Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

BATUUL CHAPTER 7

BATUUL CHAPTER 7

- - Post a Comment
BATUUL

CHAPTER 7Washe gari da asuba Batuul na xaune kan darduma ta idar da sllh Anty ta shigo dakin tace mata in gari ya gama waye ta sameta a bedroom dinta, hakan kuwa akayi wajen takwas ─Ćin safe taje tayi knocking k'ofan Aunty, sai da taji an bata izini tukunna ta shiga, Aunty na kwance kan gado ganin Batuul ya sata mik'ewa dan dama ba bacci takeyi ba, tun daren jiya bayan sun gama magana da baba ta kasa samun nutsuwa, daga gaban dressing mirror Batuul ta tsaya ta kasa k'arasawa ganin yanayin Aunty kamar wani abun na damunta, alama tayi mata da ta zauna tukunna ta samu waje daga k'asa ta zauna tareda gaisheta, magana Aunty ta fara yi mata kamar haka "Batuul ke kika cewa Baba kina son aure" da sauri Batuul ta ─Ćago kanta jin abunda Aunty ta fa─Ća gabanta na faduwa, lkci daya idonta ya cicciko da hawaye ta ma rasa mey zata cewa Aunty, sai da Aunty ta sake magana tace tambayanki nake Batuul kika min shiru", hawayen dake idonta har ya fara gangarowa ta shiga girgiza kai cikin sheshek'a tace "Aunty wlhy Allah ban tab'a irin maganan da Baba ba, ni bansan wa ya fa─Ća mishi ba, ni da nake son inyi karatu", taci gaba da goge hawayen dake kwaranya a idonta, da tausayi Aunty ta dubeta dan dama tasan babu yadda za ayi Batuul tace tana son aure, dama so take ta ga ko Batuul ─Ćin na da ra'ayin aure sai ayi mata amma ba da mai mata ba, ae kam sam baza ta yadda da wannan batun ba, baxata yrda a cutar mata 'ya ba, Aunty ta sauke ajiyar xuciya tace "rantsuwan kuma na meye,ni bance kimin kuka ba, tambayanki kawai nayi, tashi kije kici gaba da abinda kike yi Allah shi miki albarka," kasa mik'ewa Batuul tayi daga zaunen da take sai da Aunty ta sake ce mata "Tashi kije shikenan", hak'uri ta shiga bawa Aunty tana kwalla tace "dan Allah kiyi hkuri Anty amma ni bn ce ina son aure ba" tausayinta Aunty taji tace ta tashi ba komai, in ta shirya tafiya school ta sameta tukunna, da kyar ta samu ta tashi ta fita daga ─Ćakin dan har kanta ya fara sarawa.
Zaune yake a garden din gidan da yamma misalin biyar da wani abu yana kallon tsuntsayen dake ta shawagi abunsu a sama, dan yanxu bashida aiki sai na xama da tunani, wayarsa ne ya soma ringing, ya dauki wayar ganin mai k'iransa yasashi recieving da sauri cike da Mamakin kiran, daga daya bangaren Ammah tace "Ina neman ka ynxu" d'aga hka ta katse wayar, mikewa yyi da sauri ya nufi cikin gidan duk da bae san kiran da take masa ba amma ya ji ddin kiran Mahaifiyar tasa, har ya manta rabon da su yi magana ta waya da ita, bedroom dinta ya nufa da sallama ya tura kofar yaga bata ciki, dai dai nn farida ta fito daga dakinta ya juya yana kallonta yace "Ammah fa?" Tace "Tana bangaren Abui ae," a hnkli ya rufo kofar ya nufi bangaren Abui, sae dae duk jikinsa yyi sanyi ya rasa dalili, da sallama ya shiga falon kansa a k'asa ya xauna kan lallausan carpet din dake malale tsakiyar falon ya gaida iyayen nasa, Abui ne ya amsa, daga hka ya sunkuyar da kai yana jiran jin kiran da iyayen nasa suka masa, Ammah ce ta fara magana kamar hka "Aliyu kana jina koh" d'ago kai yyi yana kallonta sanin a serious issues take kiran sunansa kan tsaye, yace "Ina ji Ammah" in a serious tone tace "Aliyu a gskya mu kam bamu ga amfanin auren nn naka da kayi ba, Sam bashi da amfani, mun tilasta ka kayi aure ne don mu samu kwanciyar hankali kai ma hka, sae dae we were mistaken don tun da kayi auren nn hankalinmu ke tashe, baka yi sa'ar mata ba Abuu, da mun san abinda xae je ya dawo knn da bamu yi Na'am da yarinyar ba, kwata kwata bata san darajan iyayenka ba sae nata, don hka ni da mahaifinka mun yanke shawarar kara maka aure" d'ago kai yyi cikin rikicewa yace "Aure kuma Ammah?" Ta hade rae tace "Kwarae kuwa aure" marairaice wa yyi yace "Ammah ko shekara guda knn fa....." Tsawa ta daka masa tace "Ko ka wata guda ne, meye amfanin yarinyar da take neman rabaka da iyayenka da 'yan uwanka, kai har kana da bakin yi mana musu Aliyu, toh wllh ka guji bacin raina, 'yar mutunci da tasan darajanmu da xa kuma ta dinga nuna maka muhimmancin 'yan uwanka xa mu aura maka," ya share xufar da ke keto masa kmr xae yi kuka yace "Ammah wllh ina son Ajiddeh kuma ni bni da ra'ayin hada mata biyu, ku tausaya...." Wani tsawan da ya fi na da Ammah ta daka masa cikin fushi tace "Shknn Abuu, ni xan hakura in bar ma Ajiddeh kai sae ka maida ta uwarka, d'a na Aliyu da na sani a da baya min musu, jikinsa na rawa yake daukar duk abinda nace, ni kam wnn ba Aliyu na bne nasani...." Hawaye ne ke sakko mata sosae, jikinsa yyi sanyi ya dawo kusa da ita ya rike kafafuwanta cikin rawar murya yace "Haba Ammah, ni din bnxa xa ki xubar ma hawayenki, bani da amfani in har xa ki dinga xubar min da hawaye, kiyi hkuri ki rufa min asiri amma, hawayen ki masifa ne a gare ni, wllh na amince da kome kika ce, Aliyun ki ne ni ba a canxa maki ba wllh" duk ya rikice ba kadan ba yana rike da kafarta, kallonsu kawae Abui yake bae ce komae ba, Ammah taji ddin hkn ta shafa kansa cikin sanyin murya tace "Allah maka albarka" dagowa yyi da sauri ya daura hannunsa kan cinyarta yace "Nagode Ammah na" bata kuma cewa komae ba ya koma ya xauna ya langwabar da kai yana kallonta yace "To wace matar kika xaba min Ammah" kallonsa tayi bbu yabo bbu fallasa tace "Ba wata bace facce 'yar uwarka Bitti" xaro ido yyi ya koma baya da sauri yace "Batuul???" Ta hade rae tace "ita fa" innalillahi wa inna ilaihi raji'un, abinda ya dinga maimaitawa knn yana kallon Ammah da ke ta hararansa tana karkada kafa.A bangaren Ajiddeh kuwa tun ranan da sukayi waya bata sake k'iranshi ba saima ─Ćagawa su Mummy hankali da tayi akan abinda ke shirin faruwa tsakaninta da Abutturab, su Mummy ganin abin na nema zama matsala ne dan ta dena kula kowa ita fa sai ansan yadda za ayi mijinta ya zama kamar yadda yake a da, Jainaba ce ta kawo shawaran su ziyarci sabon bokan da taji ance yana aiki kamar da bakin wuk'a amma fa ba a k'asar nan yake ba, yana can Tchad, a ranan sukayi shiri akan gobe zasu tafi, da daddare Mummy da kanta take sanarwa Daddy akan zasuyi tafiya gobe, da ya tambayeta inda zasu tace mishi ai kakar su Ajiddeh zasuje gaidawa sabida tun kamin aure rabonta da ita kuma ba lafiya bane da ita, da mamaki yake tambayan Mum akan dama Ajiddeh bata koma ba tun bayan bikin dan shi sam baisan ma tana gida ba, Mummy ce tace mishi "ehhh wai mijinta take jira akwai abinda yakeyi a nan ─Ćin", cewa yayi "kuna dawowa ta koma wajenshi, in ta zauna a nan ─Ćin amfanin mey take mana, taje can gidan nashi su zauna idan kun dawo", toh kawai Mummy tace ,cheque yayi musu signing yace su rubuta amount ─Ćin da