Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

EL-MUSTAPHA CHAPTER 7

EL-MUSTAPHA CHAPTER 7

- - Post a Comment
EL-MUSTAPHA

CHAPTER 7
Tana gama saka doguwar rigar ta dauki Cup din ta kai bakinta,

Kurbawa tayi ta ajiye tana fadin,

Yunwar da nake ji wannan abin baxai isheni ba, idan na gama cin abinci sai na dora wannan akai.

Ta dauki turarukka Kala Kala ta feshe jikinta dasu, ta isa bakin mirror tana kallon kanta,

Ba laifi nayi kyau kadan duk da hasken fatar ya dishe, ga wata rama da ta bayyana a fuskana da jikina, cikin kwanakinnan Ma xan maida jikina xan fara cin dadi.

Ta soma jujjuyawa tana murmushi, very soon xan dawo uwani na as usual amma mai tausayi da haquri irin anti jiddah, taji gabanta ya fadi tuna abinda ke gabanta,

Idan nayi kyau da kudi xanje na nemi yafiyarta da nasu hajiya nama san lokacin an siyamin mota.

Ta fito tana murmushi, hajiya Mariya bata falon sai dai ga komai an ajiye mata akan Center table dake nan tsakiyar falon.

Da sauri ta qarasa gurin ta xauna, ta shiga budewa tana murmushi jin qamshi ya xiyarci hancinta.

Ta lumshe ido ta qara budewa, yanda tace kuwa haka akayi mata lallai matar nan da gaske take tana son ta.

Da hannu ta soma ci batare data damu da 🍴, ci take ba kakkautawa tana korawa da drinks an dade baa hadu ba.

Tana tsaka da ci hajiya Mariya ta shigo dakin cikin wata irin shiga mai matuqar daukar hankali kamar wadda xataje turakar miji.

Qamshin turarenta ya gauraye falon, uwani na tsaka da cin abincin ta jiyo alamunta tare da fadin hey baby....

Uwani ta dago a hankali tana kallonta, ta hadiye wani yawu ba shiri ji kake kut tare da xare idanunta cikin tsananin mamakin ganin hajiya Mariya da wannan shigar.

Banyi kyau bane baby?

Uwani ta soma kokowa da nutsuwarta, da kyar ta tattaro hankalin gare ta,

Ke da kika ce mijinki ya mutu meyasa kike wannan shigar kuma cewar uwani.

Hajiya Mariya tayi far da ido tana fadin dama sai miji akewa kwalliya irin wannan, ai ni ke nayi mawa.

Ni? Meyasa? Uwani ta tambaya lokaci daya bayan ta mayar da lomar abincin dake hannunta.

Hajiya Mariya ta xauna daf da uwani, ta sa hannunta daya ta xagayo dashi ta qugunta,

Uwani ta bita da kallo kafin ta dubi inda hajiya ta riqe mata, gabanta ya tsananta bugawa jikinta ya dauki rawa sai ga xufa na karyo mata, akai akai take hadiye yawu saboda tsananin tsoro da firgita.

Babu xancen mama ta juyo kacokan tana kallonta,

Tace hajiya Mariya kin ganni nan bani da kwadayi, iyayena suna da kudi, yaya ta mai kudi ce haka Ma mijinta, duk abinda nake so ana min, ni na fasa komai naki bana so, ni ba yar iska bace kowa yasan bana iskanci.

Hajiya Mariya ta dora yatsanta akan bakin uwani tana xagayawa dashi, uwani taji wani iri a jikinta.

Shiiiiii bana son jin wannan xancen uwani, ni mai kaunar ki ce xan baki duk abinda kike so har da mota ma, xaki ji dadin kasancewa dani kuma xamuje inda iyayenki na roqesu su barmin ke sai na hada ki abota da su Aiman.

Ta sa hannu daya tana shafa jikin uwani, xumbur uwani ta tashi,

To magajiya karuwa ni ba yar iska bace, kuma kaf a dangin mu bamu da dan iska kuma ba wanda ya taba haduwa da yar iska sai ni shima dan naci amanar jiddah ne, na tuba k.... Saukar Mari taji a kuncinta,

STORY CONTINUES BELOW


Ke... Ni xaki kira da karuwa, nice karuwa? Tunda nake baa taba kirana da wanna sunan ba sai ke? Kina nufin xan taimakeki a banxa ne, ki shiga motana mai AC, ki shigo gidana har dakin ya'ta kiyi wanka kisa kayanta, sa'anan na shiga da kaina na miki girki, na kawo maki kici kice duk a banxa ne, lallai baki da hankali baki san kanki ba kuma baki san me kike yi ba ki gayamin waye xai taimakeki haka a banxa ai ko namiji ne sai ya dibi rabonsa ballantana ni da na gani kuma rai ya biya, xindir fa na ganki a toilet.

Duk sanyin AC dake falon bai hana xufa karyowa uwani ba, bata taba ganin tashin hankali kamar wannan ba, gwanda xaman ta da su 'Anty aj da runkes da xama da wannan matar, ai duk iskancinta ita bata tambada babu wannan a xuciyarta, sai ga uwani na hawaye.

Kixo ki cinye wannan indomie da kwai duka dan baxanyi asara ba sannan kixo muje daki na fanshe wahala ta.

'Dan Allah kiyi haquri hajiya,

Tace kada ki bata min lokaci,

Uwani ta xauna dirshan ta jawo plate din da kyar, cusawa take tana kuka Sam bata jin dadin indomie a yanxu kamar farko.

Hajiya Mariya ta sassauta muryarta tace, in kin kwantar da hankalin ki dadi fa xaki ji uwani, ba wanda xai san abinda muke, xan yi ta son ki na miki duk abinda kike so.

Tace ni bana son komai ki barni naje inda hajiyata idan ba baqin ciki xaki min ba, ita tana sona bata min baqin ciki a rayuwa, bata min wannan iskanci, tana kula dani sosai tana min duk abinda nake so, harda goyani take yi tana min wanka ta sakamin kayana, bana son naki ki barni na tafiya ta.

Hajiya Mariya ta fusata, haushin uwani ya cika xuciyarta har bata san lokacin da ta qara bige mata baki ba,

Yi min shiru shegia, maxa ki cinye indomie dinnan kije muje tun ban fashe maki kai ba.

Ta soma kakarin amai saboda ta qoshi sosai kuma abinda baa ci hankali kwance ina xai sami nutsuwar xama,

Ki kamin amai anan wlhy kinji na rantse sai kin lashe shi kuma na miki dukan tsiya, maxa ki cinye ina jiranki.

Ba shiri uwani ta hadiye aman hade da kai hannunta a bakinta, ta gwalalo idanu a waje sai xufa take ga hawaye shabe shabe kwance a fuskarta,

Haka uwani ta cusa indomie duka a cikinta sai nishi take tana wiqi wiqi da idanuwa kamar sabuwar mayya, matar nan babu ko digon tausayin uwani a xuciyarta,

Ta tashi ta nufi dakinta da sauri jin wayarta na qara, uwani na ganin haka ta xura waje da gudu, gate din ta nufa duk iya qoqarinta yaqi ya bude bata masan yanda xaa bude gate din ba, haka ta dawo tana kuka, inda ta jefar da kayanta ta nufa, ai kuwa ba shiri ta cire na jikinta ta maida wadannan jikinta har rawa yake,

Tana shigowa falon sukayi ido hudu da hajiya, ta qara gimtse fuska,

'Yauwa kin kyautawa kanki tunda ke taurin kan tsiya ne dake bakyajin rarrashi xo ki fara gyaran gidannan, lungu da saqo duk sai kin gyaramin, kuma keda fita gidannan ba yanxu ba sai na axabtar dake tunda kika bata min rai, sai kinyi dana sanin haduwa dani. 6

Maxa kafin kiftawa da bismillah ki fara gyaramin wannan gida koda kuwa xaki kai safe kina aikin ban damu ba.

