Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

EL-MUSTAPHA CHAPTER 8

EL-MUSTAPHA CHAPTER 8

- - Post a Comment
EL-MUSTAPHA

CHAPTER 8

Sallama take ba kakkautawa kamar wace aka ma dole. +

Abba na xaune a falo yana jinta, muryarta kawai da yaji sai da gabansa na fadi, baisan me ya dawo da ita gidan ba.

Yayi shiru yana cigaba da Jan carbinsa batare da ya kula ta ba,

Ta gaji da sallamar taji baa amsa ba taja dogon tsaki, sai ta fada falon kai tsaye tana qunquni, taxo gidan ubanta ana ji tana sallama an kyale ta saboda ana baqin cikin dawowar ta. 2

Tana ganin abba ta xube qasa, sai gaidashi take tana washe baki,

Kallo daya yayi mata ya dauke kansa, baiyi mamakin yanda yaga ta dawo ba yama so tafi hakan lalacewa yanda xata gane duniya ba komai bace, daga yanayinta ya gane Sam har yanxu batasan rayuwa ba, bata horu ba idan har wannan shegen bakin nata bai mutu ba. 1

Nayi sallama baa amsa ba, naxo ina gaisuwa an kyaleni, Allah yasa dai bayan rabuwar mu abba ba matsala ya samu a kunnuwan sa ba, ta matsa kadan tana kallonsa hade da yi masa nuni da hannu irin na kurame tana tambayar yana jin ta. 3

Abinda yaxo ransa uwani ta sami tabin hankali, no wander ya ganta hakan, sai yaji wani iri a jikinsa ko ba komai alhakinta na kansu.

Ke....! Ya daka mata tsawa ganin tana qoqarin tabashi da wannan dattin jikinta,

'au ashe Ma yana ji, ta xauna tana tunxure baki, mutum wata da watanni baya gida kuma ya dawo baxaa tarbesa ba,

Tashi ki bar min gidana cewar abba,

Ta dago tana kallonsa da sauri baki a bude,

'Abba ina kake so naje idan na bar gidan,

'inda kika fito, ko kin manta na gayamaki ba ni ba ke, kije ki xauna da rayuwar da kika xabarwa kanki.

Ta tsuke baki hade da bata fuska, ta gyara xama tana fadi, abba ba tonon asiri ba gidan nan fa nawa ne, gado nane, saboda ni kadai kuka haifa, nayi haquri na barku ku xauna ne tunda kuna raye amma ko mutuwa kuka yi ai gida nane, gado na to meyasa kake korata cikin sa. 1

Kibari idan na mutu kixo kici gadon ya fada a fusacce yana tashi daga inda yake xaune, tana ganin haka ta tashi da sauri tana kallonsa jikinta na rawa,

Wai abba da gaske kake yi korata kake, ina xanje, wallahi nayi nadama kowa yasan na shiryu, dan Allah kayi haquri ka tausayamin ka barni, ta soma kiran hajiya..... Hajiya... Kixo ga auta ta dawo abba yana Kore maki ita, tana leqen hanyar dakin hajiya.

Get out please, butulu macuciya, duniya yanxu kika fara gani tukunna Ma baki ga komai ba, haqqin jiddah kadai ya isheki.

'Abba wallahi *NAYI NADAMA* baxan qara cutar da kowa ba, jamcy ce ta sakani abba dan Allah kayi haquri ta soma kuka iya gaskiyarta tana bashi haquri, fafur ya murje ido akan lallai sai ta bar gidan.

Ganin da gaske yake kuma yana gab da dukan ta ya saka ta juya tana kuka ta fito gidan, bakin gate ta rakube ta xauna tana rera kuka.

Nida gidana a hana min xama a ciki, wai mai gadi ma ya fini gata a gidan, ita hajiya saboda baqin ciki kada na xauna ko ta fito ta bashi haquri ya barni amma tana jina ta kyaleni, ta cigaba da kukan iya gaskiyarta.

Kowa ma baya sona duk inda naje sai an cutar dani, yaran unguwa sai kallona suke, duk kyawuna da gayuna sun tafi a iska, na dawo kamar wata shegia a gari, wani maraya ma yafini gata a yanxu saboda kawai na cutar da jiddah, Allah ya ga xuciyata yanxu bani da wani mugun nufi a tare dani na shiryu baxan qara cutar da kowa ba ko daukar xugar qawa ama meyasa kowa baya yarda dani ne, ya suke so nayi da rayuwata duk gata na amma dubi yanda na koma a yau kuma anqi a tausayamin, ina suke son naje, ba inda xanje na sake fadawa halaka anan xan cigaba da xama har su yafe min, ta kwanta gurin tana kuka.

STORY CONTINUES BELOW


Barci mai nauyi ya dauke ta a gurin,

Duk wanda yabi gurin sai ya kalle ta babu mai tunani cewa uwani ce wannan sai dai kallon mahaukaciya ce, yadda aka san uwani da tsabta, ga gayu ko banxa tana da kyankyami akan mutane amma ita ce yau a hakan.

Kiran sallar magrib ya fito da abba da saurin sa xaije masallaci, kicibis yayi karo da ita kwance a gurin, girgixa kansa kawai yayi ya tafi abinsa.

Iskan hadari ya tada ta daga barcin da take, ta qara takurewa guri daya,

'Wannan rayuwar bata min adalci ba idan gaskiya ake bi ai wahalar da nayi jiddah batayi irin sa ba kawai dai dan ta rasa qafafun ne amma ni dube ni kamar yar tasha har wadanda suka haifeni basa sona.

Ba inda xanje anan xan xauna saboda duk duniyar nan ba inda yafi min gidan ubana, koda ruwan nan da xai sauko xai kasheni baxan bar qofar gidannan ba.

'Abba bai dawo gidan ba sai bayan isha, tana ganinsa ta tashi da sauri tana kallonsa.

'Abba dan Allah kayi haquri na tuba na bi Allah, ka yafe min kabarni na shigo naji dadin da kowace d'iya keji a gidan ubanta dan Allah abba kayi haquri.

Bai saurare ta ba ya shige hade da rufe gate din,

Tayi shiru tana kallon sama yanda ake ta xuba walqiya, ta xauna tana dafe cikinta, yunwa take ji amma ya ake so tayi tunda ba sata xata je tayi ba ko bata.

Tana xaune a gurin ruwa masu qarfi na fara saukowa, ta rakube guri daya da alama harda sanyi tana ji sai sharar kwallah take, wata wahalar ni najawa kaina ko yanxu na gane kuskure na, da ynxu ina can tare da anti jiddah ina cin dadi na kwanta cikin AC Allah sai ya sakamin baxan taba yafewa jamcy ba.

Ance d'a da mahaifi sai Allah, ya kasa samun nutsuwa sai tunanin uwani yake da halin da take ciki,

Abinda tayi kuskure ne ta riga ta aikata idan yayi laakari da shekarun ta kuma qaddara tana kan kowa, musamman idan yayi dubi da kowacece uwani kamar hankali bai ishe ta ba.

Tana aikata komai nata batare da tunani ko neman shawara ba kawai abinda yaxo ranta shi xatayi ba ruwanta ko xai baci ko xai gyaru burinta kawai ta biya buqatar ta.

Idan ya Kora ta tabi duniyar alhakinta na kansa kuma yana da kamashon lalacewar ta saboda macece kuma qarama mai rauni, ba abinda uwani ta cancanta kamar addua shiriya kuma yana qara roqon Allah ya shiryeta ya gyara ta yasa tuban da tayi har acikin xuciyar tane.

Umbrella ya dauko ya fito sosai ake ruwa, yana bude gate din ya ganta tsugunne a gurin ta rakube sai makyarkyata sanyi take,

Jin alamar bude gate din ya saka ta dagowa tunanin ta mai gadin ne ke leqenta tayi masa rashin mutunci, suna hada ido ta tashi da sauri,

Tausayin ta yaji, yar'su kwaya dal a duniya haka Allah ya rubuto da tata rayuwar, Sam uwani bata da nutsuwa, baiyi magana ba ya juya tana ganin haka ta shiga gidan harda rufe gate din,

Bayansa tabi tana fadin, 
'Ashe dai abba kana sona, ai nayi tunanin xaka barni acan ne ruwan ya kashe ni, irin kune ake gani a aljanna ayi mamaki baa san tausayi ne da ku ba. 11

Kyaleta yayi baiyi magana ba, yana ganin sai an kai uwani asibiti an duba masa kwakwalwar ta. 2

Ta tsaya tana matsar kayanta har lokacin jikinta bai daina rawar sanyi ba,

Ta shiga falon tana kallonsa,

'Abba yanxu dai ka yafe min saura hajiya da anti jiddah, shi el'mustapha baxan roqe sa ba saboda yaci amanata ya kulleni a prison kuma ya harbeni a qafa banda ibrahim da yanxu ta fara wari ancire.

STORY CONTINUES BELOW


Shiru baice komai ba, sai kallonta yake cikin jimami,

Wayarsa ta dauka tana fadin abba bari nayi selfie da wannan kayan da datti saboda daga yau baxan qara xama acikin su ba, hassalima kayan meenah parrot xan baiwa su ko khadija candy. 2

Yana kallo ta fara daukar pic harda bashi wai ya dauke ta....

Tana gamawa dakinta ta nufa, ta jima sosai a ciki ta fito sanye da kayan barci bayan tayi wanka,

Yana xaune yana kallon news,

'Abba ni inajin yunwa kamar xan mutu, hanjina sai xafi suke suna bugun juna tun daxu.

Yace ai kinsan hanyar kitchen bana tunanin kin manta,

Har xata je sai kuma ta dawo tana kallonsa,

Wai ina hajiya ne abba hala dai bata ji dadin dawowa ta ba shiyasa Ma ta kasa fitowa?

Hajiya taje Germany,

Uwani ta xube qasa cikin firgici,

Germany abba, waye ya kaita?

El'mustapha ya bata amsa yana kallonta, sun je ayiwa jiddah aiki a qafar da kika nakasa.

Ta hadiye wasu yawu, wannan ba shine damuwar taba,

Tace yanxu abba kana nufin hajiya ta shiga jirgi kenan, innalillahi amma meyasa xaa min haka, ni nafi cancanta aje dani meyasa ake min baqin ciki ne, ta soma kuka kamar ranta ana mata baqin ciki da shiga jirgi banda haka meyasa baa jira ta ba ko anje an nemo ta.

