Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

CONEL AHMARD CHAPTER 2

CONEL AHMARD CHAPTER 2

- - Post a Comment
CONEL AHMARD
CHAPTER 2Ba Abban MADINAH kad'ai ba, hatta su chuchu hankullan su suntashi matuka, gaba d'aya sun rikice da wonnan tashin hankalin daya faru a yanzu,

Abba fadar yake "innalillahi wa'inna ilaihi rajiun....hazbiyallahu wani'imal wakiil.... innalillahi wa'inna ilaihi rajiun" kwollah kuma na zubar masa masu zafin gaske,

😭 Nima kaina reader's saida nadan zubda kwollah, wayyo Allah MADINAH, duniya tamaki k'unci, ba y'ar uwa kuma ba mahaifiya, gsky dole ki dimauce, Allah yabaki hak'uri da juriyar rashi ameen. 👏

Da ita da chuchu bansan wonda yafi kukaba dan itama chuchu har ciccika takeyi kamar wocca aka doka,
Hakama momyn chuchu da Abban ta saida suka zubda kwollan tausayi, momyn chuchu tazo tarungume MADINAH tana rarrashinta tana fad'in,

"Kidaina fad'in haka MADINAH, wonnan harabawa ce daga mahalicin ki sbd haka ki karbeta hanu bibbiyu domin kiyi kokari ki cinyeta, kuma ki daina kuka MUNAWARAH da Inna sun tafi har abada bazasu sake dawowaba, kawoi kicigaba da masu addu'ah domin itace sukafi bukata agareki a yanzu".

Miko hanu tai tace wa chuchu tabata babyn nan tamika mata takarba, kallonta tadingayi tana zubda kwollah, babyn sai sharan baccinta take, babyn kuma gwanin birgewa kyakkyawa da'ita sak mahaifinta, farace tass ga dogon hanci, sumarta har ajiki gatanan kana gani,

Kallon babyn taitayi tana zubda kwollah, yayinda takejin so da k'aunar babyn naratsa dik wota gaba da jijiya ta jikinta, a yanzu kallonta take amatsayin y'ar uwarta MUNAWARAH,

Kallon su Abba tai ahankali tace "abbana" yad'ago da jajayen idanuwonsa dasukai ja sbd kukanda yai saitace "narad'awa y'ata suna MUNAWARAH amma za'ana kiranta da JAWAHIR sbd woni dalili nawa" murmushi sukai sudika momy ta tab'a kan babyn daketa baccin ta tace "masha Allah, ubangiji yaraya JAWAHIR" chuchu tace,

"Ameeen....momy, insha Allah babyn mu saitazama daban acikin y'aya" tafad'a tana shafa kan babyn.

Cikin gaugawa Abba yakira can k'auyen Raha yasanarda abunda ke faruwa, ashe koda yakira tini sunji harma kanen mahaifin Abba wato kakansu MADINAH dawosu tsofaffi da abokanan Abba guda hud'u sun kamo hanya,

Tini Abban susi yakirata yafad'a mata itama lkcn har chuchu takirata, aikwa tana isowa kuka yadawo sabo, nan suka rungume juna suna kuka mai cike da ban tausayi, ta karbi babyn ta kamkame a jikinta tana kuka.

Kankace me wojen yacika da mutanen k'auyen Raha, komai da akayiwa gawarwakin Abban chuchu ne yabiya, bayan anmasu wonka anmasu sitira sannan aka sakasu acikin ambulance, MADINAH dasu chuchu suka shiga motar Abban chuchu, yayinda shikuma Abban MADINAH da sauran mutane suka shiga shauran motocinda Abban chuchu yasaka aka dauko daga gida, Nan suka kama hanyar garin Raha.

Acikin 30mnts suka isa garin, koda suka iso tini anshirya komai, family house dinsu dake cikin garin aka fice, suna isowa kuka yadawo sabo, kannen inna da sauran mutanen gidansu dik sunzo nan, abun dik saiya k'ara hargitsewa,

Story continues below

Nandai bayan angama sallar isha sannan aka d'auki gaworwakin akaje akamasu sallah sannan aka tafi aka kaisu makwoncinsu na gaskiya, Allah kasa mucika da imani ameen.

Abban chuchu da sauran mutanensa bayan angama suka kamo hanyar gida, chuchu da momyn ta da susi kam anan zasu kwana, har izowa yanzu kwollah sunkasa tsayawa MADINAH a ido, musamman idan takalli JAWAHIR saitaji woni sabon kuka yazomata,

Sai kusan 11pm bayan kowa ya watse sannan MADINAH dasu momy suka fice can ainahin gidansu MADINAH acan zasu kwana su sbd nandin ba fili gidan yacika ssi da mutane,

Dasukaje ma bawonda ya'iya yin banci saidai baccin dayake barawo basusan lkcnda ya daukesu ba, amma MADINAH kam har yanzu takasayin baccin.

Momy da chuchu a d'akin Inna suka kwana, MADINAH da susi da JAWAHIR kuma a d'akinsu MADINAH, can kamar wocca aka tsikara ta tashi tafita woje,

Kallon gidan take tana tino abubuwa da dama dasuka shud'e a baya, tana tino yanda suke barkwonci da raha da wasa da dariya ita da y'ar uworta dakuma iyayensu a k'arkashin bishiya, musamman ranar weekend ranarda basa zowa school, shima Abban su ranakun baya zowa gona, yakan tsayane yabama yaransa lkcn sa, MADINAH da MUNAWARAH sunmatukar shakuwa da iyayensu hakan yasa MADINAH kejin zafin mutuwar Inna da MUNAWARAH har a cikin b'argonta,

Kwollah take zubarwa takasa tsayardasu kuma sai zarya take acikin gidan, kukan JAWAHIR dayaji ne yasata komawa ciki dasauri tadauketa,

Jijjigata tashigayi tana rarrashinta amma ina yarinyar takiyin shuru da'alama yunwace takeji, gashi kuma tashin hankali yasa sunma manta da'a siyo mata madara wocca zata rika sha,

Wota gorar ruwan swan tad'akko tabude tafara bata, tanashakam ammafa taki daina kukan sbd yunwarda takeji,

Jijjigata takeyi amma taki tadaina saita rasa yazatayi gashi batasan ta tashi su momy sbd sungaji suma suna buk'atar su huta, can dabara tafad'o mata kawoi taciro nata nonon tabata, idan taja tagaji taji ba ruwa ai dole tasake tai bacci.

Hakan kowa tayi kawoi saita bude zip d'in rigarta domin taciro nonon, saidai nonon bakamar na wocca tahaihu bane maana bai fadiba sbd haka bazai ciruba, kawoi saita bude dai tad'ora bakin baby, ai tana karb'a tafara tsotsa dak'arfin tsiya takwace nonon sbd woni azabar zafi dataji,

Tana kwacewa kuma babyn tashiga tsala ihu, tausayinta yasa tasake kaimata a baki itama tasake karb'a tacigaba da tsotsa dikda nonon kansa bai fitoba kamar macenda ta haihu, taso tayi dauriya har babyn tai bacci amma ina zafinda takeji yasa takasa hakura tacire daga bakin babyn,

Aikowa nan tacigaba da kukan, rasa mezatayi tai kawoi itama tafashe da kukan, kukanta ne yatada susi daga bacci saita ganta zaune tarungume yarinya tana kuka itama babyn na kuka, cikin yanayin bacci ta tashi takarbi babyn sannan tazauna tace,

"Haba MADINAH, yazaki saka yarinya agaba kina kuka itama kuma tana kuka acikin wonnan daren, dan Allah ki kwonta kozaki samu kiyi bacci zuciyarki tasamu nutsuwa, komai yafaru yariga yafaru sai hak'uri da addu'ah kawoi" cikin muryan kuka tace,

"Susi nakasayin baccin ne, bacci yakauracewa idanuwana, gakuma yarinyar nan tana kukan yunwa, tashin hankalinda aka shiga yasa namanta baasiyo mata madara ba, taya kike tinanin zan iyayin bacci" kallonta susi tai tace "akwoi tatacciyar madara" tace "Eh... baza'a rasataba a d'akin Abba, bara nadubo" saita tashi dasauri tafita,

Jim kad'an tadawo d'auke da madarar saidai batada woni yowa, Nan susi takarba tasaka chokali tashiga bama yarinyar tanasha, tasha dayowa harsaida cikinta yad'an taso sannan tabarmata haka, aikowa nantake saitai bacci ashe dama yunwace tahanata yin baccin,

Bayan tai bacci sannan susi tasaka MADINAH agaba saida tai bacci sannan itama tai bccin.

Washe gari tinda sassafe suka tashi momy tayiwa jawahir wonka aka canja mata kaya sannan suma sukayi wonkan, bayan sunyi wonka sun shirya Abba yasiyo kayan tea aka hada aka sha, MADINAH dakyar tasha rabin kofi shima Saida momy tanata tsaye, gaba d'aya yanzu batajin dad'in komai tafisan zaman kadaici,
Bayan sungama komai Sannan suka fito sbd y'an uwon Inna dik sunzo tinda asuba, a wojema Abba da abokanan sa dawosu mutane suna nan a zaune.

Story continues below

**************

Kamar ko yaushe, zaune yake acikin office d'insa yai tagumi shikad'ai yai shuu, da'alama dai yai zirfi ssi acikin duniyar tinani,

Saif ne yashigo office d'in yanata nocking amma harya kariso ciki baima saniba, Saida yatab'asa sannan yai furgigit yadawo hayyacinsa,
Zama Saif yai kan d'aya daga cikin maka makan kujerunda suke acikin office d'in, dan shi kansa office d'in kamar parlor yake, bambancinsa da parlor kad'an ne dan har TV akwoi aciki, ga fridge gakuma sauran kayan kyalkyali na kawata parlor,

Nannauyan ajiyan zuciya yasauke "Hmmm....!!!" Sannan yadubi saif yace "what....." Saif yace "Sir. what's wrong with you Wai, edays dinnan nafahimci kana cikin damuwa, dikda Kai mutum ne mai k'okarin boye damuworsa a dik lkcnda kafiddata to tabbas wonnan damuwor tagirma tazama babba, hakan yasa yanzuma natabbatarda damuwor da kake a ciki babbace".

Shafa fuskarsa yai cikin yanayin damuwa sannan yace "Saif...kai mutum ne wonda dik wota motsi tawa kasanta kuma kafahimceta, sannan kasan komai agameda musamman halayyata, yana d'aya daga cikin halayyata mace bata gabana kuma bata acikin tsarin abunda zai dami rayuwata kokuma nasaka a habana, ban d'auki mace abakin komai ba, amfaninta agareni baifi naji dadina da'ita ba, danagama kuma zan biyata ladan aikinda taman tai gaba,

But....now tasauya zani wlh, tasauya fiye da tinaninka Saif, u know me very well, dik abunda kaji nafada ma musamman akan mace to tabbas yagirmama, so yanzu ma hakan take" gyara zamansa saif yai sannan yace,

"Inajinka Sir. kabani labarin dawowar ka, wotak'il inada hanyar worware wonnan damuwor taka, dan kasan danabarka acikin damuwa gwonda ni natabbata aciki" yafad'a with a full confidence.

Tasowa yai yadawo kan d'aya daga cikin kujerun yana fuskantar saif Sannan yafara magana "saif...idan baka mantaba wota goma dasuka woce a Nigeria, k'auyen Raha dake cikin garin BUNZA L/GVMNT akwoi wota yarinya danama fyad'e akan mahaifinta yahanani mallakar woensu gonaki domin nagina company na".

