Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

CONEL AHMARD CHAPTER 4

CONEL AHMARD CHAPTER 4

- - Post a Comment
CONEL AHMARD
CHAPTER 4
Sanye take acikin wota gown ta atampa mai kyau, green and white color mai tsadar gaske, hijab d'inta maroon color har k'asa da takalmanta plat shue masu kyau,
Tana fitowa tagansa a tsaye saita buga tsaki "mtsss....." tareda juyawa zata koma ciki,

Dasauri yaje yarik'o hanunta yadawo da'ita baya tafad'o k'irjinsa dak'arfi har saida taji tsoro dan tad'auka faduwa zatayi,

Saida tanutsu nutsuworta tadawo jikinta sannan dasauri tsjanye jikinta daga nashi tareda watsa masa harara had'e da yin tsaki mai sauti takuma sake juyawa zata koma ciki, dasauri yaje yasha gabanta tareda fad'in "dakata...dakata Madina, dan Allah kitsaya muyi magana" saita tsaya cak batareda takallesa ba, tanajin tsintsar tsanarda tamasa tana k'ara dad'uwa a cikin zuciyarta,

Gaba d'aya yanayinsa yacanja yakoma yanayin tausayi, fuskarsa takoma ta tausayi, cikin yanayin magiya daban hak'uri yaharde hannayensa gu d'aya alamar magiya muryarsa kamar zaiyi kuka yace "dan Allah...dan Allah Madina ki yafeman abunda namaki, dan Allah kiyi hkr, kiyi hakuri aka abunda yafa abaya, plss...!" woni irin killer smile tai tana kallon woni gun kamin tadawo da kallonta izowa garesa sannan tafara magana "Hmm....Mr. DEEDART kenan, ai yanzu babu buk'atar neman yafiya tinda dai nacika alk'awarin da nad'aukarwa kaina, maana nad'auki fansar abunda kama y'ar uwata, kodama ace band'auki fansaba wlh ba magiyaba, ko durk'usawa Kai agabana kana bani hkr bazan tab'a yafemaba har abada".

Woni irin k'ololon bak'in cikine yaji yatasomasa akan zuciya,

Ahankali yacemata "hmm....saikuma abu na biyu daya kawoni gareki" cikin gajiyawa da zantikansa tace "inajinka, kuma kayi sauri sbd inada abunyi, tin kan kuma Abba na yadawo yaganka a kofar gidansa dan nasan bazata maka dakyauba matuk'ar yaganka Koda a k'auyen nan ne" d'an murmushi yai sannan yacigaba da fad'in,

"Madina....yau gani agabanki amatsayin AHMARD DEEDART dina, ba Mr DEEDART ba mai tsayi da tarin dukiya wonda kika sani abaya, nazo agareki da k'ok'on barana, zuciyata ce ta aikoni izowa gareki ba'akaran kaina ne nazoba, kitaimaka ki amince da tayin soyayyarta agareki, wlh Madina tin bayanda wonnan al'amarin yafaru a tsakaninmu nakasa cireki daga zuciyata, zuciyata takamu da tsintsar k'aunar ki,

Nakamu da sonki Madina wonda zan iya rasa rayuwata kokuma woni b'angare na rayuwata matuk'ar bansameki amatsayin matata ba, zuciyata tana maki kyakkyawon so wonda yake cike da tarin alkhairi dakuma tsabta, dan Allah...dan Allah Madina kitaimaka ki amince da tayin soyayyata agareki, badan halina ba, kodon feature d'in y'ar mu" yak'arisa maganar cikin magiya.

Murmushi tai kamin tawaigo takallesa tace "daka sani daka hori zuciyarka akan tadaina so na, daka sani daka gargad'i zuciyarka akan tamanta dani, daka sani daka hana zuciyarka tinanina harta kamu da so na, dan wlh Koda giyar wake nasha, Koda narasa miji, Koda Kai kad'aine karage namiji a duniya DEEDART bazan tab'a aurenka ba,

DEEDART bazan tab'a aurenka ba har abada, DEEDART ka cutarda rayuwata, ka ruguzaman farinciki na, karabani da y'ar uwata da mahaifiyata, kasaka kwollah kwaranya daga idon mahaifi na, sannan ka gogawa ahalina bak'in fentinda har abada bazai tab'a gogewa ba, DEEDART karabani da farinciki na kakuma barman bak'incikin da har abada bazai tab'a gushewa agareni ba, ka cuceni DEEDART wlh bazan tab'a yafemaka ba har abada, I hate u.... I hate u DEEDART and u are my enemy" tafad'a dak'arfi, "Kaiyi nane na har abada".

Tana magana kwollah sai zuba suke daga idanuwonta, tasaka hannayenta tana turesa tana turesa cikin tsintsar b'acin rai, shima kwollan yake zubarwa masu zafin gaske yana kallon ta,

Jin kalamanta yake har cikin zuciyarsa suna dukan k'irjinsa, musamman kalmominta na karshe, baisan lkcnda yadurk'ushe ak'asa ba tareda riko hanunta yana kuka yana zubda kwollah yana fad'in "ki yafeman Madina, ki yafeman dan Allah ki amshi soyayyata kada ki wofantarda ni" amma ina saita turesa baya tareda ficewa dasauri tashige cikin gida,

Fad'ar yake "ki yafeman...ki yafeman Madina, nasan na cutarda ke nacutarda rayuworki amma dan Allah kiyafeman badan halina ba, ki amince dani ki karb'i soyayyata" yanata fad'ar haka harta shige ciki,

Tashi yai yakoma cikin motar yadora kansa akan sitarin motar yaita kuka yana zubda kwollah masu zafin gaske tamkar k'aramin yaro, shikad'ai yasan irin zafi da k'unarda zuciyarsa kemasa, yau shine karo na farko atarihin rayuworsa daya tab'a zubda kwollah akan mace.

Saida yai mai isarsa sannan yatada motar yafice.
Yauma dai baisami zowa fulani's day ba, sbd woni azababben ciwon Kai da zazzab'i dasuka rufesa, bayan andawo daga event d'in aka Kira family doctor na gidan yadubasa,

Abu nafarko daya fara cewa yana damunsa shine, yawon tinan da tarin damuwa, sakamakon hakan yasa ciwon zuciya ke nema yakamasa, sbd haka dole yakula da kansa domin gujewa saka rayuworsa acikin matsala.

Tinda doctor yafad'i abunda ke damunsa momy tasan inda ciwon yasamo asali, hakama abbas amma dai sukai shuru suka kyale, haka ya kwana a wohalce yanata fama da suyar zuciya dakuma ciwon zuci.
_______________________

Yau takasance itace ranarda za'a d'aura auren Dr. Ismail da Dr Madina, danhaka yau dik acikin tarin farinciki suke,

Ango sai kaikawo yake anata zirga zirgar zowa d'aurin aure garin Raha, amare kowa sai farinciki ake da zowan wonnan ranar anakuma jiran lkc yayi ashafa fatiha,

A babban masallacin juma'a na garin Raha za'a d'aura auren bayan angama sallar juma'a da k'arfe uku cif na rana.

Bahijja kowa tadage akan lallaifa saitaga bayan Madina, kokuma tahana auren Madina da Ismail, dikda kowa tana acikin sell rufe dan har yanzu Ismail yace kar asakesu.
...................

Around 1:30pm dot su Dr ismail suka iso garin Raha, dik woni d'an uwa da abokin arziki dakuma abokanai na Dr ismail da manyan iyayensa ciki kowa hadda abokanan mahaifinsa Dr Mu'azzam, dik sun hallara akatafaren masjid d'inda za'a d'aura auren sa da masoyiyarsa abar k'aunarsa,

Hakama iyayen Madina da y'an uwa da abokanan arziki dik sun iso.
Su Ismail na'isowa yakira Madina yafad'a mata, kunya takamata tarufe fuskarta kamar ababansa take,

Bayan angama sallar juma'a aka d'aura auren Dr Ismail Mu'azzam da Dr Madina Muhammad ja'ey, d'aurin aurenda yasamu halartar dibbannin mutane yakuma samu shaidar dibbannin mutane, Masha Allah Madina Allah isanya alkhairi yabada zaman lfy ameen.

Bayan an d'aura auren woni k'anen Abban madina dake garin damaturi ya gayyaci su Abban Ismail walima a woni katafaren holl dake cikin garin BUNZA L/gvmnt,
su Ismail kowa ana gama d'aura auren suka kama hanyar gida domin gudanarda tasu liyafar acan.

Tinda aka d'aura auren yakira Madina sukai woya, sunjima ssi suna woya dan har Saida zasu fice sannan yai sallama da'ita.
....................

Yau tarin farinciki a zuciyoyin su Madina baya misaltuwa, dan su chuchu sai suke ganin kamar ma sunfi ita madinar farinciki,

Around 4pm suka fice izowa gidan k'anen Abban Madina wato Abba garso na damaturi wonda kuma yake soja ne, kasancewor acan zasuyi Shirin dinner shys sukace bara sujecan su wuni, koda sukaje acan dinma cike yake da mutane ssi, danhaka suna zowa suka shige d'akin matarsa sukai zamansu.

Suna a zaune suna fira sai Madina tad'akko woyarta tashiga Kiran layin Ismail, saidai dik takira sai ace woyar akashe take, batadamuba sbd tasan yau dole yazama busy ssi.

Suna zaune sunacin abinci Madina nashan had'inda umma matar Abba garso tamata saiga umman tashigo hankali atashe a hargitse tad'auki woyarta tafita,

Ganin halinda tashigo dashi yasa hankalinsu yatashi danhaka Madina tasaka hijab tafita woje domin jin ko lfy,

Abun mamaki Koda tafita saita tadda umman da kanwor umman su dawosu kannen Abban su Madina a tsaye suna kuka suna sharan kwollah, d'ayar nafad'in "Allah sarki y'ar nan, Allah yanufa dai sai igiyar aure tashiga a tsakaninsu, wonnan k'addarar danauyi take, Allah yamaka rahama wonnan yaron ya kyautata makoncinka yasadaku a al'jannar firdausil a'ala" sauran suka amsa da ameen cikin yanayin jimami,

Dasauri tak'arisa gunsu cikin yanayin damuwa tace "Ummah, waya rasune?" Kallon kallo suka shiga yi a tsakaninsu sai akarasa Mai magana a tsakanin su, sake jefamasu tambayar "meke faruwa ne umma meroje, waya rasu ne?" nanma dai shuru sukamata,

Har umma merojen tabud'e baki zatai magana saiga Abban yashigo a hargitse cikin tashin hankali..

Dasauri umma tabi bayansa izowa parlon sa, ganin haka yasa itama tabi bayansu sbd hankalinta yafara tashi daganin yanayinda suke aciki.

Koda taisa saitaji umma nafad'in "Abban mahir, yah ake cikine, and'akko gawarwakin ne" cikin tashin hankali Abban yace "Eh..an d'aukesu anfice can birnin kebbi dasu cikin motar ambulance dan dikansu nacikin motar mutum d'aya ne baimutu ba, shima kuma Koda ya rayu to saidai woni ikon ubangiji, dan yajigata ssi".

Umma tace "subhanallah...wayyo Allah, wonnan k'addarar danauyi take, wlh Abban mahir yanda zamu fadawa yarinyar nan Madina mutuwar mijinta kawoi muke tinani, bansan taya zan fuskanceta da wonnan maganar ba".

Tanjin abunda umma tafad'a nantake gabanta ya yanke yafad'i, k'irjinta yafara dukan tara tara,

Dasauri tayaye labulen kofa tashigo cikin parlon, suna ganinta sai sukai tsaye suna kallonta suka kasa motsin kirki, k'arisowa tai kusa dasu muryanta na rawa tace "kardai kuceman Ismail ne yamutu" tafad'a tana kallonsu kwollah kuma tini suka fara ambaliya a fuskarta, Abban mahir ne yamatso kusa da'ita sannan yakai hanunsa yamatso da'ita kusa dashi yacemata,
   "Kingane Madina, bafa mutuwa yaiba, kawoi dai sunsamu d'an accident ne a hanyarsu takoma gida bayan angama d'aurin auren, amma bawonda yamutu acikin, dik suna lfy" Sam bata yarda da abunda yafad'a ba acikin zuciyarta harma a fuskarta,

Cikin damuwa tace "Abba kada kub'oyeman idan mutuwa yai dan Allah, yanzufa naji umman mahir nafad'in yanda zasu fad'aman ne suketa tinani, yanzu kuma kaceman bamutuwa yai, dan Allah kufitardani acikin duhu" tak'arisa cikin yanayin magiya.

