Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

KAWUNA CHAPTER 6

KAWUNA CHAPTER 6

- - Post a Comment
KAWUNA 

CHAPTER 6
A hankali kamar mai raɗa ya ce " coming back to you soon" ya faɗi hakan lokaci guda yana lumshe idanuwansa. Ya ɗauki awanni kusan 3 zaune yana kallon hoton Senorita kafin daga bisani bacci ya so ma cinsa har yafi ƙarfinsa, hakan ya sanƴasa komawa kan gado ya kwanta kafin wani lokutan bacci yayi awon gaba da shi.
***********************************************
" Ki samu kici wani abin ya shiga jikinki Suhailat." Mommy ta faɗa tana ƙare wa Suhailat ɗin kallo, a hankali ta ci gaba da cin abincin duk jikinta a sanƴaƴe. Bayan Mommyn ta tabbatar kuma da gamsu da abincin da ta ci ta saka ta yin wanka ta canza kaya kafin a nutse Mommyn ta kalleta ta ce " duk tsuntsun da yaja ruwa hausawa sunce shi ruwa kan doka ko?" Ta ida maganarta ta cikin sigar tambaya, bata jira amsar Suhailat ɗin ba ta ci gaba da magana kamar haka " hmmm! Na sani kina mamakin yadda na san komai ko? Hayfah ta na yawan kirana tana kuka tana sanar dani irin halin ha'ula'in da kike fuskanta a gidan mijinki, tun bana sauraronta har dai na soma karaya na fara tunani kan lamarin. Da fari nayi niyyar sai kin gama jin komai a jikinki, na so kin ɗanɗana ƙuncin da kika sanƴa aminiyarki Abeedah wacce ba zaki taɓa samin ƙawa kamarta ba, irin zafi da raɗaɗin rayuwa da kika sanƴata a ciki, na sani komai muƙaddari ne daga Allah sai dai komai a duniyar nan akwai sila kuma kin sani kece silar komai Suhay, ke da kanki kika siyawa kanki iriyar wannan rayuwar, ko wani bawa ansani da tashi kalar qaddarar amma kisani duk wanda yaƙi jin maganar iyayensa bazai taɓa ganin haske cikin lamuransa ba". Zuwa wannan lokacin maganganun Mommyn sun gama yimata shawagi a cikin kwanƴarta, ta sani tabbas maganganun Mahaifiyarta gaskia ce, ita ta siyawa kanta iriyar wannan rayuwar da take ciki a yanzun babu sisin kowa bare kobo, ta sani abin da tayin shike bibiyarta kuma take kwashe sakamakon a sannu a hankali, ina zata ga Abeeda ita kuwa a yanzun? Da babu ko shakka sai ta durƙusa har ƙasa ta bata haƙuri ta nemi yafiyarta, ta sani sarai Abeedah za ta yafe mata don yarinƴa ce mai tausayi da saurin yafiya a duk abin da ka aikata a gare ta, muddin kanaimi yafiyarta toh ko babu shakka zata yafe ma ɗin, amma bata tunanin Abeedar zata sake bata iriyar matsayin da ta bata shi a daa chan don ta riga ta rusa komai da hannunwanta.  " momy ki yafemin na tuba wallahi na tuba, naga ishara a cikin rayuwata na sani nida kaina na siyawa kaina wannan rayuwar, amma inaji a jikina hakan yana cikin KUDDIN KADDARATA ne (littafin Safiyyah huguma), ban isa na sauya hakan ba, don mai duka ya riga ya rubuta hakan a shafukan Qaddarorin rayuwata. momy ki yafemin na tuba ki roƙamin Allah ya sa na iya cinye wannan jarabawar". Daga haka kuka yaci karfinta, sosai ta kife kanta tana fidda kuka mai ban tausayi ga duk wani mai ran imani dake saurarenta sai ya tausayawa ma ta kwarai da gaske, hatta Mommy sai da zuciyarta ya karaya tama gaza lallashinta tabar ta tayi kukan mai isarta don tafi buƙatar kukan fiye da komai a yanzun, gwara ta koka ta fidda dukkanin abin da ke cunkushe a cikin zuciyarta wala'allah hakan ya sama ma ta sauƙi da raɗaɗin zuciyar da take ciki. Sai da ta yi kukan mai isarta don son kanta ta tsagaita da kukan kafin a hankali ta soma ajiyar zuciya, momy kuwa bata gaza daga shafa bayan Suhailat ɗin ba, cikin sigar lallashi ta soma kwantarwa da Suhailat ɗin hankali daga haka kuma bacci ya ci galaba a kanta, gyara ma ta kwanciyarta Mommy tayi kafin ta tofe ma ta jikinta da addu'oi daga bisa ni ta kashe ma ta  wutar ɗakin sa'annan ta fita daga ɗakin tana sauke ajiyar zuciya. sosai tausayin ƴarta ya dabaibaye ilahirin gaɓɓan jikinta, kunsan   uwa da ɗa sai Allah, wannan soyayyar dai tananan babu mai iya wargaza shi ance ko mutuwa tana shakkar idon uwa!, Sai dai Mommyn sosai take so ƴarta ta ɗauki darussan rayuwa tana matuƙar son Suhailat ɗin ta kyautata zatonta nan gaba, tayarda ta amince so babu abin da bazai saka mutum aikatawa ba sai dai komai da lalama a ke bi don samun ingantaccen rayuwa. Shi Salman ɗin wanda tayi don shi yanzun ba shi bane ya zuba mata ƙasa a ido ba? Kaɗan ma ta soma gani muddin a kan ɗa namiji take haukarta.
************************************************
Gyare-gyaren gidan da Abee ta soma gani a ke yi shi ya fara nusar da ita kan Hammad na tafe kenan? Don hatta ga abokan Asma'u da Faruk sun daina zuwa gidan, kiɗe-kiɗen da a kullum yake ta shi a cikin gidan tamkar club cikin kwana biyun nan duk an tsagaita yi, gidan ya soma dawowa shiru tamkar yadda yake zamanto wa muddin Hammad na gari. kunnuwanta cikin kwana biyun nan har sun sama  nutsuwa don ita haka take tun tana ƙanƙanuwarta bata fiye son hayaniya ba wurin da akwai hayaniya bata gigin zuwa wajen don ciwon kai yake sanƴa ma ta, shiyasa a duk lokutan da ta jiyo kiɗe-kiɗen ya soma tashi take tsinewa su Asma'u a cikin zuciyarta don suna azabtar da ita ta hanyar saka ma ta ciwon kai. Harira da shigowar ta kenan cikin ɗakin ta dubi Abeedah ta ce " Abeedah, ki miƙe muje mu ɗaura abincin tarbar Hammad, don jirginsu ya kusa isowa" da "toh" kawai Abeen ta amsawa Harirar don yau ɗin nan sam bata jin yin dogon magana, wajajen 2:30pm suka kammala dukkanin samfarin abincin da suka san yana cikin time table ɗin yau don bin ka'idar Hammad ɗin, in kaga an daina bin time table na abinci a cikin gidan toh kuwa ka tabbatar Hammad baya gari, nan kam suna dafa abincin da Hajiar nayi ra'ayin a ci a ranar. A babban dining area ɗin cikin falon Daddy suka jera komai da komai don anan a ka saba haɗuwa a ci muddin Hammad yana gari. 

