Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

BATUUL CHAPTER 1

BATUUL CHAPTER 1

- - Post a Comment
BATUUL

CHAPTER 1
Sanye take da Abaya baqa da yasha aiki da Swarovski stones ta yafo qaramin gyalen abayar ba tareda da wrapping dinshi ba, kafarta sanye da slippers din vinci shima baqi mai Swarovski Stones din à jiki .Siririyace sannan ba doguwa ba tana da shape mai kyau, bata da haske kuma bata da duhu sosai, Irin dai mutanen da ake kira chocolate color ne ko kuma wankan tarwada, dan karamin fuskar ta zagaye yake da dan karamin baki, yayinda Dogon hancinta ya dace da mazaunin sa, Idan tai murmushi kuwa dimlpe dinta yake lotsawa ya Kara hasken annurin fuskar, idanun ta kuwa haka suke tamkar farin wata wajen haske yoh masu iya magana sukace Ga Wata 🌙👈 ga Zara 😀,hooo me kr2 Idan nace zan tsaya zayyano kyawun fuskar ta toh Lalle za'a dade ban gama ba, domin dai BATUUL mai kyau ce.Riqe take da wayarta à hannun hagu yayinda dayan hannun take riqe da karamin yaro da bai wuce shekara uku ba, tafiya takeyi à hankali kuma cike da natsuwa, sannan ga hadari da ya rufe ko ina, ruwa ko yaushe kan iya saukowa sai iska mai dadi dake kadawa à hankali à filin Idin Ramat square dake Maiduguri ,ta juyo sannan ta kalli yaron dake riqe da Hannunta sannan tace "Babich kaga kasa su Aunty Sun tafi Sun barmu ko, ai shikenan in muka rasa sallah", yaron yayi dariyarshi mai kyau yace "ai zamuyi sallah har in roqi Allah ya bani irin CLS din Yaa Ahmad, Aunty tace komai nake so in roqi Allah zai bani" tace "to kaga muyi sauri sai mu yi sallahn ka roqi Allah" yaron ya dubeta sannan yace "Yaa Baatul ai kece bakya yin sauri inata Jan hannunki", tace "toh shikenan zanyi saurin muje mu samesu", haka suka karasa har wajen Sallahn daga gefen mata suka samu har an shimfida musu abun sallah sannan suka zauna wata farar mata mai kyau da baza ta wuce shekaru 35 zuwa 38 ba tana riqe da jariri ta juyo ta dubesu tace "a ina kuka sami hulan?" Baatul tace "Aunty a mota ya bari", matar da aka kira da Aunty tace "ai ke kika biye mishi da kin barshi yayi sallah babu hula tunda da gangan ya cire", Batuul tayi murmushi tace "Aunty ai da yanxu bamajin Khuduban nan da akeyi", Aunty tace "hakane kam", Baatul ta juya ta kalli wata yarinya da bata wuce sa'arta ba tace "Fa'iza kin dauko min jakata da nace ki fito min da ita dan inaso inyi sadaka in an idar da sallah", yarinyar da aka kira da Fa'iza tace "ehh yaa Baatul na dauko gashi nan ma", ta dauko wata jakar Hermès mai ruwan toka da kana gani kasan yana ihun luxury ta mikowa Batuul, Baatul ta amsa tayi murmushi sannan tace "na gode Fa'iza", daga haka suka zauna shiru suna sauraron khuduba har aka gama aka tada sallah Baatul ta dubi Fa'iza tace "tunda baza kiyi sallah ba ki karbi Aabid à hannun Aunty", tace "toh Yaa Baatul", ta sa hannu ta karbi jaririn daketa wasa sannan ta dan koma gefe su kuma sukayi kabbara suka nutsu dan su nuna godiyarsu ga Allah (swt) da yasa suka gama Azumi lafiya har yasa suka ga sallah.Ahaka suke Zaune bayan idar da sallah har Imam ya gama hudubar bayan sallah da wa'azi da tunatarwa , nan Dubban jama'ar da suka hallaci sallar suka fara kokarin kama gabansu. Batuul na riqe da hannun Hafiz suka fito lokacin iskar ta fara yawaita


