Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

EL-MUSTAPHA CHAPTER 6

EL-MUSTAPHA CHAPTER 6

- - Post a Comment
EL-MUSTAPHA

CHAPTER 6

Ya janyo qaramar jakar da ya saka kayanta ciki yana dubawa,

Doguwar riga ya ciro ya ajiye gabanta yana fadin,

Oh Allah jiddana nayi mantuwa,

Me ka manta dashi,

Ya dago yana kallonta sirri ne kada fans na pherty suji,

Ya miqa mata wata bra yana fadin xaki iya sakawa or I should help,

Ta yatsina fuska bayan ta karba tana dubawa,

'Wannan ta dade da min kadan fa tun sanda na sami ciki, yanxu bata min.

Ya karbi bra din yana duba kafin ya dubi kirjinta yana kallonta,

Yanxu wannan ce baxata miki ba, tau yanxu ya kike son tunda ita kadai na dauko, kuma kinsan baxaki xauna haka ba ana shigowa kowa yana kallonki.

Ta dauki doguwar rigar ta xura tana fadin ba wanda xai sani idan nasa hijab, anjima sai kaxo min da wasu.

Banan bata san su bane ya tambaya yana kallonta,

Banan bata sani ba cos batasan me nake sawa ba, kai xaka dauko min not banan. 1

Ya janyo wayar sa yana fadin fadamin size din idan anty yusrah ko ikram xasu xo sai su biya su siyo maki.

Ta gaya masa bayan ta saka hijab din ta,

Ya dube ta a raunane bayan ya ajiye jakar,

Ki cire hijab din jiddah, I need you....

Ta dan dube sa a raunane kafin tace kayi haquri kada mutane su shigo su same mu, kuma ynxu baka tausayina?

Mutane sun fini ne jiddah, banyi qoqari ba?

Ya tsare ta da sexy eyes din sa masu kassarata, ba shiri ta sunkuyar da kanta qasa, dan bata iya jure kallon idanuwansa masu rikirkita kowace lafiyayyar d'iya mace balle ita matar shi ta sunna, data fi kowa sanin sirrinsa na xahiri da badini baya boye sha'awarsa a gareta indai yana buqata.

A raunane tace, ba wanda ya fimin el'mustapha a duniyar nan, ba wanda nake so da qauna kamar shi, meyasa kayi min wannan fahimtar.

Yace sai wace kike so nayi maki jiddana,

Understandable irin wacce ka saba yimin a ko yaushe.

Yayi murmushi batare da yayi magana ba, nutsuwar jiddah da haibarta na birgeshi, magana take cikin nutsuwa kamar ba daga bakinta take yi ba, dauke da matsananciyar qaunarsa a kwayar idanuwanta, sonta da qaunarta na kwarara a xuciyarsa ya rasa inda xai saka ta,

Ya tallabe kansa da hannuwansa duka biyu ya xuba mata idanuwansa yana kallonta cikin so da qauna,

Duk yanda kike so haka xaa yi, idan an hanani abin abarni nayi ta kallon jiddah ko xn sami nutsuwa a xuciyata.

Murmushi tayi tana Jan dogon hancinsa, ta kai bakinta dai dai kumatunsa ta sumbata,

Kayi haquri mijin jiddah ni ban isa na hanaka ba is just.... ya katse ta🤫,

Kwanta ki huta, kafin tayi magana ya tashi ya gyara mata pillow, da kanshi ya gyara mata kwanciya ya matsa gefe nesa da ita kadan yana fadin,

Kiyi barci jiddah kina buqatar hutu kafin yan dubiya su xo, I will be with you kada ki damu.

STORY CONTINUES BELOW


Ta lumshe idanuwanta a hankali ta bude tana kallonsa, ya maida hankalinsa kacokan akan wayarsa.

Ta tuna soyayya da kulawarsa agareta, ta tuna qoqari da kulawar hajiya da abba a gareta.

Bayan wadannan mutanen babu wani a xuciyarta kamar su.

Tana tuna yan uwanta tun tana qarama hajiya ta dauke ta takaita gurinsu domin xumunci kuma tasan yan uwanta, amma suka qi karbarta suka soma yiwa hajiya habaici wai ta maida ta ne saboda ta cinye dukiya babu komai a hannunta hakan ba qaramin batawa hajiya rai yayi ba tun daga lokacin bata qara kaita ba kuma suma din basu waiwaye ta ba.

Kuma abin mamaki duk yan uwanta bafa talaka gwargwado kowa nada arxikinsa iya rufin asiri amma an rasa wanda xai riqe ta saboda babu iyayenta a duniya, ta ya xata iya bijirewa wadannan mutanen da suka nuna mata so da kauna a duniya, suka maida ta mutum kamar kowa, suka aurad da ita ga mutumin kirki wanda ya dace da rayuwarta, baya gudunta ko kyamarta akowane hali ya tsinceta a ciki.

Ya dago a hankali yana kallonta,

Yace barci nake kiyi jiddah, me kike tunani ne.

Murmushi kawai tayi ta maida idanunta ta lumshe, tana jin wani sanyi a xuciyarta.

*

Kusan kullum abokansa, abokanta suna xuwa duba ta, yan uwa Ma sai xarya suke a asibitin harda yan uwan jiddah da suka ji labari sunxo ba qaramin farin ciki jiddah tayi ba koba komai sun nuna tana da matsayi a gurin su.

Kwana su biyu kuwa suka tafi bayan sun mata dimbin alheri tare da addua samun lafiya.

Uwani kuwa tuni aka gargadata prison... 3

Arham ma ya sami sauqi har an bashi sallama.

Suna haka Nabila taxo dubinta anan ne take bata katin auren ta.

Jiddah ta tayata farin ciki sosai, bayan ta tafi el'mustapha na shigowa ta soma yi masa shaqiyanci.

Ya cije yatsa bayan ya xauna yana fadin,

Oh Allah shikenan wani ya kasani akan nabila ai duk kece Ma jiddah tun sanda nayi maki magana kika qi hadani da ita.

Ta kyalkyace da dariya tana fadin ai kaine ka tsaya sanya da yanxu da kai xaa yi,

Ya harare ta cikin qauna yana fadin, haka Ma xakice bayan kece kika kashe min gwiwowi da wata banxar uwani, ai da tuni na saka babbar riga na karkata hula na tafi dole xata xabe ni.

Oho dai sai dai abi wani sarkin yanxu,

Yace kin amince nabi wani sarkin? 2

Nidai a bar maganar ta fada cikin shagwaba,

An barta jiddatulmusty 😊.


Bayan sati lokacin xuwa da ita physiotherapy yayi suna tsaye aka shiga da ita har su ibrahim Ma sun xo.

Dr hafix ya qara yi masu bayanin qafar jiddah bayajin xata iya tashi.

Sosai hankalinsu ya qara tashi bama kamar el'mustapha,

Ya tabbata da gaske suke jiddansa ta xama disabled, Uwani ta nakasa masa mata, jikinsa ya soma kyarma shi kuka abba kuka, an rasa mai rarrashin wani a cikinsu shi kansa ibrahim rudewa yayi.

Suna tsaye aka fito da ita kallo daya xaka mata kasan tana cikin axaba da radadi na qafar, har ta canxa cikin lokaci qanqani aka jata xuwa aminity.

Yana yin su da yanda idanun el'mustapha suka yi ja jikinta ya bata ba lfy,

Ta fashe da kuka tana kallonsu daya bayan daya duk sunyi xugum suna kallonta.

Cikin kuka tace abba meyasa el'mustapha ke kuka, bai yimin bayanin komai ba, kaima kuka kake yi abba, na shiga uku, ku fiddani a duhu meya same nine?

'Abba yasa habar riga yana share kwallah ya kasa magana illa juyawa da yayi ya bar dakin, shima ibrahim kasa jurewa yayi ya fice da sauri.

Dr bakori ya dube ta yana fadin take it easy jiddah, kibar kuka, ya shiga rattabo mata al'amarin da ya sami rayuwarta, kiyi haquri wanna ba shine qarshen rayuwar ba, yau ne kake mai rai gobe ne kake gawa, yau ne kake da amfani, idan Allah yaso gobe ne ka xama tarihi,

A rayuwar jiddah bata taba tsammanin wata qaddara makamanciyar wannan xata taba shafar rayuwarta ba to ina ruwan Allah?

Ta runtse idanunta da qarfi, ita kadai tasan axabtuwar da ruhinta yake, ita kadai tasan radadin da take ji a xuciyarta, al'amarin ya shallake tunaninta, lallai dan Adam ba abakin komai yake ba. 1

Ta karbi qaddararta da hannu bibbiyu tana fatan Allah yasa hakan ya xamo kaffarar a gareta ya kuma bata ikon cinye jarabawar. 1

Ta kai duka tafukkan hannayenta guda biyu a fuskarta ta saki wani gigitaccen kuka mai daga hankalin mai saurare,

Shikenan baxata qara tafiya ba, dr ya juya yabar dakin.

Da sassarfa el'mustapha ya qarasa gareta, ya rungumeta sosai kamar xai maidata ciki shima kukan yake yi, da kyar ya iya bude baki yayi magana,

_INA SON KI JIDDAH, cikin kowane irin yanayi cikin kowane hali ina tare dake, nothing will separate us, ba abinda xai ragu a xuciyata daga qaunar dana ke maki, El'mustapha naki ne ke kadai har abada just tell me jiddana me kike so nayi UWANI?_Kuka suke babu mai rarrashin wani acikin su, +

Da kyar jiddah ta dago tana kallonsa da jajjayen idanuwanta,

Ka saki Uwani, I mean ka fitar da ita daga prison... 4

El'mustapha ya dago da kyar yana mata kallon mamaki,

Ke wace irin mutum ce jiddah wace irin xuciya ce tare dake, don't you know that yarinyar nan ta nakasa ki, kin manta abinda tayi maki ne. 3

Nasani el'mustapha, Allah gafurun rahim ne, muka yi masa laifi muka roqesa ya yafe ballantana mu d'an Adam? 'Wannan abin da ya sameni yana cikin qaddarar rayuwata Allah ya rubuto uwani ce sila, ni na ya.... Shut up please ya katse ta cikin tsawa bayan ya tashi daga jikinta, ransa yayi matuqar baci, ta bude idanu sosai tana kallonsa, el'mustapha is shouting on her today, ta lumshe idanuwanta a hankali wasu hawaye suka soma xarya a fuskarta. 3

Idan kina tunanin rayuwarki bata da muhummanci a gurina tana da, haqqina ne na kare lafiyar ki kuma na hukunta duk wanda ya cutar dake, Uwani deserve to be in prison, in taqaice maki sai nayi Shari'a da uwani, look at you jiddah, just look at your leg har kike cewa abarta, something is wrong with you, you are so silly kada ki qara min wannan maganar, ya juya xai fice a fusacce.

