Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

GAIDAN SARAUTA CHAPTER 10

GAIDAN SARAUTA CHAPTER 10

- - Post a Comment
GIDAN SARAUTA
CHAPTER 10

Haka Asma'u tazuzzuba abincin ah kulolin daya dace kafin tambayar a kakkai daukan na Almustapha tayi don kaimishi dakanta don tanason tanuna mishi yes she wants them to stay happy together like she requested kafin lokacin barinta gidan....
Knocking tayi ah kofar dakin cewa yayi"come in",hakan yasa tatura kofar tareda yin sallama ah sanyaye amsawa yayi azuciyarshi yayinda yake mamakin zuwanta after abunda yafaru jiyan yasani on normal basis inwani abu yafaru takanyi fushi dashi koda na awanni kadan ne takuma sauko dakanta batareda yabata hakuri bama sede yanzu yasha mamaki don she's acting as if nothing has happened......
Ajiye tray din tayi kan stool kafin tace..
"Ina kwana Yaya Imam"......
"Lafiya lau",ya amsa mata ahankali dubanshi tayi fuskarta daukeda murmushi kafin tace...
"kaman ma yanzu ka tashi badai bakayi bacci ba?",takarashe maganar tareda tashi daga tsugunen da take sannan tadawo saman gadon gefenshi tana duba temperature najikinshi cikeda damuwa sede everything is normal ajiyar zuwaciya tayi tareda hamdala ah zuciyarta shikuma kallonta yatsaya yi babu ko kiftawa, ahankali tadaga idanunta tasaka cikin nashi kafin dakyar ta'iya cewa...
"katashi kayi brush kaci abinci, special food ne yau Ummi tayi",takarashe maganar tareda tashi don tafiya cikin sauri ya riko hannunta wanda dukansu seda sukaji wani irin electrification shock kafin yyi magana can kasa kasa kaman meyin rada"meyene abincin?"........
Murmushi tasakar mai dakyar don bakaramin affecting nata muryarshi takeyiba barinma wayanda inyayita ah hankalinnan..
"you'll see for yourself Yaya Imam, it's a surprise from Ummi".....
Sakin hannunta yayi ahankali tatashi tafice yanabinta da kallo hakanan seya kasa bude abincin yawuce bandaki yayi brush yayi wanka yashirya kafin yazauna cin abincin bude cooler din yayi wanda yaji kamshin miyar dabazai taba mantawa ah rayuwarshi ba,miyar Ummi a very special soup dayake ganin babu wanda yakaita iyawa murmushi yasaki tareda zubawa harzai faraci seyatuna da tilon kaninshi Sulaiman daga wayarshi yayi yashiga kiranshi baajima ba kuwa yadauka.........
"Kana Ina ne?",cewar Almustapha din +

Daga daya bangaren Sulaiman yace"Ina bangaren Dad naje mugaisa da Mom ne"....
To kagaidata please inkagama kazo muyi breakfast,dan murmushi Sulaiman yayi kafin yace kaci abincinka nima naci da Mom din katse wayar Almustapha yayi don yasan definately Masan ne yaci tunda daga nan akekaima su Mom dinma abinci fara cinnashi yayi cikeda nutsuwa........
Bangaren Abba kuwa koda akakaimishi nashi abincin yana tareda Hajiya Muniba ne don haka saitace ma bayin suyi tafiyarsu kawai zatayi serving dinsa dakanta.....
Tunda tabude kulolin abincin yakejin wani irin long lost kamshi atattare da abincin besan sanda ya lumshe idanunshi ba aranshi yanason tuna ah ina yasan wannan abincin,ah inane yasan girkin nan amma gabadaya yakasa tunawa dakyar yabude idanunsa yadaura kan masar lokaci guda kuma zuciyarshi tashiga dukan uku uku yayinda wasu flashes ke mai yawo ah idanunsa amma baya ganinsu very clearly dakyar yace...
"I don't eat Masa Muniba",ganin Hajiya Muniba nashirin serving dinshi.........
Cikin sauri ta dago sannan tace"dagaske bakaci?"..
Gyada mata kai yayi ahankali yayinda tace"to miyasa zasu kawo maka bayansunsan bakaci".......
Murmushin karfin hali Mai Martaba yayi don tabbas he's yearning for the Masa in front of him sede bayason yaci yazo abun yadameshi as usual"batasan banaci ba shiyasa tayi inaga",cikeda rashin fahimta Hajiya Muniba tace "waye kuma?".....

Dauke kanshi yayi daga kan plate din kafin yace"Asma'u,itake kawomana abinci ai yanzu"....
Murmushi Hajiya Muniba tayi"Allah sarki yarinyar kirki ba inyi tasting tunda bakaci",tayi maganar tareda daukan daya daga cikin masan ta dangwali miya takai baki seda tacinye daya kafin ta'iya magana"wallahi Mai Martaba kataba Masan nan kaji I promise you won't regret eating it",takarashe maganar tareda daukan wani tanaci tanata santi ganin santin yayi yawane yasashi sa hannu suka shiga ci shidai yasan taste dinma is just so familiar sede yakasa tuna ah ina haka sukacinye Masan tas shida amaryarshi tana"Zanje gurin Daughter takoyamin yanda akeyi aikuwa".........

STORY CONTINUES BELOW


Dariya yayi mata yana"kinma fini santi nalura dole inyima Daughter kyauta".....
Murmushi kawai tayi kafin tasa aka zo akadauki kwanikan tunkan Bayin su fita Mai Martaba yace su ceda Gimbiya Asma'u yana kiranta.....
Cikeda ladabi sukace"To", ba'a jimaba kuwa sega Asma'u tazo fuskarta daukeda annuri tunkan takaraso parlourn Hajiya Muniba tace"Kai Daughter anya nataba cin Masa irin na yau kuwa,it's just the best Masa dana taba ci zo maza kikoyamin yanda akeyi ga Abban Kuma se santi yakeyi", Hajiya Muniba takarashe maganar tareda riko hannun Asma'un tazaunar da'ita gefenta......
Murmushi Asma'u tayi kafin tace "Inakwana Aunty Muniba",dan shafa kanta Hajiya Muniba tayi cikeda kulawa kafin tace "Lafiya Lau Daughter,Yasu Ummi da jiki".....
"Dasauki alhamdulillah"
To Allah yakara sauki cewar Hajiya Muniba din kafin Asma'u tajuya tagaida Mai Martaba ma cikeda ladabi..........
Murmushi yayi bayan ya amsa gaisuwar ta sannan yace...
"abincin ki yayi dadi Daughter muna matukar godiya ga kokarin dakikeyi mana Allah yayima rayuwarki albarka, we're very fortunate to have as our Daughter in-law"....
Sunkuyar dakai tayi cikeda kunya kafin tace"I'm very fortunate to Abba,nagode sosai"......

Murmushi yasakar mata irinna manya sannan yace two months back with you help I realized so many things,I couldn't thank you enough Daughter and today after so many years kindawomin da long lost taste na abincin dana jima banci ba and for that inason kifada min duk abunda kikeso i promise you indai baifi karfina ba I'll do it insha Allah.....

Kan Asma'u nakasa tace"Albarkar ka kawai nike so Abba, you've given me everything",don anata tunanin zama dasu datayi dakuma taimakon datayi ma Al umma da dama ma is indeed a great treasure mekuma zata sake nema gurin Abba dukda taso ace after eating this Masa yatuna da masoyiyarsa sede hakan beyiba.......
Abba ne yace"albarka Kam kullum cikin samuku mukeyi amatsayinku na ya'yan mu wannan Kuma alkawari ne nayi maki so kizabi duk abunda kikeso kinji,just feel free yayi maganar don bata kwarin gwiwa",amma ita tarasa abun cewa sekawai tace Masa"to shikenan Abba yanzu banida abunda nakeso amma duksanda nakeda bukata zanzo infada maka"....
"To shikenan Daughter nikuma namiki alkawarin yimiki invaifi karfina ba"
Haka tayi masu sallama tareda yin godiya takoma bangaren su tana sake sake wani alfarma zata nema gurin Abba yanzu bayan takusa barin gidan ma sede koma miyene before she.leaves she'll make sure that Abba and Ummi sunyi reuniting.......

Tundaga bakin kofa takejin surutun su Amira ah parlourn da alama kuma murna sukeyi karasawa tayi cikin parlourn tana"murnar me akeyi bana nan?"....
Aeda gudu Afiya da Amira sukazo suka rungumeta wanda harhakan yasa tayi kusan losing balance dinta tana"nashigesu zaku karyani ai"....

Dariya Amira tayi tana"Bazamu karyakiba Sister Inlaw,we want to show you our appreciation shiyasa"......
Da mamaki ta kallesu"appreciationkuma,na menene?"....

Dukansu nunamata direction din laptops dinsu sukayi dakuma phones dinsu dake kan daya daga cikin royal chairs dake parlourn,sakan Baki tayi cikeda mamaki"yabaku?"....

Gyada mata Kai sukayi suna murna yayinda Afiya tasake rungume ta tana...
"thank you,thank you, thank you,mungode sosai Sis,nidaman nasan dakinyi mishi magana zaibaki"...

Itadai murmushi kawai tayi cikeda confusion don koda wasa tasan bata dalilinta baneba yabayar din bayan ga maganganun daya fada mata jiya da daddare aranta tana kilan ma Ummi ne tasa yabasu badai itabakam seda ta tayasu murna sannan tace"Ina Yaya Imam din?"....
Amira da Afiya atare sukace yana bamu yafice zuwa bangarensu Dad daganan zeje fada nasani.......
Gyada musu kai kawai tayi kafin tawuce dakinta don Kiran Aisha tunda tace mata yau zatazo tafasa bari se Friday din kuma.....
Aikuwa har three missed calls tagani from her kiranta tayi immediately tana dagawa taji Aisha na"Ina kika ajiye wayarki inata kira bakya dauka".......
Cewa tayi
"Naje gun Abba ne kekam namanta wayar ah daki, kinfito daga gidan Aunty Suwaiban ne?"....
Aisha tace"inama layin gidanki yanzu zam sauka ah napep",cikeda Jin dadi Asma'u tace sekin shigo kafin takatse wayar tana mita kuma"wai kina ma layin gidan amma kike neman karar min da Kati"....

STORY CONTINUES BELOW


Dariya kawai Aisha tayi takatse wayar aikuwa ba afi minti ishirin ba segata ah bangaren su Asma'u din ba Asma'u kadai ba harda su Afiya suka taro Aishan cikeda jin dadi suka baje ah parlour.......
Ummi dake dakine taji hayaniya yayi yawa tafito tana....
"wannan hayaniyar na miyene Habibties?"......

Murmushi Aisha tayi tareda tasowa tazo zata tsuguna tagaida Ummin cikin sauri Ummi tarikota tareda rungume ta tana"Aisha ce ko?".....
Cikeda kunya Aisha tace"Ina kwana Ummi".....
Lafiya lau Dear, Allah dai yayi yau kinzo da gobe sede kiganmu Daughter tun shekaranjiya taketa" Aisha zatazo Aisha zatazo"....
"Gashi nazo ae Ummi",Aisha tayi maganar cikeda kunyar Ummin gawani kyau da matar tayi mata lokaci guda.....

Murmushi Ummi tayi sannan tasaki Aishan tana"kin kyauta Kam, Allah yabada ladan zumunci enjoy yourself kinji?"...
Gyada kai Aisha tayi yayinda Ummi tayi komawarta daki haka sukayita hira ah parlour abunsu har aka kira azahar daganan Aisha da Asma'u sukayi dakinta don yin sallah su Amira kuwa sukayi nasu dakin don yin sallah su shirya sunada lesson dayanma tunda yau babu islamiya makarantar ma anbada midterm break.........

Seda sukayi sallah sannan Aisha tace"ammadai Matarnan itace mahaifiyar su Amira ko?.....
Murmushi Asma'u tayi kafin tace"eh itace",wallahi kinyi dacen suruka Asma'u, she's so nice and kind-hearted kiga nidama batasanni ba irin tarbar datayi mani bare ke dakike surukarta I'm very happy for you sede kaman da batada lafiya ai ah iya sanina don har kwana nayi ah gidansu.......
"She's okay now Aisha,tasamu sauki sosai wanda hakan kuma ikone na ubangiji"......
Masha Allah, Allah yakara mata lafiya cewar Aishan kafin tasake duban Asma'u din"Ina Yaya Almustapha,hope everything is fine between you two now don bazan tambayeki batun al umma ba tunda nagani da idanuna wannan Kam"......
Murmushin dayafi kuka ciwo Asma'u tayi kafin tace"to alhamdulillahi za ace"....
Ganin yanda tayin yasa Aisha cewa"kifada min meyake faruwa please?".....
"Are you two having some problems,ko haryanzu bayasonki me?", Aisha tayi maganar cikeda damuwa Asma'u dago idanunta dasuka canza lokaci guda tayi kafin tace"to nimadai bansani ba Aisha,bansan inda relationship dinmu ke tafiyaba to tell you the truth besides there no need to talk about it tunda ma komai yakusa zuwa karshe"......
Aisha datadamu taji asalin zancen tace"stop beating around the bush, kimin bayani yanda Zan gane"....
Asma'u tayarda da Aisha dari bisa dari don haka tashiga bata labarin komai harzuwa karshe wani harara Asma'u tayi mata kafin tace"kinason kicemin you're given up on him?"......
Asma'u dayanzu hawayenta nazuba tace"to yazanyi Aisha,kinsan dai bazaka taba forcing mutum yasoka bako,Yaya Almustapha basona yakeyiba kome nayi masa he never seems to appreciate it infact ninakasa gane kansa ma wallahi,yana behaving so strange danikaina bansan tayaya zan fassafara mikiba,he always turn me down akullum Kuma seya sosa min rai dukda wani sa'in inyayi wani abun se inga kaman yadamu dani but believe me he never cares haka 99%na zuciyata ke raya mini So, it's better I just let him go.......

