WANENE SHI CHAPTER 15 THEND KARSHE - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

WANENE SHI CHAPTER 15 THEND KARSHE

WANENE SHI CHAPTER 15 THEND KARSHE

- - Post a Comment
WANENE SHI


CHAPTER 15 THEND KARSHE


ABINDA YA FARU TSAKANIN IMRAN DA NAANI WATA UKU BAYA.

"Duk sanda kake tare da ita wannan b'arin na jikinta yana mstsowa dab da gab'ar nata ruhin, yadda wanda ke jikinka zai iya sensing nata, saboda haka in har tana kusa da kai... zaka iya karb'a ba tare da wanda ke jikinka yayi raunin da zai maka illa ba."

Imran ya gyara zamansa yana kallon zanen taswirar bayanin da jaamil ke nunawa a gabansa, idonsa ya kai kan zanen wani dunkulen abu dake tarwatsewa kamar yana fitar da wani hayak'i, ba tare da ya tambaya ba jaamil ya bashi amsar da yake nema.

"In har aka samu matsala, ta haka ruhin dake jikinka zai fara k'onewa."

"Bai kamata mu saka matsala a cikin lissafinmu ba, insha Allah komai zai tafi daidai, sai dai abinda nake tunani kayi wannnan binciken ne tun kafin mu san da cikin Sa'adha, a yanzu kuma baka tunanin k'arfin dutsen zai iya shafarta ta wata hanyar?"

Jaamil ya d'anyi gajeren tunanin kafin yace.

"Ai d'aya b'arin ruhinka yana jikinta, kuma karka manta a zuciyar Dr. Turaki kai ya nufa da zai bawa, saboda haka bana ganin wani abu zai faru tunda har da wanda ke jikinka da nata kusan d'aya ne, saboda haka k'arfin dutsen ba zai illata ta ba ko kad'an."

Imran ya gyad'a kansa alamun ya fahimta, yayin da idanunsa ke nuna zurfin tunanin yadda komai zai kasance kamar yadda suka tsara.

"Har yanzu bata fara susupecting komai ba?" Muryarsa ta tambaya sanda jaamil yake nannad'e takardar.

"Ba abinda tunaninta ke kawo mata, zuciyarta ta riga ta yarda damu cewa baza mu tab'a fasa bin umarninta ba kamar yadda a baya ta sa mana yardarta, shi yasa da na gaya mata cewar sai nan da jibi zaka kawo ta ba tayi tunanin komai ba, ta yarda cewa bama son a samu wata hanyar da mutane zasu zarge mu ne... shi yasa zamu bari ta fara rashin lafiya tukunna kafin a fitar da ita daga haiyacinta."

Imran ya d'ora tafin hannayensa da ya had'e waje d'aya akan lebbensa sannan ya huro iska ta cikinsu, dogwayen gashin idonsa suka had'e da 'yan uwansu na k'asa sannan muryarsa ta fito cikin kaushi.

"Zata sha mamaki jaamil, I will make her pay!"

****

Taron kamfanin ya fara gudana ne da misalin k'arfe hud'u na ranar Alhamis a watan August, a wani open park dake can hanyar barin gari waje ne k'ato da aka cike shi da shuke-shuken bishiyoyi masu cikar ganyayyaki kuma cikin wani tsari mai ban sha'awa, sannan k'asan wajen gabadaya grass carpet ne mai taushi anyi cutting dinshi so low ga kuma shukar flowers kala-kala a zube ko'ina da suke serving as fragrant!

Daga farkon inda zaka shigo wajen ma wasu tarin fulawoyin ne da aka rataye su daga can sama cikin haruffan da suka bayar da...

ORZ AT 40!

Anyi setting din wajen kamar yadda turawa suke irin parties dinsu, babu kujera ko daya da aka jera in ka d'auke ainihin resting chairs na cikin park d'in, tebura ne kawai a ajiye tsill-tsilli cikin adon yadi da flowers pink, akansu akwai tarin lemuka da snacks da aka jera, kowanne gaban table kuma akwai mutanen dake tsaye rike da lemukan ko snacks anata gaisawa da murmushi ta cikin cool music d'in dake tashi a wajen.

Wani abin sha'wa kuma, akwai wasu fitulun ado dake rataye a jikin bishiyun cikin different colours pink, blue, yellow, red...round dasu irin fitulun 'yan china. Daga can inda yake facing tables d'in high floor ne cikin ado na pink flowers akwai mike da kuma tarin Awards d'in da aka kange cikin wani box na glass.

Story continues below


K'arfe hudu da rabi daidai Imran yayi parking hadaddiyar Hyundai d'insa cikin jerin gwanon motocin dake jere a wajen.

"Welcome to my success habibty!" Ya fad'a yana kallon Sa'adha dake zaune a gefensa.

"I'm so so proud of you Ayunie!" Ta fad'a da murmushi.

A lokacin cikinta baiyi girma sosai ba, saboda haka ya b'oye tsaf! cikin doguwar maroon rigar da tasa mai small prints d'in pitch flowers a jiki, tayi rolling da wani tattausan mayafi shima pitch colour, fuskarta ba kwalliya sai rambad'eden kwallin da ta saka a sama da k'asan idanunta wanda ya k'ara fito da girmansu ya kuma b'oye d'ashewar da suka yi.

Rigar was so flowy da bayan sun fita ta dinga ja akan grass carpet d'in, Imran ya rike hannunta cikin nasa suka nufi wajen wasu kofofin glass masu duhu da suke hanyar shiga wajen, Nanne ta d'aga kai ta kalli hadaddun flowers d'in nan da suka rubuta.

ORZ AT 40!

Ta shak'i fresh k'amshinsu ya zarce har k'irjinta, tun kafin su shiga ta san cewa wajen ya had'u saboda haka taji ta matsu d'imbin mutanen da Imran ke introducing d'inta a wajensu su k'are don su shiga ciki, sai dai ta kula kowannensu d'okin ganinta a matsayin matar Imran yake.

"Ah, Imran tun d'azu nake jira...you're a bit late."

Wata sassanyar murya tasa Nanne juyowa daga kallon hanyar da mutane ke shiga, idanunta suka ci karo da wadda ke k'arasowa gabansu, wata kyakkyawar mace cikin shiga da kwalliya ta alfarma, kalar fatarta so cream mai kyau, sannan manyan idanunta cike da kyallin farin ciki sanda ta tsaya a gaban Imran, matsatstsiyar doguwar rigar jikinta kalar fara nata haskawa cikin lumshin yammar, yankan rigar was so skillfully ta yadda hakan ya fito da duk wani rise and dent (d'agawa da tashi) na jikinta.

Imran ya d'an taka baya kad'an ganin yadda ta tsaya dab! dashi, sannan ya juya da fuskarsa yana murmushi ya kalli Nanne.

"Noory ce ta tsaida mu, she kept redoing her veil wai baiyi kyau ba kafin a samu wannan ya tsaya."

Shi bai gani ba, amma Nanne da idanunta ke kanta tsaf taga giftawar b'acin rai k'arara a fuskarta kafin wani munafukin murmushi ya maye gurbinsa.

"Let me introduce you to my wife."

Taji ya sake rik'o hannunta, tun da suka tsaya a wajen abinda yake fad'a kenan, amma Nanne bata ji dad'in kalaman ba irin yanzu da yake fad'a a gaban wannan mai kama da shahararrun 'yan duniyan da bata san ko wacece ba, shi kansa a cikin muryarsa ta fahimci wani abu kamar tink'aho da kuma alfahari.

"Habibty wannan itace maryam 'yar office d'inmu, and maryam this is my Sa'adha!"

Ta had'iye k'ullutun wani abu a mak'ogwaronta sannan ta matso ta kamo hannun Nanne.

"Barkanki da zuwa duniyarmu ta ORZ Sa'adha, it's nice to finally meet you."

"Ofcourse." Nanne ta amsa cikin sanyin muryarta. "Its nice to meet you too!"

Maryam ta gyad'a kanta sannan ta juya tace da Imran. 

"Ina jin su Ibrahim sun k'araso bari in duba." 

Da wannan excuse d'in ta saki hannun Nanne da yasha wani jan k'unshi tar! dashi sannan ta juya cike da d'acin rai, Imran ba zai tab'a zama nata ba, ta biyawa zuciyarta abinda ta shafe wata da watanni tana haddacewa, amma maimakon zuciyar ta karb'a sai ta dawo mata amsar cewa. 

Dama kema kinyi jan k'unshin! 

Kafin Nanne ta k'are kallon rigar jikin maryam, Imran ya jata zuwa gaba inda mutane ke ta layin shiga, sasassanyar yammar watan August ta sake haska kyan da kowannensu yayi! 

Story continues below


Sai dai suna taka k'afarsu cikin wajen, duk wata jijiya ta jikin Imran tayi sensing k'arfin radiation d'in dake jikin dutsen Nil, a lokaci daya kuma idanunsa suka masa zooming can cikin wannan box d'in dake d'auke da tarin Awards, kuma ba tare da b'ata lokaci ba kyallinsa ya haska a idanunsa fiye da duk sauran stones d'in dake jikin kowanne Award... 

"This is beautiful! Zamu dad'e a wajen nan dan Allah?" Muryar Sa'adha a gefe ta katse tunaninsa tana kallon adon wajen. 

Bayan kusan minti talatin, gaisuwa da  gabatarwa suka cigaba da gudana wajen, kusan saida Imran da Nanne suka gaisa da kowa a wajen har kuwa da 'yan other companies d'in da aka gaiyata, daga nan kuma bayanai suka fara...Shamsudden da yake a matsayin MC shi yayi leading taron wajen kiran mutane d'aya bayan d'aya dake zuwa suna bada speech d'insu kan abinda ya shafi kamfanin... success, challenges, failure, competition, achievements da duk dai wani abu da ya kasance da kamfanin tun farkon had'a shi, don an gaiyato manyan mutane ma da tun farko aka kafa kamfanin dasu. 

Imran shi yayi bayanin achievements d'in da kamfanin ya samu cikin shekara d'ayan da yake nan, wajen ya d'auka da lallausan turancin dake fita daga bakinsa yayin da idanunsa ke kan Sa'adha, wadda tayi masa tsananin kyau fiye da kowa a wajen, kalar mayafinta ya k'ara haskawa da fito da kyan fuskarta. 

Sannan ga d'an bump d'in cikinta da yake iya ganowa, bump d'in dake bearing babynsu ita dashi... his child! wani abu da bai tab'a tunanin zai samu da ita ba, abun dake dad'a tabbatar masa cewa itace duniyarsa... gabad'aya duniyarsa tsaye tana kallonsa da alfahari cike a idanunta. 

Sai wajen Shida da rabi sannan lokacin da Imran ke jira ya k'araso, lokacin da yayi tanadi ta tsumayinsa tsawon shekara guda, lokacin da duk wani canjinsa ya faru saboda shi, lokacin da ya zamo silar gata da tallafin rayuwarsa tun a farko, lokacin da ya shigo da Sa'adha cikin k'addararsa kuma ya mayar da ita duk wani hope d'insa a yanzu, sannan kuma lokacin da zaiyi determing fansar da zai d'auka akan Naani, fansar da zai hana ta abinda ta dad'e tana muradi, abinda ta sadaukar da abubuwa da yawa nata don kawai ta same shi. 

Shamsudden ya sake gaiyato Dr. Turaki kan high floor d'in a karo na uku bayan bayanin da yayi a baya don zuwa ya mik'a tarin Awards d'in nan ga duk wad'anda aka zab'a! 

"I would first like to say my hearty congrats to each and every member that will come up here... 

Muryarsa ta disashe a cikin kan Imran lokacin da ya lura wani a gefe na kallonsa sabanin yadda hankalin kowa ya ta'allak'a wajen sauraren Dr. Turakin, ya juya da sauri amma mutumin was so fast fiye dashi, ya d'auke idonsa da wani irin sauri kafin Imran d'in ya kai ga kamashi. 

Bayan kamar minti biyar lokacin da aka fara kiran mutane suna karb'ar Awards d'in, Imran ya sake juyawa yaga ba alamar wannan mutumin. 

"They are here! Ban san ya akayi ba yarima, amma Naani ta san cewa muna nan!" 

Da sauri Imran ya juya ya kalli jaamil wanda a lokaci d'aya ya k'araso ta cikin mutanen nan ya tsaya a kusa dashi. 

Kafin ya bud'e baki yayi magana, muryar Dr.Turaki a cikin speaker ta karad'e wajen da kiran sunansa. 

Ya juya kansa a hankali ya kalli can kan high floor d'in, a hannun Dr. Turaki wannan Award d'in ne, Award d'in dake d'auke da dutsen Nil... haskensa ya haska cikin idanunsa Sannan a gefen damansa Sa'adha ta sake damk'e hannunsa dake cikin nata! 

**** 

Zuciyarsa ta gaya masa cewa dole ne ya k'ara tsananta duk wasu matakai daya d'auka a baya, don canjin wajensu bashi ke nufin cewa Naani ta hak'ura da tunkararsa ba... abinda yayi mata wani abu ne da ba zai tab'a goguwa a ranta ba kuma ba zata tab'a hak'ura dashi ba, hak'ura da abinda ta riga ta d'ora zuciyarta akai tun wani zamani da bai sanshi ba, hak'ura da abinda take masa kallon duk wani fatan da burin da da take dashi har ma da wanda zata samu a gaba. 

Hak'ura da abinda ta riga ta ta'allaka zuciyarta akai tayi sacrificing abubuwa da yawa akansa... sannan hak'ura da abinda shine dalilin 'yanta shi ta bashi duk wani gata na duniya, abinda ta yarda cewa har cikin zuciyarta zai yi mata shi, ta yaya don ya tarwatsa duk wannan burin nata a rana d'aya kuma yayi tunanin cewa zata rabu dashi cikin sauk'i...? har yayi saken da zai bar Sa'adha under protection din da a yanzu yake ganin baya amfanin komai. 

