyasa ma ya hakura don Allah yagani bazai iyazuwa dakin Ummi neman matarshi ba duk kuwa irin matsuwar dayayi da ganinta,abinci kuwa bayama sanin waye yake kawomai don sai anfaki idonshi anga yashiga wanka sannan akezuwa ah ajiye,bata taba yarda su kebe su kadai ba sede in Ummi na gurin donko su Afiya batazama gurinsu indai Almustapha nacikin gida bare har yasamu damar ganinta wannan dalilin yasa yagane gudunshi takeyi kiri kiri shikuma yakasa cireta arai,he's badly missing everything about her baccima ah daddafe yakeyinshi wani sa'in har mamakin irin yanda tunaninta kedamunshi yakeyi yi hakanan yarasa wannan din wani irin feelings ne dake neman zautar dashi batareda ya shirya ba.........
Yau sauran kwana goma biki gashi haryanzu jikin Hamida babu wani progress sema abunda yayi gaba don batason cin abinci bare kuma azoga maganar shan magani,abun ya matukar damu Mai Martaba dasu Sulaiman tunda dai gashi likita yanazuwa yadubata kullum hakanan tanashan drugs dinda aka bata abunda basu saniba shine in sun bata maganin basha takeyi ba sema jefarwa da takeyi ah bayan gado,ita gabadaya gani takeyi she's going to be a budden to them daga ita har unborn child dinta tunda mijin ta saki uku yayimata babu halin komawa gakuma tunanin yanda zata fuskanci Abba da maganar ansaketa don duk ah tunaninta Mai Martaban baisaniba bayan kuma already Dad yafada mishi tunbayan rasuwan Magajiya dayaga mijinta ne kadai baizo ta'aziya ba yake tambayar ko lafiya,koda Dad din yafada mishi cewa yayi Allah yasa hakan shiyafi alkhairi dukda kuwa abun yadameshi............
Mai Martaba dayanzu shigowanshi dakin yazauna gefenta tareda taba temperature din jikinta da haryanzu jikin keda dankaren zafi kaman wuta sannan yashiga tambayarta yajiki wanda hakan yariga yazame masa al'ada akullum don tunda tafara rashin lafiyar indai yagama shirinshi da karin kumallo to ita yake fara zuwa yaduba kafin yawuce fada. Murmushi tasaki tareda cewa "Dasauki Abba"......
Cikeda tausayinta yace"kindai fadane kawai Hamida amma ga temperature din jikinki haryanzu da zafi anya bazamuje asibiti ba kuwa tunda abun ya faskara anan", yakarashe maganar tareda maida kallonshi ga Dad dakuma Sulaiman......
Sulaiman ne yace...
"Nima tunanin danayi kenan Abba don likitan yayi iya kokarin dazaiyi amma babu wani progress"............
Jijjiga kai tayi yayinda hawaye kebin gefen fuskarta kafin tace"Allah Abba dasauki"..........
Sa hannu yayi yana goge mata kwallar kafin yace"It's better akaiki candin don zama ah gidan babu anfani tunda likitocin mu nanan sunkasa yin komai besides kina dauke da ciki yakamata ayi examining naki to see if the Baby is fine",yanakai aya yatashi tsaye tareda cema Sulaiman din ashiryata atafi da'ita hospital yanzu.......
To Sulaiman din yace inda Dad da Mai Martaba din sukafice,duban Asma'u yayi sannan yace "ta taimaka mata ta gyara jikinta sesu tafi".........
"To",kawai tace aikuwa
cikin mintuna ashirin harta  shiryata nan suka tafi asibitin dukda seda yabi ta bangaren Zaliha kozata bisu amma secemasa tayi tana da baki,tabe baki kawai yayi batareda yace komai........
Straight wani private hospital dake cikin Zaria sukaje wanda yaji labarin anacewa asibitin nada kyau sosai abunda Sulaiman din besani ba shine asibitin su Na'im ne.......
x

Post a Comment for "GIDAN SARAUTA CHAPTER 12"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...