Numfashi Abban yasauke tareda dafe goshinsa da hanunsa d'aya, sannan yad'ago yakalleta yace "Madina, dik abunda kikaga yafaru da bawa to muk'addarine daga ubangiji, Allah dakansa yace, shin dan kunce kuyi imani shikenan sai mubarku batareda mun jarabce kuba, shys Allah yake jatabtar bayinsa domin yagwada k'arfin imaninsu, idan kayi hkr kadaure saika cinye jarabawan, sbd haka Madina kiyi hkr kicinye wonnan jarabawan taki,

Hak'ika Isma'il yarasu, Isma'il yarigamu gidan gsky, asanadin hatsarinda suka samo wonda yai sanadin mutuwar mutum hud'u dake cikin motar mutum d'aya ne bai mutuba shima kuma yana acikin mawuyacin hali".

Wosu zafafan kwollah ne kebin kuncenta zuciyarta nawoni irin harbawa dak'arfi idanuwonta kuma suna zubda kwollah masu zafin gaske, bakinta har rowa yake sbd tsintsar b'acin rai da tashin hankali,

Ahankali tafara magana "yanzu shikenan Isma'il yatafi yabarni kamar yanda Inna ta da y'ar uwata suka barni, shikenan shima yabarni har abada, shkn..nima wlh binsu zanyi Abba dan Allah karikeman y'ata jawahir nabaka amanarta nima wlh binsu zanyi bazan iya zama acikin wonnan duniyar ba, bakomai acikinta sai bak'in ciki da tarin mayaudara da mugwaye" saita juya zatai tafiya aikwa nantake jiri yad'auketa tazube ak'asa wonnan somammiya.

Dasauri sukayo kanta Abba nakiran sunanta "Madina... Madina.. Madina....!!!" cikin tsintsar tashin hankali, umma kam kuka tafashe dashi cikin tsintsar tashin hankali, jijjigata Abba yashigayi yana murza hannayenta amma ina numfashinta yatafi danisa,

D'aukanta yai suka fito woje da'ita nanfa akayo kanta domin ceton rayuworta numfashinta yadawo, ruwa aka shiga zubamata a jiki dakai dakyar numfashinta yadawo, nan aka d'auketa aka koma ciki da'ita.

Su chuchu naciki akaje aka sanardasu halinda ake ciki, aikwa dasauri suka fito sukayo gun Madina cikin kuka da tsintsar tashin hankali, 
Tinda Madina tafarka take kuka tana fad'in "wayyo Allah na...wayyo mijina abun k'aunata, mutuwa meyasa kikamana gaugawa, meyasa kika rabani da abun k'aunata, shikenan Isma'il shima yatafi yabarni har abada" saikuma tasake fashewa da kuka Mai cike da tsintsar ban tausayi da raunana zuciyar mai karatu.

Story continues below

Su chuchu ma kukan suke ssi, hakama su Inna meroje kukan suke har suka saka Abba shima kukan.

Kankace me labari yakarad'e garin Raha gaba d'aya, kowa sai jimamin abunda yafaru yake, Abban Madina yayi kuka yayi kuka ssi, hakama Madina har yanzu taki barin kuka.

Da Abban Madina da Abban mahir k'anen sa dawosu sauran k'annensa da wosu mutanen ne suka shirya suka tafi birnin kebbi domin ayi jana'izar dasu,

Madina ma kasa zama tai taroki su Abba da'abarta taje taga gawor mijinta, basu hanataba kowa saita shirya tareda su Inna meroje da umman mahir dasu chuchu suka tafi.

Koda suka iso har anmasu wonka anmasu sallah su kawoi ake jira, bahijja da iyayensa suna a zaune daga gefe kasancewor acikin parlon sa ne suke, dataje gun gaworsa dakyar kuka yatsaya mata tashiga jero masa addu'oi sannan tashafa fuskarsa takuma sumbaci goshinsa daketa haske, ta harde d'ayan hanunsa da nata kwollah nata zuba daga idonta, 

Fuskarsa sai kyalli take kuma tana d'auke da murmushi, bahijja sai harara take dalla mata ji take kamar tazo tashaketa itama tamutu d'in,
bayan tagama masa addu'oi sannan ta tashi, sai akazo aka d'auki gawor aka fita da'ita.

Bayan anfita da'ita izowa mutuware domin kaisa makoncinsa na gsky, sukuma su Madina suka fice izowa Raha,
Allah 
   _______________________

Gaba d'aya yafita daga hayyacinsa idan kagansa Sam bazakace shi bane sbd yanda gaba d'aya yacanja, yai wota muguwar rama kamar ba DEEDART ba, wonda yakeda kiba da cikar jiki.

Tinani yamasa yowa ga damuwa nasan tamasa illah, gakuma ciwon zuciya dake barazanar kamasa, gaba d'aya bikin nan da'akayi ba event d'inda ya halarta, gashi har yau and'aura auren har ankawo amarya harma sunfice izowa dinner amma baisamu yajeba sbd woni wohalallen ciwon Kai dake damunsa wonda yakeda nasaba da halinda yake a ciki na damuwa.

Kwonce yake akan kujera 2seater dake parlon hajiya, hajiya nadaga gefensa tanajan carbi, momy kuma na zaune ak'asa tana woya da dadynsu DEEDART tana fad'amasa halinda DEEDART yake a ciki,

Munira kanwor Abbas da meehash suna zaune akusa da momy suna kallon TV inda ake haska woni film Mai suna kwana casa'in a tashat arewa 24.

DEEDART kam bamaya ta kallo dan shikad'ai yasan abunda yakeji acikin zuciyarsa,

Bakomai yafi d'aga masa hankali ba kamar kalmomin da Madina tafad'a masa "Koda giyar wake nasha, koda narasa mijin aure, Kai Koda kaikad'ai ne karage namiji a duniya bazan tab'a aurenka ba har abada, I hate u...I hate u, natsaneka DEEDART, u are my enemy" woennan kalaman sune suke k'onamasa zuciya.

Dik yatina woennan kalaman saiya zubda kwollah, zuciyarsa taita masa zafi tana ciwo kamar zata fasa kirjinsa tafito sbd radadin kunarda take masa.

Hajiya ce takallesa tace "AHMARD, wlh kacire wonnan tinanin daga zuciyarka idan baso kake ka hallaka kanka da kanka ba, kafa duba kaga  yanda dik kabi karame kafita hayyacinka, kana nema ka hallaka kanka, haba wonnan wace irin rayuwa ce, dik abunda yafaru yariga yafaru bakuma zai tab'a dawowaba kokuma yacanja" momy tace "ah to, gayamasa dai dakanki ko zaiji maganarki, dan ni yariga yamaidani abokiyar wasansa, konamasa fad'an baji yakeba".
Shidai sauraronsu kawoi yake batareda yacemasu uffan ba, daga karshe ma tashi yai yakoma side d'insu na samari yai kwonciyarsa.

        ....Washe gari yadanji sauki yai wonka yafita tareda abokanan ango da ango sukaje suka gaisa da amarya, da maraice kuma sukaje sukaci tuwon b'arna kamar yanda ake cewa, 
Saidaifa yak'udiri aniyar saiya sake komawa akaro na uku yaroki Madina ko Allah zaisa ta amince da soyayyarsa.

   _______________________

Bayan kwana biyar da rasuwor Ismail su Madina suka tattaro suka dawo birnin kebbi, a katafaren gidanta da'akamata jere tasauka wonda kuma Ismail yamallaka mata shi amatsayin kyauta sbd kawoi irin soyayyarda yake mata, da gidan dakomai nacikinsa mallakitane,

Story continues below

Wonnan karon da k'annenta tazo woenda suke yay'an kannen Abban tane woenda suke uba d'aya da abba, mata su uku ne maza kuma su biyu, matan zata sakasu a college of nursing school, mazan kuma Federal University dake garin kalgo L/gvmnt acikin jihar kebbi state,

Jawahir kuma tamaidata school inda tacigaba da karatu dan can Madina sunce saitaga ma primary school sannan zasu d'auketa a secondary level.

Ahankali suka fara rayuwa acikin k'aton gidan dake cikin G.R.A kusa da gidan Alhj faruku bagudu, k'ane ga Alhj Atiku bagudu Governor of kebbi state, gidan babban gidane dayake d'auke da 4bedrooms 2parlors, sai k'aton kitchen dakuma woni kitchen d'in daban, 

D'aki namusamman tawarewa jawahir, inda tacikasa fam da kayan wasan yara, Teddy's da y'ar tsana kala kala, a bangon d'akin kuma hotunan jawahir ne, wosu itakad'ai wosun kuma tareda momynta, wosun kuma tareda momynta dasu chuchu, dik dai anmannasu a bangon, 

D'akin komai pink and blue color ne, hatta wardrobe d'inta Pink ce, itama Madina nata d'akin komai blue and white color ne.

Haka dai ahankali suka fara rayuwa aciki, har yanzu Madina takasa cire damuwar rashin mijinta acikin zuciyarta, mutuwarsa ma saita dawo mata da mutuwar mahaifiyarta data y'ar uwata baya, komai yadawo mata sabo tamkar yanzi ne abun yafaru.
  ________________________

Bayan kwana biyar dagama biki yashirya yasake komawa garin Raha akaro na uku domin neman soyayyar Madina, saidai koda yaje sai akacemasa batanan takoma birnin kebbi,

Yaso yatambayi adireshinta amma ina baisan wanda zai tambayaba sbd bamacan gidansu yajeba sbd yana tsoron yahad'u da Abban ta,
Haka ya tattaro yadawo gida batareda yasamu biyan buk'atarsa ba.

Yaso yaje birnin kebbi domin yanemi inda take yaje gunta, amma ina washe gari suka koma gida habuja,

Aikwa komawarsa tazamemasa tamkar masifa, dan kamar yakoma ciwo yamasa sallama, tin abun yana y'ar wasa harya fara fin k'arfin tinaninsa dama dik woni dake cikin gidan.

Gaba d'aya DEEDART yafita hayyacinsa, Koda yaushe kirjinsa yake fad'in yanamasa ciwo yana masa zafi, kankace me tini yafara aman jini, babban abunda yak'ara bada gudumawa wojen k'ara hab'b'aka ciwon dake damun DEEDART shine,

Zafafan kalamanda Madina tawatsa masa lkcnda yaje neman soyayyarta akaro na biyu, woennan kalaman a dik lkcnda yatinasu sukan k'ara dad'amasa da bak'in ciki da,

Suna zaune acikin parlor kawoi su momy sukaga yafara tari, daganan sai aman jini ba kaukautawa jinin yake zuba daga bakinsa da hancinsa, 

Cikin tsintsar tashin hankali momy tayo gunsa Deen ma yazo dasauri yataimaka masa yazauna yana cigaba da zubda jinin, momy tad'aga kansa sama ko jinin zai tsaya amma ina saima cigaba da zuba yai, 

Cikin tsintsar tashin hankali momy kefad'in "haba DEEDART, wonnan wace irin rayuwace kana nema ka hallaka kanka da kanka, nafad'a ma kacire wonnan yarinyar aranka tinda dai tafad'a ma batasonka, karabu da'ita kakyaleta kanemi wata tinda ba'ita kadaice y'a maceba a duniya, ga yay'an yayyena nan kaje kanema bawocca zaahanaka kuma ba wocca zatace bata sanka acikinsu, haba..haba wonnan abun dame yai kama, idan Kai bakasan kanka ni inasanka" DEEDART kam ko jinta bayayi.

A hargitse ganin jinin yaki tsayawa yasa tad'akko woyarta takira dadyn su, yana d'agawa tafad'a masa halinda abun k'aunarsa ke ciki, 

Acikin few minutes saigashi ya'iso, nan suka d'aukesa suka fice izowa wota katafariyar hospital dake cikin garin habuja.

Daisarsu aka wuce dashi emergency room domin bashi tamakon gaugawa.

Kimanin 30mnts aka d'auka kamin asamu yadawo hayyacinsa, jinin yatsaya akamasa dik treatment d'inda yadace sannan suka maidasa d'akin hutu,
Kimanin 1hr yad'auka yana bacci sbd injections d'inda akaita masa dik masu karfine woenda zasu sakashi yai bacci domin jininsa yasauka yasamu yahuta.

        
         ...Bayan doctor yagama hada bayanan abunda ke damunsa saiya Kira dady a office d'insa inda yamasa bayani kamar haka "Aabu nafarko dake damun DEEDART shine, hypotension, wato hawan jini, tabbas bako shakka DEEDART yakamu da hawan jini wonda yawon tinani da damuwa ne suka janyo masa hakan, a wonnan karonma jininsa yahau ssi har zuciyarsa tana harbawa dak'arfi shys yakaisa gayin aman jini, sannan dole akula dashi sbd idan yana yowan shiga irin damuwa dayowa to lallai zai cigaba da zubar jinin ne, idan kuma yana zubar jinin to komai zai iya faruwa, 

Sannan dole a kula dayimasa abunda yakeso akuma gujewa abunda bayaso sbd gujewa b'acin ransa domin gujewa rasashi gaba d'aya" nannauyan numfashi dady yasauke sannan yayiwa doctor gdy sukai sallama yafita.