Tunda har zasu iya turo wani abu nasu har cikin gidan da yake tak'ama baza su iya shigowa ba, don wani b'ari na zuciyarsa bai yarda ko kad'an da yarinyar dake zaune a gaban Sa'adha yanzu ba, yarinyar da tunda ya shigo gidan yaji tana nemanta zuciyarsa ta d'arsa masa wani abu game da ita. 

Bayan ta gano ta kuma a can sama da cewar fitsari tayi a toilet ba abinda ya canja game da zarginta a zuciyarsa, don daga yadda take mu'amala da Sa'adha kamar ta riga ta saba da ita ne tun wani lokaci na baya, ba wai yau kawai daga fitarsa suka shigo ita da mamanta a matsayin mak'otansu ba kamar yadda ta gaya masa, k'arin wani abu kuma yarinyar was too beautiful fiye da irin mutanen da ya saba gani. 

Yaso koda sau d'aya ya bawa Sa'adha hint d'in da zai sa ta gane bai yarda da  ita ba amma hankalinta gabad'aya baya kansa, ya tafi wajen tarairayarta da bata duk wata kulawa data buk'ata. 

"Daddynki baya dariya ne?" 

Ya tsinkayi muryar yarinyar lokacin da take shan Coco pops d'in da aka kira shi ya taho dashi, Sa'adha ta juyo ta kalle shi. 

"Yana dariya mana harda kyakyatawa." Da idonta da kuma baki tayi masa inkiya da "Smile mana." 

Kawai sai ya mik'e daga kan kujerar da ya zauna yana kallonsu yace, bari in shiga in shirya. 

Sai dai har ya gama wankansa ya fito yasa kaya ba alamar Sa'adha ta biyo shi d'akin, yaji zuciyarsa ta k'ara matsowa wuya akan yarinyar, ta yaya zata d'auke hankalinta gabad'aya har haka? Bai ko taje kansa ba ya juya ya koma k'asa. A kitchen d'in ya samesu sun baje bowls cike da fulawa tana koya mata yankan wani abu akan chopping board. 

"Daddynki ya dawo!" yarinyar data d'ago tana kallonsa ta fad'a. In one swift move Sa'adha ta d'ago ta kalle shi sannan tayi wannan murmushin nata mai dulmiyar dashi cikin duniyarta. 

"Awwn you look fine, come sit... ga abincinka na gama." 

Ta fad'a tana nuna mishi kujerar dake facing d'insu, yarinyar ta zagayo da sauri ta janyo masa kujerar alamun ya zauna, yayin da Sa'adha ta d'auraye hannunta a sink din jikin island din sannan ta shiga jero masa warmers da plates d'in data had' tana fad'in. 

"Samosa muke yi Ayunie, don haka a bar space d'inta." 

Ba yadda ya iya haka ya k'araso ya zauna yana jin kamar ya shak'e yarinyar ta b'ace daga cikin rayuwarsu. 

"Baza kici ko kad'an ba?" Ya tambaya sanda ta gama zuba masa ta saka spoon d'aya. 

"I don't feel like eating, may be ko anjima." 

Da haka bata k'ara cewa komai ba ta koma suka cigaba da aikinsu, suna yi suna hirar da take sako shi a ciki amma baya magana, daga gefen idonsa ya hango sanda yarinyar ta rad'a mata cewa. 

"Daddynki bai combing gashinsa ba." 

Ransa ya kai karshe a b'aci, kawai sai ya ajiye spoon d'in hannunsa ya mik'e ya fita daga kitchen d'in tun kafin Sa'adha tayi magana, maganar da yake zaton zata yi daga lokacin daya shigo cikin kitchen d'in, amma bata ma lura dashi ba balle wai gashinsa, sannan for the first time tun zuwansu gidan ta shirya masa abincin da yaji dad'insa amma bata ko bashi hankalinta ba balle taji complimemt d'insa. 

Bai samu sauk'in b'acin ransa ba saida ta gaya masa zasu maida yarinyar gida, bayan ta cika ta da dukkanin wani abu da a san tana dashi, don leda guda ya d'auka sanda ita kuma ta rik'e hannunta suka nufi gidan nasu wanda ke d'an gangarensu kad'an, kasancewar unguwar yanayin gine-ginenta kamar irin tsarin turawa ne.

"Are you free?" 

Muryar Sa'adha ta fad'a daga k'ofar d'akin, Imran ya d'ago ya kalleta, tayi wanka tasa wata 'yar k'aramar rigar Bacci, ta tufke gashinta baya sannan jela biyu na kalbar da tayi a gaba na reto, girman cikinta ya k'ara fitowa ta fragile jikinta, a hannunta wani k'aton littafi ne mai hardcover da rubutun... 

100 THINGS YOU SHOULD KNOW ABOUT BABIES. 

"Come here." ya fad'a yana ajiye tablet d'in daya rik'e, ta k'araso ta shige cikin hannun nasa ya rungumeta sosai, k'amshin turare sabulun wanka da kuma shampoo d'inta suka had'e cikin hancinsa, ya lumshe idonsa sannan ya rad'a mata. 

"I miss you!" he breathed. 

Da dariyarta tace. "Ina naje? tunda ka dawo fa muna tare." 

"Mhm-mhm, kina tare dai da yarinyar nan, hankalinki baya wajena." 

Ta d'ago da kanta ta kalle shi. 

"Amma na ta maka magana baka amsa ba." 

Ya d'an had'e girarsa waje d'aya. 

"Noory i hate to tell you this, but hankalina bai kwanta da mutanen nan ba, akwai wani abu a tare dasu." 

Itama ta had'e tata girar. 

"Kamar yaya?" 

A cikin kansa yayi tunanin gaya mata gaskiyar abinda ruhinsa da kwakwalwarsa suka ji game da matar nan, amma sai yayi saurin dakatar da kansa, damuwa hakan zai sa a cikin kanta, damuwar da zata iya sake illata wani abun na jikinta, saboda haka ya canja zancensa da cewar. 

"A halin da muke ciki Sa'adha da kuma yanayinki, kamata yayi muyi taka tsan-tsan da kowa, kinga dukkan abinda ya faru da idanunki, bana so mu sake experiencing makamancinsa." 

Maimakon ta bashi amsa sai ta sunkuyar da kanta k'asa kawai, da alama kwakwalwarta ta tafi irin tunanin da take yi duk lokacin da zancen abinda ya faru tsakaninsa da Naani ya gifta... don abinda ya faru wani abu ne daya tabbata banda b'arin ruhinsa dake jikinta a lokacin ba abinda zai hana zuciyarta bugawa. Shi yasa tun daga wannan ranar in har ba dole ba, basa tab'a yin zancen abinda ya faru. 

Shirunta yayi yawa, sai yasa hannunsa ya janyo littafin da take rik'e dashi sannan yace. 

"A module nawa muke?" 

Jin haka yasa ta d'ago da kanta ta kalli littafin daya bud'a akan cinyarsa, da sauri ta fara flipping cikin pages d'in sannan tace. 

"Inajin 20 ne." 

Imran ya k'ifta idonsa yana kallonta, Allah ya sani bai san wani irin so Sa'adha ke yiwa d'an cikinta ba, d'aki guda ne a yanzu ta ware da ba abinda take tarawa sai kayan 'yan babies, don duk inda suka fita ko 'yar feeder ta gani sai ta siya, da suka je siyan kayan abinci kuwa rabin siyayyar ta koma ne ta kayan yara da kuma tarin littattafan da suke guiding iyaye akan rayuwar yara, tun daga girmansu kuwa har teenage years. 

Wani abin dariya har gaya masa take cewa in babynsu ya kai shekara sha biyar za'a d'inka masa kaya da yawa, saboda wai teenagers na buqatar kaya sosai a wannan lokacin. 

**** 

A cikin kwanakin da suka biyo baya alaqar Nanne da maman yarinyar nan mai suna Safiyya ta k'ara habb'aka duk kuwa da rashin son hakan da Imran ke nuna mata a kullum, amma koyaushe sai ta kawo uzirin cewa su suke zuwa wajenta kuma ba zata iya korarsu ba. 

A cikin haka ne wata rana ya dawo daga aiki ya tarar bata nan, kuma bai fita da motar dake da key d'in gidan a jikin nata ba, mamaki ya kamashi sosai lokacin daya kira ta tace masa wai tana gidansu Safiyyan. 

Story continues below


Ransa yayi mutuqar b'aci ta yadda bai ko shiga gidan ba ya tsaya a waje yana jiranta har ta k'araso, yanayin yadda take tafiya kad'ai a hankali ne saboda girman da cikinta ya k'aru sosai, amma a haka har ta iya d'aukar k'afa ta fita ba tare da ta fad'a masa ba. 

"I'm so sorry Ulfat!... Safiyya ce ta kira ni urgently wai..." 

Ta fad'a sanda ta k'araso tana k'ok'arin lalubo key d'in a cikin bunch d'in dake hannunta, bai ko tsaya saurarata ba ya janyo hannun nata sannan ya b'alle handle din k'ofar ya cire shi gabad'aya ya jata ciki, bai tsaya ba sai da suka isa can cikin falo na biyu sannan ya zaunar da ita akan d'aya daga cikin kujerun. Idanunsa cike da tsantsar damuwa yace. 

"Sa'adha yauce rana ta k'arshe da magana ma zata had'a ki da mutanen nan ko a hanya ne kuwa, ban yarda ki sake barinsu su shigo cikin gidan nan ko ke kije wajensu ba." 

Da mamaki a fuskarta tace. 

"Kamar yaya Ayunie? me suka maka? na gaya maka wallahi matar tana da kirki, basu da wani aibu... ta kira ni ne kawai don in taimake ta hidaya ta makale kafarta a cikin kujera, and i call your phone busy kana ta waya..." 

"Ban yarda ba Sa'adha, and that's it! kawai na gaya miki ban yarda ba!" ya katseta da sauri. 

A yanzu girarta biyu ta had'e cikin b'acin rai. 

"Kana nufin kenan haka zan zauna ba zan kula kowa ba, Ayunie na baro dukkan dangina fa a can, nan d'in wani waje ne da bani da kowa and for goodness sake i need some company, ta yaya zan zauna a gida ni kad'ai ba zan yi mu'amala da kowa ba kuma kullum ka fita ka barni?" 

Ya k'ank'ance idanunsa yana kallonta. 

"Kina nufin ba zaki rabu dasu ba?" 

"Haka nake shirin fad'a." 

Bai ce komai ba sai ya saki hannun nata kawai ya mik'e sannan yayi hanyar d'akinsa. 

Wasa-wasa har dare Imran bai k'ara mata magana akan hakan ba, sannan bai fasa al'amuransa a cikin gidan ba, yaci abincinta, sunyi sallah tare har ya bata wayarsa sun gaisa da Inna, sai dai duk cikin hakan fuskarsa ba fara'a ko kad'an, hakan yasa ta takura don basu saba irin wannan zaman ba, zuciyarta ta dinga gaya mata cewa maganar da ta gaya masa bata kyauta ba kuma bai dace ba, saboda haka bayan sallar isha ta nufi cikin study room d'insa da niyyar bashi hakuri. 

A jikin wata shelf ta same shi yana kokarin zaro wani littafi, ta tsaya dab da bayansa sannan ta kira sunansa cikin wata murya a hankali, hakan yasa shi juyowa rik'e da littafin ya kalleta ba tare da yace komai ba. kanta na sunkuye tana wasa da yatsunta tace. 

"I'm sorry dan Allah, kayi hakuri, bai dace in fad'i abinda na fad'a maka d'azu ba kayi hakuri." 

Imran yaji k'afafaunsa sun manne a inda yake tsaye? Sau nawa ne wai zuciyarsa take son Sa'adha, a yanzu yake shirin zuwa ya bata hakuri don zuciyarsa ta gaya masa cewa abinda yayi mata bai kyauta ba, tayi sacrificing abubuwa da yawa a rayuwarta saboda shi amma shi ya kasa hak'ura da wani abu guda d'aya kawai da take so? kamata yayi ya kyaleta ta cigaba da mu'amalarta dasu, tunda har yana bincike ta baya akansu ba tare da ta sani ba. 

Jin yayi shiru yasa ta d'ago ta kalle shi idanunta alamun hawaye. 

"Ayunie kayi hakuri mana, na gaya maka na daina, kuma Allah na kira wayarka har..." 

Lips d'insa masu d'umi suka sauka akan nata, bakinsa na k'amshin permanent chewing gum d'insa na mint, hannayensa suka jata cikin jikinsa tare da rungumeta baki d'aya! 

Ta rufe idanunta a hankali sanda kwakwalwarta ta shafe komai da ya faru a wannan ranar, ta manta zancen wata Safiyya da 'yarta, ta manta zancen da suka yi d'azu, ta tuno kawai cewa Imran yana sonta, he wanted her and she was all his! saboda haka ta nannad'e hannayen ta a wuyansa sannan ta bud'e kowanne waje a zuciyarta don ta karb'i sak'onsa. 

Story continues below


A lokacin ne kuma abin ya faru, wani abu da bai tab'a kasancewa ba, wani abu da ya tabbatar mata cewa da gaske ne ita d'in a lokacin ta zama UWA, halittar dake cikinta yayi motsi da wani irin k'arfi! 

*** 

Karfe d'aya na daren wannan ranar Nanne ta fito daga d'akin rik'e da waya a hannunta, sleeping dress d'in jikinta iya gwiwa, ta d'ora 'yar top akai. 

"Ayunie ka gaya min inda kake mana." 

Ta cikin wayar yayi murmushi sannan yace. 

"Kina ina yanzu?" 

"Ina falo." 

"Good, now ki nemo letter N a falon." 

Girarta biyu ta had'e waje d'aya. 

"Letter N kamar yaya?" 

"Just find it." 

Mamaki ya kamata, me kuma Imran zaiyi da tsakar daren nan? ita dai ya san tayi bacci tun wajen sha d'aya saura lokacin da suke kallo, shi yasa lokacin da k'arar wayarta ya tashe tayi tunanin alarm din asuba ne, amma sai taga kiransa ne kuma k'arfe d'aya na dare, ya kira kusan sau uku kafin ta wartsake daga baccin ta d'auka... mamaki ya sake kamata da yace wai ta fito falo zai fada mata wani abu kuma kar ta kashe wayar, ta lalubo 'yar top din rigar baccinta ta dora sannan ta fito, yanzu kuma yace wai ta nemo letter N wano mamakin ya sake cinye ta, amma sai ta biye masa ta shiga bincikawa cikin falon. 