zasu buk'ata tunda ziyara zasu, basu sanar dashi ma cewa da mota za a yi tafiyar ba, washegari k'arfe shida suka ─Ćau hanyan Maiduguri daga nan zasu shiga Tchad ta can, tafiya sosai sukayi bayan sun isa Tchad kamin su isa k'auyen da bokan yake, da k'yar suka samu sukaje inda yake, wata bukka ce da gani ta da─Će ko ina duhu sai wani ─Ĺan haske dake fitowa daga windon bukkar, da zuwansu yace musu yasan abinda ke tafe dasu duk ya sai dai akwai abinda har yanxu ya kasa ganowa, shima baisan meye bane amma abin babba ne, kuma nan gaba yake shirin faruwa, har saida yace musu duk laifinsu ne da tun farko kamin bikin sun nemeshi da duk matsalan babu, hankalinsu ne ya k'ara tashi gaba ─Ćayansu babu ma irin Ajiddeh suka shiga bashi hak'uri kamar sun mishi laifi, zata iya yin komai in dai akan Abutturab ne, gaban bokan ta sake matsawa tace "naji ranka shi da─Će, amma tunda al'amarin bai faruba yanxu, ni ayi min abinda zai manta da kowa kuma bazai sake waiwayen gida ba, sannan daga baya sai mu san yadda zamu b'ullowa abun dake shirin faruwan", kai ya ka─Ća bayan ya gama jin batunta yace " hakan ma yayi", tashi yayi ya shiga wani ─Ćaki daga cikin bukkar ya fito rik'e da wani k'warya, sai da ya zauna ya zauna ya mik'o mata wani kuttu yace "ga wannan nan zaki samu tsohuwar bak'ar tsamiya, da hannunki zaki jik'ata, sai ki ajiyeshi a waje mai danshi da sanyi, kada ki bari rana ya tab'ashi, shi kuma wannan", ya mik'o mata wata bushashiyar fata yace "garin maganine a ciki, tunda dama yace kiyi tafiyarki toh aikin zai zo ma da sauk'i, wannan garin a k'ofar gidanki zaki barba─Ća, sai kuma wajen kwanciyanshi nanma zaki barba─Ća, Kinga yadda wannan tsamiyar keda tsami da duhu, haka zai rik'a ji duk lokacin da ya tuna gida, sanyin nan kuma da kika ajiye a wajan, duk lokacin da ya ganki ko ya tuna dake haka zai rik'a ji, g'arin nan kuma da zaki barba─Ća, yadda iska zai kwasa ya tafi dashi wajen ya shafu haka zai shafe babin gidansu a k'wak'walwarshi", duk maganan har suka gama da yarensu sukeyi, wani irin murna Ajiddeh takeji har cikin ranta shikenan zata samu yadda takeso, ku─Ći masu yawa suka zube mishi tareda mishi alk'awarin dawowa bayan kwana biyu, suna fita Ajiddeh ta dubi su Mummy ta ce "Mum, gobe zan koma, inada Visa ticket kawai zan siya shima online zanyi dan bansan lokacin da zai koma ─Ćin ba, gara inje tun wuri in gama abunda zanyi", Mummy ce tace "toh shikenan, duk yadda akayi sai ki fa─Ća mana a waya, Allah dai ya taimakemu ya bamu sa'a, a daren suka ─Ćau hanyan birnin Tchad, murna fal cikin Ajiddeh.Batuul na gama shirin makaranta tazo yiwa Aunty sallama zata wuce, bayan ta gaidata ne tace "Aunty yau in na tashi daga school zanje gidansu Farida", dagowa Anty ta da sauri tana kallonta tace, "mey zakije yi a gidan?", da mamaki Batuul ta dubi Aunty dan bata tab'a hanata zuwa ba, asalima ita ke sata zuwa ko bata son zuwa, cewa tayi "wajen Farida zanje, nace mata zanzo jiya banje ba shine zani yau" a takaice Anty tace "No ki bar zuwan , some other time kya je, ki dawo gida in kin gama lectures kawae", jiki a sanyaye Batuul tace "toh Aunty na tafi", "Allah ya dawo dake lafiya", a hka ta fita dakin, tana fita k'iran Abdallah ya shigo wayanta, sai da ya kusa katsewa tukunna ta ─Ćauka, a hankali tace "Hello", wani k'ayataccen murmushi ya saki yace "Habibty hope ba tada ki nayi ba, naji voice ─Ćinki so low", ce mishi tayi "No am okay, yanxu ma school zanshiga, tun ─Ćazu na tashi", yace "okay okay durlyn, i will meet you there cux nayi missing cute face ─Ćinki", ce mishi tayi "toh, sai kazo", ta shige mota ta wuce school.
Gaba ─Ćaya ji yayi kanshi yayi mishi nauyi, idonshi ya canja kala ya zama ja har wani gumi ne ya tsatsafo mishi a goshinshi, ya girgiza kai yana ci shiga gaba da ambaton innalillahi wa inna illaihir raji'un, sai da yaji bugun zuciyanshi ya ─Ćan daidaita tukunna ka kalli Ammah dake hararansa har lkcn ya marairaice murya yace "Ammah ki min rai ki aura min wata daban amma ba Batuul ba, yarinya ce fa karama, kuma kila ma baxa ta rasa saurayin da take so.....," wani irin kallo Ammah ke mishi, hkn yasa ya sunkuyar da kai ya kasa k'arasa maganar, Ammah tace "ko ma dae jaririya ce, ita din muka yi niyyan hada ka da, don nasan xata fi mana babban macen da ka aura, in kuma nuna mana xaka yi ba mu isa ba bismillah, ae dama ka saba daga sanda kayi aure" Runtse ido yyi a hnkli yace "Wane ni Ammah, in'sha Allah yanda ku ka ce hkn xa ayi." jin ya fa─Ći haka yasa Ammah sakin fuska ta juya ta kalli Abui tace "dama nasan ─Ćana zaimin biyayya, tashi kaje, Allah shi maka albarka, bbu 6ata lkci xa ayi komae don ka koma bakin aikin ka", shafa kanshi tayi tace " Allah maka albarka" da k'yar ya samu ya mik'e daga tsugunen da yake, yayi musu sallama ya fita daga falon, abubuwa ne suka mishi yawa a kanshi, shi ta ina zai fara sanarda Ajiddeh ma aure iyayensa xa su masa, kuma ma matar ba wata bace illa Batuul, yarinyar da bata wuce sha takwas ba tsabar a ja masa raini, me zaiyi da Batuul yarinyar cikinsa? shi if he can clearly remember ma ai Massa ke sonta tun kamin ya bar gari, tunawa da yayi da Massa ne ya sashi saurin ciro wayarshi daga cikin aljihu ya lalubo number shi Massan, dialing biyu ya ─Ćaga,  "dama ana jinka a gari", abunda Massa ya fara fa─Ća kenan, share tambayar da Massa ke mishi yayi yace "Kana inane?, inaso mu ha─Ću", ya tsaya jin mey Massan zaice mishi, cewa yayi na fita yanxu bana gida but i will b back in an hour", yace "Aii then, zanje gida yanxu before ka dawo zan shiga in gaida Yaa Mera, sai ka dawo ─Ćin, i need to discuss some issue with you", da haka suka katse wayan, suna gamawa ya mur─Ća k'ofan ─Ćakinshi ya shiga ya ─Ćauko key ─Ćin mota ya fito waje, direct hanyan gidansu Massa ya ─Ćauka, cikin y'an minutes ya isa gidan yayi parking bayan an bu─Će mishi gate ya shiga, Side ─Ćin Yaa Mera yayi, tayi mamakin ganinshi, dan rabonshi da gidan tun aurenshi da Ajiddeh da yazo yi mata sallama, mamaki shimfi─Će fuskanta tace "Wata sabon gani Babana kaine a gidan nan yau, ashe ka shigo gari", k'arasowa yayi gabanta ya zauna yace " *Yaa Nda dubdo, aaah u' b├Ęlan amma tusen g├Ęi*, "ina wuni Yaa, ehhh na shigo amma banma da─Će ba", ya k'arashe maganan da murmushi a fuskanshi, hira sukayi sosai da Yaa har tana ce mishi matarshi dai ba 'a ganinta, har sun manta kamanninta,suna nan zaune Massa ya shigo da sallama, tun daga can ya tsaya k'are ma Abutturab dake gaban Yaa Mera kallo, ba makawa Abu ne sai dai ya ─Ćan rame, ko meye dalili oho yaci gaba da shigowa abunshi cikin ─Ćakin, hannu ya mik'awa Abutturab tareda cewa "Man an dena ganinka, rabona dakai fa tunda naje wajenka kamin kazo gida, that is two months