Story continues below


Ƙarfe 4:30 daidai Hammad ya iso gida a sannu a hankali kowa ya soma dawowa cikin nutsuwarsa don gudun ɓata ran oga Hammad. Fitowa yayi sanƴe da ƙananun kaya, yana tafe cikin nutsuwarsa tamkar baya son taka ƙasa, Daddy yake muradin zuwa ya gaisar don ya tabbatar zuwa yanzun Daddyn ya dawo daga office, a hankali yayi sallama cikin falon sai da ya jira aka yi ma sa iso kafin ya shigo cikin falon a natse, Daddy da Hajia Nenne da Faruk ne ke zaune da dukkanin alamu dai suna tattauna muhimmin abu ne hakan ya sa Hammad juyawa don basu wuri amma sai Daddyn ya dakatar da shi wanda hakan ba ƙaramin ɓata ran Hajiar yayi ba. " Moallahidi war toi ayata bo? (Moallahidi zo ina zaka kuma?)" Alhajin ya faɗa cikin yaren Fulatanci, a hankali Hammad ɗin ya juyo ya dawo cikin falon yayi wa kansa mazauni kusa da Alhaji, gaida Daddy yayi sa'annan ya gaida Hajia da Faruk dukkanin su suka amsa masa fuskarsu babu yabo babu fallasa inka cire Daddy Wanda keta faman sakarwa Hammad murmushi, tunda Hammad ya gaida su ya ja bakinsa yayi shiru bai kuma cewa uffan ba don shi haka yake dogon magana ba ɗabi'ar sa bace kwatakwata, sanin halin yaron na sa sarai ba zai sake cewa uffan ba ko za'a shekara dubu a hakan ya sanƴa Daddyn cewa " Moallahidi kaga nayi maka kiran gaggawa ko?" Gyaɗa kai yayi don bakinsa nauyi yake masa, " Madallah dama wani aikin ne ya taso na bazata,wanda kuma dole kaine kawai zaka iya jagorantar aikin shiyasa nayi kiranka", lumshe idanuwansa yayi a hankali kafin cikin sautin muryarsa mai amo ya ce " wala ɓilla Daddy(babu damuwa Daddy)"  murmushi Daddyn yayi sa'anan ya shiga sanƴa masa albarka. Hajia Nenne kuwa ta riga ta cika fam fashewa kawai ya rage gareta, Faruk Kuwa tsananin ƙiyayyar da yake yiwa Hammad din ne keta kai kawo cikin gaɓɓansa, baya ƙaunar yaron samsam zuwansa cikin gidan nan ya ɗebe masa kaso kusan 80 cikin zuciyar Alhaji, yanzun babu wanda Alhajin ke so tamkar ransa kamar wannan Hammad ɗin ya rasa da mai Hammad din ya fisa a rayuwa..... Nutsuwa, dogaro da Kai, riƙon addini, kamala,kyautatawa, riƙon gaskia, kyawun fuska da kyawun zuci, tarbiyya, girmama na gaba da shi D.S.S wa'innan sune abubuwan da Hammad ya tserema da su a rayuwa, wani ɓangare na zuciyarsa ya tunasar da shi hakan, ƙaramin tsaki ya saki kafin ya maida dubansa kan Hajia wacce itama shi ɗin take kallo. Ya gama ƙosawa  ranar cikar wa'adin da suka ɗaukar wa Hammad ɗin ya cika dan babu makawa tsinke wannan karan sai ya tabbatar Hammad ya baƙunci lahira. A daren ranar tare suka haɗu suka ci abincin dare Abeedah kuwa ƙin zuwa tayi ta ce wa Harira ta sanarwa Hajia bata jin daɗi ne ya sanƴa bata zo ba.
************************************************
Bayan kwana biyu. 

