[Advertisements⬇️]

WANENE SHI CHAPTER 11 - Bankinhausanovels
Thu. Jun 8th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

WANENE SHI

CHAPTER 11
Da sauri ya taka steps d’in ya shiga ciki, sai da yazo dab! da ita sannan ya tsaya.

“Sa’adha me ya faru? me ya same ki? wani yazo ne?”

Yayi tambayar duk a lokaci d’aya sanda hannunsa ya lalubo nata, jikinta ya d’anyi b’ari amma nan da nan ya saki sanda ya shiga murza babban yatsansa a bayan hannunta.

Cikin sheshshek’ar kukan ta girgiza kai.

“Ba wanda yazo, na tashi ba kowa a gidan sai ni kad’ai, kuma nayi ta jin tafiya kamar za’a shigo amma ba kowa, sannan….”

“Shshhh…” yasa d’aya hannunsa yana goge mata hawayen a hankali.

Zuciyarsa ta matse da tausayinta, ya tuna cewa ba taba zama a gida ita kad’ai ba, ta tashi a gida mai mutane da yawa ne dole yanzu taji bata saba ba.

“I’m sorry habibty…kina ta baccinki mai dad’i sanda na fita shi yasa ban tashe ki ba, kiyi hak’uri dan Allah.”

A lokacin wani gefen tunaninsa ya ayyana masa cewa shine Babban abin tsoron da ya kamata ta guda ma a yanzu. yasa hannunsa a bayanta yana zagaya shi a hankali sannan yana k’ara rada mata tayi hakuri har sai da ya tabbatar zuciyarta ta nutsu sannan ya d’an sunkuya da fuskarsa side d’in kunnenta yace.

“Ban tab’a dawowa gida wani ya bud’e min k’ofa ba Noory, this is my first time…Nagode!”

Tayi murmushi a hankali cike da kunya sannan ba tare da ta d’ago ba muryarta tace.

“Ina kaje?”

Yaji murmushin shima na shirin kub’uce masa, irin wannan courage d’in nata na burge shi, bata cika k’umbiya-k’umbiya ba.

“Baki ga note d’in dana ajiye miki ba.”

Ta girgiza kai.

Ya rufe k’ofar da k’afarsa sannan ya
d’ago mata ledojin hannunsa.

“Naje samo miki abinda zaki ci ne.”

Idanunta suka kara girma da tambayar abinci ya siyo.

“Come on, na san jiya da za’a kawo ki anyi ta fad’a miki cewa ki kula dani koh?”

Bata amsa ba ya cigaba.

“Nima haka kowa yayi ta fad’a min, to ta yaya zan fara barin ki da yunwa da sassafen nan?”

Ta d’ago ta kalle shi da jik’akk’un idanunta da kuma d’an mitsitsin murmushi a lebbenta. Kwayar idanunta farare tas suka d’auki hankalinsa, yaji kamar zai fad’a cikinsu ne ya nutse. Subhanallah! ya fad’a a ransa.

She’s so beautilful…very stunning and deadly gorgeous!

Ba tare da wani dogon tunani ba ya ajiye ledojin sannan ya kai hannunsa ya shiga tab’a doguwar jelar kitsonta da suka fito ta gefe, a lokaci d’aya kuma yana k’ara sunkuyo da fuskarsa saitin tata, ya lura ta ki’fta idonta a hankali tana kallonsa, sai da ya matso da kansa dab! da ita sannan ta rufe idanunta gabad’aya.

A hankali lebb’ensa ya sauka akan cheeks d’inta, wani waje just a mere inch from the side of her lips. Sannan a hankali yaji wani abu da bai tab’a experiecing ba a rayuwarsa, wani abu daban, wani abu sabo da babu shi a register kwakwalwarsa.

Cikin kiftawar ido jijiyoyin jikinsa suka daina aiki sannan jikinsa ya k’ame kamar dutse, yaji zuciyarsa na bugawa da k’arfi kamar zata tsaga kirjinsa ta fito, ya kasa koda kwakwaran motsi, Hannunta d’aya dake rike da nasa shine kad’ai wani abu dake rike da jikinsa, jikinsa da ya tsaya a k’ame kawai, frozen! kamar mai jirin wani abu, wani abu da zai dawo dashi duniyar zahiri.

Ring Ring Ring Ring Ring.

Wayarsa dake gaban aljihu ta zama wani abun daya janyo shi zuwa senses d’insa.
D

********

BAYAN KWANA UKU. 

Imran bai tab’a tunanin cewa akwai wani farin ciki a duniya da ya kai wanda yake ji a yanzu ba, ya yarda cewa duk wani farin cikin duniya ya taru ne a gefe guda sannan farin cikin aure ma ya tattara a gefe guda. 

Ya k’ifta dogwayen gashin idonsa a hankali yana kallon fuskar Sa’adha dake kwance a gefensa tayi pillow da kafad’unsa tana baccinta hankali a kwance, tunda yake bai tab’a ganin wanda ke bacci so innocent kamar ita ba. 

Ya tuno yadda ta dinga dariya jiya da daddare lokacin da tasa rigarsa, tana cewa tayi kama da irin masu film d’in abinda dariyar nan, amma shi a idanunsa ba haka ya gani ba. she look so flushing and radiant! 

A cikin kwana uku kawai yayi mugun sabawa da ita kamar yadda ya san itama ta saba dashi, don ko bata fada ba kyallin farin cikin idanunta da kuma yawan murmushinta zai shaida masa hakan, sannan ko daga yanayin maganganunta ta sake dashi saboda tana iya masa doguwar hira har ta bashi labari, wani lokacin ma tana indicating da hannunta cikin tsiwarta. Matarsa mai tsiwa ce, ya riga ya sani, Shine farkon abinda yaja hanakalinsa game da ita. 

Bayan hakan ya kula ta fara sabawa da yadda koyaushe hannusa ke cikin nata, good morning kisses d’in da kullum yake raining a fuskarta da kuma sauran abubuwan da kullum yake iya k’ok’arinsa wajen daure zuciyarsa akanta, don ko sau d’aya a rayuwarsa bai taba experiencing irin feelings d’in dake nukurkusar zuciyarsa game da ita ba, wasu irin feelings ne kamar electricity suke yawo a kowacce jijiya ta jikinsa duk sanda yake tare da ita. 

Kuma a yanzu tare suke yin komai na gidan, tare suka gyara setting d’in d’aya falonsu da tace baiyi mata ba sannan tare suka gyara kitchen d’in gidan, suka mayar da dukkanin kayan da aka jera cikin kwalinsu suka bar iya na amfani kawai, ya fahimci bata fiye son tarkace da kaya da yawa ba, she prefferd everything plain and simple! kamar yadda nature dinta take itama. 

Tare suka zauna suka yi lists d’in dukkanin abinda suke buk’ata na gidan sannan suka fita suka ciko boot da bayan motarsa dasu, a kwana uku kawai rayuwarsa ta canja, yaji kamar duk zaman da yayi a da cikin wani kango yake sai yanzu ya shigo gida. 

Murmushi ya sub’uce a kumatunsa amma bai motsa ba, ya kwanta very still yana kallonta, Sai wajen karfe biyu suka yi bacci jiya, ba zai so ya tashe ta tun yanzu ba, don ko da asuba, sai da ya d’auketa ya kaita har cikin toilet d’in sannan ta bud’e idanunta. 

Kullum baya iya barinta tayi bacci da wuri, in suna tare lokaci tsaya masa yake yi yaga kamar ba wani sauran abu mai motsi a duniya sai su biyu, sai yaga idonta ya fara rufewa sannan yake fara rage tambayoyin da a kullum yake cika ta dasu, ya dinga jefo su d’aya bayan d’aya a hankali yana tracing k’unshin hannunta, k’unshin da a yanzu in za’a sake irinsa ya san ko mai k’unshin da tayi baza ta kaishi yin mai kyansa ba. 

Ta gefen idonsa ya kalli agogon dake mak’ale a d’akin, lokaci ya nuna masa karfe sha biyu saura na rana, a yau ya kamata ya koma office don kwata-kwata bai d’auki hutu ba, sai iya 2-days leave d’in kawai da ya zama dole na ma’aikata, amma baya jin daga yau har zuwa satin ya k’are zai koma office, he wanted to spend his time with her, akwai abubuwa da yawa game da ita da bai gama sani ba. he wanted to know every single detail of her life. 