Bayan yazo gunsu momy saiya mata bayanin abunda ke damun DEEDART kamar yanda likita yamasa bayani,

Hankalin momy yatashi matuka sbd tanasan DEEDART fiye da tinanin Mai karatu, dik acikin yay'an ta gsky tafisan DEEDART, sbd shiyafi kama da mahaifinsa itakuma tanasan dady ssi dan kusan itacema tafara ganinsa taji tana sonsa har sukai auren, sanadin sonda takemasa yasa takasa barinsa a lkcnda yake gudanarda muguwar sana'arsa.

Hakan yasa nantake taci burin samawa DEEDART abunda yakeso da dika k'arfinta dakuma abunda ta mallaka, 

Bayan yafarka ne momy taita masa fad'a akan yafitarda Madina a ransa, yarabuda ita tinda tace batasansa, ga mamakin momy saitaga kwollah nazuba daga idanuwon DEEDART bakinsa har rowa yake sbd kunar zuci.

Ahankali kuma yad'ago yakalleta cikin murmushi wonda yafi kuka ciwo yace "mom...mom...momy, wlh da inada yanda zanyi domin nacire soyayyar Madina a raina danayi, bansan lkcnda soyayyarta tashigeni ba har take nema tarabani da rayuwata, wlh inasan Madina momy, ina Santa so mara misaltuwa,

 Amma Madina tace batasona, tatsaneni bata k'aunata, kuma tace ni mak'iyintane batada makiyi kamata, ki taimakeni momy, ki taimaki rayuwata daga fadawa hall...ak...a" yak'arisa kwollah nazuba daga idanuwon sa masu zafin gaske,

Dasauri momy tazo tarungume sa tana bubbuga bayansa alamar rarrashi, a zuciyata take fad'in "tabbas SO babban abune, yau akan SO DEEDART nazubarfa kwollah da idonsa har yana fad'aman na taimakesa karya rasa rayuworsa, kuma dik akan mace, tabbas SO shu'umi ne".

Saida ta tabbatarda yadaina kukan yanutsu haryaci abinci yakwonta yasakeyin bacci sannan tafita.

Tana fita takira woya naji tana fad'in "waalaikasalam Abbas, yawwa dan Allah so nake kanemoman adireshin Dr Madina Muhammad ja'ey, zowa gobe katuroman zanzo kebbi zowa gobe, but...inasan adireshin kamin na'iso" cikin girmamawa Abbas yace,

     "Toh... Ammi na, angama, saikin iso" tace Ok sannan takatse kiran..

Abbas yai mamakin wonnan abun da Ammin sa tace yanemomata, sbd yayi tinanin DEEDART yamagance wonnan matsalar dake tsakaninsa da Madina, amma wonnan Kiran da Ammi tamasa ya tabbatar masa da akwoi wota a k'asa, wota k'il abun yafi k'arfin DEEDART,

 Saidai kuma ace yanda DEEDART yakeda k'arfin iko a k'asar nan amma ace wota mace ta gagaresa, Kai ina akwoidai abunda yasa ammin sa take neman adireshin amma badan wonnan matsalar ba.

Hmm nikwa nace, Abbas kenan, bakasan yanzu tasauya zaniba, yanzu bakamar da bane.
   .....................

Tin lkcnda aka kaishi hospital ake masa k'arin jini har yanxu, gashi har yanzu yaki samun k'arfin jiki, baya iya tsayuwa dakansa sai an rik'asa, gakuma wosu manyan injections da ake masa sbd har yanzu jininsa baidawo normal ba.

Yanzin ma kwonce yake yana bacci k'arin jini na makale a hanunsa, fuskarsa tai fari kamar mace mai yaron ciki hakama jikinsa.

DEEN da dady dakuma meehash ne zaune a gefensa, momy da neehash na daga gefensu momy nakusa da DEEDART tarike hanunsa wonda ake masa k'arin jini akansa, lkc zowa lkc kuma tana shafa sumarsa data barbaje sbd wohala,

Tsintsar tausayin d'an natane cike a zuciyarta, ji take inama ana siyan soyayya da kud'i data siyamasa soyayyar Madina, domin ceton rayuworsa daga hallaka.

Ahankali tajuyo takalli dady sannan tace "dadyn DEEDART, nifa gobe kebbi zanje gun wonnan yarinyar dakuma gun mahaifanta ko Allah zaisa suga girmana su taimaka su ceci rayuwor wonnan yaron, wlh dadyn DEEDART ina tsoron kar yarona yafad'a acikin woni mawuyacin hali, kadubafa kaga yanda yakoma, haba...yakamata Kai woni abu akai".

Tak'arisa cikin yanayin damuwa.
Nannauyan numfashi dady yasauke sannan yafara magana "wato hajiya Batoul, wonnan al'amari fa babban al'amari ne musamman idan kikai duba da irin halinda DEEDART yasaka wonnan yarinyar da iyayenta a baya, sbd haka dolene DEEDART yafuskanci irin wonnan matsalar,

Ke kanki kinsan halayyar d'an naki abaya, kekuma San abunda yafaru tsakaninsa da wonnan yarinyar, so dolene yafuskanci wonnan matsalar, amma insha Allah zanyi iya bakin kokarina domin ganin nafitardashi daga wonnan halin dayake ciki, sbd kema kinsan irin soyayyarda nakewa DEEDART, ke kanki dakika haifesa baki masa irin soyayyarda nake masa, so...insha Allah zanyi dik yanda zanyi domin ganin yamallaki abunda yake so, wato wonnan yarinyar Madina".

Neehash tace "dady dan Allah kataimaki brother, ka ceceshi daga wonnan halin dayake ciki dan Allah" tafad'a tana zubda qwalla" janyota dady yai yarungume tareda shafa sumarta dakuma sumbatarta yana fad'in "kidaina kuka neehash, insha Allah brother dinki zai tashi, zai samu abunda yakeso Insha Allah".

Wunin ranar gaba d'aya acikin bacci yayisa, jini kowa anmasa Karin kusan leda shida yanzu kuma drip ake masa Kari, da dare dady da Deen ne suka zauna momy dasu neehash kuma suka koma gida,

Washe gari tinda sassafe momy ta tashi ta tada su Neehash tareda ma'aikatansu suka shiga kitchen suka hada breakfast, bayan angama momy tadauka tareda driver sukaje hospital domin Kai masu break d'in,

Alhmdllh Koda taje kowa DEEDART yaji sauki ssi, yanzu yana iya tashi dakansa dan harma sallah yayi, aikwa ganin hakan yasa momy taji d'adi tai farinciki, dakanta tazauna tadinga bashi abinci abaki yanaci kamar k'aramin yaro, Deen sai dariyansu yake yana fad'in "yau brother tina baya ake kenan" saiya dallo masa harara yana murmushi, ko lkcnda suna yara momy kebashi abinci sbd wasa yamasa yowa baya iya zama yaci dakansa saita sakashi agaba sannan yakeci kokuma tabashi dakanta a baki,

      ......Saida yaci ya k'oshi tahada masa tea Mai kauri yasha sannan yakwanta, hanunsa har yad'an kumbura sbd karin jini da drip d'inda ake masa.
Bayan yakwonta sannan tazubawa dady abincin tabashi yakarb'a yana fad'in "Saida aka gama kula da d'a sannan aka tina dani" saitai dariya tace,

Story continues below

"Ayi hkr dadyn yara, tuba nake" shikuma yakarb'a yana murmushi.

Momy bata woni dadeba tamasu sallama zata tafi kebbi, check dady ya rubuta masa na kud'i yabata takarb'a sannan taje ta sumbaci goshin DEEDART yai murmushi yace "adawo lfy momy na, Allah yabada nasara, yasa Madina ta amince" tace "ameen..insha Allah ma zata hkr ta amince" su dady ma suka amsa da ameen sannan tafice.

Tana komawa gida cikin sauri tashirya driver yadauketa tareda su Neehash dazasu mata rakiya suka fice izowa airport.

Suna isa basufi 30mmts da zowaba jirginsu yasakko, 10am dot suka d'aga izowa kasar kebbi state.

1pm dot jirgin nasu yasauka a katafaren filin jirgin nan na Ahmadu bello international airport dake garin birnin kebbi l/gvmnt, yana sauka abbas tareda driver suka iso d'aukan ta,

Acikin mota Abbas kemata bayanin garinsu Madina Raha, sannan yafad'a mata yanzu tana nan tadawo birnin kebbi tana takaba na mutuwar mijinta, sannan yamata bayanin unguwar da take anan cikin birnin kebbi d'in.

Cikin few minutes suka iso gida, bayan sun iso ko abinci kasa ci momy tai, tana sauke kayanta tashuri jakarta da sauran kayan tafice tareda abbas,
Kai tsaye can birnin kebbi suka fice izowa gidan Madina dake cikin G.R.A wonda take zaune ayanzu, acikin d'an lkc koma suka iso birnin kebbi.

Wota katafariyar super market suka fice, inda tayiwa y'ar jikarta jawahir siyayya mai tarin yawa ta musamman, komai da komai na kayan yara Saida tasiya dikda kowa batasan yarinyar ba batakuma san girmanta ba, amma sai siyan kayan take jibgi jibgi kala kala, Saida tasiya ba adadi sannan taje tabiya kud'i aka saka acikin mota sannan suka fice.

Daganan kuma kai tsaye suka fice a unguwar GRA wato gidan Madina, 

Koda suka isa get man yana sharan woje yana tattara shara acikin mazubin saka shara, Abbas ne yafita sukai musabaha da juna cikin fara'a da sakin fuska sannan yatambayesa ko Dr tana nan, Nan get man yafad'a masa eh tana nan, gdy Abbas yamasa sannan yadawo yafad'awa momy,

Fita momy tai tashiga cikin gidan, Sam bata gane kan gidanba Saida get man yaje yashigarda ita ciki, cikin sallama tashiga katafaren main palor na gida gaba d'aya.

Jidda d'aya daga cikin k'annen Madina ta tadda zaune acikin palorn tana cin gyada saita amsa mata sallamar fuskarta d'auke da fara'a kuma cikin girmamawa, maijiddah tana kama da Madina bakad'an ba, hatta tsayinsu iri d'aya ne saidai Madina tafita kyau nesa ba kusa ba, kuma tafita cikar k'irji dan k'irjin nan na Madina a cike yake da dukiyar fulani.

Tashi maijiddah tai tama momy iso tazauna sannan suka gaisa sai jiddah tace "sannu umma, wa kike nema ne?" momy tace "am...nazo gun Dr Madina ne, ince dai tana nan" yarinyar tace "eh..tana nan, ai yanzu bata fita sbd tana takaba ne" momy tace,

    "Eyyah...Allah yamasa rahama ya kyautata tamu idan tazo" tace ameen sannan tace "bara nakira maki ita" tace to sannan tafice.

Bayan dakamar 5mnts tadawo d'auke da plate dake d'auke da ruwa da drinks da glass cup, tazo ta ajiyewa momy, momy tai gdy sannan yarinyar tafice,

Hak'ika momy tayaba da halayyar yarinyar, hakan ya tabbatar mata da matukar DEEDART ya auri y'ar gidan tabbas yai dace da mata, sbd ganin irin tarbiyyar jidda tasan sauran yaranma haka suke, sbd haka doke tayi yanda zatayi domin ganin DEEDART yamallaki Madina amatsayin mata.

Tana cikin tinani saitaji motsin mutane a bayanta, suna tafiya suna magan, ahankali tawaiga bayan saita gansu mata su uku, d'aya sanye da hijab har k'asa maroon color sauran kuma sanye da Lab Curt da farin hijab k'arami, wonda hakan ya tabbatar mata da itace Mai k'aton hijab sauran kuma y'an uwanta likitocine sukazo, a gabansu kuma wota kyakkyawor yarinya ce sanye da wandon jeans da y'ar t-shirt fara,

Story continues below

Antufke sumarta da rivom fari, kafafuwonta sanye da takalma plat shue bak'ake, tsalle tsalle take yarinyar tana wasa, tana kallon fuskar yarinyar ta tabbatar itace jikarta, jininta, wato y'ar shalelenta, sbd tsintsar kamanninta da DEEDÀRT data gani,

Tabbas Koda bakasan wonnan yarinyar ba matukar kaganta zaka gane itace y'ar sa, sbd tsintsar kamannin su dasukai yawa, gaba d'aya fuskarta fuskar DEEDART ce, hadda dogon hancinsa itama tanada shi,

Saida taga sunkusa isowa kusa da ita sannan tadawo da kallonta.