 Agogon batman din dake manne jikin bango ne yayi ticking 4:30 da rabi dai dai na safe tare da yin sauti,

    Tashi yayi tare mikewa daga kan lallausan katafaren gadon da yake kwance kai, yana mai karanto adduar tashi daga bacci (Alhamdulillahillazi ahyana ba a dama amatana wa illaihin nushur) sannan ya kara dayiwa Annabi (SAW)  salati, ya tashi ya juya ya kalli agogon da ya farkar dashi daga bacci yaga har 4:40 tayi, yayi sauri ya karasa toilet din dake manne  à dakinshi cikin hanzari yayi sauri yayi brush yayi wanka sannan ya fito daga toilet din d'aure da towel da kuma wani towel din a hannunshi yana goge fuskarshi dashi har ya karaso gaban wani babban mirror da mutum kan kalli kanshi gaba daya tun daga kai har kafa ya karasa goge kanshi. Jallabiya ya zura ya feshe jikinshi da turaruka sannan ya fice masallaci, bayan an idar ya d'an jima masallacin Kamin ya dawo gida, yana kwanciya kenan kenan  yaji karar wayarshi na ringing, da har yayi kaman bazai dauki wayarba sai kuma ya juya ya karasa inda wayar take, yana ganin mai kiran da sauri yayi maza ya dauka tare da zama  sannan ya risina kamar mai Kiran na gabanshi,  zama yayi kamin ya kara wayar a kunnanshi tare da cewa Hello  Ammah "*nda wattu*" (ina kwana) daga daya bangaren aka amsa da "*kêlewa sêlai*" (Lafia Alhamdulillah) sannan aka sake ce mishi "Abu ka shirya ne?" Kanshi ya d'aga ya kalli agogo yaga 6:45 , a hankali bakinshi ya motsa zuwa Murmushi ya "à ah Amma saura kadan yanzu zan shirya in fito" tace "yawwa Dan Shehu yace bana karfe takwas  za ayi sallah kuma kasan kaine zaka tafi da Abui" ya ce "*yo dai kêrma lukin*" ( toh gani nan fitowa yanzu ) ya katse wayar ya ajiye 


