Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

SAKAMAKO CHAPTER 9

SAKAMAKO CHAPTER 9

- - Post a Comment
SAKAMAKO

CHAPTER 9Wannan tunanin ta ke juya wa har ta cika 1 full week agidan mumy wanda ke faman bata baki da karfin gwiwa... +

Gaba daya take jin ta tsani kanta ..why did she not have taken her marriage serious before???
Gaba daya ta kasa gane makan ta it feels like Tana cikin mugun halin na dama da bacin rai..

Its clear to her that wata macen da bata kai ta goge mata shoe ba ta zo ta karbe mata komai da komai na rayuwan ta.. 1

Suhan is living All her dreams now ..

Abunda ke dada cunkushe mata zuciya shine in ta dubi yadda majeed ya dawo akan suhan she just feel like she dont even stand a chance anymore bare suyi competing gani take gaba daya bai gani bai kuma ji akan suhan so me ma zatayi ta birge?...

Ta soma cin abinci amma ba sosai ba..so ranar da mumy ta sanar mata cewa majeed zai zo ya yafi da ita ..ranar ta zo mata da wata shawaran data yanke makan ta..

Mumy na zaune ta shigo...

Tace mum kina so na?

Ta dago ta kalle ta irin wannan wani irin maganan banza ne...

" im serious mumy
Maganan da zan gaya miki ki dauka babu wasa acikin ta i really need to do this please help me mumy bana so na koma gidan majeed akashe da bakin ciki..i can't ta dan fashe da kuka gwanin tausayi...

"mumy ta jinjina kai cikin tausayi yarta she knew zarah is very well disturbed"'tell me zarah kiyi magana koma meye ne wallhy zan yi miki shi ke kadai nake da shi a duniya stop this" ki dena kukan nan haka ... Now,oya
Fadi ena jin ki

Sai Ta dan goge hawaye ta nitsu" mumy ena wannan mutumin daya taimaka mana lokacin da majeed bai sona din nan tun ena hong kong ..mumy tace duguri?
Boka duguri kike magana

...tace yeah wataeva mum...

"Me zai miki kuma zara ? Ko kina ganin zai taimka ki samu cikin ne..tace mumy ni ba wannan nake so ba gaskiya bazan iya wasa da rai na ba dovtor yace zan iya mutuwa...
Sai ta dan yi shiru can ta dago tace
"I want her out of my house bana son ta da abunda ke cikin ta su rayu da my i want her far away from us..ena so nayi rayuwa na daga ni sai majeed kamar da chan.

Mumy ta gwalo ido surprisingly tana binta da kallon this is ridicoulous" "amma bata kula ba a dame ta kama hannun ta suna facing juna tana kan mata bayani
"mumy,kinga muddin Suhan tana cikin gidan am just equal to nothing to majeed ....mum dan Allah ki fahimce ni i need to do this...

Mumy ta danyi shiru ta jinjina "tace are sure about this ? Bana so na kawo miki shawara ne daga baya kizo  kice ai kece....

Amma in kin shirya hakan nima a shirye nake don bana kaunar yarinyar ko kadan...

Ta dan yi murmushi tace am sure mumy ni dai yanzu ki samana rana muje na gaya masa me nake so ayi mata

....mumy tace toh shikenan

Yanzu kika fara tunani kamar mace kije ki shirya  tsaf kema dole ki nuna masa kin hakura kin karbi qaddarar bazaki haifu ba

Kinga bayan abubuwa sun wakana akwai zargin ko kece:" u will always be the no 1 suspect tunda kowa dai yasan baku jituwa musamman ma shi majeed din...
tace toh mumy bari naje daki ni nasan mezan yi
Akan wani katoton gheto street na bayan gari take kwance arigingine akan wani katon kazamin bola ... +

Bayan gari ne  sosai amma ba nan nigeria bane yana ta chan  wajejan niger so the place is dry and scary...

After like 2hrs ta farka ta tashi cos mutane har sun soma cincirondon kallon ta ga katoton ciki akan bola tana kwance...

Ciwon kai da daurewar tunani ya sa ta riko kan ga tana shakar wani gwamutsatsun wari..

Gefe da ita taci karo da wani kazantar kashi ne danye ga rubabben kayan gwale sai fararen tsutsa suke fitarwa ....

Bata cikin hankalin ta amma ta mike a firkice ta soma dube dube ...

She can't even talk bare ta tina wani abu ita dai kawai tana nan ne amma kamar bata nan...

A sanyaye Ta sauko kan bolar tana waige waige mutane sunan binta da kallon ko mahaukaciya ce

Bata kula ba ta tsakura cikin su ta wuce....tafiya take abunta babu takalma duk inda ta samu inuwa sai ta huta kadan ta tashi ta cigaba...

Gefen su Majeed kuwa tun dawowar sa yake faman neman ta amma shiru...

Abu wasa wasa hankalin sa ya soma daguwa dukan possible place da yasan zataje ya tambaya
..asibiti gidan mum har chan kaduna ko ena ya tanbaya amma kowa yace bata leko ba

STORY CONTINUES BELOW

Its now 2pm in the noon..ya kasa zama ya kuma hana kowa shan ruwa yana so yaji ena suhan ta ke tun safe?
Gaba daya yake jin tashin hankali a ransa sai ya tsanan ta ma kansa abun

Haka Kowa yayi tsuru tsuru a gidan  baya so ya kawo wani negative tots tukunna amma sai ya bada time yaga ko zata dawo ko bazata dawo ba

yana dame ne amma ranshi ya baci yace "toh lallai in suhan ficewa tayi bata sanar da shi yau ba koma miye daliliin ta sai ya mata fada sosai"

Don haka kawai yake jin bugun zuCiya  ....

Daga chan kuma yawo take ba kama kafan yaro ga yunwa ga kishin ruwa shes very beautiful and fresh shiyasa kowa yake noticing dinta...

