[Advertisements⬇️]

HIKIMA CHAPTER 2 - Bankinhausanovels
Sun. Mar 26th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

HIKIMA
CHAPTER 2
“Zamui referring dinku Teaching hospital na gwagwalada”

Doctor Ya fada lokacinda yazo duba babyn Hafsa, kallonshi Hafsa tayi tareda kallon babyn sannan tace

“Amma babanta yace kace zaayi discharging dinmu ne, Naga ta samu sauki referral na Meye Kuma?”

Kanshi Ya girgiza sannan yace

“Eh sallamarku Zamui amma Kinsan zaku dinga zuwa follow up ko? babanta yace dani a Abuja kuke, so is better Ku cigaba acan than ace zaku dawo nan”

Ajiyar zuciya Hafsa ta saki tayi Murmushi tana kallon halittar dake hannunta, da gaske bata taba kawo yarinyar zata murmure har Haka ba, kullum gani take yarinyar zata mutu kafin Washegari amma rai hannun Allah yake.

“Mun gode sosae, kuma Inshaaa Allah Zaa dinga zuwa follow up din”

Kanshi Ya gyada sannan yace

“Kinsan yarinyar preterm ce, akwai organs dinta da are not well developed, to akwai abu da ake kira kangaroo mother care KMC, shi Zaa dinga mata”

Cikin rashin fahimta Hafsa tace

” Bangane ba”

Tsayuwar shi ya gyara yace

“Kinsan kangaroo nada pouch jikinta Wanda take zura danta ko? ”

Kai Hafsa ta kada, ya cigaba

“zaki cire rigarki, ki daura babyn bayan kin cire kayanta a kirjinki, ki daure da zani, dumin jikinki zai dinga regulating nata body temperature, sannan breastfeeding is also essential ”

Kai ta gyada cikin fahimta, tayi mishi godiya sannan ya fita, yana fita Miss A’isha ta shigo Don hada kayan, Hafsa na zaune ita kuma Miss A’isha ta kammalla ganin Hafsa batada niyyar tashi yasa tace 

“Tashi mu tafi mana, kina bata min lokaci yau nake son tafiya” 

Dagowa Hafsa tayi tace 

“Haba Mom, tafiya zakiyi ki Kara barina? ” 

Sakaka Miss A’isha ta kalleta sannan Tayi tsaki tareda karbar babyn ta rufeta cikin Farin shawl me baza red a jiki, ganin zata fita yasa Hafsa riko hannunta tace 

“Mom me yasa kuke Haka keda Alhaji? Idanunku na nuna abinda kukeso amma kunki, Haba Mom rekindle your love mana…. ” 

Zancenta ya katse saboda shigowar Alhajin, kallon hafsan kawai yake Se kuma ya Kalli Miss A’isha kafin yace 

“Hafsa haka kikeso? ” 

Da sauri ta gyada kanta batareda ta furta komai ba saboda wani irin excitement da ya lullube ta, kallonshi Miss A’isha tayi tace 

“Ina fatan ba fada mata Kake zaka maida ni ba, Abbas ka manta nace Bazan kara komawa gidanka ba? ” 

Murmushi Alhaji Yayi yayinda jikin Hafsa ya Fara rawa yace 

“Eh kin fada A’isha, amma inasan kisan ni dake we’re match made in heaven, har yau shekaru ashirin da biyar kin kasa aure, kinga you’re telling Abbas is only you I want. Badan ke zanyi ba sedan farin cikin Hafsa. ” 

Daga Haka ya fice, Miss A’isha ilahirin gabobinta Sunyi sanyi, Hakanan tayi Shiru Ta rasa me takeji, Hafsa ce ta dafa ta Murmushi saman fuskarta tace 

Story continues below


“You should happy Mum! Alhamdulillah! ” 

Suna zuwa gida zance har ya bazu akan Alhajin sama zai maida Mum, masu farin ciki nayi, mahssada nayin nasu Wanda Dama su sukai sanadin wancan rabuwar. Masoyan Miss A’isha a familyn Sunyi murna, ga Murnar dawowar Hafsa gida. Washegari wajen hudu na rana aka maida auren Alhaji Abbas Maina da A’isha, zata huta a Nigeria na sati biu kafin ta koma California saboda aikinta duk Wanda ya samu Dama se yazo. Aminu murna Kamar me, Washegari suka juya Abuja. 

Gidan an gyarashi Wanda hakan ya bawa Hafsa mamaki seda ta shigo taji Ihun little Maina yana 

“Maa oyoyo, kince itace Matata ko? ” 

Kanta ta gyada wani kayataccen Murmushi na fitowa tace 

“Babana wannan ita ce matarka gata nan ” 

Ta mika mishi ita, gaba daya shekarun yaron basufi goma ba, shi ne Babban Dan Salima kanwar Aminu, mijinta Nafi’u yayan Hafsa uba daya, Rana daya akai musu aure dukkansu. 

Kallonta Maina Ya tsaya yi ganin tana wasa da hannunta a baki ga Idanunta sak na Hafsa Manya dasu, Murmushi yayi yace 

“My Lulu Catty” 

Shikenan Lulu ta bita Dama sunan Dada aka saka mata Baa fada kowa da abinda yake fada mata cikin dangi seda Maina yasaka mata Lulu shikenan kowa ke kiranta Haka. Duk Friday da an tashi a school driver ya sani gidan Hafsa yake kawo Maina anan zai yini Se dare kafin ya koma gidansu, Don Haka bayan iyayenta Hafsa da Aminu babu Wanda Lulu ta gane Kamar Maina. 

Ranar asabar suka karbi bakuncin Habibu da Lubabatu, ranar Ansha hira Kamar me, Aminu Ya dinga musu tsiya akan yadda basu yawo da yaransu ,Habibu Ya tabe Baki yace 

“Kuma doki kuke da zarar Kun Tara da yawa zaku daina wallahi, ta Ina zaka dinga yawo dasu.” 

Hafsa ce tace 

“Amma basu taba ganin kanwarsu ba, at least da Kun taho dasu ai ” 

Lubabatu tayi dariya tace 

“Da tuni sun hautsina ko ina, kada ku damu Hutu Zaa kawosu gaba daya” 

Dariya Duka sukai sannan sukaci Abinci, bayan Maghrib aka kaisu airport suka koma Lagos bayan Lulu Tasha abin Arziki har seda Aminu Yayi fada Wanda yasa Lubabatu fadin 

“Lallai Se Yanzun Kasan kudi akwai amfani, idan bamuyiwa gudan jininka ba se wa” 

Godiya sukai musu suka rabu cikeda kewar junansu. 

A kwana a tashi Har Lulu tayi wata bakwai, dukkan Wasu dokoki babu Wanda Hafsa ke tsallakewa, yarinyar tayi girma sosae Kamar ba bakwaini ba, ta murmure babu inda ta baro Hafsa Har skin color din, kyakyawa ce yarinyar, nan Hafsa tasa wata mata ta kawo mata Nanny Wanda da kyar Aminu Ya yarda don da farko cewa Yayi sede a Nemo professional daga wata kasar amma Hafsa tace 

“Haba dai dear Dan bata kudi, nanma Allah zai kiyaye” 

Nanny Batafi 18years ba Christian ce mazauna kauyikan Abuja, anan aka samo ta, sosae aka kafa mata dokoki kuma babu laifi yarinyar tana kokari sosae. Indai Hafsa na gida to Lulu na gurinta sede idan ta fita shi ne. 