Tun daga kan abubuwa masu muhimmanci har zuwa silly-silly abubuwan da bata d’auke su a komai ba. 

Ya riga ya tanadi tarin tambayoyin da yake son yi mata dama, amma a kullum ya tashi ya kalli fuskarta, sai jerin tambayoyin list d’insa su k’aru. ya rayuwarta take kafin ya had’u da ita? Wadanne irin mutane take mu’amala dasu? Me take so me nene bata so?  

His list grew. Koyaushe cikin tambayarta yake yi, in suna wani aikin, in suna cin abinci, in suna girkin da a yanzu tare suke yi ko kuma mafi yawan lokutan da zai jawota jikinsa yana absorbing duk wasu information d’inta. Amsoshin da take bashi, tun daga kan yanayin fuskarta da body language d’in da yake fahimta su suka bud’e kwakwalwarsa ya fahimci halayenta da yawa bayan iya wanda ya sani. 

Sa’adha wasn’t just good, she was perfect! kamar wani box guda ne da aka had’a complete set na duk abinda d’an adam zai buk’ata a rayuwarsa. Kuma tun a yanzu tsoro ya fara kama shi, tsoron ranar da lokacin tambayarta zata zo, ranar da zata fahimci shi d’in ba komai bane mai daraja, don ya san k’aryar da duk zai had’a ba zata tab’a tashin wani abu mai daraja irinta ba. 

“Wane irin chewing gum kika fi ci?” 

Ya tuno tambayoyin daya mata na k’arshe jiya kafin tayi bacci. 

A lokacin tana kwance a jikinsa yana janye wani strand d’in gashinta da ya shiga bakinta. Ta d’ago da idonta ta kalle shi, yaji d’umin jikinta yana fitowa directly akan fuskarsa, k’amshin turarenta ya cigaba da nannad’e kowanne senses na hancinsa, ya k’ifta idanunsa a hankali sanda tunaninsa ke sulalewa kan plumpy lips d’inta da yake facing. 

“Kowanne…banda d’an goma dana biyar.” 

Yayi murmushi a k’asan numfashinsa kafin yace. 

“Na Ashirin fa?” 

“In ka bani zanci.” 

“Wane colour kika fi so?” 

“Suna da yawa.” 

“Fad’a min first daya fara zuwa ranki.” 

“lemon green.” 

Ya sake yin wani murmushin, ba tun a lokacin ba ya fahimci Sa’adha tana da ra’ayin kanta, bata tab’a yin wani abu don wai hakan ya zama zab’in mutane da yawa. 

Hannunsa ya koma gefen fuskarta ba tare da amincewar zuciyarsa ba, ya sake janyo wasu tarin gashin nata, idonsa akan lips d’inta yana jin kamar ya d’ago da fuskarta sannan ya sunkuyo da tasa, zai iya had’uwa da bakinta halfway… 

Enough! 

Yayi saurin dakatar da kansa, in har hakan ta kasance, zai iya losing controll d’insa yaji mata ciwo. 

“Meye last music d’in da kika ji?” 

Her lips twisted, alamun tunani daga can tace. 

“Last wak’ar da akasa ranar bikin mu.” 

Ya dage girarsa d’aya. 

“Seriously? wacce kenan?” 

“I beleive in you.” 

Yayi murmushi a hankali. 

“I beleive in you too Noory!” 

“Kai wanne ne last da kaji?” 

“Mhm-mhm…” 

Yayi saurin dakatar da ita. 

“Har yanzu time d’ina bai kare ba, sai gobe turn d’inki zai fara.” 

“Zuwa yaushe toh?” 

“Wannan ma tambaya ce, ki bari sai goben yayi tukunna sai ki tambaye ni.” 

Tayi murmushi mai fad’i tana lumshe idonta a kansa…Her smile was infectious to him!

Hannun Nanne ya mik’a zuwa d’aya b’angaren gadon, babu kowa kamar yadda tunaninta ya bata, ta bud’e idonta a hankali, babu Imran a kwance a wajen sai alamun imprint d’in kansa a jikin pillown daya kwanta. 

Tayi murmushi a hankali sanda ta tuno event d’insu jiya da daddare, a yanzu ta k’ara yarda cewa Imran yana sonta har cikin zuciyarsa kuma ba abinda zai canja hakan. Tana ganin soyayyarta fal a cikin idanunsa duk sanda ya kalleta, sannan ko kad’an baya jin nauyin fad’a mata how much he loves her tun tana kirgawa a rana har sai tazo ta b’ace k’irgar. 

Rayuwarta ta canja a iya kwanaki uku kawai da aurenta, Imran ya kaita  wata duniyar daban mai cike da d’imbin kulawarsa da tarairaya. Ta riga ta saba dashi sosai a yanzu, ta saba da hirarsa sannan ta saba da jikinsa, yadda yake yawan tab’ata da yadda hannunsa kullum yake cikin nata. 

Sannan baya taba barinta tayi abu ita kad’ai, komai tare suke yi cikin hirarsa, hirarsa ta tambayoyi kala-kala da suka had’a da dukkan wani insignificant detail of her existence, films d’in da take so da wanda bata so, wajajen da taje a rayuwarta, wajajen da take son zuwa, sannan tambayoyi game da ita…endless tambayoyin da suka shafe ta. 

Ba zata iya tuna lokaci na k’arshe da tayi magana mai yawan wadda tayi a kwanakin nan ba, don ta tabbata in za’a tattaro jarabawoyin data amsa a rayuwarta kaf! a had’a dana Imran a yanzu nasa zasu fi yawa. Sau da yawa jikinta yana ta bata cewa zata dame shi da yawan maganarta, amma absolute yanayin fuskarsa da kuma yadda baya tab’a tsayawa da tambayoyin, suke bata kwarin gwiwar cigaba da magana. 

Yawanci tambayoyin nasa masu sauki ne, ‘yan kad’an-kad’an ne suke sata tunani ko kuma murmushi kafin ta amsa, kuma duk sanda tayi murmushin  sai an sake new sets na wasu tambayoyin. 

Da daddare suka zauna a falo da Tv a kunne, suna zaune a k’asan carpet da tulin eatries d’in daya siyo amma hankalinsu baya kan tvn, tambayoyi yake ta mata akan gidansu, da duka ‘yan gidan, yana son ya san me da me tayi missing da kuma bayanin yadda komai yake dalla-dalla. 

Tayi masa bayanin yadda fasalin gidansu yake tun asali kafin azo a canja abubuwa daga baya, yadda wajen baffa yake, yadda kitchen d’insu yake da tarin ‘yan aikinsu da kowanne sai da tayi masa bayanin nasabarsa da gidan tun asali, sannan ta dawo kan jerin d’akunan yayyenta har zuwa kan bene, hawa na farko, na biyu da kuma barandar can sama, ta dinga kwatanta masa yadda wajen yake da yamma, cike da iska mai dad’i da kuma yadda mutum ke iya ganin yadda rana ke faduwar a yamma. 

Ta dinga bayanin tana kwatance da hannunta, yadda yayi shiru yana saurarenta ta cikin dim hasken tvn, yasa ta zama freely tayi ta magana. Daga k’arshe ta k’are da bayanin yadda setting d’in dakinsu yake, d’akin kwanansu ita da Inna. 

Murmushi tayi a hankali data tuno cewa yau kuma ranar tace, daga yau nata tambayoyin zasu fara, jerin gwanon tambayoyin da tara akansa fal! gasu nan kwando-kwando zube a kowanne lungu da saqo na zuciyarta. 

Tun daga lokacin data daina ganinsa a k’ofar gidansu d’in nan har zuwa yanzu, ta k’ara ta jera su perfectly akan wanda ta tsara kwanakin baya, wancan lokacin daya maido ta gida da daddare yace mata zaizo washegari, wancan lokacin da ya zama mafarin rayuwar da take ciki yanzu. 

Excitement raced through her at all the thoughts she would unlock today. 