Dora hannu Aisha tayi abakin Asma'u sannan tace"you shouldn't do that,so kike kizama bazawara at your tender age koso kike Hajja tasake samun bakin magana gurin bakantawa Ummi mumabar wannan zancen mutuncin ki shine zaman ki gidan Almustapha, he's the best guy for you and believe me ko Almustapha baifara son ki yanzu ba he'll surely fall in love with you in the future,shi ai ba zuciyar dutsi gareshi ba hakanan zuciya nason mai kyautata mata muddin kika cigaba da kyautata masa he'll never let you go bare namiji da bakomai bane indai yashigo hannun mace kecedai baki san yanda zaki tarairayeshiba cire kunya zakiyi ki tashi tsaye please, don't give up Asma'u mutuncinki shine zaman ki ah gidan aurenki barema keda kikayi sa'an surukanai haka Almustapha ma mutum ne mai sanyin hali kekanki kifini sanin hakan bugu da kari wasu matan baswa gabanshi kwata kwata, he's just a simple person and he's a better husband for you.......

Asma'u da kallon Aisha takeyi babu ko kiftawa tace ...
"naji dadin kalaman ki sede da if you're in my shoes I know you'll do thesame thing, Asma'u da idanunta kedauke da hawaye tanuna kanta tana"....
Shidakanshifa Aisha,shidakanshi yacemin dakomai yazama normal zai rabu dani, he'll let me go not once but twice yafada aidai duk zaman mu yakamata yasan halaccin danayi mishi hakanan duk zaman mu yakamata yasan how much I love him kuma bekamata yamanta cewa akwai abunda inya fada zai taba min zuciyata, I'm so fragile you know that, I'm so weak da innafara son mutum bazan iya dainawa ba hakanan in inason mutum no matter what bazan iya fushi da wannan mutumin ba barin ma Almustapha danakeyimasa son da nikaina bansan irinsa konayi fushi dashi banasanin sanda nike saukowa,sonshi ah jinina yake Aisha inna cigaba da zama dashi I'll always show him care bazan taba kyaleshi yagane importance dina ba it's better I let him go and please karki hana ni don komai zakice nariga nagama magana dashi and no one can change my mind...........
Aisha cikeda tausayin kawartata tarungume ta tana rarrashinta tasan Asma'u nada hakuri hakanan kamar yanda tafada ita mutumce datake son nuna damuwarta akan wanda takeso tun suna secondary school tasan da haka sede koma miyene she'll never let Asma'u be hurt again insha Allah she'll try her possible best gurin ganin ta mayar dakomai normal inzata iya dakyar ta lallashi Asma'un kafin suka dawo normal suka cigaba da hiransu se bayan la'asar sannan tatashi tafiya Sulaiman ne yace zai maidashi dakansa dukda Aisha tace yabari amma yaki haka Ummi tacikata da turarraruka ah leda tatafi dasu...........

STORY CONTINUES BELOW


Harkofan gidansu Sulaiman yakaita zata sauka ah motar yace....
"I heard everything"....
Cikeda mamaki tajuyo tace"mekaji Yaya Sulaiman"...
Murmushi yayi sannan yace...
"the conversation between you and Sister Inlaw"....
Maido da kafarta daya data fidda wajen motan tayi ciki sannan takalleshi gyada mata kai yayi ahankali sannan yace"Sumayya tayita Kiran wayan Asma'u bayashiga shine tace inkai mata wayar su gaisa sun kwana biyu basuyi magana ba I was trying to knock on the door tafito senaji maganarku, I'm reallly natsaya jin abunda ba'akani aciki ba sede inason kisani ni Sulaiman bazan taba bari Yayana Almustapha ya rasa mata irin Asma'u ba,I promise you I'll make everything right karki damu please and don't tell anyone about it......

Cikeda Jin dadi Aisha tace...
"nagode sosai Yaya Sulaiman,wallahi har inatunanin wani mataki zan dauka donni kaina banason abunda zai raba Asma'u da gidan aurenta ah yanzu".....
Murmushi yayi mata sannan yace"it's my fault namanta who my Brother is, bantaba tunanin duba ya zaman su yake tafiya ba but now that I know everything I'll handle it".....
Aisha godiya tayi tayima Sulaiman din kafin sukayi sallama yakama hanyar gida already har ana kiran sallar maghrib shiyasama dayasamu masallaci nearby yatsaya yayi sallarshi sannan yakoma gida.....

*Around 10:30pm*....
Tun bayan Isha suke zaune ah inda Sulaiman yasaba zama when he's lonely hira sukeyi duk akan batun masu gidan talabijin dasuka zo dazun kan sunason hira da Almustapha din shikuma harga Allah bayaso sede su Abba sunnuna sunason hakan shiyasa ma baiyi korafiba seyanzu yaketayima Sulaiman din don haka Sulaiman daya gaji yace...
"Waini Kam daka fadama su Abban ai bakaso, I'm sure bazasu takuraka ba",don harga Allah ayanzu he's against abun indai hakan zaikawo rabuwan Asma'u da Almustapha he wants everything to be alright between them kafin hakan tafaru.......
Almustapha duban Sulaiman yayi sannan yace..
"banason hira da mutanen nan amma tunda Abba da Dad sun nuna sunaso bazan taba iya juya musu bayaba and besides someone wants it to happen for some genuine reason and if that will make all the three of them Happy I'll surely do it shiyasa kaga bangi going against it ba".....
Gyara zama Sulaiman yayi sannan yace...
"who's that third party?'.......
Murmushi kawai Almustapha yayi sannan yaja hancin Sulaiman din"Ina ruwanka".....
Dariya Sulaiman yayi sannan yace"Nasan Sis Asma'u ce ba wataba,apart from us waye yakeson farin cikin ka inba itaba?".....

Dan shiru Almustapha yayi yana wasa da fingers dinsa kamar bazaiyi magana ba cankuma yace"ya akayi kasan itace?".....
Yar dariya Sulaiman yakumayi tareda dan dafa Almustapha din"Yaya as i said earlier bayan mu babu maison farin cikin ka sai ita sannan nasan da ba ita bace you'll mention the name",dan furzar da iska yayi sannan yace"kayi dacen Mata Yaya,aduniyar nan ba kasafai akesamun irin Asma'u ba she's just so simple and unique,mutumce da abun duniya baidameta ba hakanan mutumce da bata biye maganar mutane she always do what she thinks is right kowa agidan nan yabonta yakeyi sabida haleyenta nagari akullum Abba da Dad in aka Kai musu abincin da ta girka sesun sanya mata albarka tareda yi mata fatan alkhairi bazan mantaba sau biyu inaji da kunne na Dad nacewa...
"Almustapha yayi dacen Mata,yayi dacen uwa tagari ma yayansa hakanan yayi dacen Mata wanda zata rinka taimaka mishi akullum gurin farantawa subjects dinsa she's indeed a blessing to the family and our nation as well"........
Kallon Almustapha Sulaiman yayi sannan yace...
"Dad yayi gaskiya,never let her go Yaya no matter the situation please!"....
Almustapha dakanshi yadaure lokaci guda yace"what if ita tabukaci hakan?".......
Kallonsa Sulaiman yayi sannan yace"ita tace mahaka?"......
Hararansa Almustapha yayi sannan yace"natambayeka kana Kuma tambayata bayan bakabani ansana".......
Murmushi Sulaiman yakumayi"to ai Yaya inbaka bani ansa ba tayaya zansan ansar dazan baka",cikeda rarrashi Sulaiman din yace"kunyi magana mekamar hakane da'ita?"........

Cikin sanyi Almustapha ya gyada masa kai, Sulaiman na kallonsa yace waye yafara?....
"I was the one Almustapha yabashi amsa atakaice but yesterday she requested it also and I think it's d best aurenmu was base on compromise may be ma tanada wanda takeso kaga inna barta she'll be reunited with her love",yanda yayi maganar zaka gane bawai yanason hakan baneba ......

Cikeda damuwa Sulaiman yace"kotana son wani she's your wife now so it's left for you to decide if you want her to go or not".......
"You can make her stay if you want to,donnidai in nine bazan taba barinta tatafi barema yanzu danasan how much important she'd to your life as a wife, bazaka taba samun kamanta ba Yaya sabida ita tazauna dakai ah talaucin ka ma hakanan bata taba kyaman halayen ka ba", Sulaiman nagama fadin haka yatashi yana"sanyi nikeji nikam seda safe Yaya Musty".........

Almustapha daya fada duniyan tunani ko kallon Sulaiman din baiyiba hakanan ya jingina da kujerar tareda lumshe idanunshi lokaci guda farkon haduwarsu da'ita yadinga dawo mishi ah idanunshi sabo fil,how she stand for him acikin dubbannin mutane without any fear,dayanda tadinga shishige mishi each and every time dasuka hadu dukda yana mata hali hakan baitaba sawa tayi fushi dashiba the way she always cares harzuwa yanzu bayan aurensu dede da rana daya baitaba ganin bad side dinta ba,she's always good to him and from all indication she's madly in love with him infact she said it once dawannan tunanin ne wani bangare na zuciyarshi tacemasa....
"Anya kayima yarinyarnan adalci inka rabu da'ita,anya kayima family members dinka da nata adalci inka rabuda ita dubada yanda suka shaku da juna don ayanzu Sulaiman wani irin zumunci suke da yayunta shima sukan gaisa da Mubaraq sosai hakanan insukaje gidan nan nan akeyi dasu kamar mi".......

inya sakar musu 'Ya dawani idanun zai kallesu bayan halaccin dasukayi ma Dad nadaukar yarsu dasukayi suka bashi don yanada tabbacin bawai don Dad bayason Asma'u baneba a'a harda karin yana ganin mutuncin Dad ne wanda shima wannan albarkacin yaci,to yau inyasaki Asma'u dawani idani Dad zai dubi Alhaji Muhammad wayannan tunane tunanen ne suka dinga yimasa yawo ah kwanyarsa yanata sakawa yana warwarewa shi kadai daga kashe yatashi ahankali yakoma cikin gida wutan koina ah kashe which tells him that kowa yayi bacci kunna Torchlight din wayarsa yayi ahankali kafin yafara taka lallausar kafet din dake parlourn hangowa yayi kaman mutum kwance kan three seater haskawa yayi sosai Asma'u ce kwance tana baccinta peacefully hannunta rikeda wayarta da alama baccin yadauketa ne batareda tasani ba ......
Yafi 30seconds tsaye kanta kafin yadan tsuguna ahankali yakarbi wayar ah hannunta dannawa yayi tuni takawo haske and babu password awayar wanda hakan yabashi daman ganin abunda takeyi inbox ne tana rubuta massage wanda batakai ga turawa ba karantawa yayi ahankali....
"Yaya Imam inakaje ne tundazu,i've been waiting for you zamuyi magana and it's so late in the night come back s"......bata karasa rubutaa soon dinba ma bare tatura mai daga idanunshi yayi yaga sunan datayi mashi saving ah contact dinsa...
"Mr Taciturn",besan sanda yasaki murmushi ba don bai manta randa tafara kiranshi da wannan sunan ba,that day he was very angry amma bainuna mataba ko alokacin donshi mutim ne meyawa boye fushinsa..... yayinda yafita ah massage din yashiga calls dinta ashe tayita kiranshi ma sede shibai gani ba probably tayi tryin betafi bane shiyasa ta so turamai text din......
Sa dayan wayar yayi ah aljihu sannan yadan Kira sunanta ahankali amma bata ansa ba don haka kawai se zuciyar shi tabashi yadauketa yakaita dakinta tunda she's deeply sleeping.......
Dagata yayi kamar Baby yayi dakinta da'ita akan royal bed dinta ya kwantar da'ita sannan ya kunna wutan dakin dawowa yayi ya ware katon blanket din ya lulluba mata zuwa kirjinta harya juya seyaga hijab ne akanta don haka yadawo yazauna tareda taimakawa yacire mata hijab din ahankali yana mamakin ya akayi yau baccinta yayi nauyi har haka,kallon lallausan gashinta yayi dayasha kitson dayaki nuna mata yayi kyau ajiyan sannan yadan tabasu ahankali besan ya akayi ba kawai samun kanshi yayi yana kissing forehead dinta very softly which is the first time dayayima wani hakan arayuwanshi shikanshi he was very stunned and surprised gyara mata lullubin yayi sannan yakunna AC yakashe wutan kafin yafice ah dakin abunshi cikeda tunani kala kala..........Wuraren karfe hudun asuba tafarka sede bakaramin mamaki tayi ba ganinta datayi kan gado don bata manta ba ah parlour bacci yadauke ta tana jiran Almustapha yadawo tamishi godiyar bamasu Amira laptop dayayi dukdama tasan ba albarkacin ta sukaci ba"to ya akai taganta adaki harma da lulluba mata bargo,waye da danyen aikin nan dondai tasan ba'ita bace ba",ganin batada ansane yasata tashi donyin ibada inyaso dasafe tatambayi su Amira dukdai tasan su ba iya daukarta zasuyi ba to kode ah gigin bacci tazo daki batareda tasani ba ita kadai dai tanata tunane tunane hartasamu tayo alawala tazo tatada sallah..........
Seda gari ya waye sannan taje kitchen suka yi girki seda aka gama sannan tafito dakinsu Afiya tawuce suntashi dukansu don yau zasu shiga school yin jamb registration sunata shiri...
"gaisawa sukayi kafin tace nikam kuka tasheni ah parlour jiya?"......
Amira ne tace...
"aa wallahi aimunrigaki yin bacci ma kokin manta ne,munbarki ah parlour ae"......

Cikeda mamakin abun tace"nashigesu toko aljanune suka dagani suka kaini daki",dariya Afiya da Asma'u sukayi suna "habadai aljanu Sis"......

Cikeda Jin haushin dariyar dasuke mata tace"I'm serious fa kawai yau natashi naganni ah daki harda lulluba min bargo akayi aka kunna min Ac kuma,wallahi nikam tsoro nafajima",tayi maganar sincerely dariya Afiya takumayi Amira na...
"so Yaya Almustapha can be so romantic like this?".......
Zare idanu tayi tana kallon Amiran tareda hararanta don ita seyanzu ma yafado mata arai to amma koda wasa bazata taba yarda Almustapha ne yayi mata wannan abunba ganin sunmaida abun tsokana yasata tashi tanata kumbure kumbure tayi dakinshi yaukam ko sallama babu tashiga.......
Bema tashi daga bacci ba harlokacin karasawa tayi bakin gadon tareda bubbuga shi tana"Yaya Imam katashi".......
Bude idanunsa yayi ahankali sannan yadubeta sewani turo baki takeyi ganin yabude idanun ne yasata cewa"kaga su Amira ko sunata neman tsokana na"......
Yanda tayi maganar besan sanda ya wartsake idanunshi ba yana"me suka miki?"....
"Wai cewa sukayi kai kakaini daki nikuma tsoro nikeji kar aljanu ne"....
Yar dariya yayi...
"Let them be they're just trying to tease you",yakarashe maganar tareda tashi yazauna ah tsakiyar gadon yana yaye bargon dake jikinshi.......
Kamar wata munafuka Kuma tace...
"to kaine ka daukoni daga parlour?".....

