[Advertisements⬇️]

HIKIMA CHAPTER 1 - Bankinhausanovels
Thu. Jun 8th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

HIKIMACHAPTER 1

October 1995

“Lokuta da dama Allah yakan rufe mana wata kofar saboda ya bude mana wata kofa, Aminu me yasa bazaku manta da wannan rashin haihuwan ba ku rungumi kaddara? Komai na rayuwa MUKKADARI NE ”

Wani mugun kallo Wanda aka Kira da Aminun Yayi, yana Sanye cikin Grey suit, wadda ta Kawata farar fatarshi, kana kallonshi kaga Wanda yake cikakken Dan Boko me akida, Dan gayu Wanda rayuwa tayi musu Afuwa, yace

“Kasan dalilin da yasa na fada maka plan dina? Saboda you are more than a friend to me! Amma Meye zaka dinga Wasu maganganu, seda nayi tambaya abinnan ba Haramun bane ko? Habibu Baka San ciwon Infertility ba, especially idan problem din daga gurinka yake, bazaka gane kuncin da zuciyata ke ”

Zama Habibun Ya gyara bayan Ya rage volume dim TV dake parlon, inda ake Watso labarai daga AIT channel, the discussion is getting hot! Habibun ya furta a sanyaye kafin yace

“Bansan ciwon rashin haihuwa ba, amma inajin a jikina it’s a painful thing, Abu daya nake son ka gane Aminu, Allah kadai yasan dalilin hanaku haihuwa, may be babu alkhairi a ciki”

Wani tsaki Aminu Ya saki tareda fadin

“See you! Ta Ina ‘Ya’ya suke zama matsala, bantaba ji ba Habibu, its final jibi jirginmu zai tashi zuwa Germany”

Kai Habibu Ya girgiza Don yafi kowa sanin kafiya da kuma akida irin ta Aminu amma Yaya Zaiyi? Hakan yasa yace

“All the best aboki, to kui adopting mana”

Kai ya girgiza yace

“No! ”

Handshake sukai daidai shigowar Lubabatu matar Habibu, cikeda faraa ta karaso sitting room din inda ta zauna gefen mijinta Wanda Tun shigowarta dukkan hankalinshi ya koma kanta.

“Tsoka daya a miya! Uwargida ran gida, kiyi yadda kikeso matar Habibu!”

Ta rigada ta saba jin kirarin Aminu akanta, shiyasa take sonshi a abokan mijinta, Har cikin zuciyata kirarin ke kaiwa, Murmushi ta saki tareda kwantar da kanta kafadar Habibu Wanda yake kallon yadda farinciki ke kwance fuskarta tace

“Barka da zuwa Aminu, irin zuwa babu sanarwa Haka? ”

Dan Murmushi Aminun Yayi yace 

“Ki Bari kawai, gidan Yayi Shiru Ina Yaran suke ” 

Wannan Karon Habibu ne yace 

“Suna can gurin grannies dinsu, we need a break, ko ba Haka ba darling? ” 

Ya fada yana kashewa Lubabatu ido tareda sake matso ta da jikinshi. Tsaki Aminu Ya saki tareda fadin 

“Allah Ya sawwake muku, I wonder yadda zan dauki Dana na kaishi Hutu wani gurin, that’s impossible I guess! Kukansu ma Rahama ne! ” 

Cikeda tausayawa Lubabatu tace 

“Ayya, lokaci ne Aminu, a jikina inajin zaku haihu Kasan Allah is the perfect planner, Ku cigaba da addua” 

Take fuskar Aminu Ta kara liting da wani murmushin, tabbas duk duniyar nan yana girmama Wanda zaice Yana da hope akan zasu haihu, shima kanshi yana ji a jikinshi zai haihu to amma he can’t wait anymore, yana bukatar jin kukan jariri Ko jaririya a gidanshi. 

Story continues below


“Ke kadai ce babu Kari, kuma duk ranar da Habibu Yayi gigin aure zai sha mamaki na” 

Duk seda sukai dariya saboda Haka Aminu yake commedian ne idan yaso, kudi ya ciro daga suit pocket dinshi Ya aje musu tareda fadin 

“A siyawa cutie pies dina chocolate, Habibu muje ka kaini airport kada nayi missing flight dina” 

A tare suka mike dukkansu, Aminu Ya dauki briefcase dinshi, Habibu Ya dauki car key dinshi yayinda Lubabatu take bada sakon gaisuwa zuwa ga Hafsa da kuma godiyar kyautar da yayiwa yaranta. 

Murtala Muhammad Int’L Airport dake Birnin Lagos nan ya kaishi ganin duk yadda zaiso Aminu Ya saurareshi yaki yasa kawai Yayi masa fatan alkhairi ya juya gida shi kuma ya nufi departure hall, ana kammalla screening jirginsu Ya tashi zuwa Babban Birnin tarayya Abuja. 

“In-law bantaba son aurenki da Bro ba saboda banzar akidarku, shi har Yanzun yana Abu tamkar a America yake, ke kuma har Yanzun jinin Americans na yawo cikin Veins dinki. Ina ku Ina yin abinda……” 

Da sauri Hafsa ta katse ta da fadin 

“Haramun ne? Ba Haramun bane In-law we just gonna help ourselves have a baby shikenan fa! ” 

“In-law Allah Ya bada saa, Ya bayar da me albarka, yaushe ne  tafiyar taku? ” 

Seda Hafsa ta kurba juice din dake gabanta kafin tace 

“In one week time zamu wuce, Ina fatan zaki daina bacci kiyi mana adduar nasara” 

Murmushi Salima tayi tace 

“Wannan dole ne In-law, Allah Ya bada nasara” 

Hakanan suka cigaba da hirarsu cikeda aminci, su din kawaye ne, Yan Uwa, aminai kuma surikai. Akwai kyakyawar alaka tsakanin biyun. 

Suna nan zaune Har lokacin Sallar laasar tayi suka Mike suka sauke faralli kafin Hafsa ta shirya Don komawa gidan Dan tasan duk inda Aminu yake to tabbas Ya taho. Seda tayi wanka ta bade jikinta da turarruka sannan ta canja kayan da Tazo dasu kafin suka fito itada Salima wadda ke ta koda ta, tayi kyau babu karya usulin kamaninta na black Americans din Ya fito, ga wani smooth da jikinta Ya Kara yi Se glowing yake, kana kallonta ba se an tambaya ba kaga yar gatan miji, yar gayu me ji da kanta. 