A kwana a tashi watanni suna ta tafiya, rayuwarsu gwanin dadi har shekara ta zagayo lokacin birthday din Lulu ta zagayo, ana saura sati daya Hafsa da Cynthia Nannyn Lulu suka tafi gidan Salima inda Zaa tsara grand birthday party. 

“Kinsan baayi suna ba lokacin muna asibiti, so nake nayi kara’i da suna da komai. ” 

“kina shaanin Ki matar nan, tunda grand ne mu Fara plan Tun yanzu” 

Take aka dakko paper da pen aka Fara tsarawa basu gama ba se dare tukunna Aminu yazo daukarsu, a Mota take cemishi 

“Birthday din Lulu fa next week ranar asabar” 

Cikin rashin kulawa yace 

“Lulu ta girma” 

Dariya Hafsa tayi tareda gyara zama tace. 

“So Ina shirya mata grand birthday party” 

“Birthday party kuma? Saboda me? ” 

Dan bata rai tayi tace 

“Eh mana, ka manta baayi suna ba mutane nason su ganta, kaga party zai saka suzo Ko? ” 

Kanshi Ya girgiza yacr 

“ki manta da wani birthday stuffs Kinji Hafcy na” 

Shiru tayi Batace komai ba hakan yasa yace 

“Yawwa my love! ” 

Nanma Batace komai ba hakan yasa ya yi tunanin ta hakura, ita kuwa karkashin ranta tana tunanin abinda zai Hana party dinnan abu me girma ne. Batareda sanin Aminu ba Hafsa ta cigaba da shiri Kamar yadda mutanen ta ke shiri abinsu, seda ranar Tazo Aminu Ya gama shirinsa tsaf sannan Hafsa tace 

“Kayi hakuri for the first time kace na bar abu ban hakura ba, yau zanyiwa Lulu party” 

Tsira mata idanunshi yayi yace 

“Amma nace banaso right? ” 

“Ka fada but lokacin Har cake nayi order, babu abinda zai faru Inshaaa Allah ” 

Ta fada tareda bashi peck a kumatu, mayar mata da martani yayi sannan yace 

“Its OK, ayi lafiya” 

Rungumeshi tayi wannan yana Kara jika son Aminu a ranta, akwai sacrifice, Allah Ya barsu tare. 

Karfe hudu gidan Ya cika mutane sosae abin harda mamaki, Lulu tayi kyau cikin kayan da aka saka mata dake Har lokacin bata zama se kafa da take, Tayi kyau ko ina Maina na gefenta, Haka akaci aka sha aka yanka cake, lokacin photo session Hafsa ta canza mata kaya zuwa wata riga silk ta ciki amma saman duk net ne color red Se karamin crown silver a wuyanta, hannunta tasa mata wata silver bracelet Wanda wani katako da aka lullube da takarda tayi Rubutu a jiki, duk na yadda suke sonta itada Aminu, yau birthday dinta how special ranar take garesu. Anyi hotuna sosae seda aka gama sannan ta bawa Cynthia akan taje ta canza mata kaya, nan gidan Ya Fara Bajewa daga kawayenta Se Salima, su suka taya ta gyaran gidan sannan suka tafi, nan ta samu tayi wanka sannan ta shirya abincin Aminu. Se wajen karfe Tara Aminu Ya shigo tana kallonshi taji wata muguwar faduwar gaba ta ziyarce ta, Har seda ta bude Idanunta, da murmushin nan na kullum ta tarye shi seda yaci Abinci Yayi wanka sannan yace 

“Ni Banji hayaniyar Lulu ba, ko tayi bacci” 

Kai Hafsa ta girgiza tace 

“Ta gaji na bawa Cynthia ta mata wanka har Yanzun basu fito ba, Nima gyaran gida ya dauken hankali, lemme check them” 

Mikewa tayi ta nufi dakin amma kafin ta bude taji wani jiri nason dibarta, da sauri ta daidaita Tsayuwar ta sannan ta shiga, Idanunta ta runtse ganin babu kowa a dakin, kayan da ta bayar a sawa Lulu yana yashe a Kan gado, zuciyarta na harbawa ta isa bandaki nan ma babu kowa a ciki, Shiru Hafsa tayi gaba daya ta kasa tantance meke shirin faruwa, 

“Cynthia! Cynthia!! Cynthia!!! ” 

Ta shiga kwala kira amma Shiru hakan yasa ta fito da sauri Tana zuwa sukai karo da Aminu Wanda yazo dubata jin yadda take kwallawa Cynthia kira 

“Menene? ” 

“Ban gansu ba Aminu, basa nan” 

Kallonta Yayi cikeda rashin fahimta yace 

“Wa kenan? ” 

Se jikinta Ya fara rawa ganin irin kallon da Aminu ke mata, harshenta Yayi nauyi ta kasa magana Se Idanunta da ta kafe a kanshi, gefenta yabi yana jin wani irin yanayi me wuyar fassaruwa ya leka dakin nan ma babu kowa hakan yasa ya dawo yace 

“Hafsa kidding me right? Ina Yata? ” 

Ya fada da karfin da seda Hafsa taja baya, Binta yayi ya shake mata wuya………… 

_Last post nayi mistake akan Lulu bata zama, nop bata tafiya nake nufi, shekara daya babu zama ai da matsala!  To all HIKMAH lovers I heart you lot…. One love 💕_ 

Hannunta tasa ta rike na Aminun, wannan kwalakwalan idanun sun fito Kamar zasu fado tareda kadawa sukaiwa jawur, shima nashi idanun Sunyi jawur saboda tsabar Tashin hankali, Hafsa hannunta tasa tana kokarin kwace wuyanta jin yadda rikon yayi tsauri amma ina karfin ba daya bane, cikin Tashin hankali tace 

“Aminu lemme be…..” 

Da sauri ya katse ta da fadin 

“Be what? Ki sace min yarinya na kyaleki se na kashe ki Hafsa” 

Ya fada yana Kara Kama wuyanta, hannunta tasa jin azabar tayi yawa ta hankade shi, cikin nasara Yayi baya ai tana ganin Haka yasa Hafsa nufar kofa a take Aminu Ya take mata baya sede kafin yazo har ta datse kofar parlon, fita Tayi gaba daya daga gidan Kamar mahaukaciya Tana waigewaige Har ta isa bakin Titi, wani me taxi ta Tara ta masa kwatancen gidan Salima, nan kuwa aka kaita cikin saa taga Nafi’u a tsaye a kofar gida, Idanu ya tsare ta dashi cikeda mamaki, ganin kayan jikinta Ko Dan kwali babu a kanta, baima mata magana ba ya bashi kudin ita kuma ya kama hannun ta suka shiga ciki, Salima na tsaye Tana clearing parlo inda suka ci Abinci, Babu kowa duk Yaran Sunyi bacci tuntuni, jin sallamar Nafi’u yasa ta juyo dan Batayi expecting dinshi ba tunda yace Se bayan Tara zai dawo, bata kuma mamaki ba seda ta hango Hafsa a gefenshi kana kallonta kaga wadda take cikin Tashin hankali da masifa da kuma iftila’i, sakin bowl din hannunta Salima tayi ta taho da sauri tana fadin 

“In-law lafiya? ” 

Wannan lafiyar da Salima ta tambayeta Se karya mata zuciya ta saki wani irin kuka babu kakkautawa, sosae na gaske, Tun tana iya tsayuwa har ta durkushe a gurin Tana gunjin kuka, tuni Salima ta durkusa gefenta Haka kawai se hawaye itama, Nafi’u na tsaye baisan abinda zai ce dasu ba. 

