DAWUUD CHAPTER 8

DAWUUD

CHAPTER 8

Dafasa jass yayi cikin sanyin murya yace,

please dont stress your self dawood may b he is praying or sumthing,he will call back wen he saw the missedcall.

girgixa kai yayi yanajin wani rashin sukuni na damun zuciyarsa.

shiru dukkaninsu sukayi tsawon lokaci kawanne zuciyarsa ba dadi,

har tsakar dare babu wanda ya kwanta cikinsu dawood kuwa saida sufyaan ya hada masa da allura sbd dagewa yayi saiyabi bayan maskan ayau.

restrnt na cikin hotel din dayayi order fruitsalad waiter din yadawo kawo masa chanjinsa yana dora hannu zaiyi knocking yaji qofar ta bude,

wani mahaukacin ihu yasaki yana kiran jesus…

arikice wasu roomservice biyu dasuka kawo suka matso qofar dakin ai nan take hankaki yatashi da gudu dayan yaje yakira manager da sauran securities.

hannu manager ya dora akai cikin tashin hankali nan take takira police.

ahankali suka kwanto gawarsa suka shimfide tsakiyar dakin cikin maikatan wasu harda hawayensu duk da basusan dalilinsa na kashe kansaba.

rufesa sukayi daidai lokacinda wayarsa tasake ringing babban officern yakai hannuwansa dake sanye cikin handgloves ya dauka.

sufyan naji andauka yayi saurin tashi zaune cikin qaguwa yace,

maska mey…shiru yayi tareda kallon gefen da dawood yake kwance cikin baccin dole na allura saidai yana tunanin tashinsa kowane lokaci shiyasa ya kalli gefensa.

ganin yanayinsa yasa jass dake zaune ya quresa da ido tasowa danjin abinda ake fada.

rawa yaga jikin sufyaan nayi sosai jiri na neman dibarsa atsorace yace,

what is it? 

hawaye yaga suna gangarowa daga idanuwansa tuni yasake rikicewa atsawace yace, 

tell me wat is it. 

sunkuyar dakai yayi tareda fashewa da wani irin kuka abunda baita6ayiba arayuwarsa aikawai sai jass din shima ya zube gefensa zaisake magana cikin wata irin murya sufyaan yace, 

khaleefa haydar maska is gone,
our friend our brother has left us he is no more,,innalillahi-wainnalayhirrajiun. 

kallon sufyaan jass yake ko qyaftawa bayayi idanuwansa da hancinsa tuni sukai wani ja sosai jikinsa ke wata irin rawa har sufyaan baisan sanda ya rungunesa da sauriba wani sabon kuka na zuwar masa. 

kamar daga sama sukaji andafasu sufyaan ne kawai ya dago yana ganin dawood yayi saurin miqewa tsaye yana kollonsa cikeda fargabar halinda zai shiga ciki idan yaji rasuwar maska. 

wani ja idanuwansa sukayi bakinsa ya qara bushewa yaji komai saidai jin zuciyarsa yake ta bushe masa kamar dutse babu abunda yakeson gani kawai yanxu banda maska. 

daqyar ya bude bakinsa dayayi mugun bushewa yace, 

muje maska na buqatarmu yanxu. 

sai alokacin kuka mara sauti yazowa jass ya dago yakalli dawood yaga yanda idanuwansa sukayi da yanda jikinsa ke rawa yasan tabbas zaifisu shiga wani halin rashin maska. 

sufyaan ne yayi qarfin halin sanarda taheer yakaisu airport,
suna isa cikin saa suka samu ticket na jirginda zai tashi zuwa lagos alokacin, 

harsuka sauka lagos babu mai iya magana acikinsu kowanne idanuwansa jajir abunka da dukkaninsamu farare. 

wayar maska sufyaan yasake kura sukaji sunan hotel din sbd ba’a dauke gawarsaba su ake jira. 

tunda suka isa harabar hotel dun jikin dawood ya tsananta rawa sufyaan yayi saurin riqesa. 

Story continues below


ALLAHU AKBAR,,shine abinda sufyaan ya furta da wata irin wahalalliyar murya lokacinda yabude gawar maska yatabbarda shi ‘dinne ya rasu. 

kuka sosai jass yakeyi musammam da aka sanardasu shine ya rataye kansa da kansa. 

wani irin murmushi dawood yasaki yana kallon gawar yace, 

nasanshi tun tasowana bazai ta6a kashe kansa da kansaba. 

matsowa officern yayi ya dafasa cikin jimami yace, 

a iya ‘dan bincikenmu dole zamuce shine ya kashe kansa. 

kai tsaye bayan rubuce rubuce aka basu gawar suka wuce kaduna. 

koda mamynsa tayi ido biyu da gawar ‘danta yanke jiki tayi ta fadi saida aka hada da dr ta farfado gari naqarasa washewa tuni gidan yafara cika da dangin daddynsa sbd mahaifunsa tuni ya rasu. 

wani irin yaji da zafi idanuwan dawood keyi sbd tsananin tashin hankali gashi kukanma yaqi zuwa sai rarraba jajayen iduwansa yake akan gawar yaqi masa ko ina yana kusada gawar jiyake kamar maskan zai tashi sukoma rayuwarsu tada mai cikeda farin ciki jin dadi da qaunar juna. 

lokacinda aka gama yiwa gawar komai za’a tafi da ita sai alokacin wani irin kuka nai ciwo yazo masa ya sunkuyar dakai yanayi nan jikin duk wanda ke gurin yaqara sanyi musamman dangin dadynsa dasukafi kowa sanin kirki da kyawawan halayensa sbd shine dauke da nauyin karatun ‘yayayensu. 

dad dinsa da taheer dasuka biyo jirgi da safe sukazo jana’izar suma sun tausayawa dawood dasu jass matuqa sbd ganin halinda suka shiga na rashin amininsu rabin jikinsu. 

kuka dawood yayi sosai harsukaje suka dawo nanma hankalinsu yaqara tashi sbd ganin sunrabufa kenan har abada sun rabu kenan da maska musamman ma jass dayaga yanda ake rufe gawa nan take wani irin tsoro da imani yashigesa sbd yasan wata rana zasubi maska da guda guda suna fitowa maqabarta ya kar6i musulunci yana wani irin kuka a hannun limamin dayayi sallar batareda ma su sufyaan sun saniba sbd shikadai yasan ciwon dayakeji na rashin sanin adduar dazaiyiwa maska kamar yanda yaga su sufyaan sun masa. 

suna dawowa dakinsa suka shige sunyi kuka har babu wanda zai iya bawa wani hkr acikinsu musamman ma dawood dake ganin duk akansa komai ke faruwa,
meyasa tun farko yafada soyayya,
meyasa Nur ta 6ace masa har rayuwarsa ta lalace harma data waindake taredashi,
kallonsu sufyaan yayi da jajayen idanuwansa yaga yanda sukai wani kalar tausayi bayason yarasasu ko wani abu suma ya samesu dan haka zaiyi nesa dasu sukoma suci gaba da aikinsu su fuskanci sabuwar rayuwa bayason rayuwarsu ta lalace kamar tashi sbd ya rasa NUR,yarasa MASKA, yarasa SOYAYYAR MUM dinsa sbd baya tunanin akwai so yanxu atsakaninta dashi,ya rasa FARIN CIKI, yama rasa komai tunda ya rasa maska da nur. 

bayan angama zaman gaisuwa anwatse saida suka qara kusan sati ‘daya suna qara kwantarwa da mammyn maska hankali, 

ranar dazasu tafi riqe dawood tayi tanata wani irin kuka,
kasa riqe nasa kukan yayi saida sukayi mai isarsu kafin daqyar suka tafi bayan dawood yakira taheer anema masa babban gida a abuja zasudawo da mammyn kusadasu a abuja zasu siye mata sbd shine111 babban abinda zasuyiwa maska bayan ransa. 