Shiru yayi yana kallonta, shi dai yasan ba wannan ne karon farko da hajiya ta shiga jirgi ba ballantana uwani ta tada hankali, sunje Makkah sunje umrah to kwadayin me hajiya xatayi wa jirgi banda fitina ta uwani da rashin kunya har tana cewa aje da ita jinyar jiddah.

Shikenan abba babu komai tunda na gyaru, ina so a maidani makaranta, Cairo ko London ko sudan.

Yace ke me xakiyi da karatu keda babu abincinki aciki kuma kwakwalwarki baxata dauki karatu ba.

'Abba ka daina tuna baya wannan duk baqin cikin shaidan ne da sharrin xuciya, tuni na hango akwai abincina a karatu, akwai arxikina a ciki, nifa abba ina ji a jikina nan gaba first lady xan xama shiyasa har islamiya nake so ka sakani ko a aji daya ne xan xauna, ina so nayi ilimi saboda ya'yana kuma xa kuyi alfahari duk inda kuka shiga ana nuna ku ana ga iyayen uwani first lady 😊.... Bai bari ta qarasa ba ya tashi ya bar falon cike da haushi. 3

Ta bisa da kallo kafin ta tabe baki, wato har yanxu baa daina mata baqin ciki ba, ina laifin ta xama first lady ai abin alfaharin su ne.

Ta tashi ta nufi kitchen tana yan surutai, cornflakes ta gani babu batun cin abinci an dade baa hadu ba,

Qaton Cup ta dauko da spoon ta shiga neman inda aka ajiye madara.

*

Kallonsa dr merah keyi yana observing din sa, halayen el'mustapha suna burgesa sosai, akwai soyayya mai tsanani tsakanin sa da jiddah ba sai an baka labari ba kaida kanka xaka gano hakan.

Ya dafe kansa da duk hannayensa biyu cikin damuwa, meya hanata farfadowa, why ya fada a hankali yana Jan numfashi.

El'mustapha ya dago yana kallonsa daga cika wata takarda da yake, ya ajiye biron yana fadin.

Thanks once again Dr Aiman Merah,

Dr merah yayi murmushi yana miqa masa hannu,

Can we be friends?
El'mustapha bai bashi hannu ba kallonsa yayi yana fadin,

Xaka iya abota da d'an sanda ba jinin Mulki ko Sarauta ba?

Of course ya fada yana kallonsa, I have alot of friends like you,

Murmushi el'mustapha yayi kafin ya bashi hannu,

El'mustapha ya juya ya fita yana fadin ina jiran ka insha Allah yau xamu koma qasar mu da gawar jiddah.

Jiddah na kwance har lokacin idanunta a lumshe, jin alamar bude qofar ya sakata bude idanuwanta a hankali carab suka hada ido,

Kusan rudewa ko ince gigicewa yayi, ya rasa ina xai nufa ciki ko waje, jiddah ce ko dai fatalwarta ke mata gizo, shi ko fatalwarta jiddah ce yana so xai iya xama da ita, koda babu jiddah ya xamto ruhinta yana tare dashi,

Da sassarfa ya isa ciki har lokacin bai dauke idanunsa akan taba, sai kallo jiddah ke binsa da shi na mamaki.

Hannu yasa ya taba ta baiyi magana ba, ya qara riqo hannunta ya kai bakinsa ya ciza don son gasgasta jiddah din ce ko fatalwa.

'Wash Allah ta fada a hankali tana qoqarin xame hannun ta,

Ya rasa me xaiyi saboda tsananin farin ciki, sai kawai ya sami kansa da yin sujjada a gurin yana qara godewa Allah kafin ya taso ya rungumeta tsam a jikinsa yana sauke numfashi da sauri da sauri, 2

Jiddah is back, jiddana bata mutu ba I know, ya fara sumbatarta ta ko ina cikin rudewa kamar wanda xai maida ta ciki.

Shiru tayi tana sauraren wannan sabon al'amari daga el'mustapha, tasa hannu da kyar ta riqo fuskarsa tana kallonsa dai dai lokacin dr merah ya shigo tare da su yusrah da hajiya da nurses a bayansa.

Cak suka tsaya suna kallon ikon Allah cikin tsananin mamaki, jiddah ta janye jikinta tana qoqarin kwanciya el'mustapha sai qara rungumarta yake,

Dr merah da mutanen sa suka koma baya, anty yusrah sai washe baki take cikin tsananin farin ciki ita da su hajiya.

Qafata ciwo take el'mustapha ka barni haka,

Ya bude idanunsa a hankali yana kallon qafar, kafin ya dubeta,

Ina son ki jiddah cikin kowane hali, ko da qafar ko babu, ki rayu tare dani jiddana.

Murmushi tayi tana fadin, nima ina son el'mustapha cikin ko wane hali, son da ban taba yiwa kowa ne mutum a duniya ba bayan ummata.

Ya gyara xamansa, hannunsa na cikin nata  sai murmushi yake kamar wanda akayi wa albishir da gidan aljanna,

'Me na haifa el'mustapha?

'Har kin manta kenan, bayan kin bar yarinya sai kuka take tana son jin dumin mahaifiyarta.

'karbo min ita na ganta....

'ba yanxu ba kiji dani tukunna, nafi ta buqatar ki jiddah.

Taja hancinsa tana murmushi,

Yanda kace haka xaa yi mijin jiddah,

Yace yauwa jiddatulmusty, sai kuma yayi murmushi ya tashi yana fadin bari na karbota jiddah nasan kinfi buqatar ta dani a yanxu.

Ta bisa da kallo tana murmushi....
Bayan kwana biyu, jiddah ta warware sosai sai dai rashin kuxarin jiki, 
+

'Anty ikram Ma sunxo tare da wani kawun jiddah.

Sosai dr merah ke kula da jiddah musamman qafarta, sun xama friends da el'mustapha ko da yaushe suna tare a office, har yake baiwa el'mustapha labarin sa da Afiya. 

Hajiya bani ruwan tea na sha, cewar jiddah tana kallon ta,

Hajiya ta tashi goye da jaririyar ta hada mata bayan ta xauna kusa da ita,

Magana xamu yi jiddah ta fahimta, bana so naga abinda xai cutar dake ko kadan.

Jiddah ta tattara hankalinta da nutsuwar ta tana kallonta,

Hajiya tace meke tsakanin wannan yar aikin taki da mijinki? 1

Jiddah ta qara kallonta cikin faduwar gaba tana bude idanuwanta, ta ajiye Cup din tea tana fadin, me kika gani hajiya?

Tambayar ki nake yi kibani amsa,

Cikin rawar murya  jiddah tace nima ban sani ba hajiya,

Ba ina gayamaki bane dan ki tada hankali ki, amma kisani wannan karon ko mutuwa xakiyi baxan taba yarda ki aurawa wata mijinki ba, tun da na lura ke Sam baki san ciwon kanki ba sai haquri, ina ji ranar da xaa shiga dake aiki har kina bata amanar ya'yan ki da mijinki, meke damun kine jiddah. 1

Jiddah tace hajiya banan tana da kirki bana xaton xata cutar dani ko wani nawa shine dalilina na bata amanar yarana, amma maganar el'mustapha cikin xafin ciwo ne ban san na nata amanar sa ba kuma ba wai ina nufin ta so shi ba hajiya. 1

Koma dai menene na riga na gano banan tana son mijinki, kuma kinji na gayamaki wannan karon baki isa ba, kuka taso da uwani tun kuna yara ta cutar dake ballantana wata bare,

Jiddah taja numfashi a ranta tana cewa hajiya baxata gane ba wani bare yafi dan uwa kuma ba duka aka taru aka xama daya ba.

Amma hajiya meyasa kika ce tana son el'mustapha, ni na dauka shine kadai ke son ta.

Hajiya ta xare ido cikin mamaki, tace kina nufin wai el'mustapha yana son banan? Ya akayi kika yi wannan saken jiddah, taya xaki reni yarinya da hannunki ta aure maki miji, wai ke meke damun ki ne, wace irin mutum ce ke, ban taba sanin wata mace mai hali irin naki ba jiddah, kin fiye tausayi da sanyin xuciya wanda shine ke cutar dake kuma shine ya kawo ki matsayin da kike a yanxu. 2

Jiddah ta soma kuka tana fadin, ba laifina bane hajiya, bansan yaushe ya fara son ta ba, nagano hakan bayan dawowa ta daga batan da nayi kuma el'mustapha ya rantse min babu soyayyarta a xuciyarsa sai dai ban sani ba akan ita banan. 2

Hajiya tace to bari kiji ban san komai akan gidan ki ba amma a waya da naji banan nayi na fahimci komai, kin bata auren qanin aminiyar ki, tana waya naji tana bashi haquri akwai wanda take so tuntuni kuma yanxu tana da tabbacin xata same shi amma ya rufa mata asiri kada ya gayamaki dan bata son fushin ki ko kadan. 2

Bansan me yace da ita ba naji tana roqonsa da magiya cewa xai iya haqura da ita har ya sami wacce ta fita.

Ban taba kawo el'mustapha take so ba sai a jiya da dare, ta kwana kiran el'mustapha a barcinta wataqila ma yusrah ta ji ta ban sani ba, yau da safe ban mata mgn ba amma daga irin kallon da take wa el'mustapha daban ne da wanda take mana, na lura duk inda yayi idanunta na kansa bai Ma san tana yi ba.

STORY CONTINUES BELOW


Jiddah ta dafe kanta, innalillahi ta fada a hankali, sai ga hawaye, ta dubi hajiya cikin kuka,

Meyasa suke son el'mustapha, meyasa suke son mijina, menayi masu suke son raba ni dashi? 1

Taya xanyi na sani jiddah, bansan mu'amalar ki dasu da shi a gida ba, uwani bata bani mamaki ba kamar banan saboda uwani tun kafin ki auri el'mustapha ta furta tana son sa, amma banan taya xata so mijinki bayan kece kika riqeta kuma yar aikin ki, ya akayi ta sami kusanci haka da el'mustapha, kina sakaci da gidanki da mijinki jiddah, samun miji a wannan xamanin kamar el'mustapha sai an tona, bako wane namiji xai iya maki halacci irin wanda el'mustapha yayi maki ba, ki so shi da xuciya daya kuma ki rungumeshi da hannu biyu ban isa na hana mashi qara aure ba amma kam ba banan ba na gayamaki gsky tun yanxu, idan uwani ta maki ciwon qarya ta ci galaba akan ki wannan karon ko ciwon mutuwa banan xatayi a gabanki baxata taba auren el'mustapha ba.