Ahankali suke tafiya har suka iso kusa da'ita sannan tad'ago suka gaisa cikin fara'a da sakin fuska, bayan sun gaisa sannan suka fice domin tamasu rakiya.

Almost 15mnts tad'auka kamin suyi sallama tadawo ciki tareda jawahir tana zuba rigima tana kuka woi saitabi su momy chuchu, kasancewor ana zowa school yasa tahanata binsu,

Bayan sun dawoo parlon tazauna tareda runguma jawahir sannan tasake gaisawa da momy cikin fara'a, bayan sun gaisa tace "saidai ban shaida fuskarba wlh" tafad'a cikin fara'a sai momy tace "Eh...nasan baki sanniba, sunana hajiya Batoul mahaifiyar DEEDART uban y'ar ki jawahir, ma'ana dai ni kakace agun yarki" dajin haka nantake yanayin fuskar Madina yacan,

Nantake b'acin rai ya bayyana a fuskarta, saita kauda kanta daga kallon momy, hakama momy fara'ar dake fuskarta gushewa tai sbd ganin yanda yanayin fuskar Madina yacanja, ahankali tacigaba da magana,

        ...."Y'ata Madina, nasani tabbas DEEDART yacutardaku, ya b'ata maki rayuwa yakuma b'ata feature d'inki sannan yasaka maku bak'inciki wonda baku tab'a shiga irinsaba a rayuwa, amma dan Allah dan Allah nake rok'onki Madina daki yafemasa dik abunda yamaki a baya kodon wonnan y'ar taku, wlh a yanzu DEEDART yana cikin woni mawuyacin hali wonda komai zai iya faruwa dashi, kuma dik akanki ne, 

Tsintsar soyayyarda yake maki tana nema tasa yarasa rayuworsa, a yanzu haka yana kwonce a gadon asibiti, dan Allah Madina ina rok'onki wota alfarma" sai Madina tad'ago da dara daran idanuwonta woenda suka canja sukai zajir sbd kukanda take, kwollah fal a fuskarta takalli momy,

Momy tacigaba da magana "dan Allah ki amince ki auri DEEDART kodon cigaban rayuwor wonnan y'ar taku, ki ceci rayuwor DEEDART Madina, kece kadai zaki iya ciresa daga wonnan halin dayake ciki na mutuwa ko rayuwa, sbd matukar bai aureki ba ciwon nan bazai tab'a rabuwa dashiba har abada, k'arshema yazama ajalinsa, dan Allah kitaimaka Madina kiceci rayuwa" tak'arisa cikin yanayin magiya da ban tausayi.

Cikin tsintsar b'acin rai Madina tamike tsaye tana zubda kwollah tafara magana "hajiya inaso kisani, kamar yanda kike k'aunar d'an ki, kike bakin ciki da takaicin woni abu mara d'adi yasameshi, to haka nima da mahaifiyata muke bak'in ciki da takaicin abunda DEEDART yama y'ar uwata wonda yai sanadin mutuwar mahaifiyar mu sbd tsabar bak'in ciki, kisani d'an ki yamana abunda har abada bazan tab'a mantawa dashi ba, woi shin meyasa mutane kukazamo masu yawan San kanku ne, 

Hajiya yanzu amatsayinki na uwa mahaifiya, ace yarki ce DEEDART ya aikatawa abunda yama y'ar uwata yazakiji...? Kuma wone mataki zaki d'auka idan har kinada damar d'aukan matakin" sai hajiya tai shuru kawoi tana sauraronta,

Cigaba tai da fad'in "hmm...natabbata da kece yanda kikeda dama har haka zaki aikata masa abunda yafi wonda namasa, DEEDART yacutar damu, yabata sunan gidanmu, ya manna mana tabonda har abada bazai tab'a goguwa ba a goshinmu, 

Wonnan dalilin yasa natsanesa, natsani dik woni mai hali irin nasa, nakuma tsani Mai irin sunansa,
Hajiya ina Mai baki hkrn fad'amaki, bazan iya auren DEEDART ba har abada kowa, sbd wlh natsanesa namasa muguwar tsanuwa, bana k'auran ganinsa sbd dik lkcnda nagansa saina tina da cin amanarda yamana".

Tasowa hajiya tai tazo kusa da'ita fuskarta cike da tsintsar damuwa taharde hannayenta gu d'aya tafara magana cikin magiya tace "dan Allah...narokeki Madina, kitaimaka kiceci rayuwar DEEDART, dan Allah" dasauri tajuya tabata baya tana zubda zafafan kwolla tace,

Story continues below

      "Kiyi hkr hajiya, bazan iyaba wlh, bazan iya rayuwar aure da wonda yai sanadin rabani da mahaifiyata da y'ar uwata ba, bazan iyaba".

Tak'arisa tana zubda zafafan kwolla, jawahir ganin mahaifiyar ta na kuka yasa nantake itama tafara kukan tana fad'in "mommy meyasa kike kuka, mommy kitaina kuka mana".

D'aukanta tai tarungume tareda sumbatarta a kunce tai d'an murmushi tacemata "bakuka nakeba my happiness, magana mukeyi da granny" tafad'i hakan tareda nunamata momy, 

Kallon momy tai irin kallon wacece ke..? bansanki ba, Madina talura da hakan saitace "wonnan sunanta granny, kigaisheta mana" saita kalli Madina sannan tasake kallon momy, ahankali tace,

     ...."Ina kwana" momy tai murmushi cike da k'aunar y'ar jikar tata tace "ina wuni dai jawahir, yh kk yh school" tace "Fine" kawoi sai momy tashafa fuskarta cikin tsintsar k'auna.

Saita kalli Madina tace "kozaki araman ita nakwana biyu kacal, wota kil idan DEEDART yaganta yaji farinciki jininsa yasauka" shuru Madina tai nawosu y'an sakonni kamin tad'ago tace,

     "Shikenan, amma bazan baki ita itakad'ai ba, sai tareda k'anwata, kuma kwana biyu kacal, shima dan kece yasa zan bari ta tafi, amma dabakece bace wlh bazan aminta ba" momy tasauke numfashi sannan tace "to Nagode".

Sai Madina tace "bara naje na shiryata" nan tashige ciki domin shirya jawahir,

Bayan y'an mintina suka fito, jawahir nasanye acikin wosu english wears wando da riga da y'ar teddy white color a hanunta, sai hafsat kanwor Madina wocca za'ai tafiyar da'ita, hanunta d'auke da y'ar jaka wocca kayansu suke ciki.

Suna isowa gun momy saita d'auki jawahir tana lakutar hancinta cikin yanayin wasa, Madina tadubeta tace "dan Allah hajiya kirik'eman y'ata Amana, karki bari wonnan mugun uban nata yacutarda ita" murmushi momy tai sannan tace "karki damu y'ata, insha Allah zata dawo cikin aminci kamar yanda ta tafi, am akwoi kaya woenda nayowa k'awata jawahir tsaraba, saiki turo a d'auka suna cikin mota" Madina tai murmushi tace "to angode Allah ikara bud'i".

Hajiya tace "ameen.."
     Nan suka fito atare da Madina, Saida tamasu rakiya har bakin mota get man yakwaso kayan yashiga dasu ciki, har momy tashiga mota Madina tajuya zata koma ciki sai momy tafito takira Madina,
     
      "Madina...." saita juyo tareda tsayawa, momy takariso kusa da'ita sannan tace "dan Allah kiyi tinani akan maganarda mukai, kinji ko y'ata" gyada Kai tai batareda tace komaiba sannan tajuya takoma ciki,

Nan itakoma momy takoma mota.

Kai tsaye garin gwondu suka fice, acan sukai sallar la'asar sukaci abinci, 
4:30pm dot suka fice izowa airport, 5pm dot jirginsu yad'aga izowa Abuja city.

Sai kusan 8;15pm sannan suka sauka garin habuja, koda suka sauka tini driver's sun iso suna jiransu, danhaka suna sauka aka d'aukesu suka fice izowa katafaren gidansu.

Koda suka isa neehash da masu aiki ne kawoi acikin gidan su dady dik sunacan hospital, damurna Neehash tazo ta rungume momy tanamata sannu da zowa,

Momyn ta amsa mata amma fuskarta babu wota wolwala ssi a fuskarta, ganin hafsat d'auke da fine baby yasa fuskarta tafara bayyanarda mamaki a fili, bata b'oye mamanki ba har Saida tacewa momy,

      ..."Momy bak'i mukai ne a gidan?" sai momy tai murmushi sannan tadafa shoulder d'in hafsat cikin fara'a tace "Neehash wonnan k'awarki ce hafsat, wonnan kuma y'arki ce jawahir" cikin mamaki Neehash tace,
"Momy banshaida suba ai, daga ina suke?" d'an murmushi momy tai sannan tace "hmm...neehash, kishiga dasu ciki kisaka akawo masu abinci da abin sha, bak'in ki nesu, daga baya zanmaki bayanin kosuwaye su" tafad'a tana kallon jawahir daketa Shan sweet d'inta.

Neehash tace to sannan taja hafsat suka shige ciki, momy ma sama tahaura izowa bedroom d'inta.
     Bayan dakamar 1hr momy tafito cikin wota sabuwar shigar, maana tayi wonka tacanja kaya kenan.

Bedroom d'insu Neehash tafice, Koda taje saita tadda Neehash da hafsat akan gado suna shan fira jawahir na'a kwonce tana baccin gajiya, shigowa tai ciki nan suka gaidata sukamata barka da fitowa ta amsa sannan tace,

"Au...kawar tawa bacci tai kenan" hafsat tace "Eh...hajiya, ai muna shigowa tai baccin" sai momy tace "To...zanje asibiti ne kuma inaso natafi da'ita gun dadyn ta, domin yaganta" hafsat tace "to hajiya badamuwa, saikun dawo" tace to sannan tad'auki jawahir d'in tad'orata kan shoulder dinta sannan tafice.

Koda ta sakko tini driver yafito ita kadai yake jira, danhaka tashiga motar yatada suka fice.

Dasuka isa hospital d'in driver ne yad'akko mata jawahir suka shiga cikin hospital d'in, 
Koda suka shigo room d'inda DEEDART yake sai suka tadda dady da deen a zaune, DEEDART kuma yana a kwonce yanacin ayba banana.

Shigowar momy yasa yad'ago daga kwoncenda yake, yana ganin momy da mani driver saiya tashi a zaune, Nan mani driver yashiga masa sannu yanamasa sannu da jiki ya amsa yana kallon babyn dake kan shoulder d'insa.

Cikin fara'a su dady shiga mata sannu da zowa tana amsawa fuskarta ba woni wolwala bawoni sakin fuska ssi, ahankali shima DEEDART yamata sannu dazowa ta amsa tana masa murmushi.

Ahankali yakalli momy yacemata "momy na, ina fatar kinci nasarar abunda kikaje nema, ma'ana Madina ta amince da soyayyarta zatakuma amince ta aureni" dajin abunda yafad'a nantake tsintsar b'acin rai da tarin takaici suka bayyana k'arara a fuskar momy, karb'an jawahir tai daga hanun mani saitaga ma ashe tafarka daga baccinda take, tana karb'an ta mani yafita.

K'arisowa tai gunsa sannan tazauna kan kujerar dake kusa dashi sannan tafara magana "DEEDART...inaso kayi hkr dajin abunda zan fadama yanxu dan nasan kaji fiye dashi daga bakin Madina, DEEDART inaso kayi da *HUKUNCIN ALLAH* wonda yatsara akanka, 

Dik yanda naso nashawo kan yarinyar nan wlh nayi amma taki amincewa, kasani DEEDART ba abunda bazan makaba matukar inada damar yin hakan, zankuma iyayin dik yanda zanyi domin ganin ka mallaki abunda kakeso arayuwa, Saidai wonnan yafi k'arfi na Ahmad, Madina tafadaman bazata iyayin rayuwar aure da wonda yai sanadin mutuwar mahaifiyar ta dakuma y'ar uworta, 

     Sbdhaka DEEDART inaso kayi hkr karungumi k'addara, kad'auki wonnan al'amarin amatsayin k'addarar rayuworka, ga yarka nad'akkoma kaganta kozakaji sanyi a ranka, itama dakyar tabani ita, ahakanma Saida tahad'oni da wota kanworta tace badan niceba dabazata bada itaba wa dik woni ahalinka,

  DEEDART, Madina tamaka tsanuworda batada misali, tamaka muguwar tsanuwa wocca ni banga laifintaba, dan Koda nice kama abunda kamasu wlh zan iya maka abunda tamaka a yanzu, sbdhaka inaso kayi hkr kacireta aranka, kaje acikin yay'an y'an uwana kazabi mata".