Batareda ya ansa tambayar taba yace"miyasa kika tsaya jirana har wannan lokacin sekace wanda guduwa zanyi Asma'u?".....
Ah shagwabe tace"it's because I wanted to thank you".....
Cikeda mamaki yace"for what?".....

Turo baki tayi"for returning their laptops and phones dukdama nasan badan ni kayi ba",kallon dan karamin bakinta yayi yana mamakin miyasa intana mishi magana takeyi kamar wata yar karamar yarinya dakaman bazaiyi magana ba sekuma yace"wayace miki badan ke nayi ba?"......
Ware manyan idanunta tayi tana"what?"..
Irin yasake maimaitawan nan amma seya wayance dacewa"Ummi tace zataje gida ziyara gurin su Ummi inkina da sako seki bata".......
Aecin sauri tatashi daga zaunen da take gabanshi tana......
"nibazan jeni ba kenan?".....
Daga wayarshi yayi yana duba time sannan yace...
"mezakijeyi?"....
Atake idanunta suka ciko da kwalla tana"tunda nazo gidannan bantaba zuwa bafa",yanda tayi maganar seda takusan sashi yin dariya amma seya rike dariyartashi haryana ma shirin sauka daga kan bed din kumacewa tayi"don Allah kabarni injeni nayi kewansu Ummi",wannan karan sega hawayen sunfara shatata ah idanunta cikin sauri yace"Don Allah maida kukan wallahi wasa nike miki dake zaa j",yakarashe maganar wannan karan yatashi tsaye cikeda murna tace dagaske kakeyi?....
Gyada mata kai yayi ahankali tareda sa hannu yana goge mata kwallar cikin sauri tarungume shi cikeda murna wanda hakan yasasu feeling wani shock lokaci guda tafi mintu biyu ajikinshi kafin cikin sauri taja daga jikinshi tana mishi kallon tuhuma.....
Daga mata gira yayi alamar miye,kyabe fuska tayi ahankali kafin tace"why are you being nice to me all of a sudden, it's unlike you gaskiya",ganin yayi shiru bece mata komai ba Yana kallonta yasata daga hannunta tana using fingers dinta tana counting"You take me to my room yesterday night, you're being nice to me this morning on top of that harkukana bakaso it's just so weird you know!"....
Sa hannu yayi ah both cheeks dinta yadan ja ahankali wanda hakan yasata dan sakin kara sannan yace"waye yace i should be nice to him kafin murabu".......
Nuna kanta tayi"ni"....
Dan ware hannunshi yayi sannan yace...
"to, I'm just trying to fulfill your wish".....

STORY CONTINUES BELOW


Lokaci daya setaji jikinta yayi sanyi murmushi yasakar mata sannan yajuya yashige bathroom Itama jiki ah sanyaye tashiga gyaramai dakin nashi hartagama baifito ba don hakan tadauko abincinshi takawo mai daki donta lura Sulaiman baicika shigowa cin abinci yanzunva kullum ba may be he's very busy ne shiyasa .......
Dayanma Asma'u da Ummi suka shirya Sulaiman yakaisu gidansu Asma'u din donkuwa Almustapha is very busy.tundaga bakin kofar parlour Asma'u tafara gudu ganin Ummi datayi ah tsakiyar parlournsu shigewa jikinta tayi seta fashe da kuka kuma"Ummi ne tace a'a kuka zakimin daga zuwa Kuma?".....
Cikin kuka Asma'u tace"nayi kewarki Ummi", murmushi kawai Ummi tayi kafin ahankali tace....
"kidaina gudu haka kokin manta kin girma ne?",kafin Ummin tajanyeta daga jikinta sakamakon hango wata Mata datayi daga bakin kofa fuskarta daukeda murmushi"Daman da bakuwa kukazo?",Ummi takaima Asma'u tambaya .......
Karasowa cikin parlourn Ummi tayi kafin tace"Kinga dayar Ummin ki harkin manta dani ko Habibty?"......
Yar murmushi Asma'u tayi cikeda kunya tana wani sunne kai"Ummi ban manta dakeba".......
Ummyn Asma'u ne tasaki murmushi tareda cewa"Bismillah kikaraso mana".......
Karasowa ciki Ummi tayi tazauna kan daya daga cikin kujerun sannan suka gaisa da Ummin Asma'un kafin Ummi tace"Daughter se rowarki takemin nace inason kulla kawance da Ummi amma tadinga min kwana kwana seyau akayi niyar kawoni gurin sabon kawalliyata dabata sanni bama", Ummi tayi maganar cikeda zolaya,dariya Ummin Asma'u tayi sannan tace"ba'in kawo miki ruwa"......
Asma'u dake gefe tace"Ummi zankawo".....
Gyada mata Kai kawai tayi kafin tawuce cikin gida don kawo ruwan tabarsu zaune suna yar hira dukdama Ummi ne kecema Ummin Asma'un itace mahaifiyar Almustapha.......
Mamaki sosai Ummi tayi ganin yanda matar take so friendly and nice kankace mai sun barke da hira don dukyanda Ummin Asma'u takai ga yin sukurtaka da'ita ajjyewa gefe tayi don Ummin daukanta tayi matsayin kawa ma baki daya Asma'u kam tunda takawo musu ruwa tawuce bangaren Mommy don su Munira baswanan kilan sunacan aikuwa acan din tasamo su sunata wasansu bakaramin mamakin ganinta sukayiba kan kacemai harsu Aliyu sun shigo se nan nan ake da'ita harda hawayenta tsabar farin ciki tana musu korafin babu wanda yataba zuwa mata Aliyu, Sadiq da Musa ne sukayi mata alkawarin zuwa kwana kusa yayinda Yaya Mubaraq yace"shi ai Yaya babba ne shima fushi yakeyi bataje taga gidansa ba'...
Cikeda kunya tace"zantambayi Yaya Almustapha insha Allah zanzoni"......
Murmushi yayi tareda shafa kanta yana"ikon Allah waini ne yau Ma'u na kejin kunyata dole insamu Yarima innasamu time zanmishi korafin yakwace min kanwa".....
Dariya tayi tana"Kai Yaya Mubaraq bahaka bane bafa?".....
Shima yana yar dariya yace...
"to menene Ma'u?"....
Cewa tayi
"Kawaidai kawaidai",lol kede kawai kice bakyason Inga laifin mijinki to nadaina ganin laifinsa amma fa saikin tashi kin min wannan dahuwar indomien naki I missed it so much.....

Mommy dake shigowa parlourn yanzu dukdama sun gaisa da Asma'un tace"aa aaa nifa baza a takurama Daughter na ba kuma daga zuwanta zakasakata aiki inama laifin gauraye suyi magana amma hardakai Mubaraq godai godai dakai?",tayi maganar tana hararan Aliyu.......

Mubaraq nashirin magana Aliyu yace"yishiru Yaya Mommy sotake mu gauraye muce munason cin indomie lil Sis bakaiba",sannan yayi kasa da murya cikeda zolaya yace"mutumiyas indomie nikeson ci don Allah ayimin",yanda yayi maganar seda tayi dariya..........
Wutsiya Mommy tayimai"wallahi babu abunda zata dafa maku inmutum yaji haushi yafidda Mata"......
Dariya sukayi duka Musa na"kaji zancen yafito nima Mommy namatsu yafidda matar nan kona samu asamin ido atakurani infidda donni inada ita already".....
Asma'u daketa dariya tace"Bari indafa muku"......
Koma kizauna Daughter babu abunda zakidafa meson ci yaje gidanki kiyi mishi amma ba ananba......
Hakuri suka shiga bama Mommy amma tahana sam can sega Ummi da Ummi sunzo da fara'a mommy ta tarbesu yayinda su Aliyu suka fice bayan sungaida Ummi acan bangaren Ummi ta koma tadafa musu indomie din kafin takai musu side dinsu se santi sukeyi murmushi tayi tana kallon yanda sukeci lovingly"she really missed those moments".....

Seda takoma bangaren Ummi take tambayar Munira ina Hajja tabe baki Munira tayi"tana Kaduna gidan Yaya Asiya kinsan tanada ciki kuma wai yazo da laulayi shine takoma gurinta"......

STORY CONTINUES BELOW


Cikeda Jin dadi Asma'u tace dagaske ciki gareta, I'm so very happy nakusa zama Aunty....
Dariya Munira tayi tana kai Yaya Asmy wannan farin ciki haka?.....
Murmushi Asma'u tayi tana"you don't know how much I love kids, they're so innocent and amaizing", ahankali Munira tace"Allah yabaki naki kema".......
Take se jikin Asma'u yayi sanyi murmushi kawai tayi sega Umminta tashigo tana kishirya yanzu zaku wuce magariba yakusa jiki ah sanyaye ta gyadama Ummi kai........
Shafa fuskar ta Ummi tayi cikeda son yartata kafin tace"hope everything is alright over there?".....
Gyadama Ummin Kai tayi ahankali yayinda Ummi tace Mother In-law dinki is very nice,cikeda son Ummin Asma'u tace"she's very very nice ma Ummi"......
Rungumeta Ummi tayi cikeda kaunar yarta because yanzu hankalinta yakara kwanciya atleast from all indication komai yana tafiya lafiya ah rayuwar yartata....

Shawarwari tadinga bata kan zaman takewar aure dakuma hakuri kan rayuwar duniyarma baki dayanta kafin suka fito don tafiya because already Sulaiman yadawo daukarsu Asma'u harda hawaye...
"Umminta ne tace indai zakina kukane karkusake zuwa da'ita"...
Cikin sauri tashiga goge kwallarta tana Allah nadaina Ummina,Ummin musty ne tajanyota jikinta tana "karki damu you can come home duksanda kikeso kinji karki biye maganar Ummin ki".......
Gyadakai tayi kafin suka shige motar suka tafi cikeda kewan juna...........

Washegari Sunday dayanma Asma'u na lambu tana ciran fruits dakanta tanasha wanda hakan yanzu yariga yazame mata jiki dagudu daya daga cikin bayin masarautar tazo tana haki"Gimbiya Asma'u,Gimbiya Zaliha nata dukan Rukayya dasu Safara'u........

Cikeda damuwa tace"laifi sukayi Ina?"......
Cikin sauri yarinyar tace wallahi babu laifin Rukayyan ki aciki shaida tabayar shine Itama akasakata cikin abun bakiga yanda take dukansu baneba shiyasa.......
Asma'u da hankalinta yatashi lokaci guda tace muje mu,haka yarinyar tayi gaba yayinda Asma'u tabi bayanta har bangaren bayin yayinda duk sunyi cirko cirko....

Suna kallon irin dukan da Zaliha keyima Rukayya da Halima kaman wanda zata hallaka su cikin sauri Asma'u takarasa gurin tana....
"Zaliha kibar dukansu hakanan I know you must be angry amma kada kiyi abunda zakiyi nadama daga baya"...........
Ko kallonta Zaliha batayiba sema dukan Rukayya da Halima da takeyi kafin ta dubi Safara'u datayi wiki wiki da'ido tace..
"Don ubanki kema zandawo kanki bawai kinga na kyaleki ba"..........
Ganin abun yayi yawa yasa Asma'u karasawa tajanye Zaliha gefe tana...
"wai bazaki bari bane kosai kinyi kisan kai tukunnan hankalinki zai kwanta?".......
Zaliha data kusa faduwa dakyar tayi holding kanta tadago cikeda mamaki ta wanke Asma'u dawani irin wawan mari tana"Baki da hankali ne koni sa'arkine dazaki shiga hurumin daba naki ba".....
Asma'u bakaramin zafin marin tajiba she's so speechless and out of words hannunta na dafe kan kuncinta tana kallon Zalihan cikeda mamaki nunatada yatsa Zaliha tayi tana....
"bawai kinaganin kinyi succeeding ah abubuwan dakikayiba abaya I promise you'll never get away with it"kafin takarada kifita harkana, nafada miki kifita harkana inbahaka ba zanyi miki abunda yafi marima tunda ke bakida kunya matsiyaciya kawai wanda batasan ciwon kanta ba bare mutuncin kanta.......

Sosai maganar ta sosa ran Asma'u don haka ta daga hannu zatakai ma Zaliha mari Itama amma setayi saurin capke hannunta tana"karya kikeyi yarinya,bakikai wannan matsayin ba bari infada miki".....
Kokarin kwace hannunta takeyi amma takasa Magajiya ce takaraso gurin tanayima Asma'un wani irin kallo kafin kace mai duk bayin dake zagaye agurin suna kallo suka watse se wayanda aka tara sunyi laifin ne ke tsugune suma duk sunyi kasa dakansu........

Duban Sarkin gidan yari Magajiya tayi kafin tace...
"kamaida su Cell din tunda uwar kinibibi tajamusu wani horon".......
Jiki na bari yasa akayi gaba dasu yayinda Magajiya tashiga karema Asma'u kallo wanda ita kokarin kwace hannunta daga na Zaliha takeyi amma takasa kafin tace"saki hannunta Daughter"........
Cikeda ladabi Zaliha tasaki hannun murmushin mugunta Magajiya tayi sannan tace"ke yar gidan matsiyata,yar gidan mayu meye damuwanki da aikin da bai shafe kiba?"........
Cikeda zafin rai Asma'u tace"Mama babu ruwanki awannan maganar I do respect you as my elder so don't interfare wannan tsakanina ne da Zaliha", Asma'u takarashe maganar tana hucin iska.....

Wani irin dariya Magajiya ta sheke dashi kafin tawaiga takarema gurin kallo ganin babu kowa don daman bangaren bayine bakasafai ake shigowa ba dakyar ta'iya tsaida dariyartata kafin tadubi Zaliha tace"alot has changed gaskiya Zaliha,alot has changed",takara mai maitawa tareda sake kwashewa da dariya dakyar ta'iya rike dariya kafin takalli Asma'u"amasarautar nan babu wanda yataba dubana yafada min magana kaman yanda kikayi tun farin zuwanki,babu wanda yataba tsallake dokana seke hakanan babu wanda yataba yunkurin wargazamin duk wani shirina seke",tayi maganar tana zarewa Asma'u idanu tareda nunata da yatsa sannan takuma sakin dariya kamar wata tababbiya wanda hakan haryafara bama Asma'u tsoro kafin tace......

