TATTALINTA CHAPTER 2 - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

TATTALINTA CHAPTER 2

TATTALINTA CHAPTER 2

- - Post a Comment

TATTALINTA 
CHAPTER 2

*B*ayan kwana biyu da dawowarta kwance take a cikin d'aki tayi ruf da ciki tana danna waya kamar daga sama taji an warce, saurin kallon gurin tayi karaf suka had'a idanuwa da brother Yusif yana kashe mata ido d'aya, shareshi tayi ta mik'e ta d'auki d'ankwalinta ta d'aura sannan ta fara gaidashi.
"Brother Yusif ina yini?"
"Kalau qis ya jin dad'i naga kallon pic's kike yi ko update kikeyi ne?!"
"No ni bana saka hotuna a istargram sai dai na kalli na wasu kawai."
"Meyasa bakya so?!"
"Haka nan."
"A'a kodai kin tsaida miji ne shi yasa bakya d'orawa?!"
Dariya tayi tana kallonshi ganin irin kallon da yake bin ta dashi ne yasa jikinta shiga cikin rud'ani tayi karfin halin cewa,
"Eh kuma gashi yana da kishi idan ya gani sai munyi fad'a dashi."
Baki Yusif ya tab'e sannan ya samu guri ya zauna,ajiye wayan yayi a gefenshi yana kallonta cikin wani salo wanda shi kad'ai yasan manufarshi yace mata,
"Yanzu idan nace zan aureki zaki yadda Balqis?"
Daram kirjinta ya buga tayi saurin kallonshi shima ita d'in yake kallo tayi saurin kawar da kai tana dariya tace
"Haba brother Yusif ya zaka zo min da wannan maganar haka ni dai bana so duka-duka nawa nake?!"
   "Hmm amma kike kula wani har yake kishinki yana hanaki cin zamaninki a haka kike cemin wai nawa kike?"
Murmushi tayi cikin son bagarar da zancen kafin ta mik'e,k'arasawa tayi inda mini fridge d'inta yake ta ciro ruwan jarka sannan ta d'akko glass cup a saman fridge d'in,dawowa tayi inda yake ta tsugunna tana tsiyaya mai yayin da shi kuma ya bita da kallo cike da sake-saken zuciya.mika mishi tayi ya karb'a sannan ta koma inda ta tashi ta zauna tana cewa,
    "Brother Yusif wai inasu Aisha tunda na dawo ban gansu ba ko duk shirye-shiryen biki ne ya b'oye su har ba'a iya ganinsu...?!"
    "Waya sani tunda kema da kika dawo wa kika nema."
Murmushi ta sakeyi a Karo na ba adadi sannan ta gyara zamanta,hira suka ci gaba dayi har tsawan wani lokaci sannan Yusif ya mik'e dan tafiya ya kalleta yace
    "Sai yaushe Balqis zanzo na k'arb'i amsata don ni sansamu nama a had'a namu dasu heemu su broth Jamal."
    "Yaya Yusif kenan aikai yayana ne so babu wannan maganar a tsakanin mu kawai kabarta iya nan."
    "A'a Balqis ina sonki zan aureki dan haka ki shirya zanje na sanarwa da hajiya kaka a had'amu da sauran kawai."
Yana kaiwa nan yabar d'akin Balqees ta bishi da kallo cikin takaici sam bata sonshi ita akwai wanda takeso duk da cewar shi besan tanayi ba duk abinda take mai yak'i ya gane inda ta nufa to zata fara fitomai b'aro-b'aro dan bazata yadda da auran Yusif ba wannan mara mutuncin da baya tsoran kowa.

Tashi tayi itama tafita zuwa parlor tana zuwa taga Sudais zaune sai faman latsa-latsan waya yake da alama ya jima a zaune.kusa dashi taje ta zauna nan ta fara gaidashi ya amsa ba tare da ya kalleta ba ganin haka yasa ta lek'a wayan dan ganin abinda ya hanashi kallonta,ga mamakinta chatting taga yana yi nan ta kuma zura kai tana waro idanuwa ganin da mace yakeyi ne yasa taji ranta ya sosu da sauri ta warce wayan tare da b'oyeta a bayanta.
   "Ina wasa dake zaki fizgar min waya?!"
Baki ta zumboro tana k'ara b'oye wayan,hannun shi ya mik'amata alamar ta bashi amma tak'i wani kallo da yayi mata sai da yasa taji wani yarrrrr a cikin jininta yace,
    "Mik'omin kafin ki b'ata mata rai tayi tunanin ko ina sane na kyaleta."
Balqees bata san lokacin da tace,
    "Toh Yaya wacece ita?!"
   "Budurwata ce wadda nake son in aura ki bani karkija yau idan naje gurinta tak'i fitowa."
Cikin jin haushin maganar shi tace
    "Wallahi sai dai taji ita d'inwa da zata ce taji haushi,toh yau kam saidai ku fasa yin tad'in."
Sultan yace cikin rashin damuwa,
   "Toh Umma naji amma dai yanzu ki bani wayata."
    "Sai anjima."
Tayi maganar tana kokarin kashe mai data,kyaleta yayi dan ta fuskanci yau so take ta raina shi ita kuma ganin yayi shiru yasa ta fara mai magana,
    "Yaya zulqallain bafa ayi min ankon bikinsu Yaya Jamal ba gashi lokaci sai korewa yakeyi."
   "Toh ya akayi...?!"
    "Sai kayi min."
    "Toh kala nawane inji ko zan iya kinsan dangin nakine sai karyar jaraba."
Dariya tayi dan tasan shi besan ayi abun fariya kallonshi tayi suka had'a ido tace,
     "Les 15k material 25k sai atamfar ita kuma 8500k."
Ware idanuwa yayi cikin tsananin mamaki,d'auke kai tayi dan karma taga reaction d'inshi ya jinjina kai yana cewa,
     "Tab! Wannan duk iyaye ne zasu yiwa mutum d'aya?kud'in buhun shinkafa harda canjin kayan miya nidai bazan iya ba guda d'aya zan iya miki sai ki zab'i wanne kike so a ciki,wannan ai salon a koya muku kashe kud'ine idan kika saba da irin haka yazo mijin da zaki aura bame irin wannan abun bane ya ki miki ya zakiyi?toh karki sawa ranki kuma daga wannan d'ayan da zan miki idan kikaje gurin wani kikace yayi miki sauran  sai ranki ya b'aci.."
Da kallo ta bishi tana turo baki, tashi yayi yana gyara wuyan rigarshi tare da mik'a mata hannu alamar ta bashi wayar shi,tana zumb'urar baki ta m'ik'a mai ya k'arb'a yasaka a cikin aljihu.hanyar fita yayi yana cewa
   "Idan hajiya kaka ta fito kice nazo zan  dawo anjima."
Yana fad'a yayi waje ita kuma ta rakashi da ido tana mamakin shi a haka kamar bazai yi irin wannan matsin ba amma a fili ya fice yadda ake tsammani.

