TATTALINTA CHAPTER 6 - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

TATTALINTA CHAPTER 6

TATTALINTA CHAPTER 6

- - Post a Comment
TATTALINTA
CHAPTER 6


*S*ultan na yin parking Yusif yayi saurin bud'e k'ofar ya fito,k'ok'arin d'aukar Balqees yake yi cikin sauri da tafasar zuciya Sultan yayi saurin ture shi tare da zabga mai harara idanunshi jawur yace.
"Karka sake ka ta6a ta Yusif, ka bari idan aka ce ta mutu sannan ne zaka iya zuwa ka d'auketa dan naga alamar rayuwarta kake nema."
Wuru-wuru da idanuwa Yusif yayi yana faman hura baki Sultan ya d'akko ta dai-dai lokacin nurses suka zo da gado ya d'ora ta akai,cike da mamaki sister Hadiza ta kallesu tace.
"Ohh kaga wata jaraba,kullum a gida d'aya mutum biyu ne basu da lafiya.idan ya warke sai ta kama, idan aka samu ta warke shima sai ya kama kamar tsafi."
Wata nurse d'in ce dake gefenta ta kalli Hadiza bayan ta harareta suna sauri zasu kai Balqees cikin emargance tace,
"Ke dai Hadiza kin fiye sa ido d'ai-dai kune baki sani ba a duk masu zuwa cikin asibitin nan."
Dai-dai lokacin suka shiga da Balqees cikin d'akin.a reception kuwa Sultan na ganin an shiga da ita ya juya ya kalli Yusif zuciyar shi har tafasa takeyi yana jin tamkar ya shak'eshi sai dai yana gudun raini dan yasan baza a rasa wasu d'aliban nashi ba a cikin asibitin.wayar shi ya zaro hannanshi sai faman karkarwa yake yi ya kira abban shi wanda lokacin yana police station, yana d'agawa Sultan bakin na rawa yace.
"Abba anga Baby."
"Alhamdulillah Ahmad a ina? Sannan yanzu tana ina? Cikin wane hali take ciki?!"
Duk yaji abba ya watso mai tambayoyi a rud'e cikin farin ciki.kallon Yusif ya sake yi wanda yake zaune ya dafe kai sannan Sultan ya d'auke kanshi daga kallon Yusif d'in ya numfasa yace da abba.
"Muna asibiti yanzu haka bata cikin hayyacin ta."
    "Ya subahanallahi, bari na k'araso."
Abba ya fad'a tare da katse kiran, 'yan sandan yi yiwa bayani sannan ya fito aka had'a shi da mutum biyu suka tafi asibitin.tun kafin su k'arasa abba ya dinga buga waya yana sanar da 'yan uwa da abokai cewar an ganta. Suna shiga abba ya rik'o Sultan cikin zakuwa da sanjin yadda aka yi ya ganta abba yace.
     "Ahmad a ina ka samo ta ne?!"
Sultan ya numfasa tare da satar kallon inda Yusif yake zaune, yana nan tunsan da suka shigo ya d'ora hanna a gushi be sake d'agowa ba sannan ya maida ganin shi zuwa gurin abba ya numfasa yace.
     "Abba muna tafiya ne nida Yusif zamu je gest house d'in daddy kawai muka ga mutum a yashe sai faman haki take, kamar kar mu k'arasa dan har mun wuce sai muka koma wajan, cikin sa'a abba muna zuwa sai muka ashe baby ce duk ta fita a hayyacin ta shine muka d'akko ta muka taho asibiti."
Mamaki mai tsanani ya kusan kashe Yusif dake zaune yana jinsu,kafin kace mene tuni 'yan uwa sun cika asibitin hajiya kaka kuwa har hawaye tayi dan murna. Sai da Balqees tayi kwanaki biyar a kwance tana k'ark'ashin kulawar Dr gadanya sannan ta fara samun kanta sai dai kullum cikin kuka take bata magana.misalin karfe 7:30pm tana kwance tana faman hawaye Sultan ya shiga cikin d'akin,k'arasawa yayi inda take ya zauna tana jinshi ta gane cewar shine hakan yasa ta kuma rushewa da kuka dai-dai saitin kunnanta ya kai bakinshi yace mata.
   "Koda wasa karki sake kice Yusif ne ya sace ki, kice kawai baki sansu ba kinji...?!"
Banza tayi mishi tare da kuma rushewa da kuka idanunta a lumshi,yana k'ok'arin kuma yin magana yaji muryar Dr gadanya sai yayi saurin mik'ewa ya kalleshi.bayan Dr gadanya ya gama dubata ne Sultan ya kalleshi yace.
    "Dr dan Allah ina son kayi mata test d'in ciki dana HIV dan tabbatar da ingantacciyar lafiyar ta."
Balqees da idanunta ke rufe sai gata ta bud'e su cikin tsananin tashin hankali. Tsaye ta gansu shida dr gadanya ta kuma rushewa da kuka dr gadanya ya kalli Sultan tare da cewa.
    "Ok karka damu za'ayi mata insha Allah hakan yana da kyau amma bana tunanin tana da wani ciki dan da tuni na gane hakan amma dai za'a duba dan tabbatarwa.
   "Na gode sosai Dr."
Sultan ya fad'a sannan dr gadanya ya fita shi kuma ya koma wajanta.lallashinta ya soma yi cikin nuna kulawa, tunda aka kawo ta asibitin batayi magana ba sai yanzu ta kalleshi tace.
    "Yaya yanzu ni kakewa zargin ciki harda... da...HIV?na shiga uku ni yanzu ya zanyi kayi min wannan kallon ina ga sauran mutane?!"
   "Shhhhh baby ba haka nake nufi ba,ina son tabbatar da cikakkiyar lafiyar kine.kin san Yusif mugun mutum ne ta iya yiwuwa ke baki sani ba ya...yayi...am..yayi miki wani abun ta wata hanyar, ki bari a gwadaki amma bana zarginki da komai kinji baby karki sa damuwa a ranki."
Cikin harzuk'a tamkar ma ta manta waye a gababta tace mai.
    "Karna sa damuwa a cikin raina? Sabida me? Ok sabida ni d'in banida sashen damuwa a cikin zuciyata ko? Wallahi sai yanzu na kuma tabbatar da cewa ni d'in marainiya ce, Allah sarki papa da Ummi rashinku ya janyo min matsala da shiga cikin tashin hankali wai me yasa ma aka fito dani ba'a barni nina nabi iyaye naba ah? Meyasa Yaya Yusif zai kawo ni asibiti be bari na k'arasa ba? Duk kun tsaneni kuna min kallon 'yar isa ko? Toh nima ba..."
Yayi saurin toshe mata baki da tattausan hannunshi cike da masifa ta fara bubuge mai hannun hawaye na zirarowa ta cikin idanunta.kallonta yayi cikin ido zuciyar shi na bugawa sa jin maganganunta itama tana kallonshi fuskarta cike da hawaye kawai tasa hannunta ta finciko shi ya fad'a kirjinta jikin shi na rawa ya zaro ido yana dubanta tare da waiwayawa bayan shi yana kallom k'ofa,k'ok'arin tashi yayi daga jikinta da sauri cikin kuka yaji tana cewa.
    "Alhamdulillahi! Yaya Sultan kaine namiji na biyu da kuka ta6a kwanciya a kan k'irjina, daga Yusif sai kai. Idan har aka yi bin ciken nan aka gano ina dasu gaba d'aya toh babu shakka Yaya Sultan cikin na Yaya Yusif ne HIV d'in kuma kaine ka sanya m..."
Bata k'arasa ba taji ya fizgota zuwa jikinshi ya matseta gagam a k'irjin shi bakin shi na rawa dai-dai kunnan ta yake magana.
    "Shhhhhhhh! Baby is enough, ya isa haka Allah ya huci zuciyarki an fasa yin gwajin na fita daga zargi na kuma had'a kirjina dana ki badan komai ba sai dan ina son ki ci gaba da d'auka ta a matsayin papa." 

Tana makale a jikinshi sai faman lumshe idanuwa take yi. Sam ta kasa zare jikin nata a nashi domin har wata nutsuwa take ji a cikin zuciyar ta, a hankali ya fara k'ok'arin zamewa amma ta mak'ale suna haka yaji an bud'e k'ofar yayi-yayi-yayi ya kwaci kanshi amma ta kankameshi sai kuka take mai yajiyo muryar hajiya kaka na cewa.
    "Oh kaji shashanci, memakwan da ta farka kazo ka kiramu shine kuma kuka shantake annan?jibarku sai kace wasu mata da miji baxa ku saki juna ba.."
A hankali Balqees ta zame hannunta ta koma ta kwanta shi kuwa sam ya kasa d'aga ido ya kallesu sai faman goga farcan shi yake yi a jikin jinyar shi. Umman shi kuwa kafeshi tayi da ido amma yak'i kallonta abba ya k'arasa wajan Balqees d'in tare da shafa kanta yace.
   "Ina ne yake miki ciwo yanzu?!"
Girgiza mai kai tayi alamar babu sannan ya kuma cewa,
   "Zaki gane mutanan da suka saceki idan an nuna miki su?!"
Balqees najin haka ta kuma 6arkewa da kuka kamar ranta sai hankalin abba ya tashi nan da nan ya hau lallashi sai ya fara tunanin k'ila kwakwalwar ta bata son sake jin an ambaci hakan.sai da tayi shiru sannan abba ya fita ita kuma ta ta6e baki tana k'ok'arin zama akan kujera,shi dai 6e kalleta ba bare yaga yanayin da take ciki sai da ya dad'e sannan yayi waje zuciyar shi na tayi mai sake-sake masu kyau da marasa kyau har tsawon wani lokaci. 