A bangaren Aminu, Hafsa na fita yayi dakinshi tareda dakko key din Mota, yana fitowa Ya janyo kofar parlon ya jita datse, kanshi Ya dafe yana bugawa Tun karfinshi amma kofa ko girgiza Batayi ba, dakin Hafsa ya koma ya dakko spare key ya nufi kofar, cikin saa yana murdawa ta bude Don a gigicewar Hafsa ta cire key din, Ko kofar bai rufe ba Haka ya isa inda matarshi take Ya fada Se gidan Nafi’u Dan yasan nan ne kadai inda Hafsa zataje, wannan lokacin sha daya na dare har tayi don garin duka yayi tsit, mutane yawanci sun shiga gida sun kulle, amma banda Nafi’u Wanda tsabar Tashin hankali bai bi ta rufe gida ba. Yana shiga ya sameta a durkushe Tana kuka Kamar ranta zai fita, ga Salima na tayata, yayinda Nafi’u ke ta safa da marwa har lokacin Hafsa batace komai ba, Aminu ko sallama babu yayiwo kukan kura Ya kama gashin Hafsa wadda ta saki wani razannanen ihu, kanta kawai take girgiza mishi ta kasa furta komai Se shi ne yace 

“Ina yata Hafsa? Ina kika kaimin ita? Ina kika kaita? ” 

Shima hawayen yake, da sauri Nafi’u yazo Ya kwaci Hafsa sannan ya kama hannun Aminu amma fizge, Nafi’u cikin sanyin murya yace 

“Aminu Meye Haka ne Wai? Zauna ka fadamin me yake faruwa? ” 

“Babu inda zan zauna har Se Hafsa ta fito min da yata” 

Cikin rashin fahimta ya bude Baki Zaiyi magana amma Hafsa ta rigashi fadin 

“Aminu ina zan Kai Lulu, wallahi bansan inda take ba last thing Dana sani na bawa Cynthia ita tayi mata wanka shikenan!” 

Muryarta Har ta Fara dashewa saboda kuka, a lokacin Nafi’u da Salima suka fahimci inda Maganar ta dosa kenan fada suke akan Baa ga Lulu ba? Tirkashi ana wata ga wata! Wata sabuwar Inji Yan caca. 

Da kyar Nafi’u ya zaunar da Aminu sannan yasa Hafsa tayi bayanin komai, tana yi tana kuka, Aminu nayi Salima nayi seda ta gama sannan Salima tace 

“Tabbas Cynthia ce don kuwa zamu tafi Maina yace zai ga Lulu, na kaishi dakin, babu kowa Se kayan Lulu a gado, nace da Maina Yayi hakuri wanka ake mata gobe yaje su bude gift tare. Mun shiga uku! Ina takai mana yarmu? ” 

Story continues below


Kuka Hafsa ta kara saki, Nafi’u kuwa baida abin fada Dan Baki daya kanshi a daure yake, Aminu yace 

“I never like that Nanny, seda nace miki kada kiyi birthday party dinnan amma kika ki, kinga abinda kika ja mana ko? ” 

Ya fada Wasu hawayen na kara gudu Kan fuskarshi, Nafi’u ne ya duba agogo sha biyu saura, mikewa yayi yace 

“Ba lokacin tuna baya bane, muje mu Kai report ” 

Lokaci daya suka mike Haka aka kulle Yaran a ciki suka tafi police headquarter, suna zuwa sukai reporting nan aka Fara daukar data , police officer yace 

“Ina ne gurinsu ita me renon taki malama Hafsa? ” 

kawai Hafsa Kai ta sunkuyar, jiki a sanyaye tace 

“Bansan wani gari take ba, wadda ta kawo min ita ta koma ibadan” 

Salati kowa ya saki tsabar mamakin wauta da rashin hankali irin na Hafsa, se ji su Kai Aminu Ya bige bakinta, take kuwa Ya fashe Se jini, hakan ya fusata daya officer Wanda da alama shi ne oga, bindiga ya dakko Ya saita Aminu cikin tsawa yace 

“Bakada hankali? Ka fita son yar ne? Kasan abinda takeji kuwa, useless fellow kawai, ka tsinci yarinya a bagas zaka raina mu. Wallahi ko tari ka Kara yi sena fasa maka goshi, idiot kawai! ” 

Hakan da akai Ya saita Aminu, daga karshe sukace gobe Zaa tattara dukkan bayane a Nemo yarsu, Haka suka juya jiki a sanyaye Hafsa Se kuka take. A wannan Daren duk Wanda Yayi bacci cikinsu to tabbas baccin barawo ne. 

Washegari ansha fama da Maina, kuka Kamar Ance Salima ta mutu, ya dinga kuka shida Hafsa da Aminu ko ruwa basu saka a bakinsu ba, Nafi’u ya fita airport Ya samo musu tickets zuwa maiduguri, sannan ya karbo hotunan birthday inda Salima ta fada mishi, Ya kai police station sannan ya basu number da zasu kira Don zasu wuce Maiduguri. 

Yana zuwa duk sun shirya, babu wani sauki gurin Hafsa Dan zuwa lokacin Ko magana bata iya yi sede hawaye Don kukan babu karfin yinshi, ko kallonta Kai se kaji tausayinta Ya tsirga maka balle kuma ace Kasan halinda take ciki. Suna zuwa gida suka samu yawanci duk anzo dake Saturday ce kowa na zuwa da iyalansa musamman mazauna maiduguri amma wannan karan mutum uku ne kawai babu a gidan. Tunda suka shigo jikin kowa Yayi sanyi Don kallon Aminu kadai ya isa balle Hajiya Hafsa da Maina, take katon parlon Yayi Shiru Wanda da banda hayaniya da sowa bakajin komai. Hafsa na hada idanu da Dada wadda ke zaune gefen Miss A’isha sunsha lafaya yar ubansu, da gudu ta fada jikinta tana fadin 

“Lulu Dada Cynthia ta gudu da ita! Lulu is missing Dada…..Mum I’m shattered.. ” 

Ta karasa Maganar tana riko hannun Mom wadda ta zama mutum mutumi, kowa Yayi Shiru se Alhaji Bulama ne yace 

“Kai Nafi’u me yake faruwa? Me Hafsa take fada? ” 

Tsugunnawa Nafi’u Yayi Ko gaidasu baiyi ba ya fada musu komai, take gurin Ya Kaure masu kiran Allah nayi masu kuka nayi se Wanda sukai Shiru tsabar Tashin hankali, kuka Hafsa keyi Tana fadin 

“I messed up, bansan yadda zanyi ba, har na mutu Bazan daina tunanin ni ce sanadin salwantar da farin ciki na ba, da munji Maganar Ku Haka bata faru ba, duk Wanda bai ji Bari ba yana tareda wahala, duk Wanda ya nunawa Allah shima ya iya, Allah Se ya barshi da iyawarshi…… 

Rarrafawa tayi inda Aminu ke tsugunne tace 

“…..Ka yafe min Aminu, I’m a bad wife I know, banajin maganarka, nasan…. ” 

Se kuka yaci karfinta, dawowa tayi jikin Anty ya kawu ta kwanta tana kuka Wanda mutane da yawa shi sukeyi, mazan suka fita Wasu suka koma Abuja station din yayinda Sauran suka bazu kowa da abinda yake, Hafsa bata cewa uffan se istigfari da take, Aminu ma gashi nan gashi nan, kowa tausarsu yake amma Har dare babu wani labari…. Wasawasa kwana hudu babu wani magana Har akai sati, iya azabtuwa Hafsa tayi bata gane komai bata magana Se kuka, Abinci Se taji Kamar zata mutu sannan zata sha yoghurt, Alhajin sama da kowa nausarta yake tareda nuna mata muhimmanci yadda da kaddara amma tamkar zugata suke. Ranar kwana na bakwai, Alhaji yace kowa ya hadu a Babban parlon gidan yana son magana dasu, kowa ya shigo ya zauna nan, Dada ta shigo da Hafsa wadda saboda rama har doro tayi, ta kara Baki, tayi muguwar rama, Aminu na gefe yana kallonta, ganinta a Haka yaji hawaye sun zubo mishi sede ya Zaiyi Haka kaddararsu take, Haka Allah Ya rubuta musu, kuma dole su karbeta, yasan yaji ciwon rashin yarsa amma karya yake Ya hada kanshi da Hafsa tunda shi yana cin Abinci, yana magana Don jiya Lagos ya tafi gurin Habibu ita kuwa gata nan ba yadda take. 

