HIKIMA CHAPTER 6 - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

HIKIMA CHAPTER 6

HIKIMA CHAPTER 6

- - Post a Comment
HIKIMA

CHAPTER 6

Fitowata kenan a wanka sakon kiran Hamma Aiman Ya iso min. Seda na saka kaya sannan na fito na sameshi a kofar gida, yana zaune akan motarshi, hannunsa rikeda car key yana karkadawa da dukkan alamu jirana yake. Da murmushi saman fuskata na isa gurinshi, cikin nutsuwa nace +

"Hamma morning!"

Murmushin ya mayar min yace

"Morning Dear, Kinyi bacci kuwa? "

Idanuna na shafa saboda sun Dan tashi, so Mama ma seda ta tambayi if I'm ok? Nace kawai gajiya ce,

"Ka manta jiya nayi kuka shiyasa. "

Kanshi Ya gyada sannan yace

"Anjima by 10pm flight dinmu zai tashi."

Idanuna na dan ware, naji bana son ya tafi, he's a nice guy amma ya zanyi? sannan nace

"Da wurwuri Haka? Inace se karshen month?"

Kanshi Ya girgiza yace

"Gaba daya hutun sati biyu aka bani a gurin aiki, har na cinye daya anan, kinga idan naje na huta da Sauran remaining one week din Ko?"

Kaina na gyada, cikeda yadda da abinda yace nace

"Allah Ya kiyaye hanya. Se yaushe kuma?"

Langwabar da kanshi Yayi, yana Murmushi Wanda tamkar Anyi plastering dinshi a fuskarshi ne permanently, kullum yana cikin Murmushi, hardly kaga babu wannan murmushin, shiyasa kullum yana cikin kyau, kuma mutane na sonshi sosae.

"Se Nazo bikinki kuma. "

Dariya nayi Ina rufe fuskata alamar naji kunya, dariya yayi yace

"Ni tuntuni na hakura ai, shiyasa nake son ki daina jin kunyata, kawai ki daukeni matsayin Yayanki, consult me when in need. Naso kin yarda kin aureni, I'll change your life amma Banji haushi ba."

Se naji babu dadi amma ya zanyi, Hakan yasa nayi kasa da kai ina fidgeting da fingers dina,

"Don't be nervous my Dear, Munyi Maganar school dinki da Baffa yace zakije SBRS jibi kiyi Pre test."

Dagowa nayi nace

"Ina ne SBRS kuma? "

"Kifin rijiya, doesn't know any where Se Kano. A Funtua take, katsina state. Ana yin remedial da IJMB program. "

Kaina na gyada nace

"To me zanyi ni? "

"IJMB zakiyi, akwai iya point din da zaki samu a final exams dinki, se kije level 2 a university da kike so. "

Wani shauki ne ya kamani nace

"I'm happy. Inshaaa Allah I'll make it"

Cikeda jin dadi yace

"That's good of you my Dear! Jiya kince duk maza kina daukarsu as betrayers. Tell me abinda yasa kaikayi wannan jam'in"

Tsayuwata na gyara na bashi labarin dukkan abinda ya faru tsakanina da Abdallah, bai katseni ba Har na gama sannan yace

"Abdallah bai kyauta ba, Banji dadi ba da soyayyar ki ta farko a Haka Tazo. Amma baki ganin abinda kikai stereotype ne? Kin hada maza duka Kinyi musu jam'u? Saboda mutum daya gaba daya kin mana kudin goro. Gaskiya this is not fair. Kuma lemme tell you soyayya daya, betrayal daya tayi kadan ace kin hakura. You need to try harder amma baki hakura ba. They are many good guys out there, I guess you will fall for one, one day "

STORY CONTINUES BELOW

Sosae nake kallonshi ina kokarin placing kowacce magana tashi a mizani, its takes wisdom to say what he said.

"Love is a universal solution to all human problems. It heal wounds, mends broken heart, unite enemies and encourages growth. Love is what we need everywhere and everyday."

"Bakida wani right da zaki ce bazaki kara soyayya ba, akwai mutanen da they are heart broken for uncountable times amma they still and are searching for love. Karki gaji Hikmah, Bakiyi komai ba. "

Da wannan maganganun nashi mukai sallama, ban kara ganinshi ba Har suka tafi, sede ya barmin sako wajen Nihila kanwar Abba Mr perfect ce, Ko daya Banji sonshi a raina ba, bayan Wanda muke yiwa juna na Yan Uwa ba, amma sosae naji wani Kwarin gwiwa yazo min. Wannan words din nasa Sunyi capturing zuciyata Har seda nayi jotting dinsu

_~Love is a universal solution to all human problems. It heal wounds, mends broken heart, unite enemies and encourages growth. Love is what we need everywhere and everyday."
_~

Sosae naji kewarshi, ga gidan Yayi Shiru, kowa ya tashi. Hakanan Wasu lokutan Se Inji Dama na yadda da aureshi da tuni ina London may be a Cambridge University, Oxford University Ko kuma University of central Lancashire. Haka dai. 1

Ranar Tuesday muka tafi Funtua da yamma ni da Hamma Musbahu, akan zan kwana, Washegari exams bayan nayi se mu dawo. Tun a hanya naji bana son garin, hanyar batada kyau dake ta gwarzo road muka tafi, ga nisa, lokacin Ko Abinci ban ci ba se a hanya Hamma ya siya min Nama da juice. Bamu isa Garin ba se daf da Maghrib, a gajiye nake tikis, Haka muka nemi makarantar, dukda dare ne, Babu Wanda na sani haka aka hadani da wata Raziqa Tana IJMB2 itace vice president na Association din plateau State students. Ta kaini dakinsu, ta bani Abinci Ko hutawa ban gama yi ba, muka tafi Assembly hall inda ake tutorials. Haka se 10pm na dawo a gajiye nayi bacci. Da asuba ta bani ruwa nayi wanka sannan na tafi venue. Sede Computer based test ne Dan Haka baazo kan hall dinmu ba se 3pm. Ga Yunwa, ga gajiya, Ya zamana da kyar nake karanta questions din, combination dina physics, chemistry, biology se maths and English. Babu laifi na danyi abin kirki amma Wasu kawai clicking nake. Nayi submitting na fice gate, anan aka karba phone number ta akan zaayi communicating damu idan Anyi releasing admission list.

Tunda muka koma gida Baffa ke shiri, ni kam ko tunanin school dinma ba nayi tsabar yadda na tsaneta amma da yake Allah Ya tsara rayuwar kowanne bawa, ana releasing list harda sunana a Wanda suka samu admission. Se kuma nayi murna at least dai da Sauran kokarina. A Satin mukaje mukai registration, Har accommodation komai ya kammalla sannan na dawo.

