HIKIMA CHAPTER 7 - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

HIKIMA CHAPTER 7

HIKIMA CHAPTER 7

- - Post a Comment
HIKIMACHAPTER 7Wannan furucin nashi Ya girgiza min duniyata da abinda ke cikinta. Bansan yadda zan kwatanta muku yadda sakonshi ya iso gareni ba, one thing shi ne daga ranar komai nawa Ya canza. Nasan da yawa zakuce Hamma bai kyauta ba, zakuce he messed up! Yeah Hakane amma abu daya da yasa ya fada min hakan, saboda ganin Bashida wata mafita data rage mishi banda hakan, yana ganin zai rasa ni matsawar bai fada min ba.

Kallonshi nayi Kamar yadda yake kallona, idanunshi Sunyi tas sede akwai Dana sani a cikinsu, Wanda I'm sure Dan Ya fada min abinda Baffa da Mama sukai ta harkilon rufe min ne, amma aikin gama ya gama.

"Hamma zan fita"

Na fada can Kasan makoshina, idanuna Sunyi jawur Ko ban Kalli madubi ba, nasan da hakan Dan har wani yaji yaji nakeji. Bai Musa min ba ya bude min na fito, ina jinshi yana fadin

"Allah Ya tashe mu lafiya"

Ko amsa ban bashi ba na wuce cikin gida. A hankali na murda kofar parlor, cikin zuciyata addua nake Allah yasa Mama da Baffa basu parlon. Amma ina sallama wadda a hankali ta fita saboda yadda muryar take a shake, babu wani kuzari Haka na shiga na sameshi suna zaune da alamu zamansu kenan.

"Baffa, hannu iwar tauki, Mama miwarti"

Na fada Ina daidaita yanayina, amma banyi nasara ba, Mama ta zuba min idanu, yayinda Baffa yace

"Uwata me ya sameki? Kinga idonki kuwa? "

A hankali na lumshe idon, Karo na farko kwakwalwar Kaina tace Basu suka haifeki ba, idanuna na bude ina karkaro murmushin da iyakar kokarina amma fatar baki kawai ya tsaya nace.

"Abu ya fada min a ido. Mama zan kwanta kowa na gaisheki"

Ina fadar Haka na juya da sauri, saboda Ina tsoron tambayoyi, bana son a tambayeni Dan banida amsar basu, na nufi dakina inajin Baffa na cewa Mama kada ta bini ta barni tukun. Nikam Ina shiga dakina, na tura kofar na jingina da ita ina jin yadda zuciyata ke bugawa Kamar zata fasa kirjina ta fito, ga numfashina da kyar nake iya janyo shi. There and then nasan attack zan samu, hakan yasa nayi saurin saka lock a kofar, drawer naje na ciro inhaler babu jira na dinga shakawa, hawaye ya wanke fuskata tamkar zanyi hauka haka na dinga ji a wannan lokacin, saboda naki na nutsu shiyasa asthma taki sauka Se karuwa abin yake, ganin da gaske idan na cigaba da zama to tabbas lungs dina collapsing zasui saboda da kyar nake fuzgar iska Ko kuma na mutu ban su waye suka haifeni ba, bansan ko ni Shegiya ce ba.

Mikewa nayi ilahirin jikina karkarwa yake na bude kofar na fito parlor, tunkan na karaso naji Salatin Mama daga nan ban kara sanin inda nake ba, Se farkawa nayi naga oxygen a hancina a gadon asibiti.

Hawaye a hankali ya Fara sauka saman kuncina, idanuna na runtse inajin wani abu me tsini yana piercing kirjin, ga Kaina tamkar zai fado haka nakeji. A hankali naji Mama ta kama hannuna tana fadin

"Hikmah kin tashi"

Idanuna na bude, hakan yasa ta tabbatar da zarginta, hannuna ta sake min ta fita, can Sega ta ta dawo da nurse, tana zuwa ta ciremin oxygen din sannan tace

"Zainab tashi ki zauna" 

A hankali na tashi na zauna har lokacin kuka nake, Wanda hawaye ne kawai se wani tukukin takaici da bakin ciki marar misaltuwa da nake ji cikin zuciyata. 

"Ya jikin? " 

Ta tambaya tana hada allura cikin syringe, kaina na gyada mata Dan Ko bakina bana son budewa. Anan tamin allura wadda ta kusa mintina ashirin tanayi, tana gamawa ta dubeni tace 

Story continues below


"Me yake miki ciwo? " 

Kaina na girgiza nace 

"kaina da kirjima" 

Fita Tayi can se gata ta dawo dauke da abin BP, tana gwadawa naga ta Kara Har sau uku sannan tace 

"Ke me yake damunki, me yasa BPnki Zaiyi shooting haka" 

Wannan me yake damunki da tace se na fashe da kuka me ciwo, me zance? Basu bane iyaye na? Waye ya haifeni? Kaina na girgiza Ina kankame jikina, ko mintina basuyi ba asthma ta Kara tashi. Nan da nan aka bani taimakon gaggawa sannan akai min allurar bacci Dan na huta. 

Seda nayi kwana biyar a asibiti sannan aka sallame mu, tunda nake ban taba ganin Tashin hankali irin wannan da na shiga ba a wannan lokacin ba, Ko a mafarki ban taba tunanin akwai irin wannan yanayin ba. Seda naji komai da kowa ya fita akaina. Nasha Yan dubiya amma duk idan na tuna cewar Kila babu Hadin iya balle na Baba Se sabon kuka. Mama tayi juyin duniya na fada mata abinda yake damuna amma sede kuka, ko kuma idan taci saa nace Babu komai Kaina na kawai. Baffa Dama nasiha kawai yake min. Su Anty Fadila kuwa sede kallo da ido. Ranar da Hamma Mussadiq yazo dubani babu kowa a dakin Se ni kadai na idar da sallah ina karatun Qurani ya shigo, inajinshi ya zauna amma naki dagowa balle na kalleshi, kuma tunda ya shigo na daina fahimtar Harrufan  balle har na hada karatun ya tashi 

"Hikmah kiyi hakuri, ban taba kawowa idan na fada miki hakan zaki damu kanki ba. Ba se kinyi hakan ba, ba se Kin sawa Kanki hawan jini ba kina neman kashe Kanki, simple Hamma Bazan aureka ba ya wadatar Hikma. Just ki Kalli madubi kiga yadda kika koma..... " 

Ban barshi ya karasa fadar rubbish dinsa ba na katse shi ina fadin 

"Me Kake tunani? Saboda kace kana sona zanyiwa kaina Haka? My friend stop dreaming please. Ka manta? Kodan ka manta, amma ina son Kasan ka barmin tabon da har abada bazai goge ba. Nagode sosae da ka farkar Dani daga baccin da nake, Nagode da ka fadamin Baffa da Mama ba iyayena bane. " 

Ina gama fadar Haka na Mike na nufi kofa, ban bude ba amma na tsaya nace 

"Hamma zo ka fita, bana son ganinka!" 