after your wedding, i tot baza ka shigo bama sai aure na ai", Yaa Mera ce tace "Abunda na gama fa─Ća mishi kenan, nace gashi matar bata haihu ba bare mu muje can suna tunda su sunqi su zo gunmu", sauk'ar da kanshi yayi k'asa dan shima abin nan da yayi na damunshi, gashi nan har yana son zame mishi matsala, Massa ne yasa dariya yace "Kaji ko, ashe su Yaa zaman jiran jikansu suke, sai kayi k'ok'ari ku samo musu kai da Ajiddeh, kaga sai suji da─Ćin bin naku can garinku mai da─Ći da baku son bari", wani kallo ya sakarwa Massa da ya sashi k'ara yin dariya yace "toh ba gaskiya bane", mik'ewa Yaa Mera tayi ta shige daga ciki su kuma suka wuce chamber ─Ćin Massa, suna shiga ─Ćakin ya zauna a ─Ćaya daga cikin kujerun ─Ćakin tareda mik'e k'afafuwanshi, Massa ya dubeshi yana bu─Će fridge zai ─Ćauko ruwa yace "wai gajiya kayi ne haka na ganka so slow, ko kuma duk cikin canjawan da kayi ne", wani irin glare ya wurgawa Massa ya tashi daga kwancen da yake ya zauna, k'arasowa Kujeran Massan yayi shima ya zauna tareda mik'awa Abutturab ruwa, karb'a yayi bayan yasha ya rufe ya ajiye bottle ─Ćin daga gefenshi ya fara msgana kamar haka "Musty, kwanankin baya lokacin biki na kamar naga you showed interest akan yarinyar nan, har yanxu kuna tare ne?", yayi tambayar yana kallonshi, gaba ─Ćaya kan Massa ya ─Ćaure dan shi baisan ma wace yarinyar yake tambaya ba, cewa yayi "wacce yarinyar wai, dan ni ban gane wacce kake nufi ba", ce mishi yayi yarinyar nan k'arama mana, yarinyar Aunty", tsaki Massa yaja yace "kaji ka da wani zance, Aunty ─Ćaya muke da mai k'aramar yarinya, specify inji", shiru yayi ya kasa furta sunan nata, da k'yar ya iya bu─Će bakinshi yace "Batuul", "ohhh dama wai Batuul kake nufi kake ta wannan abin, wait!, dont tell me bakasan zancen aurena ba", da mamaki Abutturab ya dubeshi yace "kayi aurene?", kai ya girgiza yace "No banyi ba but nan da two weeks za ayi", kan Abutturab ne ya ─Ćaure, yaushe Massa zaiyi aure har bai sani ba, kuma wa zai aura inba Batuul ba, yes ba Batuul bace tunda har su Ammah sukace ya aureta, da sauri ya juya ya dubi Massan da ya zuba mishi ido ganin yadda yake abu kamar ba shi ba yace "Tell me wacece zaka aura inba Batuul ba, kuma ya akayi haka bayan at that time  kace min sonta kakeyi", murmushi Massa yayi yace "Toh kai duk mey ya kawo zancen nan, kai da kace mey zanyi da yarinyar tayi k'arama shiyasa na rabu da ita", kai Abutturab ya girgiza yace "c'mon jokes apart, ba wasa nake ba, mesa ka rabu da ita kuma wa zaka aura?", Massa ne  yace "Rahama mana zan aura, y'ar Sultan, Batuul tun lokacin ta nuna bata sona shiyasa ma ban kai abun  wajensu Ammah ba, but naso in aureta, she will make a good wi.....", wani tsaki Abutturab yaja yace "hold it, okay?", gaba ─Ćaya ranshi ya b'ace, sai da ya ─Ćan nutsu tukunna yace "Mustapha am in a problem, kuma babu mai iya fiddani sai kai, kasan auren nan da nayi shekara kenan, kuma su Ammah suna ganin shine ya hanani zuwa inda suke, and ni inason Ajiddeh, like banima da ra'ayin mata biyu, i cant cope, toh ─Ćazu su Ammah suka tareni da zancen sai na k'ara aure, da nace suyi hak'uri,  amma ganin ransu ya b'aci yasa nace na yadda, toh shine da na tambayesu wa suke so in aura, dan ni i have no one in mind shine sukace min wai Batuul", yadda ya k'ira sunan nata kamar ba daga bakinshi sunan ya fito ba yayi maza ya ─Ćauke idonshi daga kan Massa , dariya Massa yasa harda kyakyatawa ya kwanta akan kujeran, sai da ya gaji dan kanshi ya gama dariyan tukunna ya mik'e ya zauna, Abutturab ko kallonshi baiyi ba har ya gama dariyanshi, sai da yayi shiru tukunna yace mishi "ka maidani ─Ćan iska ma ko, inyi maka serious magana shine kake dariya", ya k'ara tamke fuska ya tashi zai bar ─Ćakin, da sauri Massa ya sha gabanshi yace "No baza muyi haka ba, mu koma ka fa─Ćamin how am i of help dan ni gaba ─Ćaya zancen ne yazo min a bazata, kaga kuma tunda bazanyi kuka ba ai sai inyi dariya", ya fa─Ća yana k'ara smiling, wani siririn tsaki yaja ya koma ya zauna a kujerar da ya tashi, sai da dukkansu biyu suka zauna Massa yace "ina jinka, mey kakeso inyi maka?", shiru yayi ya kasa magana dan baisan ya Massa zai ─Ćauki zancen ba barema da yace aurenshi nan da sati biyu, iska ya furzar daga bakinshi sannan  yace "Inaso kaje kacewa su Ammah kai ke son Batuul, zaka aureta", a razane ya juyo jin abinda Abun ya fa─Ći yace "Are you really okay, duk yadda akayi Ajiddeh har brain ─Ćinka ta tab'a, toh in naje nace musu inasonta sai inyi yaya da ita bayan inada mata", kai ya girgiza yace mishi  "ai dama kana sonta, kuma kasha fa─Ćamin kai baza ka zauna da mata ─Ćaya ba, and as crowned prince kaga zaka k'ara wata, kaga tunda sooner or later zakayi, y not do it now", kai ya girgiza yace "No way, thats not happening with me, bazanje inyi abunda ban shirya yinshi ba besides ai Batuul ─Ćin na fa─Ća maka da kanta tace min bata sona, kaga there is no way zan auri yarinyar da bata sona", kai shima ─Ćin ya girgiza yace "Musty you are not understanding the whole thing, am telling you......", katseshi Massa yayi yace "hold on, kai mesa baza ka auri Batuul ─Ćin ba, she is perfect, beautiful, simple, religious, mey kuma zaka nema bayan wannan, like menene aibun Batuul, ni wlhy da zata soni zan aureta but ta riga da tace min bata sona, so i will b living with that intuition a cikin kaina shiyasa bazan nemeta ba, kuma tunda har su Ammah ne suka nema maka auren nan i bet its for everyones welfare, they have seen the best in her, kuma ni nasan they have a genuine reason for all this, Batuul is your sister, you can tell others who she is, kafi kowa sanin asalinta", kanshi ya sauk'e k'asa ya rasa ya za ayi ya fahimtar da Massa akan bazai iya auren yarinyar nan ba, yafi minti ─Ćaya kanshi na dafe kan hannunshi tukunna ya ─Ćago a fusace har idonshi ya canja launi yace "Na fa─Ća maka bazan iya aurenta ba", sai kuma ya sassauta murya jin ihun da yayi yace "Mustapha i cant marry her, like i cant withstand her for a day, bare kuma har aure da yake for eternity, i just cant, i dont know but there is this effect she have on me anytime nake tareda ita and am never comfortable with what i feel", ya k'arashe maganan yana mai sauk'e idonshi daga kallon Massa, Ajiyar zuciya Massa yayi ya dafa Kafa─Ćan Abu yace "okay calm down, kasan mey za ayi yanzu, ka kwantar da hankalinka,  addu'a kawai zakayi akan lamarin nan, zamuyi magana daga baya, kuma kada ka nunawa su Ammah baka so dan ransu zai b'aci", shima Abun ajiyar zuciya yayi yayi patting hannun Massa dake kafa─Ćanshi yace "In sha Allah zanyi", da haka suka canja zancen suka shiga na wajen aiki da bayan rabuwa, duk da Abuturrab Sam hankalinsa bae jikinsa.