Bayan kwanaki goma na tattara aka kaini Funtua, ni ce harda kukana saboda tsabar shagwaba. Nayi ta kuka tunda shi ne first time dina na barin gida, ban taba zuwa bulaguro babu Mama ba, ko ina muna tare amma Zaa kaini inda babu Wanda na sani Ya sanni.

Hamma Mussadiq da Anty Fadila, Hamma Mustapha da Najaatu su suka raka ni. Matan Har hostel suka kaini. Wammako hostel, Room one, bed eight. Bazan taba Mantawa ba. Dakunan ba wasu Manya bane, 8 beds ne kuma bunk, so nawa Ya tashi a sama kenan, se lockers kowacce Anyi numbering 1 to 8, 4 by each side. . Ni na Fara reporting a dakin, seda suka shirya min provisions dina Dan makarantar Baa girki, sede ka siya, Baa fita se kaje students affairs Sunyi clearing dinka shima with concrete reason. Suka kammalla sannan sukai min sallama. Anan dai na daure banyi kuka ba. Gadona dana shimfida sabon bed sheets na hau nayi Shiru Inata sakawa da kuncewa, tareda tunanin abinda Hali Zaiyi sannan wacce rayuwa zanyi anan? Ko suwaye roommates dina? Allah kadai ya sani. Ina nan se aka turo kofar, wata doguwa bahaushiya zata girmeni amma baifi watanni uku ba, ta shigo da sallama bakinta, amsa mata nayi muka gaisa, Ina a saman Har ta gyara kayanta sannan tace min 3

"Sunana A'isha I'm from Kano state and you? "

Murmushi na saki nace

"Zainab from plateau state, residing in Kano. Nice to meet you "

Hannunta ta mikon mukai musabaha, daga nan hirar Kano ta shigo, muna nan Sega Firdausi Tazo, Tana jin Hausa amma bata mayarwa, she's from Nasarawa state, can Sega khadija yar Bauchi state amma a Abuja suke. Sauran ukun Christians ne. Dayar batai reporting ba. Da daddare tare mukaje massallaci mukai sallah, mukaje wani gurin Abinci, matar me kirki mukaci rice jollof da cabbage. Daga nan muka koma hostel muka danyi hira sannan mukai bacci.

Washegari was Sunday. Gaba daya muka fita zagaya school, anan Naga class mate Dita da mukai secondary Sa'ada yar Jigawa ce ita kuma amma ita hostel dinta block C ne. Muka raka ta tayi settling sannan muka dawo.

Washegari Monday, Monday tushen aiki, formula Uwar lissafi. Wannan ranar ita ce ranar farko a higher institution, 7 Zaa Fara lectures amma 6:50am muna kofar lecture hall, Ya cika saboda Baa bude ba, gefe muka ja muka tsaya seda aka bude tuni masu harama sun Kame gaba, muna karshen baya muna baza ido. Lecture farko General physics, 7 to 9. Awa biyu Ya fita lokacin Yunwa ta Fara damuna amma kafin wani abu me general chemistry Ya shigo zuwa 11am ya fita. Daga nan se na Fara lumshe ido tsabar Yunwa, Karku manta Dani a wajen ci expert ce ni gurin cin Abinci, I'm a foodie, I love food. Yana fita me organics Ya shigo. Se 1pm Ya fita. Kowa a gajiye muka fito, massallaci mukaje saboda 1 hour interval da muke dashi. Muna fitowa mukaje siyan Abinci ya Kare saboda Yan Rems sun rigamu fitowa amma an daura wani, wayata na kalla naga babu time da zai isa mu jira a gama, mukaje cafeteria shima hakance, ai se na Fara kuka, na tuna Mama, Duka su hudun suka zagayeni suna bani baki Amma ko jinsu ba nayi. Khadija da muke kira kashmy tace

"To muje musha juice, Nazo da cake"

Wannan idea mukai using ya Fidda mu, ranar lecture har 6pm sannan muka gama. Washegari Tuesday shi ne abin yazo da sauki dan lecture uku ne kuma akwai intervals sosae, munji dadi a ranar, ranar Amina tayi reporting ita kuma yar Niger state ce amma a Lagos suke. Daga nan muka zama mu shida. Duk inda kaga daya to tabbas zakaga Sauran, sede nida Firdausi munfi kusanci, saboda mune kanana, Amina da A'isha Se Mama Sa'ada da kashmy. Haka mukai rayuwa a wannan makarantar.
Duk yadda mutum yake daukar Kansa idan yaje SBRS to abin ya wuce nan, idan takamar ka turanci zaka sha mamakin jin American and British accent, idan takamar ka kai guru ne SBRS will turn you to gugguru... Lol... Koda me kazo an fika. Munyi Karatu sosae, Karatu me cikeda kalubale Wanda a times Se Inji tamkar na tattara kayana na gudu gida amma idan na tuna abubuwan dake gabana Se na fasa. 2

Ranar Friday mun dawo daga lectures din Waves and Vibration, dake jumaa ce babbar Rana, gaba daya Munyi kyau kowaccen mu taci Atamfa. Ammashiekh ta dubi agogon hannunta tace 1

"Yanzun Zaa Fara huduba, muje massallaci."

Tare duka mukaje mukai sallah, da aka idar mukaje can wajen hostel din maza mukai order Abinci, at least munason mu taba kowanne Abinci na kowanne joint. Seda akai mana packaging muka taho dashi daki mukaci.

Da daddare ni daya na fita, dukkansu suna daki, naje meeting din state, ina dawowa bansan tsautsayi da ya biyo Dani ta C15 ba, na biyo nayi mummunan gani kuwa. Ina dawowa daki na zauna jagwab gadon Ameeyna Ina fadim

"Ku kunsan ta Ina na wuce? "

Firdausi tace

"Ina?"

Nace

"Uhmmmm kiss me sharp sharp! "

Duka suka kwashe da dariya suna fadin

"Su Hikmah Anyi Babban gani, me kika gani? "

Duka na kaiwa kashmy na danyi Tsaki nace

"Allah bansan me mutane ke daukan soyayya ba, wannan ai rubbish ne"

"Sosae ma,"

Mama Sa'ada ta bani amsa, hakan yasa Ammashiekh tace

"Talking about soyayya na tuna me zance. Hikmah Wai ya kuke da Hamma Aiman dinnan, kullum brag dinki bakida saurayi, shi me kukeyi?"

Dan dariya nayi, inason Ammashiekh with that her Sisterly advice nace

"Wallahi babu komai fa."