" Ke Ma'u wallahi tallahi mutuncinki zanci muddin kika ce zaki watsa min ƙasa a ido, In Hammad ɗin ƙanin ubanki ne sai ki hanani kashe shi, sha sha sha kawai, wallahi ahir ɗinki muddin kika ce zaki kawo mana cikas cikin tafiyar nan Ma'u! Ki fita idona wallahi ki fita, dan ubanki in Hammad din ya fiye miki ni sai nagani banza sha sha sha " Hajia Nenne ta ida maganarta tana huci da taƙaicin Asma'un, ita kuwa Asma'un ko a jikinta don babu abin da zai hanata kawo cikas wajen kashe Hammad Sai dai in zata rasa na ta ran ita ma, amma muddin tana raye tana lumfashi cikin doran duniyar nan toh ba zata bari a kashe ma ta Hammad ba. Maganar Faruk ne ya katse mata tunaninta " Hajia ki barni da ita sai na lallasata, bazai yuwu kan Asma'u ki zauna kina tada jijiyoyin wuya ba ita ɗin banza muzuba da mu da ita shege ka fasa wawiya jaka kawai"  ya ida maganarsa yana miƙa wa Hajia Nenne glass cup cike da ruwan sanƴi don ta huce taƙaicin Ma'un, taɓe bakinta tayi kafin ta miƙe tabar musu falon cike da jin haushin su, da idanuwa kawai suka iya binta har ta ɓacewa ganinsu, sauke a jiyan zuciya Hajiar Tayi kafin ta ce " Ummaru  yau saura kwana uku kacal ya rage a kawar da Hammad, wallahi kaji nayi rantsuwar musulmai ko? bana son cikas bana son jin aiki ya sama tangarɗa, gawar Hammad nake da buƙatar gani kawai"  lumfashi ya sauke cike da ƙarfafa gwiwa ya ce " Hajia baki da case faa, mutanen nan sun gama kwarewa wajen kisa kuma kin biya su sosai, so ki kwantar da hankalinki consider it tamkar kin gama ganin gawar Hammad dolen sa  yabar Duniya ko ya ƙi ko ya so" gyaɗa kai Hajiar tayi cike da gamsuwa kafin ta ce " a gama da shi kafin mu idasa sauran aikin, ina ganin su biyun nan muna gama kauda su  shikenan sauran zamu iya handling ɗin su cikin sauƙi"  Faruk ya ce " Hakane Hajia sai dai wai mai yasa ba zaki bari a fara Kashe Alhajin ba kafin Hammad?" Hararar Faruk din tayi kafin ta ce "dalla matsa can sha sha sha ina yabon ka salla ka kasa alwala, sai ka ce ka na manta waye Hammad Ko? Matuƙar muka fara kashe Alhajin toh Hammad mutuwarsa bazai zo mana cikin sauƙi ba, don sai ya zurfafa bincike a kan kissan Alhajin wanda ka sani nisanta kansa zai yi da nan garin hakan kuwa zai kawo mana cikas, gwara ya fara ziyartar lahiran kafin uban na sa yabi bayansa, komai dake mallakin Alhaji zai dawo ƙarƙashin mu, kai dai kuyi aiki successful da sauran murnar mu nan gaba" ta ida maganarta lokaci ɗaya tana sakar wa kanta murmushi masu ma'anoni daban daban, shi kansa Faruk jinjina kaidin yayarsa kawai yake a cikin zuciyarsa " Ma'u fa ya zamuyi da ita?" Ya jefa mata tambayar kai tsaye,  guntun murmushi ta saki kafin ta ce "barni da ita ni ce fa Deeje ɗiyar Sani da Lauratu, ai in tasan wata bata san wata ba, mutum ya girme maka koda da kwana ɗaya ne ya fika sanin mai duniyar ke ciki" ta ida maganar cikin gatse, gyaɗa kai kurum Faruk yayi don ya sani Asma'u ta ɗibo ruwan dafa kanta.
************************************************
a hankali ta miƙe daga zaunen da take, ranta a matuƙar jagule yau hakanan ta tashi da ɓacin rai ko Harirah ta lura da hakan amma sai ta basar don ta lura Abeedar mutum ce da bata fiye son mutum na ma ta shishigi cikin lamuranta ba. Tsaki taja karo na barkatai saboda sam zaman gidan ya fara takurawa rayuwarta don sam bata ga aikin da take yi ba, banda aikatau da take yi a cikin gidan ta rasa dalili ta rasa mafita ta kuma rasa abin da zata yi, kanta duk a cunkushe yake kwanƴarta sam baya iya tunanin komai, sosai cikin kwanakin nan ta dage da sallan dare kan Allah ya kawo mata ɗauki cikin lamuranta. Karo taji tayi da abu hakan ya saka ta yin tangal tangal zata faɗi ta baya, ji tayi an riƙe ta hakan ya sanƴata runtse idanuwanta don ta tabbatar muddin ta faɗi a ƙasan nan bayanta sai ya sha jinƴa, a hankali ta soma buɗe idanuwanta har ta ware su tas a kan kekkyawar fuskarsa, tsoro fargaba duk su suka saukar mata a lokaci guda, kallon kallo suka shiga yiwa juna har na tsawon wasu sakanni kowa da abin da yake saƙawa a cikin zuciyarsa, Abeedah kam tsananin kamanninsa da Mancy ne ya soma bata mamaki don kuwa yadda kasan ƴan biyu haka kamanninsu ya ɓaci Hammad namijin Mancy ne ita kuma Mancy macen Hammad ne hakan take rayawa a cikin zuciyarta, Hammad a na sa ɓangaren kuwa nazartar fuskarta ya shiga yi don ƙarara yake karanto damuwa shimfiɗe a kwayar idanuwanta duk da ƙaton gilashin dake make a samar fuskarta bai hana sa karantar yanayin ta ba, maike damunta?shine tambayar da ya shiga jifar kansa da ita don yana mamakin ganin ta ƴar ƙanƙanuwa da ita tana cikin damuwa ko dai Hajiar gidan ta yi halin ta ne? Abin da ta saba yiwa ma'aikatan gidan? Kiran sunansa da yaji ana yi ne ya sanƴasa dawowa hayyacinsa da hanzari ya sake ta itama cikin sauri ta shiga kimtsa kanta, da hanzarinta ta ƙara so wajen tana ƙare wa Abeedah kallo cikin zafin rai ta ce " ke! Mai kike yi anan?" Dabur cewa Abee tayi tama rasa abin da zata ce wa Asma'un, ganin iriyar ruɗewar da Abee tayi ne ya sanƴa shi kiran sunan Asma'un cikin muryarsa mai shegen amo da daddaɗar sauti " Asmaaa!" Ya faɗi a sanƴaƴe kallonsa tayi kafin tayi saurin janƴe idanuwanta a kan Hammad ɗin saboda tsananin kwarjinin da yake yi ma ta a kullum, lumshe idanuwansa yayi wanda yayi matuƙar tafiya da imanin Asma'u, Abeedah kuwa ganin hakan ya sanƴa ta saurin barin wajen zuciyarta na dukan tara tara don Allah kaɗai ya san abin da Ma'un zata mata nan gaba. " Hammy (haka Asma'un ke kiran Hammad wasu lokutan)" zuba mata lumsassun idanuwansa dake tafiya da imaninta kawai yayi ba tare da ya ce da ita uffan ba, a hankali ta ce " Daddy Ke naimanka" gyaɗa ma ta kai kurum yayi kafin ya raɓa ta gefenta yayi tafiyarsa, ƙamshin turarensa kaɗan ya rage bai tafi da lumfashinta ba harga Allah tana mutuwar son Hammad, bata tunanin zata iya barin yayarta ta kashe mata Masoyinta zata bi dukkanin hanƴoƴin da taga zata iya don dakatar da Hajia wajen kashe Hammad wannan shine alkawarin data dauka kuma tana lissafe yau saura kwana biyu tal su aiwatar da ƙudirinsu a kan Hammad, Kwafa tayi tana girgiza kai kafin tabar harabar wajen ta koma sashenta.
*************************************************
Isar sa cikin Falon ya tarar da Daddyn da Hajia Zaune da dukkanin alamu zaman jiransa suke, kallo ɗaya yayi wa Hajiar ya ga yadda ta cika fam kaɗan take jira ta fashe, ba damuwarsa bane hakan don shi mutum ne da bai shiga shirgin kowa a rayuwarsa guri ya samu ya zauna kusa da Daddy kafin ya gaida shi a ladabcce cikin sakin fuska Alhajin ya amsa haɗi da cewa " Moallahidi, Hajiar ku ce ta kawo maganar bawa ɗaya daga cikin masu aikin gidan nan aiki a Company, nayi nazari a kan maganarta don yarinƴar da ta buƙata a bawa aikin sosai ta cancanta don na yaba kwarai da gaske da halayyarta don ni take yi wa aiki, so Hajia ta ce a baiwa yarinyar aikin accountant na branch ɗin WASACO don Abdullahi dake riƙe da muƙamin zai bar nan zai koma Company ɗin mu da ke Sokoto, mainene shawarar ka a kai?" Shiru yayi yana nazartar maganganun Daddy, mamaki ne sosai ya cika shi mai yasa za'a baiwa ƴar aiki wannan matsayin a Company har wani karatu suka yi na zo a gani da za'a basu iriyar muƙamin? hmmm tanan kuma Hajiar ta ɓullo wannan karan? ya sani tabbas akwai wani maƙarƙashiya a ƙasa dalili kuwa hausawa sun ce ruwa baya tsami banza, koma dai mainene suje  zuwa shida Hajiar wannan karan baiji zai raga ma ta ko kaɗan, tabbas tana da babbar manufa a kan son bawa ƴar aiki wannan matsayin amma ko ma mainene zai kamo zaren abun. Ta tsani wannan halin da Alhaji ke yi ma ta a kullum muddin ta bukaci yayi mata wani abin dan gane da wajen aikinsa toh babu makawa tsinke sai ya naimi shawara daga wajen Hammad abinnan Yana matuƙar ci ma ta rai, amma babu damuwa komai ya kusa zuwa ƙarshe, kuma ko yana so ko ba ya so sai Abee tayi aiki a Company ɗin don cimma wani buri na ta. Maganarsa ce ta tsinke hanzarinta lokaci guda ta kai dubanta kansa " toh Daddy Allah shige mana gaba, gobe sai ta zo interview Ko?" Ya ida maganar yana mai  jiran fitowar amsar sa daga bakin Alhajin caraf Hajiar ta caɓe ta ce " a'a ba ma sai anyi ba, yarinƴar ai fannin da ta karanta kenan so no need Sai an gwada ta ko?" Ta ida maganar tana kallon Alhaji so yake ya musa wa Hajiar amma watsa masa idanuwanta da tayi sai yaji ya kasa musawa maganarta ilai ma ji yayi maganarta haƙƙun ba musu a ciki, gyaɗa kai yayi kafin ya kai duban sa ga Hammad Wanda tsananin mamakin Hajiar ke ɗawainiya da shi " ba sai an ma ta interview ba let her begin her work Kawai "  bai iya yiwa Alhajin musu ba don ba ɗabi'arsa ba ce, gyaɗa kai kurum yayi ba tare da ya ce uffan ba ita kuwa Hajia kamar ta miƙe ta taka rawa don sosai take hango nasarori a tafiyar, kiran Abee Daddy ya aika a yi kafin wasu daƙiƙu Abee ta bayyana cikin falon zuciyarta fal tunanin kiran na ta da Alhaji yayi, ganin Hajia da Hammad zaune ya sanƴa cikinta kaɗawa mai tayi ? ƙararta Hammad ya kai? Toh mai tamai? Ire iren tambayoyin nan ta riƙa jifar kanta da shi, samun wuri tayi ta zauna a tsorace ko kallon inda take Hammad bai yi ba don ya riga ya yarje wa kansa yarinƴar bakinta ɗaya da Hajiar duk da bai santa ba bai san wacece ita ba, Alhaji ya soma kiran sunanta a ladabcce cikin hausar ta da bai samu matsuguni mai kyau ba ta amsa mai haɗida gaida Alhajin, " Abeedah aiki na ke so zan baki a cikin Company ɗina........." Da hanzari Abee ta ɗago ta na kallon Alhaji, ruɗu, mamaki, firgita suka dirarwa kwanƴarta a lokaci guda, mai hakan ke nufi?......................