Amma ya nayin yadda take acting sai kawai ake mata kallon mad woman wani bin hankali yakan zo mata wani bin kuma hauka take yi muraran

Daga karshe yunwa ya sa ta rakube a wani gefen rijiya tana karkarwa tana fida ido waje ta soma kuka
Gwanin tausayi "yah Allah" zuciyan ta ke fada cikin tsananin neman taimako bakin ta na rawa...

tana so ta tuno kanta amma ta kasa da kyar wani yaro ya bata ruwa ta sha ta koma gefe gindin bishiya ta shiga deban baci mai nauyi nan akasa bata ko damu ba..


6..7..8..9pm na dare lokacin majeed har ya gama zaga ko ena agarin abuja bai jiyo qamshin ta ba bare mai kama da ita

Zarah ta san hakan zai faru dole sai ta bashi fili yaji da haukan rashin suhan da zaiyi kafin ta sa ya mance da ita kwata kwata su cigaba da rayuwar su

Daga cikin masu tsaro a gidan Kowa sai da yayi barin baki hatta wasu maids din sosai suka razana da yananyin yadda yake interogating dinsu da kakausan muryan tashin hankali ....

He blame them out of tension yace ba wanda zai huta sai an nemo masa matar sa....

Ko bacci baiyi ba haka ma a gidan zarah kawai ta ke harkokin ta bata ko damu da abunda yake ciki ba..hasali ma tunda tace masa Allah ya kyauta bata kara tahowa enda yake ba....

Abu wasa wasa akaci 2days babu suhan sai da mum ta bata rai ta tsawatar masa kafin ya kyale securites dinsa suka samu nitsuwa ..no body think he can be this restless and hard lokaci guda..

Ita kanta mum ta kwana bata iya runtsawa maganin hawan jini ke sa ta baccin dole.

Ga anty jamila tana kira akai akai tana so taji ya ake ciki..

Yadda itama ta daga hankali ma ya sa bai kawo tunanin ko suhan na tare da su ba

He cant fight the feeling idan ya zauna sai  yayi kuka yana tambayar kansa ena ta shige ta barsa  har kwana biyu"
He feel miserable ko abinci bai dubawa bare wani abun...


Bayan sati guda lokacin mum ta dawo zama da su dan dole majeed na neman fita a hankalin sa kuka ya ke sakewa ya mata muraran  sai ta rarrashe sa sosai kamar karamin yaro kafin take samun kunne"

Ba bata lokaci ya sa 15millon naira cash a media wa duk wanda ya samo masa ita ko labarin ta aka bada pictures ko ena ana kan rubibin abun...

Da kyar zarah ke duba shi cos yanzu take dada gaskatawa aranta cewa suhan is the only woman in his life ba karya ...

Tace zaka ma kaji ka bari"ai da chan babu ita arayuwar ka ni ce

ranta na baci in tana duban shi a duk lokacin da ya ke bacci a takure  ga sallaya anan gefe a kasa alaman sallah yakan yi yana rokon Allah

Daga chan niger suhan is now becoming familiar a anguwar da take har ta soma sanin yadda zata nemi abinci ta ci komin kazantar sa komin kashin sa

She is now dirty duk ta dawo kalar hauka cos akasa take kwanciya a duk enda ta yada zango...

STORY CONTINUES BELOW

A satin ta na biyu da barin gida ranar tana kan tsine tsinen ta akasa tana neman abunda zata ci
har yau dai ba wanda ya san ta sai za tayi kuka kuma ake jin sautin ta ko dai tai alama ko mutum ya mata hannu ta wannan kam tana ganewa sosai....

A kwana a tashi ta shiga target din bad boys na wajen cos bayan gari ne nan din ma wasu yara maza bata gari suka jawo ta da sunan zasu bata abinci bayan sun lura ta galabaita gashi da kyar take turo 8mont old pregnacyn ta koda yaushe tana tafiya abun a tausaya.

Sukam basu damu ba they want to have sex with her kamar yadda suka saba ma mahaukata mata wasu har ciki sukan musu

(Allah ya kare dukkan musulmi daga irin wannan musibar cos yafaru na gani sosai ana ma mad women fyade har da ciki kuma Allah ya shiryu masu aikata hakan ameen) 3

Ranar suka taru mata suka toshe ko ina suna mata dariya is the fisrt day she started crying heavily tana neman taimako

...ganin idon ta ma kawai zai sa kasan ta tsorata bata da hankali amma ta fahimci komai raping dinta zasuyi...

Bata da muryan ihu sai ta soma wasa da su tana zaga wa tana kuka sosai...

Dariya suke irin nasu na riakkun yan daba suna maganganun su na yan shaye shaye ...

Dayan ya ce tunda su hudu ne su mata irin na indian films su bata hanya ta soma gudu sai su cafko ta su aikata ta turn by turn..

suka kwashe da dariya sai suka bata hanyar guduwa.

Tana kukan a tsorace ta zame ta gudu tana waige sai binta suke da dariya sun san ba inda zata iya zuwa duk anguwar  ansan su...

Dayan ya daka tsalle yace gaskiya ya isa haka lokaci yayi bari na kamo ta ya sa gudu zai kamo ta a razane ta sabule tafado jikin wata mata....

A hujajan ta dagon kai cikin tsananin kallon magiya da fiskan tausayi gashi babu voice sai ido take fiddawa tana hawaye alaman a taimake ta ...
Gam gam ta rike matar tana karkarwa tana kuka mai cin rai da ratsa zuciya

Tallabe" bata da imani ko kadan amma ranar saida taji digon imanin wucen gadi ya shigo mata ranta"sai taji suhan ta bata tausayi

"Tuni gayun nan suka zo gaban ta suna bata kallo in respect of teritoriality sun san tallabe uwar su ce a harkan mugayen aikuyaka da kuma ta'addanci

Ta sa suhan a bayan ta tace " kai...ku baku da imani ne me zakuci anan mata da katon ciki ai babu sauran abunda zaku lasha...