Amina tayi carat tace

"Kinji ki ko? Malama kowa anan yana da saurayi, meke damunki ne? "

Shiru nayi Ina jin wani iri ,nace

"Only God knows what? Ni Kaina bansan abinda ke faruwa ba, amma one thing for sure is The perfect timing is knew by Allah, if it comes no hesitation no delay. "

Wannan abinda na fada yasa duka sukai Shiru, muka koma hirar latest songs na Maheer zain, dama kashmy ke mana downloading. Ana gama ji muka hada choco pops da madara cikin katon bowl muka sha sannan aka shiga IG na ganin post din Fatigbolady. Muna sonta sosae dukkanmu muke following dinta.

Haka rayuwar mu take kullum daga lectures, Abinci, sallah se hira Se ayi Karatu. Bama zuwa tutorials ni Kaina bansan dalili ba. Ranar muka zauna dukkanmu mukai discussing gaps dinmu Dan an fara test, chemistry practical kuma performance wasn't encouraging. Daga wannan ranar muka dage yau muje tutorial din wannan state din, gobe muje na wancan. A hankali muna picking abubuwa. Da weekends zamuje cafeteria muyi Karatu sannan a koma normal life.

Duk cikinsu kowacce Nada saurayi banda ni kadai, Ammashiekh the love birds kenan, after mintina biyar biyar suke waya itada Munnir, I can swear ban taba ganin soyayya irin tasu ba, they're addicted to each other Kamar me. Amina nata handsome take kiranshi, wannan shi ke tashinmu Sallar asuba, amma akwai side chicks da take dasu. Firdausi kuma wani Khalid ne saurayinta kullum se dare zasu fara waya only God knows when Zaa gama. Mama Sa'ada kawu ne nata though tace he's just a cousin amma kallonta kawai muke. Hajiya kashmy kam Usman ne, Jordan muke kiranshi dashi saboda can yake Karatu. Nikam ni daya ce banda saurayi, idan suna waya sede nayi tsuru Ina kallonsu, a wannan lokacin na Fara jin, I need love, no matter yadda soyayya ta gwaraka Bakada right na cewar bazaka kara ba, I believe love is the spicy of life nasan many will believe me. Soyayya ita ce abarda take wahalar damu and yet kullum ita muke nema, that's love. No one can do without it.

STORY CONTINUES BELOW

Munyi first semester exams dinmu daidai lokacin sallah Babba. Mukaje Hutu nasan nayi missing gida, dukda every month wani daga gida Se yazo ganina amma yadda kowa ke nan nan Dani abin gwanin dadi. Babu wani abu Sabo banda haihuwar Anty Fadila, yeah ta haifi Danta namiji Muhammad, yaron Kamar babanshi. Wannan haihuwa yasa Hammana Ya koma hankalinshi, Ya fara kokarin daidaita gidanshi. Najaatu da Aneeysa ta dukkansu suna da ciki wannan karan Har matar Hamma Musbahu. Ranar da zan tafi Kamar kada na dawo amma Haka dai ba yadda zanyi na koma, lokacin aka fitar damu daga Wammako hostel muka koma UZD (Umma Zaria Dantata). The life there was awesome also, sede kashmy da Mama Sa'ada basu Dakinmu, basu dawo ba se new faces guda hudu, khadija makarfi, Mameh, Fatima Nuruddeen da Hamida. Basuda matsala hakan yasa muka kara yawa. Lokacin mun zama Yan IJMB2, mun shigo second semester. Tsabar Karatu wani lokacin Har dodging wanka muke. Muna ta rayuwa me cikeda jin dadi, saboda idan ana zancen kawaye bantaba kawayen da nake so irin na SBRS ba, they were more of blood sisters than friends.

Mun Fara final exams dinmu a February, Munyi Karatu babu karya, addua wannan constant ce. A Haka muka kammalla muna fatan mu samu nasara. Ana gobe zamu tafi mukai kwalliya sosae, mukai pictures, mukaje shop din Mama jabiri mukaci jollof, mukaje muka sha lemu wajen Naira, mukaje shop 1 mukai siyayya, muka karasa Nagoya supermarket Muaki shopping sosae. Washegari ranar rabuwa, munsha kuka Kamar me, Nikam harda attack na samu saboda kuka. A Haka fiskoki a kumbure muka rabu cikeda kewar juna.

Ina zuwa gida Mama ta tare ni da duk Wasu abinda tasan ina so, ranar naci Abinci Har seda naji tsoron kar cikina ya fashe. Bacci kam nayi shi, seda nayi kwana biyar bana sana'ar komai daga na ci Se nayi bacci. Bayan sati daya muka tafi auren Abba Mr perfect a Barikin ladi. Anyi biki lafiya da amaryarsa Munnira yar Lafia ce.

Bayan mun dawo Mama ta Nemo min catering school nayi joining saboda result dinmu Zaiyi taking time kafin ya fito. Nayi registering snacks, catering da cakes. Watanni biyu na dauka Inayi, dake Inada naci, duk abinda na koya Ina dawowa gida zakiga na gyada na turawa Malamar, ita kuma tayi grading dina. A Haka na kammalla Baffa ya siya min kayan aiki, na Fara da yiwa cousins, nieces da nephews birthday cake da kawayena, a hankali hannuna Ya fara fadawa.

August results dinmu ya fito, ranar nayi zawo Kamar sau biyar saboda kidima Alhamdulillah we made it 9 points na samu, Kamar na tashi sama da murna, Sauran friends din nawa suma sunci. Sede kowacce university daban ta cike, daga ni se Amina muka cika ABU Zaria. Cikin saa da addua na samu level two a physiology department, ita kuma Amina microbiology Dama shi ta cika. Nan da nan a gida aka Fara shirin tafiyata .

Aiman my best friend kenan, inda akwai abinda yafi wannan sunan zan iya kiranshi dashi. Shi ne Mutumin da a maza bayan Baffa ya tsaya tsayin daka akan rayuwata, kowanne move dina ya sanshi, ni Kaina bana boye mishi komai ko wani abu ne ya taso Se na fada mishi komai, shiyake bani shawara akan komai nawa. Bana Mantawa ranar yake cemin

"Waini Har Yanzun babu wani motsi ne? "

Dan dariya nayi nace

"Wanne iri kenan? "

Shima martanin dariyar ya mayar min yace

"New catch mana, Ko Har Yanzun you still living in the past?"