Sallamar su Alhaji yasa ya dawo daga tunanin da take, Alhaji shi ne Babba a gidan, gidansu gidan gado ne iyaye da kakkanni, ko ina zakaje zaka dawo gidannan, Ammiey Yagana ita take binshi Tana aure a kaduna, Alhajin su Aminu Bukar yake Binta, se Alhaji Bulama, Anty Yana da auta Anty ya kawu. Mutane ne Yan Boko, masu akida, addini da kuma racism hakan yasa yawancin aurensu cikin gida suke yinshi ko kuma can Bama inda Sauran danginsu suke, Alhajin sama da Alhaji Bukar su suka Fara auro bare Wanda ansha artabu amma gashi ya wuce. Tun Hafsa da Aminu na Yara suke kawo matsala, duk kusan problem daga gurinsu ne Har sukai aure, da wannan ya tafi wannan ya dawo. Kukansu sunanshi Ibrahim Maina kakarsu juwairiyya take. 

Seda Alhajin sama Yayi magana sosae akan muhimmancin neman Zabin Allah 

“Allah da kanshi yace ku nemi zabi gurina bazaku taba Dana sani ba, Ku nemi shawarar muminai aikinku bazai baci ba, bature yace two heads are better than one, bahaushe yace Me neman shawara baida sirri amma aikinshi bazai taba lalacewa ba! ” 

Sannan ya dubi dukkansu yace 

“Dukkanin mu muna cikin tashin hankali Tun batan yarmu, sede baza mu taba jin zafin abin Kamar yadda Hafsa zataji ba, ina so ku yadda da kaddara ku Rungume ta, Ina fatan Allah Ya Baku hakuri Keda Aminu, ina fata hakan ya daidaita tsakaninku da Allah. Sannan idan da rabon ganawar ku da yarku Inshaaa Ko bayan shekaru nawa nasan zaku hadu. Allah Ya Baku hakuri Munyi iyakar kokarinmu amma babu labarin Cynthia, Bazan blaming kowa ba amma sakaci ne Hafsa ki kawo me reno Baki Santa ba Baki San daga Ina take ba, wannan Allah Ya riga da ya kaddara hakan sede hakuri, Se kuma muyi kokarin accepting what ever comes our way” 

Hafsa na ta kuka me rikitarwa jikinta har rawa yake, cak kukan ya tsaya ganin Aminu a gabanta, Tsugunnawa yayi ya kama hannunta ya zura envelope a ciki yana kuka yace 

“Kiyi hakuri Hafsa, na sakeki saki daya saboda…..! ” 

Tas! Kakeji Dada ta daukeshi da Mari, kallonshi kawai Hafsa keyi saboda wannan shi ne last thing da tayi expecting daga rayuwa, but life has many ways of showcasing itself! Lumshe Idanunta tayi jin danshi a karkashinta tasan ba fitsari bane amma tanada yakinin cikin jikinta da niyyarta ta bawa Aminu surprise jiya shi ne ya fita, mikewa tayi zata tashi wani jiri ya kwashe ta Se gata Tim! A kasa, Aminu da sauri Yayi kanta amma Dada ta hankade shi ta nufeta kafin wani lokaci Anyi asibiti da ita Wanda cikin da shekaranjiya aka sanar da ita wanzuwar shi ya fita, Ko kuka Batayi ba, akai wankin ciki tana hutawa suka dawo gida, gurin Mom ta wuce ta kwanta jikinta tareda sakin murmushin takaici tace 

“Komai ya Kare Mum, nayi tunanin duk abinda zai tunkaro mu, zamu tsayawa juna nida Aminu, Ashe I’m mistaken, Ashe Aminu zai iya sakina akan yarshi” 

Se kuka, Mum kasa magana tayi kawai ta biyeta suka sha Kukansu, Aminu kuwa Dada Kamar zata tsine mishi kowa a gidan haushin shi yakeji amma shima ya Zaiyi wannan shi ne maslaha idan suka cigaba da zama shida Hafsa Haka abin Zaiyi ta hunting dinsu. Seda Alhajin sama ya shiga Maganar kafin aka sassauta masa, yayiwa Dada nasihu sosae akan Haka Allah Ya tsara kuma dole hakace zata faru Ko suna so ko basa so. Sati biu cif Mum ta shirya komawa California anan Alhajin sama yace ta wuce da Hafsa ta sata ta Fara Karatu Ko zata dawo normal, Haka Tasha kukan rabuwa ta bar kasar da abubuwa masu yawa cikin ranta! 
2009, December 

“Hikmah! Hikmah!! Hikmah!!! Wai bazaki tashi ba? ” 

Juyawa nayi Dan ba karamin dadi baccin yake min ba amma tunda wannan nataciyyar Anty Fadila Tazo nasan tabbas baccina Ya kare, Juyawa nayi tare da bude idanuna Wanda na tabbatar Sunyi jawur tsabar baccin dake cikinsu, 

“Anty Fadila Menene kuma? ” 

Cikin sanyin murya tace 

“Tashi kiyo brush kizo kiji ” 

Babu musu na mike zaune, Kaina babu ko dankwali Se wata tujajjiyar kalba kusan guda goma, ta hade ko tsagar Baa gani, babu abinda na tsana duniyar nan irin kitso bana so bana kaunarshi ,Tun Mama tana tilasta min akan se Anyi kitson amma na kekashe bana so, ita Dama batada hayaniya hakan yasa duk abinda nake so kusan shi nake a gidan, matsalata guda daya ce a gidan Hamma Mus’ab, zaki kenan Haka nake kiranshi Dan kuwa kullum Indai ni dashi ne to babu jituwa tsakaninmu. 

“Tashi mana Hikmah, sauri nake fa ” 

Bata fuska nayi tareda mikewa na nufi bayin dake cikin bedroom din nawa, brush nayi na wanke fuskata tsaf sannan na fito ina Jan kafata ta hagu, idan Ina zaune ka kalleni bazaka taba cewa I’m handicapped ba, amma ina mikewa zakaga kafata ta hagu dingisawa nake Ina limping dinta ne hakan. 

Kallon kayan jikina nayi wata baggy shirt ce ta polio campaign da Hamma Mussadiq ya kawo min, se skinny a ciki, hula na zaro na kifa akan sannan nace 

“Anty Fadila ina zamuje? ” 

Kalloma tayi ta ja hannuna muka fito Har parlour, kasancewar ranar asabar ce yasa babu Wanda Ya tashi a gidan kowa bacci yake, a tunanina nan parlon zamu tsaya amma Haka ta ta jana har wajen gate, Bance mata komai ba seda muka isa kofar wani gida Wanda gidaje hudu suka rabamu dasu, Dayake ba barina ake na fito ba Shifaaa babu Wanda na sani. 