Sultan be samu damar dawowa gidan hajiya kaka ba a ranar sai washe gari bayan ya shirya zai tafi gurin aiki kasan cewar shi lecturer,horn yayi megadi ya bud'e mai yana shiga yayi parking sannan ya fito ya rufe motar. Balqis dake tsaye a jikin window ta hangoshi nan da nan ta sake ware idanuwanta manya tana kallonshi ba karamin kyau da had'uwa yayi ba cikin had'add'an yadi mai matuk'ar laushi da tsada ya tasamma cikin gidan hannunshi rik'e da leda katuwa bak'a.Shiga yayi da sallama babu kowa cikin parlorn hakan yasa ya wuce bedroom d'in hajiya kaka,zaune ya ganta kan sallaya da alama tun sanda tayi sallar asuba batabar gurinba ya durk'usa har k'asa yana gaida ita.
   "Na k'arfan har za'a tafi gurin aiki?
"
   "Eh kaka nama yi latti sabida ibada lecture 8 to 10am gashi yanzu har 7:56am anko d'in baby na kawo sai takai d'inki gashi nan."
   "A'ah Allah sarki Muhammad Allah yayi maka albarka ya baka ladan kula da marainiyar Allah."
   "Amin kaka ni zan wuce sai na dawo."
   "Toh Muhammad d'auki sai ka mik'a mata tana d'aki kamar kasa haka take da shegen baccin tsiya."
Mik'ewa yayi tsaye tana 'yar dariya ya d'auki ledar ya fita ta bishi da kallo cike da sonshi tana yin wani fata a cikin zuciyarta. Yana zuwa kofar d'akin ya fara bugawa amma shiru ba'azo an bud'e ba hakan yasa shi tura kofar dan yana tunanin kamar yadda kaka tace bacci take kila bazai wuce hakan ba. Kwance ya ganta daga ita sai wata yaloluwar rigar bacci fara kal wanda iyakarta cinyoyinta bata koma rufe mata komai na jikinta ba,da sauri ya kawar da kanshi gefe ya shiga ciki tare da ajiye mata ledar hannunshi,bargon da yagani yashe a gefe shi ya d'auka ya lullub'a mata yana fad'in,
    "Rubbish! Wannan wane irin bacci ne bayan gidan is not safe kowa na iya shigowa mtww.."
Ya fad'a yana jan wani dogwan tsaki tamkar zai ciro bakinshi,tana ji kamar ta tunrsire da dariya sai dai ta samu tayi shiru harya fita, mik'ewa tayi zaune tana turo baki sam ba haka taso ba so tayi yaji wani abun amma da alamar yadda taji yayi magana haushi ma yaji toh me zatayi mai ya gane manufarta akan shi?