Ya tambaya yana Murmushi me sauti, turo baki nayi nace

"Kai Hamma, Babu wani latest fa. "

"A'a Hikmah, I guess korarsu kike, Ko kuma baki basu fuska, nasan yadda kike kullum cikin fushi dinnan, may be shiyasa suke jin tsoron approaching dinki"

Dariya nayi sosae wai Tsoro, nace

"Ko kadan Hamma, Kasan dai yadda kafata take, ba kowa ke son ya auri gurguwa ba! "

It pains me idan na tuna hakan amma na yadda Allah kadai yasan dalilin hakan kuma na gani.

"kar na kuma jin kin fadi hakan Ko da wasa kinaji? Kin Kalli fuskarki kinga yadda kike da kyau? Kin kalla body structure dinki? Kinfi kowa sanin yadda zuciyarki take. To wannan kadai ya isa ki godewa Allah. Shi Dan Adam Tara yake bai cika goma ba. So bansan haka. "

Kaina na gyada tamkar yana kallona nacr

"Tohm Hamma Inshaaa Allah. "

Murmushi yayi yace

"That's my sister. Ya zancen school din? Komai ya kammalla?"

Cikeda dauki nace

"Yeah! Two weeks kadai ya rage na tafi"

"Tohm, Yanzun Kinsan ba SBRS zakije ba, ba kuma Musa Iliyasu kike ba. University wata rayuwa ce me zaman kanta, duk yadda zan miki bayani, you will not understand Hikmah. Se Kinje kin gani sannan zakiyi testifying. Ki kula da mutucinki, ki sani duk abinda kikayi is a reflect of your home, duk kuma abinda kikai Kanki kika yiwa ba Mama ba balle Baffa. Kiyi abinda ya kaiki amma ki gujewa bad company, na yadda da friends dinki na SBRS amma babu yadda zaayi tunda bazasu koma can ba, Dan Allah Hikmah ba Danni ba, saboda Kanki ki rike Kanki. Kinji Ukhty? "

Talks dinnan nashi kept me going to where I'm today. Allah Sarki Hamma Aiman, he's the best. Haka nan mukai ta rayuwa har lokacin naje nayi registration, accommodation and everything, baifi kwanaki uku na tafi ba.

Prayers please


Inason labarina ya gangaro lokacinda na Fara zuwa ABU, Lokacinda na Fara rayuwa a ABU saboda nayi tsintuwa, babbar tsintuwa wadda Bazan taba Mantawa da ita ba. Rayuwar gaba daya understanding shi ne komai, na yadda Allah yana bude maka wata kofar bayan Ya rufe wata, amma bamu realising hakan har Se gaba. Ko ni ban fahimci inda rayuwata take nufa ba seda na hadu da ABDALLAH, nasan zakuce Abdallah again? Yes Abdallah again. +

Amina hostel shi ne hostel dina a ABU, Kamar yadda nace muku direct entry na samu to level 2, ban wani sha wahala ba, saboda I believe duk Wanda Yayi SBRS to bana tunanin akwai school din da zaije yaji wahala kuma. Ko a karatu ko a copping stuffs na environment da yanayin lectures. Shiyasa ko kadan banyi wahala ba. Lecture sosae Ya kankama, babu laifi na dan Fara Sabo da mutane, musamman roommates dina, dukda kowacce course dinta daban amma idan muna tare irin da daddare Zaa zauna ayi hira kowacce akan gadonta, muna muntata juna saboda kowa yasan limit dinsa, ba Wanda ke crossing boundaries dinshi.

Ranar alhamis lokacin Munyi watanni biyu a second semester Dan tuni na share first semester, kuma ni nayi highest points a class dinmu, so yawancin duk an sassani hakanan.

Komai ya zama very deep, ana ta test ga exams ta kusa. Ni daya na taho daga hostel, Ina sanye da Abaya Off White se na dauki wani karamin veil peach na rufe kaina dashi. Daidai kofar dakinsu Nanah na tsaya tareda lekawa nace

"Nanah zamu makara fa! "

Da sauri ta janyo veil dinta ta fito, hannunta jotter ce Se handout Ko hand bag bata dakko ba. Tare muka jera muna tafe muna hira yawanci duk akan exams ne. Nanah Habib sunanta, gaba dayanmu Human physiology muke karantawa, asalinta yar Maiduguri ce, sede Ita Tundaga level 1 ta Fara, fresher ce Ko nace jambite ce. Muna shiri da ita sosae a class, shiyasa muka kulla kawance abinmu. Se Amjad shikuma Dan bauchi ne, tare muke dashi, he's a good friend also.

Muna zuwa class muka zauna inda muka saba zama, mu ba a karshen class ba, ba kuma a farko ba, a middle na ajin, anan muke zama abinmu. Cardiovascular physiology muke dashi, lecturer mace ce Mrs. Hassanah Uba. matar bata fashi bata latti amma Yau kam abin mamaki Har to Nine bata zo ba, kasancewar exams ta kusa, babu Wanda ya damu duk se muke dudduba handouts dinmu, masu discussion nayi, a Haka Har Karfe Tara daidai naji class din yayi Shiru, tsit babu ko motsin kirki, hakan yasa na dago da sauri dan ganin waye ya shigo, OMG! Oh Allah! Tsarki Ya tabbata ga Allah makagin abinda nake gani a gabana, shi ne abinda ya Fara zuwa raina.

Namiji ne me suna namiji, ba muna mata ba, Bashida haske amma skin dinshi bai cika duhu ba, yafi kama da caramel color, fuskarshi round face ce, wadda Allah Ya halitta mata komai daidai da ita, komai fits a inda yake, babu abinda zaka kalla kace da Haka yake da yafi! No everything is just perfect as it is. Yanada average height kuma jikinshi daga yadda yake a tsaye irin kamammen jikinnan ne. Dukkanmu yawancin mu da muke class din kallonshi muke, baga mata ba baga maza ba.

Seda ya gyara tsayuwarshi, ya daidaita system dinshi da tuni ya fito da ita daga cikin back pack dinshi, eyeglasses ya sanya sannan ya ciro chilled Faro daga Jakar ya daddaka, wajen rabi sannan Yayi recapping bottle din, ya aje a gefe.

Anan ya dago idanunshi Yana bin class din da kallo cikin wani unreadable expression na wajen mintina biyar, se kuma ya saki Murmushi Wanda yasa cleft dinsa lotsawa, naga hakan saboda tsira mishi idanu da nayi ne. Can yace cikin murya wadda turanci Ya mamaye ta

"I'm Abdallah Ahmad Abdallah...... "

Banma karasa jin abinda ya fada ba, kawai na saki Tsaki, Ashe class din duk Sunyi Shiru, kuma kowa ya jiyo yana kallona. Ganin Haka na bata rai amma Se naji shima Yayi Shiru bai karasa abinda yake fada ba, se ma sakkowa da yayi ya nufo inda nake, dauke kaina nayi inajin yadda zuciyata ke wani irin bugawa saboda ban taba kawowa yaji tsakin da nayi ba, yadda takun kafarshi ke isowa kunnena, haka zuciyata ke tsananta bugawar da take.