Uselessly daya daga cikin su ke mirda murya yana kukkuni yace" haba oganniya tallabe kekan ki kinsan yanzu irin wannan muke so wanda ruwan dadin su ke kasa kasa ai daga ganin wannan ma zata yi dadi...

Sai su ka maida abun joke "me ye sa kike haka ne ehhh kawai ki mana ita mu shana

Suhan ta kame rigar ta tana labewa a bayanta tana rawan dari kamar wacce take gane abun da suke cewa"
Matar tace "anki a baku ita shashun banza kawai..
kan na bude ido kar na ga kowa anan ko na fyede cikin yaro...a tsawace ta fada tana basu mugayen kallo

Ba musu suka watse suna ja mata Allah ya isa aran su

Kafin ta juya ta kalli  suhan already tayi tsuguna kasa kan gwiwar ta ta hade hannu waje guda alaman godiya tana kan bulbulan hawaye masu taba zuciya....

Tallabe tayi shiru She felt her pained itama mace ce..sai ta soma tunanin me yakawo wannan kyakkaywar mace nan wajen kara zube?

Bata tsaya dogon nazari ba ta kamo suhan ta tafi da ita gidan ta...
Anan take observing dinta tana bata abinci da sauran su har ta soma declaring binciken ta cewa suhan ba yar kasar bane ma kwata kwata...

STORY CONTINUES BELOW

But she want to protect her daga irin wannan abubuwan altho gaskiya imani ya mata kadan a zuciyan ta...

Gashi suhan bata magana bare ta tambaye ta labarin ta ko ashirme ne ta gaya mata ta lura wani bin hankali yana dan shigo mata..


Wasa wasa suhan ta dawo yar gidan tallabe 3weeks kenan da ba tan ta a nigeria
Takan je deban ruwa ta dauko karamin baho akanta da cikin ta dawo gida da shi..

Akan sata wanki da shara da sauran kanan aika..
In exchange kuma tallabe tana bata kariya da abinci da sutura tana sawa.

Ranar da ciki ya kai  9month cass suhan ta soma zazzabi sosai 
It seems like abunda ke cikin ta ke son motsawa amma aljanun sun riga sun rike dam sun hana haihuwar

Lokaci lokaci take nakuda amma sam babu progress in yayi ya bata wahala sai su dauke abunsu ta dawo normal tana aikin ta...

Majeed was hospitalised 
Sati guda yayi ana sa masa ruwa

A kulli yaumin sai ya sa an kara amount na kudin da zai bayar anemo masa ita amma shuru ba labari

Mumy rabiatu kulluma sai tayi masifa ma zarah
Akan haukar da majeed ke yi akan batar suhan"

zarah tace ai baki ga komai ba mumy a hakan ne za ace na zauna da ita ni bana haihuwa ki fa dubo yadda ya kwallafa ta arai 
na san ba don mum dinsa tana tare sa ba wallahy da ya shiga duniya zararrre "

mum kinsan ranar dana je wai zan gwada bashi baki na rarrashe shi kula yake yana roko na na gaya masa ko ni na boye masa matar sa ? Wallahy wani maganganun da yake fada min har yana sani fargaba i dont know that abun nasu yakai haka...he actually lost his mind i think he's  his menatally ill "har cewa shikam mutuwar sa kenan ta zo masa muddin bai same ta he cant go on...
'arrghhhh Ouhhh "i was so embrassed "akan cinya na fa yake fada min zai mutu akan wata mace" ta fada a raunane cikin dacin rai tana tabe baki'

Mumy ta tabe baki cikin kuna rai itama tana girgiza kai..tace tabb di jam
...aiki ja akanku..Allah ya sawwaka wannan ai sakarci ne da rashin tarbiya sam majeed din kun nan baida kunya ko irin jarumtar nan ma na maza bazai yi ba sai kace ba cikakken soja mai matsayi ba? Hmmm ikon Allah tabbb

Zarah tace ohon masa "aikuwa zaiyi ya bari he cant live on like this sai na san yadda zanyi ya mance da ita ni sun ishe ni harga Allah...

Mum tace yawwa ya ake ciki kin ji wani kotsi daga wajen boka...

Ta dan yi dube dube tace " mumy dama maganan da nake so muyi kenan dake..kinsan me?wannan abun da boka ya bani ranar yayi min magana amma kinsa inform of dream ai yake zuwa ko..

Tace ehhn so what?

Tace "cewa yayi suhan na labour amma sun rike haihuwar tana chan wani gari tana hauka ...

Mumy tayo murmushi

Tace amma kinsan nawa ya sa na ajiye masa...?
tace noo 
Check ta zaro a jakan ta na zunzurutun kudi naira milliyon tamanin...
mumy ta daura ahannu aka tace 
Wayyoooo Allah na wannan uban kudi"
Akan me? gaskiya  hakan baiyi ba ai abun yayi yawa wannan ma da kashe ta akayi kowa ya huta.. 1

Zarah Ta firgita Tace shhhhh mumy ki dena cewa haka ..kinsan fa ance zamuyi facing atrosities da yawa idan muka karya namu alkwarin so pls calm down..da na shiga a harkan yankan kan mutane ba gwara ena biya ba ?

Mumy bata ji dadi ba amma sai ta daure kawai ta ce toh shikenan amma gaskiya kudin yana yawa mu bamuci ba ana ba wani shege ai sam haka baiyi...