    *T*ashi tayi ta sauka daga kan gadon da sauri ta k'arasa wajan window tana leken shi har ya shiga mota yajata maigadi ya bud'e mai ya fita. Da sauri ta koma kan gado tare da fad'awa kai tana furta,
    "I love you Yaya Sultan."
Kamar wadda aka tsikara kuma sai ta mik'e tsaye tare da zuwa ta d'auki ledar daya shigo mata da ita,dubawa ta hauyi nan taga anko ne material ya kawo mata da mayafi tare da wani shegen hill shoe kalar mayafin wanda zai shiga da kayan tayi wani irin juyi na jin dad'i tare da buga tsalle kafin ta fara gwadawa.
   "Wow! Yaya Zulkallain, wallahi kasan duk wani forvarties nawa amma me yasa ka kasa gane inda zuciyata da gangar jikina suka nufa akanka? Idan kuma ka gane me yasa kak'i nuna min wallahi ina sonka duk duniya babu wanda ya fini sonka please dan Allah ka soni..."
Gyara zama tayi tare da janyo wayarta dan neman irin style d'in da za'ayi mata,ta dad'e a cikin d'akin har wajan goma da 'yan mintuna sannan ta fito cikin doguwar rigar atamfa. Zaune ta tarar da hajiya kaka tana shan kunu da biredi ta k'arasa kusa da ita tare da fad'in.
   "Kai hajiya koki k'irani gashi harkin kusa cinyewa.."
   "To ai yanzun ma bawai ci zakiyi ba sai dai kije kitchen ki zubo naki.
Cewar hajiya kaka tana kurb'ar kunu ganin tana kokarin shanyewa yasa Balqis karb'ewa ta matsa tana cewa,
   "Haba ai wallahi nasan babu a kitchen tunda kad'an ake kawo miki kuma bakya ragemin kullum sai dai na sha tea."
Kallonta hajiya tayi tare da tura mata ledar biredin tana cewa,
    "Toh ai saiki d'auki wannan ma kici tunda bakya son nayi kiba ai kema kuwa bakya yi tsayo ba yarinya."
Dariya Balqis tayi har tana tuntsurawa k'asa ta d'ago tana kallon kaka tace,
   "Kai jealous ne wannan."
Kaka ta harareta cikin wasan jika tace,
   "Naga mijinki baby Allah dai yasa karki zabo wanda ya ninkaki sau uku a tsayi."
Tana kurb'ar kuna take fad'in,
    "Aikuwa inda wanda nakeson na aura ne toh wallahi ya fini sosai meye a ciki ko so kika duk mu had'u gajeru sai kace a garinku.."
Kaka ta rik'e hab'a kirjinta na bugawa addu'arta d'aya Allah yasa ba wani k'atan arnan taje ta kwaso musu ba amma dan ta kawar da zargi sai tace,
    "Naji idan ba'a garinmu ba ke naki d'an wane gari ne a ina yake ya kuma sunan shi inji?!"
Balqees tayi dariya tare da ajiye kufin dan ta shanye kunun tace,
    "A'a ba yanzu zan sanar miki ba sai nan gaba haka kurum na gaya miki kije ki sanarwa dasu Abba da daddy."
    "Toh karki fad'a mana idan tayi wari maji."
     "Eh na yadda."
Balqees ta fad'a sun dad'e zaune a gurin kafin kaka ta mik'e tana son shiga d'aki tayi sallah dan haka anan parlor tabarta ita kuma ta shiga ciki, bata dad'e da shiga ba Yusif ga shigo kamshin turaren da ya daki hancinta shine yasa ta d'aga kai ta kallo k'ofar shigowa parlon yana hangota ya saki wani kayataccen murmushi cikin ranshi ya fara ayyana, Anya zai iya hakura da ita kuwa domin yanzu bawai son wasa ko dan wani abu da sukeson cinma burinsu yake yi mata ba sone na zuciya kuma na aure dan sai jiya ya k'ara gano wasu qualities a jikint da cikin qwayar idanunta hakik'a tana da kyau gata 'yar gayu wayayya kawai rashin tsawo ne matsalarta domin duwaf ce sosai yana ta ayyana haka cikin ranshi duk a 'yan dak'ik'a har ya k'arasa inda take zaune ya tsaya tare da zare dark black d'in glass dake manne a idonshi.
   "Morning my wife to be."
Murmushi kawai tayi tare da tashi zaune dan da tana kwance ne a kan 2siter ganin haka yasa shi zama a kusa da ita yana faman kashe mata ido d'aya, ta d'an matsa sosai yadda baza su dinga tab'a juna ba kasan cewar daya zauna suna gogar kafad'a tace
    "Kai broth Yusif wane irin wife dan Allah ka bari."
    "Na bar me kuma?!"
Ya fad'a yana kallon jikinta wanda yake d'an kubul-kubul gashi kwance ta ko'ina a jikinta sam bata kulaba kanta na wajan  Rani wanda take kokarin sakawa a yatsunta tace mai.
    "Ka dena cemin wani matar ka just kawai ka barni a matsayin sister d'inka nafi son haka domin ni a matsayin yayana nake d'aukar ka.."
Matsawa ya sake yi kusa da ita tayi saurin kallonshi cikin mamaki sai taji hannunshi a saman kanta ya zame mata d'an kwali yana shafar tulin gashin kanta wanda yake a tsafe gashi cukus domin natural ne yana da d'an karfe sai dai ba sosai ba gashi da uban yawa, da sauri ta ture mai hannu tare da fad'in.
    "Dan Allah broth Yusif kadena min irin haka bana so."
     "Oh my God, habba dan na tab'a gashin kanwata kuma matar da zan aura shine zaki Ce min bakya so? Meye a ciki baki son akwai wad'anda kafin suyi aure sai sun fara ganin surar Matar da zasu aura ba? Sai dan kawai na bud'e kanki ina gani zaki ce bakya so hmmm." 2

Mamakin kalaman shi suka daskarar da Balqees a wajan, shin meyake nufi akanta ko itama so yake ta tub'e dan rashin kunya da salon iskanci?ita koda taje karatu kasar masu jajayan wuya bata tab'a bari suyi shaking hands dasu bare yanzu da ta dawo k'asarta ta kunya mai tsananin bin iyakokin Allah shine zai zo mata da wannan salon iskancin. Hannunta taji ya kamo da sauri ta mik'e tsaye tare da kwacewa tana kallonshi cikin b'acin rai wanda besan tana iya yinshi ba tace,
   "A gaskiya Yaya Yusif bana son wannan salon iskancin karka sakeyi min idan ba haka ba wallahi zan gayawa kaka abinda kakeyi min."
Shima da sauri ya mik'e yana yi mata wani irin kallo wanda ta kasa fassara shi ya kuma kokarin janyo hannunta tayi saurin juyawa tare da kwasa da gudu tayi bedroom d'in hajiya kaka tana kiran sunanta.ga mamakinta har cikin d'akin ya bita suka tarar tana sallah ya tsaya daga bakin kofa yana mata dariyar mugunta yace,
    "Kin manta yadda kike da ita haka nima nake da ita?kuma babu uban da yasa ya koreni ko ya hanani shigowa gidan dan haka kidena wani zille-zille bari ma ta idar na gaya mata kiji."
Ita dai duk tsoranshi ya kamata tunda ta samu ta tsira duk abinda zaiyi yayi yana nan a tsaye har kaka ta idar da sallah ta kalleshi tun kafin tayi magana yace
    "Hajiya son jikarki nakeyi kuma da aure please ina son a had'a danasu I.b kinji kar azo ana b'aran b'atama aga laifina."
   "Kai Yusif ka kiyayeni wallahi kafita idona na rufe uban meye kuma b'aran-b'atamar da kake cewa?!"
Ba kunya ba tsoran Allah Yusif ya kalli kaka tare da k'ara shiga cikin d'akin yace,
   "A'ah kar azo ni kun hanani ita kuma ina sonta azo hakurina ya kare na afka mata shine b'aran-b'atamar gara kubani asiri a rufe."
Cikin mamaki hajiya kaka ta rik'e hab'arta tare da kallonshi sosai tace,
    "Ita dai marainiyace amanace a gurin mu gaba d'aya sannan duk abinda zakayi karka fasa baxata aureka ba mara kunya fitsararre mun rigada munce Allah dan haka baby a hannun Allah take sannan a hannun Muhammad take kaje kayi duk uban da zakayi sakarai kawai."
    "Shikenan kaka tunda na fad'a muku kunki bani abinda nakeso, and kin ce min sakarai zan nuna miki cewar ni ba sakarai bane wallahi."
Yana kawai nan ya juya zai tafi sai kuma ya kalli Balqees d'in tare da kashe mata ido d'aya cikin sigar bada haushi yace,
    "Bye-bye sweet wife."
Kaka ta wurga mai carbin hannunta ya fita yana dariya yayinda ya barsu cikin wasuwasi da sake-sake musamman kaka da ta tsorata dajin kalamanshi tasan Yusif hastsabibin yarone komai yace sai ya samu kota halin k'ak'ane ita kam bata son ya aureta tafi son taji Kalmar daga bakin Sultan amma bata ganin alamun hakan domin shi sam tunaninshi akanta yadda zai kyautata mata ya kula da ita ya bata duk wani abu da take bukata wanda iyaye zasu iya yimata baya son tayi kukan rashin Mamanta da daddyn ta wannan shine burinshi hakan yasa suka shaku sosai sai dai ita Balqees lamarin ya canza domin masifar kaunar shi takeyi so mai tsanani ma kuwa.