_Bayan wani lokaci_ 

Suna zazzaune a cikin d'akin Dr gadanya ya shigo,bayan dube-duben dayayi mata ya kalleta cikin kulawa yace.
    "K'anwata jekiyo fitsari a nan ki kawo min yanzu ina jiranki."
Da sauri Balqees ta zaro idanuwa kafin ta maida kanta wajan Sultan, gani tayi ya zaro waya yana daddannawa sam yak'i bari su had'a idanuwa wato da yace zai ce anfasa ashe karya ne ba fad'a yayi ba.amma ya mugun raina mata hankali yanzu tana ji tana gani zata yadda ayi mata wad'annan gwaje-gwajan?kunyar Dr gadanya take yi baza ta iya yi mai gaddama ba dan haka jiki a sabule ta k'ar6i 'yar robar da yake mik'o mata Aisha dake kusa da ita ta temaka mata wajan zuwa toilet ta shiga. Bata dad'e da shiga ba ta fito yana nan tsaye ta mik'a mai cike da kunya shi kuma ya k'ar6a yayi waje ta k'arasa kan gadon sai son su had'a ido takeyi da Sultan amma yak'i bari dan k'iri-k'iri yaki kallonta haka ta dinga zabga mai harara be san tana yi bama.
    "Shi kuma me zai yi da fitsarinta haka?!"
Suka jiyo muryar Umman Sultan dan yanzu kusan kullum tana asibitin kasan cewar wannan karan har hatsaniya suka yi da maigidan nata. Duk sai aka fara kalon-kalo yayin da jikin Balqees yayi sanyi ta rufe idanunta bata sake barin sun had'a ido da kowa ba tana jinsu dai kowa sai canki cankar shi yake shima Sultan be ce komai ba har tsawon wani lokacin sunata hirarsu. 

Misalin 8:17pm Dr gadanya ya sanya nurses suka d'auki Balqees akaje aka yo mata gwajin HIV, zuciyar ta banda rad'ad'i babu abinda take yi. Bayan anyo mata suka mai da ita d'aki Balqees ta kafe idanuwa tana jiran shigowar Sultan amma shiru har wajan goma na dare bashi ba labarin shi sai su Yaya Heemu dasu Al-eemin ne kawai suka shigo Yusif kuwa tun washe garin ranar da suka kawo ta Sultan ya dakatar dashi wajan zuwa,abin mamaki babu wani gaddama ya dena zuwa amma da alama kwantan 6auna yayi dan ta ciki na ciki.
   "Hello Ahmad kaxo office ka same ni yanzu."
   "Toh Dr bari na k'araso."
Sultan Ahmad ya fad'a. Cikin wasu 'yan dak'ik'a sai gashi ya shiga gurin Dr gadanya ya samu guri ya zauna kirjinshi sai bugawa yake yi yana tsoran jin saka makon Dr gadanya ya kalleshi tare da mik'a mai wasu takardu yana cewa.
    "Ahmad k'anwarka bata da duk abubuwan da kake zargi, lafiyarta lau ta wannan 6angaran sai dai tana cikin damuwa nasan kuma bazai rasa nasaba da shiga tashin hankalin nan da tayi ba dan haka sai a dinga kula da ita ana k'ok'ari wajan ganin an d'auke mata duk wani abu da zai sanya ta cikin matsala sabida kare lafiyar ta musamman ma zuciyarta da kwakwalwarta."
Nannauyan numfashi Sultan ya sauke sannan yayiwa Dr gadanya godiya ya tashi ya fita zuwa d'akin da suke. Ai kuwa yana shiga suka yi ido hudu dashi fuskar nan tata a murtuk'e shi be ma ta6a ganinta a cikin wannan fuskar ba amma yayi fuska ya shiga ba yabo ba fallasa...

    
    *Z*amaSultant yayi a kan kujerar dake kusa da gadon yana kallon takardar hannunshi. kallon shi tayi ganin shi d'in bashi da niyar yi mata magana ne yasa ta mik'a hannu ta kar6i takardun hannunshi tana kalla.
   
"Wallahi sai na gayawa Abba cewar Yaya Yusif ne ya sace ni a'hee...!" 

Shiru yayi mata dan yaga alamar tashin hankali take nemanshi da shi, haushi ya kuma kama Balqees ta tashi zaune tare da zura hannu ta zare wayan na shi dake cikin aljihun shi, nan ma k'in kulata yayi ba zato kawai yaji tana cewa. 

"Abba kazo kaji zan gaya maka...toh abba sai kazo." 

Kallonta yayi cikin mamaki tare da fizgar wayar shi, tashi yayi yaje ya rufe k'ofar d'akin sannan yayi saurin dawowa gurinta ranshi a 6ace yace. 

"Baki da hankali ne baby? wato maganata ce baza kiji bako? raini ne ya shiga tsakanin mu kome? toh wallahi idan kika kuskura kika sanarwa da abba cewar Yusif ne ya saceki babu ni babu ke bazan sake kulaki ba tunda kin raina ni marar kunya kawai." 

Yana kaiwa nan ya mik'e tsaye zaije ya bud'e kofar, da sauri Balqees ta sakko daga kan gadon sai kawai ji yayi ta rungume shi ta baya, abin ka da gajera sai ta tsaya iyakar bottom d'in shi. Kawai ya tsaya cak tare da saurin sanya hannunshi ta bayan ya janyota yana kallon fuskarta wadda hawaye ya fara cikawa tayi saurin yin k'asa tare da kama kafafuwan shi tana hawaye tace. 

"Yaya zulkallain yanzun wallahi baka sona, tayaya za'a ce kaine mutum na farko da zai fara yi min wannan mummunan zargin!duk duniya babu wanda na yadda dashi nake kaunar shi tamkar rayuwa ta sama da kai, toh kaina ka fara zargina kaga gwara na gayawa abba tunda kaima baka sona yanzu." 

"Waye ya gaya miki cewar bana sonki?" 

"Yaya duk alamu sun nuna, baka sona kafi son wannan Nadiyan." 

K'afarshi ya zare tare da k'arasawa ya bud'e kofar sannan ya dawo wajanta, hannunta ya kama tare da d'ago ta ya maida ita kan gadon sannan yayi murmushi yana kallonta yace. 

"Ta6! ke yanzu baby da Nadiya kike kishi? why? keda nake son inyi sauri inyi aure sabida ki samu Momy amma kike wannan abun?!" 

Wata uwar harara ta watsa mai tamkar idanunta zasu fad'o. "wai me ya d'auke ta ne duk abinda take baya gani ko kuma dai raina mata hankali yake yi, tana son gaya mai 6aro-6aro amma tana tsoran yadda zai d'auki maganar gashi ita ba k'awa gareta ba bare ta gaya mata ta bata shawara. tana faman sake-sake taji ya hura mata iskar bakin shi cikin kwayar idanunta ta lumshesu ahankali yayi murmushin shi mai kyau yace. 

"Hmmm baby mijinki ya bani wallahi, ina son ma nayiwa wannan friend d'in nawa da yake sonki tunda Allah ya bayyanaki gara kiyi aure zan turo shi ku fahimci juna idan an sallameki kyayi karatun a d'akin ki." 

"Kan ubancan.! Latsi...!" 

Ta fad'a a fili duk a tunaninta cikin ranta ta fad'a, fuskarta a yamutse alamar shiga cikin takaici Sultan yayi saurin kallonta baki a bud'e yaga sam ita bashi take kallo ba yana k'ok'arin yin magana sai ga abba ya shigo dashi da Yusif Balqees tayi saurin kallon Yusif tare da k'ara tsuke fuska zuciyar ta tashiga bugawa da k'arfi da k'arfi shi kuma Sultan ya kura mai ido dan ganin da me yazo abba ya kamo kafad'un Balqees cikin kulawa yace mata. 

Story continues below


"Sannu Balqees ya jikin naki?!" 

Cikin rawar murya Balqees tace, 

"Da sauk'i Abba ni nama gaji da asibitin nan dan Allah a sallame mu mutafi gida." 

"Ok karki damu Dr gadanya yace yau da dare zai sallameki idan ya k'arasa miki ragowar allurarki. Yanzu ki gaya min abinda kike son sanar dani kin gane su waye suka sacekin?!" 

Kallon Yusif tayi wanda ya kafeta da idanuwa da alama babu ko d'ar a cikin ranshi domin be nuna hakan ba yana tsaye kyam a bayan abba ta kuma kallon Sultan wanda ya kafe Yusif da nashi idon fuskar nan tashi ba yabo ba fallasa cikin sanyin jiki ta cewa abba. 

"Wasu mutanene abba irin manyan nan, sai da na dawo cikin hayyacina sannan naga wanda yasa suka kamo ni, ya ta6a cewa yana sona tun farkon dawowata k'asar nan sai dai ban amsa mishi ba domin na sanar mishi cewar ina da wanda nake so kuma wanda zan aura." 

Da sauri Sultan ya kalleta cikin zaro idanuwa cike da mamakin jin kala manta wanda be ta6a jiba, sam bata kalleshi ba taci gaba da cewa. 

"Shine shi guy d'in ya nuna min cewar a dole sai na aure shi domin shi yana sona a haka muka rabu,shine ranar da zan tafi ethopoeia yasa aka d'auke ni bayan ya shigo d'akin da nake shine yace wai na raina mai hankali da ban gaya mai cewar zanyi tafiya ba,yace ya d'auke ni bazai barni na fito ba sai yasa anyi mana aure. 

Bak'in cikin kalaman sa ya sanya ni na dena cin komai na gidan har tsawon kwanaki tun daga nan na dena samun kuzari kirjina ya dinga min rad'ad'i daga nan ban sake sanin inda nake ba sai anan gurin." 

Abba ya shiga tashin hankali sannan ya kalleta yace, 

"Yanzu zaki iya gane wad'anda suka yi miki wannan abun?!" 

Balqees ta kalli Yusif hawaye suka ziraro mata sannan ta d'aga kai alamar Eh Abba yace. 

"Kin san gidan su guy d'in ko unguwar da kuka ra6a had'uwa dashi?!" 

Kafin tayi magana ta kalli Sultan wanda yayi saurin girgiza mata kai sannan ta kalli abba hawaye na zubo mata tace. 

"A'a abba sai dai kamannin shi baza su ta6a gogewa cikin idanuwa na ba domin shine mutum na farko daya ta6a shafar jikina a matsayin shi na d'ah namiji." 

