Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

BATUUL CHAPTER 8

BATUUL CHAPTER 8

- - Post a Comment
BATUULCHAPTER 8

Yana ─Ćaukan wayan ya hau ta da bala'i, "wai ba nace miki zaki iya tafiyar ki bane, wat are yhu still waiting for, in kuma ke da amaryar za a kai sai inji", kashe murya tayi cikin salo tace mishi "Babe na wuce fa tun ranan da kace min in koma, naga ko sau ─Ćaya baka nemeni ba shiyasa na k'iraka yanxu tunda ni ina sonka ya na iya da halinka", kallon screen din wayar yyi, sae a snn ya lura da international Number ma ta kirasa, jin yayi shiru bai ce mata komai bane yasa taci gaba da cewa "Babe am missing you, wai yaushe zaka dawo ne, am so lonely without you here", d'an ajiyar xuciya ya sauke yace "soon, i gat things to do over hear, i will be back immediately when am done dear", ssae taji ddin abinda yace mata, cikin muryar shagwaba tace "Aii baby, i will be waiting, take care of yourself, i will also do that for you, bari in barka ka huta", da haka ta katse k'iran tayi wani murmushi a ranta tace zaka shigo hannu ne vry soon, baza ma ka samu k'afar zuwa Nigeria bama nan gaba bare har kaje kaqi dawowa har ka mance ni na kwanaki, wani irin dariya ta saki da ta tuna irin tanadin da takeyi a kanshi, shi kam lumshe ido yayi bayan sun gama wayan, aman da Batuul tayi mishi ne ─Ćazu scene ─Ćin ke dawo mishi kamar yanxu abin ke faruwa da yadda yaji jikinta yayi zafi lokacin da ya rik'eta, bu─Će idanunshi yayi ya mik'e ya nufi toilet yin alwalan sallar Isha don bai ma jin yau zai iya fita masallaci, yana fitowa daga toilet ─Ćin Farida ta turo k'ofar ─Ćakin, harara ya watsa mata yace "sallama ne baki iya ba ko knocking da zaki shigo min ─Ćaki kai tsaye", dariyan dake cikinta ta mayar dan tun lokacin da taji Batuul tayi mishi amai da ta tuna take k'yalk'yalar dariya, tasan halinshi na k'in amai, maida dariyar tayi da sauri ganin yana k'ok'arin tada sallah tayi maza tace "Yaa Abu", bai amsa bama bare ya juyo ya dubeta, sake k'iran sunanshi tayi tace "Yaa Abu", tayi shiru ba tare da tace mishi wani abun kuma ba, wani mugun kallo ya jefeta dashi yace mata "fita min a ─Ćaki", da sauri ta juya zata fita, ta tsaya daga wajen k'ofa ta lek'o kanta tace "Ammah ke nemanka fa", tana kaiwa nan ta fice da sauri tana dariya, sai da ya idar da sallah tukunna ya fito, a ─Ćakinta ya tarar da ita Farida na daga gefenta, harara ya sakar mata ganin ta kafa mishi ido, daga gefe ya zauna yace "Ammah gani", dubanshi tayi tace "sae yanxu kayi niyyan zuwa kenan, toh abinci zaka kaiwa Batuul a asibiti, maza kuje tun ─Ćazu aka gama na tura a k'ira ka baka ga daman xuwa ba", ido ya rintse tun da yaji inda zashi har sai da yaji tayi shiru tukunna ya bu─Će yana kallonta yace "Ammah ba driver na nn ba, wllh kai na sarawa yakeyi, ko Sadiq sai ya kaita in ma drivern bae nn kinji Ammah na", Ammah tace "bakaji inda nace zaka bane, in kaje kace su baka magani a can ─Ćin, tashi kaje kar ku b'ata lokaci", mik'ewa yayi jiki a sanyaye ya koma ─Ćauko key ─Ćin mota, shi baisan mesa Ammah ke yi masa hka kan yarinyar nan ba, k'wafa yayi tunawa da yayi da aman da ta mishi daxu ya ─Ćau key ya fito, a wajen parking ya tarar da Farida da masu aikinsu su biyu rik'e da basket ─Ćin abinci, daga jikin makullin ya bu─Će musu k'ofa suka saka kayan daga baya shi kuma ya shige gaba hka ma Farida, sai harararta yake, itadai bata ce mishi komai ba har suka fita gidan, k'ira'ar Shuraim kadae ke tashi a motar.
+

Bayan nurse da cleaners ─Ćin sun fita Aunty ta taimaka mata tayi wanka ta saka kayanta mara nauyi da ta kawo mata, tea Aunty ta ha─Ća mata tasha ta kwanta, tana kwanciya bacci ya dauketa, gyara mata kwanciyanta Aunty tayi ta gyara mata bargon sannan ta jawo kujera ta zauna gaban gadon ta zubawa y'ar tata ido tana tausayin halin da zata shiga, turo k'ofar ─Ćakin akayi, Yayya ta shigo Ahmad a bayanta, ganin wa─Ćanda suka shigo ─Ćakin yasa Aunty ta ─Ćauke dubanta daga kallon k'ofar, k'arasawa cikin ─Ćakin sukayi, daga gefen Batuul Ahmad ya tsaya zuciyarshi fal da tausayin y'ar uwarshi, rashin lafiyan kwana ─Ćaya har ta rame, Aunty ya duba yace "Aunty yaushe sukace zasuyi discharging ─Ćinta?", ya fa─Ća yana ─Ćan tab'a goshinta yaji temperature ta, Aunty tace "Yanxu doctor ya shigo ya duba ta, ta samu tayi amai, amma baice min yaushe zai sallametan ba", da jimami Ahmad ya sake cewa Aunty "Aunty wai mey ke damunta, meye doctor yace muku na damunta all of a sudden", caraf Yayya dake tsaye bakin window tana k'ok'arin ─Ćaga labule kamar an sata ta karb'e maganan da cewa "mey ko zai sameta, daga na ce mata za a ha─Ća aurenta da yaron nan yaron kirki Abutturab shine fa ta tada hankalinta har da rashin lafiya, ko xuga ta uwar tayi oho", jin abunda Yayya ke fa─Ći ya dubi Aunty da mamaki yace "Aunty aure kuma, wai hakane dagaske?", "Au k'arya zanyi maka, toh tambayi uwar taka da bata k'arya sai ta fa─Ća maka gaskiyan zancen, kuma ko nayi rantsuwa baxan yi kaffara va, ita ke da─Ća ingiza ta har aka kwantar da ita asibiti", Ahmad da ranshi ya fara b'aci jin tana aibata Aunty yace "Keh Yayya nifa bake na tambaya ba", "ehh ai nima ─Ćin nasan ba ni ka tambaya ba, amsa ce na baka don nasan ba baka xa suyi ba", Aunty dae ko kallon inda suke bata yi ba dan ita tunaninta daban takeyi, Ahmad yyi tsaki yace "kinga zo mu koma, dama Baba cewa yayi in kawoki ki ganta mu koma, toh tunda ba ma dubatan zakiyi ba kizo mu wuce, dan ni in na tafi sai dai ki nemi mai dawo dake", masifa ta shiga yi ganin yayi hanyan k'ofa yana cewa Aunty zai tafi, Allah ya bawa Batuul lafiya, binshi tayi a baya tana ta zazzaga mishi ruwan bala'i har tana cewa sai tasa an karb'e motar ya dena tuk'awa tunda wulak'anci ne abun, suna fita Aunty ta tashi ta gyara windown da Yayya ta bu─Će, wayan Batuul da ta taho mata dashi ─Ćazu ne ya fara ringing, mik'ewa tayi ta ─Ćauki wayan, ganin mai k'iran yasa ta maida ta ajiye.

