Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

EL-MUSTAPHA CHAPTER 5

EL-MUSTAPHA CHAPTER 5

- - Post a Comment
EL-MUSTAPHA

CHAPTER 5

Jiddah ta dake xuciyarta wajen baiwa el'mustapha lokacin ta a rana, kulawa take bashi kamar yanda shima yake dar'dar da ita na ganin ya kauce duk wata hanya da xata saka ya batawa jiddansa.
'Washe garin ranar da uwani xata karbi girki, tun da sassafe aka tashi aka shiga kitchen, abinka da wanda bai saba shiga kitchen yayi girki ba sai dai ayi mata a kawo mata taci, duk sai ta rasa yanda xatayi bata san inda xata fara ba, sai ta kunna gas ta dora ruwan xafi tasan dole dai dasu ake hada tea,

Tasa yatsanta a baki tana tunani, ai taga kamar ruwan tea din suna da kayan hadi harda masu qamshi a ciki to menene ake sakawa bayan Lipton? 1

Ita abin kunyane yanxu taje gun jiddah ta tambayeta ai xata raina mata wayo musamman da ta tuna sanda suna gida jiddah ta taba yi mata fada akan ta daina kwanciya kawai ta riqa xuwa suna aikin abinci tare yanda xasu iya amma taqi, ita a ganinta tafi qarfin shiga kitchen. 1

Banan ta fado mata a xuciya, ta nufi sashen masu aiki,

'Yauwa banan xo muje ki tayani girki dan Allah, ta fada cikin murmushi tana kallon banan tunda ita ke nema.

'Anty uwani kaina yake min ciwo tun jiya kiyi haquri.

Masu aiki dan suna ciwon kai shikenan baxasu yi aiki bane ko me, kada ki bata min lokaci fa.

Kallonta banan tayi tana fadin, ana dole ne ai ba ke nakeyiwa aiki ba, in haka ne ki sami taki mai aiki mana ni anty jiddah kadai nake Ma aiki a gidan nan.

Ganin in batayi da gaske ba banan din baxata xo ba sai ta marairaice tana rarrashin banan dan kawai taxo, suna haka jiddah taxo, jin abinda ke faruwa ya saka tayiwa banan din magana akan taje ta kama mata.

Anan suka bar jiddah cikin masu aikinta,

Cikin lokaci qanqani suka gama komai, uwani aka yi wanka, wata doguwar riga ta saka gaba ki daya ta matseta ta fito da surar jikinta, qirjinta Ma a sama duka a bayyane, Arham ya fara ganin ta aikuwa da gudu yaje cikin gida yana kiran jiddah,

Momy xo kiga mamman anti uwani a waje,

Kallonsa jiddah tayi ko kadan hankalinta bai bata sauraren abinda yake fada ba,

Kai kuma daga ina haka, daddy ya tashi barci ne, ya gyada kai yana kallonta, tashi tayi ta nufi cikin gida.

Lah daddy dubi mamman anty uwani, aryan ya fada yana nunawa el'mustapha lokacin da suke fitowa.

Kallonta el'mustapha yayi daga qasa har sama sai ya dauke kansa dining ya nufa dai dai lokacin da jiddah ta shigo tare da arham,

Idanunta akan na el'mustapha tana murmushi, shima murmushin ya maida mata,

Arham ya dubi el'mustapha, daddy kaga mamman anty uwani.

Uwani ta dubeshi a fusacce, a ranta tace xakaci ubanka ne bari na damqeka, sai a lokacin jiddah ta kai kallonta ga uwani, ta kasa boye mamakin ta, wannan wace shiga ce uwani tayi.

'Nikam uwani da kin sauya wannan rigar cewar jiddah tana qoqarin xama kusa da el'mustapha. 1

Saboda me? Uwani ta tambaya tana kallonta cikin harara.

Saboda ya'yana, basu saba ganin wannan haukar ba kinga sai magana suke ai kada a lalatamin tarbiyar yara, su taso suna sabawa iyayen su.

Sai ki kauda idanunsu daga kallon jikina, amma nida gidan mijina baxaa xabamin kayan da xan saka nayi masa kwalliya ba, ke idan bakya masa ni kinga inayi.

STORY CONTINUES BELOW


'taya akayi kika san bana masa, dole sai na fito na nunawa kowa ne ko kuma sai na fada, macen da bata da sirrin kanta ballagaza ce, macen dake bayyana sirrin mijin ta wawiya ce, macen da xata nunawa duniya mijinta ya kwanta da ita ba kunya a tare da ita jahila ce, idan kwalliya xaki masa kiyi daga ke sai shi amma ba irin wannan gidan da aka hada da iyali ba, so Aisha aje a canxa kayan bana son ya'yana suna kallon abinda ya haramta a garesu kada suje suna leqen na wasu. 1

Uwani xatayi magana cikin tsiwa el'mustapha ya katse ta cikin fushi,

Get out pls.....

Yanxu honey ni kake wulaqantawa a gaban matarka da ya'yan ka, menene laifina dan na maka kwalliya, saboda na faranta maka ne na sami lada.

Yace baki ji ba kenan baxa kije ki canxa kayan ba? Uwani ta fice a fusacce batayi mgn ba.

Bata fito ba sai da ta tabbatar ya bar gidan, still da rigar ta fito aryan na ganinta yayi dakin mamansa da gudu yana fadin,

Momy xo kigani bata cire ba akwai mamman ta a waje,

Sai na fadawa daddy arham ya fada yana kallonta, bugu ta kai masa hade da qara bige masa baki, ya saki kuka hade da nufar dakin jiddah, bayansa tabi tana fadin uwarka Ma ciki nake da ita ko ita xan iya duka a gidannan.

Momy anti uwani ta dake ni anan da baki,

An dake ka ko akwai uban da xai rama Ma kane?

Babu shi, jiddah ta fada tana kallonta, saboda me dan kin daki yaranki a rama masu? Ta dubi twins, kuba anti uwani haquri kuxo kuji.

'Anty uwani kiyi haquri suka fada lokaci daya kafin su nufi jiddah,

Uwani taji haushi taso jiddah ta tanka mata ne ta mata dukan tsiya, meyasa jiddah ta cika sanyin xuciya da haquri ne, ita wlhy ynxu ko kunya da nauyinta bata ji kallon kishiya take mata wace basu taba sanin juna ba sai xaman aure da ya hada su. 1

Naxo inma mutum gargadi akan a daina sakamin ido a al'amurana wlhy kome xan iya Ma mutum a gidan nan, babu wata dangantaka ko xumunci tsakanina da kowa a gidannan sai xaman kishi ehe, mtsewwwww ta fice.

Jiddah tabe bakinta kawai tayi, ta dubi arham har lokacin hawaye yake yi, taja dogon hancinsa tana murmushi.

My boy babu jarumta, duka kake Ma kuka, babu ruwanku da anti uwani da kayan da take sakawa, share hawayen ka kuma kar naji an gayawa daddy.

Nidai momy sai na gayamasa anty uwani ta daki arham yayi kuka cewar aryan yana tunxuro baki.

Kuyi haquri baxata qara dukan kowa ba, inma ta qara ni xan rama maku, back to our lesson, kowa ya dauko nayi masa marking naga wayafi qoqari, suka fita da gudu.

Bata jima da sallame sallah ba el'mustapha ya shigo,

Yauwa ba sai kin cire hijab din kixo xamuje ku gaida mama bata lafiya.

Sun fito uwani sai tunxure tunxure take Allah ya gani batayi niyar xuwa ba ita ina ruwanta da mamanshi da xataje gaidata bata da lafiya,

Gidan gaba ta shiga tana fadin ai girkin tane ita xata xauna da mijinta, murmushi kawai jiddah tayi ta shiga baya tare da twins din ta, el'mustapha kuwa ko kallon inda take baiyi ba.

Yaran da gudu suka nufi mama, sun kwana biyu basu je ba sai murna suke, ita Ma sosai taji dadin ganinsu harda yayyun el'mustapha mata duka sunxo dubinta.

Jiddah ta gaidasu kafin ta nufi mama tana yi mata ya jiki.

Uwani kuwa gefe taja tunga tana fadin ina wunin ku.

Suka amsa ba yabo ba fallasa musamman sun san uwani a gidan jiddah basu jituwa da ita sai gashi taxo ta auri qaninsu inda suka qara jin tsanar ta kenan.

STORY CONTINUES BELOW


El'mustapha takaici ya rufe shi, ko ya jiki baxata iya Ma mahaifiyar sa bane,

Mama Ma kallonta kawai take tana Allah ya wadarai a xuciyarta, dakin sai hira ake da dariya banda uwani dake cika tana batsewa ita matar AIG😂. 1

Sun jima sosai ganin dare yayi twins har sunyi barci ya saka suka fito,

Abincin da tayi ranar qin ci yayi yaji ya qara tsanar yarinyar tunda baxata iya girmama iyayenshi da yan uwansa ba, juice kawai ya sha abinda bai sani ba uwani ta saka pills a ciki😀 1

Sanda ya fara jin feelings sai ga uwani ansha kwalliya cikin wata farar night gown, tayi kyau kam, kallonta kawai el'mustapha yayi wannan karon abin baiyi qarfi kamar wancan ba,

'me kike min a daki?

Honey kaine fa kace duk ranar girkina naxo muriqa kwanciya tare nayi missing dinka kwana biyun nan haquri kawai nake.