Sai gwaff wani abu ya fado kan kafarta lokaci guda wajen yayi baki ya soma haurowa kamar kurji 
duk suka rude suka birkice..
Wayyoh wayyoh

STORY CONTINUES BELOW

A rude zarah tace Mumy ena ga sune suke warning dinki? Kingani ko 
Ai saida nace ki bari zanyi kin ki yin shiru

a rude muny ta shiga bada hakuri tana kuka tana cewa bazata sake korafi ba su cire mata abun 
Lokaci guda suka cire mata ta dawo dai dai

Minti 2 bata kara ba ta dau jakar ta ta tafi ta kyale zarah anan...

Ranar suhan na deban ruwa tallabe ta zo ta kirawo ta...
Keken a kori kura ta daura ta akai ba imani kukur kur  suka  kai bakin wani hanya...

Manyan manyan motoci ne sosai na safaran kayan cash crops da economic goods...

Hannun wata mata ta damka suhan tace bani kudi na ga mace nan harda ciki...
in ta haihu riba biyu ga abun cikin ta ga sabuwar karin kasuwanci ...

Matar ta kalli suhan da kyau sai zare ido take ..ta dauko kudi mai shegen yawa ta ba tallabe ta juya abinta..

Kuka suhan ta fashe da shi gwanin tausayi tana bin tallabe ana rirrike ta amma sam tallabe taki ta juya baya ma bare ta kalle ta don tasan suhan ita ce mace na farko data so ta dawo mata da imani cikin zuciyan ta

Hakan matar nan ta ma suhan karfi da yaji ta sa ta a mota  suka kama tafiya ...

Tayi kukan har ta gaji ta dawo tayo shiru ta rafka ta gumi

After a very long jouney ta bude ido sai gasu awani waje daban wanda aka fi sani da lagos nigeria...

Anan ma a bayan gari suke 
Sunan new madam dinta madam kande ice

A gidan ta ake sayar da mutane iri iri akan ko wani farashi inma karuwanci zaka kai su bata damu ba in ma kashe su zakayi chan maka kayi  alheri da mugun ta da su bai dame ta ba ita dai kawai zaka bata kudi sosai shikenan..

Duk wanda aka kawo suhan da su an saye
Gashi ganin kyau da dirin hallita na suhan ya sa ta sa buri mai karfi a kanta..

Ga abun cikin ta  a kullum gani take suhan Zata haihu amma  sai dai tayi nakuda gadan gadan amma babu haihuwa
Abun har ya so a damun kowa a wajen sosai..

Tun ana mata na bakon ta da tausayi har aka soma share ta

kande ice ta na jira dai tasan don duk yadda akayi watan wata rana suhan zata haihu dan dole.

Yanzu babu mai kulata in tana nakuda nata har ta yi ta gaji ya lafa...

Daga chan kuma duk randa suhan Ta motsa sai  abun nan ya bukaci kudi mai tarin yawa awajen zarah

Kan aje ko ena ta kwashe millions daga acct din ta har wajen guda uku empty..

Gefen majeed kuwa an dawo da shi gida ..

yanzu addua sosai ake yi masallatai da ko ena yau suhan dinsa 1month rabon sa daya ganta....
sai ya dawo quiet da kyar ya sa nitsuwa makan sa

Mum da anty jamila na nan basu gajiya da bin cike da neman taimakon ana musu istihara

Kaf dinsu sunki gaya ma majeed _sakamakon_ istiran... Thy alredy knew batar suhan bana alheri bane sihiri ne mai karfi sukan su malamai basu samu gayan cikaken details din ba

Amma tabbas sun gaya ma mum suhan na cikin mummanan hali wahala da neman taimako

Mum Sam taki zuciyan ta sawa ya yarda tana kan lazimi da ikon ubangijin ta amma da shike kowa abunda ke gani kenan sai abun yayi affecting zuciyan ta  sosai

Shikan sa mjeed bai 
San mum yanzu jinyar ta ake agida ba amma take daurewa take zuwa ta rarrashe shi every day...

  A cahn wajen suhan bakin ciki da kuncin rayuwa ya sa ta sake jikin ta sai yadda aka juyata kowa na aikan ta kamar karamar yarinya..

Sai dai sosai ta shiga ran wani old thug tsohon soja ne wanda rayuwan tantiranci ya masa tatil ya kuma waina sa da kasa ya dawo ya saduda...

Haka kawai yake tausaya ma suhan sosai

Daga bisani ya sa kansa yana kyautata mata

friendly gesture da yake bata ya sa ta ke sakewa da shi har in ta ganshi sai tayi murmushi

....sunan sa oga rabi'u majeh kowa ya san shi har prison yaje
amma shikam jin suhan yake kamar yar sa kuka in yaga tanayi sai yabi mata kadi...

Ranar ma tafiyar ta ke nan yana kan binta da kallon tausayi wani keke napep yayi parking gaban gidan sa

Leke yake yana mika wuya chan ya hango wani mutum jikin sa har na rawa ya sake kara ya daura hannu aka yayo kansa..

Rigar prison ne jikin mutumin so yana juyowa suka rungume juna da ogah rabiu suka fashe da kuka irin na jaruman maza mai ji kadai yasan akwai tashin hankali a cikin ta da nadama......
Dan fulani..dan fulani?
Allahu akbar dan fulani har zamu ga juna ..ashe har zan ganka a raye...

Wanda aka kira da dan fulani kukan kawai yake duk saje ya rife mai gefe da gefen fuskan sa bai iya cewa komai ba.

Yanayin jikin sa da hawayen sa ya na nuna tsananin nadaman rayuwa boro boro har karkarwa yake

Ogah rabiu ya jawo sa suka shige cikin gida..

Da kyar suka daina emotional draman su

"Yace majeh? Duniya labari in baka zo ta ba  tukun kaicon ka,, in kazo kuma halin ka ta ficce ka..

Naga rayuwa rabiu... rabi'u naga jarabawa naga karshe na...ya dada fashewa da kuka.