Babu musu sede jikinshi yayi mugun sanyi yazo Ya wuce ya fita, da gudu na fada gado na rushe da kuka. Tundaga ranar Har aka sallemeni bai Kara dawowa ba. Muna zuwa gida Mama duk ta kora su Aneeysa gidajensu Dan tunda na kwanta suke jele a gurina. Dakina na wuce bisa umarnin Mama akan nayi wanka na canja kaya kafin nan ta gama Abinci. Dakina na wuce bayan Munyi sallama dasu Anty Fadila, ni Kaina kyankyamin kaina nake saboda I hate asibiti abinda ya hanani yin clinicals kenan, Bazan iya coping warin Izal, Hypo, Jik dasu Sevulum ba. 

Ina shiga naji tamkar Bakuwa ba Kamar yadda na saba ji idan na dawo dakin bayan doguwar tafiya, mostly da na dawo zan fada gadona na kankame duvet cover din amma Yanzun se naji bai birgeni, wanka nayi Nazo na Nemo saukakkiyar Abaya red na saka, mirror naje na kalla seda na tsorata tsabar yadda na rame, idanuna da mutane ke fadar su, sun zurma ciki ga bags a Kasan su, wannan dogon hancin nawa Ya fito yayi tsaho saboda duk kumatun sun sabe Se zygomatic kadai. Wuyana kam Baa magana Dan kashin nan sun fito Sunyi kwal tamkar a aje abu su zauna. Hawaye a hankali ya gangaro min nasa hannuna na goge sannan na fita jin Mama ta Fara kwalla min kira. 

A parlor na sameta da bowl cikeda fruit salad, ina zama ta miko min, karba Nayi nasha dukda taste din was heaven amma Bazan iya ba gaba daya hankalina baya kan Abinci duk yadda nakai da sonshi. 

"Hikmah" 

Dagowa nayi na dubi Mama nace 

"Naam Mama" 

"Duk duniyar nan Kinada Wanda yafini? Kin canza iyaye ne? " 

Da sauri na shiga girgiza Kaina ina share hawayen da ya Fara bayyana a kumatuna, nace 

"A'a Mama" 

Amma cikin zuciyata wani girma da soyayyar Maman Ya kara cikani sede Bazan iya fada mata danuwata ba 

"Me yake damunki? Ki fada min Kinji. Ko Bazan miki magani ba amma nasan zakiji sauki a ranki. " 

Kaina na girgiza zuwa lokacin kuka nake sosae nace 

"Mama kiyi hakuri kawai kiyi min addua" 

Abu daya da Mama batada takura bazata taba takura maka ba, Tundaga lokacin bata kara Maganar ba sede tace Allah ya saukaka miki. 

Se dare na nemi wayata, message na Fara budewa Naga messages din Hamma Aiman rututu, hawaye sosae Ya kwance min, duk wannan abin we're not related in anyway. Se kuma wata bakuwar glo number da tayi min message. Ban bude ba na Fara kiran Hamma Aiman, bugu daya Ya katse ya kirani yana fadin 

"Kanwata ina kika shiga? " 

Kunsan akwai mutanen da naturally kana cikin damuwa, Ko hakuri suka Baka Se kayi kuka, take kuwa na Fara kuka amma bai katseni ba seda na gama sannan yace 

"Tell me, me ya faru" 

Babu abinda na boye mishi na fada masa komai sannan nace 

"Dama na dade ina tunanin Anya gidanmu nake zaune? Babu wani abu da zai nuna maka sudin Yan uwana ne..... " 

Se kuka ya hanani karasawa hakan yasa nayi iya yina sannan yace 

"Naji komai Hikmah, I'm very very sorry. Banso Haka labarin ya sameki ba. Amfanin boye zancennan ya Kare Dan tabbas Hakane abinda hammanki ya fada. Sede ke me kike gani? " 

Idanuna na goge nace 

"Babu abinda zan fadawa kowa, nasan tunda na sani iyayena duk inda suke zan gansu, kuma indai Munada rabo Haduwa zamu hadu dasu. Amma Bazan iya tunkarar Baffa da Mama da wannan zancen ba, they've done alot " 

Aiman yaji dadin abinda na fada, ina tunanin ya kamata a dauki Aiman a matsayin lecturer, Ya iya bada lecture, komai da ilimi yake yinshi. Seda yayi min nasiha sosae, ya bani baki sannan muka rabu. 

_Ranar ta kasance jumaa, Baffa da iyalanshi Mama, Musbahu, Mussadiq, Mustapha da autan Mama na gaban goshi Mus'ab. Dukkansu suna cikin motarsu sun dawo daga Samunaka kaduna. Sunje ziyarar wani Yayan Baffa Wanda shi ne Mahaifin Abba (Mr perfect). Kana kallonsu Kasan family ne Wanda zaman lafiya, kauna da shakikiyar soyayya take wakana a ciki. Sunyi nisa sosae har suka shigo wani karamin gari na doguwa, anan Baffa ya tsaya ya siya musu tsire da juices, Mus'ab kasancewarsa shi ne karami aka siyo masa milky juice. Suka cigaba da tafiya cikeda farin ciki a Haka Mustapha da Mus'ab dake back seat sukai bacci._ 

_A hankali Baffa ya Fara rage gudun motar da yake, Ya dan juyo kadan yace_ 

_Kowa Yayi addua zamu shiga Falgore game reserve_ 

_Kai dukkansu suka gyada dan lokacin, hanyar batada kyau hardly ayi sati daya ba tareda record din gagarumin robbery a hanyar ba. Shiyasa mutane ke fargabar wucewa ta gurin. Haka suka dinga tafiya babu wata Mota Se kwaya biyu da suka wuce. Seda sukaje tsakiyar hanyar sannan Wasu mutane kowanne rikeda bindigogi, ga mask a fuskokinsu sanye da bakaken kaya. Suka bayyana a tsakiyar titin._ 

_Tsabar yadda Baffa ya gigice, rikicewa Yayi yana neman sakin steering, Mama hannu ta daura akai tana Salati, sukam su Musbahu karar brake din da Baffa ya taka, yasa duk suka dawo daga abinda sukeyi, Mus'ab ganin an bude kofar an fita da Baffa da Mama, yasa ya Fara kuka. Duk wani abu dake jikin bayin Allah nan biyu babu abinda yake banda rawa, tsabar firgita, Mama se kuka takeyi tana rokonsu su kyalesu amma ko sauraronta basuyi, ga babu wata Mota da take da alamar zata wuce saboda yadda mutane suke very wary of hanyar._ 