Karfe hudu da Rabi ta isa gidansu dake jerin gidajen dake cikin Gwarumfa, ciki ta shiga straight dakinta inda ta sake gyara kanta kafin ta dawo parlor jiran Mijinta, Baifi mintina ashirin ba taji shigowarshi, cikeda yanga da yauki ta nufe shi tare da fadawa jikinshi, shima rungumeta Yayi yana yadda sassanyan kamshi yake dukanshi Wanda yake fitowa daga jikinta yana penetrating hancinsa, jikinta ta janye tareda karbar suitcase dinshi tace 

“Welcome home darling” 

Fuskarta ya shafa yana Murmushi yace 

“Thank you Wife, Lubabatu na gaisheki” 

Wani murmushin ta Kara saki tace 

“Ina amsawa, Inasu Iman? ” 

Kanshi ya girgiza lokacin suna nufar bedroom yace 

“Sun kaisu Kano, Ya Salima? ” 

“Tana gaisheka ” 

Ta bashi amsa Tana Zare Necktie din wuyanshi, a Haka yaje Yayi wanka ya shirya suka dawo parlor suna kashe kansu da soyayya. Ana kiran sallar Maghrib ya fice ita kuma tayi a gida sannan ta nufi kitchen ta hada musu abincin dare. 

Germany 

Karfe shida na safiyar Talata, Turkish Airlines Wanda Ya dakko passengers daga Birnin Lagos din Nigeria zuwa Germany, cikin passengers din akwai Aminu da Hafsa Wanda suna cikin mutanen da suka yiwa kasar ta Germany tsinke. Hafsa kanta na kafadar Aminu Wanda yake duba wani magazine da ya siya a trans in dinsu a Berlin, gyara zamanshi Yayi tareda kallon fuskar wadda duk duniya Ko fushi yake Ya kalleta Se yaji sanyi a zuciyarshi, Hafsa kenan matarshi tsoka daya a cikin miya, yana jin Bashida abinda ya kaita bayan iyayenshi. Gyara kwanciyarta tayi jin Aminu yana kici kicin daura mata seat belt saboda landing da jirgin Zaiyi, Idanunta ta bude Tana kallon Aminu, jin Idanunta akanshi yasa ya dubeta tareda sakin mata Murmushi yace 

“Sleepy head, kin tashi” 

Kanta ta gyada batareda ta furta komai ba, jirgin na tsayawa bayan an gama komai aka bawa passengers Damar fita, cikin nutsuwa dukkansu suka fito kowa yana duban inda zai ga nashi, Arrivals sukaje inda akai clearing dinsu da kayansu kafin suka samu cab ta kaisu hotel din da ya riga Yayi musu booking, suna isa wanka sukai se bacci bayan sun biya sallolin da suka bisu, Dama babu batun Abinci Haka suka kwanta sukai ta bacci har bayan azahar shima Yunwa ce ta tashesu. Wanka sukai sannan sukai sallah kafin ya Kira room service suka kawo musu abinci. Hafsa kam komawa tayi ta nade cikin bargo Ta koma bacci, duniyar nan Hafsa na Kaunar bacci a rayuwarta, Tana ganinshi Abu me matukar muhimmanci a rayuwarta. 

Aminu fita Yayi inda balcony yake yana kallon garin, a tsayen da yake xakai tunanin iska yake sha Ko kuma yana enjoying abin sede hakan daban yake da anxiety dake damunshi, zuciyarshi ta kasa nutsuwa yana ganin Ko Yaya zata kasance a asibitin, Ko Yaya aikin zai kasance……. Hannu yaji ansa an rungumeshi hakan yasa ya juyo dukda sanin Hafsa ce to amma yasan he left her sleeping, yana juyowa idanunsu suka sarke a na junansu, Murmushi take masa kafin ta sakeshi Tazo gefenshi ta tsaya itama Tana karewa Garin kallo 

“Se yaushe zaka daina damun kanka ne? Se yaushe hankalinka zai kwanta?” 

“Bansani ba nima Hafsa, sede Ina jin Tsoro! ” 

Ya fada muryarshi fal tsoron, hannunshi ta kamo cikin nata Tana shafawa da dayan hannun nata tace 

“Tsoro kuma? Tsoron me? ” 

Juyowa Yayi yana kallonta yace 

“What if it fail? Zaki cigaba da zama da Wanda baya haihuwa? ” 

“It will not Inshaaa Allah, it will be successful, Ko da bamuyi nasara ba, nayi maka alkawarin kasancewa a tareda Kai Har abada, mutuwa ce zata rabamu ” 

Ajiyar zuciya ya sauke me nauyi tareda sake rungumeta a jikinshi, yana jin Anya akwai abinda zai iya rabasu? 

“Wanne suna zamu sakawa banynmu? ” 

Dariya Hafsa tayi tare da dan buga bayanshi tace 

“Azarbabi Ko? Ma Bari ayi aikin Se mui deciding” 

Kanshi ya girgiza yace 

“Kai! A’a Yanzu dai” 

Harararshi tayi tace 

“Kai ka sani kuma” 

Daga Haka ta wuce cikin dakin Tana dariya, bayanta ya biyo yana fadin 

“To fada min sex din da kika fi so” 

Zama tayi bakin gadon dake dakin tace 

“Mace mana, do you need to ask? ” 

Kwanan su Aminu da Hafsa biyu cikin Garin na Germany, babu inda suke zuwa banda daki, shi ne ma Ya fita Nemo musu sabon SIM saboda suyi communicating da gida, yana siyowa ya dawo inda suka cigaba da kashe junansu da soyayya, they’re very romantic couples Wanda da ace hakan shi ke kawo haihuwa bana tunanin zasui shekara bakwai da aure ba tareda sun haihu ba, amma Allah shi ne Allah! Shi yake tsara mana yadda rayuwarmu zata kasance shiyasa ya jarabce su da hakan. 

Alarm din dake gefen gadon nasu ne ya Fara bugawa saboda setting dinshi da akai Ya buga a kowacce sallah don idan zasu biyewa timing lallai bazasu yi sallah ba. Hafsa ce ta Fara yunkurawa ta mike tareda fadawa toilet Don daura alwala, seda ta kammalla sannan Aminu Ya shiga yana fitowa Ya jasu sukai sallah sannan suka koma. 

Karfe takwas suka kammalla duk wani shirinsu don wannan ce ranar appointment dinsu da Doctor da zai musu aiki. Seda sukaci Abinci kafin suka biyo lift suka sauka kasa, Asibitin baifi 10 meters bane daga hotel din, hakan yasa suka wuce da kafarsu suna ta hira wadda duk yawanci Aminu keyi akan Babynsu ita kuma tana dariya don duk yadda take zumudin babyn Aminu yace bani guri don kullum zancen yake. 