"Kayi hakuri ibrahim ka dena daga min hankali zuwan ka nan ba karamin babban abu bane..yanzu dai ka samu ka sauya ka yi wanka kaci abinci  ka huta ..in kaji kamar kana  gida ne yanzu wani takaicin ma ai zai ragu 

"ya gyada kai kamar karamin yaro ya tashi ya aikata duk wayannan abubuwan 

Ogah rabiu bai barsa ya huta ba sai da ya dan zaga da shi yayi fes yayi aski ya rage gemun sa ya dawo dai dai 
suka dan zaga suka sha iska bayn sunyi sallah kafin nan suka samu waje a nan a cikin gidan oga suka soma hirar duniya...

"
Oga rabiu yace" har yau hankalin na bai kwanta ba ibrahim..tunda ka samu zuwaira ku ka maida aure ban tashi ganin ka sai ranar da aka kaika kotu akan maganan nan daya kai ka prison..meya faru ne wai kam?
Dan Allah ka fada min na dade ena zaune da ciwon nan araina

Cikin jimami Yace hmmmmmm abun ba a magana majeh..

Amma bari na baka labarin abun talunda ga tushe.

Kana sane dai na bar maryamu da yata suhan achan kaduna na zo nan lagos da dukiya mai tarin yawa da na karbe hannun inlaws dina.

"Yace tabbas..

Yawwa ai bayan nan na zo na samu zuwairah da yaya guda biyu nasha mamaki
..nidai na barta da daya ne wato garba amma sai ga wani wai shi mati tace min ai dana tafi da cikin sa na barta nidai bance komai ba...

dama ni nace zan nemo mana kudi na bata irin life din data ke so...

kasan ta fa ita ta rika azalzala min azaba da fitina akan nemo kudin nan kamin ta zauna da ni
Kuma  a lokacin gaskiya ena son zuwairah

Yana maganan ne idon sa sun gama cikewa da ruwa...ya danyi shiru ya jinjina sannan yace " tabb,... Allah sarki maryam yanzu hala Da kyar ta yafe min na cutar da ita na cuci kaina..

Ogah rabiu ba abunda yake sai girgiza kai cikin jimami...

Ya cigaba" yace  toh nazo na saida mutuncin yata arha na kuntata ma matata mairo na tafii na mance da su don na faranta ma zuwairah..

STORY CONTINUES BELOW

Da farko dai data ga uban kudin dana zo dashi rimi rimi take bina tana mun irin biyayyah da kundunbalan su na mata 
Na sake na rika zuba mata suna ci da yayar ta 
Kai... wani namiji ta kawo daga baya ya zo yana zama damu shine wannan joseph da akayi case dina da shi wai aka ce na kashe shi...

oga rabiu yace but how comes? What happend meya maka ka kashe shi

Baba ibrahim ya maida murmushin takaici" 
Su dai su ka lashe ni kaf suka maida ni akuya wawa jaki..

.sai da kudin nan ya kare kaf na dawo banda ko abinci da sutura da nake sawa wallhy a 1omillion din nan ban more ta ta ko wani hanya ba...

Ya ja ajiyan zuciya cos da kyar yake fidda maganan suna masa daci a baki

Yace" amma da kudin ya kare meye zuwirah bata sani nayi ba ..wanki shara.. markade.. tallan doya da kwai ma sai da nayi...ga masifa da cin mutunci

Wallhy rabiu wata rana da tsintsiya take zama tana duka na tana zagi na a tsakar gida ta uwa ta uba ban isa kuma na tanka ba...

Kuka ya fashe da shi anan gaban yace "

wohoho _sakamakon_ abun da na aikata ma maryam ke bina wallahu a lokacin nadama ke dawainiya dani ga tunanin ya ta suhan yadda na cusa mata bakin ciki na rabu da ita ban taba zama mata uba ba"
sai na dawo shasha bana ko iya hana zuwairah ci min mutunci wani irin bakin izaya ne ban gani ba?

matar nan Ta tayyara mutunci na ta tona mun asiri har aron sutura na yi kai satan abinci ma sai da nayi aka shafa min toka aka ci min mutinci kororo kororo A layin kasuwa...

Daga karshe shine na kamata turmi da ta barya da dan iskan da ta jawo min gida wai dan uwan ta shi wannan joseph din ashe shine ma baban yayan nawa dabnake buga kirji akan su...wallhy duk ba ciki na bane na shi ne

Ranar na kasa daurewa raina ya baci matuka zuciya ta debe ni nayi musu kaca kaca jina jina daga ranan na soma tunanin komawa kaduna ko da kafata ne na tuba na nemo gafarar iyali na ama its too late..ni dai nasan ban kashe kowa ba

Suka hade min baki kawai sai naga an zo an kame ni aka laka min laifin kisan kai wai na kashe joseph..na rasa yadda zanyi gashi na shaida da baki na na buge su kaji dalilin da ya sa na nemo ka ranar kenan ko?

Oga rabiun ya kasa tsayar da hawayen dake bin kuncin sa yana kuka mai dauke da tausayi da jimamin rayuwa...

Yace abokina tabbas wannan shine _sakamakon_ mun dau rayuwa mun daura bakar kanya akan mu ..

Amma Nagode ma Allah da ya sake bamu damar da zamu sake yaye wani shafin mu daura wani kafin ya amshi ranmu..

Me ya faru aka fito da kai?baka gaya min ba..kuma me kake tunani yanzu zamu sa agaba naka ra'ayin

Ya jin jina Yace"ikon Allah kawai nagani rabiu..
wato naje prizon din nan ena nadama amma Allah bai barni haka ba ya hada ni da wanda suka san addini suke koya min abubuwan da na watsar..hankali na ya tashi sosai ga mafarke mafarken maryamu da nake yi

a haka na shiga tsundum ena neman yafiya da adu'an samun Sauki da sauyi a al'amura na

ai gawan zuwairah aka tsinta shi joseph din da akace na kashe shi ya kashe ta 
"wai ya ce ta kwana da uban sa akan gidan gado da yake so ya karbe ya hana yanuwan sa sai  taki shine ya mata dukan mutuwa

Bayan nan Ai bai samu yayi escape bane aka kama shi nikuma aka bada izinin Asake ni..