"wakikeyima haka,how can you benefit from it?"........
Shiru tayi batacema Magajiya komai ba don gani take matar ba lafiyar taba yanzukam,wani harara Magajiya takuma sakar mata sannan tace"nasan dai bazakice min sabida kisamu zama ah masarautar nan kikeyiba hakanan bazakice min sabida ya'yanki kikeyiba sabida banga tahanyar dazasu zo masarautar nan ba tunda shi wanda kike ikirarin yakawo ki masarautar nan din to basonki yakeyi ba kuma bazai taba sonki ba!"......
Yanda Magajiya tayi maganar seda Asma'u taji zuciyarta tayi wani irin bugawa lokaci guda.....
Zaliha ma dariya tayi kafin tace"ni har tausayi take bani Mama gabadaya gani takeyi babu ya ita agidan nan akwai rashin gatan daya wuce mijinka yakika,akwae rashin gatan daya wuce ace mace taje tana rokon mijinta yayi faking smile for her ai wallahi duk son mulki na da sarauta ta dakuma duk sonda nakema 'Da namiji bazan taba rokonshi yasoni ba hakanan bazan taba nunamai inasonshi ba kenan ma yarainani,kenan ma yadaina ganin mutuncina har abada kina fifiko dakanki kina kuma ji kewata ce but believe me you're nothing Asma'u, you're nothing tun ranarda kika hada hanya da Yarima don ina iyacewa shine babbar asarar dakikayi ah rayuwarki.......
Asma'u dai so speechless,so out of words gabadaya tarasa ina sukasan sirrinta,inasukasan meyake wakana ah rayuwarta da Almustapha.......
ganin yanda expression din fuskar Asma'u yakoma yasa Magajiya cigaba da magana harshly.......
Kyaleta Zaliha balaifinta banena she was blackmailed, she's now thinking that her husband is the most pious guy on earth,gani takeyi duk abubuwan damutanen gari kefada akanshi sharri akayi mashi,gani takeyi baya shaye shaye,gani takeyi baya bin yaran mutane yana musu fyade tareda keta musu hakkiinsu bugu da kari yaje hotel ma ya hole dawasu yan matan,gani takeyi baya satan da mutane da dama suka tuhumeshi abaya yanayi......

Asma'u daranta na Kuna tace"it's okay, yaisheki haka kidaina zagin Mijina you might think that zaki iya brainwashing dina but you can never do that,I trust my husband Magajiya and nothing can change that!in akwai wanda yakamata Inga laifinsa ma to kene,in akwai wanda yacuci mijina yasa anamasa wannan kallon then on one is to be blamed but you,you did alot of things and you get away with it but this time kiyarda dani bazan sake barin ki cuci wani ba kuma wayanda kika cuta dinma nanbada jimawaba Allah zai kwace musu hakkiinsu dayardarshi", Asma'u takarashe maganar tana kuka sannan tadubi Zaliha tace kekuma gobe muhadu agaban Mai Martaba gameda abunda kikayima bayin nan because this's not the right way to lead tana gama fadin haka tajuya don tafiya jitayi Magajiya tafara magana.......

"Kijeki inbaki yarda dani ba hakanan kiyi yanda kika ga dama but the fact that your Husband is a bad person will never change besides there is no smoke without fire,kintaba ganin lafiyyayyar namiji kamar Almustapha betaba neman Matarsa ba agurin kwanciya bayan kuma yanada ita,kintabaji ko ah labari bayan shiba gunki bane ba komai ba he can't pretend to be pious but sooner or later the truth will be out Kuma inason inbaki shawara kiyi bincike akan mijinki dakike ikirarin kinfi kowa sanin koshi wanene,itadai Asma'u tafiya tayi tanajin abubuwan da Magajiya ke fadi wnda gabadaya se suka mata zuciyarta sukeyi she don't want to believe it and that's because she trust him way too much sede wata zuciyar natuna mata wasu abubuwan wanda sukeson............

"Kubi littafin ahankali inayinshi ne yanda natsara,I hope zakubini cikin harmukai karshe da yardar Allah"...Sata tayarda badon tayi niyaba dafe kirjinta tayi ahankali tana furta"innalillahi wainna ilaihir,ya Allah kaduba mini kaji tausayina karkasa magan ganun matar nan suyi tasiri akaina",dakyar tacigaba da tafiya tareda godema Allah dabatazo dasu Hindatu ba yau don daman bawanda yasan tafito yawatawa cikin masarautar da tare sukaxo definitely zasu fada ma Ummi and hakan zetada hankalinta itakuma batason hakan yafaru kwata kwata.komawa bangarensu tayi tawuce dakinta don har lokacin sallar maghrib ma yakusa haka tayi alwala tazauna jiran lokacin sallah yayi dukda kuwa maganganun Magajiya da Zaliha nayimata yawo acikin kwanyarta she can't believe they know so much about her harhaka,ta yaya akayi sukasani tunda dai itabatada kyakyawar alaka dasu hakanan wanda take tareda suma ba wani alaka sukedasu ba bare ace,dan tsaki tayi kuma tareda tashi don tada sallah jin anashirin shiga masallaci sallah koda ta idar da sallah Qur'an tadauko tashiga karantawa cikin kira'arta maidadi, har lokacin Isha tana kan darduman haka ranan babu inda tafita ko abincin Almustapha ma cewa su Hindatu tayi su mika masa daki.......

Bakaramin mamakin rashin ganinta yayi ba yau din har wajajen karfe shadayan dare donshima kwanan nan baicika kwantawa bacci dawuri ba due to some research dayakeyi ah system dinshi gashi Dan abokin Abba dayake kula da asibitinsu na wancan kauyen yahada shi dawani *Doctor Na'im* yana aiki anan asibitin garin Zaria wae he's a very good Doctor he can learn may things daga gareshi donshi ah India ma yayi karatunshi yagama medicine tun yana 24 years old yanzu almost 7 to 8 years kenan don da alama Doctor Na'im din ze iya bama Almustapha 1 to 2 years haka,at first he doesn't like the idea of meeting the guy but yanda Dan abokin Abban ya matsa ne yasashi fixing time suka hadu wanda tun ranar farko yagane cewa Na'im is a very gentle Man Kuma da alama tasu zatazo daya donshima mutum ne da bayason hayaniya.to acikin sati dayan dasukayi tare don yakai sau uku Almustapha nazuwa gurinshi don babu randa zaije baisamu sabon knowledge ba game da field din karatunsu barinma aka surgery dadai sauransu yanzu hakama yabashi topic ne yayi recearch akai inyaso next time insun hadu seya masa bayani dallah dallah,seda yagama abubuwan dazaiyi sannan ya kashe laptop din yafice ah dakin don dubo Asma'u don dukyanda yaso yakauda tunanin ta aransa kasawa yayi,koda yaje dakin bata sa key ba wannan yabashi daman karasawa cikin dakin wutan dakin akunne yake can kan darduma ya hangota tana kwance uncomfortably yayinda alqur'ani ke ajiye tadayan gefen karasawa yayi ahankali yafi minti biyu tsaye ah kanta yayinda hannunsa ke sanye cikin aljihun wandonsa kafin daga karshe ya duka yadauki alqur'anin yaje ya ajiyeshi ah ma ajiyinsa sannan yazo yashiga tashinta ahankali yau baccin nata baiyi nauyi ba shiyasa koda yakira sunanta akaro na uku tabude lumsassun idanunta tadora akanshi.......
Cikin cool voice dinsa yace..
"kitashi kikoma kan gado you might get sick by sleeping on the floor"......
Sa hannu tayi tadan wartsake idanunta yayinda hakanan tadinga jin zuciyar ta na dukan uku uku dakyar tadinga furta "innalillahi wainna ilaihir rajiun",aranta don kallonshi datayi setake jin maganganun Zaliha da Magajiya suna dawo mata fillah fillah.......
Hannunshi yasaka dede fuskarta yana waving mata ganin yanda tayi shiru tana kallonshi ne yasashi cewa"are you okay?".....
Dakyar ta'iya gyada masa kai tareda faking smile shima mayar mata yayi sannan yace taje takwanta kan gado babu musu tatashi takoma kan gadon ta kwanta tareda lullube jikinta yajima tsaye kanta batareda ya motsa ba itakuwa baccin nacinta daman shiyasama koda takwanta batabi takanshiba takoma bacci abunta ganin baccin nata kaman yayi nisa yasashi karasawa bakin bed din tareda gyara mata hulan kanta hakanan seyaji yanason yasake yimata irin na jiya"the way he kissed her forehead",don haka seya sunkuya calmly kafin yadaura lips dinshi akan soft goshinta tareda lumshe idanunshi,cikin bacci taji ana tabata ga numfashin mutum da takeji akanta hakan yasata saurin bude idanunta arba tayi da nashi idanun donshima yadago kenan cikin sauri yatashi tsaye kamar marar gaskiya haka Itama tajuya kanta zuwa dayan side din batareda yasake dubanta ba it's just so embarrassing yarasa ta'ina ma zai kare kanshi dakyar yayi bacci ranar haka Asma'u ma don tunane tunane tadingayi she just cannot believe Almustapha yayi kissing forehead dinta to inma yayi dawani niya shine nata tunanin because takasa banbancewa shin wani progress ne ah relationship dinsu ko duk saboda he's being nice to her ne kafin tatafi.............

STORY CONTINUES BELOW


***
Washegari as usual Asma'u sukayi morning chores dinsu kafin tayi wanka tayi shirinta cikin hadaddiyar atamfarta don bata manta zuwa gun Mai Martaba datayi alkawarin zataje ba yau din dukdama wata zuciyar nacemata tasamu Almustapha first dukda tafi tunanin zai iya cewa miyasa ta shiga abunda ba nata ba itakuma Allah yagani bazata bari yara su wahala ba daga laifi kadan se ace za akaisu gidan yari memakon ayi masu sulhu ah tsakaninsu..........

Duban mirror tayi tasaka kwalli tareda shafa wet lips ah Dan karamin pink lips dinta ta yafa gyalenta sannan tasaka flat shoe dinta tafice harzatayi hanyar fita seta ce ba ta duba shi don yauma ba'ita takaimai breakfast nashiba hakanan setakejin nauyinshi na abunda yafaru jiyan.......
Knocking kofar dakin tayi as usual amma be amsa ba hakan yasa tabude kofar tashige abunta still yana kwance abunshi betashi ba duban wristwatch din hannunta tayi har 7 minutes to 10:00am mamakine yakamata basatan miyasa ba kwanannan Almustapha bayason tashi dawuri mostly ma seta shigo ne take tashin shi ko ya tashi"is anything bothering him,kokuma aikine yakemai yawa", wannan shine tmbayar datakeyima kanta ahankali takarasa bakin gadon tareda kiran sunanshi cikin cool voice dinta"Yaya Imam?"....
aikuwa yabude lumsassun idanun sa dake dauke da bacci haryanzu yadaura kanta ganin kallon dayakemata ne yasata tunawa da jiya cikin sauri tadauke kanta tareda tashi tsaye"Ina kwana?".....

Be kulata ba sema addu'an tashi daga bacci daya sabayi aranshi kullum yayi yau dinma sannan yatashi yazauna yana kallonta tanata wasa da fingers dinta ganin baida niyan kulata ne yasa tace...
"kayi wanka kaxo kayi breakfast I want to talk to you about something",tana gama fadin haka tafice abunta hakanan taji gwanda tafara magana dashi kafin taje gun Mai Martaba din.......
Cikin mintuna arba'in yagama shirinshi cikin kananun kaya dasuka amshe shi koda tadawo samunshi tayi yana breakfast don haka tazauna kan sofa tana satan kallonshi itadai Allah yagani tafison ganinshi cikin manyan kaya sunfiyimasa kyau dakuma kara masa wani irin haiba dukdama kananan kayan ma ba baya ba jitayi yace "maganar me zamuyi,I'm done", yakarashe maganar yana nuna mata plate din abincin da hannunshi.....
Gyadamai kai tayi kafin tafara mai bayanin abunda yafaru jiya dukda bata cemishi Zaliha ta maretaba hakanan bata nuna mishi sunyi wani argument akanshi ba don gani take wannan din baishafeshi ba ita yashafa karkumanta duk maganarnan avoiding hada Ido dashi tadingayi yana lurada ita amma seyace"it's Zaliha's responsibility miyasa zaki shiga,ko ita tana shiga naki hurumin?"............
Cikin sauri tace dajimawa fa ankawomin kararta kan tana bullying Bayi akan laifin dabai taka kara ya karya ba amma senayi shiru tunda bantaba gani ba kuma aganina ba hurumina baneba sede wanda nagani da'ido na gaskiya ba akyataba indai haka akeyi masu hukunci dawanda yayi laifi dawanda baiyi ba duk se ahada ace za aci zaklinsu it's not fair gaskiya......
Yanda take maganar ranta abace kamar wanda ita akayimawa yasashi sakin murmushi aranshi yana"dorama kai damuwar da ba tata ba",kafin afili yace"I'll look into it basai kinsamu Mai Martaba ba".....
Gyada mishi kai tayi cikeda gamsuwa kafin takarasa tadauki tray din abincin batareda ta kalleshi ba tafice shima baijima ah dakinba yafito,ah dakinta yasameta cemata yayi"kifito muje to".....
Batareda ta juyoba tace"Ina?".....
Ganin kamar silly question tayi masa yasashi juyawa yayi tafiyarsa dasauri tabiyo bayanshi ahaka harsuka isa gidan yari din tundaga nesa Sarkin gidan yari yahango Almustapha wannan dalilin yasashi tahowa cikin sauri har jikinsa na bari.....

"Yarima ina kwana?".....
"Lafiya",cewar Almustapha kafin yace akwai Bayin da sukenan tun shekaranjiya so nake kafito min dasu.......
Cikeda tashin hankali Sarkin gidan yari yace"yanzunnan Magajiya ta aiko ayi masu hukunci kasan laifin sata aka kamasu da duka".......
Wani kallo Almustapha yayima Sarkin gidan yari wanda babu shiri yajuya don aiwatar da abunda Almustapha din yace ko minti biyar ba ayiba segashi sun fito dasu su Safara'u duk jikinsu yayi jina jina da jini tsabar dukan dasuka sha cikeda tausayi Asma'u ke kallon su harsuka karaso inda suke.....