Duk gurin babu wanda be rintsa ido ba jin abinda ta fad'a, cikin rud'ani abba ya janyo hannunta yace. 

"Hope basu yi miki komai ba yarinyata...?!" 

Tace "Eh abba babu daga haka." 

Ta fad'a tana sauke ajiyar zuciya, kanta ya shafa tausayin ta duk ya kamashi ya mik'e tsaye tare da cewa. 

"Bari naje na cewa Dr ya bani sallamar nan yanzu idan yaso ragowar allurar a kira Hawwah tayi miki a gida." 

Yana fad'a yayi waje yayin da Sultan ya mik'e tsaye yana kallon Yusif wanda ya hard'e kafa yana daga tsaye sannan yace mai. 

"Kanaji ko Yusif,tun wuri ina son ka fita a harkar baby, nace karta fad'i cewar kaine kayi mata haka asamu abin zagi da gulma da za adinga nuna zuriar muda shi. amma idan ka kuma cewa zaka kuma yi mata abinda kayi shikenan kofa a bud'e take karka fasa." 

Kwantacciyar sumar kanshi ya shafa mai matukar laushi sai shek'i take yi wadda shi Sultan baya barinta sai ya saisaye ta Yusif yayi murmushi irin na gefen baki tare da ta6e baki yana dafa lafad'ar Sultan yace. 

"Ina son yau dai a yita ta kare Ahmad, shin wai da kake hanani auran yarinyar nan toh kaine zaka aure ta ko kuwa kana nufin haka za'a barta bayan tana da duk abubuwan da zai sa tayi aure? ka gaya min son auranta kake yi ne ko kuwa ni ne baka so?!" 

Story continues below


"Mtsww! Kai wawane Yusif da kake min irin wannan maganar?kasan abinda kake fad'a kuwa? Nine zan auri baby? yarinyar da na raina a hannunna? Nake jinta kamar nina haifeta shine dan baka da mutunci zaka ce ina son auranta? So maintain your mouth, bana son haukan maganar ka ya kuma fitowa." 

Da karfi Balqees ta kwala wata uwar k'ara wadda tasa abba da Dr gadanya saurin shigowa dan dama suna gaf da shigan. hannunta a kanta suka tarar da ita yayin da Sultan da Yusif ke kusa da ita abba yana gyara babbar riga yace. 

"Ya akai?!" 

"Abba Yaya Sultan baya sona wallahi yanzu baya kaunata abba wai wani Yaya Sufee zai aura min kuma ni karatu zanyi, toh idan kuma ya dage sai nayi aure toh shi ya aure ni mana meh yasa ni baza a dinga bin zab'i naba...?" 

"Wh...wh...what..?!" 

Sultan ya fad'a cikin inina da zaro idanuwa yana mamaki, turo baki tayi tana k'ara zubar da hawaye yayin da Yusif yayi kicin-kicin ranshi yayi mugun 6aci. Yau ya k'ara tabbatar da cewar ba wani Balqees take so ba face Sultan Ahmad dan haka ranshi ya kuma 6aci zuciyar shi tayi zafi jijiyoyin kanshi duk suka mimmik'e kawai yasa kai ya fita ba tare da kowa ya lura ba. 

Abba ya d'ago ta ya mik'ar da ita tsaye sannan ya maida kallonshi wajan Dr gadanya yace, 

"Dr ina ganin tafiya zamu yi kawai akwai matsalolin da nake son warware su a gida idan mun koma." 

A take dr gadanya ya rubutawa Balqees takardar sallama, sosai suka yi ban kwana tare da yi musu fatan alkairi suka fita. Abba da Balqees ne kawai suka shiga mota domin shi Sultan a mashin yazo, sai faman dan k'arawa Balqees harara yake yi amma sam tak'i kallonshi kamar tasan a kule yake da ita. 

Gidan hajiya kaka suka sauka suna zuwa Balqees ta d'akko kayanta wanda dama ta shiryasu tun lokacin da zata tafi ethopoeia ta fito zuwa pallour hajiya kaka ta kalle cikin mamaki dan a tunaninta dawo da ita aka yi ta kasa yin shiru tace. 

"Ke! Wai ina kike shirin tafiya ne.?!" 

"Yarinyata ina zuwa haka daga sallamo ki.?!" 

Tace "Toh ni dai abba gidan ka zani wallahi bazan iya zama a nan ba tsoro nakeji." 

Hajiya kaka ta rik'e ha6arta tare da cewa, 

"Ehhhyeeee! lallai yarinya ni zaki gudurwa sabida Allah? Kiyi zamanki anan ina ganinki ina jin dad'i kinga mun saba dake." 

Kai ta girgiza mata tare da kallon abba jin ko zaice wani abun sai taga kawai murmushi yake yi, tura trolley bag d'in tayi tafita zuwa parking lot bata koma ba ta zauna tana jiran fitowar abban. Shirun da yaji ne bata dawo ciki ba ya sashi yiwa hajiya sallama ya fita hajiya kaka ta rik'e ha6a tare da cewa. 

"Kyaci kaniyar ki nasan k'ila gobe na ganki dan ba jituwa kuke da matar gidan ba mai shegen iyayin tsiya." 

Yana zuwa ya ganta jin gine a jijin motar ta kwantar da kanta a saman yace mata ta shiga su tafi. Tafiyar mintuna ashirin da biyar ne ya kaisu suna zuwa suka ga mashin d'in Sultan da alama yana gidan Balqees ta saci kallon side d'in kafin tabi bayan abba mai wankin motocin gidan ne ya biyo su da jakar kayan, suna shiga suka ga Umma zaune ita da kanwarta Umma ta had'e rai ganin jakar Balqees abba kuma suka gaisa da aunty  Rabi'a sannan ya kalli Umman Sultan yace. 

"Hajiya ga mara lafiya nan na kawo miki ita amana kafin nan da wasu 'yan kwanaki." 

Da kyar ta tattaro nutsuwarta sannan ta kalli mai gidan nata cikin yak'e tace. 

"Toh ba damuwa ta shiga d'aki kafin nazo, ke Bilkisu shiga daga ciki." 

Jiki a sanyaye Balqees ta wuce d'aki Umma ta kalli kanwarta wadda ta zuba musu ido Umman tace. 

"Wallahi sam bana son yarinyar nan tana shishigewa Ahmad bare har su fara yin soyayya, yarinyar tayi kankanta sam bata da girma sai ayi tunanin 'yarshi ce wallahi hankalina yafi kwanciya akan Nadiya sun fiyin dai-dai." 

"Karki damu kinsan wani sa'in shakuwa takan sanya a dinga yin wasu abubuwan tamkar soyayya, kuma kema idan banda abinki da ace soyayya suke yi ai da baxai kawo batun Nadiya ba, amma ki duba yadda yake son Nadiya duk sanda yaje gida na zancen shi Nadiya sai dai kawai yana nuna tausayin shi a gurin Balqees ne sabida maraicinta kuma da alama Ahmad zai iya *Tattalin mace* a duk inda ya samu kanshi, dan haka kibar sanyawa ranki wani abun ita kanta yarinyar ki dena nuna mata kyara." 

Da haka suka dinga tattauna zancen kafin aunty Rabi'a ta tafi. 

**** 

Tunda Balqees ta koma gidan Sultan be bari sun had'uba sabida ya kasa gano dalillin da yasa tayi mai wannan abun a wajan abba domin har ya sameshi da zancen wai ko yana da burin auranta yace "a'a." Dan har ga Allah shi baya jin sonta da aure Nadiya itace za6inshi kuma burinshi. Balqees kuwa duk ta damu domin ta rasa yadda zata yi gashi ta dawo gidan ne dan ta ringa ganinshi akai-akai ba tare da shamaki ba amma abin mamaki shi d'in yak'i barin hakan ta faru, Umma kuwa alhamdulillahi tun sanda kanwarta aunty Rabi ta haska mata shikenan ta rage tsangwamar Balqees dan yanzu sukan zauna suyi hira Balqees tayi ta murna tana jin dad'i matsalarta d'aya yanzu shine rashin ganin Sultan gashi har tayi kwanaki biyar a gidan. 

Kasan cewar yau karshen mako wato asabar Balqees tayi alwashin sai taganshi ko ta wani irin hali ne domin bak'aramin wahala ta shaba na rashin ganin Sultan ba. Tunda tayi sallar asubah ta fito daga d'akin da take kwana, a hankali ta fito harabar gidan ta sud'ad'a side d'in Sultan cikin sa'a kuwa tana murd'ar handle taji k'ofar ya bud'e ta shiga da sauri sannan ta mayar ta rufe. Dind'im cikin parlor'n ta samu ta fara laluban hanya dan zuwa bedroom d'in shi sai faman cin karo take yi da kujeru har ta k'arasa wajan bedroom d'in taji alamun bud'e d'akin k'irjinta ya buga dimm cikin sauri tayi bayan kujera har tana buge gushinta. 

Haske taga ya gauraye parlar'n tayi saurin zaro ido jiyo shi tayi yana murza mukulli a jikin k'ofar kafin taji takunshi ya shiga d'akin baccin shi. Yana shiga itama tayi saurin bin bayan shi lokacin tagan shi ya cire jallabiyar jikinshi wadda yasaka yaje yayi sallah, daga shi sai boxer da vest tana kallon shi ya fad'a kan gado tare da furta. 

"Washhhhh Allah." 

Pillow ya janyo ya kwanta akai ruf da ciki tare da janyo laptop d'inshi ya bud'e tare da kunnata. A hankali Balqees ta shiga d'akin ta tsaya a bayanshi tana shashek'ar kuka cikin razana yayi saurin waigowa ga mamakin shi ya ganta a tsaye cikin tashin hankali ya mik'e tsaye yana mamakin ta inda ta shigo, baki na rawa ya furta....

_#Innocent Balqees_

    
    *"B*aby....!" 