_"Malam dago muyi magana ta fahimta, Dan nan da kake ganinmu bawai fashi ko wani abu zamu yi muku ba"_ 

_Jin wannan furuci daga bakin shugabansu yasa Baffa ya daidaita kanshi, Mama ta rage sautin kukanta. Ganin Haka na Ogan yayi waving hannunshi, nan take sega yarinya an fito da ita daga jeji, hannunta dauke da biscuits tana kaiwa baki. _ 

_Ogan ne ya karbe ta, sannan ya mikawa Mama ita yace_ 

_"Hajiya, wannan yarinyar da kike gani bata san kowa ba, bata san komai ba. Mun taho daga Abuja zuwa jos shekaranjiya a motar mu da muka hau, mukaji Wasu Christians suna zancen sato ta daga gidansu zasu kaiwa dodon tsafi. Yarinyar kana kallonta Kasan yar musulmai ce, Dan Haka mukai ta binsu, cikin dare muka sace ta. Dukkanmu da kuke gani kowannenmu babu me iyali balle ya kai gidanshi, shiyasa muka yanke hunkucin tare hanya mu bada amanarta. Idan da akwai rabo Allah zai hadata da iyayenta, idan babu kuma Allah shiyasan me ya hukunta akanta. Kun amince zaku rike ta? "_ 

_Cikin sauri Mama ta gyada kanta, Baffa bakinshi Har hardewa yake wajen fadin_ 

_"Nayi muku alkawarin zan riketa matsawar raina, zan kula da ita Har Allah Ya nuna ikonshi a kanta. Ku kuma Allah Ya duba lamuranku"_ 

_Daga Haka Kamar yadda sukai alkawari basui musu komai ba, suka sallamesu, Mama kankame da Lulu a hannunta. Kayan da Hafsa ta saka mata Tun na birthday Har lokacin kwana uku sune a jikinta Baa canja mata ba. Hatta bracelets da tag din dake hannunta Cynthia Batayi nutsuwar cireshi ba. Baki daya Mama take ta bin Lulu da kallo Wadda jinta jikin Mama yasa tayi bacci, kana kallonta Kasan yar gata ce, ko suwaye iyayenta suna ji da ita, she just look like a princess. Shiru ko kwakkwaran motsi babu cikin motar se wani uban gudu da Baffa ke shararawa. Seda ya shigo cikin garin Kano sannan ya daidaita gudun amma har lokacin jikinshu bai bar Bari ba._ 

_Misalin uku na yamma suka karaso gidansu, hankalin su dukka Baa kwance yake ba. Baffa yana sauke su Ya juya, itakam Mama da Yaran ciki suka shiga, Har lokacin Lulu bacci take bata farka ba. A daki ta ajeta kan gado sannan ta fito dan gyara gidan. Su Musbahu dukkansu a zazzaune suke, jikinsu Yayi bala'in sanyi, to wannan Tashin hankali har ina? A tare ka a Baka Da Dan ma dan mutum, AI abin se addua kawai, gashi Bakada halin cewar bazaka amsa ba. Kafin dawowar Baffa Mama da taimakon su Musbahu duk ta gama abinda ya dace, ruwa ta tafasa lokacin Lulu ta farka sede Ko uhm Batayi ba balle kuka, hannunta take yawan sawa a baki alamar Tana jin Yunwa. Wanka Mama tayi mata sosae sannan ta goyata tunda batada kayan da zata saka mata. Nan da nan wani baccin ya Kara dauke ta Ko boiled egg and boiled Irish da Mama tayi mata mashing ba taci ba. Har Baffa ya dawo tana goye bayan Mama, seda yayi wanka ya shirya Sannnan ya bawa Mussadiq key akan ya shigo da kayan dake booth. Siyayya ce sosae yayi ma Lulu Tundaga papers har bargo, tamkar yar cikinshi._ 

_"Amina, Ya kike ganin zamuyi da yarinyar nan?"_ 

_Baffa ya tambaya yana karbar Lulu wadda aka shiryata cikin below elbow length riga me kyau Ash da yarfin yellow, rigar tayi mata kyau, gashi an bata Abinci duk ta wartsake ba Kamar lokacinda aka basu ita ba._ 

_"Duk yadda kace Baffan Musbahu hakan nan zaayi, amma Nidai har zuciyata inason yarinyar, Ina ganin mu riketa kawai"_ 

_Cikeda jin dadi Baffa ya murmursa, Wanda rabon da yayi Murmushi Tun kafin suje Falgore. Hannun Mama Ya kama yace_ 

_"Allah Yayi miki albarka Amina, Inshaaa Allah wannan yarinyar se ta zame mana hasken idaniya"_ 

_"Amin Amin"_ 

_Mama ta ansa mishi. Washegari suka shirya duka suka tafi Barikin ladi, inda Baffa ya kaiwa iyayenshi Zainab wadda dama sunan mahaifiyarshi ne, kuma Haka ya gani jikin bracelet din hannunta. Mahaifinshi bai wani damu sosae ba yace Da ai na kowa ne, bakasan Wanda zaka amfana dashi ba, sosae Ya sakawa Hikmah albarka Kamar yadda Mussadiq ya rada mata. Yan Uwa na kusa duk sun goyi bayan rikon Se kadan da suke ganin Ko annoba Muhammadu Ya jajibo musu. Haka suka karasa garinsu Mama Mangu nan ma duk daya, dake da ne duniyar a kwance take, kowa so yake yayi taimako ba Yanzu da kowa ke tsoron kowa ba._ 

_Cikeda nasara suka dawo Kano, inda kwanansu biyu suka koma sabuwar anguwa, nan sunje da Hikmah, babu Wanda zai kawo cewar ba yarsu bace. Seda sukai sati uku sannan Baffa ya tara duka Yayansa hudun yayi musu warning me karfin gaske akan Hikma_ 

_"Nasan Dukkanku kunsan yadda akai muka samu Hikma. Nasan ko Mus'ab bazai manta ba. Inason ku tayani rike Amana, ku Tayani jaddadda Ikon Allah, ku rike ta a matsayin yar Uwa wadda muka Haifa, ku goge hoton scenario tsintar ta a brains dinku, ku dauka cewar ita din jininku ce. Dan duk Wanda ya Bari Hikmah tasan matsayinta a gurinshi tabbas zai hadu da fushina. Ni na haramta aure tsakaninku saboda matsawar wannan ya shigo to se na fadawa Hikmah ita ba yata bace. Ina fatan kowa zai kiyaye. "_ 