Idan kayi fushi ka tafi ka barni Dame kake so naxo na rarrashe ka el'mustapha? Should I be waiting har lokacin da xaka huce ka dawo gare ni, ta fada tana kallon bayansa idanunta cike da hawaye. 1

Cak ya tsaya tare da juyowa da sauri yana kallonta cikin faduwar gaba, ya tuna yanxu fa ba irin da bane da xaiyi fushi ta bisa tana bashi haquri, suna hada ido jikinsa yayi matuqar sanyi, ya tako da sassarfa ya iso gareta, ya tsaya kyam a gabanta har lokacin xuciyarsa bata huce ba, jiddah ta fiye abin haushi da takaici taya xata ce wai a yafewa uwani kenan taci riba akan abinda tayi. 8

Ta dago a hankali tana kallonsa, kwarjininsa da kyawunsa ke qara wutar soyayyarsa a xuciyarta.

Ta soma share hawayenta a hankali da bayan tafin hannunta,

Kayi haquri El'mustapha, ya xauna batare da yayi magana ba, ta kwantar da kanta a kafadunsa batare da tayi magana ba.

Shiru har na tsawon wani lokaci banda sauke numfashi ba abinda ke tashi a dakin, ta dago a hankali tana kallonsa har lokacin bai saki fuskar saba,

Tasa hannuwanta ta juyo da fuskarsa tana kallonsa ido cikin ido,

Please El'mustapha, kayi haquri ka saki fuskar, jiddah baxata jure wannan fushin ba.

Ya sauke numfashi a hankali yana kallonta,

Xan hukunta uwani jiddah, xan sa acire mata qafar gabaki daya. 3

Da xaka bi yanda nake so da ka barta, daukar fansa ba naka bane, Allah yana gani kuma ya sani shi kadai yasan abinda ya tsara tsakanina da uwani, shi kadai yasan abinda yake shirin yi game da ita, bana so ka xama sanadi kamar yanda ta xama sanadi a qafana, ka fitar da ita daga prison ka barta taje duk inda xataje duniya xata gyara ta, kasan baxata xauna gidan mu ba kuma su hajiya baxa su karbeta ba, ina da tabbacin yan'uwanta Ma ba wanda xai xauna da ita saboda bata girmama su, allow her to go, duk inda xataje ita tasani. 1

STORY CONTINUES BELOW


Shiru kawai el'mustapha yayi batare da yayi magana ba. *

Uwani a prison, masoyanta sun qagu suji a wane hali take ciki, next page xan roqi El'mustapha ya kaini na dauko maku rahoto🤣.
16

Tunda el'mustapha ya shigo asibitin yau jiddah ke masa rigima lallai a maidata gida, ta gaji da xama asibitin.

Juyin duniya yayi da ita taqi haqura, idan ya nuna bacin rai sai ta maida abin wasa, if he is serious sai ta fara kuka ya rasa yanda xai bullo mata.

Ya dafe kansa yana fadin, bansan me xakiyi a gida ba, bansan meyasa kike son xuwa gida ba, ban sani ba ko akwai abinda kike so can wanda baxaki samu anan ba?

Tace bana jin komai ko wani ciwo a tare dani saboda me xaa tsare ni a asibitin,

Yace saboda cikin ki jiddah, EDD naki ya kusa don't you know?

Ta soma hawaye, ni ka maidani gida el'mustapha, am tired of this hospital, nagaji da xama da kwanciya, I need my children ina so na xauna tare dasu, I want to be with them please.

Ya bata rai, ina ce ko kinje gida a xaune kike ko kwance right? Kusan kullum aryan da arham sai sunxo, wane xama kike son yi dasu.

Amma ai kaine kace idan mun koma gida baxan xauna ba tunda ka siya min wheel chair, I will be happy at home than nan asibitin, cikin mutane yan uwana,

Ganin yayi shiru yayi mata banxa yana cin abincin sa yasa ta fara sheshshekar kuka, Allah ya gani ta gaji da xama a asibitin kuma taji likitan na yi masa bayanin ba komai tare da ita saboda cikin ne kawai suka riqe ta amma xasu iya tafiya gida idan suna so.

Ya dago a fusacce yana fadin,

Kiyi ta kukan har kan naki ya fara ciwo, idan kika dameni bindiga xansa na harbe wannan bakin.

Ta qara sautin kukan tana tunxuro bakinta,

Ya ajiye plate din bai qara bi ta kanta ba ya fice, qasan xuciyarsa kuwa murmushi yake shagwabar jiddah na birgeshi ko yaya ne kyau take mata.

Office din dr bakori ya nufa,

Ina so na fita da jiddah waje a duba qafar, har yanxu na kasa yarda xuciyata taqi amincewa da jiddah ta xama disabled, jiddana ta xama nakasashiya wai baxata qara tafiya ba.

Dr bakori yace tuntuni nima nake son nayi Ma wannan maganar amma rashin samun Dr Aiman Merah a waya ne ya saka banyi ma maganar ba.

Waye shi? El'mustapha ya tambayesa yana kallonsa.

Babban likita ne sosai da qasashe ke alfahari dashi, ya san aikinsa kuma shi ba maxauni bane ko ina yana leqawa a kowace asibiti, qarfin sarautarsa da izzarsa idan ba ya so ba ko yasan da xuwa naku ko kunje baxai duba ta ba kuma shi baxai xo ba yana ji da mulki sosai kuma yana so yaga ana girmama sa.

Ka kira mulki ka kira sarauta, ban fahimce ka ba, *MULKI KO SARAUTA* da me yake taqama?

Duka yana taqama dasu idan kana so xan iya baka labari, mutumina ne sosai.

Murmushi el'mustapha yayi, baxan fahimci komai ba, bani da wata buqata kamar lafiyar matata help me pls.

Gsky baa samun sa a waya, amma ga e-mail nasa you should try ko xaa dace, kada ka matsa ko jiran feedback na sa sai yaga dama idan babu yan mulkin akan sa xai neme ka am sure.

El'mustapha ya karba yana fadin, jiddah ta matsa aje da ita gida, tun daxu sai rigima take har da kuka.

Dariya bakori yayi, wannan patient tawa ta fiye rigima, xaku iya xuwa gida babu damuwa amma every week ka kawo ta physiotherapy saboda qafar sannan a kiyaye drugs din nata sosai, 3 days to her Edd a maidota asibiti cos of her condition.

STORY CONTINUES BELOW


El'mustapha yace ina ji baa nan xata haihu din ba, idan hali yayi wannan likitan dan mulkin da kace munyi magana dashi very soon we are leaving, am eager naga jiddah akan qafafunta. 5

Love and caring husband, I salute you AIG EL'MUSTAPHA MUNEER, ba kowane namiji mai muqami irinka ke tsayawa ya jajirce akan iyalinsa ba, ko office baka xuwa kana da yan uwa amma naga kafi so ka kula da ita, you so much love jiddah Allah ya tada qafafunta ya kuma bata lfy, nima I will help xan qara yi masa magana. 6

El'mustapha ya bashi hannu cikin murmushi yana godiya,

Tare suka fito yana fadin bari naje na qara ganin wannan patient tawa naji dalilin da yasa take son yi mana qaura bayan muna kula da ita.

El'mustapha dariya kawai yayi yabi bayansa batare da yayi magana ba.

Har lokacin da suka shiga tana kwance sai hawaye take yi a tunanin ta el'mustapha fushi yayi yaje ya barta, ta juya tana kallon bakori.

Yace harda kuka jiddan musty ne ko jiddatulmusty? Saboda me kike son komawa gida bayan anan Ma xaki fi jin dadi.

El'mustapha ya soma hada kayansu ba tare da yayi magana ba, abinda yaji jiddah ta fada ne ya saka shi dariya batare da ya shirya ba.

Likita mosquito ke ta cixo na kullum, ko daxu ya cije ni a qafana mai ciwo....

Dariya sosai bakori yayi yana kallonta cikin tsananin mamaki,

Sauro anan asibitin jiddah, kada ki mana sharri saboda kina son xuwa gida.

Ta soma share hawayenta ganin el'mustapha yana fita da kayansu da alama gida din xasu je, bakori da kansa ya soma taya sa fitar da kayan har motar sa.

Ya ciro wayarsa a aljihunsa ya kira anty ikram cewa kar taxo asibitin suna gida, duk wanda yake ganin xaije ranar ya kira kada su xo suna gida.

Bakori yayi masu sallama ya fice, ya shigo dakin saboda qaguwa har ta saka hijab nata,

Fuskarsa ba walwala ya cire mata hijab din sai kallon mamaki take binsa dashi lokacin da ya dauke ta ya nufi toilet da ita, kiyi tsarki kiyi alwallah lokacin sallah yayi nasan da kinje gida yanxu mutane baxasu barki yin sallah ba.

Bayan ta gama ya maidota dakin kan darduma ya ajiyeta xaune, ya barta tayi sallah a xaune kamar yanda take yi kullum, shima ya shiga yayo alwallah yaxo ya tada tasa.

Suna gamawa bai jira komai ba ya dauke ta suka fito.

Kallonsa take tana mamakin qarfi irin na el'mustapha kuma har lokacin yaqi ya sakarmata fuska alamar fushi yake da ita.

Suna yin parking harabar gidan, ya fito a hankali ya bude motar ya soma fito da kayansu daga booth,

Mummy is back.... Cewar aryan dake buga ball harabar gidan, ya jefar da ita da gudu ya nufi motar,

Arham na jin aryan ya ajiye kekensa shima ya fito da gudu yana mummy.. Mummy...

Kafin kace me sai ga maaikatan gidan da saurin su sunxo gaida jiddah, tana xaune cikin motar sai kallon su take da murmushi a fuskarta sai ka rantse bayan cikin babu wata matsala a tare da ita.

Su banan suka soma shiga da kayan cikin farin ciki, 1

El'mustapha ya shiga cikin gidan bai jima ba ya fito da wheel chair baya so ya dauke ta gaban yaran saboda surutun su amma duk da haka bai tsira ba, suna ganin ya dorata a ciki ya fara janta, arham ya dube sa,

Daddy why is she on wheel chair?

Becos of her pregnancy, baka gani ne,

Aryan yace, yaushe xata bamu New baby daddy, you olways say mummy xata kawo New baby when she is coming back.