ranar dasuka dawo gidan kamar gidan zaman gaisuwa sbd ko abincin kirki cikinsu bamai iya ci mum ce keta yawo ranason taga kowa yasake sbd bikin nan batason ace za’a dagasa, 

tunda dawood yadawo yarasa sukuni zuci sbd yakasa kankarewa zuciyarsa duk shine sanadi har lokacin jin rasuwar maska yake sabuwa gashi jass ma lafiya na neman gagararsa sbd rashin sabo da wahala gashi mum ‘dinsa takirasa akan dad dinsa kwanakin zuciyarsa na tsufa na yawan tashi. 

hakanan su dawood suka fara shirin tafiya sidney gurin dubo yanayin jikin dad din jass saidai jass din yace su bari saisun gama settlin komai na dawo da mammyn maska abuja tukuna saisu samesa daga baya.

ana gobe zai tafi saraah tabugawa siyama waya tace duk yanda za’ayi ko nawane zata kashe asamo mata abunda takeso sotake idan jass yasa qafa yatafi har abada bazai iya dawowaba ko yaso dawowar, 

gyara tsayuwa siyama tayi daga cikin toilet din datake wayar tace, 

me kike ganin zai hanasa dawowa ga aminansa biyu dasuka rage masa? 

murmushin mugunta tasaki tace, 

dariya siyama tayi tace, 

wlh koda masifa kuwa sai saqonnan ya iso hannunki.
dariya sukayi suna qarasa qulla muguwar aniyarsu kafin suka kashe ta fito toilet bayan tayi waya sa seeya har tayi masa transfer kudinda saraah ta turo mata. 

kallon nur dake kwance aleeya na miqa mata tea tayi awuqance sbd ganin kullum taqi lafiya sai wahalarda mutane take munafuka bikine dai baza’a dagaba sai anyi sbd abba yace gwara dai ayi kowacce taje mijinta yayi jinyarta.

har airport suka kaisa kallon sufyaan jass yayi da idanuwansa dasuka jeme fuskarsa jajir ahankali yace, 

take gud care of him. 

rungumesa sufyaan yayi jiki amace yace, 

take care please. 

daga masa kai yayi tareda sakinsa ya rungume dawood da tuni idanuwansa suka canza murya a matuqar mace yace, 

we’ll be there soon insha allah,take care please. 

daga masa kai yayi yana share fuskarsa da handkchf sbd hawayen dakeson xubo masa yace, 

see you guys soon. 

juyawa yayi ya wuce sbd tuni aka kira flight dinsu. 

suna tsaye har ya shige suka sauke ajiyar xuciya ahankali tareda juyowa suka kalli juna suka wuce kowanne zuciyarsa ba dadi musammqn ma dawood da ciwo ke cinsa daurewa kawai yake.

shiru yayi tareda rufe idanuwa kewa da tsananin son ganin Nur dinsa na qarawa zuciyarsa nauyi da wani irin ciwo.


Suna isa gida suka zauna shiru sarah tazo tayita surutanta babu wanda ya iya ko kallon gefenta qarshe miqewa tayi ta fice tana ta6e baki aranta tace, 

duk zaku raina kankune lokacinda kaima sufyaan plan dina yagama kammaluwa akanka ka shiga naka gararin kaikuma dawood kazo tafin hannuna. 

washe gari shiru shiru basuji kiran jass ba gashi basa samunsa tuni hankalin sufyaan yatashi yayita qoqarin 6oyewa dawood sbd ganin yanayin jikinsa daya qara dawowa. 

dawood din dakansa yakar6a wayar yayita kira baa samu daqyar sukaga maraice yasake yi nan dawood ya danna kiran num din mrs smoake mum din jass din. 

kiran farko ta ‘dauka saikawai ta fashe masa da kuka. 

tashi zaune yayi daqyar yana qoqarin tambayarta. 

kasa magana tayi saima kashe wayar datayi. 

cikin tashin hankali sabo yasa taheer yimusu cuku cuku suka bi jirgin asuba suka tafi batareda ko mum tasaniba dad kawai sai taheer ne sukasan halinda ake ciki. 

sai dare suka sauka kai tsaye gidansu jass din suka nufa anan suka tararda tashin hankalinda yasa dawood kusan sumewa sbd saida aka zaunar dashi sufyaan kuwa kuka yake resas lokacinda mrs smoake tasanar dasu ankama jass tun a airport sbd miyagun qwayoyin daaka samu ajakarsa tun jiyan aka wuce prison dashi lokacinda aka sanar dasu atake hrt attck yakama dad dinsa ya rasu. 

prison din suka wuce daqyar dasaka hannun wani abokin dadyn dawood aka bari suka gansa kallo daya sukaiwa junansu suka fashe da kuka kamar yara qanana sbd wasu irin chains ne aqafafu da hannuwan jass din kammaninsa tuni suka sauya sbd azabar da aka kwana ana gana masa, 

kuka sukeyi sosai kafin suka sanar dashi rasuwar dad dinsa, 

cikin kwana biyu suka kashe kusan fiyeda rabin dukiyoyinsu gurin ganin sun fitarda ‘dan uwansu amma tuni aka hanasu ko ganinsa ga mum dinsa tasa abin aranta sosai nan hankalinsu yatashi sunyi kuka baida iyaka kowannensu tuni yakoma sai dogon wuya da dogon hanci. 

ahaka suka dauko mrs smk suka dawo da ita new jersey tareda siya mata dan madaidacin gida tareda tattaro dukiyar dadyn jass data jass din suka damqa mata danta kulada ita bayan sun samar mata mataimaki mai qwazo da amana. 

koda suka dawo nigeria tuni aka rasa mai tallafar wani tsakanin dawood da sufyaan idan suka fita tun safe suna bar suna shan mai qarfi sai dare suke dawowa duk lokacinda abar tasakesu kuka sukeyi sosai suna istigfar, 

ana saura sati biyu bikin ranar dawood ko mai yakasa sawa cikinsa sbd komai yasa sai yayi amai nantake ciwo yayi masa mugun kamu sbd tuni giyar tafara yimasa mummunar illa, 

aranar yafara wani irin aman jini sufyaan yayi kuka har numfashinsa baya iya fita gashi dawood yasakasa yayi masa alqawarin bazai ta6a fadawa kowa bayada lafiya, 

idan mum ko dad da taheer sun shigo daurewa yakeyi ya zaune csuna fita zai fara amai ko wani abun, 

zaune sufyaan din yake gaban gadonda dawood din ke kwance cikin qarfin hali yana masa firar rayuwarsu ta da dasuke su hu’du cikin farin ciki, 

hawaye sufyaan yake yana girgiza masa kai sbd bayason firar sbd jinta yake kamar wasiyace dawoid din ke basa, 

miqewa yayi da sauri ya zari mukullai ya fice, 

yana fitowa daga harabar gidan yaci karo da saraah data dawo daga airport dauko siyama ya wuce da mugun speed, 

juyarda kan motar tayi tabi bayansa siyama tace, 

ina kuma zamu? 

binsa zanyi dama ina neman damar zamunsa shika’dai. 

binsa sukayi bayan tayiwa su seeya dake gari tun satin daya gabata waya. 

Story continues below


yana gaf da isa bar din wata black jeeb tasha gabansa 

burki yaja da sauri tareda qoqarin fara ribas motar sarah ta taresa ta baya. 

kallon anguwar yayi yaga tsit gashi dare ne fitowa yayi sbd sarai yagane sarah ce amotar bayansa yana fitowa suma suka fito tsayawa tayi gabansa tana watsa masa kallon banza tace, 

poor dr sufyaan,
kaine mai binkicen mutuwar maska da abunda yasamu jass ko?
to bari na sauqaqa maka wahalarka abinda kuke gani SAKAMAKO(SURAYYAHMS?^_-)ne na abinda kukai min,
and there is more to come
saidai im really sorry to say bakanan bare kagani,
yarinyarda kuke ta fafutukar nemewa abokinku bazaku ta6a samuntaba duk da gatanan itace wadda qanin dawood din zai aura dan haka yanzu abinda nakeso dakai shine kafadamin wayene kuke binciken mutuwar maska da jass tare? 

fadamin sbd nasan kaida wanine fadaminshi and nikuma zan saka yarana suyi maka sauqi sbd…… 

wani gigitaccen marin dayasata zubewa qasa baki na jini yasakar mata cikin tsananin takaici da danasanin neman mata sbd da ace yau basuyi neman mataba dabazasu hadu da wannan masifarba ta haduwa da saraah arayuwarsu.,
tabbas yanzu yagane neman mata na daya daga cikin sanadin shigarsu wannan balain dakum……. 