+

         Bayan Batuul ta dawo daga makaranta gida ta dawo kamar yadda Aunty ta ce mata, da sallama ta shigo taga babu kowa a palo, kitchen ta shiga taga Aunty dasu Esther na aiki, k'arasawa tayi ta gaida Aunty tayiwa sauran sannu da aiki duk suma suka mata sannu da dawowa, jikinta ne yayi sanyi ganin yanayin da Aunty ta amsa mata gaisuwan, hawaye ne ya fara taruwa a idonta don ita a tunaninta tun maganan ─Ćazu da safen nan ya ke b'atawa Aunty rai, maza tayi ta fita daga kitchen ─Ćin dan tasan kuka zata fara gashi akwai masu aikinsu a gun, anjima zataje har ─Ćaki ta sake bata hak'uri akan maganan duk da dai batasan mey ya fara kawo zancen aure ba, sama ta haura bayan ta fito daga kitchen ─Ćin, hanyan ─Ćakin k'annenta tabi, bu─Će k'ofan tayi ta shiga , ta ga dukkansu shirin Islamiyya sukeyi, wasu na saka uniform wasu sun gama, shiga tayi ta samu waje ta zauna daga ─Ćaya daga cikin gadajen ─Ćakin, ita da kanta batasan mey ya shigo da ita ba, Khalil yace "Yaa Batuul wannan takwarar taki tazo", ya fa─Ća yana b'ata rai, Mus'ab ne yayi maza ya karb'e maganan tareda zumb'uro baki yace,  "mtsew ni Allah kullum bana son zuwanta", hararanshi Batuul tayi tace "bana son rashin hankali, Mamar Baba cefa kake cewa bakason zuwanta, ita da gidan ─Ćanta", Ahmad dake fesa turarene yace "ehh mana ai gaskiya suka fa─Ća, abu duk randa tazo sai tasa ran Aunty ya b'aci, ni bana ganin amfanin zuwan nata, gara mu mu rik'a zuwa wajen nata mu ka─Ćai,ni da tace bata son Abuja ma da─Ći naji, kuma fa kamar sunanki naji tana k'ira tana ta fa─Ća, ai Aunty ce tace mu hau sama shiyasa banji mey suka fa─Ća ba", tsawa Batuul tayi musu tace "bafa na son iskanci, waye yace muku ita take b'atawa Aunty rai, wato dukkanku gulma kuke koya ko", Sa'eed da dama tun can shi bamai magana bane yace musu "ku shirya mu tafi dan Allah, its getting late", ya ─Ćauki wayanshi kan mirror ─Ćinsu ya saka a aljihu ya fita, Su Yusra ne suka shigo ─Ćakin su sun gama shiryawa sukace Yaa Ahmad mun gama shiryawa fa, inji Aunty mu k'ira ka mu tafi kar muyi latti, dukkansu fita sukayi daga ─Ćakin bayan sun gama shiryawa sukayi mata sai sun dawo, jiki a sanyaye tace "okay sai kun dawo, kuyi karatu sosai kunji ko, in kun dawo zan baku chocolate", ta fa─Ćawa su Mahir da ─Ćan dariyan yakenta, suna fita ta tashi itama tabi bayansu tayi hanyan ─Ćakin da tasan zata tarar da kakarta da k'annenta ke cewa tazo, tasan duk gaskiya suke fa─Ći, duk yadda akayi ma itace tasa ran Aunty b'aci, batasan meyesa bata sonta ba, tunda tasanta, tasan kakarta bata tab'a son Aunty ba duk da kyautatawan da Aunty keyi mata dan  Aunty tasha yiwa Yayya abun kirki tun suna Maiduguri harda suka dawo Abuja ma kuma ba tareda sanin Baba ba, amma bata tab'a appreciating ba, zuwanta bakin k'ofar ─Ćakin ne yasa ta kawar da tunanin da take ta mur─Ća k'ofan ─Ćakin.
Da sallama ta shiga ─Ćakin taga bata nan amma akwatinta da jakanta na daga gefe, sai glasses ─Ćinta dake ajiye kan mirror, zama tayi tana jiranta dan da alama toilet ta shiga, tana nan zaune ta fito tana goge ruwa a hannnunta da ─Ćan k'aramin napkin, da gudu Batuul ta tashi taje ta rungumeta tana fa─Ćin, " *Yayya nyi kammo isi min gull├Ęma, biya ngaima amme nya sorin*, Yayya ke kullum baki cewa zaki zo sai dai kawai a ganki kin fa─Ćo", Sai da janyeta daga jikinta tukunna tace " *dai fandoro let├Ę chingya nyairo gullukin, k├Ęrma d├Ę fato tadanyi yero kadiko, fanuwa na*?,  ku bari ranan da na tashi zuwa gidajenku sai in sanar daku amma yanxu gidan ─Ćana nazo, babu izinin wanda zan jira kuna jina", dariya Batuul tasa tace "duk mey yayi zafi haka Yayya,  namun ma in kin tashi zaki iya zuwa kai tsaye ba sai ki nemi izinin kowa ba", ta karashe maganan tana kallon Yayya da ta k'ura mata ido tana ta kallon ta, kai ta ─Ćaga tareda da ─Ćage girarta ─Ćaya tace " *Yaaa k├Ęrma d├Ę ai yo do, wa shimmin rumin d├Ę nyimai nya n├Ęm shawan kong├Ęna ro nonema*, Yanxu kuma menene kika zubamin ido kina kallona haka, kinsan ai ko a yarintarki baki kaini kyau ba, sai ma dai rashin tsayi da kikasa na biyoki da" tsaki taja tace " *ndu nyiro nyiro nyi shawas├Ę gullono, u awo wallimin d├Ę dai rukkin, rui futu ngam n├Ęma d├Ę, biya dai montindo jarawai ad├Ę na kwalluwa*, waye yace miki kina da kyan da har zan tsaya kallo, ja'ira ni wannan rama da kuma bak'in da kikeyi nake gani, wannan jaraba ta makaranta da bata k'arewa, gashi duk ya lalataki", rai Batuul ta ha─Će tace "kin fara ko, ni kinga ma ─Ćakina zan koma", sanin da Batuul tayi sarai akan maganar da zasu shiga nan ne ya sata cewa zata bar mata wajen, cikin ─Ćaga murya tace " *len├Ęmiya wande waltim yisimi, fuskam yaame yedai a, aima ba k├Ęnza g├Ęi ya, nyai sammaso bannaz├Ęna, afuno g├Ęi awo gade mananuwin a ba, kamme nyairo kanuri manaja shiro afunon mananuwin, Baan do d├Ę g├Ęrenge yishin ai, shima nyairo s├Ęk├Ęlima fayin ai*, in kin tafi karki dawo, da fuskanki kamar na uwarki, babu komai sai hanci da gashi da kika kwaso, duk ta fama b'ataku, inba Hausa ba babu abunda kuka iya, ana yi muku kanuri kuna maidawa mutumin magana da Hausa, ai ina nan ina jiran dawowan Baban naku, in shi ya koya muku duk zanji", ta gama fa─Ća harda kalmashe k'afa, dariya abun ya bawa Batuul ta girgiza kai ta fita, D'akinta ta koma taje tayi wanka ta saka gown mara nauyi ta fito kitchen taya su Aunty aiki, k'arfe biyar da rabi suka gama aikin da zasuyi suka jera a dinning,  K'arfe shida su Ahmad suka dawo daga Islamiyya, lokacin Baba ma ya dawo a tare suka shigo, sai da kowa yayi sallah tukunna suka sauk'o cin abinci, Aunty ce tacewa Batuul taje ta sauk'o da Yayya suyi dinner, ba b'ata lokaci ta haura sama suka sauk'o a tare, cup ─Ćin ruwan da Baba ya ─Ćauka zaisha ya maida ganin Yayya na sauk'owa daga bene, da mamakin ganinta ya mik'e ya isa inda take ya rik'o hannunta suka iso dinning ─Ćin, sai da ta zauna tukunna ya  fara gaidata, yace "Yaa baki cemin kina zuwa ba, kuma ko jiya saida mukayi waya dake fa", yaran ta duba sannan tace "toh garin naku wani nisane dashi, ko sae na nemi ixinin ka kafin in xo gidan ka," da sauri yace "A'a wllh ba hka ba yayya nayi mamaki ne kawae" ta dan kyabe baki tace 'a jiyan bayan mun gama magana da ka sanar dani abinda ke faruwa naga gara kawai inzo ayi ta ta kare, nasa Hamza yayi min booking jirgi na taho yau kawae", duk abin nan Aunty bata ─Ćago ta kallesu ba sai da taji Yayya na cewa Baba ya sanar da ita abinda ake ciki tukunna ta ─Ćago ta kalli Baba, cigaba da serving abincin tayi ganin yaqi kallo direction ─Ćinta jikinta a sanyaye.


+

      K'iran Yaa Mera ne ya shigo wayan Ammah, farida dake xaune gefenta ta dauki wayar ta mika mata, Ammah ta daga tare da sallama, gaisawa suka yi snn Yaa Mera tace, "ashe Babana ya shigo gari, ─Ćazun nan kawai na ganshi ya shigo wllh", Ammah tace "ehh ya kai sati yanxu ashe bae je gaida ki ba" Yaa Mera tace "Wllh kuwa sae daxu ya shigo min" Ammah tace "Ikon Allah, amma bae kyauta ba, nima dae ina nn shigowa Yaa akwae wata magana da xamu tattauna, ko xuwa gobe da safe in'sha Allah xan shigo" Yaa Mera tace "Toh sae kin xo" da hka suka yi sallama Ammah ta ajiye wayar tana kallon farida, hawaye taga idonta tana kkrin gogewa kadda Ammahn ta gani, da mamaki Ammah tace "Ya aka yi farida? Ya haka?" Shiru farida tayi tana share idonta, ganin ynda Ammah ta kafe ta da ido yasa a hnkli tace "Ammah why Batuul?" Ammah tace "Ban gane ba" wasu hawayen suka kuma xubo mata tana girgixa kai tace "Ammah Ya Abuu fa ba shiri suke da Batuul ba, ga kuma matarsa masifaffiya muguwa, Batuul baxa ta iya masu ba cutar ta kawae xa su yi tayi gashi ba kowa gare ta can ba, don Allah ku canxa shawara ko cikin family can Maiduguri ki samu dai dai Ajiddehn a aura masa" tsaki Ammah tayi tare da maka mata harara tace "Toh naki yin hkan, da Batuul kadae xuciyata ta Aminta a hada Aliyu, uwar me Jiddahn xata yi mata wanda Allah bae mata ba, shi kuma Abuturrab din idan aka aura masa ita yyi gunduwa gunduwa da ita ya  maido mana," mikewa farida tayi har lkcn tana hawaye ta fita daga dakin. Xaune ta ga Abuturrab dakinta ya rike kai da dukkan alama ita yake jira, yana ganinta kuwa ya mike da sauri ya karasa ya kamo hannunta suka xauna gefen gado yace "In tambaye ki farida, wae wnn kawar taki or wat ever ita tace tana son aurena?" Shi kansa jin tambayar yyi wani banbarakwae a baki don yasan Batuul baxa ta taba cewa tana sonsa ba, he is just confuse, farida ta girgixa kai tace "I don't think Batuul tasan da xancen ma, don daxu ta kirani tana ban hkurin xuwan da bata yi yau ba," ya fuzar da iska yace "Do me a favour little sis, don Allah ki xiga ta a kan kar ta amince nasan dae in har tace bata so baxa a mata dole ba" farida tace "Shknn I will try my best, but ni baxan mata magana kai tsaye ba sae in ita ta kawo xancen don ga dukkan alama bata san abinda ke faruwa ba ma" mikewa yyi rai ba ddi ya fice daga dakin.