Cikin nutsuwa Baturen doctor Ya gama duba file dinsu, lokacin ya dago idanunshi Ya sauke Kan Hafsa da Aminu da suka tsira mishi ido, cikin turanci dinsu Ya Fara musu bayanin yadda procedure yake 

“It’s my pleasure having you here, na duba file dinku bayan test da kukai running Ya nuna mana male partner yanada low sperm count, while female partner lafiya take, gashi Kunyi signing Kun yadda da aikin Ko? ” 

Aminu Ya dubi Hafsa sannan yace 

“Yes! Mun yadda amma baayi briefing dinmu yadda procedure din take ba, chances na nasara, failure da adverse effects dinta” 

Kai Doctor din Ya gyada tareda sake gyara zama yace 

“Intrauterine Artificial Insemination, procedure ce da ake yi don addressing Infertility, Yanzun Zaa duba lokacinda ya dace ayi aikin, lokacinda mahaifar ki zata fi karbar ciki, zaka bamu Sperm sample dinka Wanda Zaa saka a mahaifar ta, akwai chances me karfi na nasara, side effects very few ne, kuma ido biyu akeyi” 

Wata sassanyan Ajiyar zuciya Hafsa ta saki Don duk tunaninta yanka ta zaayi ayi aikin, hannun Aminu ta sake damkewa cikin nata hakan yasa ya gyada mata Kai alamun karfin gwiwa, basu fito daga office din Doctor ba seda sukai clearing dukkan doubts dinsu kafin akaje inda Hafsa ta kara running Wasu test, kwanaki goma Ya basu da magunguna na Fertility suka koma masaukinsu. 

Bayan Sallar ishai suka fita waje Don shan coffee Dan dukkansu biyu addict ne, da wuya kaga daya na son Abu daya baya so, perfect couples ne Wanda suka fahimci kansu sosae, a zamansu Hafsa zata iya irga sau nawa sukai fada, dukkansu free minds ne dasu shiyasa ko sun samu matsala there and then kowa zai fadi abinda ke ranshi. Matsalarsu daya wannan rashin haihuwar itama sune suka damu don kuwa kullum suka shiga dangi kasamcewarsu dangi daya yasa duk inda suka shiga Baki ake basu kada su damu haihuwa lokaci ne. Shekarar da ta gabata Baban Aminu Yayi suggesting suje Germany tunda anan an rasa daga Ina matsalar take, suna zuwa akai komai anan aka gano daga Aminu take, nan hankalinshi Yayi masifar tashi dukda Hafsa na nuna mishi itafa matsawar zata zauna dashi to haihuwa ba komai bace, bayan sun dawo Baban Aminu yace lallai Se an raba auren Dan kada a cuci Hafsa, Anga Tashin hankali marar misaltuwa kada ma Hafsa taji labari. Wannan yasa Baban Hafsa matsayinshi na Babba yace a kyalesu tunda sunji sun gani sun amince. Haka rayuwar ta cigaba har Aminu yace suje suyi Insemination dinnan, babu Wanda suka shawarta Haka suka taho abinsu saboda sunsan family dinsu babu Wanda zai yadda da hakan. Hakan yasa sukai yin kansu saboda suna ganin shi ne kadai mafita a tare dasu. 

Story continues below


“Idan na haihu wa Kake ganin zaka fi so? Ni ko babyn? ” 

Hannunta ya riko yana kallonta cikin ido, da nashi idanun masu saka zuciyarta narkewa yace 

“Ke mana! Babyn ai Bakuwa ce” 

Murmushi tayi tareda bashi peck tace 

“I love you man!” 

“I love you wife” 

Suka karasa shan coffee se suka koma ciki Don bacci, Suna shiga dakinsu Hafsa ta shiga tayi wanka da dukkan abinda ta saba kafin kwanciya sannan ta fito, shima wankan ya shiga, fitowarshi Har ta shirya Tana Dan gyara dakin. Seda ya shirya kafin ya bude system dinshi, Tana ganin Haka ta wuce gado don tasan aiki Zaiyi, shi din kuwa Yayi, ya jima yanayi kafin ya kashe system din Ya dawo gefenta ya kwanta batareda Yayi abinda zai tasheta ba. Sede kallonta kawai Da yake yana jin yadda zuciyarshi ke kara budewa sonta na shiga, hannunshi yasa ya shafa bakaken lashes din Idonta da suke a mike ya taba, Kana kallon Hafsa Kasan a yarenta akwai tambaya, Tashin farko mutum bai isa Ya sata a category wani race group din ba, saboda an samu hadakar yare aka haifar da ita, hakan yasa bazaka taba cewa itada Aminu cousins suke ba saboda kammanin kowa daban. Maman Hafsa black American ce wadda ta musulunta dalilin kawarta iyayenta suka Kore ta, Baban Hafsa Wanda usulin barebari ne na maiduguri yaje Karatu Ya dawo da aurenta, bayan anan ya bar uwargidanshi da Yaya uku, hakan yasa Hafsa yin Baki tunda gaba daya iyayenta bakake ne kada ma Babanta yaji labari, Aminu mahaifiyarshi bafullatanar Adamawa ce, a gidansu zakaga mixture wannan fari wannan Baki, anan Aminu Ya samo kammanin da yake dashi. 

Hannunshi yakai bakinta hakan yasa tayi juyi tareda ture hannun nashi, Murmushi yayi don se ta tashi hakan ya kudurce, a hankali ya dinga yawo da hannayenshi duk sensitive part dinta babu shiri ta Mike zaune Tana turo bakinta, Idanunta Sunyi jawur saboda bacci tace 

“Haba Dear! Bakaga bacci nakeji ba?” 

Ko kulata baiyi ba ya hade bakinsu guri daya, itama tasan halin mijinta dole Haka ta hakura da baccin don aure sacrifice ne, you can sacrifice anything for your partner. 

Suna kammalla Sallar Asuba sukai wanka sannan Yayi musu order Abinci amma Hafsa tea kadai ta iya sha, shi ne ma yadan taba French fries din. Kallon agogo Yayi yaga sunada wajen 3hours ya rage hakan yasa ya dakko system dinshi Don duba mails dinsa, Se da yayi Dana sanin hakan Dan kuwa Email din Baban Hafsa dashi ya Fara cin Karo, yana dubawa Ya zare glasses din idanunshi jikinshi har wani rawa yake Ya Kara kallon sakon yasan tabbas zai aikata abinda ya fada, da sauri Yayi slamming system din tareda runtse idonshi a take kuma wani Tsoro ya kara Kamashi, yasan waye Alhaji yasan abinda zai iya. 