saukar wani hakaukacin dukan qarfe yaji atsakiyar kansa nan take ya zube agurin yana shure shure, 

tafiya mai nisa sukayi ta daji saida suka kai wani daji mai ruwa suka jefasa ciki tareda motarsa suka tafiyarsa batareda sun tsaya tabbatarwa koya mutuba sundaisan yama mutu dan bazai iya daukar wannan dukanba. 

shiru shiru ba sufyaan nan dawood yalalla6a yatashi yakira taheer yafita dashi, 

duk inda yakesa ran ganin sufyaan yaje baigansa ba har gidan mammyn maska yaje duk wata bar dasuke zuwa sunje nan hankalin dawood yatashi aahankali yace, 

shima yatafi inaji ajikina sufyaan ma yatafi yabarni, 

ganin halinda yashiga yasa taheer dawo dashi gida shikuma yakoma yakai report dukkanin polince stations, 

cikin kwana biyu tuni dawood yakoma wani iri zuwa lokacin tuni kowa yasan yafara shan alcohol sbd idan yasha yanzu tana bugar dashi sosai haka zaizo yayita zagin mum baruwansa da baqinta 
tun tana 6oye 6oyen abun tuni hankalinta yafara tashi tayi kuka babu adadi gashi tuni gidanta yafara cika da yan biki ammq haka zaita abubuwansa idan yayita amai yawuce daki ya kwanta.
duk wani kwanciyar hankali da farin ciki tuni ya qauracewa gidan nan hankalin dadynsa yatashi yafara binciken abinda yasamu rayuwar dansa ya lalace, 

tunda mum taji dad zaiyi bincike hankakinta ya qara tashi tayi kuka ba adadi tasamu sarah ta sanar da ita akan tana roqonta data tafi har hankali ya kwanata. 

sarah na sanarda siyama akan sudau mataki akan dad sbd har abada bazai ta6a bari ta auri dansaba harararta siyama tayi tace, 

idan kika kashesa kina tunanin za’ai wannan auren ne yanzu?
dagasa zaayi gwara kibari bayan auren masan abinyi dashi dan wlh yana gano komai kashemu zaai dan wlh ko hukuma bata kashemuba sai dawood yayimana kisan wulaqanci. 

wani yawu saraah ta hadiye sbd sam ita ko maganar mutuwa bataso tsoronta take saidai abu daya data sani duk wanda yadauki hanyar bankado asirinsu kashesa zasuyi dan wlh bazata yarda akashetaba.

*******
yau akesa lalle tunda akai aka gama babu mai doguwar walwala acikinsu sai yaqe sukeyi siyama data dawo yau sai murna da farin ciki takeyi sbd ganin ko ahaka ta tarwatsa farin ciki da kwanciyar hankalinsu saidai qasan zuciyarta wani zafi da quna takeyi na kishin taheer dan yanda takejin sonsa da qaunarsa ko layla zata iya kawarwa dan tasamesa. 

tunda aka fara bikin take fama da ciwon qirji sosai saidai tana dannewa kar hankalin aleeya yatashi saidai abin yafara bata tsoro sbd har jini jini take gani idan tayi tari,Nana ce kawai tasani take dan kulawa da ita duk da hankalin nanar yatashi sosai da ganin hakan amma ta hanata fada, 

duk wani buri da shirin dasukaiwa aurensu bai yiyuba sbd babu wadda zatai kyawun gani musammman ma layla da tuni tafara fita kamannninta sbd rama, 

ammy ma batai wani gayyataba hakanan aka lalla6a aka daura auren aranar layla tayi kukan daya haddasa mata ciwon mai tsanani, 

tunda bilal yace mata andaura aurenta da taheer,dawood da aleeya ta sulale tashige dakin nana, 

rungumeta nana tayi da qarfi ta qanqameta sbd ganin wani irin kuka datake mai cin zuciya jikinta na tsananin rawa, 

ita kanta nanar kuka takeyi sosai na rausayin layla kamar ranta zai fita, 

ammy tunda akace angamo daurin aure take neman layla sbd tasan yau tanacikin wani mummunan hali, 

dakin nana ta nufa tana ganinsu ahaka idanuwanta suka cika taf da hawaye bayasan lokacinda ta qarasoba ta janyo laylar ta rungume hawayenta na tsiyayowa. 

kamar daga sama aleeya tashigo dakin nemansu tana ganin halinda auke ciki jikinta ya qara sanyi ahankali ta qaraso tq zauna kusada ammy tareda kiran sunan layla ahankali, 

kasa dagowa layla tayi saima wqni sabon kukanne yazo mata mai ratsa zuciya ta juyo suka rungume juna tuni itama aleeyar ta fashe da kuka, 

kuka suke sosai kowanne da abinda yake tunawa cikin ransa ammy ma saidata yi kukan daqyar nana ta lallashesu tana sakin ajiyar zuciya ganin sunqi yin shiru yasa takira bilal yana shigowa jikinsa yayi mugun sanyi ahankali ya qaraso ya durqusa tareda jawosu gabaki daya ya rungume yana mayarda hawayenda suka ciko idanuwansa, 
Ana magrib suka sauka abuja nan motoci sukazo daukarsu suka nufi gidan,
mum cikin farin ciki take sosai nan gidan yaqara hargitsewa da hayaniyar farin ciki,
layla kuwa tsabar tashin hankali da mugun ciwon da zuciyarta keyi tun amota ta sume musu hankali tashe suka qaraso gidan nan mum takira taheer yazo da dr cikin tashin hankali dan sosai ya damu da jin ciwon amaryar tasa, 

ruwa da allurai dr ya daura mata kafin aka barta tadan samu hutu, 

kukan da aleeya tasha alokacin saidata bawa kowa tausayi dan kwata kwata batajin farin ciki ko wata walwala duk da kuwa tasamu ta mallaki dawood din datake so, 

siyama da saraah kuwa daki suka shige cikin tsananin farin cikin ganin burinsu na gaf da cikewa. 

daqyar aka lalla6ata aka kaita sashen mijinta suka dawo sashen mum aka baro acan, 

tagumi ta rafka da hannu biyu hawaye na tsiyayowa daga kumburariyar fuskarta da tuni ta sauya sbd kuka.

tsakiyar dare ya dawo gidan guraren biyu saura,
tunda motarsa tashigo harabar gidan mum dake zaune tsakiyar gadon dakin dad tana jiran dawowarsa sbd dad baidawoba daga gurin daurin aure ya tsaya acan sai anwatse zuwa jibi zai dawo, 

saukowa tayi ta fito fuskarta adaure ta fito harabar gidan ta tsaya gaban motarsa tana jiran yafito, 

taheer ma jin dawowar dawood din yasashi fitowa dama baiyi bacciba sbd tunanin ya jikin layla yake yanxu, 

yana fitowa ko gefensu bai kallaba ya wucewarsa riqe da kwalbarsa dama su keys jikin mota yake barinsu, 

kiran sunansa mum tayi baiko sauraretaba ya wuce ya shige palonsa, 

daga kwalbar hannunsa yayi ya buga da qasa lokacinda yaga komai na sashen an sauya ansaka sabbi, 

qarar fashewar kwalbar tasa mum da taheer qarasowa palon da sauri, 

wani kallo ya watsa musu murya a sama yace, 

meye wannan? 

daure fuska mum tayi tareda gyara tsayuwa tace, 

aure akayi maka kuma matarka nanan ciki tana jiranka,
me kakeson mayar da kankane dawood for god sake ace yau kwananka biyu rabonka da gidannan sbd kawai banxar mace……. 

tsawar daya daka matane yasa aleeya dake la6e fitowa, 

ja sosai idanuwansa suka sakeyi yace, 

har abada nur itace rayuwata idan kin daukeni amatsayin ‘danki haryanxu to dole zaki kira sunanta da respect,
banida mata aduniya idanba nur ba,
na tsani duk wata mace dazata soni matuqar ba nur ba,
wannan dakike magana akanta itace macen danafi tsana fiyeda mutuwar data rabani da maska,
wlh mum danki zai mutu babu mata idan har ba nur bace…. 

shut up””’tace da qarfi cikin takaici da zafin zancensa takallesa cikin kakkausar murya tace, 

Nikuma idan nice mahaifiyarka bazaka wulaqanta wannan auren na aleeyaba,
ta wace hanya zanyi maka bayani ka gane auren nan is for your own gud mekakeso bayan wannan fadamin…… 

NA SAKETA…..shine zancen daya katseta dashi batasan sanda ta ‘daukesa da wani mahaukacin mariba saida ya sakashi zubewaba kasancewarsa abuge, 

cikin kwalbar gurin ya fadi nan take duka hannuwansa biyu suka fara futarda jini sosai ya dago jajayen idanuwansa dasuka cika taf da hawaye ya miqe 
taheer yayi saurin matsowa zai riqosa ya daga masa hannu tareda shigewa daki ya bugo qofa, 

tsakiyar dakin ya zube tareda dunqulewa hawayen idanuwansa na gangarowa ahankali yakira sunan NUR dasu MASKA jini nacigaba da zubowa daga hannuwansa. 