Ya sa hannu ya dauko wani ledar poly bag daya 
Zo da ita a dunkunkune yace ka ga wai compensation nan dubu dari biyu an bani daga kotun bayan gari..

.naji kana tunanin me zamuyi nan gaba kaga sai mu nemi nakan mu muyi sana'a mu cigaba da rokon Allah ya yafe mana..

Sai dai kafin nan zanje kaduna na dubo su maryam koma yaya ne na nemi gafarar su kafin nasan matsayin rayuwa ta...

STORY CONTINUES BELOW

Ogah rabiu yace wannan duk yayi Allah ya shige mana gaba....

Anan suka zauna hira sosai sukayi daga bisani ya na dan karfafa masa gwiwa har suka kwanta bacci..

duk kwanakin nan suna gida suna shan labaran duniya da suka fuskanta da nadamar su suna kuma dada kawo shawara ma juna yadda zasu kai kansu next level

  After 3 days suhan bata fito ba baba rabiu ba shima bai ganta ba

sai ranar bayan ya raka abokin sa ibrahim dan fulani tasha zaije kadunan kafin ya hango ta riki riki da aikan nika zata kai engine surfe sai ja take da cikin ta gwanin tausayi

Ya zo ya karbe daga hannun ta yana mayar mata irin murmushim data saba sakar masa mai alaman gaisuwa...

Its seems like yana mugun ganin kamar ta da matar abokin sa maryam amma he cant say"

Shi ya taimaka mata as usual ta kammala komai sannan ta shige gida..

Tun daga nan sai Shiru shiru baiji labarin suhan ba bare mahaifin ta da yaje kaduna nemo du da ummah..

Baba ibrahim Ya sha wahala sosai cikin kwana ukun don
Babu su babu labarin su gashi mutanen da ya sani kowa na jan jiki da shi suna wulakanta sa  da kyar aka masa kwantacen shamud residence yaje nan ma akargame sai uban securities

Their personality Is higly confidential musamman ma da capt majeed ke wani halin tashin hankali yanzu

iya bayani yayi akan yar sa ce suhan .kuma ya zo nema amma sam suka ki ma daukar maganan sa serious bare su gaya ma har aje ga fada ma majeed

Duk sun dauka irin mutanen banzan nan ne da ke zuwa da karareyan su don sunga kullum majeed na doubling millions akan wanda ya samo masa matar sa a media..

Da baban suhan ya matsa sojoji suka kama shi suka zane shi tsaf da dorina suka bashi purnishment da kyar wani ya tausaya masa ya fitar da shi daga wajen ya kaisa har tasha

Yace masa wallhy bazan maka karya ba..yata na aura ma mai gidan ena so ne nagan ta dan Allah..

Securityn yace baba babu wanda zai yarda da kai saboda akwai matsala yanzun da aka  fuskan ta

Ita wanda kake neman ta bace yau wata guda kenan kuma ansa kudi mai tsoka ma duk wanda yakawo ta da rai ...

mutane dayawa sunzo nan da karya kala kala 
Wasu ma na nan akulle ka rufa ma kanka asiri ka tafi kawai Allah ya baka sa"ar abunda kake nema

Wani irin Shock baba ibrahim ya shiga" suhan taba ce? Ya daura hannu akai yana salati hawaye ne na ban mamaki ke masa ziriya akan fiskan sa "yace shikenan ni na salwantar da yata gashi ance maryamah ma ta rasu ba san inda makwancin  ta take ba ...

Ya fashe da kuka a rude yana nadaman abubuwan da ke dawo masa a ransa...

Babu yadda ya iya adaddafe ya samu ya komo lagos..

Kwana ukun suhan itama ta kwanta its like na kudan kwana uku tayi ajere hade da wahalhalun ayyukan data keyi sai abun na neman mata illah sosai ko motsi bata yi tana kwance tana wash wash ba mai zuwa kanta bare ya taimaka mata

Daga chan kuwa agun boka ya sa zarah agaba da bani bani shes runing dry kudin ta ya zabge kasa sosai..

Har ta soma ganin wanda ya rage bazai isa ta bashi ba gashi ko da wasa bata so ta tambaye majeed kudi

cos suna dan fada dashi akan watsar da ita da yayi ya salwantar da lokacin sa dukiyar sa da tunanin sa akan bacewar suhan.

Which left her with no choice kawai
Sai tayi signing wani deal a wajen aiki  akan xata dauko kudin su duka ta biya makanta bukata ta ajiye gidajen ta da duk wani qaddarorin ta sa colateral security.

STORY CONTINUES BELOW

Aranta tana so in aka gama wannan watan zata sake kai ma boka bukatar a shafe suhan a brain din majeed da mum don abun nasu ba sauki
Daga nan sai ta fisge dukkan kudin ta da ta salwantar wa boka daga wajen sa su koma dai dai...

Zaazabi ya rufe baba ibrahim tun daga mota yake jimamin wani irin rayuwa ya sa suhan" ko dai an kuntata mata ne ta gudu kamar yadda ya kuntata ma mahaifiyar ta..yasan yarsa ta shiga kuncin rayuwa tunda har ance maryamu ta rasu ta bar ta

...abun nan ya mugun daga masa hankali

Ko da ya dawo lagos sai da ya dau kwana biyu kan ya samu kansa a sarari..

Har akaci 1 week Ranar suna zaune gindin bishiya oga rabiu ya ga wilgawar wata daga yayan kande ice...ya mata hannu tazo.