*

El'mustapha ya shigo dakin dauke da laptop a hannunsa, farin cikin dake dauke a fuskarsa baya misaltuwa.

Ya kalli inda jiddah ke xaune tana shan Golden morn dauke da murmushi a fuskarsa,

Farin cikin menene haka a tare da kai?

Yace albishirin ki,

Goro fari qal ta bashi amsa cikin murmushi.

Dr Aiman Merah ya turo saqo, nan da kwana biyar xamu je Germany, ga address nasa da komai ya turo yan da xamu same sa.

Jiddah ta ajiye Cup din hannunta tana kallonsa cikin murmushi.

Shikenan el'mustapha yanxu sai ka kwantar da hankalinka abinda kake nema ka samu ka daina hana kanka barci kullum kana kan wannan laptop din.

Ya xauna kusa da ita yana fadin, idan ban damu dake ba wa kike son na damu da lafiyar sa jiddah?

Ta shafi gefen fuskarsa tana murmushi,

Ina son ka el'mustapha, kayi qoqari a kaina, ka nuna min kulawa da soyayya, a xaman da muka yi idan akwai inda na kuskure Ma ka yafe min.

Kallonta yayi cikin ido jiki a sanyaye, yace babu jiddah in Ma akwai na yafe maki har abada.

Ga mamakin sa sai ya ga ta dauke fuska gefe tana share hawaye,

Yace meke damunki jiddah, why the tears? Are you not happy?

Ta juyo tana murmushin yaqe, gabana ke faduwa el'mustapha, ina jin tsoro.

Tsoron me kuma ya tambaya bayan ya jiye abinda ke hannunsa,

'Wannan aikin na qafar kuma ga haihuwa.

Ya janyota xuwa jikinsa yana shafa bayanta a hankali cikin kwantar da hankalinta da kalamai masu sanyi.

Gobe xanje na fara shirye shiryen tafiyar ta mu, duk abinda kike buqata ko akwai abinda babu cikin kayan baby you let me know.

Tace komai akwai, amma ina son ganin mama, hajiya da abba inda hali sauran families ma duka.

Ya tsare ta da idanu batare da yayi magana ba amma xuciyarsa bugawa take.Shiru yayi bai qara magana ba, ya tashi xai bar dakin, +

Tace ina kuma xaka je yanxu, nayi tunanin xaka kwanta ne,

Ki jira ni yanxu xan dawo, akwai wani magani da likitan ya rubuto ki fara amfani dashi kafin muje, bana so kiyi skipping ko wace rana na kwana bakwai ne.

Ta gyada kai tana kallonsa, a dawo lfy ka kula da kyau kasan dare ne fa.

Yace dan sanda na tsoron dare ne jiddah? Yanxu xan dawo da yardar Allah, ya juya ya fice.

Tabi bayanshi da kallo kafin ta sauke numfashi a hankali tana kallon tsinin cikinta.

Ko menene aciki Allah ya raya shi, Allah ka bata ladan wahalar da tayi da cikin ya kuma albarkaci abinda ke ciki.

Tana xaune taji sallamar banan ta shigo dama taga fitar el'mustapha,

'Anty jiddah munyi waya da kaka tace xata xo duba ki gobe, tayi fama da rashin lfy ne shiyasa bata sami xuwa ba.

Murmushi kawai jiddah tayi,

Allah ya kawo ta lfy,

Banan tace amin tana qoqarin tashi,

'Yauwa hado min tea ki kawo min, nasha golden morn bai ishe ni, yunwa kuma nake ji.

Ko na kawo maki abinci mai nauyi ne?

Aa bani ruwan tea din dai, idan da sauran cake din da anty ikram taxo dashi daxu kawo min.

Banan ta juya ta fice, jiddah ta bita da kallo har yanxu ta rasa gane dalilin da ya sa el'mustapha keda feelings akan yarinyar duk da yana boye mata.

Ba abinda banan xata nuna mata, komai tafi banan illa lafiyar qafafu yanxu, ko saboda qafafun ne el'mustapha ke neman ta, ta saki uban tagumi bayan ta fada cikin tunani mai xurfi.

Har el'mustapha ya shigo dakin bata sani ba, xama yayi yana tabata,

Jiddah..... Ya kirata da qarfi,

Tayi firgigit tana kallonsa,

Yaushe kadawo? Ya bata fuska yana kallonta bayan ya ajiye ledar dake hannunsa,

Meke damunki haka, wane irin tunani ne tun daxu ina magana baki ji ba,

Wlhy ban sani ba,

'Wannan tunanin da kike if d condition becomes worse baxan taba yafe maki ba, kece kika ja komai ina qoqarina na ganin na kaucewa duk abinda xai saka ki damuwa kamar yanda likita ya fada.

Ba abinda xai faru El'mustapha, baxan taba Ma abinda xaka qi yafe min ba, kayi haquri please.

Suna haka banan tayi sallama amma bata shigo ba sai da jiddah ta bata umarnin haka.

Ta gaida el'mustapha ciki ciki ya amsa mata, kwanakinnan bata san meyasa ya canxa mata ba duk da aikin da yake saka ta duk ya daina gaisuwar ta Ma da kyar yake amsawa, kuma ta damu sosai, tana ji kamar xata tambayesa ko tayi masa laifine, ba fuskar yin hakan. 1

Ta sunkuya a hankali ta ajiye cup din tea din a gaban jiddah, tare da bowl din da ta xubo cake din.

'Anty jiddah xanje na kwanta bakya buqatar komai ne,

Babu Allah ya tashe mu lfy,

Tace amin, ta juya a sanyaye ta fice bata san meyasa ta damu da el'mustapha ba, bata san meyasa ta kasa cire sa a xuciyarta ba duk da tana da Islam. 1

Kallon abinda banan ta ajiye a gabanta yake kafin ya dube ta,

Ba dai wani abin xaki qara ci ba jiddah,

STORY CONTINUES BELOW


'Naji ban qoshi ba ina jin wata yunwar,

Ya xaro ido yana kallonta,

Ke jiddah da daren nan fa kika ci tuwo, kika ci farfesu, kika ci pizza tare da twins, sannan kika sha golden morn duk bai ishe ki ba sai kin dora da tea harda cake Ma.

Ta dauki cup din tana juya spoon tace ban qoshi ba el'mustapha har yanxu ina jin yunwa,

Yace are you ok?

Ta gyada kai kafin ta kai tea cup din a bakinta,

Tace har xance ka biyo min da ice cream ma saboda ba waya hannuna ne.

Ya tashi yana fadin wannan xaqi da sanyi da kike sha yayi yawa, koma kin kira baxan biyo dashi ba.

Tayi murmushi bayan ta gutsira cake din tana fadin kanaso na haifi baby da rowa, daddy ya hana mata shan ice cream,

Whatever dai ya fada yana xare doguwar rigar dake jikinsa,

Ya kwanta yana fadin ke nake jira ki gama wannan ciye ciyen ga drugs din ki.

Ta gyada kai tana kallonsa, ya lumshe idanuwansa kafin ya juyo yana kallonta,

Sorry na manta abba ya kira kafin mu tafi xasu xo shi da hajiya,

Tace to mama fa, yaushe xata xo, ko ka kaini na ganta muyi bankwana.

Kuyi bankwana sai kace mai barin duniyar?

Tace dama xan tabbata a cikin tane idan ban barta ba, Allah kadai yasan gawar fari, sai kuma tayi murmushi ganin ya xuba mata idanuwa yana kallonta,

Su aryan suna son banan kuma ta dace da rayuwar su el'mustapha, hankalina yafi kwantawa da ita akan duk wacce xaka kawo Bay....... Ya katse ta, 1

Is ok pls, kada ki batamin rai da daren nan, ya juya mata baya.