"Atleast give me hint mana, ya letter N d'in take?" 

Yayi murmushi sosai kafin yace kawai ta cigaba da dubawa, sai tayi kusan minti d'aya tana d'aga abubuwa sannan ta gano ta wani sabon pillow mai shape d'in N a tsakanin kujerun. 

"A ina muka sami wannan pillown?" 

Ta tambaya a cikin wayar da har yanzu ke kunnenta. 

"Bravo habibty! yanzu ki taho dining, ki nemo double O. 

Ta d'age girata d'aya kamar yana kallonta. 

"Is This a game?" 

"I think so, just find the O's." 

Tana iya picturing yadda bakinsa ya zagaye a fad'ar O's d'in, tayi murmushi sannan ta nufi dining d'in rik'e pillown N. 

A can ma tasha duba kafin ta samo O's d'in guda biyu a tsakanin serviette tissue. 

"Now find the last letter Y a kitchen, sai in gaya miki inda nake." 

Tana shiga kitchen d'in letter Y da aka hura ta ballon was waiting a saman island. Ta zube sauran gabad'aya suka had'u suka bada sunanta, sunanta a wajen Imran. 

NOORY! 

"Awwn... this is too awesome! Thank you Ayunie." 

"Thank you too Babe. Ki bud'e back door d'in ina jiranki." 

Jin haka yasa ta juya da sauri ta bud'e k'ofar kitchen d'in wadda take leading zuwa bayan gidan, wajen kamar gidansu na can ne, d'an karamin garden ne da wajen shanya. 

At first ba abinda idonta ya gane mata sai duhun shuke-shuken, Sai da Imran ya kunna fitila ne sannan ta hango shi tsaye a tsakiyar wajen, samanshi katuwar Banner ce an rubuta. 

I'M SORRY NOORY..!
AND CONGRATULATION FOR THE FIRST KICK...! 

Ta rufe bakinta da dukka hannayenta biyun saboda tsananin mamaki, This is just out of the world. 

Oh my heart, oh my heart! 

Ta fad'a a hankali lokacin da ya ware mata hannayensa alamun ta taho, sai a lokacin ta janye wayar daga kunnenta sannan ta ruga da saurinta ta shige cikin hannayen nasa shi kuma ya binne ta a jikinsa. 

Story continues below


"I'm sorry akan abinda ya faru d'azu habibty... I shouldn't have told you ki daina kula su, kawai zuciyata ce ke bani...." 

"Shshshsh...." Tayi saurin katse shi tana d'ago da kanta. 

"Abinda ya faru d'azu ya riga ya wuce Ulfat.... and this is just.... WOW!" 

"I'm glad you like it." Ya fad'a da murmushi. 

"A ina ka samu duk wannan abubuwan?" 

Ta tambaya tana kallon flowers d'in da aka jera a jikin Banner. 

"Interior Company da suka yi mana tsarin gidan nan na kira." 

Ta jinjina kanta tana sake kallon abun, wato komai inda kud'inka da shagalinka, a yaushe har ya kira su suka had'a wannan abun. Hasken flash d'in wayarsa ya dallare idanunta. 

"You look beautiful in kina tunani." 

"Noory do you care for a dance?" 

Ta zare idonta a lokaci d'aya. 

"Rawa yanzu?" 

"Yes, I just thought we should celebrate the first kick." 

"Kusan fa k'arfe d'aya da rabi yanzu na dare Ayunie." 

"Me kike tsoro?" 

"Aljaanu mana." Ta fad'a kai tsaye. 

Ya kifa kansa cikin kafad'unta yayi dariya sosai kafin ya d'ago da kansa. 

"You can't be serious dear, wane aljaani kike tsoro in kina tare dani, beleive me ko cikin gidan nan ba zasu iya shigowa ba balle kusa dake." 

Murmushin da tayi ya bashi damar sake tambaya. 

"May I have this dance habibty?" 

"Dance ba wak'a?" Ta tambaya girarta d'aya a d'age. 

Da sauri ya matsa baya ya d'auko bluethoot d'insa. Yana dannawa wakar ta karad'e wajen cikin mid volume. 

Ya k'araso ya miko mata hannunsa, ta d'ora nata akai sannan yasa d'aya hannunsa ya nannad'e kugunta... 

"So slow..." 

Ya rad'a a kunnenta sanda suka fara bin takun wak'ar. 

Darling, just kiss me slow, 

Your heart is all I own 

And in your eyes you're holding mine 

Baby, I'm dancing in the dark 

With you between my arms 

Barefoot on the grass, listening to our favorite song 

When you said you looked a mess, 

I whispered underneath my breath 

But you heard it, 

Darling, you look perfect tonight... 

Ya sake rik'e ta a cikin jikinsa, sannan ya sunkuyo da fuskarsa ya d'ora goshinsa akan nata, tsinin hancinsa na tab'a nata, a hankali muryarsa mai taushi da zurfi ta shiga bin wak'ar... 

Well I found a woman 

Stronger than anyone I know 

Story continues below


She shares my dreams, I hope that someday I'll share her home.. 

I found a love, to carry more than just my secrets 

To carry love, to carry children of our own... 

Nanne ta rufe idanunta a hankali tana jin zuciyarta kamar zata kumbura ta fashe saboda dad'i, that moment was the PERFECT and most wonderful moment da a wajenta, tun lokacin data samu cikin nan suke fuskantar abubuwa kala-kala, ba irin tashin hankali da tudun da basu fad'a ba, amma yanzu da take cikin hannunsa a wannan lokacin ta manta da duk abun da ya faru a baya, ta manta da komai... 

She wanted to start everything afresh! 


***** 

"Yanzu toh shi ya fita?" Inna ta tambaya daga cikin wayar. 

"Eh ai kusan kullum sai yamma can yake dawowa, asabar da lahadi ne kawai yake gida." 

"Toh gaskiya kuwa zamanki bai kyautu a haka ba, kinga tun wancan watan nake faman lalubawa in samo wadda zata zauna dake amma abun na neman gagara, don can niger duk yawanci zawarawan sunyi aure wasu kuma sun koma d'akin mazajensu. 

Anan kuma su lami ne kad'ai da ba shiri kuke yi ba, in ba suba kin san duk sauran ma'aikatan da aurensu... wancan satin ma muku yi zancen da Azumi take cewa ko ita zata zo, nace ai tafiyarta ba zai yiwu ba, don kusan komai na harkar kitchen din nan yanzu a hannunta take, don haka ki tambaye shi shi a nasa 'yan uwan a samo wata dattijuwar tazo ta zauna daku, amma ba zai yiwu ace a wannan halin kina zama ke kad'ai a gida ba." 

Nanne ta damk'e wayar a kunnenta lokacin da ta lalubi kujera ta zauna, bata dad'e da gyara gidan tsaf ba, saboda haka sai k'amshin turare yake, a gabanta flat screen d'in Tv ne ke nuna tashar "Star life" a lokacin k'arfe uku saura ne na rana. 

"Ko ba kya jina ne?" Inna ta sake fad'a daga cikin wayar. 

"Eh naji inna, in ya dawo zan fad'a masa insha Allah." 

"Yawwa kinga inda wata ai ko haihuwar ce ta kama ba sai kin taho ba, daga nan ma a samo wata kafin sannan, tunda dama banda su maryama da suka rako ki ai ba wanda yaga inda kuke." 

Jin haka yasa Nanne ta turo baki kamar tana ganinta. 

"Gaskiya Inna ni nafi son in taho nan, kome za'a yi maka ai ba kamar a gida ba kinga." 

"Toh wannan kuma sai kin shawarta dashi, tunda shi ba 'yan uwa a kusa ne dashi ba, yaushe za'a barshi ya zauna shi kad'ai?" 

"Karki damu Inna, na san ma zai yarda." 

"Ko kuma zaki rok'e shi ya yarda ba." 

Tayi dariya sosai kafin tace. 

"Toh ke da ba lafiya ba, yaushe zaki yi wata jarabawa." 

"Inna ai kafin lokacin ina jin ma munyi wata d'aya." 

"Da d'anyan jego zaki kenan kamar dole?" 

Sai da ta sake wata dariyar sannan tace. 

"Inna koh a yanzu fa ba wani ciwo nake ji ba, balle a lokacin insha Allah, kawai dai ramar ce." 

A sannan ne taji kamar ta gaya mata motsin da a yanzu kusan kullum cikin nata keyi, alamun cewa ko meye a ciki yana da rai da kuma k'oshin lafiya, amma haka kawai sai taji bakinta ya k'ulle. 

"An kawo kud'in auren Rahma jiya." 

Idanunta suka zare a lokaci d'aya. 

"Amma shine bata gaya min ba? shekaranjiya fa muka yi waya da ita." 

Story continues below


"Yo ai itama bata san za'ayi haka ba, tambaya kawai suka zo a jiyan kuma aka b'ige da karbar kudi, ai kin san ma yaron, d'an mak'otansu hajiya karima... yaro mai hankali wallahi." 

"Ai shikenan na kira ta yanzu in mun gama wayar, Allah ya tabbatar da alkhairi." 

"Ameen, ina Aminatu kuwa?" 

"Tana nan ranar juma'a ma munyi waya harda ummanta tace a gaishe ki." 

"Ita ba'a fara zancen nata auren ba!" 

"A'ah gaskiya, sai dai nan gaba tukunna." 

"Toh Allah ya had'a kowa da rabonsa." 

"Ameen, mama Azumi bata kusa ne?" 

"Eh, ta fita nan baya gaisuwa, k'anwar iyan shehu ce ta rasu wajen haihuwa." 

Haka kurum Nanne taji gabanta ya bada wata irin k'ara data amsa har cikin kunnunwanta, jikinta yayi wani iri a lokaci d'aya, da kyar ta iya lalubo muryarta tace. 

"Allah sarki, Allah ya jik'anta." 

"Ameen dai, tayi shahada wallahi, ance 'yarta tana nan kyakkyawa da ita." 

Kafin Nanne ta amsa, falon ya karad'e da sound din bell da aka danna daga waje, Saboda haka tace. 

"Inna zan kira ki anjima, inaga nayi bak'i ne." 

A hanyarta ta bud'e k'ofar text d'in Imran ya shigo yayi appearing akan screen d'in wayar. 

I'll be home a bit late habibty, zan yi miki bayani insha Allah when I'm back, love you Babe. 

...like crazy! 

Da murmushinta tayi locking wayar sannan ta bud'e k'ofar. A lokaci d'aya k'arar b'allewar wani abu kamar k'ashi ta d'auka a bangwayen falon sanda wayar hannunta ta fad'i ta tarwatse a k'asa. 

"Aaahhh..." 

Muryar Nanne ta fito a hankali yayin da ta zare idanunta, kwakwalwarta ta kasa fahimta, ta kasa d'aukar abinda ke faruwa, A cikin cikinta wani abu ya fizge zuwa tsallaken b'arinsa. 

Wani irin duhu ya rufe hasken idonta lokacin da k'afarta ta kasa d'aukarta ta fad'i k'asa akan cikin nata, a lokacin tayi k'ok'arin lalubo wani abu da zata kama amma komai ya d'auke mata, makogwaronta ya cika da radad'i sannan duk wata iska ta d'auke mata. 

Hannayenta dake rawa suka lalubo kan cikinta da niyyar kare abinda ke ciki, amma d'aya ya karasa d'ayan kuma ya kasa kaiwa, sai kawai ta kwalla wata irin k'ara da wani abu kamar shak'ewa ya katse ta, sannan bakinta ya bullutso da wani tarin jini daya tarwatse har cikin falon! 

TARIYAR BAYA (FLASHBACK) 

K'ARSHEN ABINDA YA FARU TSAKANIN IMRAN DA NAANI WATA UKU BAY'A. 

"Me yasa?... 

Muryar ta fito da kaushi kamar koyaushe, cikin amonta mai girgizarwa. 

"Me yasa zuciyarka ta juya min baya?" 

Imran ya d'ago da idonsa ya kalli manyan-manyan hallitun dake tsaye a gabansu basa bada ko karamin motsin da zai nuna cewa suna raye, a wancan lokacin d'akin da suke tsaye nasa ne shi kadai, amma a yanzu wannan d'akin da suke ciki mallakinsa ne shi da Sa'adha. 

Sa'adhar dake rik'e cikin jikinsa a sume, tun bayan kallon farko da ta yiwa halittun tsananin tsoro ya d'auke numfashinta, tsananin tsoron ganin irin siffar da Allah bai halitta idanunta na bil'adama jurewa kallo ba. 

Zuciyarsa a rikice take, yana fatan suman nata ya tsaya a iya suma kawai, kar ya lahanta jikinta ko kuma halittar dake cikinta, amma duk da haka idanunsa sun gagara d'aukewa kallon wannan dunkulallen hasken dake lilo a iska, hasken daya tarwatse ya baje ko'ina a cikin d'akin, hasken dake nuna tambarin irin na adon sarautar NAANI. 

"Na dad'e da sanin cewa Bil'adama butulun mutane ne, amma ban taba sanin cewa butulcin nasu har zai iya shafar jinsin daba nasu ba don kawai kwaikwayon halitta ya shiga tsakaninsu... haka ban taba sanin cewa akwai ranar da umarnina zai zama abin wofantarwa gare ka ba yarima, ni din dana zama duk wani gata da tallafin rayuwarka, wane daraja kake dashi bayan tawa? wace rayuwa kake da ita bayan wadda na baka? 

Nice zahirinka! nice sanadin duk wani abu daka samu a cikin jinsinka da kuma wannan rayuwar da  baza ta taba d'orewa ba, na kawo ka cikinta ne don ka cika min burina ba wai don ka gina sabuwar rayuwar tare da wannan k'azamar halittar ba, k'azamar halittar da har zata sa ka iya yaudara... 

"Yaudara...?" 