Ta mike ta nufi toilet, idonta na kaiwa kan reflection d’inta a mudubi mamaki ya kamata, wani k’aton tabo ne jazur dashi ya fito a gefen kumatunta, tasa hannunta da sauri ta tab’a wajen, babu tudunsa akan fatarta sai jan kawai, kamar irin bruise d’in dake fitowa in mutum ya buge ko jini ya taru a wajen. 

Ta wanke fuskarta da sauri sannan tayi brush, anan taga wani mark d’in a gefen wuyanta da k’asan kunnenta, ta tuno yadda Imran yayi kissing d’inta a wajen jiya. 

Matsalar jikinta kenan, very sensitive yake akan komai, a gida ko kurjewa tayi sai wajen gabad’aya yayi jawur. Tayi tunanin concealer zata shafa duk su b’ace amma kuma duk a cikin kayan kwalliyarta yanzu bata da ita, sannan na cikin lefe ta gansu duk masu duhu ne, in ta shafa zaiyi daban da farar fatarta. 

Ta koma cikin d’aki ta tsaya a gaban full body mirrow d’in dake gefe, tana binciko su d’aya bayan d’aya, akwai da yawa a wuyanta da k’asan hab’arta, ta zame hannun doguwar sleeping dress d’inta nan ma akwai su da yawa, abin ya fara bata mamaki yadda suke da yawa haka, kamar wani abu na ciwo. 

A lokacin taji k’arar bud’ewar kofar d’akin. 

Tana juyawa idanunta suka ci karo da Imran rik’e da breakfast tray a hannunsa, singlet ce kawai a jikinsa sai wando three-quarter, lallausan gashin kansa a barbaje har yana saukowa goshinsa sannan fuskarsa d’auke da wannan murmushin dake dulmiyar da tunaninta, taji kamar ta d’auke shi ta kaishi can k’asan zuciyarta ko zata samu sauk’in abinda take ji duk sanda ta ganshi a ranta. 

“Good morning Habeebty!” 

Ya fad’a yana lumshe dogwayen lashes d’insa akanta. Hancinta ya jiyo mata daddad’an had’in wani abu kamar scrambled egg da fries, sannan ga sandwiches tana gani a bowl da kuma had’add’en Oats a mug guda biyu. 

Ta maida hannun rigarta a hankali sannan ta k’arasa gabansa. Sai dai kafin tace wani abu idonsa ya hango masa tarin bruises d’in dake jikinta, idanunsa suka zare da tsantsar mamaki ya lalubi kan dressing mirror ya ajiye tray d’in sannan ya matso ya shigo jikinta. 

“Me ya same ki? Meye wannan?” 

A hankali tace. 

“Nima ban sani ba, yanzu na tashi na gani.” 

Daga yanayinsa ta lura ya tsorata sosai, sai faman dubawa yake yana shafa wajen, saboda haka yace. 

“Ba ciwo bane bafa, may be wani abin ne ya same ni, I easily get bruises like this…amma ina shafa concealer zai tafi.” 

Sai a sannan taga reaction d’insa ya d’an kwanta. Ya lalubi kunnenta a hankali ya rad’a mata. 

“I’m sorry!” 

Maimakon ta amsa sai tace. 

“Zamu je mu siyo anjima?” 

Taji sautin murmushinsa kafin amsar ta biyo baya. 

“Zamu je mu siyo kwalayensu da yawa Sa’adha, don zasu mana amfani sosai.” 

Nanne ta taho da sauri daga cikin d’aki don bud’e kofar main  falonta da ake ta knocking, Wani dad’i ya kamata sanin cewa bak’i tayi, bakinta na farko a gidanta da tayi sati d’aya a ciki.

Don ta san cewa ba Imran bane tunda basu fi minti talatin da gama waya ba, kuma ya gaya mata sai yamma zai dawo, yauce ranar farko daya koma aiki, ranar farko data fara rabuwa dashi ta fara zama a gidan ita kadai. 

Dazu da tana gyara d’aki ta d’auki filonsa ta shinshina k’amshinsa dake jiki, awa uku kad’ai amma tayi missing d’insa kamar kwana uku, tayi missing muryarsa mai taushi da babu ita a gidan, tayi missing yawan bibiyarta da yake yi a komai, tayi missing tambayoyinsa da har yanzu basu k’are ba, God…! tayi missing hannunsa ma da kullum ke cikin nasa. 

Kwanakin shidan da tayi tare dashi  gani take kamar shekara shida ne saboda yadda ta saba dashi sosai, He’s the best husband anyone could ever wish for! Dukkan irin rayuwar da tayi mafarkinta a baya tare dashi ta same ta har ma fiye da hakan, Imran was caring, loving and showers her with so much affection. 

A iya tambayoyin data ware a yanzu wanda taga su ya kamata ta fara sani game dashi, ta fahimci mutum ne mai saukin kai sosai, baya tab’a d’aukan abu da zafi a rayuwarsa kuma ra’ayinsu da yawa yazo d’aya wajen so da k’in abubuwa. 

Sannan bai cika complain ba, rana farko da suka fara yin girki a gidan kusan k’onewa yayi amma haka ya zauna ya cinye baice komai ba, sannan komai tace masa za’ayi ko tana so zai biye mata suyi da dukkan iyawarsa sau da yawa tana jin kamar tana ordering yaro k’arami ne, (D’aya daga cikin abubuwan da take so a rayuwarta.) 

Sannan in har abu nada matsala zaiyi mata bayani in a simple way da zata gane ba tare da taji haushi ba. 

Tun a cikin weekend d’in nan yake bata hak’urin komawarsa wajen aiki wanda a lokacin ita bata ga komai, ba sai a yanzu da ta jita a gidan tsit tukunna! Ta tuna yadda yayi ta kissing cheeks d’inta da safen nan yana gaya mata zaiyi mata misssing d’inta da yawa. 

Taji tarin abubuwa sun tsaya mata cak a lokacin, ta rasa wanne zata fara tunkara, ta riga ta saba komai tare dashi take yi, komai k’ank’atar abu kuwa, da kyar ta tsaida ranta ta fara share gidan tas! sannan tayi mopping, kafin ta gama taji bayanta na shirin k’agewa kamar ta share wani waje mai tarin datti. 

Ta gyara kitchen ma sannan taje tayi wanka, tana komawa kitchen d’in ta sake tunowa dashi, kullum sai su shafe lokaci mai yawa ana debating me za’a dafa, in ta tambaye shi me zai ci, shima sai ya tambayeta me zata ci yana yi yana wasa da gashinta da a yanzu ta manta yaushe rabon data d’aura d’ankwali, don ko tasa ba zaifi minti biyu ba zai cire shi. 

Da kyar ta tsaida ranta akan me zata dafa, ta duba fridge taga lemukan da suka hada jiya wajen kala uku suna nan, ta ciro wanda aka had’a da gwanda, ayaba, madara da kuma sugar ta dawo dashi k’asa don ya rage sanyi. 

Sai da girkin ya kusa gamawa sannan ta koma d’aki d’auko kud’in da zata bawa malam Aminu ya siyo mata Slippers d’in da zata saka a toilet d’in cikin d’aki, a sannan ne taji bugun k’ofar falon. 

Tana bud’ewa idanunta suka ci karon da tarin mutanen da bata san tayi missing d’insu kamar hauka ba irin yanzu. Ta daka wani irin tsalle tare da ihu. 

“Na shiga uku, Nanne yaushe zaki yi hankali ne wai?” 

Aunty maryama ta fad’a sanda ta d’ane kanta, ta sake ta ta koma kan Aunty Nafisa sannan Aunty zainab, ga Rahma, ga wata ‘yar uwarsu Sadiya… idonta ya ware da taga harda Amina, Ta sake daka wani tsallen kafin itama ta rungumeta. 

“Anya Nanne k’alau kike kuwa? sai kace kin shekara baki ganmu ba, kwana shida ne fa kawai.” 

Ta juyo da bakinta a washe tana kallon aunty maryaman da suka yiwa kansu masauki a cikin falon. Tayi missing fad’anta ma kamar me. 

Story continues below


“Haba Aunty toh yaushe na tab’a zuwa wani waje na kwana shida, sannan bani da ko waya fa balle in kira gida.” 

“To sai kiyi kuka yanzu…” 

Aunty zainab ta kwaikwayi muryarta, dukkansu suka fashe da dariya. 

Basu ko gaisa ba ta fara tambayar. 