*

Ana gobe xasu bar garin, sai fama shirye shirye suke,

A tafiyar harda hajiya, anty yusrah da banan duk el'mustapha ya dauki nauyin xuwansu.

Twins xaa barsu tare da anti ikram saboda skul.

Yan uwan jiddah Ma wannan karon sunxo sun mata addua sosai tare da bata kudi kacokan ta miqawa el'mustapha su ya saka mata a account din su twins.

Banan na xaune tana shafawa jiddah magani a qafa, kallon ta tayi kafin tace...

Banan ina ji ai kin shekara da gama School yanxu ko.

Anyi shekara anti jiddah watanni kadan ne babu a ciki,

Jiddah tace nayi nayi dake ki nemi admission ki fara xuwa skul kinqi, kina da damar yin karatun amma kina wasa, ko kina nufin haka xaki tamin bauta kiqi karatu har kixo kiyi auren a haka?

'Anty jiddah karatu a wannan lokacin yanxu da kike a... Jiddah ta katse ta,

Idan ta nice wallahi bana cikin matsala, I can take good care of my self sannan ga el'mustapha Ma kina ganin komai shi yake min, idan baya nan kece, ke kuma yanxu idan bakya nan xan maida Inna ta dawo aiki nan ne ta barma su saratu na cikin gida, ba abin damuwa bane, tuntuni nake maki mgn akan karatu.

'Anty jiddah ko naje makaranta baxan iya karatu ba Allah ya gani xan ta tunanin halin da kike ciki ne, kibari idan kin haihu lafia kin sami sauqin qafafunki xan koma makaranta. 3

Jiddah tayi shiru tana kallon yanda banan din ta hade fuskarta, murmushi tayi tana fadin,

Aure xakiyi banan, Allah kadai yasan mijin ki tsakanin Islam da El'mustapha, bana son saboda amfanin kaina ki tauye naki haqqin, ki tashi ki gina taki rayuwar ki kama abinda xai taimakeki ranar da babu ni.....

STORY CONTINUES BELOW


Jikin banan ya dauki rawa, maganin dake hannunta ya subulce ya fadi daga hannunta, abu biyu a kalaman jiddah da nayi matuqar tsorata ta,

_' Allah kadai yasan mijinki tsakanin Islam da El'mustapha, ki kama abinda xai taimake ki ranar da babu ni_.

Me kike nufi anti jiddah meyasa kike wadannan kalamai masu tsauri da basu da dadin sauraro.

Jiddah tace dole ne na sama maki future mai kyau ki dandana xaqin ilimi da rayuwar aure mai kyau kafin Allah yayi hukuncinsa a kaina.

Hawaye suka cika idon banan, jikinta yayi sanyi matuqa,

'Dan Allah anti jiddah kiyi shiru ki daina gayamin irin wadannan kalaman, xuciyata da kwakwalwata baxasu jure ba, dan Allah ki daina.

Mutuwa tana kan kowa banan, ni ba nace maki xan mutu bane ina nuna maki halin rayuwa ne....

Tayi shiru sakamakon jin banan din ta fashe da kuka mai tsanani, ta xuba mata idanuwa tana kallonta cikin mamaki,

Kuka kike yi banan?

Idan kinyi kuka yau, el'mustapha yayi kuka, twins sun yi kuka waye xai rarrashi wani, keda nake so na bawa amanata da ta ya'ya na, ki basu tarbiya irin taki.

El'mustapha yana sona sosai, irin son da baxan iya misalta maki shi ba, ki riqe min el'mustapha banan bana son rashina ya tagayyara shi, bana son abinda xai dagula masa lissafi, ina son shi yadda yake sona, naso na cigaba da rayuwa d...... Banan tayi saurin toshe mata baki tana kuka tana girgixa kanta.

Bafa ciwo ne mutuwa ba, sai ni na mutu yanxu ko anjima koma gobe na barki, meyasa kike min haka ne anti jiddah.

Dariya sosai jiddah tayi tana fadin,

Wasa nake maki banan ina so naga qarfin imanin kine, ki tayani da addua, tare xamu dawo nayi rayuwa cikin ya'yana naga auren banan da Islam, na raini abinda ke cikina na ganni akan qafafuna ina rayuwa tare da el'mustapha cikin farin ciki, dan haka maxa ki share hawayen wasa nake maki.

Banan ta soma share hawayen amma har lokacin jikinta ba kuzari, ta dubi jiddah da ta maida kallonta kacokan akan TV cikin kwanciyar hankali babu wata damuwa a tare da ita, samun mace kamar jiddah a xamanin nan sai an tona, ina alfahari dake anti jiddah Allah ya baki lfy ki dawo cikin ya'yan ki, na sami rayuwa mai inganci tare da ke.

Sanda el'mustapha ya dawo daga kaisu twins inda anti ikram kallonsa jiddah tayi tana murmushi,

Har nayi missing din su kamar kaje ka dawo min dasu.

Ya nufi toilet yana fadin, me xai hana idan kina so a dawo da su yanxun nan kuwa,

Murmushi kawai tayi ya shiga toilet din bai jima ba ya fito yana kallonta,

'Anty ikram ta bada saqo a baki amma na manta dashi a mota idan na fita xan dauko maki,

Tace menene ta bada a kawo min?

Nima dai ban sani ba, abu ne acikin Leda, ya dan dube ta anty yusrah ta aiko kayan nata kuwa.

Tun daxu, suna falon ka,

Ya xauna daf da ita yana fadin, na kusa angwancewa jiddah, ki haihu na huta haka, nayi ta haquri, ko babu lafiyar qafafun I can manage amma Allah yasan abinda ke xuciya ta I need you.

Taja kunnensa tana murmushi, ban san yaushe el'mustapha ya dawo haka ba, idan munje sati nawa xamuyi ne?

Ana maganar watanni kina maganar sati, Allah ya bamu nasara a wannan aikin naki jiddah.

Amin ta bashi amsa, tace ka dauke ni pic da wayarka el'mustapha, xan riqa tuna wannan wheel chair din a duk lokacin dana kalla, baxan taba mantawa da ita ba.

Ya dauki wayar yana ta daukar ta, wani suyi tare wani tayi ita kadai.*

'Washe gari jirginsu ya daga xuwa Germany,

Satin su biyu acan, an dora ta akan drugs kafin a tashi mata tiyata, sosai dr merah ke kula da ita, tun kallon farko da yayi wa qafar ya gano matsalarta.

Amma bai masu bayanin komai ba kuma ko el'mustapha ya tambayesa akwai wata matsala sai dai ya daga masa hannu, abinda ke damun el'mustapha kenan da dr merah shi kam ya rasa gane qarfin mulkin wannan mutumin ya fiye ji da sarauta kamar a gidansu aka farata.

An saka date din da xaa Ma jiddah aiki, tun da el'mustapha ya kira Nigeria ya sanar da yan uwa banda addua ba abinda suke.

Wani abin mamaki, haihuwar taxo dai dai da ranar da xaa yi mata aikin, tun wayewar garin ta tashi da naquda gadan gadan.

Tun tana cijewa kada el'mustapha ya gano sai da ya gane,

Da kansa yaje ya kira dr merah, halin da suka same ta kuwa gwani ban tausayi.

Batayi wata doguwar naquda ba ta haifo santaleliyar d'iyar ta, jawur da ita kamar jiddah, sai dai gabaki daya yarinyar kamannin twins ta dauko illah dai tafisu hasken fata ne.

Suna tsaye tare da jaririyar suna kallo aka fito da jiddah xaa shiga aikin da ita,

El'mustapha ya miqawa banan jaririyar da sauri ya nufi jiddah, haka Ma banan tabi bayansu da sauri tare da hajiya,

Me na haifa el'mustapha?

Mace ce jiddah kyakkyawa kamar twins, ya fada yana murmushin qarfin hali yana shafa kanta.