“Anty Fadila ina kika kawo ni? Mama ta hanani fita fa” 

Takarda ta miko min tace 

“kwankwasa gate dinnan, Ki bayar Kice a bawa Abdallah” 

Idanu na zaro mata saboda ni mutum ce me Tsoro nace 

“Kai Anty… A’a gaskiya ” 

Hararata tayi tace 

“Dallah kije ina jiranki ” 

Kaina na gyada idanuna a warwaje na nufi katon ash gate din, hannuna nasa nayi knocking babu dadewa aka bude karamar kofar ta shiga, wani buzu ne yasha rawani ya kalleni tareda fadin 

“ke yarinya ya akai? ” 

Murmushi nayi don ina son accent din buzaye, dariya yake bani. Letter na Fito da ita nace 

“Gashi a bawa Abdallah” 

Babu musu Ya karba ni kuwa nayo baya Ina dingisawa Abuna se Murmushi nake. Ina isa inda Anty Fadila ke rakube ta taso tana fadin 

“kin bashi? An karba? ” 

Kaina na gyada Bance komai ba har muka isa gida, yadda muka fita a sace Haka muka koma a sace, wanka nayi na gyara dakin yadda zan iya na bar Sauran, uniform din islamiyya na saka sannan na fito, har lokacin babu Wanda ya fito balle nayi tunanin zan samu abin breakfast, maimakon naje na tashi Mama A’a kawai na bude fridge din dining anan nayi kyakyawan gani, yoghurt ne me sanyi chilled se guntuwar shawarma wadda ko rabi Baa taba ba, wani murmushin farin ciki ya subuce min ganin favorites dina, a take na zauna nayi munching shwarmar tas na bar wrapper akan table, yoghurt na jefa a jaka na fice se makaranta. 

Mahaifana dukkansu su biyun bafulataine ne usul kuwa, fulanin jos ne na Barikin ladi, Baffa Malam Muhammad lecturer ne a BUK a physiology department, Mama complete house wife ce wadda bana tunanin ta gama secondary, kuma bata taba damuwa ta karasa ba balle tayi tunanin cigabawa, Hakanan take rayuwarta damu. 

Dukkan Yan gidanmu farare ne tas Kamar ka tabasu jini Ya fito kana kallonsu kaga bafulataine ko Baa fada maka ba, kamanninsu dukkansu na Baffa ne ko Mama Wanda suma farare suke amma bandani, Baka ce ni, kuma mutane na kara ganin bakina kasancewar Wanda suke tare dani farare. 

Sunana Zainab amma ana kirana Hikmah nayi primary dina a Kano model dake muna zaune a Matan fada cikin Birnin Kano. Yanzun Haka ina Js2 a Musa Iliyasu dake Rijiyar zaki. Wannan kenan! 

Karfe sha daya na dawo daga islamiyya a gajiye, ga Yunwa dake addabata. Fuskata kwatakwata babu annuri Dan cikiciki nayi sallama, Mama dake zaune a parlour ta dago Tana bina da kallo Har na karaso na zauna 

“Mama Ina Kwana?” 

Da fullanci ta amsa min sannan tace 

“Me kikaci da zaki tafi islamiyya” 

Baki na zumburo nace 

“Yoghurt na gani a fridge, Yanzun Yunwa nake ji” 

Ta dade Tana kallona kafin tace 

“Kinsan yoghurt din na waye kika dauka? Ba nace Karki kara daukar Abu idan baki tambaye ni ba” 

Raina a bace nacr 

“To Mama Yunwa nakeji fa! ” 

Bata kara cemin komai ba, nasan taji haushi ne Dama Haka takemin, Inda take naje na rungumeta ina rada mata a Kunne ita kuma tana ture ni seda ta Fara dariya sannan tace 

“Sake ni kije abincin a dakinki” 

Da sauri na saketa Ina murna na wuce dakina sede Ina taka corridor da zai kaika dakunan baccinmu naji kamshin daya sa naji muguwar faduwar gaba, Hamma Mus’ab the lion in the jungle kenan! Sunkuyar da kaina nayi zan rabeshi na wuce naji Ya cafki hannuna, idanu na bude jikina na rawa nace 

“Hamma….” 

Kallon daya buga min yasa na hadiye Maganar a makoshina, 

“Ke kika dauka min yoghurt da shawarma a fridge” 

Matsalata daya bana karya ko kasheni zaayi, hakan yana Kara bata ran Hamma Mus’ab Don shi yana son yaga ana tsoronshi, Kaina na gyada alamar ni ce, Mari ne ya biyo baya, Tun karfi na na bude baki na fara ihu Ina kuka, ganin hakan yasa ya ciro belt din jikinshi ya dinga tafka min a jikina, abin nema Ya samu Aikuwa se kuka da ihu, hakan yasa Mama da Hamma Mussadiq fitowa a hanzarce, yana ganinsu ya sakeni, da sauri Nayi bayan Hamma Mussadiq Ina kuka Dan dukan Ya shigeni sosae, Hamma Mussadiq dakina Ya jani yayinda Mama ta Kalli Mus’ab tace 

“Mus’ab Nagode, Allah Ya saka da alkhairi” 

Daga Haka ta juya ta nufi dakina inda Hamma ke rarrashina, da kyar naci Abinci duk yadda nake daukin abincin. 

Mama na shigowa na kara bude baki Ina kuka, zama tayi gefena tace 

“Hikma” 

Dagowa nayi na dube ta sannan na share hawayena ina Kara kwabe bakina Dan ni auta ce kuma yar shagwaba ce, jikin Mama na kwanto ita kuma tana shafa bayana sannan tace 

“Banason ki Kara shiga sabgar Mus’ab kina jina? ” 

Kaina na gyada sannan ta Kalli Hamma Mussadiq tace 

“Je ka Nemo min Mus’ab yanzunnan” 

Tare suka mike suka fita na zauna na share hawayena na Fara cin Abinci abuna, Ina gamawa na shiga nayi wanka.  Inada wani abu matsawar zaayi min Abu nayi kuka a kuma rarrashe ni to ya wuce a gurina, har abada kuwa, bana riko I’ve a free mind, shiyasa Zaiyi wahala kiga abu yana damuna. 

Seda akai Sallar azahar sannan na fito parlor babu kowa se Anty Fadila da lion, naji kashedin Mama hakan yasa Ko inda suke ban kalla ba na nufi dining na dakko ruwa sannan na dawo na zauna gefe guda batareda nayi wani kwakkwaran motsi ba, channel din da suke kalla banaso amma Haka na share saboda gudun laifi. Can Anty Fadila ta dubeni 

“Hikma jeki ki zubowa Mus’ab Abinci mana” 

“Tohm anty” 

Na fada Ina satar kallonshi, wata muguwar harara ya zabga min, fuskarshi a murtuke yace 

“Idan kika kara a step se naci ubanki, Shegiya gurguwa” 

I hate it when I’m referred to gurguwa, Raina baci yake Har bansan na Harare shi ba, me neman kuka aka jefa da kashin awaki, aikuwa Ya Mike a fusace yayo Kaina, dama a tsaye nake hakan yasa naja da baya don neman tsira amma ko guri ban samu ba ya iso tareda sa kafarshi Ya take min kafata ta hagu, Anty Fadila da sauri ta Mike tareda isowa inda Muke tsaye idanuna har sun cicikko da kwalla saboda nasan tsabar mugunta ce kawai. 