Story continues below


da lalaben bango aleeya ta mayarda kanta daki ta sulale da6as tsakiyar dakin jikinta na rawa tsawon mintina kafin daqyar tasamu wani irin kuka yazo mata tasakesa da qarfi, 

kuka takeyi sosai har tana shidewa jitake zuciyarta da qirjinta na ciwo ta sulale qasa ta kwanta tana sake sakin sabon kuka. 

jiki amace taheer ya lalla6ata yakaita har bedroom dinta takwanta ya fice. 

a wannan daren aleeya tayi kukan daya haddasa mata shiga mugun yanayi,
dawood ma yayi kukan rashin abokansa har yafice hayyacinsa sbd jinin dayake zubarwa,
nur kuwa tunda ta farka tsakar dare takasa motsi sbd da sabon ciwon qirji ta farko har wani sarqewa numfashinta keyi. 

asubar fari aleeya ta hada kayanta wainda bana lefe ba wainda abba yayi musu dabam,
bayan tagama hada kayan tsaf ta zauna bakin gado tayi shiru tana jinjina quncin datakeji dan tasan rayuwarta ta riga ta ruguje sam bazata iya fadawa laylaba sbd ganin halinda take ciki itama ayanxu. 

miqewa tayi ahankali tareda fitowa palo daidai knocking dinda taheer yayi na zuwa tafiya da dawood sallar asuba a masallacin gidan, 

bude masa tayi yana ganin yanayinta hankalinsa yayi mugun tashi ya shigo ciki yana kallonta ita kuwa qoqarin tsayarda hawayenta takeyi tace, 

ka kaini airport tun kafin kowa yatashi asan halinda ake ciki. 

girgixa mata kai yayi murya a mace yace, 

aleeya babu inda zakije sbd haryanxu da aurensa akanki dan abuge yake ajiyan. 

girgixa masa kai tayi sabbin hawaye na sauko mata tace, 

hankalinsa yadawo jikinsa tun lokacinda mum takira sunan NUR ‘dinsa. 

sabon kuka tasake ahankali tareda zubewa kan kujerar gurin tana toshe baki, 

asanyaye ya matsa jikin qofar dakin yayi tura 
abinda yagani yasashi qarasawa da sauri ya tallafosa yana kiran sunansa da qarfi, 

jin haka yasata tasowa cikeda tsoro da fargaba tagansa kamar barai ga jini kwance a qasa. 

cikin tashin hankali akayi asibiti dashi mum ko sallar asuba batayiba saidai tayita acan, 

daga ita har aleeyar kuka sukeyi taheer na duk abin duniya ya ishesa sai kaida kawo yakeyi, 

yan biki washe gari saidai saraah ce ta sallamesu suka koma,
tsabar wulaqanci ta mota suka sakasu suka tafi umman siyamaa kawai sukasa jirgi bayan uban kudaden dasuka bata nan tayita sake dorasu ahanya tana sanya musu albarka, 

layla tana bude idanu da nana tafara cin karo sbd dama bada ita zaa komaba anbar musu ita aikine, 

daqyar ta tashi zaune tana lumshe ido cikin azaba ahankali tace, 

zanyi sallah nana. 

kamata tayi takaita toilet tayo wanka da alwala tazo tayi sallah tana idarwa ta jingina da gado tareda lumshe ido tanajin babu abinda tafi buri da buqata yanxu kamar tarabu da auren taheer  tabar gidan. 

cikin sanyi da rawar murya Nana tasanarda ita dawood na asibiti,

sosai taso dannewa amma saida nana tayi dana sanin sanarda ita.

ganin kamar abin yafi qarfinta yasatakira wayar aleeya tasanarda ita aikuwa nan hankali yaqara tashi taheer yadawo gida aleeya datasha kuka wani kan wani,

dr aka sake kira yayi mata allurai tareda qara daura mata wasu ruwa,

tunda taheer yashigo ta rintse idanuwanta gabanta na tsananta nauyi 
dr na fita ta bude ahankali tareda kallon aleeya datai wani mugun fadawa dare guda ahankali tace,

kiyi hkr zaiji sauqi insha allah.

share hawaye aleeyar tayi tana jinjina kai batareda ta iya maganaba.

kallon yanayinta taheer yayi saiyaga kamar batason kallon gefensa ya juya ahankali ya fuce tareda sawa aka hado mata tea mai kauri yakawo mata tareda miqa mata ahankali yana kallon yanayinta,

batareda ta dagoba ta kar6a ta aje gefe,

zama yayi bakin gadon yasake daukar cup din ya miqa mata murya a tausashe yace,

kisha ko kadan ne.

wani abu daya taso mata ta danne tareda kar6a ahankali ta kur6a.

yana ganin haka ya miqe yakoma asibiti.

kwanan dawood biyu a asibiti aka sallamosu saidai ko aranar bai kwana gidaba saida asuba yadawo ko kallon aleeya data kwana palo zaune daram tana jiransa baiyiba ya wuce bedroom dinsa ya kwanta.

share hawayenta tayi tareda miqewa ta shige daki tayi sallah ta fara wani sabon kuka sbd batasan wazata fadawa halinda take cikiba batason qarawa layla damuwa ammy kuwa batason daga mata hankali,

kwananta biyu kusan satin layla biyu a sashen mum mum itama da gangan ta qyaleta sbd batason wani abu yashiga tsakaninsu tun yanxu,

itama laylar sosai tafison hakan sbd sam ko haduwa da taheer din bataso,
ga sabon tashin hankalinda take ciki na ganin rayuwarda dawood yafada tayi kuka aranar harsaida kukan yadaina fitowa na tausayinsa da kanta harma da halinda aleeya ke ciki sbd dukkanin alamomi sun fara bayyana da tana cikin tsananin damuwa da quncin zuciya,

aranarda dawood din yayo wani dare akai rikici sosai arabar gidan shida mum da taheer aleeya banda kuka babu abinda take sbd sosai yakashe musu jiki da maganganunsa,

layla dake tsaye jikin window sulalewa tayi cikin wani irin gunjin kukan tausayinsa,
bata ta6a tunanin sonda yake mata yakai hakaba dan itama sosai maganganunsa suka daketa zuciyarta zafi take sbd babu abinda takeson kasancewa dashi yanzu kamarsa.

aleeya da mum ma sosai suke hawaye 
ayau aleeya datasan inda zataga NUR dinsa datayi alqawarin nemota sbd abinda taji tagani yanxu ya sake tabbatar mata da har abada dawood bazai kalli wata mace idanba nur ba,
ita kuwa zata iya sadaukar da nata farin cikin kan nasa matuqar zataga nur din.

ko a wannen daren babu wanda yayi bacci acikinsu musamman dawood aranar yayi kukan rashinsu maska arayuwarsa jiyake dama rayuwarsu ta baya tadawo dabazai ta6a bari yafada soyayyaba.