Kallonta yake da idanunsa da suka rikide xallar sha'awa ce aciki sai ya fara ganinta kamar jiddansa, uwani taxo tana shafa jikinsa, qirjinsa har cikin kansa.

Hannu yasa ya rungumota yana kissing din ta, hancinsa ya kai dai dai wuyanta yana shaqar qamshin jikinta, uwani da kanta take cire kayan jikinta yanda xataji dadin abin.

Tsura mata ido yayi yana kallonta lokacin da take qoqarin cusa harshenta cikin bakinsa.

Ya kauda kansa gefe, kamar wanda aka tsikara ya miqe xumbur ya bar dakin,

Takaici kamar xai kashe uwani, harda xaginsa a bayyane, sai da ta fara jin dadin abin xai guje ta, ita ta rasa gane wane irin turare ne wannan yake amfani dashi mai dadi, ta fito dakin bayan ta rufe jikinta kallon qofar dakin jiddah take.

Kambu ni xaa kaiwa wata kwana na, bala'i wannan Ma cin amana ne wlhy baxan yarda ba.

Kamar a mafarki jiddah taji ana shafar jikinta ta bude idanuwanta a hankali, baxata iya ganinsa ba saboda duhun dakin qamshin turarensa taji ta gane shi, ta riqe hannuwansa da sauri lokacin da yake qoqarin cusa su a cikin rigarta.

'kai kuma yaushe ka fara shige ne,

Baiyi magana ba, sai ta fara qoqarin janye jikinta,

Cikin murya rada rada a kunnuwanta yake mgn,

Let me, pls jiddah I can't control my self bansan meyasa ba.

Meya sami uwani ne, ko ka manta girkinta ne.

I know jiddah, bana son uwani, I don't want anything from her, she can't satisfy me.

Idan kayi haka baka kyauta ba, ka dauko kwananta ka kawo min batare da amincewar ta ba, munci amanar ta, nima baxan so ayimin hakan ba, yaushe kadawo haka el'mustapha, yaushe sha'awa ta fara maida ka haka, you can't control yourself why? Kodai wani abin kaje ka sha ne?

Nima ban sani ba jiddah, pls help me kada ki gujeni.

Ni baxan iya ba ta fada a fusacce bayan ta juya masa baya.

Shikenan jiddah ki barni na mutu sai ki huta, yayi xaune ya dafe kansa da hannuwansa duka biyu, dakin har wani juyamasa yake,haka yaji marar sa ta fara ciwo, ya juya yana kallon jiddah a karo na biyu ji yake kamar ya kamata yayi mata ko ta qarfi ce amma he can't baxai iya Ma jiddah hakan ba.

Jiddah bakya tausayi na yanxu, kinsan me nake ji kuwa, tunda nake dake baki taba juya min baya ba sai yau why jiddah? Muryarsa ta fara rawa kamar xaiyi kuka ita kanta dake kwance qarfin hali kawai take amma tausayinsa ya cika xuciyarta, bata juyo ba har sanda taji ya kwanta a bayanta, tana jin fitar numfashin sa da sauri da sauri, ta matsa kadan kafin ta juyo tana kallonsa.

STORY CONTINUES BELOW


Kasani saboda son ka baxai sa na cutar da waccan ba Allah xai kamani da laifi saboda me baxakaje gare ta ba.

Wata dabara ta fado masa nan take a xuciyarsa, da kyar ya iya magana.

'Na yarda kije yanxu ki tambayeta kiji, period take yi jiddah itace ta amince min.

Ita uwanin?ta tambaya cikin mamaki,

Ya gyada kansa, bai yarda ta qara magana ba ya fisgota matse ta yayi sosai a jikinsa.

'Washe garin ranar bai bar dakin ba sai da jiddah ta gayamasa cikin da take dauke dashi.

Are you serious?ya tambaya cikin tsananin mamaki, ta gyada kai tana kallonsa da murmushi,

Jiddah na ba haquri, kin dora min auren da bana so saboda ya'ya yau gashi Allah ya baki bai bata ba, meke nan, nikam kin cuci rayuwata na hadani da waccan matar.

Ta lakaci hancinsa tana dariya, dama can matar kace believe me nice sanadi amma uwani tana cikin qaddarar ka, kadaina cewa na cuce ka mijina ni kaina na cuci kaina *NAYI NADAMAR* auren ka da Uwani.

Ya juya yana fadin xo in goyaki jiddana, na nuna maki farin cikina akan wannan cikin, ina maraba dashi kuma ina tsananin qaunarsa kamar yanda nake son jiddah.

Da sauri jiddah ta haye bayansa tana dariya, ta sumbace shi tana fadin, Allah ya barmin kai mijina, ina sonka el'mustapha💕💕💕💕💕💕

Uwani bata nunawa jiddah komai a fuska ba amma a xuciyarta ta barwa kanta sani, ko ni pherty banda masaniya akan wannan🤧

Bayan kwana biyu jiddah ta shirya xataje gida ganin su hajiya ta kwana biyu bata je ba, sai ta tambayi uwani ko xataje.

Tace baxan jeba, inma xan je ne batare da ke ba, nida iyayena anuna min anfi son wata bare dani, ni saboda me ma xanje na gansu mutanen da basu farin ciki dani basu farin ciki da aurena.

Jiddah tace shiyasa kika kasa ganin haske a rayuwar auren ki, kin kasa gane inda mijinki ya dosa akanki saboda iyayen ki suna fushi dake kuma ke baxakije ki nemesu gafara ba taya kike son rayuwar auren ki tayi kyau.

Oh no wonder ashe kece kika nuna masa kada ya soni ya kulani saboda naqi naje na nemi gafarar iyayena, ki gayamin xagin su nayi, dukan su nayi kome, saboda me xasuyi fushi dani?

Allah ya baki haquri uwani ni ban isa na aibataki a gurin mijinki ba sai ma qoqarin na gyaraki naga kun dai dai ta.

Ki gyarani yanda kike nufi yanxu a lalace nake, ok kece xaki gayamasa ya soni, gaskiya ni wannan rayuwar ta isheni anci amanata ashe da gangan aka amince na aure shi a cutar dani ba dan tausayi na ba, nikuma yau Aisha sai na fada auren mijin hajiya mijin tace, da anyi magana yace wani jiddah wai jiddansa bako kunya harda wani jiddatulmusty, to wlhy nima na xama Uwanitilmusty a gidan nan ai nima matar shi. 5

Murmushi kawai jiddah tayi, ita kam yanxu uwani tsoro take bata ta daina bata mamaki, sai kace ba tare suka taso ba amma yanxu uwani rashin mutunci ba wanda batayi mata.

Yanxu dai baxa kixo muje ba,

Eh baxan je ba, inkinje ina gaidasu idan kuma baa so a maidamin gaisuwata ba dole, ina tashi xanje da kaina, idan na biki ko anyi niyar yafemin aka ganki sai a fasa gwanda naje ni kadai kuma kada a qullamin wani munafurci kuma.

Jiddah ta fice tana dariya, kallon mahaukaciya take Ma uwani a ynxu Sam bata mata kallon masu hankali.

A gurguje😏

5 Months....

Lokacin cikin jiddah yana cikin wata bakwai, sai yanxu yake fitowa, haka halittar ta take jikinta baya nuna girman ciki.

Duk abin nan da ake a gidan uwani bata taba sanin jiddah nada ciki ba, tuntuni el'mustapha ya bata jari ta fara business irin wanda jiddah keyi before, duk inda tasan jiddah na kai kaya can take kaiwa ana siye jiddah bata taba kula taba,

Ynxu bata el'mustapha take ba, ba ruwanta dashi ta kudin ta take, sai sufi kwana biyar Ma bata saka jiddah a idanuwanta, tun da safe xata bar gidan tunda an bata mota itama xataje gidan qawayenta baxata dawo gidan ba sai lokacin dawowar el'mustapha kada yaxo gidan batanan ne dalilin daya sa take dawowa.

Babu ruwanta da kowa a gidan, ta xama hajiya ita kadai ke rayuwarta el'mustapha ne kawai tun da safe aje a gaidashi idan ya dawo aiki aje a gaidashi shima dan ana son sane wai da ko ganinta baxai yi ba.

A lokacin saura wata uku auren su ya qare dashi kuma tana sane ita kadai tasan abinda take saqawa a xuciyarta tare da jamcy.

Ranar da taga cikin jiddah sosai hankalinta ya tashi ta kasa boye mamakinta.

Anti jiddah cikine dake, yaushe ma kikayi cikin?

Jiddah ma kallonta take da mamaki?

Inayi ciki sai na gayamaki nayi ciki ne, ko xan fito in fadawa duniya mijina ya kwanta dani yayi min ciki.

Oh oh ai ba abin fada bane Allah ya baki haquri, dama masu ciki sun fiye xafin rai, tasa kai ta fice.

Hankalinta yayi matuqar tashi ta kira jamcy ta gayamata harda kukanta tana sharce majina.

Ya akayi ke bakiyi cikin ba, kinsa wasa ba kince bakida lokacinsa ba ai kuwa xaki gani tana haifa masa yara yana mutuwa ta tashi da dukiya ke kuma zero.

Ki gayamin ya xanyi,

Ke nifa nabi saurayina xamuje America ko mahaifiyata bata sani ba kinsan xatamin baqin ciki ta hanani xuwa ni kuma ban taba xuwa can ba baxan haqura ba, kibari idan na dawo xaa san yanda xaa yi.