_Tundaga wannan ranar suka cigaba da rayuwarsu happily, mutane da yawa idan suka hadu da Mama zasu tambayeta yaushe kika haihu babu sanarwa sede tayi dariya ta bada hakuri. Kowa a gidannan San Hikmah yake, wannan ya dauketa wannan ya ajeta. DUK Wanda Ya fita to kuwa indai zai dawo se ya kawowa Hikmah abu. Wannan shi ne Farkon dasa muguwar kiyayyar ta a Zuciyar Mus'ab, saboda shi ne auta duk attention din kowa akanshi yake amma zuwan Hikmah kidan se ya canja salo. Ya zalinci Hikmah yadda baku zato gashi seda tayi shekara biyu da watanni sannan ta Fara tafiya, anan aka fahimci matsalar da ta sameta Tun a ciki ta kafarta ta hagu._ 

_Baffa da Mama Sunyi kokarin na gaske na cika alkawarin da suka dauka. Kayan da suka cirewa Hikmah a zuwanta Mama ta adana with the hope ya zama abinda zai sadata da iyayenta! _

Kwanaki a hankali suka cigaba da tafiya babu wani abu daya canza daga yanayin yadda nake rayuwa, kullum idan na tashi banda kuka babu abinda nakeyi Matsawar zan kebe ni daya, na kasa yin hakuri dukda yadda kullum Hamma Aiman ke bani baki, Rana bata taba zuwa ta fadi bai kirani ba, shiyasa yake da matsayi me girma cikin zuciyata, inajin tamkar banida wani Dan Uwa Se shi. Shikam Uban gayyar Hamma Mussadiq tamkar surikai Haka muke dashi, kunyata yakeji sosae, ko idan yazo Ya sameni a parlor, Se yayi ta sunkuyar da kanshi bazai ma sake ba balle ya dade, har ranar seda Mama ta Tambayeshi me ya hada mu amma cewa Yayi babu komai, amma idan yazo bana parlor zai dade amma da zarar Na fito zai Mike Ya tafi. Har ga Allah bana jin zafinshi, ni godiya nake mishi cikin zuciyata at least ya sanar dani matsayina, Wanda nasan yayi dana sanin hakan. 

Mama ta maida ni asibiti sau uku follow up amma amsar kullum daya ce jinina baya sauka, ranar Haka ta sani a gaba ta dinga kuka akan na fada mata Meye matsalata? Nima se kuka na rasa yadda zan saka raina Inji sanyi. Nidai alkawari na dauka Bazan taba fadawa kowa a gidannan halin da nake ciki ba. Amma Bazan iya jurar kallon hawayen Mama ba. 

"Mama Dan Allah kiyi hakuri, bansan yadda zan miki bayani ba. kiyi hakuri tunanin Abdallah nakeyi" 

Dif kukanta ya dauke tana kallona cikeda mamaki da damuwa, idanuna na kawar Kamar gaske, to ya zanyi dole nayi mata karya, 

"Hikmah dama Baki manta yaronnan ba? Daman har Yanzun kina tunaninshi. Ina ce mun wuce gurin Hikmah, Baki yadda da kaddara ba? Baki yadda komai na rayuwa MUKKADARI NE daga Allah ba? Haba Hikmah ina tauhidinki Ya tafi" 

Hawayena na share na matso na rungumeta a jikina, Mamata da babu kamarta. Idan Har wannan da ba ita ta haifeni ba tana min wannan son to inaga Uwar data haifeni? Wanne irin so zata min nima Wanne zan mata? na ayyana a raina. Shikenan na kashe Maganar, daga wannan lokacin na kara kaimin addua sosae sannan na Fara dangana da hakuri wannan yasa hankalin kowa ya kwanta. 

Bari na barku haka bari na koma zuwa rayuwata, mabudin dukkan Wasu Alkhairi. Da farko Kamar yadda kowa ya sani haduwata da Abdallah Ahmad Abdallah ba haduwar Arziki bace, Babu Maganar da na tsana a duniyata irin zancenshi saboda a ganina babu Wanda ya taba wulakanta ni irinshi. Amma wani abu da Allah shi shi ne yasan daidai, shi yasan what tomorrow will be. Duk yadda mutum ya kai zurfafa kiyayya akan abu to Allah yana iya canja lamarin labari yasha banbam, hakan ce ta Faru tsakanina dashi. 

Mun koma school bayan dogon hutun session da muka sha, kowa a wannan hutun zakaga yadda yake kyau, fresh da kiba amma bandani, kallo daya zamanin kaga tamkar nayi wata doguwar jinya ne, ni a ganina gwara doguwar jinyar akan ciwon da zuciyata take min, akan halinda na samu Kaina a ciki, ni Kaina na gaji da halinda nake ciki, na gaji da jina babu walwala, na gaji da rufe bakina bana magana, duk yadda nake son ganin hakan ya faru amma kwatakwata zuciyata da kwakwalwar Kaina are not complying. 

Dayake level 3 zamu shiga kuma normally level 3 students basuda accommodation a campus din ABU , so Tun a gida aka sama min accommodation a Empire Apartment dake nan wajen school amma Zaa iya trekking zuwa school. Daki daya ne da toilet se kitchenette attached. 

Nafi awanni biyu ina gyara sannan na Gama, Nanah na Fara kira tace min bata dawo ba se next week, mun Dan taba hira sannan mukai sallama. Su Mama na kira sannan na sanar musu isowata, sosae Mama ta dinga Nanata min Zancenta na kullum nasiha da karbar rayuwa a yadda ta zowa mutum. Da wannan mukai sallama na koma na kwanta hade da lumshe idanuna. Na tabbatar da ace lokacin ina Hikmah ne to babu yadda zaayi Naso dakinnan ni daya , Dan bana son kadaici ko Yaya yake, amma Yanzun har wani dadi nake ji ganina ni daya. 

Seda nayi Sallar ishai sannan na fita inda Wasu eateries suke don naci Abinci. Ina zuwa nayi placing order sannan na tafi can VIP section karshen gurin na samu seat na zauna, sweet din dake aje kan table din na dauka na bare sannan na jefa bakina ina bin mutanen dake zazzaune yawanci ka kallesu suna cikeda walwala da farin ciki dukda Yan tsirari ne, a raina na ayyana dukkansu sunsan iyayensu, a gidajensu suke amma ni gani bansan su waye iyayena ba, bansan me yasa na Baro hannunsu bansan yadda rayuwar su take ba ko sunada rai, ko sun mutu? Ko me yasa na rabu dasu. Itace tambayar da kullum nake yiwa Kaina Kamar sau biyar ko fin Haka a duk ranar duniya. Tsorona daya ace saboda an haifeni illegally shiyasa aka jefar Dani, tunanin wannan yasa na kifa Kaina akan table din na some Sana'a ta, Nama manta a inda nake da abinda ya kawo ni amma inajin zuciyata na wani irin zugi, kaina ya Fara Sara min. Na kusan mintina goma a Haka, su basu kawo order ba ni ban tafi ba, ban kuma daina kuka ba seda naji an ja kujerar dake gefena an zauna sannan nayi saurin dagowa ba tareda na iya goge fuskata ba. 