Dasauri saif yace "Eh sir natina" saiya cigaba "to wlh saif tin lkcnda nayi sex da yarinyar bansake jin wota mace mai irin d'andano da d'adi da zuma irin tataba, kowacce mace jinta nake kamar rowan nan nabanza, kawoi dai inayine sbd biyan bukatata amma badan jin d'adi ba, ita kanta yarinyar nasan taji jiki matuka ranarda tashigo hanuna dan gaba d'aya kasa saita kaina nayi akanta, nakasa jin na k'oshi da'ita, yi nake amma ji nake kamar zumar tata bata tsayawa,

A yanzu nafara fahimtar mata ma suna suka tara, bakowacce mace bace ta amsa sunan mace, gashi wlh nakasa mantawa da yarinyar a zuciyata, a kullum hotonta sai gezau yakeman a ido" d'an murmushi saif yai kamin yagyara zamansa yace,

"To ai wonnan bawota matsala bace Sir, I know...nasan bazaka iya auren yarinyar ba bcoz Sam ba ajinka bace, so kawoi kabari nasaka a d'akko ma ita kacigaba da holewa abunka, um koya kace" murmushi yai yace,

"Shys kullum nake k'ara jin d'adi zama dakai saif, sbd kanada tinani brain naka yana ja ssi" sai Saif d'in yai murmushi, shikuma yacigaba da fad'in "inaga haka zaayi kawoi, but..saidai kabari zankara yin shawara akan maganar" saif yace "Ok Sir...am waiting for you" yace Ok,

Daganan sukacigaba da maganarda takawo Saif.

************

Around 12pm dot Abban chuchu yazo tareda wosu abokanansa, hakama iyayen susi sunzo gaisowa, kawayen MADINAH ma da corse mate dinsu dik sunzo,

Saida akai kwana uku sannan su chuchu suka koma gida akabar MADINAH da abban da JAWAHIR sukad'ai acikin gida,
Dafarko kanwor Inna taso ta karbi jawahir amma fafur MADINAH taki amincewa, dole akabarta da y'ar ta,

Bayan sati d'aya ta tattara takoma school domin k'arisa IT d'inda sukeyi, saidai har yanzu batakoma normal ba kamar da, yanzu tamafisan zaman kadaici, babyn ta kowa saikara wayo take.

Story continues below

Koda tadawo birnin kebbi su susi sunyiwa baby jawahir siyayya tamusamman, kayan wasan yara da tifafi kala kala masu shegen kyau,
A yanzu rainon jawahir yadawo hanun mutum uku harzowa hud'u, uwarta MADINAH da susi da chuchu, saikuma baaba laure wocca take Mai aikin momyn chuchu, itace suke barwa ita kafin sudawo daga hospital,

Lkcnda suka gama IT kuma suka koma school da abarsu suka tafi, har class da abarsu suke zowa, Koda suka gama IT woni doctor ISMA'IL yamannewa MADINAH yana santa,

Dafarko bata kulasaba sbd yanzu kokad'an batasan danuwa, soyayyarma batasanta dan bata gabanta, Saida yai kamar yanayi sbd yaji tamasa shikam yana santa sannanfa tafara d'an kulasa, shima Saida su chuchu suka hadata da momy sannan ta amince tafara tsayawa suna gaisawa.

A dik kwanan duniyar MADINAH ta tashi, da burin daukan fansa take tashi, kuma kullum cikin tsara yanda zata d'auki fansar take, saidai wosu abubuwa da dama suna nema suzamemata cikas ko matsala, hakan yasa tadan dakata domin mallakar woennan abubuwan,
.....................

A yanzu rayuwa take ita da yarta wocca baza'a kirata data k'unci ba saidai ace Alhmdllh, jawahir nasamun kulawa tako'ina, Abban chuchu jinta yake kamar jikarsa ta jini, komai yasamu jawahir dai hakama momy dan yarinyar tanada shiga rai ssi, kyakkyawa ce ssi, yanzu tanada shekara 2 kuma tin tana 7months ta taka k'asa tafara tafiya, yanzuma idan kaganta gaka irin wayonta zakace takai 4yrs,
To wonnan kenan.

****** ******

_BAYAN WASU SHEKARU_

Abubuwa da dama sunfaru a shekarunda suka wuce na farinciki da jin d'adi,
Kamar zamuwar su MADINAH cikekken likitoci na fannin sanin matsalolin mata da cututukan dake damunsu,

Saikuma katafariyar hospital da mahaifin cool susi yaginamata wonda tasakawa suna JAWAHIR SPECIAL HOSPITAL inda su ukun kejagorantarta, kowacce fanninda takaranta shi take jagoranta,

Yarsu y'ar gaban goshi kowa yanzu tagirma dan takai kimanin shekara 5.

Dik rayuworda sukai a k'asar India wojen karatinsu na zama cikekkun likitoci atareda ita sukayisu, acan suka sakata makaranta tafara karatu, bayan sungama zasu dawo suka fiddata dasuka dawonan suka sakata a JO'DA INTERNATIONAL SCHOOL inda yanzu take a primary 2.
.....................

Yau takasance weekend cool susi kawoi taje hospital itama bawoni dadewa zatayiba,
Guru take tana dariya yayinda MADINAH kebinta tana fad'in "jawahir kitsaya nasaka maki rigar nan, kitsaya nace" itakowa sai cigaba da gudun take tana dariya,

Dasauri cool susi dake shigowa parlon tad'auketa tai sama da'ita itama tana dariyan, tana kawowa itakoma saita tsaya tana haki,

Cikin dariya cool susi tace "me tayi ake binta dagudu haka" MADINAH tace "wonka aka mata yanzu, shine nake sakamata kaya woi saina bari tad'akko alawa" dariya cool susi tai Sannan tace,

"Um..kinma tinaman wlh, tin jiya nasiyomaya woni sweet amma namanta damuka had'u hospital banbakiba" nan taciroshi daga cikin jakarta tabud'e taciro d'aya tabata sannan tasauketa tana fad'in,

"Ai kinsan halin jawahir sarai, matukar ba alawor kikabari tad'akko ba baza'a saka rigar da dad'in raiba" saita karbi rigar tasaka mata sannan suka shigo ciki,

Chuchu na zaune tana aiki da laptop tana dariyan rigimarsu, zama sukai sannan suka shiga gaisawa.

Jawahir fita tai tafice izowa d'akin momy tabarsu anan,

Kallonsu cool susi tai sannan tace "am guyz, woni scholarship ne nasamoma mana idan kunaso" chuchu tace "wone iri ne?" tace "akan woni curse ne wonda zaayi 1yr a Cyprus, karin karatune akan sanin kwokwolwa, dakuma abubuwonda ke cikinta" chuchu tabe baki tai sannan tace,

"Nidai gsky nagaji da yawon k'asashen nasaran nan, dudu du fa watanmu nawa da dawowa England harkuma muka samu hutunda zamu kowa Cyprus".

MADINAH kam dasauri tace "nikam zanje, sbd inada muhimman abunda zanjeyi acan, maana bakaratin kad'ai zai kaini ba, zanyi jifar tsintsi biyu da dutse d'aya ne" cikin mamaki cool susi tace "kekuwa wone muhimman abune zakiyi haka, dan nimadai kawoi nakawo maku scholarship dinne amma badan inasan tafiyar ba, nagaji yanzu aure nakeso nayi nahuta tinda dai Alhmdllh muncika burinmu naxama cikekkun likitoci kuma kwararru" murmushi MADINAH tai sannan tace,

"Hmm...nima hakan take a worina, amma saina fara d'aukan fansar abunda akaman tsawon shekaru dasuka woce tukuna, sannan zanyi aure sbd zuciyata bazata taba samun nutsuwar zaman aureba matukar bandau fansar abunda akaman ba".

Tini suka fahimci inda xancen nata yadosa, chuchu tace "muma mungoyi bayanki y'ar uwormu, kuma insha Allah zamu taimakeki domin ganin kin d'auki fansa, inaso mu nunawa DEEDART cewa komai kud'insa akwoi wonda yasha gabansa, sannan dik tantirancinsa akwoi wonda yasha gabansa har gobe" cool susi ma cewa tai,

"Nima nabada goyon baya wlh 100%, yanzu mucika scholarship d'in zansa Abbana yasaka amana komai nanda wata d'aya saimu wuce" cikin farinciki dajin d'adi MADINAH tace,

"Nagode ssi y'an uwana, hakika ku kuncika y'an uwa nagari, har abada bazan tab'a mantawa dakuba a rayuwata, amma saidai dole kamin muje saimun nemi sani akansa, nidai abu d'aya kawoi nasani akansa shine, yana d'aya daga cikin woenda sukafi kowa kudi a Africa, so kunga dolene saimunyi babban shiri domin tinakararsa dayaki sannan dole saimun hada da dabarunmu na mata tinda shi mutum ne mai shaani da mace".

Susi tace "tinda shi babban mutum ne inaga mushiga internet zamu samu cikekken labarinsa" aikwa dasauri chuchu tabude laptop d'inta tahau yanar gizo....

Tana hawa tafara searching na sunan DEEDART only sai aka nunamasu woni daban ba wonnan ainahin DEEDART ba, saisuka sake searching d'in Mr. DEEDART, nanma dai babu woni lbr dan wonnan d'in kam koma lbrn woni ba'a turomasuba,

Can MADINAH tace "kusaka Mr. AHMARD DEEDART maybe dahakan yake amfani, saikwa chuchu tarubuta, aikwa tana rubuta hakan saiga k'aaaton hotonsa yafito b'arau b'arau woni hoto dayayi da wota shaddah gizna light blue mai shegen kyau da tsada, dan a k'allah kud'in ta zaikai naira budu dari shida da doriya, saikuma hula da worth d'insa silver color mai shegen kyau da tsada, saikuma takalmansa black color kirar k'asar England wonda dik daga companyn sane aka yomasa su,

Yamatuk'ar yin kyau a hoton dan idanma kagansa zakayi zaton irin larabawon nan ne masu saka irin kayan y'an Nigeria, sbd sam color d'insa baiyi kama da d'an Africa ba, yamafi kama da d'an Arabia kokuma shuwa'arab.

Can daga gefen damansa akafara rubuta takaitaccen labarinsa acikin harshen turanci, dasauri kowa suka karance lbrn nasa, woni mugun tsaki cool susi tai kamin tace "woi ashe ma d'an Africa ne kuma d'an asalin k'asar kebbi, amma dai dole yayi jan aji, kuma dole yadinga jin kansa shi woni shegene, tinda shine d'an Chief justice, kuma dadi da kari kuma shima shine the most reachers guys in Africa gaba d'aya, hmm...".

MADINAH kam tabe baki tai sannan tace "wlh ni dik kud'insa basa gabana, burina kawoi nad'auki fansar abunda yaman" chuchu tace "insha Allah kowa saikin d'auki fansa da ikon ubangiji".

Saida suka karance komai daga labarinsa sannan suka rubuta abunda zasu d'auka sbd gudun mantuwa, daganan kuma suka zauna suna tattaunawa akan yanda zasu fara gudanarda abun.

MADINAH tace "yanzu dai kamin end of this month yadace mubar k'asar nan, dan a bincikenda nai end of this month ne zai dawo daga tafiyarda yai k'asar Canada, so kunga zamufi jin d'adin aikin idan yana k'asar" sai cool susi tace "insha Allah kaminma karshen wonnan month d'in komai zai kammala".