 
    *K*uka ta sanya a gurin hajiya mai matuk'ar ratsa zuciya kaka ta mik'e zuwa kusa da ita cikin jimami tace,
   "Menene kikewa kuka haka kuma baby?!"
  "Kaka ina tsoro,wallahi tsoran shi nake Yaya Sufee bashi da imani bashi da tausayi ya zanyi kaka?me yasa na zama zab'in zuciyar shi by force?!"
   "Babu baby sai addu'a domin itace maganin komai,ni da har ina tunanin zaki yi degree kafin kiyi aure yanzu ga hattsabibin yaron nan yazo da wannan salon iskancin dole sai mun tashi tsaye akanshi,baby ki dinga addu'a kinji Allah yayi miki tsari akanshi
"
     "Amin kaka."
K'ara rushewa tayi da kuka zuciyarta na zafi tana tunanin yadda za'ayi burinta ya ciki tana son Sultan ya zata yi shi ya kasa ganewa, muryar hajiya kaka taji tana tambayarta.
     "Baby ko kina da tsayaye wanda kike so kuka yi magana dashi gara naji sai nasan abin yi a gaba."
Kanta ta girgiza alamar a'a idanunta sai zubar hawaye yakeyi cikin sanyin jiki dana murya hajiya kaka ta kuma cewa,
     "Toh kuma baku tab'a yin maganar zancen auranki ba keda Yayanki Muhammad?!"
Daram!k'irjinta ya buga duk sai tayi tunanin ko kaka ta b'aro jirginta amma yadda taga tana kallonta yasa ta tunanin ko kawai tambayarta tayi,sai da kaka ta sake yin magana sannan Balqees tace,
     "A'a kaka bamu tab'a yiba."
     "Toh Allah ya kareki baby insha Allahu Allah na tare dake."
     "Toh kaka amma nan gurinki zan dawo ina kwana dan wallahi tsoro nakeji karya shigo min d'aki baki sani ba."
    "Toh ki dawo nan dan tsab Yusif ba hankali gareshi ba zai iya."
Wajan k'arfe 4:30pm yayi parking lepan mashin d'in shi ya k'arasa cikin gidan hannunshi rik'e da leda 'yar karama,sallama yayi ya shiga ciki a d'an hanzarcen shi har ya shiga zaune yaga hajiya kaka tana gyara murjaninta daya harhard'e kan kujerun kuma su Waheedah da Aisha sai Jamila ne zaune sai hayaniya suke saida suka ganshi sukayi shiru,zama yayi yana kallonsu cikin mamaki ya kalli kaka yace,
     "Wa innan kuma fa hajiya kaka daga ina suke zuwa ina?!"
Murmushi kaka tayi sannan ta kalleshi cikin bashi wani irin girma da ba kowa take bawa ba sai taga kuna d'asawa da ita tace,
    "Gasu nan wai rabon kati xasuje."
     "And?!"
     "Kaji daga garesu gaka gasu nan ai."
Ta fad'a ganin so yake yaji bayani sosai dan taga be gane d'an bayanin da tayi mishi.maida kallonshi yayi kansu sai a lokacin suka gaidashi amma banda Aisha dan ba k'aramin haushinshi takeji ba tsawon shekaru tun lokacin da hajiya kaka tayi had'in auransu yace baya so,kallonsu yayi tare da cewa.
     "Jamcy sai ina kuma?!"
Jamila tace,
     "Yaya Sultan zamu je rabon I.v ne kasan biki yanata matsowa.
     "Ohh kuma da yamma haka?!"
Duk shiru sukayi babu wadda tayi magana sai fitowar Balqees sukaji ta fito sanye cikin english wears riga da siket ta d'ora wata kyakyawar after dress bak'a mai kwalliyar wasu star's a jiki masu kyau ta hau wani uban hill d'in takalmi sai zagba kamshi take ta fito tana d'aura veil a kanta karaf suka had'a idamuwa dashi ya bita da kallo yana tab'e baki har ta k'arasa wajan shi tana murmushi tace.
     "Yaya yaushe kazo gidan?!"
   "Kafin na baki amsa ina zakije haka?!"
Ya fad'a yana kallonta, Murmusawa tayi tare da karyar da kai ta kalleshi tace,
    "Yaya rabon I.v sannan kuma zan biya wajan tellan Yaya Jamila na kai d'inki."
   "Oho toh dazaki fita wakika tambaya?!"
   "Hajiya kaka na tambaya wallahi Yaya."
Ta k'arashe maganar cikin rawar murya dan taga take-taken shi nasan hanata zuwa,baki ya tab'e sannan ya kallesu gani yayi duk sunyi kuru suna kallonshi suga zai barta ko zai hanata ya juya tare da cewa,
    "Sai kun dawo but kuyi kokarin ganin baku kai magrib ba waje kunji ko?!"
Dukan su suka ce,
     "Toh broth insha Allahu."
Suka fad'a Amma Aisha ko kallansa batayi ba bare ta bud'e baki tayi magana sam basa shiri ko lecture yaje dayake yana d'aukar su bata nuna ta sanshi dan ma kar wani abun ya had'asu tunda yace baya sonta, matan depertiment d'insu kuwa kamar zasu mutu akan shi sai dai tayi kamar basan sunayi ba da haka suka tashi suka fita cike da murna Balqees kuwa kamar ta had'iyi  naira ganin be gwaleta ba.