“Dear! Menene Naga mood dinka Ya canja all of a sudden? ” 

Hafsa ta fada tana dafa goshinshi, idanunshi da suka riga sukai ja Ya bude tareda riko hannunta yana kirkirar Murmushi yace 

“Bansan yadda zata kasance ba, I’m nervous! ” 

Zama tayi gefenshi tareda daura kanta a kirjinshi tace 

“Please don’t be! Let’s all have fate! ” 

Kanshi Ya gyada alamun Ya gamsu amma a Kasan ransa Tsoro ne fal ciki. Sun jima tana bashi Baki Har lokacin Yayi suka wuce asibiti, babu bata lokaci akai implantation aka gama, seda aka bata Hutu ta huta kafin aka sallamesu suka dawo gida. 

“Hafcy, Kinzo da visa dinki ta America? ” 

Hafsa dake kwance tayi saurin dago da kanta tace 

“Me zaayi da ita? ” 

Zama yayi gefenta yace 

“America zaki tafi…. ” 

Da sauri Ta tashi zaune tace 

“Dalili? Nace inason Naga Mum ne? ” 

Girgiza Kai Aminu Yayi, jikinshi a sanyaye yace 

“Hafcy, Ki saurareni and please reason with me, dazun Naga email din Alhajin sama( Baban Hafsa) Yayi min, I dunno Wanda Ya fada mishi munzo Germany a Dasa miki ciki, yace Ko Anyi Se ya zubar da cikin… ” 

Hawaye sosae Ya Fara yiwa Hafsa zarya a kumatu, Meye kuma ya taso Haka? Hannunta Aminu Ya kama yace 

“Hafcy go to California gurin Mum, itada Dada kadai zasu iya kula mana da cikin jikinki, Dada is stuck a cikinsu babu abinda zata iya amma Mum can do it, idan na gama handling dinsu Seki dawo mu reni cikin” 

Kai Hafsa ta girgiza Tana kuka shabe shabe tace 

“Ba Haka mukai dakai ba, lokacinda mukai aure Munyi alkawarin fuskantar kowanne kalubale tare, ni da Kai da abinda aka dasa min Yau we’re a team, tare Zamui komai, Zan bika Nigeria tare muyi facing Komai tare! ” 

Kanshi Ya girgiza sanin halin Hafsa akan kafiya da naci, yasan zaayi Haka amma yasan Alhaji tunda ya furta zai iya abinda yafi zubar da cikin kowa yasan tsaurin shi, hakan yasa suka boye Mai asalin zuwansu Germany. 

Ita yar Alhaji ce tasan abinda zai iya da Wanda bazai iya ba, mutum ne me tsaurin gaske, Tana kallo Mum ta koma California amma mirsisi ya hanata bin Mamanta sede duk December taje ta dawo, seda Tasha kukanta Dan ta Fara hango masifar dake kokarin binsu tunda Alhaji ya samu labari, a hankali muryar ta na rawa tace da Aminu 

“Kayi booking next flight zan tafi” 

Rungumeta Yayi yace 

“I love you Hafcy ” 

Kafin ya saketa Yayi waje, a gurin ta durkushe Tana kuka Har seda kanta ya Fara ciwo kafin ta tashi ta tattara kayanta, ta hada mishi nashi, ta dade Tana jin Inama ba Alhaji Ya haifeta ba, a tsaurinshi yake shiga hakkin mutanen dake tareda shi, shiyasa kullum Mum dinta na cewa 

“Hafsa da Abbas an halliceshi zamanin Annabi Musa bana tunanin he’ll believe in him, saboda kafiya da naci irin nashi” 

Wanda duk Yayansa Hafsa din ce ta gado wannan shima bawai sosae ba. Karfe Tara na dare jirginsu Hafsa ya tashi zuwa America, Ko mum bata fadawa ba don itama bata hayyacinta, tunda ta suka tashi cikinta ke hautsinawa ga zazzabi da ya rufe ta, Wanda tasan side effects din implantation dinne, hakan yasa tayi lum a kujera tareda rufe idonta sede Ko awa biyu bata cika ba, ta Fara amai Wanda Ya jawo hankalin hostess din nan aka Fara bata taimakon gaggawa! 

Tsakar rana Hafsa ta isa California, ta jigata matuka saboda aman da tayi ga zazzabi da rashin sukunin zuciya. Jikinta Sanye da katuwar jumper wadda wata baturiya ta bata cikin jirgi ganin yadda take karkarwa, Haka ta fito daga jirgin a arrivals ta tsaya inda ta jira luggage dinta ta karba sannan ta tari cab Se gidan Mum, yana ajeta ta biyashi Allah Ya taimaka a cikin purse dinta ta taba Tahowa da dollar daya hakan yasa ta biya sannan ta tura karamar kofar ta shiga, Idanunta lokacin da kyar take budesu Haka ta karasa main entrance din sede a kulle me nuni da cewar Mum bata gida. Zamewa tayi a gurin ta zauna don batada karfin yin wani abin kuma, a hayyacinta tasan ta jima a gurin Tana jin tamkar ana sassara mata kasusuwanta, hakan yasa ta kudundune a gurin daga karshe zamewa tayi ta kwanta tare da kulle idonta daga nan bata kara sanin inda kanta yake ba. 

Mum wadda bayan ta musulunta sunanta daga Anita ta koma Asiya, tunda Alhajin sama ya saketa Ta dawo California ta Fara rayuwarta ita daya Dama Journalist ce, daga aiki se idan tana Hutu zataje Michigan State inda anan ne iyayenta suke zataje ta gaida su tunda tasan hakkinsu a musulinci, dukda shekaru kusan talatin da faruwar abin amma Har lokacin basa Sakar mata fuska har Yan uwanta suma. Tun abin yana damunta har ta watsar ta rungumi sabuwar rayuwarta. 

Cikin motarta kirar Beetle take driving zuwa gida, Don taje wani company ne dakko rahoto, company sunayin Bulb na wuta, to mutane na korafin bindiga da Bulb din keyi har akai musu zanga zanga ta lumana, shi ne daga office ta dakko rahoto ta aika musu ta taho gida. Tana zuwa Taga kofar a bude, seda taji dum Dan tasan bata rufe ba saboda sauri amma ta karo kofar, gate ta bude Ta shigo da motar, seda ta fito na Kare mata kallo, lallai Allah Yayi halitta Dan wannan older version din Hafsa ce, Kamar ta baci, Tana cikin suit tasa karamin veil ta yane kanta dashi, dake skirt ne bai wani nuna jikinta ba, tayi kyau sede Ta manyanta koda idan mun duba Hafsa ma ba yarinya bace. 

Seda taxo doorstep din nata sannan ta lura da abinda yake yashe a kofar, daga kafafuwanta ta gane Hafsa ce, lokaci daya ta rikice gaba daya tareda sakin abubuwan hannunta tayi kanta sede Hafsa da kyar take Jan numfashi, kunsan Bature da rikicewa tuni ta Fara kuka, tareda saurin bude kofa ta shiga ta dauki waya ta kira hospital service ta sanar dasu da address dinta, kuka sosae ta dawo gefen Hafsa tanayi, wadda batasan a Ina take ba. 