Muryar Imran ta katse ta cikin kaushi da kuma tsananin b'acin rai, abinda ya haddasa motsin wad'annan halittun dake gabansu don hakan wani abu ne na farko da d'ayansu bai taba gani ba, in har akwai wanda ya tab'a yin katob'arar hakan, toh tabbas baya raye balle har ya iya bada labari. 

Story continues below


Shi kansa Imran sai da yaji sanyin jikinsa lokacin da idonsa ke manne akan hasken daya tabbata tana iya hango shi ta ciki, shugaba kona kwaikwayo ne kuwa akwai kwarjinin da yake dashi, amma ya yak'i zuciyarsa da tunanin maganganunta na cikin habler nan ya fadi abinda yake ganin gaskiyarsa ne. 

"Har zaki iya amfani da kalmar yaudara akaina? har zaki iya furta ta bayan kece abu na farko daya kasance a cikinta... rayuwar da kike tak'amar kin bani bata cike da komai face tarin yaudara wadda kika lullub'e don samun amfanin kanki, ba don tallafina ba kamar yadda kike tink'aho tsawo shekarun nan. 

Munji komai daga gare ki lokacin da kike gayawa Sareefa sirrin da kika dad'e kina b'oyewa, babu sauran wani abu da zaki kara rufe mu dashi, maganganun da duka fito daga bakinki sun haska mana duhun da kika dad'e da samu a ciki don amfanin kanki da kuma diyarki , ba don kariyar al'umarmu ba kamar yadda kike ikirari, Allah ya sani na soki kuma na girmamaki da dukkanin zuciyata, ina ganin cewa kin maye gurbin duk wani dangi nawa dana rasa, ban fahimci cewa kina sani hak'a ramin dake ta yin k'asa dani bane... kuma abin mamaki harda d'an 'yar'uwarki, wadda ta sadaukar da abubuwa da yawa a rayuwarta saboda cigaban ki, amma kike tanadin sa mata bak'in cikin da zai tsaida zuciyarta, ki kashe d'anta saboda samun cigabanki. 

Farin ciki na daya ban taba d'ora raina akan kwadayin samun sarautar da kika yi ta mak'ala min ba, balle har in d'ora raina wajen son d'iyarki, saboda haka a yanzu bana tunanin tsakani na dake akwai wani abu kuma da yayi saura. 

Da gaske ne, na karbi dutsen NIL a yau, dutsen da kika d'auko ni kika 'yanta ne saboda shi, dutsen da kika sadaukar da abubuwa da yawa akansa, sannan dutsen da a yanzu ya zama mallakina zan iya sarrafa shi ta hanyoyi masu yawa, hanyoyin dana yanke shawarar baza su taba giftawa ta gabanki ba. 

Na riga na san amfanin dutsen nan a yanzu, na san irin kariyar da yake bawa duk mamallakinsa, irin kariyar da duk karfin iko da tsafinki ba zaiyi tasiri akansa ba, shi yasa kike nemansa ido rufe... don ki k'ara girma da martabar sarautarki yadda ba mai iya ganin bayanki, saboda haka tsarin da muka yi tun farko ya wargaje Naani, ba zan taba baki dutsen nan ba kuma kema ba zaki tab'a iya tunkarata ba, na zabi in zauna a wannan rayuwar fiye da rayuwar k'aryar da kika d'ora ni akai. 

Wannan shine zahirina Naani, saboda haka godiya d'aya zan miki, ta jikin bil'adaman da kika iya sarrafa min!" 

A wannan lokacin Imran ya tabbata in har Naani tana jinsa toh tabbas mamaki da rud'anin maganganunsa sun lullub'e kwakwalwarta, saboda kowacce kalma daya fad'a.. every single word abu ne da bata taba zata ba, bata taba zaton sunji kalamanta da sareefa ba sannan bata taba zaton akwai ranar da zasu san b'oyaiyiyar manufarta game dasu ba. 

Sunfi karfin awa d'aya zaune a hakan ba tare da ta sake magana ba, Imran ya riga ya sani, ita din a koyaushe ba mai tada hankalinta bace, duk yadda abu ya kai ga rikicewa da kuma hargitsi, zata bishi ne a sannu har ta sami lagon da zata ci galabarsa, Abu d'aya dake burgeshi game da tsarinta, sannan kuma abu d'aya da yasa ta sami sarauta akan 'yar'uwarta! 

A cikin tsawon wannan lokacin, Imran ya san ba don k'arfin radiation d'in dutsen Nil dake fita daga hannunsa ba, babu abinda zai hana wad'annan halittun kawo k'arshen rayuwarsa shida Sa'adha dake rike a jikinsa, don suna fahimtar umarnin Naani ba tare da ta furta ba... sai dai a wannan karon daga ita har su d'in basu da karfin karasowa kusa dashi. 

"Zamu gani yarima, lokaci zai baiyana abinda alkalami ya riga ya bushe akansa!" 

Ya lumshe idonsa a hankali lokacin da daga hasken har halittun suka b'acewa ganinsa, ya san sarai me maganganunta suke nufi, zata nemo jaamil ta hukunta shi akansa, bata san cewa nasu tsarin yafi gaban tunaninta ba, yadda yayi wa kansa katanga daga gareta, haka ma bazata taba iya tunkarar jaamil ba. 

Story continues below


A hankali ya ware tafin hannunsa d'aya, rabin dutsen Nil ya baiyana akansa, rabi kuma yana tare da jaamil da Bwama. 

**** 

Jikin Nanne wanda gabad'aya ya baci da jinin dake fitowa daga bakinta ya shiga jijjigawa sannan idanunta dake zare basa d'auke da wani emotion. They were pale and blank! 

A cikin wannan yanayin muryoyin Bwama, jaamil da kuma Imran ke amsawa cikin k'arfi da kuma ihun da baza ka iya rarrabe kalmomin da suke fad'a ba. 

"lazzu nah se ka our tad to jikal vanmbiyarda jo! (Ka rik'e ta sosai yarima, kar ka bari ta fita daga hannunka!) 

Muryar Bwama ta fad'a tana kallon Imran wanda ke rik'e da Sa'adha a jikinsa tana jijjigawa da wani irin k'arfin dake neman gagararsa, ba zaka iya tantance cewa k'arfin abinda ke cikinta ne kusan d'aya da nasa ba ko kuma raunin dake mamaye dashi ne na ganin Noorynsa cikin wannan mummunan halin, idanunsa na manne da nata dake a zare hawaye na zirara ta kowanne gefensu, don ba zai iya kallon sauran jikinta ba, sauran jikinta dake cikin azaba... sauran jikinta da k'arar karyewarsa ta cika kunnunwansa, he was afraid to save the memory in his head! 

"Wourjuoni!" 

Muryar Bwama ta fad'awa jaamil da karfi cikin abinda baifi kiftawar ido ba ya mik'o mata wani dogon abu mai kama da allura, a cikinsa wani koren ruwa ne irin nasu dake kashe zafin waje, Imran na ganin haka ya k'ara rik'e ta yayin da Bwama tasa hannu ta yage kusan rabin doguwar rigar jikinta, jaamil ya juyar da kansa gefe. 

"Ka samo mata iska... ka samo mata numfashi, lour ni biryam!" 

Muryar Bwama ta sake bashi wani umarnin. 

Imran ya sunkuyar da fuskarsa kan tata da sauri, yayi pressing lebb'ensa akan nata masu laushi sannan ya shiga hura iska cikin mak'ogwaronta da dukkan k'arfin da zai iya, zak'in ragowar jinin dake bakinta ya gauraye a nasa bakin, yana iya jin yadda zuciyarta ke bugawa a hankali daga can k'asan k'irjinta. 

Keep it going! 

Ya ayyana da k'arfi a cikin kansa. 

You promise Sa'adha, kin min alkawari! Stay with me, kina jina? Stay! keep your heart beating! 

Ya tsaya da hura mata iskar sanda Bwama ta zura abun cikin fatar hannunta, zafin wannan koren ruwan da ya shiga bi cikin jijiyarta yasa jikinta k'ara girgizawa da k'arfi, Imran yasa karfinsa ya k'ara damk'e ta sosai cikin hannunsa, Sai da ya gama shiga duka sannan Bwama ta zare abun da sauri, a lokacin ne kuma wata k'ara a cikinta tasa kowannensu ya tsaya cike da tsananin tsoro, sannan idanunsu suka k'ame akan nata cike da tsabar hanqoro da kuma rok'o, rok'o kar tunaninsu ya zama gaskiya wajen fatan samun wata alama daga gareta, ko da kuwa motsin gashin idonta ne amma ba abinda ya biyo baya... 

A wannan lokacin, azabar da Nanne take ji ya maye gurbi da wani irin rad'ad'in ciwon baya wanda yasa taji numfashi ya tsaya a makogwaronta, taji kamar kowanne b'angare na jikinta yana cirewa ne daga jikin d'anuwansa. Zafin ya cigaba da shiga  jijiyoyinta, taji kamar ta mike ta tafi a guje ko zata iya barin ciwo anan inda take amma ta kasa motsa koda hannayenta, wani irin nauyi ya manneta a jikin Imran dake rik'e da ita, kamar an dora k'aton dutse akan kirjinta, wanda nauyinsa ya binne ta cikin azababben ciwon dake tafiya yana mamaye sauran gab'ob'in jikinta. 

Ta san tasha gaya wa kanta irin mutuk'ar wahalar da zata sha duk sanda da wannan ranar tazo amma bata tab'a kawowa wai abubuwa zasu rincab'e haka ba, idonta ya sake cika da duhu, ta kasa ganin komai amma kunnenta na iya d'auko mata sautin muryoyin da a yanzu suka cigaba da fafutuka da kuma ihu akanta sakamakon alamar data basu cewa tana raye, fuskar imran ta sake sunkuyowa sannan iska ta cigaba da shiga cikin huhunta, tana busawa da zafi a ki'rjinta. 

Story continues below


"Stay Sa'adha, dan Allah... you promised!" 

Muryar tasa ta busa a cikin bakinta, so weak yadda bata tab'a jinta ba. 

Taso kwarai ta iya bashi wata alama a sannan alamar cewa tana kokartawa da dukkan iyawarta wajen cigaban bugun zuciyarta ba don kanta ba sai don ta raya abinda ke cikinta har ya k'arasa fitowa kar burinta ya tashi a banza... sannan kuma don tarin mutanen da tasan zata ruguza wani b'angare na rayuwarsu in har babu ita. Imran a farko, mijinta da rayuwarta da tasa ke nannad'e jikin zare d'aya, in har babu ita bata san ya duniyarsa zata kasance ba. 

Sannan Inna-- tsohuwar data raine ta lokacin da ta rasa duk wani gata da tallafin UWA, tsohuwar dake mutuk'ar sonta fiye da kowa da komai a rayuwarta, ta yaya zata iya sata cikin kunci bayan b'oye mata sirrin Imran da tayi? 

Ga Baffanta ma, bawan Allah dake ganin ya cuci rayuwarta wajen aurar da ita da wuri, me zai yi tunani a yanzu in har babu ita? Ta san kuma ko yaya ne Nuratu ma zata azabtu da rashinta, bata da shak'uwa da ita amma akwai k'auna da Allah ya halitta a tsakaninsu irinta d'a da mahaifi. 

Ga tarin 'yan gidansu ma, Rahma, Mama Azumi, Sadiq da duk wasu ahalinta... Zata rayu ko don su, in ba haka ba a wannan azabar ji take yi kamar zata iya sakin komai ta sallamawa duhun dake shirin lullub'e idanunta, ta barshi yaci galaba a kanta, yaci galaba wajen tura ta zuwa wannan k'arshen da ta san zata rabu da duk wani ciwo... Mutuwa! 

Amma tunanin ahalinta shi ke sawa ta tattaro duk ragowar k'arfin jikinta wajen rik'e abinda ke cikinta, don duk yadda ta kai ga son rayuwa saboda su, ba d'aya bane da tsoron rasa jininta, dole ne ta sami hanyar da zata cece shi ko da kuwa hakan zai zama abu na k'arshe a yanzu da zata iya yi... Don shine Babban fatan zuciyarta, zata iya hakura da duk wata wahalar da zata sha amma banda rasa Babynta. 

Zafinsa ciwon da take ji ya cigaba da k'aruwa. Sosai da sosai, Sosai data kasa tantance ko yanka wajen akeyi ko kuma ruhinta ne ke kokarin fita, taji kamar ta mik'a hannayenta ta danne wajen ko zata ji sauk'i... Amma ta kasa! su d'in a yanzu ba komai bane face wasu matattun abubuwa dake rik'e cikin hannun Imran, hannunsa da baza ta iya sake shafawa ba har abada! 

Nak'udar tata ta cigaba da k'aruwa a koina har saida ya shafe duk wani ragowar k'arfin jikinta! A lokacin ne kuma abin ya faru, abinda ya zamo fata da kuma jigon rayuwarta tsawon wani lokaci... abinda ya zamo sanadin dukkan wata gwagwarmaya da kuma k'addarar rayuwarta! 

Taji alamun fitowar d'anta, fitowar dake yad'uwa tana b'alla duk wani abu da ya zama a hanyarsa ta fitowar, a lokacin kums wani abu mai kaifi ya yanka fatar cikin nata hanya ta bud'e, hanya mai fad'i data zama mafarin fitowar halittar dake cikinta tsawon watanni bakwai! 

Imran ya runtse idonsa lokacin da k'arar yankawar fatar Sa'adha ta cika kunnensa, ya damk'e hannayeta sosai a cikin nasa wajen tsaida kansa kokarin hana Bwama tsaga jikin nata da zuciyarsa ke tursasa shi yayi... ya san babu wata hanyar bayan haka, babu wata hanyar da zasu raya abinda ke cikinta bayan a bud'e cikin nata don a yanzu ko yatsanta baza ta iya d'agawa ba, balle ayi zancen karfin da zata iya haihuwarsa da kanta. Ya cije lebbensa na k'asa har sai da hak'oransa suka datsa ciki yayi zurfi. 