STORY CONTINUES BELOW

Yana isowa seat dinmu ya buga desk din, hakan yasa papers din da Nanah da Amjad suka baza tarwatsewa, dukda hakan ban dago ba seda yace

"Get out of my class stupid and useless girl!"

"Stupid and useless girl"

kwakwalwata ta maimaita min, na tsani a kirani da stupid balle har yakai ga useless, ina ganin karshen cimin mutunci kenan na Har abada, mikewa nayi tareda daukar handset dina na fita, yana bayana har na isa kofar Se ji nayi yace

"Heys, Meye sunanki?"

A hankali na juyo na kalleahi, fuskarshi a murtuke tamkar bai taba dariya ba, tamkar bashi yayi Murmushi nan Dazu ba, cikin sanyin murya nace

"Zainab Muhammad"

Rubutawa yayi sannan yace

"Ki sameni after class, and please walk out"

Ya fada yana nuna min kofa, naji haushi, iya haushi. Ban taba jin bacin rai irin Wanda naji Yau ba, fuskata Kamar wuta tayi zafi dau, kawai se nace mishi

"Wannan ne Baka isa ba! "

Ina fadar Haka Ko juyowa banyi ba nasa Kai nayi ficewata, ban nufi daki ba kawai na tafi Sculpture Garden, ina zuwa na tafi can karshen gurin na zauna. Idanuna Sunyi wani irin ja saboda tsabar bacin rai da nake ciki. Can na fito da wayata jin tana ta ringing, sunan Nanah ne ke yawo a kai hakan yasa na dauka, ko sallama Batayi min ba tace

"Kina ina ne?"

"Sculpture garden"

Na bata amsa, bata ce komai ba kawai ta kashe wayar, wajen after 30mins lokacin rage din dake burning cikin zuciyata ya ragu sosae, amma still wannan zagin da yayi min yana nan yana yawo a Kaina.

Nanah da Amjad ne su biyun, hannayensu dauke da handouts dinmu, kujera kowannensu yaja ya zauna. Amjad ne ya Fara fadin

"Hikmah ya akai Haka? Me ya faru? "

Kafin nayi magana Nanah tayi saurin fadin

"Ba wannan time din Amjad, Hikmah kawai ki tashi muje Ki bashi hakuri, magana ta wuce"

Wani mugun kallo nayi mata nace

"Wallahi bai isa ba, babu inda Zanje."

Kai Amjad Ya girgiza, yayinda Nanah ta bude baki bude cikeda mamaki, Amjad yace

"Kinsan kiyi laifi amma ko? Ya kamata ki bada hakuri. "

Kai na girgiza nace

"Ai ya rama tunda nima yamin zagin tas, tunda nake waye ya taba min cin mutuncin da yayi min. Kunsan Allah babu inda Zanje, yayi duk abinda zaiyi"

Wannan karan Amjad kasa magana yayi, basu San taurin Kaina ba se yau na Fara gwada musu, Nanah ce tace

"Hikmah forget about cin mutunci and stuffs, karatun ki nake jiwa, exams fa is past approaching, kuma Abdallah nan da kike gani yaron VC ne ....."

"What about yaron VC? Ba abinda ya dameni, Kunga test din endocrine physiology Karfe hudu"

Na fada Ina nuna musu broadcast din da class rep yayi, basu kara cemin komai ba suka bude handouts din, daidai Pituitary gland, Nanah ke karantawa ni ke musu bayani, Amjad na throwing questions. A Haka Har hudun tayi dukda muna tashi sallah, anan muka ci Abinci.

Muna zuwa akai test din, tamkar inyi rawa Haka naji da naga questions din, very cheap. Haka na tsarge ta Ko sau daya Murmushi bai bar fuskata ba, in fact Se ya mantar Dani abinda wannan matsiyacin yayi min. A tare akai submitting, yana sallamar mu na Mike nida Nanah, amma ina fitowa kofar lecture hall din muka hadu da class rep, dauke kaina nayi zan wuce, yasha gabana yana fadin

"Zainab nemanki nake fa"

Tsayawa nayi na kalleshi ina fadin

"To na tsaya"

Kanshi Ya girgiza cikeda mamaki na, saboda yadda naje musu tabbas bazasu kawo Haka nake da taurin Kai ba, tafiya ya farayi hakan yasa nabi bayanshi, seda muka Dan gota hall din sannan ya tsaya yana fadin

"Zainab muje office ki bawa Sir Abdallah hakuri."

Kauna na dafe nace

"Class rep Dan Allah ku bar wannan Maganar Danni a gurina ta rigada ta wuce."

Kanshi Ya girgiza yace

"Bata wuce ba my dear, naje office dazun na sameshi, Ya cemin kina samunshi magana ta wuce idan ba Haka ba, bazakiyi test ba, ba kuma zakiyi exams ba."

Gabana Se Da ya fadi amma na dake nace

"Damuwarshi ce wallahi"

Duk yadda yaso na yadda ki nai, hakan yasa yayi tafiyarshi shima Yayi fushi. Hostel na koma na kara gyara gadona, da komai sannan na hau na kwanta Ina shan wani chilled Malt da na siyo a hanya. Dukda alamu raina nasan ban kyauta ba, especially da nace bai isa ba, tunda rashin kunya ba halina bane amma ya na iya? Ya kaini karshe ne.
Bayan sati daya +

Wayata dake karkashin pillow na janyo jin ringing dinta, bacin rai kwance a fuskata saboda kwanciyata kenan, Tun asuba da nayi sallah nake Karatu. Se Tara nayi wanka na dafa noodles da tea sannan na kwanta, amma Har an Fara katseni. Sunan Nanah ke ta yawo hakan yasa na dauka amma kafin nayi magana tace

"Test din Cardiovascular physiology Yanzunnan, kiyi sauri. "

Tsaki nayi nace

"ke Bazan zo ba, Dan nasan ba barina Zaiyi na shiga ba. "

"Kinada damuwa Hikmah, wayace miki bazai barki ba, Inace Kinyi attending previous class dinshi. Kiyi sauri kawai Dan Kinsan rashin test me yake nufi. "

Daga Haka ta kashe wayar ta, nima mikewa nayi na dakko wani Dogon hijab Har kasa ash color na saka, flat shoes dina na koda yaushe maroon na zura a kafata sannan na dauki abinda zan bukata nayi waje. A raina Inata tunanin yadda Zamui dashi saboda class dinshi yace inhar ban same shi ba to yana nan akan bakanshi na carry over.