Ran Almustapha abace yace"waye yayimusu wannan danyen aikin?"..
Bakin Sarkin gidan yari na rawa yace"sata sukayi Yarima".....
Wannan karan har huci Almustapha keyi"Kai kakama su sunyi satan?"....
Cikin sauri yagirgiza kansa sannan fuskar Almustapha babu wasa yace"waye yayi musu wannan abun, I'm asking you for the last time?"...
Jiki na bari Sarkin gidan yari yace.....
"Gimbiya Zaliha ce tayi masu wasu raunukan tun jiya seyanzu da Magajiya taturo tace ayi musu bulala ashirin ashirin nanda kwana uku inbasu fadi gaskiya ba ah guntule hannayensu su duka"........
"Kaje ka kiramin Zaliha din"......
Babu musu Sarkin gidan yari yawuce don aiwatar da abunda akasakashi Asma'u duban Almustapha tayi dayaketa huci tace kazauna mana tayi maganar tana nuna masa wasu kujeru dake can gefe.......
Kokulata baiyi ba because bayajin yana mood din yin magana ma ahaka har Zaliha tazo tana ta wani kumburi na akan miyasa Yarima zai kirata ah wannan lokacin bayan lokacin hutun ta ne,what does he think of himself ma tukunnan donda cewama tayi bazatazo ba amma Magajiya tace taje suga miye zaice.........

STORY CONTINUES BELOW


Almustapha dake tsaye gefen Asma'u ko kallon Zalihan baiyiba bare yasan da existence dinta agurin Asma'u kuwa ganin isowan Zaliha gurin setasa hannunta cikin na Almustapha tayi interwining dinsu guri daya,shi kuwa hakan datayi seyaji wani irin comfort dabai taba jiba lokaci guda hakanan babu shiri yajuyo yakalleta lallausar murmushinta ta sakar mai kafin tace...
"Zaliha is here".....

Cikin cool voice dinsa yace"I know", yakarashe maganar tareda unlocking phone dinshi yafara dube dube........
Ganin haka Asma'u se taja bakinta tayi shiru donta san hali yanzu seya fada mata badadi,Zaliha kuwa gabadaya takaici ya cikata ganin yanda Asma'u da Almustapha ke kallon juna harma Smilling din da Asma'u keyi mai and what hurts her more shine data tuna Salma cemasu tayi baswa shiri kwata kwata amma ganin datayi masu yanzu yasata fara feeling cewa they've some deep connection,a very deep connection!ganin intacigaba da kallonsu bakin ciki zai iya hallakata yasatacewa"Yarima you called for me?"...
Bai kalleta ba barema yanuna yasan tana magana Asma'u ne tadanyi pinching hannunshi kafin in a whisper tace "Yaya Imam?".....
Dauke kanshi yayi daga kan phone dinshi yadubeta alamar yanason jin meyasa takira sunanshi turo baki tayi ahankali sannan tace...
"anayi maka magana"....
Da kamar bazaiyi magana ba can kuma seyadubi Asma'un sannan yace"ask the girls to repeat abunda yafaru the other day"......
Girgiza kai kawai tayi tareda sakin murmushi kafin tadubi Halima cikeda tausayawa tace"meya hadaku da Safara'u Halima?"......
Halima da take idanunta suka canza launi tafara magana...
"Gimbiya nida Safara'u mukanyi aiki ah bangaren Galadima ne ni inayima uwargidansa aiki se ita Safara'u ah amaryar to dai kinsan abunda yafaru da Galadima gabaki dayan mu Bayi semuke ganin in an sake shi ana iya saukeshi daga position din da yake wannan dalilin yasa wasunmu ke tsoron kada amaida su aiki kitchen kokuma gurin wankau sabida shine cheapest aiki ah gidannan to wannan dalilin yasa ah irin wannan lokacin bayi kanyi dauke dauke kama daga kan gwal,kudi ko kaya tonidai ah gaskiya banida wannan ra'ayin sabida uwar dakina tsakani da Allah muke tare da'ita hakanan sabida abun karaya ya samesu bazan taba juya mata baya ba to koda suke maganar hada baki zasuyi dauke dauke ah tsakaninsu wa'azi nayita yimasu amma ko ajikinsu hakan yasa nace tonidai karsu taba na uwar dakina inbahaka ba zan tona musu asiri duban Asma'u Halima tayi kafin tace"dukkansu babu wanda yayi tunanin Satan kayan uwardakina sabida kashedin danayi masu amma ita Safara'u dake batada godiyar Allah shine ta lallabo tazo tasaci dankunnayen Uwar dakina kuma inda Allah yatoni asirinta Ina wankin bandakin uwardakina tashigo tayi satan todanazo na tona mata asiri shine tadunga musu wai itabata dauka ba bayan wallahi da idanuna naganta bansan ya akayi tamaida abun kaina ba donkoda akazo bincike cikin kayana akasamu sarkokin wannan dalilin yasa uwardakina ta zazzageni sannan takoreni tace bani ba ita kuma wallahi ni bani bace Gimbiya,kiyarda dani don Allah", Halima takarashe maganar tana kuka me tsuma zuciyar daka ganta zakaga iyakar gaskiyar ta take fada............
Cikeda damuwa Asma'u tace kin tabbatar abunda yafaru kenan,gyada Kai tayi ahankali kafin Asma'u tace itakuma rukayya meya kawota cikin zancen nan?......
Cikin sauri Halima tace itace taga sanda Safara'u tasa gwal din cikin kayana dataga zaayimin horo shine tazo tafada kinga Itama yin hakan datayi besa ta tsiraba,"ya akayi kikasan Safara'u ne tadauki yan kunnen ba Halima ba", Asma'u tajefa ma Rukayya tambaya kai tsaye sunkuyar dakai Rukayya tayi kafin tafara magana cikin sanyi.......
"Gimbiya dakinmu daya da Halima ranar laraba dayanma bayan ance tayi sata ance za azo bincike da daddare nabar bangarenku zanje canza kaya naganta tana sawa cikin kayan Halima shiyasa nabada shaida daga baya"......

Ajiyar zuciya Asmau tayi kafin tadubi Safara'u da duk ta rude lokaci guda da alama bata da gaskiya zare mata idanu Asma'u tayi"kinyi sata ko bakiyi ba?"....
Muryana cracking tace"nifa ba...bu a..bunda nayi"........

Almustapha dake danne danne cikin wayarshi haryanzu dukdama rabin attention dinshi nakansu yayi locking phone din tareda sawa cikin aljihun wandonshi kallo daya yayima Safara'u wanda yasata sakin fitsari ah wando bakaramin kwarjini yamataba lokaci guda gawani tsoronshi daya lullube ta cikin calm voice dinsa yace...
"Zaki fadamin waye yayi satan ne ko saina sa an guntule miki hannu tukunnan?".......
Baki na rawa tadaga hannunta sama alamar roko...
"Don Allah Yarima kayi hakuri,wallahi bazan sake ba,sharrin shedan ne Allah bazan sake ba",Safara'u keta magiya lokaci guda.....
Daga Asma'u harsu Zaliha bakaramin mamaki sukeyi ba na ganin yanda tayi confessing dawuri,Almustapha kuwa jin Magiyanta nanema samasa ciwon kai yace"apologize to them"......
Baki narawa tace"eh?",don bata gane meyace ba dariya Asma'u tayi kafin tace"cewa yayi kibama su Halima hakuri".....
Jikin na bari Safara'u ta zube gaban su rukayya tana"kuyi hakuri don Allah kuyafemin,kuyimin rai dan Allah wallahi zanje infadama uwardakin ki nina dauka bakeba Rukayya"......
Rukayya da Halima cewa sukayi sun yafe mata,godiya tadinga yimasu yayinda Almustapha yace"inkika yarda kikasake daukan abunda ba naqiba I'll make sure I cut off your neck with my very own hands"......
Cikin kuka Safara'u tace"wallahi nayarda Yarima, Allah nayarda nagode nagode sosai", takarashe maganar dukda batagane karashen maganar ba ammadai tanada tabbacin ko ah mafarki akace tasake sata bazata sakeyiba.duban Sarkin gidan yari yayi kafin yace "kakaita cell ta kwana for today that's her punshment na involving wasu cikin abunda ba laifinsu bane ba and make sure you release her early morning tomorrow"......
Jiki na bari Sarkin gidan yari yace to yallabai harya juya zai aiwatar da abunda aka sakashi yaji Almustaphan yace....
"yauwa daga yau banason inji batun wani yayanke hukunci akan Bayi if they've any problem they should meet me personally katara su kayimasu wannan bayanin it's my order as the crown prince"........
Yana karasa fadin haka yayi gaba abunsa Asma'u ma taimakawa Rukayya tayi suka bi bayan Almustapha din bayan tasa wata baiwar tatafi da Halima bangaren Bayi sannan tace ta taimaka mata ta duma jikinta da ruwan zafi anjima zatazo tadubata dakanta.....
Zaliha kuwa dake tsaye kamar gunki tabisu da kallo tana hucin bakin ciki aranta tana"who the hell does he think of himself,yakirata amma ko kallon inda take baiyiba ba tsabar wulakanci and on top of that yabudi baki yace yasaukar da'ita ah post dinma bazai iyaba sedai yabada order,lallaima Almustapha dinnan be Isa ba inyanaji da kanshi itamafa *Yar Gidan sarautarnan ce* sarautar ma badaga sama ta tsince taba kamarshi ita Sarautar ma ah jininta yake hakanan acikin sarautar tatashi sabida haka be Isa yamata gadaraba,haka tayi bangaren Magajiya tanata huci ita kadai tundaga bakin kofar dakin Magajiya tahangonta cikin sauri tataso tana"meya faru yanaga kinata zufa ke kadai?".........

Zaliha batasan sanda tasaki kukan takaiciba don bakaramin bata mata rai Almustapha yayiba,harya kirata amma ko kallo bata isheshi ba,ae ko kashi tayi ajikinta sehaka..........
Magajiya data matsu taji maiya faru tace"kiyimin bayani mana zaliha?"...... Zaliha na kuka takwashema Magajiya dukyanda akayi ah zabure Magajiya tatashi tana"Don ubanshi be isaba wallahi ko uwarsa tayi kadan bare shi",Jan hannun Zaliha tayi tana"muje gurin Mai Martaban aishi yabaki aikin bashiba sabida haka bashida right din cewa bazakiyi ba"....
Haka suka kwasa sukayi bangaren Mai Martaba baya dakinshi ma amma don jaraba Magajiya tasa aka kirawoshi daga fada cikin mintuna kalilan yakaraso cikeda damuwar ganin Zaliha na kuka yace"meyake faruwa newai?".."Itada wayene wai,why is she crying", Mai Martaba yadinga jero tambayoyi donson jin dalilin kukan Zaliha din..........
Magajiya dake gefe tana rikeda qugu tace"waye kuwa inba tsinannen Dankan nanba"......
Da mamaki Mai Martaba yace"tsinannen Dana kuma",don bakaramin girgiza shi word din datayi using yayiba.........
Batareda tadamu da reaction din fuskarsa ba tadubi Zaliha cikin tsawa"ba kuka zaki tsaya yimasaba bayani zakiyimasa na abunda yafaru"......
Zaliha dake kuka harda na munafurci aciki tashiga goge kwallarta in a very calm voice mai Martaba yace...
"why are you crying Daughter,feel free kifada min kinji".......
Gyada masa kai tayi ahankali kafin tashiga yimasa bayanin yanda sukayi da Almustapha dukdama taboye nata laifuffukan jiki ah sanyaye Mai Martaba yasa aje ah kira masa Almustapha ba ajimaba segashi yazoshi barka da rana yayima Mai Martaba kafin yace"gani Abba"......

Batareda Mai Martaba ya ansa Almustaphan ba yadubi Zaliha yace"Mai maita abunda kika fada min recently".....
Bakintane yafara rawa dakyar ta'iya daure wa tasake fadan abunda tafada dazun Almustapha yasha mamakin yanda tasharara karya dubanshi Mai Martaba yayi yana"Haka akayi?"......
Kan Almustapha na kasa yace"ba haka bane ba Abba,Sarkin gidan Yari yana gurin inshi yafada maka nasn zaka yarda dani", babu musu aka aika kiran Sarkin gidan yari kafin Mai Martaban yace"meya hada Zaliha da Yarima,kafada min tsakaninka da Allah"......
Jikina bari Sarkin gidan yari yashiga fadin abunda yafaru batareda yaboye komai ba because ayanzu bazai iyayima Almustapha sharri ba koda kuwa ranshi yanaso.........
Magajiya da bakinta ke sake cikeda mamakin Sarkin gidan yarin tace..."oh lallai hada baki kukayi ko?",don bata taba tsanmanin Sarkin gidan yari bazai goya mata bayaba........
Cewa yayi...
"Magajiya kema kinsan gaskiya nike fadi ae sede kiki Allah kiboye gaskiya ba".....
Wutsiya tayi mashi tareda niyan tashi takai masa maka Mai Martaba ne ya daka mata tsawa cikeda mamakin wai ita zata iya daga hannu tace zata bugi Sarkin gidan yari,dattijon mutum godai godai dashi......
"Baki da hankaline Magajiya,mekike shirin yi?".....
Cikeda huci tace"abunda yadace dashi harni zai fadama magana don ubansa".....

Shidai Almustapha yana zaune kansa ah kasa se murmushi yakeyi, itakuwa se balbali take itakadai yayinda Zaliha tacigaba da kuka tana sharri Sarkin gidan yari da Yarima ke shirin yimata ..........
Dakatar dasu Mai Martaba yayi rai bace sannan yadubi Magajiya yana"tukunnan ke miye naki acikima in the first place?"......
Magajiya na huci tace"oh tambayatama kakeyi miye bawa aciki Abdulrahman,kama
nta waye Zaliha agareni?",tayi maganar cikin tsawa hararanta Mai Martaba yayi sannan yace"nalura kinfara samun tabin kwakwalwa, inkina Jin Zaliha surukarki ce to nima haka besides bakida right din dazanyi magana kice zaki mayarmin Indai kinsan mutuncin aure barekuma azo ga batun matsayina sabida haka kitashi kifita kibani guri tunkafin raina yabaci yanzunnan", Mai Martaba yakarashe maganar tareda nuna mata kofar fita gabadaya yarasa meyashiga kan matarnan kwanan nan .....
Tana shirin magana yadaka mata wani uban tsawa wanda ba'ita kadai ta girgiza ba harsu Almustapha dake gurin seda suka razana babu shiri tafice tana kunkuni itakadai.........