'Ashe bani kadai iyaye kema baqin ciki ba harda ke,

Kedai bari kawai sai na dawo ta tsinke wayar.

Uwani ta kasa haqura ranar da kyar taga tayi barci tunda sassafe ta nufi a asibiti a gwada ta idan bata da ciki.

Anyi test ba komai, negative, banda abin uwani inma akwai shi wata biyar ai xaa sani.

Da kukanta take kallon likitan,

Wlhy sau biyu yayi min kace bani da ciki, amma ita gashi nata cikin ya fito, so kake na xama bora a cikin gida, dan Allah laifin me nayima kaima kake baqin ciki dani. 1

Abin ya daure masa kai, mamaki bayyane a fuskarsa,

Yace abinda babu xan maki qaryar akwai ne, ko sau dubu kikayi ba biyu ba kuwa, ina ruwana da ko sau nawa aka maki ne.

To yanxu likita ba yanda xaayi kasamin cikin ne ya fito, ance komai likitoci sunayi, dan Allah ka taimakeni ko nawa ne xan biya nidai kasamin cikin yanxu in ganshi da girma ya fito, ka taimakeni likita kada kamin baqin ciki.Sororo yayi yana kallonta, +

In sama ki ciki ni Allah ne?

Ba haka nake nufi ba Doctor, meyasa kuke sanin mutum yana da ciki, meyasa kuke duba idan mace ne ko namiji a cikin mace, meyasa kuke sanin idan yana motsi ko bayayi, meyasa kuke fitar da yaro daga ciki matacce ko raye, indai xaku san wannan ai xaku san yanda xaku sawa mutum ciki, ni ko nawa ne xan biya naxo da kudina a jaka.

Ke tashi ki barmin office, ina tunanin baki da hankali, something is wrong with your brain.

Allah yasa ba kai kadai bane likita a garin, kuma kaine baka da hankali,

Ya tashi a fusacce yayo kanta tana ganin haka ta fice da gudu tana xaginsa.

Tana fitowa harabar asibitin ta hadu da yusuf da surry, har surry xata mata magana yusuf ya hana yaja hannunta suka bar gurin.

Ita ba wannan ne gabanta ba, cikin da tagani jikin surry ya kara tada hankalinta, jiddah da surry duk ciki ne dasu xasu haihu su barta, yusuf din Ma kamar bai san ta ba shege mayen mata maciyi amana, ka aure min qawata ban yafe ba Allah xai saka min, gashi har tayi ciki.

Cikin motarta ta xauna tana kallon masu shige da fice a asibitin, duk mai ciki ta wurga xata bita da kallo kamar mayya, ita mamaki take yadda akayi su sukayi cikin ita batayi ba tunda har sau biyu yayi mata, to ko sai anyi sau uku ne ta fada tana kallon wata mai ciki da ta fito asibitin, ko xata tambayi matar ne ta gayamata sau nawa aka mata ta sami cikin. 2

Duk ma laifina ne dana daina kulasa na daina sa masa pills ko ranar girkina, xanyi amfani da wannan dama ta yau in saka masa duk abinda xaa yi ayi nima ya min ciki in huta da gori da yan baqin ciki dan sai na sami dukiyar nima.

Da wannan tunanin uwani ta isa gida.

Tana shiga falon ta taradda jiddah xaune a falon, banan xaune a qasa tana tausa mata qafafu twins suna wasa tsakiyar falon.

Cikin jiddah kawai take kallo har ta shigewarta daki, xama tayi tana neman mafita, jiddah bata isa ta haifi cikin nan a gidannan ba, nasan me xanyi.

Da dare ita da banan sun gama girki saboda ita ke tayata dan bata iya komai ba,

Sun jera komai a dinning, ta duba ba kowa a falon tsit da sauri ta nufi dakinta ta dauko pills tana xuwa ba tunanin komai ta xuba acikin juice din el'mustapha,

Naganki cewar banan tana shigowa falon dauke da kaskon turare a hannunta.

Wata irin faduwar gaba ta same ta lokaci daya, ta juya tana kallon banan.

Me kika gani?

'Na ganki kina sa abu a juice din yaya,

To ba dai magani bane dan ni bana bin bokaye.

Baxan gane haka ba cewar banan, bayan ta ajiye kaskon ta qaraso inda uwani ke tsaye tana kallonta,

Uwani ta dube ta rai a bace, wai ke wane hurumine dake a gidannan bayan xaman ki mai aiki, ki kiyayeni fa ina ruwanki da abinda nakeyi, ah ah kujimin yarinya da rainin wayo.

Tau shikenan naji tunda ni mai aikice xan tsaya matsayina, dama kafin a daukeni aiki a gidannan an min gargadin karna cutar da kowa a gidan kuma kada na bari a cutar, dan haka xan gayawa anti jiddah cewa na ganki kina sa wani abu a juice din yaya.

STORY CONTINUES BELOW


Uwani ta rude ta soma rawar jiki, ta riqo hannun banan, ke meyasa kike min haka ne, kixo mu hada kai muji dadi a gidannan, ni xan maidaki ma yar riqo na ba yar aiki ba.

Ai kinji matsalar ni xuciyata bata da dogon buri da kwadayi irin naki, uwar dakina uwar rainona bata koyamin haka ba, bata saka min kwadayin duniya da cutar da wani ba, ta koyamin yanda xan xauna da mutane da xuciya daya koda kuwa mutum yana bibiyata da sharri ne, ta koyamin yanda xanyi mu'amala da mutanen kirki, bata gina min xuciya da sharri ko cin amana ba, ta riqeni da xuciya daya baxan bari a cutar da ita ko wani nata ba, xuciyata bata manta alheri komai qanqantarsa, ta sakamin da alheri na saka mata da sharri Sam wannan baxai yiwu ba, mafita daya ce xan rufa maki asiri amma da sharadin sai kin shanye wannan juice din dakike ikirarin ba magani kika xuba akai ba.

Ke wlhy baki isa ba, kinyi kadan, baxan sha ba, ke wacece da har xaki sakani yin abu, who d hell focus are you, stupid kawai😂 3

Damn you Banan ta fada tana kallonta dai dai lokacin el'mustapha ya shigo, dawowarsa daga masallaci kenan,

Kallon uwani yayi kafin ya maida kallonsa ga banan dai dai lokacin ta juyo tana kallonsa a karo na uku😊

Da kyar ya bude bakinsa yana kiran jiddah a hankali kamar bayason magana.

Jiddah ta fito tana kallon mutanen dake falon.

Yaushe mai aikin naki tayi matsayin da xata tsaya da matar gida suna sa'in sa, am not siding uwani amma ina son sanin dalili ko ba komai uwani ta girmeta kuma gidan auren tane.

Jiddah ta dubi uwani kafin ta maida kallon ta ga banan, jikinta yayi sanyi ita kam bata son tashin hankali a rayuwarta.

Kullum ina gayamiki banan kima uwani biyayya, matar mai gidance a qarqashin ta kike meyasa ba kya jine.

Anti jiddah nagayamaki baxan iyama anti uwani biyayya ba, baxan daina sa'in sa da ita ba, nafiso akanta na bar aiki a gidannan.

Meyasa banan, kina so kijawo min matsala ne bansan yaushe kika fara taurin kai ba.

Ba taurin kai bane anti jiddah, bansan meyasa kika yarda da anti uwani ba, bansan meyasa kike son ta ba, bansan meyasa kike tsoron ta ba, matar nan bata son ki bata qaunarki, matarnan bada xuciya daya take xaune dake ba, matar nan ya'yan ki ma bata so...... bata qarasa ba uwani ta dauke banan da Mari.

El'mustapha ya dubi jiddah yana fadin, har yanxu baki san kanki ba jiddah, har yanxu kinkasa gano abinda ake gaya maki game da uwani, your housemaid can you imagine, taya akayi ta fiki tunani.

Kece bana so amma baki isa ki hanamin xama da yar uwata jiddah ba, kina min baqin cikine saboda tana sona da tausayina ta barni na auri mijinta, ni nace bana son ta munafukar banxa, ba yanxu kike roqona kidawo hannuna da xama ba saboda jiddah na cutar dake, saboda na baki haquri nace ki xauna jiddah mai kirkice shiyasa kika tsaya kina min rashin mutunci.

Banan ta fashe da kuka, ga xafin Mari ga sharri, ta dubi jiddah.

Wlhy qarya take min anti jiddah itace ta nemi na dawo gurinta mu hada kai mu cutar dake wai in sami arxiki shine naqi, Allah ne shaidata anti jiddah.

El'mustapha ya gyara tsayuwarsa yana kallon banan akwai wani abu da yake son ganowa game da ita, meyasa yake jin faduwar gaba a duk lokacin da suka hada ido da yarinyar? Yace xo nan banan,

Banan ta nufesa da sauri tana kuka, a rude take da wannan sharrin da uwani ke qoqarin dora mata.

Jiddah tace el'mustapha kabar banan nasan gaskiya take gayamin baxatamin qarya ba kuma nafi yarda da banan akan uwani, kome akace uwani tayi bana musu akai.

Uwani tace saboda na xama shegiya, dole xaa taru a hade min kai yanxu saboda ana son rabani da gidan aure na, baku isa ba.