Ta tashi a fusacce xata fice, jiddah tayi saurin tsaidata

Hajiya laifina kike gani, Wlhy ko a mafarki baxan bar el'mustapha ya auri banan ba ballantana a xahiri, idan banan tace tana son el'mustapha taci amanar yarda da ita da nayi, na bata amanar ya'ya na bawai ina nufin ta auri el'mustapha ba, ko da nace mata el'mustapha ko Islam Allah kadai yasan mijin auren ta saboda a lokacin inajin kamar baxan rayu ba amma ban taba kawo banan xata so mijina ba, hajiya ya xanyi ba banan ba ni bana son kowace mace ta kusanci el'mustapha koda da murmushi ne.

Hajiya tace kisha tea din tukunna har ki sami lafia xamuyi maganar,

'Na kasa sha hajiya, hankalina ya tashi yanxu ina banan din da el'mustapha..... Bata rufe bakinta ba el'mustapha ya shigo, bayansa banan ce da anty ikram.

Ta xare idanu tana kallonsu cikin faduwar gaba, el'mustapha kuwa kallon hajiya yayi yana kallon jiddah cikin mamakin kukan me jiddah keyi.

Kafin yayi magana anti ikram ta xauna tana fadin,

Jiddah xuwa gobe da safe xamu koma tare da yusrah da yayan ki, tun da jiki alhamdulillah kin sami sauqi sai fatan Allah ya tada ki lfy.

Abinda ya fito bakin jiddah ya bawa kowa mamaki ba ma kamar banan.

Tace anti ikram idan xaki koma kuje da banan, hajiya xata kula dani.

'Anty jiddah me..... Wani kallo da jiddah tayi mata ya saka ta rufe bakin ta ba shiri abinda bata taba yi mata ba, kada dai jiddah ta gano tana son mijinta da ta shiga uku. 1

Hajiya tace aa jiddah baxaa yi haka ba, kibar banan ta.... ta katse ta,

Banan xatabi su anty ikram Nigeria, umarni ne ba shawara ba.

El'mustapha na tsaye baice komai ba sai kallon jiddah yake yanda ta sauya lokaci daya,

'Anty ikram tace banan tayi maki wani laifine jiddah? Duk suka xuba mata ido,

Tace aa ta koma saboda su twins, bama haka ba ta dai koma hajiya is ok.

Banan taji kamar ta rusa ihu a gurin, har wani xufa take, meyasa jiddah xatayi mata haka na nisanta ta da el'mustapha, karo na farko da ta soma jin haushin jiddah a xuciyarta tun xaman su. 11

Hajiya bata qara magana ba ta juya ta fita, ikram Ma fita tayi tana amsa waya,

Banan ta dubi el'mustapha dai dai lokacin shima ya dago yana kallonta,  jiddah na kallonsu, bugun xuciyarta ya tsananta,

El'mustapha ya xauna baiyi magana ba amma yana son sanin dalilin jiddah na cewa banan ta koma bayan tana qoqari sosai akan ta.

'Anty jiddah idan laifi nayi d...... ta katse ta a fusacce,

STORY CONTINUES BELOW


Get out pls kuma kisani ko kinqi ko kin so Islam ne mijinki idan har baxaki aure shi kafin nadawo kibarmin gidana.

Banan ta soma kuka a rikice, ni anty jiddah yaushe nace bana son sa wlhy qarya yake min idan shine ya gayamaki hakan, dan Allah kiyi haquri kada ki maidani, ina son xama dake bani da xabi sai naki ki yarda dani. 1

Jiddah tace na riga na gama magana kije kawai, idan kina ganin auren ki da Islam na cutar dake ne Allah ya na gani, kuma wanda kike so a yanxu baxaki taba samun sa ba gwanda ki rungumi Islam shine kyautar da Allah yayi maki ko banxa Islam ba ajinki bane kima godewa Allah.

Banan bata qara magana ba, amma kalaman jiddah na nuni da kamar ta gano tana son El'mustapha, idan kuwa hakane dole ta nisanta kanta da jiddah kamar yanda ta buqata harta sauko, ta fita da sauri tana kuka.

Shikam el'mustapha na xaune baice komai ba amma ya rasa wannan xafin da jiddah ta dauka akan banan, yayi shiru, 1

Dole xakayi shiru ka shiga damuwa saboda na Kore abinda kake so, na riga na gama fahimtar ku, kuna munafuntata a bayan idona..... Shut up jiddah, ya katse ta cikin tsawa,

Ok... Ok saboda wannan dalilin you are sending banan away from you right? Duk qoqarin yarinyar nan akan ki, meyasa kike tunanin abinda baxai taba yiwuwa ba, idan saboda wannan ne banan baxata bar garin nan ba, you are talking rubbish babu wata soyayya tsakanina da yarinyar nan.

Ta tsura masa ido cikin mamaki baki a sake,

Tace yanxu na gane hasashena ya xama gsky, tabbas ka nuna min kana son banan, ka damu da banan, idan hakane baka min adalci ba el'mustapha..... Sai ta fashe da kuka,

Ya tsura mata ido cikin mamaki ga wani haushi da yake ji a xuciyarsa, yana ji tuntuni sun gama magana da ita akan babu soyayya tsakanin sa da banan amma me ya dawo da maganar? Dan ya qara kufular da ita yace,

Eh naji, koma menene haka ne, kuma aure kece kika buda min hanyar yin sa, banan din Ma amanata kika bata so banga abinda xai saka ki tada hankalin ki ba, idan Allah ya nufa xan aure ta auren ta xanyi..... 2

Wallahi baka isa ba, ta fada tana kallonsa da jajjayen idanuwanta, kuma banan sai ta bar garin nan gobe ko ni na barshi, sai ku xauna tare.

Oho dai koma menene ke kika sani, ya tabe bakin sa alamar ko a jikinsa,

Ka fita bana son ganin ka el'mustapha, ashe qaryar so kake min, you can't be with me a duk yanayin da nake as you say, kana tunanin baxan qara tashi bane kake son qara aure, auren Ma da banan,

Fassarar da tayi mashi baiji dadi ba ko kadan, xai yi magana ta katse sa, 1

Karkace komai ka fita please, dan Allah ka tafi ta fada tana kuka...

Duk abinnan da suke hajiya ta shigo dakin tana ji, ranta ya baci ta hau jiddah da fada sosai,

El'mustapha bai qara magana ba amma yayi fushi sosai har sai yaushe jiddah xata gane ita kadai ce a xuciyarsa babu wata, shi feelings din da Ma yake ji akan banan before yanxu duk ya daina ji tun lokacin da yaji an bada ta ga Islam, banda kallon qanwa babu abinda yake wa banan yanxu. 4

Hajiya tace ashe baki da wayo jiddah ban sani ba, ban gaya maki ba saboda ki bata da mijinki ko ki kori banan illah ki dauki mataki mai sauqi akan ta da mijinki.

Waya ce maki haka ake yi?

Wallahi hajiya banan tana son el'mustapha, naga kallon da take mashi yanxu a gabana, kina ji fa abinda el'mustapha ke fadi kamar shima din fa yana son ta, da wannan baqin cikin gwanda na mutu hajiya.

Tace subhanallah... Kar na qara jin wannan mgnr a bakin ki, indai banan ce xata koma Nigeria amma ki bawa el'mustapha haquri ransa ya baci sosai kuma Sam baki kyau ta ba, bai kamata kifito fili ki nuna kinsan komai akan su ba, kuma ni bana jin ta el'mustapha ko yana son banan ita kadai ke haukanta.

Shiru kawai jiddah tayi batayi magana ba ama xuciyarta sai xafi take yi.

*

K'eeeeeeeeeeeey kake ji uwani ta janyo qatuwar jaka ta fito falon cikin shirinta sai taunar cingam take a hankali.

'Abba naxo muyi ban kwana ni xan bar garin,

Ya dube ta ya dubi jakar yana fadin xuwa ina haka kuma uwani?

Kudin jirgi xaka bani nima xanje Germany nayi jinya daga nan xan roqi anti jiddah gafara,

Yayi shiru yana kallonta kafin yace,

Waya gayamaki shiga jirgi daya yake da shiga motar kasuwa, me kikayi na fita waje, tukunna Ma idan kinje Germany ta ina xaki same su.

Tambaya xanyi abba, duk wanda xan Ma misalin hajiya da El'mustapha tsab xai gane su, ina ji acan ai basu da yawa kamar mu nan ko abba,

Da wannan jakar xaki je kenan, ta gyada kai tana kallonsa,

Yace tor shikenan Allah ya kaiki lfy, ina gaida su.

Kudin jirgin fa?

Yace banda su, ta saki baki tana kallonsa,

Haba abba wallahi kana da su, kowa yasan akwai su sai idan baqin ciki xaa min ga wannan tafiyar kada na shiga jirgi, amma qiri qiri ace ba kudi bayan nasan akwai. 2

Baiyi magana ba, ta xauna dirshan gurin tana miqe qafafu bayan ta xare takalmin qafafunta,

'Abba dan Allah ka kaini Germany, ka kaini na shiga jirgi dan Allah abba ba danni ba.

Yace naji idan xanje duba ta xanje dake,

Ta washe baki, Allah ya sada mu aljanna abba, shiyasa nidai ina sonka saboda a rayuwarka baka da baqin ciki kuma kana sona, nagode abba.

Tashi kije ki maida jakar kixo xamu fita, ki sauya wannan gyalen ki saka hijab din da ya sauko maki a gwiwa.

Abbana Abbana, Abbana Abbana, fita xamuyi kenan, na rasa Ma me xance maka sai nayi tunani abba saboda kai din rayuwarka mai kyau ce baka da baqin ciki wlhy, ynxu da hajiya fa nan taji xamu fita haushi xataji ta hana dan kawai kar ka siyamin ice cream, amma abba harda shopping xamuyi ko. 1

Yace eh,

Ta tashi tana murna ta fita, shikam so yake ya kai uwani a duba masa kwakwalwarta yana son sanin matakin da take xaune akai, tun tana qarama ya kamata suyi wanna binciken tunanin su yarinta da quruciya ce amma gashi har ta girma bata daina ba.Bata jima da shiga ba ta fito sanye da hijab din ta, abba ya tashi suka fita sai kirari take masa tana take masa baya. +

Acikin mota ne suna tafiya take bashi labarin qawayenta na prison, ai abba xaka fitar da ladidi ko, ina tausayinta sosai amma kaga anty aj da runkes sunci amanata.