Seda tabacemai dagani sannan yadawo da hankalinsa kan Zaliha dake kukan munafurci yace..
"are you still going to hide the truth ko zaki fadamin gaskiya?".........
Cikin kuka Zaliha tace"kayi hakuri Abba".........
Ajiyar zuciya yayi sannan yace"I trust you,I thought you're sensible shiyasa nabaki wannan matsayin but today you prove me wrong Zaliha.tayaya zaki hukunta wanda baisan hawaba baisan sauka ba,tayaya zakici zalin wanda yazo yataimaka miki gurin fadar gaskiya, in anahaka kenan nan gaba anbasu dama sudinga boye gaskiya kenan sabida babu wanda zaiso don yafadi gaskiya ah hukunta shi batareda yayi laifin komai ba"......
Zaliha dae hakuri tadinga bama Mai Martaba kamar wata mutumiyar kirki amma dukda haka Mai Martaba yafada mata sincerely"I can't trust you anymore and inkikace zaki biyema Mamanku you'll end of regretting,you better take care of your marital life inaganin zaifiye maki"........
Daganan yace tatashi tatafi jiki ah sanyaye tafice ah parlourn dukda kuwa zuciyarta wani irin ruruwa takeyi...........

STORY CONTINUES BELOW


Koda tafice bangarenta tawuce don batada strength din samun Magajiya ma yanzu ga Sulaiman yadaina nemanta yanzu itakuma harga Allah kuma tana jin bukatar mijinta kwanan nan........
Bayan fitan Zaliha Almustapha yace"I'll take over,dukwani hukunce hukunce zankula dashi Abba so,you don't have to worry'......
Dukda bakin da zuciyar Abba yayi sakamakon abunda yafarun seda yaji sanyi jin kalaman Almustaphan dayayi........
"Nagode Son"....
Murmushi Almustapha yayi kafin Mai Martaban yace"basu zo bane?"......
Gyadama Mai Martaba kai yayi kafin yace....
"saida yanma wai dazu Dr Na'im yakirani yake fadamin dake akwai abokin shi dake aiki agurin sunama tare lokacin"............
So you finally have a friend?......
Yar dariya Almustapha yayi baice komai ba, murmushi Abba yayi sannan yace...
"it's good, he'll always keep you company and I hope he's a very good person".......
"He's nice and genial Abba",shine abunda Almustapha yace din yayinda Mai Martaba ya ce tobarina koma fada nikam........
Gyada ma Mai Martaban kai yayi kafin suka fice tare shiyayi nasu bangaren Mai Martaba yayi fada abunsa don yabarsu Dad acan ne.......

****
Tana komawa bangarensu dakinta tawuce tadauki wayarta don kiran Zahra amma switch off wannan dalilin yasata kwanciya hartadan fara gyangyadawa setaji kaman period dinta yazo wannan dalilin yasata tashi tashige bandaki aikuwa shidinne dan tsaki tayi tareda cire kayan jikinta donyin wanka don ita mutumce me shegen kyankyami shiyasa ma intana period tadinga wanka akai akai kenan batafi minti ishirin ba tafito daga wanka jikinta daure da towel seda ta goge jikinta tas sannan tawuce wardrobe dinta tadauko pant dinta da pad tana kokarin saka pad din jikin pant dinta jitayi anbude kofa hakan yasa tayi tunanin kosu Afiya ne har aranta tana mamakin ya akayi bata rufe kofarba kafin shiga wankan, dayake kofar akwai dan katanga daya tare side din da wardrobe dinnata yake sekadan shigo dakin sosai sannan zakaganshi............

Karasowa yayi cikin dakin cikin takunshi na kasaita ba tareda yayi sallama ba Asma'u da is busy trying to fix her pant tace"inban da hali irinna yaran zamani tayaya zaku shigo dakin sister in-law dinku guda batareda kunyi sallama ba"......
Almustapha da yanzu yayi arba da ita dake kusa da wardrobe ya tsaya yana karema figure dinta kallo ga towel din dan ficici dashi dako cinyarta bekai ba gakuma duk jikinta akwai ruwa kadan kadan wanda hakan yasata looking so sexy.........
Hadiye yawun bakin shi yayi dakyar still yana kallonta don dukyanda yaso dauke idanunshi daga kanta kasawa yayi Asma'u jinsu Amiran basuce komai ba yasata juyowa da mamaki don tasansu da magana kanacewa A zasuce ma B amma setayi arba da Almustapha dake tsaye yana kallonta da lumsassun idanunshi cikin sauri tajuya mai baya zuciyar ta na beating so very fast, she's just out of words tama rasa mezata cemasa ga abunda ke hannunta da tanada tabbacin yariga da yagani gashi sotake tasaka amma bazata iyaba agabanshi, kawae saita tunbuke pad din daga jikin pant din tashiga sake mannawa batareda tasan mema takeyiba fatan ta daya kada jikinta yabaci ayanzu because wani kayan kunyan hakan zaisake jamata........
Almustapha dahar yanzu kallonta yakeyi seyaji zuciyarshi da gangar jikinshi suna ingiza shi da yakarasa inda take,aikuwa karasawa yayi gareta wanda ko footsteps dinshi batajiba tsabar rikida sejin numfashin shi datayi ah wuyanta dan dora kanshi yayi ah gefe daya na kafadunta wani irin shivering jikinta yashigayi haka hannunta ma yashiga trembling, abangaren shi kuwa lumshe idanunshi yayi tareda budesu sannan yadaura kan pant din dake hannunta gabadayan ta dukunkune pad din cikin muryar dabaisan yanada ita ba yace"wayace miki haka akesawa?", yakarashe maganar tareda sa hannunshi ta cikinta yakarbi pant din da pad din daga hannunta itadai rasa nacewa tayi daga pad din yyi da dayan hannunshi kamar kashi sannan yace"kinbata wannan ai mikomin wani to" .....
Dakyar ta'iya samun courage din motsi da jikinta tana kokarin kwace kanta"l..et me goo please", murmushi yasaki mischievously"koya miki zanyifa but you're being rude to me", turo baki tayi still tana kokarin kwatan kannata"Banaso,nikabarni",tayi maganar cikeda kunyarshi yar dariya yayi ahankali sannan yasa hannunshi daya yadauko jakan virony daya hango cikin wardrobe din kafin yabude zip din tareda ciro kwaya daya sannan yamayar mata da sauran cikin wardrobe din still yana rikeda ita cikin lumana yashiga sawa aciki yana yimata bayani itakam kasa cewa komai tayi tsabar mamakin ya akayi yasan wa'yannan abubuwan,seda yagama sannan yamika mata kin karba tayi murmushi kawai yayi sannan ya ajiyemata abaki bakin wardrobe din dake bude kafin yayi whispering cikin kunnenta"I want to talk to you,kishirya kisameni ah dakina",daganan yafice yabar mata dakin itakam tananan tsaye kamar gunki don yaukam Almustapha ya gama kureta, tashigesu wato shi baida kunyama ko kadan harma wani bayani yake yi mata buga kafanta tayi ah kasa tareda dan bugun kanta ita kadai tana"Ya Allah I'm so nervous and Shy dawani ido zan kalleshi fisabilillahi",haka tayita kunkuni ita kadai duk motsin datayi setakejin kaman zatasake jinshi ajikinta ne.......

STORY CONTINUES BELOW


Dakyar tayi karfin halin komawa bandaki tasake gyara jikinta sannan tashirya cikin wani tsadadden lace dukdama batayi kwalliya ba amma bakaramin kyau tayi abunta ba seda tagama komai sannan tasamu bakin gado tazauna tanata sake sake aranta itakadai, Allah yagani bazata iya zuwa tasamoshi yanzu ba watoma shi don baida ta ido harma cewa yake taje tasameshi zasuyi magana kowani magana ne rai oho,itafa dabadan tasan waye Almustapha ba cewa zatayi dagangan yayimata abunda yayi inbahaka ba yaza ayi mace kamarta yace bata iya using Pad ba fisabilillahi,anan tayita zama batareda tasan lokaci nata kurewa bama..........

Around 3:00pm yagama shirinshi cikin kayan sarauta don yanzu Dr Na'im yakirashi yana fada mishi by 4:30pm zasuzo nan gida cewa yayi"kaima kakoma aiiki ah gidan talabijin ne?".....
Dariya Dr Na'im yayi kafin yace....
"Dr rowaar gidanku kakeyiman?"......
Dan shafa kai Almustapha yayi sannan yace"that's not what I mean".....
Ah ah kaidai just go straight to the point kace"Na'im banason kazo gidanmu you're too low for my liking Ina Dan gidan sarauta kana pure talaka ta'ina ma tamu tazo daya", Na'im din yafada mockingly Almustapha baijidadin kalaman Na'im dinba dukda yasan cikin wasa yayi masa but definitely ze iya yuyuwa akwae wannan tunanin aranshi don haka seyace"I'm sorry inkazo zamuyi maganar".....

Dariya Dr Na'im yayi sannan yace"ni wasa ma nikemaka Yarima,semunzo din daman Saifullah ne yace inyi masa rakiya bemasan nasankaba seda nafada mishi"......
Gyada kai kawai Almustapha yayi kafin ya katse call din duban time yakumayi tareda tashi yafita ah dakinshi yana mamakin meyahana Asma'u zuwa bayan yace mata"has has something to tell her",dakinta yawuce tana zaune bakin gadonta tana dan danne danne cikin wayarta yashigo ganin shine yasata saurin kwanciya tareda rufe idanunta kamar me bacci abunda batasani ba shine yariga daya ganta batareda yakaraso inda takeba yace....
"bance miki Ina nemanki ba?",shiru tayimai yayinda zuciyarta ke beating so very fast karasowa yayi ya tsaya kanta cikin cool voice dinshi yace"open your eyes"..........
Sake damke idanun tayi wanda hakan yasake tona mata asiri murmushi yayi aranshi yana"lallaima yarinyar nan taga gadon baccin na",kafin yasa hannayenshi ya dagota ae babu shiri tabude idanunta jin yataba ta tafara magiya"kasakeni to natashi".....
Kallon fuskar ta yayi yana lura dayanda taketa avoiding su hada idanu ahankali yace"look at me Asma'u".....
Mutsu mutsu tafarayi tareda kame kame still kanta nakasa sake kasa da murya yayi"ki kalleni nace"......
Makemai kafada tayi alamar ita a'a kamar zatayi kuka sake matso da fuskar shi yayi kusa da tata yana sake kasa da murya"Asma'u!"....
Yanda yakira sunanta seda taji gabadaya tsikar jikinta sun tashi amma dukda haka taki daga idanunta shikuwa sake matsar da fuskar shi yayi wanda har sunajin numfashin juna yanzu ga hancin su har gogan na juna yakeyi"uhmm,bazaki kalleni ba?",yayi maganar kamar wanda akasashi dole itakuwa babu abunda yadameta ah yanzu irin kamshin strawberry dake fita daga bakinshi dayake sata feeling wani iri ga closeness din is too much harda kyar take iya numfashi itakam me Almustapha keson zamane kwanan nan?........

Dakyar ta'iya kallon cikin idanunshi kamar yanda yabukata sake kasa yayi da murya wanda dabadan tana kallon movement din bakinshi ba tana iya rantsewa bazataji mezaice daidaiba"miyasa kike avoiding idanu na?",yajefamata tambayar da itakanta batada ansaba cikin sauri tadan tureshi tana....
"Yaya Imam!"...
Murmushi yasakar mata"tambayarki nayi bacewa nayi kikira sunanaba"......
"Why were you avoiding my eyes since morning, I've been noticing you".....
Cikeda shagwaba tace"Kaine ai"....
Nuna kanshi yayi ahankali yana"nikuma?".....

Gyadamai kai tayi ahankali,shikanshi yarasa miyasa yake biyema Asma'u kwanan nan he just want her to know that he appreciates all that she has done for him and his family yanason tasan shiba butulu baneba dukda haryanzu yakasa making decision akan yayi exposing secret ne koko aa because yanada tabbacin once everything is out that will be the end of their relationship kamar yanda tafada din...............

Jin yayi shiru kaman yana tunanine yasata cewa"zansauka".......
Cikin sauri yariko hannunta"bamu gama magana ba ai,nace kizo kisameni bakizo ba and yanzu kina blaming dina for everything"......
Cikeda takaicin yanda yake acting as if nothing happens dazun tace"Eh mana kai kake sawa Ina avoiding dinka ae, you're acting so strange this days Yaya imam,kanamin abunda yakesani jin kunyarka",yanda tayi maganar ah shagwabe seda ta bashi dariya kafin yace"waye yace i should be nice to him harmu rabu?"..........
Turo baki tayi tana"nine amma ai bahaka nike nufi ba"......
Ware hannu yayi in an I don't care manner yace"as far as I know banyimiki komai ba I was just trying to help".......
Wannan Karan idanunta ne suka cikada kwallah tana"haka ma zakace?"......
Gyada mata kai yayi kafin yace"I kissed your forehead as a friend and friends do that right?".....
"And secondly don nayi helping naki as a Doctor and friend aswell wurin koya miki yanda ake using sanitary pad shine wani abu, besides what are Friends for?".......
Kallonshi tayi tana mamakin yanda ko shame kadan bayaji, he's really saying what's on his mind harara tabuga mai sannan tace....
"don kana friend dina aini mace ne kai namiji ne so we're all matured".....
Ware idanu yayi cikeda mamakinta kafin cikin sauri yajanyota zuwa jikinshi ba tareda ta ankara ba taji bakinshi cikin nata wani irin soft and gentle kiss yayimata wanda hakan yasata wara idanunta cikeda mamaki hakanan takasa koda motsi ne seda yayi mai isarsa sannan yasa ke ta still yana rikeda kyakyawar fuskar dayake so bright and fresh cikin cool voice dinshi yace...
"I'm your Husband first Asma'u,then your friend"......
Wasu irin hawayene suka zubo mata batareda ta shiryaba shikuwa tashi yayi ahankali cikeda mamakin kanshi hakanan yana mamakinta don ah iya saninshi dai Asma'u mutum ce me addini bama sanin alqur'ani kadai ba tasan litattafai da dama tunda yana ganin wasu lokutan inya bama su Amira assignment ita suke samu tayi masu bayani sosae so,inma ta manta he has to remind her dukda kiss din was not just intentional shima urge din yazomishi out of blue ne kawai. haryakai bakin kofa yajuya yana kallonta sannan yace"I'm going to the mosque right now by 4:30 za ayi wancan program din i need you there",ficewa yayi batareda ya jira jin amsarta ba...............