STORY CONTINUES BELOW


Kayi wa mummy addua very soon baby xai xo,

Suka fara tsalle, a tare suka riqa wheel chair din da jiddah ke xaune kafin el'mustapha yayi wani yunquri tuni sun tura ta da qarfi suna dariya,

Kai.. Kai... Kai.. El'mustapha ya nufe su da sauri kamar xai dake su, suka saki keken da gudu suka matsa suna kallonsa sanda yayi saurin riqe jiddah tana gab da faduwa, ita kanta a tsorace take.

See what am telling you jiddah, ya ja qaramin tsaki yana kallon yaran suna tsaye suna kallonsa, su duk a tunaninsu xasu riqa tura mummy ne aciki tunda baby baxai barta tafiya ba kamar yanda daddy yace,

El'mustapha yace duk na qara ganin wani a cikin ku ya tura wannan wheel din sai na dake sa ko taba ta yayi kamar haka... Ya nuna masu, sai nasa belt na dake sa.

To daddy waye xai riqa tura ta? Aryan ya tambaya yana kallonsa,

Ni xan riqa tura ta kullum, ina ga yaro ya qara taba ta ko?

Arham yayi caraf yace harda anti banan idan ta taba xaka dake ta?

Of course ya fada yana kallonsu cikin bata fuska,

Jiddah na xaune na kallon ikon Allah ba qaramin auna arxiki tayi ba da sun kayar da ita yanda suka turo ta da qarfi, 1

El'mustapha ya tura ta xuwa cikin gidan suna biye dasu a baya, suna isa falo suka soma tsalle farin ciki suke ji a xuciyarsu sosai mahaifiyar su ta dawo gida.

Ya dauke ta ya dora ta akan kujera, duk suka xauna suna kallonta suna kallon qaton cikin ta,

Arham sarkin son jiki tuni ya shige jikinta ya kwanta sai sauke numfashi yake a hankali, farin cikin xuciyarsu ba sai an tona ba.

Aryan yace mummy anan gidan xaki kwana ko?

Ta gyada kai tana kallonsa, dariya yayi wacce ta bayyana fararen haqoransa,

El'mustapha na xaune nesa dasu kadan yana Danna wayarsa, banan ta shigo da qaton tire a hannunta jikin ta har rawa yake saboda farin ciki,

'Anty jiddah kici duk abinda kike so anan idan kuma babu ki fada na kawo maki koda na girkawa ne yanxu na girka maki.

Murmushi jiddah tayi tana kallonta,

Oh banan sarkin hidima, ni na qoshi a yanxu sai dai xuwa anjima kimin d'an wake ina missing din sa sosai.

Cikin jin dadi, tau shikenan anty jiddah bari naje na fara hadawa tun yanxu, ta juya ta fice.

Jiddah tayi shiru tana kallon falon, xaman ta tare da su kurma bata taba tunanin xata dawo cikin gidan tayi rayuwa da ya'yan ta ba, sai gashi yau tana rungume da su acikin gidan ta tare da mijinta cikin tsananin farin ciki shiyasa bata debe tsammani ga rahamar ubangiji wataqila inda sauran kwana a gaba ta tashi da qafafunta.

Ta qara rungumesu a jikinta tana shafar kansu a hankali, ta dago tana kallon inda el'mustapha ke xaune dai dai lokacin shima ya dago yana kallonta, harararta yayi ya dauke idanunsa akanta, murmushi kawai tayi tana kallonsa,

El'mustapha mai son ta ne xata iya baiwa duniya labarin haka, kome xai mata birgeta yake yana fushi da ita saboda taqi xaman asibiti ita kuma xama da ya'yan ta ya fiye mata farin ciki da kwanciyar hankali.

Baxata taba mance ranar da el'mustapha ya xubar da hawayen shi na farko akan ta ba saboda ta nakasa, to wanne ne xai kasance na biyu???

*

Da dare yaran sunyi barci,

Wanka el'mustapha yayi mata ya bata kayan barcinta tunda yasan xata iya sakawa ya shiga toilet din.

Bai jima ba ya fito toilet din da qaramin towel a hannunsa yana tsane gashin kansa,

Ya xura rigarshi ta pyjamas yana kallon ta,

Tana kwance cikin doguwar rigar da ya bata mai tsantsi marar hannu,

Kyawawan cinyoyinta a bayyane, qafafuwanta a miqe sambal sai ka rantse lafiyar ta qalau baa dauke da wata lalura.

Son matarshi da qaunarta na qara girgixa xuciyarsa, yana hargitsa gangar jikinsa tare da rura wutar soyayyarta a tare dashi, ya qara qarfin AC bayan yayi wa kansa kyakkyawan matsuguni a kusa da ita,

Ta bude idanuwanta a hankali tana kallonsa, murmushi tayi masa mai tattare da gajiya,

Jikina ba dadi el'mustapha, na kasa barci.

Baxaki iya barci batare dani ba I know, wannan kawaicin ki ajiye shi a gefe ki rungumi mijinki shi kike so jiddah, I need you too, kafin tayi magana ya tashi ya soma bin jikinta da massage dan taji dadin jikinta, ta lumshe idanuwanta a hankali kamar mai jin barci.

Ki bude idanun ko na daina, baxakiyi barci ki barni cikin damuwa ba, for how many long, bakya tausayin bawan Allah nan jiddah?

Dariya ta subulce mata jin yanda yayi mgnr cikin marairaicewa, ta bude idanun tana kallonsa,

Ka gayamin na nawa kayi na biya ka kaga babu sauran damuwa sai ka barni nayi barcina hankali a kwance,

Da tsada nayi kema da tsada xaki biya, ki biyani da soyayyar ki jiddatulmusty, ki shayar dani abinda xai dade a xuciyata bai gushe ba for only today jiddah, ya qara langabar da kansa.

Jiddah taka ce har abada, soyayyar jiddah ka dade da samu tuntuni, babu wani sauran guri da ya rage a cikin xuciyata da ban cike shi da qaunar el'mustapha ba, sai ta tsinci kanta da matuqar jin kunyarsa a yau ta dauke kanta gefe tana murmushi mai bayyana farin cikin dake xuciyarta.

Shi ma yabi ta da wani murmushin da har abada baxai taba gushewa a xuciyarta ba, yabi bayanta a hankali ya kwanta bayan ya soma xuba mata xafafan kiss a ko ina na gangar jikinta.

El'mustapha ya dauke ta ya jefata a wata duniyar soyayya da ta jima bata je ba, ya mantar da ita rashin lafiyar dake jikinta, ya mantar da ita damuwarta har tana jin kanta kamar jiddah farko mai lafiya, ya rungumeta hannu biyu tare da nuna mata xallar soyayyarsa batare da ya kyamace ta na kasancewar ta nakasashiya ba, ta saka hannuwanta biyu ta rungumeshi sosai kamar xata maidashi ciki saboda so.2 days....

Yana dakin jiddah yana shirin fita office kamar yanda ya qudira a yau, tunda aka kwantar da jiddah asibiti bai je ba sai yau.

Ya juyo yana kallonta, tana xaune akan wheel din ta, ta tsura masa ido tana kallon duk wani movement nashi a dakin.

Oh ni el'mustapha, shikenan na xama gwauro komi ni kema kaina andaina min, matata sai dai ta miqe qafafu ta xauna tana kallona.

Murmushi kawai tayi batare da tayi magana ba, ya dawo gabanta ya xauna yana kallonta.

Tun daxu kike bata fuska jiddah, baxan jima ba xan dawo, I know your condition baxan je na barki ba, ya shafi fuskarta yana kallonta,

Me kike so naxo maki dashi? Sai ga hawaye sharrr na bin kumatunta, el'mustapha yaja numfashi ya dawo gabanta ya tsugunna,

Saboda xan fita kike kuka jiddah?, ta girgixa kanta a hankali, ta dora hannunsa akan cikinta,

Ni nagaji da xaman ne, cikin ba dadi duk yanda nayi bana jin dadin sa.

Yace sorry jiddah kin kusa haihuwa ki huta, in kira maki banan ta xagaya dake cikin gidan ko xakiji dadi,

Ta girgixa kanta da sauri,

In kwantar da ke ne, sai kiyi barci kafin na dawo, ta gyada kanta tana kallonsa, yaja keken har wurin gadon ta, ya dauke ta ya kwantar da ita yana kallonta.

Kiyi barci banda tunani jiddah baxan jima ba xan dawo, meeting din ya xama dole ne kinga sai kirana ake.

Ta gyada kanta tana kallonsa, ya sumbace ta yana qoqarin tashi, yaji tana fadin.

Allah ya dawo da kai lafiya,

Yace amin jiddatulmusty, cikin murmushi ya dauki wayarsa da key din sa ya fice bai qara kallonta ba dan yasan xata karya masa xuciya, kamar kada wannan lalura ta same ta duk ta xama rigimammiya bai sani ba ko cikin ne oho.

Tun da ya isa wurin meeting ake ta masa jajen abinda ya sami matarsa wadanda basu sami damar xuwa ba kenan,

Murmushi yayi kafin yace I am soliciting for your kind prayers, my wife was free and discharge, thanks for your concerns, ya xauna.

Sun dauki fiye da awa biyu suna meeting din, duk hankalinsa yana gida binni binni yake kallon time,

Qarar message yaji a wayarsa yana dubawa kuwa yaga jiddah ce,

_Feeling lonely El'mustapha, kaqi ka dawo ni na gaji da kwanciya_.

Jikinsa na rawa ya tura mata,

_on my way, am sorry_! 1

Ya maida wayar aljihu cikin qaguwa da meeting din.

Fitowarsa meeting keda wuya mutane suka yo masa caaaa abinka da babban mutum mai matsayi,

Menene el'mustapha ya tambaya cikin mamaki yana kallonsu,

Sir yan media ne suka xo, tuntuni suke xuwa basa samun ka, suna so suyi interview da akai akan kidnapping na matar ka.

Ibrahim yace, kuyi haquri yana sauri har xuwa wani lokaci,

Ka barsu el'mustapha ya fada yana kallonsu yana kallon agogon dake hannunsa, minti biyu na baku.

Da sauri suka nufe sa, bayan sunyi guntun bayanin da xasuyi suka soma tambayar sa,

Sir ance anyi kidnapping matar ka, ka ganta? Su waye suka sace ta?

Eh na ganta kuma masu laifin da aka kama suna hannun hukuma sauran kuma an kashe su, shikenan ya tambaya cikin qaguwa?

Sir ance sister din tace ta saka aka dauke ta saboda wata buqata tata daban, wace buqata ce wannan kuma wane mataki ka dauka akanta, harda ita tana hannun hukuma ne ko me?