STORY CONTINUES BELOW


Sai dare Batuul ta tashi lokacin har an idar da sallah magrib, da taimakon Aunty taje tayi alwala tayi Sallah, Ce mata Aunty tayi bari in shiga office ─Ćin doctor, tun ─Ćazu yake nemana kina bacci shiyasa ban fita ba, Aunty na fita wayanta dake ajiye gefenta yayi ringing, da kamar baza ta ─Ćaga ba ganin mai k'iran yasa ta ─Ćauka lokacin har ya kusa katsewa, a hankali murya can k'asa tace "Hello", wani irin ajiyar zuciya ya saki jin muryanta, shima murya kaman ta mai damuwa yace "Habibty dont do this to me again kinji, i was so worried abt you, tun jiya nake k'ira you werent picking, do you know how this affected me", shiru tayi tana saurarenshi idonta ya cicciko da hawaye tana tuna abinda Yayya ta fa─Ća mata jiya, jin tayi shiru ta kasa magana yasa yace mata "you there", kasa mishi magana tayi sai kukan da ta fashe mishi da, har cikin ranshi yake jin kukan nata, ki─Ćimewa yayi ya shiga tambayanta "Fatima mey ke damunki, ki daina kuka and tell me whats wrong with you, you are making me distressed, kina inane i will come right away...", da k'yar ta samu ta saita kukan nata tace mishi "Na'am", cikin shesheka, with so much concern yace mata "Its okay stop crying and tell me whats wrong with you kinji", har muryanshi na rawa, murya can k'asa tace mishi "I was sick", mik'ewa yayi tsaye daga zaunen da yake yayi hanyan ─Ćakin Mummynshi, tambayanta ya shiga yi "mey ke damunki Fatima, kuma kina inane", a hankali tace mishi " Nima ban san mey ke damuna ba, I was admitted a asibiti tun jiya", ce mata yayi "Its okay, you will get better soon kinji, i will b on my way right away, take care of yourself", har ya katse wayan sai ya tuna ashe baima tambayeta wane asibiti bane, sake kira yayi ta fa─Ća mishi asibitin da aka kwantar da ita, da haka ya katse k'iran ya karasa ─Ćakin Mummy, zaune ya tarar da ita akan abin Sallah, zama yayi daga bakin gadonta yana jira ta gama azkar ─Ćinta tukunna ta juyo ta dubeshi tace "Babana dama kana gida baka fita ba, ya akayi naga duk ka zama wani iri, what is it", ce mata yayi "Mummy Batuul, i mean Fatima ba lafiya, yanxu haka tana asibiti a kwance, Mum ki shirya muje mu duba ta kinji Mum", kallonshi take yadda ya rikice yana mata magana, bata tab'a ganinshi ya damu akan wata mace kamar haka ba, kanshi ta shafa tace "jeka canja kaya ka ─Ćauko key kazo mu tafi", da hanzari ya mik'e ya fita, girgiza kai tayi tana addu'an Allah yasa son Batuul ya zame mishi alheri ta cire Rigar sallah dake jikinta ta shirya tafiya asibitin da ─Ćanta.
Batuul na gama waya zata ajiye taga an turo k'ofar ─Ćakin, a zatonta Aunty ce ta shigo, Farida ta gani bakin kofar rik'e da Basket a hannunta, Murmushi ta saki tana kallonta, ba shiri murmushin dake fuskanta ya bace ganin wanda ke tsaye bayan Farida, sunkuyar da kai tayi da sauri, farida ta karaso ta xauna gefenta murmushi dauke fuskarta har lkcn tace "Waow Besty, I can see yhu are getting much beta ynxu, ga abinci na kawo maki, ur favourite!" Batuul tayi murmushi sae dae bata ce komae ba don ita ko kadan bata ji ddin dawowan Abuturrab ba, karasowa cikin ward din yyi ya ja kujera ya xauna fuskarsa a daure, farida ta sauka daga gadon ta nufi basket din abincin don dibar mata farfesun da tayi mata, Batuul ta kalleta tace "Don't wrry dear, am okay ynxu, bn dde da cin abinci ba, ltr sae in ci, hope yhu are spending d nyt here?" Farida ta wara ido tace "Y not love, ae da shirin kwana dama na xo" wani harara Abuturrab ya watsa mata yace "Ki gama abinda xa kiyi mu tafi, dnt waste my tym" Bata fuska farida tayi tace "but Ya Abuu Ammah fa ce tace in kwana wllh" mikewa yyi kmr xae maketa yace "Tafi mota ki jira ni" kuka ta saki, ganin ya yo kanta ta fice da sauri daga dakin, juyawa yyi yana kallon Batuul ya galla mata harara yace "C'mon sense din ki bae baki cewar hakurin filthy abinda kika min a jiki daxu ya kamata ki ban ba" ganin taki kallon inda yake bare ya sa ran amsa yasa ya karasa inda take yana mata wani irin kallo, bude kofar dakin aka yi Anty ta shigo, da sauri ya koma baya, Anty ta karaso cikin dakin ya juya kai a kasa ya gaisheta, amsawa tayi d'aga hka ta nufi inda wayarta yake ajiye ta dauka ta fita, Batuul ta dauki wayar ta da ya soma ring a gefenta ta dauka ganin me kiranta, "Hello love gani a hospital din ban san ward din da ku ke ba" satan kallon Abuturrab tayi ta ga idonsa kyar a kanta, ta sunkuyar da kai tare da dauke kai, a hnkli ta gaya masa ward nmbrn da take, snn ta katse wayar ta ajiye, shi kam har lkcn bae bar kallonta ba xuciyarsa na tafasa ganin ynda ta ki ko da kallon inda yake, Anty ce ta kuma dawowa dakin da mamaki take kallonsa tace "ga kujera Abuturrab, ya da tsayuwa" murmushi ya kirkira yace "Tafiya xan yi Anty" Batuul ta kalli Anty a hnkli tace "Anty Abubakar ya xo wae yana waje, na gaya masa ward nmbr" kallonta Anty tayi xata yi magana aka tura kofar dakin, kansa a k'asa ya shigo da sallama mum dinsa na biye da shi a baya, da fara'a Anty tace "A'ah sannun ku da xuwa" Kallon Abubakar kawae Abuturrab ke yi ko kiftawa bae yi, Anty ta ajiye ma mum dinsa kujera ta xauna tana kallon Batuul tace "Sannu Fateema, ashe baki ji ddi ba" Batuul da kanta ke k'asa ta dan yi murmushi cike da jin kunya tace "Ina yini Mama" Matar ta fa'da'da murmushin fuskarta tace "Lfya lau Batuul ya jikin?" A hnkli tace "Da sauki" tace "Allah ya sauwake" har k'asa Abubakar ya kai ya gaida Anty ta amsa murmushi dauke fuskarta tana tambayarsa ya aiki, yace "Alhmdllh Mumy" mikewa yyi yana kallon Abuturrab dake kallonsa har lkcn ya mika masa hannu, Abuturrab ya sunkuyar da kai suka yi musabaha, snn Abubakar ya juya yana kallon Batuul sae dae taki kallon inda yake, sae a snn Abuturrab ya ga daman gaida Mahaifiyar Abubakar ta amsa da fara'a, Mikewa Mumy tayi daga karshe ta nufi gun Batuul ta ajiye mata ledan hannunta tace "Toh fateema Allah ya kara lfya kin ji" Batuul tace "Ameen ngd Mumy" Mumyn ta kalli Anty tace " Hajiya ni xan koma Allah ya sauwake" Anty tayi mata gdya ssae, Abubakar yace "Momy ki jira ni gani fitowa ynxu" dariya Mahaifiyar tasa tayi tace "Dama ae xan jira ka" d'aga hka Anty ta rakata suka fita ward din, Batuul ta sace kallon Abuturrab ta ga kallonta yake, ga Abubakar da duk ya kagu ya fita ya basu waje da Habibtyn sa.Daga gaban gadon Abdallah ya tsaya a tunaninsa Abuturrab xae basu waje sae ya ga otherwise, don kujera gogan ya ja yyi xaman sa yana facing dinsu, Abubakar na ganin hka ya xauna gefenta ya shiga mata magana murya can k'asa da damuwa, Batuul ta k'asa ─Ćago kai ta kalleshi, sake matsowa yayi kusa da ita yace "Habibty tok to me mana, mey doctor yace na damunki", a hankali kamar bata son aji mey take fa─Ći tana wasa da fingers dinta tace "nima ban sani ba, but i think doctor ya fa─Ćawa su Aunty, ni ban sani ba", ta k'arasa maganan tare da ─Ćago kanta, ido hudu suka yi da Abutturab dake kallonta ko kiftawa bae yi, ya watsa mata wani irin kallon da ya sata saurin sadda kai, haka Abdallah yaci gaba da yi mata tambayoyi da yi mata sannu da damuwa, bata cewa komai daga "um", sai "um um", banging k'ofa suka ji suka juya, Batuul ta sauke ajiyar xuciya ganin shi ne ya fita, juyowa Abdallah yayi yace "Habibty who is he? your uncle", girgiza kai tayi tace mishi "brother ─Ćin Farida ne", juyawa yayi ya sake kallon k'ofan sannan ya mik'e tsaye yace " Shknn Habibty i will b going, Mum na mota tana jirana get well soon, i will b back tomorrow in'sha Allah", yayi mata wani lallausan murmushi da itama maida mishi, daga haka ya fita yana waigen ta, a bakin k'ofa ya tarar da Abutturab na waya, tsayawa yayi ya gama wayan su yi sallama, ganin ya kusa minti biyar tsaye kuma ya ki k'are wayar yasa ya ─Ćaga mishi hannu ya wuce, Abuturrab na ganin ya wuce ya katse wayan ya tura k'ofar ─Ćakin, hawayen dake idonta take gogewa da tissue, tsayawa yayi yana kallonta daga bakin k'ofa, snn ya shigi tare da tura k'ofan ya rufr, jin k'aran k'ofan ne ya sata ─Ćagowa da sauri, duk da rashin k'arfin jikinta hkn bai hanata mik'ewa cikin sauri tayi hanyan toilet ba, da gudu taje zata bu─Će k'ofan, taji ya fixgota, tsayawa tayi a wajen ta kasa motsi gabanta na faduwa, ya juyo da ita yana kallon yadda ta rintse ido hawaye na zubowa, fuskanta ya tsura ma ido da ─Ćan k'aramin lips ─Ćinta da ya koma ja, hannunshi ya ─Ćaura kan kafa─Ćunta ya matso da ita gabanshi yana kallonta da kyau yace "waye shi?" Kin cewa komae tayi har lkcn idonta a runtse, ya daga kafada yace "As if i care, kina jina dama Aunty na shigowa ki ce mata kin warke a maidaki gida kuma ke kina da wanda kike so, nasan wannan da yazo ya saki gaba yana miki surutu kmr radio saurayinki ne, toh dama kice musu shi kikeso kuma keh shi zaki aura, is dat clear?", sai da taji yayi shiru har lokacin tana hawaye ta bu─Će ido a hnkli tace "kai mey zai hana ka fa─Ća musu, kaima ai kasan su kuma zaka iya samun su ka fa─Ća musu kace kana da matarka basai an sani aurenka ba dan ni bbu abinda xanyi da mai mata, sabon jini dama ai sai sabo, mey ma zanyi da......", ganin yadda ya zuba mata lumsassun idanunshi yasa ta maida sauran maganan tana gogewa hawayen dake fuskanta, bin fuskanta yayi da kallo har idonshi ya sauk'a kan k'irjinta dake ta heaving, dariya abun ya bashi amma ya dake, yasan duk maganan da tayi a tsorace take, saketa yayi yana mata wani irin kallo yace "Really?, Fine then, zamu ha─Ću ne tun da bakiji abinda na fa─Ća miki ba, ki yadda ayi auren, xagi gane mai mata kuma tsohon jini kika aura yarinya", yana kaiwa nan ya juya ya fita daga ─Ćakin, a nan wajen ta tsuguna ta sa kuka kamar wacce aka aikowa lbrn mutuwa, a nan Aunty ta shigo ta sameta, da gudu Aunty tazo ta ─Ćagata tana tambayanta mey ya sameta, kasa magana tayi sai kukan da take tayi, Anty ta maida ta kan gado ta rungumeta hankali tashe tana lallashin ta, a nan tayi bacci jikin Aunty.


