Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

HUTU CHAPTER 9

HUTU CHAPTER 9

- - Post a Comment
HUTU
CHAPTER 9


Wanka Kausar tayi ta canza kaya sannan ta shigo dakin Binta tace "Binta hada school Uniform dinki na gobe kisa a jaka ki fito mu tafi", tashi Binta tayi dukda batasan ina zasu ba ta hada abinda zata hada ta fito, fita sukayi bayan Kausar ta sallami Hajara ta kuma shaida mata base tazo gobe ba sannan suka fita, a mota ta dau wayanta taga misses calls din Mom dinta ta kirata tareda cewa "hello Mom.... Eh yanzu naga missed calls dinki... Gani nan zuwa", da haka ta kashe wayan tace "Binta zan kaiki gidan mamana ki kwana a chan dan basan wani lokaci za'a kawo Uncle dinki ba, kuma a chan gidan bazan samu wanda ze kulamin dake ba, saboda haka zan kaiki gidanmu kinji", "toh anty", Binta ta amsa mata. A compound din gidan tayi parking ta fito suka shiga Mom dake zaune parlor tace "har kun karaso", "eh Mom", gaisawa sukayi suka gaisa da Binta ma sannan Kausar ta zayyane ma Mom abinda ke faruwa dan itama hankalin ta ya kasa kwanciya sannan Kausar ta shaida mata anan Binta zata kwana, "ba matsala, Allah ya iso dasu lfy", duk suka amsa da "ameen", Mom tace "amma ya naga kaman bakida lfy", "Mom zazzabi ne, kuma guess what", "ke dan Allah ni raba ni, in zan iya wani guessing", a hankali Kausar tace "I'm two months preggy", ta fada tana rufe fuska Mom kuwa dadi taji sosai tace "shine bazaki zauna wuri daya ki huta ba kiketa lalawulo, kedai kinason yawo amma yanzu dole ki huta, bari na kira driver ya kaiki gidansu Hydar din, ki bar motarki a nan", itadai Kausar shiru tayi tana tunanin tayaya zata fadawa Hydar tana dauke da cikinshi, tasan shima zeyi murna kaman yadda kowa keyi, "Allah ka dawomin dashi lfy", ta fada a ranta dan harga Allah basusan Hydar na coma ba, dan koda aka fadawa Abba Hydar ya shiga state of coma be fada musu ba saboda kar hankalinsu ya tashi, shiyasa duk suka ware dan basuyi tunanin raunin da yaji yayi tsanani ba.Kaman yadda sukesa rai karfe shida aka kirasu aka shaida musu su Hydar sun iso amma an wuce dashi hospital, fada musu hospital din akayi, Ummi da Anty maryam da Kausar suka tafi bayan sun bar Zeena gida dan ta kula da yaran Anty Maryam Faris da Amna. Koda suka isa asibitin Abba suka tarar zaune a reception din, suma zama sukayi Abba yace "ai da kun bari gobe kuzo tinda yamma tayi, ba'a ma dade da shigowa dasu ba", "ai hankalinmu baze kwanta ba idan bamu ganshi ba", cewar Ummi, girgiza kai kawai yayi bece komai ba dan yanzu wani sabon tashin hankalin zasu tarar musamman ma Kausar dan ya lura har 'yar rama tayi, suna zaune wani doctor yazo yace "Alhaji an gama komai, zaku iya zuwa ganinshi amma banda hayaniya", Kausar dadi kaman ya kasheta duk suka mike Abba yace "a'a ku bari matarshi ta soma shiga taga halin da mijinta yake tukun nan", kallon Kausar duk sukayi Ummi ta mata alama da taje, batayi musu ba tabi bayan doctor din cike da zumudin ganin Hydar dinta.


2

"Yana ciki shiga", doctor din ya fada sannan ya juya, a hankali ta murda handle din kofan sannan ta shiga kirjinta na dukan uku uku, tsayawa tayi bakin kofan tana kallon halin da Hydar ke ciki, mijinta, abin alfaharinta, masoyinta, wanda ya koya mata sonsa tasan meye so har ta aureshi ya koya mata zama dashi dukda she's not the perfect wife for him haka yake hakuri da dayawa daga cikin halayenta, ginshikinta, katangarta, aljannarta, yau shine a kwance rai a hannun Allah, kukan da yazo matane yasa tasa hannu tayi saurin toshe bakinta amma wannan be hana kukan fita ba, da sauri ta karasa gaban gadon tana kallon yadda duk jikinshi waya ne, ga computer nan gefe yana nuna heartbeat dinshi which is so slow kaman ze iya tsayawa at any time, for a moment ji tayi gabadaya duniyarta ya tsaya ya daina aiki, ji tayi kaman itama heartbeat dinta baya aiki, ganinshi a wannan halin ya tabbatar mata da lallai son da takewa Hydar yayi nisa, so ne wanda ita kanta bazata iya fadan ga adadin son da take mishi ba, so ne wanda ni mzzdaddy bazan iya fasaltashi ko rubutashi a littafi ba.


Lokaci daya ta tuna da abinda ke cikinta wanda wani tsastso ne daya fito daga jikin Hydar dinta, tana murna zatazo ta gaya mishi tana dauke da cikinshi amma se gashi ko motsi bayayi, badan tana ganin yadda numfashinshi ke fita a hankali ba bazatace yanada rai ba a yadda ta ganshi, zama tayi kan gadon tareda riko hannunshi wanda babu drip a jiki ta dora kan cikinta cikin kuka tace "My hubby look I'm carrying ur baby, our child, the symbol of our love, wake up and let it feel ur love, our baby needs u, we need u, pls don't be like this, fight it and wake up pls", kuka ne yaci karfinta sosai ta dora kanta kan kirjinshi tana kuka sosai kaman ce mata akayi Hydar ya mutu. Tin shigowarta har tsayuwarta har zuwa magananta dama kwanciya da tayi kan kirjinshi Hydra na jinta amma ba daman tashi, so yake ya bude ido amma abu ya gagara, so yake ya motsa koda yatsa ne ya kasa, so yake ya bude baki yace mata he loves them both her and the baby and everything will be alright, he will be there for them amma abu ya gagara, a lokacin abu daya ne yazo mind dinshi, shine ba makawa ya mutu dan dama ai ance mamaci najin duk abinda ke faruwa a kusa dashi sedai ba bakin magana ne.


Yanaji su Ummi suka shigo, tin a waje Abba ya riga ya sanar dasu halin da ake ciki saboda haka sunsan abinda zasuzo su tarar, ba karamin tausayi Kausar ta basu ba, lokaci daya ta canza kamanni, dagota Ummi tayi ta rungumeta tana bubbuga bayanta a hankali alaman rarrashi, itama din dai hawayen takeyi haka ma Anty Maryam, Abba ne ya shigo yace "kuzo kuje gida, munyi waya da Khalil yana zuwa, zan zauna dashi kafin Khalil yazo", da sauri Kausar ta girgiza kai tareda rike hannun Hydar kaman za'a kwace matashi tace "Abba ni zan zauna anan, dan Allah karkace na tafi gida pls", sosai ta basu tausayi amma bazeyu su barta ba dubaga juna biyu da take dauke dashi, Ummi ce lallashe ta akan tayi hakuri su tafi gobe da sassafe se su dawo, da kyar Kausar ta harda suka wuce se juyowa takeyi tana kallon Hydar dan gani takeyi kaman idan ta tafi kafin safe za'a ce mata ya mutu amma babu yadda ta iya haka suka wuce a mota bacci ya kwashe ta.Washegari tinda sassafe ta tashi Ummi da kanta tayi mamaki dan a gidan ta kwana, ta riga Ummi tafiya asibitin, seda taje sannan Khalil ya mata sallama ya wuce wurin aikinshi, taba jikin Hydar tayi taji da zafi da sauri ta kirata doctor akazo aka dubashi tareda mishi allura, a halin yanzu Hydar yasan a asibiti yake kuma he's in a state of coma, he's doing everything he can na ganin ya tashi ko saboda Kausar amma abu ya gagara, he's fighting for his love and baby amma da alama faith is not on his side, nurse ce ta shigo da ruwa cikin plastic bowl da towel ta gaishe da Kausar ta amsa mata da kai dan bata ganin zata iya magana, gani tayi nurse din ma kokarin gogewa Hydar jiki da sauri tace "me zakiyi?", zan goge mishi jikine", nurse ta bata amsa, wani wawan harara ta aikawa nurse din tareda cewa "kawo na mishi, mijina ne, kinjiki da karfin halin kinga matar mutum zaune amma ki wani zo kice zaki goge mishi jiki", cikeda masifa Kausar ke magana nurse din kuwa cikin jin haushi tace "Allah ya baki hakuri", sannan ta fita, Hydar dake jinsu seda ya murmusa kuma sosai Kausar taga alaman yayi murmushi abin har tsoro ya bata, gashi dai a kwance baya motsi amma yana mata murmushi, da sauri ta ajiye towel din ta fita tana neman doctor, tareda suka shigo da doctor tace "ka gani, dazu yayi murmushi", shima doctor din murmushi yayi yace "ai dan yana jinki ne, kila kin fada wani abu ne daya sashi murmusawa", cikeda mamaki tace "yana jinafa kace", doctor yace "sosai", dadi kaman ze kashe Kausar ai da ta koma ta zauna tareda cewa "pls mijina indai kana jina toh prove it to me I want to see ur smile again, pls smile for me huh", ai kuwa ya sake mata murmushi wannan karon hatta doctor din ya gani, tsabar murna seda Kausar tayi hawaye, hannunshi ta riko ta kaiwa peck tareda cewa "don't worry my husband, Insha Allah we will fight this together, i know u won't give up on me", yanaso ya bude baki ya amsa mata amma ba dama, fita doctor din yayi ita kuma ta goge mishi jikinshi, ba jimawa sega Ummi da Abba harda breakfast suka kawo mata, nan take shaida musu abinda ya faru dazu wai Hydar yayi murmushi har tausayi ta basu ganin yadda take jin dadi saboda yayi murmushi, suna nan zaune anty Maryam tazo da mijinta suka gaisa ya duba lfyn Hydar tareda yiwa su Ummi gaisuwa sannan ya wuce aiki yabar Anty Maryam a wurin.
Yau sati daya kenan Hydar na kwance, kowa zuwa yake ya gaishe shi ciki kuwa harda Binta dasu Mom din Anwar da El Ameen wanda kullum se yazo, cikin sati dayan nan Kausar ta rame ta dishe saboda morning sickness daya sata gaba amma wannan baya hanata zuwa asibiti, da taji jikin yadan yi sauki take cewa driver ya kaita, anyi mata magana anyi mata fada amma duk a banza, tinda doctor yace mata Hydar na jin abinda take fada ta zama me surutu, idan tana tareda shi ita kadai a dakin ta kama mishi surutu kenan daga karshe kuma tasa kuka saboda yadda take jin ciwon rashin farkawarshi, tsoronta daya karyaki tashi gabadaya. 
Yau zaune take ita kadai a dakin tayi shiru tana kallonshi kawai idonta cike tap da hawaye yayin da tunaninta ya lula wata duniyar daban, a hankali ya fara motsa hannunshi kafin ya fara kokarin bude idanunshi, kar ya saukesu a kan Kausar wacce a zahirance shi take kallo amma a badinance bashi take kallo ba dan batama san ya farka ba, kallonta yakeyi lokaci daya yaga ta rame ta dishe wanda yanada tabbacin yanada nasaba da cikin dake jikinta da kuma rashin lfyarshi, hannunta dake cikin nashi ya matse saboda ya dawo da ita daga duniyar tunanin da take ciki, taji matsar saboda haka ta dawo daga tunanin da ta fada kar taga idon Habibinta a kanta, hawayen da suka cika mata ido suka zubo  lokaci daya, bata yarda ya farka ba seda taji muryanshi yace "stop crying it's not good for our baby", duk da muryanshi baya fita taji me yace. 
Mikewa tayi ta kai mishi wani wawan runguma not minding a kwance yake kuma beda kwari sosai, shima rungumeta yayi hawayenta na sauka kan kirjinshi, mikewa tayi tana kallonshi hannunta kan fuskarshi ta rasa me zatayi, ta rasa me zatace mishi, daga karshe dai ta mike tareda cewa "bari na kira doctor", fita tayi ba dadewa suka dawo tareda doctor da nurse, nan suka dubashi sukaga he's stable sannan suka ciccire mishi drip da sauransu tareda cewa anjima zasu dawo asa mishi wani drip din bayan  ya huta, suna fita ya mike a hankali da taimakon Kausar tasa mishi pillow a baya ya jingina yana kallonta, sosai ta bashi tausayi saboda yadda ta rame har hannun rigarta na faduwa, "zanyi wanka", kawai yace mata dan yanaso yaji dadin jikinshi ko yaji kwari, wayanta ta dauka ta kira Ummi ta shaida musu Hydar ya tashi dama abinci sukaje  kawowa sannan tace su hado mishi da kayan da zesa. 