Jawahir ce tashigo da gudu tana fad'in "Mommy...mommy...mommy, uncle yajo" tafad'a cikin tsamin bakinta, cikin murmushi da fara'a MADINAH tadorata kan cinyarta sannan tace "are you Shure my sweetheart" saita d'aga mata kai sannan tasake cewa "Ok...yana inane" saitace "yana can gun baba mai gati suna fira".

Saitace "Ok...jeki kicemasa ina zowa" saita sauka sannan tafice da gudu, chuchu tace "oh..daina yin gudu jawahir karki Fadi" ko sauraronta ma batayiba tafice abunta tana murnar ganin uncle d'inta mai sonta,

     Tashi MADINAH tai tana fad'in "um...bara natashi naje gun mijina, karna biyemaku nab'atamasa lkc ko rai" dariya su chuchu sukai sannan chuchu tace "ai bama zaki b'ata masa lkcn ba bakuma zaki b'ata masa rai ba, dan da ransa na b'aci da tini yadade da b'acin" dariya tai tana fad'in "eh...naji dai".

Kayan jikinta tacanja izowa siket da riga na atampa super wax mai kyan gaske da tsada, maroon and white color, d'inkin yamata kyau ssi kuma yakama jikinta, rigar tad'an matseta harta fitarda rabin kirjinta a woje, sumarta kuma ta tufketa sannan tai daurin d'ankwali mai suna zarah buhari/ruky mama, wonda ake Kira da ture kaga tsiya,

Powder tashafa sannan tashafa Jan baki da kwolli, y'ar kwolliyar datai saita kara fitarda ainahin kyanta a zahiri, kallon kanta tai a mirror tana karewa kanta kallo, ita kanta tasan tai kyau ssi, to barekuma wonda akai kwolliyar dominsa, murmushi tai sannan tarufe fuskarta da tafukan hannayenta sbd tinowa da yanda Dr. Isma'il zai yaba kwolliyar tata, dakuma tino da yanda yake yaba kyanta a baya lkcnda Sam batajin dad'in yabon nata dayake, sab'anin yanzu kuma data kamu da sansa.

Akwatinta tabude tad'akko woni sabon mayafi fari tas mai kyau wonda a yanzine zata fara sakashi kamar yanda dik woni abu dake jikinta yanzin ne tafara sakashi, bayan tayafa mayafin sannan tad'akko wosu plat shue white color tasaka, bayan tasaka sannan ta fesa tirari mara k'amshi ssi.

Story continues below

Daganan kuma tad'auki woyarta sannan tafita,

Koda tafito chuchu tana kitchen cool susi kuma tana a kwonce tana kara bincike akan DEEDART, kallonta tashigayi tana murmushi kamin tace "woww...momyn jawahir, wlh kinyi matukar yin kyau, natabbata yau sai Dr. yayi mamakin ganinki acikin wonnan shigar, dan Allah kibasa dama domin yakariso daga ciki musha biki, ayi agama awuce gurin" dariya tai sannan tace "karki damu y'ar uwata, ai lkc yayi dayakamata basaka Isma'il da tarin soyayyarda ya nunaman a baya, dikda cewa naki nabashi cikekkiyar kulawa domin mu fahimci juna, Dr. Isma'il yanunaman k'auna dikda cewar ni naki nabashi lkcna, but...now insha Allah zanbashi cikekken lkc na amma kuma bayan nagama d'aukan fansar abunda akaman a baya" murmushin jin d'adi cool susi tai tace,

"To Allah yasa, yakuma nuna mana lkc" tace ameen sannan tafice.

Koda tafito saita hangosa zaune acikin lambu shi da jawahir da Ayman kanen chuchu, ahankali tafara takawa tana karisawa gunsu, daddad'an k'amshin tirarenta ne yafara dakar hancinsa wonda ko a mafalki yajisa yasan mamallakiyarsa, wato masoyiyarsa,

Aikwa cikin sauri yajuya saikwa yai tozali da'ita tana k'arisowa gunsa cikin fara'a, tattausan murmushi yasakarmata sannan tak'ariso gunsa tareda rangad'a masa sallama, cikin tattausar murya ya amsa tareda fad'in "barka da fitowa gimbiyata, fatan anfito lfy" cikin murmushi tace "lfy Alhmdllh, fatan kazo lfy" yace "Alhmdllh".

Zama tai ahankali gefensa tareda gyara mayafinta, shikowa sai satar kallonta yake yana murmushi, ransa mamaki yake yana fad'in "Wai dama haka MADINAH take da kyau, ashe dama hijab ne yake boye kyanta dakuma rashin yin ado da kwolliya".

Katse masa tinanin tai da fad'in "am..dan Allah kayi hkr nabata maka lkc, kaya natsaya canjawa" murmushi yai sannan yace "No..bkmai wlh, amma gsky kinyi kyau ssi gimbiyata, ashe dama haka kike da kyau" murmushi tai tace "godiya nake da yaba kwolliyar da nai wocca kuma dama dan Kai nayi d'in".

Woni farinciki ne yatasoma yai dariya yace "aikwa dole nabiya kud'in wonnan kwolliyar sannan kuma nakara bada kudi domin aje akaro wosu kayan kwolliyar sbd a dinga man dik lkcnda zanzo kamin aje gidana a cigaba da man acan" dariya tai har Saida dimples dinta yalotsa irin na jawahir wonda ko marigayiya MUNAWARAH tanada shi,

Shikwa binta yai da kallo lkcnda tana dariyar, sai yakeji kamar karta daina dariyar sbd yanda fuskarta tai kyau, a dik tsawon shekarunda suka kwashe, yau itace rana tafarko daya fara ganin ainahin fara'a a fuskarta harma da dariya, itace kuma rana ta farko data farayin kwolliya dominsa, kullum yazo aciki k'aton hijab yake ganinta kullum kuma bawoni sakin fuska ssi,

"Wonnan ranar ta yau dole nasakata acikin jerin ranakuna masu daraja da muhimmanci woenda kuma nake farinciki idan natinaso, wato ranarda MADINAH kika fara yin kwolliya domin ni, sannan ranarda kikafara yin dariya domin ni, inafatar kuma itace ranarda zaki furtaman tabbas kinasona kuma kinbani damar naturo iyayena domin ayi maganar aurena dake".

Murmushi tai tareda sadda kanta k'asa sannan tace "hakika Isma'il ka cancanci nabaka soyayyarta, ka cancanci na mallaka ma soyayyata, sbd kanunaman kaunarda babu woni d'a namijinda ya nunaman ita, tsawon shekarunda muka kwashe atare batareda nafurtama kalmar so ba kuma daidaida rana d'aya baka tab'a yin fushi kokaji kagaji bazaka sake dawowa guna ba, tin banajin soyayyarka a zuciyata yanzu harna farajin ina sonka kuma zan iya rayuwar aure dakai, 

Sbd haka Isma'il ina sonka, na amince katuro iyayenka gidanmu domin ayi maganar auren mu"tana gama fad'in haka saita rufe fuskarta fa tafukan hannayenta woi kunya,

Woni irin farinciki ne yatirnikesa yai dariya tareda fad'in "yesss..." sannan yace "Alhmdllh burina yakusa cika na mallakarki amatsayin matar aurena kuma uwar yayana insha Allah".

Saikuma yamatso dab da'ita tareda d'an sunkuyo kansa daidai fuskarta cikin murmushi sannan yace "to bud'e fuskar mana" saitayi dariya takasa d'ago fuskarta takallesa, murmushi yai yace "gimbiyata kenan, kunya ko" jawahir ce tazo dagudu Ayman yabiyota tafad'a jikinta sai mayafinta ya yaye, nantake tidin bobbs d'inta dayake woje ya bayyana, aikwa idanuwon Ismail nasauka anan Saida yaji woni shok ajikinsa.

Story continues below

Ayman kusan sa'ar jawahir ne, kad'an yatsofeta, dan inagama baifi wota shida ne a tsakaninsu ba, Ayman kuka yake yana fad'in "wlh bani abuna, kibani kayana" sai MADINAH tace,

"A,A.. jawahir menene, me kika d'aukan masa" cikin maganrta ta tsamin baki tace "banasa bane, nawane mommy" hanunta tabude saitaga chocolate aciki, cirowa tai tamika masa yakarba yafice yana murna,

Itakowa jawahir kuka tashigayi sai Dr. yakarb'eta yana fad'in "menene...menene my princess, daina kuka muje yanzi nasiya maki wasu, jeki mota ganinan zowa" cikin tsalle da murna ta tashi tafice, 

Kallon MADINAH yai saita sadda kanta, murmushi yai yace "gimbiyata, gwondafa ki daina wonnan kunyar, tinkan ni nacireta dakaina" wota iriyar kunya ce takamata saita rufe baki da d'ayan hanunta batareda tace komaiba, mikewa yai tsaye sannan yace "tashi muje asiyowa baby chocolate" ba musu kowa tamike a tsaye tareda saka takalmanta.

Kai tsaye gun motarsa suka fice suka shiga sannan yatada motar suka fice,

Wota katafariyar plaza suka fice mai kyan gaske, nan yayiwa jawahir siyayyar kayan mak'u lashe sannan yasaka MADINAH dole saida itama tayi tata siyar mai tarin yawa wocca hadda kayan sakawa aciki, bayan sungama sannan suka fice yamaidasu gida, kamin yaficema Saida sukadan tab'a fira sannan yafice,

Koda taisa su chuchu suna parlor, tana shigowa sukace "su masoya manya ne" saita tai dariya tareda zama kan kujera, kayanda tashigo dasu suka shiga dubawa, jawahir tashigo tanashan sweet da chocolate, d'aukan ta chuchu tai tana fad'in "Iyyeee... y'ar ango, kinsha kaya" MADINAH tai dariya tareda mikewa tashiga ciki.
   .....................

Sannu ahankali so da k'auna dakuma shak'uwa take shiga a tsakanin MADINAH da Dr Isma'il, yayinda yake kara bayyanamata da tsintsar soyayyarsa a fili yana kuma kara nunamata tsintsar k'auna a fili,

Acikin d'an lkc k'ank'ane MADINAH tasaki jiki dashi harta sakama sa suna my one and only or my husband, haka take kiransa da woennan sunayen,
Tini yasanarda kowa na gidansu lbrn MADINAH amma banda matarsa wocca takasance mai zafin kishi da bak'in jahilci,

Kowa na gidansu nantake yasan MADINAH dakuma kyawawan halayenta, domin dikya zauna bashida lbr saina gimbiyarsa,

Ganin sunfahimci juna dakyau dakyau yasa yasanarda magabanta itama tafadawa Abban chuchu yaje dakansa Raha yafadawa Abban MADINAH,

Acikin sati uku cif akai baikon Dr. MADINAH da Dr. Isma'il, ranarda akai baikon Isma'il ji yai kamar ranarne aka d'aura auren su, sai farinciki yake yana murna, saidai fa har yanzu baisanarda muguwar matarsa bahijja ba.