+

  11 o'clock bayan doctor ya dubata yayi discharging ─Ćinsu akan zai na zuwa har gida yayi mata alluranta da suka rage sannan yace a guji duk wani abu da zai rik'a b'ata mata rai kuma kar a rik'a fa─Ća mata maganan da bata expecting har ya rik'a shocking ─Ćinta tana zama unconscious, Baba ne yayi magana yace zasu kiyaye, da haka suka yiwa doctor sallama, suna komawa gida tace ita baza taje ─Ćakinta ba a ─Ćakin Aunty zata zauna, wanka tayi bayan ta shiga ─Ćakin sannan ta kwanta, ba ita ta tashi ba sai k'arfe biyu, tayi alwala ta tada Sallah, tana idarwa Aunty ta shigo rik'e da tray a hannunta, ajiyewa tayi ta zubawa Batuul abinci sannan tace mata ta sauk'o taci, da kyar taci ka─Ćan tace ta koshi,  STORY CONTINUES BELOW


       Da yamma wajen k'arfe biyar tana zaune tana kallon E.tv Aunty na ha─Ća kayan Aabid Baba ya shigo ─Ćakin, kan gadon da Batuul ke zaune ya zauna, tashi tayi zata sauk'a ta gaisheshi yace mata "Yaanyi" (Mamata), ─Ćagowa tayi ta kalleshi da idonta da ya fara kawo ruwa, hannu yasa ya goge mata hawayen ya matso da ita jikinshi ya fara mata magana kamar haka "Ya jikin ki Batuul", jiki a sanyaye ta amsa mishi da "Alhamdulillah Baa, yayi sauk'i, na warke yanxu", yace "Masha Allah, har yanzu kinason zuwa Uk kiyi karatun?, ya tambayeta yana kallonta, ─Ćagowa tayi ta dubeshi dan ta tabbatar da abinda taji yana fa─Ća mata, ganin dagaske yake da sauri ta shiga gya─Ća kai ta da─Ća rungume shi, tasan dama babu wani aure da za ayi mata kawai Yayyace ta fa─Ća, ce mishi tayi "ehh Baa inaso" murmushi ─Ćauke fuskanta, murmushin yayi shima yana shafa kanta yace "toh zan samo miki admission sai kije kiyi karatunki kinji ko, ai zakiyi karatu sosai ko?", kanta ta gya─Ća har lkcn murmushi shimfi─Će fuskanta har yafi nada, cewa tayi "Baba toh yaushe ne za ayi, ko sai na gama semester ─Ćinnan sai inyi transfer", ta tambayeshi tana jiran jin mey zaice, Aunty dake aikinta tana jinsu ta saki dariyan takaici dan tasan so kawai Baba yake ya shawo kan Batuul dan yasan tana son karatu sosai, zata iya hak'ura da komai dan tayi achieving dream ─Ćinta, Babane yace "very soon Mamata, amma kinsan mey nakeso dake", kai ta girgiza mishi yace "yawwa, kinga dama bana son zaman hostel, ko", nanma kai ta gya─Ća, yace "toh kinga sai kiyi zamanki tareda Yayanki, nasan sosai zai kula dake", kanta ne ya─Ćaure ta fara tunanin wane Yayan kuma, ce mata yayi "nasan tunanin wane yayen kike, Abutturab nake nufi", wara ido tayi ta kalli Baba tana girgiza kai tace "Baa toh zan zauna inyi a gida na fasa wllh, bana son zuwa," hawaye cike idonta ta kare maganar "k'ara janyo ta yayi jikinshi ya goge mata hawayen dake  zuba a idonta yace "ki kwantar da hankalinki kinji Batuul, nasan anytime you will be proud of whatever decision i made, nasan Aliyu tun yana k'arami, nasan abunda zai iya da wanda bazai iya ba, ki kwantar da hankalinki kinji, kuma auren da Yayya ta fa─Ća miki gaskiya ne", sosai ta shiga kuka harda sheshshek'a" muryarta na rawa tace "Baba nifa yarinya ce, just last month na cika 18, kayi hak'uri in na girma sai kayi min ko da waye ma kaji Baa", dariya maganan nata ya bashi yace "Batuul akwai Babba ne da k'arami a bautar ubangiji, babu, toh kinga ina laifin tun kina k'arama ki fara bautawa ubangijinki, kinga ladanki nema zai k'aru, ga kuma ladan da zaki samu na yi mana biyayya, ko ba kya so", ya tambayeta yana kallon fuskanta dake ta ambaliyan hawaye, kasa cewa komai tayi, ci gaba yayi da mata magana yace "toh mamata y dont you start it early and be rewarded abundantly, tunda at any point zakiyishi its better you do it now, and am assuring you Abu will b d best husband we will ever recommend for you, Nida Babanshi have been good friends for over 30yrs, har gida yazo ya sameni ya nemawa Aliyu aurenki, duk mutumin da yaso jininka har yaso ha─Ća zuriya dakai yafi k'arfin wulak'anci, kinga ba da─Ći ince musu a'a, sosai yake ganina da mutunci, friendship ─Ćinmu da muka gina based on trust yafi k'arfin ya nemi abu a wajena in hanashi", jikinta ne yayi sanyi sosai, ─Ćagota yayi yana kallon fuskanta yace "Ko in koma ince musu kince bakya so", a hankali ta girgiza kanta alamar a'a, yace "yawwa Mamana Allah ya miki albarka, yanxu ki share hawayenki ki rok'i Allah ya tabbatar miki da duk alherin dake cikin bikin nan", haka ya dinga bata baki yana kwantar mata da hankali har yasa Batuul ta hak'ura, sai da aka k'ira magrib tukunna ya fita daga ─Ćakin ya tafi yin Sallah.