"Bari na hada maka ruwan wankan", kai ya g'ada mata ta shiga bathroom din yabi bayanta da kallo sannan ya juya yana sauke numfashi, be taba jin aikin soja ya fita mishi a rai ba se yanzu da yaga yanda akewa 'Yan uwanshi kisan wulakanci a gabansu, a kashesu kuma a tafi musu da gawa, tana fitowa ta taimaka mishi yayi wanka yayi alwallah ya fito daure da towel suka zauna kan gado, hannu ta kai kan kirjinshi inda aka harbeshi tabi tana zagaye dinkin da akayi a wurin, rufe idonshi yayi danji yayi kaman tana susa mishi inda ke mishi kaikayi ne, bude idon da zeyi yaga tana hawaye hannu ya kai ya goge mata hawayenta sannan yace "pls for our baby's sake stop crying, ki daina min asarar hawayenki, kinsan banason ganinsu, humm", kallonshi tayi da murmushi a fuskarta tace "how did u knw I'm preggy?", "ke kika fada mun", ya bata amsa yana kallonta, "ashe doctor beyi karya ba dayace kana jina", ya kada kai yace "duk inajin komai, tashi kawai ne ya gagareni, har koran nurse dinda kikayi saboda zata goge min jiki duk naji", dariya tayi shima ya dara, Khalil ne ya shigo da sallama fuskarshi dauke da murmushi yace "soja mazan fama, ka farfado", hararanshi Hydar yayi yace "dana tashi se akayi yaya", dariya Khalil yayi yace "ba laifinka bane, daka sheka barza'u da bazaka samu bakin yimin magana, kiris fa ya rage ka sheka lahira se aka tausaya maka", dariya Hydar yayi yace "dan iska, ai dama nasal so kake na mutu, toh ban mutu ba ina nan da raina", Kausar dake jinsu murmushi kawai tayi Khalil yace "matarmu ga kayanshi inji Ummi, itama tana nan zuwa", karban kayan tayi Hydar yace "bakinka ya sari  danyen kashe, yaushe kuma ta zama matarka wannan matata ce wai wani matarmu", dariya Khalil yayi ya fita dan ya basu wuri. 


Jallabiya ne mara nauyi se boxers ta taimaka mishi yasa ta shimfida mishi sallaya yace "kwana nawa nayi a kwance", "fifteen days", ta bashi amsa, nan ya fara biyan bashin salolinshi dukda jikinshi ba kwari. Ummi ce ta shigo da abinci sosai taji dadin ganin danta ya tashi, hira sukayi sosai ta zuba mishi abinci ya kuwaci sosai dan dama shi baya wasa da cikinshi, kan kuce me dakin Hydar ya cika da family masu zuwa ganin lfynshi, Zeena ma tazo idon Khalil kyam a kanta duk inda tayi nan idonshi yake, badan abinda ya samu Hydar ba da yanzu an nema mishi izinin fara zuwa wurinta. Binta daga school driver ya ajiyeta a hospital, koda ta tambayeshi meyasa be fara kaita gida ba ce mata yayi Hajiya ce tace a taho da ita hospital din. Dakin Hydar ta shiga da sallama ta duk suka amsa suna juyowa, kallonta Hydar yakeyi yaga ta kara girma ba kaman last time daya ganta ba, gaishesu tayi duk suka amsa mata sannan taje kusa da Kausar ta tsaya a hankali Kausar tace "look Uncle dinki ya tashi, jeki gaishe shi", ba musu ta karasa bakin gadon tace "Uncle ya jiki", murmushi yayi yace "jiki da sauki Binta, ykk, ya karatu, hope kina ganewa?", kada kai tayi tace "duk lfy kuma ina ganewa", yace "gud a maida hankali humm", murmushi tayi dago kanda zatayi taga Ummi ta kura mata ido, sauke kanta tayi a daidai lokacin da Abba ya shigo da sallama, bayan gaishe gaishe Ummi tace "alhaji kaga abinda na gani?", cike da rashin fahimta yace "me kika gani",  "kalli yarinyar chan", ta fada tana nuna Binta, kowa maida kallonshi kan Binta yayi ba kaman Abba daya kasa dauke idonshi a kanta, "wannan kaman Aisha sak babu abinda ya bambamtasu se girma", cewar Abba da har yanzu yake kallon Binta dan dagashi har Ummi yau suka fara ganinta. 

Binta da kanta ya daure mamaki takeyi ya akayi suka san sunan mahaifiyarta, toh kodai sun santa ne, kodai sune familyn mamarta, kallon Abba ta sakeyi taga kamaninshi da mamarta, "tambeyishi kiji, kila dan uwan mahaifiyarki ne", zuciyarta ta fada mata, wata zuciyar kuma tace "kice mishi me, dan kawai ya kira Aisha, ai Aisha na dayawa a duniya", da haka taja bakinta tayi shiru dan bataso ta tambayesu suce ba haka abin yake ba, Abba ne ya katse musu tunani da cewa "badan Aisha tawa batada aure ta rasu ba dase nace ba makawa wannan 'yarta ce dan kamanin ya baci", a hankali Ummi tace "ni hanya ba 'yarta bace kuwa, ko mu tambayeta muji", Hydar da kanshi ya gama daurewa yace "Abba, Ummi wace Aisha kuke magana", Ummi ce ta bashi amsa da cewar "Kanwar mahaifinka ce, uwa daya uba daya, hatsari tayi a hanyarta na zuwa Adamawa, koda mukaji shiru kwana biyu ba lbrn ta ba lbrn driver dinda ya kaita se muka kira Hajiya kakarka itama Allah yayi mata rasuwa ta shaida mana Aisha batazo Adamawa ba, nan hankali ya tashi akasa 'yan sanda nemota, daga karshe dai motan aka gani a mararraban kauyen cakawa driver dinta ya rasu amma ita an nemeta sama da kasa ba'a ganta ba". 


Shiru Hydar yayi na en dakiku da sauri Kausar tace "Binta ai kema gada Adamawa kike ko?", "eh anty", ta bata amsa kanta a daure, Hydar yace "ya sunan kauyenku", a hankali tace "cakawa", Abba da sauri yace "ya sunan mahaifiyarki?", tace "Aisha amma indo ake cemata", nan take wani tunani yazo ma Hydar ya kalli Abba yace "Abba kila fa a lokacin bata mutu ba, kila wani ya ganta ya taimaketa", shiru Abba yayi sannan yace "idan ba mutuwa tayi ba meya hanata dawowa gida", daga sama suka tsinkayi muryan Binta tana cewa "Abbana yace mantawa tayi, ta manta komai sunanta kawai ta tuna se garin da ta fito", kallon kallo aka somayi a dakin Anty Maryam tace "da ayar tamabaya a nan wurin, mu bari yarinyar nan ta bamu lbrnta a tsanake, inyaso idan ta kama muje har kauyen dan neman karin bayani ne se muje", kowa ya g'ada kai alaman gamsuwa sannan Abba ya juya wurin Binta yace "baiwar Allah bamu lbrnki".Kaman yadda Anty Maryam ta bukata haka Binta ta basu lbrnta tin daga lokacin da ta soma girma familynta ke kiranta dame kashin tsiya har zuwa gobarar da ya kama family house dinsu, zuwa karo auren da Malam Tanimu yayi, zuwa bakar wahalan da ita da mahaifiyarta sukasha hannun Zinaru, zuwa rasuwar mahaifiyarta harma da mahaifinta, da zuwan ta Abuja da dalilin da yasa su Zinaru suka turota Abuja, gabadaya seda ta fada musu babu abinda ta bari, kaman yadda taba Kausar lbr haka ta basu, sosai suka tausaya mata tareda tsine ma Zinaru. 

+

Abba ne yayi gyaran murya sannan yace "baiwar Allah kinga rayuwa at young age, allah ya saka miki", duk suka amsa da "ameen" yaci gaba da cewa "a kauyenku kina ganin akwai wanda yasan mahaifinki sosai daze iya bamu lbrn haduwarshi da mahaifiyarki", kada kai tayi tace "akwai Malam Mamman aminin mahaifina ne, da mai gari ma", g'ada kai yayi yace "ba matsala idan an sallame Hydar daga hospital zamuje muyi tambaya Allah ya tabbatar da alkhairi", duk suka sake amsawa da "ameen", Hydar kuwa se kallonta yakeyi wato all this while da take gidanshi cikin 100% akwai 97% possibility na kila cousin dinshi ce, what a small world. 


A ranan se dare duk suka watse Kausar tace gidanta zata koma kuma da Binta zata tafi, Ummi badan taso ba ta bari driver ya sauke su a gida, suna shiga Kausar tace "it's good to be back", juyowa tayi ta kalli Binta datayi shiru tin a hospital tace "Binta ya dai", ajiyar zuciya ta sauke sannan tace "anty tsoro nakeji, idan kuma ba mahaifiyata suke neme bafa", zama Kausar tayi ta janyo Binta ta zaunar da ita gefenta sannan tace "karki damu Binta, ai ko ke ba family su bace inaso ki sani yanzu kinada family, ni dinnan ai family dinki ce koh", kai ta g'ada tace "anty nagode da abubuwan da kikemin", murmushi Kausar tayi tace "don't mention, banace ki daina min godiya ba, tashi kije ki cire uniform ki watsa ruwa kiyi sallan isha, ai kin koshi koh? Koda abinda kikeson ci?", "a'a anty na koshi bari na watsa ruwa", mikewa tayi ta shige dakinta Kausar kuma ta dau waya ta kira Hajara tace mata tayi resume aiki gobe, kuma tazo da wuri saboda Binta zata school. 