Ta juya tana kallon hajiya da kyar ta iya cewa nagode hajiya...

Sai kuma ta dubi banan dake dauke da jaririyar.

Nasan xan fito lafiya insha Allah na same ku, amma duk da haka ki kulamin da ita banan, ki kula da su twins ciki kuwa harda *EL'MUSTAPHA*, cikin kuka banan tace,

Anti jiddah El'mustapha yayi babba da na kula dashi, ke kadai xaki iya kula da shi, ke kadai xaki iya bashi farin ciki irin wanda kike so ya dauwama aciki, dan Allah kidaina wannan maganar xaki tashi lfy.

El'mustapha ya sunkuwa ya sumbace ta jikinsa na rawa, yasa hannu yana share mata hawaye,

Xafin ciwo ba mutuwa bane jiddah, jikina har ynxu bai bani xakije ki barni ba xamu rayu tare har abada mu kula da ya'yan mu, you will get well soon Jiddatulmusty and El'mustapha is for only you jiddana, bana buqatar kulawar kowa sai naki, ya janyo hannunta ya hada qaramin yatsansa da nata,

Yace mun qulla, idan har akayi nasara akan aikin aka fito dake lfy I promise you kome kike so a duniyar nan xan maki shi indai baifi qarfina ba, 3

Tayi murmushi tana qara riqe mararta dake ciwo,

Idan kuma na mutu fa,

Baxama ki mutu ba jiddah stop saying dat rubbish ya bata ransa sosai, ta shafi fuskarsa tana murmushi,

Sorry Musty na, pray the best for me, xan dawo na cigaba da rayuwa da kai ina matuqar son ka.

Yace yauwa jiddatulmusty, ya sunkuyawa dai dai kunnenta yana rada mata addu'o'i da xatayi,

Tayi murmushi tana nanata addu'ar da ya gayamata a xuciya cikin hope din xata rayu tare dasu.

Haka aka jata aka shiga da ita, banda addua babu abinda suke.'Hajiya dan Allah kiyi haquri ki maidani titin da kika dauko ni ko ki bude min wannan gate naki na fita da qafafuna,
2

Hajiya Mariya ta tsaida cin Apple da take tana kallon uwani a wulaqance,

Tace kin gama gyara kitchen dinne,

Uwani tace da ban gama ba xaki ganni nan ne, har toilet din da kika ce na wanke, duk dakunan gidannan na gyara, ni nagaji dake nagaji da ganinki ki barni nayi tafiyata. 1

Kallonta take batare da mamaki ba xaman da sukayi da uwani ta fahimci yarinyar bata da tsoro gurin maida magana sai kaje dukanta ta soma baka haquri amma bakin baxai yi shiru ba ta rasa wace irin yarinyace wannan,

Tace kije tsakar gidannan shima duk sai kin share sa'anan ki dawo.

Uwani ta gyara tsayuwarta, hannayenta akan qugunta kerere take kallonta,

Nifa bamai aikin ki bace, ban taba yiwa kowa bauta ba sai ke, kibarni nayi tafiyata, na rasa me kike nufi dani, baki gaji da ganina bane.

Tana ganin Mariya ta tashi ta fita da gudu da tsintsiya a hannunta, ta daga murya tana fadin,

Kin sato nine kiyi kudi dani, nafi qarfin ki ko wanda xai yankani kisha jinina na kalleshi sai ya girgixa, tun da naxo gidannan ban taba ganin kowa yaxo ba sai kace mayya, ku.... Tayi shiru sakamakon ganin hajiyar ta fito da wata xungureriyar bulala, ba shiri uwani ta sunkuya tana shara, 2

Tace me kike cewa uwani, maimaitamin banji da kyau ba,

A sanyaye uwani ke kallonta,

Hajiya tunda baki ji mgnr ba abarta kawai ta wuce ta sunkuya da sauri tana sharar.

Dogon tsaki hajiya taja ta juya,

'Na daukowa kaina jaraba wannan shegiya ni ta isheni a gidannan, sai na gama axabtar dake xan fiddaki.

Uwani ta nufi gate din bayan ta ajiye tsintsiya, ta soma kiciniyar bude gate din amma ta kasa kusan kullum sai ta gwada yin hakan, ta leqa ta gate din tana fadin,

Wayyo a taimakeni, akwai wani a kusa ne, wata mata ce ta sato ni, a taimakeni.

Shiru bataji alamar motsin kowa ba,

Ta tsugunna tana leqe ta qasan gate yanda xata ga mai wucewa da kyau,

Kicibis idanunta na sauka akan wani qatoton kare baqi wulik sai fiddo harshe yake, taja da baya da sauri hade da dafe qirjinta saboda yanda yake bugawa, yanda taga Karen yana huci kamar xai cinyeta, aikuwa da ya tona mata asiri idan ya rabata da duniyar saboda baqin ciki ne xai mata. 1

Ta tashi ta cigaba da shara, tana gamawa ta shiga gidan,

Mariya.... Mariya take kiran hajiya🤔

'Na gama kixo ki sallameni idan ba haka ba wlhy sai in qona gidannan, nifa banda mutunci baki sanni bane sai na nuna maki, tun muna mu biyu kixo ki fiddani cikin wannan gidan naki mai wari da qaxanta, ashema dadin komai baa ci, ya'yan ki ma cikin wahala suke, tuni na gano kina daya daga cikin mutanen dake min baqin ciki da jin dadin duniya shiyasa kika kawo ni gidannan, to baxan xauna ba, hajiyata nake so ehe, itace ke sona bata min baqin ciki tana tausayina.

Tayi shiru tana saurare, bata ji an amsa ba kuma babu alamar motsi a gidan, ta lallaba a hankali ta isa dakin hajiya Mariya.

Ta xare idanu lokacin da ta tsinkayota kwance ta ware qafafunta tana tura wannan abun tsakanin cinyoyinta.

Jikin uwani ya dauki rawa ta juya da sauri tana maida numfashi.

Ita kam nata taba ganin musiba irin wannan ba, kaico da wannan rayuwa ta matar nan, ta xauna ta buga tagumi tana hawaye. 2

STORY CONTINUES BELOW


Wai ni meke faruwa dani ne, me nakeyi xaune a cikin wannan gidan da wannan matar, yaushe xan barshi naje ga iyayena, ina so na roqesu gafara, nayi aure na da el'mustapha na xauna gidan mijina cikin jin dadi, tasan yanda jiddah take da haquri xata barta ta auri mijinta tunda tana sonta kuma jiddah bata mata baqin ciki da jin dadi. 3

Allah na tuba kuskuren da nayi a baya, inda ban tada hankalina ba da yanxu ina can ina cin samosa, ina cin kayan dadi, ina sa masu aiki sumin aiki, amma yanxu nice ma mai aikin, kai jamcy ta cuce ni, surry tana sona, dama hajiya da abba sunce duk na cutar da jiddah Allah baxai barni ba, gashi kuwa, na shiga uku ni uwani Allah ka yafe min, ta soma kuka.

Bayan minti ashirin ta qara tashi suduf suduf taje qofar dakin tana leqen hajiya Mariya.

Tana gani tana kallon wani abu a waya tana shafa jikinta,

Uwani ta rumtse idonta, ta qara budewa dai dai lokacin matar ta sauko daga saman gado, tana kallo ta fito da wasu kaya da alama su xata saka kafin ta nufi toilet tana waqa da wani yare da ta kasa fahimtar ko wane iri ne.

Kayan da ta ajiye akan gado tabi da ido tana kallo, sadaf sadaf ta shiga dakin ta daga rigar tana kallo doguwar rigace mai kyau.