A b'angaren MADINAH ma hakan take, kullum k'aunar Isma'il dad'a k'aruwa take acikin zuciyarta.
   _______________________

Izowa yanzu komai na shirye shiryen tafiyarsu k'asar Cyprus sungama, kawoi ranarda zasu tafi suke jira tazo, a wonnan karon ma tareda yarsu zasuje danhaka hadda itama sunmata nata shirye shiryen, saidai fa har yanzu MADINAH bata fadawa Isma'il zancen tafiyarsuba, haka kuma bata tab'a basa lbrn jarabawanda ta sameta ba shekarunda suka shud'e,

Tinda tafarajin sonsa a zuciyarta tayanke hukuncin fadamasa, saidai takasa sanin taina zata fara basa lbrn sbd tana tsoron karya gujeta akan taki fadamasa tin farko sai yanzu da'akamasu baiko.


        Zaune suke acikin lambu kamar yanda suka saba dik sadda yazo anan suke shan firarsu, sanye take acikin doguwar rigar abaya red color, tai rolling da veal din rigar, yaukam bata shafa janbaki ba tadai shafa lipgloss da kwalli.

Fira yakemata tana murmushi, can tacemasa "am Dr, dama inaso nafad'a maka wota magana" saiya gyara zamansa cikin fara'a yace "inajinki gimbiyata" saitad'an sadda kanta k'asa sannan tafara da fad'in "dama inataso nafad'a maka, zamuyi tafiya izowa k'asar Cyprus ni da y'an uwana dakuma y'ata wojen yin karati na karo ilimin sani kan abunda mukai karati akansa, zamuyi shekara daya ne kacal" dajin abunda tafad'a nantake yanayin fuskarsa yacanja, annurin fuskarsa yasauya yacemata "haba MADINAH, yakamata kiwa kanki fad'a, kidubafa kiga tsawon shekarunda mukwa kwashe, lkc yayi dayakamata muzama ma'aurata, wlh nagaji da wonnan zaman gwaurancinda nakeyi" cikin mamaki takallesa tace,

"Gwauranci, kamarya gwauranci, bacin nasan kanada mata yayane bakada" hmm...!!! yasauke nannauyan numfashi sannan yace "yau zan fad'amaki abunda bantab'a fada makiba, sbd ni nakasance mutum Mai rufe sirrin iyalinsa dakuma gidansa gaba d'aya, MADINAH...dani da wonda bashida aure  bambancin mu kad'an ne, yau kimanin shekara biyar kenan da aurenmu amma bantab'a sanin miye dad'in aure ba, a kullum cikin yin azimi nake domin kare kaina daga fadawa hallaka,

Matata takasance d'aya daga cikin mata masu zafin kishi ssi, a kullum cikin zargina take inacan tareda wasu mata a woje, idan nadade a gun aiki saitace inagun mace ne shys, idan kuma nai fitar dare nadade bandawoba saitace inacan gun tadi ne, ranar kuma bazata tab'a barina nakusanceta ba, nakanyi kwana biyar har shida batareda tabari na kusanceta ba Koda kuwa inacikin buk'atar hakan ne, a kullum cikin yin azimi nake domin kare kaina daga afkawa acikin zina, 

Sannan tahana mahaifarta tad'auki ciki, woi ita aceworta yarinyace bata isa haihuwa ba, bata isa ace tahaihuba, sbd hakan yasa a kullum take cikin yin allurar hana haihuwa dakuma Shan kwayoyi, wonnan dalilin yasa nayanke hukuncin k'ara aure tin munada shekara d'aya da aure nafara wonnan tinanin, a karon farko kuma cikin nasara Allah yahadani dake a hospital lkcnda aka turoku yin IT".

      Nannauyan numfashi tasauke sannan tace "Isma'il... azahirin gsky inamatukar sonka, kuma ina tausaya maka, ina tausaya halinda kake ciki, saidai wlh Isma'il zuciyata da ruhina dama gangar jikina gaba d'aya, bazasu sami nutsuwar zama dakai kuma zaman aureba matukar banje na aiwatarda abunda nakeda burin aiwotarwa ba a k'asar Cyprus".

Dasauri yace "haba MADINAH yakamata pa kiyi tinani, ilimin nan daidai gworgwodo kinsameshi kinadashi, yakamata kibar karatin haka kizo muyi aure muci moriyar rayuwormu"  dasauri takallesa tace,

"Waya fadama karatinne zai kaini k'asar, nifa Sam karatu yanzu baya gabana, daukar fansa zanje nayi" tafad'a cikin kakkausar murya tareda zubda kwollah,

Mamakine ya bayyana k'arara a fuskarsa, cikin mamakin yace "daukar fansa kuma MADINAH, ban...ban...banfahimceki ba, me kike nufi dahakan" shware kwollanda suka zubomata tai sannan tafara da fad'in "kamin nafara da baka lbrn ina rokonka dakai hak'uri akan boyemaka gsky da nai,  jawahir y'ata ce amma banice nahaifeta ba" daganan tafara basa lbrn abunda yafaru tin farkon haduworta da DEEDART har izowa mutuwar MUNAWARAH da Inna, sannan tad'ora da cewa,

"Tin bayan rasuwar y'ar uwata da mahaifiyata nad'auki alk'awarin saina d'auki fansar abunda akamana kamin nai aure, sbd Sam zuciyata bazata taba samun nutsuwar zaman aureba matukar bancika wonnan alk'awarin dana daukarwa kaina ba, a dik kwanan duniyar nan idan natashi cikin tsara yanda zan d'auki fansa nake acikin ruwan sanyi kokuma acikin masifa da balai, kwatsam saiga wonnan damar tazoman danhaka nai saurin karbanta domin ganin nacika burina".

Juyowa tai takallesa da dara daran idanuwonta dasuka canja launi sbd d'an kukanda tai yanzu, share kwollan tai sannan tace "dan Allah Dr karkace zaka hanani yin tafiyar nan, wlh namaka alk'awarin idan ranarda nadawo kakeso a d'aura mana aure na amince matukar dai bazakace baka aminceba da wonnan tafiyar tawa".

Matsowa yai dab da'ita yana kallon idanuwonta cikin yanayin tausayi, Saida yad'an d'auki wosu seconni kamin yace "share kwollan, banasan fararan idanuwon nan naki suna fitarda kwollah acikinsa, sbd Sam hakan baidace dasuba, shikenan na amince Allah yabada nasara" ji tai woni irin farinciki yatirnike ta kamar tarungume sa taji saita rufe fuskarta tana fad'in,

"Thank you so much my love, thanks alot, Allah yabarman Kai yakuma barmu atare" yace "ameeeen matata, Allah yakuma yanunamana ranar aurenmu ko" saitai murmushi tareda d'aga masa Kai, saiya cigaba da fad'ar,

"Allah I nunamana ranar, hmm....ranar yarinya saita....." saikuma yai shuru yana dariya, itakam kunyace takamata saita dingayin murmushi kawoi danta fahimci Ismail kam bayajin kunyarta, Sam bayajin fadamata magana koya take, sab'anin ita dakejin kunyarsa kamar tanitse acikin k'asa,

Yajima ssi agunta sunashan firar soyayya kamin daga bisani yamata sallama yafice.
   ........................

Bayan kwana biyar kacal su MADINAH sukama k'asar kebbi bankwana  jirginsu yad'aga izowa k'asar Cyprus su hud'u..


Kimanin 5hrs suka d'auka suna tafiya kamin su isa k'asar ta Cyprus, kasancewor suna tsayawa ne a wosu k'asashen suna sauke fasinjoji,

Around 4pm dot jirginsu yasauka a katafaren filin jirgin k'asar Cyprus.

Suna sauka sai suka k'arisa cikin filin jirgin domin jiran isowar motocin school d'inda zasuyi karatu acikin,

Jawahir d'auke take a hanun MADINAH, su ukun sanye suke acikin wando jeans da t-shirt blue, sai takalma bak'ake rufaffi, saikuma rigar sanyi wocca takeda tsayi har guiwa girmanta, kansu kuma sunyi rolling da woni veal baki idanuwonsa sanye da glass,

Yayinda itakuma y'ar tasu take sanye da wandon jeans white color da rigar sanyi mai hula pink color ansaka hular anrufe mata Kai sbd yanayin garin akwoi sanyi ssi, sumarta an tufketa gu d'aya da rivom pink color, a kafarta kuma takalma ne Pink color rufaffi da socks white color mai kyau,

Shigar tasu tayi matukar yimasu kyau, saisuka fito tamkar jinin larabawa, hanun jawahir d'auke yake da balloon guda biyu, dayan kuma yana d'auke da teddy white color, atak'aice dai itama tai kyau ssi gwonin birgewa kamar y'ar tsana, kamanninta da DEEDÀRT dik sun kara fitowa a fili, dakaganta matukar kasan DEEDART to saikaga kamminsu.

Gunda aka tanadar domin zama sukaje suka zauna jawahir nakan cinyar MADINAH ta rungumata, duban MADINAH tai sannan tace "mommy, ruwa nakesh" saita tashi sannan ta ajiye jakarta tadauketa suka tafi domin ta nemomata ruwan tasha, dama itama tanajin fitsari tanaso tad'an zaga band'aki, danhaka tadauketa suka fice,

Ruwan tafara nemomata tabata tasha sannan sukaje gunda ake fitsarin, wurin akwoi cinkoso ssi saita rasa yazatayi gashi tanajin fitsari, can yana waige waige saita hango wota mata wocca tana ganinta tasan y'ar Africa ce, nantaje yamata sallama suka gaisa sannan tabata jawahir tace "dan Allah kulaman da'ita inaso nai fitsarine" matar mai suna Nana tace "ok bdmwa" saita amshi jawahir sannan MADINAH taje domin tai fitsari,

Akwoi woni gu kusa da worin inda ake siyarda ice-cream, aikwa jawahir nagani nantace itafa ice-cream takesha, cikin fara'a nana tadauketa sukaje gunda ake siyarda ice-cream d'in, nanma akwoi cinkoso saitace mata "Kinga kitsaya anan nashiga nasiyomaki, karkije koina yanzinnan zan fito" saitace to sannan nana tashiga wojen daike siyarwa,

Jawahir na tsaye tana jiran fitowar aunty nana sai balloon d'inta yafige daga hanunta yai sama, nanfa tabisa domin yakamo abunta sbd tanasan balloon d'in nata, haka tadinga binsa shikowa yana tafiya sbd iskar dake kad'awa shys yake k'ara tafiya.

Basu tsaya a koina ba sai ajikin rigar woni kyakkyawan mutu, had'adden gaye mai jini a jika, cikekken mutum mai kirar maza da cikar halitta, a boturan d'in rigarsa igiyar balloon d'in tamakale saisuka tsaya, tana ganin haka saitaje dagudu domin tama mutumin magana yabata abunta,

Koda MADINAH tafito saibata nana da jawahir ba, aikwa nantake kirjinta yafara dukan tara tara, nantafara dube duben inda zaga hango nana ko jawahir, amma wayam ba nanar bakuma jawahir,

Ganin hakan yasa nantake hankalinta yatashi tafara neman nana acikin dandazon mutanenda ke wojen,

Nana ma koda tafito d'auke da ice-cream a hanunta saitaga wayam bataga jawahir ba, nantake hankalinta yatashi tafara dubata acikin dandazon mutanenda ke wojen, tana cikin dubawa saisukaci karo da MADINAH,

Nannauyan ajiyan zuciya MADINAH tasauke sannan tace "kintada man da hankali, y'ata kwaya daya tilo ace nazo wonnan k'asar bangantaba" sosar Kai nana tafarayi kamin tace "wl...wlh...naje siyomata ice-cream Koda nafito yanzu sai bangantaba" dak'arfi MADINAH tace,

     "What......!!! mekike nufi da wonnan maganar, kardai kiceman y'ata tabata ne?" dasauri tace "bahaka bane, maybe woni abune yaja hankalinta, amma mufara dubawa acikin mutanen nan dan nasa bazata wuce nandin ba".