“Mus’ab Meye Haka wai? Dan Allah ka saketa” 

Wani mugun kallo Yayi min sannan ya dawo da dubanshi gurin Anty Fadila wadda ta bata rai yace 

“Na tsani yarinyar nan, dangin mayu, wallahi I’m sure duk daga inda yarinyar nan ta fito mayu ne IYAYENTA” 

Ya fada yana emphasizing akan iyayenta, tuni na kura mishi idanuna lokaci daya naji wani irin abu yana mamaye min jikina duk kuwa da karancin shekaruna Wanda basufi 13 years ba. 

“Mus’ab at least yar uwarka ce, me yasa Kake irin Haka? ” 

Anty Fadila ta fada muryarta na nuna bacin rai, Kallona tayi fuskarta babu walwala ni kuwan tuni idanuna sun Fara zubar da hawaye, wata dariya Mus’ab ya saki irin ta rainin Wayo yace 

“Kin jiki da wata magana Fadila, waye yar Uwata? Wannan dangin mayun? Wannan yar tsintu….. ” 

“Stop it Mus’ab, Kai me yasa Kake Haka ne? ” 

Anty Fadila ta katseshi cikin hanzari kar ya karasa amma ina abin ya dakeni, Ya girgiza ni tareda sake saka zuciyata cikin wasiwasi. 

“Kinsan Dalili? Saboda I hate her! Ta karbe min dukkan Wasu Abu da nake kalla matsayin farin ciki, Dan Haka nayi alkawarin da hannuna zanyi destroying dinta Nima…. ” 

Tari mukaji hakan yasa mukai saurin kallan daga inda sautin yake, Baffa ne bayanshi Hamma Mustapha da dukkan alamu daga airport suke, ni tsabar abubuwan da Mus’ab ya saka ni bai Bari na tuna Yau ce ranar da Baffa zai dawo daga Calaba ba, inda yaje wani seminar. Dukkansu daga Hamma Mus’ab Har Anty Fadila Sunyi kuri da idanu, ni kuwa da sauri na shiga goge hawayen fuskata Don banga dalilin kukan ba, idan Har zan cigaba da kuka saboda Mus’ab ina ganin Har duniya ta nade Bazan daina ba, Ko a karamin tunanina ban kawo da gaske ya tsaneni Kamar yadda yasha fada amma Yau na yarda saboda kallon da yakemin irin kaga kashi dinnan. 

“Meye kuke a tsatsaye Kamar kuna fada, Uwata Meye kike kuka? “

Da dukkan alamu Baffa baiji abinda Hamma Mus’ab ya fada ba, I’m happy he didn’t sede zuciyata da hankalina sunki tsayawa guri guda, Murmushi na kirkiro na nufi Baffan tareda rungumeshi Ina fadin 

“Baffana oyoyo!”

Hannuna Ya rike yana kallon gidan Wanda na tabbatar Mama yake nema, hakan yasa nace 

“Sun fita itada Hamma Mussadiq”

Kanshi Ya gyada sannan muka karaso, Hamma Mus’ab ya riko hannunshi, ganin Haka na saki hannun Baffa na wuce dakina, kwanciya nayi akan gado nayi shiru bansan abinda nake tunani ba. 

Washegari kowa na gida, da wuri na tashi saboda Nama ko baccin bayan Sallar asuba bata barni na koma ba, ina zuwa a kitchen na tarar da ita da Anty Fadila sun rigada sun dau harama, Ina gaishesu ta miko min batter din pancake, nonstick na daura muka fara aiki sede Ina son magana da Mama har na bude baki Anty Fadila tayi beating dina

“Mama next week zan koma Inshaaa Allah”

Mama na juye kunun gyadar da ta gama cikin flask tace 

“Ina ce Se Hutu ya Kare zaki tafi? “

Shiru Anty Fadila tayi hakan yasa Mama fadin 

“Zan Kira Maryam muyi maganar”

Daga Haka muka karasa aikin, Anty Fadila ta fita se ya rage daga ni se Mama hakan yasa nace 

“Mama! “

Kallona tayi amma Se na kasa magana gaba daya naji nauyin abinda nake kokarin fada, kusa dani ta matso tace

“Yaya akai autar Mama? “

Shiru na kunayi Ina wasa da yatsuna sannan nace

“shi kenan ma Mama “

Hakan da nayi ya kara sakata a mamaki don ba halina bane boye abu ba, I’m always straight forward akan magana, zaunar Dani tayi akan stool itama ta zauna, har zatayi magana Se kuma taja hannuna muka nufi dakinta, a bakin gado muka zauna tace

“Fada min Menene? “

Hannuna nasa na share hawayena sannan nace

“Mama da gaske Wai ni ba yarku bace? “

Idanu Mama ta zaro, ta dafe kirjinta Tana Kallona cikeda Tsoro sannan tace

“Waye ya fada miki Hikma? “

Kuka sosae na Fara se naji ban yadda da Maganar ta ba, rungumeni tayi tana shafa bayana tace 

“Ya isa Kinji, kawaye ya fada miki to karya yake miki, mune iyayenki. Kin taba ganin wani abu da zai nuna miki hakan? “

Kaina na girgiza nace

“A’a amma me yasa ni kadaice Baka a gidannan?”

Dan Murmushi tayi tana min bayanin Haka Allah yake halittarshi amma ko daya kar na dauka hakan wani abu ne. Hakanan tayi ta lallashina Har Baffa ya shigo, lokacin na daina kuka hakan yasa ina gaisheshi na fita shi kuma ya zauna Yana fadin

“Me ya samu Uwata?”

Cikeda damuwa tace

“Ka Bari kawai, Tazo tana tambayar wai ko mune iyayenta na gaskia”

Idanu a warwaje cikin firgici yace

“Da gaske! Ya akai Haka? A Ina to…. “

Kawai se ya dafe kanshi cikeda damuwa, itama Mama da damuwar a fuskarta sede bata furta komai ba. Ganin zaman bazai karesu ba yasa suka koma parlour don cin Abinci, amma still fuskokinsu kadai zaka kalla Kasan akwai damuwa a tare dasu. Seda aka gama cin Abinci, no na Fara tashi don gaba daya raina a jagule yake. Anty Fadila ma bayana tabi muka koma daki, muna zama tace

“Hikzee”

Dagowa nayi da Murmushi Dan inasan a fada min sunan, nace 

“Me kike so? “

Dan nasan bribe ne, Murmushi tayi tace 

“Muje gidannan na jiya Ki kaimin sako”

Nima I’m bored hakan yasa nasa dankwali muka fito ta gefe muka fita se shagali na nake kamar ba ni nake kuka Dazu ba, muna zuwa Kamar jiya mukai knocking same buzun jiya ya fito, na gaisheshi sannan na Mika mishi letter nace

“Abdallah Zaa bawa Baba buzu”

Karba Yayi Har na juya yace

“yarinya wa Zaa ce mishi? “

Juyawa nayi nace

“Zainab”

Bansan me yasa na fada mishi sunana ba, wucewa mukai zuwa gida hakan yasa na dubi Anty Fadila nace

“Wai me muke kaiwa cikin letter din can? Waye Abdallah”

Murmushi tayi me kayatarwa tace

“Crush dina ne “

Ban masan me crush din yake nufi ba, Nima ban tambaya ba har mukaje gida. Ashe Tashin mu a gurin cin Abinci Baffa fada Yayi sosae akan abinda ya faru dani