Bayan wannan k'arar yankawar fatar cikinta, wata k'ara ce ta biyo baya... wata k'ara da ta firgitashi yaji kamar an jona wutar lantarki ta cikin jijiyoyinsa, k'arar b'allewa da dagargajewar abu daga cikinta, alamun koma meye a cikin nata yana neman hanyarsa ne ta fitowa a yanzu da ya sami hanya. 

Don hana kansa ganin hakan da kuma k'ara bawa jikinta k'arfi, ya sake sunkuyar da bakinsa kan nata ya cigaba da hura mata iska cikinta, hakan yasa tayi wani d'an guntun tari idanunta dake kusan a rufe suka juya kamar mai k'ok'arin lalubo wani abun. 

"Kina jina Sa'adha? stay! Ba zaki tafi ki barni ba... keep your heart beating! kinyi alqawari!" 

Idanunta suka sake juyawa, kamar tana so ta lalubo shi a cikin su, duk da bata ganinsa ya tsaida nasa a cikinsu sannan ya k'ulle su bada niyyar daina kallonta ba. 

A lokaci d'aya sai jikinta yayi sanyi k'alau cikin hannunsa amma numfashinta mai nauyi na cigaba da fita kuma zuciyarta na bugawa a hankali, hakan yasa ya fahimci cewa komai yazo k'arshe kenan... hargitsin dake azabtar da ita yazo k'arshe, abun da ke cikinta ya fito duniya... duniyar da a yanzu take a hargitse! 

Shiru na wani lokaci ya biyo baya kafin muryar Bwama ta karad'e cikin falon a hankali kamar mai rad'a. 

"Masha Allah... Ourjaani yam!" ( He's so beautiful!) 

Imran bai d'auke idonsa daga kan na Sa'adha ba, wad'annan chocolate idanun nata masu kyau da a yanzu suka hargitse suka koma jawur! 

A cikin wannan azabar da Nanne take ji, a cikin wannan lokacin tunaninta ya gangara da ita can baya, lokacin data fara had'uwa da Imran, lokacin da ta fara ganinsa tsaye daga jikin wannan tsohuwar container ta dawo daga islamiyya, lokacin da ya fara shiga cikin tunaninta...  wannan lokacin da bata san WAYE SHI ba, wannan lokacin da bata san komai game da rayuwarsa ba, wannan lokacin da zuciyarta ta fara sonsa ba tare da wani tunani ba, Sannan wannan lokacin da duk wani hargitsin rayuwarta bai faru ba! 

Babu wani abu guda d'aya da taji zuciyarta tayi regretting yinsa tun daga wancan lokacin har zuwa yanzu, saboda daga sanda da ta fahimci fara son sa, she knew she would follow him anywhere... and she have! kuma inda ubangiji zai sake dawo mata da komai baya, she beleived she would'nt change a thing! game da rayuwarta. 

Imran k'addararta ne kuma tana sonsa, tana sonsa da dukkan ruhinta! 

Ta san cewa a lokacin dukkaninsu a hargitse suke wajen ceton ranta daga yadda take jin ana tab'a kowacce gab'a ta jikinta da sauri da kuma k'ok'arin had'e yankan dake cikinta, da abubuwan da ake zura mata a baki da shigar tarin abubuwa cikin jikinta... amma kwakwalwarta bata d'auko mata dukkan hayaniya da maganganunsu, sai 'yan k'ananan abubuwan da bai kamata ace su take iya fahimta ba. 

Tana iya k'irga kowanne sauti na fitar numfashin Imran dake kusa da ita, na Bwama da jaamil da yayi nesa dasu sannan 'yan k'ananan shallow numfashin da ta tabbata na abinda ta haifa ne, Tana iya iya jin faint k'arar A.C dake cikin d'akin, daga can kuma sautin k'arar wani abu, tana iya jin k'arar iskar dake kad'awa daga wajen gidan, tana iya jin fitar numfashi da kuma motsin abubuwa dake a can wajen... 

Tana iya jin komai! 

Tana iya jin komai d'in da bai kai muhimmancin bugun zuciyar Imran dake bugawa kamar zata fito daga cikin k'irjinsa a kusa da ita ba, Sannan tana iya jin komai d'in dake zamewa daga cikin kwakwalwarta kamar lokacin da mutum ke k'okarin rike ruwa a tafin hannayensa. 

Bayan Second d'ari shida da tamanin da uku komai yazo k'arshe, komai yana nufin duk wani fata da burin rayuwarta! 

Komai kuma yana nufin komai... sannan komai kuma yana nufin duk wata gwagwarmaya da k'addarar rayuwar SA'ADHA/NANNE! 

*** 

Tsawon lokaci babu wani abu dake wanzuwa a falon sai fafutukar da Bwama da Imran keyi akan GAWAR dake gabansu! 

Saboda abinda ya rage kenan, abinda ya rage daga karyayyen jikin Nanne dake kwance so still a gabansu, siffarta dake b'ace baja-baja da jinin jikinta. 

Wa'adi ya cika, alk'alami ya riga ya bushe, Allah yayi hukuncinsa, Lalle ne kowacce rai lokacinta k'ayyadadde ne... Babu wani k'ok'arinsu kuma da zaiyi tasiri! 

Amma duk da haka Imran bai daina  k'okarin ganin ta farfad'o ba, bai daina kokarin gyara jikin da ya zama gawa ba. 

... ya sani. 

Amma, ta mutu... 

... bai yarda ba! 

K'arfe bakwai da 'yan mintuna na safiyar juma'a a cikin garin katsina, wayar Sulaiman ta shiga vibrating a kusa dashi, yaja tsaki a hankali cikin baccin nasa... don ya san kiran ba zai wuce na yazo ya kai 'yan makaranta ba in har an samu wani uzirin daga Idris direba. 

Allah ya sani dole ne ma ya k'ok'arta a had'a aurensa dana 'ya'yan hajiya Babba Nasir da Muhammad da za'ayi cikin shekarar nan, don kusan duk wani responsibilty na gidan yanzu akansa aka d'ora, tunda ya d'auki annual leave d'insa bai samu ko kad'an ya huta ba, sunansa ne ke fara zuwa kwakwalwar kowa a duk sanda wani abun ya taso. 

Yasa hannun ya jawo wayar zuwa kunnensa. 

"Hello." 

Daga d'aya bangaren muryar cikin wayar tace. 

"Sulaiman kana gida koh?" 

"Eh." ya amsa ransa a b'ace. 

"Sunana jaamil, ni dan'uwan Imran ne mijin k'anwarka Sa'adha." 

Jin haka yasa ya d'ago da kansa yana kallon silin kafin yace. 

"Okay na gane.." 

Muryar ta d'anyi shiru bata amsa ba, hakan yasa shi k'ara bud'e idanunsa sosai sannan yace. 

"Ina sauraronka." 

Kusan sakan talatin kafin muryar ta sake magana da wani irin tattausan amo da ya ratsa har cikin jijiyoyinsa. 

A cikin abinda baifi kiftawar ido ba Sulaiman yaji tunaninsa ya zille daga cikin kwakwalwarsa ya rataye a iska, Mutuwa? Nanne ta mutu? Wace irin Mutuwa? Nannen da jiya ya shiga wajen Inna yaji suna waya da ita? 

"Dan Allah malam ka gaya min gaskiya, wace Sa'adhan kake nufi?" 

"Babu wanda yake wasa da mutuwa sulaiman, ba zan taba kiranka in maka karya ba Sa'adha k'anwarka nake nufi, Allah ya amshi ranta jiya wajen haihuwa, muna... 

Bai ji k'arashen zancen ba saboda ya kasa gasgata kunnunwansa, ya kasa gasgata al'amarin, ya kasa gasgatawa wai da gaske Sa'adhan/ Nannen da yasani ce ake gaya masa ta rasu, rasuwa ta mutuwa irin wadda in ta kasance mutum ya tafi kenan har abada! 

Hannunsa dake rik'e da wayar ya shiga rawa lokacin da muryar wanda ya kira kansa da jaamil ke cigaba da bayani wajen gaya masa cewa ya taimaka yayi wa su Baffa bayani cikin nutsuwa kafin k'arasowarsu, Nutsuwa? wace irin nutsuwa ke tattare da labarin mutuwa? 

Sai ya ajiye wayar ya d'ora hannayensa aka kawai ya shiga rero Inalillahi wa Inna ilaihir raji'un! Inalillahi wa Inna ilaihir raji'un! Inalillahi wa Inna ilaihir raji'un! 

Yanzu wa zai tunkara da wannan labarin? Baffa zai samu yace masa 'yarsa ta rasu ko kuwa wajen inna zai je ya gaya mata Nannenta ta mutu? wannan wane irin sak'o ne ya rataya a wuyansa haka? yaji kwalla ta cika idanunsa lokacin da tunaninsa ya cakud'e ya rasa madafa, sai kawai ya janyo wata T-shirt dake gefensa ya d'ora akan wandon shaddar jikinsa sannan k'afafunsa suka nufi d'akin hajiya Babba, bai ko tunkari na mahaifiyarsa ba don ya yardarwa kansa cewa wannan aikin na manya ne, a yanzu Hajiya Babban ce kad'ai zata iya samun Baffa da wannan hargitsatstsen bayanin.! 

**** 

Kafin k'arfe takwas na safiyar ranar, labarin rasuwar Sa'adha yayi tambari a cikin unguwarsu, haka nan kuma ya cigaba da watsuwa kusufa-kusafa na garin Katsina, sannan gidan ya fara cika da 'yan uwa da kuma mak'ota na kusa wanda hakan ya dad'a sanya hargitsi a zukatan al'ummar gidan. 

Story continues below


Lokacin da motoci uku nasu Imran da kuma su ya Ahmad da suka je taro su suka k'araso cikin gidan, hawaye ko d'igo bai fito daga idanun Baffa sai sannan, sai a lokacin da ya d'aga ido yaga manyan 'ya'yansa na kiciniyar fito da gawar daga cikin mota, ya kalla yaga wai yau Nanne dake dake zagaye gidan da kafarta ce ake d'aukowa babu numfashi kuma babu wani abu dake motsi a jikinta, jikinta sanye da doguwar riga kamar zasu sauke ta ne ta taka da k'afarta duk da cewar an rufe fuskarta da hijabin kanta. Yaji wani sabon Imani ya shige shi sai ya shiga salati yana k'ok'arin maida kwallar dake shirin tunkud'uwa daga idonsa. 

Wai Sa'adha ta tafi a yau, Sa'adha mai tsananin biyayya a gare shi, ta tafi a k'ananan shekaru masu cike da k'uruciya, ta tafi bayan tayi masa biyayyar da yake ganin ya tauye wani b'angare na rayuwarta... 

"Allah ya jikanki Nanne, Allah ya yafe miki kurakuranki, Allah ya baki Aljannatul firdausi mad'aukakiya, Allah ya ingata shahadarki, Allah ya shafe zunubanki, Allah ya kyautata aiyukanki na alkhairi, Allah ya karbi ruhinki cikin daraja, Allah ya kyautata zuwanki, Manzon tsira ya karbi bakuncinki, Allah yasa mutuwar ta zamo hutu a gareki, na yafe miki duniya da lahira, Allah yayi miki rahma da gafararsa...." 

K'okari yake kar hawayensa ya fito a gaban 'ya'yansa, kar ya fiddo da raunin da zai haddasa karyewar zuciyarsu alhalin yana iya ganin tsananin dauriyar kowannesu a cikin idonsu. 

A lokacin kuma gidan ya k'ara rud'ewa, mata suka shiga kuka mai d'agawa kamar a da suna tunanin jiran da suke zai zo musu da wani abun ne sab'anin hakan. 

Aka shiga da gawar Nanne har cikin d'akinsu ita da inna, Innar da a lokacin bata cikin haiyacinta, tun bayan shaida mata labarin da akayi take ta hailala mai cike da maganganu, maganganun da suke nunawa tar! cewa bata cikin haiyacinta, don har fad'i take cewa Nanne bata mutu ba watakila tayi bacci ne kawai a mota kuma zata tashi da zarar sun kawo gida, sai dai duk da wannan sambatun harshenta na kiran Lailaha ilallahu muhammadur rasululahi duk sanda ta juya taga irin kukan da mutanen dake gewaye da ita keyi, tana yi tana fad'in. 

"Na gaya muku ku bar fidda hawayenku, ba dai ance suna hanya ba? da sun iso zaku ganta garau... Azumi ki gaya musu mana ba jiyan nan nake ce miki munyi waya da ita ba? har nake gaya miki tace zata sake kirana bamu gama magana ba tace tayi bak'i? Ke Halime dauki wayar mana ai zaku ga lambarta a ciki..." 

Lokacin da aka shigo da ita cikin d'akin, da saurinta ta kwace hannayenta dasu Mama Azumi ke rik'e dasu ta rarrafa ta bud'e fuskarta dake lullube da hijabin, kyakkyawar fuskar Nannenta da ke fes! cike da annuri da kuma alamun nutsuwa irin ta mai bacci, kamar za'a kira sunanta ta bud'e wad'annan fararen idanun nata ta amsa. 

A lokaci guda ta d'anyi sororo tana kallonta, kamar mai son lalubo wani abu nata daya fad'i akan fuskar, amma ba wani abun take son lalubowa ba face fahimta da tayi cewa  babu alamun rai a tattare da ita, babu rai a jikin Nannen da take mutuqar so a rayuwarta, Babu rai a jikin Nannen da taci burikka da yawa akanta, Babu rai a jikin Nannen da taci burin ganin 'ya'yanta na yawo a tsakar d'akinta, Babu Nannen da taci burin ganin ta samar mata rayuwa mai kyau da inganci, Babu Nannen da take tsananin so fiye da 'ya'yan da ta haifa a cikinta! Sai kawai ta hau girgiza kafad'unta tana fad'in. 

"Da gaske suke kenan? Da gaske ne abun da suke fad'a kin mutu? Ta yaya zaki mutu a yanzu? Don kawai jiya mun yi waya na gaya miki k'anwar iyan shehu ta rasu wajen haihuwa sai kema ki mutu? Ki dubi girman Allah kiyi hakuri ki tashi wallahi ba zan kara gaya miki zancen mutuwar kowa ba, wayar ma zan yar da ita, ke da kika ce min watan gobe zaki taho gida haihuwar? ina nan ina tanada miki kayan wanka, me yasa zaki haihu yanzu? me yasa zaki haihu ki mutu Nanne? me yasa zaki mutu da k'uruciyarki bayan nice tsohuwa? me yasa zaki tafi ki barni? me zanyi da rayuwar....." 