washe gari taheer yagama hada komai na tafiyarsa dazaiyi da layla cyprus sbd sosai yakeson tafara sakewa dashi sbd sam yakasa gane inda aurensu ya dosa sbd sosai yalurada gudunsa take ko ganinsa batasonyi yanason su fara fuskantar rayuwar aurensu dan idan suna gidan mum bazata ta6a bariba.

sosai hankalin mum yatashi daya fada mata tafiyar batasan sanda tafara kukaba ahankali tace,

taheer haka zaka tafi kabarni da dawood acikin wannan halin dayake ciki,
kana gani ciwo nacinsa amma taurin ransa ya hana yabari ayi masa magani,
taheer dan allah karka tafi kabarni cikin wannan halin ina tsananin buqatarka akusa.

girgiza kai yayi ya lalla6ata akan bazai dadeba zasu dawo.

lokacinda taheer yakirata awaya yasanarda ita maganar tafiyar qiris yarage ta zube tsabar firgici da tashin hankali.

sulalewa tayi qasa jiki na rawa ta zauna kusada aleeya dake zaune shiru tayi nisa a tunani.

zazzare idanuwa taitayi sbd danne kukanta kar tayi gaban aleeya taqara mata wani tashin hankalin dan tana iya qoqarinta gurin danne damuwarta gaban aleeya dan yanzu kowa nada tasa kalar damuwar.

da daddare tayi kuka mara iyaka kafin ta dangana tana fatar allah yasa kafin tadawo aleeya da dawood sun daidaita.

washe gari tunda suka suka wuce bayan aleeya tasha kuka ajikin layla sbd yanzu taqara tabbatarda rayuwar qunci zatayi arayuwar aurenta,
kukan datayi harsaida jikin layla yaqara yin sanyi sbd sosai aleeya ke bata sosai.

suna barin gidan hawayen datake dannewa suka tsinke ta lumshe idanuwa ahankali.

kallo ‘daya yayi mata yaji jikinsa yayi mugun sanyi.

wayarsa ce tayi ringin yana dauka ahankali yace,

yes junaid.

daga can 6angaren junaid din yace,

barr dama maganar binciken mu ne na marigayi maska jiya mun samu ganin sambo wanda shine mutum na qarshe da maska yagani a adamawa kuma duk wasu bayanai na abunda yasakasa na nemo wata yarinya yabamu bayanan harma da hotuna gasunan ahannuna.

gud job junaid thank you,
yanxu ina hanyar zuwa airport kasameni kabani takardun yanxu.

ok sir insha allah.

kusan atare suka isa airport din ya miqawa taheer din babban envelope dinda ke daukeda bayanan kafin ya wuce.

cikin jakar laptop dinsa yasaka envelope ‘din suka wuce sbd jirginsu da aka fara kira.tunda suka wuce sarah takasa zama sai kaida kawo takeyi cikin rashin sukuni,

kallonta siyama tayi tace,

wai lafiya kika kasa zama?

tsayawa tayi tareda dafe goshi cikin rashin sukuni tace,

hakanan nakejin hankalina bai kwantaba akan taheer sbd kinsanfa seeya yace sun gansa da wani ‘dan bincike a hotel ranar.

aje wayar hannunta siyama tayi tana qoqarin daure abinda ke taso mata tace,

to me kike tunani yanxu?

murmushi sarah tayi tace,

so nake shima na koya masa hankali tun wuri sbd……

kallonda siyama ke matane yasa tayi saurin hadiye zancenta murya na rawa tace,

me…me meye haka?

wani mugun riqo siyama tayi mata idanuwanta na fitowo sbd masifa cikin wani irin yanayi tace,

wallahi duk kika ta6a lafiyar ko takalmin taheer ne saina aje duk wani abu dake tsakaninmu na lalata rayuwarki ta yanda har abada bazaki mantani ba.,

qwacewa sarah tayi da qyar tana fito da ido tace,

kina nufin musa masa ido asirinmu ya tonu?

bansan wannanba amma abu daya nasani duk wanda ya ta6a taheer wlh saina lalata rayuwarsa kowaye bazan ‘daga masa qafaba koda uwardata haifesa ce zan iya wullawa akansa bare ke dan haka ki kiyaye.

zarar wayarta tayi ta fice zuciyarta na tafarfasa.

wani mugun kallo sarah tabita dashi tareda jan numfashi mai zafi tace,

zan nuna miki nice boss dan nikeda kudi banxa kawai.qaramin murmushi yasake tareda juyawa ya fice. 

saidata share hawayen dasuka gangaro mata tasamu tayi sallolin tana gamawa ta cusa kai tsakiyar qafafunta cikin taraddadi da damuwar irin zaman dazasuyi da taheer. 

ta dade sosai ahaka kafin yasake knocking yashigo ‘daukeda kwalin kfc na order abinci dayayo musu ya aje mata ahankali yace, 

kici abinci. 

ya miqe ya fice. 

coke din kawai tasha sai burger data gutsiri kadan ta ajiye sam batajin yunwar cin abinci. 

kwashe kayan tayi takai fridge tadawo ta kwanta sbd zazza6i datake ji ahankali. 

washe gari saida yayi mata order breakfask kafin yashirya ya fice, 

baidawo gidanba sai magrib sosai baiji dadiba sbd wani aikine ya riqesa yayita bata hakuri duk da dai kamarma ya lura tafi nutsuwa idan baya kusa, 

kwana biyu baicika zamaba shiyasa yayo mata shopping na komai na abinci duk lokacinda ta buqata taci sbd damashi rayuwarsa aikine kawai, 

kullum kafin yafita zaiyi mata knocking yace mata zai fita hakama idan yadawo sbd sam bayason takurata, 

kullum da damuwa take tashi da ita take kwana ga tausayin taheer din data faraji sbd sosai yake iya qoqarinsa na ganin ya kyautata mata bai takurataba, 

duk lokacinda tayi waya da aleeya aleeyar na qoqarin danne tashin hankalinta da danuwarta ta nuna mata komai yafara sauqi tsakaninta da dawood sbd kawai ta kwantarwada laylar hankali, 

tayi kuka tayi farin jin hakan shiyasa tafara sawa kanta dauriya tana dan fitowa palon gidan  yanxu duk da tsananin damuwarta, 

idan yadawo yanxu takan gaishesa batareda ta dago ta iya kallonsaba hakan ba qaramin dadi yakemasa ba shiyasa yanxu yake qoqarin rage ayuka yana dawowa gidan da wuri, 

sannu ahankaki lokaci yafaraja sosai suna tana iya qoqarinta na danne ciwonta da damuwarta gurin fahimtarsa da kulasa duk da harlokacin doguwar magana bata ta6a shiga tsakaninsu ba saidai yana iya qoqarinsa yaga ya kyautata mata sb yagano tana girmamasa da hakan, 

abu daya yasani yake kuma damunsa shine yagano har abada bazata ta6a daina son wanda takesoba,
sam arayuwarsa bai ta6a tunanin auren wadda wanine azuciyartaba. 

Story continues below


gashi kwana biyun nan mum nayawan kiransa kullum cikin kuka take takai har kusan kwaciyarta ciwo biyu. 

shiru yayi tareda qurawa takardar gabansa da biron hannunsa ido,
arayuwa yaso layla har cikin ransa yaso su shimfida rayuwar aure ta farin ciki da mutunta juna saidai hakan yakasa samuwa, 

babu amfani ko wani cigaba arayuwar dasukeyi tsawon shekara guda babu mai farin ciki acikinsu,
kullum dare yanajin kuka da ciwonta baya barci kamar yanda bata barci,
aikinsa da komai nasa ya tsaya sbd damuwar rayuwar dasuke,
zuciyarta naga waninsa babu ranar dazata daina sonsa dan haka babu ranarda aurensu zai samu chance shikuma har abada bazai iya takurata ba sbd yanasonta kuma zai iya rabuwa da ita taje tasamu wanda takeso sbd yana sonta. 