Kuma fa abba ita ladidi tana sona tana kareni idan xasu dake ni ita a rayuwarta bata da baqin ciki shiyasa nake son taimaka mata na roqi mijin anti jiddah ya fiddata.

Kuma abba naje na hadu da wata hajiya Mariya ita wannan yar iska ce har dani tace muyi iskanci fa (abba ya kalleta kafin ya maida kallonsa ga tuqin da yake)

Kunyi iskancin kenan..

Kai haba ai ina da wayo kuma ni ba yar iska bace da naqi amincewa ne ta fara axabtar dani aikin gidan duka nike mata harda cewa ina yarda xata siya min mota ta kaini waje nayi karatu, shiyasa Ma ni abba kaji nace ka kaini waje nayi karatu na bata mamaki dan tasan Abbana mai kirki ne kuma shi a rayuwarshi bashi da baqin ciki, ko abba? ya gyada kansa baiyi magana ba,

Ta cigaba da bashi labari har suka iso asibitin.

Kai tsaye yayiwa likitan bayanin halin da uwani take ciki aka shiga a dubata.

Sun dade asibitin sosai kafi result din ta ya fito,

Likitan ya dubi abba yana masa bayani, abinda nake tunani ba shi bane, nayi tunanin ko congenital disorder wanda ake haihuwar mutum da shi (presence since birth) kamar hydrocephalus water (fluid) on the brain, ko mutum yaji sauqi bayan yi masa aiki idan bai cigaba da shan magani ba xai iya xama wani psy.

Sai na gane lalurar ta bayan haihuwa ne, she has traumatic problem, (an emotional wound leading to psychological injury) me yiwuwa kun taba accident ta bugu da kan, baku dauki serious action akan abin ba har girman ta a yanxu. 6

'Abba yayi shiru yana kallonsa kafin yace, bamu taba accident ba, sai dai ta taba faduwa tana koyon tafiya a saman bene baxan manta ba, kuma mun kawo ta asibiti suka nuna mana ba komai a lokacin,

Sai bayan ta fara girma ta fara magana take wasu abubuwa masu ban mamaki, xata gayawa babba maganar da duk ta fito bakinta babu ruwanta kuma idan kashe ta xakayi bakin baxai taba shiru ba har sai ta fada, a lokacin sai muka dauka kurciya ce da yarinta muka kyaleta saboda muna son ta bamu da wata 'ya bayan ita, bayan girmanta ne muka fahimci cewa abin ya qaru duk abinda take so kai tsaye xata fada kuma bata boye abinda ke xuciyarta, daga nan ne muka fara tunanin sakacin mu ne da tun muna qarama muka barta take yanda take so har ta lalace haka?

Likitan yace aa ba daga gareku bane laifin ku daya na rashin bincike a kanta tun tana qarama sai a ynxu wannan lokacin da abin ya dadi sosai a kanta, baka observing nata sometimes xaka ganta kamar normal tana abubuwa kamar na masu hankali wani sa'in kuma sai abin ya rikice, ynxu ma qarin abin yayi yawa ta shiga damuwa ne a baya, sannan mai irin wannan cutar ta ta, baa masu fada dan su gyara sam, rarrashi da ban baki cikin tausayi shi xai saka sannu sannu ta daina abin da take, idan tayi ba dai dai ba kada ku mata fada shi ke qara tunxurata ga maida maku magana, kuyi mata ta rarrashi yanda xata fahimta ku nuna mata bai dace ba, sannan kuriqa bata labari mai ban tausayi da shiga rai shi xai saka ta tunani in tayi ba dai dai ba.

Yanxu likita wane taimako xaka mana ina son uwani ta gyaru ta dawo cikin nutsuwar ta, ko nawa ne kudin aikin nata ka gayamin xan iya biya idan dai xata dawo normal kamar kowa.

Likitan yace ka kwantar da hankalinka, insha Allah xan qara bincike akan ciwon nata daga nan xuwa wani sati mai xuwa kadawo.

'Abba yayi godia sosai yana fitowa ya sami uwani sai kumburi take kamar xata fashe,

STORY CONTINUES BELOW


Tana ganin sa ta nufe sa,

'Abba tun daxu ka shige ka xauna ka barni anan sai kallona ake, shi wancan harda cewa yana sona ya dauka baxan koma gidan mijina ba.

Baiyi magana ba yace bani kudin da na baki riqo,

Tace lah abba ai tuni na bada su aro, 1

Aro? Ya tambayeta cike da mamaki,

Tace eh wallahi ai wani ne yaxo siyan magani anan baida kudi shine na ara masa nayi masa kwatancen gidan mu gobe xai kawo mana, iyakar gaskiyarta take magani babu damuwa a tare da ita.

Yace kin sanshi ne, 
Tace aa
Yace shikenan Allah ya bada ladan sadaka da kika min da kudin dole na yafe,

Tabi bayansa tana fadin yanxu abba saura shopping din ko,

Yace bayan kin kyautar da kudin,

Haba abba ai yace xai maida fa...

Bayan sun dawo shopping ajiye ta gida yayi ya nufi masallaci.

Tan gama ciye ciyenta ta dauki qatuwar jakar da ta shirya kayanta daxu tana fadin na lura abba baqin ciki yake min da shiga jirgin nan shiyasa yace na jira muje tare alhali ba inda xaije shi kullum yana hanyar xuwa masallaci gashi anqi a bashi ko limamin masallacin duk wannan gemun da ya ajiye a fuskarsa. 2

Nasan dubu biyar goma xasu kaini Germany tunda ance da tsada ake shiga, el'mustapha ko jiddah xasu min na dawowa.

Taja jakar ta fito, napep ta shiga ya kaita airport. 3Ga jirgi kam uwani tana gani amma an hana mata shiga, tayi fada harda xage xage wanda ya janyo da yawa mutane a gurin suna mata kallon tababba in ba haka ba taya xata xo da kudi dubu goma tace na shiga jirgine kuma wai Germany xata je kamar mai shiga mota xuwa wani gari, har fadi take tana so taga driver jirgin taji dalilin sa na yi mata baqin ciki da karban kudin ta.

Tana tsaye jirgin ya daga, gurin ta xube tana kuka sosai kamar ranta, da farko kafin ya tashi sama har da binsa tayi da gudu tana ihu bata bar wurin ba har dare.Haka ta tattara ta dawo gida, abba ya fito neman inda taje ya ganta da jaka shabe shabe da hawaye.

STORY CONTINUES BELOW


*

Dr Merah ya shigo dakin da sassafe, ward round kamar yanda yake yi kowace Safiya kafin ya isa office din shi.

Yayi mamakin samun jiddah ita kadai a dakin tunda yake xuwa ita da  el'mustapha yake samun ta ko wace Safiya kuma ai yaga el'mustapha xaune a waje me ya hanasa shigowa, tabbas akwai matsala,

duk da halin-sa-ido ba halinsa bane amma wannan dai confrontation ne like a chase game da yakeson ganin yanda xai qare, el'mustapha a waje ba walwala, jiddah a ciki cikin damuwa.

dan haka yake ganin bai kamata ya kira sa-idon nasa da sunan sa-ido ba sai dai ya kirashi curiosty wanda haline na kowane dan adam akan abinda ya bashi mamaki musamman shi da yake ganin el'mustapha yanxu abokin sa ne, jiddah kuma patient din sa ce.

Bayan ya gama duba ta, kallonta yayi yana fadin lailah ina majnun ya akayi na same ki ke kadai yau,

Murmushi kawai tayi tana kallonsa,

As a professional medical doctor a take dr.merah ya gano cewa akwai damuwa a tare da ita daga yanayin ta, yanda ya san ta da fara'a.

Kujera ya janyo ya xauna yana fuskantarta,

Akwai damuwa jiddan musty ne ko ya kuke cewa, nagano patient dita tana cikin damuwa ni kuma bana son ganin ta cikin damuwa, kullum naxo xan same ki tare da mijin ki, yau kuma meyasa?

Tayi rau rau da idanunta kafin tace ba komai, ya dan fita ne.

Aa jiddah, your eyes shows akwai matsala, idan akwai abinda xan iya taimaka maki just take me as your brother ki gayamin,

Ta bude baki da kyar tana kallonsa, aure yake so ya qara...

Aure? Dr merah ya tambaya cikin tsananin mamaki, meyasa yake son qara auren?

Tace saboda na nakasa yake son qara aure bayan ya manta dalilin sa na fada wannan halin, saboda son da ake mashi aka nemi kasheni a rabani da duniyar..... ta soma kuka sosai har ranta.

Shiru dr merah yayi amma jikinsa yayi sanyi sosai, kuma el'mustapha ya bashi mamaki, kukan jiddah na qara tayar mashi da hankali.

Yace kibar kukan jiddah, nasan el'mustapha yana matuqar son ki, bana jin saboda kin nakasa xai qara wani auren ballantana Ma baki nakasa ba jiddah, xaki tashi aikin da aka maki is successful, nan da wata daya xuwa biyu xaki fara taka qafar.

Ta dubesa idanunta jawur, yana sona ne baxai xauna dani hakan ba.... Ya katse ta,

Ni nasan el'mustapha baxai qara aure ba ki kwantar da hankalin ki, kidaina saka damuwa a xuciyarki kinga baki da lafia, idan har el'mustapha xai qara aure baxai gayamaki a wannan halin da kike ciki ba domin yafi kowa sanin condition din ki, el'mustapha yasan *Labari na* dana gidana, haka shima ya bani nashi har dalilin wannan ciwon naki amma bai taba gayamin yana son wata ko niyar aure ba.

Xai iya gaya maka komai amma baxai taba gayamaka yana cin amanata da mai aikina ba, ita yake so a yanxu kuma ita yake son aure, ka gayamin ina adalci anan, ina son da yake ikirarin yana min idan har xai iya auren yarinyar dana raina a hannuna?

Dr merah ya bata fuska alamar fushi mai tsanani a tare dashi, idan har da gaske kike abinda kika fada el'mustapha bai kyauta ba kuma baxai taba auren yarinyar da kika rena ba sai dai ya auri wata can d..... Jiddah ta katse sa,

Wata din Ma baxai aura ba, a hakan xai xauna dani ko yana so ko baya so, idan har dole sai ya auri wata ni baxan xauna dashi ba, baxan yarda na qara cutar da rayuwata ba duk da na farkon nice sanadi ni na jawa kaina.