Yace mata dan Allah ena tambaya ne"

Tace Allah sa na sani
Sai Yayi kwatancen suhan yace kin gane ta? Tana da ciki sannan bata magana naga kwana biyu bana ganin ta shin ko bata nan ne?

Tace aiyoooo yar fulani mai ciki... ai tana nan cikin ke mata ciwo shiyasa bata ma fitowa  ta dae kwance a gida

Yace Allah sarki...toh nagode 
Ta juya ta tafi

Baba ibrahim yace wacce kuma wanann ?

ogah rabiu yace ai wata yarinya ce wallhy abun tausayi  aka kawo ta nan enaga daga niger ne

Kar ka ganta kama ya baci da matar ka maryam ga ta ga tsohon ciki amma kurma ce bata magana..
gaka ma ko sunan ta bamu sani ma suma yan gidan kande ice " yar fulani mai ciki suke ce mata

Yayi shiru yana jin sa cos Haka kawai yaji kirjin sa ya buga amma sai bai bada wani strong reaction ba yace Allah ya bata lpya..

Daga lokacin ogah maje ke neman hanyar da zaije ya duba suhan yasan anan ba bu wan da zai taimaka mata..
gashi yarinyar ta shiga ransa sosai..

Baba ibrahim na lura da shi wani bin har ya tambaye sa meyasa ya damu da ita hakan?

Shi dai Yakan bashi labari mayuwacin halin da yara da mata yan mata ke shiga ne a wannan kazamar harka na gidan hajiya kande ice 
Duba da suhan nada ciki ya sashi yake mugun jinjina ma al'amuranta atunanin sa da ma ace tana magana da da sauki..yana tausaya mata..

Wasa wasa abun ya soma shiga ma baba ibrahim kwalkwa shima sai ya ce toh me zai hana muje mu duba ta?
Kuma hakan ne..

"ogah Yace bai sani ba amma suje din dai

Da yamma wajen karfe 5 saura suka kama hanyar gidan kande ice ko rabin da kofar gidan basuyi ba saiga suhan ta fito riki riki a wahale ta zube kasa tana kwaza amai...

Tayi ta sake yi ta rike cikin ta hannun ta sai karkarwa yake she's in pain sosai ba sai angaya ba zaka gani a fuskan ta...

Ogah rabi'u yayi saurin zuwa gaban ta lokacin kanta nakasa yana jera mata sannu sannu..gwanin tausayi take kukan radadin azaban labour

Babu kowa anan gidan sai dai dai kun mata da basu ko nuna alaman kulawar su ga ita ba

Baba ibrahim ya debo ruwa a cup ya zo da shi zai bata ta wanke baki ta dan sha

... He looked at her lokacin bata dago ba tana faman amai a ranshi yace lallai abun tausayi ne gata karamar yarinya ga tsohon ciki

Cikin tausayi yace sannu ko.. ga shi wanke bakin ki"
wanii zuuuttt taji a kunnen ta
Ta dago a firgice da wani irin ido mai razanarwa

Jin muryan sa ya dan girgiza tasirin asirin

"Bushewa yayi a tsaye cup din ruwan ya fadi hannun sa  kasa ruwan ya fancama

STORY CONTINUES BELOW

Kallon sa take tana neman tuno wani abu amma ena bazata taba warkewa Ba sai majeed ya kira ta ta amsa

A hankali Ta ke maida numfashi ogah rabiu ya wage baki na kallon su suna maida ma juna kalon kalon in shock and intense feeling na an dade ba a hadu ba...

Hannu na rawa Baki na bari jiki na karkarwa baba ibrahim yace" suha..nnnn..suhan..yata suhan ya kamo ta ya soma girgiza ta ..

Bata gane sa ba again amma ta san tabbas shi din wani abun ta ne Kuka ta fashe mai 
Da shi mai rauni ta fada jikin sa ta rungume sa

Kowa sai da ya taro hankalin sa waje guda yana kallon su suna kuka tare "

Babu wanda ya iya tare hawayen sa musamman lokacin da yake neman ta gafara kamar zautacce itakam bata san ma meyake yi ba amma she's feeling differnt bata kuma magana...

Yace rabiu yata ce..suhan ne fa wannan itace...

Ogah rabi'u ya kam tini ya shiga godiya ma uban giji..

Abun gwanin tausayi yana kan shafa yarsa cikin kula yana bata hakuri yana neman ya kamo ta su tafi yana cewa na dawo gare ki yata ..bazan sake tafiya na barki ba ki zo mutafi...

Ya riko hannun ta suna ficewa Daga bakin kofar gidan aka taro su

Kande ice ne da boys dinta tace: tace "dakata malam ena zaka kai min kaya na..

Yace kayan ki?
Toh yata ce kuma tafiya da ita zanyi...

Tace wallahy baka isa ba..kutuman uban chan kai waye?

Babu wanda ya isa ya zo nan ya dau kayan dana saya da kudi na yace zai tafi da ita..

"boyyys tayi tsawa anan kake ganin adduna da wukake har ma da bindiga na fita daga jikin su "abu kadan ke tsorata suhan sai ta koma boya a bayan su ogah maje da baban ta

Haka fir kande ice ta turje 
Gashi sun san tana da kyakkwan alaka da hukuman garin ba halin kai kara police station..

Don dole aka buga yarjejeniya kwana biyar ana kai kawo akan zata musu sauki karshen sauki kenan zasu bata dubu dari 300 da hamsin

Haka ya fasa taba kudin da ya samu altho sun ci wani abu daga ciki

Suka hada karfi da karfe suka sake raising almost 100k  da kyar da cin bashi suka saye suhan a hannun kande ice..

Tsaban son su nisantar da ita daga wannan waje ya sa suka sayar da gidan su suka koma chan cikin wani kauyen wajen boader state din lagos suka samu simple flats two bedrom da bayi daya da kitchen suka zauna..is poor but managable.