Da hanzari Abee ta ɗago ta na kallon Alhaji, ruɗu, mamaki, firgita suka dirarwa kwanƴarta a lokaci guda, mai hakan ke nufi?. Gaza samun amsar tambayarta tayi don haka kawai ta zubawa Alhajin idanuwanta ba tare da ta ce masa uffan ba, ganin tsananin mamaki shimfiɗe a saman fuskarta ya sanƴa Daddy cewa " karki damu, kwanaki na tambayeki matakin karatunki, kin ce dani NCE gareki ko? zan baki aiki a Company na saboda iriyar riƙon gaskia da kikawa aikinki, ban ta ɓa samun ma'aikaci daya riƙe amana bai min sata sai ke, don haka ki godewa Allah da kuma Hajia, don ita ce ta kawo wannan shawarar, na zauna nayi nazari naga cewa lalle tayi tunani mai kyau. Allah tayaki riƙo jibi in sha Allah zaki soma zuwa office". Gani kawai su Daddyn suka yi hawaye na bin kuncin Abeedar babu ƙakƙautawa, farin ciki, mamaki duk suka taru suka turnuƙe ta, sosai take hango wa kanta nasarori muddin ta fara aiki a kamfanin Daddy, ta tabbatarwa kanta Allah ne ya amsa addu'arta shi ya dafa mata har hakan ya kasance a gareta ba tare da tayi tunanin wannan ranar zai zo mata ba, lallai Ubangiji mai amsar addu'ar bayinsa ne, jinkirinta a she jinkirin alkairi ne. Cikin rawar murya ta soma magana cikin bahagon hausarta " Nagode Nagode Alhaji, Allah Ubangiji ya saka da alkairi ya biyaka da aljannah ya jiƙan mahaifa, Ubangiji ya albarkaci zuri'arka Allah ƙara lafiya da nisan kwana, Hajia nagode sosai Allah biyaki da alkairi". Daga haka kuka ya suɓuce ma ta har hakan ya soma bama Daddy da ita kanta Hajiar mamaki a ganinsu wannan bawani abin tashin hankali bane, amma tuna cewa ita ɗin ƴar aiki ce kuma abin yazo ma ta a bazata ya sanƴa su kauda mamakin, Hammad kuwa baƙin ciki kamar ya kashe shi so yake yayi magana ya dakatar da bata wannan muƙamin amma tsabagen miskilanci irin na shi bazai barsa yayi maganar ba ya gwammaci ya mutu a kan dai yayi magana, don a ganinsa duk acts ne Abeedah ke yi duk Hajiar ce ta ƙissa ma ta yadda za tayi, a hankali ya miƙe ba tare da ya ƙara bi takan kowa ba yayi ficewar sa a cikin falon ransa a matuƙar ɓace. Abeedah ma Hajia ta sallame ta ranta cike da farin ciki ta koma ɗakinsu, tsalle ta buga tana dariya wanda yake daɗa fidda natural kyawunta dukda tabon dake manne a fuskarta ta bai hana dariyarta ƙawata fuskarta ba, wayanta ta sura ta shige ban ɗaki ta danna lamban Mancy kira ɗaya biyu Mancy ta daga, jin muryar ƴarta cike da annashuwa ya sanƴata jin daɗi na ziyartar ilahirin jikinta " Mancy albishirinki?" Ta katse wa Mancy tunaninta, murmushi Mancy tayi kafin ta ce " Abeen Abbi ai sai kibari a gaisa kafin a min albishir ɗin ko?" Mancy ta ida maganar tana dariya, itama Abeen dariyar tayi don shaf zumuɗi ya sanƴata manta gaida mahaifiyarta, " laaa Mancy kiyi haƙuri don Allah, shaf farin cikin da nake ciki ne baya misaltuwa naƙosa kawai na faɗa miki wannan albishir ɗin" dariya Mancy ta kuma yi sa'annan ta ce " toh ina sauraranki" kamar jira take Mancyn ta bata dama, ta soma zuba kamar gidan radio har ta kai aya kafin ta ce " Mancy, ina ganin lokacin dawo da martabar ki gidan kakanmu yayi, ina hango ɗin bin nasara a tattare da hakan, kimin addu'a Mancy Allah ya sa wannan shine silar dawo da martabar ki gidan mahaifinki", Farin ciki ne keta zirya a gaɓoɓin Mancy tama rasa ina zata sanƴa kanta don farin ciki, a hankali ta ce " Barka Abee, Allah yayi miki albarka Ubangiji ya baki nasara, ya kuma kareki daga sharrin mutum da aljan Allah miki albarka mamana" sosai addu'ar da Mancy tayi ma ta yayi ma ta daɗi don haka sai taji farin cikin da take ciki na qara linkuwa, "Ameen Mancy" daga haka suka ci gaba da hira har ta gaisa da ƴan kannenta sosai tayi kewansu har kwalla ta zubda, da kyar sukayi sallama dukkanin su cike da kewan juna.
********************************************* 

" Haba Hajia, ki rasa wanda zaki saka Alhaji ya baiwa wannan matsayin a Company sai wannan kulacar inƴamurar, gaskia yanzun na dai na gane miki, cha nake nima tsaf zan iya riƙe wannan matsayin amma kika baiwa ƴar aiki mai kwalin NCE Kawai, Ni Ina nan riƙe da digree, masters da Phd amma babu aiki, mtsweww" Asma'u ta ida maganarta tana mai jan tsaki cike da haushin Hajia Nenne. Kaɗa kai Hajia Nenne tayi sa'annan ta ce " toh uwar marasa Kunƴa, kin gama na ce? Ke ma'u kifita idona fa, wallahi ina jiye miki fushina, kin sanni kin san halina gaba da baya ba sai an baki labari ba, a toh! Ki bi a hankali don ubanki ko naci mutuncinki, ai tunda kika ce kin zaɓi Hammad a kaina kya je shi wanda kike son baima san kina yi ba ya baki duk wani abin more rayuwa ba dai ni Deejee ba, banza" daga haka Hajia Nenne ta miƙe ta haura saman upstairs da zai sadata da bedroom ɗin ta. Da idanuwa Asma'u tabi Hajiar har taɓacewa ganinta, dogon lumfashi ta sauke kafin ta taune baki tana saƙa da warwara. Shigowar Faruk ne ya katse mata tunaninta, nazartarta yayi na wasu sakanni kafin ya ja lumfashi ya kira sunanta yana mai idasa zuwa wajen da Ma'un ke zaune dan yiwa kansa mazauni shima. " Ma'u!" Ta wutsiyar ido ta kallesa ba tare da ta amsa ma sa ba, sanin halin ƙanwarsa ya sanƴa sa matsowa daf da ita ya soma lallashinta " kinga Ma'u kibi Hajia a hankali kin san halinta muddin tayi fushi da mutum, ki lallaɓata shine zaman lafiya don ina jiye miki ranar da zata sauke fushinta a kanki tsaf zata iya maidaki ƙauye atoh!" Dogon tsaki Asma'u ta jaa kafin ta juyo tana watsa ma sa harara kafin ta ce " Rijiya ba wurin wasan makaho bane, Bismillah ta maidani kauye mugani, kuma ina kan bakana babu mai taɓa Hammad" daga haka ta miƙe ta bar masa wajen, da idanuwa kawai ya iya bin Asma'un har ta ɓacewa ganinsa. A jiyan zuciya ya sauke kafin ya gyaɗa kai ya miƙe yabar wajen shima. 

Story continues below


####################################
Suhailat ce zaune tana danna wayarta, gama wayansu kenan da Hayfah inda take sheda mata akan ta koma gida sa'annan tayiwa Hayfa godia sosai akan taimaka ma ta da tayi wajen sanarwa da iyayenta halin da take ciki, Hayfah tayi matuƙar murnar jin Suhailat ɗin ta koma gidansu, don a wancan lokacin ƙemadages Mommyn Suhailat ke nuna ma ta kan ba zata je ta taimakawa Suhailat ba komai take gani ita ta siyo da kuɗinta. A sannan ne Hayfah ta sake tabbatar da cewa uwa dai uwace a ko'ina kuma ɗa da uwa sai Allah. " Suhailat sai yaushe ne zaki fara zuwa asibitin ne wai?" Mommy ta watsa wa Suhailat tambayar lokaci guda tana yiwa kanta mazauni kusa da kujerar da Suhailat ɗin ke zaune, ɗago da kanta tayi ta kallo Mommy kafin ta mayar da kwayan idanuwanta kan cikin dake jikinta wani qullutun baƙin ciki taji yana ziyartarta don tuna mahaifin uban cikin, canza maganar tayi don sam bata son abin da zai riƙa tuna mata da Salman, " Mommy nikam har yanzun babu Labarin Abeedah ne? Mommy kodai gidansu zani ne? san dai iyayenta bazasu rasa sanin inda take ba." Kallonta mommy tayi sosai kafin ta ce " yanzun ke Suhailat a ka ce miki kije gidansu Abee sai ki kwasa ƙafafunki ragwajab-ragwajab kije? Toh in kinje ki ce da su mai? Kinzo su faɗa miki inda ƴarsu take? Hmmm kibari dai ki fara ganin dawowarta sai kije hakan zai fi" gyaɗa kai kawai tayi don har ga Allah tana matuƙar kewan Abee.

%%%%%%%%%%%%%%%%%%%%%%%%%%%%
Wayar salula ce manne a saman kunnensa yana amsa kiran tamkar anmasa dole, abin da mutum zaiyi tunani kenan muddin ya gansa a wannan lokacin, sai ka zauna da shi ne zaka san cewa halinsa ne haka nature ɗin sa ne, magana bata cikin ɗabi'arsa. Rashin wadata ciyar network a cikin ofishinsa shi ya sanƴasa fitowa don amsa kiran Daddy, tsaye yake yana sauraren abin da Daddyn ke faɗa masa hankalinsa a nutse. 
"Dole ku tabbatar ya mutu kafin ku daina zuba masa ruwan bullets" Hajia Nenne ta daɗa shaidawa Faruk, daga ɓangaren Faruk kuwa cewa yayi " baki da Matsala Hajia, yanzun haka ya fito farfajiyar Company ɗin In sha Allah yau dai Hammad ya gama shaqan lumfashi a duniya" kyalƙecewa Hajia Nenne tayi kafin ta datse kiran tana kuma sakin wani sabuwar dariyar a ganinta yau matsalarta ta zo karshe harda yar rawar ta a tsakiyar falo, kallon ɗakin da ta sanƴa a ka kulle ma ta Asma'u tayi bayan ta sanƴa mata maganin bacci cikin coffee ɗin da ta sha da safe saura a wanni uku kacal maganin ya daina aiki a jikinta zuwa wannan Lokacin kuma a ganinta andaɗe da aika ma ta Hammad lahira! Tsaki taja tuna iriyar dramar da zasu sha ita da Ma'u muddin taji mutuwar Hammad tsaki taja kafin ta ɗago wayarta ta dannawa teacher Kira (teacher shine sunar data sanƴawa bokanta) bugu ɗaya biyu ya ɗaga daga gefensa ya ce " Hajjaju makkatan," " teacher a sanƴa mata mantuwa a birkita ƙwaƙwalwarta ta manta Hammad bayan ta farka" wani kaliyar mahaukaciyar dariya teacher ya kyalƙece da shi kafin ya tsagaita ya ce " kinfi shaiɗan shaiɗan ci, ko shaiɗanun suna sarawa kaidinki Hajjaju baitullahi, aikinki a minti 10 zai kammalu kede turo bugun nasarah kawai" " ba kada matsala da wannan gidansu kazo" zai fara yi ma ta kirarin da ya saba yi ma ta ne ta katse kiran, kafin ta shiga mobile bank tayi ma sa transfer ɗin kudin aikinsa, daga nan ta kunna waqan hamisu breaker ta soma taku ranta a kwance (hmmm!).
____________________________________ 