Washegari misalin goma na safe Abuturrab na kwance falo kan 3sitter abun duniya ya taru yyi masa yawa ganin ynda Ammah ta dage sae Shirye shiryen aurensa take ba ji ba gani, Ammah ce ta shigo falon ya mike xaune ganinta, da fada ta fara magana tace "anya kuwa Abuturrab kana son gamawa da mu lfya, tun jiya ina bin ka ka je gida ka duba yarinya an sallamesu ka ki xuwa?" Sakkowa k'asa yyi da sauri yace "Don Allah kiyi hkuri Ammah, ynxu nake son shiryawa in tafi wllh" bae jira cewarta ba ya mike ya nufi stairs, cikin mintunan da basu wuce goma ba ya sakko sanye da kananun kaya yana rike da makullin mota, cikin falon ya karasa yana kallon Ammah yace "Xan tafi Ammah" ta d'an sake fuska tace "Toh Allah ya tsare, kuma saura ka je masu empty handed, don nasan ba kai ya isheka ba"  murmushin karfin hali yyi ya fita daga falon, parkin space ya nufa ya dauki motar da xae dauka ya bar gidan rae ba ddi. A waje ya bar motarsa ya fito ya shiga gidan, har xae danna bell ya fasa ya murda kofar a hnkli ya ji sa a bude, turawa yyi ya shiga falon da sallama, bbu kowa falon sae kamshi me ddi dake tashi da sanyin Ac, da alama duk yaran gidan sun tafi makaranta, ya karasa cikin falon ya xauna kan kujera, motsin da yake ji a kitchen ya sa shi sanin da mutum, ba a dau lkci ba ta fito rike da bowl din fruit salad da alamar lkcn ta hada ganin ynda taje jujjuya shi, sanye take da d'an mini skirt da top, ta bar gashinta in a messy bun s, cak ta tsaya tana kallonsa gabanta yyi mugun faduwa, shima kallonta yake daga sama xuwa k'asa, mikewa ta ga yyi, bata tsaya wani tunani ba ta nufi sama da gudu, yyi kwafa ya koma ya xauna, ya kusa awa daya xaune falon masu aikin gidan sae kai komansu sake bae ce su kira masa kowa ba,  Anty ce ta sakko don shiga kitchen ta daura girkin rana da masu aiki ganin sha biyu ya kusa, da mamaki take kallonsa tace "A'a Abuturrab, yaushe ka xo" ya sunkuyar da kai yace "Ban jima ba Anty, ina yini" tace "Lfya lau, maimakon ka aika su fa'ixa su kira mu" murmushi kawae yyi bae ce komae ba, Anty ta nufi kitchen fa'ixa na biye da ita a baya, sae da suka shiga kitchen din snn tace "Tafi ki kira Batuul" juyawa tayi ta fita daga kitchen din. Batuul na kwance dakin Anty sae dae ban da faduwa bbu abinda xuciyarta ke yi, da ta tuna maganganun baba sae ta ji hawaye ya sakko mata, ynxu shknn hka tana ji tana gani xa a aura mata Ya Abuu, fa'ixa ce tayi knocking, ta share hawayen fuskarta tayi mata ixinin shigowa, fa'ixa ta ba ta sakon Anty snn ta fita, mikewa xaune tayi jiki a sanyaye.Jiki a sanyaye ta mik'e ta fito daga ─Ćakin ta sakko downstairs, ganinshi zaune a palo yasa ta jin da─Ćin kimonon  da ta ─Ćaura kan kayan dake jikinta, ─Ćauke kanta tayi kamar bata ganshi ba tayi hanyan kitchen, da ido ya bita har ta shige tukunna ya ─Ćauke idonshi daga wajen, tana shiga tace "Na'am Aunty, gani", tray da aka cika da snacks iri iri sai drinks da ruwa Aunty ta nuna mata tace mata "─Ćauki ki kaiwa Abuu", da sauri ta ─Ćago zuciyanta sai fa─Ćuwa yake tana kallon Aunty dake ta aikinta tace "Aunty ni kuma", ba tareda da ta juyo ta kalleta ba tace "ehhh ─Ćauki ki kai mishi tun ─Ćazu yake zaune ban sani ba kuma babu wanda ya fa─Ća min", zuciyanta duk babu da─Ći har  idonta ya fara hawaye ta matsa gaban Island ─Ćin ta kinkimi trayn tayi waje, tunda ta fito yake kallonta har ta iso palon, ─Ćan nesa dashi ta ajiye mishi trayn fuskarta daure ta juya tayi tafiyarta, murmushi yyi ya ci gaba da kallon tv da yake, kitchen ─Ćin ta koma ta tsaya bata cewa kowa komai ba ta hau kan deep freezer ta zauna, juyowa Aunty tayi zata cewa Janet ta mik'o mata abu a Fridge taga Batuul zaune kan Fridge, kallonta Aunty ta tsaya yi da mamaki tace "Batuul meye hakan, mey kika dawo yi kika barshi shi ka─Ćai a palon", kanta ta girgiza tana kallon Aunty tace "Aunty toh ai abinci zai ci kuma ma nifa.....", bata k'arasa ba ganin kallon da Aunty keyi mata ta sauko tace "kiyi hak'uri zanje", ta juya jiki a sanyaye ta fita daga kitchen din, da k'yar take ─Ćaga k'afanta har ta isa palon, yana nan inda ta barshi yana kallonn Discovery channel, sau ─Ćaya ya ─Ćaga kai ya kalleta ta sadda kai k'asa tana ta fidgeting yatsunta, ya ─Ćauke kai yaci gaba da kallonshi har ta k'araso ta zauna can nesa dashi, lokaci lokaci yake satan kallonta ita ma hka, sai da programm ─Ćin ya k'are tukunna ya dubeta, ta sadda kai k'asa tana wasa da yatsunta, sauk'a yayi daga kujeran ya janyo trayn yana kallonta murya can kasa yace "Baki fa─Ća musu sak'ona ba knn har ynxu koh?" Kin cewa komae tayi kuma bata d'ago kanta ba, kallonta ya tsaya yi, ta dan sata kallonsa jin shirun yyi yawa, suka hada ido ta dauke kai da sauri, kallon hanyar kitchen yyi kafin yyi kwafa ya dauki glass cup ya bude lemon kwalin dake kan trayn da ta ajiye masa ya tsiyaya ya mayar ya rufe, ba tare da ya kalleta ba yana girgixa kai cikin sanyayyan muryarsa yace "Ni tausayin rayuwar ki da nake yasa ki ka ga ina maki kashedin kar ki yrda su makala min ke, yhu are too young to start facing challenges or rather I shud put it as problem, ni ina da matata kuma muna son junan mu like! har kika kuskura aka yi auren nn u will only end up shattering ur life, it's still not late for yhu...." Bata Bari ya kai karshe ba ta xamo kasa da sauri hawaye na bin kuncinta xuciyarta na tafasa tace "Kai wae me xae hanaka yin magana sae ni? Naga kai ma xaka iya gaya masu baka son auren ae koh?" Yyi wani murmushin da ta kasa fassara nufin shi yace "Ni baxan iya yi ma iyayena musu ba, ina ganin darajan su shi yasa kika ga har ynxu ban musa masu ba" wani mugun kallo ta shiga yi masa har lkcn tana hawaye ssae tace "Kai ne kasan darajar iyaye ni ban sani ba koh, toh kmr ynda baxa ka iya masu musu ba nima baxan iya ba, sae dae idan an makala maka ni ku kashe ni kai da matarka" tana kai wa nn ta mike tana kuka ssae ta haura sama da gudu, bin ta da kallo yyi yana murmushi, kafin ya fara shan drink din hannunsa, cake kawae ya dan ci ya mike yace ma Janet da ta fito daga kitchen ta ce ma Anty xae koma, fitowa Anty tayi bayan Janet ta bata sakon shi, tayi Mamakin rashin ganin Batuul a falon sae dae bata nuna ba tace "Har xaka tafi Abuturrab" Yace "Eh Anty, it's almost time for sallat ne" tace "Toh shknn, Allah ya tsare" fita yyi daga falon, ita kuma ta nufi sama don xuwa jin dalilin kin jin maganarta da Batuul tayi rai a bace, dakinta ta sameta kwance tana kuka har da sheshsheka, Anty ta tsaya daga bakin kofa tana kallonta tace "Meye hkn Batuul?" Mikewa xaune tayi da sauri ta kuma fashewa da kuka tace "Don Allah Anty ku rufa min asiri a fasa auren nn wllh bana son ya Abuu shi ma baya sona ..." Harara Anty ta galla mata tace "Wnn kuma sae ki jira idan babanku ya dawo ki sanar da shi" tana kai wa nn ga juya ta fice daga dakin.+

   Aunty na shigowa daki taji wayanta na ringing, kamin tayi picking taga har ya katse, ─Ćauka tayi ta duba taga wa ya k'ira, missed calls biyu ta gani duk Ammah ce ta k'ira, zama tayi daga bakin gado zata k'ira kenan wayan ya fara ringing, Ammah ─Ćince ke k'ira, ─Ćagawa tayi tare da yi mata sallama, bayan sun gaisa Ammah ke tambayan Aunty "Maryam ya shirye shirye", murmushi Aunty tace "Alhamdulillah Ammah", ita har yanxu mamaki take na zata aurar da Batuul nan da y'an kwanaki, Ammah ce ta katse mata tunani da cewa "dama kayan Batuul ne nakeso a tambayar min ita inda akwai abunda take buk'ata dan Aliyu ya tambayeta tace ita bata son komai, toh ni ba yarda nayi dashi ba shine nakeso a bincika min sannan gyaran jiki zan turo a kawota gida sai ayi mata duk abinda ya kamata", shiru Aunty tayi har sai da Ammah ta kai aya tukunna tayi ajiyan zuciya tace "Toh Ammah zan tambaya miki ita, sai dai gyaran kamar zai fi tayi a gida nake gani ba sai taje can ─Ćinba ai hidima zaiyi yawa, har nayi magana mai gyara gobe zata zo daga Ndjamena", cewa Amma tayi "toh shikenan hakanma yayi", da haka suka gama wayan, zaman tunani Aunty ta yi dan ita bata da wani shiri ma da zatayi na bikin, ko y'an uwanta ma bata fa─Ća musu, waya ta sake ─Ćauka tana k'iransu ─Ćaya bayan ─Ćaya duk ta sanar dasu auren Batuul, sai mamaki sukeyi ganin abun yazo da wuri.
STORY CONTINUES BELOW