Wani tunani uwani tayi ta ajiye ta fita da sauri tana fadin,

Matar nan idan ban nuna mata koni wacece ba baxata barni na fita ba,

Bata jima ba ta dawo dauke da scissor a hannunta, daga rigar tayi ta soma yankata a tsaye tana mata tsaga ta ko ina yanda rigar baxata moru ba,

Tana gamawa ta ninke yanda ta ganta ta ajiye ta fita da sauri tana numfashi.

Binni binni take dubawa tagani ko ta fito, tana tsaye gurin taga fitowar ta xindir kuwa, ta bude bakinta bayan ta dora hannunta akan bakinta,

Shegiya yar iska, tambadadiya, tana gani ta bude wani qoqo ta laqato wani abu a dan yatsanta ta ware cinyoyinta tana shafawa.

Uwani ta saka a xuciyarta sai taga ko menene, ta koma ta xauna bayan minti talatin ta qara dawowa har lokacin bata shirya ba amma ta saka pant da bra, tana kallon sanda ta janyo rigar xata saka sai da gaban uwani ya fadi.

Cike da mamaki take kallon rigar, ta soma tunani,

Uwani.... Uwani ta soma kiranta da qarfi,

Saboda tsananin tsoro da firgici Sam uwani ta manta Ma a bakin qofar take tsaye, sai ta soma amsawa da qarfi,

Hajiya Mariya ta juyo cikin mamaki tana kallon qofar,

Tsayuwar me kike yi anan,

Ta rikice aa dama xan shigo ne ince maki nagama sharar na kwashe Ma, cewar uwani tana sosa kanta cikin washe baki😁

Kece kika bata min kaya, yaushe Ma kika shigo dakin?

Ni😯, yaushe bani bace, kinsan bana shigowa ai, haba hajiya sai na shigo dakinki bada ixini ba, cab ai ni bana xuwa dakin mutum saboda gujewa ganin mugun abu, ni banxo ba dan Ma karna ga kayan baqin ciki.

Tayi shiru tana kallonta kafin tace wannan scissor din na hannunki na menene, ni xaki Ma qarya.

Uwani ta xare idanu, ta hadiye yawu da kyar kafin ta sami abin fada,

Hajiya tsaya kiji dauko shi nayi yanxu inxo in tambayeki xan iyawa flowers dincan na waje aski, naga leaves ya masu yawa.

Aski kuma? Me kike nufi kina son raina min wayo ko, wlhy sai kinyi dana sani bata min wannan rigar, kinsan daga inda na siye ta kuwa?

Uwani ta girgixa kai tana kallonta,

Saboda ina sauri ana jirana ne, amma kisa a ranki yau baxakiyi barcin kirki a gidannan ba xan ta axabtar dake ne sai na fanshi kudin ta a jikinki, ta juya a fusacce ta ciro wata rigar,

Uwani na tsaye a gun kamar statue har ta shirya ta dauki key da wayarta ta fice tana amsa waya.

A hankali ta sauke numfashi, koma me xaki min baxai hana gobe na rama ba har sai kin gaji kin sallameni, yar iska kawai mai yin lalata.

Ta matsa tana kallon abinda taga ta shafa tsakiyar cinyoyinta,

Qilama iskanci xataje yi, gobe baxaki qara ba, yaji xan xuba masa, in kin dawo kin hanamin barci kika shafa kema na hanamiki barci, do me I do you man no go vex, if you touch me I touch you man no go vex, if you beat me you go suffer man no go vex, ta fita ta dauko yajin taxo ta xuba aciki ta gauraye ta fita tana dariya.

*

Sai safa da marwa yake a corridor a asibitin, hannunsa goye a bayansa,

A hankali lips dinsa ke motsawa wanda idan baka qura masa ido ba baxaka taba ganin motsin su ba,

Banda addua babu abinda yake, gabansa sai tsananta bugawa yake,

Anti yusrah na kishingide barci ya dauke ta ita da hajiya, tun jiya da dare basu runtsa ba,

Jaririyar kuwa kuka take banan na rarrashinta amma kacokan idanunta na kan el'mustapha, duk wani feelings akansa ya dawo mata batasan dalili ba,

Kukan jaririyar ya saka el'mustapha juyowa, carab suka hada ido, ya bata fuska bayan ya dauke kansa da sauri,

Ya qaraso ya karbi jaririyar, a qirjinsa ya rungumeta sosai yana jijjiga ta amma sai kuka take ba kakkautawa,

Yunwa take ji ya sani, lips dinshi ya tura mata a baki ta fara tsotsa da sauri.

Ya qura mata ido yana kallonta, son yarinyar na shiga cikin jikinsa har yafi wanda yayi wa twins a baya, duk kukan nan da take ba ko digon hawaye a fuskarta, bai san sanda dariya na subulce masa ba, aikuwa ta saki wani kukan da sauri ya maida lips din yana tafiya a hankali gurin wasu nurse's ko akwai wani taimako da xasu masa na madarar da xai siya mata.

Bai jima da tafiya ba ya dawo lokacin har tayi barci tana kafadarsa,

Ganin hajiya ta tashi ya miqa mata ita, ya juya yana kallon banan cikin lalabar aljihunsa,

Kudi ya ciro ya bata tare da wata takarda,

Dai dai lokacin Dr Aiman Merah ya fito tare da wasu nurses a bayansa fuskar nan tasa a daure kamar kullum.

Bai gayawa banan kome xata siyo ba ya juya da sauri gabansa na faduwa ya tunkare sa, su hajiya ma duk suka taso bayan ta goya yarinyar.


Hannu dr merah ya daga masa wanda ya saka el'mustapha tsayawa cak cike da mamaki,

Yana kallo fadawa ke cire masa rigar aikin da ya shiga da ita kafin su saka masa doguwar alkyabba, suka nada masa rawanin sa cikin sauri, nan take ya fito yarima merah.

El'mustapha na tsaye cikin haushi wanda ke ta lafiyar matarsa ina ruwansa da wata sarauta, Merah ya soma tafiya a hankali fadawa suka take masa baya tare da wasu nurse's,

Alama suka Ma el'mustapha da ya biyo bayan su,

Ba yanda xaa yi Dr Merah ya fito tiyata ko duba patient ya tsaya yima bayani batare da ka same shi office na shi ba koda kuwa mutuwa ce, bai damu ba, a ganinsa mulkinsa da sarautar sa duk sun xube.

Suna shiga office din duk suka fice ya rage el'mustapha da Dr merah.

Tsaki yaja a xuciyarsa kusan minti goma da xamansa a office din amma yaqi ya masa mgn, yana son sanin condition din jiddah is d work successful or not amma mutumin yaqi magana saboda mulki.

El'mustapha ya xuba mashi idanu hade da sakin uban tagumi yana kallon ikon Allah,

Abinda el'mustapha bai gane ba idan xasu shekara a gurin batare da ya fara tambayar dr merah lafiyar jiddah ba baxai taba gayamasa ba, halin sa ne, a jinin sa yake, ka fara tambayarsa kafin ya bama bayanin komai.

Rashin sani ya saka el'mustapha xuba mashi idanu yana kallonsa yaga qarshen girman kan nasa.Fiye da minti goma xaune a wurin ba wanda yayi magana a cikin su.

Tashi el'mustapha yayi ya fice daga office din a fusacce, Dr Merah yabi bayansa da kallo yana tabe baki.

Yana fitowa hajiya da anty yusrah suka tare sa,

Ya akayi ne el'mustapha? An nasara ko?

Ya bata fuska yana Jan tsaki mai cike da takaici,

Taya xan sani wannan likitan mai baqar sarautar tsiya yaqi yamin mgn ballantana naji halin da jiddah take ciki.

Hajiya tace oh Allah munga sun fito da ita a lullube, hankalina ya kasa kwanciya el'mustapha, kayi haquri kaje ka qara tambayarsa meke faruwa da yar'mu.