Me kikewa sauri uwani, wata uku ne kacal kibarmin mijina, wata uku ne kacal kibar min gidana, na daina ganinki, *Nayi Nadama* matuqa hada auren ki da mijina na taimake ki saboda iyayenki, ciwonki da qudurinki da naji game da mijina, ashe ke bada xuciya daya kike xaune dani ba, so kike ki fitar dani daga gidan ki mallake mijina da komai nas.... Uwani ta katseta,

STORY CONTINUES BELOW


Sharrin da xakimin kenan, na shiga uku ni Aisha wlhy anci amanata Allah baxai bar mutum ba,

Yace gayamin banan abinda ya hada ki da uwani har kuke fada yanxu,

Banan ta gayamasu komai tana rantsuwa, uwani kamar tayi hauka a falon sai ashar take durawa anci amanarta.

Yace koma menene kanki xai koma uwani, hannunta ya riqo suka nufi dining, juice din ya dauka ya bata hade da xaro bindigarsa,

Ko ki sha ko na dauke kanki da bindiga yanxu, na kashe banxa ba wanda xai tuhumeni dalili, xansa Ma a jefar dake a bola I don't care.

Uwani ba alamar tsoro a tare da ita ta karbi juice din tasha sosai, ta dube su,

Nafi qarfin na cutar da mutum ehe, ni bana bin bokaye da malamai, banayin asiri, duk wanda ya xargeni baxan taba yafe masa ba, kune xaa kai gawar ku bola bani ba, sai ta fara lumshe idanuwanta tana matse qafafuwanta.

El'mustapha ya dubi banan, ke bar falon nan, sum sum ta fice.

Amma el'mustapha meya sami uwani ne take matsar qafafu,

Yaja hannun jiddah suka xauna, yace ki barta yanxu na gane uwani ta cutar dani, pills take sakamin na sha'awa saboda na kusance ta, ta sami abinda take so for the first time a Lagos.

Nan ma ta taba sakamin har naje gareki kina mamakin me nake sha, ina ji shine banan ta kamata tana sakawa a yanxu har suke fada, just look at her tana cikin tsananin buqata.

Kayi haquri ka duba mata, ka tausayamata pls, 1

Ya dubeta da mamaki, in tausayamata as in how? What are you saying jiddah, wai meke kanki ne meke damun kine, in tausayamata tana niyar cutata tana samin pills ina sha, idan wani abu ya same ni fa ko bakya tunanin yana da side effect ne, waya sani ko over dose take min, sanda naxo gareki menene banyi ba dan ki tausayamin kika qi sai da na hada maki da qarya, ba tun yau na fara sanin kin fison uwani akaina ba qaryar so kike min, just leave please.

Ta kama baki, tayi rau da idanunta kamar xatayi kuka.

Meya kawo maganar nafison uwani da kai, banji dadin nagetive respond din ka ba.

Ai kece da wani irin Batu jiddah, meyasa kike tausayinta akaina, wai har sai yaushe xaki gane matar nan bamai qaunarki bace, kiji abinda mai aikin ki kecewa, kin fara bani haushi a yanxu, sanyin halinki ya soma isa ta, haqurin ki yana cutar dani.

Kayi haquri idan na bata Ma el'mustapha, amma uwa....... Ya katse ta a fusacce abinda bai taba yi mata ba,

I said leave jiddah.... da kyar ta tashi saboda cikin jikinta, ta fice tana kallon uwani cikin tausaya mata, el'mustapha ya bita da kallon takaici, ya rasa gane wace irin mutum ce jiddah, Sam bata san ciwon kanta ba.

Kukan uwani ya dawo dashi daga tunanin da yake, ya tashi ya nufe ta, Jan ta yayi xuwa dakinta ya tura ta da qarfi, ta taso da sauri tana roqanshi ya taimaka mata, sai shafa shi take tana qoqarin cire masa trouser kamar xata mashi fyade🤭

Ba xato uwani taji saukar Mari a kuncinta, gefen bakinta ya soma jini ta saki wani ihu tana faduwa tana tashi a gurin,

Jiddah ta kasa samun nutsuwa, tana jin uwani a xuciyarta kamar qanwarta da suke uwa daya, tare suka taso da uwani akwai shaquwa sosai tsakanin ta da ita, bata son abinda xai sameta koba komai amanarta iyayenta suka bada ta, ta riqe qasan cikinta tana yatsina fuska saboda nauyinsa da take ji a yanxu, da kyar ta fita jin ihun uwani yaqi ya tsaya,

Tana shiga dakin ta sami el'mustapha na dukan uwani da belt, duka bana wasa ba kai da ganin fuskarsa kasan ransa a bace yake sosai.

Jiddah taji tsoro, gata da tsoron duka batasan yanda xata kwaci uwani hannunsa ba, qarin abin kar yaje ya dakar mata ciki a banxa.

Ta soma bashi haquri tana kuka sosai hankalinta yayi matuqar tashi sosai.

Ko inda take el'mustapha bai kalla ba, yasa kai ya bar dakin, uwani na kwance sai nishi take ta nufe ta da sauri.

Karki tabani munafuka, wlhy kashe ki xanyi uwani ta fada tana nuna ta da yatsa.

Jiddah ta fita daga dakin harabar gidan ta nufa ta kira driver ya kai uwani asibiti.

Ko da ta dawo tayiwa uwani maganar xuwa asibiti kyaleta tayi tace baxata je ba kuma har lokacin tana jin feelings din.

Jiddah sai xirga xirga take tsakanin dakin ta dana uwani da kyar ta samu uwani ta amince xataje asibitin, hankalinta bai kwanta ba sai bayan fitar su gidan.

Uwani ansha jiki, hardasu allura aka rubuta mata drugs, ta fito sai ga kiran jamcy.

Tana kuka ta gayamata abinda ya faru.

Kina ina ne yanxu jamcy ta tambaya cikin bacin rai.

Ina asibiti.

Jiddan fa?

Tana can gidan,

Kije gida yanxu, da dare ki fito can qarshen layin gidanku saboda kada yan sanda su ganshi, xan turo maki Kurma, ma'anar sunansa baya ji a kowane aiki aka sanya shi, xaki bashi kudi yayi maki aiki kome kike so game da jiddah, ina ganin idan bata bar duniya ba baxaki taba samun el'mustapha ba, baxaki taba jin dadin rayuwar ki dashi ba.

Tau shikenan ina jiransa yaxo da sauri dan Allah, ta tsinke wayar tana maida numfashi cikin farin ciki.Suna gama wayar ta shiga mota suka nufi gida, ta shige dakinta tasa key kada ma a dameta da ya jiki na munafurci. +

Kusan sau biyu jiddah na xuwa tana buga qofar baa bude ba, sai bata qara xuwa ba.

Da dare kawai uwani ta fice daga gidan, can qarshen layin nasu ta nufa, cikin sa'a kuwa ta sami kurma akan bike xaune, ganin bindiga a hannunsa ta qara tabbatarwa shine.

Ta qarasa cikin tsoro tana kallonsa,

Ke wace yar rainin wayo ce xaki je ki shanya mutum anan, tun yaushe nake jiranki, banda darajar jamcy sai na tattakaki anan, baa wulaqantani ki kiyaye.

Cikin tsoro ta soma bashi haquri,

'menene aikin naki, kissa ce ko me?

'A'ah bana so a kashe ta kuma bana so ayi mata komai, so nake a dauke ta a boyeta na wani lokaci har na sami kwanciyar hankali tare da mijina, inta kama Ma a batar da ita daga garinnan taje ta barmin shi yanda xai bani kulawa ya soni saboda itace damuwata a duniyar nan.

Kurma yace aikin ki million biyu ne, saboda xamu ajiye tane mu kula da ita, mu bata ci mu bata sha amma babu sutura babu wanka, kuma idan tayi yunqurin gudu na kamata idan ban cire mata qafafu ba ko na dauke kanta da alburushi kice ni shege ne.

Duk wannan ba damuwa bane, kudin ne dai ka rage min dan Allah, ta marairaice.

Baki tashi aiki ba sai anjima, ya soma qoqarin tayar da bike dinsa,

Shikenan yi haquri na amince tunda dai inaso tabar gidan, amma matsalar yan sanda ke gadin gidan sosai saboda mijinmu AIG ne ta fada tana washe baki😀,

Yace ita bata fitowa ne,

Tana fitowa amma da securities, duk inda xataje tana tare dasu wai saboda kada wani abu ya same ta.

Tsakanin yan ta'adda da yan sanda ana ruguntsumi sai ayi wasan alburushi har mai rabo ya dauke ta, mu kashe ko akashe mu, ni game da kissa bana ji bana gani dama xaa kawar da itane a duniya xanje har gidan na harbeta kuma baxaa kamani ba, na gwane da yin wannan.

Aa abarta da rayuwarta, ita din yar uwatace, plan xamu hada xan kiraka a waya in gayama.

Kada a dauki lokacin inba haka ba har gidan xan xo dan baxan yafe million biyu akan wata banxa ba.

Aa bama sai kaxo ba uwani ta fada cikin rudu, ta karbi number tasa har xata juya ya kirata.

Ke mekike nufi inxo gurin ki baxaki bani ko sisi ba, kinma rainamin wayo.

Dubu biyu ne kawai a hannuna yanxu ta fada a tsorace,

Bani sunan, ya karba ya saka aljihunsa, ya tayar da bike din sa ya fice kamar xai bankade ta, uwani ta sauke numfashi tana mamakin wannan kurma da alama kam yana shaye shaye ita kam tsoronsa take.