    Closet din kayanshi ya bude sannan ya dauko wani sky blue din shadda mai kyau ya saka ya dauko cuff links dinshi na Mandarina duck sannan ya sanya su a hannayen rigartasa tare da dauko hular Rawaram blue mai dan ratsin black brown ya seta ta a kanshi , hular ta zauna kamar a kanshi kamar da kan akayi hular ta zauna d'as, agogon shi na Fendi ya makala à hannunshi na dama sannan ya dauki Turaren Tom Ford da Rasasi dake gaban mirror dinshi yafesasu à jikinshi kamin ya koma gaban  coffee table din dake gefe ya dauki key din motar dake ajiye akai da kuma wayarsa sannan ya sako takalminshi baqi na Haven ya fito  daga dakin tare da kallon agogon hannun shi yaga bakwai daidai Saukowa yake daga kan benen cikin kwanciyar hankali da natsuwa har ya karasa sauka ya isa wani kaftareren parlour da girmanshi ya dauki set din kujeru uku, karasowa yayi cikin parlour ya isa wajen wani kyakyawan dattijon mai dan haske yana sanye da kaya na alfarma , sanye yake da farin glass à  idonshi, hannunshi kuma riqe yake da remote ya saka tashar Iqra yana kallon yadda musulmai ke nuna farin ciki ga ubangijinsu,  gabanshi kuma glass table ne dauke da flask din tea an zuba Kadan a *finjal* ( karamin transparent kofi na shayi) Ya karasa tare da zama dab da kafan dattijon tare da Ce mishi "Abui nda wattu" (ina kwana) "Bara ngêmêro(Barka da Sallah)  "Bara Ngêmêriro ABUTTURAB" (barka dai ABUTTURAB)  ka tashi lafiya yace "Alhamdulillah Abui" sannan yace mishi "Jiya na tura Abubakar yace maka an sanar da ganin watan sallah daga SHEHURI (palace din sarkin Borno) yace min ka rufe kofa kuma wayoyinka ma duk a kashe", yace "ehh Abui na gajine jiyan shiyasa na shiga da wuri kauyukan da mukaje kai sadaka ne hanyoyinsu babu kyau amma Massa ya kirani ya fadamin that babanshi yace anga wata gobe sallah kuma nasan shehu da kanshi zai qira ya sanar da kai shiyasa ban sauko na fada ba", yace "ehh tun jiya shehu ya kirani", yace "okay bari in shiga  inga Ammah dan tun sassafe ta kirani wai ka shirya kana ta jirana" yayi murmushinsu na manya yace "ai Ammah tun karfe biyar da ta tashi bata koma ba sai da tashi kowa har masu aiki tun karfe biyar suka tashi suna ta hidima yace "ai Ammah akwai kokari , Allah ya k'ara mata lafiya da tsawon rai mai amfani" sannan ya tashi ya sauka daga kan matakala da basu fi biyar ba yabi wata hanya har ya isa kitchen tare da sallama wata mata mai dan madaidaicin jiki kyakyawa fara ta juyo ta dubeshi tare da amsa sallamanshi tace "Abu kowa ya tashi à gidannan kai baka tashi ba kuma bana karfe takwas za ayi sallah, Abui tun dazu ya shirya yana jiranka"  murmushi yayi tareda karasawa wajenta ya  rungume matar tareda da sumbatar goshinta yace mata "Ammah barka da Sallah", tayi murmushi kamar ba ita ke fada ba yanxu "Baaran3m Abu" (Barka Abu, Allah ya maimaita mana) suna tsaye a haka wani saurayin yaro fari kyakyawa dogo amma daga gani bai kai Abu girma ba ya shigo tare da gyaran murya yace "Ammah muna nan fa, Yaa Abun nan in yana nan mancewa akeyi damu", ta juyo tace "Babana har ka shirya ne" ya karaso tare da daukan Apple dake cikin basket a kan kitchen Island din ya dan bata rai yace "Ammah an manta da damu ana kula da Babban da ya dace ace yana gidanshi yanxu, I can't wait to have my sister Inlaw taking care of you dan a bar mana Ammah mu for us", Abu ya juyo ya harareshi yace "ai sai ka kaini gidan nawa", Ammah tace "ai gaskiya Sadiq ya fada", Abu ya girgiza kai ya fita Ammah ta dubi Sadiq tace "muje kuyi breakfast mu tafi masallaci" 

Sun fito kenan sun karasa dining area  mai dauke da round dinning table mai adon royal gold, kan dinning table din dauke yake da abinci na alfarma irin  su ndalayi, kisre(sinasir)  kêmoniye(farfesun kayan ciki) ngaji(burabusko) miyar  kubewa, yakuwa, peppered chicken, sai kunun gyada. zagaye table din yake da kujeru guda sha biyu sunja kujerun zasu zauna kenan wata yarinya fara kyakyawa da baza ta wuce 16 yrs ba ta fito à guje tana fadin "Ammah wanne zan sa........", bata karasa maganar ba tayi shiru tareda da riqe baqi tace "ooops Yaa Abu ina kwana" ya dubeta yace "kin tashi lafiya?", tace "Alhamdulillah, Barka da Sallah" ta juya ta kalli mamansu tace "Ammah Yaa Abu ba ya tafi Umara ba?", Sadiq ya juyo yana dariya yace "bai tafi ba, kuma da shi zaki tafi masallaci", ta zumb'uro baki ta d'auke dubanta daga Sadiq tana kallon Ammah tace "amma lokacin da mukayi waya da ina school ai kace min ya tafi", Sadiq ya sake murmushi yace "toh ya fasa tafiya Umaran", tace "toh", ta sake duban Ammanta tace Amma "ndaso yikêkin?", (wanne zan saka ?) Ammah tace mata "ki saka blue din", tace "toh",  ta juyo ta dubi Yaa Abu tace "da Abui zaku tafi masallaci?", Kanshi à duke yana danna waya ba tare da ya dago ba yace mata "ehhh", Ammah da Sadiq basuce komai ba sai tsayawa da sukayi suna kallonta dan suji dalinlinta na tambaya amma bata ce musu komai ba ta koma jikinta a sanyeye tana fara tafiya taji yace "Farida", tace "na'am Yaa Abu", yace mata "saura ki tsaya kwalliya ki bata min lokaci", ba tare da cewa komai ba ta juya taci gaba da tafiya har taje daki sannan ta zauna akan makeken gadon dake dakinta ta fara yiwa kanta magana tana cewa "Yaa Abun nan kullum wai sai da Abui zai tafi dan yasan kullum Abui nake bi shine kuma yace shima dashi zaije, kuma ya dinga hana mutane magana wai shi bayason surutu, Ni nan gaba zan dena bin Abui ina bin Ammah ma", tayi d'an tsaki tareda tashi dan ta saka kayanta