Story continues below

Haka d'in kowa sukafarayi, nan suka shiga nemanta acikin wojen.

Itakowa tana isa ahankali tariko hanun mutumin daketa faman magana dawosu mutane masu kaya iri d'aya, da'alama dai bodyguards ne,

Yana waigowa wazan gani reader's, hmm Mr. AHMARD DEEDART nagani acikin wosu suit bak'ake masu kyan gaske, idonsa sanye da glass baki mai tsadar gaske, yai kyau matuka shigar tamatukar karb'an sa, Saida yajuyo sannan naga kamanninsa da jawahir ssi, fiye da tinanin mai karatu, komai na jawahir irin na DEEDART.

Kyakkyawor yarinya yagani tsaye tarike hanunsa tana kallonsa, a zatonsa y'ar turawa ce jajayen fata sbd ganin yanayinta dakuma yanayin shigarta irin ta yay'an turawa, saikuma yaji tace,

"Sannu Uncle, balloon dinane yamak'ale a rigarka, plss kaciroman abuna kabani dan Allah" mamakine yak'ara cikasa jin yanda yarinyar dabazata woce shekara hud'u zuwa biyarba take magana acikin nutsuwa kamar wocca tamallaki hankalin kanta,

Dukawa yai dai dai fuskarta cikin fara'a da murmushi sannan yaciro igiyar balloon d'in yamika mata takarba cikin murmushi sannan tace "Thanks....but uncle ya sunanka ne, ni sunana MUNAWARAH AHMARD DEEDART amma ana kirana da jawahir, kaifa?" tajefa masa tambayar,

Jin complete name nata datafa yasashi dazk'arewa a gu d'aya, nantake tsintsar mamaki ya bayyana k'arara a fuskarsa, sake karewa yarinyar kallo yai sannan yace "ni sunana Uncle kawoi" dariya tai sannan tace,

"Uncle ai ba sunane ba, kaga tinda bazaka fadamanba shikenan" shifa mamaki yake ssi yana kuma kallon yarinyar, tinda yake a rayuworsa baitab'a jin mai irin complete name nasa ba, amma yasan akwoi woni DEEDART, but...shi DEEDART ne only, tokuma yasan shima woncan DEEDART d'in bashida aure bare har ace yanada y'a wocca tai girman wonnan.

Itace tadawo dashi daga zirfin tinaninda yake tana fad'in "Mr. Uncle nidai zantafi gun mommy na" dasauri yaharde hanunsa da nata cikin rashin son tafiyar tata yace "kinga, dakata mana muyi fira" saikuma tatsaya.

DEEDART yana matukar San yara, yakan b'ata lkcnsa akan yara amma baib'atasaba gun manya musamman mata daya daukesu mak'askanta,

MADINAH tarikice acikin airport d'in, hakama su chuchu dan tini taje tasamesu tasanardasu halinda ake ciki, gaba d'aya sun rikice acikin airport d'in, tini MADINAH tafara kwollah sbd dik hankalinta yagama tashi,

Nana ce tabada shawarar aje asanarda security's d'inda ke kula da wojen, nankwa cikin sauri sukaje suka fadamasu, kayanda ke jikinta da shekarunta dakuma kalar fatarta, nantake sukafara sanarwa ta microphone yanda kowa da kowa zaiji,

Nan sukuma sukacigaba da nemanta acikin mutane, suna biyowa ta daidai kusa dasu, kamar ance MADINAH tawaiga tana juyawa saita hangota hanunta rike da Sweet tanasha shikuma yai zaune yana magana da'ita yana dariya itama tana dariya, mamakine ya bayyana k'arara a fuskarta.

Cikin mamaki ta tab'a cool susi sannan tanunamasu, tsintsar mamaki ne yabayyana a fuskokinsu, chuchu tace "mezan gani haka, kardai DEEDART yagane jawahir yarsa ce" cool susi tace "Kai ina...yama zaayi yagane bayan shi baimasan MUNAWARAH tasami cikiba" MADINAH kam cikin fushi da tsintsar b'acin rai takama hanyar zowa gunsu,

Tana isa taduka ta taso da jawahir, tana waigowa saita ganta saita rungumeta dasauri tana dariya tace "mommyyy...." tafad'a cikin murna,

DEEDART naganin fuskar MADINAH dasauri yamike a tsaye cikin tsintsar mamaki, fuskarda yakwashe shekara da shekaru yana nema yaugata yaganta a inda baiyi tinaniba, saidai abunda yabashi mamaki shine, jin jawahir takirata da sunan mommy, to hakan yana nufin kenan tayi aure harta haihu, Kai ina wlh hakan bazata tab'a faruwa ba, kodama tafaru dole tasauya.

Kallon wulakanci tabisa dashi sannan wonda ya tabbatar masa da itad'ince ba gezau idanuwonsa kemasa ba, batareda tacemasa komaiba kawoi tajuya zata fice abunta, ji tai yarik'o mata hanu ta baya, hakan yasa tasata tareda juyowa cikin tsintsar b'acin rai zata wonka masa mari saikuma wota zuciyar tahanata, tana juyowa tnunasa da yatsa cikin b'acin rai idanuwonta harsun k'ada tace,

"Idan kasake tabani ko taba yata, uhm wlh saikayi nadamar zowanka duniya, shashashan banza, mtssssss....." taja uban tsaki sannan tajuya tafice abunta.

A zatona zanga b'acin rai a fuskarsa amma saikuma naga akasin hakan, wato dariya har saida fararan hakoransa suka bayyana,

Shafa sumarsa yai taredayin killer smile sannan yajuyo yacewa mutanensa "Let's go my guyz" tareda ficewa agaba sukuma sukabi bayansa,

Tana isa chuchu takarbi jawahir tarungumeta cikin k'auna tace "meyasa kika tafi kika tadamana da hankali jawahir" cikin murmushi tace "balloon dinane yskufceman, shine naje nakamosa" batasake cemata komaiba suka fice,

Tini motocinda zasu daukesu sun iso batan jawahir yahanamasu tafiya, danhaka suna isowa suka shiga aka fice,

MADINAH kallon jawahir tai tace "jawahir waye wonnan wonda naganki dashi kuna magana, kinsansa ne?" cikin murmushi tace "a,a mommy, balloon dinane yamak'ale a boturan rigarsa, amma yace sunansa uncle" tafad'a tareda kyalkyalewa da dariya,

Shan kunu MADINAH tai tace "karki sake zowa wurinsa kokingansa wota rana, d'an yankan Kai ne, kisa yakeyi ya yankewa mutum Kai yamutu" tana fad'an haka saitaga yanayin yarinyar ya canja alamar taji tsoro, saita cigaba da fad'in,

"Ko kinaso a yanke maki Kai kidaina ganina dasu momy chuchu?" dasauri tajuya Kai alamar a,a tace "banaso mommy" saitace "to karki sake zowa gunsa kokin sake ganinsa kinjin ko" tace eh, saita janyota ta rungume.

Koda suka iso tini tai bacci saita d'akko ta sannan suka shiga aka nunamasu masaukinsu,
2bedrooms ne da parlor sai kitchen,
   _______________________

Washe gari suka shirya cikin shigar larabawa suka fita suka zaga gari sukashiga kasuwa sukai y'ar siyayya sannan sukaje gun shakatawa sukasha ice-cream, daganan sukaje wosu wuraren daban woenda bansan ainahin abunda yakaisu ba,

Sai kusan 5pm sannan suka koma gida.

Bayan kwana biyar da zuwansu suka fara d'aukan lecture, yayinda kuma suke cikigaba da shirye shiryen fara aiwotarda abunda yakawosu.
   _______________________

_AFTER ONE WEEK_

Iya tinaninsa yakasa gano abunda yakawo wonnan yarinyar k'asar Cyprus, sannan yakasa samun nutsuwa akan shin dagaske kowa wonnan yarinyar tayi aure, kuma itace uwar wonnan yarinyar, Kai ina bahaka bane".

Saiya d'auki sigarinsa yazuka, laptop ce kan cinyarsa yana sarrafata amma tinda yafara wonnan tinanin yakasa cigaba da aikin.
  
Yana zaune yai shuu sai zukar sigarinsa yake saiga Saif yashigo a hargitse, cikin tashin hankali yace "Sir. wonnan yarinyar fa nema take taci mutuncinka, kabude TV kaga abunda ke faruwa"

Dasauri yad'akko remote yakunna TV tashar CCTV NEWS dake cikin garin na Cyprus, abunda yaganine yasa kirjinsa yafara bugawa da k'arfi..
Baisan lkcnda kalmar "lahaula..wala k'uwwata..illah billah" tafito masa a bakiba, dasauri yamik'e daga zaunenda yake sannan yamatsa kusa da TV d'in domin yatabbatar abunda yake gani yanzu gsky ne.

MADINAH ce kwonce a k'asa jikinta ba mayafi ko hijab, kafafuwonta d'auke da jini faca faca, fuskarta d'auke da shatin yakuci ko duka sannan a bakinta ma akwoi jini, hakama goshinta akwoi jini agaresa, kayanda ke jikinta sket da riga na material kanta kuma ba d'an kwali sumarta dikta barbaje, 

      A gefenta kuma cool susi ce tarike hanunta tana kuka wiwiwi tana fad'in "yacucemu, wlh yacuci rayuworki MADINAH, ya lalatamaki rayuwa, dik abunda yamaki a baya bai ishesaba saida yasake biyoki a baya yasake cin amanarki, shikenan wlh Allah ya'isa kuma sai Allah yasakamaki, bazamu tab'a barinsa yatashi a b'agas ba, Mr. AHMARD DEEDART ka cucemu, Allah ya'isa bamu yafeba" dik acikin harshen turanci take maganar,

Yayinda daga gefenta kuma y'an jaridune sunfi a kirga suna d'aukansu,

Tana gama fad'ar haka mai d'aukan rahoton na gidan TV d'in yacigaba da fad'in acikin harshen turanci "wonnan abunda yafaru kenan jiya damisalin karfe 2am na dare, wonnan dakuke gani tana mahana aminiyar Dr. MADINAH kenan, wocca Mr. AHMARD DEEDART yayiwa fyad'e a yanzu bayan fyad'enda yamata a baya a Nigeria wonda yai sanadin tasami ciki harta haifi y'a mace,

Wocca a yanzu take a babban hospital d'in dake  cikin birnin Cyprus ana kula da'ita kamin ashiga da'ita operation,

Yanzu kuma shine yasake biyota yasake mata fyad'e na biyu, to saidai anya kowa gomnatin k'asar Cyprus zasu barshi haka batareda sun hukuntasaba kowa, domin ganin sunkwatowa Dr. MADINAH hakk'inta, haka kuma zakuji cewa, k'ungiyarnan ta human rights sun k'arbi case d'in sannan sunce suna neman Mr. AHMARD DEEDART, sunaso yakawo kansa cikin gaugawa karya bari azo nemansa,

To haka kuma wosu k'ungiyayi na kare hakkin bil adama suma sunshigo acikin case d'in domin kwatarwa Dr. MADINAH hakk'inta, sbd sunce DEEDART ya aikata d'aya daga cikin manyan lefuka woenda suke fama dasu a yanzu kuma suke yaki da dik wonda ya aikata d'aya daga cikin laifikun, haka kuma sun tanadarda babban hukunci wa dik wonda aikata lefin komai girmansa kuma komai kud'insa kowaye shi kowa,

Kucigaba da bibiyarmu domin cigaba dajin yanda case d'in zai kasance" saikuma aka d'ora k'aaaton hotonsa dana MADINAH a gefensa saikuma na jawahir can daga k'asan nasu tarika teddy d'inta tana dariya.