     Bayan Abuturrab ya koma gida da daddare Abui ya k'irashi har si─Će ─Ćinshi, daga palo ya tarar dashi kishigi─Će yana kallon News, da sallama ya shiga ya zauna k'asa sannan ya gaidashi, gyaran murya yayi sannan ya k'ira sunanshi, "Aliyu", a hankali ya ─Ćago dan gaba daya jinshi yayi wani iri dan Abui baya k'iran shi da sunanshi, yace "Aliyu na nema maka auren Batuul bawai dan na isa inyi maka abinda nakeso ba, bawai kuma dan bana sonka ba sai dan inason ci gabanka, yarinyar nan amana zan baka, ba iyayenta ka─Ćai bane suka baka amanarta, har ni amananta zan baka, ka rik'eta kamar yadda zata zauna a gun iyayenta, in ka cuceta toh ka cuci amanar mu, yarinyace ita sannan mace, she is so naive and weak sai kayi hak'uri da ita, sannan bawai dan an ha─Ćaka da ita ka fifita matarka da kakeso kanta ba, kayi k'ok'arin adalci tsakaninsu sai kaga Allah yasa komai yazo maka da sauk'i, Aliyu ban yadda da saki ko yaji a tsarin zaman aurenka inba maishi ya sab'awa shari'a ba da bama fatan faruwanshi, ka kula da ita kamar yadda zaka kula da Farida, bana son ka zama silar rugujewar abotan da yake kulle tun kamin zuwanka duniya, kaji tsoron Allah a duk inda ka tsinci kanka, In sha Allah aurenka da Batuul alheri ne", k'asa ─Ćagowa yayi dan wani nauyi kanshi yayi mishi, ji yayi kamar abu aka ─Ćaura mishi a kan, Abui ne ya sake k'iran sunanshi, da k'yar ya ─Ćago ya iya cewa "Na'am Abui", wani chest box ya ─Ćauko daga gefenshi ya mik'o mishi yace "ga wannan shine  Sadakin Fatima, shi za a mik'awa Waliyyin Batuul as Sadaki, sannan a can zataci gaba da karatunta, kayi supporting ─Ćinta in every way to the best of your ability tunda tana karatunta muka nema maka aurenta, Allah yayi muku albarka", wasu makullai guda biyu ya mika masa yace "wannan na motane bayan an ─Ćaura muku aure sai ka bata, wannan kuma gidana na farko dake Mississipi street na bata shi halal", da sauri ya ─Ćago ya kalli Abui da mamaki, shi ya rasa gane wane irin so suke yiwa Batuul dashi da Ammah, ko aurenshi na fari basuyi wannan abin haka ba, da k'yar ya iya bu─Će baki yace "In sha Allah Abui, zanyi yanda kace,", yace "yawwa, ka gama arranging gidan da zata zauna na nan da can ko kuma ha─Ćasu zakayi waje ─Ćaya", kai ya gya─Ća tareda cewa "Yeah a can dai tare zasu zauna amma a nan Asokoro nacewa Mum zata zauna", Abui yace hakan ma yayi kyau, Nasa Mustapha da Sadiq suyi duk necessary arrangement ─Ćin ─Ćaurin auren, Allah ya tabbatar muku da alheri ya taya ka riko, Allah yayi muku albarka", jiki a sanyaye ya mik'e yayi wa Abui sallama ya fita.
       Har gida Abui yasa sukaje shida Baba da Uncle ─Ćin Abutturab da yaji lbrn Abdallah ke neman sonta suka samu iyayen Abdallah suka bashi hak'uri, Basu nuna komai ba suka ce dama wani ai baya auren matar wani, dama can Allah yayi ba matarsa bace, suka musu add'uan Allah ya bawa Batuul da Abutturab zaman lafiya, kuma sukace zasu bawa Abdallah hak'uri su bashi baki, da haka sukayi musu godiya suka tafi.       Ranar asabar k'arfe goma aka ─Ćaura auren Aliyu Ahmad Kyaree da Fatima Kashim Goni akan sadaki sisin gwal 60, a k'ofar gidan kakanta dake Goni Mukhtar street a Maiduguri, tana kwance ─Ćakin Aunty babu abunda takeyi sai rawar sanyi, Yayya ce ta shigo tana cewa "Keh Batuul fito ai an ─Ćaura, tashi daga kan gadon nan tun jiya kike kai, maza fito a ida miki kitson da kike ta gudu tun jiya", kan gado ta hau ta yaye mata bargon, hawaye ta gani idonta, sai rawar sanyi take, hannu tasa zata ─Ćagota taji jikinta zafi, ba shiri ta janye hannunta, Farida ce ta turo k'ofan ta shigo janye da wani akwati, ganin Yayya kan gadon yasa ta tambayan mey ya faru, da gudu ta k'araso ganin yadda Batuul ─Ćin take yasa ta fita a guje taje ta k'ira Aunty, a rikice Aunty ta shigo, da kanta tayi k'ok'arin ─Ćago Batuul sannan ta nemi key ta mik'awa Farida tace suje dan su Ahmad na Maiduguri ─Ćaurin aure kuma batasan ma ina driver ─Ćinsu yake ba, mutanen dake gidan ne suka tashi ganin yanayin jikin Batuul suna tambayan mey ya faru, babu wanda ya iya basu amsa dan Yayya da kanta ma kuka take tana k'iran sunan Batuul ─Ćin, ikon Allah ne kawai ya kaisu asibitin dan gaba ─Ćayanta Faridan ta rikice, suna isa asibitin aka taso aka karb'i Batuul akayi emergency da ita, Yayya duk ta ishi mutane da kuka wiwi a asibitin, Anty kam xama tayi reception ta jinginar da kanta jikin kujera,  da ganinta kasan hankalinta a tashe yake, farida ce tayi karfin halin kiransu Ammah ta sanar da su halin da ake ciki, kan kace me sae ga Ammah da Anty Amnah sun taho asibitin, sae bayan kusan minti talatin likita da nurse uku suka fito daga emergency ward, likitan ya bukaci Anty ta bi sa office sanin da yyi ita ce Mahaifiyar Batuul, jiki a sanyaye Anty ta shiga office din likitan, likitan ya dauki farin gilashinsa ya sa yana kallonta yace "Gskya Madam 'yar ki na cikin wani yanayi, a daina daga mata hankali don Allah, dab take da kamuwa da hawan jini" hawaye cike idon Anty tace "Ya jikin nata Dr?" Yace "Da sauki, ta samu bacci ynxu, sae dae meyasa baxa ku tuhumeta ku ji damuwar ta ba Hajiya?" Anty ta share hawayen idonta tace "Xa muyi hkn Dr, mun gode," yace "Gud!" Tace "xan iya shiga in ganta Dr?" Yace "Xa ki iya, amma kada a tada ta" mikewa tayi ta kuma yi masa gdya ta fita, bacci me nauyi ta tarar Batuul na yi an sa mata drip, su Ammah ma duk suka shiga suka dubata, ganin bacci take duk hankalinsu ya kwanta, sae a snn suka iya barin asibitin, Farida ta maida Yayya ma gida don sae gyangyadi take a asibitin, Anty bata kira baba ta sanar da shi halin da ake ciki ba sanin suna Maiduguri har lkcn, Karfe sha biyu kiransa ya shigo wayarta ta daga, nn yake gaya mata sun  sauka Abuja lfya, sae a snn ta sanar da shi halin da Batuul ke ciki, hankalinsa ya tashi ssae, ya sanar ma Abui daga airport suka nufo asibitin.   Karfe daya saura Abuturrab ya shigo gida duk a gajiye ga damuwa da yyi masa yawa bae san ynda xae yi da Ajiddeh ba idan ta ji xancen auren nn, sa'arsa daya bbu wanda ya sani cikin 'yan uwanta, tun da aka daura auren gabansa ke faduwa ya ji kmr an daura masa abu me nauyi ne a kai, part din Abui ya nufa direct don Avoidin mutane dake cike gidan, ko minti biyar bae yi da kwanciya ba Ammah ta shigo, ya mike xaune ya gaisheta yace "Mun dawo Ammah" murmushi tayi ta xauna gefensa tace "Toh Allah ya taya ka riko babana, sae dae fa Batuul din na asibiti ya kamata ka je dubata ynxu duk da nasan yhu are tired" yace "Asibiti kuma Ammah, me ya sameta?" Ammah tace "Kai dae ka je ka dubata, Allah dae ya bata lfya" a hnkli yace "Toh," Ammah ta mike, yace "Ammah ki ce Sadeeq ya kawo min makullin mota" fridge ta nufa ta bude ta dauko chill yoghurt ta mika masa tace "Gashi ka sha Abuu, nasan baka ci komae ba yau" karba yyi yace "Nagode Ammah" ta juya ta fita tana cewa bari in dauko maka makullin, ajiye yoghurt din yyi don bae jin xae iya sha.     Driving kawae yake amma gaba daya hankalinsa baya jikinsa, a hka ya iso asibitin, Ahmad ya hadu da a haraban asibitin, Ahmad ya gaishesa da ladabi snn ya kai sa har ward din da Batuul take, Wata Sistern Anty ce xaune ward din, don Anty ita ta koma gida sbda baki, har lkcn Batuul bacci take, Abuturrab ya gaida Anty Hafsat, ta amsa masa da fara'a tana tsokanansa don sun saba, murmushi kawae yake kansa a kasa, har dae ta tashi ta tace masa tana xuwa ta fita, Ahmad ta bi bayanta. Ya dde tsaye yana kallonta snn ya ja kujera ya xauna, ya kusa minti talatin xaune ya ga tana juye juye, ya kafa mata ido ko kiftawa bae yi, a raxane ta mike xaune ta bude ido tana kwala wa Anty kira tana kkrin sauka daga kan gadon, ya Mike da sauri ya riketa, hkn bae hanata ci gaba da kiran antyn da take ba tana kuka xata sauko, ko kadan bata lura da wanda ke rike da ita ba don idonta rufe yake, rungumeta yyi jikinsa, lkci daya ta daina fixge fixgen da take tayi lamo jikinsa tana sauke ajiyar xuciya, lumshe ido yyi yaki budewa..Sunfi minti biyar a haka, har lokacin idonshi lumshe, hannu ya sa yana kwantar da dogon gashin kanta da aka kitse rabi aka bar rabi, k'amshin turaren da ya cikata ne yasa ta tunanin inda tasan turaren, a hankali ta bu─Će ido tana k'ok'arin janyewa daga jikinshi, saketa yayi ya ─Ćan matsa da baya, idonta cike da hawaye ta juya tana k'arewa ─Ćakin da take kallo, ganin shi ka─Ćai ne ─Ćakin yasa ta matsa can k'arshen gadon ta fashe da wani matsanancin kuka, sosai take kuka tana k'iran Aunty, tsayawa yayi yana kallonta, can ya k'arasa inda take ya ha─Će rai yace "Wai kukan mey kike yi ma mutane hka, baki ga inda kike bane or did yhu want to worsen yhu condition, tunda na dawo nake sintirin asibiti, am even wondering anya ke ba sicker bace, da ko tawa ta sameni" ko kallonsa bata yi ba ta shiga kkrin sauk'a daga saman gadon zata fita daga ─Ćakin tana kuka, yayi maza ya fixgota, baya tayi zata fa─Ći yasa hannu ya taro ta ya maido ta k'irjinshi, ─Ćago kanta yayi har lkcn tana kuka yace "Allah zan mareki in baki nutsu ba, mey ke damunki da zaki rik'a abu kamar yarinya, are yhu okay!" kai ta girgiza mishi ta ─Ćago rinannun idanunta ta sauk'e kan kyakyawan fuskanshi cikin sheshek'an kuka tace "Yaa Abuu wai an ─Ćaura ko, tunda baka sona bana son ka dan Allah ka taimakamin kacewa su Baba su barni a nan inyi zamana, in kayimin haka nima Zan yadda da duk wani condition ─Ćinka ko na meye ne, ko kuma zanyi zamana ba tareda da kowa ya sani ba sai ka saken......", bai bari ta k'arasa maganan ba ya k'ara k'arfin rik'on da yayi mata ya daka mata tsawa yana mata mugun kallo yace "Da alama baki da hankali, sae ynxu kika san da hka, C'mon wuce kije ki kwanta", ssae ta tsorata ganin yanayinshi, tana hawaye ta juya tayi kan gadon, sai da ta koma ta kwanta tukunna ya juya ya danna bell ─Ćin k'iran doctor.