Batuul na xaune dakin Anty duk hankalinta ya tashi ganin ynda uwar tata ke hawaye gashi ta ki gaya mata abinda ya faru, ae bata san lkcn da ita ma ta saka kukan ba tana durkushe kusa da Anty, da kyar Anty tayi controlling kanta ta shiga lallashinta sae dae ta k'asa gaya mata dalilin kukan nata don bata san ynda 'yar tata xata dauki xancen aurenta da Abuturrab ba, bude kofar dakin aka yi Ahmad ya shigo da sallama sae dae ganin ynda Batuul ke kuka hankalinsa ya tashi ssae don xuwa lkcn Anty ta daina nata kukan, hankali tashe ya shiga tambayar Anty abinda ya faru, Anty tace "kanta ke ciwo wae shine take kuka, ya aka yi Ahmad?" Ahmad ya durkusa kusa da Batuul yana mata sannu, sae da Anty ta kuma tambayarsa ya aka yi snn yace "Yayya ce tace in kira ta, kuma gashi kanta na ciwo bari kawae inje ince she's not okay" har ya mike Anty ta dakatar da shi tace "A'a bari xata je, ae ta sha magani" tayi hkn ne gudun wani maganan don har ynzu xuciyarta bae yi sanyin abinda yayya tayi mata daxu ba daga tace ita Batuul baxa ta auri mai mata ba in ma aurar da ita ake son yi gwara ta fito da saurayinta kawae, nn fa Yayya ta dinga xaxxaga mata ta inda take shiga ba nn take fita ba, mikewa Anty tayi daga karshe ta bar mata falon, shine tun lkcn take kuka a daki har Batuul ta shigo ta sameta. Kallon Batuul tayi tace "Tashi ki je Batuul" ba musu Batuul ta mike tana share hawayenta ta fita. Yayya na kishingide tana cin Apple, Baba na xaune daga gefenta ya tankwashe kafa suna magana da kanuri, k'arasowa cikin dakin Batuul tayi sae dae bata da walwala don tasan Yayya ce ta bata ma Anty rae ko bata fada mata ba, Xama tayi dan nesa da su tace "Ga ni Yayya" Yayya ta tabe baki ta mike xaune da kanuri tace "Wato har uwar taki ta xuge ki shine xaki wani shigo ma mutane ko sallama bbu, kin wani hade rae koh" Baba dae bae ce komai ba kansa na kasa, Yayya ta ci gaba da cewa "Toh auren Aliyu dae bbu fashi wllh, yaro d'an arxiki mai asali gaba da baya, waye bae san kakansa ba a Maiduguri?" Xumbur   Batuul ta mike xuciyarta na wani mugun bugun da bae taba yi ba har wani rawa jikinta ya shiga yi tana kallon Kakar tata tace "Ban gane ba Yayya" da kanuri Yayya tace "Ohh ke da duk baki san abin da ake ciki ba, toh ae shirye shiryen bikin ki ake da Aliyu jikan  Kyari, wato d'an wajen Ahmad" Batuul ta xaro ido cikin kidemewa tace "Ni Yayya?" Ae bata jira cewar Yayya ba ta fice da gudu daga dakin ta nufi dakin Anty, Har lkcn Anty na xaune ta xuba tagumi, ta xube jikin uwar tata cikin rawan Murya tace "Anty ban gane abinda Yayya take gaya min ba ynxu," K'asa cewa komae Anty tayi tana kallonta, hkn yasa Batuul ta fashe da wani matsanancin kuka tace "Wayyo Na shiga uku Anty, wae Ya Abuu ake cewa xan aura, ni ban gane ba" Rungume ta Anty tayi sae dae she's lost of words.

Bayan Magrib Abuturrab na xaune daki abun duniya ya ishesa duk ya rasa tunanin da xae yi farida ta shigo tace "Ya Abuu Ammah na kiranka" mikewa yyi yace "kin yi abinda nace maki farida?" Farida tace "Ya Abuu bata fa ce min komai ba har ynxu, meaning she is still unaware, ni kuma baxa ta soma jin komai a bakina ba ka bari..." ficewa yyi daga dakin ba tare da ya tsaya jin sauran xancen nata ba, dakin Ammah ya shiga ya sameta tana waya, ya xauna har ta gama snn yace "Gani Ammah" Ammah tace "Dama cewa xanyi ka shirya kaje can gidansu Batuul ka gaida Yayya, ta shigo tun da rana" rasa me xae ce da ita yyi don bae son bacin ranta, da kyar yace "Toh Ammah" daga hka ya mike ya fita hankali tashe yasan shknn wani ikon Allah kawae xae hana a manna masa Batuul, wae for God's sake me suke son yyi da 'yar yarinyar nn?? Ya ma xae fara tunkarar Ajiddeh da wnn xancen, da kyar ya iya shiryawa ya dauki makullin motarsa ya fita daga gidan.
Kuka sosai Batuul ke yi kanta kife jikin Anty dake hawayen ita ma, ─Ćagowa tayi daga karshe jin Anty ta ki cewa komae cikin rawan murya tace "Aunty mesa za a min aure nida ke karatu, mesa Yayya ta matsu inyi aure har tasa Baba ya yadda zaimin ynxu, Aunty dan Allah ki tashi muje ki fa─Ća musu banason yin aure, idan basu yrda ba to su canxa min wani mijin ba ya Abuu ba, don Allah  Aunty ki tashi mu tafi nasan in kika fa─Ćawa Baba zai yadda", ganin Aunty ta ki tashi yasa Batuul mik'ewa har lkcn tana kuka tana fa─Ćin "Nasan in na fa─Ćawa Baba zai yadda, kullum duk abinda nace mishi yana min, wannan ma zanje in bashi hak'urin ince mishi karatu xanyi...." cikin hanzari Aunty ta mik'e ta tareta ganin tayo baya zata fa─Ći, ta fada kanta, sabon kuka Aunty ta fashe da ta shiga girgiza ta ganin jikinta duk ya saki idonta lumshe, sunanta ta shiga k'ira tana cewa "Batuul, Batuul ki tashi kinji, babu wanda zai miki auren nan, wasa sukeyi miki dama, ki tashi yanxu zanje in samu Baba da Yayya ince suyi hak'uri, kiyi hak'uri ki tashi kinji Batuul, babu mai sake saki kuka, ki tashi muje tare Batuul", Batuul kam ko motsi batayi sai dai har lkcn hawaye na tsiyaya daga idanunta, wani ihun Aunty ta sake sawa tana jijjiga ta, bu─Će k'ofan ─Ćakin akayi su Ahmad suka shigo jin ihun Anty, cirko cirko suka tsaya ganin kan Aunty kife jikin Batuul tana ta Kuka, da k'yar ya iya yin k'arfin hali ya ja k'afanshi ya k'arasa inda su Aunty suke, tsugunawa yayi dab da Batuul ya rik'o hannunta, ─Ćayan hannun kuma ya ─Ćaga Aunty, cikin sanyi yace "Aunty ciwon kan nata ne har yanxu", kasa bashi amsa tayi sai hawayen dake ta zuba daga idonta, juyawa yayi ya dubi sauran k'annen nashi da har lkcn sun kasa motsi suna nan inda suke sai hawayen da suma suka fara har y'an k'ananan yace "kuje ku k'ira Baba, yana ─Ćakin Yayya", ya juya yaci gaba da murza hannun Batuul yana ─Ćan jijjigata, ba a fi minti biyu ba da fitansu Baba ya shigo ─Ćakin yana tambayan tana ina, ganinta kwance jikin Aunty ya kasa magana, sosai jikinshi yayi sanyi, yasan duk yadda akayi kan maganan auren nan da taji ne ya dameta, Bai sake cewa komai ba sai da ya sunkuya ya ─Ćauketa cak sannan yacewa Ahmad, "─Ćauko key mu tafi asibiti", a bakin k'ofar ─Ćakin suka ci karo da Yayya tana tambayar "meye ya faru wai, inata magana ja'iran yara kun qi kulani kun zuba min idanuwanku kamar na mujiya", ido ta wara ganin Batuul hannun Baba tasa ihu tana cewa na shiga uku ni Zara'u, mey zan gani haka, meye hakan wai kunyi min shiru, mey ya sameta, baza kuyi min magana ku fa─Ćamin mey ya samu Batuul ─Ćin ba", babu wanda ya kulata a dakin, gaban Aunty ta k'araso tace "Maryam bafa nason wulak'anci, mey kuka yiwa Batuul ─Ćin ina tambayanku kika min shiru, mayafi Aunty ta ─Ćauka ta yafa tabi bayan su Baba ko kallon inda Yayya take batayi ba, tasan indai ta bu─Ći baki toh kowa bazai ji da da─Ći ba dan ranta yayi k'ololuwar b'aci, hanyan Nizamiye hospital Ahmad yabi dan nan ne family hospital ─Ćinsu, har lokacin bata farfa─Ćo ba, suna zuwa cikin gaggawa aka karb'eta akayi emergency da ita, har lokacin babu abinda Aunty take sai kuka da addu'a Allah ya bawa y'arta lafiya, Abuturrab kam xaga gari yyi ya koma gida Karfe tara saura ya shige daki yyi kwanciyarsa.+