“Duk Wanda Yayi Maganar nan tabbas Ya raina ni, amma I want to make something straight to everyone here, ko kuso ko ku ki Hikmah yata ce, ina jinta tamkar tsatsona and its been 12years Yanzun Ina boye abinnan duk Wanda ya Bari taji wannan labarin daga bakinshi se na Baku mamaki na gaske”

Dukkansu jikinsu Yayi sanyi ganin yadda Baffa ke fada abinda ba halinshi ba, kuma yasan Mus’ab kadai zai fadi hakan amma yana son ya Fara warning dinsu kafin komai. Sallamar Mus’ab da Hamma Mustapha yayi sannan ya kara gyara zamanshi yana duban Hamma Mussadiq yace 

“Ya zancen aurenka da Fadila “

Da sauri Hamma Mussadiq ya dago tareda fadin 

“I taught…. “

Da sauri Baffa ya katse shi da fadin

“What? An fasa? Zancen yana nan, aure babu fashi, inason zamannan da take ku saba da junanku kaji ko”

Kamar Zaiyi kuka yace

“Amma Baffa ni Hikma nake……. “

Wani mugun kallo Baffa yayi mishi yace

“Don’t blabber that nonsense kaji ko? Rukayya kiyiwa Danki magana”

Daga Haka Baffa ya Mike zuwa dakinshi, Mama na zaune Tana jujjuya kunun mug dinta Wanda Ya huce tuntuni, shikam Hamma Mussadiq da bacin rai yace 

“Wai Mama Dan Allah me yasa Baffa yake Haka, ta Yaya bazaku fadawa yarinya ba kune iyayenta ba, ita nake so a barni na jirata”

Kallonshi Mama take kafin tace

“Mussadiq babu ruwana a Maganar nan, tsakanin ku ne, zancen kana son Hikmah bana son kara jin Maganar, ka dauka Uwa daya uba daya kuke da Hikmah”

Hannunsa ya dunkule yace

“For goodness sake Mama, me yasa Allah Ya bamu uwa saboda irin haka, ke ya kamata ki tankwara Baffa amma kullum Se Kice babu ruwanki? “

Kallonshi tayi baki a sake tace

“To Sannu Ubana”

Daga Haka ta bar mishi dining din ta koma daki Tana hango kwamacala nan gaba, tunda Fadila bata san abinda ke faruwa ba. Shikam Hamma ya jima zaune a gurin kafin ya Mike cikin tsananin takaicin komai ya nufi dakinshi. 

Wasa wasa seda mukai kaman sati kullum Se munkai wannan letter da bansan ta mecece ba, Haka zalika bansan dalilin kaiwar ba. Ranar ta kama Alhamis babu islamiyya ina gida Mama ta sani a gaba seda ta tsefe min cukurkudadden Kaina, seda ta gama muka tafi toilet da kanta ta wanke min Inata bata rai da raki amma Haka ta wanke shi tas, tasa towel ta daure min sannan ta hada ruwa cikin bucket me dumi tace 

“Maza kiyi wanka Kinji?” 

Kaina na gyada mata, Itakuma ta fice daga toilet Din Baki daya, gaba daya se naji dadi da wata iska Tana shiga Kan. Sosae nayi wankan sannan na fito, a zaune na sameta Tana waya 

“Eh to idan Babansu ya dawo se ya fada mata” 

Banji abinda aka fada mata ba se naji tace 

“A’a Fadila bazata bamu matsala ba, amma Naso tuntuni ace tasan da Maganar ba kawai ace se Yanzun ba ” 

Can ta kuma fadin 

“Allah dai ya bamu nasara kawai, Bari na sallami Hikmah. Se Munyi magana a gaida Yara. ” 

Aje wayar tayi ta dubeni, ina tsaye na kafeta da ido, Kalloma tayi tace 

“Tsayuwar me kikeyi ne, zo ki zauna” 

Gefenta na zauna na shafa Mai sannan na dawo kasa na zauna Ta gyara min Kan sannan ta dakko min kaya, wani lace ne fari da blue na saka sannan na nufi dakin da Anty Fadila take, ina zuwa Naga Tasha kwaliyya, ta saka lace sak irin na jikina, zama nayi ina fadin 

“Anty Fadila Kinyi kyau” 

Murmushi tayi tace 

“Nagode Hikma, Hamma Mussadiq zan raka unguwa” 

Nima Murmushi nayi mata nace 

“Iyeee Kinyi kyau kuwa, se Kun dawo” 

Kanta ta gyada Tana Kara bada turare a jikinta Wanda Har ya Fara damuna, itakam yar gayu ce, gata kamanninsu daya dasu Hamma Mussadiq din shiyasa idan kazo gidanmu ni dince dai Odd a ciki, da babanta da Baffa Uwa daya uba daya suke immediate brothers ne. 

Tare muka fito se Naga taja hannuna mun koma sannan ta ciro wata paper Kamar kullum tace 

“Ki kaiwa Abdallah” 

Babu musu na amsa, muka fito Har main parlor inda Hamma Mussadiq ke tsaye fuskarshi a dinke babu ko digon  annuri, hakan kuwa ba halinshi bane, mutum ne very jovial and nice. Nima se na shiga taitayina, na samu cushion na zauna ina wasa da jelar gashina da ta fito, Kamar daga sama naji yace 

“Tashi ki dakko hijab kizo muje kema” 

Dagowa nayi nace 

“Ni? ” 

Na fada Ina nuna kaina, harara ya wurgo min yace 

“A’a ni” 

Kallon Anty Fadila nayi naga Tana kyafta min ido Don itama tunda muka Kalli fuskarshi ta shiga hankalinta don naturally ita dashi basu fiye shiri ba, su basu fada kuma ba wani dasawa suke ba. Daki na nufa na dakko mayafin kayan amma kafin na karasa mukai karo da Mama Tana fitowa daga daki hannunta da wata Leda, Kallona tayi tace 

“Ina zakije na ganki da hijab? ” 

“Hamma Mussadiq ne yace na dakko zamu fita” 

Ba tace min komai ba ta nufo parlour nan Nima na biyo ta, Tana zuwa tace dashi 

“Tsayuwar me kuke Har Yanzun baku tafi ba?” 

Ranshi a bace yace 

“Hikmah muke jira” 

Hararar shi tayi sannan tace 

“Musaddiq ka fita a idanuna kaji ko? Bana son taurin Kai. Tohm” 

Baice komi ba yayi gaba abinshi, itama Anty Fadila da sauri ta take masa baya, seda mukaji fitarsu a Mota sannan Mama tace dani 

“Kinsan gidan Hajiya Talatu? “

Kaina na gyada, matar kawar Mama ce anan bayan layinmu suke, ledar ta bani tace

“Ki kai mata”

Amsa nayi cikeda jin dadi zan fita in samu kai sakon Mama, seda nasa hijab ta rakoni har bakin parlor Tana min kashedi akan kada na tsaya Ko ina, tasan da gagan take don matar nada sa’ata Indai naje bana dawowa da wuri, shiyasa bata son aikena se su Hamma. 

Gidan na Fara zuwa, bayan na gaisheta na bata sakon sannan na taho tunda Fannah  din basu nan, straight gidansu Abdallah naje ,Kamar kullum nayi knocking maimakon Baba buzu se wani matashin saurayi fari, kyakyawa kyau me sunan kyau, babu tantama shidin ya hada iri da buzaye Don lebenshi pink ne, gashin kanshi a kannanade yake, kina kallon fatarshi kinga ajebutter Dan gayu dashi. 