" Shamo, yanzun zai iso wajen ku tabbatar kun zamana cikin shiri bana son a sami tangarɗa" daga ɗayan ɓangaren wanda a ka kira da shamo ya amsa da " Ok Sir komai zai zo cikin sauƙi" "all the best" Faruk ya faɗi hakan lokaci guda yana mai katse kiran ganin Hammad yayi hanyar car park, da hanzarinsa ya fita a wajen maɓoyinsa don wucewa na sa offishin. Tayar da motar sa yayi ya bar harabar Company in don cimma aiken da Daddy yayi masa can bayan gari, a cewar Daddyn ya na so yaje ya duba masa wajen don ya na son ya siyi filin gona a wajen, mamaki sosai Hammad yayi da Daddyn ya aikesa yaje can ɗin don a iya saninsa ba shi ke siyan ma Daddy filaye ba Ko wasu kadarorin Faruk shike wannan sabgar amma musu wa dady ba ɗabi'arsa ba ce don haka ya amsa kai tsaye za shi. A hankali yake tuqinsa karatun Alkur'ani na ta shi a hankali cikin kira'ar maher almu'aqili a ƙaramin sautin muryarsa mai daɗi yake bin karatun yana mai jin wata iriyar natsuwa na shigarsa. 

Gudu take yi sosai ba tare da tasan inda take shiga ba, burinta ɗaya shine ta isa wannan kangon don ta tabbata anan ne mutanen suke, anan a kayi za'a ka she ma ta ɗan uwa. Duk wanda ya ganta a wannan yanayi zai tabbatarwa kansa bata cikin hayyacinta duba da yadda duk tabi ta fita cikin hankalinta gudu take yi tana haki don zuciyarta na tsoratar da ita a kan sun riga sun kashe sa, isarta wajen yayi daidai da saukowar sa daga cikin motarsa. A hankali kuma ya shiga ƙare wa wajen kallo a tunaninsa mutanen da daddy ya ce ma sa zasu haɗu zai zo ya iske su ne, amma ga mamakinsa babu alamar mutum mai rai a wannan waje, iface ifacen tsuntsaye kawai yake iya ji da tafiyar ruwa wanda ƙatuwar rafin dake a tsakiyar wajen ke fidda wannan sautin. Wayarsa ya dauka don kiran Daddy amma yaga network ɗin sa ta dauke gaba ɗaya dafa kansa yayi kawai yana jan tsaki, In ma banda Daddy ne ya aikesa da babu abin da zai sanƴasa zuwa wannan wajen da babu motsin ɗan adam. A hankali ya jiyo don tafiya amma mutanen da ya gani suna tunkaro wajensa ya sanƴa sa tsayawa a tunaninsa sune mutanen dake da mallakin wajen kuma sune Daddy ya aikosa wajensu, a hankali suka ci gaba da takowa inda yake, ganin tabbas ta bari suka ƙara so inda yake babu ko shakka sai sun hallakasa ya sanƴata soma tunanin abin da zatayi don tawa kanta maɓuya a bayan bishiyar mangoro, kamar almara yaga mutane kusan biyar suna saito bindiga daidai ƙirjinsa hakan yaso tsorata sa amma da yake namijin duniya ne ya sha mur yana jiran saukan bindiga don ya san abin da ya taka . Da ƙarfin tsiya ta kwalo kiran sunansa "Hammaaaaaaaaaaaad!" A daidai wannan lokacin mutumin dake gaba ya danna bindigarsa don harban Hammad, ita kuma a daidai nan tayi kukan kura ta shige jikinsa tana mai runtsa idanuwa, Hammad tsabagen ruɗu har daina motsi yayi na wasu sakanni don ganin ta a wannan wajen, tabbas inba kallon tsoro yayi mata ba toh tabbas ita ɗin ce dai bai kaiga ƙarasa tunanin mai ya kawo ta nan ba ya ji saukar bindiga wanda ya dauke lumfashinta cak da na sa lumfashin, da dukkanin ragowar ƙarfin jikinsa yayi azamar juyar da ita ta fuskanci gabas shi kuma ya fuskanci kudu inda tawagar mutanen suke, ganin haka suka shiga sauke ma sa ruwan bindiga a bayansa amma ga mamakinsu babu ko daya dake samun sa face ma zubewa da bullet ɗin ke yi ƙasa, ganin haka ya sanƴa su tsorata sa'anan suka soma rugawa a kuje don barin wajen, zuwansu UK last da Alhaji ya sanƴa a kayi wa Hammad rigar bullet proof Kuma ya jaddada ma sa akan duk inda zai je kar ya kuskura ya fita babu wannan rigar a tattare da shi don bai san inda zai iske maƙiyi ba watarana, a cewar Daddy duk wani ɗan kasuwa musamman wanda yayi fice a cikin kasuwanci rayuwarsa a kullum cikin hari yake wala'allah en fashi ko maƙiyi ko dai wani can daban shi ya saka Daddyn ya sanƴa a ka yi wa Hammad rigar bullet proof ta musamman, sanin halin Hammad Sarai Zai iya qin sakawa ya sanya Alhajin cewa Hammad din Yayi ma sa alkawarin ba zai yi sake ba zai riƙa sakawa, a wancan lokacin Hammad ganin abin kawai yake kamar wasa don shi yayi imani in har Allah bai yi lokacinsa ya ƙare a duniya ba toh babu mai iya daukan ransa, amma sanin girman alkawari da sanin hukuncin wanda ya saɓa alkawari ya sanƴa sa riƙa saka kayan a kullum kafin yayi normal dressing ɗin sa, yau dai yaga alfanun wannan kayan. A hankali ya soma buɗe idanuwansa yana saukesu a kan fuskarta wanda a lokaci guda yayi fayau tayi uban haske idanuwanta a kulle, da hanzari ya ɗagota sai dai ganin jini baja baja a hannunsa ya sanƴa sa saurin juyo da ita, innaalilahi wa'inna ilaihir rajiun shine abin da Hammad Ke furtawa jikinsa har kyar ma yake, da ƙarfi ya sunkuceta gudu gudu yayi hanyar mota da ita don ceto ranta jini sosai baiwar Allar ke fiddawa don bullet ɗin da ya same ta a gefen kafaɗarta, gudu sosai Hammad Ke tsulawa ga tsoron dake addabar sa na kar ya rasata a karo na biyu ga kuma firgita da ya matuƙar yi a kan ganinta a wannan wajen, da ikon Allah suka isa a asibiti a gaggauce likitoci suka amsheta suka yi hanyar emergency da ita.........