**
Bayan kwana biyu a yan kwanakin kullum su Balqees basa nan suna rabon I.v yau kam basu fita ba duk wasu sa'anninta da amare suna gidan hajiya kaka a d'akko D.J ana koya musu rawar gad'a wadda za'ayi a wajan kamu ciki kuwa harda Balqees ta zage sai yi suke a haka Yaya Jamal da Yaya Ibrahim da kuma Sultan suka shigo suka gansu,cak suka tsaya suna kallonsu sai murmushi suke musu banda Sultan daya had'e girar sama data k'asa yana kallonsu.ita kam Balqees sabida shagala sam bata kula dasu ba sai rawar gad'a take abin gwanin ban sha'awa.
Sharesu yayi ya wuce cikin gidan zuciyar shi fal haushi sam baya son wannan raye-raye I.B shima da kusan ra'ayinsu d'aya ya take mishi baya yana tab'a baki,zaune suka tarar da hajiya kaka da wasu kawayanta sai hira suke nan suka gaida su sannan suka zauna ba jimawa k'awayan kaka suka tafi su kuma suka ci gaba da hira tana jansu da wasa irinna jika da kaka,hakurin Sultan ne ya kasa jurewa dan haka sai da ya magantu lokacin ne kuma Yaya Jamal ya shigo shima.
     "Hajiya wai me yasa kika bar yaran nan suna wani banzan raye-raye ba ko tsari..?!"
Yayi maganar yana yatsina fuska yana saukewa Yaya I.b ya d'ora da cewa,
     "Toh ma wai wayace ayi wannan bidi'ar ne bridles d'in ko iyayansu dan nasan ni ba'ayi shawarar za'ayi wannan abun dani ba?!"
    "Ikon Allah! kujimin yara, na d'auka saida kuka wuto su sannan kuka zo inda nake,me yasa baku tambaye suba sai da kuka shigo ciki dan kinibibi?!"
Tayi maganar tana rik'e hab'arta dan tasan raini ne basa so shi yasa basu kulasu ba ita kuma tayi alwashin baza ta dinga shiga irin wad'annan abubuwan ba tunda sune suke buk'atar gyran ba ita ba,ta sake kallon su nan taga sunyi shiru sai ma waya da Sultan ke matsawa shi kuma I.b yana forwarding t.v sun ma maida ita wata sakarai sai Jamal ne yace,
     "Rabu dasu kaka ni nasan za'ayi abun kuma har gudun mawa na bayar dan a k'arawa abin armashi."

Sudai basu sake yin magana ba sai Jamal ne da hajiya kaka suka ci gaba da hirar su, sai kusan k'arfe 6:15pm sannan suka tashi duk suka yo cikin gidan a parlor suka yadda zango nan heeda tayi wajan Yaya Jamal Jamila kuwa da yake tasan halin kayanta ko gurinshi bataje ba ta  koma wajan kaka ta zauna ita da Aisha da Fido yayin da Balqees tayi wajan Sultan wanda hayaniya take son hanashi sakewa tana zuwa ta zauna kusa dashi har suna gogar juna tace,
     "Lah!Yaya zulkallain yaushe kazo ban sani ba?!"
Tayi maganar cikin harshen turanci fuskarta fal murmushi,banza yayi da ita kamar bejiba hakan yasa ta kuma maimaitawa da hausa amma ko d'agowa beyiba waya kawai yake kallo yana murmushi da alama chatting yake yi,nan da nan Balqees ta had'iya wani haushi yayi mata kululu a cikin zuciyarta da sauri ta fisge wayan daga hannunshi ta kalla abinda ta gani ne yasa jinta da ganinta suka tsaya cak ta zaro idanuwa kirjinta sai bugawa yake ana iya gane hakan ne ta hanyar yadda gaban rigarta ke d'agawa sosai....

    _Between love & friendship, if you have to choose one what would it be?both, giving up is not my vocabulary *Sultan & Yusif*_