STORY CONTINUES BELOW


El'mustapha ya gyara tsayuwar sa yana fadin what I know if you are working on something that you really care about, you don't have to be pushed, the vision pulls you...... Ya fara tafiya, sukayi ruuu xasu bisa yan sanda dake gurin suka hana har sanda ya shiga mota yabar wurin da sauri.

*

Wayyo Allah, Wayyo Hajiyata, Abba kuxo ku taimakeni, wlhy kashe ni xasu yi, na tuba abba ka yafe min..... 1

Sautin muryar uwani ke tashi dakin da aka rufe ta tare da wasu mata hudu wadanda kusan kullum sai sun axabtar da ita saboda kafiya da taurin kai irin nata.

Duk suka mata magana sai ta maida, idan suka saka ta abu batayi, bata respecting dinsu su kuma basa raga mata ko yaya ne a xamantakewar su.

Yanxu ma daga wurin karbo abinci suke, sun amshe nata sun cinye ta masu mgn suka yi taron dangi suke dukan ta.

Sai da suka mata liga liga su ka barta suna huci,

'Dan ubanki ni xaki gayawa magana akan wani abinci na banxa to an cinye idan akwai wanda xai kwatar maki yaxo kuma yau bake ba cin komai ko kin karbo anjima wlhy baxaki ci sa ba sai dai ki mutu, shegia tsigagiya cewar runkes tana numfashi.

Wadda ake kira da A.j kuwa xama tayi tana numfashin,

Ke har kin isa ki same mu a gidan mu kice xaki mana rashin kunya, yar firit dake haka wannan ko sa'an autan gidan mu kinyi, xan koya maki hankali ne, tasa hannu ta jawo uwani keeeey,

Tashi xaune ki share hawayen nan tun ban nakasa ki ba,

Uwani ta tashi jiki na rawa, ga qafarta sai ciwo take sosai duk da gurin ya warke wajen dukanta suka ji mata ciwo a wurin.

Jikinta sai kyarma yake, ga yunwa dake damunta,

'Dan Allah kiyi haquri anti Aj, karki qara dukana, 2

Aj ta bige mata baki tana fadin, shegiya mayya inta fara baka haquri kamar gadon ubanta kaci.

Runkes ta xauna batare da tayi magana ba banda hararar uwani ba abinda take.

Ladidi ce kawai ba ruwanta, bata hayaniya da kowa a cikinsu kuma tasha gayawa uwani idan bata gyara ba xasu kashe ta ne a banxa tunda kusan kullum sai sun dake ta saboda taurin kanta.

Ladidi tace yi haquri aj ki kyaleta dan Allah,

Ladidi ki daina tausayin wannan ja'ira yanxu ne kin taimaketa anjima ta fara maki rashin kunya ni maganin ta xanyi.

Babu komai yi haquri ki barta baxata sake ba.

Kinci albarkacin ladidi da sai kin yabawa aya xaqin ta, tashi ki ban wuri sakarya, kuma da kin karbo abincin nan ki kawo shi idan ba haka ba wlhy daren yau baxakiyi barci ba, uban ki xanci a dakin nan.

Ladidi taja hannun uwani suka matsa can nesa dasu kadan, sai dingirsa take, suka xauna

Tace wai uwani meke damun kine tun da kika xo gidannan kwana biyu kacal kikayi kowa ya sanki, ko abinci akaje karba sai kinyi fada da mutane, ayi maki magana kina maidawa meyasa.

Uwani ta share hawayen tana fadin, ke ina ruwanki dani ne, tunda kin gayamin naqi ji basai ki barni ba, idan sun kashe ni miye damuwar ki, ai gwanda su kashe ni na huta da wannan rayuwar dana ke ciki. 2

Ladidi tayi shiru bata mamakin kalaman uwani ta saba gayamata magana mai xafi fiye da wannan.

Tace uwani gayamin laifin me kikayi aka kawo ki nan,

Sai ke kin fara fadamin naki tukunna, haka kawai kiji sirrina batare dana ji naki ba.

Ba abin damuwa bane uwani, sunana ladidi, inda na fito basai na fada maki ba, mu biyu ne a gurin iyayen mu nida yaya na, akwai wata maqociyar mu mai suna bilkisu bata taba haihuwa ba kuma tana son yara sosai, haka kawai Allah ya dora mata sona a xuciyarta.

STORY CONTINUES BELOW


Kullum xata je gidan mu ta daukoni, tabani abinci tamin wanka, tana min komai da nake so, kasancewar mijinta yafi iyayena kudi sai suka bata ni a matsayin yar riqo.

Ta riqeni da amana tamkar yar cikinta, tana sona ta sakani a makaranta boko da islamiya, tana min sutura sosai idan kika ganni sai ki dauka itace ta haifeni.

Sai ya xamana babu ruwana da iyayen da suka haifeni sai nafi sati Ma banje gidan ba, su kuma basu damu dani ba tunda ga yaya na.

Girmana na tasowa a lokacin mijin nata ya soma nema na da lalata, wai xai aureni ya jima yana sona tun ina qarama, idan Ma ina so xai iya sakin anti bilkisu ni ya aure ni dan idan bai same ni ba rayuwarsa xata iya lalacewa.

Ban taba jin sonsa ba uwani, ina masa kallon ubana kuma yaya na, ina son anti bilkisu kamar yanda take sona, ban taba ji ko sau daya a rana xan iya cutar da ita ba ballantana har na iya lalata da mijinta ko auren sa.

Matar da ta raine ni tun ban san kaina ba, ta fito dani a mutum, nayi karatu na sami ilimi, wlhy yayana baiyi karatu ba iyakar sa primary, saboda iyaye na basu damu da su nemawa ya'yan su ilimi ba, har gobe ina jin dadin da ban taso a gurin su ba da ko na arbiya banda a yanxu.

Ban sanar da ita komai ba saboda bansan yanda xata dauki xancen ba ina matuqar tsoron abinda xai hadani da ita taxo tana min kallon muguwa mai manta alheri.

Nayi qoqarin boye sirrin amma kusan kullum dare sai yaxo min dakina, ina barci xanji yana shafa jikina, da kokowa da komai nake samu na kwaci kaina naje na buya a toilet.

Ko na rufe dakin da key xai bude da wani ya shigomin, idan kuma fita unguwa tayi ta barni saboda nayi girki wlhy a gidan mu nake xuwa nayi mata saboda tsoron sa.

Da abin ya soma yawane na tattara kayana xan bar gidan, abinda anti bilkisu ta dauka saboda na girma xan mata butulci naje na barta, ta wahala dani tun ina qarama sai yanxu da girma yaxo mata nake son gudu na barta.

Ranar nayi kuka kamar me kuma tayi ta tambayata dalili naqi na gayamata illah na haqura na cigaba da xama a gidan.

Sai wani dare ne daya riskeni a daki ashe bayan fitowarsa ta tashi bata ganshi ba sai ta biyo bayansa,

Yanda yake qoqarin yi min fyade ta qarfi ya saka na soma ihu sosai iya qarfina a daren ashe ummana taji.

'Anty bilkisu na shigowa taga abinda yake qoqarin min ta saka ihu tayi kansa tana neman kwace ni a hannunsa kada ya jimin ciwo.

Tun da ya ganta kunya ta lullubeshi amma saboda halin su irin na maxa sai ya fara borin kunya ya hau dukanta,

Ina tare mata dukan, ya soma dukana iya qarfinsa, ta kasa jurewa ne taxo tana jansa tana kuka tana roqonsa ya daina kada ya jimin ciwo.

Marin ta yayi tare da hankadata ta bigi qarfen gadon da nake kwanciya akai, faduwar da tayi gurin ashe bata numfashi, yana ganin haka ya fita da gudu ya bar gidan,

Naje gareta ina kira sunanta tare da jijjigata amma ko motsi batayi, kuka nake bana ko ganin gabana naje ina debo ruwa ina kwara mata a tunanina ko suma tayi amma ko motsi batayi.

Ina cikin wannan halin ne sai ga mijin ya dawo tare da iyayena da yan sanda cewa na kashe masa mata harda kukan sa uwani.

Tsoro da faduwar gaba, ga tashin hankali suka min yawa, ummana bata yarda da maganarsa ba saboda ihu na da ta jiyo a lokacin sai ta soma kwankwanto, amma Abbana dukana ya riqa yi yana jifana da mugayen kalamai kan cewa naci amanar matar data riqeni da amana.

Hankalina ya tashi na soma jijjigata ina fadin ki tashi anti bilkisu ki gayamasu gaskiya, ki gayamasu bani ce na kashe ki ba, amma ina, inaji ina gani aka samin ankwa aka fiddani gidan ni kuka ummana kuka. 1

Ba wai ina kuka saboda qaxafin da aka min ba ina kuka rabuwa da anti bilkisu, ina kuka na rasa wannan matar mai haquri da amana,

Wlhy bani na kashe ta ba shine abinda kawai nake fada a kullum amma bani da shaida sai Allah kuma shi kadai xai iya fiddani a wannan hali da nake ciki.

Uwani ta xuba mata idanu tana kallonta, labarin ta ba qaramin girgixata yayi ba, bata ji wata nadama a tare da ita ba sai da ta tsinci kanta tana baiwa ladidi labarin tata rayuwar.

A lokacin ne take tunawa da alherin jiddah a gareta, haqurin ta da kawaicinta, soyayyarta da kulawarta, sacrifice din ta akan abinda take matuqar so da qauna a duniya,

Ta matsa kadan cikin tsoron irin kallon da ladidi ke mata na tuhuma,

Karo na farko a rayuwar uwani da taji tayi nadama akan wani abu da tayi a rayuwarta, xuciyarta ta cigaba da bugawa, idanuwanta na hasko mata jiddah da halin da ta saka ta a ciki, 3

Ta rumtse idanuwanta. da qarfi bayan ta kai tafukkan hannuwanta a fuskarta ta saki wani irin kuka da bata taba yin sa ba.......Kuka kike Uwani? Saboda me xakiyi kuka, mai xuciya irin taki bai kamata ya karaya da wuri haka ba..... Cewar ladidi tana kallonta cikin takaici.

Uwani ta dube ta idanunta taf da hawaye,

Ban taba nadama a rayuwata ba sai wannan karon, ban taba ganin banyi dai dai ba sai yau, ban taba jin tausayin wani a xuciyata ba sai yau, na dauka cewa duk abinda nake yi dai dai ne saboda ina son cimma wani buri nawa, babu mai gayamin gaskiya na dauka..... Nikam ya xanyi da rayuwata, ya xan gyara rayuwata, taya xan tunkari jiddah nace ta yafe min, na cutar da ita na sani kuma *NAYI NADAMA*, ta fashe da kuka.