2weeks later

Alhmdllh Hydar lfy ta samu yau za'a sallameshi daga hospital, suna zaune suna jiran doctor ya kawo musu takardar sallama harda Binta dayake yau weekend, Hydar yace "idan an sallameni gidan Ummi zamu fara zuwa dan tace ta dafa mun delicious", Kausar tinda take bata tabajin rashin iya girkinta ya dame ta ba se yau dataji mijinta na cewa gidan Ummi ze fara zuwa, sosai taso ace gida ya fara zuwa amma yanzu dole se sunyi branch, "ka bari muje gida, seta aiko Zeena da abincinka", girgiza kai yayi yace "nah, inaso tayi feeding dina da kanta", harara ta watsa mishi tace "nice bakaso nayi feeding dinka koh", kallonta yayi dan yaji bitterness lokacin da tayi magana ya girgiza kai yace "ba hake nake nufi ba", "toh in ba haka kake nufi ba muje gida na bari Hajara tayi maka girki", daga sama taji yace "Allah ya tsareni da cin girkin me aiki", shi kanshi besan ya fada ba seda maganan ya fito sannan yayi register a mind dinshi, kallon Kausar yayi yaga ranta ya baci Binta tace "uncle abincin yayi dadi, tare mukayi, na tayata, kaje kaci", kallon Binta yayi yace "ni ba dadin abincin bane matsalata ba, tsaftar abinci, yi hakuri Binta amma bazan iya ci ba". Doctor ne ya shigo ya katse musu maganan da sukeyi ya basu takardar sallama, basu dade ba suka tattara kayan su suka bar dakin Kausar kam ta cika fam kama zata fashe, a kunne ya rada mata "my wife ki daure ki koyi girki saboda in dinga ci kina feeding dina kinji", rai a bace tace "kasha kuruminka ka jira har Allah ya saukeni lfy, zan koya girki kodan ka daina yawon zuwa gidan Ummi cin abinci, kar taga kaman bana kula da kai ne", cike da mamaki yace "da gaske zaki koya girki", tace "hmm I promise", ta fada tana turo baki, murmushi yayi tareda kama kumatunta yana cewa "awwwnn my wife's so cute", bige mai hannu tayi tace "pple are watching", "and so u are my wife", bata tanka shi ba har suka shiga mota suka dau hanyar gidan Ummi. Da murna Ummi ta tarbesu ba bata lokaci duk sukayi dinning harda Abba da Anty Maryam full family sukayi, gabadaya se Binta taji kaman da en uwanta take zaune har addu'a takeyi Allah yasa en uwanta ne, bayan sun gama cin abinci Hydar yace "Abba ya maganan zuwa cakawa din, akwai shi", Abba yace "kwarai akwai shi, kusa rana, amma nida Hydar kawai zamu se kuma Binta", "shikenan Abba tinda gobe sunday muje gobe", Abba ya g'ada kai yace "Allah ya kaimu seki shirya". Abba ciro wayanshi yayi ya shiga gallery ya fito da hoton Aisha daya dauka a family album ya nunawa Binta yace "wacece wannan", kallon hoton tayi sosai sannan tace "tana kama da inna ta" murmushi Abba yayi ya mayar da wayan aljihu yace "gobe zamu tabbatar", Binta kuwa badan wannan da alama kanta ya waye ba da tace innarta ce amma koda ta taso bata taba ganin innarta cikin lesi ba balle tace itace, se yamma suka bar gidan Ummi suka koma gida, suna shiga Hajara ta musu sanda zuwa tana me zubawa Hydar ido tana yaba hallitarshi, kallo daya ya mata yaji bata kwanta mishi ba amma gudun kar ya samu matsala da Kausar se ya watsar ya amsa gaisuwarta sannan yayi dakinshi wanda yake nan a share fes se kamshin turare ke tashi, Kausar ce ta biyo bayanshi tace "Hubby na zakayi wanka yanzu", kai ya g'ada mata alaman eh, ta ajiye mayafinta sannan ta shiga bathroom ta hada mishi bubble bath, koda ta fito har ya cire kayanshi ita yake jira tace "shiga kayi na hada maka ruwan", murmushi yayi yace "ban yarda ba ke zakimun", "da alama yau kana jin rigima amma muje nama", murmushi yayi yace "cire kayanki karki jika", tace "bazan jika ba muje", yace sam besan zanjen ba, haka dan ba yadda ta iya ta cire tabishi suka shiga tub din tare suna nishadantar da juna har suka gama suka wanke jikinsu suka fito, nannade ciwon bathrob ya dauko ta be ajiyeta ko ina ba se kan bed yana murmushi yace "I miss u alot", yayi kissing hancinta zuwa cheeks dinta zuwa wuyanta daga karshe dai ya tsaya a bakinta, bathrob dinta ya kwance ya shafe cikinta sannan yace "baby daddy is going to show you how much he loves you in his own way", da fadan haka yayi kissing din mararata da nan kuma salo ya canza nace bari na basu privacy.
Kaman yadda suka tsara haka suka shirya Hydar da Binta sannan suka biya suka dau Abba suka dauki hanyar Adamawa, da yake tafiyan safe sukayi kafin zuhur sun shiga garin da tambaya suka gane kauyen, kallon ko ina Binta keyi tana tunowa da rayuwarta ta baya, duniya kenan komai tafiya yake kaman ba'ayi ba, ita ta musu kwatance har gaban gidan mai gari sukayi parking, washe hakora mai gari dake zaune gidan bishiya yayi yau yaga masu babban mota da babban riga a garinshi, sallama su Hydar suka musu duk mutanen wurin  suka amsa sun kuwa ci sa'a Malam Mamman ma na zaune wurin amma gabadayansu babu wanda ya gane Binta.+

Zama su Abba sukayi Binta kuwa ta duka daga chan baya tana gaishesu duk suka amsa, shiru gabadayansu sukayi mai gari yayi gyaran murya yace "amma ban gane fuskokin ba", murmushi Abba yayi irin nasu na manya yace "bakin fuska ne, amma nasan zaku gane wannan", ya fada yana nuna Binta, gabadayansu kallonta sukayi mai gari yace "kai ban gane ta ba", Mallam Mamman yace "niko kaman nasu na gane ta, seta min kama da Bintoto 'yar gidan marigayi Malam Tanimu", murmushi Binta tayi a ranta tace "har nayi canzawan da basu gane ni ba", Hydar ma murmusawa yayi yace "ba kama bane, itace", gabadaya wurin suka kabbara "Allahu akbar", Mallam Mamman yace "ikon Allah Bintoto kece", tace "Mallam nice", g'ada kai sukayi suna kara kallonta, suna kallon yadda tayi haske tayi fresh ga wani kyau data kara, sannan ko ba'a fada musu ba sun sannan tareda manyan mutane take, "toh me hadinsu da ita, ita da taje aikatau, kodai iyayen gidanta ne inda take aiki?", tambayar da suka dinga yiwa kansu kenan dan kuwa Zinaru ce musu tayi Binta aikatau ta tafi. Mai gari ne ya gyara zama yace "ince dai lfy", Abba yace "lfy lau, dama maganace zamuyi idan ba takura", da sauri mai gari ya washe hakora yace "a haba ina takura a nan, ai ba matsala, amma sedai an kira sallah, kwa bari mu sauke farilla tukunnan koh", Abba yayi murmushi yace "Bismillah", nan duk suka mike Binta kuma akace ta shiga cikin gida. Matan mai gari koda suka ganta basu gane ta ba har seda ta fada musu ko ita wacece sosai sukasha mamaki, sannan ta fada musu abinda ya kawota amma koda wasa bata tambayi inda Zinaru take ba dan a ganinta idan Zinaru taji ta dawo zata hanata komawa. Ana idar da sallah Kallamu ya shigo gidan dan a masallaci yaji lbrn ai Bintoto ce tazo da masu motar nan, sosai taji kunyar ganinshi dan tunawa da tayi da lokacin da yake cewa yana sonta, badan Zinaru ta hana aurensu ba da yanzu fa mijinta ne, kallonta yakeyi yana mamakin girman da ta kara da wayewa, gaisawa sukayi sannan ya kira matarshi suka gaisa da Binta har mamaki take wai yayi aure. 
Chan waje kuwa Abba da Hydar sunyi mamakin ganin a gaban gidan mai gari ake sallah da alama dai ba masallaci a kauyen, bayan sun idar Hydar ya tabo wani dan saurayi dake gefenshi yace "babu masallaci a nan ne?", saurayin ya g'ada kai tareda cewa "ai har islamiyya a nan gaban gidan akeyi, amma naji ana cewa wai za'a gina masallaci", g'ada kai Hydar yayi ba tareda yace komai ba, duk an watse saura yara daketa kallon motarsu Hydar suna shafawa seda aka koresu sannan suka tafi. Bayan wuri yayi tsit Abba yace "dama so muke muji lbrn Binta, tindaga mahaifiyarta har mahaifinta, ta bamu lbrnta a matsayinmu na wacce ke zaune a hannunmu amma bamu gamsu da lbrnta ba, sedai ta shaida mata muddin mukazo nan toh za'a warware mana komai cikin sauki", gyara zama mai gari yayi yace "eh toh Bintoto dai marainiya ce, mahaifiyarta kuma dukkanmu nan babu wanda yasan asalinta dan kuwa hatsari sukayi a mararraban kauyen nan Mallam Tanimu ya taimaka mata amma sedai ta manta komai nata wanda wannan yasa ta cigaba da zama a wurin mahaifiyarshi har yayi sha'awan aurenta, anyi aurensu Allah ya azurtasu da Bintoto wacce taci sunan mahaifiyar  mallam Tanimu, bayan tasowan yarinyar gobara ta kama gidan 'yan uwan mahaifinta saboda haka basuda kowa a kauyen nan, sannan akwai matar mahaifiyarta me suna Zinaru", nan mai gari duk ya basu lbr a nutse har ya kai aya inda ya fada musu amma aikatau Zinaru tace zata kai Bintoto. 
Jinjina kai Abba yayi sannan yace "idan kaga hoton ita Indo din zaka ganeta", "gaskiya bazan ganeta ba", cewar mai gari, Mallam Mamman ne ya gyara zama yace "ni zan ganeta", da jin haka Abba ya ciro wayanshi daga aljihu sannan ya fito da hoton ta ya nunawa Mallam Mamman, "tabas Aisha ce wannan matar aminina Mallam Tanimu", ajiyar zuciya Hydar ya sauke yana hamdala a zuciyarshi, shima Abba hamdalan yakeyi sannan ya juyewa mutanen haduwarsu da Binta da lbrnta data basu, salati dukkansu sukasa jin wai karuwanci Zinaru ta tura Binta amma Allah ya kubutar da ita ya gefa ta hannu na gari wanda ya kasance ashe ma hannun 'yan uwanta na jini ta fada ba tareda ta sani ba, dan kuwa Abba ya shaida musu Aisha mahaifiyar Binta kanwarshi ce uwa daya uba daya wacce tayi hatsari suka nemeta suka rasa. Tsinewa Zinaru sukayi suna kwashe mata albarka tareda Allah wadar da hali irin nata, Hydar ne yayi gyaran murya duk suka maido da hankalinsu kanshi yace "ko za'a iya kiran ita Zinaru din tazo nan yanzu dan kuwa se an hukunta ta daidai da laifinta", murmushin takaici Mallam Mamman yayi yace "ai Zinaru tinda Bintoto ta bar garin nan da watanni itama aka nemeta aka rasa, se kwanaki ta dawo tasa gidan margayi kasuwa, ganin haka muda mai gari muka yanke hukuncin siyan gidan da kudin fisabillahi da muke tarawa duk juma'a in yaso se mu gina masallaci dan gwamnati ba ruwanta da kauyen nan, toh tinda ta siyar mana da gidan koh kurarta bamu sake gani ba", jinjina wa su Abba sukayi Hydar yace "ba damuwa, nasan tana birni, zamu nemeta duk inda  ta shiga, sannan inaso in shaida muku zan dauki nauyin ginin masallacin, idan akwai filin siyarwa a nan ku sanar dani zan siya a gina Islamiyya", murna sosai sukayi, shi kanshi Abba abinda ke ranshi kenan amma Hydar ya rigashi furtawa, Mallam Mamman ne ya jero musu addu'a tareda cewa "Bintoto da ake wulakantawa yau gashi ta zamo mana alkhairi" ganin yamma nayi yasa Abba dire musu makudan kudade yace su raba a tsakaninsu, Hydar kuma ya musu alkawarin ze dawo sabon sati dan a fara ginin masallacin, sannan suka aika aka kira Binta dansu tafi, har kofan gida matan mai gari suka rakota, seda sukaga tafiyansu sannan suka koma cikin gida tareda hiranta, Binta kuwa a hanya shiru tayi bini bini Hydar seya juyo yace mata "lil sis", jin  haka tasan ko basu fada ba ita jinin su ce, Abba kuwa ya kasa daina murmushi dan be taba tunanin zega jinin kanwarshi Aisha ba, se gashi ta bar doron kasa amma kuma ya hadu da tsatson ta lallai zeso Binta kaman yadda yakeson kanwarshi Aisha.Se chan bayan isha suka isa Abuja, gidan Ummi suka sauka dan dama Hydar ya fadawa Kausar taje gidan in sun dawo se su koma gida tare, tin daga annurin dake fuskokinsu Ummi da Kausar suka san amsan tambayoyinsu, se bayan sun zauna sun huta Ummi tace "Alhaji ya akayi, 'yar Aisha ce?", kallonta yayi da murmushi yace " 'yarta ce, bari muyi sallah se na warware miki yadda mukayi", da murna Ummi ta janyo Binta dake zaune gefen Kausar ta rungumeta tana hawaye, ita kanta Bintan hawayen farin ciki takeyi yau gata ga danginta masu sonta, abunda bata taba experiencing ba, dan koda dangin mahaifinta ke raye basa sonta, sema hantarar ta da sukeyi suna kiranta me kashin tsiya, sosai Ummi ta rungumeta Binta tana shafa bayanta danji take kaman cousin sis dinta Aisha ta runguma (idan baku manta ba Ummi da Abba auren gida aka musu, bayan iyayen Abba sun rasu suka koma hannun kanin mahaifinsu wanda shine mahaifin Ummi). 