     
     *M*ikewa tayi jikinta na rawa tayi hanyar d'akin kaka da gudu ya bita da kallo cike da mamakinta haka duk wad'anda suka ankara suma kallon suka bita dashi suna mamakinta. Tana shiga ta kulle kofar tare da jingina bayanta a jikin kofar tana hawaye sosai,a hankali ta sake kallon wayar nan ta kuma ganin abinda ta gani hakan yasata kulle datar sannan ta kira layin wadda suke chat d'in tare,cikin zazzak'ar murya taji tana cewa.
    "Ya naji kayi shiru a online bayan ina tayi maka magana kana gani?!"
Shiru taji beyi magana ba har zata katse kiran sai kuma can taji muryar mace tana cewa,
    "Bashi bane."
Da mamaki ta can b'angaran da aka kira d'an tayi shiru can kuma tace cikin son tambatarwa tace,
    "A'ah kardai ace baby ce idan itace zan iya cewa nafi kowa sa'a yau tunda gashi an had'a mu yau zamu gaisa."
Wani tukuk'in haushine ya k'ara mamaye zuciyar Balqees dan haka cikin kufula muryarta a shak'e tace,
     "Wace babyn?!"
      "Baby Balqees mana."
Ta fad'a cikin son nuna ta san wani abun game da ita,haka kurum kuma sai Balqees taji tana son jin ya akai ta santa bayan ita bata tab'a saninta ba bare labarinta a hankali ta sulale k'asa jikin k'ofar tace mata.
     "Toh ya akai kika sanni?!"
Ta cikin watar tayi murmushi wanda har ita kanta Balqees d'in sai da taji tana son ganin yadda aka yi shi a fili,cikin sassanyar muryarta tace.
    "Na sanki mana a wajan yayanki daddynki Ahmad,yana bani labarinki sosai ta yadda yawancin labarinshi indai zai yi su toh nakine baby Ahmad yana sonki yana kuma tausayin maraicinki hakan yasa ya shaidamin cewar shine daddynki a nan duniya yana son duk wani farin cikinki ya k'ara min da cewar indai mukayi aure zaki dawo gurinmu domin yafi son ya aurar dake da hannunshi."
Kit ta kashe wayar ta zame gurin tayi kwance tana hawaye,anata kiran magriba hajiya kaka dasu Jamila suka taho d'akin bubbuga mata suka shiga yi dan hajiya kaka so take tayi sallah amma tak'i zuwa ta bud'e. Su kuwa su Sultan Ahmad fita suka yi dan zuwa masallaci kota kanta bebiba dan yaga alamar neman rainashi takeyi hakan yasa yak'i bin bayanta so yake yaga iya gudun ruwanta. A can kuwa da kyar ta iya mik'ewa bayan ta b'oye wayar tazo ta bud'e musu k'ofar duk sai suka bita da kallon tuhuma amma fur tak'i yadda su had'a ido da kowa a cikinsu.
    "Ikon Allah ko dai a wajan rawar nan kin kwaso mana almatsutsai baby?!"
    "Shine ai hajiya kakus bin cika manadai."
Cewar Waheedah tana dariya ita dai Balqees ko kulasu batayi ba zuciyar tace keyi mata zafi da sauri ta wuce d'akinta wanda ta gudarwa sabida tsoron Yusif tayi saurin fad'awa toilet, alawala tayi tazo tayi sallah tana kwance kan sallaya ta idar da sallah sai kuka take ko su Jamila da suka idar da tasu sallan tafiya sukayi ba tare da sun sake dubata ba,shima be samu damar dawowa ba sai da yayi sallar isha'i sannan suka shiga gidan shida Yaya Heemu(I.b),ganin babu kowa a parlorn yasa Sultan kallon I.b yace,
    "Ina zuwa wayana yana wajan baby."
     "Ok ina nan idan ka fito."
Cewar i.b yana kokarin zama akan kujera, d'akin kaka ya fara zuwa yaga bata nan sai kaka dake sallah ya juya dan a tunaninshi kosu Aisha tabi dan haka yayi kokarin komawa parlon ya zauna sai kuma yaji yana son zuwa d'akinta ya juya ya koma yana shiga ya ganta tana shaahekar kuka saida ya samu guri a bakin gado ya zauna kusan tsawon minti biyar kamar bazaiyi maganaba sai kuma yace.
    "Ya akai kuma kike kuka baby?!
     "Ko wani abun akayi miki ne?!"

Da sauri ta mik'e zaune lokacin da taji muryar shi,kallonta yayi da mamaki ganin kuka tayi sosai nan da nan ya shiga damuwa ya nuna mata kusa dashi ta dawo ta zauna har lokacin hawaye basu bar zubo mata ba ya kuma maimaita mata tambayar farko duk sai ta rasa abinda zatace can dai ta daure cikin muryar wadda tayi kuka tace,
    "Amma kawai dan ana ganin banida mahaifa wad'anda da nazo nayi musu magana zasu kulani shi yasa ake min haka ciki harda kai Yaya Sultan kuma kaine ma kafi yi min hakan."
    "Ke! Ni d'in ne nake miki duk wannan abun?!"
    "Eh wallahi kuma ni gara kowa yayi min da ace kaine kake yi min..."
    "Toh ni d'in me nayi kece mafa kikayi min laifi amma dan kin raina ni shine zaki zo kina cewa ni nayi miki laifi,toh gaya min abinda nayi danni bansan nayi ba har ake min korafin ba'ada iyaye ko ni d'in meye amfanina oho."
Ya fad'a yana d'aga kafad'a dan yaji haushin kalamanta na cewa wai dan anga batada mahaifa,kallon yanayin shi tayi sai taga duk yayi kalar jimami amma idan ta tuna yadda yake d'aukarta wato matsayin 'yarshi bama wadda zai aura ba sai taji wani katon abu kamar dutse ya tsaya mata a makoshinta murya k'asa-k'asa tace,
    "Bayan nazo inata yi maka magana amma sai chat kakeyi Yaya zulkallaini amma ni kayi banza dani bayan dakai nake alfahari bayan iyauena da suka kawo ni nan duniya amma kaine jigona gatana sirrina abin alfahari na anan duniya."
Murmushi yayi jin abinda tace,yau da ace soyayya suke zai iya d'aukar hakan a matsayin kishi amma yanzu sai ya d'auki hakan da tunanin ko ta d'auka wulakantata yake bayan shi ba haka bane hasalima haushinta ya keji daya ganta tana rawa shida baya ko mafarkin yaga wani nashi nayi bare ita da yake burin yaga yayi tattalinta dan kar tayi kukan maraici.Hannuwanta ya kamo cikin nashi har saida taji wani yarrr tsigar jikinta ta tashi tayi saurin rintsa idanuwa haka kurum taji bata son ya saki hannun nata cikin kulawa yace mata,
    "Toh shine kuma zaki kwace min waya?kinsan abinda nake yi da ita a lokacin?!"
Balqees tayi mai shiru jin abinda ya fad'a ganin tayi shiru idanunta a rufe yasa shi zare hannunshi amma ga mamakinsa sai yaji ta kuma damkewa hannu biyu-biyu yayi murmushi cikin wasa yace,
    "Toh ko anan zan kwana ne baby?!"
    "Eh Yaya dan Allah ka kwana dama tsoron gidan mukeyi daga ni har hajiya kakan."
Ta fad'a tare da bud'e idanuwanta akan fuskarshi nan da nan ra kuma jin fad'uwar gaba ya hure mata idanuwa da iskar bakinshi sannan yace.
     "A'a ina da abinda zanyi a gida kuma da yawa ku denajin tsoro kuma Allah yana tare daku ki dinga addu'a idan zaki kwanta banda tunanin rawar da akayi d'azo kinji ko?!"
    "Eh Yaya thanks you ina sonka sosai."
    "Me too baby ai idan nayi aure toh gidana zaki koma ko baby..?!"
Ai nan da nan ta had'e fuska cikin takaici tace mai.
    "Yaya wai wacece wannan d'in a ina take, kuma ya kake jinta a ranka dan nima nasan irin matsayin da zan bata a cikin zuciya ta?!"
Tayi magana da d'an k'arfi-k'arfi tana turo mai baki,shi kam be kawo komai ba a ranshi dan haka yayi murmushin shi me kyau yace.
    "Zan gaya miki baby amma kawai abinda yanzu zan iya ce miki shine, Nadiya itace wadda zan aura insha Allahu domin ina yi mata wani irin so ne wanda bazan iya fad'arshi a baki ba sai dai idan zuciyata zata iya fitowa sai mutum ya gani dan haka baby ina son ki girma min Nadiya kiso ta kamar yadda nake sonta ki kuma d'auketa a matsayin uwa a duk lokacin dana aure ta."