Tinda tafara magana yafara zubda zafafan kwolla masu zafin gaske yana murmushi batareda ma yasaniba, Koda tagama magana fuskarsa dik tai faca faca da qwollah, hancinsa yai zajir hakama bakinsa.

Miko hanunsa yai alamar yad'auki jawahir saita noke kafad'a alamar bazataje ba, Saida momy tamata dabara sannafa ta amince taje,

Kan cinyarsa yazaunarda ita yakafeta da dara daran idanuwonsa yana kallonta cike da tsintsar k'auna, kallonda yake mata gaba d'aya fuskar Madina yake hangowa a fuskarta, 

Dady ne yamatso sannan yace "wai wonnan amaryata ce kenan" momy tai murmushi tace "lallai kam, gatanan tazo karb'an kud'in kayan make up" sai sukai dariya atare harshi d'in DEEDART, Deen ma matsowa yai yazauna kusa da momy sannan yashafa sumar jawahir cike da son yarinyar sannan yace cikin fara'a,

"Babyn sak dadyn ta, she look exactly like her father, kamanninsu iri d'aya, wlh brother komai nata irin nakane sak komaima, hatta yatsunta irin nakane" DEEDART yai murmushi yana share kwollah tareda sumbatar jawahir a goshi,
       Kallonsa take tana tinanin inda tasansa kota tab'a ganinsa, murmushi yai sbd yafahimci hakan.

Lakutar hancinta yai yace "baki shaidani ba ko baby" again kallonsa take cigaba dayi, hanunsa tariko wonda ake masa k'arin jini dashi tace "uncle bakada lfy ne?" Saiya gyada mata Kai alamar eh saita sake cewa,
   "To kaje momy na tamaka injection mana, zaka worke kadaina ciwo" murmushi yai kawoi sai momy tace "ki kira masa momyn naki dakanki taxo tamasa" saita kalli momy dake mata dariya.

DEEDART yashafa fuskarta saita waigo da kallonta gunsa saiyace mata "baby, woncan lkcn damuka had'u airport kin tambayeni sunana ko, kintina nacemaki sunana Uncle kawoi".

D'an shuru tai alamar tana tinanine, dan yarinyar akwoi shegen wayou, can saitai dariya tareda gyada kanta alamar eh tatina, shima murmushi yai sannan yace "toba sunana Uncle ba, sunana AHMARD DEEDART wato dadyn ki, nine dadyn ki jawahir" dajin abunda yafad'a nantake mamaki ya bayyana a fuskar yarinyar tai shuru tana cigaba da kallonsa kawoi.

Momy ce tadafata cikin murmushi tace "of course jawahir, wonnan shine dadyn ki, daga yanxu ba sunansa uncle ba sunansa Dady, kinjin ko" saita gyada kanta alamar taji, 
     Rungumeta DEEDART acikin jikinsa tareda sumbatarta a goshi, yanajin k'aunar yarinyar har acikin bargonsa.

Ahankali yafara d'an tari yana kare bakinsa da hanunsa, momy namagana dasu Deen dake fad'in kamannin jawahir iri d'aya dana DEEDART saitaga DEEDART yana tari gakuma jini a hanunsa dayake kare bakinsa da hanun,

Waro idanuwonta tai tafito dasu woje cikin razana, kamin ta ankara har jinin yafara zuba a bakinsa, dasauri tadauke jawahir tad'orawa Deen ita sannan tai saurin riko DEEDART d'in daketa faman tari jini yana zubarmasa a bakin.

Dady ma yana ganin hakan dasauri yataso daga inda yake a zaune yazo yatallafo fuskar DEEDART, tarin yake cigabada yi jini kuma Yana cigaba da zuba, yanzuma har a hancinsa jinin yake fita,

     ... Dasauri momy tafita tasanarda likitoci abunda ke faruwa,aikwa dasauri suka shigo nan suka shiga bincike bincike a jikinsa, bai daina tarinba jini kuma bai daina zuba ba, ganin hakan yasa suka fitarda su momy waje domin yin aikinsu.

Almost 30mnts suka d'auka sannan d'ayan likitan yafito cikin sauri, Nan sukai gunsa domin jin halinda yake ciki, Nan likitan yashiga koramasu bayani, 
   "Tabbas Mr DEEDART yana acikin critical condition, wonda ahalin yanzu komaima zain iya faruwa dashi, likitoci suna iya bakin kkrnsu dan yanzuma za'a shiga theater room dashi, dole amasa operation domin kwashe jininda ya taru a zuciyarsa wonda yake zubarwa asanadin bugunda zuciyarsa takeyi dak'arfi,

A gsky Alhj bazan b'oyemaka, yaronka yana cikin mawuyacin hali wonda sanadin woni abu dayakeso yakuma kwollafawa rai akansa baisamuba yashiga, da'alama zuciyarsa tanasan woni abune wonda batasamuba shys tashiga wonnan halin, sbd haka kuyi k'okarin ganin yasamu wonnan abun matukar kunsan ko mene shi, 
    Idan kuma bakusaniba to kuyi kkr kusani domin sama masa shi kodon ceton rayuworsa, wonnan gsky ce nake fadamaku, wonnan hanyar ita kadaice hanya mafi saukin samun lfyarsa, don ko yanzin munmasa aiki matukar yacigaba da shiga wonnan halin to next gsky ina Mai fargaban fadamaku abunda zai iya faruwa" nannauyan numfashi dady yasauke cike da tsintsar tashin hankali.

Momy kam tinda likitan yafara magana take kuka ssi, hakama Deen dik juriyarsa Saida ya zubda kwollah sbd ganin halinda d'an uwansa yake ciki dakuma abunda doctor yake fad'a.

Dady yace "OK doctor, yanzi dai aje ayi aikin, daga baya saimusan mafita" doctor yace ohk...sannan yafice.
       Momy kuka take ssi tana fad'in "wonnan woce irin jarabawa ce, jarabawa akan SO, oh... ya rabbi katausayawa bawanka" jawahir sai kallonsu kawoi take dan bata gane abunda ke faruwa ba.
Cikin gaugawa aka gama kammala komai domin yin aiki wa DEEDART,
  Bayan ankammala komai sannan aka canja masa kaya domin shiga dashi operation.

A kwonce yake sanye da oxygen a hancinsa wonda yake taimaka masa wojen numfashi acikin theater room dan tini aka shigo dashi yanxu isowar likitoci kawoi ake jira, ahankali yacire oxygen d'in jikinsa na makyarkyata yacewa yad'ago ahankali yacewa dady dake kusa dashi,
        ...."Dad..daddy in..inaso naga y'ata jawahir, domin nasan matukar bangantaba a yanzu to bazan sake ganinta ba, sbd nasan ni tawa tazo karshe, mutuwa zanyi dad..."

Bai k'arisaba dasauri dady yarufe masa baki cikin tsintsar tausayin d'an nasa, kwollah nazuba a idanuwonsa yafara masa magana,

    "AHMARD kadaina fad'ar haka, ciwo fa ba mutuwa bane, dik tsananin zafin ciwo akan warke daga baya, sbd haka kadaina fad'ar haka kaji, insha Allah zaka worke katashi harka raini yarka jawahir" d'an murmushi k'arfin hali yana cije leb'ensa na k'asa sannan yace "nasani dady mutuwa zanyi, Koda anman wonnan operation d'in zan mutu tinda Madina taki ta amince ta aureni, wonda yanzu kuma ita kadaice zata hana zuciyata cigaba da harbawa dak'arfi, sbd itace cikar burinta dik woni magani bazai tab'a mata aikiba matukar batasamu abunda takeso ba".

Yak'arisa yana dafe k'irjinsa sbd yanajin yanda zuciyarsa ke harbawa dak'arfi dak'arfi.

Kallonsa kawoi dady keyi, zuciyarsa cike da tsintsar tausayin sa, a zuciyarsa yake fad'ar "inama ana siyan soyayya, inama ana siyan k'auna daya siyawa d'an sa DEEDART soyayyar Madina, amma kash hakan bazata tab'a kasancewo ba, saidai a rok'eta kokuma anemota.

Dady woyarsa yaciro yakira layin Deen yace ashigo da jawahir ciki, nantake kowa saiga Deen d'in yashigo d'auke da jawahir, momy kam tinda aka shigo da DEEDART har yanzu kuks take takuma kasa shigowa tagansa kamin likitoci sushigo,

Deen naisowa yasauke jawahir sai DEEDART yacire oxygen d'inda ke hancinsa tareda miko da hanunsa alamar jawahir taje yana mata murmushi, ahankali kowa ta taka taje gunsa saiya riko hanunta tareda shafa fuskarta cikin so dakuma k'aunarta,

Hartace uncl... saitaki k'arisawa tasake cewa Dady tana kallonsa da daran daran fararen idanunta irin nasa, murmushi yasake yi ahankali yace,
  "Dother me, yah kike" tace "am fine" saiya sake cewa "kina Sona ko?" saita gyada masa Kai alamar Eh, murmushi yai sannan yad'ago ahankali ya sumbaceta a goshi sannan yace adoramasa ita kan gadon, nankwa deen yadorata saiya sakada hanunsa acikin nata yana kallonta, itakam kallonsa kawoi take.

Anan su dady suke a zaune har Saida doctor's suka shigo sannan deen yadauki jawahir suka fita,

Acikin y'an mintina aka fara gudanarda operation d'in,
Bayan anfara dady yacewa su momy "zan tafi kebbi garin Raha gun mahaifin wonnan yarinyar ko Allah zaisa yaji tausayin halinda yaron nan yake ciki ya aura masa ita" momy tace,

    "Shikenan, Allah yasa kasamu nasararsu" yace "ameen, zowa dare insha Allah nakeso naisa, zanbi flyt d'in dare" nan sukamasa fatan nasara dakuma addu'ar sauka lfy.

Cikin hanzari dady yakira anema masa Visa yanzu, sannan yakira acan kebbi yasanarda zowansa, cikin sauri kowa aka samu Visa card d'in, nan yashirya tareda driver dinshi da security's d'insa masu bashi tsaro suka fice izowa airport,

Dazuwansu bawoni b'ata lkc jirginsu yad'aga izowa kasar kebbi state.

Tafiyar kusan 3hrs suka isa kasar ta kebbi state, suna saukowa driver's na isowa, nan suka d'aukesu,
   Kai tsaye garin Raha suka fice, inda sukai tafiyar kusan 30mnts kamin su isa garin na Raha.

Lkcnda suka isa dai dai lkcn ana Kiran sallar magrib, danhaka suka fice masjid domin yin sallah.

Bayan angama sallar suka fito, sai dady yasami woni dattijo dai dai tsaransa dai wonda shima atare sukai dallar, bayan sunyi sallama sun gaisa sai dady yacemasa "am mallam, dan Allah woni bawan Allah nake tambaya Mai suna mallam ja'ey mahaifin Dr. Madina wocca take aiki a asibitin jawahir special hospital a garin birnin kebbi" murmushi mutumin yai sannan yacewa dady,

Story continues below

"Alhj. ince dai lfy kake neman mallam ja'ey?" sai dady yai murmushi sannan yace "lfy klw wlh" sai mutumin yace "to a yanzu haka dai kana a tareda mallam ja'ey, ard'on garin Raha mahaifin Dr Madina mahaifiyar munawara konace jawahir".

Woni irin farinciki ne ya bayyana a fuskar dady yai murmushi sannan yasake mikawa Abban Madina hanu sukai musabaha, bayan sun sake gaisawa sai Abba yace "to muk'arisa gida ko saimuyi magana acan, naga kamar yafi Nan" dady yace to sannan suka fice izowa gidansu Madina.

A k'afa suka taka sbd banisa daga masjid zowa gidan, security's d'in dady kuma suka biyosu a baya da motoci.

      ....Bayan sun iso Abba yamasu iso ixowa cikin parlonsa, sannan yakawomasu fura da tatacciyar madara Mai sanyi, dady kowa dama yanasan fura ssi, zanma iya cemaku shi DEEDART yabiyo dasan abincin gargajiya musamman na yarensu fulani.

Bayan dady yasha fura sannan yagyara zamansa yana fuskantar Abba yafara magana kamar haka "mallam ja'ey, nasan baka shaidaniba, amma dikda haka ka karramani tamkar wonda kasani" Abba yai murmushi sannan yace "ai karrama bak'o Sunnah ce taanzon tsira, annabi dakansa yace ku karrama bak'inku, bak'onka kuma annabinka" dady yace "hakane".

Saiya cigaba da magana "to mallam ja'ey, nidai sunana Alhj Bukar maccid'o shugaban kotin duniya, mahaifi ga AHMARD DEEDART wato mahaifin jikarka jawahir kena".