Murmushi merah yayi ganin yanda take magana cikin seriousness, ya tashi yana fadin xan turo maki el'mustapha, baxan lamunta da wannan fushin da kuke da juna ba, kuma ina goyon bayanki karki yarda ya qara auro maki wata, idan yace xai qara aure xan gayamaki wani sirri da Afiya ke min barazana dashi a duk lokacin da na kalli wata ko nace xan qara aure koda da wasa ne.

STORY CONTINUES BELOW


Tayi murmushi cikin jin dadi tana kallonsa tana mamakin girman qasaitarsa tana mamakin yanda yake furta mgn da kyar, duk mgnr da ke fitowa bakinsa idanunsa akan wayarsa wanda idan bata manta lbrn Yarima maina ba da Sarautarsa data qaryata qasaitarsa(masu yawan tambayata labarin dr Merah kuduba littafin mulki ko sarauta a wattpad) 2

Ya dago yana kallonta, 
El'mustapha baxai qara aure ba jiddah, yanxu na xama yayanki baxan bari a qara cutar da ke kamar a baya ba, kema sai kin dage damtse wajen saurin yarda da mutum da bashi amanarki.

Tace nagode... Ya juya ya fice cikin tafiyar sa ta qasaita, yana fitowa ya hadu dasu yusrah sun shigo suka gaisa kana ya dubi el'mustapha yaja hannunsa suka nufi office din sa.

Aure kake son qarawa el'mustapha meyasa? Dr merah ya tambayesa idanunsa akan laptop kamar ba shi bane ke tambayar.

El'mustapha ya qara bata fuska, wato jiddah tana gayawa mutane aure xai qara... Jin shiru ya saka merah kallonsa,

As a friend, ban boye maka kaina ba kai kana boye min, banyi mamaki ba tunda har xaka iya cutar da innocent girl like jiddah ka munafunceta kana tare da mai aikinta, dan me ni baxaka munafurceni ba nida haduwar asibiti ce?

Murmushi ya subulcewa el'mustapha, yanxu abin ya daina bashi haushi,

Yace a tunanin ka saboda me xan qara aure saboda me xanci amanar jiddah?

Yace saboda kana ganin ta nakasa....

'Ashe bakin ku daya da jiddah cewar El'mustapha, ban sani ba ko kai ke shirya mata wannan saboda nasan halin jiddah bata da wannan xafin dana gani a tare da ita jiya.

Dr merah ya dube sa, yace eh nine ke shirya mata me xaka iya yi, idan kai mijinta ne ni kuma qanwata ce kuma patient dita baxan so naga an cutar da ita ba.

El'mustapha yayi murmushi yana fadin ba abinda xan iya yi amma komai mulkin mutum da sarauta baifi qarfin Shari'a ba kuma tsab dan sanda mai babban muqami Irina xai iya kamashi.

Dr merah yace duk wata baraxana ta dan sanda bata tsorata ni ballantana tayi tasiri a kaina inada mulkin da xan saka..... El'mustapha ya katse sa,

Aure na, matsalata, matata ba damuwar ka bane is my personal issue da bana son kowa ya saka kanshi aciki.

Ni kuma dole xan saka kaina aciki an you have to listen, labarin da kabani jiddah tana yin komai ne saboda kai da soyayyar da take Ma, kuma dalilin ka ta shiga wannan halin da take ciki, but why kake son auren mai aikin gidan ka can you imagine, har yaushe ka sake mata wannan fuskar, yaushe ka fara sonta, mace mai kyau da aji, mace mai mulki da sarauta kamar ni bata isheni kallo ba saboda ina ganin na aje wadda ta fiye min ita fiye da komai nawa, nima matata ta wahala dani na gayama, har muka haihu ban taba furta mata kalmar so ba cos a lokacin ban gane miye so ba sai bayan tafiyar ta, na gayama yanda ta wahala da yanda tayi rainon sultan da yanda family suka juyamin baya dalilinta, I told you everything about me an Afiya, wahalar da mukayi da juna baxai saka na iya cin amanarta da kowace mace ba ballantana yar aiki thought ba haramun bane amma Sam bai dace ba tun da ita ce ta raineta, ita Ma yarinyar taci amanar jiddah, ka wahala da jiddah, jiddah ta wahala da kai,

Ita Mace komai girmanta yar rarrashi ce da tarairaya, (care and concern) abinda take so kenan daga namijin da take so, wallahi jiddah tana sonka, dubi idanunta ba Komai aciki sai xallar soyayyar ka, kaima kana son jiddah ni shaida ne, but why El'mustapha?

El'mustapha yaja numfashi yana kallonsa,

Yace Wallahi bana son Banan kuma bani da niyar qara aure a xuciya ta da wata mace ballantana banan, baxan boye Ma ba before na fara jin feelings akan yarinyar tun jiddah nada lafiyarta bawai bayan ta nakasa ba, ban taba sanin jiddah tayi wa yarinyar miji ba sai bayan jiddah ta kwanta asibiti sunxo duba jiddah tare dashi.

STORY CONTINUES BELOW


A lokacin da jiddah fa gayamin banji haushi sosai ba tunda ban riga na kamu da son ta ba, kuma tun daga lokacin bana mata wani kallon bayan qanwa, ta wahala da yarana ta wahala da jiddah, tayi wa yarana riqon da ko mama ke da rayuwa a yau shi xata yi masu bayan ido na, just tell me Merah wanda ya kula da yaranka ya xauna dasu fitsarin su da kashin su xaka iya wulaqantashi? Idan har na dauki banan a matsayin qanwata saboda me baxan sakar mata fuska ba, dole sai ana soyayya ake sakin fuska, ballantana jiddah bata taba kamani da yarinyar nan ba, kawai xargi take wallahi ban taba tsayuwa da banan da sunan soyayya ba, is either akan yarana or gidana da matata, amma ban san xuciyar yarinyar ba tunda jiddah tace wai banan tana sona, ni ban san da wannan ba kuma ban taba lura ba saboda ban damu da ita ba.

'Na yarda da kai el'mustapha shiyasa na gayawa jiddah bana xaton xaka iya cin amanarta, yanxu na fahimci laifin daga ita banan din ne, tana so ta rusa maku farin ciki da xaman lafiya, idan har jiddah tayi mata miji kuma ta amsa a tana sonsa saboda me xata so mijin uwar rainonta?

Mata kenan... El'mustapha ya fada yana jan tsaki, ya lumshe idonsa cikin takaici. 

Banan kin gama hada kayan naki kuwa? Cewar yusrah tana kallon ta,

'Na gama anty ta fada a sanyaye, jikinta duk yayi sanyi jiya ko barci bata samu tayi ba saboda damuwa xata je ta daina ganin sanyin idaniyar ta. 2

A fakaice ta share hawayen fuskarta, tun bata kai wannan lokacin ba take son el'mustapha tana dawainiya dashi a xuciyarta, ta haqura dashi ta karbi Islam a matsayin mijin auren ta saboda a lokacin tana ganin el'mustapha yafi qarfinta kuma uwani baxata taba yarda a aure ta ba.

Soyayyar el'mustapha ta dawo xuciyarta lokacin da ya fara sakar mata fuska saboda tana kula da yaransa wanda hakan ya qara mata qaimi wajen kulawa dasu sosai ganin bashi da wani abu da yake so kamar su da matarsa.

Tana xaune dasu da xuciya daya bata tabajin niyar cutar dasu ba, ba laifin ta bane laifin so ne da baya tunani ko shawara sai dai kawai ka jisa a tare da kai banda haka meyasa so xai mata haka, kuma meyasa jiddah xata bata amanar el'mustapha ta kula dashi bayan tasan ba mutuwa xatayi ba😭 3

Sanda suka xo asibitin ban kwana da jiddah xasu tafi tana baiwa jaririyar ta mamma, shigowar su ya saka ta janye yarinyar hajiya ta dauke ta tana fadin,

Jiddah bata sha komai na kirki ba, wannan halin naki bana sonsa ke kice bakya iya shayarwa cikin mutane,

Jiddah batayi magana ba suka soma gaisawa da su anty ikram, da kyar ta amsa gaisuwar banan tana qara daure fuskarta,

Suka mata sallama suka fita suna neman el'mustapha, ya rage dakin ita kadai da banan.

Jiran me kike yi anan kika min tsaye, ko el'mustapha din kike jira?

Banan ta dago tana kallonta xuciyarta na bugawa, jikinta ya dauki rawa shikenan ta shiga uku tunda har jiddah ta gano tana son mijinta,

Xatayi magana jiddah ta katse ta,

Kiyi gaggawar cire son el'mustapha a xuciyarki dan baxaki taba auren sa ba, baxaki taba samun sa ba, baxan iya korarki daga gidana ba saboda kin xauna dani da amana da yarana baya ga wannan wallahi Islam din Ma hana maki auren shi xanyi, tsab xan iya nema masa auren yar anty ikram domin itace dai dai da shi ke kije ki auri talaka dai dai dake. 1

Banan ta soma kuka, dan Allah kiyi haquri anti jiddah kada ki juyamin baya kada ki canxa min fuska...

Baxaki taba ganin annurin fuskata ba har sai kin bar mijina, kuma hankalina baxai taba kwanciya dake ba har sai naga auren ki, saboda banan din dana sani a da ba itace a gabana ba wanna  xuciyarta cike take da cin amana da yaudara idan har xata iya auren mijin jiddah.

'Dan Allah anti jiddah kiyi haquri,

In haqura in maki me, in barki ki auri el'mustapha ko me, kifita daga dakin nan kar na maki illah, kuma kar na qara ganin ki cikin gidana, ki koma can ciki da masu aiki inda kika saba xama, ya'yana ma kada ki qara kula su tunda dasu kike fakewa kina cin amanata, da su kike ganin el'mustapha kina jin dadi, xaki fita ne ko sai na rotse maki kai...

Ta juya da sauri tana kuka kicibis sukayi karo da El'mustapha, ya matsa gefe da sauri,  tafi ta tana waiwayen sa shikenan ta rasa shi har abada...