El'mustapha ya shafi sumar sa, baxai je ya qara tambayarsa ba ai komai mulki da sarautar likita baxaiyi akan patient din sa ba, sai ya koma fada yayi wannan mulkin amma baa asibiti ba, ya furxar da iska a bakinsa yana kallon hajiya.

Ina suka je da jiddah,

Wani daki suka ajiye ta cewar hajiya tana tafiya suna biye da ita a baya.

Ta window suke kallonta, baxasu iya gane komai a tare da ita ba kasancewar tana nesa dasu sosai.

Indai tana raye alhamdulillah, ba dole sai ta rayu da qafar ba, xan iya xama da ita a hakan, ya juya ya soma tafiya a hankali, anty yusrah tabi bayansa.

Hannunsa ta riqo bayan ta kira sunansa,

Juyowa yayi yana kallonta ga mamakinta idanunsa cike suke da kwallah,

Tace meyasa el'mustapha, jiddah xata tashi insha Allah kuma da qafafunta, ganinta haka kwance ba shi xai saka mu cire tsammanin daga gare ta ba, be a man pls, idan kai da kake namiji kayi kuka mu kuma muyi me?

Yace kin lura da jiddah bata motsi anty yusrah, baki ga yanda suka ajiye ta ba kamar gawa, meyasa suka ajiye ta anan, just tell me anty yusrah me suke nufi da jiddah, baxan yarda ba idan suka kashe min mata.

Gabanta ya tsananta faduwa, taja hannunsa da suka suka fito cikin asibitin ganin yanda mutane suke kallonsu, juyo dashi tayi hade da saka tafin hannuwanta ta riqo fuskarsa tana kallon sa.

Me yake damun ka el'mustapha? Yaushe ka canxa ka dawo haka mai xafin rai, da nasan jiddah da xafin rai da nace daga ita ne amma jiddah kowa ya san ta da sanyin rai, idan mutuwa jiddah tayi meyasa xakayi qarar su, meyasa baxakayi tawakkali a xuciyar ka ba, meyasa kake tunanin baxaka iya rayuwa sai da jiddah ba, ka manta wanda yayi ta yayi mu ya fimu son ta, baka tunanin lahirar ta fiye mata wannan duniyar da duk abinda ke cikinta, ko kana nufin baxaka yi imani da abinda Allah ya yanke akan ka ba, mama ta mutu ka haqura ballantana jiddah, wace irin shaquwa ce tsakanin ka da ita wacce bakayi da mama ba?

A hankali ya sauke ajiyar xuciya bayan ya janye fuskarsa daga riqon da tayi masa, kallon ta yayi,

But why wannan likit..... Tayi saurin katse sa,

Is ok ni xanje na tambayesa, wait for me, ta juya tana tafiya, binta yayi da idanu jikinsa a sanyaye kafin ya nemi guri ya xauna, mutane yake kallo dake shige da fice.

Assalamu Alaikum, tayi sallama cikin muryarta mai sanyi,

Batare da ya dago ba ya amsa sallama cikin isa da taqama,

Bata jira ixini ba ta shiga ta xauna tana kallonsa, duk abin nan da take ko sau daya bai kalle ta ba, ya maida hankali sosai akan laptop dinsa,

Ta tabe baki bayan taja numfashi,

Tace sannu da aiki, naxo ne kan maganar patient din da muka kawo Hauwa Ahmed, ko a wane hali take ciki.

Kallo daya yayi mata ya maida hankalinsa kan abinda yake yi batare da yayi magana ba kuma bashi da niyar yin haka.

STORY CONTINUES BELOW


Ta tsare sa da idanu cikin takaici, meyasa maxa masu kyau da mulki suka fiye wulaqanci da taqama, kamar ba wanda take magana da shi ba, tana da xafin xuciya ba kamar el'mustapha ba, ta bata fuska sosai tana fuskantar sa,

Allah yasa wanda nake magana dashi is not dump, ba kallonsa naxo yi ba ko son xama dashi halin da yar uwata take ciki nake son sanin.

Murmushi yayi amma bai dago ya kalle ta ba, su dai mata halin su daban ne, wannan da xata gane da ta daina daga masa murya kada ta fasa masa dodon kunne, dole xai kulata cos yana respecting mace ko ya take kuma a duk inda take.

Kallon ta yayi yana ajiye laptop din,

Yace Hauwa is ok, xata sami sauqi insha Allah, addua kawai ake buqata da aikin da akayi mata domin ni baxan iya tada ta tayi tafiya ba sai da ikon Allah, but am sure the work is successful.

Yusrah ta saki murmushi tana sauke ajiyar xuciya,

Yace matsalar har yanxu bata farfado ba amma wannan ba babbar matsala bace, nayi tunanin kamar alluran da akayi mata ne basu sake ta ba, amma mgnr gaskiya idan tayi awa biyar a hakan bata motsa ba sai dai ayi haquri,

Gabanta ya tsananta bugawa, hankalinta ya tashi,

Tace meyasa Dr, dan Allah kaje ka duba ta a yanxu kada mu rasa jiddah.

Ko naje ba abinda xan iya mata a yanxu tunda bata farfado ba, tun da aka shiga aikin da ita na lura tana jin jiki, akwai nurses tare da ita da ta motsa xasu sanarda ni, just pray for her domin shine abinda take buqata, nan da awa biyar idan bata farfado ba sai wani iko na Allah.

Jikinta yayi sanyi farin cikin dake xuciyarta ya kau, ta tashi a hankali cikin dauriya xata fice ya tsaidata,

Wani rubutu yayi akan takarda ya miqa mata,

Asiyo su yanxu because of the child xaa yi mata amfani da su, sai a bawa wata nurse ta hada mata,

Tace meyasa sai nurse xata hada mata, kai baxaka yi bane? Ta fada cikin son gwada shi taji,

Murmushi yayi batare da ya kalleta ba, yace ba abin damuwa bane, ki kawo xan hada mata, ai d'a na kowa ne beside Ma am here to safe a life,

Duk mgnr da yake fuskarsa a sake, wanda baisan halin sa bane yake masa kallon mai girman kai da mulki kamar yanda mutane suke fada, dr merah yana da sauqin kai da son mutane amma mulki da sarauta sun rinjaye shi wanda mutane ke masa wani kallo daban.

Ta juya ta fita batare da tayi magana ba,

Ya kishingida hade da lumshe idanuwansa yana tuna halin da jiddah take ciki, yana ji itace mace ta uku da ya taba tausayi a rayuwarsa bayan Dr Fulani Gafai.

Yayi saurin kauda tunaninsu a xuciyarsa ta hanyar janyo wayarsa yana laluben number Gimbiya Afiya.

*

Alamar shigowa gidan taji, tana leqawa ta window ta tsinkayo fitowar ta cikin motar tare da wata yarinya da baxata wuce sa'an ta ba.

Hajiya Mariya bata manta da abinda uwani tayi mata ba cos sosai ranta ya baci da yanda ta lalata mata riga.

Uwani ta dauke kanta tana hade fuska cikin tambayar,

Wacece wannan kuma, me taxo yi gidan mu?

Gidan mu? Hajiya ta maimaita tana kallon uwani, can you imagine, ta bata fuska tana fadin xo ki rage min tsawon ki anan uwani I have to deal with you,

Cikin rashin fahimta tace taya xan rage maki tsawona bayan haka Allah ya yini idan gaskiya ne ke ki rage naki mugani, ta tunxure baki tana rungume hannayenta,

Wai wacece wannan hajiya, meyasa wannan qaxamar take xaune a gidannan, ni ban san ta ba cewar budurwa.

Cikin bacin rai hajiya tace barta mai aiki ce na dauko take min wannan iskanci, maganin ta xanyi yanxu, ta shiga dakin ta a fusacce,

Uwani ta dubi yarinyar ta matsa kadan cikin shigar munafurci, tace kin shiga uku, wannan matar yar iskace ta dauko ki tayi iskanci dake, nima haka ta daukoni amma ni ba yar iska bace ban yarda ba shine taqi maidani, karki bari ta lalata ki a banxa ki fara kuka tun yanxu ta maidaki.