Bata kai k'arshe ba idanunta suka juya luu sai kuma ta tafi ta fad'a kan jikin nata... nan d'akin ya kara rud'ewa aka d'auke Inna zuwa cikin d'aki, yayin da Ya Ahmad ta koma motarsa da sauri don d'auko first aid box d'insa, Kafin ya kai ga dawowa Rahma wadda tana shigowa tayi ido hudu da gawar ta fad'i itama. 

Story continues below


Haka waje ya k'ara rudewa cike da alhini da kuma tashin hankali, Ya Ahmad ya dinga zarya tsakanin Inna da Rahma don ceto nasu ran, yayin da mutane suka cigaba da cika a gidan, musamnan maza kowa na son samun sallar jana'izar da ake shirin yi. 

Duk wannan abin da akeyi, wannan d'an kyakyawan Babyn na k'udundune cikin hannun Bwama dake zaune daga can wani b'angare na d'akin, rikicin ganin gawar Nanne ya hana mutane da yawa biyowa ta kansa, kuma 'yan k'alilan din dake zuwa ganinsa, ba wanda take mik'awa don ta kafa sharad'in cewa shima ba cikakkiyar lafiya ce dashi ba don haka ba'a d'aukarsa, sai dai duk da haka tsananin mamakin irin kyawunsa ya fara zagaye cikin al'ummar gidan. 

Wajen k'arfe goma na safiyar juma'a aka gama shirya gawar Nanne tsaf cikin farin kyallen dake jiran duk wani mai rai! Mama Halime, Aunty Maryama da wata malama zahra'u su suka wanke jikinta da babu ko kwarzane sai alamun warkewar ciwo a k'asan mara da gefen cikinta, suka tufke dogon gashinta cikin tufka biyu, wadda tasa fuskarta ta koma kamar ta k'aramar yarinya saboda kyau, Aunty Maryama ta fashe da kuka sanda suke nannad'eta cikin likkafanin, gani take kamar jiya ne suke shiryata cikin kwalliyar aure yayin da taron gidan ya kasance na farin ciki, gashi ko shekara bata zagayo ba suna yi mata shirin tafiya kabari, yayin da taron gidan ya kasance na makoki. 

A wannan lokacin Inna ta farka daga suman ta, kuma abin mamaki wannan karon bata rikice irin d'azu ba, rarrafowa ta sake yi cikin tsakar falonsu da aka sake dawo da gawar don yi mata addu'a kafin a fita da ita. 

Ta durkusa a gabanta daga gefen Baffa wanda ya bud'e tafukan hannayensa yana ta zubo addu'o'in neman yafiyar ubangiji da gafarsa akan ruhin d'iyar tasa, Idon Inna baya iya gane kowa ne a lokacin amma zagaye da ita ta kowanne gefe 'yan gidansu ne kaf! daga mazan har matan su ashirin da uku, jaamila dake can Niger ce kawai bata nan, sai ko mahaifiyarta Nuratu da a lokacin suke kan hanyar tahowarsu, Kowannensu na zubo kalar addu'oinsa, wasu kuma amsawa Baffa... daga bayansu ne 'yan uwa na kusa irinsu Aunty Maryaama ke tsugunne suma suna nasu addu'o'in. 

Zuciyarta na zafi jikinta na girgirza tasa hannu ta janye likkafanin da yayi mata katanga da fuskar Nanne, fuskarta dake cike da annuri kamar wadda ke cikin tsananin farin ciki, kamar wadda ba taba fuskantar wani b'acin rai ba a cikin 'yar gajeriyar rayuwarta. 

Yafiya har yafiya, albarka har albarka, neman gafarar ubangiji da neman Rahmar ubangiji ba wanda Nanne bata samu daga wajen Inna ba, tun tana fadar addu'oin cikin hankalinta, har komai ya kai k'arshe ya zamo maimaci kawai take yi. 

Allah ya sani, zuri'arsu irin mutanen nan ne da basa mutuwa da wuri, kafin kaji mutuwa a danginsu toh ka tabbata ta tsoho ce ko wanda ya bawa hamsin baya, Saboda haka mutuwar Nanne ba k'aramin girgiza su tayi ba, kamar wata katanga ce daga wani b'angare na gidan ta fad'i ta rugurguje har garinta! 

Nanne mutum ce mai d'imbin kirki da alkhairi, tana da mutuk'ar kyautayi da son 'yan uwanta, tana hak'uri da tsananin biyayya ga iyayenta, tana da kuma tsanani kulawa kan duk abinda take so a rayuwarta! tana iya sadaukar da komai nata don samun farin cikin wani... ita d'in mai nasibi ce da faffad'ar zuciya, ga duk wanda ya fahimci halinta, toh tabbas zai so ya zauna da ita tsawon rayuwarsa! 

Wanda ganin mahaifiyarsa cikin wannan halin ya sashi kasa daurewa kukan dake nuk'urkusar zuciyarsa, sai kawai ya saki labulen yayi hanyar waje ta cikin dimbin jama'ar da suka cika gidan a lokacin. 

K'arfe Goma sha d'aya daidai na ranar juma'a aka fitar da Nanne daga gidansu a matsayin gawa, gidan da ta taso tun yarintarta, gidan da mahaifiyarta ta tafi ta barta a cikin sa, gidan da Inna ta raine ta da dukkan kulawarta, gidan ta fara gina rayuwarta a cikinsa, gidan da ta fara haduwa da Imran a k'ofarsa, sannan gidan da aka d'aura mata aure a cikinsa! 

Da da gaske ne da ake cewa duniya ba matabbatace, Lalle ne komai mai k'arewa ne... can d'in shine gida na gaskiya! 

*** 

Don komai dake faruwa ganinsa kawai yake yi yana wucewa kamar a shirin wasan da aka zauna aka tsara shi, baya yarda da dukkan abinda idanunsa da kunnuwansa ke d'auko masa, har kuwa sanda ya kama gangar jikinta shida Baffa suka zura ta a cikin ramin kabarinta, da sanda ake jera tukwane a kanta, da sanda ake zuba k'asa akan tukwanen, har saida ta shafe hasken farin likkafanin dake lullub'e da ita, da sanda k'asar tayi tudu aka kafa allon alama akanta. 

Da sanda aka kusan shafe awa guda ana jero addu'o'i a gefen kabarin, da sanda jaamil ya sake jan hannunsa suka koma cikin motar da suka zo, da sanda kowanne motsin tayar motar ke k'ara nesanta shi da Ayuninsa, da sanda suka dawo cikin layin gidan nasu, da sanda suka fito daga mota saboda cunkuson mutane da ya fara yawa, da sanda suka iso daidai jikin wannan tsohuwar container data raba gate din gidajen biyu.... 

Sai kawai ya zame hannunsa daga na cikin jaamil ya tsugunna har k'asa a wajen, wajen da ya zama mafarin had'uwarsa da Sa'adha, ranar da ya fara ganinta sun dawo daga islamiyar nan, gashi wai a yau yaje ya raka ta cikin kabarinta ya dawo, ya dawo daidai wannan wajen dake cikin duniyar da babu Noorynsa! 

Sai ya kifa kansa cikin tafin hannunsa ya shiga rero kuka tamkar karamin yaro, jikinsa na girgizawa tare da zuciyarsa, jaamil na shirin sunkuyawa ya bashi baki, Baffa ya tsaida shi ta hanyar d'aga masa hannu, ya yarda cewa duk duniya ba wanda ke da hurumin hana Imran kukan da yake yi a lokacin... Matarsa ce ta mutu, irin matar da ba'a koyaushe Allah ke azurtar bawa da ita ba, don haka hakk'insa ne yayi makokinta! 

Zai iya yiwuwa mintoci, ko kuma awanni, irin wanda suke dunk'ulewa cikin jimla, jikin Imran bai bar girgizawa tare da kuka ba, Abu d'aya kawai da ya sani kuma yake ganewa a wannan lokacin shine zai kashe NAANI! 

Zai kashe ta dukan iyawarsa! 


Har zuwa ranar da aka shafe zaman makokin Nanne da kwanaki bakwai, Bwama na cikin gidan a matsayin mai kula da Babyn nan, domin har a lokacin hankula da yawa baya kansa, sai bayan sadakar uku ne ma su Aunty maryama suka fara karb'ansa don yi masa wanka da kuma bashi abinci, wanda ba komai bane face tatacciyar madarar shanun da ake kawowa daga gonakin Baffa, wanda shi da kansa ya bada umarnin hakan, a cewarsa mahaifiyarsa ma da abinda ta rayu kenan.

Sai dai abinda basu sani ba shine, a duk sanda aka kawo madarar, Bwama na fakar idonsu ta zuba garin wani abu mai suna 'jerul' a ciki, abu ne da suke amfani dashi ne wajen dakushewa irin halittunsu possibilities d'insu a duk sanda suka yi laifi don a samu a iya hukunta su, saboda haka a yanzu da bata san irin abinda Babyn zai iya ba wanda  ta san zai fi k'arfin hankalin bil'adama, yasa take amfani da jerul wajen dakushe koma wani irin abu ne ke tattare da jininsa. 

A ranar sadakar bakwai ne, Baffa ya kira taro a gidan gabad'aya wanda ya hada harda Nuratu da itama take kwana da tashi a gidan ita da 'yan uwanta, Nuratun da basa shiri da Inna a yanzu tana d'aya daga cikin mutane mafi soyuwa a wajenta, don duk sanda ta kalleta sai taga kamar taga wani b'ari ne na ragowar Nannenta da ya rage, saboda haka kullum tana gefenta suna karb'ar gaisuwa tare... gaisuwar tarin mutanen da cincirindonsu baya tab'a raguwa a gidan, don har daga can Niger ba'a daina zuwa ba. 

Hakika mutuwar Nanne ta girgiza duk wani mahaluki a gidan, ta guntule farin cikinsu, ta wargaza tunaninsu kuma ta k'ara sanya musu tsoron Allah a zukatansu. Don haka fuskar kowa na falon in ka kalla a wannan lokacin d'auke take da alhini irin na rashi. 

Bayan doguwar addu'a daga bakin Muhammad, Baffa ya fara bayanin cewa ya kira taron ne don ya gaya musu cewa anyi rad'in sunan Babyn da asubahin ranar kuma Imran ya rad'a masa sunan mahaifin Inna wato HISHAM. Anyi yanka kuma su mama Azumi har sun gama suyar naman. 

Yanzu abinda ya rage shine inda rik'on yaron zai kasance, za'a barshi anan wajensu ne, ko kuwa Inna tana ganin a bawa dangin Imran su rik'e shi. Daga yadda ya fad'a kowa ya san cewa ya fad'i hakan ne kawai don a kwatanta adalci a kowanne b'angare, amma ba ta yadda za'ayi Inna ta bari d'an nan ya matsa daga kusa da ita. 

Ai kuwa yana rufe baki, tayi tsalle ta dire cewar ba inda za'a tafi dashi, ai hakk'in dangin uwa ne kula d'a karami yaro irin haka, saboda haka yadda ta raini Nanne, a bar mata shi zata raine shi da dukkan iyawarta. Aunty maryaama kuma tace Inna ta tsufa, d'awainiyar yaro k'arami zata yi mata wahala a wannan shekarun saboda haka ita a bata shi, ta san mijinta zai amince, amma bata k'arasa ba Inna ta hau sababi wanda ya had'a da kuka tana fad'in bata yarda a matsa koina dashi daga cikin gidan ba, saboda haka Nuratu ma dake shirin magana tayi shiru da bakinta. 

Sai Aunty amarya tace ita zata karb'e shi amma Inna tayi saurin katse ta tun kafin ta k'arasa. 

"Kar ki kuskura ki k'arasa zancen nan, Hadiza, kar ki kuskura ki k'arasa, yau har kece mai bakin cewa a baki d'a? Duniya makaranta! Shekaru ashirin kenan baya muka yi irin wannan zaman a d'akin nan, ba irin yadda bawan Allahn nan bai rok'e ku ba akan ku taimaka ku rik'e masa marigayiya ke da Halime, amma kuka k'ek'ashe idanunku kuka ce baza ku raini 'yar kishiya ba, shine kike da bakin magana a yau? yo me kuma zaki yiwa d'anta a yanzu? me...." 

Bata k'arasa ba Baffa ya katse ta da girman Allah akan tayi shiru, abinda ya faru a baya ya riga ya wuce. Bayan ya gama 'yan koke-kokenta da rantsuwar baza a bawa Aunty Amarya ba, Baffa ya tambayi Imran game da ra'ayinsu, a karon farko cikin kwanaki bakwan nan ya bud'i baki yayi magana, don hatta jaamil ba yadda baya yi dashi ba wajen tambayarsa abubuwa amma baya tab'a cewa komai, ko wajen karbar gaisuwar baya zama, a kullum yana can cikin dakin Baffa inda yake kulle kansa yayi ta kukan da har hawaye sai sun daina bin kumatunsa, don Allah ya sani daya zauna a waje wani yace masa. 

Story continues below


Ya hakuri? 

Gwara ya shafe yinin ranar bai ga kowa ba, yana faman yi mata addu'ar da bata k'arewa! Tun lokacin da karfin rabin ruhinsa da ya bar na Sa'adha ya dawo jikinsa yake fatan k'arshen zaman makokin yazo don ya sami damar yin abinda Bwama da jaamil keta hana shi tsawon kwanaki. 

So yake yaje Muzaffar ya gayawa Naani cewa abinda dake fata ya dawo jikinsa, dama tace ruhinsa ba zai taba barin jikinta ba sai in har ta mutu, zai gaya mata tayi nasara ta kashe ta, b'arin ruhinsa ya dawo jikinta kuma zaiyi amfani dashi itama ya kashe ta! 