“Inna inna? tace a gaishe ta? yaushe zata zo? muryarta ta washe yanzu? jikinta bai mata ciwon gajiya ba? ya k’afar tata? ta koma asibiti bayan bikin…” 

“Mu nan duk ba mutane bane ai da bama zaki bari mu gaisa ba.” 

Sai kuma ‘yar kunya ta kamata, ta fara gaishe su d’aya bayan d’aya, Aminah tace. 

“Rufa min asiri ke yanzu ai Aunty ce, matar Aure guda.” 

Ta juya idonta tayi magana yadda Aminan ce kadai zata ji. 

“Kamar kuwa kin san dama in nayi waya da Aunty Sa’adah zance kiyi saving numberta.” 

“Ai in baki fad’i haka ba, ba zan tabbatar ke d’in bace. 

Rahma dake gefe hankalinta na kansu  ta kyalkyale da dariya. Ta tashi taje kitchen ta kashe girkinta sannan ta d’auko musu lemon data fito dashi da ruwa sannan ta had’o da ragowar cupcakes d’in daya siyo. 

“Mu fa yanzu zamu wuce, kasuwa zamu kar rana tayi mana.” 

Ta kalli Aunty Nafisan sanda ta mik’a hannu ta k’arbi ‘yarta Shukra. 

“Kasuwar ina?” 

“Ta can k’ofar gabas, gobe duk zamu koma gida.” 

“Wayyo, zaku bar inna ita kad’ai.” 

“Ke ba tafiya kika yi kika barta ba.” 

Kafin ta amsa Aunty maryama tace. 

“Ke ni kamar ba haka kujerun d’akin nan suke da farko ba koh?” 

“Eh, mun canja tsarinsu ne, wancan style din yasa sun had’e a waje d’aya.” 

“Ke da wa?” 

“Nida shi, shi ya taya ni.” 

Amina ta kalleta baki a sake sannan tace. 

“Gaskiya Aunty nima aure zaku min, yarinyar da muka bari tana kuka kamar ranta zai fita ita ke wannan bayanin…” 

Nanne ta d’aka mata duka a bayanta. Suka yita hirarsu ana dariya, kasancewar su Aunty Nafisa basu fiye d’aukan kansu da girman kai ba ganin su Nannen ba sa’anninsu bane. 

Sai da zasu tafi Aunty Maryama ta jata d’aki tana tambayarta game da zancen ‘yan uwan mijinta da basu ga ko d’aya ba ranar kawota. 

“Wallahi Aunty nima banga ko d’aya daga cikinsu ba har yanzu, ya dai ce min ne dukkansu sun koma saboda wai basu da wajen zama anan garin sai kuma ranar da muka gaisa a waya da matar k’anin baban nasa daya bani labarin ta taimake shi sosai a rayuwarsa, amma bayan ita ni ba wanda na sani.” 

“Toh dole ne kuwa ki dinga tambayarsa game dasu, tunda a yanzu dole danginsa kema sun zama naki, kuma shi mutumin kirki ne Nanne kinyi sa’ar miji dole ki san yadda zaki dinga kula dashi, ince dai kin rike duk abinda na gaya miki ranar nan koh?” 

Ta had’iye wani abu a makogwaronta, don ko kalma d’aya baza ta iya tunawa a tarin zancen da akayi ta d’ura mata ranar ba, don a lokacin abinda ke gabanta daban ne, amma sai ta d’aga kanta da sauri tace. 

“Na rik’e komai Aunty.” 

“Toh madallah, ga numbobin wayoyin mu nan duk jna rubuta a wannan paper, harda tasu inna da sauran ‘yan gidan naku, duk randa kika samu waya ki kira kowa ku gaisa kafin ki samu zuwa.” 

Kanta tsaye tace.

“Ai watakila ma a cikin satin nan zani gidan, tunda tun ranar da aka kawo ni yace zamu je.”

Aunty maryama ta d’auko salati tun daga farko har k’arshe ta dire.

“Ai na san zaki aika uwar san yawo…wato har kin fara tambayarsa zuwa gida ko sati baki gama rufawa ba, toh kar ki fasa…yi ta tambayarsa ya kaiki gidan, in kinje bayan fad’an Baffa na inna ma kad’ai ya ishe ki.”

Ta had’e rai a lokaci d’aya.

“Toh dan Allah meye dan naje gida yanzu, gidanmu ne fa ba wani waje ba, daga tafiyata da kwana shida har sai a fara korata?”

Bata kai amsa mata ba Aunty Nafisa ta shigo d’akin.

“Daga kitchen d’inki nake Nanne, komai tsaf-tsaf an zama matar gida, amma tun yaushe kika fara girki?”

“Tun washegari muka je muka siyo komai.”

“Danginsa basu kawo muku komai ba?”

Ta girgiza kanta.

“Da safen ma sai da ya siyo abinci.”

Aunty maryama ta karb’i zancen.

“Yanzu nake gaya mata ai, dole ne a hankali ta dinga tambayarsa game dasu gar ta gano wani abin in akwai.”

“Gaskiya dai, idan matsala ce yake dasu dole ne ki gano ta ki kuma san yadda zaki gyara tsakaninsu, in ba haka ba ke kanki bak’in jini zaki yi a wajensu da kuma ‘yayan da zaku haifa, saboda haka dole ne ki gyara bakin zaren tun yanzu.”

Nanne tayi shiru kawai tana jinsu, a tunaninta dangin Imran ba matsalarta bace, dasu da babu su duk uwarsu d’aya ubansu daya a wajenta, indai har tana tare dashi kuma yana cigaba da nuna mata kulawar da a yanzu suka fara.

Zancen Aunty Nafisa na farko ya d’auki hankalinta, da tace ‘ya’yan da zasu haifa, Ya Allah! Zuciyarta ta narke da tunanin ‘yan little babies d’in da zasu zama combination d’inta ita da Imran. Zasu yi kyau sosai ta san, musamman ace su d’auko kammanin Imran sosai…..

“Kina jin mu wai kuwa?”

Muryar Aunty maryama ta katse tunaninta. Da sauri ta kalleta tace.

“Aunty Naji komai, kuma insha Allahu zanyi yadda kuka ce.”

Da haka suka yi ta cika ta da wasu shawarwarin suka tafi bayan Aunty maryamah ta mata dogon kashedin daura d’ankwali. Aka bar Rahma da Amina kad’ai.

“Wai ta yaya kika biyo su, ko har yanzu kina gida.”

“Haba dai na koma tun washe-gari,  Rahma ce ta kirani jiya tace zata biyo su Aunty Nafisa yau ko zanzo, shine naje muka taho tare.”

“Kin kyauta wallahi, baku san yadda nayi missing d’inku ba kamar me?”

“Ni ban gani ha, kinga wani irin fresh da kika yi?”

“Dan Allah? ni kuwa ban gani ba.”

Ta kalli Rahma da tayi kwanciyarta akan kujera tana facing Tvn dake nuna tashar Bollywood tace.

“Wai kin koma islamiyya?”

“Eh ranar laraba kawai naje.”

“Yawwa ai dai kinje, ko bakya so kuwa sai kin bani labarin irin gulmata da aka kafa a makarantar nan, don na san tabbas za’ayi.”

Rahma tayi murmushi tace.

“Kema kin san wannan dole ne, don yanzu maimakon mijinki ke kika koma General topic d’in islamiyyar.”

“Dan Allah, me da me suke cewa?”

“Ina zuwa dai su maryam suka hau ni da zancen wai dama ni da ke mun san shi zaki aura muke jinsu suna ta b’ab’atu akansa.

Su kuma su Aysha suka dame ni da tambayar wai in gaya mata ta yaya kuka had’u, a ina ya ganki yace yana sonki, da wasu tarin tambayoyi dai.”

“Ni ba wannan na tambaye ki ba, negative d’in zancen nake son inji.”

Rahma tayi shiru tana murmushi, Nanne ta tashi daga gefen Amina ta koma wajenta.

“Ai na rantse ko ba kya so sai kin fad’a min.”

Ta cafki hannayenta ta murd’e su ta baya, ta kwallara k’ara had’e da dariya tana fad’in ta sake ta.

“In kina so in sake ki fara bayani.”