       Washegari kamar yadda Ammah tayi alk'awari, k'arfe biyu ta shirya tayi gidan Yaa Mera, da driver ta tafi dan so take ya jirata su koma, a falo ta tarar da ita zaune ta mik'e k'afa dogaranta mata biyu na mata tausa, sallama tayi ta sa kai cikin ─Ćakin, da fara'a ya Mera ta tashi ta yiwa y'an matan alaman su wuce, kansu a k'asa suka gaida Ammah sukayi waje, waje ta samu daga palon ta zauna tace "Maryam wannan gidan naki da tafiya yake, dubi duk na gaji", murmushi tayi tace "kai Yaya, ai babu wani tafiya kawai dai kin da─Će ne baki zo ba", biyu ─Ćaga cikin y'an matan da suka fitane suka shigo ─Ćauke da manya tray ─Ćauke da fruits, abinci, sai nama iri iri, direwa sukayi suka koma daga waje, Yaa Merace ta fara magana "jiya kawai sai ga Babana, nayi mamakin ganinshi, shine yake cemin wai yayi sati ma", ruwan dake kan tray ta ─Ćauko ta ajiye gefenta sannan tace "ai yanxu ma zuwan nan dan shi nayi, auren Mustapha nan da sati biyu kenan ko, toh inaso a ha─Ća ayi da na Abutturab, dan matar nan tasa bazan zauna in zuba mata ido su cutar min da ─Ća ya zama mara amfani ba", ido Yaa Mera ta wara tace "Yaya aure Babana zai k'arayi, yaushe? kuma wa zai aura?", kai ta girgiza tace "Maryam auren ne kawai zai min maganin halin nan da yake ciki, yaro gaba ─Ćaya ya zama bashiba, shine nayi magana da Babanshi ya nema mishi auren Batuul, so nake ma a ha─Ća da na Massa tunda saura sati biyu, in yaso sai ya koma bakin aikinshi da ita, dan yarinyar na da nutsuwa, kamar jinina nake jinta", kallonta Yaa Mera ta tsaya yi tace "Yaya badai Batuul ─Ćin Maryam ba?", kai ta ka─Ća tace "k'warai kuwa ita", tace "toh Yaya ai na Massan ma jiya Babanshi ke cemin wai sun ─Ćan ─Ćaga, sun k'ara wata ─Ćaya dan Mamar yarinyar bata jin da─Ći, yanxu haka an fita da ita waje, Amma Yaya baku tunanin ko Batuul nada wanda takeso, ko kunyi magana da iyayenta sunce bata da kowa, dan kar azo a shiga hakkin yarinya", Ammah zatayi magana kenan wayanta ya shiga ringing, ─Ćauka tayi taga Farida ke k'iranta, recieving tayi tasa a kunnenta tace "Farida ya akayi", cikin shesheka tace "Ammah Batuul", cikeda da damuwa jin ta ambaci Batuul kuma tana kuka tace " Batuul kuma, mey ya sameta", cewa tayi "Ammah tana kwance a asibiti bata da lafiya, tun jiya she is still unconscious tun.....", Ammah bata bari ta k'arasa ba tace "Farida, kina jina, kije ki samu Abu kice mishi maza ya tashi ku tafi asibitin tare, nima yanxu zan wuce daga nan", maida kukan nata tayi tace "toh Ammah", suna gama waya ta mik'e tace "Maryam kinji, Batuul din ma ba lafiya tana kwance asibiti, yanxu gunta zani in duba ta", bakin k'ofa Yaa Mera ta rakota tayi mata sallama tace Allah ya bawa Batuul ─Ćin lafiya ta gaisar mata da Anty, itama zasu zo dubata idan mijinta ya dawo, da haka sukayi sallama akan zasuyi waya.