Ya fad'a yana kokarin sanya jallabiyar shi. K'arasawa yayi gabanta jikin tsananin rud'ani dan baya kaunar a ganta anan da asubar fari,jan hannunta yayi suka koma parlor yaje ya bud'e k'ofar d'akin gabaki d'ayanta harda d'aga labule dan yasan idan Umma tasan tana side d'inshi sai ta biyo su. 

Komawa yayi gurinta tare da kamo hannunta suka zauna kan kujera fuskar shi a d'an had'e ya kalleta itama shi take kallo yace. 

"Baby meya faru? Sannan kuma ta ina kika shigo d'akin nan bayan na rufeshi...?" 

Kuka kawai take ba tare da tayi mai magana ba,sake tambayar yayi ta kuma yin shiru ganin haka yasa shi mik'ewa zai koma cikin d'aki tayi saurin kamo hannunshi tare da mik'ewa tsaye tana goge kwallar fuskarta tana faman ajiyar zuciya tace mai. 

"Yaya Zulkallain kayi hakuri ba zuwa nayi na takura maka ba,alfarma nazo nema a gurinka dan Allah." 

A hankali ya juyo tare da dafa kafad'unta yana lumshe idanuwa tamkar mejin bacci ya zaunar da ita akan kujerar da ta tashi shima ya zauna yana rik'e da hannunta yace. 

"Me kike so a gurina baby?!" 

Tana faman sauke ajiyar zuciya tace mai. 

"Yaya Sultan ina son kayi min alfara kayi min viser ina san komawa dangin Ummi na." 

Cikin tsananin mamaki yake kallonta dan sam be ta6a kawowa cewar abinda zata fad'a ba kenan. Sake matse hannunta yayi a cikin nashi ta rintsa ido siririyar kwallah ta fito ta ziraro kuncinta jikin shi yayi sanyi yaji duk ya tsani kanshi domin yasan shine silar da yasa tace zata koma dangin mahaifiyarta,cikin sanyin murya yace. 

"Wai kina nufin ki koma gabaki d'aya?!" 

Balqees ta kuma fashewa da kuka tare da fad'in. 

"Eh Yaya Sultan, a can zanyi karatuna." 

"A'ah baby bazai yiyu ba sam, ina can ina k'ok'arin yi miki registration sannan yanzu kizo kice min wai zaki koma ethopoeia. Wai ma sabida da me kike son komawa gabaki d'aya kin gaji da mune?!" 

Ya fad'a cikin kakkausar murya yana karantar yanayinta. Balqees tayi murmushin takaici tare da kawar da kai gefe tace. 

"Ban gaji daku ba Yaya Sultan kune kuka gaji dani, dan haka zan bar k'asar gabaki d'aya sabida ku dena ganina na dinga yi muku zuwan da zaku dinga marmarina, wato inzo in koma." 

"Bazai yiyu ba." 

Taji ya fad'a tare da mik'ewa tsaye ya kalleta sai yaga ta had'e rai ya sassauta fuskar shi yace mata. 

"Meh yasa kika yiwa abba karya a asibiti rannan?!" 

Tashi tsaye itwma tayi ta gyara zaman hijjab d'inta sannan tace. 

"Na fad'a ne kawai domin na 6atawa Yaya Yusif rai kuma alhamdulillah domin kuwa ina fad'a yabar d'akin sai dai kai kuma daga lokacin na dena samun duk wata kulawa daga gareka duk da cewar sabida kai na dawo gidan nan amma ka dinga k'ok'arin kaucewa ganina hakan yasa ni zuwa gurinka yau dan in nemi alfarmarka,idan kuma bazan samu ba sai nayiwa aunty Fatima waya susan yadda zasu turo a tafi dani.wallahi na gaji kuma insha Allahu bazan kuma yin sati cikakke a k'asar nan ba." 

Story continues below


Kallon mamaki yayi mata tare da shafa quarter million d'in fuskar shi wanda yasha gyara, sake kallonta yayi cikin sauke ajiyar zuciya sannan tace. 

"Okk karki damu insha Allahu zan miki abinda kike so shike nan?!" 

Balqees ta d'aga mai kai sannan ya nuna mata k'ofar fita dan har lokacin zuciyar shi bata dena bugawa ba sabida kar Umman shi ta shigo ta gansu. 

Sai da aka gama komai ranar da zata tafi abba da Sultan suka shirya tafiya da ita airport, gidan kaka suka je sai a sannan suka sanar mata Ai kuwa sunsha fad'a su dukan su nan suka dinga bata hakuri kafin tayi mata fatan alkairi tare da dawowa lafiya domin Sultan yace wata d'aya zata yi ta dawo ya isheta ta gaida kowa nacan. Suna fita babu inda suka tsaya sai filin jirgi, suna zaune har aka gama komai ta wuce inda zasu shiga jirgi tana hawaye shima Sultan jikinshi duk yayi sanyi sai yaji ina ma tare zasu tafi amma ba dama domin yana da lectures da yawa da zaiyi daga nan suka fito suka wuce gida. 

*****
Bayan sati d'aya da tafiyar Balqees aka sanya ranar auran Sultan da Nadiya wata biyar cikin tsananin farin ciki yake dan haka da dare yana kwance a parlor'n shi suna chatting da Nadiya sai yaga Balqees ta hau online. Murmushi yayi dan dama yana san ya kirata ya gaya mata albishir, itace ta fara mai sallama ya amsa tare da tambayar ta mutanen gidan tace. 

"Yaya duk suna nan lafiya, ina hajiya kaka?!" 

"Bata nan taje umara." 

Ya bata amsa ta turo mai d'an hotan nan mai zaro ido amalar mamaki mai tsanani kafin tace. 

"Lallai hajiya kaka shine ba ko sanarwa?" 

Sultan ya tura mata murmushi kafin yace, 

"Cewa tayi wai ramawa zata yi kar wanda ya fad'a miki." 

Balqees ta turo mai dariya wanda a zahirima yi takeyi sosai sabida maganar tasanya ta dariya, ganin tayi dariya ne yasa shi ce mata. 

"Baba albishirinki..?" 

"Goro fari kyal Yaya." 

Ta turo mai yayi dariya duk da cewar wani 6arin na zuciyar shi yana hanashi sanar mata, amma kuma murna da zumud'i sun rinjayi hanawar dan haka yace mata. 

"Zaku sha biki nan da wata hud'u da 'yan satittika." 

"Yeeeee....!" 

Ta tura mai tare da sanya 'yar macen nan mai rawa sannan ta tambaye shi. 

"Yaya bikin wa zamu sha?!" 

A hankali tamkar suna kallon juna jikin karyar da kai ta tura mata. 

"Me and my beautiful wife Nadiya." 

Dam-daram-dam,k'irjin Balqees ya buga da k'arfi jikinta ya hau rawa tayi kuru tana kallon inda yasa beautiful wife d'in sai hawaye shaaaa ta kasa bayya na masa yadda taji koda k'arya take yi.ganin bata bashi reply ba gashi tana ganinta online yasa shi cewa. 

"Baby baza ki murna bane?!" 

'Dif yaga ta sauka yayi saurin kiranta ga mamakin shi sai yaji naurar computer na sanar dashi cewar a kashe take. Ba tare da ya kawo komai a ranshi ba yayi tunanin ko bata da chaji daga nan suka ci gaba da hirar su shida Nadiya har tsawon wani lokaci. 

Ita kuwa Balqees tana jin ya fad'i haka ta fara neman jinta hakan yasa ta kashe wayar tare da juyawa kan katifa ta fashe da kuka mai tsanani Aamanee dake gefenta tana kallo a you tub ta k'arasa kusa da ita tare da tambayar. 

Story continues below


"Lafiya Balqees what happens?!" 

Balqees ta kasa magana sai ma komawa da tayi jikin Aamanee tana ci gaba dayin kukan. Kyaleta tayi har sai da tayi mai isarta sannan cikin dabara da nuna tsantsar soyayya da yadda Aamanee ta tambaye ta abinda yake damun ta. 

Kwanciya tayi akan k'afarta Aamanee ta girmeta sosai domin zatayi shekaru Ashirin da hudu 'yace a wajan Momy Sa'adatu wato yayar mahaifiyar Balqees tana karatu har lokacin ba tayi aure ba. Balqees ta numfasa tare da share hawayen fuskarta ta fara bawa Aamanee labari. 

"Yayya Aamanee ina son shi so irinna aure wanda idan bashi na aura ba zan iya mutuwa a yadda nake jin zuciyata akan shi." 

Aamanee ta zaro idanuwa hannunta a saman gashin Balqees tana warware mata inda ya harhad'e, da kyar ta had'iyi yawu kafin tace. 

"Balqees kina nufin kice min yanzu haka you're in love with someone..?!" 

Balqees ta d'aga mata kai alamar "Eh."sannan ta kuma fashewa da wani irin kuka mai ban tausayi.cikin d'imuwa Aamanee tace. 

"Toh meye na kukan hakan, ko cewa yayi bazai aure ki ba?!" 

Nan ma Balqees ta girgiza mata kai alamar "a'ah." Aamanee ta kuma cika da mamaki sannan ta d'ago da Balqees daga jikinta,kallonta tayi cikin ido sannan tace. 

"Toh waye shi? Kuma me yasa kike kuka bayan be ce miki bazai aure ki ba?!" 

Kuma kwanciya Balqees tayi akan kafafuwan Aamanee sannan ta lumshe idanuwa tace. 

"Yayya Aamanee be san ina yi ba, idan kuma ya sani toh hak'ik'a sona ne bayayi domin nayi duk abinda zanyi na ganin ya gane inda zuciyata ta dosa amma sam yak'i sai wad'anda bana so ne suke sona harda sace ni gashi yanzu ya gaya min cewar an sanya ranar auran shi da wadda yake tsananin so kamar ranshi, yayya Aamanee ki gaya min ya zanyi?ina jin zuciya ta na tafasa kamar zata kone na shiga uku..." 

Aamanee tana jin haka ta rik'e ha6a tana faman kad'a kai alamar tsananin tausayawa,juyo da fuskar Balqees tayi ta kalleta sosai kafin tace. 