Nan akacigaba da nuno taron dandazon mutanen dake wojen da y'an jarida daketa d'aukan abun suna magana da tambayoyi wa cool susi tana basu amsa, kamin daga bisani motar ambulance tazo aka d'auki MADINAH aka saka suka fice izowa hospital.

Daganan kuma aka d'auke aka cigaba da wosu news d'in.

Cikin b'acin rai DEEDART yadafe kansa tareda fusrta "ohhh.....shiiittttt, anya kowa yarinyar nan tanada hankaki kowa, me take nufi, so take taga baya kenan" saiya juyo yakalli Saif sannan yace "Saif woi meke faruwa ne, nakasa gane komai".


     Cikin b'acin rai Saif yace "wlh Sir yarinyar nan a shirye take domin d'aukan fansar abunda kamata a baya, kaduba yanda tai amfani da hankali wojen aiwotarwa wonnan abun, tanaso tad'auki fansa ne acikin ruwan sanyi batareda tasha wohala ba".

Zama DEEDART yai yana zare zaren ido kamar zararre, can yasake dafe kansa tareda mikewa tsaye, brain d'insa tadau zafi gaba d'aya MADINAH tajagula masa lissafi, 

" Woi harda kungiyar human right kuma" yafad'a yana kallon Saif cikin daburcewa, Saif yace "Sir. kawoi kabari muje mudakkota mujefata acikin ruwa kawoi, bcoz idan kabari kungiyar human rights suka sakaka a gaba wlh bamai kwatarka sai Allah, kakuma san yanda woennan k'asashen sukeda tsattsauran hukunci bakamar kasarmu ta Nigeria ba, ina tinanin ma shys wonnan yarinyar tai amfani da damar domin tafi daukan fansa dazafi,

Story continues below

DEEDART kam gaba d'aya yarikice hankalinsa yatashi matuka, yakasa samo mafita a yanzu.

Zama yai kan kujera yad'ora kansa akan hanun kujerar tareda saka hanunsa yadafe goshinsa, can yad'ago da jajayen idanuwonsa dasuka kada sukai zajir yakalli Saif sannan yace "dik yanda zaayi inaso kudakko man yarinyar nan tareda wonnan babyn da'akace y'ata ce, nanda 2hr nabaka".

    "Ok Sir, angama" Saif yafad'a sannan yafita, shikowa zarya yashigayi acikin parlon yana tinanin mafita, kamin daga bisani yad'auki laptop d'insa yashige ciki.
   _______________________

Acikin lkc k'ank'ane wonnan lbrn yakarad'e k'asar Cyprus harma ya'iso a gida Nigeria, y'an jaridu dik sun yad'a abun a labarun safe da dara dasukai, hakama a mujjalu dik anbuga, dik sabuwor mujallarda tafito yau d'auke take da tambarin hoton DEEDART dana MADINAH da jawahir dakuma cikekken lbrnda cool susi tabada nacin zarafin MADINAH da DEEDART yai a baya tsawon shekara biyar, dakuma irin wohalarda tasha ta kyara da tsangwama ita da mahaifinta dakuma rashin mahaifiyarta datai a sanadin wonnan iftila'in da DEEDART yajanyo mata.

Chuchu na zaune tana kallon news saigashi ansako abun, aikwa dasauri tamike tsaye tabuga tsalle taredayin ihun farinciki, harzata d'akko woya takira cool susi saita tina dik wayoyinsu anan gida suka barsu kuma akashe saita zauna tareda shafa fuskar jawahir dake bacci cikin tsintsar farinciki tace "Alhmdllh...burin y'ar uwata yana gab da cika, Mr. DEEDART saika shirya kare kanka agaban kotu kuma agaban dubban jama'a, tabbas karshenka yazo Mr. DEEDART yanzune zaka girbi abunda kashuka dakanka" saita tashi kuma tashiga kitchen.

  MADINAH na a kwonce abunta tana kallon TV cool susi nakan kujera tanashan fruit's saiga doctor Aliyu yashigo,

Doctor Aliyu Haidar, kwararren likita daga k'asar Nigeria, anan k'asar Cyprus yai karatinsa harya zama likita, hakan yasa suka rikesa suka hanasa tafiya sukace saiyayi aiki dasu natsawon shekara biyu kamin subarshi yakoma kasarsu, yana d'aya daga cikin manyan likitocinda ke koyardasu MADINAH anan school d'inda sukazoyin wonnan karatin nasu, sun had'u dashine ta hanyar Dr. Ismail daya hadasu, shine sukamasa bayanin komai tareda fadamasa abunda sukeso yamaso,

Atareda shi suka hada wonnan plan d'in kusanma shine yak'ara nunamasu yanda zasuyi domin cin galaba akan DEEDART.

Yana shigowa yamayarda kofar yarufe, dika saisuka mayarda attention d'insu agaresa, ahankali yafara magana kamar haka "am...yanzu munsanar cewa yanzu zamu shiga operation dake after 1hr zamu fito, sbd haka yanzu saikuzama cikin shiri sannan kukashe wayoyinku, saikuma woni albishir" ai sunajin haka dik suka tashi zaune dakyau,

Saiya cigaba "kungiyar human right ta wonnan k'asar tashigo wonnan case d'in, takuma bama DEEDART nan zowa gobe yakai kansa ofishinsu, sannan sauran k'ungiyayi na kare hakkin mata da bil adam sunmaka DEEDART kotu, kunga burinmu yanadab dacika dan matukar akai bincike a Nigeria aka tabbatarda gsky DEEDART saidai uwarsa tahaifi woni, dan ina mai tabbatar maku woennan kungiyoyin bazasu tab'a barinsaba harsai sunfitar wa da y'ar uworki hakk'inta, sbd hakan yazama izini ga masu hali irin nasa".

Woni irin murmushin farinciki MADINAH tai tareda furta "Alhmdllh...Allah kanunaman wonnan ranar, ranarda DEEDART zai k'ask'anta" cool susi tace "ameen, insha Allah takusa zowa, tana gab da zowa ranar" sai sukai dariya sudika sannan doctor yafita,

Bayan yafita dakamar 1hr cool susi tashiga toilet yayinda MADINAH kuma bacci yafara satarta, bata ankaraba kawoi taji anrufe mata fuska da woni abu sannan aka d'auketa tareda rufe mata baki aka tafi da'ita.

Sai acikin mota sannan suka sauketa sai mutsu mutsu take tana nema takwace amma ba halin yin hakan.

Koda cool susi tafito daga toilet sai bataga MADINAH ba, danhaka tafara nemanta, 

Story continues below

Cikin tashin hankali tafito tafice izowa office d'in Dr.

A hargitse tashiga office d'in cikin sa'a kuma shikad'aine aciki yana aiki ba kowa, cikin tashin hankali tace "Dr. wlh and'auke MADINAH, bangantaba, nashiga toilet koda nashigo sai bangantaba" ai dasauri yafita tabi bayansa cikin tashin hankali,
  ________________________

Kai tsaye katafaren gidansa suka fice da'ita, basu budemata fuskaba Saida suka kawota acikin makeken parlonsa sai suka zaunarda ita tareda bud'e mata fuska, DEEDART tagani zaune akan kujera 2seater  agabanta yana zukar sigari,

Can daga gefe kuma wosu y'ammata ne guda hud'u zaune kowacce sanye take da brez da wando iya guiwa suna shan shisha ta ainahi ba irin wocca samarin Nigeria keshaba, ta ainahin, saikuma kwalaben giya dake kan woni table.

Ahankali yataso yazo kusa da'ita yana kallonta yana zukar sigarinsa, itama kallonsa kamin tace "kadaina huroman wonnan sigarin naka mai warin kashin jaki, au dama kaine kasaka a d'akkoni, tome kake nufi, kokuma yanzu kasheni xakayi sbd kar incigaba da tonamaka asiri".

Cikin tsintsar b'acin rai yai jifa da sigarin sannan yacakumo sumarta dak'arfi harsaida tai k'ara sbd zafinda taji sannan yace "kinaso kiga bayana ko, to kisani nafi k'arfinki kuma bazaki tab'a yin nasara akainaba" yak'arisa tareda sake sumar tata, wota iriyar dariyar mugunta ta kyalkyale daita kamin tacigaba da fad'in,

"Nasara kam, kama d'auka nayita kenan akanka, koda yake ni badani zakayi Sharia ba, da human rights zakayi" saikuma tamike tsaye cikin b'acin rai taje har kusa dashi tace,

"A da kad'auka cewa Kai kad'aine mai nasara, bayan ka kwace filayen mahaifana saikuma kasake d'aukan y'ar uwata kamata fyad'e amatsayin ni sbd nice namaka laifi, saidai cikin rashin sa'a dakuma rashin sani bani bace kama fyad'e ba y'ar uwata hussaina ta wato MUNAWARAH".

Jin abunda tafad'a yasa dasauri yajuyo yakalleta cikin tsintsar mamaki, hakama saif mamakin ne yabayyana k'arara a fuskarsa, murmushi tai kwollah nazuba a idanuwonta tacigaba da fad'in "tasanadin wonnan fyad'en dakamata ne yasa tasami ciki harta haifi jawahir, ko second biyar bata karaba a duniya tarasu" kwollanda suka zubomata ne tashare sannan tacigaba da fad'in "narasa y'ar uwata da mahaifiyata alokaci d'aya, asanadin bakin cikinda kacusawa ahalinmu yasa narasa farinciki na, kwanyar mahaifiyata Saida akai tsintarta akan titi" kuka yakwace mata tashiga rerasa kodan zuciyarta tasami sauki,

Gaba d'aya guiwowinsa sun sare, yayinda tsintsar tausayin MADINAH ya mamaye zuciyarsa batareda yasaniba, ji yai kamar yaje ya rungumeta, karo na farko kenan dayafara jin tausayin wota y'a mace a rayuworsa,

"DEEDART ka cuceni, ka cutarda rayuwata, cutarworda har abada bawonda zai man irinta, kaine kai sanadin rabuwata da y'ar uwata da mahaifiyata abar k'aunata, y'ar uwata ta tafi tabarni da jinjira sabuwar haihuwa wocca batasan babu ba, kasaka kwollah kwaranya a idanun mahaifina, kamanna mana tabonda har abada bazai tab'a gogewa ba, DEEDART ka cuceni ka canza ainahin tarihin gidanmu,

     DEEDART kaine Kai sanadin zubar hawaye na tsawon shekaru dayowa, woenda a sai ayanzune zasu daina kwaranya.