ya jima ahaka kafin ya tashi ahankali ya fara kwashe kayansa yana jerawa cikin akwati,
saidaya kwashe komai tsaf ya dauki laptop dinsa zai saka ajakarta yaga envelope ciki ahankali yasake ajiyar zuciya sbd damuwar halinda yake ciki tasa ya manta da envelope din, 

fiddosa yayi ahankali tareda 6an6arewa ya bude, 

zaro takardu da hotunan ciki yayi lokaci daya hotunan suka zube da hoton aleeya yafara cin karo, 

mamaki da faduwar gabane suka dirar masa lokaci daya kafin jikinsa yayi wani mugun sanyi lokacinda ya birkito sauran hotunan yaga matarsa, 

hotunan yaqurawa ido kamar ranar yafara ganinsu dukkaninsu, 

”””layla nur yar uwatace rabin jikina ina tsananin kewarta sosai””’     
kalmomin aleeya na farko aranar daya fara ganin hoton layla awayarta, 

LALYA-NUR,
nur din dawood itace matarsa layla,,, 

watsi yayi da hotunan tareda fuxgo takardun ya bude yakaranta daki daki da address da numbers dakomai sune arubuce ba banbanci sakin takardun yayi ya zame qasa ya zauna baisan me zaiyiba sai kawai ya tallafe kai hawaye masu zafi na tsinke masa sbd har cikin ransa yakeson layla yana fatar wata rana zata iya dawowa garesa idan bata samu wanda takesoba amma ganin wannan gskiyar ya dakatar da komai, 

baita6a sakaran zaiyiwa wani abu kukaba saigashi kuka yayi sosai saidai yasan farin cikin dan uwansa yadawo  dan kuwa yanxu babu mai hanasa hadasu, 

takardar daya rubuta mata yajawo yamayar da sakin saki biyu tareda qurawa takardar ido. 

wayarsa ya daga yayi musu booking ticket ya kashe. 

toilet yashiga yayo alwala yazo yayi sallar ishai kafi ya miqe ahankali ya dauki takardar ya nufi dakinta, 

ahankali yayi knocking, 

zaune take tsakiyar dakin tunda tayi sallah take zaune gurin ta kashe wutar dakin, 

tasowa tayi asanyaye ta bude qofar ahankali, 

batareda ya kalletaba ya miqa mata cikin wata irin murya maisanyi yace, 

ki hada kayanki da asuba zamu wuce insha allah. 

bayansa tabi da kallo akaro na farko tun rayuwarsu data qare masa kallo, 

sanyi jikinta yayi sosai sbd tasan bata ta6a kyautata masa amatsayinta na matarsaba,
takawo masa damuwa arayuwarsa baijiba baiganiba,
meyasa duk wanda yasota yake shiga masifar rayuwa. 

ahankali tadawo ta zauna bakin gadon dakin tafeda kunna bedside lmp ta bude takardar. 

kuka tayi na fitar hankali tana zaune har asuba tamiqe daqyar sbd jiri da ciwon kai tayo alwala tayi sallah,

tana idarwa ta hada kayanta tsaf cikin akwati ko gama rufewa batayiba yayi mata knocking.

sake damqe hakardar tayi cikin hannunta tareda jawo akwatinta ta fito tareda qurawa fuskarsa ido tanason taga idan da sauran tausayin ya mayar da ita,

dauke kansa yayi tareda kar6ar akwatin yayi waje dashi,

cikin mota yasaka yayi saurin shigewa gaba kusada mai taxi din yazauna.

ahankali ta bude bayan ta zauna tareda sunkuyar dakai idanuwanta na qara rinewa,

harsuka isa airport suka shiga jirgi babu wanda ya iya cewa qala acikinsu saima qoqarin hana ha’duwar fuskoki dasuke,

tunda suka shigo jirgi hankalinta yaqara tashi kukanma tuni ya qafe mata sai idanuwa datake rarrabawa awahalce sbd sosai take agalabaice,

ana kiran magrib suka iso gida,

mum na ganin danta ta rungumesa tareda sakin wani irin kuka ahankali shikansa baqaramin dauriya yayiba gurin hana kansa kukan sbd he is really broken,

hawayensa ya mayar tareda rungume mum din yana bubbuga bayanta ahankali batareda ya iya cewa komaiba,

tunda suka ha’da ido da juna kowacce idanuwanta sukai jajir nan take,

kukan dake son zuwar mata take qoqarin dannewa sbd mugun ganin datayi,
kallon juna suke ba qyaftawa,
sunkuyar dakai aleeya tayi hawayenta suka sauko ahankali,

daqyar laylar ta iya ‘daga qafafuwanta dasukai mata mugun nauyi ta qaraso gabanta ahankali tace,

aleeya,,,,,

rungumeta aleeyar tayi da sauri hawayenta na sake 6allewa,

kaka layla tasaki tareda qanqameta tanason magana takasa,

zama sukayi bakin gadon dakin mum takasa dauke idanuwanta daga aleeya,

wani irin baqi da wata muguwar ramace atattareda ita tako ina jiki da fuska sai idanuwanta dasuka futo sosai sbd rama,

riqo hannunta layla tayi da hannunta dake rawa yakasa tsayawa cikin muryar kuka tace,

aleeya meyasa kika 6oyemin damuwarki?
meyasa zaki danne damuwarki sbd tawa,
wlh nayi baqin cikin ganinki ayanda kike ayanxu,
aleeya mutafi gida mukoma gurin ammy….

wasu sabbin hawayene suka gangarowa aleeya ta sharce cikin wata irin sanyin murya mai amon ciwon datake daukedashi cikin zuciyarta tace,

arayuwata bayan iyayena dake babu abinda nakeso sama da dawood,
layla ada ina cewa zuciyata bataimun adalcin son wanda baya sonaba saidaga baya nagano qaddaratace,

wasu hawayen ta sharce tareda sunkuyar dakai tace,

rayuwar aurena daban takeda takowa,
kullum da soyayyar wata mijina ke tashi ya kwanta da ita,
kullum dare bana kwanciya sai lokacinda mijina yadawo yana fadar sunanta abakinsa,
kowane dare zai kwana yana ciwo yana kukan rashinta ina zaune ina tayasa kukan rashinta,

tun ina zaman jiran dawowarsa nakoma kowane dare nice nake zuwa ‘daukosa daga mashaya,

banida hutu,banida sukuni,na rasa walwala,na rasa farin ciki,

ciwo nacinsa yaqi yarda da ayi masa magani babu abinda yake fata koyaushe fiyeda mutuwa,
ya tsanane fiyeda mutuwarda tarabasada aminansa,
ya lalace,rayuwarsa ta lalace,
yakoma babu sauran abu mai kyawun gani atare dashi,
na tsani kaina da rayuwata dana zamo sanadiyar shigarmu awannan halin nidashi,

layla ina cikin mummunan quncinda nake ha’diyesa nikadai kullum tsawon shekara ‘daya….

kukane maicin rai ya sarqeta ta zame qasa tareda cusa kai tsakiyar qafafuwanta tanayi sbd ta jima tanason yazo amma ya daina zuwa sbd masifa sai yanzu,

jajir idanuwanta suka sakeyi kukan take tsananin buqata amma takasa samu,

damqe takardar hannunta tasakeyi jikinta na tsananta rawa,
shiru sukayi dukkaninsu tsawon lokaci aleeyar na kuka kafin ta dago takalli laylar taga itama duk ta zabge sai qashi ahankali ta bude baki zatai magana layla tayi saurin miqewa tana qoqarin mayarda kukanta tana sake damqe takardar sakinta ahannunta.

tasowa aleeyar tayi riqota taga yanda take jan numfashi,
zaunar da ita tayi bakin gadon tana qoqarin tambayarta saiga mum tashigo,

sunkuyar dakai layla tayi tareda gaidata asanyaye ta amsa tareda qura musu ido dukkaninsu taga yanda suke gasar rama da da qashi ta juya da sauri ta fice tana dafe qirji duk da dai danta yafi bata tausayi.