Story continues below


Abdallah ne ya zuba min idanunshi, tamkar Wanda zai zukeni dasu, cikin sauri na sunkuyar da kaina tareda share hawayen fuskata na Mike Dan bar mishi gurin. Haka kawai zai zo yasa ni gaba da kallo, gashi indai zanji kamshin turarenshi, Ko idanuna su shiga cikin nashi to gabana ya dinga faduwa kenan. 

Gyaran murya Yayi, hakan yasa na dan juyo, baiyi magana ba se nuna min seat dina da yayi, na fahimci na zauna yake nufi amma na dauke kaina tareda kokarin barin gurin a karo na biyu. Bansan ya akai ba se hannunshi me tsananin taushi naji cikin nawa Ya kama, da sauri na kalleshi saboda wani current daya zuba min a jiki, shima kallona Yayi a tare muka saki hannun yace 

"Koma zaki zauna" 

Bakina na dan tura nace 

"Tafiya zanyi na gama" 

Harara ya wurgo min yace 

"Sit I said" 

Wannan karan banyi masa musu ba na koma na zauna tareda jinginar da bayana sosae na lumshe idona. Tunda na zauna jikina ke bani kallona yake, gaba daya se naji na takura saboda bana son kallo amma shi Naga Kamar Sana'ar shi ce kallon. Turo baki nayi tareda pouting face dina kuma har lokacin idanuna a lumshe ban budesu ba, hakan yasa ya saki siririyar dariya yace 

"Zainab amma ke last born ce Ko?" 

Bude idanuna nayi na sake tura bakin gaba Bance komai ba, shima bai kuma bi ta kaina ba ya shiga making call wadda da alamun mamanshi ce saboda yadda yake ta shagwaba yana melting Kamar wani jelly. Dole na zuba mishi ido ina sakin murmushi, bansan na shagala ba seda ya dan daki Table din, hakan yasa nayi firgigit tareda tsuke fuskata ni a dole kar Yayi Magana. Aje wayar hannunshi Yayi saman table din yace 

"Mutane da yawa sunce Inada kyau, ban taba yadda Ba se yau da Zainab ta fada." 

Ware idanuna nayi jin yadda ya Fara min sharri nace 

"Kai Sir! Yaushe na fada? " 

Murmushi yayi tareda fadin 

"Gashi dazun Nazo kinata kuka Yanzun kuma gashi Kallona kawai ya saki dariya. I'm genuis" 

Dariya nayi na rufe fuskata da hannuna daidai lokacin waitress din ta kawo mana order ta aje sede Ina duba nawa nace mata 

"Waffles nayi order ba solid food ba" 

Na fada Ina yatsina fuska, cikin Murmushi tace 

"Oga ne ya canja order naki" 

Ta fada tana nuna Abdallah, bude baki nayi zanyi masifa and he beat me to it yace 

"Tafiyarki, Eat" 

Muryarshi na bada umarni, bansan me yasa komai yakeyi ba yake affecting dina, Wai ni ce Hikmah wani kato ke bawa command haka, sosae nake mamakin hakan. Ya zanyi Haka na nutsu na Fara ci Tun Ina cakula har na ware naci na koshi, nasha lemu sannan naga Anyi min packaging waffles din. Kallonshi nayi nace 

"Sir Bari na tafi dare nayi. " 

Mikewa yayi ya dauki wayarshi sannan ya nuna min hanya alamar nayi gaba, nokewa nayi nace 

"A'a ka wuce mu tafi" 

Kanshi Ya girgiza kawai sannan ya wuce gaba ina bayanshi, seda yayi settling bill din sannan muka fito, bai shiga matarshi ba ya cigaba da taka min har apartment dinmu sannan yace 

"Ki shiga ciki" 

Kaina na gyada tareda ce mishi 

"Thank you so much, Allah Ya bamu alkhairi" 

Murmushi yayi min tareda kashe min idanunshi baice komai ba, yana tsaye har na shige ciki. Ina shiga naji zuciyata a hankali tana washewa, har Ina sakin murmushi. Sosae abin ya bani mamaki is Abdallah that lucky? Na tambayi Kaina ganin bakina ya kasa rufuwa. Shiga nayi na zauna akan katifar da Tasha gyara da wani sabon bed sheet, wayar na saka a gaba Inata kallonta nayi zurfi sosae cikin tunani kawai Sega text da wata bakuwar Airtel number 

_Have a nice night Farin cikina_ 

_Farin cikina?_ 

Na maimaita sannan na saki karamar kara, I can't believe Nike wannan farin cikin, ban masan waye ya turon Ba amma kowaye Ya samu lada Dan kuwa ya sani farin ciki. Alwala naje nayi sannan nayi light off na kwanta bayan nayi addua na canja zuwa nighties dina. Kwanciya nayi daidai shigowar kiran Hamma Aiman, shi kanshi seda yayi mamakin jin yadda muryata ta ware na dawo Kamar da, ya nuna farin cikinshi sannan muka Dan taba hira kafin mukai sallama. 

Da asuba da na tashi sallah wani message ne aka turo da same number 

_Farin cikina, asuba tayi. Kiyi sallah kiyi mana addua_ 

A hankali Murmushi ya Kara kubce min, seda na idar da sallah sannan nayi wanka na dakko waffles dina bayan na hada tea nasha. Lecture se 10am hakan yasa na nade a katifa Se bacci abuna. 