Rahma ta dinga k’ara tana neman taimakon Amina wadda ke ta kyalkyala dariya tana kallonsu. Sai da taga da gaske Nanne baza ta sake ta ba sannan ta lallab’a tace zata gaya mata.

“Ina jinki toh.”

“‘Yan ajin malam isma’il ne suke yad’a zancen wai k’ila wani abu kika yi masa ya aure ki tunda har kika shigo islamiyyar baki sanshi ba, kuma kowa ya san ba wadda yake kulawa a unguwar tun zuwansa.”

Nanne tayi kwafa tace.

“Toh me kika ce musu?”

“Me kuwa zan ce musu? masu fad’a fa da yawa ba wai mutum d’aya bane kuma nima tsintar zancen nayi.”

“To ba kince daga ajin malam isma’il aka fara ba, nan zaki je kici mutuncinsu gabad’aya.”

“Kema kin san ba zan iya ba, da dai kina nan ne.”

“Yanzu ma ai bai wuce duk ranar da zanje gida sai na tabbatar ranar makaranta ne, inje inci uw*rsu wallahi, yadda suka fara zancen nan haka zasu san yadda zasu tsaida shi.”

Ta sake yin kwafa.

“Wato ma wani abu nayi masa, toh zanje in gaya musu asiri nayi ba wani abun ba kuma gwara ni nawa yaci akan nasu.”

“A’uzubillahi…” cewar Amina.

“Wannan wace irin magana ce?”

“Ke baki san yaran nan bane Aisha, tun da haushinsu nake ji wallahi.” Rahma tace.

“Wato Nanne yara, duk fa sun girme mu.”

“Ke kuwa yanzu tayi aure ai muma duk kallon yara take mana.”

Nanne ta kalleta da gefen ido tace.

“Ga ku nan ‘yan matasa dai haka.”

Amina ta jefo mata d’aya daga cikin throw pillows d’in gefenta, suka yi dariya gabad’ayansu.

Bayan sunyi sallah, Nanne ta zubo musu abincin da ta dafa sannan ta mik’awa malam Aminu ma nashi, suka ci suka k’oshi sannan aka sake dasa wata hirar, Nanne tayi ta dariya tana jin dad’i, ji take a yanzu kamar duk sanda Imran ya fita suzo suyi ta hira.

“Tunda kazo garin nan baka da abokai ne? Su waye freinds d’inka ? ban tab’a ji ka fad’i sunan kowa ba, ko baka dasu?” 

Muryar Nanne ta wancan lokacin ta dawo cikin tunanin Imran, yana zaune a cikin office d’insa a lokacin amma ya kasa k’arasa ayyukan dake gabansa, tunanin tambayoyin da tayi masa kwanaki uku keta yawo akansa. 

Kafin lokacin yasha tunanin yadda zai amsa mata su a cikin kansa, ta yaya amsarsa ya kamata ta kasance? da k’arya mai ma’ana ko kuma da k’aryar da baza tayi kama da gaskiya ba? 

Sai gashi tambayoyin sun fito a yadda bai zaci zasu kasance ba, don duk cikinsu ba wanda ke da alak’a da nasabarsa, nasabar da zata kaita ga sanin WAYE SHI..? sun ta’allak’a ne kawai akan sanin intrest d’insa akan abubuwa da kuma Habit d’insa, kuma masu sauk’i ne, they gave away nothing! sannan shima duk amsoshin daya bata masu tsafta ne, suna dacewa da labarin k’aryar daya d’orata akai tun farko, k’aryar da ya fad’awa Iyayenta suka amince da bashi aurenta. 

Bai bada ko k’aramin hint d’in da zaisa ta fahimci wani abin daban game dashi ba, sai dai ma shi daya gane inda tunaninta ke tafiya akansa, and it was nowhere close to suspense! 

Shi yasa a kullum ya d’aga ido ya kalleta, ya kalli irin tarin yardar dake cikin idanunta, sai yaji rauni ya kama shi, yaji kamar ya zaunar da ita ya gaya mata gaskiyar dake b’oye a zuciyarsa, ya amsa tambayoyinta da dukkan gaskiyarsa, ba wai don abin ya daina damunsa ba ko don ya samu yardarta, A’ah sai don kawai yana son ta sanshi, ta san shi d’in na gaskiya. his real personality! kuma yana fatan in ta san hakan, wad’annan chocolate eyes d’in nata su cigaba da kallonsa da trust d’in da take bashi a yanzu. 

Sai dai wani abu ne daya kwana ya tashi da sanin cewa duk yadda ta kai ga sonsa, kwakwalwarta ba zata tab’a iya karb’ar irin sirrikansa ba. Wani abu ne beyond expectation d’in tunanin d’an adam! 

Don shi d’in wata halitta ce daban, d’aya daga cikin d’imbin halittun ubangiji da babu saninsu a wajen mutane, shi yasa ranar da yaga wadannan marks d’in a jikinta, ya la’anci kansa fiye da sau d’ari akan kasa fighting emotion d’insa da yayi har ya bari yayi kissing d’inta so deep haka, ya k’ara tabbatarwa kansa cewa da gaske confidence d’in da yake dashi a da ya juye zuwa luck yanzu, baya tab’a iya controlling zuciyarsa indai akan Sa’adha ne, abinda ya jawo masa komai tun farko. 

Shi yasa tun daga ranar yasa a ransa cewa zai dage da dukkan iya k’ok’arinsa kar ya sake maimata irin mistake d’in ya nemi wata hanyar da zata d’auke hankalinsa daga kan jikinta ba tare da ita d’in ta fahimci komai ba, saboda haka a duk sanda yake tare da ita, sai yayi k’ok’arin maida full attention d’insa kan gashinta…sassalkan gashinta mai santsi da tsawo dake sashi manta duk wani shirmen cikin kansa. And it worked! 

Ya tuno ‘yan kad’an d’in tambayoyinta da sauka sashi tunani kafin ya iya bata amsarsu… 

“Sanda ban sanka ba, sanda kawai nake ganinka a layinmu, daga baya nazo na daina ganinka, wani wajen ka tafi a lokacin?” 

Babu inda naje. ya fad’a a cikin zuciyarsa don ya tuna lokacin sarai! wannan lokacin ne da ya takura kansa ya daina bibiyarta kusan watanni biyu, lokacin daya lura idanunta na iya ganinsa duk da cewa yana zuwa ne a yanayin da mutane basa iya ganinsa…wani abu da har yau bai san dalilinsa ba. 

“Na manta lokacin Sa’adha, amma ina tunanin ko na tafi gida ne lokacin hutuna.” 

Kamar sauran amsoshin da yake bata, ta yarda dashi ba tare da tayi tunanin komai ba. 

Story continues below


“Toh wajen wa kake zuwa? har sadiq na tambaya a lokacin yace min bai sanka ba.” 

“Da gaske? tun a lokacin kin damu dani haka? har kina tambaya a kaina?” 

Kumatunta suka yi flushing zuwa red, abinda ke faruwa duk sanda ya fahimci tana jin kunya. 

“Kawai na tambayeshi ne…” 

“Don’t budge please…zuciyata har ta fara tsallen murna, kar kisa ta tsaya dan Allah.” 

Tayi k’ok’arin fighting murmushin bakinta, his words pleased her! a hankali tace. 

“Ina jinka toh, wajen wa kake zuwa?” 

“Watakila Sadiq bai gane kwatancen da kika yi masa ba, amma wajen mutanen da kike gani na nake zuwa, akwai wani d’an office d’inmu da muke zuwa tare.” 

Karya ne, amma sai ta gyad’a kanta alamun ta fahimta. 

“Ka tuna ranar da ka shigo gidanmu da daddare?” 

“Na tuna Noory, bana tab’a manta duk wata rana da idona ya ganki.” 

“Me yasa a sanda muka had’u baka min magana ba, sannan da gaske dama kana zuwa wajen ya umar? saboda ni ban taba ganinka ba.” 

“That’s more than one…” 

Ya fad’a a k’asan numfashinsa, amma yayi deciding ya bata amsa kai tsaye, don tambayar bata da matsala, dole ne ta san akwai dalili, kuma shima yana da dalilai da yawa da zasu dace da amsarta. 