Budurwar taja tsaki tana ture uwani,

Tace ke dallah matsamin a jiki sai tsamin dauda kike, ai kece yar iskar ma kuma sai na gayamata.

Uwani tace to idan kin gayamata me xata min, daga kawai nace mata yar iska, to nace na qara cewa yar iska ce, kuma har dake din, tsamin dauda da nake yafiki tsabtar jikinki mai qamshi domin gurbatacce ne, maqiyiyar Allah, lalatatta mai qaton hanci, dubi bakin ta kamar na kare, qilama kwadayi ya kawo ki gidanmu, kinxo kici dadi da shegen bakin nan mai kama da...... Bata qara saba taji saukar duka a bayanta.

Kafin tayi wani yunquri ta soma jin ana dukanta da bulala ta ko ina,

Sai ihu take tana neman ceton wannan budurwar,

'Dan Allah kiyi haquri hajiya baxan qara ba, na tuba, wayyo hajiyata kixo xata kasheni ta rabani da duniyar saboda baqin ciki, ke shegia kixo ki taimakeni kixo kice mijinki ya daina dukana, yar baqin ciki to baxan mutu ba.

Tun tana magana har tayi shiru tana maida numfashi,

Hajiya Mariya ta yarda bulalar tana fadin sai na gyara ki a gidannan wlhy,

Uwani dake kwance tana nishi da kyar tace nima sai na gyara ki duk kika min sai na rama,

Har xata qara dukanta budurwar ta tare ta,

Kyaleta dan Allah a matse nake idan mun gama kixo ki daki shegia son ranki,

Kece shegia tambadadiya, ina tashi sai na karya maki wannan qugun da kike girgixawa karuwa kawai.

Basu kula ta ba suka shige rungume da juna suna shafar juna.

Suna shiga dakin suka soma cire kayansu, batare da tunanin komai ba hajiya Mariya ta dauko wannan qoqon ta debo abin a yatsa, ita Ma yarinyar ta diba kowacce ta sunkuya suna shafawa a qasan su.

Lokaci daya suka dago suna kallon juna idanunsu a waje saboda wani radadi da suka ji.....Da gudu kowacce su ta nufi toilet neman ruwa.

Hargowar da suke ya dakatar da uwani daga kukan da take, ta kashe kunne sosai tana sauraren su,

A hankali ta tashi ta nufi dakin basa nan suna toilet, tayi shiru tana tunanin ko ihun me suke haka? Qilama iskan cin ne suke, yan iska.

Sadaf sadaf ta shiga dakin, hanyar toilet din ta nufa, qofar a bude take ta leqa taga me suke yi haka ne,

Abinda ta gani ya saka ta xare ido hade da dawowa baya da sauri tana kallon qoqon da ta sakawa yaji.

Gabanta ya tsananta bugawa ta san mai hana suci ubanta yau sai Allah,

Ta dora hannuwanta duka biyu aka sai ga hawaye shar na bin kumatunta,

'Na shiga uku ni uwani, Allah na tuba ka yafe min ka ceceni,

Ta fita daga dakin da sauri, harabar gidan ta nufa tana kallon gate din gidan,

Ta rasa yanda ake bude wannan gate, ga katangar mai tsayi ballantana ta haura.

Dabara ta fado mata, xata sami mabuya ta buya idan sunxo fita da mota ta fita ta gudu, ta koma cikin gidan da sauri dakin nasu ta nufa har lokacin basu fito ba.

Ta kyalkyace da dariya tana jin wani farin ciki a xuciyarta yanxu, ta qara leqawa tana kallonsu yanda suka bada muhimmanci wajen wanken abin da ruwa, ta dora hannunta a baki tana dariya🤭,

Jakar hajiya Mariya ta bude batare da tunanin komai ba ta dibi kudi bata san ko nawa bane, jikinta na rawa ta fice daga dakin, can harabar gidan ta nufa ta boye bayan wata flower tana jiran fitowarsu, yau kam xata bar garin sai inda hajiyarta, sai murna take.

Sun dauki kusan rabin awa aciki kafin su fito kowane fuskarsa ba annuri tunanin budurwar sharrin hajiya ne ko dama da saninta, sai ta soma hada kayanta tana maida kayanta a jiki.

Kallonta hajiya tayi sheqeqe,

Tace me kike yi haka Hadixa, ba dai tafiya xakiyi ba.

Batayi magana ba ta dauki jakarta da gyalenta, hajiya ta riqo ta da sauri,

Kiyi haquri wallahi ba laifina bane, ni kaina bansan da abin haka yake ba, kuma ko da safe da naje gurin ki na saka shi lfy lau ba wannan abin, ban san menene aka saka ba, banma san wanda ya saka ba, amma kiyi haquri ki tsaya har gobe kinji.

Ko na tsaya ba abinda xan iya maki, gurin xafi yake min sosai, ina so naje gida na duba kaina,

Haba hadixa yanxu ya kike so nayi, xo ni nasan yanda xan maki ya daina xafi, nima nawa ai xafin yake amma na haqura.

Bata saurare ta ba ta fice da sauri saboda xafin da take ji, tana son taje gida ta baje gurin a iskan fanka, idan tace tayi hakan gaban hajiya baxata barta ba da jarabarta.

Fitowarta duk akan idon uwani dake labe, tayi mamakin yanda ta bude gate din kai tsaye, dama dai ban iya bane, tana ficewa uwani ta biyo bayanta da gudu ta bar gidan har tana bankade hadixa a hanya, bata damu ba ko waiwaye burinta taga ta fice daga unguwar gabaki daya.

Sai safa da marwa take tsakiyar dakin cikin tunanin ko waye xai mata wannan danyen aikin.

Uwani ta fado mata a xuciya, lallai kuwa xanci ubanki a yau domin ke xan saukewa buqatata ko kina so ko bakya so,

STORY CONTINUES BELOW


Ta fita a fusacce tana kiran uwani, shiru baa amsa ba, ta soma duba wa ko ina tana kiran sunanta,

Wayam babu uwani ba alamarta, tana fitowa harabar gidan taci karo da gate din a bude.

Taja numfashi cikin jin haushi, rufe gate din tayi ta koma cikin gida tamkar xuciyarta xata fado saboda haushi da baqin ciki, Allah ya hada ta da uwani ko a hanyane.

Uwani na barin gidan a haukace ta shiga taxi sai tasha, duk da dattin dake jikinta bata damu ba, haka ta shiga motar ana hantarar ta da kyamarta ko a jikinta illa qara baje duwawu da tayi tana fadin

Mutum kudi ya biya na biya muka shigo motar, bata gidan uban kowa bace ballantana a fiddani, wanda ke jin wari ya saka hancinsa a window ina ruwana, ta cigaba da cin biredi ta da pure water batare da damuwa ba. 2

Da yawa kallon da suke mata a motar bata da hankali, in ba haka ba wane marar hankali xai fito haka ba mayafi ba takalmi kuma cikin datti, bugu da qari cin biredi da pure water cikin maxa.

Tana gama ci ta qulle sauran biredi ta rungume abinta a qirji tana fadin,

Duniyar nan bata da tabbas idan kayi sake ayi maka sakiya, nasan mutane da yawa acikin motar nan guntun biredi nan suke jira idan nayi sake a sace min na rasa wanda ya dauka yanda ake ta kallo na haka, gwanda na rungume abina idan na tashi barci na qarasa cinyewa. 4

Sai kallonta suke suna tausaya mata qila sabuwar hauka ce, amma da uwani tasan tunanin da suke kanta na cewa mahaukaciya ce da sai ta xage su tsab😂
1

Suna cikin tafiya barci ya dauke ta rungume da biredi ta, ta kwantowa wanda ke kusa da ita a kafada, sai matsawa yake cikin kyankyaminta yana ture ta, ta bude idanunta da suka soma ja tana kallonsa,

Saboda me kake ture ni, ina ruwanka da barcina, tukunna Ma miye damuwar ka dani banda baqin ciki barcin Ma baxaa bar mutum yayi ba.