"Waye shi Balqees?!" 

Wani kukan ta saki cikin rawar Murya tace. 

"Yaya Ahmad ne ina son shi tun kafin na mallaki hankalin kaina sosai, ina son shi domin shine yake nuna min soyayya wadda tasa alkairin shi gareni da kulawar shi gareni sannan da tattalin shi gareni ya sani ban san lokacin da zazzafar kaunar shi ta shiga cikin zuciyar soyayyata ba ya zanyi...?!" 

"Innalillahi wainna'ilaihir raji'un, wannan shi ake kira da baya da kura. Balqees kin sanar dashi yadda kike jinshi ya nuna miki bayayi ne, ko kuwa hasashen kina na cewa lallai bazai aure kiba?!" 

Balqees ta mik'e zaune tare da bawa Aamanee labarin duk yadda suka yi har wasan da ta fad'a a asibiti sai da ta gaya mata sannan ta d'ora da cewa. 

"Tunda na fad'i haka be sake kulani ba har sai da naje nace mai yayi min viser zan taho nan. Yayya Aamanee Yaya Sultan be min soyayyar aure, hasalima jina yake tamkar shine ya haife ni, duk wani kallo da yake min a matsayin 'ya ne ki gaya min tayaya zai gane inda zuciyata ta nufa?wallahi tallahi na tsani Nadiya bana sonta duk itace taja min..." 

"Ta6 d'i jam! Ke yanzu Balqees akan namiji kike wannan azababban kukan? Kina son ya rainaki idan ya gano irin zazzafar soyayyar da kike yi mai...?!" 

Aamanee ta fad'a cikin takaici domin ita bata ta6a yin makamanci wannan soyayyar ba, hasalima bata gabanta sam shi yasa ta maida hankali wajan karatunta. Balqees ta kalleta sannan tace. 

"Da ace zan samu ya gane inda zuciyata ta nufa harma yaji shima yana yi min irin soyayyar wallahi dan ya rainani bazai dameni ba, bare ma nice dama a kasa dashi kuma babu abinda beyi min ba kama daga wanka, tsarki both ki gaya min meye ya rage a cikin raini? Kinga nice ma zan dinga jin nauyi ba shiba shi yasa ya kasa gano inda na nufa." 

Aamanee ta girgiza kai domin ita tama rasa ta cewa. Numfasawa tayi kafin tace. 

"Toh ki ciresa a cikin ranki kiyi watsi dashi zakiji kin dena jin abinda kike ji a game dashi." 

Wani kallo Balqees ta watsawa Aamane cikin takaici tace. 

"Yayya Aamane waye yace miki ina son na rasa jin soyayya Yaya Sultan koda dai-dai da second d'aya? Tof ki tufar da yawun bakinki domin hakan ba me yiyuwa bane da soyayyar shi na rayu a cikin zuciya ta, mafita nake son ki bani please.." 

Aamanee ta ta6e baki gani take tamkar Balqees ta samu ta6in kwakwalwa dan haka cikin rashin damuwa tace mata. 

"Kawai ki share shi zai dawo gare soon." 

Wani mugun takaici ya kuma rufe Balqees kawai ta gyara kwanciyar ta tabar yayya Aamanee a zaune dan taga alamar bata san meye so ba, ta rintsa ido amma abin mamaki Sultan take gani da Nadiya cikin farin ciki mai tsananin gaske tayi saurin bud'e idanuwan ta tare da cusa fuskarta cikin pillow tana kuka... 

**** 

Washe gari tunda asuba Sultan ya dinga kiran Balqees amma baya shiga ya fara tunanin ko lafiya sai ya tura mata guntun text message. 

_"Idan kin kunna wayarki kiyi min plashing."_ 

Koda ta kunna ta gani k'in yi mai tayi taci gaba da da harkokinta duk da cewar ba haka ne a cikin zuciyarta ba. 

Sosai Sultan ya dukufa akan gyaran gidanshi wanda dama ana tayi a hankali yanzu kama da zafi-zafi ake gudanar dashi dan baya son abubuwa suzo suyi mai yawa. 

Kwanaki na tafiya yau gashi har Balqees tayi kwanaki d'aya-y'aya har 28 ya kama sauran kwanaki uku ta koma Nigeria. Ganin su aunty Fateema dasu Aamanee su Afrah zasu tafi gurin kakan ninsu wato mahaifan su Umminta a can asibin madina yasa tasanya rigima da kuka sai anje da ita gashi dubiya zasu je dan jinya aka kaisu hakan yasa uncle Adam yayan su Ummi ya sa aka tafi da ita ko gida Nigeria ba'a sanar dasu ba. 

Suna tafiya da kwana d'aya Balqees ta yiwa Sultan waya, yana d'agawa yace. 

"Uhmm..." 

Sabida besan number d'in ba, tayi dariya sannan tace. 

"Yaya nice fah." 

Da mamaki yace mata, 

"Ke! Wannan number'n fah...?!" 

"Tawa ce nan." 

"Eh naji taki ce, but naga ne number Saudi shi yasa na tambaya. Wait wai ma kin gama shirn dawowa ko kuwa kin san dai jibi zaki taho ko?!" 

Ta6e baki tayi tamkar yana kallonta tace. 

"No bana ethopoeia yanzu haka ina jidda." 

"What..?!" 

Ya fad'a da k'arfi har sai da ta d'auke wayan daga jikin kunnanta, cikin fad'a ya fara mata magana. 

"Yanzu dan rashin mutunci zaku yi tafiya shine bazaki bugo waya ki sanar dani ba sai da kukaje sannan zaki kira ni? Kin girma har kin fara yin abun kanki ko? Good..." 

Ya fad'a tare da kashe kiran.tsaki ya zab ga tare da d'aukan key d'in mashin d'in shi ya wuce gidan da yake ginawa ranshi a 6ace. 

Tun daga lokacin be sake d'aukar kiranta ba bare shi ya buga duk da zuciyar shi bata yi mai dad'i amma ya share dan yana son nuna manata kuskurenta akan abinda take yi mai. 

Balqees kam duk ta damu har rama tayi tsabar rashin ku'in kula da Sultan yake mata, yau gashi har sun kuma dawowa ethopoeia ta share kusan watanni biyu akai wanda ya Kama sauran bikin su Sultan da Nadiya  wata d'aya da sati d'aya amma bata dawo ba dan suma 'yan uwa sunji dad'in ganinta an saba hakan yasa suka hanata dawowa a cewar Momy Sa'adatu sai zasu je biki sannan zata koma, tayi kukan har ta gaji amma ba'a maida ita Nigeria ba. 

Ana sauran sati d'aya a fara programs na bikin suka taho ita dasu Aamanee su Yaya Ahmad dasu Afrah duk jikinta yayi sanyi har tsoron ma had'uwa take yi da Sultan Ahmad d'in.sai da suka fara zuwa gidan 'yan uwan baban su Aamanee suka huta sannan aka kaisu gidan su Sultan inda aketa shirye-shiryan biki mutane har an fara cika gidan. 

Su Balqees na shiga sunyi parking motar su shima Sultan ya shigo yayi parking d'in mashin d'in shi hannunshi rik'e da wata medium d'in trolley be kalli ko'ina ba ya wuce side d'inshi dan da alama ma baya son mutane suyi mai magana, taku d'aya biyu yayi yaji an kira sunanshi, sunan da duk duniya mutum d'aya ce ke kiranshi dashi tace. 

"Yaya Zulkallain...!" 

Cak ya tsaya tare da saurin.....

    
    *C*ak ya tsaya tare da saurin rintsa idonshi, be waigo ba yayi tafiyar shi har wani sauri-sauri yake yi tayi saurin bin bayan shi yayin da ta bar su Yayya Aamanee a tsaye duk suna kallonsu har suka shiga side d'in shi, yayya Aamanee ta ta6a baki cike dajin haushin Balqees taja su Afrah suka shiga cikin parlor'n Umma. 

Yana sanya k'afa cikin parlor'n shi itama ta shiga, jin tana binshi ne ya sanyashi tsayawa tare da juyowa ya watsa mata wani gigitaccan kallo wanda yasa a take Balqees ta saki kuka ganin lallai yayan nata fushi yake da ita. 

  Da sauri ta yardar da handbag d'inta ta k'arasa kusa dashi tare da marairaice fuska cikin kukan ta fad'a jikinshi tare da kankameshi a hankali ta ce. 

"I love you Yaya,I really love you with whole my life." 

Zareta yayi daga jikinshi ya kuma kallonta fuskarshi duk a 6ace duk da cewar a zuciyar shi yaji dad'in dawowarta amma haushin wofintar dashin da take yi musamman ma akan sha'anin rayuwarta ya ta6e baki tare da rik'e trolley d'inshi yace. 

"Love?! Uhmm which kind of love baby? Ni zaki yaudara kizo ki nuna min cewar Ai har yanzu kina sona kamar da? No!ni yanzu ina da yara kuma sun maye gurbinki wato Fateema da Kairat so ke sai ki koma jidda ko ethopoeia inda suka fi kula dake da nuna miki soyayya kamar papa da Ummi." 

Yana kaiwa nan ya d'aga mata girarshi tare da juyawa ya shige cikin d'akin shi. Zaman dirshin tayi a gurin ganin yadda yayi mata, wato Yaya Sultan ya k'aro wulak'anci ita yake yiwa haka yanzu?yayi k'iba yayi fresh dashi kai da ka ganshi kasan ango ne domin gigin angwanci na walagigi dashi tayi da6ar a k'asa tana kuka gwanin ban tausayi. 

Ya jima a bedroom kafin ya fito cikin shirinshi sai zuba k'amshi yak'e yi, sanye yake cikin light green d'in shadda tayi mai masifar kyau. K'arara mamaki ya bayyana a saman fuskar shi ganinta kwance a gurin har tayi bacci, k'arasawa yayi kusa da ita ya tsugunna tare da sanya hanna ya bud'e fuskarta wadda ta rufe da mayafin jikinta. 