“Na san bakya kula kowa a waje lokacin, na san duk namijin da yayi miki magana a hanya bakya amsawa shi yasa nima banyi wannan gangancin ba, sannan da gaske ne ina zuwa wajen umar amma a ranar kamar yadda na fada miki wajenki nazo ba wajensa ba.” 

“Toh me yasa kazo bani hak’uri?” 

Ya d’an hadi’ye yawu, tayi tambayar ne ba tare da wani tunani ba, amma amsarsa zata iya sa mata wani tunanin, saboda haka yayi deciding sirka zancensa da gaskiya. 

“Bayan na koma gida, zuciyata ce ta kasa nutsuwa da tunanin abinda nayi ban kyauta ba, tunda har na tab’a miki magana kuma kin amsa min, kin tuna ranar?” 

Tayi murmushi a hankali sannan tace. 

“Adduwa, kad’anya, taura, magarya, d’inya da kuma d’ayan mai kwallo da yawa a ciki….” 

Yayi murmushi shima. 

“Right, wannan ranar…shi yasa nazo na baki hakuri saboda a rayuwata bana tab’a son in zama sillar b’acin ran wani…musamman ma kuma ke.” 

“Ka kyauta sosai saboda da baka zo ba, bana jin zan iya wani baccin kirki a a ranar.” 

Zancen ya masa dad’i sosai, yayi dariya a hankali amma kuma mai zurfi har saida jikinsa ya jijjiga tare da nata, tunda tana kwance ne a jikinsa ne wajen karfe sha d’aya na dare, ya murza ‘yan yatsunta dake sarke da nasa kafin yace. 

“Nagode for ur cocern Noory!” 

Daga nan dukkan wata tambayar data biyo baya ta shafi likes and dislikes d’insa ne da take son sani, kuma baya tunanin akwai kalma d’aya da ba ainihin gaskiyarsa ya fad’a ba anan. 

******* 

“Tunanin me kake yi Imran?” 

Muryar ta janyo shi daga duniyar space d’in daya tafi a cikin office d’insa. ya d’ago da kansa a nutse ya kalli Shamsudden dake tsaye a gaban table d’insa. 

“Na tabbata baka yi sallama ba shi yasa kake zaton tunani nake yi.” 

“Amma nayi knocking kuma har na shigo baka jini ba.” 

Yayi murmushi a gefen kumatunsa kafin yace.

“May be tunanin amaryata nake.”

Shamsudden yayi murmushin shima tare d’aga hannayensa sama.

“Afuwan, ai na manta kai d’in sabon ango ne, watakila ko don bamu ga ka d’auki hutu bane.”

“Karka damu, Kwanan nan zan d’auka insha Allah.”

“Allah ya kaimu, dama kayi baqo ne nazo in gaya maka.”

Girarsa ta had’e waje d’aya.

“Baqo? me yasa bai shigo ba toh?”

“Ban sani ba, shigowata kenan malam hamisu masinja yace in taimaka in gaya maka don Dr. Turaki ya aike shi.”

Ya gyad’a kansa a hankali.

“Well nagode, bari inje in gani.”

Shamsudeen na fita ya rufe file d’in dake gabansa, wanda bai ko yi halfway na signing sababbin arrangement d’in da zasu fara da wasu companies ba.

Ya bud’e drawer gefensa yasa shi a ciki, idanunsa suka gane masa kwalin hadaddiyar wayar da ya siyowa Sa’adha d’azu, murmushi ya sub’uce a kumatunsa hango irin farin cikin da zata yi yau, ya maida drawer sannan ya fita daga office d’in ya nufi hanyar elevator, yana sauka ground floor yaci karo da malam hamisun ya dawo daga aikensa.

“Yawwa yallab’ai wallahi aiken Alhaji ne ya tsaida ni, shi yasa nace da maigidana ya taimaka ya gaya maka.”

“Ba komai Baba, a ina yake mai jiran nawa?”

“Yana daga wajen ajiyar motoci ranka ya dade.”

Da jin haka Imran ya fahimci waye baqon nasa. Yana isa parking lot d’in ya hango wannan matashin tsaye a jikin wata mota kamar wancan lokacin daya wuce a baya.

“Na san dai sati d’aya ya isa ace ango ya huta, tunda gashi har ya fito aiki.”

Muryar jaamil ta shiga kunnensa.

“Kwana bakwai fa jaamil, ka san dole zan neme ka amma kayi zamanka saboda ka san ba ta yadda zanyi na sameka.”

Maimakon ya amsa sai yayi murmushi ya kalli wajen yace.

“Abin da mamaki, last time da muka tsaya anan nazo ne in k’ara jaddada maka cewa kar kaje wajen yarinyar nan…yanzu kuma gata a matsayin matarka.”

“Sunanta Sa’adha.”

“Ko kuma habeebty ko Noory.”

Mamaki ya kama Imran a lokaci d’aya.

“You’re spying on me?”

“Ba komai ba, kawai irin part d’in da kuke hira a falo, kuke cin abinci tare da kuma in kana wasa da gashinta ko…”

Kafin ya k’arasa Imran ya jefe shi da wayar hannusa, tana k’arasowa ya cafe ta da wani irin sauri irin wanda idanun mutum ba zai iya d’auka ba.

“Ka kwantar da hankalinka yarima, I assure you baka yi wani abu ba daidai ba, ya kamata dama kayi komai yadda zai dace da tunaninta, ‘yan mistake d’in kad’an ne kuma I didn’t blame you, yarinyar tana da d’auke hankali.”

“Ba wannan nake son ji ba, me ya hana ka contacting d’ina har tsawon sati d’aya?”

“Wani dalilin ne yarima, wanda ya shafe naka.”

“Wane dalili ne da kai a yanzu da yafi abinda yake gabanmu?”

Maimakon ya amsa sai yace.

“Ya ciwon nata?”

Imran yayi shiru kamar ba zai bashi amsa ba shima kafin yace.

“Kamar yadda ka sani ne ai ba abinda zai faru in har muna tare, yana nan kwance a jikinta.”

Jaamil ya gyad’a kansa a hankali yace.

“Allah yayi wahalarmu ba zata yi tsawo ba yarima, don a yanzu komai yazo k’arshe.

Naani ta dawo kuma zata raba yarinyar da b’arin ruhinka a yau d’in nan!”

**********

Imran ya bud’e k’ofar motarsa da wani irin k’arfi da yasa handle d’in  b’allewa ya fito gabadaya, Alarms d’in jikinta suka hau k’ara da k’arfi, amma bai damu ba tunda har kofar ta bud’e, ya tayar da ita sannan ya danna button d’in hood d’in jikinta alarms d’in suka yi shiru.

Ya juya ya sata a reverse sannan ya bar cikin parking lot d’in da dukkan saurin da zai iya, ya canja gear jiki zuwa ta farko sannan ya shiga canja k’afarsa daga wajen clutch zuwa danna accelerator da sauri, hakan yasa motar ta cilla kan hanyar da zata kaishi main gate d’in fita daga wajen cikin wata irin k’ara data dauki hankalin gabadaya mutanen dake wajen, amma bai damu ba, burinsa kawai a lokacin tayoyin su cigaba da cillawa dashi zuwa inda hankali da ruhinsa ya tafi.

Ya canja gear zuwa ta biyu sanda yasha kwanar data hau dashi kan titi, ya sake danne accelerator sannan ya maida gear zuwa uku, injin motar yayi wani irin kuka kamar shima yana fad’in amincewarsa game da yadda motar ke tashi akan titi.

Maganganun jaamil suka karad’e kunnensa kamar daga cikin speakers d’in motar suke fitowa.

“Bama buk’atar wani b’ata lokaci, ina tunanin komai zai gamu a yau….. sai mu nemi hanyar kuma da zaka rabu da ita cikin sauqi.

Naani tace abinda muka yi ba kuskure bane, sai dai garaje….munyi garajen yanke hukuncin cewa ka aureta….

Ya kalli agogon kan dashbord d’in motar, minti uku ta wuce tun sanda jaamil yake fad’a masa wad’annan maganganun, minti uku ya k’ara akan halin da Sa’adha ke ciki a yanzu, yaji kamar ya cillar da motar ya fita yabi iska amma ya kasa saboda ya riga ya d’auki hankalin mutane da yawa kuma kowa na kallonsa.