Ammah ce ta kira daya daga cikin masu aikin gidan tace "Fanne ba a kawo shayin Abu ba", da sauri mai aikin taje dauko flask din ta ajiye ta juya ita kuma Ammah ta tafi bawa mijinta abincinshi , ya dauki flask din tare da zubawa a cup yana kurba kadan kadan kanshin shayin ne ya sani matsawa baya saboda in naci gaba da shaqa toh sai  nace musu su zubamin, kanshi ne da ya hada na lemon grass, na'na',citta, kanumfari da cardamom seeds da mint leaves, cinnamon da Star Anis.

Bayan ya gama shan shayin ne ya dauki saucer ya Saka kisre guda daya da miyar kubewa danya da yaji naman kaji à ciki.  Ahankali ya dinga ci har ya gama sannan ya miqe ya yaje wajen hand wash basin din dake dinning area din, ya wanke hannunshi ya tsane da towel sannan ya bude fridge ya dauki robar ruwan faro,  ya juyo ya tambayi  sadiq  bayan ya kurbi ruwan "Sadiq wane masallaci zakuje da Ammah?", Yace "polo field zamuje kasan bata cika Son zuwa Ramat square dinnan ba", yace "Toh ni zan wuce bari inje inga ko Abui ya gama sai mu tafi, Allah ya kaiku lafiya, sai kun dawo", ya sake cewa Sadiq "kayi tuqi à hankali, dont play rough with my life on the road, dan na san halinka",  Sadiq yayi dariya yace "she is mine too" ya  k'arasa falon ya tarar Abui ya gama cin abinci har ya miqe yana saka babbar rigarshi Ammah kuma na tayashi ta fesa mishi turare sannan ta gyara mishi hula, Abu yayi murmushi yana son yanda suke kula da junansu dukda Sun tsufa, he admires yadda suke showing care towards junansu, Kallon da suke wa junansu kadai ya isa kasan masoyane, Abui ne ya juyo ya kalleshi "yawwa Abutturab muje lokaci ya kusa kurewa", sai kuma ya tuna ashe sarkin rigimar tasa ba ta fito ba ya bude baki kenan zaiyi magana sai gata ta fito da murmushinta mai kyau ta saka riga da skirt din  super yellow mai shudin flower ta saka hijab  shima blue hannunta riqe da jakar cardio baqa ta karaso taje ta rungume babanta sannan ta tambayeshi "Abui shawangêna?" (nayi kyau)? Yace mata " Mamana is always beautiful, sosai kinyi kyau Mamana, muje ko?", Tace "okay", su ukun suka fita su kaje inda motar take pake Abu ya budewa baban nasu mazaunin dake gefen driver farida kuma ta shiga baya. kamin su fita Ammah ma suka fito ita da Sadiq tana sanye da laffaya green and red suka nufi Motar dake pake à wajen parking mota, sai da suka shiga suka tada suka fita tukunna Abu ma yabi bayansu, su sukayi hagu ta su Sadiq kuma tayi dama.

Post a Comment for "BATUUL CHAPTER 1"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...