Cikin mamaki yake kallonta yace saboda me baxan ture ki ba kina kwanta min a jiki,

Tace to na kudi na biya ba, ai ba bashi bane ko kyauta.

Kudin jikin nawa kika biya ko na mota. 1

Kudin mota na biya dan haka duk abinda ke cikin motar na biya ina da haqqi akansa, in banda baqin ciki na dauko barci Mai dadi saboda me xaa ture ni a katsemin barci, wlhy aka qara tada ni barci sai dai driver ya tsaya a dokar dajin nan ayi duk wadda xaa yi, taja tsaki hade da gyara kwanciyarta. 2

Kowa shiru yayi yana kallonta, wanda ke kusa da ita yana ji yana gani ta kwanto a kafadar sa tana barci harda dan minsharinta mai nuna alamar tana cikin gajiya,

Xaiyi magana na kusa da shi ya hanashi,

Yi haquri ka barta baka san haukar nata ko na duka bane, 1

Driver dake kallon su ta mirror yace,

Malam kayi haquri kabarta dan Allah kaima da ganin yanayin ta kasan abin bai ishe ta ba, karmu xo mujawa kanmu masifa cikin wannan dajin da ta ambata qilama akwai aljannu a tare da ita.

Haka ya haqura ya barta har suka iso,

Slippers ta siya ta sakawa qafafunta tana sauke numfashi sai kallon kallo ake tsakanin mutanen dake kallonta, napep ta shiga, bata dau wani dogon lokaci ba sai gata a qofar gate din su.

Murmushi tayi cikin jin dadi, I miss home, Allah yasa kada abba yamin baqin ciki ya koro ni ya fiye fushi da riqo, taja tsaki tana bude gate din gidan.

Ta shiga tana kallon mai gadin nasu, tsaki taja ta dauke kanta tasa kai tana tafiya,

Ke... Ke... Ke ina xuwa haka, waye ke, wa kike nema ne,

STORY CONTINUES BELOW


Kerere take kallonsa,
Tace nida gidan ubana kake tambayar ina xanje, chab,

Yace 'au ashe uwani ce ai sai da kika yi magana na gane ke, ke kuma haka duniyar taxo maki da nata salon, 2

Kadai iya bakin ka, ina nan ba canxawa nayi ba, nadama kawai nayi, ta fice fuuuuuu 1

*

Awa biyu kacal suka rage daga cikin awannin da likita ya dibawa jiddah, kuma har lokacin bata farfado ba.

Gabaki daya hankalin su a tashe yake, bama kamar hajiya tayi kuka sosai kamar ranta,

'Anty yusrah duk ta jigata saboda fitinar jaririyar, madarar da ake bata taqi karba, an goyata taqi barci sai kuka,

Da kyar el'mustapha ya kalle su, wai baxa kuje gida haka bane, tun daxu nake maku mgn.

Muje gida muyi me el'mustapha, hankalin mu baxai taba kwanciya ba, cewar yusrah.

Ya karbi jaririyar hannun banan yana kallon fuskarta tayi jawur sosai, wataqila akwai abinda ke damun yarinyar take wannan fitinar tun daxu, ya bawa yusrah yana fadin,

Sister ko xakije da ita inda dan gidanki ya duba ta, ina ganin bata da lfy fa, 1

Ta karbeta tana fadin, nima nayi tunanin haka, ko cikin ta ke ciwo.

Yayi shiru baiyi magana ba, yana kallo suka fice, yunwar cikin sa Ma ta ishesa amma bashi da kuxarin sakawa cikinsa komai banda ruwan lemu tun daxu.

Dakin da aka kwantar da jiddah ya nufa, xama yayi kusa da ita ya tsurawa fuskarta ido yana kallo,

Hannunsa ya saqala cikin nasa ya matse a hankali,

'ya kamata ki tashi haka jiddah, we are ol here for you, idan kika tafi kibar twins a gurin wa, with our new baby,

Ya xubawa agogo idanu, awa kadai ya rage, ya juya yana kallonta gabansa na tsananta bugawa,

Pls jiddah, ko kadan ne ki motsa, time is going, ki bari mu rayu tare da ya'yan mu cikin farin ciki as before,

Shigowar dr merah ta katse sa, suna hada ido el'mustapha ya dauke kansa gefe,

Dr merah bai kula sa ba, kai tsaye gurin jiddah ya nufa ya soma duba ta yana kallon time,

Shi kansa hankalinsa a tashe yake, amma meyasa bata farfado ba har wannan lokacin, ya soma dubata yana examine wasu abubuwa, duk dube dubensa ya kasa gano wata matsalar a tare da ita komai is normal.

Yayi shiru yana qara duba time, 30mnt ya rage, shi kansa el'mustapha wannan karon tashi yayi har lokacin hannunsa na riqe da nata.

Duk suka yi shiru an rasa mai magana a cikinsu illah idanu da suka xuba mata kowane cike da fargaba,

Pls jiddah... El'mustapha ya fada cikin rawar murya kamar xaiyi kuka, Dr merah ya kallesa tausayinsa yake ji,

Hajiya da banan suna tsaye ta window suna kallo binni binni suke sharar kwallah,

Sunkuyawa el'mustapha yayi dai dai kunnenta, Allah kadai yasan abinda yake fada a kunnen nata, yana jin sanda agogon dakin ya buga,

Ya tsaida hankalinsa da tunaninsa cak cikin faduwar gaba, a hankali ya dago yana kallon jiddah har lokacin bata motsa ba,

Ya maida kallonsa da sauri ga dr merah idanun sa cike da kwallah,

Can't believe jiddana is death, inaji a jikina bata mutu ba xata tashi, ka qara bata awa daya xata tashi,

Magana yake kamar xautacce yana fadin xata tashi, jiddah ki tashi pls, You promised to be with me, idan kika tafi ya kike so nayi rayuwa without you, ba uwa ba uba kuma ba jiddah, miye amfanin duniyar.

Har lokacin bata motsa ba,

Dr merah ya riqo kafadarsa cikin sanyin jiki ya hada shi da jikinsa, rarrashinsa yake cikin kalamai masu sanyi,

Jiddah has gone kuma baxata taba dawowa ba, inda taje ya fiye mata nan duniyar da duk abinda ke cikinta, kuma kowane mai rai sai yaje inda taje.

Yaja hannunsa suka fito yana waiwayen jiddah shi kam ya kasa gasgasta jiddah ta tafi, baiji hakan a jikinsa ba gani yake xata tashi su cigaba da rayuwa cikin farin ciki.

A hankali ta bude idanuwanta, tana Jan numfashi da kyar,

Dishi dishi take gani kafin idanun su fara waye wa tana kallon dakin da take kwance, a hankali ta juya ta window ta tsinkayo wucewar el'mustapha yana kuka riqe a hannun Dr merah, 2

Me ya saka el'mustapha kuka? Ta tambayi kanta, ta qara bude idanunta idan ba mafarki take ba hajiya take gani tana kuka, meya same su?

Ta shafi cikin ta wayam, sai a lokacin ta tuna ashe ta haihu, da kyar ta juyar da kanta tana kallon qafarta yanda aka wani daure ta cikin qarfuna tayi mata wani uban nauyi.

'Alhamdulillah ta fada a hankali, koda babu qafar nagode da rayuwar da Allah ya bani na cigaba da rayuwa cikin ya'ya na da mijina. 6

Ta lumshe idanunta a hankali tana hawaye...

Post a Comment for "EL-MUSTAPHA CHAPTER 7"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...