STORY CONTINUES BELOW


Itakuwa cikin sauri tatashi dukda kuwa babu wani karfi sosai ah jikinta,kenan yau ne komai zai faru to miyasa befada mata dawuri ba dasunyi preparing komai ae ga Talatu ma bata dawo ba,right now tasa zuciyar ta is divided into two the other part na tunanin rabuwa da Almustapha dazatayi while the other one is happy sabida finally goal dinsu will be fulfilled.............
Daure zuciyarta tayi tafita zuwan bangaren Hajiya Muniba batawani tsaya gaidata sosai ba tace"Aunty zaki bada shaidanba?".......
Cikeda mamaki Hajiya Muniba tace"wani shaida?"......
Wanda mukayi magana ranar masu daukar labaran sunkusa isowa da anyi sallar la'asar.....
Oh seyanzu nagane mekike nufi to ita Talatun tadawo ne?......
Aa Aunty basaita dawo ba banason muyi losing wannan chance dinne,we've you ga Laure gakuma Mallam Audu mai kaji and nayima su Iya Hindatu magana kan sunemo min yaran dasuka bada shaida kan Yaya Imam yayi musu fyade,I want them to tell the world that it was all a lie,I want them to Clear all the alligations against My Husband in fyadene bayau akasaba yinta ba amasarautar nan and ah tsakaninsu ne su slaves din and I'm very sure sunsan the right person dayayi masu wannan aika aikan, they'll tell the world who that person is and he'll surely be punished for cutan young girls dayayi koma wanene Kinga sunsamu Justice and Yaya imam ma yasamu justice and you too inkinyi exposing komai gaskiya zata bayyana with all this witnesses Magajiya will be punished for all her Deeds and believe me this time nothing will go wrong insha Allah,cikeda gamsuwa Hajiya Muniba tace toshikenan Dear I'm with you.....
Murmushi Asma'u tasakar ma Hajiya Muniba din kafin tace"To Aunty kikira Mallam Audu din yazo gida nan nikuma zanje inyima Bayin nan magana and Laure should be around too.......
Shafa kanta Hajiya Muniba tayi cikeda son Asma'un sannan tace"you're indeed a blessing to this family Dear", murmushi kawai tayi mata kafin tafice cikin sauri don zuwa tasamu su Hindatu cikin minti talatin Asma'u tatara duk wani evidence da take bukata sannan tace sujira zuwan Yarima ........
Almustapha kuwa yana idar da sallah ya koma bangarensu sede da mamakinshi yaga wani dattijo da he look very familiar dukda yakasa tuna Ina yataba ganin fuskarshi amma saibaice komai ba yayi wucewarsa ciki to ah parlourn ma Bayi sunkai shida ah yayinda Hajiya Muniba da Ummi suna zaune kan three seater suna hira abunsu gaisheda Hajiya Muniban yayi dukdama shibawani son matar yakeyiba sosai ansamai tayi fuska cikeda annuri kafin Bayin ma suka shiga gaidashi yawuce ciki abunsa abakin kofar dakinsa sukayi kicibis da Asma'u murmushi tasakar mai sannan tace"I've been waiting for you".......
da mamaki yace"to gani ae nazo"......
Kamo hannunshi tayi sadly don lokaci daya tatuna rabuwarda zasuyi after today kallon hannunsu dake sarke dana juna yayi kafin yadubeta faking smile tayi ahankali yayinda tadaga dayan hannunta tanuna mishi Bayin dake zaune sannan tace"they're here for you Yaya Imam,sune wanda suka bada shaida kan ka keta musu mutuncinsu but now they've regret it and they're willing to speak out,sunyi nadama Yaya,zasu fadi wanda yayi musu hakan yau and you'll be free from all those alligations"takarashe maganar idanunta cikeda kwalla at thesame time tana murmushi kafin tasake daga hannunta tanuna direction dinda Hajiya Muniba take"And Aunt, she's here to stand for the truth too, she's here to take revenge akan abunda akayima family dinta,tazone ta tona dadadden sirrin da babu wanda yasan dashi akan tsohon Galadima da Allah yayimashi rasuwa tareda iyalinshi, she's his very own Daughter batacikin gidan sanda gobaran yatashi and it was not an accident intentionally akayi, Magajiya was responsible for their death cikeda shock Almustapha yadubeta yana mamaki don gabadaya yarasa gane metake fada shidai ah iyasaninshi ancemasu tsohon Galadima da iyalinshi baki daya sun rasu sakamakon gobara dayatashi ah gidan cikin dare and babu wanda aka iya akayi saving, ahankali Asma'u na hawaye ta gyada mishi kai irin she's saying the truth dinnan sannan tashiga mammatsa hannunshi cikin nata ahankali tace"kaga wani Dattijo awaje?"........
Gyada mata kai yayi ahankali, murmushi tayi still hawayen nazuba"doesn't he look familiar?"......
Ahankali yace"yea,kaman nasan fuskarshi".......

Murmushi tayi tareda dan goge hawayenta sannan tace"Mallam Audu ne wanda aka hada bakidashi akayimaka sharri kan kasaci kaji he's also here to clear everything Yaya Imam,today you'll be save, you'll be free from all those alligations against you and I",tayi maganar tareda kallon cikin idanunshi muryarta na cracking tacigaba"I'll be free from this relationship and my family will never think of you as a bad person daga yau"... ...........

Lokaci guda yaji jikinshi yayi sanyi yayinda ahankali yacire hannunshi cikin nata yadan jinginu da ginin dake bayanshi tareda lumshe idanunshi"today is a very special day may be because with all this evidences Magajiya will be behind boss and shima zargin da mutane keyi mishi zaitafi and on top of that yau relationship din da is base on compromise will come to an end,yes from the very beginning yayi mata alkawari zai rabuda ita with full of confidence but as of now shikanshi besan miye decision dinshi ba,if he wins today,then he'll loose two great people that plays a very important roll to his life that's "Sulaiman and Asma'u",sabida yanasane da cewa Sulaiman was the one that raped those girls,he was very aware sabida alokacin yana wucewa yaji wasu dogaraye na maganar and beji aranshi they were lying tunda sarai yasan kowaye Sulaiman indai akan Mata ne he never said something that time sabida bayason hayaniya hakanan alokacin yariga yayi giving up ma happiness aruwarshi gabadaya but yanzu he has a 100% reason to live if not for his subjects but for his family members sede will be be able to leave without this two people? ......
Wannan shine tambayar dayayima kanshi batareda shikanshi yanada kwakwaran amsa ba,yana cikin wannan tunanin ne yaji wayarshi tayi kara ahankali yadubi screen din wayar number Dr Na'im ne yayi appearing jiki ah sanyaye yadaga, daga bakin kofa kuma su Asma'u sukaji anyi sallama juyawa Asma'u tayi ahankali arba tayi da figure din Talatu dake tsaye bakin kofa wani irin ajiyar zuciya Asmau tasaki kafin tashiga takawa don zuwa ga Talatun
............Murmushi Talatu tasakar mata kafin tace"Ina wuni Gimbiya?"......
Batareda Asma'u ta amsa gaisuwar taba tashiga tattaba jikinta tana"Talatu are you alright,yakike,how was you journey nayi tunanin wani abu yafaru dake ne ganin baki dawo dawuri ba"........

Talatu Kara fadada murmushinta tayi kafin tace"Gimbiya nariga nadaukar Miki alkawari tun wancan lokacin kan cewa bazan taba dawowa ba harsainayi abunda yafitar dani daga masarautar nan Kuma alhamdulillah komi yatafi daidai",tsabar dadi Asma'u batasan sanda tarungumi Talatu ba aranta tana"ikon Allah kenan gashidai Talatu tadawo at the right time,dede lokacin da suke tsananin bukatarta",babu wata wata tafada mata halin da ake ciki itakuwa tace"Ina taredaku Gimbiya yau se inda karfi na yakare gurin fadan gaskiya koda kuwa hakan zai zamemin rugujewar farin ciki ah rayuwarta,kafin takaraso cikin parlourn ta tsuguna tareda gaida su Ummi kanta akasa ansawa sukayi fuskarshi blankly wanda itakanta takasa gane expression na fuskarsu............

Asma'u dake kallonsu duka tayi hanyar inda Almustaphan ke tsaye haryanzu ganin ya sauke wayar daga kunnenshi alama yagama making phone call din murmushi tasakar mishi kafin tace"alhamdulillah ma Talatu is back Yaya imam,she knows everything ita tana daya daga cikin masu yima Magajiya aiki and ita tahannun damanta ne,i've alot to tell you about her amma bayanzu ba tunda inada tabbacin suna jiranka by now",gyada mata Kai kawai yayi don shi gabadaya ma kanshi wani irin zafi yadauka lokaci guda,yarasa abunyi,yarasa wani mataki zai dauka ah yanzun gashi Dr Na'im yakirashi yace mishi suna ma Fada shi suke jira ...........
Ahankali yadubi Asma'u sannan yace I want to talk to Talatu and those slaves in private.......
Dukda tayi mamaki amma sebata cemashi komai ba cikin lumana tayimasu Talatu da bayin dake zaune magana kan Yarima nason zantawa dasu cikin sauri suka tashi sukayi inda yake daman suna neman hanyar neman yafiyanshi ne insun samu sukuni batareda yakallesu ba yayi hanyar dakin Ummi suma binshi sukayi itadai Asma'u komawa tayi parlour tazauna don ah ganinta bekamata tashiga ba tunda shidin benuna yanason hakan ba fatan ta daya Allah yasa lafiya..........

Seda suka gama shiga dakin baki dayansu kafin yacema Talatu datashigo ah karshe"kirufe kofar".......
Cikeda ladabi tace to sannan tarufe kofar kafin takaraso tsakiyar dakin ta tsuguna gabanshi kaman yanda sauran sukayi shiru dakin yayi sosai nawurin mintuna biyar kafin Talatu tayi karfin halin cewa"Yarima don Allah inbabu damuwa inason inneme gafararka akan abubuwan damukayi maku abaya nida Magajiya,don Allah kayafe min nibanmasan dawani idanu zandube ka ayaudinnan ba", Talatu takarashe maganar tana sharar kwallah kan kaceme sauran bayin ma suka shiga neman yafiyarshi suna wallahi Magajiya ce tasasu suyi masa sharri amma in Allah ya yarda yau zasu fadi gaskiya ..........
Yanajinsu sunata maganganunsu seda suka kai aya kafin yace"Wayene yayi muku wannan aika aikan?".......
Cikin sauri harsuna hada baki sukace"Yarima Sulaiman"......
Dukda Almustapha yasan hakan zasuce amma saida zuciyar shi tashiga bugawa dakyar ya'iya cewa"you don't have to tell the world about that,Nina yafemuku tunba yauba"....
Godiya suka shiga yimasa ahankali yadakatar dasu tahanyar daga hannunshi kafin yacigaba"Sede Ina neman alfarma agareku yau inafatan zaku bani hadin Kai",Talatu dake gefe tace munajinka Yarima........