Jiddah tace ki kallesa a yanxu da nake kwance, watarana kika qara masa wannan kallon idanun xan cire gabaki daya, gani nan bari nan keda shi har abada. 2

El'mustapha na tsaye yayi shiru ya xuba mata idanuwa, wallahi har a xuciyar shi ya kasa yarda wannan jiddar sa ce tun daga jiya xuwa yau kwata kwata ta canxa ta dawo mai xafi da fushi, bai taba sanin tana da fada haka ba,

Ta juyo suna hada ido ta soma harararsa tamkar idanunta xasu xubo qasa, taja dogon tsaki cikin fushi hade da juya masa baya.

Ko dai jiddah tayi gamo ne, yaushe jiddah xata iya kallonsa ido da ido haka ta hararesa,

Bai yi magana ba sai ya juya da xumar xaije ya rakasu ikram airport, tana jin alamar xai fita ta juyo,

Ina kuma xaka je?

Kome take mamaki take basa,

Yace xanje na raka su anty ikram airport,

Tace aa xakaje dai ka raka banan kake fakewa da anty ikram, ka xauna ba inda xaka je. 1

Yace ok tor banan xanje rakawa xaki hana ni ne,

Ta yunqura ta tashi da sauri, qafar da aka mata aiki take yunqurin saukowa da ita,

Hankalinsa ya tashi ya nufe ta da sauri ya riqe qafar yana kallonta cike da haushi,

Kina da hankali, keda akace baa so kiyi dogon motsi har kike neman saukowa, kije ina jiddah.

Tace muje raka banan tunda xataje ta barka, 

Wai meke damun ki jiddah, meyasa kika dawo kamar wacce bata da hankali,

Tace eh naji bani da hankali indai akan kane baxan taba hankali ba, dalla Malam sake min qafa kuma wlhy ba inda xaka je, xaka je rakiyar anty ikram saboda ku kalli juna kuji dadi barin Ma ita shegiyar dana ga tafi xaqewa wurin kallon ka...

Ganin in baiyi da gaske ba jiddah xata iya bata aikin da aka mata a qafa aiki ya dawo sabo, sai ya kwantar da murya cikin rarrashi duk da bacin rai da yake ji.

Yace shikenan naji baxan je ba, yi haquri ki kwanta jiddah saboda aikin qafarki,

Ta kwanta ba musu hade da dauke kanta gefe,ya gyara xaman qafar kamar yanda take kana yayi tsaye yana kallon jiddah kafin ya nemi guri ya xauna yana kallon ikon  Allah. 
Shiru dakin yayi, kowane da saqe saqen xuciyarsa. +

Hajiya tayi sallama ta shigo da jaririyar a hannunta tana kuka, a tunanin ta jiddah barci take yanda taga ta lumshe idanuwanta.

Yarinyar nan sai kuka take tun daxu, dama jiddah ba wani abin kirki ta bata ta sha ba,

El'mustapha ya karbe ta, hajiya ta juya ta bar dakin, tsurawa yarinyar idanu yayi, shi kadai yasan tunanin me yake yi,

Ya dago yana kallon jiddah dai dai lokacin ta bude idanuwanta suka hada ido, turo baki tayi ta harare sa tana dauke kanta gefe,

Yace gata ki bata tasha, tayi masa banxa kamar bata ji ba, ya taso da jaririyar yana miqa mata,

Just feed the baby jiddah don't involve her  cikin baqin halin da kika kwaso tsakanin jiya da yau.

Ta bude idanu tana kallonsa, why should I feed her? Inaji kaima kana da shi a qirjinka, ka bata ta sha kada ta dauki baqin halin da na kwaso. 2

Wai meke damunki ne jiddah, har akwai ranar da xaki iya min rashin kunya, idan nace xanyi auren akwai wanda ya isa ya hana ne, ni ba mijin mace hudu bane ko anyi ni ne saboda jiddah kadai, ko kin manta sanda kike roqona akan nayi aure, You even cry for that, idan har xaki iya tilastamin auren wata yanxu banga abinda xai daga hankalin ki na kishi ba, gida nane I have the right nayi duk abinda nake so kuma nasa duk macen dana ga dama,kiyi abinda duk xakiyi. 1

Idan har kana tunanin ban isa na hana maka auren ba kaje kayi ni kuma xan nuna maka gida ba nawa bane amma na fika iko dashi dan ba shegiyar da xata xauna a wannan gidan wallahi sai dai na qona shi duka........ Kuka yaci qarfinta, Inna lillahi wa Inna ilaihir raji'un ta fada a hankali cikin kuka, bata taba tunanin akwai ranar da xata iya maidawa el'mustapha magana ba ballantana ta kai ta da yana fada tana fada,

Cike da bacin rai ya miqa mata baby, feed her jiddah.

Nace baxan bada ba, nawa ne ko shima xaa min iko akan shine, ka bata ta sha ko ka kaiwa banan din ta shayar da ita. 1

Xaiyi magana wayar sa ta dauki qara, yana ganin anty ikram ya dauka da sauri, jiddah ta kafe shi da idanu.

Autan mama yarinyar nan banan tace bata da lafiya na taba jikin nata naji xafi sosai shine nace ko a dawo da ita ne a duba ta tun da duk asibiti ce, 1

Ya dubi jiddah yanda ta kafe shi da idanu kusan Ma kamar tana jiyo abinda ikram din ke fada, ya tsinci kansa da tsoron jiddah,

Yace aa basai kun dawo ba idan kun sauka taje asibiti amma bari yanxu xan x....

Kaje ina?yaji muryar jiddah baisan sanda ya katse wayar yana kallon taba,

Xanje na duba yarinyar mutane...

Wallahi baxaka je ba, kaje ka duba yarinyar mutane You are not even ashamed of saying that, sai kace akan ka take bani ce na dauke ta aiki ba, wai me kake nufi el'mustapha?

Ke xan ma wannan tambayar jiddah, me kike nufi, sam wannan abin da kika dauko bai dace dake ba. 1

Baxai taba dacewa dani ba idan har baka cire wannan yarinyar a xuciyarka ba,

Don't you understand, so nawa xan gayamaki bana son yarinyar, ko sai na rubuta a goshina  na nunawa duniya bana son banan, saboda yarinyar nan kike min rashin kunya, telling me any word da yaxo bakin ki, abinda baki taba min ba shi kike min a yanxu, shikenan ki cigaba and don't feed the baby sai me, sai aka ce maki baxata rayu ba, mtsewwwww ya fice da yarinyar a hannunsa, ta bisa da kallo tana sharar kwallah,

STORY CONTINUES BELOW


Wayarsa da ya ajiye a saman gadon ta dauka  ta shiga neman layin anty ikram amma sam baya shiga, Allah yasa Ma jirgin ya tashi, lallai Ma banan, yarinyar nan da gaske take yi kenan, ai ana barin halas dan kunya amma sam banan bata wannan tunanin, dole xata tashi tsaye kan banan.

Gaba ki daya yinin ranar tayi shine cikin kadaici da kewar el'mustapha tun da ya fita bai sake dawowa ba, abinci ma kasa ci tayi, bata da wannan kuxarin, xuciyarta ta kasu kashi biyu na farko tunanin inda el'mustapha yaje ya barta abinda bai taba yi mata ba, na biyu matakin da xata dauka akan wannan yarinyar dake neman tarwatsa mata farin cikin ta dana mijinta. 1

Kici abincin jiddah, ga maganin ki Ma baki sha ba, tun daxu sai tunani kike kina kuka kada dai duk akan banan ne?

Ni baxan iya ci ba hajiya xuci.....

Uhm uhm fa jiddah, el'mustapha ya gayamin abinda kika masa sam banji dadi ba, na gayamaki tun farko idan har mataki xaki dauka ki tsawatar wa banan itace mai laifi ba el'mustapha ba,

Ita Ma fa el'mustapha take so hajiya, meyasa suke son rabani da farin cikina, meyasa sai el'mustapha suke so, meyasa mutanen dana yarda dasu na basu amana ta suke yaudara na, na rainesu da hannuna su taso suna son mijina.

Ki kwantar da hankalin ki jiddah, idan har uwani ta yaudare ki ta auri mijinki ta cutar dake banan baxata auri el'mustapha ba, ya rantse baya son yarinyar nan, kema ya rantse maki, ya kike so ya yine xai maki rantsuwa da qarya ne?ni kam ban baki tarbiyar da mijinki yana fada kina fada ba dan baki taba ganin nayi da abban ku ba, idan yana fada shiru nake koda nice da gaskiya indai ransa ya baci na bashi haquri sai kiga ya sauko daga fushin ya xauna mu fahimci juna, ban san ki da wannan ba sam ba halin ki bane, banan din ya kamata ki hukunta ba el'mustapha ba, yaron nan yana son ki jidda. 3

Amma hajiya s.... bana son gardama idan ya shigo ki bashi haquri kece baki da gaskiya nayi masa rashin kunya ki tsaya ki saurare sa kinqi sai fada kike, kuma kada ki sake sako yarinyar nan a fadan ku har kice baxaki shayar da ita ba.

Jiddah ta fara kuka sosai kowa laifin ta yake gani, sunqi su gane halin da take ciki da abinda take ji a xuciyarta, wane haquri ne batayi ba a baya, wane jajircewa ne batayi ba na ganin ta aurawa uwani el'mustapha wanda haqurin bai mata amfanin komai ba sai Ma wahala da ta shiga, saboda me yanxu xata haqura ta bar banan tana son mijinta, idan su basu san xafi da radadin da ta fuskanta a baya ba ita ta damu da ta ta rayuwar kuma baxata taba bari el'mustapha ya auri banan ba indai tana numfashi a doron qasa.

Ba kuka nace kiyi ba, kici abinci kisha magani, yau na lura ko barcin rana da kike yi bakiyi ba kada ki jawo wa kanki wata matsalar.

Jiddah bata kula ta ba illah kukan da ta cigaba da yi, suna haka el'mustapha ya shigo dakin, duk da taji shigowar sa hakan bai sa ta dago ko daina kukan da take ba.

Hajiya tace naji dadin xuwan ka, taqi taci abinci tun daxu maganin Ma bata sha ba sai kuka take.

Ya ajiye kayan da je hannunsa har lokacin fuskarsa ba walwala akwai sauran fushi a tare da shi,

Yace saqo ne Dr merah yace a bata daga gurin matarshi kafin taxo duba jiddah, ina ji kamar abinci ne aciki.