Kanta ya shafa a hankali sannan ya shiga tashinta ta mik'e a razane tana furta. 

"Dan Allah kayi hakuri Yaya." 

"Oh my God! Ke baby lafiyanki kuwa?!" 

Batare da tayi magana ba ta mik'e zaune sosai tana murza ido yace mata, 

"Oya tashi kije side d'in Umma kiyi wanka kici abinci tukuna." 

A hankali ta kalleshi sai taji kirjinta ya buga tayi saurin yin k'asa da kai tace, 

"Toh Yaya ka hakura da duk abinda nayi maka?!" 

Sultan yayi murmushi tare da mik'ewa tsaye yace. 

"Eh yanzu dai kije ki shirya anjima idan na dawo kizo ki k'arbi kayanki na fitar biki." 

Bata ce mai komai ba ta mik'e suka fito tare lokacin Ahmad wanda suka zo tare yana zaune a can rumfar da Sultan yake zama dan shak'atawa ya kallesu tare da ta6e baki yana kur6ar drink. 

Side d'in Umma ta shiga shi kuma ya shiga motar Umman wanda yasa aka wanke ta ya wuce gurin Nadiya domin idanuwan shi sun k'agu su ganta kwanaki biyar kenan be sanyata cikin idanunshi ba. 

**** 

Tun ranar alhamis aka fara event, kowa na ta faman shiryawa amma banda Balqees wadda ke kwance tana kallon su Aamanee sai shiri ake yi ta kalleta tana sanya janbaki tace. 

Story continues below


"Ke wai bazaki tashirya ba sai mun gama kike son mu jiraki?!" 

Aamanee ta fad'a Fateema ta matsa kusa da ita tare da d'ago ta tana cewa. 

"Haba Balqees wai me kike nufi ne." 

"Kuje kawai baza ni ba." 

Ta fad'a tana yatsina fuska, Aamanee ta kalleta cikin tsananin mamaki gabaki d'ayan su sunyi masifar yin kyau cikin material d'in coffee color d head yellow, kasan cewar sai faman horn ake musu yasa suka fita suka barta sai mamakinta suke yi. 

Wani katafaran guri suka kama wanda sai kana da dattijai biyun abuja zaka iya tsararshi. K'arfe 8:00pm duk an hallara ango da amarya sunyi bala'in yin kyau sosai suka yi matching idan ka gansu sai fara'a suke yi abin gwanin ban sha'awa, sai hotuna aka yi kafin a barsu suje inda aka tanadar musu suka zauna Sultan na mak'ale da hannun Nadiya ita kuma kunya sai faman zazzamewa take yi amma ya kafa ya tsare da alama kuma zai raka. 

'Yan group d'insu Balqees ya hango sun nufoshi kowacce hannunta rik'e da waya,suna zuwa ya kalli Fateema kanwar Yusif cikin kunnanta ya sanya bakinshi yana tambayar ta. 

"Ina baby take?!" 

"Yaya Sultan tana gida, cewa tayi baza ta zo ba." 

Da mamaki ya kalli Fateema ta matsa kusa dashi dan yin abinda ya kaita wato hoto sannan ta wuce gurin su Bilki 'yar gidan Adda Aisha sukaje suka zauna. 

Wayar shi ya zaro nan ya fara k'ok'arin kiran Balqees d'i, tana kwance ita kad'ai a d'aki sai faman kuka take yi babu wanda yasan tana ciki.k'arar wayarta ne ya tsayar da kukan ta sanya hannu ta d'auka, ganin shine yake kiranta yasa ta ajiye har sai da taji bazata iya k'in d'auka ba ta kara a kunne ba tare da tayi magana ba. 

"Ki shirya yanzun nan zansa Yazid yaxo ya d'aukeki bana son gaddama." 

Yana kaiwa nan ya kashe wayar, kuka ta kuma fashewa dashi shi kuma ya nemi Yazid abokinshi wanda yake son Balqees d'in yace dan Allah yaje ya d'auko ta a gida, Yazid kuwa yaji dad'i dan tun d'azu yake raba idanuwa yana nemanta be ganta ba ashe tana gida. 

Yazid na zuwa ya kirata da wayar Sultan domin ita ya bashi a memakwan number'n ta. D'auka tayi ta kara a kunne sai taji muryar Yazid  yace mata. 

"Madam na zo." 

Ba tare da tace komai ba ta sauke wayar sannan ta mik'e daga kwancan da take fuska kawai ta wanke sannan ta zira zurmeman hijjab a saman sleeping gowan d'in jikinta wando da riga ta sanya hill sheo d'inta ta d'auki wayarta sannan ta fito. 

Da Umma suka ci karo ta kalleta da mamaki ganinta a gida kuma babu kwalliya Umma tace mata, 

"Ke kuma daga ina haka, ko daman bakije ba?!" 

Balqees duk ta daburce ta fara muzurai bakinta ya gaza cewar komai sai faman kif-kiftan ido take yi, ganin amsa Umma ke jira yasa ta cewa. 

"Umma dawowa nayi jikina ne ya 6aci shine nazo na gyara komawa zanyi yanzu." 

"Ok tohm idan kinje ki samu yayanki kice mai idan an tashi ina nemanshi karya manta." 

"Toh Umma zan gaya mai." 

Ta fad'a tare da wucewa tana tafiya tamkar kasar da kwai ya fashewa a ciki. A parking space taga mota duk da bata san ko ta waye ba hakan ya tabbatar mata da cewar wanda yazo d'aukar ta ne, yana kallonta yasha mamaki ganin shigar jikinta tamkar ba arab night zata ba sai dai beyi magana ba har ta kwankwas mai glass ya zuge tare da bud'e mata k'ofar motar ta shiga ba tare da ta kalleshi ba ta zauna tare da gaida shi a ciki-ciki. 

Tunda suka fara tafiya Yazid yake janta da hira amma Balqees daga eh sai a'a take mai wani sa'in ma shiru take mai duk da cewar shima bashi da surutu, har suka k'arasa babu wata babbar kalma da ta shiga tsakaninsu. Yana yin parking ya fito amma ita still tana zaune domin ji tayi zuciyar ta na tsananin bugawa musamman da ta jiyo kid'a na tashi. 

Story continues below


"Baby fito mushiga." 

Yazid ya fad'a yana kallonta ta cikin eyes glass d'inshi,k'in kallon shi tayi ta kad'a mai kai alamar a'a sannan ta kuma maida bayanta jikin kujera tare da lumshe ido tana jin zuciyarta sai tsananta bugu takeyi Yazid ya matsa kusa da ita yana rik'e da murfin kofar motar yace. 

"Dan Allah ki tashi kinga yana can yana jiran mu." 

Jin ya isheta da ban bak'i, musamman da ta tuna ba motar ubanta bace hakan yasa ta fitowa ya rufe motar sannan suka shiga cikin gurin. Ya ilahi suna shiga suka yi ido hudu da Sultan domin idanunshi kyar akan kofar yana jiran shigowar su, tana hangosu kirjinta ya buga da k'arfi sabida wani azababben kyau da dacewa da taga sunyi gashi sun manne da juna ai sai kawai tayi waje da gudu tana hawaye. 

Sultan na ganinta yasan akwai matsala domin duk ankon da akayi yayi mata shi harda extra kaya sabbabbi yayi mata amma yasha mamaki daya ganta sanye cikin uban hijjab tamkar wanda ta dawo daga islamiyar dare. A hankali yayiwa Nadiya magana a kunne, ba tare da ta kawo komai ba ta d'aga kai shi kuma ya mik'e yana k'ok'arin fita mutane na faman tsayar dashi yana d'aga musu hannu alamar yana zuwa a haka har ya fita harabar wajan yana nemansu dan yaga Yazid ma yabi bayanta lokacin da ta fito. 

A can wajan wata mota ya gansu Balqees ta kifa kanta jikin motar da alama kuka take yayi azamar k'arasawa wajan aikuwa yaji kuka harda shashek'a ya kalli Yazid cikin mamaki Yazid ya d'aga mai kafad'a alamar besan me aka yi mata ba Sultan ya nuna mai agogon hannunshi dake ta faman walwali da shek'i yayi mai alamar ya bashi lokaci Yazid ya koma ciki shi kuma ta jata zuwa motar Yazid d'in suka shiga bayan motar dukan su. 

Kallonta yayi cikin hasken fitilar wayar shi wadda ya kar6a a hannun Yazid, gani yayi tana faman rik'e ciki tare da cizon le6enta tana mammatsa ido  da alama nuni take mai da cewar akwai abinda yake damunta,cikin tattausar murya sai faman zuba k'amshi yake wanda yake sanya zuciyar Balqees kara dulmiyawa cikin azababban son shi yace mata. 

"Baby menene hakan? K'in zuwa biki na gudu! Shin me yake damunki ne da har sai nace kizo sannan zaki zo....?!" 

Kwalla yaji na sauka akan saman bayan hannunshi yayi saurin d'ago kanta idanunta a lumshe hawaye na bin kyakyawar fuskarta ya rungumuta zuwa jikinshi yana bubbuga bayanta alamar lallashi, ai kamar jiran hakan take sai kawai ta saki kuka mai tsananin gaske wanda be hanata yi ba har sai da suka d'auki tsawon lokaci a haka sannan cikin sanyin murya yace. 

"Baby meh yake damunki..?!" 

"Ba komai Yaya ciki nane kawai yake ciyo..." 

"Subhanallah baby tun yaushe ne? Kin sha magani?!" 

Kai ta girgiza mai alamar "Eh." Sannan ta kuma narkewa a jikinshi yace mata. 

"Toh har yanzu yana miki ciwon?!" 

Rasa me zata ce mai tayi karta ce ya dena yace su shiga ciki dan abinda bata kauna kenan, na biyu kuma karta ce a'a yace zai barta ita kad'ai a motar yace ta zauna su fito. Jin bata ce komai ba yasa shi cewa. 

"Bari na kira Yazid ya mayar dake gida ki kwanta, idan an tashi daga nan nakai Nadiya gida zanzo gidan kinji ko?!" 