+

Zeena ce ta matso kusa da Ummi cikin sanyinta tace "Ummi lemmi hug my sister" murmushi duk sukayi sannan Ummi ta janye Zeena ta rungumeta tana cewa "welcome to the family sis", zuwa school din Binta ba'a banza ba dan kuwa taji me Zeena taci, murmushi tayi tace "thank you", sannan Zeena ta janye, seda duk sukayi sallah sukaci abinci sannan Abba ya warware musu komai akan zuwansu cakawa sannan Hydar ya kara da cewa "ze bari a bincika mishi  Hajiya dan yasan idan tazo hannu toh Zinaru ma zata shigo hannu, Ummi waya ta dauka ta kira Anty Maryam ta shaida mata komai Anty Maryam tsabar murna harda cewa asa wayan a handsfree tayiwa Binta magana, sosai tayi mata murna sannan tace Hydar ya kawota a daren nan a gidanta Binta zata kwana, nan Zeena tace batasan zancen ba a gidansu Binta zata kwanta, kallon Kausar Binta tayi su biyun duk idonsu yayi rau rau, Hydar ma kallon Kausar yayi ta kyafta mishi ido ya juya yace "erhm, Ummi ku bari weekend za'a kawota dan zataje sch gobe", shiru Ummi tayi na dakiku tayi nazari, be kamata su dauke Binta daga wurin Kausar ba dan tun farko ita ke dawainiya da ita, murmushi tayi tace "ba komai Allah ya kaimu weekend din, ke kuma Maryam se kiyi hakuri idan anyi mid term break se tazo tayi hutu a gidanki", badan Zeena da Anty Maryam sunso ba suka hakura, sosai Kausar taji dadi harda sauke ajiyar zuciya dan ba karamin jin dadin zama da Binta takeyi ba, Zeena ce cikin sanyinta tace "toh Ummi in dau Uniform dina in bisu?", Ummi tace "yanzu seki tafi ki barni ni kadai auta", marairaice fuska tayi Abba yace "in ta tafi ai ni ina nan", cikin tsigar wasa tace "toh ai kai ba zama kakeyi ba", Hydar kallon Zeena yayi yace "hado kayanki muje", kafin Ummi tayi magana har Zeena ta haura da murna. 
Se karfe goma suka bar gidan, koda suka kai gida Zeena cewa tayi a dakin Binta zata kwana, basu hanata ba sukawa juna seda safe kowa yayi hanyar dakinshi, seda sukayi wanka sannan suka kwanta Zeena dukda bame surutu bace amma a haka take jan Binta da hira dan she has been longing for a younger sibling amma Allah be bata ba, se gashi yanzu ta samu cousin sis, a daren sukayi exchanging number Zeena ta budewa Binta watsapp wai su dinga chat sannan ta bude mata IG da Snapchat tareda mata alkawarin zata koya mata yanda akeyin duka, Zeena laptop dinta ta dauko ta kunna musu cartoon na Barbie as a mermaid princess, kallo sukeyi har karfe biyun dare, Hydar daya sauko dan ya hada coffee yaji alaman suna kallo, a hankali ya bude kofan dakin Binta ya leka yace "na kamaku", sosai suka tsorata dan basuji shigowanshi ba Zeena tace "Ya Hydar ka bamu tsoro", dariya yayi sannan yace "oya kallon ya isa haka, kunada school gobe, a kashe a kwanta kafin nayi seize din lapi din", kashewa Zeena tayi tana zunguro baki ita kuwa Binta dama chan baccin takeji, seda yaga sun kwanta sannan ya musu addu'a ya kashe hasken dakin ya bar musu dim light ya fita yaja musu kofa. 
Washegari Hydar ne ya tashesu sallan asuba dan har sun kusa makara, suna sallah Zeena tace "muje mu hada breakfast", Binta tace "ai akwai me zuwa hadawa", (ni kuwa nace hattara dai, karki biyewa halin Kausar), girgiza kai Zeena tayi tace "bamu saba da girkin masu aiki ba, zo muje karna makara danni 6:30 nake wucewa school dan akwai lesson dinda nakeyi kafin assembly kinsan shekeran nan zanyi waec", g'ada kai Binta tayi tace "nima ajinmu ance mu dinga zuwa shida da rabi", kitchen suka shiga Zeena tace "wani class kike?", "js3", ta bata amsa, "shekaranki nawa?", ta sake tambaya "14", ta bata amsa a haka suna hira suna girki har suka gama soya potato da kwai suka dora ruwan tea, Zeena ce ta fara shiga wanka  acewarta kafin ta fito ruwan ya tasafa".  Kafin 6 sun gama shiryawa sosai Zeena tayi mamakin ganin uniform dinsu daya wato school daya kenan suke zuwa amma bata taba ganin Binta ba dukda class dinsu beda nisa dana juna, "laa  Zee school dinmu daya", murmushi Zeena tayi tace "nima haka na gani, zo muci abinci", da asuba suka karya suka ragewa Hydar da Kausar, Hydar da Kausar ne suka sauko sannan cewa kafin 6:30 zasu wuce, kudin break ya basu sannan yama daya daga cikin basawanshi magana yace a saukesu a sch, sallama sukayi Kausar har waje ta rakasu dukda zazzabin da takeji amma bataso ta kwanta saboda kar ciwon yabi jikinta. 
Hydar ma karfe goma ya bar  gida, ya bar gida Kausar na shirin fita aiki, be tsaya koh ina ba se police station inda duk suka dinga bashi girma dan duk wani me sa uniform a aikin gwamnati yasan da zaman General  Hydar Ali Mahmoud Mai Turare, har office din DPO ya shiga inda shima din ya tashi tareda salute mishi sannan suka zauna, sosai yayi mamakin ganin Hydar, bayan sun gaisa yace "akwai wani case da nakeso kuyimin aiki akai ne, naso na dauka case din da kaina amma saboda karna karya doka yasa nazo nan, saboda haka idan naga alaman case din na neman gagarar ku zan dau case din kuma idan naci nasarar toh fa se yadda nayi da wa'anda nakeso a kama mun", gyara zama DPO yayi yana Jinjina kai yace "ina jinka", Hydar yace "akwai mata a nan cikin garin Abuja ta bayan gari, tana sa yara kanana karuwanci kuma..... ", tun be gama ba DPO ya katseshi da cewar "Hajiya me gidan dadi kenan", "ya akayi kasanta", murmushi yayi yace "ai case akayi da ita sosai kwanan nan akan wasu mata biyu da sukazo suka kawo kararta wai ta sanwaltar musu da yarinya ita kuma tace sunyi settle a tsakaninsu tintini", "toh ina take yanzu?", Hydar ya tambaya "bamu kamata ba har yanzu dan muna bincike a kanta ne munaso se mun gama bincike",  g'ada kai Hydar yayi yace "koh zan iya ganin file dinta, kuma zan iya sanin sunan wa'anda suka kawo kararta", "zaka samu", cewar DPO din sannan ya kira daya daga cikin yaranshi yace su dauko mishi case file din Hajiya, ba jimawa ya dawo da file din Hydar ya duba DPO yace "mata biyu suka kawo kararta Zinaru da 'yar uwarta wai ana ce mata antyn birni, sun yi kara kan cewar wai Hajiya tace zata kai yarinyarsu aikatau me suna Bintoto, toh shine daga bata yarinya aka nemi yarinya aka rasa, ita kuma Hajiya ta karyatasu da cewar ba haka abinda yake ba, wai ita antyn birni ce ta kawo mata yarinyar daga kauye wai asata karuwanci saboda suna facing financial problems, toh ita kuma ganin business dinda takeyi kenan seta karbi yarinyar, toh wai akwai wani yaro me suna Anwar wanda a halin yanzu shima muna nemanshi amma babushi babu dalilinshi, toh yaronne me zuwa daukanta yana fita da ita, ana cikin haka yaron ya kirata ya shaida mata yarinyar ba lfy wai har zuwa sukayi suka duba yarinyar a hospital, toh tin daga wannan lokacin kuma suka nemeta suka rasa shima yaron haka, toh daga baya ita Zinaru tazo tana claiming wai yarinyar 'yarta ce kuma bazata yarda ba seta fito mata da 'ya in takaice maka dai daga karshe miliyan biyar suka karba a hannun Hajiya wai dan karsu kai karanta, shine yanzu suka sake komawa wai seta basu miliyan uku ita kuma tace bazata bayar ba, toh kaji yadda ake ciki", ajiyar zuciya Hydar yayi yace "lallai Zinaru anyi makirar mace, yanzu kasan me nakeso da kai, ka kirasu su duka idan sunzo ka kullemin su dan dukkansu masu laifi ne, da yamma zan dawo da yarinyar da suke hayaniyar akanta dan kuwa yarinyar ba kowa bace illah cousin sis dita", baki sake DPO ke kallon Hydar (ni kuwa nace tab, Zinaru taki tazo karshe).
Ina lbrn Zinaru? +