+

       A gida can Ammah ta ha─Ća kayan lefen Batuul Babban mota guda, su Aunty Amna da sauran Aunties ─Ćinsu matane suka kai, su bakwai suka ha─Ću sukaje, da mutunci aka karb'esu can gidansu Batuul ─Ćin, abinci kala kala aka shiga serving ─Ćinsu, kowa ya ya6a ganin yawa da kyan kayan da Batuul ta samu, Basuci abubuwan da aka kawo musun ba sai juye musu Aunty tasa akayi, tukuicin 1million ta bawa Sisters ─Ćin Baba su basu, k'in karb'a sukayi har sai da Yayya ta saka baki tukunna suka karb'a sukayi godiya suka koma.

       A can asibiti kuwa nurse ce ta shigo da saurinta jin bell ─Ćin yayi ringing, ganinshi tayi tsaye daga gefen gadon ya nuna mata gadon yace "call her doctor immediately" da sauri ta fita suka shigo tareda da doctor da stethoscope rataye wuyanshi da wani ─Ćan board haka a hannunshi, nurse ─Ćin kuma rik'e da wani k'aramin silver tray da allura akai, yana zuwa ya saka stethoscope ─Ćinnan a kunnenshi yana ─Ćan gwada gudun pulse ─Ćinta, alama yayiwa nurse ─Ćin ta mik'o mishi alluran zai yi mata , ba shiri ta mik'e tana kuka, sosai ta bawa likitan wahala da Aunty Hafsat dake k'ok'arin rik'eta itama, yana tsaye jikin bango yana ganin shure shuren da take tayi, ganin taqi tsayawa ne yasa shi matsowa gaban gadon ba tare da yyi wani tunani ba ya kwanto da ita jikinshi, cikin ra─Ća yace mata "I will slap you idan baki tsaya kin dena bawa mutane wahala ba", lamo tayi jikinshi gabanta na faduwa, har sai sai da aka tsikara mata alluran ta da─Ća k'ank'ameshi ssae tana hawaye, bai ─Ćagata daga jikinshi ba bayan likitan yayi mata allura itama dae kasa tashi tayi don duk bata da karfi, a nan jikin nashi bacci ya ─Ćauketa ya shimfi─Ćar da ita ya dubi Aunty Hafsat dake ta kallonsu da sha'awa don sae ka rantse masoya ne, yace zaije gida ya dawo.

       Sai yamma Aunty tazo tare da Baba, a kan gado suka tarar da ita tana bacci, daga bakin gadon Baba ya tsaya yana kallonta, sosai ya tausaya mata ganin yadda ta rame ta k'ara haske, hannu ya ─Ćaura kan goshinta ya tottofa mata addu'a, snn ya ja kujera ya zauna bayan ya gama ya kalli Aunty yace "Yaushe sukace zasu tafi da ita?", Aunty tace "D'azu dai da suka zo basu ce komai ba toh inaga sai gobe", Aunty Hafsat ce tace "Uncle a barta mana in ta warke sai su tafi da ita, amma yanxu ai bata jin da─Ći", sai da ya gama jin abinda Aunty Hafsat tace yace "A'ah Hafsat, in kuma yana da abin yi a can fa?, in dae xa a sallameta ko xuwa gobe kawae su tafi ta warke a can din", tashi yayi ya fita yacewa Aunty zai je wajen doctor ya tambayeshi yaushe za a sallametan, ita Aunty bata cewa komai sai ido da ta bishi da, tausayin Batuul sosai takeji a cikin ranta, Babane ya dawo yace musu gobe doctor yace za a sallameta, a nan ya tafi ya bar Aunty da Aunty Hafsat, yana fita Aunty ta dubi Aunty Hafsat tace "Hafsat wlhy tausayin Batuul nake, ban tab'a kawowa zatayi aure so soon ba, sannan kuma ma mai mata, Batuul yarinya ce amma sun k'asa fahimtar abinda nake nufi" Aunty Hafsat ta girgiza kai da damuwa tace "Yaa Maryam ko ni yanxu jimamin abin nakeyi, danma dai naga Aliyun nada hankali da nutsuwa sosai, ko ─Ćazu shi ya taimaka akayi mata allura da k'yar", Aunty tace "dama nifa bata Aliyu nake ba, nafi kowa sanin Aliyu tunda rainona ne, matarshi nake jiyewa Batuul, familyn su basuda da─Ći akan kishiya, bare Batuul da take yarinya, bata ma san meye kishiyar ba", ajiyar Zuciya Aunty Hafsat tayi tace "Yaa Maryam addu'a kawai zamu tayata yi, itama a sata ta dage da yin addu'a, duk abunda zatayi ta kasance shine a bakinta, kuma ai can zata ci gaba da karatu ko?", kai Aunty ta gya─Ća tace "Ehhh haka Babanta yace, har admission ─Ćin wai ya nemata a can, yace gidan nasu ma da makarantar babu nisa, makarantar na Houghton street, gidan kuma na ST GEORGE'S, kinga da kanta ma ta rik'a zuwa", Aunty Hafsat tace  "yawwa hakanma yafi kinga zata rage damuwa sosai in tana zuwa school, baza ma tana zaman gidan ba bare su ishi junansu har su samu misunderstanding, Allah dai ya basu zaman lafiya", Aunty tace "Amin ya Allah, sosai zansa ana yiwa Batuul addu'a , duk sati a rik'a mata sauk'an Qur'ani", Aunty Hafsat tace "Allah ya dai ya rufa asiri Yaa Maryam, Allah ya karemu daga sharrin duk mugun abu naji ko na gani", daga nan suka ci gaba da hirarrakinsu.
      
       Sai dare Abutturab ya dawo tare da Ammah, Ammah ce ta fara shigowa yana biye bayanta, Batuul na cin abinci lokacin Aunty Hafsat na kishingi─Će kan sofa dake can angle, tana ganinsu ta mik'e ta zauna suka gaggaisa, Ammah tana tambayanta ya mai jiki, Kan gadon ta zauna ta jawo Batuul jikinta tace "Bitti ya jiki, kina samun sauk'i dai ko", kai Batuul ta gya─Ća dan wani kunyan Ammah takeji yau, Abutturab dake tsaye Ammah ta kalla tace "kai baka yi mata ya jikine ka tsaya kana kallonmu", kallon Batuul yayi a takaice yace "ya jiki" hararanshi tayi ta ─Ćauke kanta cike da jin haushin alluran da ya rik'eta yasa akayi mata daxu, mamakin hararanshi da tayi yayi ya girgixa kai ya ─Ćauke idonshi daga kanta, sunfi minti talatin wajen Ammah sai nan nan take da Batuul ta rasa ina zata sa Batuul ─Ćin, shi dai kujera yaja ya zauna lokaci lokaci yake ─Ćaga kai yana kallonsu, suna ha─Ća ido take hararanshi, daga baya dariya ma abun ya fara bashi, mik'ewa Ammah tayi tace "Bitti zamu tafi kinji, Allah ya k'ara lafiya, Aunty Hafsat ta fita rakata shi ya tsaya daga baya, kallonta ya tsaya yi amma taqi ─Ćagowa ta kalleshi, gabanta ya matso yace "kin gama harare hararen mara kunya, irin na fara sake maki fuska a tunanin ki ko, Gud! yhu had beta stop decievin ur self coz am still the Abuturrab yhu knw!," bata ─Ćago ba dan mugun bugawa zuciyanta yake, ya dago kanta yana mata mugun kallo yace "Baki ji na ne?" Kuka ta saki kmr jaririya tana kallonsa, ya koma baya da sauri yana kallonta da mamaki, ya buda manyan idonsa yace "Na maki wani abun ne? Daga magana?" Kin cewa komae tayi sae kukan da take, mamaki ya sa shi k'asa cewa komae, can ya sauke ajiyar xuciya ya runtse ido yana shafa kansa murya can kasa ba tare da ya shirya fadin hkn ba yace "ohkk srry!" Lkci daya ya bude ido jin abinda bakinsa ya furta, D'ago kai tayi tana kallonsa ya maka mata harara ya nufi kofa da sauri, ta bi sa da kallo har ya fita kafin ta tabe baki tana share hawayen fuskarta, lkci daya jikinta yyi sanyi qalau tunawa da tayi ynxu fa ita matar Abuturrab ce, tafiya fa xae yi da ita ya raba ta da iyayenta da 'yan uwanta ya kai ta garin da bata san kowa ba, ta fashe da matsanancin kuka ta fada kan gadon tana tausayin rayuwarta.