Dajin abunda yafada dasauri Abba yad'ago yakallesa, yanayin fuskarsa yacanja, dik annuri da fara'a dake fuskarsa suka kau, dady yacigaba da magana,

    "Mallam ja'ey, yau gani a gabanka nazo amatsayina na Bukar maccid'o, nazo neman alfarma agareka" batareda yakallesa ba yace "woce alfarma ce, kayi sauri kafad'a sbd inada abunyi agabana" 

Dady yakallesa sannan yacigaba da fad'in "nasani tabbas DEEDART bai kyauta makuba, akan abunda yamaku, nasani tabbas ya aikata babban laifi wonda mafi yawan zukata basu yafewa, amma dan Allah...dan Allah mallam ja'ey kutaimaka kuyafewa DEEDART abunda yamaku,

Ahalin yanxu AHMARD yana buk'atar taimakonka, sbd yana a cikin mawuyacin hali, wonda zai iya rasa rayuwarsa a Koda yaushe, kuma hakan tafarune a sanadin y'arka  Madina,

AHMARD yakamu da matsanancin son Madina wonda na tabbatarda hak'k'in y'arkan kune kebinsa, son yarka Madina yana nema yasa yarasa ransa, sbd taki tayafemasa abunda yamata barehar ta amince da soyayyarsa agareta, 
   Hakan yasa nazo gareka tinda Kaine mahaifin ta, kataimaka dan Allah badan halinsa ba kabata hak'uri ta amince ta auresa takuma yafemasa abunda yamata a baya, ubangijinmu ma muna masa laifi kuma rokesa ya yafemana, bare kuma mutum,

Dan Allah mallam ja'ey kataimaka, wlh DEEDART zai iya rasa ransa, dan ahalin yanzu ma anacan anamasa aiki a zuciya, aman jini yake wonda yawan tinani da damuwar kin amince masa da tai yajanyo masa shi, likitoci kuma sunce Koda anmasa aikin matukar baisamu abunda zuciyarsa takeso ba, to aikin bazaiyi woni tasiri ba".

    Saiya ciro woyarsa yakira video call da deen yatambayesa idan anfito da DEEDART, nan yafad'a masa anfito dashi harma ankaisa d'akin hutu, sai dady yace yanunomasa shi,

Nan deen yakai woyar yanunamasa DEEDART yana a kwonce sanye da kayan aiki oxygen yana a hancinsa yanata bacci, Karin jini na makale a hanunsa, gaba d'aya yarame yacanja kamar bashi bane Mr AHMARD DEEDART.

Shuru Abba yai qwalla nazuba daga idanuwon sa, can yad'ago yashare kwollan sannan yace "uhm...Alhj kenan, shys wonnan k'asar tamu ta Nigeria tsk'i cigaba sbd rashin adalci, a baya sbd y'ata batada gata akaci zarafinta, akamana cin mutunci mara misaltuwa, dik sbd rashin gata sbd ni mahaifinsu bakowa bane a k'asar face talaka manomi kuma makiyayi, 

Mutane sunkasa gane cewa "Allah Mai iko ne akan komai, to yanxu gashi, DEEDART yamanta dacewa Allah shine ke bada arziki gawonda yaso sannan yabar talauci ga wonda yaso bakuma dan bayason d'ayan bane yasa yayisa a talakaba, 

Story continues below

DEEDART yamana abunda har mutuwa bazamu tab'a mantawa dashi ba, woni abu dabaka saniba Alhj shine, Madina ba'ita ce DEEDART yayiwa fyad'e ba, bakuma itace mahaifiyar jawahir ba, y'ar uworta ce MUNAWARAH kasancewor su tagwaye ne kuma masu kamanceceniya da juna, hakan yasa taboyewa duniya cewa ba'itace abun yafaru da'ita ba domin taji saukin d'aukan fansa,

Y'ata jaruma ce, jajirtacciya, mara tsoro, macece amma tamkar maza shida nake ganinta, 

     Saidai dik abunda Ahmard yayi, bazai hana a yafemasa ba, tinda shi ajizine, wonnan abun daya faru kuma k'addara ce, nidai nayafemasa wlh Allah kuma yabashi lfy, insha Allah kuma gobe zanje gun Madina kuma insha Allah itama zata yafemasa,
    
        .....Sai batun aure kuma, kafad'a masa ya kwontar da hankalinsa, yanxu takaba takeyi na mijinta daya rasu, idan tagama zankirasa da Kai saimuyi magana" woni irin farinciki ya lullub'e dady, baisan lkcnda yataso yazo yarungume Abba ba yanata masa gdy kamar zai had'iyesa.

Abba yai murmushi yace bakomai,

Kud'i mak'udai dady yaciro a jaka yabama Abba, Abba yace bazai karb'a ba, dakyar dady yasamu yakarb'a sannan yak'ara masa gdy suka fito atare yamasa rakiya kofar gida,

Nan dady yashiga mota sannan suka fice.

      A daren ranar dady yahau flyt yakoma habuja sbd halinda yabar d'an sa bazai iya kwonciyaba batareda yaga halinda yake ciki ba da idonsa.
   _______________________

Washe gari around 12pm Abba yakama hanyar garin birnin kebbi izowa gun y'arsa Madina,
      Sai kusan 12:30pm sannan suka iso birnin kebbi, Kai tsaye yahau a daidaita sahu domin k'arisawa gidan.

Yana isa Madina tadinga farinciki tana murna kamar tagoyesa dan farinciki, nan tasaka mai aikinta tahado masa ferfesun kayan ciki da kayan fruit's kala kala, sbd tasan Abban nata yanasan y'ayan itatuwa ssi,

Dakanta tazauna tazuba masa ferfesun yasha sannan tadinga yankamasa fruit's d'in yanasha suna fira, fira suke ssi cikin farinciki da k'auna irin ta uba da y'arsa.

Can sunacikin fira sai Abba yace "woi nikam ina amaryata ne, ko sunje makaranta ne ?naji gidan shuru banji hayaniyarta ba, batakuma zo takawo gaisuwa ba" murmushi Madina tai sannan tace "wlh jiya ne kakarta tazo tarok'eni akan nabata ita ta tafi da'ita tamata kwana biyu, badan nasoba wlh Abba nabata ita, sbd yanzu kokad'an banasan jawahir tai nisa dani, tareda Fatima suka tafi sbd nafada mata kwana biyu kacal zasuyi sudawo".

Murmushi Abba yai sannan yace "ai hakan nada kyau Madina, kinga koba komai zatasan danginta dama sauran y'an uwanta, sannan zatasan mahaifinta takuma shak'u dashi, dama nima nazone domin muyi wata magana mai matukar muhimman ci".

Kallonsa take sai tace "woce irin magana Abba na" gyara zamansa yai sannan yacigaba da fad'in "Madina inaso kiyiwa maganata kyakkyawor fahimta, dik abunda kikaji zan fad'a to kimasa kyakkyawor fahimta dan Allah" gyada masa Kai tai sai yacigaba da magana,

"Jiya ne Alhj bukar mahaifin wonnan yaron DEEDART wato kakan ita jawahir kenan yaje can Raha yasameni, yabani hkr ssi akan abunda yafaru a baya sannan kuma yafad'a man wota magana wocca tarazanani matuka, ta d'agaman hankali" yana fara wonnan maganar tafahimci abunda yake fad'a,

   Cigaba yai da magana "Madina yasanardani cewa DEEDART yana cikin woni mawuyacin hali wonda yake gab daya rasa rayuworsa, 

     .....Dan Allah Madina narok'eki kiyi hkr kiyafewa wonnan yaron abunda yamaki kinji ko y'ata, yayi nadamar abunda ya aikata a baya, yatuba yanxu dik yadaina aikata abunda yakeyi a baya, hakan dikta farune a sanadin matsanancin son ki daya kamu dashi, 

Madina kitaimakawa wonnan yaron kiyafemasa sannan ki amince ki auresa kinji y'ata, a yanzu haka anmasa aiki a zuciya sbd  yawan aman jini dayakeyi yasa har zuciyarsa ta tabu, gakuma hawan jini daya kamasa dik akan sonki Madina, kink'i ki yafemasa bare harki amince da soyayyarsa,

Story continues below

Haba Madina, Allah mafa muna masa laifi kuma murok'esa ya yafe mana, bare kuma mu yay'an Adam, annabi ma yace assabru siya'u hak'uri haske ne, dik Mai hak'uri tabbas bazai tab'a tabewaba zaiga haske, habadai y'ata kada kibari shaid'an yai galaba akanki mana, yanxu kodon wonnan shiryuwar dayai akanki bazaki iya yafemasa ba sannan kijanyosa ajikinki kikuma bashi cikekkiyar kulawa sbd karya sake komawa akan rayuworsa ta baya,

Idan kikayi hakan kinsan adadin yay'a matanda kika taimaka kika ceci rayuworsu daga fadawa hanyarda y'ar uwarki tafad'a, matukar kika auri DEEDART to natabbata zaibar mummunar sana'arda yakeyi har abada tinda gashi tinma kan ki amince din yadaina,

Sannan Madina kiduba rayuwor yarki mana, matukar kukai rayuwa ba'a tare da mahaifinta ba to tabbas babu abunda zai hana duniya tasan wacece ita, amma matukar kika amince kika auresa, bakowane zai San asalinta ba, kiyi tinani akai kinji y'ata, kikumayi tinani Mai kyau,

Sbd ahalin yanxu AHMARD DEEDART yana buk'atar taimakonki, a Koda yaushe zai iya rasa rayuwarsa kuma asaboda ke" tinda yafara magana take sharan kwollah har yanzu,

Wosu zafafan kwolla tashare masu zafin gaske, tabbas bazata tab'a iyayin musu da mahaifinta ba sbd shine komai nata, tana matukar sansa fiye da rayuworta, a duniya shine mutum kadai wonda ranta zai iya zama fansar nasa ran, to dagashi saikuma farincikinta jawahir, kamar yanda take kiranta kenan "My happiness".

Ahankali tashare kwollan da majina sannan tafara magana kanta yana k'asa tace "Alhmdllh...naji d'adi ssi da Allah yasa DEEDART yasan matsayi da muhimmanci dakuma darajar y'a mace, a da yad'auki mace tamkar rigar sakawansa, yau yasaka wonnan gobe kuma yacanja yasaka woccan, yanzu kuma yasan tabbas mace tanada daraja da k'ima,

Nagode Allah dayasa yagane haka, Abba na, bazan tab'a iyayin musu dakaiba, dikda cewa maganarda kaxoman da'ita tanada nauyi ssi agareni, dikda kuma zuciyata tatsani Koda Mai irin sunan DEEDART ne, amma hakan bazai hana namaka biyayya ba na amince abunda kazoman dashi,

A baya zuciyata tamasa bak'ar tsana amma a yanzu tasakko, zan amince da buk'atarka Abba na, amma wlh darajarka yaci, badan kaiba wlh koma waye yazo bazan tab'a amincewa na auresa ba, 
         Shikenan Abba na, nayafemasa nahak'ura kuma na amince da aurensa bisa abubuwanda kafada, sbd banasan jawahir ta tashi acikin tsangwama da kyarar mutane, sannan banasan wota y'a mace tashiga irin halinda y'ar uwata tashiga ba, na amince Abb....a...na" tak'arisa tareda fashewa da woni irin kuka maiban tausayi Mai tsuma zuciyar Mai karatu.

Numfashi Abba yasauke nannauya sannan yace "Allah yamaki albarka Madina, a Koda yaushe ina alfahari dake amatsayin y'ata, kuma insha Allah saikinga haske acikin rayuwar ki dakuma rayuwar aurenki, hasken alkhairi zai cigaba da bibiyar rayuwarki har aljannah insha Allah, Allah yamaki albarka" ta amsa da ameen tana share kwolla.

Nantake yaciro woyarsa yakira layin dadyn DEEDART, bayan sungaisa nan yake fad'amasa jibi yazo yanaso zasuyi magana, dady ya amsa masa da to, Nan Abba yatambayi Mai jiki dady yace Alhmdllh daganan sukai sallama,

Bayan sunyi sallama shima yamike yamata sallama zai koma gida, kud'i tabashi da kayan abinci sannan tahadasa da driver d'inta domin yakaisa har gida, daganan tamasa rayika har bakin gate suna fira yanakuma kara mata nasiha akan hak'uri dakuma yafiya, 

Bayan sungama sannan yashiga suka fice.
   .....................