Ladidi tace kadan Ma kika gani uwani, kinji haushi kuma ke butuluce maci amana kuma muguwa at the same time, xama da mace irin ki babu amfani domin ke abin gudu ce,

Koma me xakice wlhy nasani, na cutar da matar da ta riqeni amana kamar qanwarta, ta dauki iyayena tamkar nata, ta sakani makaranta tare da kula dani da xuciya daya, na dauki soyayya na dorawa mijinta tayi shige da fice wurin jajircewa dan ganin na mallakeshi saboda ciwon da nake mata na qarya, ta bani shi a matsayin mijin aure na, ni kuma na cutar da ita, na banxantar da rayuwarta, nayi qoqarin kashe ta da ya'yan ta domin na mallaki mijinta, na manta alherinta a gareni, nayi sanadiyar xamowar ta gurguwa, dan Allah ni wace irin mace ce marar imani, Dame duniya xata kirani, wane hali iyayena suke ciki a yanxu na baqin cikin dana saka su, ta cigaba da kuka sosai.

Shiru ladidi tayi bata tanka ba amma cike take da haushin uwani, ita wace irin xuciya ce da ita haka?

Ina ma nice ke uwani, ina ma nice na tsinci rayuwa irin taki mai cike da kulawa da amana, ina Ma nice akan position din da kike ciki before not now, ta ya xanyi wasa da dama ta nayi sake da kyautar rayuwar da Allah ya bani tare da uwargida mai sanyin hali irin na jiddah, ban ganta ba amma naji ina son ta a xuciyata, ita macece da xaa yi alfahari da samun irin ta, Allah ka jiqan anti bilkisu ka gafarta mata ka kuma dubeni da idon rahama ka fitar dani cikin wannan halin da nake ciki.

Runkes ta tsame hannuwanta cikin abincin da take ci, tana sud'e yatsun hannunta tana kallon ladidi, batare da tunanin komai ba ta shafe hannun a jikinta tana murxa yatsun hannuwanta.

Labarin ki ladidi yayi matuqar bani tausayi, naji tausayin ki matuqa, amma kinga wannan shegiyar ko kadan ban tausaya mata ba, kuma baki Ma ga komai a cikin rayuwar ki ba tukunna matuqar bakije kin roqi iyayenki da jiddah gafara ba.

Ni kin ganni na, Mahaifina na kashe da hannuna.... duk suka xuba mata ido suna kallonta da mamaki cikin tsoro.

Murmushi tayi mai dauke da kwallah a idanuwanta,

Tace bana nadama kuma bana jin xan taba nadamar kashe sa a rayuwata.

Sunana Rukayya, makarantar boarding nayi acan suke kirana Runkes, ina matuqar son iyayena da qanena a xuciyata, nice babba a gurin su.

Tun da na taso a gidan mu na sami mahaifiyata cikin qunci na rayuwa dalilin mahaifina, auren hadi ne aka masu daga iyayensu, bai taba son ta ko tausayinta ba, amma mamana tun sanda aka daura auren su ta dauke sa matsayin qaddarar ta, ta rungumeshi da hannu bibbiyu, tana girmamashi, tana qoqarin ganin ta faranta mashi ko yaya ne amma shi baya ganin, kullum cikin mata fada, mistake kadan xata masa ya hauta da duka koda a gabanmu ne ba ruwansa, koda baqi ne a gidan bai damu ba.

Mu uku mata sai yara maxa, in taqaice maku ban taba ganin axxalumin mutum da baisan darajar mace ba kamar sa, yes babana ne amma xan iya baiwa duniya labarin sa, I don't care ko xata xageni ban damu ba.

STORY CONTINUES BELOW


Sanda na gama secondary School dina na koma gida ne na tarar da wani tashin hankali a gidanmu, can you imagine babana yayi lalata da qanwata dake bimin, yar cikin sa kuma a gaban idon maman mu tana gani tana kuka, qanwata kuka.

Bansan yanda xan gaya maku halin da na tsinci kaina aciki ba ranar,

Muka dauke ta muka je da ita asibiti, ko kwana batayi ba ranar ta mutu, nan take mamana ta xube gurin a sume.

Xuciyata da kwakwalwata baxasu dauka ba, as my age at that time, ban isa na dauki irin wadannan tashin hankali ba, ban san yanda xanyi da rayuwata ba, babban tashin hankalina ace mamana ta mutu yanda naga likitoci sun duqufa neman ceton rayuwarta.

'Na bar asibitin naje na sanar da yan uwanmu, sai gasu kuwa sun xo asibitin cikin jimami.

Ni na boye masu abinda mahaifina yayi akan qanwata, nace wasu ne suka mata fyade kuma baa gane ko su waye ba.

Kowa ya tofa albarkacin bakinsa na tsinewa duk wanda keda sa hannu a mutuwar qanwana, haka suka dauko gawar suka dawo da ita gida, aka mata wanka, sutura da sallah kafin akaita makwancinta duk wannan abin da ake mahaifina bai sani ba sai da ya dawo gida.

Daya sami labarin mutuwarta babu tsoro ko nadama a tare dashi kuma ko addua bai mata ba, ni na rasa gane kansa qiyayyar da yakewa maman mu harda mu baya sone ko me?

Har aka sallamo mamana asibiti bai taba xuwa asibitin ya duba ta ba, haka muka cigaba da rayuwa dashi da dadi babu dadi.

Duk wanda yaxo neman aure na baya bari sai yace wai ni yar iska ce,

Da mamana ta same sa da maganar har dukanta yayi a ranar

In taqaice maku sai ga mahaifina yana neman lalata dani kamar yanda yayi da qanwata,

Mamana ta ceceni ranar a hannunsa,

Baa dauki wani lokaci ba ta kamu da hawan jini mai tsananin gaske da yan uwanta suka sami labari suka xo suka dauke ta acewar ta bar mashi ya'yan sa daya kashe ta a banxa gwanda mu mutu a hannunsa ba damuwar su bane itace tasu.

Hankalin ta ya tashi sosai bata iya barin mu a hannunsa sanin halinsa, ta roqe su su barta taje da ya'yan ta mata kada ya lalata mata su idan ya so a bar masa maxan.

Maxan ma sune qanana a cikinmu kuma suna buqatar kulawar uwa idan mama taje ta barmu da su ya xamuyi da rayuwar mu.

Sai a sannan ne baba yayi magana ya bada haquri akan komai ya wuce insha Allah.

Kamar gaske ya daina shiga shirgin mu babu ruwanshi damu yana yin rayuwarsa shi kadai baya kula kowa a gidan koda kuwa mun gaidasa baya amsawa.

Babu ruwanshi da cin mu ko sha, sutura ya dade da daina yi mana komai maman mu ke mana dayake ita tana da abinta kuma tana karban salary irin na local government haka, so bata damu ba, hakan da yayi ya fiye mata alheri na ganin ya daina kula mu.

Bayan kwana biyu sai ya fara kawo mata a gidan ya kwanta dasu har Safiya dan baya tsoron Allah, a haka washe gari xai sallame su batare da yaji kunyar ko mu dake ya'yan sa ba.

Maman mu da baqin cikin haka take kwana kullum dare na Allah sai tayi kuka kafin ta kwanta, a boye takeyi kada mugani kuma ni bata san nasani ba, sannan ta hana muyi masa magana ko rashin kunya duk wanda yayi da kyau ya sani.

Haka muka xubawa sarautar Allah ido muna roqon Allah ya kawo mana sauqin abin.

Bana manta wannan ranar a rayuwata, ina wanka sai ga baba ya shigomin a toilet kafin nayi wani yunquri sai naga ya soma cire kayan jikinsa yana tunkaro ni.

Kokowa mukayi sosai har na samu na kwaci kaina daga gare sa, ina qoqarin fitowa ya biyoni tsantsin ruwa suka ja sa ya fadi ragwaf a gurin,

Bacin rai da gushewar tunani ya saka ban lura da jinin dake fita a hanci da bakin sa ba na dauki bucket na soma dukan sa dashi ina kuka.

STORY CONTINUES BELOW


Jinin dana ga yana fita a jikinsa ya saka na saki bucket din na fito a gigice ina ihu.

'Na kashe baba.... Shine abinda ya fito bakina lokacin da mukayi ido biyu da mamana.

Jikinta na rawa naga ta nufi toilet din hankalinta a tashe bata jima ba ta fito da sauri tana kallona.

Me kika masa rukayya? Jikina na rawa na gayamata komai ban boye mata ba.

Ta dafa ni tana kuka sai dai ta rasa me xata ce,

Ana haka sai ga qaninsa yaxo gidan da kayan wankinsa a hannu dama shi ke masa, koda ya ga abinda ke faruwa ya fita da gudu neman yan sanda.

Rukayya ta cigaba da kuka tana fadin, mamana tace ita ta kashe babana, ta dauki laifin ta dorawa kanta bata yarda aje dani ba.

Ni kuma naqi amincewa da hakan saboda qannina, idan taje ta barmu taya xan iya kula da su, bani da komai da xan kare kaina da su, gwanda ita mahaifiyace sunfi buqatar ta akaina, kuma taya xata dorawa kanta laifin da ba itace ta aikata ba, axo a hukuntata a banxa.

Ta share hawayen ta tana fadin, an kusa yanke Mani hukunci bada jimawa ba, ni na kashe mahaifina kuma nasan dole a kashe ni nima, duk maana taxo nan sai tamin addua tana kuka take barina.

Qaddara ta kenan haka Allah ya tsaramin tawa rayuwar kuma na karba da hannu biyu tare da fatan Allah ya bani ikon cinye jarabawar har lokacin da xaa yanke min nawa hukuncin cikin wannan watan.

Kuka sukeyi sosai babu mai rarrashin wani a cikinsu.

Daga sama su kaji muryar Aj na basu nata labarin.

Labarin ku ya bani tausayi matuqa nawa duk mai sauqi ne akan naku, Sunana Amira, ana kirana da Aj kasancewar sunan saurayina Jamal.

Baxan boye maku ba ni macece mai matuqar kishi sosai, ina son Jamal kamar raina bana son mace ko wace iri ce ta rabe shi, ko qanwarsa ban yarda da ita ba indai akan sane.

Idan yaxo hira inda nake ina bashi kulawa sosai na ganin na faranta masa, bawai na bashi jikina baa, tsabtacciyar soyayya muke dashi kuma na tabbata har a ransa yana matuqar sona.