         Washegari tunda aka sallameta bayan taji ranan za a wuceta da ita take kuka kmr ranta xae fita, duk ta fita hayyacinta, k'arfe takwas aka zo ─Ćaukanta, lokacin Aunty ta bata wani lace blue mai kyau da tsada ta saka, ta bata wani laffaya shi kuma Golden, ta saka mata costumes ─Ćin gwal, Batuul dai babu abinda take sai kuka, duk da ba wani kwalliya tayi ba tayi kyau sosai, wajen Baba aka fara kai ta yayi mata Nasiha sosai, rungumeshi tayi sosai tana rusa kuka, da k'yar ta sakeshi, k'annenta ma kukan sukayi tayi ganinta tana kuka, Ahmad, Sa'eed da Khalil ne kawai basuyi kuka ba amma suma jikinsu yayi sanyi, Aunty kam kasa mata magana tayi dan ji takeyi itama zatayi kukan idan ta bude baki, kanta kawai ta shafa cikin sanyin tace "Allah ya miki albarka, ya kare ki a duk inda kike", daga nan ta juya tayi ─Ćaki, Sistern Baba ce ta kai ta har mota, suka shishshiga convoy ─Ćin motocin dake waje akayi gidan Ammah da ita.Suna isa bayan an shishiga dasu gidan Aunty Hafsat ta d'ago Batuul dake ta faman razga kuka, sauran Aunties ─Ćin Aunty  da suka taho tare suma suka fiffito daga motocin, Aunty Amnah ce ta fito ta tarbesu da fara'arta, babu abinda Batuul takeyi sai kuka kmr xata shide tana rungume  jikin Aunty Hafsat, k'anshin turaren wutane kala kala ke tashi ta kowane angle ─Ćin babban palon, ga wani sanyi dake bugasu, babu abinda matan palon suke sai gu─Ća, sama akayi da Batuul zuwa ─Ćakin Ammah, Farida na biye bayansu ta rasa farin ciki take taya Bestyn nata ko kuma bakin ciki take da auran Yayanta, A kan lallausan rug ─Ćin dake ─Ćakin Ammah Aunty Hafsat ta zaunar da ita, ─Ćagota Aunty Amnah tayi ta maidata kan gadon tace "A ah baza ta zauna a k'asa ba", Aunty Hafsat dai batace komai ba sai murmushin da tayi, haka akayi ta shigowa gaida amarya amma fir taqi bu─Će fuskanta sai faman zubda hawayen da take, saida duk suka gama suka fita tukunna Ammah ta shigo ─Ćakin, hannu tasa ta sake janyo gyalen yadda baza a gane ba, Ammah na k'arasowa ta zauna daga gefen Batuul, mayafin dake kan Batuul Ammah ta ─Ćaga tana kallon fuskan Batuul da ke hawaye, "Masha Allah", abinda Ammah ta fara fa─Ći kenan gani yadda Batuul tayi kyau sosai, matso da ita gefenta tayi tace "Bitti kukan har yanxu, toh kiyi hak'uri kinji, ai nanma gidane, karki damu kinji, ki kwantar da hankalinki", ita dai Batuul taki cewa komai sai hawayenta da ya da─Ću, mik'ewa Ammah tayi tasa Aunty Amna su kawo musu abinci tace tana zuwa itama ta fita.


+

       Yana kwance rigingine ─Ćakin Massa idonshi lumshe kamar mai bacci, Massa ne ya shigo ─Ćakin yana waya ganinshi kwance yasa ya katse wayan ya zauna daga arm ─Ćin kujerar ya ─Ćan tab'ashi, a hankali ya bu─Će idanunshi dake lumshe ya sauk'esu kan Massa yana jiran jin mey zaice, mik'ewa yayi ya zauna ganin Massa ya ki cewa komae yace "wai meye kake kallona haka ne, is this your first time seeing me", murmushi Massa yayi yace "ango irinka ne ni ban tab'a gani ba, yau za a kai maka amarya shine kazo ka kwanta min a ─Ćaki, da ni nake ango yau ai da tun rana zan tafi, da kanku ma zaku kaini in na isheku", ─Ćan tsaki Abutturab yaja zai koma ya kwanta Massa yasa hannu ya rik'oshi yace "Man what are you doing wai, tun ─Ćazu kazo ka kwanta, kai ko marmarin ─Ćauko amaryar taka ma bakayi, dukda nasan ba kai zaka ─Ćaukota ba ai sai kaje ka dubata koh", wani irin kallo ya sakar mishi yace "ni ba sai ka tsaya yimin surutu ba pls, just tell me you need privacy, i should excuse you", ya koma ya kwanta, baki Massa ya bu─Će zai yi magana yaji wayanshi na ringing, tashi yayi yaje ya ─Ćauko, ganin Ammah ke k'iran yasashi amsawa a risine, a nutse yace "Ammah Nda dubdo, ya gajiya", ta amsa mishi da "Lafiya Massa, kana tare da Abu ne", juyawa yayi yana kallon Abun da ya mik'e da sauri tun sanda yaji Massa ya ambaci Ammah, ce mata yayi "Ehh Ammah, gashi nan muna tare", tace mik'a mishi wayan", "Toh kawai yace ya isa inda Abutturab yake ya mik'a mishi wayan, ansa yayi yasa a kunnenshi a hankali yace "Ammah Nda dubdo", bata ansa gaisuwan da yayi mata ba tace "Shine har da kashe waya tsabar raini ko Abu, Yayi maka kyau ai, bakaje ka ─Ćauko matarka ba dan ka nuna mana kai ka isa ko, toh Abui yasa anje an ─Ćaukonta hkn kuma bae sa ka xo gaida wa enda suka kawo tan ba yayi maka kyau, kayi abunda kaga dama Abu",  bai samu yace komai ba tana kaiwa nan ta katse k'iran, kanshi ya dafa tareda cewa  "Shit not again, wlhy bana son Ammah na fushi dani akan yarinyar nan", wayanshi ya janyo dake gefenshi a kujera a sanyaye tareda da ─Ćaukan key ya shiga neman layin Ammah, ringing yakeyi amma taqi ─Ćagawa, mik'ewa yayi yacewa Massa da ya kafeshi da ido yace "Am going", bayanshi Massa yabi yace "Mu tafi tare", tare suka fita Abu na tuk'a motar, tunda suka shiga gidan matan dake cike falon suk'e tsokananshi, Farida ya gani na sauk'owa kan stairs, tsaidata yayi ya tambayeta "Ammah fa" ce mishi tayi "tana side ─Ćin Abui", daga nan bai tsaya jin komai ba ya juya yayi side ─Ćin Abui, Ammah kawai ya gani tana k'ok'arin rufe wani akwati, k'arasawa yayi har wajenta yace "Ammah kiyi hak'uri kinji, bansan kina nemana ba, wayan na silent ne, I was having a slight headache shine na tafi gun Massa in huta", ya k'arasa magana tareda da yi mata side hug, ji tayi baza ta iya ci gaba da yi mishi fushin ba, juyowa tayi itama ta kalleshi tace "Abu mesa kullum sai kasa ni yin magana", kai ya girgixa da sauri yace "In sha Allah Ammah bazan sake saki magana ba", tace "Allah yasa, kaje ku gaisa da y'an uwanta da sukazo tare da ita, wannan akwatunan ma nasune zansa a fidda musu inda motocin ke pake", yace "Toh" ya juya ya fita, a palo ya tarar dasu Aunty Hafsat har sun sauk'o k'asa, a nan ya gaggaisa dasu cikin jin kunya, Aunty Amna sai tsokanarshi take, shi dai baya cewa komai sai murmushi da yakeyi kanshi a k'asa, da haka sukayi sallama suka wuce, su Aunty Amna suka rakosu har wajen motocinsu, sukayi Godiya suka bar gidan.