Ina zuwa venue din daidai yana fitowa daga matarshi wadda yayi parking a gefe, kowa sauri yake ya shiga, Nikam tamkar babu inda Zanje na cigaba da tafiyata cikin normalcy na. Ina jin takunshi a baya na amma ko juyowa banyi ba balle na gaisheshi, Haka zalika shima Ko inda nake bai kalla ba seda muka shiga cikin class din, kowa ya zazzauna se ni da Wasu mutum biyu muke kokarin zama. Bai min magana ba Har seda na zauna sannan yace na tashi tsaye, jikina a sanyaye na mike, zuciyata na wani irin bugawa. Bai Kara bi ta kaina ba seda ya gama raba duk multiple choice question paper sannan yace

"You have only ten minutes to attempt the forty questions."

Gaba daya ajin Ya kaure da hayaniya, kowa yana protest akan hakan amma no one is bold enough to raise the motion.

"Silence!"

Ya fada muryarshi a kausashe, a take Kuwa duk sukai Shiru, sannan yace class rep ya maimaita abinda yace idan banje office na sameshi ba. A take ya maimaita sannan Abdallah yace

"So Zainab, can you kindly walk out of my class?"

Ya fada yana Kara tamke fuska, duk se naji am embarrassed, a hankali bakina ya Fara rawa inason bashi hakuri amma inner thoughts dina suka rinjaye ni, haka jiki babu kwari nayi waje, zan fita naji yace

"Ki rufe mana kofa and be ready for your CO"

Idona na lumshe sannan nayi yadda yace na fita na rufe kofar, wani irin tukukin takaici nake ji cikin zuciyata, wani irin bacin rai yake taso min, Ni banyi bacci ba, ni banyi test din ba. Wannan shi ake kira 2-0 babu Wan babu kanin. Na juya Dan komawa hostel Se naji muryar Mrs Hassanah Uba tana fadin

"Zainab Ya kika fito? "

Juyowa nayi tareda dukawa nace

"Good morning Ma'am"

"Morning Zainab, ya baki shiga test din ba? "

Dama zuciyata a kusa take hakan yasa duk yadda naso na daure na kasa, kawai na Fara kuka

"Ya Salam! Me ya faru? "

Kaina na girgiza mata Inata goge hawayen amma tamkar I'm calling for more Haka suka cigaba da sakkowa. Ganin muna Bata lokaci ga Naki daina kuka yasa ta fahimci nida Abdallah ne. Hannuna ta kama tace

"Muje ciki"

Ita ce a gaba ina biye da ita a baya, yadda ya bude kofar a zuciye I'm sure da ni ce to Mari na Zaiyi. Ganin Mrs Hassanah yasa ya ja da baya yana gaisheta, amsawa tayi tace

"Shigo mana Zainab, Sir me ya faru na ganta a waje? "

Shigowa nayi Ina wasa da Hannayena, ko ban kalleshi ba nasan kallona yake, Nima gabana faduwa yake saboda muna mugun shiri da Mrs Hassanah bansan yace na mishi Tsaki taga banida tarbiyya. Maimakon abinda nayi expecting ya fada Se cewa Yayi

STORY CONTINUES BELOW

"Question paper ta bude kafin nace a bude. "

Wata Ajiyar zuciya na sauke me nauyin gaske ina hamdala ga Allah, bansan na dago na kalleshi ba da fuskata wadda tayi kacakaca da hawaye, he was looking at me also, wannann idanun nashi masu haske Ya tsareni dasu, kawai se nayi mishi Murmushi.

"She's eager Kasan ita ke Jan class din. Ke kuma bashi hakuri kije Ki zauna"

Mrs Hassanah ta katse mana kallon kurillar da muke yiwa juna. Da sauri na karbi paper daga hannunshi nace

"Thank you Ma'am, Sir I'm sorry! "

Kawai yan class Se ihu Wanda yasa yayi Murmushi da a wannan lokacin, a iya murmushin da na taba gani a fuskokin mutane, ban taba ganin kyakyawan Murmushi irin wannan ba, ganin ina kallonshi yasa ya dage min gira tareda maida hankalinshi akan Sauran Yan class din. Da sassarfa na samu seat na zauna na Fara test din.

Tunda na zauna ya dawo Kaina ya tsaya hannayensa cikin pocket din Wandon suit din jikinshi. Gaba daya se naji na kasa nutsuwa ga kamshin turarenshi da ya cika ko ina na gurin. Lokaci zuwa lokaci Se na gyara zama na, can Mrs Hassanah ta kirashi hakan yasa ya tafi ni kuma na samu na sake.

Test din was Alhamdulillah kawai, muna fitowa na samu guri na zauna can gefen department dinmu inda mutane sukai parking motarsu na tsaya a jikin motar, wayata na ciro ina amsa call din Hamma Mussadiq, shima kwana biu ya takura ma rayuwata, ban fahimci kwatakwata inda kiran da yake min ya nufa ba kawai ina Bari a Yan uwantaka dan baki daya na manta zancen Anty Fadila.

Sosae na shagala da wayar, se honk naji a gefena, dagowa nayi na Kalli inda honk din Yake, karaf idanuna suka hade cikin na Abdallah Wanda yake cikin motar dana jingina da ita. Cikin sauri na matsa ina turo bakina, tareda zabga mishi harara. Kawai se ya bude motar Ya fito ya nufo inda nake, ganin hakan yasa nayi saurin katse call din tareda tura wayar cikin purse. Yana isowa inda nake yasa middle finger dinshi da na gefen shi ya dalle min bakin da na turo gaba.

"Ouch! "

Na furta saboda abin yazo min unexpected sannan kuma ga radadi da yazo min lokaci daya.

"Se nayi maganin fitsararren bakin nan. Wuce muje! "

Ko musu banyi ba nabi bayanshi muka koma cikin department din, se kallonmu ake, kada ma Yan ajinmu suji labari. Wanda basu ganmu ba Har tabo su ake dan su ganmu. One thing dani to na tsani kallo, gaba daya se naji an takura min amma babu yadda na iya haka na cigaba da tafiya Dan yana bayana se directives yake bani, a Haka Har muka iso kofar wani office, a saman office din Anyi carving Abdallah Ahmad Abdallah a jiki, Wanda ya tabbatar min office dinshi ne. Gefe na matsa Ya bude sannan nabi bayanshi bakina dauke da duk adduar da Tazo min zuciyata.