Hajiya ta duba kayan, abinci ne da kayan marmari na lambu da ganin yanda aka hado kayan fruit din kasan gidan sarauta suka fito, ta debi abinda take so ta fita goye da jaririyar tana fadin idan bata ci ba kanta, ka xauna kaci ka qoshi sauran ka bani na cinye sai tayi ta cin kukan.

El'mustapha dai bai ce komai ba, xuba abincin yayi ya qarasa gurin jiddah, tana jinsa a kusa da ita ta dago tana kallonsa, fuskar nan tasa ba walwala sai taji ba dadi jikinta yayi sanyi, ba qaramin abu ke saka el'mustapha wannan fushin mai tsanani ba.

Ya debo abincin a spoon ya kai bakin ta, ta riqo hannunsa, cikin rawar murya tana xubar da hawaye, 1

Tace kayi haquri el'mustapha, baxan qara ba.

Yace ba komai ya wuce kici abincin,

Baka haqura ba idan har wannan fushin bai bar fuskar ka ba, forgive an forget baxan qara ba I promise you.

Yasa qaramin yatsansa yana share mata hawayen kafin yace na haqura jiddah nasan ba halin ki bane kuma bana son ki dashi ki barshi da uwani yafi dacewa not you.

Tsura masa ido tayi tana kallonsa, shima kallonta yake kafin yace saboda damuwa kinga yanda kika dawo just for only today,

Bata ce komai ba ta soma karban abincin da yake bata, nan da nan suka shirya kamar wani abu bai taba hada su ba. 4

Koda hajiya ta dawo dakin tayi mamakin ganin jiddah kwance a jikin el'mustapha sai dariya suke cikin farin ciki.

A gurguje pls😒

2 months.... 

'Alhamdulillah jiddah na samun kulawa sosai gurin dr merah har ta soma takawa da qafar sai dai ba sosai ba.

Cikin wannan lokacin harda aikin uwani anyi batare da sanin su hajiya ba.

Ganin jiddah ta sami sauqi sosai har tana iya taka qafar ko bada stick ko wani ya riqa ta ba suka soma shirye shiryen dawowa gida cike da farin cikin dimbin nasara da suka samu akan aikin jiddah bayan sun cire tsammani daga qafar baxata qara moruwa ba.Saukar su Nigeria ke da wuya, motocin gidan El'mustapha suka iso airport. +

Cikin masu tarbar su jiddah harda su anty ikram da yusrah,

Cike da tsananin mamaki suka rungumeta suna kallonta qasa da sama, kamar bata taba samun wata lalura tare da ita a qafar ba.

Welcome back jiddah, Allah ya qara lafiya mai amfani cewar Nabila tana kallonta cikin murmushi.

Jiddah kallonta tayi tana fadin kin goge laifin ki na rashin xuwa duba ni a Germany, kika xo tarbata, naji dadi sosai Allah ya bar xumunci.

Amin ta fada cikin murmushi.

El'mustapha yayi gaba da baby rungume a jikinsa, Allah kadai yasan irin farin cikin dake xuciyarsa.

Suna iso wa gida sunyi mamakin samun mutane haka duk yawanci daga gurin aikin el'mustapha ne sunxo taya sa murna, kuma sosai ya nuna farin cikin sa,

Shiru jiddah tayi tana kallon gidan bayan ta fito, ba abinda ya canxa daga gidan yana nan yanda ta barshi, Alhamdulillah take nanatawa a xuciyarta yafi a qirga na murnar dawowar ta gida cikin qoshin lafiya tare da dimbin nasarori da ta samu.

Ji tayi an rungumeta, ko baa fada ba tasan twins din tane,

Welcome back mummy, we miss you,

Ta sunkuya tana kallonsa cikin tsananin tausayinsu yanda suka rungumeta sosai a jikinsu,

Mummy baxaki qara xuwa ki barmu ba ko? ta gyada kanta tana murmushi.

Da kyar suka barta suka nufi inda el'mustapha, sai tambayar sa suke baby waye, ya kyale su.

A falo suka yada zango, hajiya kam a gajiye ta nufi dakin baqi, duk falon ya cika da yan uwa cikin farin ciki.

Mummy baby waye a hannun daddy cewar aryan,

Arham yace mummy kice daddy ya ajiye ta ya dauke ni, tun daxu bai cirani sama ba nayi masa oyoyo.

Aryan yace mummy  wheel chair dinki yana dakin daddy, kixo ki xauna ni xan riqa tura ki.

Banda murmushi ba abinda jiddah keyi, falon kuwa sai dariyar yaran ake yi.

Banan tayi sallama ta shigo, da murna ta isa inda jiddah ta rungumeta tana mata sannu da xuwa,

Jiddah ta amsa sama sama,

Tace anty jiddah me kike so na kawo maki, nayi maki girki Kala Kala irin wadanda kike so.

'ki barshi anjima xanci.

Batare da tunanin komai ba banan ta juya tana kallon el'mustapha dake ta surutu da twins, ta saki ajiyar xuciya kamar wacce ta dade tana neman abu bata samu ba sai yau, 1

Tace yaya me xan kawo maka ka ci, kafin yayi magana jiddah tayi caraf tace ya qoshi ki tashi ki tafi idan yana buqata xan neme ki.

Banan ta tashi jiki a sanyaye ta nufi kitchen kamar xata dauki wani abin, leqen sa ta soma yi, Allah ya jarabceta da son el'mustapha ta kai har bata iya boye feelings dinta akansa, ina ma jiddah xata fahimce ta, ina Ma jiddah xata bata dama kamar yanda ta baiwa uwani saboda baxata taba nadamar aura mata el'mustapha ba, bata da niyar cutar da jiddah ko wani abu nata xama take so suyi na amana, amma jiddah taqi ta saurara mata kamar Ma ta tsaneta a yanxu. 8

Allah ka cire min son wannan bawan Allah idan ba alkhairi bane. 2

Yusrah ta tashi tana fadin, anty ikram xan tafi ina so na dauko su amira skul,

STORY CONTINUES BELOW


Tau shikenan nima xuwa anjima kadan xan tafi.

Jiddah Allah ya huce gajiya ya qara lafiyar jiki, kuma a kula da qanina yanda ya dace saboda yayi haquri cewar yusrah.

Murmushi kawai jiddah tayi suna wasa sosai tsakanin su,

Yusrah ta dubi el'mustapha tana fadin, xo muje ka taka min akwai maganar da xamuyi,

Yace ok sister, ya tashi yana ajiye baby akan sofa, twins suka mata caa suna kallonta sai yanxu suke ganin fuskarta da kyau.

She is beautiful daddy, who gv you?

Yace Allah, babyn mummy ne idan kuka taba ta tashi barci ba ruwana, mummy xata dake ku.

Suka juya suna kallon jiddah cikin mamaki, el'mustapha ya fita tare da yusrah.

Wai haka ne mummy? Ta gyada kai tana kallonsu,

Jiddah ta juya tana kallon kitchen tana lura kamar banan din bata fita ba,

'me kike yi a kitchen dinne banan?

'Anty jiddah ina hada abincin ne ta fada cikin rawar jiki, ta fito da sauri da warmers a hannunta ta nufi dinning tana shiryawa duk abinda take idanun jiddah akan ta, tana gamawa kuwa tace ta fita...

Wai me banan tayi maki ne jiddah, na lura tun a Germany kika takura mata cewar ikram.

Jiddah ta tunxuro baki, batayi magana ba,

Baki ji bane? Ta qara tambayarta fuskarta ba walwala, sosai jiddah tasan anty ikram bata wasa ko akan el'mustapha ne kuwa shi kansa yana tsoronta itace babba a gurin su duk yanda tace haka xaa yi musamman yanxu da take kamar uwa a gurin su.

Tace El'mustapha  take so...

'Anty ikram ta kalle ta da mamaki,

Tace ba dan na san ki nasan halin ki ba jiddah dana qaryataki, saboda banan xata so el'mustapha, ba ajin ta bane she knows, dan haka baxatayi wannan tunanin ba.

Idan har uwani xata iya son el'mustapha ta aure sa saboda me banan baxa ta so sa ba? Ita da take ganin xama kawai tayi a gidan bata da alaqa damu ba kamar uwani da muka taso tare ba.

Amma dai banan ta bani mamaki jiddah, sosai kuwa wannan simi simi nata ashe dai munafuka ce tunanin ta el'mustapha xai aure tane, mtsewwwww aikin banxa kada Ma ki wahalar da kanki wajen dorawa kanki damuwa dan el'mustapha baxai aure ta ba, ba abin da xaiyi da banan.

Jiddah tace tunanin ki kenan anty ikram, amma namiji idan ya tashi iskancin sa babu ruwansa da yanda mace take ko matsayinta, banan tana da kyau da diri saboda me el'mustapha baxai so ta ba tunda ba arxiki yake nema ba, so sone haka namiji namiji ne, baka sanin inda ya dosa a koda yaushe canxa sheqa yake, kina ganin kamar el'mustapha baxai so banan ba saboda tana talaka ko dan saboda ni na fita kyau amma el'mustapha ya taba son banan. 1

Shi el'mustapha? Ta tambaya cikin mamaki, ta yaya, ya xaa yi el'mustapha ya so wannan yarinyar, yar aikin gidansa, me ya ruda shi a jikin banan wanda ke baki dashi.

Jiddah ta tabe baki batayi magana ba,

In kuwa haka ne banan xata bar gidannan, ni bana son xama da munafuki, nifa shiyasa ban yarda da yar aiki ba ko kadan kina ganin duk masu aikin gidana tsofaffi ne bani da yarinya ko budurwa baxan iya ba, ai kece Ma da wata shegiyar xuciya yanda kika cije lallai sai el'mustapha ya auri uwani, ba dan mama ba lokacin wallahi baxai aure ta ba kuma banan xata bar gidannan.

Tace aa anty ikram ki barta ba sai ta bar gidan ba a ynxu, idan el'mustapha yaji wannan mgnr xaiyi tunanin na kawo shi qara ne gurin ki, kibari idan wani abin ya tashi daga baya sai ki dauki mataki ni kada Ma ki masa mgnr banan yanxu tuntuni yace baya son ta kar na qara tada maganar.

STORY CONTINUES BELOW


Ok inyi shiru in barki da yarinyar kenan, shikenan ba matsala gidan kine ke kika ji kina iyawa amma fa el'mustapha baxai taba auren banan ba.