Idan xai koma gida baya sani nake bin bayansa a cikin napep ko saman Babur idan ban sami mai napep ba,

Ina bin bayansa na gani ko xai tsaya da wata mace a hanya ko kuma xai biya gurin wata mace ne ban sani ba, sai na tabbatar ya shiga har cikin gidansu da motarsa hankalina ke kwanciya na dawo gida na biya mai napep din.

A school kowa ya sanmu tare ana kirana Aj shima haka ake kiransa, Department din mu ba daya ba amma duk da haka na saka a dubamin duk ranar da ya kula wata macen a gayamin.

Harta kai bana boye masa kishina a gurinsa, ya sani har baya son ganin ya batamin.

Amira indai akan mace ne ki kwantar da hankalinki Jamal ne kin riga kin samu har abada baki da miji kamar ni..... Kullum mgnr sa kenan a duk lokacin da kishina ya motsa.

Nifa har mamanshi ina kishi, duk ranar da yaxo gurina da wuya ne bata kirasa a waya cewar yaxo ba ko kuma tana buqatar yaxo ya xata aikeshi, sosai abin ya fara damuna har nake ganin kamar da gangan take min haka.

Yace amira ummana Ma bata san ina xuwa wurin ki ba kawai dai buqatar ta tana xuwa dai dai da sanda naxo nan ne kuma baxan qi xuwa gurin ta saboda ina matuqar son ta mahaifiya tace.

Kalamansa sun matuqar bata min rai ashe har akwai macen da Jamal xai so a duniya bayan ni ya dauketa da muhimmanci haka, kwata kwata kishi ya rufe min idona na manta cewa wannan matar fa mahaifiyar sa.

'Washe gari na shirya naje har gidan saboda nayi warning din ta akan abinda take min bana so.

Tace ke kuma wacece, daga ina haka? Wane yaro kike magana akai Jamal ko Mubarak?

STORY CONTINUES BELOW


Jamal nake magana hajiya, nasan ke kika haifesa kina da iko akansa amma ba hakan xai saka ki shiga haqqina ba, kinci naki xamanin kixo kici nawa sai yaxo hira gurina ki soma damunsa da kira akan yaxo meyasa kike min haka?

Tsananin mamakin ta ya saka hajiyar xuba mata idanu, bata gama mamakin ba taga Amira ta xube qasa tana kuka tana roqonta,

'Dan Allah hajiya kiyi haquri idan kinji haushi ina matuqar sonsa da kishin sane dan Allah kidaina min haka idan yaxo.

Tau shikenan cewar hajiya, tace ya sunan kine.

Tace amira,

Kije gida ba komai..... Bayan fita ta Jamal ya dawo gidan take tambayar sa wacece Amira?

Da tsananin mamaki yake kallonta,

Hajiya ina kika san amira?

Tace ina tambayar ka kana tambayata, wacece amira?

Jikinsa yayi sanyi yace wacce xan aura ce hajiya.

Tace Sam ba dai a gidannan ba, kuma tun wuri ka cire ta a xuciyarka baxaka taba auren ta ba.

Meyasa hajiya ya tambaya cikin tsananin mamaki, ina sonta tana sona, kada ki biyewa xancen mutane suxo su bata ta a gurin ki hajiya.

Har akwai wani xance da xanji bayan wanda naji da kunnuwana kuma na gani da idanuwana,

Nan take ta gayamasa komai duk da baiji dadi ba amma ya shiga bata haquri maganar gaskiya yana sona, haka yaxo har gida ya sameni yayi min fada sosai tare da nuna min bacin rai, ni kuma a ganina bani da laifi duk yiwa kaine ai abar mu muji dadin soyayyar mu ba takura.

Kwana biyu ya kauracemin baya kirana baya xuwa idan na kira baya dauka, hankalina ya tashi har skul na daina ganin sa na shirya naje gidan hajiyar bata manta dani ba,

Tace kinxo ne kuma ki gargadeni akan yarona?

Matar nan ina kuka na bata haquri taqi sai Ma wulaqanci da tamin har da cewa indai tana numfashi a duniya Jamal baxai aure ni yar uwarsa xai aura.

Sanda na dora idanuna akan sa da matar bansan Randa na rarumi qaton dutse na buga mata aka ba, nan take ta xube gurin a sume, sanadiyar wannan ta'asar aka xo dani nan, amma bata mutu ba tana kwance a gadon asibiti ance ta rasa hankalinta is like she loose her memory yan uwanta baxasu taba yafe min ba......

*

Xaune yake da laptop a gabansa, ya duqufa wurin aikin shi batare da ya damu da rigimar da jiddah ke masa a yau.

Ya rasa meke damun jiddah kwanakinnan banda rigima babu abinda take masa, kamar kada wannan lalura ta same sa,

Duk yanda yayi da ita baiyi dai dai ba, ko twins basa rigimar da take amma shi yafi kallon abin a shagwaba lura da yanayin da take ciki na wannan cikin.

Ya shafi sumar kansa batare da ya juyo ba lokacin da yaji ta jefo sa da pillow a bayansa.

Yayi biris da ita bayan ya cigaba da dannan laptop din, burinsa saqonsa ya isa ga dr Merah.

Qafarta mai lfy tasa tana xungurinsa, yayi mata banxa, babu xato ko tsammani yaji saukar Cup a kansa, ba shiri ya juyo yana kallonta dafe da kansa.

Tun daxu nake magana kayi min banxa,

Kin fa dame ni jiddah, ki barni nayi aikin dake gabana mana..... ya juya a fusacce ya na kiran Banan,

Me banan xatayi maka ne,

Yace xata fitar min dake ne nayi aikina, gwanda taje dake can tana tura ki din yafi kwanciyar ki anan kina min rigima.

Kafin tayi magana ya tashi ya fita yana gyara xaman rigarsa,

STORY CONTINUES BELOW


Banan..... ya qara kiran sunan ta bayan ya fito falon jiddah, amma shiru bata amsa ba kuma baiji duriyar twins ba,

Ya fita harabar gidan yasan baxasu wuce gurin suna wasa ba,

Acan ya tsinkayo su kuwa su biyu suna wasa abinsu sai tsalle suke, kamar ance ya juya, ya tsinkawo banan da Islam a garden taci uban kwalliya sai dariya take xubawa.

Yayi tsaye kyam kamar an dasa sa a gurin yana kallon ta,

Tana juyowa sukayi ido hudu ta tashi da sauri cikin jin nauyi ta dubi Islam tana fadin,

Ga yaya yaxo kaxo ka gaidashi,

Ba musu Islam ya tashi, suka nufosa ya dauke kansa gefe yana kallon su aryan har suka qaraso.

Islam ya bashi hannu suka gaisa,

Banan tace anti jiddah tana nema na ne?

Ya girgixa kansa batare da yayi magana ba, ya juya ya koma ciki, su banan ma suka koma inda suka fito.

Yana shiga dakin, kallonsa jiddah tayi tana observing yanayin sa.

Meya same ka, ina banan din, ina su aryan?

Ya xuba mata narkakkun idanuwansa yana kallon ta sai kuma yayi murmushi bayan ya xauna yana fadin.

To maman su aryan suna waje suna wasa ba abinda ya same su.

Ina banan din, ba kace xata fita dani ba.

Yace banan tana da baqo wannan yaron da kika min bayanin sa.

Tace oh ashe yaxo, sai kuma ta dubi yanayin el'mustapha sai Ma qoqarin rufe laptop din yake, ta qara kallonsa gabansa na tsananta bugawa. 1

Tace me ya same ka el'mustapha, meyasa kake rufe laptop din bayan kace aiki kake da shi.

Anjima xan qarasa, ya ajiye ta gefe yana qoqarin kwantawa a kusa da ita.

Tace ko ka damu da baqon banan ne, meyasa ka damu da yawa haka, kada kace dai kana son banan ne..... 1

Gabansa ya tsananta bugawa ya tashi da sauri yana kallonta,

Ni jiddah.... ni kuma kike xargi akan banan saboda me xan damu da baqon ta?

Tace nasani ne el'mustapha, tun asibiti ina lura da yanayinka daga lokacin da ka gane banan tana tare da Islam, yanda ka fita yanxu ba haka ka dawo ba, daga yanayin yanda kake mgnr banan tana da baqo mai hankali xai gane.

Yaja numfashi jikinsa na rawa xai yi magana tayi saurin tsaidashi da hannunta.

Ba sai kayi min bayani ba, nasan dole xaka buqaci mace mai lafiya ba Irina ba, kuma nasan komai daren dadewa dole xaka qara aure, amma yaushe ka fara son banan el'mustapha?

You are not serious jiddah, baki san me kike yi ba, something is wrong with your brain, bana son wannan maganar kwata kwata kuma kada ki taba tunanin ina son banan I don't.

Batayi magana ba ta kwanta jikin pillow tana kuka sosai,

Jikinsa yayi sanyi yaji hankalinsa ya tashi, shi kam baya son wanna kukan na jiddah ko yaya ne,

Ya hau gadon kacokan ya rigota,

Wallahi jiddah babu wata yarinya da nake so a yanxu bayan ke, bana son banan reaction dina akanta ba shi xai saka ki yanke min hukunci akan ina sonta ba, yaushe kika fara xargina Hakan jiddah, Wallahi bana son ta kuma ban taba tunanin qara aure ba saboda kin nakasa jiddah, cikin kowane hali kike ina son ki, xan kasance dake a hakan har qarshen rayuwa ta ki yarda dani jiddah.... 3

Ta xame jikinta a hankali daga garesa, Allah yasa abinda el'mustapha ke fadi har a xuciyarsa ne baxata taba yarda ya auri banan ba, idan ma auren xaiyi ta fiso ya auro wata bare yanda ko ta cuce ta baxata damu ba kamar yanda uwani tayi mata, amma me el'mustapha xaiyi da banan, kai baima isa ba wlhy ba macen da xai aura.....

Wallahi baka isa ba el'mustapha, babu macen da xaka aura a gidannan ba banan ba kowace iri ce kuwa idan kana da wannan niyar is better ka kunce ta a yanxu.

Yanda take maganar cikin seriousness ya saka shi dariya harda tafa hannayensa.

Nagane ba komai ke damun jiddah ba sai rigimarta bnda hakan taya xaki hadani da banan for goodness sake, ki daina sako min ita a xance just relax kwanta ki huta. 3

Ta tunxuro baki tana kallonsa,

'Na dai gayama inma akwai wannan niyar ta aure a xuciyarka ka cire ta na dawo jiddana as before, indai akan kan baxan qara haqura da wata mace ta rabe ka ba, is better ka shirya xama da jiddah a duk yanda take kamar yanda kace as before cikin kowane hali you will be with me.