Office din yayi kyau, komai in order and place, kan kujerar shi ya zauna sannan yace

"Zo ki zauna mana"

Ya fada yana nuna min kujerar dake facing dinshi, Yanzun babu wani abu daya rage a gareni banda in bi dukkan abinda yake so. Zama nayi a daddara fuskata cikeda Tsoro kamar kace kyat na fita a guje, ina kallonshi ta gefen idona yana min dariya amma halinda nake ciki Ko damuwa da hakan Banyi ba.

"Fada min me yasa kikai min Tsaki ranar? "

To anzo gurin na furta a hankali, banma san abinda zance mishi ba nayi Shiru Ina wasa da hannuna.

"Kina bata min lokaci fa, me yasa kikai min Tsaki?"

Ya kara maimaitawa, tamkar ina koyon magana nace

"Ai ba dakai nake ba.... "

"Da wa kike?"

Ya tambaya yana dage min girarshi, abinda na lura dashi hakan tamkar normalcy dinshi ne dage gira. Shiru nayi Dan ni dai ban iya karya ba, ba kuma zan Fara Yau ba, sannan nasan idan yaji dalilina tsaf zaiga Kamar karya nake amma Haka na bude baki nace

"Kawai bana son me suna Abdallah ne! "

"What? "

Ya fada yana zare glasses din idanunshi tareda tsare ni da ido cikeda mamakin furuci na. Kaina na sunkuyar tunda nake ban taba samun mutum irin wannan ba tunda nake babu Wanda ya taba sakani a corner na kasa fita, yana daya daga cikin abinda ya hanani zuwa bashi hakuri saboda dole zai bakaci sanin dalilin Tsaki na, ni kuma bazanyi karya ba.

"Sir Dan Allah kayi hakuri, it came out unexpected"

Na fada Ina hade Hannayena guri guda alamun ban hakuri, kanshi kawai ya gyada yace

"Is ok, tashi ki tafi"

Da sauri na mike ina mishi godiya nayu hanyar waje amma Se ji nayi yace

"Kin taba karyewa ne? "

Cikin rashin fahimta na juyo, yanayin fuskata cikeda tambaya hakan yasa yace

"On your left leg? "

Se nayi Murmushi tareda kallon kafar sannan na girgiza Kai nace

"Haka aka haifeni, Ina ganin congenital abnormality ne. "

Kanshi Ya gyada alamun yarda sannan nayi waje Ya bini da kallo Wanda bansan yana yinshi ba.
Tundaga wannan ranar bamu Kara Haduwa da Abdallah ba, ban kara bi ta kanshi ba nima. Cikin saa muka fara exams, gaba daya bani da lokacin komai banda na Karatu. +

Ranar da muka kammalla exams dinmu se yamma around 5pm muka fito. Tareda Nanah muke tafiya tace

"Wai ina mutuminki ne? "

Kallonta Nayi naga Tana dariya, Se na bata rai nace

"Wa kenan? "

Seda ta gama dariyarta sannan tace

"Sir Abdallah mana."

Wata harara na wurga mata nace

"Meye hadina dashi da har kike kiranshi mutumina? "

Kanta ta girgiza tace

"Maida wukar, kawai dai ina hango something big da zai faru nan gaba"

Tsaki nayi nace

"Kin fara duba kenan? Tsubbu kikeyi da zakice something big will happen. Allah Nanah Kinada abin haushi, Allah yasa gobe zan bar miki garin. "

Dage kafada tayi tana ta dariya irin do I care dinnan, ban kara mata magana ba Har mukaje hostel sannan ne nace da ita

"Kar kiyi girki, zanyi se kizo muci"

Rungumeni tayi tana fadin

"My Hikzeey is the best"

Hararta nayi na wuce dakinmu, mu biyu muka rage Dan duk Sauran sun tafi sun gama exams. Itama kuma ba zama takeyi ba, friends dinta a Ribado hostel suke so most times acan take.

Abdallah Ahmad Abdallah shi ne sunanshi, Mahaifinshi Dan asalin Garin Jimeta ne ta Adamawa state, mahaifiyarshi Mrs Hassanah Uba bakatsiniya ce a mashi. Sunyi auren su na saurayi da budurwa. Service ya kawoshi katsina akai posting dinsa Fggc Bakori, ita kuma lokacin tana SS3, a Haka soyayya me karfi ta shiga tsakaninsu bayan ya gama serving dinshi ya dawo da iyayenshi aka nema mishi aurenta. Basu sha wahala ba sukai aure saboda dukkansu Sun fito daga manyan family ne sannannu, so bincike baiyi wuya ba akai aure, lokacin yana Karatu a Unilag yana Msc dinshi. Yana da masifar kokari Dan Yan set dinsu 4pointer suke kiranshi dashi, bai taba yin kasa da 4.7 ba, Hatta thesis dinsa da research work din da yayi seda aka kaishi international level saboda aiki ne babu ha'inci yanada jajircewa sosae aka aikinsa da karatunsa. Anan suka Fara zama ya sama mata admission tana Human physiology, Shekarar farko ta haifi Yarta Asma'u wadda taci sunan mahaifiyarshi Ahmad kenan. Tasha Gata sosae, bayan sun yayeta aka maida ita Jimeta gurin me sunanta. Daga nan sukai family planning Har suka kammalla karatunsu, shi ya samu lecturing ita kuma ta Fara masters dinta. Tafi tafi seda sukai shekara bakwai sannan ta Kara haihuwar Namiji aka saka mishi sunan Mahaifin Ahmad Abdallah, suna kiranshi Abba karami. Tundaga wannan haihuwar aka mata daurin mahaifa Dan basu kara haihuwa ba.

Abdallah Nada shekaru uku suka tafi London shida iyayenshi wannan karan hadda Asma'u suka tafi wannan yasa suka samu Karatu me kyau. Sede suna dawowa Nigeria kaddara ta gifta tsakanin Ahmad da Hassanah suka rabu a lokacin dukkansu suna aiki ABU ne, Asma'u akai mata aure a kwara state haka Abdallah ya tafi Chicago yana Karatu, gaba daya sunji effect din broken home dinsu, duk walwalar su ta dauke Mussaman Abdallah daya tashi a tareda su. Shiyasa duk yadda Prof yayi dashi akan ya yadda yayi karatunshi a Nigeria yaki, gani yake zaman me Zaiyi babu Ummiey da Abbu a tare dukda yasan suna gari daya, aiki guri daya amma Meye maanar basu tare.