Karfe goma a lecture hall tamin, Reproductive physiology muke dashi, Tareda Amjad muka shiga, munata hira abinmu Har lecturer yazo muka gama sannan na lura da Pop din message 

_Farin cikina you looking take away_ 

Amjad ne yace 

"Hikmah dariyar me kikeyi ne haka? " 

Daidaita kaina nayi tareda girgiza Kai nace 

"Babu fa" 

Kafada ya daga irin ya wuce dinnan. Muna nan zaune Har time din shigowar Abdallah yayi, tunda ya shigo Amjad ke min kuskus amma na shareshi. Kamar kullum seda yayi booting system dinshi, Ya kwankwadi Faro, Ya zura glasses dinshi kafin ya Fara bin class din da idanu, Se naji tamkar Danni yake hakan, zuciyata wani bugu take, yayinda naji duk tsikar jikina ta tashi, ban gama tantance hakan ba se jin zazzakar muryar shi me cikeda Amo yace 

"Zainab Muhammad, come forward" 

A razane na dago na kalleshi, shima kallona yake hakan yasa na langwabar da kaina Ina rokonshi amma mutuminnan se ya kawar da kanshi gefe irin ban gane me kike nufi ba. Amjad da na gaban sit dinmu nata fadin 

"Hikmah Ki tashi mana" 

Badan Naso ba haka na Mike, Ina tafiya a hankali tamkar marar kuzari, ko ya manta muna class ne? Oho! Tunda na fito ya zuba min idanunshi Har seda na karaso gaban class din sannan ya sakko ,Se hayaniya ta Kaure a class din, ko a jikinshi bai musu magana ba, yazo kan wata slay queen Amratu yace ta tashi ta koma baya, ni na zauna a gurinta, Inata bata rai Haka na zauna........ Mafarin komai kenan! 

Tunda ya fara lectures bai Kara komawa ta kaina ba, Haka zalika Nima concentrating nayi sosae ina assimilating abubuwan da yake fada, time to time nakanyi jotting abubuwa masu muhimmanci, a Haka Har lokacinshi ya cika, yana rufe system dinshi Ina fara tattara komatsaina, ina gamawa wayata nayin Vib alamun text Ya shigo, dagowa nayi na dubi Abdallah shima kallona yake hannunsa rikeda wayarshi, nasan ba coincidence bane dama kallon yake, kaina na mayar kasa tareda bude text din 

_Eager to leave? Ki sameni a office idan na fita_ 

Da sauri na dago idanuna Wanda suke cikeda mamaki da kuma tambaya, amma sede wayam gaban class din babu kowa Wasu har sun Fara fita, Shiru nayi tareda sake kallon number da kuma text din da aka turon jiya da yau da safe, ban masan waye ba amma Ynxun da ita Abdallah yayi min text, me kenan? Shi ne ke kirana da farin cikinshi Ko kuwa? A hankali na Mike ganin yawancin mutanen class din sun fita, shoulder bag Dita na rataya a kafada sannan na fito, Na jima a tsaye a kofar class din ina tunanin naje kiran Ko kada naje? A karshe dai na juya na nufi office dinshi. Tunda na tsaya gaban office bugun zuciyata ya canja order na rasa me hakan yake nufi, me zuciyata take nufi Dani ne da dole se na haduwarsu da Abdallah sannan hakan ke faruwa. To Kodai banda lafiya ne? Zuciyata ta ayyana min. 

Ina nan tsaye ina shawarar shiga Ko Juyawa naji an bude kofar, a rikice na juya idona cikin na Mrs Hassanah, da mamaki ta kalleni yayinda Na sunkuyar da kaina Kamar marar gaskiya nace 

"Ma'am ina yini? " 

"Lafiya lau Zainab, kin dawo Ashe? " 

Ban iya magana ba se gyada mata Kai da nayi, kafin tayi magana Abdallah ya fito, fuskarshi fal Murmushi yace 

"Thank God Ummiey baki tafi ba, kinga ba se na sha wahalar yi miki bayani ba. " 

Jin abinda ya fada yasa na dago da sauri, itama cikin rashin fahimta ta dubeshi tace 

"Menene Abdallah? Zainab Ya akai" 

Ya sani, yasan matsawar na bude baki to tabbas bazai ji daidai ba shiyasa ya rigani fadin 

"Ummiey Zainab ita ce sirikar ki, aurenta nake Sonyi saboda Ina sonta" 

A matukar razane idanuna a warwaje na kalleshi, sannan a tsorace na Kalli Mrs Hassanah wadda banda Murmushi babu abinda take irin na farin ciki dinnan, Juyawa nayi cikin sauri Kamar zan hantsila na bar gurin, ina jinshi yana kwalla min kira amma ko waiwayowa banyi ba. Sauri nake sosae zuciyata Kamar zata balla kirjina saboda yadda take bugu, idanuna na runtse sannan na bude inajin yadda hawaye ya Fara min tsartuwa. 

Acan Ina barin gurin Abdallah ya biyo bayana amma Umminshi ta riko hannunshi, cikin wani yanayi yace 

"Ummiey bata sona kenan?" 

Ya fada hankalinshi a matukar tashe, hannunsa Ummiey ta rike sosae sannan ta maida shi office din ta samu guri itama ta zauna tace 

"So, da baka fada mata ba? " 

Kanshi Ya gyada yace 

"Yanzun nayi niyyar fada mata kuma kawai se naga tunda kina nan Bari ayi a gabanki" 

Murmushi tayi tace 

"Idan ta yarda da kai ta amince to albishir me karfi na farin ciki, Kayi saa kayi dace. Amma ya zakayi da Maganar Mupheeyda?" 

Kanshi Ya shafa fuskarshi tayi ja saboda tsabar Tashin hankalin da yake ciki, shi a duniyarshi ya manta da zancen wata Mupheeyda. Mikewa Ummiey tayi tace 

"Idan kayi tunani I'm readily available for you Son " 

Daga Haka ta fice ta barshi ya rasa abinda yake mishi dadi, Ya rasa inda zai saka ranshi. 

Ina zuwa daki na wullar da kayan hannuna na fada kan katifata Se kuka, bansan kukan me nakeyi ba, bansan dalilin kukana ba amma inajin wani bakon yanayi, wani yanayi Wanda bantaba jin irinshi ba. Nafi mintina ashirin a Haka sannan na mike Kamar wata yar Maye har layi nake nayi alwala nayi sallah sannan na koma na kwanta Inata expecting call dinsa Ko message dinsa amma har na gaji da jira na hakura. Da daddare restaurant din da muka hadu jiya na koma with the hope ko zaije amma nafi awanni uku babu ko alamar shi. Take kuwa na koma halinda nake ciki a da. 

Wasawasa abin Kamar a film kwatakwata Abdallah bai Kara nemana ba, bantaba jin tashin hankali irin wannan ba a rayuwata, Haka na zauna na cigaba da rayuwata tareda jin komai ya fita a Kaina, naji na tsani dukkan komai tareda kara Jinjina abin maza. 