*

Bayan kwana biyu jiddah na falo ita kadai xaune, t.v take kallo sanda uwani ta shigo falon.

Kallonta tayi a wulaqance tana yatsina fuska, ta xauna tana fadin.

Sai kaga mutum a fuska kamar na kirki a xuciyarsa kuwa kamar na fir'auna, mutum yasan Allah yake kwace miji ana shiga haqqin baiwar Allah da bataji ba bata gani.

STORY CONTINUES BELOW


Kallonta kawai jiddah tayi, ta dauke kanta gefe tana murmushi.

Anci amanata, ansa an dakeni, ansa miji baya xuwa gurina, ba ruwanshi dani, anyi min wayo an bani mota da Sana'a dan kawai na bar miji a mallakeshi, Allah xai sakamin dan baxan yafe ba.

Nan ma jiddah bata tanka ba, sai Ma qoqarin tashi take ta bar mata falon, uwani Ma ta tashi tana fadin,

Iyayena sun riqi mutum amana amma su anqi a riqa masu amana, iyayena sunyi qoqari su ba mutum tarbiyar dama uwar mutum baxata iya bayarwa b...... bata qarasa ba taji saukar Mari a kuncinta, kafin tayi wani yunquri jiddah ta qara dauke ta da wani Mari, xatayi magana ta qara dauke ta da wani Mari, uwani ta gigice ta fara ihu dafe da kuncinta.

Xan dauki kowane irin iskanci naki amma banda na iyayena, nasan darajar su da qimarsu ke baki isa ki xagi iyayena na barki ba, yanxu Ma darajar cikin nan kika ci da sai kin yabawa aya zaqin ta, daqiqiya kawai, ta fice ranta a matuqar bace.

Wlhy Allah xai sakamin kuma baxan yafe ba sai na dauki mataki, ke ki dake ni mijinki ya dake ni, ai ni ba boya bace, kinci darajar wannan cikin da sai nayi qasa qasa da namanki a gidannan, sai na ji maki ciwo na fasa maki baki, ai ba qarya nayi ba iyaye na ne suka miki tarbiya, idan kin cika ki qara fitowa kice xaki dake ni k...... tayi shiru ganin jiddah ta fito, tana nufo ta, ta yunqura da gudu ta shige dakin ta hade da saka key, still uwani batayi shiru,

Ai ba tsoron ki nake ji tausayamaki nake saboda cikin jikinki, da sai na farfasa maki baki yau, sai na jimaki ciwo kin kwanta a asibiti, insa likita ya cire min wannan baqar xuciyar taki, kuma Allah xai sakamin.

Ta sauke numfashi, ta nufi mirror tana kallon fuskarta har tayi wani kumburi, taja dogon tsaki tana shafa fuska, akwai lokacin da xai xo nima xan rama inda baki da ikon dukana, ashe jiddah xata iya duka kenan, tana nufin kyaleni ne takeyi karma ta qara ragamin nima xan dage damtse infara dukanta ne, harda wani kirana daqiqiya har yanxu tana jin haushi saboda naqi karatu to baxanyi ba sai dai ki mutu, sum sum da ita kamar kifin ruwa mtsewwwww.

A ranar jiddah tana cikin bacin rai sosai, shi kansa el'mustapha yaga hakan,

Ko dai jikin ne jiddah?ta dauke kanta gefe batare da tayi magana ba, ya xauna yana kallonta cikin seriousness,

Talk to me jiddah, what's wrong?

Ba komai ta fada a hankali tana kallon,

Akwai komai, from your face nagani, indai ba nine akace nayi wani abin ba,

Idan kaine wannan xaman da kayi a gabana xan rufe ka da duka ne,

Dana ji dadi jiddana ta bige ni, nasan nayi mata laifi ne ta hukuntani da hakan.

Shiru batayi magana ba, babu walwala a fuskarta,

Idan bani bane waye, please tell me...

Uwani ce ta bashi amsa kamar xatayi kuka,

Me uwani tayi?

Iskancin ya tashi kaina ya koma kan iyayena da basu a duniyar ma, I can't take it anymore el'mustapha,

Yaja numfashi yana kallonta, uwani.. Uwani... Uwani... Am tired of her jiddah duk laifin kine, meyasa tunda uwani ke maki rashin mutunci baki daukar mataki, yanxu ta bata maki rai kinxo kin xauna kina fushi kina kuka an you know your condition meke nan,

Tana min gorin iyayenta sun min tarbiya, ita meyasa batayi amfani da tarbiyar da suka mata ba, ta tashi tana fadin idan ban daki uwani ba baxan sami nutsuwa a xuciyata ba.

El'mustapha ya sha gabanta da sauri,

Calm down jiddah, idan kika ce kiyi fada da uwani da wannan cikin ai xata ji maki ciwo, idan taci riba akan ki gobe kome xai hadaku qoqarin fada xatayi dake, respect yourself, tun a lokacin da tayi maki iskanci ya kamata ki dauki hukunci akai.

STORY CONTINUES BELOW


'Na mare ta sau uku, amma xuciyata batayi sanyi ba, ina jin haushin uwani a yau, I can do anything for her idan bata kiyayeni ba ko.....

'Ashe haka jiddana keda xafin xuciya I don't know, yau uwanin da ake tausayi ce aka Mara har sau uku, how I wish ina gurin ne na ganewa idanuna jiddah ta dauki hukunci da hannunta, ya riqota suka xauna.

Haqurin da kike bani akan uwani nima shi xan baki, wata uku ne xata bar miki miji harda gidan Ma, xata koma gidan iyayenta ta cigaba da xama dama saboda karatu take xaune a gidan kuma ta ajiye batayi kinga sai ta tattara komai nata ta bar mana gida.

'Naji kamar wata uku yaxo gobe, dana sani ban hada wannan auren ba, har yau na kasa gano inda uwani ta dosa akaina.

Is better ki gano jiddah ina so naji kin furta da bakinki uwani taci amanar ki, uwani bata sonki.

Tayi shiru kawai batare da tayi magana ba.

*

Tun daga lokacin suka soma wasan buya, uwani ko kadan bata so taga jiddah ko abinda xai hada ta da jiddah cos a tsorace take da ita tun lokacin da taga fushin jiddah, ashe haka jiddah take, shiru shiru kamar baxatayi fada ba ballantana ta kai ga duka.

Sai plan suke hadawa ita da kurma yanda xasu bullowa su sace jiddah.

Islam ke son banan, yasmeen ta fada tana kallon jiddah, tun ranar da kika aiko ta gidana ya ganta yake min maganarta.

Jiddah ta bayyana farin cikinta tana kallon yasmeen,

Kice banan tayi sa'a, amma yasan wacece banan din kuwa, bana son abinda xai xo ya cutar da yarinyar, marainiya ce bata da kowa a duniyar ni sai ni da kakarta, rayuwar Islam daban ce da banan, she is not dat wise irin yanda Islam ke so you know it, last month ta gama skul.

Tun da Islam yace yana son ta nasan da gaskiya yakeyi yana son ya, kuma kinga shine ya ganta yace yana so har ya matsamin lallai sai naxo na sanar dake, banan tana da kyau kuma yarinyace kamar shi so banga rashin dacewar su anan ba, sai idan kece ba kyaso jiddah.

Lol, saboda me xance baxan so dan'uwanki ba, kinsan yaran yanxu baa masu dole, kuma banda tabbacin tana da wanda take so ko kuma babu, xan tuntube ta yasmeen ki kwantar da hankalin ki insha Allah xata auri Islam nima ina mata sha'awa dashi.

Murmushi yasmeen tayi, ta kawar da xancen tana fadin jiya baban baby ya dawo daga dubai, ya kawo min kaya masu kyau na jaririrai.

Xan gayawa el'mustapha idan ya dawo, sai ki aiko da kayan ya gani duk da ya gama siyayyar kayan haihuwa tuntuni amma nasan idan sun masa kyau xai siye.

Insha Allah xan aiko, wannan cikin naki wai wata nawa ne?

Bakwai ne fa kin ganshi da girma barakallah.

Wlhy kuwa kuma girman ya taso lokaci daya, before ma baa gane kina da ciki, qila wasu biyun ne xasu xo again.

Murmushi kawai jiddah tayi tana fadin Allah dai ya raba lafiya.

Amin cewar yasmeen tana qoqarin barin gidan.

Kinji Islam ke son ki banan, am happy for you, yaron yana da kirki sosai.

Banan ta bata fuska tana kallon jiddah,

Waye shi anti jiddah ni ban san shi ba.

Qanin qawata ne yasmeen, sanda kika je gidan ya ganki yana so, nikam nace xan bashi banan saboda na yarda dashi nasan baxai cutar dake ba.

Banan ta dafe kanta, sai yanxu ta tuna shi, shine Ma ya maidota gida, tayi shiru batayi magana ba, ita dake son el'mustapha ya xatayi da Islam, wai samun guri inji wata xuciyar, masu aiki nawa ne suka sami irin gatan da ta samu saboda jin dadi xatace xata auri mai gidan, baxata iyama anti jiddah hakan ba.

Taji muryar jiddah na magana, idan kuma kinada wanda kike so ne to, baxan maki dole ba, duk wanda kike so dashi xaa yi, buri na ki auri wanda xai riqe ki amana kuma yasan darajar ki, kada ki biyewa xuciyarki ga samarinnan na yanxu masu qaryar banxa ki xauna kina ta jiran warabuka dan baki da tabbacin xasu fito neman auren ki ko baxasu fito ba, nidai baxan cutar dake ba ko na kaiki inda xaa cutar dake kinsani, kije kiyi tunani akai.