Kudin da Zinaru ta karba a hannun Hajiya a wulakance suka kashe kudin, yau sune shiga kasuwa, sune siyan atampopi, manyan lace da shadda acewarsu business suke amma riba baya fitowa dan daga karshe ma hakura sukayi saboda ba uwar kudi ba riba kuma daga ita har antyn birni sun rasa inda kudin ke shiga (ni kuwa nace dama ina wannan kudin zeyi albarka), ganin sun karye kudin hannunsu na neman karewa yasa antyn birni ziga Zinaru wai taje ta siyar da gidan mijinta tinda Binta batanan balle ace gadonta ne, Zinaru ba tareda wani tunani ba taje tasa gidan a kasuwa inda cikin sa'a mai gari ya siya, nan ma dai cikin en watanni kudi suka kare har gwara antyn birni tana dan samu a harkar karuwancinta, ganin suna nema su koma gidan jiya yasasu yin shawara suka koma wurin Hajiya akan lalle lalle seta kara musu miliyan uku ita kuma tace batasan zancen ba, sun tsorata ta da cewar zasu kai kararta tace sukai tinda tasan ta riga ta fita hakkinsu, ganin batada niyyar bayarwa suka shigar da kara idan aka dinga cin case dasu, toh wannan ne dalilin da yasa nemansu yazowa Hydar cikin ruwan sanyi.

Cigaban lbr

Kaman yadda Hydar ya bukata haka kuwa DPO yayi, kiransu yayi gabadaya akan case din duk suka hadu a station en sandan basuyi wata wata ba suka sasu a cell, da suka nemi ba'asi akan dalilin da zesa a kullesu aka ce musu in lokaci yayi  zasu sani, Zinaru kuwa zage zage ta dingayi abunku da wacce ta fito daga kauye kai be waye ba, banza da ita kowa yayi babu wanda ya kula ta ita kuwa Hajiya gabadaya hankalinta a tashe yake amma bata nuna ba, rokon en sandan wurin tayi akan su bata wayarta minti biyu amma suka hana, haka ta hakura tayi shiru inda Antyn birni kuwa se hakuri take bawa Zinaru akan tayi shiru, da kyar ta samu tayi shiru duk suka nutsu zuciyoyinsu cike  da wasiwasi. 


Hydar koh direct company din mahaifinshi ya nufa inda ya kuwaci sa'a sun fito daga meeting kenan, office din Abba suka nufa suka zauna Abba yace "ya akayi Hydar", gyara zama Hydar yayi sannan ya fayyacewa mahaifinshi komai akan zuwanshi police station da yayi, da yanda ya samu komai yazo mishi cikin sauki, sosai Abba yayi murna yace "toh yanzu yaushe zaka koma?", "da yamma idan an tashi Binta daga school zanje na daukota daga nan mu wuce chan, nasan idan ta gansu zata gane su" gyad'a kai Abba yayi yace "hakan ma yayi, idan ka dauki kanwarka daga sch ka kirani se mu hadu a chan", da haka yama Abba sallama sannan ya koma gida, koda yaje gida Kausar na wurin aiki se Hajara dake share share. 


Da yamma Hydar ya biya school dinsu Binta ya daukosu, sosai sukayi mamakin ganinshi Zeena tace "yaya yau saboda kayi kanwa shine kazo daukanmu", murmushi kawai yayi yace "ku shiga mu tafi", maimakon suka ya dau hanyar gida se sukaga ya canza hanya, babu wanda yayi magana ga mamakinsu sukaga yayi parking gaban station, "ku fito mu shiga", fitowa sukayi gabadayansu suka shiga ciki, koda suka shiga Abba na wurin, gaishe shi sukayi DPO yace "bismillanku", office dinshi suka shiga sannan yasa yaranshi kiransu Zinaru, da zage zage ta shige amma ganin mutanen dake ciki yasa tayi shiru, sosai Binta ta tsorata da ganin Zinaru dan har yanzu da wannan tsoron a ranta, bayan Hydar taje ta tsaya wanda kowa a wurin ya lura da hakan, Zinaru kuwa zaro ido tayi dan ko yaya Binta ta canza zata ganeta, baki na rawa tace "Bintoto kece?", amma shiru Binta ba bakin magana ita duk a ganinta Zinaru tazo daukanta ne, Hajiya kuwa shiru tayi kaman ruwa ya cinyeta a wurin dan tasan shikenan kashinta ya bushe, murmushi Hydar yayi ganin yadda suka sha jinin jikinsu Hydar ya janyo Binta daga bayanshi yace "kunsan ta?", shiru sukayi babu me magana a wurinsu ya juya wurin Hajiya yace "kece me karfin halin bata rayuwar yaran mutane koh, bakya tunanin ya rayuwarsu zata kasance idan sukaci gaba da aikata irin ayyukan da kike sasu, akan kudi, akan abin duniya, kike neman batar da yaran mutane, yanzu tsakaninki da Allah yaran na irin wannan harkar?", shiru tayi kanta kasa yace "magana nake", ta girgiza kai tareda cewa "bani da yara", Abba yace "dan baki yara shine kike lalata na wasu, bakya tsoron ranan da Allah ze kamaki, ranan da ze tsayar dake yayi miki hisabi, ranan da babu abinda ze ceceki ze ayyukan ki, ranan da kowa ke nafsi nafsi ba ruwan wani da wani, yanzu duk zunuban da yaran nan me aikata kinsan da cewar kinada kamasho, yanzu idan Allah ya dauki ranki a wannan hali me zakije kice masa, da wani idon zaki kallesa, da wani bakin zaki roki gafara, toh wlh tun wuri ki tuba ki koma ga Allah tun bakiyi dana sani ba", kuka Hajiya keyi sosai harda majini dan ta dade wani mahaluki bezo ya fada mata Allah Annabi ba, shiyasa ma take manta za'a mutu dan ta shagala da duniya tana sheka ayarta son ranta, se yanzu take nadama da dana sani, yau ina zata kanta, da wani baki zata roki Allah daya gafarta mata akan wannan kazanmin rayuwa data zabama kanta, amma sedai kuma ance Allah Al gafurun rahimun ne saboda haka zata tuba ta koma ga Allah. 

Kallon Antyn birni Hydar yayi yaga idonta a bushe, fuskarta ba alamun nadama yace "ke kuma kece me bada shawaran akai mun er uwa karuwanci koh", a razane ita da Zinaru sukace "er uwa kuma", ya kada kai yace "er uwata ce kuma kanwata, kuma tinda kukayi kuskuren tabamin lfyrta kuma se nasa kun dandani irin azabar da tasha musamman ma ke", ya nuna Zinaru da taji maranta ya cika lokaci daya, kiris ya rage bata saki fitsari ba, kallon DPO yayi yace "DPO a kullemin biyun nan", ya nuna Antyn Birni da Hajiya sannan yace "wannan kuma tafiya da ita zanyi, nan da sabon sati zan dawo da ita, banson a bada bail dinta, idan na dawo da wannan me fuskan fir'aunan zan shigar da kara kotu dan se na tabbata an yanke musu hukunci daidai da laifinsu", Hajiya hakuri ta fara bayarwa, Antyn birni kuwa se a lokacin taji jikinta yayi sanyi, Zinaru kuwa tini ta saki fitsari a wando, abin dariya abin takaici, tsugunnawa kasa tayi ta fara rokonshi, "bawan Allah dan Allah kayi hakuri karka cutar dani", "karna cutar dake kika cutar da marainiyar Allah", kuka takeyi wiwi tace "Bintoto kisan ni na zauna a yayinda bakida kowa, ki taimaka ki rokarmin dan uwanki tinda yace shi dan uwanki ne", shiru Binta tayi amma idonta cike yake tab da hawaye, "DPO zamu wuce kasa yaranka su kawomun ita gida", da fadan haka yaja hannun Binta suka fita idanunta na zubar da hawaye, nan aka kulle Hajiya da Antyn birni inda Zinaru kuma aka sata a mota sukabi bayan su Hydar. (Zinaru u never see anything, u never pee for body finish 😂).
Har suka kai gida Binta bata sake ba, bakar wahalan da tasha hannun Zinaru ya dawo mata sabo a ranta, yanda take cin jagwalgwalon ragowar Zinaru, yanda take kwana a soro ga uban sanyi da sauro, yanda take zuwa mata talla idan kudi be kai ba taci ubanta, take wutar tsanar Zinaru ya kara ruruwa a cikin zuciyarta. Suna parking ta fito ta shige gida da gudu, daki ta shige tasa makulli ta rufe kofa tareda sakin wani kuka me cin rai, ba ita kadai ba hatta mahaifiyarta da mahaifinta sunsha wahala a hannun Zinaru, hanya ma zata iya yafe wa Zinaru kuwa, kai da wuya. 

+

A cikin gidan en sandan da suka kawo Zinaru suka dire ta, se kallon gidan takeyi dukda a tsorace take wannan be hanata santin gidan ba, Kausar jin jiniyar en sanda yasata fitowa dan ta dade da dawowa, a parlor taga Zeena zaune tace "yau kun dade", "Yaya ne ya daukomu", ta bata amsa tareda da fada mata inda sukaje, da sauri Kausar ta fita compound inda taga sojoji sunsa Zinaru tsakiya se hawaye takeyi Hydar kuwa se murmushin mugunta yakeyi yace "take care of her ur own way, make sure batada shelter, a waje nakeso ta kwana taji ya kwanan waje yake, abinci kuma se wanda kukaci kuka rage zataci koda kuwa loma daya ya rage", "ok sir", suka sara mishi gabadayansu suna murna sunsamu nama dan dama sojoji ba imani ne dasu ba, "dan Allah bawan Allah karka min haka wlh na tuba bazan kara ba dan allah ka min rai ka taimaka", Zinaru rokonshi take amma in dutse na magana toh Hydar yayi, jan hannun Kausar dake kallon Zinaru cike da tausayawa yayi suka koma  cikin gida. 