Kamar yanda Abba yafad'awa dadyn DEEDART haka kowa takasance, 
       Washe gari around 3pm bayan anfito daga sallar juma'a suka isa garin Raha, bayan karamci da Abba yasaka aka masu sannan suka zauna acikin palornsa sukai magana akan Madina da DEEDART,

Abba ya tabbatarmasu Madina tahak'ura tayafewa DEEDART sannan ta amince zata auresa, Saidai yanzu tana takabar tsohon mijinta, idan tagama saisuzo ayi baiko akuma saka rana,  

Dady yaji d'adi sosai kamar yarungume Abba sbd tsabar farinciki.

Sai kusan 5pm bayan sunyi sallar la'asar atare sannan sukama garin Raha bankwana, sukabar garin cike da tarin farinciki,
    Tin akan hanya dady yakira waya yasanarda momy, nan itama tafadawa DEEDART, dan farinciki Saida yazubda kwollan farinciki sannan yad'aga hanunsa sama yayiwa Allah gdy farinciki dikya mamaye zuciyarsa nantake fara'a ta bayyana a fuskarsa, annuri da haske dakuma tsintsar nishadi da farinciki wonda baitab'a jin irinsaba suka mamaye zuciyarsa da fuskarsa.

           .... Around 4:35pm Madina na kwonce kan gado sanye da hijab dakuma carbi a hanunta, ba bacci takeba lazimi takeyi, saiga jiddah tashigo cikin sallama sannan tagaidata itakuma ta amsa saitace,
     "Aunty kinyi bak'o, yana a parlor" cikin mamaki ta tashi zaune sannan tace "bak'o kuma, a wonnan lkcn, waye?" sai jiddah tace "wlh bansanshiba, amma daalama Mai gadi yasansa dan naga yanda suke magana daalama sunsan juna".

Ok... tafad'a sannan tace "kije kicemasa ina zowa" saita amsa da to sannan tafita.

Itama tashi tai tagyara hijab dinta sannan tafice.

A zaune ta taddasa kan kujera balkisu d'ayar kanworta takawo masa drink's agabansa kan center table, ahankali takariso cikin sallama sannan tazauna, cikin fara'a ya amsa sallamar sannan yamata barka da wuni,

Itama cikin sakin fuska ta amsa masa sannan tace "Saidai banshaida fuskarba" d'an murmushi yai sannan yace "hakane, ni sunana Abbas k'ane agun DEEDÀRT, dama nazone domin nahad'aki dashi ta woya dazun yakirani ina gwondu yace dan Allah nazo nakawo maki woya yanaso kuyi magana" batace komaiba tajuya fuskarta tana kallon woni gu daban.

Abbas kowa ciro woyarsa yai yakira video call ta woyar deen, Jim kadan aka d'aga yai sallama Deen ya amsa sannan yajuya woyar izowa gunta,

Ahankali tad'ago saitai tozali dashi a kwonce kan gado, hancinsa sanye da oxygen yasaka hanunsa d'aya yana k'okarin cire oxygen d'in, yana cirewa yajuyo ya kalleta taredayin murmushi ai batasan lkcnda kuka yakufce mataba sbd ganin yanda DEEDÀRT yazama ba, dasauri tasaka hanunta tatoshe bakin sbd kada kukan yafito woje.

Cikin muryansa ta marasa lfy yafara magana yana murmushi "Madina naga sak'onki ga dady na, nagode ssi da taimakonda kikaman Nagode ssi da ceton rayuwata dakikayi, dikda nasan kinyi hakan ne sbd biyayya, amma hakan bazai hana ngd makiba, ngd ssi Allah yasaka maki da mafificin alkhairi, insha Allah kuma zaki sameni kamar yanda kikeda burin mijinki na aure yakasance" yana kawowa nan saiyai shuru yana kallonta,
      Ahankali tad'ago itama takallesa tace,

"Matukar kanasan ka kasance kamar yanda nakeda burin mijin aure na yakasance to kacika woennan sharud'an, matukar kacikasu to tabbas zaka sami cikekkiyar soyayyata, dikda nasan yanada wohala kamin zuciyata tasaba dakai takuma karb'eka harta amince dakai takuma fara sonka, amma dai nasan matukar kacika woennan sharud'an to ahankali zaka fara samun soyayya".

"Woenne sharud'a ne...?" yajefa mata tambayar, ahankali tace "inada burin mijina yakasance soja, Mai cin halaliyarsa maikuma kaucewa haram a dik inda yagansa, Mai kaunar talakawa sannan Mai tausayin mata dakuma nakasa dashi, Mai Sona Mai kuma San ahalina, matukar ka kasance haka to watak'il zaka iya samun soyayyata" d'an murmushi yai sannan yace "indai wonnan insha Allah zaki sameni ahaka, fatana kawoi zaki karbeni hanu biyu amatsayin mijin aurenki".

       "Insha Allah, kodon nasamu aljannah ta" saiyai murmushi dajin hakan, 
    "Ina y'ata...?" tajefa masa tambayar, cikin fara'a yace "tana gida gun momy, gobe insha Allah zasu dawo gunki, sai anjima ko" bata amsa ba saima kauda kanta datai daga kallonsa,

 Abbas yajuyo da woyar yakatse Kiran sannan yacemata "toh...ni zan koma sbd naga dare yanayi" to kawoi taiya cemasa saiya tashi yafice itakuma takoma ciki...

Kamar yanda DEEDÀRT yafad'a mata kowa hakan takasance, washe gari around 2:30pm deen da momy sukayowa su jawahir rakiya har gida, Madina taji d'adin hakan da momy saima tafarajin kunyar momyn.

Liyafa tamusamman Madina tasa akamasu, atare dasu momyn sukaci suka sha sukai hani'an, 4pm bayan sunyi sallar la'asar sukamasu bankwana suka fice,
      A d'an zamanda jawahir tai ataredasu kowa Alhmdllh tafara sanin su momy hartadan fara sabawa dasu, washe gari kuma suka koma school.
   _______________________

Sannu ahankali rayuwa tacigaba da tafiya, inda Madina takammala takabar mijinta Dr Ismail, bayan sungama takabar sai aka raba gadonsa akabaiwa magada, Madina tasamu mak'udan kud'i da mota d'aya dakuma wosu k'adarorin,

Bayan anbata nata saita biyawa kanta da jawahir dakuma abban ta umrah suka tafi atare.
     ........................

Alhmdllh DEEDÀRT yaworke daga jinyarda yai, kuma Alhmdllh nasara tasamu dan ya murmure ssi yaworke sarai harda y'ar k'iba yai, Saida yai 1month cif sannan aka sallamesa daga hospital, bayan yakoma gida kuma akacigaba da kula dashi cikin kulawa.

Madina suna wojen gudanarda umrah DEEDÀRT yacike form d'in soja harya tafi shi dakuma Saif babban amininsa kuma yaronsa dan duniya bashida amininda yakai saif, 
            ....Saif yasan komai nasa, yariga yasaba dashi danhaka yanzuma bazai iya tafiya wonnan aikinba batareda shi ba.

Bayanda momy bataiba akan karya tafi wonnan aikin na sojohn tace "haba DEEDÀRT, dika dika yaushe ne  kasakko daga kan gadon asibiti dahar zaka cike form d'in soja harka tafi, kokamanta likitoci sunce kana bukatar hutu kuma kadayi woni aiki na k'arfi ssi, sbd d'inkinda akamaka acikin jiki, haba DEEDÀRT kada soyayya tarufema ido kaje ka illata kanka".

Cikin fara'a yacemata "momy na, indai akan Madina ne, to Koda zan rasa rayuwata ne tinda tace tanasan wonnan soja d'in, to yazama dole kowa agareni naje nazama soja kodon nafaranta mata nakumayi k'okarin cusa soyayyata acikin zuciyarta, sbd haka ki kwontarda hankalinki, insha Allah ma babu abunda zai faru, zanje cikin aminci nakuma dawo cikin fara'a".

Bayanda taiya badan tasoba dole tabarsa sbd taga giyar soyayya nad'ibansa yakumayi nisa acikinta bayajin kira, haka tabarsa ya tattara kayansa ranar asabar da safe suka fice.

Yaso yakira Madina lkcnda zasu fice amma ina bashida contact dinta, haka yatafi batareda yagantaba kokuma sunyi woya,
         Yatafi soja ne da zimmar daya dawo sai ayi bikinsu shi da Madina abar k'aunarsa.

Bayan sati biyu da tafiyarsu su Madina suka dawo gida Nigeria, itakama tini tama manta da labarinsa sai sabgoginta takeyi da y'arta dan zowanda ma tayi can saudiya umrah harda kayan siyarwa tasiyo, gadaje dakuma kayan d'aki da bedsheets kala kala masu kyau,

Saidai momy kam dik kusan bayan kwana biyu ko uku takan Kira su gaisa sannan tayi woya da y'ar jikarta, sannan dik bayan d'an lkc takan aikowa da jawahir kud'i, dakuma kayan amfani na rayuwa, dakuma kayan wasa kala kala na yara mata, hakan kowa bak'aramin d'adi yakewa Madina ba,

     Sbd dik Mai San jawahir to itama masoyinta ne, dan jawahir itace farincikin ta.
   _______________________

Ahankali rayuwa tacigaba da gudana cikin jin d'adi dakuma farinciki, Madina tini takoma bakin aiki, hakama jawahir takoma school, su maijiddah ma sunkoma school suna cigaba da karatinsu, danhaka yanxu rayuworsu suke cikin jin d'adi dakuma wolwola, Madina yanxu babu abunda ke damunta.

Bikin chuchu yazo danhaka suka zage dantse akasha buduri da chasu, mijinta barrister Sadiq d'an asalin garin jihar adamawa ne, aikine yakawo mahaifinsa garin kebbi har suka zama yan gari, 

Story continues below

Sun had'une a lkcnda aka kawo kanworsa hospital dinsu, to anan suka hadu har suka san juna suka kuma fara kaunar junansu, yanzu kuma har Allah yakawomu lkc,
         1st may 2019 around 12pm dot aka d'aura auren Dr fatima da barrister Sadiq akan sadaki mafi tsoka 100k,

Da dare around 10pm aka fice izowa dinner, sai kusan 2am sannan aka gama kowa ya watse, su jawahir ma gida suka fice Madina kowa Saida sukama amarya rakiya gidanta dake unguwar gesse phess 1 sannan sukuma suka fice.

Cikin farinciki akai biki lfy aka watse lfy kowa yakama gabansa.

Madina da cool susi ssukaci gaba da kula da hospital kamin chuchu tagama cin amarci tadawo.

 _*BAYAN WONI LOKACI....*_

Yau takasance Saturday weekend danhaka kowa na gida amma banda ita, itakama Saida taje hospital taduba patient dinta 12pm sannan tadawo gida.

Koda tadawo jawahir na a kwonce tana birgima tana kuka, woi dole sai anbata wuka tayanka cabaje, dasauri taje tad'auketa tana fad'in "Kai..Kai..Kai, waya tabaman my happiness, waye yanzu nabulaleshi" cikin shagab'a da muryan nan tata Mai shegen zak'i kamar ta gyatumarta tace "Adda jiddah ce, woi bazata baniba nayanka cabaje" tak'arisa tana shagwab'e baki.

Cikin Shan kunu tafara kwollawa jiddah Kira, tana zowa saitace "meyasa kikak'i bama my happiness wuk'a ta tayaki aiki, kodan kinsan tana yanka mutane ne woenda basu iya aiki da'ita bane, to daga yau karki sake barin wuka a woje har shalelena tagani, kinji ko karta d'auka wuk'ar tayankata" cikin murmushi tace,

      "To add Madina" sannan tamata sannu da zowa tareda karb'an kayanda tashigo dasu, itakowa chocolate d'inda tasiyowa farincikinta ce tashiga bare mata tareda zama akan kujera,

Bayan tabare mata sannan suka fice izowa cikin bedroom d'inta,
       Wonka tai tacanja kaya izowa wandon jeans gajere iya guiwa da t-shirt pink, sai hula bak'a.

Bayan tagama Shirin saisuka fita izowa filin wasa inda suke motsa jiki, Nan suka shiga motsa jiki atare ita da farincikinta wato jawahir.

Sund'an jima sunayi kamin daga bisani suka koma ciki,
    Bayan sunkoma suka sakeyin wonka suka canja kaya, Madina tasaka gown ta atampa jawahir kuma woni wando da riga da rigan sanyi sbd yanayine na damina ana d'an sanyi.

Bayan sun shirya sannan suka fita atare da jiddah izowa Azbir Arena domin shakatawa sukuma sha ice-cream, sunjima ssi acan jawahir tahau shilo tai wasa sukasha picture's cikin farinciki daga bisani suka fice gidan chuchu,

Acan gidan chuchu sukai sallar magrib sannan suka koma gida.