Ta sunkuyar da kanta feeling guilty idanunta suka ciko da hawaye,

Shikenan ta rasa el'mustapha har abada, mutumin da bai san tana yi ba, ita kadai ke haukanta kuma tasan baxai aure ta ba, koma xai aure ta baxata iya xaman kishi da jiddah ba, jiddah ta xama tamkar uwa agare ta yanxu dole kuma xata haqura da el'mustapha ta yaqi xuciyarta na ganin ta cire sonsa.

Ta yarda ta rasa el'mustapha har abada, xata cigaba da rayuwa babu el'mustapha sai xabin Allah, yeah tafi kowa sanin jiddah baxata cutar da rayuwarta ba,

Da gaske kenan da jiddah tace ta kama mai son ta wato Islam domin shi kadai ne yanxu wanda ke son ta, ta rabu da jiran tsammanin wato el'mustapha saboda shine baisan tanayi ba, dan haka ta rungumi mijin da duk Allah ya rubuta mata da hannu bibbiyu Kuma xatayi biyayya ga jiddah dan cimma rayuwa mai amfani a duniya da lahira.

Ta amince ta yarda Islam shine xabin Allah, ta soma siffantoshi a idanuwanta....

Tunanin me kike banan? Jiddah ta katse ta.

Ba komai anti jiddah na amince da duk mijin da kika xaba min, ni mai yi maki biyayyace.

Sosai jiddah taji dadi, banan kuwa ranar tasha kuka kamar me.

Bayan kwana biyu, twins sunje islamiya tare da banan, ba kowa a gidan sai jiddah kadai xaune a falo,

Wayar ta, ta soma ringing, tayi mamakin ganin call din uwani a lokacin, kamar baxata dauka ba sai kuma tayi receiving,

'Dan Allah anty jiddah kixo ki taimakeni, gani a hanya na kasa driving baxan iya dawowa gida ba saboda banda lfy dan Allah kixo ki taimakeni.

Kina wajen ina ne na aiko maki driver kinsan condition dina ai.

'Dan Allah karki aikoshi anty jiddah kixo da kanki kuma kada kixo da kowa saboda duka jikina ya lalace da jini, ashe ina da ciki ne ni ban sani ba, dan Allah kixo yanxu anti jiddah kada na mutu sai ta fashe da kuka.

Jiddah ta rude, yaushe uwani tayi ciki bata da labari, el'mustapha ya munafunceta yanda yake nuna mata babu komai tsakaninsa da uwani.

Ko wane hali uwanin take ciki, abin na buqatar sirri basai taje da wani namiji ba dan batasan halin da xata isko uwanin ba, amma ita kadai baxata iya taimaka mata ba, ta kira uwani a waya,

Kinsan ni kadai baxan iya taimaka maki ba uwani ko naxo da Inna ne,

Aa anti jiddah bana son kowa yasan halin dana ke ciki ballantana mai aiki, ga wata mata anan tare dani bataso tabar motar ta da yaranta a gurin ne da itace xata maidoni gida,

Kina wajen ina ne?

Da kyar uwani tayi mata bayani.

Jiddah ta dauki hijabin ta da key din motarta, batare da tunanin komai ba ta shiga motar ta.

Taxo fita ne wani security ya tsaidata,

Madam ke kadai xaki fita ne, oga yace kada abarki kije ko ina batare da ko daya daga cikin mu ba.

Tace karka damu, its urgent yanxu xan dawo, kafin yayi magana ta ja motar da qarfi ta fita daga gidan.Tafiya tayi mai nisa, a xuciyarta tana tunani kome yaxo da uwani gurin.

Tun daga nesa ta hango motar uwani a gefen titi, ta rage gudun motar tana observing wani abu, 1

A waya uwani tace akwai wata mata tare da ita da ya'yanta, to ina suka shiga?

Tayi parking nesa da motar uwani, ta cikin glass din ta tsurawa motar uwani ido har ta hango kamar wasu maza a cikin motar, gabanta ya fadi, kada dai uwani ta kirata ne domin ta cutar da ita, dama bata kashe motar ba, ta soma qoqarin juyawa ta bar gurin, abinda bata sani ba tayoyin motar, qusoshin da aka xuba akan titin duk sun fuda motar, ta fito cikin motar da sauri tana kallon motar, sai a lokacin tsoro ya xiyarce ta mai tsanani musamman da ta gane plan ne aka hada mata, ta juya da sauri tana qoqarin gudu amma baxata iya ba saboda cikin da ke jikinta, 1

Kurma na ganin haka ya fito da gudu daga inda yake boye cikin grass, ba zato jiddah taji saukar duka a qafafunta wanda yayi sanadiyar faduwar ta gurin a sume.

Su uwani suka qaraso da saurinsu tare da wasu maxan abokan aikin kurma, kurma ya yarda qaton qarfen dake hannunsa wanda shine ya bugawa jiddah a qafafu.

Ai na gayamaki idan tayi qoqarin guduwa sai na harbe qafafunta ko na ciresu gabaki daya, inda na bige ta a qafar ina sa rai baxata qara tafiya ba ballantana tayi qoqarin guduwa.

Uwani ta xare idanu cikin tsoro, wayyo Allah anti jiddah baxata qara tafiya ba kake nufi, amma ai munyi magana da kai aciki ba cutarwa. 2

Saboda kada na cuce tane ya saka ban cire qafafun gabaki daya ba, kuma xan iya babu imani a xuciyata ko kadan ki tambayesu, nine na kashe mahaifina saboda ya kamani ina yiwa qanwata fyade, tunda na kashe mahaifina da hannuna uban kowa Ma xan iya kashewa kuma kowanene akace na kashe sai na kashe shi nake samun nutsuwa,

Uwani ta nufi inda jiddah ke kwance a sume, ta rungumota sosai a jikinta, taji wani tausayinta ya kamata wanda yake sanyata dana sani a yanxu, idan ita ce jiddah baxata taba mata haka ba.

Kurma ya dubi daya daga cikinsu,

Goga dauki matar nan saka mana ita a motar mu kada musa wasa axo a riske mu, ke kuma sati daya kacal na baki ki kawo min kudi na idan kika qi wallahi summa tallahi sai na kashe wannan matar kuma naxo har gidan na kashe ki sai dai nima a kasheni, bana wasa da kudina, ya juya ya fice sauran suka bi bayansa yayin da goga ya dauki jiddah yabi bayansu.

Jiki a sanyaye uwani ta tashi ta nufi motar ta, tana kallo suka sanya jiddah a motar su suka keta cikin dajin, gidansu yana can ciki sosai.

Wata xuciyar ta soma xuga ta, saboda me xata damu ai abin farin cikin tane jiddah ta xama nakasashiya baxata taba moruwa ba kuma el'mustapha baxai taba xama da ita a hakan ba, dole xai dawo mata tunda itace mai lafiya, baxata damu ba tunda har sun furta baxasu kashe taba idan ta kawo kudin, xatayi qoqari ta kawo saboda bata son a kashe jiddah tana so abarta da ranta yanda xata riqa ganinta da el'mustapha tana juyashi kamar yanda ake juya waina, ta saki murmushi, 4

Wani tunani tayi ta isa motar jiddah ta bude, wayar ta ta ciro, ta sami dutse tayi mata ratsa ratsa, ta cire sim din ta yarda har wayar ba kana ta shiga motar ta tabar gurin da sauri.

Tafiya sukayi mai nisa acikin dajin kafin su iso gidan nasu, gida mai kyau baxaka taba tunanin yan iska ke xaune a cikin sa.

Goga dauko wannan matar sharp sharp,

STORY CONTINUES BELOW


Goga ya dauki jiddah
Ya shiga da ita gidan, wani daki suka kaita suka kwantar da ita, kurma ya dauko qaton bucket cike da ruwa ya watsa mata batare da tausayi ba.

Har lokacin bata motsa ba, ya sake debowa ya watsa mata, ta saki ajiyar xuciya, numfashin ta na dawowa a hankali.

Abinda ya faru ke dawo mata akai, sanda kurma ya bigi qafarta wani irin radadi da axaba da taji tunda take a rayuwa bata taba jin irin sa ba, ta bude idanuwanta da sauri tana kallon dakin da take, ambaton Allah take a xuciyarta, ta soma qoqarin tashi amma me qafar ta riqe bata iya motsa ta ko kadan,

Meke nan? Ta maida dubanta ga qafar cikin rudani, meke faruwa, meyasa na kasa motsa kafar, meya sami qafar, innalillahi wa Inna ilaihir raji'un, ta saki wani kuka sosai gwani ban tausayi. 1

Jiddatulmusty 😒 1

Uwani tana xuwa gida ta shigewarta abinta kada Ma a xargeta akan batan jiddah,

Ita yanxu abinda ke damunta yanda xata sami million biyu, ta sani idan tayi wasa tsab kurma xai iya kashe su ita da jiddah, ta ciro wayarta ta kira jamcy,

Tayi ta ringing bata dauka ba, haka ta sake gwada kira, gab da xata tsinke ta dauka, abinda taji jamcy na furtawa a bakinta yayi tsananin rudata,

Uwani ina cikin wani hali, guy din dana biyo muka xo ashe yana dauke da cocaine, sun kama shi sun tafi dashi gani bansan inda xan nufa ba nima nemana suke.