Da daddare Ina zaune a daki wajen sati uku da faruwar abin, Ina kwance Sega message, cikin sauri na mike tunanina Abdallah ne amma Se naga Nana ce, message ne akan na sameta a dakinta. Rufe littafin nayi na tafi dakinta. Ina sallama naji sheshekar kukanta da sauri na karasa Ina fadin 

"Nana me ya faru? " 

Tana ta shesheka tace 

"Deeda ne Hikmah, Ya daina kirana, nayi mishi text baya responding, na Kira bai dauka ba baya kuma returning calls din" 

Wani kululun bakin ciki ne ya tokare min makoshina, mudai mata bamida wata matsala da ta wuce ta da namiji, kullum mu matsalarmu akan namiji ne. 

"Shine kika zauna kike kuka saboda kanin ubanki ya daina kulaki? Meye na damuwa Nanah." 

Tana kuka sosae tace 

"Hikmah bazaki gane yadda nake ji ba, ba zaki gane halinda zuciyata ke ciki ba, tamkar ana babbaka wuta Haka nakeji. Ina sonshi!" 

"Kuma dole Ki rabu dashi ba, tunda he's  not attached to iskar da kike Shaka. Zancen Bazan gane halinda nake ciki ba, Nanah da heart break na tashi a cikin zuciyata, a Yanzun da kike ganina, zuciyata is broken and is shattered into thousands of pieces. Amma dole Ki zama strong, rabuwa da Masoyi ba shi ne karshen rayuwa ba. " 

"Allah Nanah wallahi na daina soyayya, Bazan kara ba. Maza azzalumai ne, duk yadda nake son Deeda Haka ya rabu Dani." 

Shiru nayi kawai Dan bansan me zan kara cewa Nanah ba kuma. Seda tayi kukanta me isarta sannan ta hakura, Inata nuna mata yadda rayuwar take ciki wayata ta Fara ringing, dauka nayi ganin Baffa ne me kiran. Cikin fullanci muka gaisa sannan yace 

"Uwata waye Abdallah ne? Kin sanshi? " 

Shiru nayi Ina tunanin Abdallah kuma, jin nayi Shiru yasa yace 

"Wani lecturer dinku, shekaranjiya yazo da iyayenshi akan suna neman aurenki" 

"Aure kuma Baffa? " 

Na fada Ina zare idanu, Dan Murmushi yayi na Manya yace 

"To Meye a auren" 

Kaina na girgiza Kamar yana ganina nace 

"Babu komai amma nayi tunanin se na gama school sannan" 

Dariya yayi yace 

"Ba haka mukai dake ba Zainab, mun yarda akan da zarar miji yazo zanyi miki aure ko ba Haka ba? " 

Shiru nayi Dan nasan Haka mukai dashi, amma Har wani ma Abdallah zaije yayimin Haka, yabi ta sama. Kenan ba rabuwa yayi Dani ba. Se naji wani sanyi a raina, nifa Har mamakin hakan nake, gaba daya Ya shiga zuciyata da rayuwata Yayi min karan tsaye. 

"Tohm na bashi izinin neman aurenki, sannan na yaba dasu idan kin amince zan saka iyayenshi su zo ayi final magana. " 

Daga Haka Ko sallama bamuyi ba ya kashe. Bin wayar nayi da kallo Bance komai ba se tsabar mamakin komai dake faruwa nake. 

Na dade a tsaye a gurin tamkar an dasa ni, mamaki ne kwance akan fuskata na irin kokarin Abdallah, Ya daina nemana kenan ya zagaya yaje ya nemi aurena. Kaina na girgiza a raina Ina ayyana Dama tunda  hadu da Abdallah jikina ke bani akwai wani abu a tattare dashi game Dani. Ganin kafata ta sage yasa na janye jikina na koma gefen Nanah wadda har lokacin babu walwala a tare da ita. Dafata nayi nace 

"Nanah Karki manta abubuwan da na fada miki, wannan ba komai bane a soyayya, kada hakan yasa kiji kin karaya Ko Kin fasa, A'a soyayya Baa mata Haka, love is something that makes us complete beings, it destroys us and yet everyday we search for that. Kinga soyayya ita ce rayuwa, a person is not complete without it, so ki manta Deeda da qualms dinsa, a fara sabuwar Rayuwa. Inada muhimmin abu da zanyi Inshaaa Allah Anjima zan dawo." 

Banma jira abinda zata cemin ba nayi gaba, inajin ina haki saboda doguwar Maganar da nayi babu Hutu, Ina shiga daki na kwanta rub da ciki ina nazarin rayuwata da yadda alamuran suke zuwa, a raina kullum hoping nake zanji Wasu na cigiyar yarsu, Baka me gashi, me doguwar fuska, Idanunta Manya, bakinta matsakaici, hancinta dogo irin na fulanin Adamawa, kafarta ta hagu bata da kyau tana limping dinta Wato dingisawa. To amma har yau ko sau daya ban taba jin irin wannan cigiyar ba, kullum na kwanta na tashi hope dina zanga iyayena amma Shiru, though nasan Allah kadai ya shirya min rayuwata shi yasan me Zai faru gobe. 

Hawayena na share da suka Fara min zarya, tashi nayi na zauna tareda daukar wayata na Fara neman layin Hamma Aiman, bai dauka ba Kamar koda yaushe katsewa yayi ya dawo da call din, Ina dauka yace 

"Abdallah ya tafi Abdallah ya dawo, Iyeee kaga Amarya! " 

Bata rai nayi hade da turo bakina nace 

"Harda kai aka hada Baki kenan Ko?" 

Dariya yayi sosae yace 

"Sister kenan, ni na isa Yanzun Mamaa ke fada min Wai Mama ta kirata tana fada mata" 

Bance komai ba jin Har an Fara yamididi da Maganar, matsalar wide family kenan magana kadan zakaji ta bazu 

"OK tell me, Ya kamarshi take? Kina sonshi? Kodan ya kamata nayi fushi tunda ban kai matsayin da zaki fada min ba. " 

Ya karashe Maganar Kamar Wanda yaji haushi, duk se naji babu dadi a cikin raina se nake ga tamkar har Yanzun yana sona, naji Kamar na Faye son kaina da yawa da Naki saurarshi sede kullum ni ina Kai masa tawa damuwar ni ban taba sauraron tashi ba, balle naji Meye tashi damuwar. 

"Hamma Aiman, ka daina sona ne?" 

Murmushi yayi yace 

"AI ban taba cewa ina sonki ba dama, na dai ce zan aureki saboda Mamaa Tana sonki sosae. All this while ina jinki Kamar ni kadai ne Wanda kike juyewa damuwar ziciyarki. Kamar ni kadai ne Dan uwan daya damu da damuwarki, ina fatan banyi hurting dinki ba." 