Babu jimawa akazo aka tafi da ita, Mum ta bisu, Tun cikin ambulance aka Fara bata emergency remedies Don temperature jikinta Yayi mummunan Hawa, a Haka sukaje akai admitting dinta, seda Mum tayi settling dukkan Wasu bills kafin ta koma gurin Hafsa wadda ta dawo hayyacinta sede ciwon Kai da take yasa sukai sedating dinta Don ta samu Hutu. Haka Mum ta koma gida tunda su a kasarsu Baa zaman jinya. 

Wasawasa seda Hafsa tayi kwanaki hudu a asibiti kafin ta Fara farfadowa, ta Fara cin Abinci. Yau tana zaune ta idar da Sallar azahar nurse din dake kula da ita ta shigo, hannunta rikeda tray da magunguna akai, seda suka gaisa da Hafsa ta bata magani,bayan ta tabbatar Hafsa ta sha sannan ta juya Dan fita anan Hafsa tace 

“Nurse! Can I talk to you ” 

Dawowa tayi ta zauna Tana fadin 

“Sure! ” 

Anan Hafsa ta fada mata insemination din da sukai, Murmushi kawai Tayi tace 

“Ya kamata kin fada tuntuni but nevertheless, zan sanar da Doctor dinki.” 

Daga Haka ta fice Itakuma ta cigaba da zama tana ta tunanin halinda Aminu ke ciki, tunda ta zo basuyi waya ba balle tasan a inda yake. Tana nan zaune tayi tagumi da tunannuka Kala Kala a ranta Sega Doctor da nurse din sun dawo, gado ta koma anan yayi mata tambayoyi Tana bashi amsa yana rubutawa cikin file dinta, seda ya gama sannan yace 

“Is very risky ki biyo plane daga yin dashen, amma zamu rikeki Har se Anyi confirming cikin tukunna. ” 

Cikeda jin dadi Hafsa tave 

Story continues below


“Thank you Doctor, I’m grateful nurse” 

A hankali taji hankalinta ya kwanta, Tana zaune Sega Mum ta dawo, hannunta da basket Wanda ke dauke da warmers. Rungume Hafsa tayi tace 

“You almost gave me a heart attack baby” 

Dariya Hafsa tayi tareda janyo basket din Dan duba me Mum ta kawo mata, stuffed broccoli ne Se noodles da appetizer, yawunta Har tsinkewa take tace 

“Mum na gode, you’re always amazing” 

Dariya Miss A’isha tayi tace 

“Eat, amma ya akai kika taho ke daya babu Aminu? Bayan Kinsan bakida lapiya” 

Spoon din hannunta ta aje tace 

“Mom Kince zakiga Doctors, meet him first se mui maganar” 

Mikewa Miss A’isha tayi ta shafa Kan Hafsa sannan ta wuce. Cikeda jin dadi Hafsa ta cigaba da cin abincinta, Tana tsananin son girkin Mum it’s always yummy. Ta manta rabonta da ta ware taci abinci. Seda ta kammalla tas sannan ta juya Dan kwanciya taji shigowar Mum, gyara zamanta tayi ganin yanayinta ya canja Dan ita ta jima tana tantamar idan Miss A’isha batada mood swing, tunda faraa take ta fita gashi ta dawo amma rai bace, take itama ta bata tata fuskar Har Miss A’isha ta zauna tace 

“Ashe keda Aminu mutanen banza ne bansani ba? ” 

“Me mukai kuma Mom? ” 

“Rufe min Baki, tambayata ma kike kenan? Seda kukaje akai implantation dinnan? Shiyasa kika taho nan tunda Kinsan halin ubanki Ko? ” 

Kirirkiri Hafsa tayi tareda rasa abin fada, Mom ta cigaba da fadin 

“Meye ban nuna miki ba akan yadda da kaddara, time without number nace miki shekarata goma da auren Abbas kafin nayi conceiving, Karki manta irin tsangwamar da nasha a gurin dangin babanki, amma ke duk inda kika shiga assurance ne, to Don me yasa bazaku hakura ba tunda kowa ya nuna muku Ku yadda da kaddara kuka take! Wallahil Azim da nasan abinda kikai da ban kulaki ba” 

Tana gama fadar Haka ta Mike bata saurari kukan Hafsa ba.


Kwanakin Hafsa daya da tafiya Aminu Ya shirya Ya bar Germany hankalinshi a tashe tunda baisan abinda zai tarar a Nigeria ba. A Abuja ya sauka Ya kwana a gidansu yana jin missing din Hafsa a jikinshi, Land-line din gidan Ya Kira ta Miss A’isha amma Shiru baayi picking ba hakan yasa ya hakura. Washegari se Maiduguri abinshi, a family house dinsu Wanda anan kowa Yayi rayuwa Dan iyayensu maza hudu kowanne da part dinshi se mata biyu Wanda Sunyi aurensu a Wasu garuruwan. Da yake duk babu me haihuwa cikin gidan yasa babu kananun Yara, mafi kankantar shekaru sha biyu kuma duk suna makaranta, straight part dinsu Ya wuce, Dada na zaune Tana lazumi da alama Walaha ta kammalla, gefenta ya zauna Yayi Shiru har me aikinta ta kawo masa breakfast amma ko kallon gurin baiyi ba Dan Bashida appetite din Abinci, ba abinda ya kawo shi kenan ba. 

Juyowa Dada tayi kamilar mata wadda kana kallonta kaga nutsuwa, shekarunsu zasu taya itada Miss A’isha kusan lokaci daya akai aurensu Dada ta Fara haihuwar Aminu hakan yasa Miss A’isha ta rikesshi Har aka yaye ya koma gurinta, bayan ta haifi Hafsa ta hadasu seda aurenta ya mutu sukaa koma gurin Dada har akai musu aurensu suka bar gabanta. 

“Aminu kaida Hafsa Se yaushe zaku daina jamin magana a gidannan? ” 

Haka muryar Dada ta katseshi, da sauri ya gyara zamanshi yace 

“Dada barka da safiya. Kiyi hakuri Dada ” 

Kallonshi tayi cikeda tausayi Wanda bata Bari Ya fito ba duk ya rame kana kallon Tashin hankali a kwayar idanunshi da fuskarshi Baki daya. 

“Rike Hakurinka, Ina ita hafsan take? ” 

Kanshi ya sunkuyar yace 

“Nace ta wuce America gurin Mom…..” 