Kasa tsaye kasa zaune yayi, ziryarsa zuwa ɗakin theatre da in da yake zaune yana jiran fitowar su yayi sa sau babu adadi, burinsa be wuci yaga fitowar likitocin ba. Awowi da basu wuci uku ba yaji ala'mar buɗewar ƙofar theatre room ɗin da hanzarinsa har yana tuntuɓe ya isa gaban likitan da ya fito a ɗakin, cikin wata iriyar murya da bai san yana da irinsa ba ya ce " Doctor Pls fatan Senorita ta samu lfy? Ya take, ya jikinta, pls na sani bata mutu ba tell me she is still alive!!" Cike da mamaki likitan ke ƙare wa Hammad kallo, can ya nisa ganin duk yadda Hammad ɗin ya shiga cikin ruɗani ya dafa kafaɗarsa kafin ya ce " Alhamdulullah, tana raye! amma mu na  da buƙatar yi ma ta ƙarin jini, because she loses massively blood ( saboda ta zubda jini da yawa ) muna bukatar sa yanzun, Pls follow me to my office Sai na ƙarasar ma ka da bayanin"  likitan ya faɗi hakan tare da kallon Hammad ɗin da yayi masa kane-kane a gaba tamkar mai karatun littafi.
%%%%%%%%%%%%%%%%%%%%%%%%%%%% 

"Uban mai kake cewa haka Faruk!?" Hajia Nenne ta Ida maganarta a lokaci guda tana mai miƙewa daga zaunen da take, zufa har ya soma feso ma ta a jiki, duk kuwa da sanƴin ACn dake fidda ni'imtaccen iska a cikin falon. Haɗiyar  wani uban yawu tayi cikin takaici da musiba ta ce " Zanci mutuncinka Umar! Muddin ka dawo min cikin gidan nan ba da gawar Hammad ba, Kenan kana nufin nayi asarar Naira miliyan uku a banza?! Wallahil azeem bazai saɓuba zaka dawo ka sameni bazai yuba!" daga haka ta tsinke wayar tana fidda huci lumfashinta har sama-sama yake tsabar tashin hankali, ruwan goron faro dake a jiye kan Centre table ta dauka ta kafe kanta sha ɗaya tayi ta ƙarar, wurgi tayi da gorar tana fidda huci ta koma ta zauna kan 3cta tana mai sauke lumfashi tana lallashin kanta, can kamar wacce a ka tsikara ta miƙe da hanzarinta tabar falon ta haura upstairs, tana mai sake nanatawa kanta dole Hammad ya mutu dolen sa!. (Niko Na ce ko ita ce ke riƙe da ran Hammad ɗin sai haka, Allah kyauta ya shirya Allah ka rabamu ta baƙar zuciya).
%%%%%%%%%%%%%%%%%%%%%%%%%%%
A hankali ta soma buɗe idanuwanta dishi-dishi ya soma gitta wa idanun nata da hanzari ta mayar ta rufe idanuwanta tana furta sunayen Allah, a hankali abin da ya faru ya soma dawo ma ta a cikin kwanƴarta, daga lokacin da ta ji abin da Hajia ke shiryawa a kan Hammad har fitowar ta daga gidan Alhaji, wanke tabon fuskarta da tayi zuwa gurin Hammad har kawo harbin da ta jiyo anyi da zafin data ji lokacin da bullet ɗin ke shiganta taaas!, Da sauri ta buɗe idanuwanta tana furta innaalilahi wa'inna ilaihir rajiun lokaci guda kuma tana miƙewa a kan gadon da take. Ƙare wa ɗakin kallo Abee ta shiga yi tana tunanin yaushe a ka kawo ta asibiti da sauri ta soma bin hannunta da kallo daga kan canula da'aka sanƴa ma ta har kawo kan ledan jini da'ake ƙara ma ta takai dubanta, "jini a ke ƙaramin?!" A firgice ta soma ƙare wa ledar jinin kallo a hankali jinin ke ɗiga kuma saura kaɗan ledar jinin ta ƙare, gefe ta sake kallo ya iske wasu ledan jinin har biyu a kan table stand ƙirjinta ne ya buga dum kar dai duk ledar jinin nan ita za'a ƙarawa? In Hajia ta fito naimanta fa? gashi zata yiwa Alhaji girkin dare, da sauri takai dubanta kan agogon ɗakin dake manne a bango ƙarfe 5:30 "shikenan tawa ta ƙare" ta faɗa a can ƙasar maƙoshinta hawaye taji sun soma sauka a  saman kuncinta yau ina zata saka kanta? In har mutanen gidan sun fahimci bata cikin gidan dole suje su sanarwa Hajia don sun sani sarai babu In da ake aikanta zuwa waje. Da sauri ta fisge canula ɗin hannunta ba tare da ta damu da jinin da ya soma rububin fito ma ta ba ta soma kici niyar miƙewa, amma mai? Wani kalan azabtar ciyar zafi taji yana ziyartar ilahirin jikinta da sauri ta koma ta zauna don har wani jiri-jiri taji na naiman kamata, dafa wajen da taji zafin yafi yawa tayi gabanta ya tsinke ya faɗi bandeji daji an liliƙama wajen hakan na nufin a wajen a ka harbe ta," na shiga uku Allah ka kawo min mafita" da sauri ta sake miƙewa tana ambaton sunayen Allah da kyar har ta iso bakin ƙofa, ba tare da ta damu ba ta buɗe ƙofan ta fito, babu kowa a waje ban da nurses dake shige da fice. Hijabi ta hango a kan wani kujera da saurinta ta wuce ta dauka ta sanƴa cikin sauri sauri ta fita daga cikin asibitin duk da ciwon da take ji a cikin jikinta hakan bai hanata fasa barin asibitin ba don tabbas in asirinta ya tonu ta gama yawo. Da kyar da taimakon Allah ta iya ƙara sowa gaban titi, wani iriyar jiri sosai take ji yana ɗibarta har matse idanuwanta take bata son buɗe wa da kyar ta iya tarar abin hawa ba tare da ta faɗi ma sa inda zai kaita ba ta hau tana mai fidda lumfashi da kyar, so kawai take su bar harabar unguwar nan don kar ma a fito naimanta a cikin asibitin, ta tabbatar zuwa yanzun an farga da barin ta asibitin. "Malama ina zan kaiki ne? Naga kamar duk a firgice kike lafiya dai ko?" Mai Napep ɗin ya katse ma ta tunaninta, da sauri ta kallo wajen mai Napep ɗin kafin ta runtse idanuwanta ciwo azaba na cin jikinta da kyar ta iya faɗi ma sa sunan unguwar da zai kaita, koda daga sautin muryarta kawai ya isa mutum sanin bata cikin ƙoshin lafiya. Tafiyar mintuna 30 ya kaisu unguwar, mai Napep ya waigo ya ce "Hajia mun iso" firgit ta dawo cikin hayyacinta da kyar ta soma ƙare wa wajen kallo tamkar yau ne farkon zuwanta cikin unguwar a hankali ta soma fitowa cikin Napep ɗin jikinta duk a sanƴaye, ganin tamkar yarinyar na cikin wani hali ya sanƴa mai Napep In cewa "kiyi haƙuri Allah baki lfy" daga haka yaja Napep ɗin ya bar ta anan tsaye, ƙirjin Abee ke ta faman dukan tara-tara mai zata cewa mutanen gidan? Ina zata shiga ta zana tabonta? waiyoo Allah shine abin da take ta furtawa a ƙasar zuciyarta.
*************************************************
7:30pm, Adnan clinical hospital. 