Tunda ya fara kwarzanta Nadiya ji da bugawar zuciyar Balqees ya tsaya na wani lokaci,sam bega yanayinta ba har saida yakai k'arshe ya kalleta sai yaga ta kafeshi da idanuwa tamkar tana neman wani abu akan fuskarshi.
    "Baby ya ne?!"
Shiru ba magana ba motsi ganin haka yasa shi d'ago hab'arta yana kallonta,gani yayi ta kifo jikinshi yayi saurin mik'ewa yana girgiza ta tare da kiran sunata har hakan ya janyo hankalin I.b wanda ke zaune a parlor yana kallo shima yayo d'akin da gudu nan suka rufa a kanta Heemu ya d'akko ruwa ya shafa mata wai ko suna tunanin suma tayi amma ba alamar zata motsa sai idanuwanta ne da suke kiftawa a hankali a hankali Sultan ya kalli I.b cikin tashin hankali yace,
     "Jinin muje hospital."
      "Ok tom."
Nan suka fito Sultan ne ya d'akko ta suka ci karo da hajiya kaka wadda ke kokarin shiga d'akin ta gansu suna k'ok'arin fita cikin tashin hankali tace,
     "Subhanallahi lafiya Muhammad?!"
     "No hajiya nima bansan meke going ba amma zamuje asibiti ki bari yanzu zamu dawo."
Yana kaiwa nan ya wuce suka tafi hankalin hajiya kaka yayi matukar tashi ta koma ta zauna tana yin addu'a.wani karamin asibiti sukaje nan wani abokin I.b likitane a gurin ya k'arb'eta ba jimawa ya fito yace su bishi office nan duk suka bi bayan shi baki d'aya hankalin Sultan a tashe yake nan Dr Auwal ya kallesu yace......