Yayi ta kurd’awa ta tsakanin motoci baya ko lura da ihun horn d’in da ake danna masa da kuma yadda hannuwa suke fitowa ta window alamun zagi, kwakwalwarsa kawai aunawa take da tunanin hanyar da ta rage a gabansa kafin ya isa ga Sa’adha, wani irin abu mai zafi ya yanke kwakwalwarsa da tunanin wane hali take ciki yanzu, meke faruwa da ita ko kuma me ya riga ya faru?

Yayi rantsuwa a zuciyarsa tafi cikin k’irga cewa in har wani abu ya sameta, sai ya dagargaza ruhin jaamil, sai ya dagargaza shi yadda ba zai sake amfanuwa ba tunda har zai iya yanke wani abin a cikin al’amarinsu ba tare da shawararsa ba.

Ya sake danna pedal d’in k’asan k’arfasa da k’arfi sannan ya tura gear zuwa ta hud’u, RPM d’in motar ya tafi zuwa wajen Eight thousand, motar ta sake cillawa saman titi.

Zai isa wajen Sa’adha ba tare da komai ya faru ba, ya cigaba da gayawa zuciyarsa da fatan zata fahimta ta rage k’arfin bugawar da take yi, ba abin da zai same ta, ba’a yanzu zamansu zai zo k’arshe ba…komai zai cigaba zuwa tsawon watanni kamar yadda tunaninsa ya tsara tun farko. Ya danne clutch d’in motar da k’arfi sannan ya maida gear zuwa biyar, motar ta k’ara gudu akan mahaukacin wanda take yi da farko, ya dinga wuce motoci da ginunnukan da suka zama blur a idonsa.

Daga can gaba idonsa ya hango masa wani had’dd’en traffic na jerin motocin da basa ko motsawa, taraffic a wannan lokacin? taya zai zauna yana jira alhalin bai san halin da Sa’adha ke ciki ba? kowanne wucewar second d’aya ji yake kamar lattin awanni yake yi.

Kawai sai ya maida gear zuwa uku sannan ya juya kan motar cikin wani irin sauri ya shiga wata kwana daga gefensa, bai tab’a bin hanyar ba kuma bashi da tabbas d’in inda zata kaishi, yayi ta binta kawai yana yin kwanoni lokacin da mutane da yara ke ta gudu suna matsawa gefe don kar ya buge su.

A haka ya samu ya lalubo wata hanyar data maida shi kan titi, yana fahimtar inda yake ya sake danna accelerator k’asa, ya d’ane kan titin tare da tura clutch sannan ya maida gear zuwa hud’u. Ya dinga wuce shaguna da mutane a hanya suna ta harkokinsu ba tare da sanin had’arin dake faruwa gaba dasu kad’an ba.

Idonsa ya kai kan wani sign dake jikin street d’in da yake kai, few more minutes! ya sake fad’awa zuciyarsa, few more minutes suka rage ya k’arasa wajen Sa’adha, a da in yazo wajen gani yake kamar ya zo gida ne, amma a yanzu titin ya k’ara yi masa tsawo, yaga kamar ba hanyar da ya sani bace, sai da kwakwalwarsa ta jiyo masa bugun zuciyar Sa’adha sannan ya tabbatar hanya daidai yake bi, wani irin releif ya sauka a jikinsa, releif sosai da yasa zuciyarsa matsewa cikin zafi…sai dai bugun zuciyar tata was weak, bata bugawa a normal rate d’in data saba. Me ya same ta?

Har ya k’araso kwanar gidansa bai rage gudun motar ba, sai da yazo dab! da kwanar sannan ya taka birki da k’arfi motar tayi sliding sideways ta shiga kwanar.

Tun daga nesa idonsa ya hango masa malam Aminu ya bud’e kofar gate d’aya kamar yana gyara wani abu, ya danna masa horn wanda ya karad’e layin gabadaya, yana d’agowa yaga shine yayi sauri ya rarumi d’aya kofar ya bud’e, da kyar Imran ya iya tsaida motar sanda ya shiga cikin gidan, ‘yan inches ne kawai suka rabata daga hawa balcony da zai kaika k’ofar falo.

In one swift move ya tura k’ofar motar da kad’an ya rage ta b’alle daga hinges dinta, ya nufi kofar falon ya b’alle handle d’inta don ba zai iya tsayawa bud’ewa ba.

K’ofar na wangalewa idonsa ya gane masa abinda yake tsoro, abinda zuciyarsa ke taraddadin faruwa, yaji yaji dukkan jijiyoyin jikinsa sun tsaya cak da aiki, bugun zuciyarsa ma ya d’auke na wani lokaci…idanunsa suka tsaya akan abinda ke gabansa.

Wani dunkulallen haske dake lilo a iska, haskensa ya tarwatse ya baje ko’ina a cikin falon, daga k’asa kuma jikin inuwarsa, wani tambari ne ya fito, tambari irin na adon sarautarta!
Imran ya tattaro dukkan wani ragowar k’arfi na jikinsa ya k’ifta idanunsa a hankali sanda wannan hasken ya d’auke cikin abinda baifi second d’aya ba, daga shi har inuwarsa suka dunk’ule suka bi cikin iska. 

Yana taka k’afarsa cikin falon, k’amshin wani daddad’an turaren wuta ya shiga hancinsa ba tare da shawara ba, gidan yana nan kamar yadda yake a kullum, komai zaune a muhallinsa cikin gyara tsaf! sannan shiru babu alamun wani abu mai rai a cikinsa, tunani kala-kala suka karad’e kwakwalwarsa a lokaci d’aya, yaji kamar ya ture bagwayen gidan, koina ya fito a lokaci d’aya. 

Zai iya yiwuwa Sa’adha na d’aya daga cikin d’akunan a wani irin hali, watakila tayi ihu da kuka har ta gaji maigadi ba jiyota ba tunda yana can bakin gate, watakila tana dunk’ule a waje daya cikin muryarta ta dashe cikin mawuyacin hali… watakila kuma abinda ya faru da ita ya shafe duk wani hasashensa. 

Ba abinda bai kawo ba cikin zuciyarsa kafin ya isa k’ofar d’akin da yake iya jiyo bugun zuciyarta a hankali kamar irin bugawar zuciyar jariri, ba tare da wani tunani ba ya buga k’ofar d’akin da karfi ta bud’e. 

Kunnensa ya jiyo masa k’arar shak’ar numfashi cikin tsoro kafin idanunsa su gane masa Sa’adhan, tsaye cikin wata had’dd’iyar riga royal blue data wuce gwiwarta kad’an, gashin kanta a tufke cikin bun sannan hannunta rike da kunnenta na hagu tana mak’ala wasu ‘yan kananan silver d’ankunne. 

Cikin giftawar abinda bai kai second d’aya ba, Imran ya manta duk wasu rules na mu’amalar d’an adam yayi appearing a kusa da ita, Idanunta suka zare cike da tsoro tana kallonsa. 

“Yanzu ka dawo? me ya faru…?” 

“Sa’adha me ya same ki? me ya faru.?” 

Tambayoyinsu suka had’e a lokaci guda hakan yasa kowannensu yayi shiru, ta had’iye yawu tana kallonsa kafin ita ta fara magana. 

“Ba abinda ya same ni, me ya faru?” 

Maimakon ya bata amsa sai kawai ya shiga lalubar gabad’aya jikinta kamar me neman wani abu daya rasa. 

“Me ya faru ne? me ya same ni?” 

Ta sake tambaya muryarta na shaida alamun tsoro. Ya cigaba da duba koina a jikinta yana yayyage rigar wajen da duk hannunsa ba zai iya kaiwa ba. Nanne taji zuciyarta ta cika da wani irin tsoro, hannayenta suka shiga rawa, meke faruwa? meya same shi? ko kuma ita me ya sameta yake nema a jikinta. 

Tasa hannayenta duk biyu ta rike nasa sanda yake kok’arin yage d’aya kafad’ar rigar, wanda ya zama shi kad’aine abinda ya rik’e ta a jikinta, ta kalli idanunsa sosai sannan tace. 