      Washe gari ma bayan tagama duba patient d'inta tadawo gida suka shirya suka fice Raha, acan suka wuni sai maraice sannan suka dawo gida birnin kebbi,

Ahankali kuma shak'uwa tacigaba da shiga a tsakanin momy da jikarta jawahir, dan dik kusan kwana biyu saita kira sunsha fira, DEEDÀRT kowa har yanzu bata tab'a woya dashiba dan Madina ko number nashi batada.

Haka rayuwa mai cike da jin d'adi tacigaba da gudana acikin wonnan ahalin, dik bayan kwana biyu sukanje Raha su wuni sbd yanayin aikin Madina yasa basa kwana gakuma karatin su jawahir amma idan sunyi hutu sukanje can suyi hutun.

A yanzu jawahir tana primary 3 a shekarunta kuma tana gab da cika shekara shida, hakan yasa Madina tafara shirye shiryen had'amata gagarumar liyafa.


        .....Zaune suke acikin parlon chuchu su dika ukun, Madina chuchu Cool susi, fira suke a tsakaninsu chuchu nad'auke da matashin cikinta wonda yakai kimanin wata biyar,

Firar duniya suke had'e da firar shagalin bikin cool susi dayaketa matsowa, yanayin firarne yajanyo firar DEEDÀRT inda chuchu tace "woi..nikam ormme jawahir, yah labarin dadyn jawahir ne, munji shuru" d'an murmushi Madina tai sannan tace,

Story continues below

"Uhm...najefashi can wota uwa duniya, cemasa nai matukar yanaso yasami soyayyata to saiyazama soja, ai dagangan nafad'a masa haka, dan wlh badan darajan biyayya ba, wlh dabazan iya aurensa ba, kinga yanzu idan Allah yabani mijina kamin yadawo daga sojan sai nayi aurena, wotak'il ma harda new baby" tak'arisa tareda rufe fuskarta da tafukan hannayenta tana dariya.

Sumadin dariyar suka kyalkyale daita cool susi tace "bakida dama y'ar uwata, wlh bakida dama, yanzu wato dasaninki kika turasa soja ko, Allah sarki Mr. CONEL AHMARD DEEDÀRT, Allah i bada sa'a, Saidai mukam kamin kadawo munzama mommy's" tafad'a cikin tsokana tana kyalkyale wa da dariya, Nan suma suka sake kyalkyale wa da dariyar.

Haka suka cigaba da firar inda firar tayau takasance gaba d'aya ta DEEDÀRT ce, around 4pm bayan sunyi salla sunci abinci sannan sukama chuchu sallama suka fice, Madina tai dropping cool susi gida sannan tafice kasancewor yanzu tana driving dakanta idan bawota babbar fita bace, idan kuma babbar fitace dole driver yajata.
     ..................

Zaune suke acikin main palor sudika kowacce sanye da kayan sanyi ajikinta sbd yanzu aka gama ruwa garin yadau sanyi ssi,
    Gyad'a sukeci kuma suna kallon tashar Zeeworld inda ake haska film d'in marriage again, daalama sunajin d'adin kallon,

Around 10pm dot aka Kashe kallon kowa yafice domin kwonciya, Nan Madina tad'auki jawahir datai bacci tafice izowa bedroom d'in jawahir, bayan ta kwontarda ita tatofeta da addu'oi naneman tsari da kariya, daga bisani ta kwonta a gefenta itama tai addu'oin dan yau tanasan kwonciya tareda y'ar tata,

Ahankali takashe fitilar d'akin sannan tajanyo blanket tarufesu dashi, nantake itama baccin yad'auketa.


          ......Kwokkonce suke kuma a b'oye daga mab'uya acikin filin daga, adadin yawonsu yanada yowa ssi kuma dikansu sanye suke acikin kayan sojoji, dika shigar ta soja kuma ta yaki itace a jikinsu, d'auki ba dad'i suke a tsakaninsu da abokanan fad'an nasu su suharb'osu da bindiga suma kuma su harbesu da bindigogin,
        Yana a kwonce daganan yake harbawa yana kashe abokanan fafatawar ma'ana enemies, yayinda d'ayan gefensa na dama yakeda mutune biyu hakama dayan side d'in akwoi mutane hud'u.

Cigaba da harbi suke hakama cigaba da aiko masu Harbin ake, can ana cikin Harbin sai aka harbi daya daga cikin abokanansa sojo nantake yafad'i matacce.

Dasauri yad'aga domin yaje gun mutumin cikin rashin sa'a shima aka harbomasa nasa bullet d'in, dak'arfi kuma cikin jin radadi da zafin Harbin yai wota iriyar k'ara Mai sauti sannan yazube anan k'asa wonnan,
       A daidai lkcnda yai karar a daidai lkcn ne itama tai k'ara mai sauti tareda farkawa daga nannauyan baccinda takeyi har tai wonnan mafalkin, had'e da kuma ambaton sunan "DEEDAAARRTTTT......" sannan tabud'e idanuwon nata, nantake tashiga waige waige tanaso ta tabbatarda mafalkine ba gaske bane.

Mitsirtsika idanuwonta tashigayi, Saida ta tabbatarda mafalkin ne tabbas sannan tai zaune tareda rafka uban tagumi tana nazari akan wonnan mafalkin.

Can dakyar tasamu takwonta amma bacci yaki zowa, baccin gaba daya k'auracewa idanuwonta yai, har safiya tawaye bata sake bacci ba.

Tajima ssi tana nazari akan wonnan mafalkin dayake tab'a mata kashi da tsoka na jiki dakuma zuciyarta.
      Acikin satin gaba daya haka tayisa ba wolwala takuma kasa fahimtar abunda yasa takasa samun nutsuwa tin bayanda tai wonnan mummunan mafalkin akan DEEDÀRT.
   ...................

Zaune take acikin office d'inta tana rubuce rubuce akan wosu file's, ahankali kuma tana kurb'an coffee,

Can saiga cool Susi tashigo sanye da uniform na aiki jikinta alamar yanzu tafito daga operation tana cire hand gloves a hanunta, kallonta Madina tai tace "sai yanzu kuka fito?" tace "Eh..wlh, aikinne yad'an bamu wohala" tafad'a tana zama kan kujera,

Story continues below

Bayan tagama cire kayan jikinta saita mayarda ainahin kayanta, bayan tagama sannan tace "so nake naje nad'akko jawahir a school, lkcn tashinsu yayi naga kuma kinada aiki ssi" batareda tama d'agoba tana cigaba da aiki tace "Ok..adawo lfy" tace Aha...tana ficewa daga office d'in.

Bayan tad'akko anan hospital d'in tazo daita sbd lkcn tashinsu baiyiba, 
     Sai 5pm dot sannan Madina tagama aikinta sannan suka fice gida, Koda suka isa Abban Madina yazo yana jiranta,

Aikwa farinciki saiya mamaye zuciyarta naganin mahaifinta datai, Abba gaba daya yacanja, yai k'iba hadda ciki yai sbd tsabar wodata da kwonciyar hankali daya samu, ainahin fari da hasken fatarsa daya b'ace a da, yanzu dikya dawo, yai k'iba ssi,

Nanfa aka hade dasu jiddah suka dawo daga school, atare suka dinner cike da farinciki, anacin abincin ana fira ana raha da barkwonci, bayan sungama ma parlor suka koma akacigaba da shan firar, sai kusan 11pm sannan kowa yaje ya kwonta, asuba tagari.
     ......................

Haka rayuwa tacigaba da tafiya ahankali cikin jin d'adi dakuma kwonciyar hankali da farinciki.

     Ranar 1st May shine ranar birthday d'in jawahir, shine ranarda zata cika 6yrs, 
       Yau kuma kwana daya kacal yarage ranar birthday d'in tazo.

Danhaka Madina sai shirye shiryen zowan ranar take, kud'i masu yowa tacire tadinga siyan kayan celebration d'in.

Gaba daya gidan nasu anzagayesa da balloon's da flowers kala kala, dakuma gloves masu fitarda kyalli, hakama harabar gidan ancikata da tsarin kujeru kala kala da wojajen wasan yara, jawahir kowa tahada mata kayan sakawa namusamman masu tsadar gaske,

Pink color aka had'amata komai nata is Pink.
    ...............

Washe gari kowa tin 10am aka fara shirye shiryen shagali, girke girken snacks da had'in cake dakuma drinks different colors gasunan anayi, wasunsu kuma ordering nasu tai daga restaurant, sweet kowa ba'amaganar yawonsu, gasunan birjit ansiyo.

Koda 3pm tai tini ankammala komai lkc kawoi ake jira, kasancewor by 4pm ne zaayi shagalin.
       Madina dakanta tashirya y'arta cikin shiga Mai tsada dakuma kyan gaske, rigace gown Pink Mai stones agabanta da flowers iya guiwa, sannan ta tufke mata sunarta da rivom pink sumar tabazo har gadon bayanta tana kyalli sbd gyaranda tasha, takalmanta Hill's suma Pink color masu kyau.

A bayanta ansanya mata botterfly ta roba fara may kyalli ajikinta, fuka fukan suna motsi kamar nagaske, a kanta kuma andoramata crown akanta tadawo sarauniya.

Powder da janbaki red tashafa mata sannan tasa mata kwolli, nantake ainahin kyan yarinyar ya bayyana, dakuma tsintsar kamanninta da mahaifinta, Madina na kallonta tai murmushi sbd tsabar kamannin DEEDÀRT datagani b'arau b'arau a fuskar jawahir, bayan tagama sannan tafesheta da tirare, Nan itakuma tashiga shiri,
        Nantake tashirya tsab acikin wota tsadajjiyar abaya Mai kyan gaske red color wocca tasiyo a umran da sukaje, bayan tasaka rigar sannan tai rolling da veal na rigar bak'i, itama powder da janbaki red tashafa sannan tashafa kwolli.

Bayan tagama sannan tariko hanun jawahir suka fita.

Abun mamaki Koda suka fito saisuka tadda momy da dady dakuma Deen da Neehash da meehash dakuma Abbas zaune acikin palor, aikwa jawahir naganinsu dagudu taje gun dady tana dariya da farincikin ganinsa nan yadauketa yai sama da'ita cikin farinciki yana fad'in "oyoyo my amarya na, I miss you so much" Madina ma cikin fara'a taje tagaidasu cikin girmamawa da tsintsar ladabi.

Neehash dasu abbas nan suma suka shiga gaidata cikin fara'a sannan suka bama jawahir gift d'inta dasukazo mata dashi na Happy birthday d'in, Madina tacemata "to bazakiyi godiya ba" cikin dariya tace,
      "Thanks" tana kallon dady, hancinta yaja yace "kinwuce haka agaremu amaryata" saita sakeyin dariya, momy kallonta take sbd gaba daya komai na jawahir gani take irin na DEEDÀRT ne, musamman shima sadda yana k'arami kamar jawahir.


       ....4pm dot kowa ya hallara, kawayen jawahir na school dik sunxo tareda iyayensu, hakama Aunty's dinsu na school wato teacher's d'insu sunzo, gidan dai yacika sai shagali akeyi, ganin kowa ya hallara yasa aka fara gudanarda abun.

Firstly akafara da yanka cake ana mata tafi had'e da wak'ar "happy birthday to you, Happy birthday to you...." bayan tayanka saita dibo tabama Madina a baki sannan deen yad'aga ta takaiwa dady a baki, nan itama momy tskaimata abaki da dai sauran mutanen.

Madina itama diba tai takaimata a baki sannan talakuta matashi a tsinin hancin, shima dady d'iba yai yslakuta mata a kunce, haka dai akaitayi ana farinciki, chuchu bata sami xowa ba sbd tayi nauyi, amma cool susi da sauran doctors kawayensu sunxo.

Bayan angama da yanka cake sannan mutane suka shiga bama jawahir gifts, bayan angama da wonnan  sashin sannan  akabamayara lkc sukai wasanni daban daban kala kala, daganan kuma akaci abinci akasha drinks aka kuma ci cake da snacks.
   5pm su dady sukamasu sallama suka fice, sai kusan 6pm sannan aka gama komai kowa ya watse.
   _______________________

Rayuwa tacigaba da tafiya, cikin tsintsar farinciki da wolwala.
      Wota ranar Saturday around 8pm Kiran mijin chuchu yashigo woyar Madina, bayan tad'aga suka gaisa sannan yacemata "dan Allah kizo gida Fatima batada, gatacan a kwonce d'aki" tanajin haka cikin sauri takammala aikinda take saura kuma tabarwa doctor shamsiya tafice,

Cikin sauri taisa tai parking, Koda tashiga saita tadda nak'uda ce, danhaka tashiga aikinta,
        Cikin ikon ubangiji batawoni jimaba tana nak'uda tasantalo kyakkyawan baby boy d'inta fari tas mai kama da mahaifinsa..

Post a Comment for "CONEL AHMARD CHAPTER 4"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...