Salati Dada ta saki tana tafa hannu sannan cikin fushi tace 

“Tashi ka fita Aminu ka barmin daki, me yake damunka daga Kai Har Hafsa? Ashe Bazaa taba fada muku Abu kuji ba? Ashe bazaku daina Jamin magana cikin gidannan ba? ” 

Tayi Shiru kuma tana kallon yadda ya marairaice yana fadin 

“Dada! Kiyi hakuri amma ni banga aibun abinda mukai ba, amma duk gida ya dauka Kamar Munyi shirka. ” 

Kanta ta gyada mamaki fal ranta tace 

“To Aminu bukuyi laifi ba, kaje babu damuwa” 

Zaiyi magana yaga ta Mike ta bar mishi parlon, shikam Kamar Zaiyi kuka Haka yaji ansa Dada da Mom are their only hopes amma ga abinda suke, shi wallahi takaicin kasancewar shi a wannan family yake, don she he sees nothing wrong a abinda sukai, haihuwa suke so basu samu ba sunje Anyi musu dashe to Meye abin daga wannan commotion duk dangi sun hade mishi Kai. 

Tashi Yayi ya fice yana jin takaicin abubuwan dake faruwa. Bayan Sallar ishai Alhaji Abbas, Alhaji Bukar (Mahaifin Aminu), Alhaji Bulama suna zaune parlon Alhajin sama, Aminu Wanda ke zaune kanshi a sunkuye Yayi tsuru Kamar kura a gaban damisa. 

“Aminu? yaushe aka haifeka? yaushe A’isha ta yaye ka a gidannan? har ni Abbas Maina zan kafa doka ka karya, ni zance ka fawwalla Allah Abu amma kaki, Dama hankalina bai taba kwanciya hada aurenka Dana Hafsa ba, Babu Wanda suka raina mu a gidannan irinku. Tana Ina Hafsan? ” 

Kamar an jikashi da ruwa yace 

“Tana….na barta acan” 

Wannan Karon Bulama ne yace 

“Aminu me yasa kukai Haka? Baku yadda da kaddara ba” 

Shiru Aminu Yayi Wanda Ya fusata Alhaji Abbas Ya dinga fada Kamar Dan Haka Allah Ya aiko shi, wayaga Rana zafi Inuwa kuna. Seda Aminu Ya tsani kanshi tsabar abubuwan dake faruwa, amma ko gezau baiji Wai dashen da sukai kuskure bane. 

Bayan Wata Biyu. 

Bayan an tabbatar da dashen cikin da akai Ya dasu, Hafsa na dauke da ciki a jikinta Wanda ranar ta zame mata ranar farin ciki Har ta manta da Wasu matsalolinta. Murnar da tayi ba abar a bayyana bace don harda kukanta na murna. A wannan ranar aka sallame ta amma ko keyar Mum bata gani ba wadda ta dauke kafarta Tun ranar da tasan gaskiyar abinda ya faru, kimanin sati uku kenan. Ana gama mata duk abinda zatayi ta fito da kanta tunda jikinta Yayi kwari sosae ta samu lapiya, cab ta samu Ya kawo ta Har gida, Se lokacin ta tuna batada kudi hakan yasa ta roki alfarmar dakko masa a cikin gida, tana shiga living room din Mum na fitowa daga kitchen hannunta dauke da warmers cikin basket wadda niyyarta a ranar taje gurin Hafsa tunda tasan ko Abund ya riga ya faru bazai canja ba to tabbas tasan dukkansu Sunyi laushi. 

“Mom kudi zaki bani na bar me cab a waje” 

Wallet Mom ta bude ta ciro kudin sannan ta fita da kanta ta biya kudin ta dawo ciki inda ta tarar da Hafsa tana zaune, gefenta ta zauna Hafsa ta gaisheta ita kuma tana tambayar ta jiki, 

“Am fit as you can see Mom ” 

Ta fada tana sakin murmushin jin dadi, kanta Miss A’isha ta shafa sannan ta umarceta tayi wanka suyi breakfast, Haka ta shiryo cikeda murna se shafa cikinta take Tana jin wani farin ciki marar misaltuwa yana addabar ta. She can’t wait ta bawa Aminu wannan daddan labarin, tasan Se ya fita murna, cikin budadiyyar gown ta fito ta samu Mom Tana jiranta sede tunda aka bude warmers din ta toshe hancinta Se amai kuma ya biyo baya, sosae ta galabaita don babu komai a cikinta. Mom kam Se Jera mata Sannu take  hankali a tashe, seda Tasha black tea sannan ta iya zama, lokaci daya Idanunta sukai zuruzuru ga waccan Ramar da tayi ga wannann daya tunkaro ta 

“Hafsa karkiyi wata Jinyar kuma, da kin fada min kin daina son broccoli anymore” 

Murmushin karfin Hali Hafsa tayi tace 

“Mom I’m pregnant shiyasa” 

Shiru Mom tayi ta tsira mata ido kafin koma ta Rungume ta cikin jikinta tana murna sosae ita ta manta Ashe dashen ciki sukai se Yanzun abin ya dawo mata. 

Da daddare Hafsa ta dauki land-line ta kira office din Aminu amma bata sameshi ba, tayi Shiru Tana tunanin yadda zatai, can ta kira Maiduguri nanma Baa daga ba hakan yasa taji babu dadi a ranta. System din Mom ta dauka tareda tura mishi Email ko Allah zaisa ya gani. 

Wasa farin girki! Tundaga wannan ranar Hafsa ta Fara laulayi me firgitarwa, gaba daya ta lalace gashi tunda Tazo Aminu bai waiwaye ta ba, shima ya gama kashe matsalar shi da su Alhaji dukda bawai sun sauka Duka bane amma abin Yayi sauki hakan yasa ya shirya zuwa America amma Kiran gaggawa yazo mishi daga Abuja akan Yayi reporting office, gaba daya Ko me yake hankalinshi yana Kan Hafsa, daida second daya Indai idanunshi a bude yake to Hafsa ce a ranshi sede duk hanyar da zasui communicating tamkar an toshe ta, gashi abubuwan da suka faru yasa yaji gaba daya son haihuwar Ya fitar mishi akanshi amma Hafsa na nan daram. 

Sati uku da turowar wannan Email din na Hafsa sannan Aminu Ya gani, ranar murna Kamar zai zauce Dan farin ciki, duk wani Wanda yake kusada Aminu yasan da cikin har Yan maiduguri seda ya fada musu kuma yayi mamakin yadda suke murna suma, Habibu kam harda hawayen farin ciki na taya abokinshi murna. Duk yadda yaso zamewa ya tafi America abin ya gagara Haka yana gani sede suyi exchanging mail amma bata taba fada masa halin da take ciki ba, shi kuwa kullum yana siyan kayan taryar baby. 