“Me ya faru dan Allah? meya same ni? in bruises d’in nan kake nema gabad’aya sun tafi, dama na gaya maka baza su dad’e ba, guda d’aya ne kawai ya rage a nan…” 

Ta k’arasa tana nuna masa k’asan hab’arta, ya d’ora hannunsa a wajen sannan ya zamo dashi kan k’irjinta daidai saitin zuciyarta, yayi shiru kamar yana sauraren wani abu sannan a hankali da muryarsa mai zurfi yace. 

“Me ya sami zuciyarki?” 

“Huh? zuciyata kuma?” ta tambaya blankly tana kallonsa. 

“Bayan na fita wani yazo?” 

Ga mamakinsa sai yaga tayi murmushi mai fad’i sannan tace. 

“Su Aunty ne suka zo, su wajen biyar baka ji dad’in dana ji ba wallahi, harfa dasu Amina da Rahma, su basu dad’e ma da tafiya ba…” 

Jin haka yasa yayi saurin katseta. 

“Yanzu suka tafi?” 

“Eh, baza sufi minti talatin ba dai…” 

Minti talatin, a cikin minti talatin komai zai iya faruwa ba tare da ta sani ba…sai ya juya da sauri ya bud’e wardrobe dinta, ya d’auko first kayan da hannunsa ya fara kaiwa yazo ya sasu a cikin hannunta. 

“Ki saka yanzu ki fito ina jiranki.” 

Bai jira me zata ce ba ya juya ya koma main falon, ya tsaya daidai tsakiyar carpet d’in inda wannan hasken ya fito, hasken dake nuna cewar gabad’aya duk wani hoto na gidan ya riga ya baiyana ga Naani, ta riga ta ga komai a can wajenta, sai dai abinda bai tabbatar ba shine in har ta shafi jikin sa’adha, zata iya yin komai ta gama cikin abinda baifi minti biyu bama amma in har hakan ne ba lallai yazo ya sami Sa’adha a yadda take yanzu ba. 

“Na shirya, ina zamu je?” 

Ya juya ya kalleta, ta saka wata doguwar riga ta atamfa mai kyau da mayafinta sky blue, gloss d’in da ta saka a bakinta mai kyalli ya taimaka wajen haska manyan kyan fuskarta, tana kallonsa da idanunta so innocent masu d’auke da tsantsar sonsa. Ya Allah! taya zai iya bari a cutar da wannan halittar ta dalilinsa. 

Har ta bishi cikin mota suka hau titi suka bar gidan, baice mata komai ba itama ka bata k’ara tambaya ba, don ko maigadi baiyi tambaya akan yadda ya shigo gidan d’azu ba, watakila fuskarsa ta nuna musu alamun rashin son magana a lokacin. 

“Da ka shigo falo d’azu kaga wani abu?” 

Sa’adha ta katse shirun motar sanda suka hau kan main titi, a lokaci d’aya ya d’auke idonsa daga kan titin ya kalleta. 

“Wani abu me?” zuciyarsa cike take da fatan amsarta ta zama sab’anin tunaninsa. ilai kuwa! 

“Wani abu ne kamar k’adangare kamar tsaka ya mak’ale a jikin taga muka yita korarsa ni dasu Rahma yak’i tafiya.” 

Yaji zuciyarsa ta fad’a can k’arshen k’irjinsa, kamar ka cilla katon dutse cikin rijiya mai zurfi kana kallon tafiyarsa har lokacin da zai daki ruwan ya nutse, abinda suka gani ba k’adangare bane balle tsaka, d’aya daga cikin hakiman Naani ne, kuma in har sunzo gidan tun kafin tafiyar su Rahma kenan sun dad’e kenan. Dole ne akwai wani abu da ya sami Sa’adha wanda daga shi har ita basu sani ba. 

“Ina zamu je?” Muryarta a hankali ta k’ara tambaya, ba tare da tunanin komai ba ya bata amsa. 

“Asibiti.” 

Can d’in suka nufa, don in har bashi da tabass d’in abinda ya faru, dole neya sami mafita a yanzu, Sa’adha bil’adama ce, kuma jikinta irin na mutane ne, don haka in har wani abu ya canja a jikinta, asibiti zasu iya ganewa duk da ya san cewa baza su tab’a iya gano musabbabin abinda ya sameta d’in ba. 

“Asibiti? waye bashi da lafiya? na fad’a maka ba abinda ya sameni…” 

“Shshshsh….” 

Yayi saurin katseta a k’asan numfashinsa ba tare da ya d’auke idonsa daga titi ba. Allah ya sani baya son magana a lokacin don abubuwa ne da yawa ke tarawa da d’ebewa a cikin zuciyarsa, sai akayi sa’a itama ta fahimci hakan bata k’ara magana ba. 

Wani private hospital ya kaita, irin k’ananan asibitocin nan masu jiran suci kud’in patients. Yace a mata general check-up na komai da komai a jikinta, aka yanka masa kud’i ya biya, sannan suka shiga da ita. 

Ya samu waje a waiting area d’in da ba kowa ya zauna jira, a lokacin ne jaamil ya turo glass door d’in ya shigo cikin siffar wannan matashin. 

Imran bai ko d’ago da kansa ba har ya zauna a kusa da shi, jikinsa ya riga ya bashi cewa d’an uwansa ne wanda ba mutum ba. Ransa ya k’ara b’aci akan wanda yake a da, bai taba jin haushin jaamil kamar yanzu ba. Don me yasa zai tafi ya cigaba da abubuwa ba tare da saninsa ba, me yasa har Naani ta dawo bai sanar dashi ba? ta yaya ma ta dawo? a yadda lissafinsu yake ai har yanzu suna da kusan watanni biyu a gaba. 

“Me ya same ta?” jaamil ya tambaya shima ba tare da ya kalle shi ba. 

Bai ko nuna alamun yaji shi balle yayi niyyar bashi amsa, yana zaune perfectly still, ya dunk’ule yatsunsa na hannu d’aya akan bakinsa, kamar yadda dutse ke zama stiff a waje d’aya babu ko alamun fitar numfashi a tare dashi. 

“Na san laifina kake gani a yanzu yarima, amma dan Allah ka saurare ni, ka san ba zanyi komai don na b’ata maka rai ba.” 

Imran bashi da niyyar magana saboda ya cigaba da cewa. 

“Ranar da na koma muzaffar, ranar bwama ta same ni da zancen cewa sun sami labari Naani zata fito a daren, ban yarda da zancenta saboda a yadda Ma’amun ya shaida min lokacin dawowarta bai yi ba. Sai dai abinda nima ya bani mamaki shine a wannan daren Naani ta dawo d’in kuma ban sami ganinta ba har kwanaki biyu, saboda a washegari ta zauna da mukkarrabanta kan matsalolin da suka faru bayan bata nan, saboda haka sai a rana ta biyu na same ta. 

Tun kafin in fad’a mata komai yarima ta riga ta san zancen da zan gaya mata, ta riga taga komai ta san dukkan abinda muka aikata, sannan ta shaida min cewa abinda muka yi ba laifi bane, sai dai nayi garajen yanke hukuncin cewa ka aure ta, tace da ka cigaba da zuwa duk sanda ciwon ya tashi kana kwantar dashi da hakan yafi, amma na fada mata cewa kana loosing k’arfi ne da yawa duk sanda kayi hakan kuma baka iya maida hankali akan abinda ke gabanmu. 

Saboda haka tace min zata cire ruhin daga jikinta sannan mu san hanyar da zaka rabu da ita ba tare da bil’adama sunyi wani tunanin ba a cikin abinda bai kai wata daya ba. Don tace lokacin da take jira yana k’aratowa kuma har yanzu bamu cimma manufar ba. 

Naso sanar da kai hakan a washegari amma sai ciwon bwama ya sake tashi saboda haka ban sami kaina ba sai a yau da Naani ta sake kirana, nayi directing haskenta zuwa gidan da kuke. 

Amma banyi tunanin cewa raba jikinta da ruhin zai iya tab’a matsalarta ba yarima, saboda ni shaida ne akan wahalar da nasha kafin na iya juya zuciyar mahaifinta zuwa son yi mata aure yanzu, naga irin tarin k’aunar da iyayenta da ‘yan uwanta ke mata, ba zanso ace cikin sati d’aya kawai mun yi mata lahani ba. 

Sai dai tunda har an cire….” 

“Ba abinda aka cire.” 

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]