     *"A*bokaina! maralafiyar ku a binciken da muka yi yanzu tana cikin wani yanayi,akwai abinda ya daki zuciyarta wanda har yayi barazanar tab'a mata zuciya amma alhamdulillahi Allah yasa hakan be faruba sai dai akwai tsoro a tattare da ita wanda yake taka muhimmiyar rawa wajan razanar da zuciyarta."
    "Innalillahi wa'innailaihir rajiun meke nan likita?meye yake barazana da zuciyar marainiyar Allah jinin ko dai kai ne?!"
Cewar I.b yana kallon Sultan wanda tunda aka fara musu bayani zuciyar shi ke tsananin bugawa hankalinshi yayi kololuwar tashi ya tafi tunanin abinda ya janyo mata hakan har ya tuna lokacin da tace mai ya kwana a gidan suna jin tsoro,toh me yake janyo musu jin tsoran shine ya kasa ganowa sai yanzu tunanin shi ya katse jin abinda I.b yake zarginshi dashi,cikin damuwa da kuma tashin hankali Sultan yace.
   "Me! Akan mefa jinin?!"
   "Naga ne kuna tare abin ya faru kaga kenan kaine ka kuma san komai da ya sanyata cikin wannan abun."
Dafe kai Sultan yayi tare da rintsa ido tabbas kota police station sukaje shine mutum na farko da za'a fara zargin yayi mata wani abun amma shi yasan ba shi bane dan haka cikin damuwa ya kalli I.b tare da cewa
    "Bani bane jinin amma dama tace min wai na kwana a gidan sabida suna jin tsoro ita da hajiya babbah, sai dai bankai ga tambayarta ko tsoron meye ba na d'auka kawai so takeyi taga na kwana sai kawai nace suyi ta addu'a iya abinda na sani kenan sai dai idan ta farka muji abinda ya razanatan."
Dr Auwal ya mik'e tsaye tare da kallonsu yace,
     "Ok muje ku ganta sai dai nasan yanzu ta samu bacci sabida allurar da aka yi mata."
Gaba d'aya suka mik'e tare da bin bayan shi sai dai jikin Sultan duk yayi sanyi kanshi har ya fara mai ciwo da haka suka shiga cikin room d'in da Balqees ke kwance.a bakin gadon I.b ya zauna yana kallonta cikin tausayawa,idanuwanta a lumshe tana bacci gaskiya ba k'aramar kyakyawa bace domin baccin ma kara mata kyau yayi ba kad'an ba. Sultan kuwa a gefen gadon ya tsaya dan har lokacin zuciyar shi bata cikin nutsuwa yana son gano matsalarta ya tabbatar tana cikin damuwa ya kuma fara gano hakan ne ta yadda idan taganshi yana waya ko chat ko kuma idan yak'i zuwa gidan hajiya kaka duk sai yaga tana mai wani gani-gani.
    "Jinin ya kamata muje gida mu sanar ko?!"
    "Ok amma ni bazan iya komawa ba sai dai ko kaje sai ka taho da hajiya babba dan nasan duk inda take yanzu tana cikin rashin kwanciyar hankali."
Mik'ewa I.b yayi tare da fita shi kuma Sultan ya koma inda ya tashin ya maye gurbin,hannunshi yasa ya riko nata yana kallonta wani mugun tausayinta na ratsa zuciyarshi yana nan zaune agurin sai gasu hajiya kaka da abban shi sai I.b a baya suka shigo shi kuma yayi saurin mik'ewa tsaye hajiya kaka ta k'arasa kusa da ita tare da cewa.
   "Oh ni 'yatasu wai meke damun yarinyar nan ne yau, ba sid'i ba sad'ad'a yau ta kulle kanta taci uban kuka yanzu kuma tana neman had'iyar zuciya.
Tayi maganar tana kallon Balqees dake kwance Abba kuma ya kalli Sultan tare da cewa,
    "Sultan meke faruwa da ita ne?!"
    "Abba ban sani ba nima amma tace min wai sunajin tsoran gidan ita da kaka har tana cewa na kwana a gidan nace mata a'a sudai yi addu'a toh kuma muna magana sai kawai na juyo na ganta ta sume shine muka taho nan."
    "Tsoran lafiya kuma, mu dai gaskiya babu abinda muke jin tsoro ita dai tasan menene ya bata tsoron."
Hajiya kaka ne da Sultan suka kwana a wajanta sai misalin karfe 7:20am sannan Balqees ta farka,a hankali ta dinga bin d'akin da kallo can ta hango Sultan zaune akan wata blue d'in kujera yayi sama da kanshi sannan ya janyo hular shi ya d'orata ya rufe idanunshi kamar me yin bacci babu abinda ake gani a fuskar sai kwantaccen kwata million d'inshi da yake bakikkirin mai laushi hajiya kaka kuma na kan sallaya sai faman zabga gyangad'i takeyi sai tayi d'an tari wanda yasa Sultan saurin zame hular ya waigo dan ganin ko itace karaf suka had'a ido hudu ya k'arasa wajanta da sauri.
    "Baby sannu ya jikin naki ya kekiji yanzu?!"
Maganar shi ta janyo hankalin hajiya kaka tayi saurin mik'ewa itama ta k'arasa wajan su, dai-dai lokacin kuma aka bud'e kofar aka shigo babu ko sallama duk suka juya ga mamakin su Yusif ne ya shigo har ya k'arasa ciki basu dena kallonshi ba, Sultan ne ya fara d'auke kanshi ya maida shi wajan Balqees tare da cigaba da tambayarta yadda jikin nata yake. Ido kawai ta kura mai ba tare da tace komai ba,zama yayi a bakin gadon yana kallon yadda ta kafeshi da ido muryar Yusif ta katse musu kallon yana cewa.
    "Ayya my wife too be ashe an binciki file d'inki sorry kinji dear."
    "Wai kai yaron nan wane iri ne? Koh banace karka sake ce mata wife d'inka ba?!"
     "Ohh haka akayi fa, amma nima nace kidena hanani fad'a tunda idan ban aureta ba ai kema ba auranta zaki yi ba."
    "Ubanka kake gayawa haka mara kunya fitsararre kawai."
    "Naji na kuma san bakin ciki kike yi mata sabida ta samu miji ke naki ya mutu."
    "Wify to be wai meyake damunki ne haka har kin d'an fad'a kinyi k'ashin wuya."
Ya maida akalar zancen akan Balqees,kallon shi kawai tayi amma batayi magana ba sai ma maida idonta da tayi ta rufe Sultan ya tashi yana cewa,
    "Tashi kiyi sallah gashi dama ko sallar isha'in jiya bakiyi ba."
Da kyar ta iya mik'ewa sannan hajiya kaka ta rakata zuwa toilet d'in cikin room d'in, shi kuma Yusif duk ya damesu da surutu sai dai in na dariya ne sai Sultan yayi murmushi amma hajiya kaka sai dai ta tab'e baki dan yanzu d'aure mishi fuska takeyi taga sam be iya wasa ba komai ya maidashi gaske ga fad'ar magana gatsal.Sai da ta idar sannan ta rab'a kusa da hajiya kaka cikin mamaki tace,
    "Kakus meyasa aka kawo ni nan?!"
     "Karki rainamu mana muma ke muke jira ki farfad'o ki gaya mana abinda yasa ki doguwar suma."
     "Suma hajiya kaka?!"
Ta fad'a cikin razana da dafe kirji,Yusif ya matso kusa da ita tare da kashe mata ido d'aya sannan yace,
     "Wifey to be meyaja miki sumewa ko markina kikayi jiyan?!"
Satar kallon gefen inda Sultan yake tayi gani tayi sam ba gurin ma yake kallo ba ya juya ne yana kallon wata poster dake manne jikin tiles d'in d'akin sannan ta juya tana kallon Yusif tace,
     "Haba broth Sufee wannan wane irin magana ne haka please banaso ka bari dan Allah."
    "Olrt na bari amma kinsan dai dole ne na kula da abinda nakeso kuma Matar da zan aura ko?!"
Tsaki taja a hankali yadda babu wanda yaji sannan ta kwantar da kanta akan cinyar hajiya kaka tana tunano maganganun Sultan na jiya yadda yake kwarzanta Nadiya nan da nan zuciyarta tayi zafi ta dafe wajan tana rintsa ido, a kid'ime Yusif ya dawo gabanta yana cewa.
     "Lafiya dai ko wifey?!"
      "Lafiya lau."
Ta fad'a da kyar ji take kamar ta nausheshi sam batason ganinshi sabida yana sa zuciyarta kuna,Sultan ya k'araso tare da cewa,
     "Bari na sanarwa da Dr Auwal sai yazo ya dubaki."
Yana kaiwa nan ya fita,ba jimawa sai gasu sun taho tare nan ya dubata yayi mata tambayoyi ta bashi amsa wadda rabi duk ba gaskiya bane dan ta b'oye ainahin gaskiyar lamarin sabida batason su gane tafison wanda takeyin abin danshi ya gane inda tasa zuciyarta da haka Dr Auwal ya rubuta mata magunguna sannan ya basu sallama Sultan yayi mishi godiya sannan suka kimtsa Yusif da kanshi ya maida su gida yanata jiddadawa hajiya kaka zancen auranshi da Balqees din sai dai har ya kaisu bata kula shi ba.....

Post a Comment for "TATTALINTA CHAPTER 2"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...