Uwani ta tsinke wayar yayin da dakin ke juyawa da ita, har wani duhu take gani a idanuwanta.

Banan suna dawowa makaranta taje da yaran ta cire masu uniform na islamiya, ta shiryasu cikin kayan su na gida.

'kuje ku gaida momy kafin naxo, suka nufi sashen jiddah da gudu.

Mummy... Mummy we are back,

Dakin ta suka nufa bata nan, kitchen bata nan, toilet, har sashen el'mustapha suke bata nan suka sake komawa dakinta, aryan ya kwanta saman gadonta yana kuka,

Momy ta tafi ta barshi ita da daddy yau baxai ci abinci ba.

Arham bai damu ba, keken sa ya dauko ya soma yawo da ita a tsakiyar dakin yana wasa tare da bindiga a hannunsa na yara.

Uwani na jin kukan aryan ta qara lafewa tana xaginsa a xuciyarta, yau babu momy sai dai kaci ubanka, kaima daqiqi yanda mamanka ke cemin daqiqiya, kuma daqiqai ne wawaye kawai.

Tun da banan ta nufa falon take jin kukan aryan ta qarasa dakin da sauri sukayi kicibis da keken arham har ya taka mata qafa,

Ta dauke qafar da sauri tana yatsina fuska, arham ya soma dariyarta.

Meyasa aryan ke kuka, ina anti jiddah?

Bata nan shine yake kuka?

Bata nan, banan ta maimaita cike da mamaki, ta juya ta fita xuwa harabar gidan, tabbas bata nan dan babu alamar motarta a gidan,

To ina anti jiddah xataje da magrib haka, ita bata da waya ballantana ta kira ta taji, tana tsaye gurin yaran suka fito, haka ta riqa jin faduwar gaba, taji bata jin dadin jikinta babu nutsuwa a tare da ita wanda bata san dalili ba tunda ba yanxu bane jiddah ta fara fita.

Ta dauki aryan dake kuka, kukan sa na qara rikitata tana jin ba daidai ba a jikinta, bata da nutsuwar da xataje tayi sallah, sai ta tsinci kanta tana xubar da hawaye.

Asp Bello yaxo alwallah ya ganta tsaye da aryan yana kuka, ya tambayi dalili ta gayamasa.

Yace tun daxu ta fita gashi bata dawo ba kada oga ya dawo bata nan, sai da akace wani a cikin mu ya bita tace nan ne kusa urgent aka kirata baxata jima ba.

STORY CONTINUES BELOW


Shiru kawai banan tayi, shima ya juya, ta Goya aryan bayanta tana jijjigashi sai safa da marwa take a harabar gidan, arham na rakube gindin wata flower.

Suna haka aka wangale gate din duk suka juya suna kallo.

Motocin el'mustapha ne suka shigo, gabanta ya tsananta faduwa, aryan ya soma qoqarin saukowa ba musu ta sake shi daga shi har arham suka nufi motar mahaifinsu da gudu suna murnar dawowarsa.

Daddy is back...

Duk da gajiyar da yake dauke da ita bai hana masa daukan su duka ba, babu walwala a tare dashi, tun daxu yake jin weakness a jikinsa, ga wata irin faduwar gaba da yake ji, tare yake da babban aminin sa ibrahim wurin aikinsu daya sai dai kowa da nashi matsayin.

Ba ku gaida second daddy ba cewar el'mustapha yana kallon yaran,

Suka soma dariya suna kallon ibrahim,

Second daddy ina wuni...

Daga ibrahim har el'mustapha ba wanda baiyi dariya ba, ya sauke su yana kallon banan sanda suka qaraso gurin,

Ta gaidashi tare da abokinsa kanta a sunkuye.

Me kukeyi anan keda twins?

'Anty jiddah ce tun daxu ta fita bata dawo ba, sai ga hawaye sharrr na bin kumatunta.

Nan take yaji gabansa ya fadi, ya juya yana kallon motocin gidan duka suna nan har ta uwani banda ta jiddah, kenan jiddah ita kadai ta fita.

Ibrahim yace kun duba ko ina a gidan bata nan ne?

Tace wlhy ko ina mun duba bata nan.

El'mustapha ya juya ya nufi gate,

Yaushe jiddah ta fita daga gidannan.

Daxu sir, suka amsa masa cikin girmamawa,

Ya akayi kuka barta ta fita ita kadai ko akwai wanda ya bita ne.

Suka soma inda inda cikin rudewa, kowa ya kasa magana saboda tsoro abinda ya qara fusata el'mustapha har yayi masu tsawa, ba shiri daya ya soma magana,

Munyi iya qoqarin mu ta bari muje da ita taqi, tace its urgent an kirata ne yanxu xata da..... Bai qarasa ba el'mustapha ya dauke shi da Mari cikin bacin rai abinda basu taba gani ba tun tarayyar su dashi.

What nonsense are you telling me, ya nayi daku a gidan nan saboda tace haka sai kuka barta ta tafi, kuka xauna kuka miqe qafa anan, to miye amfanin ku if you can't stop her.

Sorry sir suka fada jikinsu a sanyaye,

Waye tace ya kirata..

Bata fada ba sir...

El'mustapha ya furxar da wani xaxxafan iska a bakinsa

Yace believe me idan wani abu ya sami jiddah, ya sami aikin kune, daya bayan daya duk sai na sauke ku, kuje ku nemo ta duk inda ta shiga ina jiranku.....

Ba bata lokaci suka shiga motoci suka raba hanya, el'mustapha ya dafe kansa da hannuwansa biyu, tunani yayi da sauri ya xaro wayarsa aljihunsa ya soma qoqarin kiran layin jiddah, kwata kwata bata shiga, ya kira mamanshi yana tambayar jiddah taje,

Bata xo ba el'mustapha, me ya faru, me ya sami jiddah ne?

Ba komai ya tsinke wayar, hajiya ya kira yana tambayar ta jiddah,

Ba muyi magana da ita xata xo ba kuma bata xo din ba,

Ya tsinke wayar da sauri, hankalin hajiya ya tashi, ta gayawa abba Sam jikinta bai bata akwai lfy ba, Allah yasa ba wani abin ne ya sami jiddah ba.

Duk inda el'mustapha ke sa rai ga ganin jiddah yaje sai ace masa bata je ba, gidan qawayenta duk inda yasan tana xuwa sunje ranar shida ibrahim.

Duk wannan bidirin da ake uwani na dakin ta kwance abinta ta saka earpiece a kunnenta tana shan waqarta abinta batare da damuwa ba.

Banan kuwa tayi qoqarin ganin twins sunci abinci ta saka su barci da kyar saboda fitinar mom din su, ta gabatar da sallolinta tare da addu'ar Allah ya bayyana jiddah ya kare ta daga sharrin masu sharri.

Dawowar su el'mustapha tayi dai dai da dawowar yaransa, kowane jikinsa a sanyaye babu labari amma ga motar ta sun sama a hanya sun rufe sunxo da key kasancewar babu iska a tayoyin.

El'mustapha yayi shiru kamar xaiyi kuka, tunani yake me ya fitar da jiddah, waye ya kirata urgent, su waye suka dauke jiddah, meyasa suka dauke ta, me jiddah tayi masu, sai ya juya xuwa cikin gida, hannunsa yasa yana dauke wasu kwallah.

Insha Allah xaa ganta ka kwantar da hankalin ka xamu tsananta bincike daga yau xuwa gobe, kada kasa damuwa a xuciyarka, cewar ibrahim yana kallon el'mustapha bayan sun xauna a falon.

Innocent jiddah, sun dauke min jiddah akan wane dalili?

Wa kake xargi el'mustapha, waye kake ganin xai iya yi maka hakan.

Mutum daya nake xargi, jiddah bata da abokin gaba ko fada, kuma ni a iya tunani ban san nayiwa wani ko wata wani abin da xaa kullace ni ace xaa dauki mataki akan matata ba.

Waye kake xargi,

Uwani nake xargi, el'mustapha ya fada yana kallon ibrahim cikin seriousness.

Nafi kowa sanin uwani bata son jiddah, she can do anything for her I know, idan har uwani na da sa hannu a batan jiddah believe me ibrahim wlhy xan iya kashe ta, I hate her.

Ya daga murya yana kiran banan.

Ina uwani?

Ina ji tana ciki, ita Ma ban ganta ba duk yau.

Kiramin Uwani taxo yanxu. Uwani ta shigo falon tana tauna cingam, yanayin fuskar el'mustapha yasa ta shiga taitayinta, ta tattaro nutsuwarta guri daya ta xauna tana gaida su.
+

Kallonta el'mustapha keyi da idanunsa da suka rikide, observing yake akan ta, yana son sanin wani abu a tare da ita,

Muryar ibrahim taji yana fadin, Jiddah bata sanar dake inda xata je ba kafin ta fita.

Uwani ta yatsina fuska tana kallonsa, idan xata fita bata gayamin ai, nima bana gaya mata kowa yana rayuwarshi ne shi kadai.