Hawaye a hankali ya gangaro min Wanda koda wuka bansan na Meye ba, zuciyata tambaya ta tayi Dama Ina expecting yana sona ne ko kuwa? kaina na rausayar nace 

"If that's the case Nagode sosae Hamma, Allah Ya Kara zumunci " 

Daga Haka na kashe wayar tareda kwanciya ina sakin sabon kuka. Sede Gabaki daya ji nake kamar something is missing, Kamar akwai abinda yake ba daidai ba, zuciyata se tuhumata take akan dalilin kukana, Dan yace baya sona to da yace yana sona me zanyi kenan, I'm to love him back. Gaba daya se na dawo inajin haushin kaina. Ina nan har aka kwalla kiran Maghrib, Kaina zuwa wannan lokacin Har ciwo yake ga idona da yayi ja saboda kuka da halinda nake jefa zuciyata, Wanda ni akaran Kaina banga dalilin hakan ba, watakila bansan Zaman lafiya ne. 

Ina idar da sallah naji wata azabbabiyar Yunwa tana damuna, Allah Ya taimaka nayi girki Tun safe hakan yasa na janyo flask din na saka tuwo da miya na wanko hannuna naci, naci sosae kuwa sannan nasha ruwa na jira akai ishai sannan na Fara shirin bacci. Seda na gama shirina tsaf sannan wayata ta Fara ringing, hannuna na Kai zan dauka na fasa ganin Abdallah ne me kiran, dauke kaina nayi na cigaba karkade katifar ina kokarin daidaita kaina amma ina hakan bai samu saboda yaki daina kirana ni kuma nutsuwata taki tsayawa in cigaba da abinda nake, cikeda masifa na dauki wayar tareda fadin 

Story continues below


"Menene Kake damuna? " 

Tamkar baiji me nace ba yace 

"Ki fito ina kofar apartment dinku Ina jiranki" 

Bai Ko saurari ansa ta ba ya kashe wayar, bed sheets din na saki mamaki fal raina Ina ganin gadara, iko da kuma isa a gurinshi. Duk yadda naso kada na fita amma sam zuciyata taki bani Hadin Kai, Haka na dauki dogon hijab na fita, can gefe na sameshi shi daya yana ta faman danne danne a wayarshi Ya jingina da motarshi, yana sanye cikin kananan kaya Jeans coffee banga top din dake ciki ba saboda sweater dake saman kayan sede collar top dinshi ta samu damar lekowa ta wuyan, Yayi kyau Dama shidin me kyau ne, inda yake na isa tareda tsayawa a gefenshi ina wasa da yatsuna raina a hade nace 

"Ina yini? " 

Dagowa yayi tareda tsura min idanun nashi masu sakani in duburburce, saurin kasa nayi da kaina, Ina kara tamke fuska. Murmushi yayi yace 

"Bakiyi kyau da shan kunu ba, gwara Ki saki fuskarki ko a samu kiyi kyau. " 

Bakina na zunbura nace 

"Aini dama me kyau ce tuntuni, bana bukatar na saki fuska ko nayi dariya sannan aga kyauna. " 

Ganin yadda nake bace bacen rai da kuma abinda na fada yasashi dariya wadda kular Dani kawai take, a ganina ya raina min hankali ne zai sani gaba yana dariya, gyara zamanshi Yayi tareda aje wayarshi akan bomber motar yace 

"Da gaske? Kinga ban taba ganin kyan kiba hasalima nasan nafiki kyau" 

Da sauri na dago idanuna Ina kallonshi, wata harara na wurga mishi nace 

"Shiyasa Naga mutum ya dage dole seni, yana tsoron kar ya rasani ya tafi ta sama, yana ganin bai kai Yayi confronting dina ba" 

Ina rufe baki naga ya bude nashi cikeda mamaki yace 

"Dama kina magana Har Haka? Wayace miki Tsoro naji? Kawai nabi abinda musulinci yace ne, banda abinki namiji Kamar ni ta Yaya zaiji tsoron mace. " 

Dariya nayi jin yana kokarin kare kanshi yace 

"Duk ba wannan ba Hikmah, Kinada kyau sede gaskiya bashi yaja hankalina Kanki ba, I can't say ga abinda ya birgeni game dake kawai zuciyata na fada min kada na Bari ki tafi, ke din kika birgeni not looks ko wani abu, gaba dayanki nake so. Ummiey tace min inhar na aureki na gama saa, na aza ta fada ne saboda Kece best student dinta amma da naje gurin Baffanki naji babu wata yarinya data cancanci na aureta seke. Farin cikina Baffa yana sonki, ya yabeki to the core da har seda na Fara jin anya I'm I worthy enough na aureki? Inasonki Farin cikina" 

Lumshe idanuna nayi a hankali inajin wata nutsuwa tana saukar min a dukkan jikina, wani abu ne ke fuzgar zuciyata, inajin Tana budewa wani sonshi yana shiga Ko ina. 

"Farin cikina" 

Ya fada yana kallon yanayin da nake ciki, dagowa nayi nace 

"Baffa yace maka basu suka haifeni ba? Ba sune iyayena ba? " 

Idanunsa a warwaje yace 

"How comes kika sani? Waye ya fada miki? " 

Wani faint smile nayi nace 

"Duniya da fadi, all my life sir ban taba kawowa cewar iyayena basu Baffa bane, bana tunanin ko iyayena zasui min wannan rikon da sukai min, basu taba bani wani gap da zai nuna min cewar basu suka haifeni ba amma dukda haka a gidan seda aka fada min matsayina aka cemin basu suka haifeni ba.... " 

Se kuka ya kwace min, ni daya nasan ciwon da nake ji duk lokacinda na tuna hakan, na tuna rayuwata amma Haka Allah ya tsara, bai hanani seda nayi Dan isata amma jikinshi duk Yayi sanyi 

"...Ina jin tsoron kada ya zamana I was born illegitimate.... " 

"Don't, don't ever Farin cikina, Ki kyautata zato. Tunda Baffa ya sanar damu Jikina ke bani tabbas kaddara ta rabaku, komai na ranar da suka tsince Ki seda ya nuna mana which shows ke din yar gata ce. Inshaaa Allah I'll be the reason da zakiga iyayenki. bana son ki Kara kuka, ki fawallawa Allah komai yana sane dake. " 

Se naji dadi naji nutsuwa ta saukar min, shi ne mutum na biyu bayan Hamma Aiman da yasan yadda Zaiyi lecturing dina, ranar Har kusan Karfe goma muna tare dashi, kafin ya tafi seda ya sauke duk Wasu hadda dake Kaina seda ya barar da ita completely, Ya daura min sabon karatunshi Wanda ya tsaya min a raina, seda naji idan babu shi to Se rijiya..... Lol

Post a Comment for "HIKIMA CHAPTER 7"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...