Jiddah tayi shiru,

Haba haba, kowace mace ta taso sai qanina kuma abin haushi yaran da suke qarqashin sa matarsa ke riqo, banda xalunci da rashin imani sai su rasa namijin aure sai mijinki, me suke nufi da el'mustapha, namamajo ko me? A bata masa suna ace yana aure aure a gari to baxai yiwu ba idan har na qara jin qishin qishin cewa banan na son el'mustapha wallahi har ke jiddah sai ranki yayi matuqar baci. 3

Sai kiyi ta xama simi simi kamar ba mace ba, sanyin ki yayi yawa, haqurin ki Ma yayi yawa, duk wadda taxo tace mijinki take so, ki bar banan din ta auri el'mustapha kina xaune a gida Inna mai maki aiki xata xo tana son el'mustapha ita Ma.

Jiddah ta subulce da dariya har tana rufe bakinta da hannunta,

Tace anty me el'mustapha xai yi da Inna, ai xata haife sa Ma.

Gaskiya na gaya maki yanxu dai mama bata raye ballantana ta goya maki baya ga el'mustapha ya qara aure.

Cikin rashin fahimta jiddah ke kallonta gabanta na faduwa,

Mama bata raye kamar ya anty ikram, wace mamar kike magana?

Ikram ta dube ta dai dai lokacin el'mustapha ya shigo,

Tace bana son rainin hankali jiddah ina wasa dake ne, wace mamar kika sani bayan tamu, tun bayan dawowar ki kallon ki kawai mukeyi ba wanda kika yiwa gaisuwar mutuwar mahaifiyar m.....bata qara sa ba taga jiddah ta xube gurin,

El'mustapha ya qaraso cikin falon da sauri yana kallon yayar tasa cikin tuhuma..

Me kika mata sister, me ya sami jiddah? Ita ma hankalinta ya tashi sosai, a tare suka nufi jiddah suna kiran sunan ta amma bata motsi,

Daukarta el'mustapha yayi jikinsa na rawa xai fita da ita,

Tace bari na kawo ruwa ina ji suma ne tayi,

Me ya sumar da ita? ya tambaya yana kallonta cikin bata fuska,

Mgnr mama nake mata bata san ta mutu bane,

El'mustapha ya ajiye jiddah yana fadin,

Saboda me sister?

Ko duka na xakayi ne saboda jiddah, matarka fa ba wanda tayi wa gaisuwar mahaifiyar mu, mun riqeta a xuciyar mu da wannan so kake... Ya katse ta,

Wallahi jiddah bata san da maganar mutuwar mama ba, you know her condition sanda aka ganta saboda me xan gayamata ina ji dake Ma akayi mgnr cewa kada a gayawa jiddah saboda cikin dake jikinta at that time, ko yaushe jiddah tana tambayana mama sai dai nayi mata qarya, amma meyasa sister,

Sam na manta da wannan xancen wallahi, bari na kawo ruwa ai suma ne ba wani dogon abu ba, ta juya da sauri.

Ya bita da kallo cikin takaici, yana Jan tsaki a xuciyarsa, ba dan yayar sa bace da qanwar sace ba abinda xai hana masa xuba mata kyawawan Mari a fuska, meyasa mace komai girmanta wani lokacin bata da tunani?

*

Da daren ranar duk da jiddah na cikin damuwa bai hana mata sauraren Islam ba lokacin da yaxo yayi mata ya jiki.

Sosai ya gayamata canje canjen da yake fuskanta a gurin banan wanda sam baya jin dadin sa kuma da ace baya son ta da gaskiya da tuni ya dade da barin ta.

Xan yi magana da banan idan har bata son ka nasan me xanyi islam, kuma ai xaka so Mamee yar wajen anty ikram tama fi banan din komai illah shekaru da banan xata nuna mata.

STORY CONTINUES BELOW


Baice komai ba shidai banan din yake so,

Idan munyi magana xan kira nabila a waya amma kada ka damu,

Yace to shikenan nagode anti jiddah,

Ya ajiye mata qatuwar Leda bayan ya tashi, 
Yace a bawa our new baby,

Murmushi jiddah tayi tana fadin, baby tana godia sosai islam,

Ban ma san sunan ta ba,

Sunan mahaifiya tane Zubaida amma ake kiranta Airah,

Allah ya raya ta,

Tace amin,

Ya tashi ya fice, ta dauki ledar tana dubawa, kayan babies ne masu kyau kuwa.

El'mustapha yana tsaye qofar falonsa ya xuba mata idanuwa,

Jiddah har yanxu dare fa yana tafiya, tun daxu na saka airah barci.

Ta dube sa kafin tace, xo kaga islam ya kawo wa mai sunan mamana,

Ya tako a hankali ya shigo falon, kayan ya karba ya ajiye gefe batare da ya duba ba, yace ni bana son wasu kaya a yanxu jiddah kadai nake so da buqata kin barni tun daxu sai raino nake maki.

Ta riqa hannunsa tana kallonsa,

Muje na baka ladan rainon nasan shi kake wa safa da marwa tun daxu.

Dariya El'mustapha yayi yana shafar sumar kansa.

*

2 days....

Jiddah ta sami banan da mgnr islam,

Tace kiyi haquri anti jiddah ki sake min fuska kamar da, na amince xan auri islam.

Jiddah tace baxan cigaba da sake miki fuska ina yarda dake kina cin amanata ba, babu yarda yanxu tsakanin mu idan har kina son mijina, maganar kina son islam a yanxu nasan qarya kike domin da wadannan kalaman kika yaudare ni da farko kika ce kina son islam bayan kinsan kina son mijina.

Cikin kuka banan ta riqo qafafunta,

Tace kiyi haquri anty jiddah ki yafemin, ba laifina bane wallahi xuciya tace tun ban ganshi ba na kamu da soyayyarsa a dalilin yawan kallon hotunan sa dake falon ki, ni kaina bansan yanda akayi na fara son sa ba, ki yafe min na amince ko a yau ne ki aura min islam shine xabin Allah.

Jiddah bata jima da dawowa daga inda banan ba sai ga sallamar su abba,

Cikin murna ta janye airah da take shayarwa tana kallonsa,

Oyoyo abbana, sannu da xuwa,

Jiddana tashi tashi naga yanda kike takawa, tashi naga tafiyar ki jiddah.

Cikin dariya ta tashi ta nufe sa,

Alhamdulillah Allah mun gode maka, ya karbi airah cikin farin ciki, 
Jiddah ta daga murya sosai tana kiran hajiya,

Hajiya kixo ga abba,

'Abba ya xauna yana fadin, barakallah yarinya tayi bul but da ita, girmanta yafi na yan watanni biyu, me kike bata ne haka jiddah.

'Abba duk abinda kake ci shi take ci, bari na kawo maka abinci, ta juya ta bar falon.

Hajiya na shigowa aka fara kallon love anyi missing juna🤭

Inna ta shigo tare da jiddah dauke da kayan abinci,

Tace bari na kira el'mustapha bai jima da dawowa ba gurin aiki.

Idan barci yake da kin barshi jiddah tun da ina nan,

Tace aa abba ko barci yake sai ya tashi ai miji bai fi uba ba, ballantana ba barci yake yi ba wasan ball yake kallo.

Yace to shikenan, ta fice hajiya ta sauko tana xuba mashi abinci.

Jiddah tare suka fito da El'mustapha, cikin doguwar jallabiyarsa da gani yanxu ya saka ta da xai fito,

Suka gaisa da abba, yana qoqarin xama sai ga uwani ta shigo falon cikin sallama.

Duk suka xuba mata idanu banda el'mustapha, jiddah kuwa kallo daya tayi mata ta dauke kanta gefe,

Hajiya tace ba dai tare kake da uwani ba, ina ka ganta alhaji.

Uwani xo ki xauna abba ya fada yana kallonta,

Idanu uwani ta xubawa el'mustapha  daga inda take tsaye, ji take kamar taje ta lashe shi saboda so, bata taba jin sonsa ya ragu a xuciyar ta ba koda na minti daya ne, gabanta ya tsananta bugawa lokacin da tayi arba da jiddah.

Sosai jiddah ta canxa daga yanda ta Santa, tayi haske ta qara kyau gwani sha'awa, da ka ganta kasan tana cikin jindadi da more rayuwa babu wata damuwa a tare da ita.

A hankali ta qarasa cikin falon ta xauna jiki a sanyaye.

'Abba yana lura da yanda yanayin su ya canxa duka kamar basa murna da xuwan uwani har hajiya Ma,  uwani yar'sa ce ba abinda xai hana masa xama da ita illah ya cigaba da mata addua matsalar da take ciki anyi aiki sai dai ace alhamdulillah amma kam uwani na nan yanda take sai wasu abubuwa kadan da ta daina, dama lafiya sannu sannu take shiga. 1

Tashi el'mustapha yayi yana kallon abba,

'Abba bari na barka kaci abinci kafin na fito,

Yace tau shikenan el'mustapha, duk da yasan saboda uwani ne yabar falon baiga laifin su ba dan sun tsani uwani a yanxu.

Uwani ta bisa da kallo har ya shige, ji take kamar tabi bayansa, inama da aure tsakanin su da ta rungumeshi ko xata samu sauqin xuciyata amma ta lura sam el'mustapha baya gabanta ko kallo bata ishe sa ba.

Jiddah kuwa tun da ta maida hankalinta ga airah bata sake dagowa ko magana ba,

Hajiya tace alhaji muje ciki kaci abincin, ta soma kwasar kayan cikin son gujewa uwani.

'Abba yabi bayanta, jiddah Ma ta tashi da sauri rungume da yar'ta,

Uwani tayi saurin tsaida ta,

'Dan Allah anti jiddah ki yafe min, nasan kin tsane ni a ynxu amma kiyi haquri ki bani dama ta biyu na xauna dake baxaki taba dana sani ba, ki aura min El'mustapha a karo na biyu wallahi ina son.... bata qara sa ba jiddah ta dauke ta da Mari, kafin tayi wani yunquri ta sake wanke fuskarta da Mari hade da hankadata ta fadi ragwaf. 3

Ko yawo xakiyi tsirara a duniyar nan kina bin bokaye, ko ciwo xakiyi kina aman jini kina mutuwa kina tashi baxaki taba auren *EL'MUSTAPHA* ba kuma kiyi gaggawar barin gidan nan kafin na fito nasa a wulaqantaki a  gidannan.

Post a Comment for "EL-MUSTAPHA CHAPTER 8"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...