Amma Bwama da jaamil sunce alamar tambaya zata d'arsu akansa in har ya bar gidan zaman makokin ya tafi Muzzafar a wannan lokacin, sunce yayi hakuri ya daure wad'annan kwanakin don ya rufe asirin sanin WAYE SHI daga dangin Sa'adha, sunce bai kamata ya bada wata k'ofar da zata sa su fahimci wani abin ba kamar yadda ta rufa asirinsa da dukkan iyawarta, shi yasa jaamil ya sake dawo da wad'annan tarin mutanen a matsayin 'yan uwansa suka zo suka yi gaisuwa kamar yadda kowa yake zata. 

Yayi gyaran murya kad'an lokacin da hankalin kowa ya dawo kansa. 

"Baffa duk abinda Inna ta fada gaakiyane, a yanzu wajenta ne mafi cancanta da yaron ya zauna, sai dai kuma abinda Aunty maryama ta fada itama gaskiyane, bai kamata a d'ora mata d'awainiyar jariri a shekarunta ba, tunda kuma bata yarda da kowa ya rik'e shi ba ina rok'on alfarmar ta bar 'yar uwata (yana nufin Bwama) a wajenta ta taya ta rainonsa." 

"Wallahi na amince, ko su nawa suzo, idan har zaku bar min shi a gabana." Inna ta amsa kai tsaye. 

Cikin wannan tattausar muryar tasa mai zurfi, Imran ya cigaba da magana. 

"Sai dai ina rok'on ya dawo wajena daga lokacin da shekarunsa suka kai na shiga makaranta, na riga nayi mata alk'awarin zan kula dashi." 

Ba sai ya fasa ba, kowa ya san yana nufin Nanne ne, yayi wa Nanne alkawarin cewa zai kula da Babynta/Hisham tsawon rayuwarsa! 

"Wannan ba wani abu bane Imran, kai ubansa ne kana da hakkin karb'arsa a duk sanda kaga dama, saboda haka ko bayan raina kowa ya shaida nayi alkawarin zamu baka shi daga lokacin da ya shekara uku." 

Da wannan alkawarin taron ya tashi, Inna bata ja da hakan ba saboda itama ta san yana da hakki akan d'ansa kuma ko ba komai an had'a da cewar alk'awarin da aka yiwa Nannenta ne. 

Da hakan kuma Imran da jaamil suka had'a bangarorin dutsen Nil suka dank'a a hannun Bwama a matsayin abinda zai cigaba da  bata karfin da zata iya maintaning jikin bil'adama a cikin shekaru ukun da zata yi na kula da Hisham, da hakan kuma aka yi sadakar bakwai aka share zaman makokin Sa'adha, gidan ya sake shiga sabon yanayi na alhini, kewa da kuma k'unci. 

Ance sabo akewa kuka ba mutuwa ba, duk da auren da tayi, d'aukacin al'ummar gidan kaf! sun saba da Nanne, don ita d'in mai tsokana ce da  karamniya, ko mutum bai shiga shirginta ba, dole zata nemi abinda zai had'oka da ita, wanda daga baya za'a zo ana dariyarsa, hatta su Lami da ba shiri suke ba sun sha kuka da idanunsu akan rashinta, saboda haka dole alhini ya shafi wani b'angare na walwalar gidan. 

Da hakan kuma Imran ya shirya tsaf! ya d'auki hanyarsa ta zuwa Muzzaffar!! 

**** 

BAYAN SHEKARA GOMA. 

Yamma ce, amma gari yayi duhu sosai alamun bak'in had'arin dake manne a sama na iya narkewa ya sauko a kowanne lokaci. 

Imran ya bud'e k'ofar cikin d'aki da saurinsa ya fito... Nanne ta biyo bayansa da gudu ta cikin corridon da ya kawo su main falon gidan, tana sanye da wata 'yar k'aramar vest kalar ja da  kuma da d'an blue short da bai ka gwiwa ba, hannuta rik'e da wani k'aramin towel yayin da Imran ke sanye da dogon wando da singlet kawai, lallausar sumar kansa na d'iga da ruwa. 

Story continues below


"Ayunie dan Allah mana sau d'aya." 

Ta fad'a tana turo d'an bakinta alamu shagwab'a. D'aya daga cikin manyan abinda Imran baya so shine a goge masa gashi in ya wanke shi, ita kuma tunda ta fahimci hakan shikenan ta samu hanyar tsokanarsa. 

"Dan girman Allah kiyi hak'uri, wallahi ba dad'i ne." 

"Dan girman Allah nima ka barni inyi sau d'aya.." 

Ta fada tana k'okarin zagayowa ta bayan kujerar da yake tsaye, aikuwa yana fahimtar haka ya fara matsawa shima. 

"Toh kije ki d'auko hand dryer, amma ba da wannan ba." 

"Saboda me?" Ta d'age girarta d'aya. 

"Towel d'in nan yana da laushi, zaka ji kamar massage nake maka." 

"A'a Noory, ki hak'uri dan Allah." 

Ta matse kafad'arta d'aya. 

"Allah ba zan hak'ura ba." 

Da haka ta fyalla da gudu ta nufe shi, suka shiga zagaye kujerun falon da gudu tana ta kyalkyala dariya, shi kuma yana ta rokonta don har ga Allah baya so, a haka yayi tuntub'e da wayar extension ya fad'i k'asa, ai kuwa ta d'ane kansa ta shiga murza towel din a cikin gashinsa, da kyar ya iya cafke hannayenta ya wullar da towel d'in. 

"Ba kya jin magana you sweet little dickkins!" 

Ya fad'a yana ware tufkar gashinta itama, ta dinga dariya sanda yake hargitsa shi da hannayensa har saida ta fad'a kan jikinsa tana fadin. 

I'm sorry! 

Muryar ta mai sanyi ta ratsa dukkan jijiyoyin jikinsa, it was so real da yaji ko kad'an baya son ya bud'e idonsa ya koma wannan zahirin da babu muryar. 

"Noory... 

Ya kira sunanta a hankali, ta d'ago ta k'ifta chocolate idanunta masu d'auke da kwalla a hankali, so slow ta yadda yana ganin yadda dogwayen lashes d'inta suka had'e dana k'asa kafin ta sake bud'e su, gashinta a hargitse kan kafadunta wani ma ya zubo kan fuskarta... the way he always wanted it! the he always missed it! 

"I've missed you, I'm always missing you..." 

Muryarsa ta rad'a mata a hankali sannan ya k'ara da. 

"... like crazy!" 

Sai tayi wani guntun murmushi da ya k'ara fito da yawan kwallar idonta, sannan a hankali ta ware hannunsa d'aya dake rik'e da ita, ta d'ago shi sama sannan ta lankwasa yatsunta a tsakanin nasa, ta juya kanta da wani irin slow motion ta kalli hannayen nasu sanda shima ya lankwasar da nasa yatsun a cikin nata, amma bai bar kallon fuskarta ba. 

"I miss you too Ayunie!" 

Lallausar muryarta ta fito kamar rad'a, Imran ya kalli yadda kwallar ke gangarowa gefen fuskarta a hankali tana shigewa cikin sassalkan gashin kanta, yaji zai iya nutsewa cikinsu ya manta da duk wata damuwarsa. 

Ring. Ring. Ring. Ring. Ring..! 

K'arar wayar dake ajiye a gefensa ta farkar dashi zuwa zahirin da yake gujewa. Ya kalli inda yake, kan sallayar nan ne dai a gefen gado inda yayi nafila bayan tafiyar Hisham makaranta. 

Ya dafe kansa cike da takaici sanda idanunsa suka koma suka lumshe, zuciyarsa ta dagule ta hasala kamar yadda hakan ke faruwa duk ranar da yayi mafarki da Sa'adha ya farka. 

Wayar data katse a gefensa ta sake d'auka da wani ringtone d'in, ya zamo da hannunsa ya shafa kwantaccen sajensa sannan ya mik'a hannu ya d'auke ta. 

Story continues below


"Hello mr. Siddiq?" Muryar baturiyar daga d'aya gefen wayar ta ambata. 

"Yes." ya amsa cikin husky voice d'insa. 

"There's an emergency about your son, we need to see you at the school now." ( Muna nemanka da gaggawa akan wata matsala data shafi d'anka.) 

"Okay." 

Hankalinsa a kwance ya amsa sannan ya kashe wayar, saboda hakan ba wai bak'on abu bane a wajensa, in dai matsala ce akan Hisham ya san yanzu suka fara, don makarantar da ya cire shi bayan dawowarsu daga madina, daga shi har malamar tasu sun riga sun saba da irin wannan wayar, tana d'auka zata ce. 

'The usual.' 

Shi kuma ya shirya ya tafi yaje Office d'in guidance and counselling yayi shiru yana jin dukkan k'orafinsu in sun gama ya basu hak'uri sannan ya d'auko shi su taho, a hanya shima ya bud'ewa Hisham nasa babin fad'an daga k'arshe kuma ya koma biya nasihar da dukkanninsu sun haddaceta. 

Wannan shine kusan rabin yadda suke tafiyar da rayuwarsu a wani d'an karamin gari mai suna "Bottesford" dake k'ark'ashin birnin Nottingham a k'asar England. A zamansu na madina ne suka fuskanci k'alubale kala-kala saboda su da gaske hukunta Hisham suke yi duk ranar da yayi wani abu da ba daidai ba wanda hakan ya dad'a janyo baiyanar abubuwa mamakinsa saboda duk lokacin da ransa ya b'aci ko yayi fushi ne baya iya controlling kansa. 

Dalilin da yasa har suka tafi dashi babbar headquarter d'in da ake hukunta masu laifi don yin bincike akan genesis d'insa saboda bayan sun d'ebe extraodinary possibilities d'insa, abubuwan da yake yi gabad'aya sun wuce irin abinda yara masu shekarunsa su kanyi. 

Wannan dalilin yasa ba shiri Imran ya tattaro suka dawo England da niyyar zaiyi dedicating rayuwarsa wajen canja k'asashe da kuma garuruwa har zuwa lokacin da Hisham zaiyi hankalin da zai dinga b'oye possibilities d'insa, yayi wa kansa wannan alkawarin kamar yadda yayi wa Sa'adha alqawarin zai kula dashi har tsawon rayuwarsa. 

Ya tuno rayuwar da yayi tsawon shekaru uku a hannun Bwama tana kula dashi kafin ya dawo hannunsa, rayuwar da yayi a cikin garin katsina kuma a cikin gidansu Sa'adha, rayuwar data sanya tsananin shak'uwa tsakaninsa da al'ummar gidan ya zama kamar ya maye musu gurbin mahaifiyarsa ne, rayuwar da Bwama bata tab'a barinsa ya baiyana wani abu daban nasa ba har ya gama zamansa tare dasu, bata taba bari ya bada wata kafar da zata kaisu ga sanin ainihin WAYE SHI ba. Abinda har yau har gobe ya kasa sanin da irin abinda zai gode mata, in banda tarin addu'ar da yake binta dashi a kullum. 

A hankali ya mik'e ya ninke sallayar sannan ya shiga toilet yayi wanka sosai, bayan ya fito ya shirya cikin wata jacket mai kama da jallabiya data wuce gwiwarsa da kuma wandon jeans, ya taje gashinsa sannan ya d'auki key d'in motarsa ya fita, har ya kai waje ya tuna da wani abu, ya dawo ya shiga kitchen, ya d'auko robar lemo mai sanyi guda biyu sannan yayi locking gidan. 

**** 

"Mr. Siddiq I just don't know how to explain but look at this and tell me how in the world can a 10- year old do this?" 

(Ban san ta yaya zanyi maka bayanin abinda ya faru ba, amma ina so kalla sosai ka gaya min ta yadda yaro d'an shekara goma zai iya hakan.) 

Mrs Judy, Malaysian-British Principal d'in makarantarsu Hisham ta fad'a tana kallon Imran dake zaune akan kujerar tsallaken teburinta. 

Imran ya cije gefen lebb'ensa na k'asa yana kallon zungureriyar jelar kitson dake ajiye a gabansa, a gefensa na hagu, Wani ba'indiye ne rik'e da hannun 'yarsa wadda tasha plaster a gefen gashinta kusa da irin kitson da yake kallo a gabansa. 

Daga d'aya gefensa kuma Malamin ajin su Hisham d'in ne da wasu Malamai biyu zaune suna jiran amsar sa.... 

Sannan hisham d'in kansa a tsaye daga gefe, wani kyayawan yaro mai kama da siffar mahaifinsa sak! in ka d'auke farin fatarsa da kuma da wad'annan manyan chocolate eyes d'in irin na Nanne sak! ya cije gefen lebb'nsa na k'asa shima kamar yadda mahaifinsa yayi sannan yana tsaye da wata irin tak'ama da kuma isa irin wadda ta wuce na yaro mai shekarunsa, yana sanye da wandon jeans da kema jar T- shirt, sai top mai had'e da hood wadda ya jawo hular ya rufe tarin gashin kansa da yake kar na jinsin jar fata, wanda duk da haka ya fito ta gaba perfectly styled dashi, girman jiki irin na yanayin abincinsu da weather ta can yasa zaka ce ya kai shekaru sha biyar. 

Story continues below


Tun shigowarsa cikin office d'in, manyan idanunsa na kallon k'asa kawai ya zura hannayensa cikin aljihun wandon, ya had'e girar sama da ta k'asa yadda wani zai rantse ba akansa ake magana ba, yana jira ne a gama ya fad'i abinda ya kawo shi daban. 

Cikin lallausan turancin nan nasa Imran ya bud'e baki yace. 

"Ni kaina ban san me zan ce muku ba principal, ba san ta yaya yaro irin hisham zai iya aikata hakan ba, saboda haka sai dai mu danganta al'amarin da tsautsayi kawai, ina mai basu hakuri da kuma fatan zasu yafe masa sannan a gaya min tarar nawa hakan ya kama, zan biya yanzun nan." 

Duk yadda principal din nan da mahaifin yarinyar suka kai ga jin haushin Hisham ba yadda suka iya haka suka hakura, aka fad'awa Imran tarar cire gashin ya fito da card d'insa nan take ya biya yana k'ara basu hak'uri, da haka ya bar office d'in Hisham na bin bayansa ba tare da ya ko kalli inda Malamansa suke binsu da kallo ba. 