Tsawon shekaru jawahir tanata tambayata waye Abban ta, waye Abban ta, iya sunanka kawoi tasani amma bata tab'a saninkaba sbd banasan tasan salinta dakuma hanyarda aka sameta sbd hakan zaizamemata bak'incikinda zai dawwama a zuciyarta, a kullum nakan tsinci kaina acikin kunci da bak'inciki wonda Kaine sila, ahaka kuma kake tinanin zan kyaleka katafi a b'agas batareda nad'auki fansaba" saita dakata tashare kwolla sannan tai murmushi tacigaba da fad'in,

  Koda band'auki fansaba tabbas ubangiji bazai tab'a barinkaba, tin anan duniya zaka fara girban abunda kashuka dan inada tabbacin ba akan y'ar uwata kafara wonnan mummunan aika aikanba, 
Shin woi kukan masu kud'in nan mekuke tinanine, kund'auka kukadaine Allah yakeso dazai baku dama kuyita aikata yanda kukeso a duniya,

A baya ka kwace gonakin iyayena sunje sunkai kararka a ofishin y'an sanda domin a kwatar masu da hakkinsu, amma sai aka tabbatar masu da bazasu iya shari'ah dakaiba sbd Koda sunyi basuda riba kaine zakaci riba,

A yanzu kuma kasaka a ranka tabbas nice da riba akanka" tak'arisa tareda yin murmushin mugunta,

Nannauyan numfashi yasauke cikin rasa abun yi, hakama saif yai shuru yai tagumi, cikin disasshiyar murya yace "yanzu wonnan yarinyar y'ata ce, nine mahaifinta" yai maganar yana kallonta, cikin shan kunu tace,

"Tabbas kowa, idan kuma bakaso ni inasan abata, sbd dama bakasan wohalantaba, cinta da shanta dakuma lafiyarta ba abunda kasani, dama kuma banasan y'ata tarayu acikin dukiyar haram, banasan aginata da mummunan tubali, 

Dan tabbas nasan Koda a hanunka ta girma ba abunda zata koya sai yanda ake zukar sigari da yanda akeshan giya, dakuma yanda ake shashanci da b'atanci, saikuma rashin tausayi da iya cin zarafin mutane da fitsara, dakuma...." Dasauri ya dakatarda ita da fad'in,

"Yaisheki haka...!!!" yai maganar cikin kakkausar murya harsaida tad'an ja da baya sbd yanda yai maganar, hayaniya sukaji a k'asa alamar kamar akwoi wota matsala, hakan yasa dasauri saif yaleka ta window domin yaga abunda ke faruwa,

Dasauri yawaigo yace "Sir. akwoi matsala, police ne sukashigo" dasauri DEEDART yad'ago cikin fargaba yakalli MADINAH, itakowa dariya ta kyalkyale daita kamin tace "ai tab'ani yanzu bak'aramin tashin hankali bane agareka, dan yanzu nafi k'arfin tinaninka" kallonta kawoi yake cike da mamaki, kanya ankara kawoi yaji ana buga kofa sai MADINAH tasake kyalkyalewa da dariya,

Dasauri Saif yaje ya bude kofar, yana budewa itakuma tana zubewa ak'asa alamar tasuma, dasauri kuma atare police d'in suka shigo dauke da bindigogi nan sukai arresting d'in DEEDART dakuma Saif, commissioner da Assistance d'insa ne agaba saikuma yaransu dasuka zo dasu kusan 25 kowonne d'auke da bindiga, saikuma Dr. Aliyu dawosu nurse's guda uku mata biyu da namiji d'aya,

Dr. Haidar kam gun MADINAH yaje dasauri tareda nurse's d'inda yazo dasu.

Cikin b'acin rai commissioner yaje gun DEEDART yacemasa cikin harshen turanci "haba Mr. DEEDART, amma wlh kabani mamaki, wonnan Sam ba halinka bane" MADINAH dake kwonce kamar tad'ago tace "tbd aikwa bakasan kowaye DEEDART bane shys kake fad'an haka".

MADINAH dauke a kwonce suka fara d'auka, sannan aka saka DEEDART da saif agaba kowannensu sanye da ankwa aka fice dasu MADINAH kuma aka sakata acikin mota domin akaita hospital.

Koda suka fito kofar gate tini y'an jaridu sun iso nan suka shiga d'auka suna tambayoyi wa DEEDART da commissioner, bawonda yasami damar tsayawa basu amsa aka saka su DEEDART acikin mota aka tada suka fice.
  ________________________

Dadyn DEEDART ne zaune aka kujera yana kallon abunda tashar Farinwata ke haskawa na kama d'an sa gudan jininsa akaje akayi har cikin gidansa tareda babban yaronsa,

Abubuwan duniya dik sun taru sunmasa yowa sun cakud'e masa, kwokwolwar ta cushe, ankama motocinsa dake d'auke da kodin dakuma d'ayar wocca take d'auke da yara mata y'an kimanin shekara goma sha takwas zowa sha tara dasukeyin safararsu izowa k'asashen woje.

Gaba d'aya hankalinsa yatashi komai ya cakude masa, koina yatab'o bawota mafita.

Momy ce tashigo parlon fuskarta babu wolwala, hakama yanayin jikinta babu alamar wolwala ko fara'a a tattare da fuskarta.

Yanayinda ta tadda dady aciki ya tabbatar mata da awkoi wota matsala, dan gaba d'aya ma baya a cikin hayyacinsa yalula acikin duniyar tinani, tai sallama tafi a k'irga amma shuru bai amsaba sbd tinaninda yake,

Ahankali tak'ariso kusa dashi sannan ta tab'asa tareda fad'in "Alhaji..." dasauri yai furgigit yadawo hayyacinsa, ganin momy yasa yasauke numfashi tareda shafa fuskarsa sannan yagyara zamansa.

Itama zamad'in tayi akusa dashi tana fuskantar sa.

Tagumi taga yayi wonda hakan yak'ara tabbatar mata da akwoi matsala, ahankali tace "Alhj. lfy kowa?" shuru yad'anyi nayan wosu seconni kamin yace "inafa lfy batool, manyan tankokina na mai da manyan motoci da ake d'akko man kayana a boda guda shida aka kama, woenda biyar d'in dik kodin da sauran kayan maye ne aciki, saikuma d'ayar dake d'auke da y'ammata da za'a kai k'asashen woje aiki, tankokina kuma guda goma sha biyar ne, tin last week aka kamasu amma yaran basu fadaman ba sai yanzu,

Nafada masu kada sufadi sunana suce nawane amma ina sunki ji saida suka fad'a, gakuma wonnan shashashan yaron DEEDART ankamasa a k'asar Cyprus yayiwa wota likita fyad'e bayan wonda yamata anan Nigeria harta haihu, yanzu kuma yasake binta yakuma sake mata woni a k'asar ta Cyprus, 

Narasa yanda zanyi batool, dik wota hanya da dabara nakasa samunta wocca zan kare kaina a lkcnda akazo kamani, dakuma yanda zan kare DEEDART agaban babbar kotin dake k'asar Cyprus".

Kwollah suka fara zubowa daga idonta tafara kuka tana fad'in "wlh Alhj. nayi dana sanin aurenka, nayi nadamar aurenka, aurenka ba abunda yajanyoman sai b'acin rai da dana sani, gaba d'aya yay'ana biyune kacal woenda Allah bai nufa sun hau kan mummunar tirbanda ka dorasuba, dik ka lalataman yara"  saita fashe da kuka tareda mikewa tsaye tafice ciki,

Shuruu yai tareda binta da kallo, a zuciyarsa yanajin tabbas abunda hajiya batool tafada gsky ne, san duniya da rud'in shaid'an yasaka idanuwonsa sun rufe da neman duniya, yakuma manta da lahirarsa,

Shafa kansa yai tareda gyara zamansa cikin tashin hankali da damuwa dakuma dana sani wonda akace k'eyace.
  ________________________

Aranar akaje dasu DEEDART kai tsaye gidan yari aka fice dasu domin atsaresu acan kamin agama bincike sannan agurfanardasu agaban alk'ali,


     .......Bayan kwana biyar da faruwar wonnan abun k'ungiyar human rights taje Nigeria a k'auyen su MADINAH wato Raha, tai kwakwaran bincike akan abunda yafaru a baya batareda kowa yasaniba, cikin ikon ubangiji babu wota matsala dik abunda suke tsammani hakan ce takasance dan saida suka sami kwararan shaidu harma saida suka rage wosu sbd sunyi yowa shaidun,

Story continues below

Lkcnda mutanen sukazo gun Abban MADINAH aka kaisu, Nan abban MADINAH yakirawo woennan tsofaffin da DEEDART yakwacewa gonaki, bayan sunzo yamasu cikekken bayanin bakinda sukazo daga k'asar woje suna bincike ne akan wonnan matsalar data faru da iyalinsa wocca DEEDART yai sanadin sakasu aciki,

Wosu daga cikin tsofaffin kuka sukafarayi sbd tino da abun dakuma tino da cin zarafin da DEEDART yamasu, nantake sukamawa bakin bayanin komai harda gonakinsu daya kwace sannan kuma suka kaisu companyn daya gina acikin gonakinsu,

Tambayoyi bakin sukamawa tsofaffin nan suka basu cikekkiyar amsa, daga bisani bayan sun sami abunda sukeso sannan sukamasu sallama suka fice izowa birnin kebbi L/gvmnt,

A birnin kebbi kowa gun Abban susi suka fara sauka sbd a bayaninda aka masu yana d'aya daga cikin likitocin babbar hospital inda aka Kai MUNAWARAH akamata operation aka cire babyn, tambayoyi ssi sukamasa akan case d'in,

Nantake yafed'e masu biri har wutsiya, tin kawo MUNAWARAH na farko lkcnda DEEDART yamata fyad'e dakuma kawota haihuwa har mutuwarta dakuma mutuwar mahaifiyar su, bayan sunsami abunda suke buk'ata sannan sukamasa sallama tareda fadamasa cewa idan zasu tafi dashi zasu tafi sbd yabada shaida agaban kotu, ba musu yamasu gdy tareda fatan nasara sannan sukamasa sallama suka fice.

Dik woni bincike dayakamata suyi Saida sukayi daga bisani kuma dazasu fice Cyprus suka d'auki abban MADINAH da doctor Abban cool susi dakuma Abban chuchu, sai tsofaffin k'auyen su MADINAH guda uku woenda aka kwacewa gonaki,

Bayan sun fice Dr. Ismail yabi bayansu tareda abokinsa Dr. Fu'ad.

Acan kuma ga chuchu ga cool susi gakuma Dr. Haidar.

Washe garin ranarda aka kama DEEDART dadyn sa yazo tareda su Neehash da momy, dasukazo dakyar dawola haula aka barsu suganshi, nanma Saida  aka dibamasu adadin lkcnda zasu gansa d'in, suna shigowa akace sutsaya a daidai kusa da woni korido haka sannan wosu police dake tsaronsa sukaje domin fito dashi, yana fitowa yaga su momy saiya fashe da kuka kamar woni k'aramin yaro.

Dasauri dady yaje ya rungumesa yashiga rarrashinsa, momy kam tsaye tai kawoi tana kallonsa, k'arisowa yai suka zauna sannan suka shigayin magana, dady nasan yamasa wota mgn amma bahali sbd ga police nan tsaye da bindigogi suna jiran time d'inda aka dibarmasu yacika su d'aukesa akoma dashi ciki,

Saiya juya fuskarsa cikin tsintsar b'acin rai yacigaba da fad'in "haba...haba dady, dagirmana da kud'ina ace nazauna acikin wonnan gidan, ba abincin kirki, ba makwoncin kirki, babu wota kulawa mai kyau, a k'asafa nake kwana abinci sau biyu kacal ake bamu, haba...haba kai ina" yafad'a yana share kwollan takaici dasuka zubomasa,

Hmm nikwa nace kwollah ai yanzu kafarayin su, hmm Allah shi kyauta kwwoi.