Yace insha Allah jiddatulmusty, ya sumbace ta yana murmushi itama murmushin take tana kallonsa.Yaja numfashi a hankali hade da sarqe hannuwanta da nasa yana murxawa.

Kallon sa tayi,

Mama bata xo asibiti ta duba ni ba, kuma bata kirani a waya ba sannan ba wanda na ji yace mama tana gaidani, Allah ya sa ba laifi nayi mata ba el'mustapha. 1

Gabansa ya tsanan ta bugawa ya juyo yana kallon ta a hankali, yama rasa me xai ce mata, yayi shiru yana kallonta.

Ko tana fushi dani ne, nidai ban san nayi mata wani laifi ba.

Mama bata fushi dake jiddah, saboda me Ma xatayi? Ita ma jikin nata ba sauqi shiyasa kika ga bata xo ba amma kullum naje sai tace a gaidaki,

Baya son gayamata gsky saboda halin da take ciki ya fiso sai ta haihu tukunna.

Tace to kabani ita a waya mu gaisa, ko ka kaini wajen ta mana.

A hakan xan dauke ki na kaiki, kin fiye sakawa ranki damuwa ita mama da kanta naji tana maganar xata xo idan jikin yayi sauqi.

Allah ya bata lafiya,

Amin kawai yace a hankali ya koma ya kwanta, mgnr mama da tayi duk ta tada masa wata kewa ta mahafiyarsa, ya soma yaqi da xuciyarsa na ganin yayi mata addua batare da wata alama ta damuwa ta bayyana a fuskar sa ba.

Ta sa hannu tana Jan yatsun qafarsa a sanyaye.

*

Tun da Uwani ta sami labarin kowa tayi sanyi, babu komai a tare da ita sai tsananin nadama sannan duk a cikinsu tafi tausayawa ladidi ina Ma tana da wata hanya da xata taimaka mata na ganin ta fitar da ladidi ko da ita xata dauwama a prison din.

Ta share hawayenta tana kallon ladidi.

Anti ladidi dan Allah ki yafe min abubuwan da nayi maki a nan, nikam ina ji qarshe na yaxo mutuwa xanyi, baxan taba yafewa kaina ba domin na cutar da rayuwata.

Ladidi ta dafa ta tana fadin, baxaki mutu ba uwani sai lokacin ki yayi kuma kowane mutum da kike gani a rayuwa yana kuskure kuma ya nemi gafara a yafe masa, kada ki karaya tun yanxu ki fara istigfari kuma idan Allah yasa kin fita daga gidannan kije ki nemi gafarar iyayenki da jiddah.

To wai ke ina jamcy ne cewar aj tana kallonta,

Nima ban sani ba kuma bani da labarin ta tun ranar da mukayi waya tace an kama saurayinta kuma inaji itama din xasu kama ta ne tunda neman ta suke a yanda ta gaya min.

Runkes tace amma fa ta cutar dake ba qawar arxiki bace surry ce tafi dacewa dake domin itace mai gayamaki gsky.

Aj ta tabe bakinta bayan ta gyara kwanciyarta nifa duk wannan muqu muqun da kike na tuban muxuru baya tasiri a gareni idan kika cigaba da min iskanci a gidannan ubanki xanci na gyara ki bana daukar raini ko kadan kuma bana so a rainani, idan kina so mu xauna lfy dake ki kama kanki da bakinki ga maidamin magana.

Insha Allah anti aj xan kiyaye baxan qara maki iskanci ba.

Kimayi din kigani, taja tsaki.

Runkes ma ta tashi tana yan waqoqinta tana gyara gurin da xata kwanta.

*

'Washe garin ranar suna xaune suna cin abincin da suka karbo amma banda uwani ta takure guri daya sai tunani take,

Ita fa tun da take a rayuwa tana jin bata taba abinda iyayen ta suka ji dadi suka yaba ba amma tana ganin yanda suke sanyawa jiddah albarka, taya xata gyara rayuwarta a sota kamar yanda ake son jiddah?

STORY CONTINUES BELOW


Aj ta dube ta rai a bace, wai ke uban waye ya saka ki a damuwar ne da xaki xo kina mana kuka anan?

Xaki matso kici abincin ne ko sai na tattakaki, wlhy sai in cinyeshi gabaki daya ba damuwa ta bane, muguwa mai manta alheri, matso nan ta fada cikin tsawa.

Uwani ta matsa da sauri hade da tsoma hannunta cikin plate din, jikinta na rawa take cusa shinkafa a bakinta babu ko taste ballantana taji dadin ta abaki.

Bata taba tunanin akwai ranar da xata iya cin wannan abinci ba, dama haka rayuwa take watarana da dadi watarana ba dadi.

Suna haka wani police yaxo ya bude qofar yana kiran waye Aisha Adam anan?

Uwani tayi xuru tana kallonsa gabanta na tsananta faduwa, jikinta ya dauki rawa.

Nace waye Aisha Adam anan dakin kun min shiru.

Nice.... Uwani ta fada tana hawaye.

Xo.. Kin wani tsare ni da ido sai kace mayya, kada ki batamin lokaci.

Ta tashi tana kallonsu cikin wani irin tashin hankali, shi kenan qarshen ta yaxo, ta hade hannuwanta guri daya tamkar mai neman gafara a gurin su sai dai ta kasa furta kowace kalma a bakinta saboda tsananin tsoro da fargaba.

Ta soma tafiya a hankali idanunta akan na ladidi, xaman da suka yi da ita taji tana son ta tana matuqar tausayinta,

Haka ya cusa qeyarta gaba suka fito.

Tayi mamakin ganinsa a wannan lokacin, gabanta ya tsananta bugawa ta xubawa kyakkyawar fuskarsa idanuwa kamar xata hadiye sa dan so.

Yana tsaye yana rubutu a wani littafi da bata san kona menene ba, duk da yaji alamun tahowarsu hakan bai sa ya dago ya dube su ba.

Fuskar nan tasa ba walwala sanyi da farin glass,

Sir gata na xo da ita....

Bai dubi inda take ba ballantana ya san wane hali take ciki.

Yace ina inspecta kabir,

Sir gani,

Xo nan akwai wani case da nagani ranar a wannan littafin, yaron da aka kama yayiwa yarinya fyade ya akayi aka sake shi bada sani na ba, waye ya bada izinin hakan?

Sorry sir, amma... Amma?

Amma me? Ya katse sa bayan ya kafe sa da idanuwansa.

Kun saki yaron ne ya tafi a banxa bayan ya cutar da yarinya, kada kuce min kun karbi cin hanci ne?

Kabir yaji gurin na juya masa yasan waye el'mustapha Sam baya wasa da aikinsa haka kuma duk wanda ya kama da cin amana a gurin korar sa yake yi ba ruwansa, ya rikice yana rantse rantse.

Sir ni bansan komai ba akai, bani ne on duty ba ranar, ka duba kagani nima koda naxo an sake shi.

Waye da duty ranar?

Inspecta Ayuba ne, ya qara nuna masa jikinsa na rawa,

Idan yaxo ya same ni office ina neman sa.

Ya soma tafiya a hankali batare da ya kalli inda uwani take tsaye ba.

Sir wannan fa a maida ta ne?

Ku barta idan taga dama ta kwana a gurin.

Ta bisa da kallo har sanda ya isa motar sa,

Kinji dadi oga yace abarki ki tafi, sai ki kama hanya in kuma anan xaki kwana ne sai naxo na tayaki kwana.

Ta dubesa tana xabga masa harara tamkar idanunta xasu fado, taja dogon tsaki bayan ta soma tafiya jikin ta ba kwari.

El'mustapha yace a sake ta kenan sun yafe mata, tasan ba mai mata wannan sai jiddah tasan jiddah kadai ce xata roqa mata wannan alfarma, wace irin xuciya ce da jiddah, lallai jiddah mai son ta ce da gaskiya, bata da kamarta a duniyar nan, ina ma jiddah xata bata second chance da ta nuna mata qaunar da bata taba yiwa wani a duniya ba amma is too late for her.

STORY CONTINUES BELOW


Tasa hannu ta share hawayen fuskarta bayan ta fito,

Ina ta nufa duk bata sani ba, kaduna xataje inda iyayenta ko kuwa gida xata je inda jiddah, idan taje inda jiddah ta ce mata me da wane idon Ma xata dube ta, qila Ma jiddah tana asibiti, gidan iyayen ta xata nufa amma Dame xata je garin ita da ko sisi babu a hannunta?

A hankali ta share wasu hawaye masu xafin gaske a fuskarta, ta soma tafiya a titi ba ko takalmi a tare da ita.

Tafiya tayi mai nisa sosai har ta iso babban titin da xai sa da ta da tasha, waye xai taimaketa ya bata kudin mota, taga mutane sai kallon mahaukaciya suke mata.

Ta sami guri ta xauna a gefen titin, ta hade kanta da gwiwarta tana kuka.

Ina ma batabi son xuciya ba, ina ma batabi xugar qawa ba ta xauna a gidanta da iyayenta, da yanxu tana can acikin AC, taci mai kyau tasha mai kyau, da yanxu tana xaune da kowa lafiya, da yanxu tana tare da el'mustapha wanda shine sanadin komai a rayuwarta, soyayyar sa ce ta janyo mata hakan kuma dai dai da minti daya bata taba jin soyayyarsa ta ragu a xuciyarta ba illa qara linkuwa da takeyi a duk lokacin da tayi toxali da shi, tana son el'mustapha, tana son kasancewa da shi a karo na biyu amma tasan abu ne da baxai taba yiwuwa ba. 1

Ta cigaba da kukan sosai, horn aka soma yi mata, ta dago da sauri bayan ta tashi tana kallon motar.

Glass din aka sauke a hankali, kyakkyar mace ce ta bayyana a cikin motar sanye da baqin glass, ta xare glass din tana kallonta qasa da sama.

'ke kuma me yayi xafi a duniyar ki da xaki xo bakin titi ki xauna kina kuka, titin ma irin wannan na abuja, baki tsoro ayi kidnapping naki ko masu yanka kai su dauke ki?

Jikin uwani ya soma rawa, batayi magana ba,

Matar ta bude mata daya bangaren na motar tace kixo ki shiga naga kamar a tsorace kike.

Ganin da uwani tayi mata na mace cikin shigar mutunci yasa batare da gardama ba ta xagaya motar da sauri ta shiga.

Matar taja motar ta qara juyowa tana kallon uwani tana yatsina fuska.

Ke kam hala bakya wanka ne, duk kin cika min mota da tsamin dauda, dubi jikin ki ko takalmi babu a qafarki, mtsewwwww ta dauki freshner tana fesawa a motar.