Samun bedside drawer din Ummi yayi tareda zama sannan yayi ajiyar zuciya yakallesu"inason murike sirri tsakanin nida ku,inason ku boyema duniya cewa kanina shiya keta muku hakkin ku,inason kurufamasa asiri nasan bai cancanci haka daga gareku ba and yacuce yakuma raba ku da Martabarku da kowacce 'ya mace take takama dashi,I might sound selfish as a Brother but kuyarda dani Sulaiman is a changed person,yayimuku mugunta abaya amma yanzu yatuba yadaina hakanan shikanshi inya tuna abunda yayi nasan abun nadamunshi",gyara zama yakumayi sannan yace bazansaku dole kuyafema Sulaiman ba I'm just requesting hakanan ina nema mishi yafiya daga gareku on his behalf",yayi maganar yayinda idanunshi suka canza launi lokaci guda hakanan yayi folding hannunshi agabansu alamar roko",cikin sauri su Talatu sukace"Wallahi munyafe mishi Yarima tun tuni",daya daga cikin bayin ne takarada,"mukan mu bason fada mukeyiba sabida Yarima Sulaiman yahaskaka rayuwarmu ta fanni da dama wanda bazamu iya lissafa makaba kuma kobakomai Dan adam ajizine babu wanda yafi karfin yin kuskure abun Jin dadin anan shine yayi nadama dakanshi tunda tun da jimawa yazo yaneme mu dakanshi yanemi yafiyarmu ko awancan lokacin munriga da munyafe masa bare yanzu,yanda kaganmun Nan Yarima zamu bada shaidar ne kawai sabida babu yanda muka iya sannan munsani hakan zai iya taimaka wurin wanke kanka daga zargin jamaa shiyasa amna tunda kabukaci murife asiri in Allah ya yarda Babu Wanda zamu fadama"....
Wata irin sassanyar ajiyar zuciya yayi ashema Sulaiman din yanemi yafiyarsu dakansa,Talatu ne tace"to ae Gimbiya yakamata amata bayani"......
Cikin sauri Almustapha yace"kibari kawai Talatu,you can tell everything but karkiyi including maganar nan please"........
Cikeda ladabi ta sunkuyar da kanta kasa sannan tace"to Yarima",godiya yayi musu sannan ya sallame su seda suka fice ah dakin sannan ya lumshe idanunshi ahankali"atleast one problem is solved now",Don shi Allah yagani bazai iya zuba idanu yaga antonama Dan uwanshi asiri ba,he has changed so much kuma yanada tabbacin yanemi yafiya gurin ubangiji tunda Kuma Allah yasa bakowa yasaniba hakanan ayanzu ana matukar ganin darajar Sulaiman acikin masarautar dama gari baki daya yau in akace ga abubuwan dayayi abaya yasani wannan mutuncin da ake ganinshi dashi zata zube ah idanun jama'a da dama hakanan ko mutane sun yafe mishi ba lallai sumanta da abun aransu ba zasuna kallonshi dashi shiko Asma'u bayason tasan da zancen nan sabida bakaramin yarda dashi tayiba hakanan tana ganin girmanshi Itama tabbas intasani wannan kiman da darajan zai ragu ah idanunta sosai besides it's their secret between him, Sulaiman and wayanda suke gabanshi yanzu Magajiya kuwa yasani ko duniya zata nade bazata taba fadin cewa Sulaiman ne yayima bayi fyadeba sabida ita mutun da she's so very selfish on top of that dawanne Sulaiman din zaiji?....
Rashin uwa tagari koko betrayal from a Brother donshi aganinshi inyayi ma Sulaiman haka kaman yayi betraying dinshi ne,kaman ya butulceshi ne adaidai lokacin dayake tsananin bukatarsa......
Yana cikin tunaninnan ne yaji wayarsa tayi kara dubawa yayi wannan karan Mai Martaba ne ke kiran cikin sauri ya tashi sannan yafito ah dakin ah parlour yasamu su Asma'u kafin yafice cikin sauri Asma'u tacema bayin da Talatu su bishi tunda za anemesu acan....
Babu musu suka bi bayanshi itakuma tashiga wasa da hannunta nervously tana addu'a aranta Allah yasa komai yatafi daidai...........
Hajiya Muniba ne tataso daga gefen Ummi kafin tazo tazauna gefen Asma'u din tareda dan dafa kafadunta in a comforting manner kafin tace"Relax Daughter everything will be alright".....
Faking smile Asma'u tayi kafin Hajiya Muniban tace....
"ku kunna TV they're going to show it live"......
Mom dayanzu shigowanta parlourn ita takunna TV din kafin tazauna gefen Ummi suna gaisawa Hajiya Muniba kuwa ficewa tayi don zuwa fadan Itama Asma'u dai shiru kamar wanda ruwa yacita Allah ne kadai yasan abunda take ji aranta....
Tun ahanya yahadu da Sulaiman kallon kanin nashi yayi cikeda tausayawa yayinda Sulaiman din is just trying to be strong yace"they've been waiting for you ah inaka tsaya Yaya?".......
Murmushin dayafi kuka ciwo Almustapha yayi kafin yadafa kafadan Dan uwanshi yace"to ganinan nazo ai Bro".......
Kama hannunshi Sulaiman yayi suka fara tafiya yana"you don't have to be scared of anyone, it's about your future not only you but the subjects and Asma'u with your future children as well wannan opportunity ne mekyau don't loose it Yaya, because if you do that you might never get another chance........
Tsayawa Almustapha yayi wanda hakan yasa Sulaiman dinma yajuyo yana kallon Dan uwanshi cikin murya mai rauni Almustapha yace"I'm very Sorry Bro"........
Sulaiman besan sanda yajanyo Almustapha suka rungumi juna ba he's just so weak,he was just faking a smile amma azuciyarshi only God knows how he's feeling right now, tapping bayanshi Almustapha yadingayi in a comforting manner yana"If you really don't want Mama to be exposed I can do that for you Suleiman,indai hakan zaisa ka cikin damuwa it's better we stop".........
Cikin sauri Sulaiman yajanye jikinshi dagana Almustapha kafin yadaura yatsanshi kan lips dinshi yana girgiza masa kai dukda kuwa idanunshi sunyi jazir"My Mother is a monster Yaya Imam,I cannot deny that fact besides everyone has his own destiny so,inaga wannan shine tawa kaddarar,karka damu I'm used to it I've tried so many times wurin ganin tagane gaskiya Amma hakan beyuyuba so, it's better she get punished for all her deeds,in akabarta ma bazatabar mutane suzauna in peace ba".......
Almustapha dae kallon shi yake cikeda tausaya wa yayinda Sulaiman yayi murmushin dayafi kuka ciwo sannan yace"just pray for me that's all that I need right now, kayimin addu'a Allah yabani ikon jure abunda zangani"......
Amin ya Allah shine abunda Almustapha din ya'iya cewa kafin Sulaiman yarike hannunshi suka karasa fadan tundaga nesa yan jaridu da masu aiki agidan television sukayo kanshi suna saka masa microphone dinsu ah dede bakinshi alokavi daya kuma sukafara bombarding mishi different questions wanda yana iya rantsewa ma beji ko daya ba tsabar yanda kowannensu yakasa hakuri hakanan kowa so yake Yariman ya amsa masa tambayarsa dakyar dogaraye sukayi kokari gurin taimakawa aka buda masa hanya suka wuce........

STORY CONTINUES BELOW


***
Acan bangaren Zaliha kuwa tana daki taji bayinta nadan hayaniya daga waje tun tana shiru har tajj abun kaman yanason yin yawa cikeda bacin rai tatashi tafita zuwa parlourn ta gani tayi suna tsatsaye yayinda daya daga cikin su ke kokarin kunnan TV cikin tsawa Zaliha tace"Ke lantana,don uwaarki mekikemin agaban Tv?"......
Ba lantana kadai ba harta sauran bayin seda suka tsorata don kuwa basumasan tanaciku ba sunyi tunanin tana bangaren Magajiya ne shiyasa sukayi wannan karambani don baswason missing hirar daza ayi da Yarima Almustapha....
Jiki na bari lantana tajuyo tana"kiyi hakuri Gimbiya"...
wani irin dakuwa Zaliha tayi mata aranta tana lallai masarautar tagama lalacewa har baiwa ce takeda guts din kunna TVn uwardakinta"......

Daya daya daga cikin bayin ne tayi karfin halincewa "Gimbiya hira za ayi da Yarima shine mukeson mugani ah TV don ance yanzu za ah nuna".......
Cikin sauri Zaliha tadauki mopper data gani jingine ah gefenta kafin tayo kansu cikeda bakin ciki wanda hakan yasa sukafice ah parlourn da gudu cikeda tsoron kada tasamu daya daga cikinsu,huci take tana shegu tsinannu don za ayi hira dashi ni ina ruwana dahar zakuwani zo kuce zakuyi kallo ah TV na,to don ubanki insake ganin kafar wani anan tayi maganar tana nunasu da sandar moppern datake hannunta,lantana dake parlourn haryanzu sakan kuka tayi don ita Allah baibata ikon tsira ba juyowa Zaliha tayi tana kallonta da manyan idanunta tayokanta...
"wato kece gwana ta gwanaye ko?"......
Dora hannu tayi ah tsakiyar ka tana"kiyi hakuri don Allah Gimbiya wallahi bazan Kuma ba",magiyan datakeyi behana Zaliha karasa gunta ba tana shirin kaimata sandar ahijikinta taji muryar Sulaiman yana"what the hell are you trying to do Zaliha?"......

Cikin sauri tasauke sandar sannan tajuyo tadubeshi wani irin harara yadaka mata sannan yace "Meta Miki kikeshirin Kai mata wannan sandar?"
Zaliha na huci tace"aedaman Kai bazaka taba sanin metamin ba", takarashe maganar tareda ficewa daga parlourn ma baki daya shikam jijjiga kai yayi sannan yazauna bayan ya kunna TV din don can hayaniya yayi yawa yana son gani kuma live dukda main aim daya kawoshi bangarenshi don bayason abundama zaisa ayi pointing dinshi ace shi Dan Magajiya ne...
Lantana kuwa tuni tasamu hanyar ficewa ah parlourn ganin Zalihan ma tafice......

Zaliha babu inda tawuce inba bangaren Magajiya ba, Magajiya nazaune anayimata fifita yayinda Laure ke zaune tana mata massage dukda kuwa ranta ah kuntace yake.......

Kamar wanda aka wurgota daga sama haka Zaliha tashigo dakin cikeda bacin rai Magajiya tace kekuma ya haka kinshigo kamar wanda aka jefoki.....

Girgiza kai Zaliha tayi aranta tana "lallema matarnan batason meyake faruwa ba shiyasa",same tambaya Magajiya takuyimata yayinda Zaliha tace"Mama yan jaridu da yan gidan talabijin sunzo jin tarihi rayuwar Almustapha wanda inada tabbacin ze basu tunda yayarda zaiyi hira dasudi"......
Magajiya seda taji kirjinta yabuga lokaci guda amma seta daure tasaki fake smile"Toya fada musu Mana wata tsiyarce", zare idanu Zaliha tayi"kedin fa Mama,what if yafadi abubuwan dakikayi ah baya?".......
In an I don't care manner Magajiya tace"koya fada ba lallai ayarda dashiba,bashida concrete evidences so kosu hukuman basuda hujjan kamani,nasan dai bazai wuce yafada musu ho horrific his life was and he will not include me ma kwata kwata shimutum ne da yakeda wani irin Hali anyi mishi abuma ba lallai yafada ba sabida girman Kai"....
Wani irin harara Zaliha takai ma Magajiya Wanda itakanta batasan lokacinda tayiba sannan tace"girman Kai fa kikace Mama?"...
gyada mata Magajiya tayi,cikeda takaici Zaliha tace"kinmanta abunda yayimi dazune mama,kokin manta abubuwa dayayitayi two months back, you've to agree that he has changed,that witch had changed him so kada kima fara wannan tunanin it's better we find a time a way out muje musan me zasuyi"......
Murmushi Magajiya tayi sannan tace"kinada Dora makanki abunda baikai yakawo ba Daughter,zauna"....
Zama Zaliha tayi badan ranta yaso ba yayinda Magajiya tadubi Laure tace"ke kunna min TV"......
Tashi tayi ta kunna sannan takama channel din kafin Magajiya tadubi Zaliha daketa hada zufa itakadai tace"ki kallo program din,I assure you it's not something serious"......
Gyada Kai kawae Zaliha tayi batareda hankalinta yakwanta ba still......

Acan bangaren su Almustapha kuwa da akasamu aka bude masa hanya karasawa cikin fadan yayi kafin yazauna gaban Mai Martaba tareda sake gaidashi, cikeda Jin dadi Mai Martaban ya ansa yayinda yace masa kakarasa sunacikin parlourn can Son, they've been waiting for you,kashiga kasame su Allah yabaku sa'a.....
Amin yace kafin yawuce parlourn Dr Na'im yafara hangowa zaune kan seater yayinda wani young Man wanda zasuyi sa'anni kezaune gefenshi..........

Kallo daya nayima Dr Na'im nagane cewa shi typical Fulani ne donkuwa Masha Allah shima ba baya ba gurin kyau ga shi hutu da kwanciyar hankali da alama sunzauna ah jikinshi.......
Ganin Almustaphan dayayine yasashi tasowa daga inda yake yazo ya rungume shi yana"Buddy wannan jan aji haka kodai amaryace taboye mana Kai"....
Murmushi kawai Almustapha yayi kafin yace"yakake?".....

Lafiya Lau, they've been waiting for you Dr Na'im din yayi magana yana nuna side din da Saifullah kezaune murmushi Saifullah yasakarma Almustapha din yayinda yataso yazo yamika masa hannun sukayi musabaha yana bawa Almustapha din girmamawa sannan yace inbabu damuwa munason mufara program din yanzu wanda ni dakaina dakuma Kai Mai girma Yarima zamu kasance acikin wannan shiri........

Gyada masa kai Almustapha yayi kafin yace "okay then"....
Da hannu Saifullah yanuna ma Almustapha kujerar datasha ado sosai cikeda ladabi yayinda shima yaje yazauna kan daya kujerar masu daukan abun kuma suna daga can gefe....
introduction Saifullah yafara yi tahanyar yima mutane sallama tareda fadin sunanshi sannan yace....
"To masu kallon mu yau munzo muku da shirin dakuka Jima kuna bida hakanan munkawo muku babban gwarzonku dakuka jima kunason ji daga gareshi wato Yarima Almustapha"..........

Mika ma Almustapha microphone din yayi sannan yace
"ko zamu iya sanin cikakken sunanka?"......
Cikin cool voice Almustapha yace"Almustapha Abdulrahman Sulaiman".....
Murmushi Saifullah yayi sannan yace "To kundai ji daga gwarzon naku nasan kuma tabbatar kunyarda cewa shidinne bawani ba", yakarashe maganar yana dan dariya murmushi Almustapha yayi yayinda Saifullah yace"ah to kada suce fake Almustapha nakawo musu sabida dayawa basusanka ba labarinka sukje"....
Wannan Karan ba Saifullah kadaiba har Almustapha seda yadara kaman yanda mutane da dama dake kallon program din suka dara suma from their different homes and locations ciki kuwa harda yan gidansu Asma'u gabadaya sun zauna gaban Tv suna kallon hirar da akeyi da Almustapha hakanan su Asiya da Hajja ma ba abarsu bayaba don Aliyu dakanshi yakira yafadama Asiya yace su kalla sannan tasa Hajja ma tagani ko Allah zaisa tacire kahon tsanar da takeyimata tahanyar ganin mijin Asma'u mutumin kirki ne.... ........
Dan tsagaita dariyar sukayi sannan Saifullah yaca...
"Yarima Almustapha kozaka iya bamu takai taccen tarihin rayuwar ka?"........

Gyadama Saifullah kai yayi sannan yasaka microphone din ah bakinshi amma seya kasa magana kaman ance yadaga idanunshi sesuka sauka cikin nata datake tsaye can bakin kofa gefen Hajiya Muniba gakuma su Afiya da Amira ah gefe wanda sune suka janyota tabiyo badon ranta yaso ba samun guri sukayi suka zauna yayinda ita still tana tsaye sakamakon kallon da taga Almustapha nayi mata murmushi tasakar mai tareda dan bashi courage tahanyar daga mishi hannu,dauke kanshi yayi da gare ya hakanan yafi minti uku kafin yafara magana in a very calm voice"kaman yanda nafada muku sunana Almustapha Abdulrahman Sulaiman wnda mahaifina sananne ne wato Sarkin Zaria Mai Martaba sarki Abdulrahman Sulaiman, shekaruna 31 nayi primary and secondary school dina cikin masarautar nan yayinda nayi degree dina ah babban jami'ar Ahmadu Bello University Zaria,nakaranci Medicine and to tell you the truth through the struggles I encountered alot of difficulties and hardships but, alhamdulillah with Allah everything is possible because I'm now a well pronounced medical Doctor"............

Post a Comment for "GAIDAN SARAUTA CHAPTER 10"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...