"How many times do we have to talk about this Rhea, I told you he's a single father." 

(Sau nawa zamu yi maganar nan ne wai Rhea, na gaya miki bashi da aure.) 

"I know, I knew! but I just can't control myself everytime he came into the view, and he's an african you said? oh my God! I swear Africa never look this beautiful and handsome an dashing and..." 

(Na sani, Na sani! amma bana iya rik'e kaina ne duk sanda na ganshi, kince daga Africa yake koh? na rantse Africa bata taba min kyau irin haka ba, da shek'i da kyau da...) 

"Hello Rhea, he's not Africa, he's from  Africa! and you better be careful.. he's Emily's crush as well!" 

(Kinga Rhea, bafa shine African ba, k'asar ce, kuma ya kamata kiyi hankali.. don Emily ma tana son shi!) 

Imran ya tura main k'ofar fita daga makarantar ya fita, ya riga ya saba da jin irin wannan hirar daga wajen mata a kusan duk inda ya taka ya shiga cikin k'asar turawa, k'asa irin wadda kunya tayi k'aranci a cikinta, ire-iren abubuwan dake sawa yaji kewar arewacin Nigeria ta kama shi, wajen da yake cike fal! da tari al'adun Hausa-fulani masu tsananin kyau da burgewa, abin alfaharin duk wanda ya kasance a cikinsu. 

Amma ba yadda zai yi ne, ya riga ya yiwa Sa'adha alk'awarin kula da Hisham tsawon rayuwarsa, kuma alk'awarin ya had'a har da bashi kulawa ta gari da kuma d'ora shi akan hanyar da zata fi karkarta ga rayuwar bil'adama, shi yasa yake bin makarantun turawa dana larabawa, wad'anda suka fi Nigeria wajen bada ingantaccen ilimi boko da kuma na addini, don duk wani abu da zai bawa Hisham a duniyar nan, sai ya tabbata mafi kyau ne! 

Ya sawa hadaddiyar motarsa k'irar 'Venza' key suka juya suka fita daga harabar makarantar suka cilla kan titi, hasken ranar da yayi tar! a lokacin ya haska kyawawan fuskokinsu su duka biyun, wadda banbancinsu ya kasance abu biyu, na farko fuskar Imran cike take da kwantaccen saje da gashin baki wanda a yanzu suka k'ara yawa fiye da lokutan baya, yayin da na Hisham sid'ik take, in banda lallausan gashi kad'an da ya fito har wajen hab'a, alamun nan gaba shima sajen ba zai masa wahala ba. 

Sai kuma banbancin yarinta da ta alamun matashi d'an shekara talatin da takwas. Imran ya janyo wani bak'in space ya saka saboda hasken ranar da ya masa yawa, sai ya k'ara wani kyau kamar yana shirin gabatarwa da kamfanin space d'in talla ne, ya d'ago robar lemon nan guda biyu da har yanzu ke d'igar sanyi ya mik'awa Hisham d'aya. 

"Ina jinka." Ya fad'a ba tare da ya d'auke idonsa daga titi ba. 

"Daddy cewa tayi tana sona." 

Sai da Imran ya kware a lemon da yake sha kafin ya rage gudun motar ya juyo ya kalle shi. 

"What?" 

Hisham ya d'aga kafad'unsa shima ba tare da ya kalle shi ba. 

"Ai ba ita kad'ai ce bama, ita nata abin ne yafi bani haushi tayi ta zuwa wajena, wallahi da an barni sai na cire gabad'aya gashin kanta." 

Story continues below


Imran ya buga kansa da jikin kujerar sannan ya tura hannunsa cikin gashin kansa. 

"Hisham for goodness sake! shekarar ka fa goma, kana grade 4... me mamanka zata ce in taji haka?" 

Ya riga ya saba masa, suna maganar Nanne ne a kullum kamar zasu koma gida su same ta, don ya yarda in ba da hisham ba babu wanda zai iya hirarsa da ita, kuma shima ya kamata ya san wani abu na mahaifiyarsa. 

Hishaam ya kurb'i lemonsa kafin yace. 

"Cewa zata yi duk wanda ya sake cewa yana son Babyna, kabi su duk mammare su sai sun koma ja kamar tomato." 

Imran ya d'anyi murmushi kafin shima yace. 

"Sannan kuma tace dukkansu ka had'a musu da Allah ya isa!" 

Hakan yasa suka kyalkyale da dariya gabad'ayansu kafin kuma dariyar ta mutu a hankali, yadda suka saba duk lokacin da suka tuna cewa babu ita d'in. Kusan a tare suka cusa hannunsu d'aya cikin gashinsu sannan hisham yace. 

"Yaushe zamu je Nigeria?" 

"Yaushe zaku yi hutun Summer?" 

"In the next three weeks." 

"Then ka had'a kayanka!" 

Suna isa gida Hisham wayarsa ya fara lalubowa ya kira number Sadiq, bugu d'aya biyu ya d'auka. 

"Man, ya akayi ne?" 

Cewar Sadiq daga d'aya b'angaren, wanda shigarsa d'akin Inna kenan bayan ya dawo daga wajen aikinsa, tunda a lokacin har ya gama masters dinsa a b'angaren economics. A yanzu sune samarin gidan Baffa shi da 'yan biyu, duk sauran yayyen nasu sunyi aure da 'ya'yayensu. Aunty Amarya ta sami abinda take so, 'yayanta ke juya kusan komai na harkar gidan tunda tsufa ma ya kama Baffa baya iya abubuwa da yawa. 

Cikin irin hirar da suka saba Hisham yake gaya masa zai zo Nigeria nan da sati uku, daga k'arshe kuma ya bawa Inna dake ta mik'o hannu jin ance Hishaam ne ke wayar. 

"Hey, Baby girl! ya k'afar taki?" 

Imran na tsaye daga jikin dining hannunsa d'aya a aljihu d'aya kuma rik'e da mug din coffee yake kallon Hisham, yana iya jin magiyar Inna ta cikin wayar wadda a kullum bata gajiya da ita kan suzo taga Babanta, koda kuwa a yau suka je suka dawo in an sake waya sai tace su taimaka su dawo, a yanzu tsufa ya kamata kwarai! don ko tafiya bata iya yi sai an kamata. 

Hisham nata dariya cikin wayar kamar bashi ba yana tsokanarta, Imran yaji wani sanyi a kasan zuciyarsa daga yadda yake kallonsa daga nan. Kaf! duniya yanzu baya tunanin akwai abinda yake k'auna sama da d'an nasa, dama Sa'adha ta riga ta fada. 

"Ina ji a jikina ulfat Babyn nan alkhairi ne a garemu, ba zai tab'a zama irin tunanin da kake ba...ina son shi sosai Allah, kuma kaima na gaya maka zaka zo ka so shi fiye da tunaninka insha Allah." 

"That's true Noory!" ya fad'a a hankali yana kub'ar coffee d'insa. 

"So true!" Muryar jaamil ta amsa a gefensa. 

Yayi saurin juyawa ya kalle shi sannan yaja tsaki. 

"Jaamil don muna k'asar turawa fa haka baya nufin an daina sallama kenan." 

"Ko kuma ya kamata mutum ya daina tafiya  zurfin tunani yana amsa sallama in anyi ba." 

Ya fad'a yana karbar mug d'in hannun nasa. 

"Me ya kawo ka ma ne wai? it's less than a week fa da kazo? An gaya maka haka ake shugabantar al'umma?" 

Jaamil ya d'age kafad'unsa yana zama akan dining d'in. 

"Ya zanyi, kewarku nake kullum kamar me... can din ba wani abu mai gamsarwa daga hukunci sai zartarwa! inaga ya kamata in canja tsarin abubuwa da yawa wallahi." 

Story continues below


"Ko kuma ya kamata ka sami wadda zata canja ka ba, nasha gaya maka it's high time wata ta shigo cikin rayuwarka, ya kamata kayi aure." 

Imran ya fad'a yana zama shima akan kujerar dake fuskantarsa. 

Shekaru goma kenan baya, da jaamil ya kasance shugaban nahiyar Muzzaffar! sakamakon kashe Sareefa da Imran yayi, don a lokacin da ya isa Muzaffar bai tarad da Naani a raye ba, Sareefa ta kashe ta bayan dukkan abinda ta tanada saboda ita, bayan dukkan d'awainiyar data yi mata, ta kashe mahaifiyarta sakamakon tsananin k'ullatar ta da tayi da kuma son mulkinta, wanda a lokacin kuma take fafutuk'ar ganin yadda zata ga bayansa shi da jaamil. 

Saboda haka a lokacin da ta ganshi, bata b'oye masa komai ba na yadda ta kashe mahaifiyarta saboda ta fahimci bata da niyyar d'aukar fansa akansa, sannan ta shiga ganin bayan matarsa kafin ta k'araso gare shi. Ta gaya masa dukkan abinda yaji daga cikin habler nan Naani ta fad'a mata ne saboda ta kwantar da hankalinta ba wai don haka komai yake a zahiri ba, Tace da gaske ne tun farko Naani ta d'auko shi ne saboda wannan aikin da take so yayi mata, amma daga baya zuciyarta taso shi tsakani da Allah, So irin wanda ita da take d'iyarta bata  taba mata. 

Saboda har a lokacin da ya hana ta dutsen Nil, zuciyarta ko kad'an bata da nufin cutar dashi, tace mata ne kawai zata kyale shi don ta san bayan wani lokaci zai dawo gareta shi d'in mai tsananin biyayya ne, Saboda haka a tunaninta na son farantawa Sareefa itama, sai ta bata kusan dukkan karfin jikinta, sannan tayi murabus ta nad'a ta matsayinta, wanda da wannan damar Sareefan tayi amfani ta kashe ta bayan kwanaki biyu. 

Sannan ta shiga kokarin ganin bayan matarsa, don tayi rantsuwar sai ta guntule farin cikinsa tukunna kamar yadda suka hana ta itama kafin shima ta kashe shi, sannan tazo kan jaamil da mahaifiyarsa Bwama. Sai dai a lokacin bata da ikon kusantarsu saboda karfin dutsen Nil dake cikin gidan da suke, saboda haka daga nesa ta karanci halayen Sa'adha tsaf! da kuma mutanen da take mu'amala dasu. 

Ta haka ta gano cewar hankalinta yafi karkata ga Safiyya maman yarinyar nan Hidaya, ta gaya masa cewa matar bata tab'a zama muguwa ba kamar yadda yayi tunani a baya, kawai bai yarda da ita bane saboda jikinsa ya bashi alamar da bai iya ganewa ba a lokacin, alamar cewa rayuwarsa zata hargitse ne ta dalilinta, saboda da ita tayi amfani, ta shiga jikinta taje har kofar falonta, ta bugawa Sa'adha 'Kambun Turaz' a cikinta, wani abu da suke hukunci dashi wajen karya gab'ob'in irin halittarsu. 

Sai a lokacin Imran ya fahimci Sa'adha ba karamin k'ok'ari tayi ba na iya tsaida bugun zuciyarta har sanda Hisham ya fito duniya, don in har za'a bugawa irin halittarsu wannan kambun gab'obinsa su karye inaga an bugawa halittar bil'adama wadda take mai rauni? 

Mummunar kisa irin wadda in ido ya gani zai rikice, kwakwalwa ta hargitse hankali ya tashi, ita yayi wa Sareefa a lokacin da take ganin tayi k'arfin da ba zai iya galaba akanta ba, ya kashe ta amma bai cigaba da farfasa halittar jikinta ba har saida jaamil ya janye shi da k'arfin tsiya. 

Bayan nan kuma bai k'ara zama cikin hankalinsa ba tsawon watanni, jaamil shi yayi fafutukar kula dashi a duk lokacin nan, alhali ya karbi sarautar nahiyar Muzzafar! domin shai kad'ai ne jinin sarautar da ya rage a cikin zuri'ar Naani. 

Damuwa da depression kala-kala ba irin wanda bai shiga ya tafi ta gaba ba, saboda ba don d'aya b'arin ruhinsa dake jikinsa ba ya tabbata da tuni zuciyarsa ta dad'e da bugawa ya mutu! don sai a shekarar da rik'on Hisham zai dawo wajensa ne sannan ya samu ya fara dawowa haiyacinsa... amma Allah ya sani, ya azabtu fiye da tunanin mai tunani! 

"Kar ka damu, zanyi aure kwanan nan yarima." 

Imran ya zare idanunsa a lokaci d'aya, sannan ya matso da jikinsa ta kan table d'in. 

"Kace min mafarki nake yi jaamil, kaine yau kake fadar kalmar aure da bakinka? ya salam! you seriously need to tell me this, wacece haka?" 

Kafin jaamil yayi magana Hishaam ya taho da wani irin sauri da yafi k'arfin ganin idanun d'an Adam ya d'ane kan jaamil yana ihun murna. 

"Hishaam sau nawa zan gaya maka ka daina irin wannan saurin?" 

Imran ya fad'a da k'arfi amma Hishaam bai ko saurare shi ba, ya dinga kyalkyala dariya yana jijjiga jaamil har sai da ya suka sauka daga kan kujerar suka shiga birgima a k'asa. 

Sai yayi murmushi kawai sannan ya janyo wayarsa ya kunna ta. 

Hoton Sa'adha tar! ya baiyana akan screen d'in, ta lumshe idanunta tana murmushi, shima ya lumshe nasa idon a hankali yayi murmushi. 

"I love you so much Nanne!" 

Sunan da baya tab'a jin ya kirata dashi a tsawon rayuwarta! 

"Allah yayi miki gafara!" 

KARSHE. 

*** 

Alhamdlilah!  Alhamdlilah!! Alhamdlilah!! 

A yau mun kawo k'arshen labarin WANENE SHI? munji komai kuma ina k'ara baku hak'uri da ta'aziyya akan rashin Nanne da muka yi. 

Ba yadda muka iya ne, k'addarar labarin tafi soyayyar da muke yi mata! 

Nagoode! Nagoode!! Nagoode!! 

Post a Comment for "WANENE SHI CHAPTER 15 THEND KARSHE"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...