Uwani ta qanqame jikinta, banda hawaye ba abinda take, baa taba mata toxarci irin wannan ba yau an wayi gari da ko slippers ta rasa na sakawa a qafafunta.

Wani qatoton gida suka shiga flat house mai kyau da tsari,

Ta fito motar tana kallon uwani,

Ki fito mana....

Ba musu ta balle murfin motar ta fito jikinta na rawa.

Matar ta bude qofofin motar duka tana fadin gwanda tasha iska ko warin xai fita dana rufe ta, ta dube ta tana fadin ya sunan ki?

Uwani... ta bata amsa tana kallonta,

Daga ina haka, hala aiki kike a wani gidan kika masu ta'asa suka koro ki, masu aikin nan kun fiye sharri da mugunta.

Uwani ta girgixa kai tana hawaye tace kudi nake so naje gida,

Gida? Dama baa nan kike ba to me kika xo yi?

Sai ta tsinci kanta da kasa gayamata gaskiya wataqila idan taji labarinta ko tasan ita wacece baxata taimaketa ba xatayi tunanin itama xata cutar da ita.

'Mun xone da qawayena bikin aure sai na bata bayan na fito, kwana biyu kenan na kasa gano gidan kuma bansan yanda xan koma gida ba.

Ta yatsina fuskarta tana kallonta,

STORY CONTINUES BELOW


Ban yarda da wannan xancen ba, ba yanda xaa yi kixo abuja biki ki rasa kudin komawa a hannunki har ki kai wannan lokacin iyayenki ko qawayenki basu neme ki ba, hala haka ake xuwa biki gari wa gari ba jaka ko waya a hannunki.

Uwani tayi shiru gabanta na tsananta bugawa,

Xan taimakeki kiyi wanka kici abinci gobe na baki kudi kije garinku idan har da gaske kike,

Ni sunana Hajiya Mariya wannan gidana ne da mijina ya mutu ya barmin nida ya'yana, dukansu basa nan suna Cairo acan suke karatu, ni kadaice xaune a ciki sai qawayena dake yawan xuwa akai akai harma akwai masu tayani kwana anan, xan taimakeki nima ki taimakeni, shigo daga ciki ta soma tafiya.

Uwani tabi bayanta batare da ta gane inda xancen nata ya dosa ba.

Suka shigo hadadden falon nata sai kallo uwani take, tana yaba kyawun gidan a xuciyarta,

Ta ajiye qaramin gyalenta tana kallon uwani,

Da alama kina da kyau kina cikin daudar kenan naga hakan, ina ga kinyi wanka.

Shiru uwani tayi mata,

Ni bana so ana min shiru idan ina magana kuma bana son wannan kukan tunda nace xan taimakeni ki, ki saki jikinki idan kika bani hadin kai xakiji dadi, maxa share hawayen nan.

Da sauri ta share hawayen hade da washe bakinta cikin yaqe😁 ba dan ta so ba kada taqi taimaka mata.

Wanka xakiyi ko abinci xaki fara ci?

Ta qara washe bakin tana fadin wanka xan fara yi,

'Yauwa kinga kafin ki fito sai na girka maki abinda xakici dan ban ajiye ba, me kike so mai sauqin dafawa a yanxu dare ya soma yi.

Da sauri tace indomie da kwai da kifi sannan da drinks koma wane iri ne xan sha na dade ban ci ba.

'Yauwa yar garin haka nake so ki saki jiki kome kike so xan maki.

Uwani taji dadi sosai, rabonta da taci wani abin kirki harta manta, har wani sanyi take ji a xuciyarta,

Indomie nawa xai ishe ki dan ni a qoshe nake?

Idan qanana ce uku, idan manya ce biyu, ki soya min kwai biyar ki dafa uku duk xan iya cinyewa😁 4

Hajiya Mariya ta ajiye wayoyinta tana fadin,

'Ashe haka kike da ci amma bakya qiba, karki damu xan girka maki yanxun nan, xo muje na nuna maki inda xaki xauna.

Uwani tabi bayanta tana murmushi Allah ya taimake ta, 1

Wani daki suka shiga, ta bata towel hade da nuna mata qofar toilet, ta bude closet ta dauko wata doguwar riga mai kama da ta barci ta ajiye mata,

Kicire wannan kayan na fitar dasu a gidannan, ga rigar Aiman ki saka nasan xata maki duk girman ku daya.

Uwani tace wannan dakin kine?

Aa na Aiman ne itace babba, sai na qanin ta yaseer yana dayan bangaren can, su biyu ne ya'yana, idan kina so xaki cigaba da xama dani idan sun dawo sai na hada ki dasu ku xauna tare.

Ina so wallahi cewar uwani tana kallonta cikin murna,

'Yauwa bari naje na dora maki uwani, ta fita tana murmushi.

Uwani taji dadi, me Ma xai sa ta koma gida inda ake mata baqin ciki gwanda ta xauna da wannan matar ta lura Sam ba munafurci ko baqin ciki a xuciyarta, gashi har ya'yanta take kai waje Cairo suyi karatu amma ita an barta Nigeria tsabar mugunta bayan akwai kudin, shiyasa taqi karatun ma, inma ta koma gida suka matsa mata da karatun sai dai akai ta Cairo itama. 5

STORY CONTINUES BELOW


Ta cire kayan ta daura towel, ta dauki kayan cikin kyankyami, dama xan ga Serdia ko qaumi da na basu wannan kayan, nasan suna so, ko Sural na ba ma xata so, ta tuna ma ummy da Sumy Ma suna so, qila ma harda Kdeey tace tana so,

Ta fito tana kiran mama a yangance,

Hajiya Mariya ta fito kitchen da wuqa a hannunta tana kallon uwani,

Tace ina xan xubar da kayan ne kafin mmn boy ko Ayusher Mohd suxo su dauka?

Har akwai wanda xaiso wannan kayan ne kamar nuceey da Billy, duba waje akwai dustbin xuba aciki tsakanin mmn khady, hajja ko Seemby Luff duk wanda yayi saurin xuwa ya dauka, in kuma sadiya nagwari tayi saurin dauka shikenan.

Uwani ta fita da sauri da kayan a hannu cikin kyankyami, inda ma xata ga Sally ko mom of 12, ko Zahrah ko xoxo duk xata basu harda ma zuhura suje su kashe kansu,

Hajiya Mariya ta bita da idanu tana kallon uwani acikin qaramin towel din, xata mori yarinyar da alama, uwani ta dawo tana dariya. 1

Mama na xubar...

'Yauwa uwani je kiyi wanka kici abinci yau kwana xamuyi hira mai dadi kinji,

Cikin farinciki tace tau shikenan, ta shige dakin da ta fito, har wani tsamin datti take jin tana yi a yanxu da tun daxu bata jisa ba, tana shiga toilet din ta shige bathtub, kwana biyu baa hadu ba, ta cire towel din ta ajiye gefe, pant din Ma tana cire shi ta yarda.

Harda kanta tana son wankewa dan yayi datti, wajen neman abin wanke kan ne taci karo da abin maxa na roba (dick)

Ta saki ihu cikin rudewa wanda ya janyo hankalin hajiya Mariya xuwa toilet din da sauri,

Tana shiga ta sami uwani ba komai a jikinta sai ihu take,

Ke lafiya meya faru,

Tace mama kayan yaya el'mustapha nagani?

Menene shi ta tambaya cikin tsananin mamaki,

Uwani ta nuna mata jikinta na rawa, tabi yatsan uwani da kallo inda yake nuna mata, tana gani ta sauke numfashi hade da Jan guntun tsaki.

Tace kin sanshi kenan?

Tace eh na yaya el'mustapha ne,

Waye kuma el'mustapha?

'Mijin anti jiddah ne,

Oh..... Hajiya Mariya ta fada tana kallonta, da alama baxata sha wuya ba tunda har ta san abin, amma me mijin yayar ta yake mata da abin.

Yi wanka ki fito xamuyi magana.

Uwani tayi saurin katse ta tunda take a rayuwarta bata taba ganin wannan abin haka ba, bayan na yara da take gani na el'mustapha kadai ne xatace ta taba gani a cikin manya shima sau daya a Lagos,

Tace meyasa kika dauko masa abinsa, ki bani na maida masa.

Karki damu xamuyi magana qila idan kinji dadin abin xaki manta da wani ki maida masa kayansa,

Hajiya Mariya ta fita ita duk a tunanin ta uwani na nufin yana da irin sa ko kuma nasa ne ta dauka bata san ita kuma uwani na jikin el'mustapha take tunanin kamar ta ciro ne😂 3

Uwani na wanka tana kallon abin, tana tuna daren su na farko da el'mustapha, a gurguje ta wanke kan nata tayi wanka ta fito tana kallon abin.

Kicibis sukayi tayi karo da hajiya Mariya tsakiyar dakin da qaramin towel a hannunta,

'Yauwa baby har kin fito,

Uwani tayi murmushi cikin jin dadi har wani baby take kiranta qilama haka take kiran yaranta,

Ta gyada kai tana kallonta, gashi ki tsane jikin kafin naxo idan baki iyawa kijira naxo na yi maki har kayan Ma na saka maki bana so 'ki wahala sosai.

Wani dadi ya qara kashe uwani, yaushe ma hajiya xata ce bata son ta wahala, qila tun tana qarama rabon da hajiya ta saka mata kaya kome ita ke Ma kanta shiyasa ta girma babu alamar hutu ko jin dadi a tare da ita, wannan matar ya'yan ta sunji dadi harta so ta gansu.

Bari naje na duba girkin, ga wani hadi na kawo maki a wancan Cup mai dadi kisha harda madara a ciki, ina so najiki cikin ruwa sosai.

Wani dadi ya qara kashe uwani kai lallai matar na son ta yanda take kula da ita tana bata abun dadi haka, ita kam yaushe Ma taga lokacin barin gidan ballantana taje ga iyayenta, ta leqa Cup din tana murmushi, harda yawun ta ya tsinke.

Nagode mama, naji dadi.

Tace karki damu duk yiwa kaine ai, bari na baki wuri ki shirya, ga turare nan Kala Kala masu sanyin qamshi kisa ko ina kuma kowace kusurwa a jikinki, nima yanxu xanyi wankan na fita.

Uwani ta gyada kai tana washe haqora farin ciki fal a xuciyarta, matar ta juya ta fice, ita kuma ta xauna bakin gadon tana kallon doguwar rigar da aka bata ta saka.

Post a Comment for "EL-MUSTAPHA CHAPTER 6"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...