4

"Hubby na hukuncin be mata tsauri ba?", Kausar ta tambaya tana kallon Hydar girgiza kai yayi yace "I want her to go through what Binta went through amma fa na sati daya kacal saboda taji koda dadi", "amma..... ", "shiiii", ya katse ta sannan yace "let me handle dis alone", shiru tayi dan tasan Hydar ba abinda ze canza mishi abinda yayi niyyar yi a wannan lokacin, direct kofan dakin Binta ya nufa ya fara knocking, tsagaita kukan tayi sannan ta tashi ta bude kofan, tsaye ta gansu Kausar ta karasa ta kamo ta tace "kuka kikayi?", shiru tayi kanta kasa Hydar yace "ki daina kuka, Insha Allah komai yazo karshe, zan tabbata an hukunta ko wannensu daidai da laifinshi", kai ta kada Kausar tace "yi wanka kizo kici abinci", da haka suka fita suka bata wuri Zeena ta shigo tace "shine kika kulleni a waje koh", murmushi Binta tayi tace "sorry", ta fada tana rike kunne, dariya sukayi a tare sannan suka fara cire uniform. 


A waje kuwa su Hydar na tafiya sojojin suka fara kwade Zinaru, in wannan ya kwade ta wannan ya mangareta, wani kuma ya rankwasheta, cikin lokaci kankani idon Zinaru ya rena fata kiris take jira ta fara kuka wai yau en yara kanana ke magareta suna dukanta tsabar mugunta da wulakanci (nace ashe ba dadi kikewa),  daya daga cikinsu wani baki mummuna daga ganinshi bayarbe ne yace "oya frog jump", zaro ido Zinaru tayi dan batasan me suke nufi ba, wani inyamuri ne ya nuna mata yadda zatayi, da kyar ta fara dan tuburewa tayi ita bazatayi ba, seda taji saukan doruna me baki biyu a bayanta sannan ta fara, tuni takalmanta suka raba hanya, daya yayi gabas daya yayi arewa, se zufa takeyi, da ta tsaya zataji saukan doruna, cikin minti biyar ta fara kuka wiwi amma kusan sojoji zuciyarsu kaman ta fir'auna  take shiyasa basuda tausayi, seda wuraren isha suka sarara mata, abincin da sukaci suka jagwalgwala suka tura mata wanda ko kare albarka, amma tsabar  yunwa haka Zinaru ke turawa, loma uku tayi ta cinye, ta tambayesu ruwa suka hanata, tanaji tana gani suna shan ruwan gora amma suka hanata, daya daga cikinsu ya taso ta bude ruwa ya fara tsiyayeshi a kasa, a da sauri ta kawo harshenta tana sha kaman wata kariya gabadaya ta jika kanta se dariya suke mata dan mugunta, kneel down suka sata a haka ta kwana ga sauro cikin dare aka tsuge da ruwa, kafin safe Zinaru ta canza kamanni g
a kafanta yayi tsami batama iya takawa. 


Ta gabanta su Binta sukabi suka shige mota babu wanda ya kalleta a cikinsu dan Binta batamaso taga fuskarta, da Kausar ta tashi tafiya office ta fito da cake da bawa Zinaru sannan ta gargadi sojojin da karsu gayawa Hydar sannan ta fita, Zinaru kuwa ci uku tawa cake din ya kare, duk abinda Kausar tayi Hydar na kallonta ta window dan be fara fita ba tukun saboda an bashi hutu, murmushi yayi yana mamakin kirki da tausayi irin na Kausar. Cikin kwana uku Zinaru tasha bakar wahala wanda seda ta fara addu'an allah ya dau ranta da wannan wahala da takesha, hatta Binta da Zeena sun fara tausaya mata, da dare se Binta ta fito ta tsaya bakin window tana kallonta  tana hawaye, ta kara baki, ta rame, jikinta duk cizon sauro, ga yunwa, ba yanda Kausar batayi da Hydar akan wahalan ya isa haka ba amma ko kulata bayayi har fada sukayi taki mishi magana amma ya share dan yasan in Kausar ce zata dawo ta mishi magana. Ranan Friday Hydar ya tafi masallaci Kausar ta tafi aiki su Binta suka dawo daga school, da sauri Zinaru ta kirata dukda muryarta baya wani fita sosai saboda wahala, karasowa wurinta Binta tayi tace "gani", Zinaru ta kamo kafan Binta a wahale tace "dan girman allah ki yafemin kicewa dan uwanki ya sakeni na tafi", kallonta Binta tayi tana mamakin hali irin na Zinaru, wato tana rokar yafiyarta ne badan tayi nadama ba sedan a saketa, murmushin takaici Binta tayi tace "Goggo kenan, karki damu zan yafe miki amma ba yanzu ba, se randa kikayi nadama zan yafe miki sannan maganan a sakeni wannan ba a hannuna yake ba, ki bari in yaya ya dawo seki rokeshi", tana fadan haka tayi ciki, Zeena kallon Zinaru da tayi rau rau da ido tayi sannan ta girgiza kai ta mika mata goran ruwan dake hannunta, da sauri Zinaru ta karba ta kwankwande, sojojin wurin kam sun dan rage ganawa Zinaru azaba ganin idan sukaci gaba toh tabbas se kafarta ya tashi aiki. Binta da Zeena shiryawa suka cikin jallabiya baki da pink din mayafi suka fito dan a gidan Ummi zasuyi weekend, sosai suka shaku yanzu, cikin sati daya suka zama BFF.
Zinaru sati dayan da Hydar ya diba mata seda tayishi, sosai ta raina kanta a cikin sati dayan nan, banda nadama ba abinda takeyi, gashi tin randa su Binta suka fita bata sake  ganinsu ba, yau monday kuma yaune Hydar ze mayar da ita cell, karfe daya ya fito daga gida saboda Kausar bataji dadi ba, seda ya tabbata taci abinci tasha magani ta kwanta sannan ya fito, motarshi ya shige bayan ya kira en sanda da suzo su dauki Zinaru, daga gida hospital din Khaleel ya nufa suka zauna a office dinshi yace "Maza ya akayi ne?", "Kausar ce", Hydar ya bashi amsa, "me tayi?", Khaleel ya sake tambaya yana kallon Hydar, "wlh yanzu kullum da zazzabi take tashi, gashi kome taci seya dawo" dariya Khaleel ya mishi yace "don't worry zata samu lfy, ai dama shi pregnancy haka yake, natama bame laulayi bane, da me laulayi ne se kafi tausaya mata", shiru Hydar yayi kaman wani me nazari sannan ya dago yace "for how long zata daina morning sickness din?", "it depends gaskiya, wasu 4mnths wasu 5,wasu 6 amma ita bana ganin zata dade tinda naga alaman bata yadda ciwo ya mata kaka gida, ba irin matan nan ne dasuke langwabe wa mazajensu da zarin sun dau ciki bane", girgiza kai Hydar yayi ya kuma cewa "toh bazaka mata prescribe din magani ba", dariya Khaleel yayi yace "karka damu, taci gaba da shan wanda take sha", a hankali yace "shikenan bari na yafi, daga nan station nayi  dan zanyi filing case akan wa'annan matan". 


+

Da sauri Khaleel yace "yauwa dat changes d topic, Hydar kana son Binta ne", cike da daurewar kai Hydar yace "meyasa ka tambaya, me ka gani", murmushi Khaleel yayi yace "naga yadda kake kallonta sanda tazo hospital da kake kwance", wani dogon tsaki Hydar yaja yace "kai dai gaja ne wlh, wawa kawai, indan ma sonta nake se akayi yaya", dariya Khaleel yayi yace "just answer me with a yes or no", murmushi Hydar yayi yace "nima bansani ba, all I knw is ina like dinta saboda batada matsala, she's gentle and simple gashi batada surutu just like Zeena amma dai even if I do love her, that is 'if' ina sonta bazan fadamata ba, zan gwammace nayi dakon sonta har Allah yayemun", kallonshi Khaleel yayi yace "Allah koh", Hydar yace "kwarai kuwa", Khaleel yayi murmushi yace "meyasa?", kai tsaye Hydar yace "saboda bazan iyama Kausar kishiya ba, in ma kuma zanyi din ba dai da Binta ba wacce take so ta dauke ta 'yar uwa kaman ciki daya suka fito, baza'ayi wannan rashin aldalcin dani ba", shiru Khaleel yayi sannan yace "kuma hakane, toh kai kun daina samun matsala da Kausar ne?", dariya Hydar yayi yace "ai yanzu table din ya juya, nawa bukatan nifila akan nata a yanzu", kai Khaleel ya gyad'a yace "dats because she's preggy, Allah dai ya sauketa lfy", "Ameen", Hydar ya amsa mishi yana mikewa, har bakin mota Khaleel ya raka Hydar sannan ya koma ciki. 


1

Zinaru koda police din sukazo daukan ta bata musu gardama ba dan ta riga ta gama gajiya, duk yadda zasuyi suyi da ita amma ita dai batada karfin kwatar kanta, station suka wuce da ita, su kansu en sandan sunyi mamakin ramar da Zinaru tayi kaman wacce tayi cutar shekara, cell dinda su Antyn birni suke aka sata, sosai suma sukasha mamaki, banda meyasameta ba abinda suke tambaya, ita kuwa ba bakin basu amsa , Hajiya ta samu tayi waya da Asabsy akan ta samo mata lawyer inda Antyn birni ita bamata da wanda zata kira kaman yadda Zinaru ma bata dashi, direct station din Hydar yayi, yayi filing case aka kai court, cell dinsu ya leka da murmushi a fuskarshi yace "se mun hadu a court", babu wacce ta iya bashi amsa cikinsu, duk shiru sukayi ya juya ya koma gida, karfe hudu ya shige gida bayan yayi sallah a masallacin unguwarsu, ba kowa kasa saboda haka yayi sama, dakin Kausar ya shiga yaji tana wanka seya fito ya bude dakinshi amma se yaji da alaman mutum a dakinshi kuma ya tabbata Kausar ce ke wanka "toh waye a ciki", ya tambayi kanshi, shiga yayi inda yaga Hajara a closet dinshi tana gyara daurin zaninta, bega abinda tayi ba dan haka yace "ki dinga gyaran dakin kafin na dawo, banson na dinga dawowa ina ganinki a nan", da sauri ta juyo gabanta na wani mugun faduwa dan bataji shigowarshi ba, cikin rawar murya tace "zan dingayi kafin ka dawo", da sauri ta fita amma ga mamakinshi babu tsintsiya balle mopping stick koh rag, toh me ta shigo yi? Ba amsa, daga kafada yayi ya shiga ya canza kaya sannan ya fito ya koma dakin Kausar.