Cikin karyar da kai tace mai. 

"Yaya Sultan ka kaini da kanka wallahi wancan ya fiya surutu kuma kaina ciwo yake yi idan ana hayaniya." 

"Oh Yazid kenan toh ai inajin dan kece ya dinga surutun amma bashi da magana sosai kece kika ciri tuta, bari wannan karan zance karya takura miki da magana." 

Da sauri Balqees tace. 

"A'ah Yaya idan baxaka maidani ba ka bari kawai zan hau napep na koma da kaina." 

"No kwanta bari nayi sauri na kaiki kar ayi ta jira na." 

Yana fad'a ya fita daga bayan ya koma drive seat ya zauna sannan yaja motar suka bar gurin.farin ciki a zuciyar Balqees kamar me, yana kaita yace ta shiga ciki nan ta fara kokarin hillatar dashi amma kemudugus yace sauri yake Nadiya nacan tana jiran shi, badan Balqees taso ba ta fita q motar tana kallonshi ya koma taja tsaki cikin jin haushi kafin ta nemi guri a wajan ta zauna dan kar su had'u da Umma. 

*** 

K'atan gida ne na gani na fad'a kai da kagani kasan anyi 6arin naira haka zalika kayan da aka zubawa amarya qarshe ne domin idan aka yi musu kud'i zasu iya siyan wani gidan irinshi harda canji. Anyi shagalukuwa kala-kala kowane 6angare yayi bajinta musamman 6angaran amarya Nadiya domin sune masu mace kuma sunfi su Sultan komai babu abinda zai nuna mata sai dai shi yayi zurfi a ilimi dan haka ya fita sanin wasu abubuwan tunda shi namiji ne. 

Qarfe 11:00am aka d'aura auran Ahmad sultan Abdullah da Amaryarsa Nadiya Nassurddin akan sadaki dubu d'ari lakadan kuma dubban mutane suka shaida wanda a lokacin Balqees na can bayan gida inda baza'a ta6a sanin akwai mutum a gurin ba tana faman kuka tamkar ranta zai fita. 

Tana nan zaune sama-sama take jiyo muryar mutane anata sanya alkairi a cikin auran alamar an dawo daga d'aurawa. ji tayi an kamo hannunta tayi saurin kallon gurin mamakinta k'arara ganin hajiya kaka ce tayi saurin saka bayan hannunta tana share hawayan fuskarta. 

Hannunta hajiya kaka ta kama suka wuce motar Yaya I.b  yana ciki a zaune ya fita dasu, gidan hajiyan ya mai dasu sannan ya koma wajan reception. Zama suka yi a cikin uwar d'akin hajiya kaka ta kalleta. 

"Tun ba yau ba na gano cewar kina son Muhammadu amma kin gaza fad'a ko bayyanawa sai faman 6oye-6oye kikeyi, har tambayar ki nayi ko akwai wanda kike so kika ce min sai tayi wari zaki gaya min, gashi kuwa sai da tafi wari wari naji kuma nagani domin yau na gazgata hakan." 

Kuka Balqees ta kuma sanyawa tana jikin hajiya kaka domin bata da ta cewa komai ya k'are mata cikin damuwa hajiya kaka tace. 

"Kiyi hakuri baby a wannan ga6ar banida ta cewa, a duk cikin jikokina ku biyu ne bana iya 6oye kaunarku a duk inda nake, baby kiyi hakuri a yanzu bazan iya yiwa Muhammad maganarki ba domin idan nayi haka na faranta miki shi kuma zan 6ak'anta mishi musamman a lokacin da yanzu yafi kowa jin farin ciki na ranar auran shi, 

Muhammad yana son Nadiyatu matuk'a gaya,da ace baya sonta zan iya yi mai magana amma yanzu kiyi hakuri har muga yadda zamu 6ullowa al'amarin, nayi alkawarin indaivina da rai bazan yi miki auran son raina ba." 

Dirar mota suka jiyo kafin suji muryar Sultan yana k'ok'arin shigowa ciki. Da azama Balqees tayi saurin kwanciya tamkar me bacci dan bata son gaya alamun tayi kuka, ya kalli kaka dake faman gyan-gyad'i daga zaune yayi murmushi tare da shiga ciki yana fad'in......

    
    *"W*ai shin hajiya me yake damun baby ne? tun fa da aka fara bikin nan take faman nuna rashin lafiya, yau tace ciki,gobe mura,jibi kai toh yanzu kuma ta wani taho nan gidan me yake damunta ne..?!" 

Sultan ya fad'a yana matsa yatsun k'afar Balqees dake kwance sai wani faman lumshe idanuwa take yi alamar tanajin dad'in ja mata yatsun da yake yi. 

"Kaji min yaro,toh mutum yanajin ciwo bazai fad'a ba sai yayi shiru? yanzu ma bata jin dad'i shine ta taho nan sabida hayaniyar mutane." 

"Amma dai hajiya kaka bikina guda ace kowa na daurewa yayi nishad'i yayi farin ciki amma banda baby da nake tunanin sai tafi kowa murnar bikin.." 

Shiru hajiya kaka tayi mai ya kalli Balqees dako motsi bata yi ita a dole mai bacci yace. 

"Hajiya kaka zuwa nayi fa takanas kiyi min fad'a kinga yanzu nima na shiga sahun manya." 

Hajiya kaka tayi murmushin jin dad'i sannan tace mai. 

"Yaron kirki ai kai ba sai anyi maka fad'a ba dan bamu da haufi akan ka,Allah yayi maka albarka ya baka ikon fitar da hakkin iyalinka, nan da wani lakacin kaxo kace min ta biyu zaka k'ara har kazama jarumi kayi hud'u cacas ku rage mana 'ya'yan mu da basu da tsayayyu..!" 

Sultan ya zaro idanuwa still hannunshi na jajjan yatsun k'afar Balqees, yayi kalar tausayi tare da cewa. 

"Habba hajiya kakus ni mezai jamin k'ara wani auren? Nadiya ta isheni nasan banyi za6in banza ba insha Allahu dan gaskiya bana son mata biyu indai ba kaddara ba." 

Da sauri yaji Balqees ta janye k'afarta tare da matse su dan karma ya kuma ta6a mata yaje can ya ta6a ta Nadiya,ya d'an kalleta da alama duk cikin bacci ne sannan ya kalli hajiya kaka jin anata mai waya yace. 

"Kaka bari naje zamuje wani guri, please idan ta farka kice ta shirya za'aje d'akko amarya anjima k'arfe 8:30pm,idan sun zo nan kinyi mata nata fad'an zan sa Yazid yaxo ya d'auketa bari naje abokaina na jirana..." 

"A dawo lafiya toh Allah kuma ya bada zaman lafiya da zuria d'ayya ba." 

"Amin kaka ta I love you so much." 

Ya fad'a tare da ficewa kai da ka ganshi kasan yana cikin nishad'i,yana fita Balqees ta tashi sai faman turo baki take tana hararar hajiya kaka har Allah yasa ta ankara ta kalleta tare da cewa. 

"Ke! Ni Wannan kallon da kike minfa na meye? wai ma tsaya ni na hanashi ya aureki ko kuwa me kike nufi?na ga alamar yanzu kin fiye tonan fad'a wallahi na ba gaira babu dalillih." 

Balqees ta kuma fashewa da kuka tare da cewa, 

"Amma yanzu da kuna magana kakah zaki iya d'an fara haska mai ya fara sani amma shine harda yi mai wani addu'a." 

"Zaki tashi ki tafi can gidan bikin wallahi,abu d'aya nasan zaki fad'a dan naji haushi nayi miki abinda da kike so yanzu kice dan anga ke marainiya ce shine ake yi miki haka.toh yau ko kin fad'a bazan yi miki ba dan babu abinda zai saka ni na 6atawa Muhammadu ranar yau d'in nan a'he.." 

Tashi tayi tsaye fuuuuu ta fad'a toilet sai kuka,nan da nan jikin hajiya kaka yayi sanyi domin tasan ba'a son a sanya maraya kuka an fison kullum ya kasance cikin farin ciki da nishad'i yana dariya. 

Story continues below


Kwala mata kira ta dinga yi amma k'emudugus tak'i fitowa,ba yadda hajiya kaka ta iya dole ta rabu da ita tana yi mata fatan Allah ya yaye mata wannan soyayyar wadda bama asan tana yi ba.sai da ta jima a cikin bayin sannan ta fito idanu nan yayi jawur kanar garwashin wuta nan hajiya babba ta dinga bata hakuri tana nuna mata abinda zata jawowa kanta idan ya gano irin azababban son da take yimai,sannan ne Balqees ta sassautawa zuciyarta amma bawai ta hakura bane dan kuwa motsi yafi le6ewa. 

***** 

Qarfe 8:03pm aka kai Nadiya gidan su Sultan Umma da abba suka kar6eta tare da yi mata fad'a da addu'ar hakuri da zaman lafiya. Nadiya na cikin wata rantsatsiyar laffaya sai kuka take yi suka yi mata fatan alkairi sannan aka kaita gidan hajiya kaka. Balqees na jiyo su tayi saurin komawa d'akin da yake a matsayin nata ta kulle kanta a ciki. 

_"Na shiga uku ni Balqees ya zanyi?wannan wane irin bala'ene yake shirin faruwa da ni,Allah ka yaye min soyayyar yayana ka bani dauriyar hakuri dashi."_ 

Ta fad'a a fili tana dafe da kirjinta wanda keyi mata mugun ciwo. Tana jin sanda aka fita dai-dai lokacin kuma Sultan ya bugo mata waya tana ganin kiran amma tak'i d'auka sai faman bugo mata yake amma fir tak'i d'auka sai guntun text message yayi mata. 