A Parking lots ya tsaida motarsa ya fito kafin ya zagaya wajen Boot ya soma ciro tarin siyayyar da yayi mata, da taimakon securities ɗin wajen suka shigar da kayayyakin cikin asibitin, straight offishin likitan ya nufa don jin ya jikin nata kafin yaje ya duba tan. Da sallama a samar laɓɓansa ya ƙarasa shigowa cikin offishin, Dr ya ɗago yana kallonsa cike da mamaki ya ce " Muna ta kiran layin ka ba kayi picking ba," murmusawa yayi kaɗan kafin ya ce " bana kusa ne afwan" gyaɗa kai kurum likitan yayi kafin ya ce " patient ɗin ka ta gudu!" Jin maganar yayi kamar daga sama da sauri ya kallo likitan ya ce " what?!" Bayani likitan ya shiga yi ma sa a kan suma basu da masaniyar ficewar ta daga asibitin nurse taje cire ma ta ledar jini ta sanƴa ma ta wani ta taras bata nan an naimai ta sama da ƙasa babu ita babu labarin ta sa'annan babu wanda ya bada tabbacin ganin ficewar ta cikin asibitin. Hammad Ji yayi duniyar nayi masa shawagi he lost her for the second time Kenan ? (Ya Rasa ta a Karo na biyu kenan?") Mai yasa yarinƴar take yi ma sa haka? Ko dai ba mutum ba ce ? Yana da matuƙar tarin tambayoyi da yake so yayi ma ta kuma yake son jin amsa daga wajenta amma bata nan ta gudu! Toh Ina ma taje? Ɗinkin da'aka yi ma ta fa? Jinin da ta zubar fa? Jininsa leda uku aka ɗiba a ka sanƴa ma ta! Mai ya sa ta gudu? Dama ta san shi ne? tabbas ta kirawo sunansa infact ya akayi tasan zaizo wannan wajen? Wa'innan tarin tambayoyin bai da mai amsa ma sa su sama da ita, toh a ina zai sake ganinta?..........
A tsorace take sosai tafi ƙarfin mintuna 10 tsaye ƙeƙam a waje ta rasa yadda zata yi, tabbas ta shiga cikin gidan nan a haka komai nata ya ruguje kenan wanda har ga Allah ba zata taɓa son hakan ya kasance ba, a hankali ta soma takawa a ƙasan zuciyarta tana mai faɗin "Allah kazama gata na". Ƙaramin ƙofar da ta saba fita ta wajen ta nufa a hankali ta shiga buɗe ƙofar gudun kar wani ya ji sautin buɗewar ƙofar a lokaci guda kuma tana mai sadaƙarwa don a iriyar wannan lokaci Asma'u da Hajia Nenne suke zuwa shan iska a farfajiyar wajen, tabbas tana buɗe ƙofar da su zata fara cin karo runtsa idanuwanta kawai tayi a lokaci guda tayi shahada ta sanƴa kanta ciki, tsayawa kawai tayi cak tana jiran taji wani yayi ma ta magana amma har aka kwashe mintina uku babu motsin kowa da ta ji don haka ta soma buɗe idanuwanta a hankali har ta ware su tas a farfajiyar wajen. Wayam ta taras da wajen babu kowa wani mugun ajiyar zuciya ta sake tana mai godewa Allah da hanzarinta ta wuce side ɗin su nan ma taci sa'a babu masu aikin duk suna bakin aiki basu kaiga dawowa ba, da sauri ta shiga cikin ɗakinsu ta rufe ƙofar ɗakin da key ta jingina da bayar ƙofar tana mai sauke ajiyar zuciya, zafin da taji haɓar hannunta nayi shi ya sanƴata saurin runtsa idanuwanta a hankali ta ke furta "wash Allah'am" tana furzar da huci ta bakinta, a daddafe ta ƙarasa bakin gado tayi wa kanta ma zauni tana sake runtsa idanuwanta zafi sosai ke shigarta, ga hannunta dake fidda jini da sauri ta miƙe har tana harɗewa ta shiga toilet dogon ajiyar zuciya ta sauke, fanfo ta buɗe tana mai sanƴa hannunta a kan fanfon, ruwa na tafiya a kai sai data wanke jinin tas sannan ta ɗaure hannun ƙam da ɗankwali, a jiyar zuciya ta sake saukarwa a karo na barkatai, sai da ta zauna ta huta na kusan mintuna 3 kafin ta miƙe ta je gaban mirror ta zana tabon fuskarta, mintuna da basu wuci 7 ba ta kammala zanen sa'annan ta waiga tana ƙare wa kafaɗarta kallo, runtsa idanuwanta ta kuma yi kafin ta fito daga cikin bayin jikinta duk a sake lokaci guda kuwa taji zazzaɓi na ƙoƙarin rufeta "oh Allah!" Ta furta a can ƙasar maƙoshinta, sosai Abee ta so daure wa ta fito taje ta ɗaurawa Alhaji abincin dare amma inaa jikinta yaƙi bata haɗin kai dole ta koma ta kwanta tana fidda zazzafar huci, cire wa mutum bullet a jiki ai ba ƙaramin abu bane ita kam yau ta ga ta kanta. A haka bacci yazo yaci ƙarfinta ba tare da ta shiryawa zuwansa ba but definitely baccin Shi tafi buƙata sama da komai a yanzun wala'allah hakan ya rage ma ta raɗaɗin da take ji a cikin gaɓoɓinta.
*************************************************
Faruk ne durƙushe a gaban Hajia Nenne, Kallo ɗaya zaka yi wa fuskarsa ka tabbatar yana cikin damuwa ba kaɗan ba, ita kuwa oganniyar sai kai kawo take yi tana zagaye Faruk ɗin, Asma'u dake gefe a zaune tana ƙare masu kallo ta taɓe baki, don ita harga Allah haushi suke bata a yanzun. Maganar Hajiar ce ta katse ma ta tunaninta " katattara inaka-inaka nace kabarmin cikin gida Umar!" Runtsa idanuwa Faruk Yayi yana mai tsoron furucin Hajiar,  yanzun fisabililahi ina take so yaje? Tafi kowa sani da nan gidan da kuma aikin da yake yi a ƙarƙashin Company ɗin gidan da shi kawai ya dogara daga ita har shi har ƙanwarsu, laifinsa Hammad bai mutu ba shine zata hukunta sa ta wannan sigar?, Tsawar da ta daka  ma sa shi yayi azamar dawo da shi duniyar tunanin da ya afka, "don ubanka Umar! Baka ji mai nace bane? asarar kuɗi ka riga ka saka nayi su, sai dai na ce maka na Barka da Allah za kuma ka biya su a inda babu su (🙄kuji wannan jahilar matar fa) yanzun nan kafin na buɗe idanuna nake son ka tattara kabarmin cikin gida kafin in Mugun sassaɓa ma ka wallahil azeem" cak Asma'u ta miƙe taje gaban HAJIAR ta ce " toh kuwa in har kince ma sa ya bar gidan nan kema tare zamu haɗu duka mubar cikin gidan, tunda kema ba gidan ubanki bane sa'annan babu ɗan da kika bari yaci miki gadon gidan, ko wallahi tallahi yau In tona miki asiri, tunda mu zamu iya rufa miki asiri ke kuwa baa zaki rufa mana asirin ba kanki kawai kika sa..........." Asma'u ba ta kaiga ƙarasa zancen ta ba taji saukar mari taas!! a saman kuncinta , da hanzarinta ta ɗaga fuskarta tana ƙare wa Hajia Nenne Kallo Faruk ma ɗagowar yayi yana kallonta cike suke duka da mamakinta. Dafe kuncinta Asma'u tayi kafin ta tuntsure da dariya ta ce " kiyi min abin da yafi hakan ma, amma wallahi saina tona miki asiri matuƙar ba zaki rufa mana namu asirin ba" daga haka tayi juyawarta tabar falon ranta a matuƙar hasale. Hajia NENNE ta furzar da huci Asma'u da Faruk na naiman saka ma ta hawanjini amma zatayi maganinsu a kufle ta kallo Faruk ta ce "ka tashi ka tafi karna sake ganinka cikin part ɗina sai na naimeka" daga haka ta juya itama tabar wajen, taɓe baki Faruk yayi ya ce a fili "at least I will still survive anan gidan".
*************************************************
Yafi ƙarfin mintuna 30 zaune ya kife kansa a saman sitiyari ya kasa koda ƙwaƙwarar motsi a cikin motar, tunanin inda ta shiga kawai yake yi ya sani yanzun haka In dai har ita mutum ce toh tana cikin ƙuncin ciwo sabida cire bullet a jikin mutum ba abu bane mai sauƙi, jinƴar wanda a ka harba daban yake da kowani jinƴa sabida harsashe ne ya shiga cikin jikin kuma  a ka cire dole zaman jinƴar ya ɗau tsawon lokaci kafin mutum ya warke. Shi sam bama wannan ke daminsa ba abin da ya fi ɗaga masa hankali shine tsananin jinin data fitar gashi leda ɗaya kawai likitan ya shaida masa ta samu sauran ledan biyun ba'ayi nasarar saka ma ta ba ta gudu, sake dafe kansa yayi a karo na uku yana mai furzar da huci anƴa ba gamo yayi ba? dalili kuwa shine tunda yake a rayuwa bai taɓa sanƴa mace a cikin ransa ba samsam bai taɓa soyayya ba hakanan bai san yadda a ke yinsa ba, shigowar yarinyar nan cikin rayuwarsa duk ta tawarwatsa komai da komai ji yake yi muddin bai sanƴata a cikin idaninsa yau ba bazai iya runtsawa ba infact bazai iya taɓuka komai ba. Da kyar ya iya miƙewa yaja motarsa yabar harabar asibitin ba tare da yasan inda zai nufa ba, tafiya yayi mai tsawon yawa ko wai Allah zai taimaka ya ganta a hanƴa amma ina har wajen 12:30am na dare babu ita babu alamarta, ganin iriyar wahalar da yake sha kansa har wani mugun juya masa yake yayi tunanin komawa gida kawai ba wai don ya gaji da naiman na ta ba a'a sai dai kansa daya matukar riƙe masa yana kuma barazanar bugawa, a wahalce da kuma ikon Allah kawai ya iya isowa cikin gidan straight part ɗin sa ya nufa idanuwansa a matuƙar gajiye, buɗe ƙofar falon nasa ya yi sa'annan ya saka hannunsa ya kunna wuta nan da nan hasken lantarki ya gauraye falon da wadata ciyar haske. Ɗago da manƴa idanuwansa da zaiyi ya sauke su a kan fuskarta, tana zaune tana ƙare ma sa kallo duk sai taga ya canza mata ya dawo wani iri kamar ba Hammad ba fuskarsa duk a sanƴaye kamar wanda abu ke matuƙar damunsa kardai mutanen sunyi nasarar taɓasa? shine tambayar da take yiwa kanta. Tsananin mamakin ganinta a wannan lokacin zaune kuma a falonsa a iriyar wannan lokacin ya sanƴa sa tsayawa cak yana ƙare ma ta kallo.........
Ɗago da manƴa idanuwansa da zaiyi ya sauke su a saman fuskarta, tana zaune tana ƙare ma sa kallo duk sai taga ya canza mata ya dawo wani iri kamar ba Hammad ba, fuskarsa duk a sanƴaye kamar wanda abu ke matuƙar damunsa. kardai mutanen sunyi nasarar taɓasa? shine tambayar da take yiwa kanta. Tsananin mamakin ganinta a wannan lokacin zaune kuma a falonsa a iriyar wannan lokacin ya sanƴa sa tsayawa cak yana ƙare ma ta kallo, da sauri ta miƙe ta iso daf da shi bakinta na karkarwa ta ce " Are u alryt?" Da mamaki ya ci gaba da kallonta ganin bai da niyyar amsata kuma ta san dalilin wannan kallon da yake jefa ma ta ya sanƴata saurin cewa " am sorry naga ka daɗe ba ka dawo bane shiyasa ka na ce bari na shigo naga ko lafiya" ta ida maganar tana muzurai tamkar mara gaskia, a jiyar zuciya ya sauke kafin ya raɓa ta gefenta yayi tafiyarsa ba tare da ya sake koda kallon gefenta ba, har ga Allah ta cire ran zai ma ta magana kamar munafuka haka ta juya zata wuce ta tsinkayo muryarsa kamar wanda a ka tilasta wa magana ya ce " don't repeat that again Asma'u!" Daga haka ya sanƴa kansa ciki yayi tafiyarsa ya barta a wajen, waigowa Asma'u tayi idanuwanta cike da ƙwalla tabi bayansa da kallo sosai take tausayin kanta da kanta don tasani a girme ta girmewa Hammad da kusan shekaru 12 amma So bai barinta ta san da hakan ba a tunaninta watarana Hammad zai so ta, ta sani sarai halayyarta ba abu bane mai kyau, kuma babu namijin da zai so kasancewa da mace mai kaliyar halayyanta, amma akan Hammad sosai take kiyayewa abubuwa da yawa ta rage aikatasu a yanzun, a da tana qin yin wasu abubuwan a gabansa amma a bayansa sumi-sumi kamar kilalliyar kuliya zata sheqe ayarta son ranta, a yanzun sosai take wa kanta faɗa tana hana kanta aikata abubuwa mafi yawa da ta san Hammad baya so kuma Alhamdulullah ko a bayan idonsa yanzun tana iya ƙoƙarinta wajen kiyayewa. Share Hawayenta tayi kafin ta ja ƙafafuwanta tabar part ɗin sa ranta a matuƙar jagule wai sai yaushe Hammad zai tausaya mata ya so ta tamkar yadda take sonsa?!
*************************************************Da shigarsa bedroom ɗin sa ya soma kiciniyar cire kayan jikinsa, bayan ya rage kayan jikin na sa ya nufa toilet hot shower ya sakin ma kansa ya jima sosai yana jin ɗumin ruwan zafin na ratsa kota ina a sassan jikinsa ya ɗau kusan mintuna 50 a haka kafin yayi wanka ya ɗauraye jikinsa haɗida ɗauro alwala ya fito daga toilet ɗin ɗaure da towel a ƙugunsa. Bayan ya gama shafe shafensa da feshe fehen turaruka masu ƙamshin gaskia ya zaro farar jallabiyarsa ya sanƴa, a ƙa'idar Hammad farin Jallabiya itace kayan sakawansa lokutan bacci sam bai shiri da pyjamas ya zira farar jallabiyarsa yayi kwanciyarsa Shikenan ta wadatar masa. Abin salla ya shimfiɗa ya kabbara salla shafa'i da wuttiri ya soma gabatarwa kafin ya ɗaura da nafiloli kafin ya sallame ya duƙufa sosai wajen kai kukansa ga jalla-jalalu mafi yawancin addu'in da yake yi a kan Abeedah ne addu'a yake yi a kan Allah ya kare ta da kwarewar sa a duk inda take sai daya sami nutsuwar zuciya sa'annan ya miƙe ya linke daddumar ya mayar ma'ajinsa, kan bed ɗin sa ya koma ya zauna a hankali naji yana furta "Please come back soon!". 2