1

Zaune ya ganta ya karasa ya zauna tareda kwanto ta jikinshi yace "ya jiki", "da sauki", ta bashi amsa "kinci abinci", ya tambaya tace "naci amma inaso inci tuwo da miyan gyada Hajara kuma wai bata iya miyan gyada ba", wayanshi ya ciro yace "bari na kira Ummi ta mike se inji in karbo", kallonshi tayi tace "ba zamu takura mata ba, koh mu kira mommy", kafin ta gama magana ya dannawa Ummi kira, dauka tayi bayan sun gaisa ya fada mata abinda yakeso, Allah ya taimakesu itama tuwon tayi, miyan ne kawai za'a mata sabo, "zaki rakani muje mu karbo", girgiza kai tayi tareda gyara kwanciyarta tace "barni haka, bazan iya zuwa ba, jiya su Binta basu dawo ba, in kaje ka dawomun dasu, gidan ba dadi da basanan", murmushi yayi yace "shikenan, zan dawo dasu, bari naji", mikewa yayi tareda pecking dinta sannan ya fita, yana kaiwa gidansu mahaifin Khaleel da Uncle dinshi na parking, sosai yayi mamakin ganinsu dan Khaleel be fada mishi zasu ba, gaisawa sukayi sannan ya kaisu parlorn baki tareda ce musu bari ya kira musu  Abba sannan ya fita, cikin gida ya shiga ya shaidawa Ummi Abba yayi baki, nan da nan tasa aka kai musu ruwa da drinks da snacks sannan tawa Abba magana wanda be dade da dawowa daga aiki ba, dama yasan da zuwansu saboda haka babban riganshi kawai ya dora kan wando da jumper dinshi sannan yasa hula ya fita, a parlor yaga Hydar suka gaisa sannan yace "taso muje", bayanshi Hydar yabi suka shiga parlorn bakin da sallama su Dad suka amsa musu, zama duk sukayi suka gaggaisa sannan Abba yace "ashe dai zaka zo din, ai ganin lokaci ya wuce nace toh kodai bazaka samu zuwa bane", dad yayi dariya yace "ai banga ta zama ba dan kuwa danka ya sani gaba", Abba ya gyara zama yace "ince dai lfy". Gyara zama Dad yayi yace "lfy kalau, Alkhairi ce ta kawomu", Abba yace "tohh, inaji", "Dan wurina Khaleel yace yaga 'yar wurinka yana so", murmushi Abba yayi yace "toh toh toh, madallah, ai hakan yayi kyau, amma wacce daga ciki", da mamaki Dad yace "dama su biyune?", Abba yace "kwarai, akwai Zeenatu akwai Fatima Bintu", kallon Hydar Dad yayi dan yasan dole Hydar zesan ko wacece daga ciki Hydar yayi murmushi a zuciyarshi yace "Shege Khaleel yanzu idan naga dama sena mishi mugunta se yazo zance yaga Binta", a fili kuwa sosa keya yayi yace "Abba Zeena ce", murmushi Abba yayi yace "toh ai shikenan, kaje kace mishi an bashi, inya shirya yazo a daura aure", dariya Dad yayi yace "haba dai ai yace se in tana sonshi sannan dai baze mata dole ba", Abba ya gyad'a  kai yace "hakane, amma in da kudi jikinku ku biya sadakinta yanzu danni har ga Allah na bashi", sosai su Dad sukaji dadin karamci irin na Abba, nan Alhaji Hamza Uncle din Khaleel ya ciro bundle din 1k dubu dari kenan ya direwa Abba, Abba ya girgiza kai yace "a'a bazamuyi haka ba, ai albarkar auren ake bukata wannan kudi sunyi yawa", da kanshi ya kirgi 50k ya mayar musu yace "50 ma ta isa, Allah yasa albarka a ciki", duk suka amsa da ameen sannan sukayi sallama suka wuce, har bakin mota su Abba suka rakasu sannan suka koma cikin gida, su Binta har sun dawo daga makaranta Hydar yace "karku cire uniform dan yanzu zamu wuce, basket dinda ummi ta miki mishi ya karba ya musu sallama ya wuce, se a lokacin Abba ya fadawa Ummi abin arzikin da ya samesu na Khaleel da Zeena, itama sosai taji dadi ta kuma sa albarka.
Yau sati daya kenan da aka mayar da Zinaru cell, inda ta gwammace zaman cell din da zaman gidan Hydar dan kuwa a cell bame dukanta balle hantarar ta gashi za'a bata abinci da dadi ba dadi, har yau har gobe ba digon nadama tattare da Zinaru dan a ganinta bazata dade ba za'a sallame ta, burin ta da an sallameta ta wuce kauyensu gidan malaminta ya mata maganin Hydar kaman yadda ya mata maganin  Malam Tanimu, ita kuwa Antyn birni hankalinta kwance yake dan a ganinta baza'a bata sentence me tsayi ba kuma da ta fito harkarta zataci gaba dayi dan dama ba yau ta fara zuwa prison ba, so biyu tana shiga ta fito yanzu gashi zata shiga na uku, Hajiya kadaice ke nadaman abubuwan da ta dingayi ita dinma guntun wa'azin da Abba ya mata ne ya dan shigeta gashi batasan wani abu waishi zaman prison ba. +

Suna zaune en sanda sukazo suka kwashe su saboda a yau Thursday za'a zauna court dasu, basuyi gaddama ba aka kwashe su zuwa mota se babban court dinda ke Abuja, a bakin wurin suka hango Hydar ,Kausar, Binta, Zeena, Ummi da Abba suma zuwansu kenan, ba komai ya sasu zuwa ba se dan suga hukuncin da za'a yankewa Zinaru kuma su tabbatar cewar hukuncin yayi, kallon kallo sukewa junansu ba kaman Zinaru dake makawa Hydar da Binta harara dan yanzu batada makiya daya wuce su kuma a ganinta ta sanadin Binta aka kamata shiyasa ta kullaceta a rai, shiga court din sukayi inda su Hydar suka nemi wuri suka zauna ba jimawa judge ya shigo kowa ya mike in form of respect seda ya zauna sannan kowa ma ya zauna, ba bata lokaci aka fara gudanar da abunda ya kawosu. 

Bayan judge yaji komai kuma ya fahimta ya gamsu dukda Hajiya nada nata lawyer din amma be gamsu da maganar lawyer dinta ba dan bega dalilin da zesa ta bude gidan karuwai tana lalata rayuwar yaran da akeso su zama leaders of tomorrow ba, seda yayi en rubuce rubucenshi sannan ya dago ya kalli su Zinaru kallon da seda gabadayansu gabansu ya fadi dan da ganin fuskarshi ansan bazeyi mutunci ba, gyara medicated glass dinshi yayi sannan yace "ke Hajiya kotu ta yanke miki 5yrs imprisonment saka makon lalata rayuwar kananan yara da kikeyi kuna bata gari da yawaitar zinace zinace ga al'umarmu, saboda haka zakiyi shekara biyar with hard labor sannan gidan karuwanki ya zama na gwamnati haka kuma duk wacce ke wannan gidan kuto zatasa a maida ita asalinta tareda kashedin inta kuskura ta kara dawowa toh zata gamu da fushin kotu", kuka sosai Hajiya keyi tana tunanin ina zatasa kanta, yau idan tabar prison ina zata nufa, ita marainiyace ba uwa ba uba wahala ne yasata shiga wannan harkar datake danasanin shigarsa yanzu.

Antyn birni ya kalla wacce dukda gabanta na faduwa idonta a bushe yake ko dar bata yarda idonta sun kawo ruwa ba tsabar barikanci, "kema kotu ta yanke miki shekara biyar sakamakon hadin kai da kika bayar wurin kai baiwar Allah inda za'a gurbata  mata rayuwa", kallon alkali takeyi alkali na kallonta yana mamakin iya shege da barikanci irin na Antyn birni, yasha zama a wannan kujerar tashi ya yankewa mutane shekara daya, shekara biyu kuma susa kuka cike da nadama amma wannan daya yanke mata shekara biyar ko dar sema kallonshi da takeyi ido cikin ido, girgiza kai yayi yace "Allah ya shirya", ba tareda kowa yajishi ba, kowa a wurinma mamakin Antyn birni yakeyi da taurin rai irin nata, Zinaru kam kafin ma akai kanta jikinta ya fara rawa, ji take kaman zata saki fitsari, taso taba mutanen wurin dariya, kallonta judge din yayi yace "Zinaru kekuma laifinki dayawa yake, na daya kin tauyewa marainiyar Allah hakkinta, kin zalinci baiwar Allah, kinci mutumcinta sannan kuma kika nemi ki turata inda bazata samu rahamar Allah ba amma dayake Allah ba azzalumin sarki bane sai komai yazo da sauki har gashi anzo dake inda bama bari a wulakanta hakkin mutum semu tabbata mun hukunta koma wanene saboda haka kema Zinaru hukunci ya hau kanki", tuni hawaye ya fara tsiyaya daga idonta har dariya ta bawa mutane judge ya bubbuga table akayi shiru. 

Kallonta yayi yace "kotu ta yanke miki shekara goma sha biyu tareda horo me tsanani, wannan shine hukuncin da kotu ta yanke miki", kuka sosai ta fashe dashi tana rokonsa Allah Annabi ya rage shekarun amma ko kallonta judge beyi ba, da haka kotu ta watse jikin Binta duk yayi sanyi sosai ta tausaya ma su Zinaru musamman ma Hajiya, kowa ya lura da yanayinta amma ba wanda yace mata komai dan ansan dama dole taji ba dadi ganin ana kulle mutane a sanadinta, gida duk suka koma kowa jiki a sabule, su Hydar na parking motar Khaleel na parking, murmushi Hydar yayi yana mamakin Khaleel dan tinda su Dad sukazo sukayi magana yaki zuwa wurin Zeena wai shi kunyarta yakeji ita kuwa baiwar Allah batamasan wainar da ake toyawa ba, duk saukowa sukayi bayan sun gaisa da Khaleel sukayi cikin gida idonshi kyam kan Zeena ko kyaftawa, duka Hydar ya kai mishi tareda cewa "maza dai ta rainaka kana wani binta da ido kaman baka taba ganinta ba", tsaki Khaleel yaja yana hararan Hydar yace "kai dai wlh bakayi ba, ya ina kallon sanyin idaniyata kana wani duka na", "toh ai kai dinne, gwara kaje ka sameta kafin wani ya rigaka dan har yanzu batamasan da kudinka a kanta ba", cewar Hydar,  sosa keya Khaleel yayi yace "abinda ya kawoni kenan, maza ya zamuyi", dariya Hydar yayi yace "ya zakayi dai, se kace ba namiji ba", ajiyar zuciya Khaleel yayi yace "shiga ka turomin ita, yau za'ayita ta kare", dariya Hydar ya sakeyi yace "badan halinka zan kirama ita amma Allah kabimun sister a sannu, in tace batayi toh ka hakura", shiru Khaleel yayi dan idan Zeena tace batayi besan ya zeyi da kanshi ba dan ya dade yana dakon sonta. 