Anan ya soma tunanin yadda suhan ta dawo haka

Yayi observing dinta ta yana ga kamar bata gane sa sosai ba..shidai kullum sai yayi kuka yana neman gafarta

Ogah rabi'u da kyar yake karfafa masa gwiwa

Suka yanke hukuncin zasu kai ta wajen neman lpya ta dawo dai dai suji kan labarin ta kafin ya sanaar da cewa ya tsince ta 
Don sosai suke jin labarin a bakin wasu mutanen in sunje gari
Sai dai basu san asalin gaskiyar lamarin ba
wani bin sai yaji kamar ya mayar da ita abuja gidan mijin ta wani kuma sai yaji kar yayi garaje ya sake tafka kuskure

Tsoron sa har yanzu kar dai muzguna mata ake gidan daya aurar da ita ta samu ta kubuce

Don yaga alaman yarsa ta wahala sosai..and he bow not to eva let that happen again sai ya daura kyakkwan niyyar ajiye ta ya mata jinya kawai suji kan gaskiyar lamari daga bakin ta kafin su yanke hukunci ko wani next action...

A haka suka mike hujajan da sauran karfin su sukan providing mata komai kamin su fice
Neman aikin da zai basu kudin da zasu yi jinyar ta..

Zarah ta shiga aiki gadan dagan da kudin kamfani
Abu yaki ci yaki karewa
Sai dai improvement daya shine yanzu majeed baya koke koke ko ciwo idan haukan ciwon suhan Din ya taso masa sai dai yayi shiru kamar wanda ke cikin kuncin rayuwa..

Amma baiya kula uban kowa he always want to be alone

Mum tayi masa fadan har ta gaji ta kyale sa ko meeting baiya zuwa
iya kaci idan zuciyar sa ta masa nauyi ya dauro alwala ko ya karanta qur'ani ko yayi ta salloli ya na neman Sauki daga Allah...

Zagi ya sha sosai wajen zarah musamman yanzu dabai amsa ta...

She cant even remember ranar da taga smiles dinsa bare kuma har su hada gado.

Gashi she is frustarated 
Kudi fa na mugun tafiya 
Suhan dai ta bar rayunta amma she is not happy at oll.

Daga wajen majeed babu dadi...mum is always promising her zata masa fada yana bata hakkin ta since suhan is nowhere amma shiru

Mumyn ta achan kuma tana zugata ta biya ma boka da abunsa bukatun su don kar wani abu ya same su don suna jin labarin suhan bit by bit daga bakin aljanu

"Daga business dinta kowa ya sa mata ido yana jira ya ga wannan massive movement da transactions na cash da take yi me take zuba wa

Gashi yanzu Da hadin bakin bestyn ta Ahmad aka kafa wani karkarfan comitee na bincike akan zarah sun dauka kawai so take tayi musu wayo tana gina kanta wani waje basu sani ba..

Wasu kuma su kace kawai atsige ta daga kan position din ta tun kafin abu yayi nisa ta zo ta karya musu hard earned business din su....

Duk bata sani ba .tana kan dawainiyan abubuwan dake damun ta 

Ranar jumu'a su ogah majeh da baba ibrahim suka kai suhan asibiti..
Da dan abunda suka samu

Ba abunda ba a gwada ajikin ta ba amma babu ciwo babu musabababin sa...yayan cikin ta kuma lau suke wannan karon doc ya gan su tsaf yan biyu ne"

Basu yarda ba  shi dai yasan suhan dinsa ba haka take ba tana da hankali kuma tanajin magana tana kuma amsawa toh a hakan suka rika kashe dan kudin akan asibitai babu wanda ya basu kwararran bayani har suka koma suka hakura.


Bayan kwana biyu ogah majeh bai jin karfin jikin sa sosai..

So,sai baba ibrahim ya hutar da shi  agida akan yana lura da suhan kawai shi sai ya shiga gari kulle kullen yadda zaije gwada nemo wani kudin susan abunyi

hakan akayi sai dai....kullum yana fita
Amma kamar baida sa'a"

sosai yake shan wahala ga wulakanci ga cin fuska duk bai damu ba

His motivation is his doter now
He wants to pay back"

yasan ko sadakin ta da majeed ya biya bata gani ba shi ya cinye.

and he has neva being a father for her from start
Sai kawai ya rusuna ya sa kansa wahala tikurun ba dare da rana yana neman kudi..

Suhan Ta dan samu nitsuwa da tsafta yanzu bakamar da a gidan kande ba tana ci tana sha tana bacci mai kyau

Sai ma nakudan yake mata sauki in ya motsa atleast a yanzu ba su bari tayi wahalan komai hatta ruwan wanka kai mata suke..

Da yamma ita da baba majeh Sun dan zaga suna yawo  da shike ma mutumin tane yana da fara'a so duk masu kiwon shanu ta yankin sai da suka gaisa a mutunci ya shiga jeji neman ganyen zobo ma suhan ...

A wannan hayin  wani bafulatani makiyayi ya da jakar sa ta tsinta..

Kamar da wasa ta rataya jakar tana binsu abaya..ba murya bare tayi kira amma tana hango su ..sai haki take
Har Allah ya sa wani ya ganta..

Ba fulatanin tsiriri ne dogo yana da bakin zane a idanun sa irin bororin nan ne asali yan gadon jeji...

Sai murmushi take tana mika mai jakar sa...

Shikuwa kallon ta yake cikin wani irin yanayi mai tsoratar wa

Daga bisani ya karbi jakar ...

Ta juya za ta koma wajen baba ogah maje

"har ya juya shima zai tafi "Kai fulanin nan yaga bazai iya ba abunda ya gani tattare da suhan ya girgiza sa ..

A sace ya komo yake binta har suka kawo wajen ogah rabi'u maje tare...

Post a Comment for "SAKAMAKO CHAPTER 9"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...