STORY CONTINUES BELOW


      Hijabi kawai Farida ta ─Ćaura kan top da wandon dake jikinta tayi ─Ćakin Abutturab, knocking tayi taji bai amsa mata ba, bu─Ćewa kawai tayi ta sa kai, wani sanyi ne ya ka─Ća har cikin jikinta duk da hijabin dake jikinta, kai ta ─Ćaga ta dubi Acn ─Ćakin nashi taga yana lowest temperature, k'arasawa tayi daga ciki ta ─Ćau remote ─Ćin ta kashe Acn gabaki ─Ćayanshi, yana kwance kan gadonshi rigingine ya ─Ćaura hannunshi kan goshinshi idanunshi lumshe kamar mai bacci, a hankali ta k'araso cikin ─Ćakin ta zauna daga bakin gadon, sunanshi ta shiga k'ira taji bai amsa mata ba, sarae tasan kuma idonsa biyu, ce mishi tayi "Yaa Abu Ammah cefa tace inzo in fa─Ća maka ka shirya mu tafi asibiti", jin ta ambaci asibiti ya sashi bu─Će idonshi dake lumshe ya zuba mata su, bai tashi ba yace "waye ba lfya?", a hankali tace "Batuul ce bata ji da─Ći tun jiya, shine.....", wani tsawa ya daka mata, "tashi ki fita", a gigice ta mik'e sai da taje bakin k'ofa ta juyo tace mishi "Yaa Abu Ammah cefa ta aikoni", wani harara yabita dashi, ba shiri ta saki k'ofan tayi waje, tana fita ta k'ira Ammah ta fa─Ća mata yadda sukayi da Abutturab, ran Ammah ba k'aramin b'aci yayi ba ta katse wayan ta shiga neman numbershi, jin wayanshi na k'ara ya janyo wayan, ganin mai k'iran yasashi saurin tashi zaune yayi recieving, yana ─Ćagawa Ammah ta fara magana "Abu kana jina, bana son shashanci, in aiko yarinyar ta fa─Ća maka sak'ona shine zaka korata, toh yayi maka kyau, ina kan hanyan zuwa asibitin, ka tabbata kamin in isa kana can", tana kaiwa nan ta katse wayan, ji yayi gaba ─Ćaya kanshi na sara mishi, mesa Ammah baza tayi understanding ─Ćina bane, mik'ewa yayi ya ─Ćauki key ─Ćin mota ya sauk'o k'asa rae ba ddi, a palo ya tarar da Farida zaune tana ta jimamin rashin lafiyar k'awarta, tana ganinshi ta mik'e, harara yabita dashi ya fita waje a fusacd, yana tafiya tabi bayanshi a ranta tana tausayin halin da k'awarta zata shiga in ta auri masifaffen nan, sai da ya shiga motar tukunna itama ta shige, bayan ya fita daga gidan ne ya tambayeta asibitin ba tareda ya ─Ćago ya kalleta ba, fa─Ća mishi sunan asibitin tayi daga nan ya ─Ćau hanya.
    Suna isa asibitin da gudu Farida ta bu─Će ta fice, bata damu da hararan da yake binta dashi ba tayi wucewar ta ciki, k'in fitowa yayi daga motan har sai da Farida ta dawo tace mishi Ammah tace ya shigo, tana gaba yana biye da ita suka isa har ─Ćakin da aka kwantar da Batuul, a VIP ward aka kwantar da ita, Su Aunty da Ammah na daga palon yayi sallama ya shigo kanshi a k'asa, durk'usawa yayi ya gaida Aunty, fuskanta babu yabo ba fallasa ta amsa mishi sannan yayi mata ya mai jiki tace mishi "Alhamdulillahi taji sauk'i", daga nan bai sake cewa komai ba sai hararar da Ammah ke jifanshi dashi da sun ha─Ća ido, juyawa yayi zai fita Ammah tace "ka shiga ka gantan ne da ka juya zaka fita", juyowa yayi yana kallon Aunty yace "i tot ba a shigane dan naganku zaune a nan", murmushin karfin hali tayi tace zaka iya shiga , bacci take", ta nuna mishi k'ofan ─Ćakin, a hankali yake ─Ćaga k'afanshi har ya isa bakin k'ofar ─Ćakin, hannu yasa zai mur─Ća kenan wata nurse ta bu─Će k'ofan zata fita, hanya ya bata ta wuce tukunna yasa kai cikin ─Ćakin, xaune ya ganta tana hawaye cotton wool a hannunta alamar allura nurse din ta mata, Yayya na xaune d'aga gefenta tana mata sannu, suna hada ido da shi gabanta yyi mugun faduwa ta gyara zip din skirt dinta da sauri, sunkuyar da kai yyi ya karaso ciki kmr bae son taka kasa, Yayya ta washe baki ganinsa tace "A'ah sannu da xuwa mai gida," gaisheta yyi murmushi dauke fuskarsa don ba laifi sun d'an saba, ta amsa da fara'a tace "Ehh ynxu da taku ce ta kawo ka ae na ganka, tun jiya na iso ban ga keyar ka ba sae ynxu da kishiyata ba lfya koh" murmushi kawae yake yace "Jiya ae na xo aka ce min kina bacci" ta yo waje da ido tace "Kai Haba, halan wnn yar bakin cikin ce tace maka hka" ta fadi ta na nuna Batuul da kanta ke kasa har lkcn gabanta na faduwa don ko kallonsa bata son yi, Abuturrab yace "Ae kam ita tace min kina bacci" Yayya tace " kaji bakin ciki kiri kiri, toh ko taki ko taso dae ni ce ta farko ita ta uku, bbu ynda xata yi" daga hka ta mike tace "bari dae in baku waje kadda inyi rashin hnkli" duk da Mood din Abuu sae da ta basa dariya, ya bi ta da kallo har ta fita, snn ya hade rae ya juyo yana kallon Batuul, hawaye ne ke sakko mata, ya kusa second talatin yana kallonta, kafin ya karasa gadon ya ja kujera ya xauna bbu yabo bbu fallasa yace "I knw by now kina da masaniyan abinda ke shirin faruwa koh?" K'in cewa komae tayi sae hawayen da take ssae, cikin rashin damuwa da shirun da tayi yace "Wato ke kika ce masu ni kike so knn koh?" Da sauri ta d'ago kai tace "Allah ya kyauta! ko kuma kai kace kana sona ba!" Ido ya kafa mata cike da mamakinta, ita kanta tayi Mamakin furucin nata don unexpectedly taji ya fito bakinta, ya mike tsaye yana mata wani irin kallo yace "Kinsan Allah kika kuskura kika yrda suka makala min ke, kin dauko hanyar tarwatsa farin cikin ki ne, ni ina da mata kuma ina sonta, infact ko bani da mata ma ni me xanyi da ke? Kawae daukan magana ne wnn, wllh tun wuri kice masu ke kina da wanda kike so, kar ki yrda a soma kai xancen nn da nisa idan ba hka ba...." Kuka ssae take har da shessheka tana kallonsa, hkn yasa ya kasa karasawa ya koma ya xauna xuciyarsa na masa xafi, can ya kalleta yace "Dama ki daina wnn silly tears din mu sama ma kanmu mafita ynxu, kina da saurayi ko baki da?" Wani kallo tayi masa ta dauke kai ya mike a fusace xae yi magana Ammah da farida suka shigo dakin. Sunkuyar da kai Batuul tayi, Ammah ta Karaso tana kallon Abuu da ya shiga shafa kai daga tsayen da yake, Ammah tace "Kukan me kike bitti?" Da sauri yace "shine nima nake tambayarta taki bani amsa tun daxu" Farida ta kallesa ta gefen ido ta tabe baki sanin karya yake ta xauna gefen kawartata da damuwa tace "Sannu Dear, I was so worried da Ahmad yace baki da lfya" Ammah ta xauna kujerar da Abuu ya tashi tana kallon Batuul tace "Sannu Bitti, ya jikin?" A hnkli tace "Da sauki ynxu" Ammah ta galla ma Abuu harara tace "A garin ku hka ake xuwa duba mara lfya empty handed?" Shiru yyi bae ce komae ba, ya rasa me yasa Ammah ke yi masa hka shi kam, gefen Farida ya karasa yana kallon Batuul yace "Me kike son in siyo maki?" Farida ta amshe tace "Fruits, Shawarma, Chill yoghurt da gasasshen kaza will do" harara ya maka mata rae a bace ya juya ya fice daga ward din, ko da ya dawo Ammah sun tafi da farida dake son xuwa yi ma Bestien nata girki ta dawo asibitin, Yayya ma Ahmad ya maida ta gida, Anty kadae ce ward din sa Batuul gaba tana cin abinci, don tun jiya rabonta da abinci, kansa a kasa ya karaso ward din, ledan hannunsa ya ajiye kan table din dake gefen gadon bayan ya kuma gaida Anty, Anty tayi masa gdya ta dauke abincin gaban Batuul sanin ba ci xata yi ba ta rufe, ta tattara komae a basket tace "Bari in je gida ynxu in dawo Abuturrab" yace "Toh sae kin dawo Anty"
Aunty na fita ya jawo kujera ya zauna kusa da gadon yana kallonta, ita kam kanta a k'asa yake, dan ji tayi kamar ta bita su tafi, har ji take ─Ćakin na suffocating ─Ćinta, tabe baki yyi ya mik'e ya isa wajen da ya ajiye ledan da ya shigo da ya ─Ćau wani bowl da Batuul ta wanke a hannu ciki da zata ci abinci ya zuba apple, grapes sai pomegranate a ciki ya bude table water dake wajen ya juye ciki ya nufi toilet, tana zaune ya fito ya zuba fruits din kan plate ya dawo ya zauna kan kujerar da ya tashi  ya fara b'are pomegranate yana shan abin shi, Batuul kam kin ─Ćagowa tayi ta kalleshi bare tasan abinda yake, cikin nutsuwa ya shiga maimaita mata maganan ─Ćazu ya kara da cewa "yhu beta pretend yhu are nt recovering, ki kuma gaya ma likita auren dole xa a maki, I bet he will find a solution" ko kadan Batuul bata san mey yake cewa ba dan ji tayi abincin da taci yana son dawo mata tsabar tashin xuciya, ranshi ne yayi mugun b'aci ganin ynda tayi banxa da shi tak'i cewa komai, a fusace ya tashi ranshi a ha─Će, cikin tsawa yace mata "keh kurma ce ina miki magana kin wani min shiru kina jina, are yhu stupid", ko ─Ćagowa batayi ba bare ta nuna mishi tasan abinda yake fa─Ći, ranshi ne ya da─Ća b'aci yace "Kehh!" k'ala bata ce mishi ba, jin amae na shirin taho mata yasa ta tuge drip ─Ćin hannun ta ta yunk'ura xata sauka daga gadon yyi saurin rik'eta yana mata mugun kallo yace "ina zaki?", hawaye ne ya shiga zuba daga idonta tana girgiza mishi kai alaman ya saketa amma yaqi, sai ma da─Ća rik'eta da yayi da k'arfi don mamaki reaction din nata ya bashi to ko dae ba ita kadae take ba, bai ankara ba kawai yaji ta kwararo mishi amai a jiki.
+

     Aunty na komawa gida tasa aka kawo mata Aabid dake wajen Fa'izah ta bashi abinci, dan rabonta dashi tun jiya da Batuul ta zama unconscious, tana gama bashi ta mik'ashi ta shiga yin wanka, fitowanta kenan daga toilet taga Baba zaune akan gado, har ta ─Ćan tsorata, ganin shine ta k'arasa fitowa daga toilet ─Ćin, dubanshi tayi taga ita yake bi da ido, ce mishi kawai tayi "Uncle sannu da zuwa", snn tayi gaban mirror, kwaso mayukan da zata shafa tayi ta dawo bakin gadon itama ta zauna, Kallonta yayi yadda takeyin abu kamar bata san yana ─Ćakin ba, hannunta ya rik'o tare da cewa "Maryam", bata ─Ćago ta kalleshi ba tace "Na'am", yace "ya jikin Batuul ─Ćin, waye a wajenta", k'ok'arin maida hawayen dake shirin zubo mata tayi a hankali tace "Abu na wajenta, wanka nazo inyi in kai mata kayan da zata canja itama", matsowa yayi kusa da Aunty ya jawota jikinshi, hawayen da take ta k'ok'arin maidawa ne ya shiga zubowa, kuka sosai ta shiga yi mishi, patting bayanta ya shiga yi , bai hanata ba har sai da ta ─Ćan tsagaita dan kanta tukunna ya ─Ćago tareda da k'iran sunanta, ajiyar zuciya tayi tace "ina jinka", yace "Maryam yanxu akan nace zanyi wa Batuul aure shine kika bi kika ─Ćagawa kanki hankali?"  yayi tambayar yana kallonta, ganin tak'i magana sai hawayen dake zuba daga idanunta yasa yace "auren nan da zatayi kamata yayi kifi kowa murna, wannan yaron ─Ćanki ne, kinfi kowa sanin waye shi, ke da kanki kinsan babu wanda Batuul zata aura hankalinmu ya kwanta da yafi Aliyu, da bakin ki kin yabi nutsuwarshi, toh sai yanxu dan zai auri y'arki shine kike qi, wani hali garesa da har baki son ba shi 'yar ki? Naga dae auren nan ko ba yanxu ba dole ta yishi, toh meye amfanin a barshi nan gaban bayan yin hakan shine gatan da zamu iya yi mata, kuma shine rufin asirinta da namu baki ─Ćaya, inma karatunta kikeji, da kaina zan sa a nemo mata admission a can inda zatayi auren, babu abinda zai tauye mata karatun ta, kiyi hak'uri kiyi mata addu'a Allah ya bata zaman lafiya da kwanciyar hankali a duk inda zata tsinci kanta", jikinta ne yayi sanyi har yanxu hawayen na ci gaba da zubowa ta shiga gogewa cikin sheshek'a tace "Uncle Batuul k'arama ce fa, batasan meye aure ba bare abinda ke cikinshi, kuma fa mai mata zaku aura mata, abin ai zai yi mata yawa, kai da kanka kasan yadda Batuul ke da rauni, haka zataje a cutar da ita tunda ita ba wani wayo gareta ba", murmushi yayi tareda ─Ćagota yace "yanxu naji dalilinki na k'in auren, bakiso y'arki ta auri mai mata saboda kema ke ka─Ćaice gidanki ko, nima ─Ćin ai zan k'ara", da sauri ta ─Ćago tana kallonshi ya sake jawota jikinshi yana murmushi yace " Be optimistic Maryam, in kika nuna tsoron kishiya y'ar taki kuma tayi yaya, addu'a zakiyi musu Allah ya ha─Ća kansu ya basu zaman lafiya, shi kuma Allah ya bashi ikon rik'esu da amana, sannan Batuul fa University take, tana second year ─Ćinta, kinga ba yarinya bace, she is matured enough, she can decide what is wrong and right, tasan abinda zai cutar da ita da wanda zai amfaneta, mubita da Addu'a Allah yasa hakan ne mafi alkhairi", ya fa─Ća yana goge mata hawayenta, da haka Baba ya rarrashi Aunty har ta hak'ura da zancen auren, tace Allah sa hkn shine mafi alkhairi.
STORY CONTINUES BELOW