Haka rayuwar ta cigaba da tafiya har ya kammalla first degree dinshi Ya dawo, with the hope cewar iyayenshi Sunyi reuniting, Dan tuntuni Abbu ke fada masa akwai surprise yana jiranshi, Haka zalika Ummiey.

STORY CONTINUES BELOW

To his greatest shock yana dawowa Ya tarar dukkansu Sunyi aure bawai sun maida aurensu ba, duk yadda yakai zuciyarshi Nesa seda yayi kuka saboda bakin ciki. Yana Gama serving ya koma Chicago Yayi Masters dinshi. Dawowarshi kenan Abbu Ya Sama mishi lecturing nan cikin ABU din tunda dama field din da Ummiey tayi Shi yake, hakan yasa ya zama lecturing assistant dinta.

Washegari na koma Kano cikeda farin ciki da daukin son ganin Mama, cikeda farin ciki na shiga gidan na bar kayana a bakin gate ina ihu. Ina shiga parlor na ganta a zaune Tana ta buga lissafi jikin paper, ko dagowa ba tayi ba balle ta kalleni, hakan yasa na Fara diddira kafa Ina fadin

"Kai Mama baki ji Inata kiranki bane? "

Dagowa tayi, Allah Sarki Mamata, shekarunta kara ja suke kullum na ganta se Inga tsufa takeyi dukda Tana cikin jin dadi yana biyewa, amma still abubuwa da Dama canjawa suke a tare da ita. Ko yaushe zata mutu? Ko yaushe zata tafi ta barni? Tunanin hakan se kuka, na Fara kuka sosae Wanda yasa ta Mike hankalinta a tashe tana tambayata lafiyata. Rungumeta nayi nace

"Mama tunani nayi idan kika mutu Ya zanyi? "

Bubbuga bayana tayi tace

"Hikmah dai se a barki, shi ne kike kuka Haka Kamar ance na mutu din? Inshaaa Allah Se na aurar dake kafin na mutu Kinji? "

Idanuna na share hawayen nace

"To Bakiyi Murnar dawowa ta ba? "

Hannuna taja na zauna gefenta tace

"Murna Kai! Ko so kike na taka rawa? "

Dariya nayi cikeda jin dadi tareda rungumeta nace

"Mamata ta kaina. "

"Hikmata! Yaya jarabawar, Allah yasa Anyi a nasara? "

"Amin Amin "

Na bata amsa sannan na mike na janyo trolley dita wadda aka kawo min daga gate. Seda nayi wanka sannan na fito nayi lunch, ranar Gabaki daya hira mukai tayi harda Baffa da ya dawo daga office dinshi.

Haka nayi ta Hutu Abuna, Ranar na shirya Tun safe na tafi gidan Najaatu, Munyi akan zamu hadu dukkanmu, ni, Aneeysa da Anty Fadila. Nida banida wani nauyi akaina ni na Fara zuwa lokacin Hamma Mustapha ko fita baiyi ba, da nayi knocking shi yazo Ya buden yana fadin

"Kin bamu ajiya ne zaki zo mana gida da sassafe?"

Dariya na danyi ina fadin

"Hamma an tashi lafiya? "

"Lafiya lau"

Ya bani amsa yana matsa min gefenshi na shigo gidan sannan ya biyo bayana. Tana parlor Tana yiwa Mimi wanka, yarinyar tata tayi Wayo sosae ina school aka haifeta itada Aslam din Aneeysa. Ni na Hada musu breakfast Dan nima banyi ba saboda indai naji zancen yawo to ni ce akan gaba.

Sauran basu zo ba se wajen Karfe sha biyu, ranar nayi yinin dadi, mun sha hira munci Abinci Masoyina. Se bayan Sallar ishai sannan Hamma Mussadiq yazo Ya tafi damu seda ya Fara sauke Anty Fadila da Aneeysa sannan ya wuce Dani gida. Tunda muka fara tafiya bai cemin komai ba seda yayi parking kofar gida sannan na Fara kokarin fita yace

"Zainab! "

Juyowa nayi na dubeshi Dan I can't remember yaushe naji Ya kirani da Zainab ba, Bazan iya tunawa ba, ban amsa mishi ba se gyara zamana da nayi Ina sauararenshi. Rage volume din Radio yayi hakan ya bani insight akan serious magana zamuyi

"Hikmah, Menene matsayina a gurinki?"

Cikin rashin fahimta na kalleshi nace

"Why this all of a sudden?"

Kanshi Ya gyada Yana Kara tsatssare ni da idanunshi yace

"Ina jinki. "

"Hammana! "

Na bashi amsa Ina tsuke fuskata, kawar da kanshi Yayi, nafi tunanin yana nazarin amsa ta ne, to me zance dashi na ayyana a raina, tunda Bashida mukamin daya wuce Hammana!

"Idan Ina sonki zaki aureni?"

A zabure na dago idanuna Wanda na budesu Baki daya akanshi, kafadarshi ya daga irin to Meye dinnan?

"Meye na zabura tamkar nace zaki kasheni? See inasonki Hikmah, so na soyayya na aure, for all this while ina tattala kine saboda na maida ke Matata, amma Fadila tayi miki shigar sauri"

Idanuna na lumshe cikeda wani yanayin da bazai Rubutu ba, bansan yadda zan fada muku yanayin da na shiga a wannan lokacin ba, ko magana kasawa nayi se kokarin bude kofar da nayi Dan na tafi amma ya rigada yasa lock a kofar, idanuna da suka kankance na dago nace cikin stern voice

"Hamma zan shiga gida"

"Babu inda zakije har Se kin fada min abinda ke ranki"

Dagowa nayi nace

"Hamma ka barni na fita, Ina ganin mutuncinka, don't provoke me"

A yadda nasanshi baya San raini nasan zai iya zama provoked ya barni na fita amma Se cewa Yayi

"Hikmah amsa kawai zaki bani, kin amince na nemi aurenki"

"Wai a garin jahillai muke ne Hamma? Mu fa musulmai ne, ka taba ganin inda Yan Uwa ciki daya sukai aure? Haba Hamma da iliminka da komai Kake fadar Haka? Na shiga uku! "

Na fada cikeda ihu, hawaye na bin kuncina ,ban taba tunannin haka zata faru ba, ban taba tunanin akwai ranar da wani mahaluki zai furta min abinda Hamma ya fada min ba, nayi Dana sanin fitar da nayi, naji mugun magana daga bakinshi.

"Saboda basu suka haifeki ba, bamu hada komai dake ba, ke ba yarsu bace, tsintar ki sukayi!!!"Hamma Mussadiq has messed up Ooooo...... Poor hikmar mu..... Let's join and mourn together

Post a Comment for "HIKIMA CHAPTER 6"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...