Cikin yana watanni uku wani dare Wanda Hafsa bazata taba Mantawa dashi a cikin rayuwar ta ba, saboda ita kanta bata saka ran zata rayu ba, Mom ta hada mata Salad taci dake yawanci shi tafi ci Se kuma wani lokacin tace tuwo ko abincin Nigeria Wanda Bazaa samu ba, Haka Mom zatai ta lallashinta Har ta hakura, sun gama ta kwanta wajen biyu na dare wani irin zazzabi me tsananin zafi Ya lullube ta, ta dinga amai Har Mum ta tashi a firgice ta kira Ambulance suka dauketa se asibiti, bayan shudewar mintuna Doctors ya fito yace da Mum idan sun yarda zaayi terminating cikin saboda wahalar da cikin yake bata, gashi akwai risk din cikin ya fita da kanshi idanma Baa zubar ba, Kai Mum ta girgiza cikin turanci tace 

“This child is a precious one, gaskiya Bazan saka hannu a zubar dashi babu decision din Babanshi ba. A kyaleta kawai, I can’t risk that” 

Zuwa safe Hafsa ta girgije nan Mom ta fada mata yadda sukai da Doctor, Shima yazo ganinta Ya tuntube ta akan abin, ai take Hafsa tace Ina Babu wannan Maganar zaman asibiti kuwa ta gama kada suje suyi mata wani abu batareda saninta ba, Duk yadda Mom ke mata bayanin kin yarda tayi Haka akai discharging on request. Suna zuwa gida tayi wanka Tasha tea Se taji karfin jikinta, Mom ta fito hannunta rikeda key tace 

“Hafsa Bari naje na dawo” 

Kai Hafsa ta kada, Mom ta fice. Daki Hafsa ta koma ta Tarar Mom ta hade mata Duka kayanta cikin trolley, addua take Allah yasa Mum korata Nigeria zatayi, she can’t wait to be in her husband embrace. Bayan wajen 3hours se Gata ta dawo, ta zauna gefen kafafun Hafsa tana fadin 

“Exhausted” 

Dan Murmushi Hafsa tayi tace 

“Sannu Momma ta, Naga Kin hada min kaya cikin trolley, Ina zani? ” 

Gyara zama Mom tayi tace 

“Nigeria zaki koma….. ” 

“Saboda me, nace na gaji da nan ne? ” 

Kai Miss A’isha ta girgiza tace 

“No, cikinki na wahalar dake, Ina tsoron ya fita kina nan is better ya fita gaban ubanshi, so time din flight dinki 1am in the night, nayi communicating da Aminu akan yana jiranki” 

Hafsa bata kara cewa komai ba, Dama kara take itama mijinta take so, Tana ganin idan da suna tare bazata dinga wannan Jinyar ba. Kunji Hafcy da magana! 

Karfe daya na dare jirginsu Ya Mike zuwa Nigeria, tunda aka Fara Hafsa ke bacci Wanda ta manta last da tayi irinshi, ita dai karfin jikinta kawai take ji. Basu tsaya wani Trans in ba seda ya saukesu Babban Birnin Tarayya, Tana dira kafafunta ta hango Rabin ranta, her better person, her soul mate, da kyar ta iya clearing kanta ta isa inda yake jira, tana zuwa ya Rungume ta itama kankame shi tayi dukkansu suna jin sanyi a ransu tareda jin tamkar shekara sukai basu hadu ba. 

Dayake weekend ce hakan yasa ranar babu inda Aminu yaje banda hidimar Hafsa, da ace akwai possibility wani yayiwa wani numfashi tabbas Aminu Zaiyi mata, Kamar ciwon da take yasan ta dawo gurin mijinta ya kwanta, a Haka sukai sati daya cikeda farin ciki da kwanciyar hankali sede Tana cika sati daya, masifaffen zazzabi Ya dawo mata, Babu shiri Yayi asibiti da ita anan ta Fara bleeding Wanda ya kara daga musu hankali.

“Aminu I’m bleeding, ka take motar nan, kada cikinnan Ya fita” 

Hafsa ta fada muryarta a dashe saboda ciwo ga hawayen dake tartsatsi a fuskarta, her only fear shi ne kada cikin ya fita. Hannunta Aminu Ya rike idanunshi akan titi yace 

“Don’t worry Hafcy, babu abinda zai faru” 

A wancan shekarun health care delivery system na Nigeria ba standard Yake ba, hakan yasa Aminu nufar wani private facility da ita, suna zuwa aka karbe ta, cikin kankanin lokaci aka tsayar da bleeding din sede alamu sun nuna cikin ke son fita ta karfi da yaji. Seda tayi bacci kafin Aminu Ya samu ganin likitan Wanda fitowarsu kenan, bayan sun zauna yace 

“Man, Munyi kokarin ganin cikin bai fita ba sede dole a kiyaye Don cikin na rawa ” 

Zufa Aminu ya goge wadda ta karyo masa yace 

“Likita Meye mafita kenan? ” 

Seda ya gama Rubutun da yake yace 

“Zamu riketa anan na sati daya Ko zuwa lokacinda zata zama stable, zata zauna on bed rest complete, banda aiki Kaima zaka daina having affairs da ita Har se cikin Yayi kwari. ” 

Kanshi Ya gyada sannan ya karba prescription yaje Ya siyo sannan Yayi settling bill. A take ya Kira Dada ya sanar da ita halinda ake ciki, sosae hankalinta yayi matukar tashi, Dama Alhaji Bukar na nan, da kanshi ya kaita har airport tayi catching next flight Se Abuja, kafin taje har Salima ta isa. Dukkansu seda sukai hawayen ganin halinda Hafsa ke ciki, tayi baki tayi rama Har lokacin baccin wahala take. Suma acan Maidugurin hankalinsu ya tashi sede Aminu Ya kwantar musu amma dukda Haka seda Alhaji Abbas yazo Wanda yana cikin Abujar yazo wani meeting dake tsohon general ne, shiyasa zafi Ya hadu da zafi ya bada wuta, tunda ya daura idanunshi kanta yaji dukkan wani fushi da fada ya kauce se tsabar tausayin Aminu da Hafsa ya kamashi. 

Lokacinda Hafsa ta farka jikin babu laifi da sauki sede weakness da take ji Wanda aka tabbatar mata zai tafi Se a hankali. Tundaga wannan ranar bata kara bleeding ba se Dan spot da take gani jikin pant dinta. Seda tayi sati uku a asibiti, Yan dubiya kam babu adadi tunda daga ita har mijinta masu mutane ne, hakan yasa akai ta tururuwa dukda restricting shiga da ake Wasu lokutan. A hankali karfin jikinta Ya fara dawowa ganin Haka yasa aka sallameta Dada tace da ita zata wuce Maid, ko musu Aminu baiyi ba Haka aka tafi da ita, don shima jikinta tayar masa da hankali yake tareda bashi Tsoro. 