   
       Su Ammah na isa gida tayi summoning chefs guda biyu, mace ─Ćaya dattijuwa sai ─Ćayar budurwa, order ta shiga basu na abinda takeso a dafawa Batuul kuma kar su ─Ćau lokaci, waya ta ─Ćauka ta k'ira Farida data haura sama, ba jimawa ta sauk'o, Ammah tace mata "je ki ─Ćauko min computer yanxu kizo kimin ordering wasu abubuwa, babu b'ata lokaci Farida ta haura sama bata jima ta sauk'o rik'e da Macbook ─Ćinta ta ─Ćaurashi kan table ─Ćin dake gaban Ammah sannan ta samu waje daga k'asa wajen k'afan Ammah ta zauna ta bu─Će system ─Ćin tana k'ok'arin jonawa da internet, sai da ta gama taga yayi connecting to internet ta ─Ćago tace "Ammah mey zakiyi ordering, Jumia za a shiga ko konga ko kuma universal shopping zakiyi? ta dubi Ammah tana dariya, zama Ammah ta gyara tace mata kayan lefen Abu nakeson ha─Ćawa, lokaci ya k'ure bazan samu aje a ha─Ćo kayan ba, shiyasa zanyi ordering komai", da sauri farida ta kalleta tace "Ammah wai auren nan dagaske kukeyi sai anyi, rashin lafiyan nan mafa da take nasan lbrn da taji ne ya sata" harara Ammah ta maka mata tace "sannun gyatuma, ai fimu son Batuul ─Ćin kikayi, in baza kiyi abinda na saki ba tashi ki bani waje in Sadiq yazo anjima in sashi yayi min, xancen banxa kai", jiki a sanyaye tace "zanyi Ammah,mey za a duba miki yanxu, tace "customised designer akwatuna nakeso kimin order, wanda babu wani da za a sake yiwa irinshi sai ita", murmushi Farida tayi ta shiga surfing sai gashi ba b'ata lokaci tace "Ammah gasu nan da hotunansu, wai akwai na Macs n spencer, sai D&G, LV, Mandarina Duck, Versace, paclane, cartier, ralph Lauren da BOSS, Ammah suna da yawa mafa", sai da Ammah ta karb'i Laptop ─Ćin ta ga pictures ─Ćin tace "ki zab'i ten best kiyimin ordern su, kije credit card ─Ćina yana kan shelf a ─Ćakina ki dawo ki gama", Farida na fita Ammah ta ─Ćau waya ta k'ira Aunty Amna dake Paris, sai da ya kusa katsewa ta ─Ćauka, Ammah ce tace mata "keh kullum sai waya ya kusa katsewa kike ─Ćauka, watarana har ya katse ma ba a samunki", tace "Ammah wayan ne tana hannunsu Nawwal basa barina dashi, yanxu ma ita ta kawo min a guje", Ammah tace "toh yanxu duk bama wannan ba, turaruka nakeso ki siya ki turomin da English Golds, Diamonds, Inner wears, vanity sets sai English wears, sai perfumes, shoes, da nighties sai bags" da sauri Aunty Amna tace "Ammah ba dai auren Sadiq bane ya tashi ban sani ba, yaushe za ayi, wace ma matar", ta tambaya with so much excitement sounding vry surprised, Ammah tace "A'ah ba shi bane", Aunty Amna tace "toh waye za a siyawa kayan nan haka da naji kaman lefe",  ta fa─Ća excitement ─Ćinta na komawa ciki jin ba Sadiq ne zaiyi aure ba, cewa Ammah tayi "Aliyu ne zai k'ara aure", da mamaki Aunty Amna tace "aure kuma Ammah, yaushe yyi aure har yake son kara wani, wace matar da zai aura ─Ćin, kardai Abu ya zama mai son aure aure fa", cewa Ammah tayi "Amna auren Aliyu na farko ba amfani ne dashi ba", tas Ammah ta gama gayawa Aunty Amna yadda auren Abutturab ─Ćin na farko yake da dalilin da yasa take son ya k'ara auren, jiki a sanyaye jin abunda Ammah ta fa─Ća mata tace "Ammah ni inace ma ni ka─Ćai ya share baya nema, ashe har gidan ma hakane, toh Allah ya rufa asiri, wacece matar da xae auran yanxu", Ammah tace "Batuul", da sauri Aunty Amna ta karb'e tace "Batuul dai, Batuul ─Ćaya da na sani?", Ammah tace "k'warai kuwa ita", gu─Ća Aunty Amna ta sa tace "Ammah dama yarinyar nan nada hankali, sosai nakeson yarinyar tana birgeni, Toh Allah ya tabbatar da alheri, yaushe ne bikin, idan yara na hutu sai muzo kawai gaba daya" Ammah tace "ai next week kenan ─Ćaurin auren, biki ko daga baya ne sai ayi", da mamaki Aunty Amna tace "Laah Amma, everything so fast, toh shikenan, zan duba sauran, amma Ammah perfumes ─Ćin bazai yiwu su biyo plane ba, kuma in za ayi shipping zasuyi taking time, so akwai wani abokin Babansu Nawal yana da perfume shop a Aminu Kano crescent, yayi sabon order recently, so kawai zan mishi magana ya kawo har gida, inma container zaki duba, that will be better sai ku zab'a mata, amma sauran yanxu zan shiga in dudduba", Ammah tace "toh shikenan Amnah, zan turo miki ku─Ćin sai kiyi siyayyan, yanxu zansa Farida ta turo miki sizes da details ─Ćinta tunda k'awartace tasan komai", da haka sukayi sallama, suna gamawa ta shiga k'iran mai gold ─Ćinta dake Dubai, yana ─Ćagawa shima ta bashi order ─Ćin Gold har na wajen 50 mil zai turo mata samples in ta zab'i wa─Ćanda take so sai a sakosu a jirgi a turo, shima da haka suka rabu, Farida ganin Ammah dagaske take kuma tasan kayan da k'awatar tafi so tace "Ammah a saka mata abaya a ciki, tana sonsu sosai", Ammah tace sai ki dubo mata suma online shima ki mata ordering ko set 30 ne", sai da ta tabbata ta gama order komai har atampopi daga London tasa aka turo mata su sai laces da lappayu daga switzerland, sai da tabbata ta gama tukunna ta tashi taje tayi sallah.
   

    Har ta gama aman bai saketa ba yana nan rik'e da ita duk ta wanke su gaba daya, murya can kasa yace " Srry!" Kkrin sauka ta shiga yi yaki sakinta, a hka wata nurse ta shigo ta samesu, da sauri ta karaso bakin gadon tana cewa "Wat happened?" Sae a snn Abuturrab ya sake ta, nurse din ta shiga yi mata sannu, shi kam unbutton din shirt din jikinsa ya shiga yi ya nufi toilet, nurse din ta shiga cire mata rigar jikinta ganin tana da vest a ciki, da sauri ta rike rigar taki barin ta cire mata, nurse din tace "Haba! you've messed the blouse, ki cire sae in baki wani abun ki lulluba da shi kafin a kawo maki kaya" bbu ynda Batuul ta iya hka nurse din ta taimaka mata ta cire rigar jikinta, ta sakko daga kan gadon, nurse din tace bari ta kawo mata wani abu ta rufe jikinta, Cleaners ta fara kira su je su  gyara wajen su canxa bedsheet, Batuul na tsaye duk ta kagu nurse din ta dawo ta rufe jikinta kafin ya fito, ae ko sae gashi ya fito da singlet rike da shirt dinsa da ya wanke, suna hada ido ta juya masa baya da sauri ta ji kmr ta nutse wajen, dai dai nn nurse din ta dawo rike da hijab cleaners biyu na biye da ita, daya rike da xanin gado daya kuma na rike da bucket da mopper sae Freshner, da sauri ta karasa ta karbe hijab din tasa, ficewa yyi daga ward din bayan ya dauki makullin motarsa da wayarsa, ko minti biyar bae yi da fita ba Anty ta shigo rike da kayan Batuul a leda.    

Ammah ta bi sa da kallo bayan ta amsa gaisuwarsa ganin ya nufi stairs tace "Meye hkn Abuu?" Ba tare da ya kalleta ba yace "Amai tayi min" daga hka ya haura sama, farida ta saka dariya sanin ynda Amai ke bala'in irritating yayan nata sae gashi an masa a jiki, Ammah tace "Allah sarki, Allah dae ya bata lfya". Da daddare yana kwance kiran Ajiddeh ya shigo wayarsa, ya dde yana kallon wayar kafin ya d'aga ganin ya kusa katsewa.

Post a Comment for "BATUUL CHAPTER 7"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...