duk yanda taso fadawa aleeya maganar sakinta kasawa tayi sbd fargaba da gudun qara mata wata damuwar,

da daddare tana zaune qasa jikin gado ta dunqule shiru idanuwanta har lokacin jajir suke,

turo qofar dakin yayi ahankali yashigo da sallama sbd dama yanada tabbacin batayi bacci ba,

dagowa tayi tai masa kallo daya tareda mayarda kanta ta sunkuyar damuwarta na qaruwa,

saraah acikin daren ta fito dakinta da juice dinda tahada da gubar dazata bawa mum acikin daren sbd korar karen datayi mata bayan tagama gaya mata har abada bazata bari danta ya auretaba,

girgiza glass cup din tayi cikin qunar zuciya,
idanuwanta har wani jiri jiri take gani dasu tsabar buguwa sbd giya tasa tayi tatul sbd baqin ciki da takaicin mum,
idanuwanta arufe suke data aikata koma meyene akan mum din,
fitowa tayi ta nufi dakin mum din sbd batasan su layla sun dawoba,

cak ta tsaya qofar dakin jin abinda taheer kefada,

layla nasoki tun kafin naganki,
naso mu shimfida kyakkywar rayuwa mai dorewa,
hakan bazata ta6a samuwaba sbd akwai soyayyar ‘dan uwana aranki,

dagowa tayi da sauri ta kallesa da jajayen idanuwanta yace,

na sakeki ne tunkafin nasan da soyayyarki da danuwana sbd aurenmu baxaita6a samun chance ba,
rayuwar aurece da babu soyayya,shaquwa da qauna acikinsa,
kiyi hkr sbd koda babu so acikin auren yanada zafi saki agurin kowace mace saaidai inason kibani dama na gyara muku abubuwan dasuka lalace.

sai alokacin hawaye suka gangaro mata sunkuyar dakai sbd batajin akwai gyara a alamarinsu.

girgixa kanta tayi tareda bubbugasa da hannu tana sake bude idanuwanta dasukai jajir tana qoqarin son qara  fahimtar me taheer din yake fada, 

kasa jurewa sauran zancen nasa tayi tai wurgi da cup din hannunta cikin bugaggiyar murya tace, 

bazaka ta6a rabani da dawood ba kabawa wata,
dawood nawane nikadai,
nikadaice zan auresa,
babu wanda ya isa yarabani dashi… 

kicin tayi lalabo wuqa ta fito tana cigaba da cewa, 

dawood nawane nikadai,,, 

qara da salati mai qarfi yasake lokaci daya tareda zubewa qofar dakin tana ganin haka tayi dakinta da gudu daidai fitowar mum da gudu cikin tashin hankali kuma taga shigewarta ‘daki da gudun amma batabi kantaba tayi tsakiyar palon inda tajiyo qarar taheer, 

arikice layla ta taso tareda durqusawa gabansa tana kiran sunansa batasan sanda tasa hannu ta birkitosaba wani razannan ihu tasaki ganin wuqa da a gefen cikinsa bata tsaya komaiba ta zare wuqar daidai isowar mum gurin tareda kunnu wutar palon taganta da wuqa ahannu ga taheer din kwance cikin jini, 

wani mahaukacin ihu da qara tasaki tareda jefar da wayar hannunta ta qaraso da gudu hartana faduwa ta damqosa tana kiran sunansa da qarfi cikin tashin hankali, 

kuka layla keyi sosai nan su Nana da sauran masu aikin gidan suka fito arikice dan harsunyi nisa a bacci tuni, 

cikin tashin hankali nana takirawo aleeya tana zuwa da gudu ta tsaya turus ganin abinda ke faruwa arkice ta matso cikin tashin hankali tace, 

mum muje hospital tun kafin wani abu yasamesa. 

kuka mum keyi sosai saidai aleeyarce tafita da gudu takirawo maigadi suka shigo shima arude ya daukar musu shi yasaka amota, 

jiki na rawa takalli mum tace, 

mum muje. 

da sauri mum din ta miqe hartana hadawa da gudu suka wuce da mugun gudu dan har lokacin kamar yana numfashi,
tun ahanya takira dad tana kuka tasanar dashi masifar data samu taheer nan take ya katse kiran yace komai tsakar dare zai taso asuba ya iso sbd yana ghana. 

kasa miqewa layla tayi saida Nana ta dagata daqyar sbd rawar da jikinta keyi matuqa ga kukan tashin hankali datakeyi. 

suna isa asibiti daqyar aka kar6esa da sharadin saisun kawo police sbd police case ne, 

share hawaye mum tayi cikin wani irin zafi da 6acin rai mai tsanani tacewa aleeya tazauna ita zataje takira police, 

daga asibiti direct office na commisioner of police ta nufa nan take aka bada motar police. 

saraah kuwa tana shigewa daki jikinta yafara rawa dan tuni giyar tasaketa tsabar tashin hankali ta dora hannu akai tace, 

na shiga uku menayi,
yanxu shikenan mum taganni na kashesa nima kasheni zaayi wayyo allah na shiga uku, 

birkice kayanta tayi ahaukace tafara neman passport dinta acikin daren zata gudu bazata bari akamata ba, 

wayarta ta dauko hannuwanta na tsananin rawa ko zama wayar batayi dakyau ahannunta ta danna kiran siyama tana tsiyayo hawaye, 

siyama na dauka ta fashe da kuka tace, 

siyama ina cikin matsala wlh kasheni zaayi bansan ya zanyiba,
bansan meyasa nakasa riqe kainaba na kashesa,
siyama kitaimakeni na kashe taheer…. 

tashi zaune siyama tayi daga kwancen datake tareda saukowa daga gado tace, 

me kike cewa? 

wlh siyama bana cikin nutsuwata ba kashesa nayi niyaba,,,fada mata komai tayi cikin tsananin kukan tsoro saijintayi siyama ta kashe mata waya. 

Story continues below


sake kira tayi siyama taqi dauka sai kawai ta zube wasa tareda fasa sabon kuka tareda harhada sauran kayanta ta zuba jaka ta fito da sauri cikin tashin hankali sai kawai taji jiniyar motar police cikin harabar gidan, 

daki takoma da gudu tana sakin fitsari cikin wandonta wani irin gumi yafara jiqota tako ina, 

suna shigowa palon cikin zafin muryan mum ta nuna layla dake zaune palo cikin rashin sukuni tayi kuka har baya fita tace, 

arazane layla da nana suka dago takalli mum da jajayen idanuwanta dasuka qanqance sbd kuka cikin rawar murya tace, 

bansan wayayi ba ahaka nasamesa wlh bazan ta6a cutatar da taheer ba mum. 

hawaye mum din ta sharce tana kallon inspecter tace, 

itace sbd kowa yaganta agabansa da wuqa ahannunta,,,, 

mum wlh bani bace,banyi masa komaiba mum ina qoqarin cire masa ne….. 

matsowa yayi da ankwarsa tareda daka mata tsawa yana cewa asa mata ankwa sutafi da ita idan taci azaba tayi bayani dakyau. 

sarah dake la6e tayi saurin barin qofar takoma tsakiyar dakin tana jin dadin samun hanyar tserewa duk da dai harlokacin hankalinta amatuqar tashe yake tasake danna kiran siyama, 

siyama na kashe wayar tarasa ina zatasa kanta sbd tashin hankali da baqin cikin saraah,
tabbas ta ta6ota a inda ba’a ta6awa,
wlh saita kasheta itama matuwar taheer dinta ya mutu kuma wlh saita hanata samun abinda takeso aduniyarnan komenene, 

shigowar wani kiran yasa ta dauka amatuqar fasace kafin tayi magana saraah tarigata da cewa, 

siyama nasamu mum tacewa police layla ce dan haka dasun tafi zan fito kiyi sauri ki kiramun su seeya kice sujirani a airport komai dare ko asubanci zan sauka a airport na lagos yanxu zan fito…. 

katse kiran siyama tayi hawaye na tsiyayo mata tace, 

wlh kinyi bankwana da kwanciyar hankali tunda kika rabani da taheer har abada bazaki ta6a samun dawood ba wannan alqawarina saina lalata rayuwarki saraah yanda ko kare bazai kallekiba. 

wayarta ta ‘daga kai tsaye ta nemo number dawood ta danna masa kira, 

kira take bai dauka takasa dainawa jikinta har rawa yakeyi zuciyarta kamar zata fado ga hawaye sun kasa tsaya mata babu abinda takeson gani kamar taheer dinta, 

sake kira tayi cikin maye ya ‘dauka ahasale yace, 

you fool bakusan inkun kira baa daukaba ku saurara idiots…kashewa zaiyi tayi saurin cewa, 