A hankali rayuwa ta cigaba da tafiya sede tun ranar da Aminu da Hafsa sukai wannan dashen hankalinsu bai Kara kwanciya ba, daga anga Hafsa ta samu sauki ko kwanaki Bazaa kara ba wani zai dawo, ana tunanin ko cikin idan ya wuce watanni hudu zai daina bata wahala amma abu Kamar wasa Har cikin yakai watanni shida babu wani improvement. Ranar wata alhamis Aminu Ya dawo maiduguri daga Abuja anan ya tararda shockest sight of his life, Yana parking a Katon inda aka tanada na parking motoci, cikin saukakken kananan kaya yake, yana tafiya Kamar wani dawisu tsabar gayu da jin Kai, part dinsu Ya Fara dosa Kamar yadda ya saba sede kafin ya shiga yaga Dada ta fito a gigice, cikin Tashin hankali Wanda Ya kasa boyuwa a saman fuskarta, shima da hanzari ya nufeta yana fadin 

“Dada lafiya? ” 

“Ina lafiya Aminu? Hafsa ce” 

Seda yaji tamkar kanshi zai tarwatse tsabar yadda kalaman suka dakeshi, Hafsa again? Muryar Dada ta katseshi da 

“Muje mu wuce asibiti, kada yar mutane ta mutu” 

Ai ganinshi kawai Yayi gaban inda Hafsa ke durkushe Tana kelaya amai, ga jini kacakaca a inda take tsugunne, ga murkususu da take faman yi, jin Dada ta ambaci mutuwa, babu bata lokaci yasa hannunshi Yayi sama da ita, dukda jinin dake jikinta, a yau yasha alwashin a zubar da cikin koda kuwa wannan ne kadai rabonsu, Se lokacin yaji haushin kanshi, Ina amfanin badi ba rai Sunyi abinda ba Haramun ba, babu yarjewar kowa, babu neman Zabin Allah, Se lokacin ya tuna bai taba neman Zabin Allah ba shidai Hafsa tayi ciki ta haihu Ko Ta yayane, to Allah ya basu cikin ya dauke kwanciyar hankalinsu wani musiba kenan, tunda sukaje Germany Har zancen lokacin babu Wanda zuciyarshi ta kwanta, daga wannan se wannan. 

Daidai isarsu inda motar Aminu take, daidai parking din Ammar (Babban yayansu Hafsa) yana fitowa Ya zare glasses din idanunshi yana fadin 

“Subhanallah! Aminu lafiya? Hafsa ce? Ku shigo mu tafi asibiti ” 

Kusan a breath daya Yayi Maganar saboda yadda ya firgita, babu bata lokaci suka shiga sukaiwa Teaching hospital maiduguri tsinke, suna zuwa aka dubata akace CS zaai mata don sakaci zai iya sa yaron mutuwa, babu bata lokaci Ammar yasa hannu Kamar yadda Aminu yace, seda aka dauki Leda daya na jini daga Aminu daya daga Ammar sannan aka shiga da ita, gaba daya Dada banda Jan carbi babu abinda take,  can Sega Anty Yana matar Alhaji Bulama ta taho Itada Ummiey Mamansu Ammar, sun hado kaya. Ko mintina ashirin baayi ba aka fito da babyn wadda wata nurse ta fito da ita, Gabaki daya suka mike sede nurse din ta girgiza Kai tace 

“Mace ce kuyi hakuri itama ta wahala Se anyi mata Yan dabaru” 

Daga Haka ta wuce su zuwa ward inda suka cigaba da dakon fitowar su Hafsa, Ko awa baayi ba Sega shi an gunguro ta akan gado inda akai ward da ita, Haka suka bisu jiki a sanyaye da adduoi dauke a bakinsu. 

Bata dauki wani tsawon lokaci ba ta farka, nan dangi suka dinga shigowa yi mata barka, itakam Tana kwance ta lumshe Idanunta Tana tunanin Haka ciki yake? Haka ake shan wahala? To Meye su Ya kaisu neman ta har Haka? Indai ta kara samun ciki ne to ta hakura ta yafe itakam. 

Nurse din ce ta shigo ta dubi na ciki tace 

“Se kun ragu Don ta samu ta huta” 

Lokaci daya suka Fara fita aka barta itada Dada, babyn dake nannade cikin shawl pink aka miko mata bayan an tashe ta ta zauna, Idanunta ta kafe akan Babyn wadda ta rasa kammanin wa ta dauka, yarinyar kawai kyakyawa ce, ta zura yatsanta a bakinta tana sucking, Dada ta leko Tana kallon yarinyar yar mitsitsiya kasancewar ta preterm bata isa haihuwa ba, yatsa ta kai ta dungure mata kai tace 

“karama yar Baka ta Hana yata sakat” 

Murmushi Hafsa tayi ganin yadda yarinyar ta bude idonta ta kurawa Hafsa ido, that motherly love a take Ya mamaye Hafsa, Rungume ta tayi nan nurse din ta koya mata yadda zatai breastfeeding babyn Haka nan shigowar Aminu Yayi wukiwuki dashi, Ko ya manta da Dada na gurin kawai ya Rungume Hafsa da babyn tareda kissing goshin Hafsa yace 

“You nailed it baby, you’ve given me every happiness in my life sweetheart” 

Bayan Aminu Yayi Sallar ishai suka taho da iyayensu maza, don duba Hafsa shi baima karasa ba, Ya nemi wani call center ya Fara kiran Miss A’isha Kamar tasan da labarin kuwa Tayi picking, seda suka gaisa ya bata albishir din haihuwar Hafsa Kamar zata tashi sama dan murna balle yace daga ita Har babyn duk lapiya suke, Haka sukai sallama bayan Ya roketa akan Tazo ta gansu shima da kyar ta amince Don babyn Hafsa kawai zata zo. 

Seda Hafsa tayi kwanaki bakwai a asibiti kafin aka sallameta amma banda babyn saboda jaundice (shawara) dake damunta ga wata irin Mura da zazzabi datake fama dashi, Haka suka cigaba da zama kullum ciwon yarinya gaba yake karawa, Haka nan a wannan Dan tsukin Miss A’isha ta iso ta tadda wata sabuwar. Rashin lafiyar yarinyar tuni hakan ya Fara tayarwa da kowa hankali Dan wani lokacin sede a saka mata oxygen, a Haka sukai kwanaki talatin amma jikin baby kam se a hankali kullum aka kwanta gani ake Kamar zata mutu kafin Washegari. 

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]