Ciki Hydar ya shiga ya kira Zeena tareda cewa "Khaleel na kiranki yana waje", "toh", kawai tace ta dauki mayafinta dan ba yau Khaleel ya fara kiranta ba, jingine jikin motarshi ta sameshi tace "Ya Khaleel gani", kallonta yayi yana hararowa kanshi ranar aurensu, gyara tsayuwa yayi yace "Zeenatu ykk, ya sch? ", "lfy lau", ta bashi amsa tana kallonshi ganin yana zufa kuma ga iska anayi, "ya karatu? " "karatu alhmdllh", "yaushe zaku fara waec", "nan da one month", ta bashi amsa cike da kaguwa, murmushi yayi yace "Zeena magana nazo muyi, i don't knw koh zaki fahimceni ki kuma amince, amma koma dai menene inaso ki bani amsan da nake sonji batareda kinja min rai ba", cike da mamaki tace "toh wannan wani magana ne zamuyi", shiru yayi yana kallonta sannan yaja numfashi yace "Zeena na dade ina sonki, so kuma bana wasa bane, so ne na aure dan maganan nan da nake miki ma yanzu da sadakina a kanki", dariya tasa sosai cike da mamaki yake kallonta, seda ta tsagaita dariyar tace "haba yaya dan Allah mubar wannan wasan, kaima kasan bada gaske bane, wasa kakeyi,  ina ni ina kai yaya, kafa bani almost 15yrs nida nakeson na auri dan yaro dan 25yrs dats is inma auren na gabana kenan", baki bude yake kallonta, ganin beyi magana ba ya kureta da ido yasa ta kalleshi jiki a sanyaye tace "kodai da gaske kake", kai kawai ya iya gyad'a mata ta sauke ajiyar zuciya tace "kaifa yaya na ne, do u think this is possible", kai ya kara gyad'a mata tareda cewa "of course it's possible", "toh yaya karatu na fah", "zakiyi insha Allah, amma a dakina", murmushi tayi tace "yaya kenan, a gaskiya bazan iya hada aure da karatu ba, sannan idan nace ka jirani na gama university five yrs dan law nakeso na karanta, sch of law one year, youth service another one year, kaga seven years kenan kafin lokacin ka tsufa saboda haka yaya kawai ka hakura ka nemo daidai kai", shiru yayi yana mamakin ta, ana ganinta shiru shiru ashe haka takeda tsatsaurar ra'ayi akan karatu, turkashi. Kallonshi tayi tace "yaya kayi shiru", yayi murmushin takaici yace "me kikeso nace", shiru itama tayi yace "shikenan Zeena bazan takura miki ba, amma inaso kije kiyi shawara da zuciyarki, bance kiyi shawara da kowa ba, sannan kuma inaso ki sani bazan taba hanaki karatu ba kaman yadda aurena baze shiga karatunki ba", shiru tayi yace "zan wuce, zan dawo next week inji me kika yanke", kai ta iya daga mishi tace "se kazo", da haka sukayi sallama ya wuce ita kuma ta koma cikin gida tana mamakin Khaleel wai sonta yakeyi.
Sosai Zeena ta shiga tunanin Khaleel tin daga ranan da yazo mata da maganan sonta yakeyi, hankalinta be kara tashi ba seda taje wurin Hydar dan ta tabbatar koda gaskene da kudin Khaleel akanta kuma ya tabbatar mata da gaskiyan hakan, abokin shawara take nema amma kuma ta mishi alkawarin bazatayi shawara da kowa ba se zuciyarta, wannan dalilin ne yasa bata fadawa kowa halin da take ciki ba, kullum da tunanin Khaleel take kwana take tashi, shida yace mata bayan sati daya ze dawo se gashi har sati biyu be zo ba, sosai ta shiga damuwa na rashin zuwan nashi, bawan Allah Khaleel kuwa da gangan yaki zuwa saboda yanaso ya gani in Zeena ta damu dashi ko a,a.

+

Yau ya kama Sunday wanda yayi daidai da washegari su Zeena zasu fara waec, gani take kaman idan Khaleel bezo ba bazata iya rubuta komai ba, ganin idan ta shareshi ita zata cutu yasa ta dau waya ta danna mishi kira amma kafin ya fara ringing ta kashe, tayi hakan yafi a kirga daga karshe dai tayi shahada ta kirashi, yana ganin call din ya saki murmushi sannan ya dau wayan tareda yi mata sallama, faduwan gaba taji daga jin muryanshi cikin sanyin murya tace "ameen wa'alaika sallam", ajiyar zuciya ya sauke tareda cewa "yan matana ykk, ya sch",tace "lfy lau, dama na kira ne inji ko lfy, yau two weeks kuma bakazo ba kai da kace one week", dariya yayi mara sauti sannan yace "banaso nazo naji amsar da zeyi breaking heart dina ne, shiyasa ban zo ba", cikin marairacewa tace "toh ai bakasan wani amsa zan baka ba da kake tsoron jinshi, ka sani ko amsata ta saka farin ciki", daga yadda take magana ya gane da yardar Allah da karfin addu'a ze samu nasara, mikewa yayi daga kwancen da yake yace "toh kin shirya inzo yau muyi maganan", kai tsaye tace "eh kazo, dan daga gobe bazan samu lokaci ba saboda zamu fara waec", cike da murna yace "toh bani 30mins gani zuwa", da haka suka kashe waya Zeena na murmushi Binta da ta dade da tashi daga bacci tace "saurayi kikayi shine koh ki fadamun", zaro ido Zeena tayi tace "ya Khaleel ne fah ba wani ba", kallonta Binta tayi tace "hmmm, ai in tayi wari zamuji", murmushi kawai Zeena tayi ta tashi ta shiga bathroom.
Riga tasa atampha dinkin riga da skirt me 6pieces, sosai dinkin ya zauna mata das a jiki, powder ta shafa se nude lipstick bata daura dankwali ba ta yafa mayafinta a kai Binta dake zaune tace "duk na ganin Ya Khaleel ne?", murmushi tayi sannan ta zauna kusa da Binta tace "kisan me, ban taba sanin inason Ya Khaleel ba seda yazo min da maganan, yanzu ji nake kaman idan bashi ba bazan iya rayuwa ba", murmushi Binta tayi tace "ai hakan keda kyau, Allah ya tabbatar da mafi alkhairi", "Ameen", Zeena ta amsa ta dashi, suna cikin haka wayan Zeena ya fara ringing, ganin Ya Khaleel ne yasa gabanta tsananta faduwa, "yanzu idan na fita me zance mai?", ta tambayi kanta, har wayan ta tsinke ya sake kira sannan ta dauka yace "gani a compound", batace komai ba ta kashe wayan tana kallon Binta, mikewa Binta tayi ta dauko turare ta mata wanka dashi sannan ta rakata har bakin kofan fita compound din ita kuma ta koma ciki tareda zama kan gado hawaye na bin kuncinta daya bayan daya, ba komai yasata hawaye ba se tunowa da nata masoyin wanda a halin yanzu data kara wayo ta gane cewar dama chan ba sonta yakeyi ba jikinta ya keso se gashi ita ta kasa mantawa dashi. 
Khaleel tin daga nisa ya hango Zeena wacce ke tafiya kaman tana tausayin kasa, murmushi ne kwance a fuskarshi dan gani yayi ta kara mishi kyau kaman ba ita ba, sallama ta karaso wurinshi ya amsa mata tareda cewa "barka da isowa yake tauraruwa ma'abociyar kyau da kwarjini", kunya yasa tama kasa amsa mai se sunkuyar da kanta kasa da tayi, murmushi yayi dan kunyar Zeena da rashin son maganarta na daya daga cikin abinda yaja hankalinshi kanta, "ba gaisuwa?", ya tambayeta ganin tayi shiru tace "ina wuni, anzo lfy", yace "lfy lau, ya na sameki", "lfy lau" ta bashi amsa kanta kasa har yanzu taki dagowa, "toh baza'a dago a kalleni ba, koh a haka zamuyi maganan?", bata saba jin kunyar Khaleel ba amma tinda ya bijiro mata da maganan sonta yakeyi taji duk duniya babu wanda take kunya sama dashi, "dan dago mana kinji", yayi maganan a marairaice wanda hakan yasata dagowa ta kalleshi yace "yauwa koh ke fa, toh yanzu fada min what do you think about my proposal, kin amince", gad'a mai kai tayi yace "fadamin inaso naji ya fito daga bakinki plss", a hankali tace "na amince amma......", se kuma tayi shiru yace "amma me?", kallonshi tayi tace "karatu na fah", yayi murmushi yace "believe me idan nace zakiyi, har masters idan kinaso duk zan barki kiyi wannan duka ba matsala bace", kanta kasa tace "toh shikenan, Allah yasa hakan shi yafi alkhairi", cike da murna kaman wanda akawa bishara da aljanna yace "Ameen my wife to be", murmushi tayi tana rufe fuska daga haka suka bige da hira wanda a kowani minti se ya kara jaddada mata yadda yake sonta yake kuma jinta a zuciyarshi, basu sukama juna sallama ba seda sukaga fitowan Hydar zashi masallaci sallan magrib sannan Khaleel ya mata sallama yabi bayan Hydar daya basar dasu saboda kar a jawo mishi raini (lol). 

BAYAN SATI DAYA 

Familyn ne gabadaya zaune kan dinning suna dinner Hydar gabadaya hankalinshi na kan Kausar dake tsakuran abincin tana toshe hanci, cike da tausayi yake kallonta danta rame kaman ba Kausar dinshi ba, da farko cikinta kaman bame laulayi ba seda ya karasa shiga wata uku sannan ya fara wahalar da ita dan zuwa aiki ma ta ajiye shi gefe saboda bazata iya ba, hannunta ya kamo ta dago ta kalleshi yace "don't force yourself ", ai kuwa kaman jira takeyi ta ture plate din jollof jin daga gabanta ta mike zata bar wurin danji take kaman 'ya'yan cikinta na hautsinawa, dakinta ta wuce yabi  bayanta kaman yadda ya ayyana kuwa tana bathroom tana hararwa, shiga yayi yana bubbuga bayanta cike da tausayawa harta gama sannan ya gyara wurin suka fito, kan gado suka zauna yace "me zakici", "bakin lipton zansa", dama yasan abinda zatace kenan dan kwanan nan shi yazama abincinta, shi kadai takesha yake zama, zuwa yayi ya hado mata amma ga mamakinshi kafin ya dawo tayi bacci, murmushi yayi ya ajiye lipton din kan bedside drawer sannan ya gyara mata kwanciya ya zauna yana kallonta, be taba sanin ciki zesa Kausar tayi sanyi tabar rigima haka ba, gabadaya se yaji yana missing din old Kausar dinshi wanda zece ta bari tace se tayi, ya hanata fita tasa kafa ta tafi ta dawo suyita rigima, amma se gashi babaynshi na wahalar da ita daga bacci se bacci dan ko abinci taci ba zama yakeyi ba baccin ne kesata samun relief. Hannunshi yakai kan cikinta yana shafawa a hankali yana surutai shi kadai yana gayawa babyn ya daina wahalar da momma dinshi, a nan wurin Hydar ya zauna ya kasa tashi yana jira ta tashi tasha lipton din dan bayaso ta kwana da empty stomach gashi kuma bayaso ya tasheta, ganin karfe goma yasashi mikewa yayi mata warming din tea din ya dawo a hankali ya dinga tashinta harta tashi yace "tashi kisha se kisha magani", tashi tayi zaune ta karba shi kuma ya dauko mata maganinta ya bata ta sha da ruwan lipton din sannan ya dauko mata nighty tasa ta kwanta, peck ya mata a goshi sannan ya kashe mata fitila ya fita zuwa dakinshi, shima wanka yayi ya shirya cikin PJz dinshi sannan ya sauka kasa, koda ya leka dakinsu Binta karatu sukeyi ya musu seda safe ta kashe wutan parlorn ya koma dakin Kausar shima ya kwanta dukda ba bacci yakeji ba amma baya ganin ze iya barinta ita kadai.

Post a Comment for "HUTU CHAPTER 9"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...