STORY CONTINUES BELOW


       Su Aunty Hafsat na tafiya Farida ta shigo ─Ćakin ta hau kan gadon da Batuul ke zaune, mayafin kan nata ta yaye, jikinta ne yayi sanyi ganin yadda Batuul ke hawaye babu k'ak'k'autawa, janyota tayi jikinta itama ta fara hawayen tace "Batuul you are making me emotional, kiyi hak'uri ki bar kukan nan haka dan Allah kinji, everything happens for a reason, it was destined to happen kuma In sha Allah its for d best, ni nasan ko ba komai Ammah will b there for you always kinji, as it is kuma, Yaa Abu is not that bad, just that baison raini and baya sakewa da mutane but bayan haka he is a very nice person at heart, nasan he will take care of you, kiyi hak'uri ki bar kukan nan kinj, kar ya sa miki ciwon kai, kinga Ammah ma in ta shigo taga har yanxu kina kukan nan baza taji da─Ći ba", ta gama maganan tana sharewa Batuul hawayen da yaqi ya dena zuba daga idanunta, da kyar Farida ta samu tasata tayi shiru, Ammah ce ta shigo ganin Batuul zaune a inda take bata motsa ba tace "Bitti baki tashi kin canja kaya ba tun ─Ćazu, maza tashi shiga kiyi wanka, ai kayan nan sun miki nauyi", kanta a k'asa dan wani kunyan Ammah takeji kwana biyun nan, Ammah ta dubi Farida tace "taimaka mata ta shiga tayi wanka", ita kuma Ammah ta juya wardrobe ─Ćinta ta cirowa Batuul kayan baccin da zata saka, tana ajiyewa ta fita.
    
       Sai wajen k'arfe goma ya shigo cikin gidan, kai tsaye ─Ćakin Ammah ya nufa, sallama yyi can kasa ya tura kofar dakin ya shiga kansa a kasa, Ammah na waya daga xaune gefen gado, Batuul kuma na xaune kasan lallausan rug din dakin ita da farida da ta sata gaba ta ci abinci, gabanta ya fadi ba kadan ba ganinsa tayi saurin d'aga mayafin dake kan kafadarta ta mayar kanta ta rufe har fuskarta da shi, shi kam Karasowa cikin dakin yyi ya ja stool din gaban mirror ya xauna, Farida ta gaishesa ya amsa ba tare da ya kalli inda suke ba, Batuul ta shiga jujjuya spoon din hannunta cikin shinkafa da miyan gabanta, a hnkli Farida tace " Ki ci mana besty, ko in dibar maki sinasir din ne?" Batuul ta girgixa mata kai kawae, Ammah ta juya tana kallon Abuturrab bayan ta gama wayar da take, ya sauka kasa ya gaisheta, tace "Sae ynxu Abuu" dan shafa kansa yyi yace "Muna tare da Massa ne Ammah" Ammah tace "ina massan?" Yace "Bae dde da tafiya ba" Ammah tace "Toh ka ci abinci kuwa?" Bata jira cewarsa ba ta juya tana kallon Batuul tace "Bitti kin gama cin abincin?" Farida tace "Taki ci Ammah" dawowa kusa da su Ammah tayi tace "sbda me Bitti? Nan fa ba bakon waje bne ki ci abinci" sunkuyar da kai Batuul tayi, Ammah tace "Maxa ki ci Kinji" mikewa Ammah tayi tace "Bari in je gun su Amnah ina xuwa" d'aga hka ta nufi kofa Abuturrab ya bi ta da kallo ganin ko ta kansa ba ta kuma bi ba, girgixa kai yyi cike da takaici, Farida xata mike Batuul ta riko ta da sauri murya can kasa kmr xata yi kuka tace "Plss kar ki tafi farida" tausayin ta ne ya cika ta, ta juya tana kallon Abu ta ga hararanta yake yi, a hnkli tace "ynxu xan dawo Batuul waya ta xan dauko" a sanyaye Batuul tace "Promise?" Farida ta gyada mata kai snn  ta mike ta fice daga dakin. Mikewa yyi ya dawo gefen gado ya xauna kusa da inda take xaune a kasa, girgixa kai yyi yana wani irin murmushi yace "Happy for yhu an makala min ke, ba dae kince kin ji kin gani xa ki iya ba koh?" Banxa tayi masa gabanta na faduwa hawaye na bin kuncinta, yace "Toh wae ma wa kike rufe ma fuska ma tukun?" Nan ma dae bata tanka sa ba, ransa ne ya fara baci yace "Kehh!" Still taki cewa komae, sakkowa kasa yyi ya dawo gabanta yana facing dinta a fusace yace "How dare yhu ina maki magana kike kyaleni?" Kmr jira take ta fashe da kuka ssae ta shiga rerawa, bude baki yyi yana kallonta cike da mamaki, can ya runtse ido yace "Na maki wani abun ne?" Kukanta kawae take bata ce komae ba ya bude idanuwansa yace "Ohhk Allah ya baki hkuri" mikewa yyi ya koma inda yake ya xauna, ya kusa minti goma xaune bata bar kukan da take ba shi kam sae kallonta yake sae dae fa xuciyarsa tafasa yake, gashi yana shakkar kuma ce mata komae don yasan sae kwanan gidan ya gagaresa daren, don kanta tayi shiru daga karshe, abincin gabanta ya kalla xae yi magana Ammah ta shigo, karasowa gun Batuul tayi tace "Kin cinye abincin Bitti" a hnkli Batuul tace "Na koshi" Abuturrab yace "Ammah ban fa ci abinci ba duk yau" daukan plate din gaban Batuul tayi ta mika masa tace "gashi ka kara a nn kar a xubar bata wani ci ba" kallonta yake da mamaki, kafin ya sa hannu a hnkli ya karba, ya mike yace "Sae da safe Ammah" Ammah tace "da wuri hka," yace "Na gaji ne da yawa" Ammah tace "Toh Allah ya tashe mu lfya" tana fadin hka ne tana kallonsa ta ga ko xae yi ma Batuul sae da safe, ae ko tuni ya fahimci hkn, kusa da Batuul ya tafi ya dan duka yace "Sae da safe" ba karamin mamaki Batuul tayi ba, ta dago kanta dake cikin mayafi tana kallonsa, murya can kasa tace "Allah ya tashe mu lfya" ita ma tayi hkn ne sanin Ammah na jiran jin abinda xata ce ne, ssae Ammah taji ddin hkn a xuciyarta tace "Alhmdllh, tunda sun fara fahimtar juna" Abuturrab ya kuma yi ma Ammah sae da safe snn ya fice daga dakin rike da plate din abincin da Batuul ta rage.         Tun k'arfe biyar Batuul ta tashi dan dama ba isasshen bacci tayi ba, sai kuka da tayi ta yi cikin dare, tana jin k'iran Sallah ta sauk'o daga kan gadon, kayan baccin dake jikinta ta cire ta ─Ćaura towel, sai da tayi brush, tayi wanka tukunna tukunna ta tayi alwala, tana fitowa tasaka bak'ar abayar da ta gani cikin akwatin da Ammah tace nata ne da zatayi sallah jiya,  ta saka Hijab tayi raka'atainil fajr sannan ta tada Farida tukunna tayi Sallahn asuba, bata koma ta kwanta ba har k'arfe bakwai, akwatin ta jawo ta shiga dubawa ko da kayan shafa a ciki, ganin akwai yasa ta shafa mai ta saka ta ─Ćan fesa turare, kwalli kawaita saka a idonta sannan ta ─Ćauko wani lace purple daga cikin kayan akwatin dan duk ya fisu simple, duk a sanyaye take bata da wani kuxari, ─Ćinkine mai kyau riga da skirt amma yayi kyau sosai, daidai yayi mata kamar dama can a jikinta aka ─Ćinka kayan, ta saka silver jewellery, komawa tayi kan gadon ta zauna tana tunanin y'an gidansu, wayanta ta shiga nema, tunawa tayi bata ma zo dashi ba can ta baroshi gida, idonta har ya cicciko da hawaye, zama tayi kan gadon tana ta tunane tunane, daga yau shikenan zata bar gaban iyayenta ta koma zama da wani mutum daban da ba sabawa ma tayi dashi ba, ba shiri ta shiga kuka sosai, sai da tayi mai isanta dan kanta tayi shiru dan bata ma bari Farida taji ba, haka tayi ta zama shiru ita ka─Ćai, k'arfe tara Ammah ta turo k'ofan ─Ćakin itama har tayi wanka ta saka atamfanta mai kyau, ganin Ammah ce ta shiga gyara ─Ćankwalinta kanta, a hankali ta gaida Ammah, da fara'a Ammah ta amsa mata tace "Bitti har kin tashi", kai kawai ta gya─Ća ta kasa ─Ćagowa, Farida ce ta fito toilet ─Ćaure da towel, Ammah ta tace "Bitti sauk'o kiyi breakfast kinji, Farida in ta gama tazo daga baya", kasa motsawa tayi a inda take, Farida ce ta dubeta tayi murmushi tacewa Ammah "Ammah yanxu zan gama shiryawa zamu sauk'o tare", Ammah tace "Toh karki b'ata mata lokaci", daga haka ta fita, a tare suka sakko falon da Farida bayan ta gama shiryawa sae dae ta dan rufe fuskarta da mayafin jikinta, har dinning farida ta kai ta tana rike da hannunta, Ammah da Anty Amnah na xaune sae Sadeeq da Abuturrab dake rike da cup din tea yana sha a hnkli, tun da suke saukowa daga stairs yake kallonsu har suka karaso dinning din, Sadeeq yyi murmushi yace " Ina kwana Anty Amarya" dariya duk suka yi bnda Abuturrab dake ta shan tean sa, Anty Amnah tace "Toh ku xauna mana kin bar ta a tsaye Farida" kujerar dake gefen Abuturrab Farida ta ja mata tace "Xauna Batuul" Batuul bata so hka ba sae dae bbu ynda ta iya don idansu Ammah na kansu ta xauna a hnkli kan kujeran, kamshin turarensa me ddi duk ya cika ta, farida kuma ta xauna daga gefen Sadeeq.

Post a Comment for "BATUUL CHAPTER 8"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...