Dafa shoulder d'insa dady yai yana fad'in "am sorry my son, don't worry insha Allah zansan yanda zanyi domin ganin nakwatoka daga hanun woennan mutanen, bcoz Kai kanka kasani, wonnan k'asar ba kamar gida Nigeria bane, sunada tsattsauran hukunci da dokoki fiye da gida Nigeria, babbar matsakarsu kuma basa karb'an cin hanci bare nazube kud'i domin ganin na cetoka, but...insha Allah I will try my best".

Story continues below

Kallon momy yai dady yace "toke bazakice komaiba?" cikin b'acin rai momy tace "to me kakeso nace ne..." saiyace "au...bamakida abunda zakice kenan, aikwa dama nasani wlh bazanzo dakeba saidai nabarki a gida".

Tabe baki tai batareda tasake cewa komai, harya waigo zaiyi magana saiga security's d'inda ke kula da DEEDART sunzo daukansa domin komawa dashi ciki, bayanda suka iya dole yatashi suka koma yana tafiya yana waigowa yana kallon su, momy kam kasa cigaba da tsayuwa tai tafita woje, bayan anfice da DEEDART sannan suka fito suka fice izowa masaukinsu.

    Washe gari tinda sassafe dady yafita izowa neman kwararrun kauyoyi woenda zasu tsayawa d'ansa domin karesa, saidai kash dik inda yaje kuma yafadi sunan wonda zasu kare d'in sai lauyoyin suce bazasuyiba, sbd tsayawa Mai laifi irin wonnan laifin da DEEDART ya aikata babban asarace dan bazakataba yin nasaraba,

Dik yanda yaso baisamu hakan saiya nuna zai bada makudan kud'i, yana fad'in haka kawoi sai aka koresa tareda gargad'insa madama yasake tako kafarsa izowa office d'in,

Ransa gaba d'aya yabaci komai ya jagule masa, dakyar dawola haula yasamu lauya d'aya shima dakyar yasamu ya amince zai tsayawa DEEDART, aikwa dady kamar ya durkusa yama lauyan sujjada dan farinciki,
  ________________________

A b'angaren lauyoyin MADINAH dana kungiyar human rights kowa, tini suka gama hada shaidunsu, komai da komai sungama hadawa lkc kawoi suke jira yazo, 

MADINAH kowa har yanzu tana nan a hospital acewar Dr. Haidar tana karb'an magani, likitoci suna bata cikekkiyar kulawa, su chuchu da Dr. Isma'il kowa kusan kullum suna hospital d'in dan yanzu security's d'in suna barinsu sushiga sbd Dr. Haidar yamasu bayanin kosu waye agun MADINAH.
  ________________________

5th Dec 2019.......

Sai 12pm dot zaashiga kotu domin sauraron shari'ar amma tin 10am y'an jaridu da y'an gidajen TV dana radio suka iso a Curt d'in,

Hakama su chuchu tini suka iso tareda dadynta da dadyn cool susi, hakama su Dr Isma'il da abokinsa Dr Haidar dik sun iso, anan su Abban MADINAH da y'an kauyensu suka taddasu,

Koda 11:30am tai kowa ya hallara a kotin mai shari'ah kawoi ake jira.

      12pm dot mai shari'ah yashigo, nan kowa yatashi aka gaidasa yazauna sannan kowa yazauna, bayan ya zauna sannan woni yatashi yagabatarda shari'arda za'a gudanar ta MADINAH da DEEDART, wonda ake karar DEEDART dayayiwa MADINAH fyad'e har sau biyu, wonda yai sanadin tasami ciki harta haifi y'a mace.

Bayan yagama karantawa saiya juya yamikawa mai shari'ah takardar sannan yazauna, ahankali lauyoyi suka tashi suka gabatarda kansu, lauyoyi tara ne ke kare MADINAH sai lauya d'aya tareda mataimakinsa wonda yake kare DEEDART.

Security's d'inda ke kula da DEEDART ne suka shigo dashi, Saida suka kaishi har gunda ake tsayarda masu laifi ko shaidu sannan suka juyo suka sami wuri suka zauna, can nahango dadyn sa da momy dasu Deen.

Can kuma saiga cool susi tashigo tana zizo madina dake kan keken guragu ko marasa lfy, fikansu sanye suke acikin abaya baka sunyi rolling da veal din rigar, tareda kuma security's sunabin bayansu d'aya na d'auke da jawahir.

Bayan sun iso cool susi taje ta ajiye Madina gunda aka bata umarni sannan taje itama tazauna, 

Ahankali d'aya daga cikin lauyoyin dake kare DEEDART yatashi yafara tambayoyi wa Madina woenda Sam basuda kan gado, Saida baifi tambaya d'aya zowa biyu ba lauyan Madina d'aya yamike cikin zafi yafara jefa nasa tambayoyi wa Madina, nantake nasa tambayoyin suka shafe na lauyan DEEDART.

Story continues below

Bayan yagama sannan yakoma kan DEEDART wonda Saida DEEDART yakusa ya kurma ihu gaba d'aya yarikice harya fara rasa amsarda zai bada,

Tini yafara zubda kwollan dana sani yafara zomasa acikin zuciya, tareda Allah wadaran da wonnan mummunar hali daya tsinci kansa aciki.

Lauyan nacikin tambayoyi sai woni lauyan yatashi yacewa Madina kotu na buk'atar jin cikekken lbrn abunda DEEDART ya aikata mata, aikwa batareda bata lkc ba tafara bada lbrn tin farkon haduworta dashi a shataletale har fyad'en da yamata tasami ciki dakuma haihuwar jawahir, har izowa wonnan fyad'en nabiyu daya mata.

Bayan tagama sannan suka fara gabatarda shaidu, Abban Madina aka fara gabatarwa, shima kamar yanda Madina tai bayani haka yai, sannan yak'ara da fad'in "DEEDART yaruguzaman farinciki, ya ruguzaman ahali wonda har yanzu bansake samun mata kamar jab'bo ba, sbd nakasa samun nutsuwarda zan tsaya harna nemi mata nai auren" yakarisa tareda fashewa da woni irin kuka Mai cike da bantausayi.

Gdy barrister yamasa sannan yamasa izini dayaje ya zauna, daganan kuma aka cigaba da fafatawa tsakanin lauyoyin guda tara, kowanne yana fadar abunda yasani daga wonnan yazauna sai wonnan yatashi, 

Dik shaidunda sukazo Saida aka gabatardasu kuma suka Fadi iya abunda suka sani, saidai dik acikin shaidun bawonda yafadi cewa ba Madina ce akama fyad'e ba y'ar uworta ce, hakan ne kowa yak'arawa zuciyoyin y'an kallo tausayin Madina dama shi kansa Mai shari'ah.

Awa biyu kacal aka dibawa shari'ar amma Saida aka kwashe kusan 4hrs lauyoyin Madina suna gabatarda shaidu, daga karshe dai mai shari'ah yadakatardasu yatambayi lauyan DEEDART, koyanada abunda zaice ko tambaya wa shaidunda aka gabatar kokuma wa Madina, cikin in ina lauyan yana kallon DEEDART daketa faman zubda kwollah da dadyn DEEDART yafurta,

    "Non..non....no no my Lord" jin haka sai Mai shari'ah yacigaba da rubuce rubucensa domin yanke hukunci.

Gaba d'aya dadyn DEEDART zufa yakeyi dikda kowa sanyin AC dake ratsa wojen, su Neehash kowa kuka suke ssi hakama momy, tana kuka kuma azuciyarta tana Allah wadaran da mai hali irin na dady da DEEDART.

DEEDART kuka yake yana zubda zafafan kwolla, yayinda zuciyarsa take a cike da tarin bak'inciki da nadama dakuma dana sani wonda bashida amfani, abunda yafi tsana a rayuworsa yau shine yafi k'arfinsa harma yaci galaba akansa, tabbas dik abunda ka raina wotarana shine zai baka mamaki.


      ......A b'angaren su Madina kowa farinciki ne fal a zukatansu sbd ganin nasara tana tinkarosu musamman gogar Madina da Abban ta dakuma su cool susi,

Bayan yan rubuce rubucen da Mai shari'ah yai woenda suka d'auki kusan 15mnts, can sannan yad'ago ahankali yafara magana kamar haka acikin harshen turanci "Uhm...am bayan sauraran jawabai daga bakin lauyoyi dakuma sauraran bayanai daga bakin kwararan shaidu, wonda hakan ya tabbatarda cewa tabbas Mr DEEDART ya aikata abunda ake tuhumarsa, hakan yasa kotu tayanke masa hukunci kamar haka,

Zaibiya naira million goma sha biyar na fyad'enda yayiwa Madina har sau biyu kokuma zaman gidan kaso natsawon shekara talatin, saikuma naira million shida wonda tai d'awainiya da y'ar sa tin tana ciki harta fito woje hartasakata school tin nursery School up to primary, kokuma zaman gidan kaso na tsawon shekara ashirin, saikuma tarar naira million tara da dubu d'ari wonda kotu tacisa sbd laifinda ya aikata kokuma zaman gidan maza na tsawon shekara goma, muna fatar wonnan zai zama izini wa sauran mutane dakuma masu hali irin na Mr. DEEDART,

Da wonnan kuma muka kawo karshen wonnan shari'ah...." saiya buga gudumarsa sannan yamike a tsaye nan kowama yamike Saida yafita sannan kowa yakoma ya zauna.

     "Alhmdllh..." tafurta tareda rufe idanuwonta sannan tabudesu, ji tai woni sanyi yaratsa zuciyarta dama gangar jikinta gaba d'aya,

Dagudu cool susi da chuchu sukazo suka suka rungumeta cikin tsintsar farinciki, cikin dariya tace "yau burina yacika, na tabbata y'ar uwata da innata farinciki zai rizk'esu har acikin kabarburansu, yau zanyi kwanan farinciki nacika burina na daukarwa y'ar uwata fansa, gakuma ribar y'ata da tarin dukiya a hanuna, tabbas ubangiji shine abun gdy" cikin fara'a suka furt,

   " Alhmdllh....Allah Kaine abun gdy" atare sannan suka sake rungume juna yayinda jawahir take makale a jikin chuchu tana bacci,

A gabansu aka fice da DEEDART izowa gidan kaso, yana kallon Madina yana murmushi kwollah nazubar masa, itakuma tana kallonsa cike da tsintsar tsana, Saida yakure yadaina hangota sannan yabar kallonta,

Atare suka fice izowa gunsu Abba nan taitayiwa su dady gdy, hakama abbanta gdy yadinga masu akan kokarinda sukai naganin sunbada cikekkiyar shaida domin kwatowa yarsa hakk'inta, 

Daganan bayan angama komai suka tattara suka fita woje domin ficewa zowa shirye shiryen tafiya gida, Koda suka fito y'an jaridu da dik wota tafa tasada labarai tana a wojen suna jiran fitowar Madina ne, aikwa Nan sukayo caa da tambayoyi, wosu takan amsa wosun kuma bahali sbd cinkosa yai yowa ssi,

Dakyar Saida akahada police sannan suka samu hanya sukashiga motoci suka fice.

Daren ranar yau acikin tarin farinciki Madina takwana, har yanzu tana a hospital kamin DEEDART ya tattaro mata kudinta.

Bayan kwana uku kacal dayanke shari'ah aka turomata makudan kudinta acikin account, washe gari suka tattaro suka dawo gida Nigeria zuciyoyin su cike da tarin farinciki..

Post a Comment for "CONEL AHMARD CHAPTER 2"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...