_"idan kina kusa ki shirya Yazid yananan yazo zaku taho nan baby."_ 

Bata gani ba sam domin wayar ta wurga ta bayan ta. shi kuma Yazid ya gaji da zaman jira ya kira Sultan ya sanar mai cewar bata fito ba shi zai tafi, sai Sultan yayi mamaki yace gashi nan zuwa, ya hau napep yazo gidan hajiya direct ya wuce d'akin kaka tana sallah sannan bega Balqees ba ya tafi d'akin ta ya bubbuga mata. bata yi zaton shi bane dan haka da kyar ta mik'e taje ta bud'e cikin tsananin mamaki ta ganshi cikin wani rantsatsan yadi milk color me masifar kyau ta yi saurin yin baya kirjinta na bugawa da sauri da sauri ta kura mai ido shi kuma a hankali ya matsa har inda take har suna jiyo numfashin junansu Balqees ta tokare jikin wardrobe tana rintsa ido. 

Bugun zuciyarta ne ya tsananta yayi gaf da ita tare da sanya tattausan hannunshi ya d'ago da fuskarta yana kallonta cike da mamakim ganin yadda fuskarta tayi sutu-sutu cike da tashin hankali yace. 

"Baby akwai abinda yake damunki amma duk ba wad'an nan ciwoce-ciwocan da kike fad'a bane,ki gaya min meye matsalarki ko aure na da Nadiya ne baki so?idan ba kya sonta kin tanadar min wadda kike son na aura ne..?!" 

Hawaye suka sake zubo mata sai yayi k'asa kan gwaiyoyinshi sannan ya janyota k'irjinshi ya rungometa ai da sauri ta shige tana kuma tsananta kukanta son shi da kaunar shi suka kuma narkuwa a zuciyarta.sun dad'e a haka kafin ya d'ago yana kallon fuskarta yace, 

"Meye matsalar ki baby ne eyi?!" 

"Ba komai Yaya Sultan." 

"Akwai komai baby ki sanar dani bana son wannan yanayin da kika d'aukarwa kanki,ni d'an uwanki ne meson farin cikin ki ina son a duk sanda hawayanki suke zuba na zamo me share miki su dan haka sanar dani abinda yake damunki tun fara bikin nan da kuka zo." 

Share hawayanta tayi tana neman abinda zata fad'a mai a cikin zuciyar ta,ganin babu ne yasa tace mai. 

"Yaya ba komai fa ka tashi ka tafi kaga dare na kuma yi." 

"Zan tafi amma harda ke kije ki gano gida kamar yadda kowa yaje yau, kafin nan da wani satin ki tattara kayanki ki koma can gurin mu." 

_"Wato lokacin sun d'an soye me yasa bazai ce ta koma yau ba sai yace wani satin toh bama zata koma ba gara tabi su Aamanee su koma ethopoeia tare."_ 

Ta fad'a cikin ranta shi kuma sai faman kallonta yake yi sam ya kasa gano meye matsalarta ya mik'e tare da d'agota sanye take cikin riga doguwa dai-dai ita ta roba ce hannun d'an siriri tayi mata matuk'ar kyau kirjin nan yayi d'as-d'as a tsai-tsaye suke yace mata. 

Story continues below


"Oya jeki sake kaya ina jiranki a parking lot." 

Balqees ta d'aga mai kai alamar toh amma sam zuciyarta ba haka taso ba dan bata son zuwa bare ranta ya kuma 6aci sai dai dan kawar da zargi yasa zata je amma ba dan haka ba ji take tamkar ranta zai fita. 

Wani tsadaddan material tasa wanda yana d'aya daga cikin kayan da Sultan yayi mata.sosai tayi kyau d'ainkin riga da skit aka yi mata ta sanya uban sun he'll shoe tare da yafa mayafi ba tare da ta d'aura d'ankwali ba,ta shafa turaruka sannan ta fita ba tare da tayi wani make-up ba dan dama bayi take ba sai dai ta Sanya lipstick. 

Zaune ta gansu a saman mota shi da Yazid suna ganinta suka diro Yazid sai faman kallonta yake yi dan ba k'aramin kyau ta yiba Sultan ya kalleta tare da yin murmushi yace. 

"Inyeee baby kinsha kyau." 

"Na gode Yaya..." 

Ta fad'a tare da k'arasawa ta shiga gidan baya ta zauna, Yazid ya zauna a mazaunin drive shi kuma Sultan ya zauna a gefenshi suka bar gida. Tafiya suka yi me d'an nisa kafin su doshi wata unguwa a kofar wani gidan suka tsaya inda mutane suke wasu na shiga wasu na fita Sultan ya juyo ya kalleta tare da cewa. 

"Baby shiga ciki duk sauran suna nan nasani..." 

Kamar ta kurma ihu haka taji sai dai ba halin yi,fita tayi ta nufi hanyar da taga mutane sunfi yawa ta shiga. Tana shiga suka had'u dasu Fateema da Bilkin Adda Aisha su Aamanee da sauran su ta k'arasa inda suke nan sukayi ta tambayarta inda ta shiga yau sai dai tayi musu murmushi kawai ba tare da tace komai ba domin yadda taji k'irjinta na bugawa baxata iya yin kwakwarar magana ba dan zata iya yin kuka. 

"Balqees tashi muje muga gidan su sun gani nice dama sai yanzu na shigo." 

Cewar Bahijja 'yar k'anwar Umman Sultan,yatsina fuska Balqees tayi tana dafa goshi alamar ciwo ta kalli Bahijja tace. 

"A'a ni bazan iya zagaye ba jiri nakeji, ki samu wata ta rakaki." 

K'iri-kiri ta nuna musu baza taba Bahijja ta samu Fateema ta rakata ita kuma tayi zamanta a parlor ta kurawa wani k'aton elergement ido tamkar kwayar zata fad'o k'asa. Nadiya ne da Sultan a jiki sunyi masifar yin kyau tana daga zaune shi kuma a tsaye ya d'an rankwafo yana kallon fuskarta duk sunyi murmushi sai kawai ta mik'e ta fita, ganin anata shiga mota za'a koma gida yasa itama ta fad'a wata motar ba tare da ta sanar dasu cewar ta tafi ba ko ta nemi Yazid kawai suka wuce. Suna zuwa gidan su Sultan ta fito ashe meh motar yana lura da ita dan haka tana fitowa yasha gabanta tayi saurin kallonshi tare da d'auke kai tana faman had'e fuska cikin 6acin rai. 

"Haba beauty gaskiya baki dace da wannan yanayin ba ki d'anyi murmushi mana." 

Ya fad'a yana hard'e hannunshi a k'irjinshi, Balqees tayi mai banza wani haushin shi na ratsa zuciyarta ya kuma cewa. 

"Oh sorry beauty na cika ki da surutu ko? Nima ba yin kaina bane kice sanadi, sunana Muhammad bello kabir ana kira na da Ameer but bana son sunan sabida yayi sunan yara da yawa Mama nane kawai take kirana dashi na amsa sai kuma ke idan zaki kirani da sunan zan amsa da sauri, ni abokin ango ne tun a wajan bautar k'asa muka had'u dashi ko zan iya jin sunan ki beauty? dan gaskiya ni dai kin yi min.." 

Wani kululun takaici ya tokare a wuyan Balqees ta tsaya tana mamakin jin arnan surutun shi ca-ca-cahh kamar bafadan sarki kafin tayi magana su Aamanee suka shigo bilkisu tace. 

"Lallai Balqees shine tahowa ko magana kika samu nemanki ashe ke har kinzo gida...!" 

Banza dasu tayi ita yanzu sam bata son yin magana dan kuwa zuciyarta duk babu dad'i ganin tayi shiru yasa suka wuce sai faman mita suke yi yayin da Muhd kabir yayi murmushi tare da cewa. 

"Wow! Balqees nice name, dole ayi min rowar jin shi amma dan Allah kiyi min magana mana ko zuciyata ta samu nutsuwa." 

Rasa me zatace mishi tayi gashi yayi bake-bake a gabanta cikin sa'a ta samu aka yi mai waya ya zura hannu cikin gaban aljihun rigarshi ya d'akko tare da karawa a kunne nan taji yace. 

"Ango ya aka yi?...ok...toh gani nan ina nan nayi kamu but taki min magana ta barni sai surutu nake yi...ah anan gidanku fa naji ance sunanta Balqees gata nan ma a kusa dani...kai au Yazid ya rigani?oh my God,gaskiya guy d'in nan ya kwafsa min bari na taho toh.." 

Tana ganin ya mayar da wayar cikin aljihunshi yace mata. 

"Ashe Yaz yayi min shigar sauri,amma dan Allah kina da yayya?!" 

Kai kurum ta samu damar girgiza mai ba tare da tayi magana ba, yayi murmushi tare da yi mata sallama yabar wajan ita kuma ta shiga ciki duk ranta babu dad'i musamman ta take tunanin Yaya Sultan ce mishi yayi Yazid ya rigashi wato bama shi kanshi ba.haka ta dinga gudanar da abubuwa sukuku tayiwa hajiya kaka wayar cewar kawai zata kwana nan gobe zata dawo suka yi sallama tayi stwich off d'in wayar tata kamar tasan zai nemeta ya dinga kira amma a kashe lokacin suna k'ofar shiga parlor shida abokanshi da zasu kaishi,haka ya hakura suka shiga bakin shi bud'e kai da ka ganshi kasan yana cikin farin ciki mai tsanani. 

Bayan an kammala siyan baki ango ya raka abokanshi sannan ya rufe ko'ina na gida ya nufi bedroom d'in da Nadiya take a kwance. Sai da suka yi sallah suka godewa Allah sannan ya ciyar da ita duk kunya tabi ta addabeta shi kuma sai faman tarairayarta yake tamkar zai had'iye ta. Sai da suka gama komai sannan yaje ya watsa ruwa ya dawo ya ja hannunta zuwa d'akin shi domin atsarin shi yadda ya tsara itane zata dinga zuwa suna kwana a d'akin shi dan haka acan suka raya daran su Nadiya duk ta rikitashi ya rasa inda zai sanya ta har asuba be rintsa ba sai dai ita tayi baccin wahala.(Allah ya sanya albarka ya kawo zuria d'ayyaba SulNadi)....

Post a Comment for "TATTALINTA CHAPTER 6"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...