'Wannan rayuwar bata yi ba Sam uwani, cewar ibrahim yana kallonta fuskarsa ba walwala, keda bakinki kike fadar baki damu da rayuwar jiddah ba? Ke wace irin mace ce mai manta alheri? Ki tuna jiddah ta taimakeki ta tallafi rayuwarki, abinda take matuqar so fiye da komai a duniyar nan ta sadaukar maki uwani, ba kowace mace xata iya abinda jiddah tayi akan ki ba, tana xaune dake da xuciya daya ne, tana sonki tana son kyautata maki tana so ku xauna xama na amana ku hade kanku domin farin cikin mijinku, duk wanda yasan jiddah yasan mutuniyar kirkice bata da keta a rayuwarta ko niyar cutar da wani, kiji wata magana da kike fada yanxu ba dadin ji wai ba wanda ya damu da rayuwar wani kowa yana tasa rayuwar nan, na tabbata da jiddah ce baxakiji wannan kalma a bakin ta ba.

Jikin uwani yayi sanyi, tabbas gaskiya yake gayamata akan jiddah, sai tayi qoqarin fooling dinsu kada su xargi wani abu a tare da ita.

Nagode da nasihar da kake min a ynxu kuma insha Allah xan gyara, bari Ma naje na bata haquri.

Ibrahim ya qara tsaidata, kina nufin wai bakisan abinda ake ciki bane game da batan jiddah.

Kallonsa take baki a bude,

Wlhy ban sani ba, ina taje ne.

Banan da el'mustapha sai kallonta suke, kwata kwata banan bata xargin uwani akan batan jiddah ba kamar yanda el'mustapha ya kafe ta da idanuwa yana observing wasu abubuwa.

Yau na shiga uku, baa ga anti jiddah ba, ina taje da wannan cikin me ya same ta, sai ta soma hawaye. 1

Banan ma ta soma sharar kwallah,

Abinda uwani taji el'mustapha ya furta ne yayi kusan sumar da ita daga inda take xaune,

Jiddah ta gayamin kece kika kirata a waya ta fita, ina kika kai min matata ta?

Ni? Uwani ta tambaya tana fiddo idanuwa saboda tsananin tsoro da rudewa,

Wlhy ban kira ta, bana waya da jiddah, saboda me xan kirata ta fito?

Jiddah xata min qarya kenan ya qara tambayar ta bayan ya kafe ta da manyan idanuwansa yana son ya gasgasta xargin sa akanta.

Uwani ta qara rudewa ta fashe da kuka wanda ke nuna a tsorace take, amma tunani take har yaushe jiddah ta kira el'mustapha ta gayamasa, kodai so yake ya nuna mata halin su na yan sanda ya gani tunda haka suke bincike mai tsanani akan wanda suke xargi.

Wlhy bani na kirata ba, kowa yasani bana waya da jiddah, ban ma san sanda ta fita daga gidan ba ina daki a kwance, wlhy bani bace ban san komai a kai ba.

El'mustapha ya qara kallonta, Uwani idan nagane da sa hannunki a batan jiddah........ sai kuma yayi shiru ya barwa kansa sani, ya cigaba da fadin ke nake xargi kuma har yanxu xuciyata ke take xargi, xan iya shigar da qara kotu akan ina xargin ki da batan matata saboda nasan ba kyason jiddah baki da buri a duniya na ganin kin kawar da jiddah saboda ki mallaki xuciyar el'mustapha, kinsan nasan bakya qaunar jiddah itace din dai bata gano hakan ba, itace ta rasa gano illar uwani a tare da ita, ta dauki so da amana ta baki wanda ke baki da wani buri na ganin kin cutar da jiddah,

STORY CONTINUES BELOW


A matsayina na dan sanda xan cigaba da bincike lungu da saqo na ganin masu sa hannu a batan jiddah, xanje na nemota a duk inda take, indai kina da sa hannu a batan jiddah ayi gaggawar maidata inda aka dauketa, ko rantsuwa nayi baxanyi kaffara ba indai da sa hannu uwani a batan jiddah believe me ibrahim alqawari ne nine mutum na farko da xan fara kamata dumu dumu da hannuna, ya tashi ya fice zuciyarsa na quna.

Ibrahim ya kalle ta shima jikinsa yayi sanyi sosai,

Kinji abinda el'mustapha yace uwani, tsakanin ki da Allah ba hannunki a batan jiddah, ki fada min gaskiya ni xan iya kare ki a gurin sa kuma nayi maki alqawari baxan taba bari ya sake ki ba hassalima xanyi qoqarin ganin na dai dai ta ku ya so ki kamar jiddah.

Iya kar gaskiya ta nake fada maku banda masaniya akan batan jiddah. 1

Indai kinsani dan Allah karku cutar da jiddah,

Ya tashi yabi bayan el'mustapha suka barta anan, banan Ma tashi tayi ta barta.

Washe gari tunda sassafe ibrahim da el'mustapha suka baxa yan sanda bincike ta ko ina, sai sanarwa ake ga duk wanda ya ganta idan kuma kidnapping ne a sanar da su ko nawa ne xasu biya amma kada su taba lafiyar jiddah.

Sai lokacin da hajiya taga hoton jiddah a TV ana sanarwa batan ta sa'anan ta san halin da ake ciki, kuka tayi shi sosai, ranar ita da abba suka je abuja babu kwanciyar hankali tare dasu.

Mama Ma baa barta baya ba, batan jiddah ya taba xuciyarta har ciwon ta ya dawo saboda damuwa, gwanda ace mutum ya mutu da ace ya bata baa san halin da yake ciki ba.

Duk sisters din el'mustapha suma sun shiga damuwa sai dai babu mai xargin uwani duk a cikin su sai hajiya kadai da el'mustapha.

Yanda uwani ta dage tana kuka tana neman jiddah ya saka sauran mutane basa xarginta amma banda hajiya.

Tace nice na haifeki uwani, na raini ki da hannuna har kika kawo wannan lokacin, ba wanda xai bani labarin halinki ciki da waje sai Ma ni da xan bayar, nafi kowa sanin wacece uwani duk da jiddah ta fini kusanci dake amma Sam bata san halin ki ba, nasan ba kyason jiddah, nasan kin auri mijin tane saboda ki raba ta dashi, ki tuna yanda yarinyar nan tayi shige da fice na ganin kin auri mijinta duk da kowa baya so, ta dauki nauyin karatunki, cin ki, shan ki da suturar ki duk yana hannunta, bata taba aiko mana ko kudin handout naki a bada ba duk itace, ta dauke ki tamkar qanwarta uwa daya uba daya, ta dauki iyayenki da daraja fiye da yanda kika dauke su, ta girmama su tana masu tarbiyar da bakya masu, ta rufa wa iyayen ki asiri da dukiyar ta wacce itace mahaifinki ke juya mata, ta so ki da xuciya daya, ta xauna dake babu cutarwa, ki dubi girman Allah ba dan iyayenki da basu da daraja a gurin ki ba idan kina da sa hannu a batan jiddah kiyi gaggawar maidata kada ki bari a cutar da baiwar Allah, salihar mace mai haquri da yakana.

El'mustapha na labe duk basu sani ba, inda yake labe hawaye yake sai kunga yanda ya koma cikin kwanaki biyu da batan jiddah, ya fita hayyacinsa bashi da lokacin kowa da komai sai na kewar jiddah, xuciyar shi babu sukuni sai faduwar gaba a duk lokacin da ya dubi twins suna neman mahaifiyarsu,

Uwani ta dubi hajiya sosai kalaman hajiya sun shige ta, wannan karon kukan da take na gaskiya ne ba dan komai ba sai dan tausayin jiddah, meyasa jiddah keda masoya haka, meyasa mutane da yawa suka damu da batan jiddah, meyasa mutane da yawa suke kuka suna mata addua, meyasa kowa ke fadin alherin jiddah ake yabata a ko ina,

Taurin kai irin na uwani Sam bai sa taji xata fadi gaskiya ba duk da tayi nadama, tafiso sai burinta ya cika tasan akwai lokacin da watarana xasu manta da jiddah su shafe shafinta a rayuwarsu hakan xai bata damar cimma burinta na ganin ta mallaki el'mustapha yanda take so.

Uwani batayi magana ba sai sharar kwallah take, ita Ma hajiyar kuka take,

Tace indai uwani akwai sa hannunki aciki baxan taba yafe maki ba, kuma baxaki taba cimma duk wani buri naki ko quduri akan jiddah ba, idan kuma babu hannunki ciki ina roqon ko waye Allah ya Toni asirinsa da gaggawa.

Duk wadannan kalamai na hajiya bai sa xuciyar uwani ta karaya ba ita a tunanin ta haqqin mahaifiyarta baxai taba kamata ba tunda ba cin amanar ta tayi ba.

A hankali el'mustapha ya janye jikinsa daga qofar dakin, tafe yake baya ganin gabansa, kuka yake kamar mace idan ya tuna jiddah da cikin dake jikinta, jiri ya soma dibansa, lokaci daya ya fadi gurin ragwaf ba numfashi a tare dashi.

Inna ta saki ihu domin itace a gurin sanda el'mustapha ya fadi, hajiya da uwani suka fito a firgice, securities Ma suka shigo a firgice kowane dauke da bindigarsa tunanin su ko wani abinne daban.

Ganin el'mustapha kwance a gurin yayi matuqar tsorata su, nan da nan aka dauke sa suka nufi asibiti dashi.

Gida da waje maqota abokan arziki, yan uwa babu abinda suke a duk lokacin da suka kai goshin su qasa yayin sujjada banda addu'ar Allah ya bayyana jiddah ya kare ta ya kuma Toni asirin wadanda suka sace ta.

Post a Comment for "EL-MUSTAPHA CHAPTER 5"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...