************************************************
Wa shegari da safe Abee ta farka bakinta ɗauke da addu'an tashi daga bacci, "awwwwsh!" Ta furta da sauri sakamakon fama hannunta da ta yi mutsuke manƴan idanuwanta tayi tana karanto addu'ar samin warakar kowani iriyar ciwo da manzon Allah SWA ya umarce kowani Musulmi ya karanta a duk sadda ya tsinta kansa cikin halin rashin lafiya "As'alu Allaha al-zheem rabba al-'arshi al-azheem an yashfiyane."
Sai da ta sami ƴar nutsuwa kafin ta miƙe ta shiga toilet sosai jikinta ya rage ciwo sai dai zafin bullet nanan yaƙi barinta wanka tayi ta fito ta shirya cikin uniform ɗin ta kamar koda yaushe kallon a gogo tayi 6:50am ajiyar zuciya ta sauke tana tunanin yadda zata fara zuwa office ayau don fara aiki, Kitchen ta nufa na side din Alhaji bayan ta gama haɗa masa break don yau a menu simple dish ne tea da scrambled eggs sai ta sanƴa kifin sardine a kai ta gasa mai bread ta haɗa komai a tray Kamar yadda ya saba a koda yaushe, fitowa tayi hannunta riƙe da tray ɗin duk da zugin da hannun damarta keyi bai sanƴata fasa kai tray din Kan dining area ba, da shigowarta taji gabanta ya yanke ya faɗi da kyar ta iya saita kanta ta idasa shigowa, idanuwanta ne suka yi azamar sauka a kan samar fuskarsa. Zaune yake kan ɗaya daga cikin kujerar dining ɗin hannunsa riƙe da wayarsa yana daddanawa, a zahirin gaskia zaka dauka bilhakki da gaskia hankalin na sa na a kan wayarsa amma a baɗini sam ba hakan bane, kacokam jinsa da ganinsa da tunaninsa na a kanta (Senorita) Mai take yi Yanzun? Tana ina? ya jikinta? ina ke mata ciwo yanzun? Mai ya saka ta gudu? Mai nene dalilin taimakonsa da tayi? Wake farautar rayuwarsa? Ya kuma a kayi tasan ana farautar rayuwarsa? Mainene sunanta? Waye ita? Mai yasaka take yi ma sa kama da wata wanda ya sani da shuɗewar shekaru?" Wa'innan sune tarin tambayoyin da Hammad ke kissawa a cikin zuciyarsa tun daren jia har wayewar garin yau!.

Satan kallonsa tayi ta wutsiyar idonta a hankali, tana nazartar yanayinsa duk yadda kakai ga iya maitarka baka isa ka faɗa iriyar halin da Hammad ke ciki ba, farin ciki? Bakin ciki? annashuwa? walwala? DSS yake ciki ko akasin haka a'a ba zaka taɓa iya tantancewa ba shi mutum ne da ko yana cikin damuwa da wuya ka iya karantar hakan a saman fuskarsa. "Ke!!" Taji ya kirata a tsorace ta ɗago tana kallonsa shima kallon na ta yayi sau ɗaya kafin ya kahawar dakai gefe, kamar kuma wanda a ka mintsila ya sake kai dubansa wajenta wannan karon babu inda ya dire kwayar idanuwansa sai a kan hannunta na dama wanda alamun taruwar jini ya gama bayyana a samar hannun na ta abinka da farar fata! tsura ma wajen yayi ido baya koda kyaftawa, Abee kuwa tsabagen ruɗewa jikinta har ya soma ɓari, shikenan innaalilahi wa'inna ilaihir rajiun yau karyarta ya ƙare shikenan Hammad ya ganota hande en boni(yau na Banu) Abee ta faɗa a ƙasar zuciyarta ba takai ga dawowa daga cikin ruɗun data shiga ba ta ji ankira sunanta kai tsaye "Abeeedah!" Da sauri ta ɗago jikinta babu inda baya shirin soma rawa, ganin mai kiran na ta ya sanƴata daɗa firgita shikenan fa ita yau tata tazo daf da qarshe!...........

Post a Comment for "KAWUNA CHAPTER 6"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...