Bansan Inata kallonshi ba seda ya saka hannunshi Yayi waving akan fuskata sannan na dauke idona da sauri inajin yadda jikina ke kyarma, ba wani Babba bane Dan bazai wuce saan Mus’ab ba ko ya girmeshi da shekara daya, tsayuwarshi ya gyara yace

“Se kallona kike ,kin sanni ne?”

Da sauri na girgiza mishi Kaina, cikeda in Ina nace

“Da…da.. ma gurin… Ab….dallah aka aiko ni”

Girarshi ya dage min yace

“Kece Zainab? “

Da sauri na gyada Kaina, Se Naga yayi Murmushi Harda tafa hannunshi sannan yace

“Kece kike kawo letters kina sona Ko? Kece Ko?”

Ya fada yana nufo inda nake, da sauri na shiga ja da baya idanuna a warwaje nace 

“wallahi aiko ni akeyi”

Ya wani bata rai yace

“Ina wadda ta aiko ki din?”

Kaina na girgiza amma bai barni nayi magana ba yace

“Se na kaiki Har gida na fadawa Mamanki abinda kike”

Jin Haka yasa na fara kuka ina rokonshi amma mutuminnan Kamar zuga shi nake haka ya tiso keyata har kofar gidanmu, zuciyata Kamar zata fito tsabar yadda take bugawa, hawaye kuwa dama wannan ai a kusa yake, Se fita yake Kamar lalataccen famfo, muna isa na jiyo Ina kuka sosae nace

“wallahi bani nake turo maka ba, Nima aikoni kawai takeyi, kayi hakuri Mama dukana zatayi”

Kanshi Ya gyada tareda nuna ni da yatsan shi yace 

“Next time kika kara Se na zaneki sannan na kawo ki har gida kinji?”

Da sauri na gyada Kaina sannan na shige gida da sauri ina goge hawayen fuskata sannan na karasa, straight fridge naje na sha ruwa sannan na wanke fuskata a sink kafin na sanar da Mama na dawo. Dakina na wuce na dakko letter na buda Ina karantawa, gaba daya content din Ya girmi kwakwalwar Kaina, ninke wa nayi Inata yiwa Kaina Murnar Mama bata samu labari ba, sannan ina tunanin yadda zamu kwashe da Anty Fadila idan ta dawo. 

Se da aka idar da Sallar Maghrib sannan suka dawo, lokacin muna tareda Mama Ina bata labari mukaji sallamarsu, da murna na Mike amma ganin mood dinsu yasa na koma na zauna babu shiri, suna cewa Mama sun dawo Duka sukai daki nasan sallah zasui, Nima assignment dina Na islamiyya na dakko ina fitarda Tajwid din dake suratul Anfal. Har akai Sallar ishai mukai sallah Anty Fadila bata fito ba, duk babu dadi hakan yasa nace

“Mama Bari naje Naga me Anty Fadila takeyi”

Kanta ta gyada min saboda lazumi da takeyi, dakin na wuce na tura kofar na shiga bakina dauke da sallama, gaba daya dakin a hargitse yake, duk ta fito da kayan ta daga wardrobe Tana zubawa cikin trolleys dinta, dake tayi kusan wata uku a gidanmu, da sauri na karasa Ina fadin 

“Anty Fadila Meye kike hada kaya”

Sautin kukanta kawai naji hakan yasa na karasa jikina a sanyaye na riko hannunta ina fadin

“Menene Wai? “

Hannunta ta karbe daga nawa batareda ta kulani ba ta cigaba da abinda take kuma Se kuka take, na dade a tsaye har ta gama sannan tayi zipping dukkansu kuma bata daina kukan ba

“Bari naje na fadawa Mama tunda bazaki daina kukan ba”

Na fada Ina nufar kofa, ji nayi ta ture ni sannan tayi locking kofar tana harara ta, hawaye na zuba, abin se ya bani dariya har nayi Murmushi, hannuna taja muka zauna Kan gado tace

“Hikmah Wai Hamma Mussadiq zan aura kuma nan da wata daya”

Ai mikewa nayi na buga tsalle ina fadin 

“Shi ne kike kuka? Yeeeee ni ta koina, Ango Hammana, Amarya Addata. “

Duka ta sakar min a bayana tace 

“Bakida hankali, Yanzun da muka fita cewa Yayi Wai Baya sona fa Hikmah”

Se naji Banji dadi ba hakan yasa nace 

“Ki rabu dashi, wasa yake miki Gaki kyakyawa waye zaice baya son ki”

Tana son a koda ta Aikuwa taji dadi, da wasa da dariya nasa ta maida dukkan kayan wardrobe, muka bude ledar da suka shigo da ita, Burger ce guda uku, Se kaza gasashiya guda biyu, yoghurt da juice masu sanyi. Abin nema Ya samu zama na gyara na dauki burger daya na kai bakina, lumshe ido nayi saboda dadi daya dakeni, Duka Anty Fadila ta kaimin Tana fadin 

“Dadina dake baki ganin Abinci kiyi wasa dashi”

Dariya nayi nace 

“Food is life ai!”

Karkashin pillow ta daga ta dakko Tawa ta sameni Wanda take karanta mana nida ita, a zuwanta novels din Hausa da muka karanta bazasu kirgu ba, ita a gidansu ita kadai ce shiyasa take abinda take so, ni kuwa nasan duk ranar da Mama ta ganni to kashi na ya bushe. 

Munata Karatu ina buga tsalle idan akai wani show din dake a part 3 muke, ga kaza Inata ci Ina korawa da juice Ashe mun manta bamu rufe kofa ba, Mama taji Shiru Ta biyo mu, tsabar yadda muka zama engrossed Ko sallamar da tayi bamu jiba se jinta kawai mukai tana fadin 

“Me kuke karantawa? “

AI tsabar tsoratar da nayi se na Fara tari, Mama tayo Kaina anan Anty Fadila ta boye littafin, A’a abu Kamar wasa se na Fara numfashi samasama, ina janshi da kyar, Mama a rude tace da Anty Fadila 

“Jeki dakko ruwa”

A guje ta fita se Gata ta dawo da ruwan roba, da kyar nasha ruwan amma bai lafa ba, hakan yasa Mama tace

“Jeki ki kira min Musaddiq muje asibiti”

Hijab ta dauka tayi waje, Haka ta saka min Hijab Nima ta kamo hannuna hankalinta duk a tashe, Hatta Hamma da yazo seda ya tsorata, a gaggauce muka shiga Mota, zamu fita gate motar Baffa zata shigo, lekowa Yayi yana fadin 

“Lafiya? “

Kafin a bashi amsa yace

“Subhanallah! Me ya samu Uwata?”

Mama ce tayi briefing dinshi, Mota ya koma Se asibiti, A emergency aka karbe ni,  allurai akamin a hankali se numfashi Ya fara daidaita Nima na dawo daidai. 

File aka bude min sannan doctor Ya karbi history daga wajen Mama anan take fada mishi yadda nake mura kullum kullum, daga baya ya gama rubuce rubucenshi yace da Baffa ai Asthma ce dani, amma zamu dawo ayi gwajegwaje Don a tabbatar da komai. 

Haka muka dawo gida da tulin magunguna da dokoki, Tundaga ranar Mama ta Kara kaffakaffa Dani, Munje Munyi test aka tabbatar ita ce kuwa. 

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]