NUR CE. 

kwalbar hannunsa ya saki ta watse tareda miqewa tsaye nan take yaji giyar tasakesa cikin wata irin sanyayar murya yace, 

NUR? 

daidaita muryarta tayi cikin dakewa tace, 

Nur ‘dinka na gidanku ayanxu haka police zasu tafi da ita kaje karka bari sutafi da ita daga baya zankira namaka bayani kayi sauri kaje… 

bai tsaya tunanin komaiba ya ture wanda ke gabansa yabar gurin da gudu isanuwansa har wani cikowa da hawaye suke dan tsabar farin cikin dabaita6a sanin akwaishiba. 

wani irin mugun gudu yake yana tsiyayo wasu irin hawayen farin ciki zuciyarsa har wani bugawa takeyi da qarfi kamar zata faso qirginsa. 

da wani irin mugun gudu da horn yashigo kwanar layin gidan daida lokacinta police biyu suka fito da ita daga gidan nana na biyedasu tana kuka kamar ranta zai fita, 

kasa gasgata idanuwansa yayi sai kawai yayi cikinsu aguje da motar yayiwa motarsu wani mugun bugu nan take tafara hayaqi da gudu ya fito ya damqota ya cilla cikin motarsa yayi ribas yabar layin da mugun gudu babban inspectern da mum aguje suka fito cikin tashin hankalin jin qarar bindiga suka tararda tuni motar dawood din tabar layin,

da gudu suka shiga motarsu suka rufa masa baya.

sabon tashin hankali da baqin cikine tasowa mum tadawo cikin gida daidai leqowar sarah tana hada gumi,

kallonta mum tayi dakyau nan take wani zargi yafado mata gabanta yayi mummunan faduwa ta hadiye wani mugun miyau ta nufota tareda bude qofar dakin taga akwatinta da passport tayi saurin kallonta murya na rawa tace,

saraah kece kika kashesa…..

kuka tasake da sauri ta matso tana cewa,

wlh bansan lokacinda na…..

wani mahaukacin mari mum tasakar mata saidata kife ta nunata da yatsa saita kasa magana ta fashe da wani sabon kuka mai qarfi tana cewa,

wane irin balai da masifa ne wannan na jawowa kaina.

kuka tayi sosai harsaida muryarta ta dashe ta miqe daqyar ta fice batareda ta iya cewa qalaba takoma asibiti kukanta na kasa tsayawa.

kodata koma asibiti sabon kuka tasaki aleeya datayi kuka harta fice hayyacinta ita tafara rarrashinta amma sam takasa sbd babban tsoronta na biyu bayan na halunda taheer ke ciki shine makomarta idan CJ yaji itace mafari idan aka gano saraah ce taso kashe taheer.

gudu yakeyi sosai kamar zai tashi babu ruwansa da tudu ko ina fadawa yakeyi gashi police basu bar binsuba gashi sunyi waya anturo musu wasu motocin cike da police sosai suka bude masa wuta amma taqi tsayawa harsunyi nisa da gari sosai sai kawai ya yanka daji cikin rashin sa’a motar ta qwace masa tayita gudu saidata kai gurin wani qaton ice ta dakesa tafara hayaqi,

daqyar ya dago kansa daya bugu harda jini ya fito motar ya bude baya ya cicci6ota sbd tun aqofar gidan ta some batareda taga wanda ya daukotaba,

cicci6arta yayi yakutsa dajin da ita yacigaba da gudu yayi nisa kadan motar takama da wuta sosai daidai isowar police suka tararda takama da wuta nansuka buga suka sanarda wainda ke ciki sun mutu suka juya.

gudu yayi sosai cikin tsakiyar dajin har asuba ga gajiya ga qafafuwansa dasuka fara farfashewa sbd tafita cikin manyan qayoyi,
yana kaiwa gurin wani qaton kogi jiri ya dibesa agurin suka zube asume dagashi har ita.


dad qarfe bakwai na safe ya dira a asibitin mum na ganinsa hankalinta yaqara tashi,

cikin saa dr yafito lokacin yakallesu tareda miqawa dad hannu yace,

mu gode allah he is out of danger wuqar bata samesa a cikiba a gefe tasamesa kuma bata shiga irin sosai dinnanba munyi masa aiki mun ‘dinki gurin kowane lokaci zai iya farkawa saidai kuma gskia zai dade sosai bai fara miqewa tsayeba sbd akwai jijiyar data ta6u kadan.

ajiyar zuciya suka sauke cikin farin ciki da hamdala nan dad ya juyo ya kalli mum yasake tambayarta yanda abin yafaru,

kallon gefen aleeya tayi ta hadiye wasu yawu daqyar murya na rawa tace,

matarsace ta sokesa nima bansan daliliba yanxu haka ta gudu police sunbita….

isowar police gurin yasayin shiru tana kallon inspectan.

kalllonta yayi cikin jimami yace,

haj saidaifa haquri yarinyar motarsu ta qone qurmus muna tsaye ta cinye babu wanda yafita acikin…….

ganin sukayi aleeya ta yanke jiki ta fadi agurin bata motsi,

juyawar dazatayi sai ganin ammy da bilal tayi kowannensu ya daskare ga dukkan alama ma suma suman ne sukayi atsaye jin abinda inspectr yafada daga isowarsu.

hankali tashe akayi emergency da aleeya ammy ma nan take hawan jininta yatashi akai gaggawar kwantarda ita sbd kartayi kwalapsin,
bilal kuwa tsayawa yayi cak gaban gadon ammy idanuwansa jajir jijiyoyin kansa har wani motsi sukeyi tsabar tashin hankali sam kwaqwalwarsa takasa daukar cewa ‘yar uwarsa ta tafi tabarsa.

sulalewa mum tayi takoma gida afusace ta banka qofar dakin sarah tareda fusgota ta jehota waje tareda watso mata kayanta tace,

duk wata masifa data afkomin nida yayana kece,
nayi baqin ciki da dana sanin kawoki gidana,
kin tarwatsa rayuwar yayana,
na hana yarona farin ciki ina kallo rayuwarsa ta ta6ar6are sbd ke,
yanxu kinzo kinyi qoqarin kashemin taheer inaji ina gani na maqalawa wata sbd kar laifin yashafeni gashi ta rasa ranta ta rasu ta sanadinki amma bazan iya fadaba sbd dole nima saina fuskanci sharia dan haka tun kafin kowa yasani kitashi kibarmin gidana bana buqatar sake ganinki inason gyara abubuwan dana lalata da kaina.

muqewa sarah tayi tana kallon bayan mum din ido a waje,
juyawa mum tayi tayi ido biyu da dad tsaye idanuwansada fuskarsa qunshe da tsananin 6acin rai,

mummunan faduwa gabanta yayi wani mugun zufa ya karyo mata tadaga qafa zata matso ya daga mata hannu da ido jajir,

sarah na ganin haka ta sulale takwashi kayanta tabar gidan.

cikin wata irin murya mai tsananin sanyi yace,

faraah kanki kika cuta,
dasaka hannunki cikin lalacewar danki,
dasaka hannunki cikin mutuwar yar mutane,
bazan miki komaiba sbd haryanxu duniya bataimiki darasin daya kamata saidai nizan dauke ‘dana mutafiyarmu bazaki sake ganinmuba insha allah dawood ma zan dawo na daukesa sbd yanxu matarsa na buqatarsa na rashin yar uwarta datayi.

matsowa tayi da gudu ta zube gabansa tareda riqo qafafuwansa tasaki wani irin kuka mai qarfi ya zame qafafuwansa ya wuce ya tattaro duk wasu takardu da abubuwan buqatarsa dana taheer yafice tabisa har jikin mita tana kukan tashin hankali amma ko kallonta baiyiba yawuce da gudu yabar gidan.

yana isa asibiti cikin qanqanin lokaci yasaki kudi sosai nan take suka samu flight aka saka taheer suka tafiyarsu bataredama taheer din ya farfadoba.

About Ismail

Check Also

DAWUUD CHAPTER 7

DAWUUD CHAPTER 7 Washe gari sai guraren qarfe goma ya tashi Idanuwansa kawai ya bude …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *